Baki d'aya ta rasa sukunin ta, har Skul d'in ma ta daina
zuwa sai fama take da ciwo duk tabi ta rame, tun abun baya damun Mom har ya
fara damunta, ta samu Dad da maganar, har sabbatun da tajita tanayi sai data
fad'a mashi, tare suka nufi tinkarar ta a d'akinta tana kwance.
"Yauwa Mom
'kwara da kika shigo, Mom gashi nan kullun yana zo mun a mafarki, wallahi Mom
ina 'kaunarshi, bazan iya airen kowa ba sai shi, Dad ka taimaka ka nemo mun shi
duk inda yake, indai da gaske kuna sona tou dole ku nemo mun shi saboda shine
farin cikin rayuwata".
Cikin tausayi
Dad yace "Safna me kike fad'a ne wai? Waye shi a ina yake?",
"Dad ban
sanshi ba ban san inda yake ba, dan Allah ku nemo mun shi",
"Ki
kwantar da hankalinki Safna, kiyi min bayanin komai cikin natsuwa mana",
Share hawaye
tayi tace "Dad so d'aya kawai na ganshi a bakin wani layi, tunda na ganshi
naji na kamu da sonshi, kullun idan na dawo Skul sai nabi ta hanyar amma bana
ganinshi, shine kullun yake zo mun a mafarki, yana nufo inda nake, da zarar ya
na nufo shi sai ya 'bace, Dad kullun haka nake".
Sosai suka
tausaya ma 'yar tasu, Mom ta matsa Inda take tace "kiyi ha'kuri kinji auta
ta? Yau saura kwana biyar 'yar uwarki ta dawo, ki kwantar da hankalinki insha
Allahu idan ta dawo za'a san yanda za'ayi".
Cikin shagwa'ba
tace "tou Dad zaku nemo mun shi idan ta dawo?",
"Insha
Allahu kuwa" ya bata ansa tare da goge guntun hawayen daua rage a
fuskarta.
Bayan
kwana uku.
Shirye shiryen taryar Baby kawai sukeyi, hankalin Safna ya
d'am kwanta saboda al'kawarin da Dad yayi mata. Sukam ma'aikatan gidan mu rna
kawai sukeyi saboda sunji dad'in dawowar da Baby zatayi, dama kuma tunda Safna
ta kamu da son Dream guy ta raga masu, sam babu ruwanta da kowa, hakan ba
'karamin dad'I yayi masu ba.
Nawwaf da Hamza
ne suka shirya suka nufi gidan Malan Shazali kamar yanda sukayi al'kawari.
Sallamah sukayi ya fito dama ya shirya su kawai yake jira. Tafiya sukayi suka
hau keke Napep har UMYU ta sauke su.
Office d'inshi
suka direct amma suka samu baya nan, har sun jiya zasu tafi wani Labourer yace
"kaine Nawwaf Sani?",
"Ehh
nine" Nawwaf ya bashi ansa.
Labourer'n
yace "tou yalla'bai yace wai ince maku ku same shi a gida, wai kuyi amfani
da wannan katin zaku gane address d'in" ya mi'ka mashi wani d'an card
'karami.
Kar'ba sukayi
suka samu wata napep d'in, kallo d'aya yayi wa card d'in yace "ai nama san
gidan wannan, koba shi bane wannan mai kud'in? Wanda da yake aiki a Inland
revenue daga baya ya samu d'aukaka?",
Nawwaf yace
"indai ka gane shi tou shine, bana son yawan magana".
A daidai 'kofar gidan mai napep d'in yayi parking. Alhaji
Shazali da kanshi ya biya kud'in sannan suka nufi 'kofar shiga gidan.
Direct suka
shiga kasantuwar babu gate man tun tafiyar baba tsoho. Wani mai bama flowers
ruwa suka gani Nawwaf yace "Dan Allah malan muna da tambaya",
"Allah yasa
na sani" ya fad'a yana 'ko'karin matsowa inda suke.
"Nan ne
gidan Alhaji Sani kuwa? Mun so tambaya tun a waje sai bamuga kowa ba har bakin
'kofar",
"Ehh ai
nan ne, Alhaji mai son mutane kenan, mara wula'kanci, sai dai kuma baya nan
wallahi yanzu suka fita su duka gidan wai zasu taro babbar 'yar shi data dawo
daga 'kasar waje",
Yana cikin
maganar sai ga Mati driver yace "ko kune wanda yace zakuzo? NAWWAF
ko?",
Saurin d'aga
kai Nawwaf yayi yace "ehh mune",
Mati yace
"tou yace in kaiku d'akin ba'ki idan kunzo wai bazasu dad'e ba".
Bayan shi
sukabi har cikin wani katafaren d'aki mai d'auke da kayan jin dad'I da more
rayuwa.
Umurni yayi
masu da su zauna kan wasu luntsumammun kujeru, zama sukayi suna ta f aman kalle
kalle.
Bayan Mati ya bar d'akin ne Hamza yace "ohh! Masu kud'I
suna jin dad'in su, kuga fa yanda d'akin nan yake dan'kare da abubuwan duniya,
ga sanyi ta ko ina yana ratsa fata, 'kanshi kuwa sai ratsa hanci na yake,
wannan fa itace aljannar duniya".
Nawwaf yace
"kai fa Hamza matsalata da kai magana gareka wallahi, yanzu miye amfanin
hakan? Idan fa maeu gidan suka shigo ko kana so su raina mu ne? Dan nifa bana
son raini kuma kafi kowa sani",
Malan Shazali
yace "ayi ha'kuri dai".
Wata budurwa
ce tayi sallamah hannun ta d'auke da serving tray tana turawa, har 'kasa ta
du'ka ta gaishe su cikin ladabi sannan tace "ga wannan kuci kafin masu
gidan su dawo".
Godiya suka
mata sannan ta tafi ta barsu. Food flasks d'in da aka zuba abincin kanshi abun
kallo ne, cikin fasaha Nawwaf ya bud'e ya fara zuba yellow rice, d'ayan ya
bud'e yaga vegetable soup da taji hanta da 'koda, zuzzuba masu yayi sannan yace
wa maoan Shazali "ga naka", ya mi'kawa Hamza ma nashi sannan suka
fara kwasar girki suna santi.
Bayan sun gama
tass ya zuba masu exotic drink a glass cups ya basu, shi kuma ruwan faro ya
zuba saboda baya son za'ki sosai.
Murna sosai tayi lokacin data hango 'yar uwarta tna sauka
daga jirgi. Da sauri tayi hugging d'in ta daidai isowarta wurin su. Cikin
tausayi tace "Safna me ya same ki kika koma haka? Kinga yanda kikayi rama
kuwa?",
Kamar tana
jiranta ta fashe da kuka ta rungume ta. Rarrashinta ta fara yi amma sam ta'ki
yin shiru. Da 'kyar ta tsagaita da kukan suka nufi inda Dad da Mum suke.
Sunji dad'in
yanda suka ga 'yar su ta 'kara kyau abunta, dama kuma gata jar fata. Shiga
motar sukayi suka kama hanyar gida.
Dad da
kanshi ya sauka ya bud'e gate sannan ya dawo motar yace "wallahi ina
haushin rashin gate man d'in nan, gashi kuma mutanen yanzu wuyar yarda gare su,
tunda Safna ta korar mana da gate man shiknan. Na yarda da mutumin nan sosai
ban ta'ba zama da wanda naji lokaci d'aya ya kwanta min ba kamar shi, kawai sai
dai na dawo na tarar babu shi, dama kuma ban san garin su ba a masallaci kawai
muka had'u dashi".
Baby tace
"Dad wai ashe har yanzu Safna bata daina wannan halin ba? Ai ni nasha ta
girma ta daina",
Dad yace
"ina kuwa zata daina? Ai banga ranar ba".
Safna ta
fashe da kuka tace "Dad ai fa tunda Aunty Baby ta dawo nasan bazaka sake
sona ba, indai tana gida haka muke da kai". Kuka sosai t akeyi cikin
si'kewar murya.
Mum tace
"gaskiya ku 'kyale mun 'yata ta huta, bana son ana mata haka fa".
Da wannan
maganar suka 'karasa cikin gidan fuskar Sagma duk hawaye ya bushe mata.
Duka ma'aikatan gidan suka fara du'kawa har 'kasa suna
gaishe da Baby, saboda sunfi sonta Miy da kowa dake gidan. Fuskarta d'auke da
murmushi take ansa gaisuwar. Mati driver yace "yalla'bai bakin ka fa sunzo
tun d'azu kai suke jira",
Dad yace
"ok ka shiga kace masu ina zuwa".
Abinciccika
kala kala suka tayar kan dinning Zarah ta jera. Sallah kawai sukayi sannan suka
fara kwasar girkin Zarah. Dady yace "gaskiya ina alfahari da yarinyar nan
Zarah indai wurin girki ne, duk irin ba'kin da zanyi bana haufin ta".
Mum tayi saurin
'bata fuska tace "tou ashe shi yasa nake barinka da ita tana dafa maka,
tun da kai baka son girki na kullun sai dai na Zarah".
Caraf Safna ta
kar'ba tace "kema dai Mum tun yaushe nake ce maki ki bari in kori yarinyar
amma kin 'ki bari, indai baki barni na koreta ba har hawan jini sai ta saka
miki".
Baby tace
"haba Safna! Wai ke yaushe zakiyi hankali ki daina wula'kanta mutane?
Safna kiji tsoron Allah! Duk wanda zaki gani a duniya tou yana da tashi
darajar, kuma mutun da kike gani ba abun wula'kantawa bane, idan kuma baki
daina ba tou wallahi dole akwai ranar dana sani".
Mum tace
"Allah ya rabata da dana sani, insha Allahu bazata ta'ba yin dana sani ba
a rayiwarta.
Murmushi Dad yayi
yace "duk laifi na ne dana tado maganar ai, yanzu dai ba wannan ba, ina da
ba'ki suna can suna jirana".
Mum tace "su waye?",
"Wannan mai
saida ruwan dana baki labari mana, Nawwaf",
"Au! Wanda
kace ya taimake ka ko?",
"Ehh shi
fa, nayi masu al'kawarin zamu had'u a office ne yau, so kuma sai ga batun
dawowar Rabi'atu, shine na bada sa'ko idan sunje ace su same ni a gida".
Mum tace
"ok".
Tashi Dad yayi yace
"idan na shiga sai kuzo ku gashe su kuma". Bai tsaya jin amasar su ba
ya tafi.
Sallamah yayi
suka amsa yace "afwan fa ma barku",
"Babu
komai" Nawwaf ya fad'a. Sai a lokacin Dad ya kula da malan Shazali, wata
irin fad'uwar gaba yaji, kawai ya samu kanshi da son mutumin da bai ta'ba gani
ba sai yau.
Bayan sun gaisa
su Mum suka shigo, itace gaba sai Baby da Safna bayanta. Wurin zama suka samu
Baby ta gaishe su cikin girmamawa. Safna kuwa ko kallon arzi'ki baeu ishe taba.
Sun d'auki kimanin minti biyar zuwa shida ta mi'ke tace "Mun na tafi sai
kun shigo" fuskarta yatsine kamar mai tsohon ciki.
Har ta tafi kuma
ta waigo, had'a idon da zatayi kawai taga dream man d'inta. Idonta ta murza
sosai sannan cikin tsoro tace "bawan Allah kayi ha'kuri ka tafi, kullun
gizon da kake mun kenan, ka hanani duk wani jin dad'in rayuwa ta" ta juya
ta kalli Dad tace "Dad kayi min al'kawarin duk inda yake zaka gano min shi
amma ka'ki, Dad wallahi bazan iya rayuwa ba tare dashi ba".
Duka wurin kowa kallon ta yake yanda ta koma oamar
mahaukaciya lokaci d'aya. Musamman ma Nawwaf da yaga tana nuni dashi alamar duk
maganganun da take fad'I dashi take.
Mum tace
"wai Safna meke damun ki ne? Waye dream man d'in naki?",
"Mum gashi
nan a zaune, wallahi mum shine kullun yake zo min a mafarki, son shi ya zame
min ciwo wanda bazan iya maganin shiba matu'kar ban aure shi ba" ta fad'a
cikin kuka da 'karfi.
"Safna
wannan shine kike mafarkin?" Mum ta fad'a.
"Ehh
shine Mum, shikenan nasan ciwo na ya warke tun da gani gashi, ai zaka aure ni
ko?" Safna ta fad'a tare da matsawa inda Nawwaf yake tana murmushi.
Kyakkyawan mari
Mum ta wanka mata, cikin fushi tace "Safna kina da hankali kuwa? Yanzu ke
wannan matsiyacin kike so? 'Kas' kantacce mai tallar ruwa a baro? Baro fa yake
turawa da jarkoki manya a ciki, Safna ki kalle ki ki kalle shi, ai wallahi The
different is clear, tou tun wuri ma gwamma ki fidda son shi a ranki, saboda
kinfi 'karfin wahalalle".
Cikin tsawa Dad
yace "ya isa haka, Hajiya bafa na son wula'kanci, dan me zaki ringa cima
bawan Allah fuska a gaban shi?",
"Ai kuwa
cin fuska yanzu na fara matu'kar bai bar gidan nan ba, rufin asirin shi d'aya
ne kawai ya tafi kar ya sake dawo wa, wama yasan ko asirce min 'ya yayi? Idan
ba haka ba mai zai sa yarinya ta haukace lokaci d'aya akan shi alhali bata san
shi ba?"
Nawwaf yayi sairin katse ta da "ke Hajiya ki kama
kanki, wallahi kawai ina d'aga miki ne saboda ina ganin kimar mijin ki, amma
daba haka ba wallahi ba'ayi wanda zai yi min wannan furucin in 'kyale shi ba,
kuma da kike maganar ni wahalalle mai tallar ruwa a baro ai nan halaliyata
nake, ni banga wahala anan ba, ki tambayi mijin ki kiji ai har sai da na'ki
yarda da yace zai sama min aiki shi ya matsa lallai sai nazo, ki kama kanki
wallahi nafi 'karfin ki, Hamza ku tashi mu tafi".
Baby tayi
saurin tashi cikin kuka tace "dan Allah kayi ha'kuri bawan Allah, ni kaina
banji dad'in yanda take gaya maka magana ba, amma banda magani ne yasa nayi
shiru, and zan ro'ke ka wata alfarma ka taimaka kayi min ita",
Nawwaf yace
"mecece alfarmar?",
Magana tayi
mashi da koni maribuciyar banji me tace ba, kawai dai naga ya koma ya zauna
yana ajiyar zuciya.
Safna tayi d'an
guntun murmushi tace "zaka aure ni ko?",
'Kara murtuke
fuska yayi bai bata ansa ba.
Dad yace
"ya isa haka dan Allah, yanzu dai abunda nake so dakai Nawwaf ka saurare
ni kaji me zan fad'a maka",
Da 'karfi Mum
taja Safna a dole sai sun bar d'akin amma sam Safna ta'ki binta, dole ta tafi
ta barta anan.
Dad yayi gyaran murya yace "Nawwaf da farko dai ina mai
baka ha'kuri da cin fuskarka da Hajiya tayi, nasan nine naja maka da nace maka
ku same ni a gida, inda a office muka had'u da duk haka bata faru ba, sannan
kuma ina so ka d'auka abunda tayi maka can tsakanin ku ne bata shafe ni ba, ka
d'auka komai bata faru ba kuma zan baka aiki kamar tanda nayi al'kawari",
Murmushin 'karfin
hali yayi yace "babu komai yalla'bai komai ya wuce".
'Kara matsawa
Safna tayi inda yake tace "tou zaka aure ni?",
Da sauri Dad ya
daka mata tsawa yace "ku tashi ku tafi ku bamu wuri".
Baby taja ta
suka nufi 'kofar fita, juyowa safna tayi tace "dan Allah Dad kace kar ya
tafi ya barni, wallahi ina cikin tsananin damuwa, nasan dan ya tafi bazai sake
dawo wa ba saboda kar Mum ta 'kara yi mashi wani wula'kancin".
Sosai safna ta
bama Dad tausayi, gyad'a kai yayi cikin ranshi yace "insha Allahu zanyi
bakin 'ko'karin samo maki soyayyar Nawwaf" a zahiri kuma yace "tou
naji jeki".
Haka ta fita
tana waigen Nawwaf har suka bar arean d'akin.
Dad ya juyo yace "barin d'auko maku upper'n",
"Tou"
kawai Nawwaf yace yaci gaba da bin Dad da kallo.
Da fitar shi
malan Shazali yace "Nawwaf a ringa ha'kuri dan Allah, kasan Allah yana
tare da mai ha'kuri, kuma indai kana shiga mutane dole ka rage wannan ZAFIN ran
naka",
Hamza yace
"gaskiya ne kam, nima dai abunda na gani kenan, dan wallahi furucin da
yayi wa matar nan shi yayi amma ni naji kunya, dan ji nayi kamar in fita in bar
d'akin".
Nawwaf dai baice
komai ba sai kallo. Suna cikin haka sai ga Dad ya dawo hannun shi d'auke da
takardu.
Zama yayi ya
mi'kawa Nawwaf wata takarda guda d'aya, Nawwaf ya kar'ba ya duba sosai yaga
Upper ce.
Dad yace
"Nawwaf ka samu junior lecturer kasantuwar karatunka bayyi nisa ba, amma a
ko wane lokaci zaka iya 'karo karatu don ka samu 'karin girma",
Ya kuma mi'kawa
Hamza wata yace "kaima ga wannan, zaka ringa share share da goge goge,
kuma insha Allahu zaka ringa samun albashi mai 'kwarie".
Godiya sosai
suka yi mashi, ya fad'a masu cewa su fara zuwa aiki daga ranar Monday. Haka
suka bar gidan cikin jin dad'I da farin ciki, malan Shazali ma ba 'karamun
farin ciki yayi ba.
A ranar Nawwaf
ya shirya ya kama hanyar Bagaruwa dan ya shaida wa mahaifan shi.
Da shigar shi gida ya samu Abbah da Ummah zaune suna hira,
yayi sallamah ya zauna inda suke. Ba 'karamin farin ciki sukayi ba da suka
ganshi, Abbah yace "Nawwaf lafiya dai kazo yanzu ko?",
"Lafiya
lau Abbah, nazo na baku albishir ne",
Ummah tayi
murmushi tace "wane irin albishir Nawwaf?",
"Yau dai
na samu aiki, na zama malamin jami'ah".
Sosai sukayi
murna da jin haka. Abbah yace "aikuwa tare zamu tafi zanyiwa mutumin
godiya, eaboda a wannan lokacin ba lallai bane a samu mutane irin shi",
Ummah tace
"lallai kam, nima dai sai inbi ku ayi dani",
Nawwaf yace
"ehh sai mu bari sai zuwa gobe mu tafi".
Haka suka
shirya washe gari suka kama hanyar Katsina, sai da suka biya ta gidan Malan Shazali
dan dama haka yace dashi. Sun samu baya nan, Nawwaf ya bar sa'ko yace
"idan ya dawo a fad'a mashi sunzo tare da babanshi, kuma zasu wuce gidan
Alhaji Sani sai ya same su acan",
Sun isa gidan
daidai sallar azahar, sun samu Alhaji Sani ja shirin tafiya masallaci, yayi
farin ciki sosai daya gansu, ya dai ga Nawwaf tare da wani tsoho da wata
dattijuwar mata, yayi masu umurni da su shiga d'akin ba'ki. Ya koma cikin gida
yasa Zarah ta kawo masu abinci.
Suna cikin cin
abinci ne malan shazali yazo, daidai shigar shi ne Alhaji Sani shima ya shigo,
kawai gaban Safna ya fad'I, jikinta ya bata Nawwaf yana cikin gidan. Da gudi ta
nufo d'akin ba'ki, ganin tana gudu ne yasa a rud'e Mum da baby suka biyo
bayanta.
Tir 'kashi! Kome wannan had'uwar zata zama? Sai kuci gaba da
kasnacewa dani don jin 'karshen labarin.
Da hanzari baban Nawwaf ya mi'ke tsaye cikin sar'kewar murya
ya fara 'kokarin magana amma sam ya kasa, komawa yayi ya zauna ya ri'ke kai
yama rasa abunda zayyi, ganin haka ne yasa maman Nawwaf cewa "malan me ya
faru ne?",
Bai bata amsa ba
naji muryar Safna cikin kuka tace "Nawwaf ka taimaka ka rufa mun asiri ka
aure ni, wallahi I cant live without youh, kai ne jinin jiki na, wallahi tunda
nake ban ta'ba jin son wani namiji bayanka ba",
Sai a lokacin ta
kula da baba tsoho,
Cikin mamaki ta
zaro ido tace "baba mai gadi!"
Shi kuwa Abbah
tunda ya du'kar da kanshi babu abunda yake sai tariyo wasu abubuwa da suka faru
a baya, so d'aya kawai ya d'ago kai ya 'kara kallon malan shazali da shima shi
yake kallo, 'kara sunkuyar da kanshi yayi wasu zafafan hawaye na binshi.
A gaban baba Tsoho ta koma ta risinah tace "ban san da
wane irin baki Zan maka magana ba, nasan naci mutuncin ka naci zarafin ka, na
maka abunda duk wacce ta aikata shi tou bata cancanci a yafe mata ba, na kira
ka da munanan kalamai, kuma tunda na maka haka ban 'kara samun natsuwa ba, tun
tafiyar ka nake faman dakon son wanda bai san dani ba, bai san da halitta ta a
doron 'kasa ba, na shiga tsantsar tashin hankali mara misaltuwa a dalilin
sonshi, sai gashi kuma ashe d'anka ne na cikinka, yau gani a gabanka ina ro'kon
alfarma a gareka akan ka taimaka kasa Nawwaf yaso ni, ka sani Baba tabbas Allah
ya kar'bi addu'arka, a gabana ka d'aga hannu kace "Allah ya kawo ranar da
nima zan ro'ki wata alfarma a gareka",
Na kiraka da
tsohon najadu, yau gani a gabanka na risinah ina mai baka ha'kuri, nayi nadamar
munanan halaye na, nayi nadamar hud'ubar da Mum ke bani, nayi nadamar d'aukar
kaina da nayi wata high class, nayi nadamar jiji da kai da girman kaina, sai
gashi yau basu amfanar min da komai ba sai dana sani, da na sani kuma wanda
bashi da wani amfani"
Sosai Safna ke
kuka ta ri'ke 'kafar wandon Baba tsoho da ko saurarenta baya yi.
Kowa idon sa akan Safna da Baba tsoho, sun dad'e a haka
kafin Baba tsoho yace:" Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah
mad'aukakin sarki! Abunda na dad'e ina fata yau ya tabbata",
Kowa ya maida
kunnuwan shi ga baba tsoho dake bayani kafin yaci gaba da: "kunga wancan
da kuke gani" ya nuna malan Shazali,
"Ehh"suka fad'a su duka.
Yace "d'ana
ne Marwan",
Bai gama maganar
ba naji sallamar Dr. Nasir da matan shi.
Sai a lokacin
Baba tsoho ya 'kara rikicewa, Dr. Nasir da sauri yaxo ya rungumi baba tsoho
yana kuka.
Sun d'auki
tsawon lokaci a haka kafin Dr. Nasir yace " Sani! Yau dai abunda muka
dad'e muna ro'kon Allah ya tabbata, dama ance addu'ah bata fad'uwa 'kasa banza,
yau dai gaka ga mahaifinka wanda ya haifeka",
Ido bud'e
Alhaji Sani yace "what? Dad! Kana nufin baba mai gadi ne mahaifina?",
"Tabbas
kuwa, ashe ma ka sanshi" dr. Nasir ya fad'a,
"Ehh Dad,
dan ma dai baka zuwa gidan nan ne ai da ka sanshi, ya dad'e yana aiki a gida na
tun kafin mu dawo sabon nan",
Dr. Nasir yace
"tou shine mahaifinka, wannan wani dogon labari ne wanda bazai yiwu yanzu
ba",
Baba tsoho
yayi sujada yace "Nawwaf yau kam Allah ya had'a ka da 'yan uwanka da na
dad'e ina baka labarin rabuwata dasu, wancan shine na sani dan yana da shekara
takwas muka rabu, shi kuma Sani ban ma sanshi ba, saboda a wurin haihuwar shi
ne maman shi ta rasu".
Dr. Nasir ya sunkuya gaban malan Shazali yace "Marwan
ina ka shiga tun shekarun baya? Munyi nemanka har mun gaji amma bamu same ka
ba",
Malan Shazali
ya goge hawaye yace "nima dai abunda zan iya tunawa kad'an ne bada yawa
ba, na dai san Mum ta aike ni da kud'I suka 'bata, ni kuma sai nayi tunanin
zata duke ni idan na koma babu su shine nayita tafiya ba tare da nasan inda
zanje ba, a hanya na had'u da wani mutumi ina ta kuka shi ya taimaka ya tafi
dani gidan shi, ya saka min suna shazali ne saboda yaron shi mai irin sunan ya
rasu, tun daga nan sunan ya bini, a hannun shi na koyi sana'o'in hannu har
Allah yayi mashi cikawa lokacin ni kuma ina da 'karfin neman na kaina, nayi
aure yanzu yaka ina da yara hud'u, dama tun ranar da Nawwaf ya fara zuwa wuri
na nake jin shi a jikina, sai gashi kuwa ashe d'an uwana ne na jini uban mu
d'aya dashi".
AlhajI Sani yace
"nima abunda naji knan a jiki na lokacin da Nawwaf ya taimake ni, ashe
'kani na n...",
Bai gama maganar
ba Safna ta mi'ke tsaye tace "kar ku raina min hankali mana, kuna nufin
Nawwaf 'kanin babana ne kome? Kenan babu aure a tsakanin mu? Aikuwa bazan ta'ba
iya rayuwar aure da wani ba",
Tsawar da Dad ya
daka mata ne yasa tayi shiru tana ajiyar zuciya had'e da kuka.
Baba tsoho yaita bata baki har tayi shiru, sun dad'e suna
mayar da labari akan abubuwan daya faru ga kowa, baba tsoho ma ya bada labarin
tun tafiyar shi prison har sako shi da akayi kasantuwar an gane ba laifin shi
bane.
Safna tayi
nadama sosai dan kuwa har yanzu ji take ina ma ace mafarki ne take, ina ma ace
zata auri Nawwaf, sai dai kuma kash! Hakan bazata ta'ba yi wuwa ba.
Wannan labarin
ishara ce ga duka kan masu hali irin na Safna, domin kuwa a kwaisu da dama
wanda basa ganin kimar babban mutun. Allah ya shiryi masu irin wannan halin
amin.
Bayan
wata uku.
Shirye shiryen biki ake sosai a familyn, duba nakai domin
ganewa Ido na wanda akewa biki, can na hango Zarah mai aikin su Safna taci ado
cikin alkyabba fara, daga gefenta kuma Nawwaf ne yanata fara'ah.
A d'ayan gefen
kuma Baby ce na hango itama cikin wata jar alkyabba tasha ado, hannunta ri'ke
da wani kyakkyawan matashi dogo fari mai tsarin halitta sai fara'ah suke.
'Kara murza ido
na nayi naga Safna daga gaban su ri'ke da selfie stick tana masu selfie. Ita
kam Safna anyi cim'bu babu mijin aure, domin kuwa ko wane namiji tsoron
tinkarar ta yake.
A filin da ake
kamu ne na hango members na Amrah and Rerbee'art novels suna ta rububin pop
corn, kusa dasu kuma na hangi Nafee and Amrah Novellas suma suna ta 'ko'karin
su samu souvenirs, members d'in Zarah bb na gani har da dambe suke wai basu
samu ba, Extreme Hausa writers kuwa bakin 'karfin su suke don ganin sun shiga
filin rawa, sai dai kuma basu samu wuri ba saboda wisdom Hausa writers sun cika
wurin.
Excellent
writers kuwa Nafee Ankah ce na gani ta wakilce su tana ta shoki. Mufarka mata
kuwa su suka gyara amare domin indai wurin gyaran amare ne tou ba daga baya ba,
su kuwa na Amrah's kitchen girke girke suka koyawa amaren biyu.
Bayan Shekara
uku.
Dad ne na hanga cikin masallaci bayan an gama sallah ya
bayar da hoton Safna yace inda wanda yake sonta ya aura, kowa tsoronta yake
saboda duk ansan halinta na wula'kanci, ganin basu da niyyar tanka mashi yasa
yace "na bama liman sadakar 'yata safna indai yana sonta, na d'auke mashi
komai nata tun daga gida, lefe, kayan d'aki da komai, zai kuma biya sadaki mafi
'karanci wanda shima nine zan bayar, idan liman ya amince gobe za'a d'aura aure
insha Allah.
Take kuwa liman
ya fara fara'ah, yaji ance za'ayi mashi komai. "Na amince ko yanzu ma a
d'aura" ya fad'a cikin jin dad'I,
Dad yace "a
bari goben dai tukuna".
Batayi wa Dad
musu ba saboda itama mijin take nema, Mum ma taji dad'in hakan. Washe gari aka
d'aura auren Safna da limamin masallacin 'kofar gidan su.
TAMMAT BI
HAMDULILLAH
Anan ne zan d'igawa labarin aya, labari ne wanda banyi zaton
zayyi tsayin haka ba, sai gashi har ya d'auki wannan lokacin, ina fatan masu
karatun sunji dad'in shi kuma sun fad'akartu a cikin shi. Kurakuren dake ciki
Allah ya yafe min, inda nayi daidai kuma Allah ya 'karo baseerah mai amfani.
Kunfi kowa a gareni
Iyayena abin alfahari na, ina 'kaunarku kuma ina yaba maku.
Sadaukarwa
Na sadaukar da wannan littafin ga 'yar uwata kuma 'kawata
RABIATU SK MASHI, naki ne Zafin so, kina da damar wallafa shi.
Bazan manta daku ba 'kawaye na; Zarah BB, Ummeeter Gidado,
sadiya Afka, Kirratul-Ayn, Munayshat, rash Kardam, maman khairat, maman
Abideen, mum hairullah, kdeey, nafee anka, ummu abrar, maman usman, kausar luv,
mimi B, mrs. Umar, hajar, stylish, teemah luff, zee hrt, meesha lurv, autar
hajiya, maryam mukhtar, Nuccee luv, Nana Diso, Futha, Zahra, khadeejah candy,
Aunty M. Jabo and Xeenur.
Bazan manta daku
ba Abdul jega, Muhammad abba gana, Raheem jega and Mr. Smiles.
Naso ace duk
sunayen ku su fito amma babu hali, duk wadda ban ambaci sunanta ba tayi ha'kuri
tana raina kawai dai babu fili ne saboda mai karatu zai iya gajiya dani.
Tabbas hausawa sunce MAHAKURCHI mawadaci ne, domin kuwa BABU
MARAYA sai raggo, ku duba irin YAUDARA data faru tsakanin FADEELAH DA NABEELAH,
da kuma RAMUWAR GAYYA da YARIMA SAIFULLAH yayi, wannan wane irin SO DA SHAKUWA
ne tsakanin Rabiatu da Imran? Tabbas DAUKAKA DAGA ALLAH take, akwai TSANTSAR
ZALINCHI a cikin labarin RADIYAH, sai dai kuma DR. RAFIQ ya magance masu komai,
oh! INA ZANGA KDEEY abar alfahari na?, mujiya ce ME BAQIN JINI inji hausawa,
soyayyar da KHAULAT tayiwa Tahir ba ta wasa bace har iyayen su na fad'in
"wannan wane Irin ZAFIN SO ne suke wa junan su? Ni kuma nace ku rakani
wurin HAYDAR DA HAYBAR don ganin wace Irin rayiwa suke ciki.
Alhamdulillah!
Littattafan Marubuciyar kenan, HAYDAR DA HAYBAR na naj zuwa bayan sallah insha
Allah, karku bari a baku labari.
Inawa kowa fatan shiga wata mai albarka lafiya, Allah ya
sada mu da duk alkhairan sake cikin shi.
Amrah ke gaishe da
duk wani masoyinta na nesa dana kusa.
Luv youh all