AMINAN KWARAI Page 31-40
.
Washe gari tun shida Nasrin ta tashi tayi wanka tayi breakfast ta shirya tana jiran NY, Zinat sai taji wani irin Nasrin tana tsaye daga bakin cikin sai k'arewa d'akin kallo take yi.
Zinat ce tace"Nasrin lafiya kuwa?"
Murmushi Nasrin tayi tace"Wallahi Zinat ji nake kamar bazan kuma dawowa d'akinnan da zama ba"
"Uhmmmmmm Nasrin kenan wato zaki tafi ki barni Allah yasa rashin dawowanki alkhairi ne"cewar Zinat
A sanyaye Nasrin tace"Amin Zinat nagode sosai"
Tana gama fa'din haka kuwa taji karar text ya shigo wayarta, tana dubawa taga NY ne"Baby ki fito ina waje"
Murmushi tayi tace"NY da sabon salon tsokana wai nice baby"
Tace "Zinat tayani fidda kaya NY yazo?
Zinat tare da wasu course mates d'inta su suka kai mata kaf kayanta NY ya bu'de boot yasa yashiga ya zauna yana jiranta.
Saida ta da'da yin sallama da mates d'inta tukun tafito Zinat har bakin mota ta rakota"Nasrin tace pls Zinat ki kula da kanki ki ri'ke min al'kawari kada a koma gidan jiya, Allah sada mu da Alkhairi"
Hawaye ne ki bin 'kuncin Zinat cikin Zuciyarta wani sabon son Nasrin ne ke wanzuwa, A sanyace tace"Amin,Insha Allah Nasrin ba abun da zai kuma faruwa, Nagode Allah ya kiyaye hanya agaida su mum"
Tana fa'din haka ta juya ta bar wurin domin kuka yaci k'arfinta
Nasrin ma saida tayi k'wallah tace"Zasuji insha Allah, nagode"
Ta bu'de mota ta shiga yayinda ta fara gaishe da NY,kallonta kawai yake yi domin wani kyau yaga tayi mishi,sai da ta natso daf dashi ta hura mishi iska a ido tukun ya daidaita nutsuwarsa sannan tace"hey me kake kallo ko ka hango wata ce in fita inyi mata magana?"
Murmushi yayi a zuciyar shi kuwa cewa yayi ke nake kallo, a fili kuwa cewa yayi"Uhnmn nassy bby wallahi wani tunani nake dabam, kin kwana lafiya"
Tace"lafiya lau, kaifa?"
Yace"same"
Murmushi yayi sukayi addu'a tukun yayi bismillah ya kunna mota sai jos.
Suna tafe kowa da abinda da yake sa'kawa a ransa, NY ko satar kallonta yake jifa-jifa shi kanshi tambayar kanshi yake me yake damunsa sai dai amsa d'aya zuciyarsa take bashi sonta kake, murmushi yayi yace"Am in love"
Baisan maganar zuci ta fito fili ba sai ji kawai yayi Nasrin tace" with who??"cikin tashin hankali wanda ya bayyana k'arara a fuskar ta.
Juyowa yayi ya kalleta yaga yanayinta ya sauya sai duk ta bashi tausayi sai yacr"Am in love with my phone,haba ay inda da wata kece zaki fara sani"
Ya'ke tayi wanda yafi kuka ciwo tace"Uhmmm Allah yasa"
Yace"yawwa Nasrin yaushe ne aurenki ni kuwa?
"Uhmmmmm ka tambayi Abba" ta bashi amsa a ta'akaice
Yace"To yanzu ya za kiji in akace amininki ya zama angonki?"
Dariya tayi mai isar ta sannan tace"Tab'di angona mai sa oversize shoe ga rigunansa maji gaba, lallai banni yarda"
Dariya suka yi dukkansu tukun NY yace"Wollah karya kike yarinya,lokacin da nazo walimarki nasan bakiso na tafi ba kinga gaye d'an k'wallisa"
Tabe baki tayi tace "Sannu magori"
Yace"Eh anji d'in"
Haka dai suka dinga tsokanar juna,can dai NY yace "wai da gaske in tambayi Abba maganar aurenki?"
A hankali tace "Allah kuwa"
Yace"Uhmmm,ai ni nasan angon,sai dai baison hira sosai saikin koya mishi bayan aure kanari, Don haka dani za kina hiran yana gefe yana jinmu"
Tace"kut, wai da gaske kake?"
Yace" sosaima"
Ta ta'be baki tace"Shikenan"
Tun daga tayi shiru tanata tunani, yanzu shikenan mafarkinta na son mallakar NY ya ruguje, Allah yasa hakanne mafi alkhairi.
Ta d'auko sandwich d'in da tayi musu ta'dan ci ka'dan tukun tace NY ya tsaya ta koma baya tayi barci kanta na ciwo.
Ba musu yayi parking ta fita ta koma baya ya ja suka Cigaba da tafiya.
Ita ko data kwanta tunani ne ya addabi zuciyarta ta ro'ki Allah yasa barci ya d'auketa nan bada jimawa ba, cikin ikon Allah ko barci mai nauyi ya d'auke ta.
NY ko ya lura da yanayin data shiga tunda yace mata yasan angonta, sai duk yaji ba da'di amma hasashen da yake yi kanta gaskiya ne ma'ana tana da matu'kar sonsa.
Murmushi yayi yace "Nasrin Insha Allah zan ninka miki son da kika yimin duk da dai bansan iya lokacin da kika d'auka kina DAKON SO na ba Allah sarki nassy baby Ina mai matu'kar jinjina miki saboda DAKON SO masifa ne, nagani kan wani abokina.
Bi'iznillah Nasrin naki yazo karshe"
Shi ka'dai yake tu'ki yake magana abinsa, Abin kawai daya ke tunani shine lallai so halitta ne.
Yana ta tu'ki abinsa gashi mai taya shi hira nata barci abinta kuma bayyi tunanin tashinta ba.
Sha biyu saura dai-dai yayi horn a 'kofar gidansu Nasrin, Maigadi ya taso da gudunsa ya bu'de mishi gate ya shiga ya parking.
Nabil ya fara fitowa ya nufo motar yana ganin NY mamaki ya baibaye fuskar sa yace"Yaya Nasir barka da zuwa,gashi adda Nasrin bata nan"
Murmushi NY yayi yace tana baya bu'de ka tasheta, yana le'kawa kuwa ya ganta ay cikin hanzari ya bu'de ya fara Adda Nasrin!Adda Nasrin!! Ta bude ido a hankali taga Nabil ta kulle ta kuma bu'dewa hakan ya tabbatar mata da cewan ba mafarki bane ay kuwa tashi tayi ta rungumesa tana murna, NY bin ta kawai yayi da ido komai nata yanxu burgesa yake.
Ya fito su Nabil da Najwa suka shigar da kaya tukun suka jera shi da ita har cikin fallon su, Ai kuwa da gudu ta fa'da jikin mum tanata farincikin ganinsu.
NY ne ya fara gaisheta tukun ta saki Nasrin ta amsa fuska fal fara'a.
Hayaniyar suce ya tada Nawas ala dole ya nufo fallon yaga me ke faruwa, Ai yana ganin lil sis rai yaga rai da gudunsa ya taho itama haka ta taho suka rungume juna.
Hakan yayi dai-dai da tasowar wani kishi a zuciyar NY(mr kishi bro dinta ne inji jidda) ko zaka bugesa ne???
Masu karatu ayi hakuri dani na rashin typing wlh skul ne,Mrs Abdul
.
Princess ta gani cikin shiga ta alfarma, murmushi ta sakar ma ta yayinda itama princess ta mayar ma ta zuwa tayi ta rungume ta sannan ta ja ta suka zauna tace"Princess sannu da zuwa,yasu Abba da hajiya ke dawa kuka zo?"
Murmushi princess tayi tace"lafiya lau amaryar mu, kowa na gaishe ki, tare da ango muke ga kayan fitar biki nan" ta nuna ma ta wasu manyan akwati guda biyu, murmushi Nasrin tayi tace nagode sosai.
Nan suka haye sama suka je suka dinga hira ango kuma yana tare da Naufal kasancewar Nawas baya nan.
Sai biyu dai-dai NY ya kira princess a waya yace tazo zasu wuce,suka gangaro da Nasrin har k'ofar parlour amma Nasrin ta'ki fita princess tayi-tayi taje su gaisa da angonta amma k'ememe Nasrin ta'ki zuwa tace ma ta kunyarsa take ji kuma in banda abinsa ai an kusa kaita garesa koh,da dai princess taga ba ta da niyyar zuwa sai ta k'yale ta suka yi sallama tayi musu fatan isa gida lafiya.
Shi ko NY yana mota yana hangen duk abun da suke yi, da yaga princess ta taho ita ka'dai sai tausayin Nasrin ya kamashi yasan ba don komai ta'ki zuwa ba sai ganin wanda zata aura zai da'da ma ta tashin hankali, a hankali yace"nassy baby kin kusa dawwama cikin farin ciki hak'uri da addu'a zai miki rana"
Yana gama fa'din haka princess ta iso ta bu'de mota ta shiga ta zauna ya maido da kallonsa gareta yace"ta'ki zuwa koh?"
Princess tace"eh kunyar ka take ji amma tace in gaisheka Allah kiyaye hanya"
Murmushi yayi yace"Amin, nagode"
Yasan ta Fa'di hakanne kawai bawai tana nufinsa ba, sukai sallama da Naufal yaja mota sai Kaduna.
Nasrin ko da ta koma d'akinta ta nufa yayinda yan'uwansu suka bu'de akwatu nan kowa na tofa albarkacin bakin ta.
Key tasa ta kulle ta fa'da gado sai taji wayarta na ringing ganin NY ne me kiran yasa ta goge hawayenta ta picking tayi sallama, can b'angaren taji NY yace"ai munyi fa'da tunda kika'ki zuwa gaishe da ango"
Murnushi tayi tace"kunyar sa nake ji shiyasa, kace yayi ha'kuri"
Yace"bakomai da dai kinje kin ganshi da kinji da'di" tace"uhmmmmm kwana nawa ne zamu kasance tare"
Yace"hakane barin concentrate ina driving we talk ltr koh"
Tace"ok safe journey bye"
Da haka ta katse wayar ta ajiyeta gefe ta fara aikin kuka.
NY yana tu'ki yana ta tunanin Nasrin domin yaji damuwa tsantsa cikin muryarta ji yake kamar ya sanar da ita shine wanda zata aura ko ta samu sukuni, amma ina yayi al'kawari sai an kai ta gidansa zata ga shine mijinta amma zuciyarsa ta fara rauni baya tunanin zai iya cigaba ganinta cikin damuwa.
Koda mum ta tambayi Nasrin ko tana son yin wani program ne a bikin? ce ma ta tayi kawai ayi saukar Al'quran ayi addu'a a ci a sha kowa ya watse, mum tayi matu'kar jin da'din mganar nan ta sanya mata albarka ta fita ta barta sai dai ta fuskanci Nasrin d'in kamar tana cikin damuwa ga rama da ta yi, sai tayi tunanin ko barin gida da zata yi ne ya sanya haka.
Ana gobe sa lalle Zinat ta diro jos bayan an gama sauka anyi addu'a sosai kowa yaci yasha aka rarraba jakan kuna masu d'auke da sunan ango da amarya, amma da yake ance hankali shine mai gani ba ido ba Nasrin bata kai idonta ga duban abubuwan da aka raba ba, asalima tashi tayi tashiga ciki abinta.
Ganin zinat kuwa ba k'aramin sanya Nasrin jinda'di yayi ba ta kuma samun y'an hira dama tun ranar laraba cousins d'inta suka zo tare da k'awarta Aisha da Nazira a cewar su har Kaduna zasu raka amarya.Ko da zuwan su ma ita bawani saka baki a hirarsu takeyi ba banda waya da NY domin a wannan lokaci shine ka'dai ke kwantar ma ta da hankali duk da dai ba ta fa'damishi tana cikin damuwa ba shine ya fuskanci hakan amma yasan komai yazo k'arshe da yardar Allah.
Ranar sa lalle ranar ne gidan matar naufal za suyi kamu a permanent side saboda haka yan'uwan maman Nasrin da na Abba suka shirya domin zuwa wurin kamun Nawwarah.
Sauran yan'uwa kuma suka d'auki hanyar zuwa kaduna don yiwa amarya Nasrin jere.
B'angaren gidansu NY kuwa ba masaka tsinke gida ya cika ma'kil domin Abba zaiyi bikin d'ansa na fari, Abba mutum ne mai kirki wa danginsa masu shi da marasa shi da abokan arziki, hajiya ma ba'a barta baya ba domin mace ce me mutunci da ganin girman manya, uban biki kuwa Nasir halinshi kaf unguwa da dangi ro'kon Allah suke ya baiwa ya'yansu irin halayyar sa shiyasa dangi uwa da uba suka zo bikin NY.
Ango kuwa baki har kunne zaiyi auren biyayya da kuma so da k'auna domin shi mutum ne mai son mace me sonsa tsakani da Allah sai gashi Allah ya bashi Nasrin baiwar Allah me kwana da tashi da sonsa shiyasa ya d'au al'kawarin faranta mata har iya tsawon rayuwarsu.
Masu zuwa jere kuwa sai biyu da rabi suka isa Kaduna, a gidansu NY suka ya da zango suka yi sallah suka ci abinci tukun aka yi musu jagora zuwa gidan amarya dake unguwar malali inda suka jere ma ta kayanta, gaskiya iyayen Nasrin sun zuba ma ta dukiya koni ummu arif da na ga d'akuna nan musamman ma kitchen wollah na zaci a turai nake abin dai sai sam barka ko su yan'uwan NY sun jinjinawa iyayen Nasrin domin sun b'ar da naira.
Can jos kuwa anata bidiri wurin kamu amaryar Naufal Nawwarah tasha kyau har ta gaji tayi ado cikin wani tsaddadan net ba'ki mai adon golden ta sa gwaggwaro da jaka, sar'ka da d'ankunne gold, tayi kyau sosai.
Sai da aka kusa kammmalawa ango Naufal yazo da Abokansa inda yayi shigarsa ta alfarma cikin farar shadda gezna da agogon rolex ga takalmi na gucci da hula ba'ka mai suna minister yayi kyau sosai shima, ya d'an taka rawa da amaryar sa inda yan'uwa da abokan arziki suka yi ta musu li'ki tukun shida abokansa su ma suka yi b'arin naira suka k'ara gaba.
An gama kamu kowa ya koma gida yana sanya alkhairi, yan'uwan Naufal suna ta murna domin anyi musu kar'ban mutunci a wurin ka mun iyayen nawwarah sunyi bajinta sosai.
Masu zuwa sa lalle daga Kaduna zuwa jos sai k'arfe bakwai suka iso, su kuwa wa'yanda suka je jere sunce sai an kawo amarya tukun zasu koma nan aka basu masauki.Amarya tasha k'unshi da kitso tayi kyau sosai kawaye ma ba'a barsu baya ba su zinat k'irjin biki ansha kyau, Nasrin dai in tana tare da su tana k'ok'rin danne damuwarta sosai don kada su fahimta.
Nasrin ce kwance a d'aki taji anata ranga'da guda an dawo daga sawa matar yaya Naufal lalle tasan tabbas saura ita ji tayi wasu zazzafan hawaye na gangaro ma ta k'arar wayar ta ne ya katse ma ta tunanin da take yi ta kai hannu ta d'auka don gannin me kiran ta, murmushi tayi domin......
.
Murmushi NY yayi ma ta tukun yace"Nasrin an bada sadakin ki, zuwan da muka yi dama akan maganar auren ne cikin saa kuwa ashe Abban Nasim yasan Abbana shine abu yazo da sau'ki ba bu'katar dogon bincike kawai yayan Abbana ya mi'ka sadaki an sanya bikin wata d'aya da kwana Ashirin daga yanxu wato dai-dai da na Naufal kenan, Nasrin ina miki fatan alkhairi Allah ya kai ran mu.
Nasrin nasan akwai wanda zuciyarki ta da'de tana so amma kiyi ha'kuri ki amshi duk wanda kika gani matsayin mijin ki, ki sani cewa wani hanin ga Allah baiwa ne san nan sanin kanki ne Abba bazai za'ba miki wanda bai da tarbiya ba don haka nake ba ki ha'kuri Allah ya bar zumunci mungode".
Nasrin tunda NY ya fara magana jikinta yayi sanyi hawaye ya yi ta zuba a idonta ka sa cewa komai tayi NY ne ya ciro handkerchief da ga aljihunsa ya matso gab da ita ya cire hannayen ta da ga fuskarta ya fara goge ma ta hawayen. Dukkansu sai da suka ji wani yarr a jikin su domin in ba yau ba ko mayafin ta NY bai ta'ba ri'kewa ba, ahankali ta kar'bi handkerchief d'in da ga hannunsa ta ci ga ba da goge fus'karta bayan tace mishi ta gode a ta'kaice.
Mamaki ne ya yi ma ta yawa shin da ma NY yasan akwai wanda take so?, ko dai ma yasan shi take so?
Ji take kamar ta tambaye shi da ma yasan tana dakon son wani ne? sai wata zuciyar tace ma ta kada ki soma kawai ki'dau shawarar da ya ba ki tunda haka rayuwa ta zo miki sai ki kar'beta ki gode Allah, tayi zurfi cikin tunani da zancen zuci hura ma ta iska da aka yi ne a fuska ya maido dubanta ga NY.
Murmushi ta yi mishi tukun tace"Nagode sosai Nasir Allah ya k'ara zumunci ya saka muku da mafificin alkhairi" ta k'areshe maganar tana zubda hawaye NY sai duk yaji ba da'di kamar yace ma ta shine angon sai kuma ya fa sa ya sauya hirar tasu ta koma tsokana har sai da ya ga Nasrin ta ware tana ta dariya tukun yaji da'di cikin ransa.
Da haka suka tashi suka nufi fallon da su Abba su ke, sukai sallama yayin da su Abba sukai ta yiwa iyayen Nasrin godiya.Har bakin mota su ka rako su suka yi musu fatan isa lafiya, NY ya ja mota suka d'au hanyar Kaduna bayan ya tabbatarwa da Nasrin su na isa zai kira ta.
Tana shiga ciki d'akinta ta nufa ta kulle 'kofa ta hau gado tasha kuka daga baya barci yayi gaba da ita.
Sai bayan la'asar ta tashi kasancewar mum da nawas sun san halin da ta ke ciki shiyasa ba wanda ya tashe ta, sallah tayi tukun ta sauko k'asa ta samu su mum suna hira sannu kawai ta musu ta nufi kitchen ta zubo abinci taje kan dining tana cin abinta tana sauraron wa'azin shiek muhammad kabir gombe a wayarta.
Nawas ne da yaji shirun na ta yayi yawa yace"lil sis yau y'ar hiran ma babu ne?"
D'ago kai ta yi ta kalleshi tayi murmushi tace"bro nemana kake da magana, dana sauko bance sannunku ba"
Yace" ai sannunku ba magana bane, kawai kizo nan muyi hira amaryar kwanan nan"
Ya k'areshe maganar da zolaya, tasowa tayi takai plate d'in kitchen tazo ta zauna tace ma nawas"to gani koh"
Murmushi Nawas yayi mata wanda ke k'ara fiddo mishi da kyawunsa yace"ai labari zaki bamu me da'di" mum da ke gefe ta fuskanci akwai abin dake damun Nasrin amma tasan koma meye yana da nasaba da kawo sadakin ta, murmushi tayi tace "Nasrin lafiya na ganki haka?" Itama Nasrin murmushin tayi tace "lafiya lau mum"
Duk da dai mum bata yarda da amsar da ta ba ta ba tashi tayi ta nufi d'aki tace Allah ya sawaqe.
Nawas ne ya matso kusa da Nasrin yace "yawwa lil sis ban wayarki inga al'kawarina"
Murmushi tayi ta mi'ka mishi da ma al'kawari tayi mishi zata nuna mishi k'annen NY da room mate d'inta Zinat.
Yana kar'ba kuwa ya shiga gallery ya fara kallon pics d'in ba tantama k'annensa ne domin kama da suke sai dai akwai wata cikinsu wacce taja hankalin Nawas.
Shi tunda yake bai ta'ba yiwa mace kallo sama da biyu ba amma sai gashi sai kallon wannan y'ar budurwa yake yayinda yake ta murmushi, nasrin ta fuskanci kamar akwai abinda ya d'auke hankalinsa cikin wayarta ta zaga bayan sa a hankali ta ga ya k'urawa hoton Anisa ido.
K'anwar NY ce wacce ba ta wuce shekara sha takwas ba yarinyar akwaita da kyau na d'aukar hankali duk da dai ba fara ba ce ga ta ba ta da surutu sosai she's very calm kusan duk gidan ta fisu kyau shi yasa suke ce mata PRINCESS.
Nasrin kuwa yau abun tsokana ya samu tayi caraf tace"wai-wai-wai rana bata k'arya,kai yau wacce rana yaya nawas na yiwa wata d'iya mace kallon k'urilla gaskiya princess ta d'aga tuta, murmushi yayi yace"Nasrin lower your voice please zagayo muyi magana"
Sai dai tayi dariya sosai tukun ta zagayo.
Nawas yace lil sis wallahi inajin wani abu game da yarinyar nan duk da ban sani ba so ne idan kika yi la'akari da kallonta dana dinga wanda a tahirin rayuwata ban ta'ba ba, murmushi Nasrin tayi tace"wannan shine love at first sight"
Yace"kedai bari, yanzu meye abinyi?
Nasrin tace "bro kabar komai a hannuna zan yiwa NY magana anjima sannan daga baya sai inyi mata"
Cike da zumu'di yace"pls do that for me sis, nagode"
Nan dai suka Cigaba da hirar su Nasrin nata mamakin Nawas lallai so halitta ne.
Sai bayan sallar isha'i NY ya kira Nasrin yace mata sun isa tuntuni kasancewar bata son d'anuwansa shine kota kira su koh,yayi dai ta k'orafi,ita dai hakuri take ta bashi domin tayi ta kira ya'ki shiga amma ya tsaya ya saurare uzurinta sam ya'ki k'arshe ma katse wayar tayi.
Nasrin bin wayar tayi da ido kasancewar hakan bai ta'ba faruwa tsakaninta dashi ba ai kuwa sai kuka kamar wacce aka buga, tayi ta kiranshi amma ya'ki picking daga k'arshe ta yanke shawarar kiran...
.
Nasrin Murna Nawas Murna.Sakinta yayi yayinda ya fuskanci wani kallo da ba'kon Nasrin yake yi mishi.Nasrin ce fuskar nan kamar gonar auduga tace"My Nawas meet NY, NY meet My Nawas"
Cike da mamaki Nawas yake kallon NY domin lokacin daya rungumi Nasrin yaga kishi tsantsa a idon NY amma sai ya basar yaje gareshi ya mi'ka masa hannu sukayi musabaha nan fa suka fara gaishe-gaishe.
Nawas ne yace"Nasir muje ciki ka watsa ruwa koh kayi sallah sai akawo ma abinci, ba musu NY yabi Nawas ciki.
Bayan yayi wanka yayi sallah Nawas ya gabatar mishi da Abinci.Yana ci suna hira nan NY ya bashi labarin yadda Nasrin ta taimaki mahaifinsa cikin rashin sanin waye shi har jininta aka k'ara mishi, nawas baiyi mamakin taimakon data yiwa Abban NY ba domin yasan sis d'inshi zata yi fiye da haka, mamakin da yayi kawai shine yadda bata gane shiba.
Suka Cigaba da hira yayinda Nawas yakejin da'din abinda sis d'insa tayi cikin ransa.
NY ya Cigaba da labarta mishi yadda suka yi da Abban sa na son ya aure Nasrin kuma shima ya amsawa mahaifinsa.
Sai dai b'angaren Nasrin bata san wanda Abba na ya bata ba domin ce mata yayi cikin ya'yansa zai ha'data aure da wani.
NY ya tashi ya d'an matsa kusa da Nawas ya numfasa tukun yace"Nawas Nasrin ta amsawa Abba ne badon taso ba sai don tana ganin girmansa,kuma tanajin wani b'oyayyen al'amari game dashi sannan kuma tana sonsa bisa ga son daya nuna mata lokaci guda, wato Allah Al-hakim ne son da Nasrin take yimin shine ya shafi mahaifana da yan'uwa, tunda takai Abbana asibiti har aka sallame shi kullum sai taje duba shi, kwa'dayin halayenta ne Abba yayi sha'awar ha'data aure dani domin baida masaniya cewa nasan Nasrin da da'dewa, in ta'kaice maka zance dai Insha Allah nine ANGON NASRIN sai dai ina so kar tasan nine wanda abba ya za'ba mata, gaskiya halayyar Nasrin sunyi".
Nawas wanda tunda NY ya fara magana k'wallah ke bin k'uncinsa murmushi yayi na jin da'di bayan ya yiwa Allah godiya yace
"Nasir wato na yarda Maha'kurci Mawadaci lallai Allah maji ro'kon bawa ne, nasir baku da'de da fara k'awance da Nasrin ba kyawawan halayyarka suka dasa mata sonka a zuciyarta.Allah sarki sis tasha dokon sonka na lokaci mai tsayi domin har yanxu tana kai, Saboda sonka ta kasa barci,ta yini d'aki ta kwana kuka, ta kori ko wanne saurayi daya zo mata, addu'arta kullum Allah ya mallaka mata NY matsayin Abokin rayuwar ta, duk 'yan gidan nan kowa yasan halin data ke ciki na sonka.Amma yau kaine a gabana kake sanarmin cewa burin lil sis ya kusa cika Alhamdulillah".
Matsawa yayi ya rungumi NY cikin jinda'di yayinda yake tayi masa godiya, murmushi NY yayi yaji duk tausayin Nasrin ya kamasa lallai haka abin yake, yace"Nawas nine da godiya bisa ga taimakon da Nasrin ta yiwa Abbana Allah tabbatar mana da Alkhairi, zan kwana anan gobe saina wuce pls kabari saina tafi ka sanar da mum kada na fara jin kunyarta".
Nawas kwashewa yayi da dariya yace"Ai yanxu kuwa zan sanar mata"
Dariya suka yi duka suka Cigaba da hirarsu cikin jinda'di da nisha'di.
***********
Nasrin ko ana can anyi d'ai-d'ai a gado wai ita nan ta gaji.
Sai hu'du saura ta tashi don kanta domin mum cewa tayi kada a tasheta.
Da sauri ta nufi toilet tayi wanka ta d'aura alwala ta fito tayi sallah tukun ta shafa cream ta zira doguwan riga ta sauko k'asa.
Parlour shiru ba kowa, kitchen ta nufa domin ta jiyo hayaniya amma me zata gani........Nawas ne da NY sanye da apron suna ta faman girki mum na zauna tana basu order Nasrin tsabar dariya saida takai k'asa lokaci d'aya suka juyo suna kallonta cike da mamaki ko meye ya sata dariya oho.
Sai da tayi dariya ma'ishiya tukun tace"Yau zamuci kwa'do yanzu mum don Allah sune suke girki, don Allah dubesu kowannen su ya gwafe sai aiki yake kamar da gaske harda sanya apron"
k'ara kwashewa da dariya tayi, mum ta kalleta tace"In anyi kar kici uwar tsokana"
Nawas kuwa wanda ya fara k'ula cewa yayi
"lil sis dama muna hakane, kece sabon ganina ina girki tambaye su nabil su baki labari sanda bakinan wake girki"
"Uhmmmmm"abinda tace kenan, sannan tace"Ba girin-girin ba"
NY kuwa tun shigowar Nasrin kitchen d'in yake jin wani sanyi na ratsashi koda ta fara magana baiso ta daina ba, murmushi yayi yace"kardai mugama yarinya tazo k'ari ehe"
Itama murmushin tayi tace na gaida"Chef NY da Nawas"
Daga haka tabar kitchen d'in ta nufi d'akin nabil.
Ta taddasu yana koyawa Najwa Assignment nan ta zauna tace itama ayi da ita.
Chef NY da Nawas sun kammala girkinsu sun jereshi a dining table, jollof macaroni ne sai farfesun kayan ciki sai lemun Tufa da Abarba da suka yi Abincin yayi kyau a ido Allah sa dai a baki ma hakan take.
Suka nufi D'akin Nawas don yin wanka da gabatar sa sallah.
Nasrin na mamakin NY sam bashi da ba'kunta,murmushi tayi tace"Nima fa haka nake cikin yan'uwansa.
Sai bayan sallar isha'i kowa ya hallara dining, bayan su Nasrin sunyi waya da Abba da yaya Naufal, abba ya tabbatar musu cewa Insha Allah suna nan tafe ranar litinin.
Nawas ne yace kowa ya serving kansa haka kuwa akayi saidai NY ne ya serving mum taji da'di matu'ka. Nasrin tace"Nasir bari na serving d'inka"
Murmushi yayi yace "Nagode"
Ta serving d'inshi ta serving kanta Sukai Bismillah gaba d'ayan su, suka fara bawa ciki hakkinsa.
Kasan cewar Al'adarsu in suna cin abinci basu magana hakan yasa Nasrin yi musu alamu da hannu irin abincin yayi da'di fa, murmushi dukkan su suka yi mata suka maida hankali ga cin abincinsu.
Bayan angama cin abinci ne Nasrin da Najwa suka gyara dining d'in.
Dawowar su keda wuya hira ta b'arke yayinda Nasrin ta jinjina musu wajen iya girki, tayi mamaki sosai ya akayi suka iya girki haka wannan abincin ko ita tayi iyaka kenan.Mum dai da taga hirarsu bata da k'arshe jan Najwa tayi suka yi d'aki bayan su Nasrin sun mata sai da safe.
NY ne ya kira Abba suka gaisa ya bawa Nasrin ma suka gaisa yayi mata ban gajiya harda Nawas ma sun gaisa tukun daga bisani sukayi sallama.
Nabil ne ya tashi yace"Brothers, adda Nasrin mukwana lahiya"ya nufi d'akinsa parlour ya rage saura Nawas, NY da Nasrin.
Suka Cigaba da hirar su cikin jin'dadi musamman ma Nasrin wacce bata gajiya da kallo da jin muryar NY, b'angarensa ma hakan take.
Nawas ne cikin zuciyarsa yace ya kamata fa...............
.
Nawas ne cikin zuciyarsa yace"ya kamata fa in d'an basu wuri su d'an zanta domin gobe Nasir zai wuce"
A fili kuwa cewa yayi"Guys barin shiga in fito koh"suka amsa da"ok"ya tashi ya shiga ciki.
Shigar sa keda wuya Nasir ya k'urawa Nasrin ido, ita dai murmushi kawai take mishi abinma harya soma bata mamaki.Can dai da taga bai da niyyar daina kallon sai tace cikin sanyin murya"NY wannan irin kallo haka, ko zaka rasu ne ko kuma ni?"
Murmushi yayi yace"Matsoraciya babu ko d'aya, kawai dai kinga gobe zan tafi so ina kallonki ne don in fa'dawa bro d'ina yadda na baro ki beside nima zan missing d'inki"
Murmushi tayi wanda ya narka zuciyar NY tace"Am gonna miss u more, ni ko bro d'inka na sona kuwa?"
Yace"uhmmmm me yasa kika fa'di haka"
Tace"Najishi shiru ba call ba text ba komai, but I trust Abba ba zai za'bamin mara sona ba" ta kareshe maganar tana murmushi, shima murmushin yayi yace"Ai bro d'ina sai ha'kuri yace ina mishi hiran so karki damu anytime you're welcome sannan zanna yawan kiranki inji mishi lafiyarki, yana sonki he is just busy ne kinji nassy baby"
Tace"uhmmmmm shikenan Allah sa hakanne mafi alkhairi"
Yace"Amin"
Tace"gaskiya kaje ka kwanta domin dare nayi kuma gobe zaka yi tafiya fa"
Yace"To madam yadda kikace haka za'ayi"
Murmushi tayi shima ya mayar mata, Daga haka suka yi sallama ta rakashi har d'aki tukun ta dawo itama tayi nata d'akin.
Koda ya shiga d'aki tarar da Nawas yayi yana chatting, murmushi Nawas ya sakar masa sai NY yaga kamar Nasrin domin suna matu'kar kama da Nasrin yace"Har hiran ya isheku haka?"
NY yace"Wato ma da biyu ka tashi koh, ai hiran mu ba zata k'are ba kawai tace inje in kwanta saboda gobe zanyi tafiya"
Nawas yace"Kaji masoya"cike da zolaya.
NY yace Nawas"Wallahi na hangi tsantsar so na cikin idon Nasrin, na maka Al'kawari zan so ta fiye da yadda take sona, zan zamto mata abin alfahari zan bata dukkan gata, kulawa, so da tattali, zan zame mata miji nagari, nawas trust me insha Allah Nasrin ba zata ta'ba dana sanin aure na ba, kaidai Allah tabbatar mana da Alkhairi".
Cike da jin da'din kalaman NY, nawas yace"Amin ya rab" bayan ya jero mishi godiya da haka kowannensu yayi addu'a ya Kwanta.
Nasrin kuwa data kwanta tunani take tayi na wannan aure nata.Aure ba wata soyayya gashi ba hira a waya bare mu d'an saba, koda shike ni macece in munyi auren zan saito sa beside zanna hira da NY duk sanda naso Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi.
Washe gari Nasrin sai bakwai ta tashi kasancewar lahadi ne dama basu tashi da wuri.
Ta shiga kitchen ta ha'da breakfast ta shirya a dining taje tayi wanka ta komo k'asa.
Tana zaune tana kallon tashar manara sai goma saura saiga kowa na fitowa kamar wa'yanda suka ha'da baki.
Gaba d'ayansu gaishe da mum suka yi tukun su ma kowa ya gaida kowa sannan suka nufi dining.Bayan sun gama karyawa ne NY yake sanar da mum zaiyi wanka ya wuce, Ta mishi godiyan ziyara sannan tayi mai fatan isa gida lafiya da cewar ya mi'ka gaisuwarta ga mahaifansa sukayi sallama ta tafi makaranta.
NY ya tashi ya shiga ciki domin ya shirya Nasrin kuma ta tashi ta gyara parlon taje ta gyara kitchen ma. Najwa na d'akin Nabil suna karatu.
Tana zaune a parlour k'amshin turaren NY ya bugi hancinta murmushi tayi domin tasan shine ya fito Ai kuwa sai jin muryar shi tayi yace"Nassy baby ba'ko zaiyi halinsa".
Ji tayi kamar ta bisa su tafi tare amma ba dama murmushi tayi tace"Ba'ko ya kuma kwana biyu"
Yace"Tab kisa Abba yamin duka"
Kwashewa da dariya tayi tace"Waya ga ana dukan ka"
Shima dariyar yayi yace"Allah ma ya kyauta"
Tace"Amin"
Saida suka d'anyi hira tukun Nawas ya shigo
Su Najwa sukai mishi sallama yayinda Nasrin da Nawas suka yimishi rakiya har bakin mota.
Suka yi sallama yaja motar sa ya tafi bayan ya mata al'kawari zai dawo sannan yana isa Kaduna zai kirata.ya tafi zuciyoyi biyu na kewar juna.
Nasrin lokaci-lokaci takan kirasa taji ya hanya, sai shida da kwata ya shiga Kaduna.
Mum koh bayan ta dawo ne Nawas ya risketa a d'aki ya fa'da mata komai da suka tattauna da NY, mum taji da'di k'warai har salla tayi raka'a biyu ta yiwa Allah godiya k'arshen wahalar zuciyan Nasrin yazo saidai itama ba zata fa'da mata ba kamar yadda NY ya bu'kata.
A fallon Abba ya sauka, sunji da'din ganinsa matu'ka.Nan yake sanar dasu irin kar'bar da akayi masa a gidansu Nasrin har yace"Abba kasan me? Jiya fa mune mukayi girkin dare nida yayan Nasrin me suna Nawas gaskiya suna da kirki"
Murmushi Abba yayi yace "wato ko kunyar suruka bakaji ba ka zage kayita sha'kiyanci"
NY yace "Abba ba haka bane kasan banda ba'kunta"
Karan wayarshi ne ya sa bai kareshe maganar ba yana dubawa kuwa yaga Nasrin ce murmushi yayi ya d'aga tare da yin sallama.
Suka gaisa yace mata gashi parlourn Abba, tayi mishi ban gajiya yayinda Abba ya bu'kaci a bashi wayar domin su gaisa shima d'in gaisawar suka yi yayi mata godiya, suka gaisa da hajiya ma tukun suka yi sallama.
Abba ne yace "Nasiru inaga sati me zuwa insha Allah za muje Jos wurin Abban Nasrin don haka ka shaida mata" Nasir yace"Angama Abba, ni barin shiga ciki
Hajiya ki bada abinci na a kawo min bazan kuma shigowa ba"
Tace"To Nasir Ahuta gajiya" Da haka ya tashi ya nufi gefen sa..
Da shigarsa Nawas ya kirashi sai Da suka d'an zanta tukun sukai sallama ya tashi ya shiga toilet don yin wanka da alwala.
***************
A ranar da Abba ya dawo Nawas uban Zumu'di ya sanar mishi da komai daga Abba har Naufal sunyi matu'kar jinda'din maganar suka ce Allah Tabbatar da Alkhairi.
Washe gari Nasrin wani uban ado taci cikin wata jar super tayi mata kyau sosai tace da Mum ta tafi ziyara.
D'akin Naufal ta shiga ta gaishe shi kasancewar sun dawo daga tafiya yace bazai je wurin aiki ba sai ya huta.Ta langwa'bar da kai"tace pls yaya Naufal mota zaka bani zan fita ziyara"
Yace"Ga key can kan dressing mirror ga dubu uku kisa mai sai ki kiyaye ki lura Adawo lafiya" Zuwa tayi ta rungumesa ta sumbace sa a kumatu tace"Nagode yayana na kaina Allah barmin kai"Daga haka ta zari key d'in tayi waje, murmushi yayi yace"Amin Nasrin uwar da'din baki"
Nawas ne ya fito ya goge mata motan, sukayi sallama bayan ya garga'deta da ta kula sannan yayi mata fatan dawowa lafiya.
Tana fita Total ta nufa tasha mai tukun ta nufi cikin gari.
Tana traffic hold up dai-dai Zololo juyawa gefe da tayi suwa zata gani.......
.
Nasim da Nazira ta ga ni a cikin mota su ma hold up ya tsayar da su, suna ta hira abinsu gwanin sha'awa murmushi tayi ta kau da kanta tace"Allah k'ara don'kon so".
Ita ko Nazira kamar ance juya kawai idonta ya sauka kan Nasrin wacce ta mayar da duk hankalinta ga titi.
Gani tayi ta da'da wani kyau sai dai ta d'anyi rama, ga kayan da ta sa sunyi ma ta kyau sosai.Wayar ta ta d'aga ta dialing numbern Nasrin ringing biyu ta picking kasancewar tana hold up ne amma sam in tana tu'ki bata ansa kira."Hello Nasrin"cewar Nazira, nasrin tace"Yes Nazira kina lafiya" Nazira tace"lafiya lau, pls inkin crossing ki'dan parking mu gaisa mu ma muna hold up ne"
Tace"to" ta ending call d'in.
Tana wuce wa kuwa ta samu wuri ta parker.
Ji tayi ana knocking glass d'inta wa zata gani.......Nasim ne, murmushi tayi ta sauke glass d'in suka gaisa bayan ya mata wani kallo mai fassara da da ma, Nazira ma ta zo suka gaisa yaushe gamo k'awa ta ga k'awa su ka d'an zanta tukun tayi musu sallama a cewar ta batason yin dare zata wurare da dama.
Gidajen yan'uwa ta fara bi tana yi musu gaisuwa, duk inda ta shiga bata fin minti goma ta fito da haka ta je gidaje da da ma ta sada zumunci a k'arshe ta je gidansu Aisha inda suka sha hira tukun tayi ma ta sallama ta nufo gida.
Ta shigo gida biyar saura a gajiye sannu kawai ta yi wa su mum ta haye sama kasancewar tana hutun sallah ruwa kawai ta watsa ta fito ta haye gado towel ne kawai a jikinta ko mai ba ta sha fa ba bare tasa kaya.
Ringing d'in wayar ta ne ya tashe ta, duba wa ta yi ta ga takwas saura lallai tasha barci a hasale ta d'aga wayan"Hlo" d'ayan b'angaren taji an ce"Nass baby lafiyar ki kuwa?" Jin muryar NY abin k'aunar ta yasa ta wartsake, Cewa tayi"NY kana lafiya"
Yace"Amaryar mu ina lafiya, u sound somehow is everything ok", murmushi tayi tace"Lafiya lau na d'an je ziyara ne na dawo a gajiye so shine na kwanta kaine ma ka tashe ni" yace"Ayya sannu ko kiyi ha'kuri na tada ki so nake inji lafiyar ki" tace"Nagode, lafiya ta lau hope kaima haka yasu Abba?"
Haka dai hirar ta su ta Cigaba su ka d'au kusan awa ita dai Nasrin tana mamakin yadda NY yake furta mata kalaman soyayya in tayi magana sai ya ce bro d'inshi ne yasa shi yana gefe amsarta ka'dai kesashi jin da'di,ai kuwa ta za ge tayi ta bada amsa ita dole tana hira da saurayi(wauta)
*************
Haka dai lokuta suka dinga wuce wa NY kullum sai ya kira Nasrin a waya tun bata biye mishi harta fara domin inta yi mishi maganar ina bro d'inshi sai ya kira hydar ya bashi wayar su gaisa yace mata ai yana kusa yana jin su gaskiya ta iya hira in sun yi aure zata koya mishi.Hakan yasa Nasrin amince wa da gaske bro d'in na gefensa shi yasa ta saki jiki su sha hira abinsu.
NY ya sanar ma da Nawas cewan suna nan tafe shida su Abban sa ranar asabar.Nawas ya sanarwa da Abba, abba ya kira Abban su Nasim ya sanar mishi cewa ranar asabar za suyi ba'ki masu neman auren Nasrin don haka ya zo da wuri.
Naufal biki ya matso ba zama sai tsayu wa yana ta shirye-shirye.
Duk wannan abun da ake yi Nasrin bata sani ba domin NY cewa yayi ba zai fa'da mata ba zai mata zuwan bazata yan'gidansu ma kowa ya'ki sanar da ita har mum.
Ranar Asabar da wuri mum ta tashi Nasrin su ka shiga kitchen su ka soma girki-girke ko da Nasrin ta tambayi mum, ce mata tayi Abba ne zai yi ba'ki daga haka ba ta kuma ce ma ta komai ba.
Sai wuraren goma suka gama aiki tukun su ka nufi d'akunansu don kintsawa.
Sha'daya dai-dai Suka iso jos direct gidansu Nasrin suka nufa.Sun samu kar'ba me kyau gaskiy, nan suka zauna suka gaggaisa ashe Abban hydar da Abban Nasim abokai ne abin yayi musu da'di sai sam barka.
Abba ya yaba da hankalin NY matu'ka daya ke abu ne na ansan juna take yayan Abban hydar ya ciro sadaki ya mi'ka bayan sun gama tattaunawa Abban Nasim ne ya kar'bi sadaki yayinda Abban ya bada shawara akan a ha'da auren dana Naufal kawai, nan ta ke kowa yayi na'am da shawarar aka sanya auren dai-dai dana naufal kowa ya sanya albarka, daga haka aka gabatar musu da abinci.
Nasrin ko tana d'aki bata san ma ba'kin sun iso ba, NY ne ya kira ta a waya yace ta fito, cike da mamaki tace"In fito" yace"yes" daga haka kashe wayar yayi.
Ta d'au mayafin doguwar rigarta ta yafa ta sauko k'asa ta nufi hanyar fita abin mamaki tana fita wa za ta gani.......NY ne tare da Nawas a tsaye su na magana tsananin mamaki ka sa magana ta yi sai ido da ta bi su dashi domin yayi ma ta ba zata sosai.Nawas ne ya katse ma ta mamakin da cewa"Nasrin ki je ki serving Nasir koh, sannan ki shiga ki gaida su Abba
"To" kawai tace mishi ta yi ciki NY ya bi bayan ta.Direct NY dining ya nufa yaje ya zauna, Nasrin ta shiga kitchen ta ha'do mishi abinci ta kawo mishi ita ma ta samu kujera kusa da tashi ta zauna.
NY ne ya d'ago idanunsa ya k'ura mata ido sai duk taji jikinta ya mutu tace"Nasir barin gaisa da Abba in zo" bata jira amsar shi ba ta tashi ta nufi hanyar fallon ba'ki, da sallamar ta ta shiga Abba ne ya amsa yayinda murmushin sa ya fa'da'da bu'de hannayensa yayi yana"oyoyo yar'albarka" cike da kunya ta k'arasa jikinshi, yace "Ya'ta kina lafiya" tace"Lafiya lau" ta gaida sauran yan' fallon ta tashi ta fita.
Komawa tayi ta tarar da NY na ta cin abincin sa ta zauna ta sakar mishi wani murmushi shi ma murmushin ya mayar mata tukun yace"Nasrin Albishirinki" tace"Goro" yace kuma cewa"fari ko ja"
Tace"uhmmmm fari abani nasha"
Yace"well ban san ya zaki d'auki me zan fa'da miki ba, hala kiji da'di hala akasin haka.Wato Nasrin an.......
.
Abba ta kira, bugu d'aya biyu ya d'auka suka gaisa tayi mishi sannu da hanya jin tayi shiru yace Nasrin lafiya kuwa? ahankali tace mishi da ma na kira yaya nasir ne inyi mishi sannu da hanya bai dauka ba.
Murmushi yayi irin na su na manya har cikin ransa yaji da'di sosai domin hakan ya tabbatar mishi da cewa Nasrin tayi na'am da za'binsa, cewa yayi bari a kirashi sai in kira in bashi koh"to" tace a ta'kaice sannan ta kashe wayar.
Sai kuma ta fara tunani anya ba tayi rashin kunya ba kuwa sai kuma tace yooo ai ba wanda zan aura na tambaya ba, ba ta gama zancen zuci ba wayarta ta so ma ringing tana dubawa ta ga Abba ne sai tayi picking tayi sallama muryar NY taji yace "nassy baby k'ara ta kika kai koh" murmushi tayi tace"nifa ba k'arar ka na kai ba kawai naga ba ka picking call d'in bane shi yasa"
Yace "to ya akayi ne amaryar mu bayan yau kin manta ni"
Murmushi tayi tace"to ba na kiraka ka'ki picking bane"
Ta k'areshe maganar cikin shagwa'ba baiso ta daina ba.
Yace"to kiyi ha'kuri our bride mun isa lafiya fatan kema kina lafiya"
Cike da shagwa'ba tace" lafiya lau"
A haka dai suka sha hirar su da ga k'arshe suka yi sallama ba don zuciyoyi sun so ba.
Nawas yaji shiru-shiru Nasrin ba ta kuma yi mishi maganar princess ba gashi son ta kullum da'duwa yake a zuciyarsa dole zuciya ta tirsasa shi ya kira NY.
Bayan sun gaisa ne Nawas ba kunya ya sanar da NY abinda ke ransa game da yar' k'anwarsa har cikin ran NY yaji da'di yayi fatan alkhairi bayan ya tabbatar wa da Nawas cewa zai ma ta magana insha Allahu bazai gagara ba Nawas yaji da'di matu'ka yayi ta yiwa NY godiya daga bisani suka yi sallama kowannensu najin da'di cikin ransa.
Soyayya me k'arfi ce ta k'ullu tsakani Nawas da princess, shi kanshi mamaki yake domin bai ta'ba tunanin zai tsaya yana fa'din magana ga wata mace ba sai gashi har rarrashin princess da kukan k'arya yake mata banda kalaman so da yake fa'da mata domin princess kamar ni Ummu Arif take tana so a sota,a shagwa'bata sannan yawaita fa'damata kalaman so wanda suke tafe daga zuciya ba na k'arya ba, ai ko Nawas aiki ya gan ka.
Biki nata k'aratowa yayinda Nasrin ta koma gidan auntyn ta domin an kawo wata mata daga Niger me gyaran amare don ta gyara Nasrin.Ai kuwa amarya tasha gyara da ma gata fara kyakkyawa sai ta da'da kyau jikinta kamar a ta'ba jini ya fiti ita kanta tasan ta gyaru ga wani k'amshi ko zama tayi a wuri sai k'amshin ya kama wurin amarya dai sai sam barka.
Ita ko komai yinshi a dole domin tasan auren biyayya zata yi ba auren soyayya ba shiyasa bata wani damu d auren ba don ma tana k'ok'arin danne damuwarta.
Waya da NY kuwa abin sai da'duwa yayi ita data keso ta yi nesa dashi domin bai san yadda take ji bane amma kullum da'da kusantar ta yake acewarsa shine kan biki komai take bu'kata ta sanar mishi.
Ko wajen fidda anko ma wasu cousins d'inta ne suka fitar ita ko a jikinta suka kaiwa Aisha da Nazira da ma ita ba wasu tarkacen k'awaye gareta ba, ta d'au pic din ankon a waya ta turawa zeenat ai kuwa taji da'di tayi mata al'kawari zata zo insha Allah.
Wajen kai d'inki ne kawai tace a ba ta kayanta zata kai, haka kuwa akayi kayan fitar biki kala goma a kayi mata duk ciki bana k'asa da dubu goma ta kaiwa tailor d'inta ta za'bi ha'da'dun d'inkuna domin Nasrin akwai son gaye ta biyashi kud'inshi yayi mata al'kawari bayan kwana bakwai zai kawo mata.
Biki saura sati biyu aka kai lefen Naufal,akwati set biyu amarya Nawwara tasha kaya ba laifi iyayenta ma sun nuna murnarsu domin sun ba da tukwici ba ka'dan ba.
Ita ko uwar biki Nasrin wacce ji take kamar ana gab da sata cikin prison ne akwatin ta goma sha biyar set uku,zinare biyu ga gold dasu azurfa tasha kaya gaskiya, wajen bada tukwici ba'a bar iyayenta baya ba sunyi bajinta sosai abin dai sai ni UMMU ARIF dana gani.
Ranar ko Nasrin kwana tayi kuka shikenan zata rabu da NY, me yasa ya kasa gane son da ta da'de tana mishi,tashi tayi ta fara nafila har aka kira sallar asuba tukun ta d'aura sallar nan barci yayi gaba da ita kan sallayar.
Tailor ya kawo mata kayan ta d'inkunan sunyi kyau matu'ka yayinda ta d'aga su tana kallo saida tayi kwallah inama da NY za'a d'aura ma ta aure da anga bidiri, haka ta tattara kayan ta chusa cikin wardrobe ta shiga toilet ta soma aikinta na kuka.
Washe gari ne Nasrin tana kwance misalin sha biyun rana aka ce mata ta fito tayi ba'ki daga kaduna, fitowan da za tayi wa ta gani....