🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣2⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
*Wannan page din na sadaukar dashi ga dukkan masoyan wazai furta*💞💗
Shi yasa yau na saki biyu don kuji dadi farincikin ku shine nawa wallahi.😭😭 Ina son ku😍😘🥰 kullum sai nayi kukan dadi.
**************
*ABUJA NIGERIA*
........ Ya tallabo bayanta ta dawo ta tsaya dai dai Amma ta kasa yarda su hada ido, *INA SON KI BILKISU* Yau na *FURTA* Abinda kike son ji..... Ta Kara kasa da Kai jikinta har lokacin bai daina kyarma ba....Wai mafarki takeyi ko kuwa da gaske ne?
Ya rungumota ta sunne Kai jikinsa.... Ya Kara Rada Mata... *ina son ki* tsikar jikinta ta tashi Yarrrr..... Duk wannan haukan da Kika ga inayi sonki nakeyi, Shi yasa na kasa boye kishina gareki...... Nasan kin fahimta Yanzu Kuma kin Sami amsar fadawa su daddy ko?
Ya dago fuskarta....ta koma da sauri.... Ya kyalkyace da dariya yau Kuma jikina ake son Hawa?
Kin wahalar damu da yawa, kina kawo rigima kullum because you want me to say it.... Ni nasan kina Sona I knew it...Kuma ko Baki furta ba nasan kina Sona wallahi....... Ki daga ni na tafi... Ya fada Yana dariya.
Kinga duk laifin ki ne, da kinsan zakiji kunya da hakuri kikayi muka tafi a Haka bakiji komai ba..... Ta zame a hankali ya mayar da ita da sauri, kafin ki gudu Dan Allah gobe kada ki Sanya mun hijab din nan kuma kiyi mun girki da kanki Zan zo around 10:00am kinji ko?
Ki ce b lefe na kawo ba, hasafi ne saboda Ina son ki.... Ta zame yayi saurin rike hannun ta ki jira na Baki kudin dinki Mana ..... Ka barshi nidai... Bakya so?
Ta daga Kai..... Da gaske bakya so?
Um, tace a hankali.
Yayi Yar dariya kudin ke Baki so ko Ni?
Kudin ta fada tana sim sim da Kai.
Yayi murmushi Ni kina Sona Kenan?
Ta yi alamar fizge hannunta.... Ya rike gamm. Kice inji Mana kina Sona?
Ta yi kasa da Kai ji takeyi kamar ta bude kasa ta shige ta huta.. ...ya Kara dariya sosai ohh ni Anwar Ashe akwai ranar da bakin nan zai mutu?
Ai Dana San wannan kalmar ce zata sa in Sami saukin tsiwa da tuni na Gaya Miki saboda na Dade Ina dakonta.......
Idan daddy ya Baki zabin auren mu kice kinfi so ayi kafin mu Gama school....... Lokacin ne ta banka mishi harara da sauri ta kawar da Kai.
Ya Kama dariya ya figi hannunta zo kiyi mun rakiya naga alamar nema kikeyi ki gudu ciki ko?
Ta biyoshi a hankali yasa hannu ya fiddo rafar kudi ya ajiye hannun kujera idan kin shigo ki wuce dasu na dinki ne....na gode. Ta fada a hankali. Tayi murmushi ya ce my pleasure dear.
Ta Dan harareshi ya tuntsure da dariya shin na Riga na *FURTA* ai to boye boye name?.
Suka fito tayi saurin fizge hannunta ya Kama murmushi Yana fadin ke dai Yar kauye ce...... Allah yayi?
Sadeeq ya taresu.
Allah yayi sadeeq yau kwana ta saka ni sai da na *FURTA* Ina son ta...... Sadeeq ya you firgigi ya ce waoooh *Anzo wurin kenan*.... Duk suka bushe da dariya ita ko sai murmushi takeyi kasa kasa...... Munafuki ai duk Kaine tun farko kayi ta wahalar da ita... Shin ai nadai FURTA gobe Zan dawo *Zance* ya bangajeta da kafada ko Bilkisu???
Ta galla mishi harara suka kwashe da dariya.....
Kiyi mun tuwo goben.... Ya shiga mota tana tsaye har suka fice gate din....
Wai da gaske ka furta kana sonta?
Wallahi kuwa, sadeeq rigimar Bilkisu bana iya daukar ta, ta tsareni lallai sai tasan wanene Ni...... Saboda me zaka boye Mata Wai?
Ai na fada.... Amma fadar sai ta tsorata Kuma. Na rasa me take so, Kuma Wai ita ya zata fada a gida wace amsa zata bawa su daddy....na ce kice *Ina son ki* saura kadan tayi penting .....suka bushe da dariya...... Amma ka Mata gatsal! To ya zanyi da ita? Kaga yanda ta nemi ta firgice mun?
Banza finally ka furta dai.
Yayi dariya *Anwar ya furta* naji tsoro yarinyar Ina son ta saboda class wallahi.....gidan sa dake *Minister's hill* suka nufa.
Mommy..... Mommy ta Fara kwada Mata Kira tana Hawa sama.
Tana faman shirya jaka ta shigo dakin, mommy Anwar fa ya kawo Kaya da yawa ..... Wane irin Kaya?
Ina daddy?
Sunje sallah kasa.
Wane irin Kaya ne ya kawo.
Jikunkuna ne set hudu.... Ta kalleta da sauri jakunkuna? Na menene????
Ta sunkuyar da Kai ta sunga Mata kudi Kinga Wai su Kuma nayi dinki...... Duk Akan me?
Ta Kara kasa da Kai, ya ce tsaraba ce ya kawo mun.... Saboda???...... Ta Kara katseta da sauri.
Ya ce Yana Sona ne???
Muje naga kayan, bazaki ce mishi daddyn ki ya hana karbar kaya ba?
Wallahi duk abinda na kokari in sanar dashi bai yarda mommy.
Wohohoho ta fada tare da rabka salati...... Amma kin San daddyn ki zaiyi fada ko?
Mommy Anwar Shi ne *Hamza bushara*..... Mun sani. Ta ce a takaice ta zaro ido Kun sani mommy?
Yes, ta fada tare da wucewa tana fadin jekiyi sallah nasan fada ne yau duk sai mun Sha ni da ke.....
Ta falon ya shigo Yana ganin kayan ya kwala ma Bilkisu Kira.
Ta fito da gudu gudu.....
Wadannan kayan fa? Ta sunkuyar da Kai, Anwar ne ya kawo su daddy.
Na menene?
Ya ce tsaraba ce kada yazo hannu biyu....
Saboda me?
Tayi jimmmmm kafin ta ce *Wai Yana Sona ne* yanayin yanda ta Fadi maganar kamar Yar koyo mommy ta shigo ya kalleta Kinga Kaya?
Hada kudi....
Ya kalli Bilkisu ke kina sonsa?
Tayi shiruuuu kinji mamana kina son sa?
Tayi kasa da Kai kawai.... Yayi murmushi kina son sa kenan.
Ki mayar mishi da su kice bana karbar irin wannan kyautar idan har da gaske yakeyi ya turo iyayensa.... Ta dora hannu saman Kai.... Daddy bayar Dani zakayi haka da wuri ta kurma ihu tana kuka.
Ya yi Yar dariya, to tunda kin Sami Wanda kike so me ake jira..... Nidai kada a turo...ke bama son rashin wayo.
Turowar an fada Miki Yana nufin za'ayi Aure?
Hakan zai nuna idan da gaske yakeyi sai a ajiye magana.
Ta danyi shiru alamar ta gamsu.
Ya wuce Yana girgiza Kai Yana murmushi,
Mommy ta kalleta tana hararar ta, wannan koke koken ba komai zai janyo Miki ba sai raini wurin Miji. Komai ke sai ki bare Baki saboda kina ruwa ruwa.... Mtsew ta ja tsoki.
Wannan rawar Kan da Anwar keyi inba auren ba meye zai kamance ku?.... Mommy..
Yi min shiru, Ina ce Nan Kika diririce Kika firgice saboda yayi fushi da ke ko?
Ta zumburo Baki kaiii mommy....... Ke arrr kilibabba.
Ta wuce , ta Mike ta bita da gudu mommy yace zai zo gobe by 10... Sai kije ki fadawa su Rahina don su shirya mishi kin dai San ba Mai sauko Dani da safe ko?
Mommy cewa yayi ni Zan girka baya son nashi...... Sai kawai tayi dariya tace yaron nan hooo.
To ya kyauta ma kansa sai kiyi asubanci saboda na sanki da shegiyar nawa da duminiya, Bilkisu za a Fara wa miji hidima..... Kai mommy ta bita tana shagwaba....
Ta kyalkyace da dariya. Ai munji dadin zuwan sa saboda kullum daddynki cikin waya yakeyi Yana jiyo labarin badakalar ku.....kamar ya mommy??
Tayi Yar dariya akwai wadanda kebin movement dinku kullum...... Ta zaro ido yasan Anwar na zuwa gurina mommy???
Tayi murmushi har ciwon cikin da kikayi ya je har cikin dakin ki,sannan ya balla Miki kofa.... Ta zare ido na shiga uku na... Ke dakata, tunda bai nuna Miki ba wallahi kada ki nuna kin sani Babu ruwana.... Cikinta yayi kulululu ta hadiye miyau kut!.
Mommy Dan Allah laifina ne? An fada mishi Nima bana son haka ko?
Ina Jin abinda yayi saving din ki kenan....
Ta saki ajiyar zuciya kaiii Anwar case ne.
Ko bude kayan basuyi ba yanda suka ajiye haka aka barsu a wurin.
*WASHE GARI*
Karfe bakwai tana kitchen, daddy ya fito zai je office ya leka... Bilkisu a bani abinda ya sauka na jiyo kamshi ko Anwar din kawai keda shagalin?... Ya karasa maganar Yana murmushi.
Kaiii daddy ta fada cikin Jin kunya....
Har ciki ya shiga Rahina nata fere dankali, saratu na grating kwakwa, ya kallesu yau aiki ya karu ko?
Iyye hada kaza haka?
Ya bude oven.... Ta rufe fuska lallai yarinyar ashe catering school din bai tashi a banza ba...
Menene can?
Wipping cream daddy... Zakiyi cake ne?
Na Gama gashi can ma.... Ya sa hannu ya dauki daya ya Kai Baki..... Um um..ya naji wannan kamar ba irin Wanda ake Mana ba?...... Kai daddy ta Kara fada yayi dariya....
Mommy ta shigo ga break din can fa.... Zo kiga sonkai Bilkisu na hadawa Anwar gara ba irin ..... Kai daddy... Eh Mana.
Ta matso iyyeh lallai Shi yasa baji gida ya Fara daukar harami.... Ta bude tukunya.. hada Kan rago?......
Kai Kai Kai daukon kwano Shi zata zuba mun ja'ira..... Duk suka kama dariya.
Rayuwa irin ta gidan su Bilkisu tana da ban sha'awa......mommy ta kalli Rahina, yau taku ta sameku ko?.... Abinda na fada Yanzu kenan.... Daddy ku je falo Zan kawo muku nidai... Duk suka kwashe da dariya... Mommy tace komai Zaki debo Mana ko sai ankai wa Anwar din nazo na ce Zan Dauka..... Kaiii mommy Wai ya Zan ce baza ku ci ba ????
Suka fita suna dariya hannun daddy rike da cup cake Yana gutsira...
Ya kalli mommy in shaa Allah tarbiyyar da muka ba Bilkisu bazai taba Sanya muyi Dana sani ba.... In shaa Allah.
Ina ta fada akan catering school din nan Kika dage Kinga Yanzu amfanin yazo ko?
Ai na fada ma Kuma wallahi cewa yayi nata yakeso baya son na Yan aiki kaga Idan Bata iya ba zai aureta Yana sonta Amma can gaba matsalar dole ta taso.... Yaron Yana da rawar Kai akan Bilkisu hakan na bani tsoro, ya kasa danne feelings dinsa kin lura ko?
Hada yarinta ke damunsa..... Yes da giyar kudi.
Yama arzikin sa kankanta kawai hankali da natsuwa yaron ke bani sha'awa...da kunya Kuma....yes Yana da kunya of course.
Bilkisu ta shiryo musu komai a tray ta kawo Yana Shan Lipton da biscuit....daddy biscuit Kuma???
To wancen kwalayen biscuits idan bama ci ya zamuyi dashi na ce ku rabar Kun jibgesu.... Dasu mommy zata tafi sokoto ne na dibar Mana namu Yana store... Ohhh ban sani ba ... Ta ajiye ta koma.
Ya bita da ido, abinda ke tayar mun da hankali shine yanda yake son ringa nuna Mata komai da karfin tsiya..... Gaskiya fa.
Yanzu idan ya turo iyayen zuwa taushe zaka ce su kawo kayan baiko?
Eh, ki Bari zuwa dare zamu maganar kiji yanda na tsara lamarin.....
Karfe takwas ya fita office mommy Kuma ta Haye sama domin komawa barci.
Sauri sauri suka karasa aikin , goma saura kwata an shirya komai ta fada wanka.
Ta fiddo Kaya sunfi ashirin ta rasa wane zata saka?
Tabbas Bata son ta saka matsattsu tunda ya tilasta gyale zata saka.
Da kyar ta dauko wata doguwar riga bubu na boyel peach an mishi kwalliya da *Stones* blue. Dinkin ya bude sosai, ta yi simple kwalliya ta shafa light pink na lipstick..... Rahina ta kwankwasa Mata kofa... Aunty kizo.
Inji waye? Ta fada tana gyara lagen gyalen... Uncle Anwar ne gashi can na bude mishi falo.... Ki ce Ina zuwa..
Ta Kara feffesa turaruka a jiki.... Ta juya ta Kara juyawa a madubi sai Kuma ta danji kunya tayi murmushi ta fita tana takawa dai dai cikin plat shoe light blue kalar gyalen.
Tana bude kofa sai kawai ta kwashe da dariya ganin sa bisa dining table Ya Fara cin abinci.... Na shiga uku Kai baka bakunta ne Wai??????
Ya kyalkyace da dariya inayi Mana gashi ni nake zubawa kaina? Idan bana bakunta ai zanje ciki na Kira ki zuban ..... Ta galla mishi harara Kai baka da aiki sai ci..... To ai yunwa ba kanwar ubana bace ko?
Ta kyalkyace da dariya ya akayi Kika San Ina son kan rago?
Ta ce hmm, ya lunkuma harshe a Baki Yana um...um...um please budan can menene?
...... Wai Kai baka ko irin Jan ajin Nan?
Ya kyalkyace da dariya kaiii Ni Zaki Sanya na kware wallahi.
Daukon lemu Mai sanyi ni bana Shan tea wannan sai ku Yan gayu..... Ta Kara hararar sa.... Ya kamata na Sanya wa hararar nan doka duk lokacin da kikayi ta ......
Ta Mike kawai ta Isa inda fridge ta bude wane kala Zan kawo maka?.... Peach daukon peach dinnan Amma fa roba biyu Ni daya bata Isa ta.... Ta Kara dariya ohh Allah gamu gareka....
Ya Miko Mata chips da egg Fara ci Nim zanci irinsa..... Kana da cikin Zane ne?
Yayi murmushi Amma kajin nan dasu Zan tafi fa don sai dare Zan dawo.... Zaka dawo Ina?
Anan.... Ya fada Yana kallonta.. ke na dawo Abuja fa sai an koma school nida Kano......ta zaro ido duk kana me?
Ya nutsar da idonsa cikin nata yace duk Ina zuwa Ina ganin ki... Tayi kasa da Kai tana murmushi.....
Kill babba abinda kike son ji kenan ko?
Tun karfe nawa Kika tashi yau?
Ta Dan zumburo Baki ban koma barci ba tun asubah..... Nima haka ya fada Yana murmushi. Ta harareshi kana meye?
Ina kallon agogo na kagara 10 tayi kamar na Miki waya na ce na mayar dashi eight..... Ta yi Yar dariya yabi kuncinta da kallo..... Kinyi kyau sosai fa.
Ta ce hmmm.
Ni na yi kyau? Sabbin Kaya na dunka saboda zuwa Nan fa.... Ta kyalkyace da dariya Kai na bani yau to me nace?
Ya Dan Sha mur naga kamar Baki fahimci hakan ba.... mtsew ta ja guntun tsoki.
Yayi Yar dariya ya Mike Yana goge baki da tissue taso idan bazakiji ba muyi magana ba dadewa zanyi ba Zan barki kiyi barci sai na dawo da dare ko? Ya na maganar Yana tafiya tare da janyo hannunta..... Ohh Shi baya Jin komai ya Kai hannu ya tabani ni Bilkisu??.
Ya zaunar da ita sannan ya zauna kusa da ita.... Ya akayi Kika bar kayan can anan? Daddy yace ki mayar mun?
Ta daga Kai alamar eh,
Kin fada mishi in sonki?
Nan ma ta daga Kai?
Duk da haka bai karbi kyautar ba?
Ta ce eh,
Sunyi yawa?
Eh,
Yayi murmushi to Yanzu me yace?
Ta yi kasa da Kai yace ka turo iyayen ayi magana.... Ihu ya daka kawai sai ya Mike tsaye ya janyota ya Bata wani hot hug.
Ta zame ahankali ta zauna tana murmushi....... Dan Allah kizo na you hugging dinki...
Ta galla mishi harara ya zauna Yana dariya *Amma fa nazo da sa'a* .......kawai ta jiyo motar daddy alamar ya dawo.... Gama daddy Nan ya dawo.... Gooood ya fada tashi kije kice Ina son magana dashi.....
Ta zaro ido.... Meye zaka fada mishi?
Zan rokeshi yabar Miki kyautar nan bazan koma da ita ba.... Kai Anwar daddy fa baya son gardama.... Haba?
Allah.
Yayi murmushi jeki ce Ina magana...... Tashi kada ya shiga ciki please.... Ya mikar da ita...
Yana kokarin shiga ta fito daddy ka Kuma dawo? ..... Bilkisu kice ma Anwar securities din nan ya Basu damar Zama Mana tsayuwa ai babu dadi ko?...... Shine yace Wai zaiyi magana da Kai.... Ya kalleta da sauri Yanzu?
Eh, okay Zan biyo ta Nan Ina sauri ne nayi mantuwa.....
Police din da suka rako Shi suka bude mishi kofa ya shiga ta dayar kofar.
Ta dawo, yace na fito?
No. Zai biyo ta.... Ya banko kofa Anwar lafiya dai ko? Ana jirana office.... Da sauri ya sauka kujera ya zukunna.... Yayi saurin Mika mishi hannu taso inji menene???? Ya rike hannun sukayi hanyar fita.... Ya Kara kallonsa menene?
Ya kasa magana kunya duk ta kamashi.... Ya tsaya chak ya fuskance Shi...Anwar!
Ya Dan rusuna daddy Dan Allah abar Mata kayan bana son na koma dasu..... Ya kura mishi ido... Amma kasan sunyi yawa ko?
Ayi hakuri Zan kiyaye next time Amma now abar Mata don Allah.
Ya Kara kallonsa sosai sai Kuma yayi murmushi... Shikenan Amma bana so ka daina kaji ko?
Ya rusuna na gode Allah ya Kara lafiya da shekaru masu albarka...... Aminnnmm ya Rabbi.
Ta fada maka nace ka Aiko?
Ya Kara sunkuyar da Kai In shaa Allah zasu zo gobe... Yayi dariya
gobe yayi sauri zuwa asabar dai ko?
Ya noke Yana murmushi.... Shikenan sai na dawo ana jirana ......
Ya dawo Yana murmushi tana zaune.....ya karasa Yana fadin yace ki dauki kayan shikenan ko?
Ta kalleshi da sauri.
Yayi dariya rokonsa nayi, ya Kuma amince ... Ta ce hmmm.
Na ce mishi Zan turo gobe yace sai zuwa asabar....
Ta ce hmmm kawai... Yanzu Kinga Ina da hujjar cin uban Suleiman ko?
Ta zaro ido.... Dan Allah ka bar maganar sa, Zan fada mishi an Mana baiko...... Ban yafe ba Kika Kuma magana dashi ..... Ta zaro ido..lallai idan aka koma school akwai chakwakiya.
Ya Mike Zan tafi sai na dawo anjima kinji ko?
Ta ce toh itama ta mike, daukon kazar da wancen cake din dasu Zan tafi.
Ta sungumo mishi suka jera ya fizge gyalen tare da shafa gashin ta yaja.... Nayi sa'a fa domin Ina son yalo yalon gashi..... Rufen gashi ko na saki kayan Nan su zube... Da kin sake wasu wallahi.
Ya Kara shafa gashin Yana murmushi sannan ya mayar Mata da gyalen... Ta banka mishi harara... Kana da matsala wallahi hakan haramun ne... Astagfirullah na daina.
Ya fada Yana dariya...
Yana tafiya ta saki ajiyar zuciya tace kaiii Anwar case ne.
Ita da mommy suka bude jakunan.... Tsoro yasa suka mayar suka rufe..... Ta kalli Bilkisu yaron nan sai ya kusa haukata ki idan kukayi Aure...
Tayi jimmm... Kawai.
Tare da Sadeeq ya dawo..... Tana shigowa yace koma ki sako hijab........
Ikon Allah sadeeq ya fada tayi saurin juyawa.... Banza wallahi kwakwa ke kawo ka marar zuciya..... Naji kome zaka ce kai ne ka jawo ni dole na biyoka kuma na gama zaman zuruu...... Ya yi murmushi.
Abinda Zan Rama?? Kai kishin naka ma da bashi da aji..... Ya Kara kyalkyace wa da dariya, kishin har akwai Mai aji?
Ya mishi banza.....
Ta dawo rike da mango juice a cups..
.... Bilkisu kinji sadeeq Wai kishina baida aji kin yarda?
Ta ce hmm, kawai ya Miko Mata sim card ungo Ciro mun layinki.... Ta zaro ido...
Yasha mur yes dole ki canza layi ..... Dashi fa nake jin alert....wane bank ne?
Access bank. Ta fada cikin fushi.
A nan Kika bude account din ko sokoto?
Ta bishi da kallo.... Anan Abuja... Kawai ya dauki waya...hello , yes nine lafiya.
Zan turo ma wani account number please ayi blocking din sa zamu bude sabo amayar da komai can.... I don't know buh I'll ask her...
Ya kashe meye account number din???
Sadeeq kaga rigimar da Anwar ya kunno ko?
Ya danyi murmushi zamanki lafiya ki canza don tabbas kishin wannan zai janyo ma bank din matsala..... Tayi zugummm....
Ya figi wayar kawo na canza Miki..... Zan dauki no. Su Aisha.... Zan saka Miki duk no.s din kawayenki Mata Amma wallahi Kika yi saving maza sai......... Kana ganin Ina kula maza ne... Ta fada a hasale.... Ya dalla Mata harara su ai suna kulaki ko?
Ta Bata rai.... Sadeeq ya jiyo zaku Fara ko?
Hakuri zakiyi dashi fa halin sa ne ba yarda Kika iya... Ni bana son wannan zargin da yake mun... Na daina ya hakuri shikenan ko?
Tayi shiru. I'm sorry please. Shikenan ta fada tana hararar sa.
Yayi Yar dariya.....
Firar rigima rigima soyayya soyayya don ma sadeeq nasa Baki idan sun nemi rikicewa.....
Ya ce zai tafi Kano gobe zai dawo asabar Amma sai dare zai shigo bayan Baki sun tafi.
Ta masu rakiya ya hanata karasawa waje ya ce ta koma kawai....
Daddy ya buga ma kanen sa sokoto cewar yazo don su tarbi Baki, ya Kira yayan mommy da aminan sa biyu ministers.
An shirya gaggarumar tarba.
Misalin karfe Sha biyu suka karaso.
Abin mamaki ba kudi kawai suka kawo na neman Aure ba hada halawa da goro da biscuits.
Bayan an gama gaisawa aka ci abinci aka Kara gaggaisawa kowa ya gabatar da kansa, iyayen Anwar biyu ne daya kanen maman sa daya Kuma aminin mahaifinsa ne sai wasu dangin babansa daga kauye saboda baya son da yawa asan abinda yake ciki kamar yanda Hajiya ta gargadeshi. Daddy na gefe kanin sa ya Fara magana....
Alhamdulillah munji dadin kasancewa daku ayau ya Allah yasa wannan yaza alkhairi garemu Baki daya....
Mune da jin dadi hakika Hamza ya kawo mu gida na mutunci masu karamci Alalh yasa wannan yarinya tayi Hali irin na iyayenta....duk aka amsa da aminnn.
Ga Kaya mun kawo na neman Aure da kudi dubu dari biyu ya Allah yasa muga ranar da zamu taru haka da sunan dauruwar auren su, aka ce ammmmeeenn...... Alhamdulillah daddy ya katse Shi.
Duk aka kalleshi... Da sauri.
Kamar yanda na yanke shawara nida mahaifiyar yarinyar Nan da dangin mu, Ina ga a wannan haduwar mun Isa mu shaida Aure saboda haka na yanke shawarar wadannan kudin zamu karbe su matsayin sadaki goron Kuma aba kowa ya shaida Amma bisa ga sharadi..
Bana son yaran nan su San Haka har sai bayan sun kammala karatu tukun....
Masha Allah Masha Allah duk falon ya dauka nan da Nan aka Fara Shirin daurin
Aure kowa ya bada wakili..... Cikin mintuna da basufi ashirin ba aka ce faaaaatiiihaaaa.....😄✍🏼
*Zainab Dahiru wowo*💖💖😆
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣4⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
****************
*KADUNA RIGASA*
Wannan doka da tsari ya Kara taimaka wa zaman su sosai da sosai, gidan ya zauna qalau ba sauran tashin hankali idan Yana gari ko wace zata kama tsaginta har ya gama kwanakin sa ya koma sannan zasu ci gaba da ziyarar juna, Koda yaushe Ummi na sashen Amira musamman da ta Fara laulayi...........
***************
*ABUJA NIGERIA*
...... Juyowar da zaiyi suka hada ido da Anwar din cikin wani irin yanayi.....ya razana ya firgita, sannan yayi baya da sauri tare da fadin *You scared me*...... Meye naji kana fada?....idanun sa sun kada sunyi jawur kamar garwashin wuta..... Ya daka mishi tsawa nace meye naji kana fada??????
Look please understand...... Ya shako wuyan rigarsa Kai munafuki na ne ba Amini ba sadeeq?????
Ya girgiza Shi ya tura baya da karfi... Yayi taga taga zai Fadi.... *What the hell are you doing*..... Shima ya daka mishi tsawa.... Sai kawai ya dafe Kai ya duke wurin Yana fadin *Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un*..... Hankalin sadeeq ya tashi ya kamo sa Anwar please.... Ya ingije Shi.. kyaleni sadeeq...kyaleni bana so... Zan maka bayani Anwar please calm down..ya Mike a hargitse ni za'a daura ma Aure ba tare da na sani ba??? Ya nuna kirjinsa Yana zaro mishi idanu.... Please.... Ya tura Shi baya I don't want to hear it..... Ya yi gida da gudu... Shima ya rufa mishi baya ya biyo shi....tare suka shiga daki Yana kokarin turo kofa ya rufe sadeeq din ya banka da karfi .... *Get out*.... Ya daka mishi tsawa... Ya maida kofar ya rufe , mutanen gida kowa ya fito yayi jugun , jigumm ......
Cikin bacin Rai sadeeq din ya Fara magana; Kana ganin laifi nane??
Ko kana tunanin Ina da laifi ko hannu aciki????....... Ya akayi ka sani ni ban sani ba???
Sadeeq wane laifi nayi da za a dauran Aure ba tare da na sani ba??
Ya bude fridge ya dauko ruwa Mai sanyi ya Mika mishi a cup ungo kasha let's talk peacefully please..... Bana Sha ka fada mun waye ya dauran Aure Kuma meye hujja???
Ita Bilkisun ta sani???? Ya Kara zaro mishi idanu...
Daddyn Bilkisu ya ce a daura.... Dalili????? Ya Kara tsareshi da ido....
Wallahi itama Bilkisun bata da masaniya, Kai waye ya fada ma???
Ban sani ba ya daka mishi tsawa..... Ya Mike tsaye bari kaji Anwar bana tsoron ka bana shakkar ka, ka saurara Zan fada ma abinda na sani akan wannan daurin auren idan kaga dama ka yarda idan Kuma ka ga dama ka Sanya a daureni sannan kaje ka dauki duk matakin da ka dauka...... Ya kura mishi ido, yau sadeeq ke mishi tsawa haka?
Lokacin da aka Kai kayan daddyn nasu ne yace a daura Aure saboda yanayin rawar kanka musamman yanda kake kakkama mishi 'ya.... Ko kasan cewa ya bada labarin duk bidirin da akeyi school???? Musamman Yana da wadanda suke bin yarsa suna monitoring?? Kasan gidan akwai CCTV wacce yake ganin duk zancen da kakeyi da Bilkisu???? Kaga laifin sa don ya kubutar daku daga halaka?
Muharramar ka ce da zaka na irin wadannan abubuwan?
To Alhaji Hassan ya sanar dani dalili kuwa saboda sun san nine shakikin ka ni kuma na shaida wa mahaifina akara samun shedu kasan duk duniya maganar nan bazata taba fita ba daga bakunan mu bacin da ka jiye ma kunnen ka.
...... Ya juya zai bar dakin cikin bacin Rai Anwar din ya riko hannun sa da sauri, sadeeq din yace good cikin zuciya saboda yayi hargagin ne don ya nutsar dashi.
Ya dawo dashi a hankali duk jikin sa ya mutu ya ce zo zauna sadeeq.... Bazan zauna ba Ina ce ni munafukin ka ne ba Amini ba ..... Kayi hakuri I regret it.... Kayi hakuri.... Shima sadeeq din duk jikin sa yayi sanyi ya dawo ya zauna.
Sadeeq meye shawara?
Ya kalleshi kamar zaiyi kuka.... Kayi hakuri Anwar I know how you feel about this...... Forget about my feelings please what shall I do????
Shawara daya ce Anwar pretend as you don't know. Ka nuna Sam baka sani ba..... Zanyi haka saboda Zan tayar ma Bilkisu da hankali.... Ai anyi shawarar ita a sanar da ita saboda ta kiyaye sharuddan Aure...... Ya dafe Kai tare da runtse ido to ni me yasa basa so na sani?????? ...... Saboda rawar kanka. Sadeeq ya fada Kai tsaye..... Zan basu mamaki sadeeq.... Wallahi Zan nuna masu how true I love 'yarsu........ Alhamdulillah sadeeq ya fada tare da janyo Shi ya rungume Shi..... Anwar wannan ba karamin gata akayi maku ba wallahi hakan da akayi ya faranta zukatan dangin ka..... Ina ka taba ganin anyi Haka? Ka tabbatar gida kamar na su Bilkisu ba za su taba hakan don kwadayi ..... Mtseww please I don't suspect that.
Ya tashi zaune sadeeq an dauran Aure da Bilkisu?????
Ya kara runtse ido yayi baya ya kwanta bisa gado har lokacin bai bude ido ba.... Sadeeq Ina son Bilkisu, wallahi duk abinda nakeyi ina sane am just testing her , Ina jaraba ta ne sadeeq Kuma yarinyar taci jarabawa ta, tana Sona sosai I knew it amma kullum tana kokari ta danne don ta tsira da mutuncin ta Ina son Mata Mai Hali irin nata *she's exactly the wife am praying for*........ Ka Basu mamaki Anwar..... Ya bude ido ya dago da sauri..... *I will* wallahi zasu Sha mamaki *trust me*
...... *How I wish ita ma su Kyaleta bazasu fada Mata ba?*
No, is better su fada Mata Anwar kasan Mata da wauta....... Yes ni Kuma ga kishi.... Duk sukayi dariya... Ya Mike tsaye ya buga wata Kara... Wuuuu *Mrs Bushara* wawwwwww!
Sadeeq ya bishi da dariya.
Ko su Hajiya baza su san na sani ba. Sadeeq Zan ba guys din nan mamaki..... Dan ubanka su daddyn ne guys.... Duk suka kwashe da dariya sadeeq yace *Yaro da kudi*...... Ya Kara sa da *Abokin tafiyar manya* suka tafa.
Ya zuki iska ya hurar *Honestly I can't believe we are now husband and wife*..... Kai zanje na kwanta I'm feeling sleepy. Sadeeq ya fada tare da mikewa..... Sadeeq Ina zamu je hado lefe?
Ya banka mishi harara sai Corona tayi sauki Dan ubanka....... Ya kyalkyace da dariya, Shi Kuma ya fice yaja mishi kofa.
Ya fada bisa gado..... Wai ni nake da rawar Kai, zasu karyata hakan da kansu lallai Basu San waye *Bushara* ba.
Ya dauko waya lemme call her idan sun fada Mata nasan she's awake now, idan Kuma basu fada ba tayi barci....
Taci kuka har ta bani tayi lamoo bisa gado, wayar ta Fara Kara a hankali...... Kamar kada ta dauka sai Kuma ta tuna da nasihar daddy cewar Yanzu duk abinda tayi mishi na rashin Jin dadi Allah zaiyi fushi da ita.
Hello.... Ta fada cikin dusasshiyar muryar da Tasha kuka...... *What are you crying for?*....... Gabanta yayi mummunan faduwa Taya akayi yasan kuka tayi?
Um? Ya Kara fada.
Tayi shiru kwallan suka shatato Mata.
Bilkisu? Ya kirata a hankali.
Gabanta ya Kara faduwa tsoron ta daya Anwar ya San ita matar sa Yanzu tasan kawai *Ta mutu* Yanzu ma ya ta Kare dashi bare yasan matar sa ce....... Bazakiyi magana ba?
Ba komi, ta fada a hankali.
*Is that because you missed me?*
Ta buga tsoki..... Ya kyalkyace da dariya to kukan na meye daddy ya dake ki?
Tayi shiru,
Ki jirani karfe takwas da safe Zan zo inji dalilin.....
Ba sai ka zo ba....
Ta fada kamar zata Kara rushewa da kuka.
Saboda me?
Huh?,
Sai da safe Ina son nayi barci.... Karya kikeyi ba Zaki iya barci ba yau..... Gabanta ya fadi.
Bazan iya barci yau ba?
Eh,
Me yasa?
Saboda na tafi na barki.... Ta buga tsoki ya kyalkyace da dariya.
Kilibabba Allah ya kamaki Ashe kullum nabarki sai kinyi kuka ko?
Wallahi a'a .
To kukan meye kikeyi?
Ba komai.
Na Jin dadi kenan?
Eh. Ta fada cikin tsawa ya Kara dariya..... Ko dai ni nayi laifin?
Ta ce hmmm,
Ya lumshe ido, kiyi hakuri toh.
Tayi shiru....
Kinji?
Um,
Ba um Zaki ce ba toh ake cewa, ko inzo nan mu kwana....... Kamm, ta fada tare da latse wayar..... Ya Kama kyalkyatar dariya Yana mirgina bisa gado, dukkan su babu Wanda ya samu yayi barci, Shi Murna ita zullumi.
Yana gama sallar asubah barci Mai bauyi ya daukeshi, sai Sha biyu ya tashi,
Ita kuwa ta tashi idanu kumbure saboda kuka, karfe Sha daya mommy ta tafi airport, daddy Kuma ya na gida saboda hutun Corona virus.
Karfe biyu ya karaso, Rahina ta shigo Aunty ga Uncle Anwar....... Gabanta ya Fadi.
Daman tayi wanka ta Dan gyara fuskar ta har lokacin ana gane tayi kuka.
Yauma da kananan kaya, ya mayar da facing cap din gefe ya rufe idanun sa da bakin goggle.
Jiki ba kwari ta shigo ya kura Mata ido har ta zauna sai kawai ta bashi tausayi.
Ina kwana...... Wuni dai ko?
Yanzu Kika tashi barci ne?
Yana maganar a dake,
Tayi shiru.
Kin dafa mun abinci?
Ta girgiza Kai,
Saboda me?
Yanzu meye zanci toh?
Tayi shiru,
Ke me Kika ci?
Nan ma tayi shiru.
Jeki kawo mun abinda Zan karya..... Ta Mike sim sim....ya bita da kallo.
Ya zuki iska ya fesar tare da Dan zamewa ya kwantar da bayansa a kujera.
Wayoyi kawai yake amsawa har ta shigo da tray a hannu.....kawo nan bazan hau ba table ba.... Okay Zan Kira anjima kaci gaba da lissafi ka turon brake down...
Ya ajiye wayar Yana Mai saukowa bisa carpet.
Indomie da kwai ta kawo mishi da oat.
Ya hada oat din da kansa ya cika Madara yasa sugar kadan ya tura Mata bowl din wallahi tallahi sai kin shanye duka ni zanci indomie din....... Ya Sha mur,.
Zatayi magana ya harareta Zan hada Miki da indomie din Kuma itama nayi rantsuwa... Ai yamun yawa... Ba abinda ya dameni ko zakiyi amai sai kin shanye.
Yaci gaba da cin indomie din yanayi Yana satar kallonta, tana tsakura, tana tsakura har ta daga bowl din ta kafa Kai.... Da kyar ta shanye.
Ya mike zanje Kano anjima sai next week Zan dawo kinji ko?
Toh,
Ya kalleta kinyi zaune ba rakiya ko cikin ya cika da yawa?... Ya karasa maganar Yana dariya..... Ta banka mishi harara ta mike.
Yana tafiya ta koma daki, ashe hada yunwa ta hanata barci ko mintuna 3 batayi ba barcin yayi awon gaba da ita.
....... Kwana biyu ta warware, kullum basa yin waya sai cikin dare.
Hankalinta ya Fara kwanciya saboda sam da alama bai San an daura masu auren ba.
Hajiya ta kasa boye farin cikin ta Koda yaushe maganar ta Bilkisu.....
Ja'iri ashe mace kabi Shi yasa ka dage Kai anan zakayi karatu.... Ya yi dariya Wai waye ya fada miki mace nabi?
Coincidence ne ya hada mu, amma ni ba ita nabi ba.....yaki nuna ma kowa yasan wainar da ake toyawa.
Har suka je sokoto suka dawo bai nemeta a waya ba. Hakan ya Bata mamaki, ta Fara tunani ko daman rashin sanin inda alakar su ta dosa yasa yake yawan takura Mata Yanzu da ya tabbatar magana taje ga iyaye yasa ya Sami natsuwa?.
Har iyayen nata sai da suka fahimci hakan.
Shi kuwa yayi amfani da wannan Dan hutun ya Fara zirga zirgan nemar Mata transfer zuwa University of Abuja. Ko sadeeq bai fadawa ba yasa aka had a mishi transcript dinta cikin sati biyu ya kammala komai. Hatta kayan ta kafff yasa an balle dakin an kwashe sannan ya gyra kofar ya rufe.
Yana jira akoma ya Mata registration......
Ranar da aka koma, ya aika da komai washe gari yazo da takardun gidan su.
Tana ta shiryen komawa, bai Mata waya zai zo ba sai dai suka ganshi kwatsam, ta gama kulewa fushi sosai takeyi dashi saboda kusan sati daya kenan basuyi waya ba.
Yanayinta kawai ya kalla yasan fushi takeyi.
Yana zaune bisa hannun kujera alamar kamar sauri sauri yakeyi, ta Kara daure fuska..... Wai fushin na menene?
Ta mishi banza.
Yayi Yar dariya, kiyi hakuri abubuwa sun mun yawa ne, bana zaune..... Kuma shine baka da lokacin kirana???
Ya Dan yi murmushi to ke ba sai ki Kira ba?
Ko laifi ne Mata ta Kira mijinta..........dammmm gabanta ya Fadi ta kalleshi da sauri yayi murmushi yes tunda na Aiko gidan ku ai kin Zama matata ko wani ya Isa ya shigo Yanzu neman aurenki?
Ta Dan saki ajiyar zuciya, ya kusa sakin dariya..... Nayi missing dinki sosai Bilkisu, Ina ma ciki amma nasan komai na Dan lokaci ne daga ranar da aka mikon ke nasan komai ya Zama labari....... Gobe Zan koma school. Ta fada a hankali.
Keda waye Zaki koma?
Ban sani ba daddy yace na Fara sanar dakai tukun.
Da banzo yau Kuma fa?
Zan maka text.
Saboda me bakya son kirana?
Tayi shiru,
Ya kamata ki rage kunyar nan fa.
Tunda na Aiko gidan nan Bilkisu duk kin canza kinyi sukuku Anya kina Sona?
Ko baki son kiyi rayuwa Dani?
Baki magana?
Kina damuwa ne akan rabuwa dasu mommy??...... Sai kwallah suka zubo mata sharrrr...... Ya Salam ya tashi yaso gabanta , tunanin ta zai kamata kamar yanda ya Saba sai taga ya zauna gabanta ya harde kafa.......
Kinga ki kwantar da hankalinki wallahi Bilkisu bazakiyi dana sanin Aure na ba, bazan taba Bari ki tozarta ba.
Ke shaida ce, duk kudi na da commitment nawa bai hana na baki time din kanki ba, Ina son kula Shi yasa Nima nake kulawa dake, Ina son ki fiye da dukiya ta, wallahi tallahi ko Yanzu da Kika ga na Dan kaurace Miki I wanted to prove your parents how good I am, and how I truly loved you.
Kin San cewar nasan an daura Mana Aure?........ Ta Mike tsaye ta zaro ido, ya Kara Yar dariya yes I knew it and I promised my self I'll never touch you again, tunda an ce *Ina da rawar Kai*
Ta Kara kallon sa da sauri, ya Kara dariya.
Ya Mika Mata takarda ga Shi gobe gobe Zaki je kiga registration officer na nan University of Abuja akwai abinda Zaki karasa, ta Kara zaro ido.
Me kake nufi?
Ya Dan Sha mur, Ina nufin na mayar da ke can anan Zaki gama.... Kai kuma fa?
Ni Zan karasa a dutsinma..... Wallahi ban yarda ba ta Mike tsaye.... Shima ya Mike, wannan shine umurnin da na Baki Kuma abinda na zartar a matsayina na mijinki....... Akan meye zakayi haka?
Saboda na nunawa kowa cewar ba sha'awar ki nake ba sonki nakeyi saboda Allah......Anwar.... Bilkisu kada Kija maganar nan, kada kuma ki sanar wa iyayen ki cewar nasan an daura Mana Aure kawai Ina son ke ki amince da *Ni Anwar son da nake Miki na Aure ne ba na sha'awa ba*.............😄✍🏼
*Zainab wowo maman Abdallah*💖
Masu kirana waya kuyi hakuri ku aiko da sako ta whatsapp👏🏼👏🏼👏🏼
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣3⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
***************
*ABUJA NIGERIA*
...... Falon ya dauki surutai kowa sai fara'a yakeyi da murna.
Alhaji Hassan ya kalli daddy ya ce, ranka ya dade Ina neman afuwa amma Zan yi tambaya....
Cike da fara'a ya ce bisimillah Alhaji.... bisimillah kowa ma na jinka....
Akan daurin auren nan ne, a gaskiya kaina ya daure ban taba ganin irin wannan ba, mun zo neman Aure ne ba Sanya baiko ba, Jin magana ya kawo mu, amma kwatsam ka karbi Kaya da kudi a matsayin kayan Aure da sadaki dan Allah me yasa ka yanke wannan hukunci Kuma ka saka sharadin baka son yaran su sani....
Ya Kara fadada murmushi kafin ya Fara magana Yana kallon Alhaji Muhammad tambuwal, kaga maganar ka ta fito na wata kila su bukaci dogon bayani ko?
Duk sukayi Yar dariya ya maida kallonsa ga Alhaji Hassan ya na magana cikin natsuwa:
Abinda ke faruwa a gaskiya rawar Kan Anwar yayi yawa, tun asalin tura Bilkisu karatu dutsinma na kaita tare da masu tsaronta ba tare da ta sani ba, na baza securities sosai akan sanar Dani duk wani movement dinta.
Lokacin da suka Fara takun saka ita da Anwar na Sanya aka mun bincike akansa, Ashe babu Wanda ma yasan yaron shine *Bushara*, shaidar da ya samu ya sanya ban dauki mataki akansa ba saboda naji cewa yana da halin ko in kula, gadara, Yana Kuma da son addini.
Bayan mun Kai Mata ziyara na hadu dashi sai naga fuskar yaron kamar na Sansa, kwatsam kuwa taron da kamfaninsa yayi a Lagos nagan Shi a daily trust.
Boye boyen daya ringa yi ma Bilkisu yasa na bashi dama amma a gaskiya zafin sa yayi yawa daga baya muka gane kishi ne. Yana da rawar Kai musamman idan Yana tare da ita, ga kuruciya, ga giyar so da giyar kudi kunga komai zai iya faruwa, Shi yasa na yanke shawarar kawai mu daura masu Aure yanda komin ya Kai hannu ya taba ta Yanzu hankalin mu bazai tashi ba matar sa ce.
Dalilin da yasa bana so a fada masu shine, matukar ya ji matar sa ce Yanzu tabbas bazai barta anan gidan ba, kuma a gaskiya bamu shirya aurar da ita Yanzu ba abun yazo Mana kwatsam Babu yanda zamuyi...
Na biyu, wallahi sai ya Mata ciki Kota halin Kaka duk da ba haramun bane Amma ga al'ada irin tamu ta hausawa hakan zaifi dacewa idan ta tare a gidan sa kuma gashi wuri daya suke karatu..... Zahiri, inji Alhaji Hassan.
Yawwah, to Shi yasa na ce mu kyalesu har sai sun gama makaranta sannan tunda saura shekara daya..... Amma wani hanzari ba gudu ba Alhaji Muhammad ya fada...duk aka mayar da hankali wurinsa..
A sanar da yarinyar domin ta san cewa akwai hukuncin Aure akanta, kasan yaran Yanzu kuma tabbas Kun San cewa shaidanu Yanzu zasuyi ta kunno Kai.
A fada Mata sannan a ja Mata kunne a sanar da ita implication na fadawa Alhaji Hamzan ita abun zai ba ruwa...... Kuma fa. Kowa yafada Yana girgiza Kai.
Kenan idan mun fahimceku Anwar din kawai za'a boye mawa?
Haka ya kamata gaskiya daddy ya fada.
Masha Allah hakan yayi Amma dole mu sanar da Hajiya na tabbatar baza ta Bari ya sani ba zahiri..... Hakan Yana da kyau. Duk suka fada lokaci guda.
Nan aka kasa komai aka Basu nasu aka masu Sha Tara ta arziki suka tafi suna Murna......
Tafe suke suna al'ajabin dattakon wadannan mutane, abun ya matukar birgesu Alhaji Hassan yasha alwashin shima zai ma yarsa irin wannan gatan da tsare mutunci.
Tana kwance yau duk ta tashi tana Jin jikinta wani iri babu kwari, ga kasala ga yawan faduwar gaba, tayi lamoo wayar ta tayi Kara.
Tayi shiru don tasan shine kawai zuciyar ta a yau najin haushin sa kadan....ga naci ya dunga Kira ba arziki ta daga...
Hello ..ta fada a hankali.
Ke yunwa nakeji kiyi mun faten dankalin nan da kikayi mun last week.
Kamar ta kurma ihu Shi duniya baida wata damuwa sai ta abinci?
Kinji? Ya fada da karfi.
Naji..
Ya danyi kasa da murya Zan Sami gasassar kaza?
Lokacin ne ta danyi murmushi, ka lissafo kawai abinda za a maka Yanzu zaka Fara Zan Sami kaza?? Sai ka lissafo goma.
Ya kyalkyace da dariya sai meat pie da Dan yam balls Amma kada ki cika mun yaji irin wancen kinji ko?
Naji sai me?
Yayi murmushi sai kiyi kwalliya sosai kisa gyale Banda wannan Dan iskan zanzo don bama zai San fita ta ba.
Ta ce hmmm.
Ya naji kin yi la'asar ko an Fara fargaba ne?
Ta galla ma wayar harara fargabar meye?
Ya Kara dariya ya ce wallahi basan an mako mun harara.
Tayi murmushi hmm Kai dai ka sani.... Kema kin sani kilibabba Anwar na kalbinki amma kina wani sharewa irin ba sosai din nan ba..... Ta kyalkyace da dariya kaiii Anwar Allah ya shirya ka... Hubby zaki ce bagidajiya. Ke wallahi kina Abu kamar wata Yar kauyen kumus.... Tayi murmushi kawai.
Yayi kasa da murya kidan canza mun suna Mana sweetheart....... Kai wallahi Zan ajiye wayar Nan ...ya Kara kyalkyacewa da dariya yace ya hakuri nayi shiru.
Ta zumbure baki.
Yaushe Zamu fita yawo cikin gari?
Ana wannan Corona virus din zaka fita yawo?
Ke ban son unnecessary excuse.... Cutar ce unnecessary???
Ya ja guntun tsoki.... Ko *Amigo* muje please...... Anwar kana so asanya ni a labarai ko?
Yayi murmushi to muje ShopRite nasan kinfi son can.
Ki bari anjima Zan baki labarin abinda ya faru ranar da na ganki a ShopRite din na buya.... Ta zaro ido ka ganni?
Yayi dariya eh,
Fada mun Yanzu,
Ki Bari sai nazo,
Yanzu nake so .
Yayi murmushi. Kin tuna ranar da Kika tarar da securities a bakin kofa kikayi ta fada a Baki wuri??
Ta zaro ido ba munyi waya lokacin ba, Ina kallon ki ai nine a wurin..... Innalillahi.
Ranar ne na biyoki har gida naga address dinki.... Na shiga uku.
Kin fita uku....ya fada Yana dariya.
Yau Zan baki labarai kala kala idan nazo kinji ko?
Tohm, ta fada a hankali.
Sai nazo ko?
Okay.
Ta latse.....
Daddy bai Sami damar shiga gida ba sai biyar saura.
Suna falon sama ita da mommy ya shigo... Ta Mike daddy oyoyo... Bilkisu meye kike dahuwa Kuma naji gidan duk ya hargitse da kamshi?
Mommy tayi karaf tana dariya.... Aikin Anwar ne.
Yayi murmushi da alama kin gaji uwaki wurin kula da miji ....... Maganar ta makale. Yayi saurin canza Babi da kallon mommy muje na ganki ya juya zuwa daki.
Suna shiga ta kalleshi har an daura?
Eh, Amma fa sun kawo shawara..
Ta me fa?
Ya zauna Baki gado, sun ce a sanar da Bilkisun Kuma I reason with them, kin ga yarinya ce karama kada ta je tana janyo ma kanta bala'i ba tare da tasan akwai sharadin Aure a kanta ba Kinga mu Allah zai Kama da laifin rashin sanar da ita tunda Bata sani ba..... Zata firgice gara ayi shiru.
Ba wani firgici kar ki nuna kin sani Ni Zan Mata magana da kaina.... Me zai hana ka mayar da ita nan gwagwalada ta karasa ..... Biyota zaiyi, wallahi Anwar bazai yarda ba.
Shikenan, Yanzu goben zamu tafi sokoton?
Eh, ke zakiyi gaba Zan biyoki bayan kwana biyu tare da Bilkisun.
Shikenan Allah ya tabbatar Mana da alkhairi......ammeeenn.
Bisa bike yazo yau, karar yasa ta fito da sauri ta leka ta taga daidai Yana cire helmet.
Kananan Kaya ne jikin sa, ya ajiye helmet din ya saka facing cap.... Mommy zo kiga Anwar yau a bike yazo.... Ta yi murmushi, daga race ya wuto nan din ko?
Race Kuma?
Eh, kin manta da marece idan mun fita muna haduwa dasu da yawa yaran ministers, president da su Anwar din?
Wai sune?, Hada Shi kenan?.... Gashi Kinga alama.!.
Zata Kara magana ta ce kije tun kafin ya nemeki ta Haye sama abinta.
Yana tsaye bakin kofar ta karaso, bazaka shigo daga ciki ba kayi tsaye?
Ta juya ciki ya biyo bayanta kin yi wa mommy magana Zan daukeki muje yawo?
Ta mishi banza har suka zauna bisa dining.
Kinji?
Ta ce a'a bazamu fita mu biyu ba..... Saboda kada na gudu dake?
Ta Dan kalleshi, Yanzu fa wannan maganar na iya haddasa matsala...kinji?
Kaci abincin Mana..... Ya janyo plate gabansa zanci amma kibani amsa.
Tayi shiru,
Ko na tamabayeta da kaina?
Ta kalleshi da sauri, yayi murmushi Allah kuwa.... Ya kamata kana da kawaici fa.... Akanki fa bani da Shi gara ma ki sani....
Zamu je?
Kaiii Wai Kai me yasa ka fiye naci?
Saboda na turo da maganar neman auren ki.
Ka bari sai Nan gaba....
Family na sunji dadin zuwa gidan nan fa, suna ta mun addu'a da murnar na dace da Mata in shaa Allah....
Ta ce hmm.
Yayi dariya Allah kuwa, an karamta su mood din su ya kasa boye hakan Amma sun dawo da wasu Kaya da goro Wai namu ne Haka akeyi?
Kai ni ban sani ba...... Ya kyalkyace da dariya ke wannan kunyar fa dole ki ajiye ta gefe kinji.... Ta galla mishi harara. Ya Kara yin dariya.....wannan hararar bansan lokacin da za a daina ta ba ko kuwa salon kallon love din naki ne Haka...... Sai kawai tayi murmushi tare da doka guntun tsoki....Kai dai ka sani....kema kin sani. Duk sukayi dariya.
Hajiya na son ganinki duk ta rikice na aika Mata da hotunan ki Wai Bata yarda ba zakuyi video call..... Ina ka Sami hotuna na?
A wayar ki na dauka lokacin Dana tafi da ita kin tuna????
Ta galla mishi harara tun lokacin abinda ke ranka kenan???
Ya kyalkyace da dariya meye ke Raina?
Tayi mishi banza.
Ya Dan gyara Zama ya lunkuma yamball baki kin San fa tun ranar da Kika raba kudin da hahilin nan ya baki class zuciyata ta bani na Sami matar Aure....ta Kara galla mishi harara.
Ya yi murmushi me yasa Wai ranar bakiyi gardama ba Kika bani kudin?
Ta ce hmm.
Anya ba tun tsiwar farko kin kamu da so na .....ta dauki robar ruwa ta Mike kawai ya taso bowl din yamball din a hannu da sauri Yana dariya zo ki daukon meat pie din idan kin gaji da table din..... Nima fa nafi son Zama kasa..... Ya zauna bisa carpet ya Mike kafa.
Ta dauko ita ma ta zauna dan nesa dashi kadan suna kallon juna.... Ya kalleta yace kamar irin Amarya da angon Nan ko?
Ta galla mishi harara. Yayi murmushi, Dan matso Nan kin mun nisa gaskiya... Ta Dan matsa kadan kada taja kuma ya kamota.
Ina son wannan rigar ina Kika siye ta?
Mommy ta siyo mun Dubai...okkay.
Me yasa bazakiyi mun kwalliya da wadanda na kawo Miki ba ko kina Jin kunya?
Tayi murmushi kawai.
Dan Allah ki saka,
Waye telan ki?
Mace ce,can cikin Area 8 ne shagon yake.
Ki debo kayan da Zaki Kai dinki gobe idan mun fita mu biya kinji ko?.....
Nifa bazan bika ba..
Ya kalleta dalili??
Tayi shiru.
Kina Jin nauyin tambayar mommy ko?
Tayi shiru.
Shikenan, Yanzu Zaki iya magana da Hajiya?
Ta danyi kasa da Kai tana murmushi nidai ka jira ba yau ba...
Ya kura Mata ido Anya ba sauri zanyi a daura Mana Aure ba?
Ta dago da karfi... Ya maida bayansa jikin kujera ya Dan kwanta.... Yes, saboda kunyarki tayi yawa gaskiya gara kawai na kawar da ita da wuri don Zaki ringa takurani.
Yar tsiwar ma an daina mun sai uwar harara .......Kai zaka karasa mun karatun?
Waya fada miki Aure na Hana karatu?
Ta harareshi Yanzu ma kana neman kisan Kai Ina ga da Aure Kuma???
Yayi murmushi ko Yanzu ma nikaf Zan siya Miki masu yawa ba shegen da zai Kuma ganin wannan beauty face din ba.... Ta zaro ido nikaf?????
Kwarai kuwa.
Ta zumburo Baki...
Ya danyi dariya ya tashi zaune ko kin fi son kullum ana tashin hankali????
Tayi shiru yaga kamar ranta ya baci.
Ya Kira sunanta a hankali..... Kinji haushi ko?
Ai wannan tsananin ke bana so, kana abu kamar Wanda bai yarda Dani ba kullum...
Yayi murmushi, wallahi na yarda dake.... To me yasa kake da takura?
Saboda *Ina son ki*
Ta kalleshi da sauri.. watau duk lokacin da yake cewa saboda ..yayi shiru abinda baya son fada kenan?
Kin gane ai Yanzu ko?
Ta Dan harareshi kawai. Ya kyalkyace da dariya yace *Bilkisu H. Bushara*........ Ta Kara galla mishi harara.
Sai goma da Rabi yabar gidan.
Tana shiga ta tarar da daddy falon Yana kallon News.
Ta wuce sum, sum, sum..... Zo nan Bilkisu.
Cikin Jin kunya ta karaso ta zauna kasa kusa da kafafun sa.
Anwar din ya tafi?
Eh,
Da alama zaiyi kula sosai ko?
Tayi shiru tana sunne Kai.
Sai dai Shi din ya fiye damuwa ko?
Ta Kara yin shiru tana murmushi.
Ya Aiko da iyayensa kamar yanda na umurta hakan ya nuna tabbas sonki yakeyi da gaskiya.
Amma kina ganin zaman ku makaranta Yanzu a Haka bazai takura ki ba yayi affecting karatun ki ba Bilkisu?
Nima Ina tunanin haka daddy, saboda Yana da rigima sosai..... Na sani.
Ko muyi wata shawara nida ke bazaki fadawa mommy ba?
Eh, daddy. Ta fada da sauri.
Kinga tashin hankalin baya shakkar kowa kada yaje wata Rana ba fata akeyi ba yayi aika aika.....ko ?
Ta daga Kai.
Ko in sa iyayensa su dawo na daura Miki Aure dashi cikin sirri ba tare da ya sani ba?
Ta zaro ido cikin firgici zatayi magana yace jira kiji dabarata.......
Bazamu yarda ya sani ba, dalili kuwa shine irin damukar da yake Miki tabbas Yanzu zai Kara sake salo Kinga hakan akwai haramci Amma idan akwai Aure ko hannun ki ya taba ga Allah babu laifi iyaka kici gaba da nuna mishi Baki so har a Samu ku Gama... Kin gane ai ko?
Ta daga Kai.
Koda wasa kada ki fadawa kowa kinji ko?
Ta ce toh, Yanzu mubi wannan shawarar tayi ko?
Ta daga Kai yawwa,to ungo ya Mika Mata kudi...sadakin ki ne dazun kafin su tafi an riga an daura Miki...... Kudin suka Fadi sai kyarma kyaf,kyaf,kyaf..... Ya Bata labarin duk yanda akayi sannan yaci gaba da lallashinta har ta daina zubda hawaye.
Amatsayin sa na uba na gari ya fada Mata sharuddan Aure don ta kiyaye.........
Tana shiga daki ta fada Kan gado ta rushe da wani irin Kuka Mai tsima Rai.
Anwar kuwa na shawo kwana ya haska sadeeq can nesa bisa wani dakali da alama waya ce yakeyi.
Ko gida bai shiga ba masu gadi suka bude gate da sauri securities suka fito....
Ya sauka yace su shiga dashi ciki ya koma Yana sando a hankali ya nufi gurin da ya hasko sadeeq....
Zaune yake ya bada baya Yana waya.
Ya daga hannu zai bashi tsoro sai kawai yaji Yana cewa...... Wallahi tallahi baba an daura mishi Aure yau.. ya koma ya tsaya tare da rungume hannu.
.... Hajiya ke fada mun Amma basa son Anwar din ya sani..... Gabansa ya bada dammmmm....
Yaci gaba da cewa, wallahi kudin neman aure suka Kai shine mahaifin yarinyar kawai yace sun Isa shaida Aure aka daura... Wallahi kuwa.
Amin amin...
Eh, bana tunanin yarinyar ta sani gaskiya.
A yanda aka ce mahaifin yarinyar ne yace lallai sai an daura auren saboda rawar Kan Anwar yayi yawa..... Eh sai dai mun dawo din. Amma Dan Allah baba kada ka fada ma kowa babu Wanda yasan hakan.
Amin ya Rabbi.
Ya Mike ....juyowar da zaiyi suka hada ido da Anwar din cikin want irin yanayi ya razana ya firgita yayi baya da sauri ..........😄✍🏼
*MAMAN ABDALLAH* 💖💖💖
Assalamu alaikum. Ina Kara godiya ga masoya, Kuma Ina Kara bada hakuri Dan Allah masu kirana a waya a ringa mun chat saboda Kiran Yana hanani typing da wasu ayyuka. Duk wacce ta Aiko da sako Zan gani Zan kuma bada amsa ko amun voice idan bayanin nada tsawo Zan tura Mata hotunan magungunan da bayanan su.
Na gode Ina maku fatan alkhairi.👍🏼
Alawiyya🗣🗣🗣 Aiko da 24 yau an Sami daya as usual😄😄🏃🏻♀🏃🏻♀ *Uwa Mai bada mama, I love you Mom ( Maryam adamu tikau maman amannas)*
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣5⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
******************
*ABUJA NIGERIA*
.... Na rantse da Allah ban aminta ba, sai dai kaima ka dawo nan mu gama tare .... What do you take me for?
Bilkisu...... Da su mufeeda a school Zan Barka acan bana nan?.... Ya zaro ido...
Ta rike kugu billahil azim tare zamu koma FUDMA.... Abinda nake so ki fahimta..... I'll never understand you, amma ka mayar dani shashasha.... Wallahi bazan aminta ba,
Ya harde hannuwa a kirji ji yakeyi kamar ya kamota ya rungume....
Ta banka mishi harara, yanda kake da kishi nima haka nake dashi, dole ka zaba ko nan ko dutsinma Amma kafa ta kafarka....... Ya kyalkyace da dariya...
Ikon Allah Bilkisu ta dawo..... Ta banka mishi harara, Shi yasa ka daina kula ni ka kaurace mun?
Kana son proving meye?, Wannan ne prove? Ai prove shine gani ga ka ba Ina can kana can ba..... Naji maida wukar yanzu zauna ya kike so madam.....
Ta galla mishi harara kaje ka yo cancelling din komai mu koma FUDMA.... Ya maganar Sanya nikaf???? Wannan ce damuwar ka?
Zan saka...... Ya kura mata ido.... Sai Kuma kunya ta kamata ta sunkuyar da Kai..... Ya yi murmushi yace *Akwai chakwakiya*.......
Tayi shiru..... Watau kina son gani gaki ko?
Ni Zaki kure Bilkisu????
Kome zakace sai dai kace amma wallahi ba school din da zance ba tare da Kai ba, idan Kuma ka dage na rantse da Allah sai dai a warware..... Dal!.. ya buge bakin da yatsa... Mutu ka raba yarinya duk yanda kike so haka zanyi what next?
Ta zumbure baki shikenan....
Yayi murmushi yace *nawaoooo*
Har na siya Miki mota wallahi gata can awaje don bana son wani driver kawai da akwai masu binki a baya da tsaronki Koda yaushe..... Sai ka koma da abinka su Kuma ka canza masu aiki.... Ya tuntsure da dariya.... Anya Baki fini kishi ba????
Ta Dan harareshi cikin kunya.
Ya Kama dariya, Watau bazaki yarda gani ga mufeeda bakya Nan ba ko?
Ta rufe fuska nidai ya Isa,
Ya Kara dariya anya wannan semester din Babu damuwa????
Ba wata damuwa,
Ba Kya Jin tsoron anything can happen bayan nasan ke matata ce Bilkisu?
Ta harareshi ashe baza ka iya ba daddyn mamaki ba...... Yayi murmushi Zan iya Mana.
To Kuma.
Ya bi ta da kallo, ya zuki iska ya fesar tare da sakin ajiyar zuciya.
Gaskiya rigimar ki tafi tawa... Ta dan harareshi, but I'll try my best ya karasa maganar Yana murmushi.
Ta Dan sunkuyar da Kai, ya Mike Amma bazaki koma gobe ba sai next week ki fadawa daddy Zan Aiko a daukeki Zaki hau private jet na from Abuja direct to katsina zamu tare ki a can kinji ko?
Ta daga Kai kawai.
Yana Isa gida ya tarar da sadeeq a basket ball ground, ya chabe ball din .... Malam ya akayi ? Ya rike kugu,
Wai kasan nayi wa yarinyar nan transfer taki yarda?
Ka mayar da ita Ina?
Wallahi nan Abuja , ya danyi dariya, could you imagine kishi ke damunta??.... Sadeeq ya kyalkyace da dariya na fada ma miskilanci ke hana Bilkisu nuna maka so amma wallahi zaka Sha wahalar ta idan ta goge ...Amma fa ta birgeni.
Kai ta birge ko Ni sadeeq kasan dai akwai rigima ko?
Babba ma kuwa suka kyalkyace da dariya tare da tafawa.
Ya wurga mishi ball din suka Fara bugawa cikin nishadi.
Yanzu ya zakayi kenan?
Zan siyi gidan nan Wanda naga angama sabo na darawa ko nawane yayi Masa kudin bala'i Zan biya Mata,sai ta zauna ita da Aisha da Maryam Amma banda khausar don bana son yarinyar... Daddy zai yarda?
Dolen sa ma, Zan Sanya Mata masu gadi sosai Nima na siya Mana gida bayan gidan redio zamu bar hostel...... Sadeeq ya buga tsalle amma ka gama birgeni nawan suka tafa suna dariya...
Na Kira VC na fada mishi ayi meeting wallahi duk lecturer din da ya Kara Kira mun Mata Zan daure Shi..... Sadeeq ya zaro ido ai FUDMA sun gama shiga uku Yanzu...... Suleiman Kuma na mishi text na fada mishi na auri Bilkisu kallonta idan yayi ya gama Jin dadi har abada don zai Kare rayuwar sa a prison..... Anwar kada ka firgita makarantar can.... Yayi dariya kawai.
Da mota zamu koma yanzu?
Ya kyalkyace da dariya Kai mota ce dakuwar ka Wai?
To motoci ba mota ba, Zan fito musu a mutum sak!
Nawaoooo... Sadeeq ya fada.
Bilkisu kuwa, Miskilancin ta da zurfin ciki ya hana ta fada wa mommy abinda ya faru ba.
Haka suka taru sukayi Mata nasiha cikin hikima na duk darasin maganar bai wuce ta kiyaye tarayya da shi Kuma ta kula.
*******************
*Federal University dutsinma*
Aisha da Maryam abun ya daure musu Kai, gidan tsoro ma yake Basu, har basa son fita saboda kattin da gewaye da gidan, komai an saka gida abinda ke gida ga masu aikin abinci da gyaran gida.....
Da yake sun rigata komawa da kwana biyu shine yakai su ya masu bayanin anan zasu zauna tare da Bilkisu ranar duk da suka gayyato wata kawa ko namiji wallahi sai yayi maganin su....
Su Kam sunyi tsuru tsuru gashi har yau basuyi waya da Bilkisu ba.
Misalain karfe shidda na marece jirgin ya ajiyeta motoci hudu an musu layi Yana tsaye ya goya hannu a kirji ta Fara saukowa da zumbuleliyar hijab har kasa ya kura Mata ido tun kafin ta karaso ya bude Mata kofa....
Tana shiga ya shiga suka rufe kofa aka fizgesu sai dutsinma.....
Ya kalleta ba gaisuwa hajia?
Ta danyi murmushi,
Kin gaji ko?
Ta ce hmm kawai,
Ya makarantar?
Ta tambayeshi tana kallon fuskar Wayarta,
Lafiya Lau, Amma fa ban shiga ba har yau sai gobe nima Zan Fara zuwa lecture... Ta Dan kalleshi saboda me?
Ya Dan yamutsa fuska haka kawai.... Sai tayi dariya.
Dariyar me kikeyi?
Naga kana mun karairaya kamar mace... Ya kyalkyace da dariya Wai Ina son in birgeki.... Ta dalla mishi harara.... Ya Kara dariya.
Su Aisha sun kagara ki dawo...
Kai meye hadin ka da Aisha???.... Ya zaro ido ya watsa hannuwa ba komai fa....
Sai tayi murmushi,
Anya Bilkisu???, Ya leka fuskar ta.
Ta rufe tana Yar dariya.
Kin iya mota?
Um.
Good, to na ajiye Miki tana nan, zaku zauna keda su Maryam, nima nabar hostel muna bayan gidan redio nida sadeeq, idan daddy ya Miki magana kice ninayi Haka, akwai masu gadi da ma'aikata Amma fa ki sani idan zakiyi mun abinci kada kisa kowa naki nake so kin gane ko?
Ta mishi banza.
Ko bakiji ba?
Karatu nazo ko girki?
Komai ma kinzo yi, kin sani cewa akwai Aure na akanki ko?
Gabanta ya bada ras!
A bakin gate ya fita yabar su suka shiga gidan driver ya fito yabar Mata motar tare da Mika Mata key, ta zaro ido Wai wannan motar ce tawa?
Ya sunya eh Hajia, ta amsa kawai tayi ciki..... Su Aisha suka kwaso da gudu tana ganin su ta fasa ihu itama sukayi ciki suna Murna.........Suka tsareta da tambaya Wai ya Haka?
Ta fada masu ya tura iyayen sa neman Aure Bata sanar dasu akwai Aure akanta ba.
Mufeeda kuwa hauka kadai ke batayi ba da taji Anwar ya siya ma Bilkisu gida ba.
Zuwanta biyu Amma ko layin gidan Bata iya kaiwa saboda body guard, shima ta gano nashi gidan cikin Daren Nan ma securities ne gewaye unguwar.....
Ta dunga kunduma ashar tare da Shan alwashin gobe sai ta ji dalili.
Bakwai suke da lecture ta munafuki Richard, akayi sa'a Aisha ma nada 7am
Suka fito abin mamaki har an goge motar...
Ta kalli Aisha wallahi kunyar hawan motar Nan nakeji Aisha..... Meye na kunya?
Kuma ba ga nikaf kin saka ba?
Kai nasan yau na gama shiga uku makarantar Nan..... Ke muje ni ki ajiye ni kada na makara ta bude motar ta shiga ... Ko Zaki ja mu....??? .... Ni??? Ta daki kirji.
Anwar yau ya mayar dani kauyen mu kike so ko?
Ba yanda ta iya dole ta shiga tare da bata wuta suma suka tayar da mota suna jiran ta fita su bita ( securities biyu ),, ta fita gate din a hankali tana Hawa titi ta chilla da gudu saboda sun kusa makara. Suma suka rufa Mata baya.
Duk da safiya ce duk tsiraren mutanen da wuce sai sunbi motar da kallo.....
Kai Anwar karshe ne, shida sadeeq kasa suka tako, a bakin gate ta wuce su, ya kyalkyace da dariya Sadeeq yarinyar can gudu take da mota fa...
Dan ubanka mu ba ka hana mu dauko ba?
Ya Kara dariya suna ta sauri....
Ta tsaya Aisha ta sauka saboda ba hanyar su daya ba ita ciki zataje Aisha Kuma nan farko farko.
Tana zuwa kowa yayo ma motar chaaaaaa..... Chinayye ta gane ta da gudu ta makale tana fadin Bilkisu oyoyo.....
Ya akayi Kika ganeni?
Ta fada a hankali , haba ya bazan gane ki ba?
Wai kinyi Aure?
Inji waye?
Eh Mana ance you are married woman now....no, not yet. But am engaged... With Anwar??.... Shigowar sa yasa ta Kyaleta, ya rufe idanun sa da facing cap abin mamaki kawai ya wuce baya yaki Zama kusa da ita.
Suleiman ya shigo sai kawai ya chanza layi ya koma can baya saitin Anwar din.
Sai mazurai yakeyi cikin facing cap.
Mugun na shigowa sai cewa yayi test... Hankalin kowa ya tashi, ko ajikin Anwar,
Nan da Nan Bilkisu ta Fara kyarma.....
Question biyu ce, ba Wanda ya sani Anwar kadai ya amsa da kyar Bilkisu tayi attempting ta biyun sai kuwa su chinayye.
Yana fita ya taso da sauri... Kin amsa?
Ta zumburo Baki Ina na sani?
Bakiyi ba kenan?
To me Zan rubuta?
Ya buga tsoki this man .
Nan da nan Yan class suka Fara kallon kallo.
Shi kuwa Suleiman Richard na fita shima yabar ajin.
Ya zauna bisa table Yana kallonta, budo in Miki bayani ya saboda gaba... Ta Mika mishi book din, duk nikaf din ta ishe ta ba yarda zatayi ne.
Ya Fara Mata bayani a hankali ya lura sai mutsu mutsu takeyi yace Wai ya akayi?
Nikaf din nan ta isheni wallahi Dan Allah in cire?
Ya danyi dariya cire Mana .
Ta kalleshi da sauri da gaske ko gatse?
Sai kawai yasa hannu ya cire mata..... Dai dai shigowar mufeeda.... Ta tabbata wallahi, kutumar uba... Anwar da gaske An daura muku Aure da wannan banzar..... Ji kake tasssssssss! Fassss.....ratssssss duk illahirin hankalinta ya bace ta gigice ta kidime shima ya razana ainun ganin Bilkisu tsaye tana wanka Mata wadannan marukan.............na rantse da Allah Akan *Anwar Zan iya kisa* don Haka ki kiyaye... Body guards suka gani cirko cirko nan da nan Yan ajin suka fara direwa ta taga saboda firgici.......✍🏼 Ayi hakuri da kadan.
*maman Abdallah*💖
*uwa Mai bada mama mom ( Maryam adamu tikau maman amannas) mom you are the best I love you so much Mom*
Wadanda ke cewa ba ni ke rubutawa ba a fada wa Mai rubutawa ta ci gaba da kokari Nima Zan dage wajen sharing.....😄✍🏼