*UMMU AYMANA PART 6*
Suna isa Asibitin likitoci suka rufu akanta,wanda da taimakon Allah bata jimaba ta farfaɗo se kuka takeyi,prince kasa rarrashinta yayi.
Koda aka sallamesu ƙin binshi tayi seda ya zare mata ido sannan ta yarda ta shiga motar,jansu yayi zuwa gidanshi nanma dakyar ta shiga cikin gidan kuka kawai takeyi.
Suna shiga cikin falon yajawota ya rungumeta,yana bubbuga bayanta alamar rarrashi,itako kamar me jira ta shiga kuka sosai,cikin kukan ta fara magana.
"Dama mummy karuwace ashe?kaikuma farkanta,wannan wacce irin masiface kuka jefa kanku aciki?wlh da nasan haka kuke bazan zauna ku ci damu da haram ba,in sonta kake meyasa baka aureta ba?".
Kukane ya sarƙeta ta kasa ci gaba da maganar,shi ko Ayman runtse ido yayi kawai yana sauraronta,ya rasa da wacce kalma ze rarrasheta,ƙwace jikinta tayi ajikinshi taja hannun jinior zasu fice daga gidan.
da hanzari yasha gabanta,ya fara magana.
"Hayati zaki iya yimin kowanne irin hukunci in ɗauka amman bazan taɓa bari ki gujeni ba shine hukuncin da bazan yarda dashi ba wlh kinji na rantse".
yana gama maganar yakira securities ɗin gidan ya basu umarni kamar haka.
"Duk ranar da kuka bari wannan ta fita acikin gidannan a bakacin ranku,wlh sena harbeku dukanku".
bejira amsarsuba yaja hannun jinior suka shige ɗaki suka barta tsaye tana kuka.
Suko securities ɗin tsorone ya kamasu sosai,sabida ogansu be taɓa kafa musu doka me tsanani irin hakaba,kuma sun sanshi sarai,duk abinda yace zeyi ba makawa se yayin.
Har dare ummu nanan a falon taƙi shiga ciki se kuka takeyi abinci ma anbata taƙi ci,prince yayi rarrashin har ya gaji,daga ƙarshe fitowa yayi ya sureta gaba ɗayanta ya shige da ita ɗakin,lokacin jinior yayi bacci.
ƙoƙarin kwacewa takeyi amman ta kasa har seda ya shigar da ita,abinci ne ajiye a ƙasa zama yayi sannan itama ya zaunar da ita yafara ɗura mata abincin,in taƙi buɗe baki ya toshe mata hanci,a haka har taci ta ƙoshi,gaba ɗaya ya ɓata mata kaya.
Umarni ya mata da taje tayi wanka,amman taƙi jawota yayi yafara ƙoƙarin cire mata kayan,da gudu ta shige toilet ɗin dariya hakan ya bashi miƙewa yayi ya gyara gurin ya fice a gidan ya nufi gidan ƴarfillo.
koda ya shiga gidan a zaune ya sameta tana gasa bakinta daya kumbura a sakamakon dukanta dayayi ɗazu.
Tana ganinshi miƙewa tayi da sauri,tana neman gurin ɓuya,dan ta ɗauka dukanta ze sake yi.
Dariya yayi sannan yace,
"kishiga ki haɗomin duk wani abu da kikasan na ummu ne da jinior yanzu ki kawomun".
"ban gane ba ina kakai min yara?".
"Namaida ruƙon su hannuna sabida baki da isasshiyar tarbiyyar da zaki basu,yanzu ummu ta fahimci ke karuwace,taya kike tsammanin zan cigaba da barin tarbiyar uwar ƴaƴana a hannunki,ayna kashe kaina inde na bar hakan ta faru".
"What!!!!!"
Ƴarfillo ta tambaya jikinta na ɓari.
Ƴarfillo ta tambaya jikinta na ɓari.
"Nufinka ummu ce uwar ƴaƴanka?".
"ƙwarai kuwa itace uwar ƴaƴana wacce zan aura insha Allahu,".
"kutumar ubancan kayyasa,ashe ko zaayi bura uba kenan,wlh baka isa ka auri ummu ba nice nafi cancanta daka aura,dan haka wlh ko zanyi yawo tsirara se naga bayan duk wata mace dake ƙoƙarin rabani dakai,kasha ƙarya wlh".
Har kumfa ke fitowa a bakinta dan masifa,
Dariya furucinnata ya bashi,dan haka shigewa yayi ɗakin su ummun ya jido komai daya gani,yakai mota,sannan yadawo gurin ƴarfillon yace.
"Ƙe baki isa ki sani ko ki hanani ba,dan haka zan auri ummu koda dagani se itane muke son auran a duniya,kuma ki xuba ido ki gani".
"Hakan ze farune in na mutu,amman wlh ka rubuta ka ajiye,ni ƴarfillo sena rabaka da duk wata mace da ka nuna kanaso,shege ka fasa tsakanina dakai,shiyasa akace in kaga mutum arana inda hali ka ƙara tunkuɗashi ciki dan da zaran ka kawoshi inuwa tofa kai ze wurga Ranar,daga kai har ummu baku san wacece ƴar fillo ba labarina kukeji,da sannu,zan baku mamaki".
bata jira amsarshi ba tashige ɗakinta kamar kububuwa,shi ko dariya yake har yafice a gidan dan tabbas abun abin dariyane.
Kai tsaye gidanshi ya koma koda ya isa gidan tuni ummu tayi bacci,ajiye kayan yayi yabar ɗakin ya tafi nashi ɗakin.
Tundaga wannan lokacin kulawar ummu da jinior ta koma hannunshi,makaranta in zaa kai su akwai kyakkyawan tsaro musamman ummu,ko class ta shiga gefen window da ƙofa duk sojojine,hakan be mata daɗi Amman bata da yadda zatayi.
Anata ɓangaran ƴarfillo ko kwana tayi tana kuka,gami da tunanin mafita,daga ƙarshe de ta samu mafitar,dan kwana biyu da zuwan Ayman,jirgi ya ɗaga da ita zuwa ƙasar china.
Yau tunda asuba marar ummu ke mata ciwo,wanda dama duk lokacin da zatayi period haka takeyi,se murƙususu takeyi a ɗakin ta rasa inda zata sa kanta gashi duk ta ɓata jikinta kasancewar bata da always,ga jinin rushing yakeyi.
kuka takeyi sosai,dan azabar da takeji,jinior ne ya fice da gudu yaje ya faɗowa Ayman.tare suka dawo ɗakin,hankalinshi sosai ya tashi rasa yadda zeyi yayi.
Waya ya ciro ya kira office ɗinsu inda ya bada umarnin a turo mushi soja guda ɗaya ta mace,ayko ba jimawa aka turo masa tana isowa,ta ƙame ta sara masa,amsawa yayi sannan ya mata jagora zuwa ɗakin da ummu take ya nuna mata ita,sannan ya ƙara da cewa.
"Bansan ya zan kula da ita bane shi yasa nasa a turo ki,so pls help me".
Murmushi sojar tayi,sannan tace.
"don't worry oga i will handle this problem insha Allahu,abinda nakeso kawai ka ayka asiyo mana always".
Amsawa yayi da to,ita kuma ta shige ɗakin,ɗaukar ummu tayi kamar jaririya ta shige da ita toilet,shiko Ayman kunya yakeji ya ayki wani siyo always ɗin dan haka da kanshi yaje ya siyo ya dawo,carton guda ya siyo mata na always ɗin.
Koda suka shiga toilet,wanka sojar nan,me suna tamilola tayiwa ummu,sannan ta gasa mata marar da ruwa me zafi sosai wanda dan daɗi ummu har bacci tayi a toilet ɗin,sosai ta samu sauƙin ciwon.
Suna fitowa hakn yayi daidai da shigowar Ayman ɗauke da carton ɗin always,ummu da sauri ta ɓoye a bayan tamilola,itako dariya takewa Ayman,sannan tace.
"Oga wannan always amman harda na haihuwa ko kasiyo?".
Murmushi yayi kawai ya ajiye ya fice,be jimaba ya dawo ɗauke da mopper,ya goge inda ummu ta ɓata da jinin,ba ummu ba har tamilola seda tayi mamaki,shiko ko ajikinshi ya fice daga ɗakin .
Shiryawa ummu tayi tana ta yiwa tamilola godiya musamman da ta fahimci musulma ce ita bayarabiya,sallama ta musu ta tafi,bayan Taba Ayman shawara akan ya kai ummu Asibiti.
Bayan tafiyarta,shiryawa yayi yasa aka kai jinior makaranta shikuma ya shiga ɗakin ummu,inda ya sameta a kwance,koda ya shiga ƙin tashi tayi,zama yayi a gefeɓ gadon sannan yace.
"Hayati ya jiki?ki taso muje asibiti a dubaki a baki magani kinji".
"Ni ba inda zani,ka barni kawai naji sauƙi".ta bashi amsa cikin muryar mara lafiya.
Murmushi yayi ya miƙe yaje ya ɗauko mata takalmi da hijab,sannan ya dawo gurin gadon,hannu ya miƙa mata alamar ta kama,harara ta wurga masa sannan ta gyara kwanciyarta,almar babu inda zata.
"ko ki taso mu tafi kokuma wlh,na ɗaukeki".
Ɗan ƙaramin bakinta ta turo gaba tana ƙunƙuni.
"Au Hayati dan nace kizo muje asibiti shine kike zagina?"cewar Ayman.
ido ummu ta fiddo waje sannan tace.
"Nifa ban zage kaba,kai qurratu aynin nan kacika fitina wlh,da takurawa mutane"ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa.
Murmushi yayi kawai ya miƙa mata hannun ba musu ta miƙa masa nata ya tada ita tsaye,hijab ɗin ta amsa tana juyawa a hannunta,sannan tace.
"Nifa in zan fita bana saka hijabi sallah kawai nake dashi".
"Cabɗi jan nufinki haka zan barki ki yafa gyale ki fita ko ina na jikinki yana juyawa ƙartin banza suna kallemin ke?to wlh bazan iyaba danma kiji".
Baki ta turo gaba sannan ta saka hijab ɗin tasa takalmi suka wuce Asibitin.
Bayanin da likita yayiwa Ayman sosai yaba ummu kunya,dan ji tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki.muryar Ayman ce ta ƙara mata wata kunyar.
"So doctor yanzu dole se in tayi aure mijinta ya sadu da itane zata dena wannan ciwon marar?".
"Haka nake nufi,amman wasu ko sunyi auran be denawa,sakamakon ciwon infection dasuke ɗauke dashi"cewar likita.
Sosai Ayman ya masa godiya ya amshi magungunan da aka bata suka fice,kai tsaye office yace driver ya wuce dasu.
koda suka isa office ɗin,kan kujerar dake office ɗin taje tayi kwanciyarta,shi kuma ya kama aykinshi basu baro office ɗinba se biyar na yamma,suka isa gida.
Da daddare Ayman ya kirata falo dakyar tazo,kuɗi ya bata masu yawa akan ko zata buƙaci wani abu sabida gobe da safe zeyi tafiya zeje kano.
Ummu jiki a sanyaƴe ta amshi kuɗin,gamida yimasa adduar zuwa lfy da dawowa lfy,ta miƙe ta shige ɗakinta,shima nashi ya wuce,bakomai ze kaishi kano ba se neman yardar iyayenshi akan a ɗaura musu Aure shida ummu.
Asubar fari,ya ɗaga zuwa kano wanda tunda ya rabu da fiidah rabonshi da ita.
Sosai danginshi sukayi murna da zuwanshi,ba ma kamar mahaifinshi,kowa se farinciki yakeyi.
Bayan komai ya lafane,ya shige ɓangaranshi,yayi wanka ya shirya,wayarshi tayi ƙara,koda ya duba abokin shine ismail,ɗauka yayi ya koma kan kujera ya zauna,yafara magana.
"mutumina gani a kano fa"
Dagacan ɓangaran ismail yace.
"amman wlh naji daɗin hakan sabida nima jiya na shigo garin,amman yanzu ganinan zuwa gurinka".
Kashe wayar sukayi,inda baa jimaba ismail yazo.
Hira sukeyi sosai,inda ismail yafara jajantawa Ayman game da lalurar da ta sameshi,wacce ta jawo har aka rabashi da matarshi.
Wata shewa Ayman yayi wacce tayi daidai da ƙarasowar mai martaba,sarki ƙofar ɗakin,zuwa yayi dakanshi dan ya tambayi Ayman cigaban daya samu game da lafiyarshi.
Abinda yaji Ayman na faɗi ne yasashi tsayawa shida fadawansa a ƙofar ɗakin.
Acikin ɗakin ko Ayman ne yace.
"Kai wlh lafiyata ƙalau,ba abinda yake damuna kawai na musu takune irinnamu na yaran zamani,tun farko nacemusu bana son Auran amman suka ƙi yarda suka auramin abinda bana so,niko shiyasa namata wayo nasa tazo ta faɗawa sarki wanda nasan ba makawa sarki cewa zeyi a raba auran kuma ilai hakan akayi ,yanzu ma zuwa nayi akan auran danakeso nayi da wacce nakeso"ya ƙarasa zancan cikin dariya.
Dariyarce ta maƙale sanda yayi arba da fuskar me martaba sarki ɗauke da matsanancin fushijikin Ayman rawa ya farayi sabida ko baa faɗa masa ba yasan sarki yagama jin komai.
"Banyi mamaki ba Ayman dan tantiri kamar ka ya aykata abinda ka aykata,yana ɗaya daga cikin ayyukanku maida iyayanku yara,to bari kaji in faɗa maka,wlh tlh blh,inde nine mahaifinka baka da matar aure a duniya se fiddah,ko bayan raina ka auri wata mace bayan ita Allah ya isa ban yafe makaba duniya da lahira"yana gama faɗin haka ya juya ze fita.
A gigice Ayman ya kamo ƙafar mahaifinnasa yana kuka,yafara magana.
"Abba kayimin rai inba ummu bazan iya rayuwa ba hasalima sonta ne yasa nakasa bin abinda kakeso,wlh in kace bazan auretaba mutuwa zanyi".
hankaɗeshi sarki yayi,sannan yace.
"Ayman!!!koda se ka aureta ne zaka shiga Aljannah ƙarshe kenan to wlh bazaka Aureta ba,inkuma ka tsallake maganata Allah ya haɗaka,da masifar da tafi ƙarfinka"be jira amsarsaba yafice daga ɗakin.
Wanda hakanne ya haddasawa Ayman yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme,sarki ko waigowa beyiba ya fice,ismail ne ya nufi Ayman A gigice,ganin baya numfashine yasa ya leƙa waje yakira securities ɗin Ayman ɗin suka ɗaukeshi zuwa Asibiti.
.
Emergency aka shiga da Ayman,likitoci suka duƙufa gurin ceto rayuwarshi.
Shiko me martaba daya shiga cikin gidan matanshi ya kira ya shaids musu abinda Ayman ɗin ya masa,da kuma irin hukuncin daya yanke masa.
Mahaifiyar Ayman ta goyi bayan hakan ɗari bisa ɗari,Hajiya babbace de taja da hukuncin inda tace.
"Haba ranka ya daɗe!taya zaka kafawa ɗanka irin wannan mummunar dokar?yau in ta Allah ta riskeka kuma fiddah ɗin da kakeso ya Aura ba macan arziki bace,ya kake so yayi?ko ko so kake ya dauwama cikin baƙin ciki?".
"Duk abinda zesa Ayman baƙin ciki,zanyi iya bakin ƙoƙarina wajan ganin nasashi a cikin sa,ni akace na bishi ko shi akace ya bini?da har zan kafa masa doka ya karya,sabida ya raina hankali da girmana,wlh kinji na rantse inde ina numfashi,Ayman ya gama Auran wata mace a duniya bayan fiddah,sabida shima yaji irin baƙin cikin da na ji,in kuma ya ƙetare dokata,wlh na sallamawa duniya shi har abada".
Yana kaiwa nan yace musu.
"Kuje na sallameku,kuma duk wacce ta sake ta bishi Asibiti,a bakin Auran ta".
Jiki a sanyaye suka fice a ɗakin,ita kanta yanzu mahaifiyar Ayman se yanzu ta gane illar dake tattare da furucin na sarki,amman basu da zaɓin daya wuce suyiwa abin addua Allah ya sanyaya zuciyar shi.
Acan Asibiti kuwa,Binciken likitoci ya nuna Ayman ya kamu da ciwon zuciya,dan haka suka ɗorashi akan magani.
Tsawon wata biyu ya kwashe a Asibitin sannan ya sami sauƙi,kuma tsawon wannan lokacin ba wanda yazo dubashi acikin ƴan gidansu,ismail ne ds body guard ɗinshi suke jinyar shi,dan haka ya takura akan a sallameshi
koda aka sallameshi daga Asibitin ko ta gidansu be biba ya ɗauki hanyar Abuja,dan kullum da tunanin ummu yake kwana yake tashi,bashi da burin daya wuce yasa ta a idanunshi.
A nata ɓangaran ummu tunda Ayman yayi tafiya ta rasa natsuwarta,kewa da tunaninshi duk sun addabeta,ga gabanta dayake yawan bugawa wanda yasa ta shiga cikin tunani inda take ganin duk inda Ayman yake bashi cikin kwanciyar hankali.
Kullum cikin yi masa addua take ta rasa da wanne zataji,in ta gaji tayi kuka jinior ya tayata,kullum haka suke.
Yau ko tunda ta tashi gabanta ke faɗuwa,ta rasa dalili,dan haka seta duƙufa addua akan Allah yasa alkhairine.
Da misalin ƙarfe tara na dare Ayman ya iso garin Abuja,direct gidanshi aka wuce dashi,bayan sun sauke ismail a nashi gidan.
Koda suka iso gidan,shi kaɗai ya shiga cikin falon gidan,a daidai wannan lokacin ummu na zaune,a falon tana aykin tunaninshi,shiko jinior tuni,ya jima dayin bacci a ɗakin.
Sanye take cikin rigar baccinta,maroon colour,da kaɗan ta wuce mazaunanta,tasa rigar ne kasancewar taga su kaɗaine a gidan.
.Ayman da sallamarsa ya shiga falon,Ummu a gigice ta ɗago kanta dan ganin shi ɗinne da gaske ko gizon daya saba matane,ganin shi a tsaye yana mata murmushi ne ya sata kwalla ihun murna sannan ta rugo da gudu ta rungumeshi,sam ta mance kalar shigar dake jikinta,shiko Ayman tunda ta taso da gudun yaga yadda rigar tayi a jikinta,ƙwaƙwalwa da numfashin shi ne suka tashi Ayki na wasu ƴan mintina,sanda ta rungumeshi na shanunta suka haɗu da ƙirjinshi kusan faɗuwa yayi,dan faruwar hakanne ya jefashi cikin wani yanayi wanda be taɓa samun kanshi a ciki ba.
Itako ummu dan murna har da ɗan dukan bayansa take sosai tayi murna da dawowarsa,shiko ɗagata yayi yana jujjuyawa da ita a falon a haka har suka ƙarasa ɗakinshi.
Kai Abu tun,ana na murnar ganin juna har yazo ya sauya darasi,bakin Ayman na hango acikin na ummu yana kissing ɗinta,yadda yake kissing ɗin da gani kasan baya cikin hayyacinshi.
cak ya ɗagata ya ɗora a kan gado,yaci gaba da sarrafata,ummu irin matannanne masu ƙarfin shaawa da zaran namiji ta taɓesu,basa iya controling kansu,bare kuma yanzu da abin ya haɗu da sharrin so,ga shaiɗan acan gefe yana buga musu ganga.
Ayman fa besan a wacce duniyar yake ba,tuni ya jima da fatali da duk wata sutura dake jikinsu,ci gaba yayi da sarrafata ta yadda yake so,sanda bakinshi ya sauka akan.....yafara sucking,ummu numfashinta har ɗaukewa yakeyi,take ta fara ambaliya,ganin hakane yasanya Ayman cilla kwallonsa a raga.
Se a wannan lokacin tunanin ummu ya dawo gareta,wanda shi kuma Ayman ya rasa nasa a daidai lokacin,kuka take na neman ya kyaleta amman ina bemasan tanayi ba,hasalima yadda take kukan shima kukan yakeyi.
be saurara mata ba,seda ya sami biyan buƙatarshi,se alokacin ya fahimci abinda ya aykata,a firgice ya ɗagata ya diro a gadon,dan gani yake kamar mafarkin daya saba yine,sanda ya tabbatar ba mafarki yake ba,rushewa yayi da kuka matsananci yana buga kansa da bango faɗi yake.
"Na shiga uku,Abba ka cuceni,meyasa Abba kamin haka,me na maka,dan kawai nace banason zaɓinka,gashi ka janyo nayi abinda har na mutu bazan dena nadamar aykata shiba,why Abba,yau ina zan saka rayuwata",cigaba yayi da buga kansa a bangon,har seda ya fashe jini ya wanke masa fuska amman be denaba.
Ummu dake kwance tana kuka na baƙin ciki wai yau itace aka maida ita cikakkiyar mace ba ta hanyar aure ba,se yanzu danasanin zama a gida ɗaya da Ayman ya kamata,tabbas sunyi kuskure,a matsayinsu na masoya hakan ba daidai bane sabida so abokin shaiɗanne,dan gashi yau yakaisu ya baro su.
Ganin Ayman na ƙoƙarin kashe kanshi ne yasa ummu ta miƙe da kyar ta maida rigarta ta nufeshi,dafashi tayi itama tana kuka,waigowa yayi dan ganin waye ganin itace da sauri ya rungumeta yana kuka yana faɗin.
"Ki gafartamin Hayati,na cutar dake nasani,amman don Allah ki yafemini zan iya kashe kaina in baki yafeminba"kukane yaci ƙarfinsa,wanda itama kukan takeyi,da kyar tace.
"Qurratu Ayni,bani kayiwa laifiba,hasalima ni da kai duk masu laifine,Allah mukayiwa laifi,dan haka gurinshi zamuje neman tuba,in kuma akwai wani laifi da kamin na yafe maka duniya da lahira"kwace jikinta tayi a nashi tana kuka ta fice a ɗakin ta nufi nata,jikinta ta tsarkake sannan ta dawo ts kwanta akusa da jinior ta rungumeshi tana kuka me tsuma zuciya.
So da ƙauna,da son ganin mahaifiyarta,na ƙara bijirowa zuciyarta kamar kullum.
Ranar kwana sukayi kowa zuciyarshi ba daɗi babu kamar Ayman wanda cikin dare zazzaɓi ya rufe shi yayi kuka har hawaye ya ƙafe a idonshi,yayi nadama taƙin ƙarawa,tsoron Allah da abinda ya aykata su suka kamashi.
Ranar kwana sukayi kowa zuciyarshi ba daɗi babu kamar Ayman wanda cikin dare zazzaɓi ya rufe shi yayi kuka har hawaye ya ƙafe a idonshi,yayi nadama taƙin ƙarawa,tsoron Allah da abinda ya aykata su suka kamashi.
Ummu Aymana ko gani take ƙarshen jin daɗinta ne yazo,shiyasa hakan ta faru da ita,koma menene tasan hakan yana daga cikin ƙaddararta,inda Allah be ƙaddaro mata ba baze sameta ba.
Yanzu ba abinda takeso da buri irin taga mahaifiyarta,shine kawai burinta,dan bata ji zata iya ci gaba da zama tare da Ayman.
Washe gari tinda asuba Ayman ya samu waya daga office ɗinsu akan ya shirya,takarda ta fito da sunanshi acikin wainda aka tura course ƙasar jamani,na tsawon shekara guda.
Sam Ayman beso hakaba dan yanaso ya zauna ya ba ummu kulawa dan yanaso tayarda ba kowane dan yasan mace a waje yake gudunta ba musamman su da ƙaddara ta faɗa musu.
Koda gari yayi haske kowa cikinsu na kunyar haɗuwa da ɗan uwansa,haka Ayman ya shirya ya fice gurin Ayki,inda aka bashi takardar shi ta tafiyar nan da kwanaki uku masu zuwa.
wuni yayi a gurin Ayki inda daga ƙarshe de ya daure yakira hajiya Babbah ya sanar da ita tafiyar da ze yi ƙasar jamany,fatan Alkhairi taimasa,sukayi sallama.
Tana kashe wayar taje ta shaidawa me martaba,shiko beyi ƙasa a guiwaba yakira amininsa akan gobe yanaso a maida Auran,dama sun daɗe da zancan maida auransa da fiddah.
Haka akayi washe gari aka maidar da auranshi da fiddah batare da saninsa ba,akaro na biyu,se kiranshi Sarki yayi ya bashi umarni akan kar ya sake ya tafi batare daya tafi da fiddah ba .
Ayman be damuba dan yanzu ya gama yarda mahaifinshi yafi kowa ƙinshi a duniya,hasalims godiya yamasa.
Fiddah ko tayi rawa tayi juyi na murna anmaida auran ta,salmab ko baa magana sosai ta tayata murna gamida shawarwari.
Ayman visa tare da fiddah ya nema,kuma yasamu,dakyar ummu ta tarda tazo sukayi sallama inda ya miƙa mata ATM card ɗinshi ya kuma faɗa mata pin ɗin Gami da mata alƙawarin komai wiya komai rintsi ze dawo gareta ya aureta,ta riƙe mushi kanta amana,kuma ta rufe sirrinsi,.
Haka suka rabu suna kuka,sosai ummu taji ɗacin tafiyarshi bataso yafara tafiya ba ita taso tafara gudunshi,amman tsarin Allah shine daidai,fatan alkhairi ta masa sukayi.
.washe gari da safe Ayman ya wuce airport yana isa fiddah ma ankawota jirgi is ready shiga kawai sukayi suka ɗaga ƙasar jamany.
Safe trip Ayman.
.
Ummu Aymana bayan tafiyar shi ji tayi duniyar ta mata girma tanaso ta fita neman mahaifiyarta amman batasan ta inda zata fara ba gashi tana tsoron zuwa garinsu dan batasan me zasuyi mata ba.
Haka ta haƙura taci gaba da addu'a,akan Allah ya bayyana mata ita aduk inda take cikin sauƙi.
Ayman tunda suka isa jamany a wani gari me suna Balyn,ajiye fiddah yayi a gidan da aka bashi shi kuma ya haɗa tarkacanshi ya koma hotel da zama.
Waiwaye.
Ƴarfillo ta isa ƙasar china da niyyar ayiwa Ayman Asirin da ze manta da ummu har ƙarshen rayuwarsa,ita kuma asa sonta a zuciyarshi kota halin ƙaƙa.
Tayi nasara inda aka gudanar mata da duk abinda take buƙata akace ta jira lokaci kawai.
Ayko farinciki a gurinta baa magana,zamanta tayi a ƙasar,acewarta se ayman ya nemeta,zata ɗawo.
Kullum cikin saurare take taga Ayman ya nemeta,shiyasa wayarta bata canja number whatsapp ɗinta ba sabida tadan in ya kirata be samuba ze mata magana tacan.
Wannan kenan.
Bayan wata biyu da tafiyar Ayman,ummu gaba ɗaya ta rasa abinda yake damunta,ko sunyi waya da Ayman cikin tambayarta yake abinda ke damunta amman ta rasa abinda ke damunta kwatakwata bata jin daɗin jikinta,hakanne yasa yace ta jira ze turo doctor ya dubata.
Ayko haka akayi yaturo maya likitanshi,gwajin farko likita ya tabbatar mata tana ɗauke da ciki har na tsawon watanni biyu.
Ummu ji tayi kamar a mafarki likitan yake shaida mata wannan saƙon na baƙar qaddara,gudun tonawa Ayman Asirine yasa ta danne duk damuwarta ta nuna tayi farinciki,sabida Ayman ya turo shine da sunan ita matarshi ce.
likitanne ya kira Ayman ya masa albishir da ƙaruwar daya samu.
Hasbunallahu waniimal wakil,itace kalmar dake fita a bakin Ayman har likitan ya masa sallama besan me yakw,cewaba seda yaji wayar ta cinke sannan.
Kuka ya rushe dashi kamar yaro yana faɗin.
"ka gani ko Abbah kaga abinda kajawowa zuriar ka ko,da akwai rabon haihuwa a tsakaninmu kuma rabon yana kusa ne amman ka hanani raya sunnar maaiki da ita,kasa na raya sunnar shaiɗan sanadin haka harda rabo,why Abba,me na maka har haka,wlh fiddah da kakeso na raya sunnar da ita hakan ze farune amman da gawata".
Haka yay ta sambatu shi kaɗai yana kuka ya rasa inda zesa kansa har zuwa dare.
Ummu ko da ƙyar ta iya tashi a inda take kuka take me tsuma zuciya.
Se dare Ayman ya samu ya kirata.
.tana ɗagawa ta rushe mishi da kuka faɗi take.
.tana ɗagawa ta rushe mishi da kuka faɗi take.
"am finish,qurratu ayni,am finish".
Cikin kuka shima yake bata amsa.
"No hayati,you are still my life,my wish,my happiness,without you am nothing,pls stop saying that my heart is burning,faruwar hakan ya ƙaramin sonki a zuciyata,wlh ina tare dake,kuma don Allah karki salwantar da abinda ke cikin ki Allah ya fimu sanin,dalilinsa na wanzar dashi a tsakaninmu,ki soshi kibashi kulawa tamkar sauran ƴaƴa,wlh hayati ba abinda ya ragu a son da nake miki,ina sonki keda abinda ke cikin ki don Allah ki tayani sonshi"ya ƙarasa maganar cikin kuka.
"tabbas nasan jarabawace Allah yakemin tun daga ƙuruciyata har zuwa yanzu,na godewa Allah da zaɓata da tayi yake kuma gwadani,ko kaɗan bazanyi baƙinciki da abinda Allah ya tsaro a rayuwata ba,cikin jikina bashi da laifi bashi ya kawo kanshiba,kawoshi akayi ya zama izina agaremu,dan haka na godewa Allah daya nunamin kuskurena tun a duniya".
Haka sukai ta kuka a wayar da kyar Ayman ya rarrasheta tayi shuru,sukayi sallama akan ze kirata anjima.
Sede me suna gama wayar saƙon da ƴarfillo ta turo masa na ya manta da Aymana ya iso gareshi.
ya ajiye wayar kenan yaji kamar anbuga mishi abu akai,kawai se yafara mamakin abinds ya sashi kuka,a iya bincikensa ya rasa dalilin kukan nasa.
Cikin dare tunanin ƴarfillo ne ya takura zuciyar Ayman,ji yake kamar ze mutu in beji muryarta ba.
waya yaciro yakirata be shigaba hakanne yasa ya turamata voice note ta whatsapp.
Kamar a mafarki ƴarfillo taga saƙon Ayman,ihu tasa na murna,daganan ta tura masa numbern ta na china.
Wasa wasa soyayya ta shiga tsakaninsu me ƙarfi,Ayman ko bacci baya iya yi in beji muryarta ba.gaba ɗaya sungama tsara yadda zasu gudanar da rayuwar auransu inda Ayman yayiwa ƴarfillo alƙawarin auranta da zaran ya dawo gida nigeria,fiddah ko kota kirashi baya ɗauka sabida ya tsaneta,ita ko ummu gaba ɗaya ya manta da ita da labarin ta.
Baiwar Allah ummu yau wajan watanni biyar kenan rabonta da jin muryar,Ayman ko ta kirashi bata samu,faɗin tashin hankalin da take ciki baze misaltuba,ga cikinta yanzu ya tsufa dan watansa bakwai.
Kullum cikin addua take akan Allah ya sauketa lfy,ba abinda yafi mata daɗi da ta samu ta gama secondry school ɗinta tun cikin na ƙarami.
Rayuwa ta fara yiwa ummu zafi sabida ko securitie ɗin da Ayman yasa A gidan yanzu babu su,uwa uba ATM card ɗinshi in taje cire kuɗi bazasu ciruba.
Ayman ganin yana zaune besan dalili ba sede yaga ancire kuɗi a account ɗinshi ne yasa yayi magana da bankin akan a dakatar da account ɗin har se ya dawo,danshi besan wanda yake cire kuɗinba.
Sannu a hankali ummu ta fara siyar da duk wani zinari nata dan ta samu ta rufawa kanta asiri da ƙaninta, shima kamin wani lokaci kuɗin sun ƙare.
Yau Ayman yayo waya ga megadin gidan nashi wanda su Ummu ke ciki ya bada umarnin a kulle masa gidan dan aciki ze ajiye fiddah itako ƴarfillo sabo ze gina mata yadda zasu ji daɗin rayuwarsu.
Me gadin abun ya bashi mamaki sabida yadsn akwai ummu aciki,amman be ce komaiba ya amsa umarnin ogan nasa,cikin gidan ya nufa dan ya sanar da ummu saƙon oga.
Ita ko ummu tun cikin dare take fama da ciwon mara,kasancewar watan haihuwarta ya tsaya,amman dayake batasan ya abin yakeba haka tai ta murƙususu ita kaɗai har zuwa lokacin da me gadin yazo.
Lallaɓawa tayi tazo kiran megadin,koda ya sanar da ita saƙon Ayman to kawai tace,dan tasan ze iya yimata abinda yafi hakama tunda ya iya gudunta sanda ta fi buƙatarsa.
cikin gidan ta koma dakyar ta iya haɗa kayansu taja hannu jinior suka fice a gidan tana kuka ga mararta dake ciwo kamar zata fashe,dakyar take iya ɗaga ƙafa.
Sun ɗanyi tafiya me tsawo taji bazata iya ci gaba da tafiyarba,kasancewar gurin akwai yalwar bishiyoyi ,gindin wata bishiya ta ƙarasa dakyar,kuka take jinior na tayats,abun gwanin tausayi,ummu ji take kamar zata mutu.
Unguwar ta manyan masu kuɗi ce dan Anan Gidan shugaban ƙasa ma yake,inda ummu take kwance ƙofar wani gida ne,me ɗan karan kyau kai da ganin gidan kasan meshi yaci ya tada kai.
Haka ummu taita fama ga faya ta fashe amman haihuwa shuru zuwa lokacin har numfashinta yafara sarƙewa.
jin ƙarar buɗe get ɗin gidanne yasa jinior rugawa da gudu gurin,wata arniyar motace ta cinno hancin ta waje,da sauri jinior yasha gaban motar yana kuka.
Da sauri na cikin motar ya fito,saurayine,kyakkyawa na ajin farko wanda kallo ɗaya zaka masa kasan naira najin tsoronsa.
Ƙarasowa yayi gurin jinior yana tambayarsa lafiya.
Shiko jinior yana ganin mutumin ya fito da sauri ya kama hannunshi yafara janshi har seda yakawoshi inda ummu take kwance.
Agigice mutumin ya ƙarasa kusa da ita,taɓata yayi amman ina ko numfashi batayi a gigice ya ɗauketa ya nufi motarshi da ita yayinda jinior ke biye dashi abaya.
Gudu yake na fitar hankali har ya iso Asibiti.
Daga saman Asibitin an rubuta,
*Doctor Na'im Chiroma,Special Hospital.*
*Doctor Na'im Chiroma,Special Hospital.*
yana parking da sauri ya ɗauketa yayi cikin Asibitin da ita,duk wani maaikaci na Asibitin seda ya kamu da tsananin mamaki na ganin doctor ɗinsu ɗan ƙwalisa ɗauke da me tsohon ciki kuma yana kwasar gudu mutumin dako sauri be iyaba.
Kai tsaye labour room ya shiga da ita,duk wani abu daya dace shi ya mata har ya samu numfashinta ya dawo,ruwan naƙuda ya ɗaura mata.
kamin wasu mintoci ummu tafara kukan neman taimako,hannun shi ta riƙe da ƙarfi tana salati,gaba ɗaya tausayinta yagama cika shi,injin scarning ya matso dashi kusa da ita inda yafara yimata scanning ɗin dan ganin yanayin kwanciyar yaron.
Ilai kuwa yaron a karkace yake,dan haka hannu yasa ya gyara mata,ummu ji tayi kamar zata mutu,sanda yake gyara kwanciyar yaron.
Ba jimawa Allah ya sauketa lafiya,inda ta haifi ɗa namiji tamkar Ayman ne yayi kakin yaron.babu,wata halitta ajikin yaron wacce ba irin ta Ayman bace.
muje zuwa.
.
Murna sosai Doctor yayi da nasarar daya samu,ta ceton ran ummu da abinda ke cikinta.
Shiko jinjirin se tsala kuka yakeyi alamar dake nuna yana cikin ƙoshin lafiya.
Ummu tayiwa Allah godiya daya turo me taimakonta,ta kuma gode masa daya rabata da cikin lafiya.
Dayake Asibitin private ne komai akwai a ciki dan haka kayan jarirai doctor ya bada umarnin a kawo,ayko ba jimawa nurse har ta gama shirya babyn ta kawowa doctor shi.
Gurin ummu ya kaishi wacce fitowarta daga wanka kenan.
"madam hala haihuwar fari ne wannan naga tunda yazo duniya baki buƙaci a kawo miki shi ba,kinajin kunyar shi ne?"doctor Na'im ya wurga mata tambayar yana dariya.
Ɗago ido ummu tayi ta kalleshi,ji tayi gabanta ya faɗi da sauri taƴi ƙasa da idonta tana murmushi.
miƙa mata yaron yayi,hannunta na rawa ta amsheshi,tana amsar yaron ya buɗe ido yana kallonta,yana turo harshenshi waje.wani matsanancin kukane ya kufcemata,rungume yaron tayi cikin kuka take faɗin.
"Na gode maka Allah daka bani shi,babu bsƙin ciki a zuciyata na game da samun shi,Allah ka gafartamin laifin dana aykata na samar dashi,ya Allah albarkacin naƙudar haihuwar sa danayi,da rainon cikinsa da nayi,ya Allah ka dubeni ka gafartamin na tuba ya Allah natuba"ta ƙarasa zancan cikin matsanancin kuka.
Gaba ɗaya kan doctor ya gama ɗaurewa gameda furucin na ummu,yana buƙatar ƙarin haske game da hakan amman ya barwa cikin shi.
Miƙewa yayi ya fice yaje ya shigo da jinior,da gudu jinior yaje ya rungumeta yana kallon babyn yace.
"lah Aunty kin siyo mana baby ne?".
kai ummu ta ɗaga masa wasu hawayan na ƙara biyo fuskarta.
Ɗakin hutu aka kaisu,se a lokacin ummu ta ciro nono taba babyn ay kamar jira carab ya cafke yafara sha,tanajin zafin tsotson da yakeyi amman ta daure sabida tasan in ta shayar da yaron ma Allah ze ƙara yafe mata.
Da daddare doctor ya shigo ɗakin,lokacin jinior har yayi bacci ummu da babyn ta ne kawai idonsu biyu,tana riƙe da hannun babyn tana kallonshi shima ita yake kallo abin gwanin sha'awa.har doctor ya samu guri ya zauna ummu batasan ya shigo ba hankalinta nakan babynta wanda da gani zeyi wayo sosai.ba abinda yake ƙara faranta ran ummu se kama da yaron yakeyi da Ayman,wanda tasan ko giyar wake yasha be isa yace ba nashi bane.ɗauke babyn da akayi shi ya dawo da ummu cikin hayyacinta a gigice takai raruma zata kwace ɗanta,ganin doctor tsaye akanta riƙe da babyn shi ya haddasa mata jin kunya.
"wannan kalar soyayyar da kike nuna masa ita zata sa ya ganeki da wuri mu kuma uncles ɗinsa ya dunga yimana ƙiwya".
Ummu de murmushi kawai takeyi,ta kasa magana,har seda doctor ya sake jefo mata tambayar data hargitsa kayan cikinta.
"Madam zuwa yanzu ya kamata ki sanar dani inda ƴan uwanki suke domin aje a sanar dasu halin da kike ciki musamman baban yaron nasan yana can cikin damuwa".
kuka ta rushe dashi me tsuma zuciya,cikin kukan take faɗin.
"Dama duk abinda ka tambaya ina dasu dana shaida maka inda suke,wannaɓ ɗan da kake gani babanshi be damu ɗashi ba,hasalima ya gujemu tun cikinshi na wata biyu bamusan inda yake ba,ƴan uwa kuma bani dasu ksga kenan babu wani wanda hankalinshi ke tashe da rashin ganin mu,da ace mahaifiyata na kusa dani shine zan iya faɗa mata komai game da ɗana,dabida uwace kawai zata iya share kukan ƴarta"ta karasa faɗi cikin kuka.
Tausayinta ne ya mamaye zuciyar doctor,cikin sanyin murya yace.
"na gamsu da bayananki,amman ina roƙon,alfarmarki da ki bari in kawo mahaifiyata gareki domin ta share kukanki,mahaifiyata mace ce me tsoron Allah,dason ɗan da ba nata ba fiye da kanta,namiki alƙawari inde ta muamalanceki zaki iya mantawa ma da taki mahaifiyar"ya ƙarasa zancan yana dubanta cikin tausayawa.
"ko baka yabi mahaifiyarkaba nasan mutuniyar kirkice ta lura da irin kirkin ɗanta,na amince ka turota gareni,amman batun mantawa da tawa mahaifiyar abune me wuya"ta sake fashewa da kuka.
"to nagode da damar da kika bani,yanzu zan wuce zan tafi da wannan ƙaramin dan,asamu ayimasa wanka,amman se kin amince".
"Doctor kenan!ay tunda ka iya ɗaukomu batare danasan inda kaina yakeba kataimakemu baka cutar damuba to banajin zaka iya cutar damu sanda na dawo cikin hayyacina,dan haka kaje dashi ɗin".
Murmushi yayi sannan yace, "to nagode da yarda dani".
Miƙamata babyn yayi sannan ya ɗauki jinior yafice daga ɗakin.
Kai tsaye gida ya nufa,yana parking ya ɗauki jinior ya shige dashi cikin gidan a falo ya sami mahaifiyar tashi se safa da marwa takeyi.
yana sallama ta nufeshi a gigice tana faɗin.
"Haba ɗan umma yanzu dan Allah abinda kayi ka kyauta kenan taya zaka tashi ka kashe wayoyinka kuma kaje kayi zamanka a waje har ƙarfe goma na dare"ta faɗi cikin damuwa.
Se a lokacin ta lura da jinior dake rungume a kafaɗarshi,da sauri ta miƙa hannu ta karɓeshi,tana tambayarsa ina ya samo ɗa.
Shiko jinior matar na karɓar shi a hannu doctor ya buɗe idonshi a firgice,ƙureta yayi da ido,itama kallonshi take cike da mamakin irin kallon da yaron yake mata,zuwa can kuma se jinior ya saki ajiyar zuciya yakwantar da kanshi a ƙirjinta gamida riƙe mata riga alamar dake nuna yana gudun a kwace mishi ita.
Murmushi doctor yayi sannan ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar da ita,Allah sarki baiwar Allah harda kukanta,sallama doctor ya mata ya wuce ɗakinshi ita kuma ta haura sama ɗauke da jinior.
Ko cikin dare al amarin jinior ci gaba yayi da ɗaure mata kai,dan gama miƙa hannu yake cikin rigarta,kamar yadda yara suke in suna buƙatar nono,gefe ɗaya kuma hannun shi ɗayan na riƙe da rigarta,tausayin shi ne ya kamata gamida sonshi,tabbas ta fahimci yans cikin kewar mahaifiyarshi ne shiyasa yake mata hakan,rungumeshi tayi sukayi bacci.
washe gari da wuri suka tashi sabida zasuje asibiti gurin ummu.
gurin me gadi doctor yaje yasashi ya ɗauko jakar kayan su ummu,wacce suka bari tun jiya a ƙofar gidan.
Hajiyar shi ya kaiwa ta buɗe ta cirowa jinior kayan daze saka sannan ta ciro na me jego tamayar ta rufe,da kanta tayiwa jinior wanka dan so ds tausayin yaron tun daran jiya suka gama cika zuciyarta,shirya shi tayi tsaf ts bashi abinci yaci,sannnan doctor yazo ya ɗauki kayan abincin da ta shiryawa me jego na abinci,suka fice zuwa Asibitin.
Koda suka iso Asibitin maaikatan Asibitin se duƙawa suke suna kwasar gaisuwa gurin mahaifiyar doctor ahaka suka nufi ɗakin da ummu take.
Ummu wacce ke tsaka da baccinta ita da babynta a gigice ta farka,kamar wacce aka tsoratar,gabantane ya shiga faɗuwa da ƙarfi,miƙewa tayi tsaye,hakan yayi daidai da shigowar su doctor.
Kallon kallo suka shiga yi tsakanin ummu da mahaifiyar doctor,kallo irin nason gano a inda suka san juna,a lokaci guda suka tuno.
ƙara ummu Aymana ta ƙwalla tana faɗin,
*UMMA NA !!!!!*.
*UMMA NA !!!!!*.
bata ƙarasa faɗi ba duka suka yanke jiki suka faɗi sumammu.
A gigice doctor ya nufi mahaifiyarshi yana kiran sunan ta amman ina ko motsi batayi, a sukwane ya fice a ɗakin zuwacan se gashi ya dawo da kayan ayki da nurse na biye dashi da gudu.
Kai da ganin yadda doctor ya ruɗe ya gigice kasan akwai soyayya me ƙarfi tsakaninshi da mahaifiyar tashi.
Ceton ransu suka shigayi gaba ɗaya,wanda ba jimawa dukansu suka farka.
Ummu kuka umma kuka,rungume suke da juna dukansu,ba abinda sukeyi se kuka ganin hakane yasa doctor ya tattara su gaba ɗaya suka wuce gida,Dan karsu tara masa mutane.
Koda suka isa gidan basu bar kukanba ,gaba ɗaya sun saka doctor cikin damuwa da ƙyar ya samu sukayi shuru sannan umma ta fara magana.
"Haƙiƙa na yarda Allah maji roƙon bawane tunda Allah ya bani lafiya nake nemanki ƴata,Allah be haɗamu ba se yanzu nagode masa daya sadani dake,sede na shiga damuwa ganinki ɗauke da yara har guda biyu wanda ban sanki dasuba ko kinyi Aurene?".
Kuka ummu ta fashe dashi ta rungume mahaifiyarta,ta kamo hannun jinior tasa ana umman tace.
"Umma wannan ɗanki ne na cikin ki,ke kika haifeshi,ranar da kika haifeshi kika ɓace ban sake ganinki ba se yau,shi kuma wannan jinjirin....."se ta rushe da kuka ta kasa ƙarasa maganar.
da kyar tasamu kukan ya barta tace.
"shi kuma wannan jinjirin umma ɗana ne wanda na sameshi bata hanyar aure ba"ta sake rushewa da kuka.
Ba umman ba doctor kanshi seda ya faɗo daga kan kujera.
.Kuka umman tasa me tsuma zuciya tace.
.Kuka umman tasa me tsuma zuciya tace.
"Nasan haka zata iya faruwa dake ƴata,nasani,wlh banyi baƙin ciki ba ,da ace kashe shi kikayi ko kika zubar da cikin ko kika yardar dashi wlh zuciyata se ta buga da baƙin ciki,ƙaddarace wacce tana iya samun kowa,Allah ya gafarta miki zunubin da kik aykata shi kuma in rayayyene Allah ya albarkaci rayuwarsa".
Daga ummu ta kwashe labarin komai ta faɗawa ummanta,Cikin kuka umma ta rungume jinior tana faɗin.
"Allah sarki ɗa na tun jiya kake nunamin alamar ni mahaifiyarkace amman ban fahimta ba sabida nasan ban haifa ba se yanzu nagane hakan se yanzu naga kamannin mahaifinka a tattare dakai,Allah na gode maka daka kuɓutar da zuriata daga sharrin masharranta,na gode daka bani ƴa maabociyar imani nagode ya Allah".
Haka sukai ta kuka dakyar umma tafara bada nata labarin bayan ta baro ƙauyan su.
*waiwaye*
Tunda na baro ƙauyan bansan inda nake nufa ba,bansan me nakeyi ba.
haka na dunga rayuwa cikin daji da bakin titi,har Allah ya kaini garin kano,na jima a garin kano sosai ina yawon haukata.
Kwatsam rana ɗaya nazo tsallaka titi motar ciroman kano kuma gomnan bankin nigeria ta bugeni.
Basu wuceba seda suka kaini asibiti,anan aka dunga bani kulawa,ƙarƙashin jagorancin ciroman,seda nayi shekara guda a Asibitin mahaukata na dawanau amman kullum ba sauƙi se na Allah.
Ba inda ciroma be kaini neman maganiba amman ban warke ba,seda wata aljana tazo ajikina ta shaidawa ciroma asiri akamin sannan ta faɗi inda aka birne asirin,acikin gidan,mu na ƙauye,kuma tabashi shawara akan ya ayka da mota aje garin a zuwan anzo siyan takin kashin shanu na gidan,wanda inde aka tashi ɗiba zaa ɗebo harda asirin.
Ayko haka akayi ciroma ya ayka dayake idonsu rufe yake da son kuɗi shaf sun mance da mugun ƙullin da sukayi,haka aka haƙo harda asirin da suka burne,koda aka kawo kashin shanun ciroma da kanshi yadunga tonawa har yagano asirin ya ɗauka yaje ya ƙona.
faruwar haka shine sanadin samun lafiyata,ciroma yaci gaba da bani kulawa.
Ana tsaka da hakane Allah yayiwa matar ciroma rasuwa wato mahaifiyae na'im,tun bayan rasuwarta,se ciroma ya nemi na amince da ya aureni sabida ya samu me kulawa da ɗansa ƙwaya ɗaya da ya mallaka wato naim,sabida mutuwar mahaifiyarshi har so tayi ta taɓa kwakwalwarsa.
To na amince mukayi aure da ciroma,tunda mukayi aure ciroma yaso aje akamo su jameelu,ni na hanashi sabida ina tunanin kina hannunsu kar su illatamin ke.
Yanzu haka na haihu da ciroma inda na haifi ƴanbiyu,duka maza,amman yanzu suna kano,gidan sarkin kanon kasancewar sarkin shida ciroma uwa ɗaya uba ɗaya suke,to shine yanemi alfarmar in an tashi yayesu akaisu gidanshi to yanzu sunacan.
murna sosai ummu ta taya mahaifiyar tata gameda ci gaban da tasamu.
Ranar wuni sukayi cikin farinciki inda umma tayiwa ummu wankan jego na asali kuma ta wanke jikanta wanda Naim yayiwa huɗuba da sunan sarkin kano kasancewar sarkin yana nuna masa ƙauna sosai amatsayinsa na wan mahaifinsa.suna kiran yaron da Abu Ayman樂.
Ummu batasan Ayman ɗan sarkin kano bane dan tunda suke be taɓa bata labarinshiba.shiyasa bata kawo komaiba a ranta.
Shiko doctor,kamannin da Abu Ayman yake masa da na ɗan uwansa Ayman yafi komi bashi mamaki,amman ya danganta hakan da ikon Allah ne.
muje zuwa.