.
A falo Ju ta hadu da Mami da Ya Sagir suna hira. Mami tace wa ya taba min ke naga kina ta kumbura bakin nan na tsiwa. Ju tace Ya Rayyan ne ya koro ni, Mami a gabansa fa ya hauni da fada. Ya Sagir da bai gane me akeyi ba yace gaban wa am confused. Ya Rayyan daya shigo a lokacin yace gaban Lawal mai shago mana. Cikin fushi ya cigaba da kallon Ju yace wai ni waye ma ya baki izinin fita. Ya Sagir yace Mami Ju zance take yi ban sani ba. Mami taga yara zasu mata taron dangi tace kwana hudu kenan yana turowa kiranta ina hanawa dazu Hajja tace kada na sake hanata fita don dole tayi aure wata rana. Ya Sagir yace to ni zan mata magana ai su bata gama secondary ba. Ya Rayyan kwance akan gado yana kallon hotunan Amal cikin zuciyarsa yana dada tausayin halin data shiga dalilin auren su amma abinda yafi damunsa yadda Ju ke neman zama centre of his thoughts. Wai shine har yake fadawa wani shine mijin yarinyar nan mai tsiwa. Ya tashi ya dauko papers din jarabawar da aka yi mata farkon shigarta makaranta ya sha dariya. Karshe dai alwala yayi ya sallah tare dadewa yana addua musamman ga matarsa Amal.
Lokacin WAEC ya matso su Ju an maida hankali ga karatu don ita bata da burin da ya wuce ta zama likitan ido ta taimakawa babanta. Ita da Yasmin sun dage da karatu cikin ikon Allah sunyi sun gama lafiya. Result din Jamb ne ya fara fitowa ita tana da 214 Yasmin kuma 221. Kowa ya tayasu murna. Kanwar Ju ma Nafisa wadda saboda demotion din da akayi mata tare suka gama itama ta sami 187.
.
Washegari abin mamaki sai ga Abba da Baba da wani Kawun su kanin babansu. Bayan sun gaisa da Baba suka gabatar da abinda ya kawo su na son nemarwa Rayyan auren Ju. Baba yace Alhaji Bashir ban tari numfashinka ba amma yaron nan ba shine mijin Amal ba. Abba ya amsa da shine...sai baba yace to don Allah ku bani mintuna kadan ina zuwa. Sandarsa yasa ya shiga cikin gida ya nufi daki tunda yau da gobe tasa yana iya yawoba gidansa. A daki sautin kukan mama yaji yace Mariya me ya faru? Tace yanzu muka gama magana da yaya da kuma Dada akan abinda ya kawo su Alh. Baba yace to me kuka yanke tace ka amince don duk shawarar da suka bani kenan saboda tunda aka fara maganar auren nan idan ma munki to zasu nema masa wata karshenta ya rabu da Amal din. Kuka yaci karfinta tace ko kadan ba irin rayuwar danake wa Juwairiyya fata ba kenan amma wai mahaifiyarsa ce ta kawo shawarar kada mu aurar da ita a rabasu. Ta share hawaye tace kuna kasan ina tausayawa Yaya kafin najib ya kawo karfi duk dawainiyarsu ta karatu ta dauke mana. Fatana Allah Yasa abin nan ya kara mana zumunci. Yace amin nagode Mariya da dukkan abinda kuke yi min ke da yar uwarki. . Baba ya fita ya koma falon waje yace da bakinsa yaushe kuke son a daura auren kunga ni banyi wani shiri ba ko zaku bani lokaci. Abba yace haba Alhaji Idris juwairiyya ai yata ce don nafi ka morarta idan ka amince a yau zas daura auren. Bidaya Baba ya kira yace ta kira masa Najib da yazo ya tura shi kiran mal Yau da Liman da wasu yan uwansu da abokan arziki.
.
Bayan sallar laasar aka daura auren Rayyan Umar Tafida wanda wurin aikinsu aka tura shi Germany na sati biyu da Juwairiyya Idris Muhammad wadda ke daki suna hira da su Nafisa bata san me yake faruwa ba. Akwai rigima a gaba daga dukkan alamu . Rayyan tsaye a reception yana ta kallon agogo ya gaji da jiran abokinsa Abbas wanda suka yi alkawarin haduwa a reception din hotel din da akayi musu masauki zasu je shopping domin sun gama abinda ya kawo a germany saura kwana biyu su koma gida nigeria. Da gudu Abbas ya fito daga elevator yana bashi hakuri. Rayyan sanye yake da wani ash din wando da riga light blue kayan sun masa kyau. Fuskar nan tasha gyara don shi baya aske gemu duka yana barin kadan wanda ya hade da gashin bakinsa. Da yake shi fari ne sai gashin yake masa kyau. Suna tafiya Abbas wanda tuni ya kawo kudin auren Fauza yace mu shiga kantin kayan matan can kasan mai hada lefe idonsa idon kayan mata. Rayyan yayi dariya to bana son rashin kunya dai kanwata ce. Dukkansu sunyi siyayya shi Rayyan banda Amal harda kannensa ya hada. Zai je wurin biyan kudi ya hangi wata farar night gown sleeveless wadda bazata wuce gwiwa ba kawai sai yayi imagining Ju a cikinta nan da nan yayi tsaki Abbas yace mutumina lfy. Rayyan wanda hannunsa har ya kai kan rigar yace yarinyar nan is getting under my skin and I don't like it. Abbas yace Ju ko. Cikin mamaki yace what do you mean..Abbas Yace ni kaina I cant remember when it started amma baka da zance sai na yarinyar nan tayi kaza ko tayi kaza kana fada kana wani lumshe ido. Rayyan ya kai masa duka yace to tunda ban ambaci suna ba ya akayi kasan da ita nake. Abbas yace sau biyu muna tare da kai zata wuce gaba daya hankalinka sai ya koma gareta. Ka siyo rigar baccin don nasan zata yi rana very sooooon. (fauza ta tsegunta masa auren da aka daura amma tace yayi shiru kada ya fada). Rayyan dai ya dauko irin rigar har biyu duk tsiyar da Abbas ke yi masa sai ya share kawai. Yau kwana biyu Ju tana aikin kuka ko abinci bata ci tunda Baba ya fada mata zancen auren da aka daura mata da Rayya.