TUDUN DAFAWA Part 3
.
Karasowa ciki yayi kana ya dago Bilkisu daga jikin Ramlan,ya watsa mai mari wanda zai sa mutum ganin taurare..
"Wallahi yaya sharri zai yi min,I don't know how it happened na gan kaina a jikin shi",tace tana kuka..
"Bro zaka yarda da ita neh,can't you see,kawai tana son tayi defending kan ta ne,she was seducing me.?",cewar Ramlan..
Ja'afar da ya gama kulewa ya juya ta bangaren Bilkisu ya dago hannunsa da ya dunkula,duk idanunsa sun kada sunyi ja tsabar kunar rai da yake ji..."dummm!",da sauri na jiyo domin ganin wanda yayi wa kullin sai naga Ramlan a kasa yana zazzare idanu....
"Ramlan I'm suspecting you,yaya ka san da zancen fyade da aka yi wa mata ta?,who the hell told you about it??",ya karasa zancen cikin tsawa...
"Ni ban san komai ba fah"..
"I swear I'll kill you and no one dare ask me the reason for that!"
"I know nothing,kan karuwar ga ka daga hannun ka ka mare ni,you shall see. Wallahi sai na zamo ajalin ka!",Ramlan yace tare da mikewa a wahalce ya wuce..
Juyawa yayi ta bangaren Bilkisu ya gan ta a tsugune tana kuka.."why,yaya why?meh nayi musu da suka yi min irin azabar ga,I kept myself for you but they deprived you of that,why???, yaya abinda yafi ci min rai shine ban san ko su waye ba neh",ta karasa zancen tana kuka mai ban tausayi...
"I love you that way,ina ji a raina cewan Ramlan yana da hannu a case din nan saboda naji abinda yace miki a lokacin da na mare ki,I'm so sorry,I never meant to hurt you.Na rasa ta yaya zan gano wanda yayi miki haka neh shiyasa na dau shawarar da zuciya ta ta bani akan na aiwatar dashi duk lokacin da Ramlan ya dawo"...
"Yaya ban san da wani baki zan gode maka bah,yaya ina jin kunyar ka I couldn't protect my pride for you,please ka duke ni son ranka duk da na san ba zai sa ka huce bah amma saboda ban san ta ya zan biya ka bah, I prom...."
"Shhh its ok baby nah,miko hannun ki na daga ki"..
Wani tingles suka ji yana bin jikin su a lokacin da ya riko hannun ta,kura wa juna ido suka yi suna ji kamar su rungume juna..Da gudu ta ja hannun ta ta gudu zuwa main house da taga ya rage kiris Ja'afar ya rungume ta..Lumshe idanuwa yayi yana jin son ta yana Kara ratsa shi..
"I'll always be there for you kissy",sunan da yake kiranta da shi kenan..Fitowa yayi yaja ciki shima yana jin dadi matuka a zuciyar shi kuma ya dau alwashin dauka mummunar hukunci a kan duk wanda yake da hannu a fyaden da aka yi mata..
******######*****
Da dare tana zaune a daki bayan ta idar da sallah,sai tunanin abinda ya wakana a garden dazu take yi..Kafin ta ankara sai taji karar wayan ta alamar sako ta shigo,da sauri ta dauka ta duba..Sako ne daga HUBBIL KHAIR..
_"Don't hate me,desert me,don't give up on me.I'm sorry if I've never counted on you,You are my one and only love..Sorry for all the times I've shunned you..ina matukar sonki my kissy...Have a stressfree night"_
Murmushi tayi har sai da kumatun ta ya lotsa.."ina matukar son ka nima",ta furta a hankali tare da kissing wayar...Qur'anin ta ta bude ta karanta Suratul mulk sannan ta mike ta nannade sallayan ta ajiye shi a ma'ajinshi..Rigar baccin ta,ta ciro ta saka sannan ta sa hula ta kakkabe saman gadonta,ta yi addu'a ta kwanta..Waya ta dauka ta Kira Mahneerah da Sameera ta san ko sun kai gida lafiya saboda anyi wa Mahneerah urgent call,Sameera kuma wai bro dinta zai dawo,shiyasa suka wuce..Bayan ta kammala ta tuna Zahra,tun da ta gan su a garden basu hadu ba kuma,"meh yiwuwa tana dakin Mami,gobe zan neme ta",cewar Bilkisu..
Hoton handsome dinta ta bude tana kallo har bacci mai dadi yayi gaba da ita.. Ja'afar shima wayarsa ya bude ya shiga kissyfolder yana kallon pics din su har bacci barawo ya sace shi...A takaice wutar da Ramlan yaso yasa wa fetir ta juyo kanshi saboda sharrin da yaso ya kulla wa Bilkisu ya zamo sanadiyyar Kara rurin wutar so a zuciyar masoyan.
*Bosso Estate*
.
"Wato mallam haka za ka sa ido su ajiye yarinyar nan a can koh,suna Kara tambadewa...."
"Meh yasa kin cika surutu neh,don Allah ki bari naji da abu daya mana..mtssw",cewar Baba sannan ya mike ya shiga dakin sa..
"Wallahi ni kam sai naga bayan yarinyar nan kafin mallam ya fara son ta....",tace tare da shigewa dakin ta itama.
Baba dai Allah yana ta Kara musu budi saboda yayi modernizing kasuwancin kwanukan sa da taimakon Allah ta Abba,yanzu shaguna biyu gare shi,daya a can garin su wanda yaran aikinsa suke kula da wurin sai kuma na nan cikin gari...Ya gyara gidan sa,anyi wa gidan sabon fenti..Umma da Saleema kuwa sai sheki fatar su ke yi don jin dadi...Duk da wannan jin dadin amma Umma tana so taga bayan Bilkisu saboda tana tsoron idan mahaifin Bilkisu ya rasu,a bai wa Bilkisu kaso Mai yawa na gadon...Allah ya shirya!
*Gidan su Mahneerah*
.
"Assalamu alaikum"
"Wa alaikumussalam, Mahneerah karaso ciki da wuri,Daddynki ne bashi da lafiya shine nake shirya shi muje asibiti"..Da sauri Mahneerah ta karasa ciki har tana cin tuntube.."Kira min uncle Babur (The brave or jarumi shine ma'anar sunan)yazo ya kai mu asibiti"..Juyawa tayi zata fita amma Daddynta ya rike ta gam yana kallon ta yana murmushi..
Rungume shi tayi sannan ta dauki wayan ta ta Kira Uncle..Cikin minti sha biyar suka kai Daddy asibiti..Yana fama da ciwon diabetes kuma yayi tsanani sosai..Haka ake ta abu daddaya har da gari ya waye, rai yayi halin sa..
Su Ja'afar da su Bilkisu,Mami da sauran dangi duk sun hallara..Kuka mai tsuma rai Mahneerah take yi..Irin kuka na masu hankali ba na hauka bah(mutum za iya yi wa dan uwansa kuka idan ya rasu amma ba kukan hauka ba,haka zalika zaman makoki har na kwana uku ya halatta,amma zancen sadakan uku bai samo asali daga Qur'ani ko sunnah bah.Allah yasa mu dace)...
Sultee zama yayi kusa da Mahneerah yana zubda hawaye.Tabbas sunyi babban rashi.Daddy mutum ne Mai tausayi da son zumunci shiyasa a jana'izar sa yayi mutane musamman talakawa da ya tallafa wa a lokacin da yake raye.Kowa sai addu'a da fatan alkhairi suke yi mai da fadin kyawawan dabi'unshi..(Allah yasa mu cika dah imani.ameen)..
*****####*****
Sai da aka daga bikin su Ja'afar da sati biyu...Basu so hakan ba amma ba yadda suka iya sannan ma yana son yayi amfani da dan lokacin da ya rage domin kawar da wata annoba da ta addabe shi..Asmee kuwa sai shige shige su ke yi,su je nan suje can har wurin wani malami suka je yayi mata sihirin mallakar mijin da zata aura da zarar ya kwanta da ita...Murna a wurin Asmee ba ya misaltuwa,at last zata mallake Ja'afar..
Zahra kuma tun ranar da taga Bilkisu da Ramlan a garden ta wuce,bata Kara waiwayo ta ba kuma ko Bilkisu ta kira bata daukawa..Ita ta rasa dalilin da yasa take feeling wani iri,ko dai kishi neh??,a'a ina?,na rasa wanda nike so sai yaron nan,no it can't be!!.....
Mahneerah kuma ta koma gidansu Mami da zama gabadaya saboda Momynta ta kulle gidan ta koma garinsu,bayan ta gama takaba itama zata dawo gidansu Mami da zama..Haka rayuwa ke ta tafiya masu har aka shiga makon da za a fara biki ..
Ranar laraba suka je Ar-riyadh Saloon domin gyaran gashi da faratai...Gyaran gargajiya aka yi musu daga ita har Asmee sabody Mommyn su Asmee ta nace tare zasu to komai a tunanin ta kila Bilkisu zata je wurin boka cikin kwanakin da ya rage..Kitson karkashi aka yi musu,na Asmee yayi kyau sosai saboda tana da suma mai tsayi,na Bilkisu kuma average amma shima yayi kyau sosai saboda sumar ta baki ne wul...
.
Bayan an gama musu kitso aka yi musu gyaran faratai da kuma lalle Mai dankaren kyau...Duk wanda ya gan su lokacin da suka fito daga saloon sai ya san Amare ne su..Bilkisu ne ta ja su zuwa store suka dan yi siyayya saboda Asmee tace sai dai tayi tuki,a tunanin ta ba za ta iya bah,bata san cewan Ja'afar yana ta koya mata manual ba,bare ma motar Asmee da ya kasance automatic..Sunyi siyayya sosai har ta siya wa Saleema wani ready made gown Mai kyau sannan suka ware gidan su Mami.Asmee ta koma mazaunin direba taja motar ta zuwa gida..
*Ranar daurin aure*
Ranar juma'a bayan anyi sallah aka daura aure a babban masallacin garin Minna wato Central Mosque....Ango sai sheki ya ke yi da abokanan shi musamman Ashraf..Dariya sosai Ja'afar keyi tamkar ba shi za a daura wa aure da Asmee wacce ba ya so ba..
Zahra ma tayi kyau sosai,Mommy ta tursasa ta cewan tare da yayan ta zata tsiya,in ba wawanci ba,ya zata je wurin kishiyar yayan ta bayan ga yayan ta.Ja'afar ya Kira Zahra yayi mata bayani game da abinda ya faru ran nan,shine ta kira Bilkisu ta bata hakuri..Su Asmee hoo,wai kishiya..Ni kam dariya nayi na kakkabe saratu na,sai anjima da dare zan dawo in za aje kai amare...
.
Da dare motoci suka jeru a cikin gidan su Mami.Umma ce ke tayi wa Bilkisu wa'azi kamar da gaske,Mami ma tayi nata sannan aka kai ta bangaren Abba,yayi mata nasiha ya sa mata albarka,abinda baban ta yace fafur shi bazai yi mata ba.Ya za ayi yasa wa wannan annobar albarka,ta karata can...
Sai da jikin Abba da na 'yan rakiya yayi sanyi da suka ji maganar da Abba ya yaba wa diyarsa.Kowa nata Allah wadai da wannan halin.Bilkisu kam tayi kuka har ta gode wa Allah. Haka aka fita da ita zuwa wurin da aka faka motoci..Wani lafiyayyen ash color car aka saka ta ciki.Sameera da Mahneerah suna gefen ta,sannun su 'yan uwa da school mates dinta a sauran motocin..
Can bangaren su Asmee ma Daddyn ta kadai yayi mata nasiha na kwarai,Mommyn ta da kawayen ta sai suburbuda mata hudubar shaidan suke tayi..Itama motoci neh jibge a gaban gidan su..Sallama tayi da 'yan uwanta da Daddy sannan ta shiga mota..Daddyn ta dai sai murmushi yake ta yi wanda daga ita, har su Mommy da Zahra basu san me ke tattare da murmushin nan bah..
An kai amare lafiya kowa ya watse.Bilkisu dai tana dakinta ko ina shiru,babu hayaniya.Tana tunanin ko dai an kai Asmee wani gidan neh,amma da taji dadi saboda ita bata son tashin hankali..Asmee ma tana can tana tunanin inda Bilkisu take,in so samu ne ma ta hallaka ta amma taji wuri shiru...Sallama taji da wata bakon murya,shiru tayi bata amsa ba.Sai da ya kara maimaitawa sannan ta amsa..
Karasawa ciki yayi ya ajiye ledoji."Sannu amarya",da sauri ta dago kai jin muryar wanda bata yi tsammani bah.."Ashraf!!,meh kake yi a nan,ina Ja'afar".."Calm down,nine angon ki!".."Never!,wallahi karya kake yi","Haba Asmee na,kin san yadda nike mutuwar son ki,ki tausaya min muyi zaman lafiya",yace tare da matsawa kusa da ita.Shiru tayi kamar maganar shi ya shige ta..Ya ajiye mata ledoji,yace taje tayi alwala suyi sallah sannan ya fita..
Yana fita ta rufe kofa da key sannan ta zube a gado tana ta rizgar kuka,"wallahi sai sunyi nadama..dukkansu!!",ta karasa zancen tana bubbuga hannu akan gado.Ashraf ya dawo ya bubbuga kofa ta share shi,haka ya hakura yaje dakin shi ya kwana...
Bilkisu tana zaune Ja'afar ya shigo bayan yayi sallama,amsa sallamar tayi ya shigo dakin.."amarya Kin sha kamshi",yace tare da yaye mayafin dake fuskar ta..Naseeha ya fara yi mata,kana tace masa ai ita da Asmee zai yi wa nasiha amma sai cewa yayi ai Ashraf ne angonta..kallon shi tayi da alamar tambaya, sai yace mata zaiyi mata bayani gobe.......
_Washegari_
Bilkisu na hango a kicin tana soya chips,duk kamshin chips da tea ya gauraye kicin..Tana kammalawa ta shiga dakin da ke gefen wanda suka kwana a ciki.Ita kunyar hada ido take yi da Hubbil khair saboda abinda ya wakana a tsakanin su daren jiya..
"Hmm",ajiyan zuciya tayi yayin da ta rufo kofar dakin.Komai na dakin pink and maroon color ne,yayi kyau sosai.Tana bude durowa taga kayan mata neh a ciki,lokacin ta Lura da akwatunan ta dake sama.A nan ta gane cewan wannan dakin ta neh...
Murmusawa ta kuma yi ta shiga bude wani akwatin ta da kayan ta na gida ke ciki domin cire tawul,sai da ta cire har zata rufe box din,sai ta zuge zip din da wuri ta bude wani karamin zip ta ciro wani paper rose flower..Sai da na ware idanu na da kyau,shine na gano cewan flowern da tayi masa ne lokacin da take school,koh me yasa bata bashi ba?,zamu ji dalilin nan gaba...
Wanka tayi sannan ta fito ta shafa mai. Duk abin nan da take yi,Ja'afar yana dakin sa yana bacci.Tunda suka idar da sallah suka koma bacci,da wayo Bilkisu ta kwace jikin ta daga nashi lokacin da ta farga...
Pink lace ta ciro daga kayan da ke wardrobe ta sa, sannan tayi make up daman ta zama gwana a make up tunda suka kulla kawance da Zahra da Sameera..Tayi kyau sosai da pink lipstick da ta sa a baki..Turarukan da ke kan mirror ta feshe ko wani lungu da sako na jikin ta yadda Mami tayi mata bayani..Sannan ta dauki sweet na freshening baki ta fara tsotsa,yana sa baki kamshi kuma bashi da side effect..
Fitowa falo tayi sannan ta zauna a kushin ta na kare wa falon kallo da kyau...fentin falon shima yayi matching da komai na falon.. Karan footsteps taji alamar mutum yana dosar inda ta ke,da sauri ta saukar da kai kasa.......
******""""******
Abba da Mami ne zaune suna hira.."oh Allah sarki ina jin kewar 'ya ta",cewar Mami yayin da tayi murmushi..
"Ji min wifey fah,kika kaini jin kewar ta?,she is my daughter too y'know"
"Yawwa Habeebee ina son muyi wata magana if you don't mind please.."
"Go on,ina jin ki"
"Dama akan zancen Ja'afar neh nag......"
"Shhh,na san mai kike son kice,wallahi ni ban rike Ja'afar a raina ba kuma ni ban yadda cewa zai aikata wannan aikin bah ko saboda irin son da yake ta nuna mata fun tana karama,sai da aski ya kai gaban goshi sai ya kasa hakuri?,no way!I just played along,na san mutanen musamman matan,they are up to something but who knows??"...
"Kai..amma naji dadi Habeebee yadda ka fahimci abinda nike zargi nima,in ka Lura bata bari Saleema tayi magana ba although the poor girl was trying to say something",cewan Mami tare da gyara zama..
"Eh toh,na nuna musu bacin raina ne so that karda idan ma da hannun su a fyaden da aka yi mata,su sa ayi mata worse than that.."
"Toh Allah ya shirya, gashi dai mun samu Mahneerah kuma,yarinyar tana aiki sosai,very nice to be with,lallai Hajiya Rahma da marigayi sun bata tarbiyya mai kyau despite itace only child na su"
"Allah ya jikan shi"
Suka amsa da "ameen"
"Ina fatan da daya daga cikin su zai so ta,kinga sai muyi tuwo na miya na"
"Ai Alhaji kai tsohon zance kake yi,na lura ita da Sultee are attracted to each other amma dai mu jira su kara girma muga ko da gaske son junan su suke yi saboda karda muyi amfani da assumption mu aurar da su in ba so a tsakanin su,kaga zai zamo auren dole kenan"
"Haka ne,we shall not go into conclusion,Allah ya tabbatar da alkhairi","ameen"..
"Yawwa wifey,kinga business sai bunkasa yake yi har na bar wa baban Bilkisu business na kera kwanukan,yanzu shagunan kayan kicin da na bude da kuma nasu accessories da nike da sai kara cigaba yake yi,so,ina son na bude babban kamfanin kera jewelries and accessories na gwalagwalai don na samu wani agent a India wanda muka shirya zai dinga aiko min da materials da muke bukata sannan na biya shi.."
"Amma gaskiya wannan tunanin naka yayi,Allah ya taimaka"
"Ameen,kin ga ba sai mun ringa siyar gwalagwali daga wasu guraren bah,sannan Ja'afar zan sa as manajan wurin,banda wannan kuma na yi musu visa na honey moon da na yi musu planning a London"
""Kai Abban Ja'afar don't know how to thank you,kana kokari wurin faranta mana, Allah ya bamu ikon faranta wa juna rai..Ameen",cewar Mami...
"Ameen my dear".........
*****************
"Ni yaya zata yi wa wannan rashin mutuncin,no wonder bamu ga Ja'afar a bangaren mu ba ranar bikin,so ta zabi bare a kan jinin ta,stop crying my baby Asmee,trust me,zanyi komai saboda ku, just take care of yourself,karda ki bare yazo koda kusa dake or else kinsan sauran..Yawwa that's my baby..toodles",dukkan maganar ga akan waya Mommyn su Asmee ke yin sa,Daga ji da Asmee take magana..
"Wo...Mommy meh ya same teddyn ki",cewar Zahra da ke zaune a sofa tana chatting da Sameera..Nan Mommy ta zayyana mata komai,dariya tayi sosai although she was surprised yadda komai ya kasance..
"Ke kina hauka neh??,da ma ban gaya miki bah"
"Awwn! serves her right!"
"Meh kika ce??!",Mommy ta tambaye ta fuska a murtuke..
"Ban ce komai ba",sannan ta mike ta wuce daki abin ta yayin da take ba wa Sameera labarin da Mommy ta bata..Sunyi wa Bilkisu murna sosai,Allah ya raba ta da musiba...
Mommy kuwa car keys dinta ta dauka,sai gidan su Mami ko mayafi bata yafa ba bare hijab..........
**********
"Hello,guy how far, wallahi ba lafiya fah,bro na ya fara suspecting dina batun aikin nan da na sa boiz din mu,kai dai bari,so abinda nike so da kai yanzun nan shine ka tara su kayi warning nasu da kyau cewan karda su bari yar karamar yarinyar nan ta hadu da su ko a ina neh,eh ka san yara basa mantuwan abu da wuri,yawwa zan turo ma sauran balance din su yanzu before I think of the next step, har Mari na banzan nan yayi kafin bikin su fah saboda bitch din nan,don't worry sai min hadu",duka zancen nan a waya Ramlan ke yin sa..Tun ranar da Ja'afar ya mareshi ransa a jagule yake, har lokacin bikin ana ta tambayan sa ko lafiya?saboda babu ko digon fara'a a fuskar sa ko da na pretence ne..Mikewa yayi ya dauki key din motar da Ja'afar yake tukawa da saboda Abba ya siya wa Ja'afar wani as wedding gift,shiga motar yayi ya sa mata key da dabsi kamar motan zai yi tsalle don irin sautin da ke tashi a cikin sa,sannan ya fita a guje har tayar motan tana wani kara"kiiiiiiiiiiii".................
*********
"Amarya kin sha kamshi",cewan Ja'afar tare da rungumo ta ta baya yana shinshina wuyan ta da su kunnuwa..
Shiru tayi tana jin wani irin tickling sensation yana bin jijiyoyin jikin ta..Zagayowa yayi ya zauna a gefen ta tare da sa hannu a haban ta ya dago fuskar ta,da sauri ta lumshe idanu tana wani shagwaba fuskan ta..hakan ba karamin birgesa yayi ba..
"Masha Allah my kissy kinyi kyau fah amma kunyar ga da kike yi ya bata show",ya karasa maganar tare da lakutar hancin ta...
"Ina kwana yaya",tace a kunyace..
"Lafiya lau my kissy,ya daren jiya?"
Mikewa tayi zata gudu ya jawo ta ta fado kan kirjin sa,rufe ido tayi,da yaga da gaske take yi sai ya kyale ta..
Tashiwa tayi ta dosa hanyar kicin,"kissy na zo ki taya ni wanka mana",da gudu ta shige kicin ta rufe.. Murmushi yayi kawai ya shige dakin sa..Har ga Allah yana jin son ta a kowani sassa na jikin sa..Wanka yayi sannan ya fito ya shafa mai yasa farin T-shirt da pink wando saboda yaga kalar kayan da Bilkisu ta sa kenan..Feshe sumar sa yayi da turaren kai mai kamshin gaske sannan ya feshe ilahirin jikin sa da turare kana ya fito,a dinning area ya same ta...
Mikewa tayi ta jawo masa kujera ya zauna sannan ta fara serving din sa still kan ta a duke,shi dai Allah Allah yake yi ta gama,ya fara ci,gani yake Lamar first time dinta na dafa Mai abinci ke ga..Bayan ta zuba musu ta zauna a gefen sa,a natse suka karya sannan ta kwashe kofunan da plate taje ta dauraye sannan ta fito daga kicin..Tsayawa cak tayi ta rasa ko taje daki ne,ko ta tsaya a falo neh,toh in ma zata tsaya ina zata zau...?,kafin ta karasa zancen zucin ta kawai ji tayi an dauke ta cak sai kushin,yana zaune ita kuma ya kwantar da ita a jikinsa..
Labarin yadda komai ya gudana ya fara sambado mata.lokacin ta daga kai tana kallon sa..
_Bayan an daga bikin su,Ja'afar ya fara neman hanyar da za ya bi ya rabu da batun aurenshi da Asmee.Ashraf ya tuna cewan yana matukar son Asmee.Gidan su Ashraf ya nufa ya gaya masa abinda ya kawo sa,he was so happy har kuka yayi don murna.Ja'afar yace masa su shirya suje gidansu Asmee shi zai yi wa Daddynsu Asmee bayani..Da sauri2 ya shirya suka wuce gidan su Asmee.Sunyi sa'a Daddy yana nan.Kai tsaye Ja'afar yayi wa Daddy bayani,a take Daddy ya amince saboda ya yadda koma waye Ja'afar zai kawo saboda Ja'afar yaro neh Mai hankali so,ya san ba zai yi yawo da mutanen banza ba.Kuma Daddy ya amsa batun auren Ja'afar da Asmee, shi baya son ya takura ma dan wani..Nan take Daddy ya Kira Abba yace zasu zo yanzun nan da su Ja'afar.. Suna isa aka sasanta komai,Mami ma taji dadin zancen sosai amma dai ta dake kuma Daddy yace karda su kuskura su bari Mommy ko Asmee su ji..Abba ma ya biya wa Ashraf sadaki sannan Mami ta bi shi gida suka zanta da mahaifiyar sa saboda baban shi ba ya da rai.Maman shi taji dadi sosai saboda itama ta kosa yayi aure saboda tana tsoron karda ya fada sharrin shaidan..A satin nan aka yi siyayyan su akwatuna sannan aka gyara mashi daya daga cikin gidajen gadon sa......Wannan kenan!_
Ajiyan zuciya tayi bayan ya gama..."su kissy na hoo,sarkin kishi harda ajiyan zuciya"
Dariya tayi tare da rufe fuskarta da tafukan hannayen ta..Hannu yasa ya janye hannayen ta kana ya soma sumbatar ta...hmm daga nan labari ya canza..............Karar waya ya dawo da su hayyacin su!.................
"Assalamu alaikum,hmm Fateema kenan kin kyauta,daman haka zaki ce ai,I was expecting you a wurin biki na amma naji ki shiru,toh shikenan ya su mama da baba,toh ki gaishe su sai kin zo",cewar Bilkisu da ke waya da Fateema..
Ajiye wayar tayi sannan ta gyara kwanciyar ta a kan jikin sa.Sunnah TV ya sa musu inda Sheikh KG yake yin wa'azi a kan ma'aurata.Inda ya ke cewa:
_"mu musulmai min bar abubuwa da ya kamata mu yi a zamantakewar aure ma yahudawa.Zaka ga idan bayahude yana tare da matan shi,da sun dan motsa kadan yace I love you.Ko wurin aiki za shi.idan ya manta bai ce mata I love you bah,sai ya kira ta a waya ya gaya mata........."_
Haka suka cigaba da sauraron wa'azin ya na yi yana ce mata I love you.Ita kuma sai murmushi take yi,itama tana mamakin irin son da Ja'afar yake mata,ace bai same ta da mutuncin ta ba amma ko mugun bai hada su ba tun jiya har yau.. A hakan bacci ya kwashe su,sun wani kankame juna kamar za a sace dayan su.....
********
Knocking na hauka take yi.Mami na ji ta san cewa Mommy ce,daman ta san za a rina.Fitowa Mami tayi daga daki taje ta bude kofan,shigowa tayi ko sallama babu, duk a hargitse take..
"Lafiyan ki zaki shigo mana gida a hargitse babu ko sallama?"
"Ina amfanin yin sallama a irin gidan nan,da munafikai neh a cikin sa!",ta karasa zancen tana karkada kugun ta..
"Wato baki da kunya koh,ki zo har gida na kina zagin ni da iyalina?,meh muka yi maki?"
"Oh meh kuka yi min ma kike tambaya na,da kuka yi duping din *NI DA 'YATA* ai dole ki tambaye ni meh kuka yi.Harda dan kwaron nan Ja'afar,shegen ya...."
"Tasssss!",karan saukan mari na jiyo."jar uba!,saboda tsinannen yaron ki kika mare ni??"
"Duk abinda zaki ce,ki ce amma karda ki kuskura ki shegen ta min yaro don a gidan uban shi na samu cikin shi na haife shi,'Yar ki dai yace baya so,don haka ba za ayi wa yaro na auren dole ba,so get out!"
"Haba yaya ki ji kan 'ya ta,'yarki ce fah itama",tace tare da share kwallan da ya zubo mata a kan fuska saboda marin ya shige ta..
"I said get out!!!!"
"Shikenan mu zuba mu gani tunda ba kya jin magiya,mtssssw,we shall see!",Mommy ta ce tare da banko kofar falo a fuskar Mommy..
"Allah ya shirye ki wallahi",Mami tace sannan ta je upstairs inda Abba ke kiran ta yana faman cewa ita da waye ke magana..
#######
"Kai har kana zaton zaka samu wani kulawa neh a wurina,kazo kana wani kakkashe murya,don Allah ka rabu dani naji da raba ni da masoyi na da aka yi,mtsssw"
"Haba yanzu ni fa mijin ki neh,ai ko saboda igiyan aure na da yake kan ki,ya kamata ki daraja ni,ki kwatanta min so da kauna ko da kadan neh daga cikin wanda nike yi miki, kin san.... "
"Dan Allah jeka,ka ishe ni da surutu da sanyin safiyar nan,allow me to sleep"
"Shikenan lokacin ki neh,amma ba zan zuba miki idanu kina min duk iskancin da kika ga dama bah,dare me!",ya karasa zancen tare da banging kofar dakin..
"Mtchhhw,mutum kenan ba za a bari yaji da abinda yake damun shi ba kawai kazo ka tsaya min a kai ina breakfast,breakfast yana wajen uwar.......",haka ta cigaba da kundume kundumen ashar sannan ta ja comforter ta rufe jikin ta,ta cigaba da bacci....
*********
"Alhaji!,Alhaji ka tashi muyi magana,yaya zaka yi min haka"
"Haba Khadija, meh yasa kike yin abu kamar karamar yarinya wani sa'in"
"Ai dole kace hakanan bayan da kai aka yi kulle kulle,aka ci mana fuska"
"Kamar ya?,ni ban gane ba"
"Ohho,ka aurar da 'yar ka ga wani dan iska bayan ka san Ja'afar take so,sannan kana tambaya ta wai kamar ya"
"Oh! ashe can kika dosa,nifa gani nayi cewan yaron nan Ashraf yana da halayya mai kyau,kuma yana son ta sosai don haka na san zai iya koya mata son sa,kuma"
"Ka ga,ya isa haka nan,ya isa, tunda har baza ka iya ba wa 'Yar ka abin da take so ba,toh ni zan zamo gata a gare ta,I'll do what it takes to make her happy,daman kai ba son ta kake yi bah"
"Meh zaku yi ne wai"
"Ba ruwan ka,wannan tsakanin *NI DA 'YA TA* neh"
"Toh Allah shi kyauta",yace tare da mikewa ya shige bayi yayi brush.Sannan ya fito ya ga bata daki,dinning area ya nufa..
"Good morning Daddy",Zahra ta gaishe shi tare da gyara mai kujera ya zauna.
"Morning dear,kin tashi lafiya my baby?"
"Lafiya lau Daddy,I prepared your best coffee da omelet"
"Allah shi yi miki albarka",lokacin ya Lura da Mommy dake faman zuwa da dawowa a tsakiyan falo, murmushi yayi ya girgiza kai..
"Mommy ba za kici abinci ba?",Zahra ta tambaye ta tana dariya..
"Abincin uwa ki na ce,zan ci kaniyan ki"..Dariya ita da Daddy suka yi,suka yi breakfast abin su,suka bar mata falon...
**********
"Gaskiya mallam ban ji dadin abinda kayi wa 'yar ka bah,ko tsanan ta ka yi bai kamata ka nuna hakan a gaban jama'a ba",cewan Abba..
"Alhaji ba za ka gane bah,baza ka gane ba kawai"
"Gaskiya nima Alhaji ban ji dadi bah da naji maganar a bakin mutane,bai kamata ba sam2",cewan Abban Fateema,kawar Bilkisu..
"Atoh kaima ka taya ni fada,Allah ya shirya",ameen suka ce gaba dayan su sannan suka yi alwala suka wuce masallaci..
*******
"My kissy,kinji Abba wai yayi mana visa na zuwa London honeymoon",cewan Ja'afar da yake taya ta warming naman kaza a warmer..
Murmushi tayi tace"Abba kenan,Allah ya bar mana su mu faranta musu rai yadda suke faranta mana"
"Ameen my kissy,so zuwa next week Saturday zamu wuce,daga nan sai nayi ajiya na a nan",yace tare da shafa cikin ta.Murmushe tayi ta sunne kai a kirjin sa..Warin konewar nama ya dawo dasu duniyar da suka fada,da sauri suka karasa gaban warmer din Ja'afar ya sa hannu,da sauri ya cire yana tsalle kamar karamin yaro,handkerchief ta dauka ta jawo plate din sannan tazo ta fara hura masa hannu,daga nan suka Lula duniyar masoya...hihi
_*Dubai*_
Jirgin su ya sauka a Dubai karfe 02:00pm.."toh kissy na, alhamdulillah mun iso".Murmushi tayi ta kara matse hannun sa a cikin nata.Suna karasa saukowa wani balarabe yazo ya karbi kayan su tare da fadin, "welcome to Dubai"...
"Thank you",suka amsa a tare,sannan yayi directing din su zuwa inda motar da aka yi musu charter yake.....
A Armani hotel ya ajiye su..Suna isa reception ya gaya masu suna da reservation a wurin..Sai da aka yi musu 'yan tambayoyi sannan aka basu dukka info. Da suke bukata,saboda har inda zasu je yawon shakatawa da siyayya yana kan booklet da aka basu..Dukka wannan aikin Abba neh.
Wani daki mai bala'in kyau aka kai su.Falon yana da dan fadi,sannan ga HD TV a bangon falon da sauran kayan kallo..Kushins din su ma 'yan medium sizes..
Rufo kofar Ja'afar yayi sannan suka karasa cikin dakin.Ko ina kamshi yake yi.Ga wuta da ya haskaka ilahirin dakin.Closet dake gefen mirror,Bilkisu ta ajiye akwatunan su a ciki kafin tazo ta jera kayan anjima..
"Kissy na,ya kika ga dakin,yayi miki ko mu canja??",cewar Ja'afar.Duka na wasa ta kai mai sannan tace,"haba dai, ai ni zabin Abba shine zabi na"
"Iyye masu Abba,toh ni mijin ki kuma ogan ki nace dakin bai yi min bah,so kizo muje wani room".
Marairaice fuska tayi kamar wacce zata yi kuka."Haba yaya,don Allah kayi hakuri mu zauna a nan,zabin ka ai nawa ne nima but please nan din ma yayi please,kaji?"
"Toh zan yarda only on one condition",yace tare da riko hannun ta ya jawo ta kusa da shi."ok tell me the condition"..
"Zaki daina Kira na yaya,call me with sweet names yadda nima nike kiran ki da Kissy"..Dariya tayi tace,"kai yaya har mene ne a sunan da baka so na Kira ka,"..
"Toh shikenan kinga wucewa ta",yace tare da Kama hanyar fita daga dakin.Bata san lokacin da tace "YOU ALONE",bah.Cak ya tsaya ya kara jin ta maimaita abin da tace..
A hankali ta tako har gabanshi kana tace,"haba you alone,wasa nake yi ma fah"
"Gaskiya I love this name kuma in shaa Allah kema you alone ce a gare ni in shaa Allah",yace tare da manna mata kiss a goshi..Da sauri ta janye kan ta saboda ta san halin shi,daga nan zarcewa zai yi..
Dariya yayi sannan ya bi ta zuwa bakin gado da ta zauna suka cigaba da hiran love dinsu kowannen su,zuciyar su cike da kaunar juna.
A yau neh Umma ta nema ganawa da Ramlan.Bayan sun cimma burin su ta farko na sawa ayi wa Bilkisu fyade.
"Ke ya aka yi neh?",cewar Ramlan. Ni kam nace oh su Umma girma ya zube,har yaron da kika isa ki haifa sau biyu ko uku ya tsaya yana kiran ki da ke.Allah wadai!!.
"Yawwa na Kira ka ne saboda naga yadda muka so abin nan ya kasance,ba haka ya zamanto bah"
"Toh sai yaya?"
"Eh nazo mana da wata sabuwar hanya neh wanda na san baza su iya tsallake shi bah"
"Ina jin ki"
"Yawwa naji ance sun tafi Dubai koh ko ina ne ma?"
"Ni ina ruwa na da inda suka tafi,ke in zaki yi maganar straight forward kiyi,bana son dogon zance!"
"Toh daman cewa nayi ko zaku samu wata ko wani a can da za ya/ta shiga tsakanin su yadda kwata2 baza su jitu ba a zaman da zasu yi a can?"
"Eh toh,kin kawo harka mai kyau.Amma sai dai wani hanzari ba gudu bah.Ba zai yi sauri da yawa bah?ai kamata yayi mu bar su su dan shana",cewar Ramlan tare da yin wani shu'umin murmushi..
"Ai bai yi sauri bah tunda baka riga ka samo wanda za a bai wa aikin bah"
"Eh toh,in dai wannan neh babu matsala,akwai wata babe dina da ke can. Ita zan ba wa aikin tayi mana,amma ita Bilkisu'n ya za ayi da ita?"
"Kai ka barni da ita kawai..Naka dai ka sa su rasa sukuni a duk inda su ke!"....
"toh shikenan an gama",cewar Ramlan yayin da yake makala no respect din sa a idanu.
"Yawwa zamu yi maganar kudin idan aikin yayi kyau"
"Toh Allah ya sa,ko kuma nayi sanadin mutuwar ki".."hmm"kawai tace sannan ta juya ta fita daga uncompleted building din ta wuce.Bayan ta wuce da minti biyar shi ma ya fito ya shige motar sa,ya wuce.....
_*Shu'uma*_
Itace babbar yarinya da ke tashe a Dubai.Ta kasance tantiriya tun a secondary sch..Ta hadu da su Ramlan neh a wajen rubuta exam.Tun lokacin suka zama friends saboda halin su ya zo daya.
Ta rasa mahaifiyar ta tun tana karama,don haka bata samun kyakkyawan tarbiyya bah kasancewar mahaifin ta dan siyasa neh.Baya zama a gida,kuma ko meh take so yana yi mata.A yanzu ma ta kai shekara biyu kenan da zuwa Dubai saboda wai ita kasar najeriya ta ishe ta..Wasu 'yan iskan mata ta hadu da su a nan,duk ta Kara tabarbarewa.Duk club din da kaje,kana cewa S.H an san ta..Sunan ta Sumayya Hashim wacce zan dinga kira da Shu'uma har karshen novel din nan...Wannan kenan!!
"Hello,watsup,yeah na gane ai,Real guy koh,okay ya 2days?.Toh that's good,OK ina jin ka..uhhum wannan ai karamin aiki ne a wuri na,I can do it free for you so,karda ka damu da zancen payment,yeah never mind.Ka turo min pic din su da every details about them so that inyi studying na su da kyau kafin na fara,aha take care..!",dukka zancen nan kan waya Shu'uma ke yin sa,daga ji da Ramlan ta gama magana..
"Hey babes mun samu wani work fah"
"Ok muna jin ki,mun san duk wanda zai baki aiki toh bana wasa ba neh",cewar kawayen ta,Jumy da Shola.
"Yawwa ina jira a turo pic dinsu tukun,wai couples neh ake son na raba su",ta ce tare da yin katkat da chewing gum din ta.Karar wayar ta taji,alamar notification neh ya shigo a messenger din ta...
Sai da ta karanta dukka details din a bayyane domin kawayen ta su ji,sannan ta mika musu wayar,su ga hoton."wow",suka fadi lokaci daya..
"Cute couples,amma meh ya sa yake so a raba su??!",cewar Jumy.
"Ke forget kawai,all I know is that,guy din nan nawa neh,no one dares to come close to him.Ku barni dashi kawai,kuje Ku samo min details din su,Suna Armani hotel,room 15.."
"Ok,let's go",suka ce tare da mikewa suka shige arniyar motar su...sai Armani hotel.
*ARMANI HOTEL*
.
Su Shu'uma na isa hotel din daidai lokacin Ja'afar da Bilkisu suke fitowa.Sunyi shirin larabawa,shi yasa jallabiya itama sanye take da jallabiya sai dan karamin hijab da ya rufe mata kirji..Sun yi matukar kyau.
Nan take Shu'uma taji wani irin kishi,ita ina koma yaya neh,dole ta mallaki fine boy din nan.Su Ja'afar kuwa hankalin su kwance suka shige mota ba tare da sun lura da su Shu'uma dake kallon su bah tunda kowa harkar gaban sa yake yi.
Wani madaidaicin pick up van suka shiga ya kai su *DUBAI SAFARI*. A nan ne inda city da concrete na Dubai yazo karshe,daga nan sai desert din dake wurin..
Suna isa,wani mai land rover yazo ya dauke su bayan ya bukaci ko sune Mr and Mrs Ja'afar suka ce mai eh..Nima da sauri 2 na sauko daga pick up da ya kawo ni har ina cin tuntube,ina isa na shige wani land rover nima,ina ciki na hango su Shu'uma suma a cikin nasu landrover'n sai wani shan kamshi suke yi irin bad girls din nan.
Gaskiya wani wurin idan kaje sai ka tambaye kan ka cewan Anya duniya kake?.. Wurin yayi ne kawai.Muna kaiwa can karshe sai ga wani oasis setup inda na hango barbarque yana wani irin welcoming dina, duk yawu na ya gama tsinke wa...hahha
Wasu belly dancers na hango wai suna rawa abin su da yake d yamma suke fara rawa sai dare ake gamawa.Inda Bilkisu da Ja'afar suka zauna,nan nima naje na zauna domin kwasan rahoto..
Mutane na sai zuba love suke tayi ni kuwa ina murmushi a gefen su ina con barbaque dina. Ina hada ido da Shu'uma ta watsa min harara,tuni na kama kai na,na daina yin murmushi.Haka nike ta zaman banza a wurin yayin da masoyan suna love,Shu'uma kuma sun hana ni sakewa..
Sai can da daddare direbobin land rover'n suka mayar da mu inda muka sauka a farko.Pick up kuma ya kwashe mu zuwa Armani hotel kuma.Dukka abinda dai suke yi,Shu'uma da kawayen ta suna biye da su,har booking daki suka yi a hotel din.Dakin su Ja'afar na nufa abina ina sanda don karda su jiyo shigowa na...
"Washhh! Gaskiya na gaji you alone",tace tare da cire hijabin ta sannan ta ciro towel.
"Wallahi nima I'm so tired kissy na,muyi wanka sai muyi sallah mu kwanta koh??"
"Eh wallahi",tace yayin da ta daura towel sannan ta cire jallabiyar jikin ta da su undis ta zuba a closet.
"Toh bismillah nima a cire min"
"Kai yay..wai you alone,ka cire da kan ka mana"
"Ni kam in ba ke zaki cire min bah toh na fasa yin wankan",yace tare da langabe kai irin na shagwaban nan.
Ba magiyan da bata yi mai ba,yace sam sai dai ta cire mai,harda cewa tare zasu yin wankan.Haka dai ta hakura,suka yi wankan tana wani noke2 sannan suka dauro alwala..Dauko ta yayi tamkar wata jaririya,ya shirya ta sannan itama ta shirya shi bisa ga umarnin shi..
Suna kammalawa ya tada iqama da yake daman akwai dadduma a wurin da kuma alamar inda zasu yi facing wato alqibla..
Suna idarwa suka yi addu'a sannan ya dauki waya yayi order'n coffee.Cikin mintuna kalilan aka kawo,shi ya tashi ya karba sannan ya rufe kofan da doorlock..Bayan sun sha kowa yaje ya kurkure bakin sa sannan suka yi kwanciyar su.Ni kam tun ina jin hirar su har bacci barawo ya sace ni...... *Asuba ta gari Loverbirds*....
_*Bayan Kwana uku*_
.
A lokacin su Shu'uma duk sun gama observing Ja'afar da Bilkisu sosai,saboda haka suka fara shirin afka masu..
Sun hadu da su a rana ta biyu a Burj khalifa har suka gaisa da Bilkisu saboda shigar mutunci suka yi don haka ita bata kawo komai a ran ta bah.Har nombar ta suka karba kafin Ja'afar ya same ta a wurin mota.
A rana na uku ne suka shirya afka masu..Ja'afar da Bilkisu sun shirya cikin English wears sannan Bilkisu ta sa abaya a saman kayan ta da yake rigar jikin ta bai kai cinya da kyau ba kuma wando ta sa saboda yau Dubai ski za su..
Suna isa wurin,suka sanya woolen coats da thermal caps din su wanda zai yi keeping din su warm a wurin.Da farko Bilkisu ta ji tsoro ganin irin wurin da zasu yi skiing kai,amma da Ja'afar ya rike ta ya fara moving sai tsoron ya dan ragu..
"Kissy na ki rike ni da kyau fah!",yace da karfi.
"Toh ai wannan ya zama dole you alone"
"Wow! Yeah! Wow! Wayyo Allah na!",shine abinda suke ta fadi suna faman zuwa da dawowa.Gwanin sha'awa abin su.
Duk abinda suke yi,hankalin su Shu'uma ya na kan su amma su basu ma san da mutane a wurin ba.Anjima kadan Bilkisu ta saba sai ta fara yi da kan ta,sai ihu take yi na jin dadi.
Bayan kamar awa daya, Ja'afar yace mata yana zuwa ya samo abin motsa biki tunda ita ta ki ta raka shi.Yana juya baya,su Shu'uma suka karaso,abin nema ya samu.
"Hey friend!",cewar Shu'uma yayin da ta karaso ta inda Bilkisu ta ke.
"Hey ya kike",Bilkisu tace ba tare da ta kawo komai a rai bah.
"Lafiya kalau,na ga kina jin dadi abin ki,I'm I welcome to join you?"
"Sure!",cewar Bilkisu tare da murmusawa.
"Mother fucker!",Shu'uma tayi murmuring a hankali.
"Let's go!!!",cewar Bilkisu da take kara jin son skiing ke shigan ta.
Sun yi round daya, biyu lafiya.A na uku neh Shu'uma ta fara buge ta.A round na hudu su Jumy da Shola suka yi joining.
A farko ta dauki abin as mistake.Da ta Kara na biyu,na uku sai Bilkisu tace,"ouch! that hurts.!"
"Oh yi hakuri dear!",bata karasa zancen ba ta Kara buge ta.Bilkisu na dagowa ta sake mata wani irin murmushi.Haba wa ba sai suka fara rough skiing da ita bah.Wannan ta bige ta,wannan ta hankade ta.
"Its okay please!,zan je na jira miji na a can",tace tare da yin nuni da wani resting place tana haki..
"No ai yanzu muka fara,the game has just began!",cewar Jumy.Bilkisu tana dagowa ta ga irin kallon da suke mata ta juya da sauri zata wuce su ka jawo ta baya...
Suna jan ta,tana ihu amma mutane basu lura da hakan ba,gani suke duk cikin jin dadi neh..Cikin 'yan mintuna suka dagula mata lissafi sai ji kake fummm ta fadi a kasa.
Kinkimar ta suka yi kamar zasu ba ta taimako,suna wucewa Ja'afar ya dawo.Zubar da ledar hannun sa yayi da yaga ko inuwar kissy'n sa bai gani bah.
Gashi kowa yana harkan gaban sa ne bare ya tambaye su amma dai ya maze ya na ta tambaya.Duk wanda ya tambaya suce no basu gan ta ba.Har yayi loosing hope zai je ya zauna yayi figuring yadda zasu yi sai ya hango su Shu'uma.
.
Da sauri ya karasa wurin su yana haki.Shu'uma na ganin shi ta san yes hakan ta zai cimma ruwa.Daman sun zauna a wurin neh domin ya hango su.Gyara zama tayi ta langabar da kai tana jiran sa.
”Hey..hey please did you...did you help me see my wife a nan wurin",bai ma san da wani yare zai tambaye su."calm down,tare Ku ka zo nan",cewar Shu'uma.
"Eh naje siyo abu ne na dawo ban gan ta bah.."
"Oh sorry,toh ka zauna bari muje mu dubo ta"..Shine magana ta karshe da Ja'afar ya ji saboda tana gama fadi ya juya zai wuce sai ta dafa shi ya juya ta fesa mai wani abu a wurin shima ya zube.
Ciccibar shi suka yi zuwa motar su,suka wuce.Ni kam nace Allah kadai ya san mai zasu aikata wa bayin Allah nan...
*************
_*A Gida Najeriya*_
"Wai ke ba kya da aikin yi neh kullum sai kallace kallace da chatting?iyye"
"Mtsssw kan ka ake ji"
"Ni kike yi wa tsaki don kinga ina barin ki?"
"Toh meh zaka yi?in ka gaji ka sake ni mana, na ce bana son ka,dole neh?"
"Toh wallahi yau sai na karbi hakki na,Ba zan yi azumi don kare kaina daga zina ba bayan gani da mata a gida!"
"Lallai ma,in your dreams"
"Wallahi yau ba zan hakura ba sai na biya bukata ta"
"Wallahi baka isa bah,mutum daya na tanada wa budurci na kuma..."
Tasssss# ya wanke ta da lafiyayyen mari. Kinkimar ta yayi,tana ihu tana bugun shi amma ina bai ma san tana yi bah.Abinda yafi bashi haushi shine yadda take sa tsirarrun kaya tana zama dashi.
Kiciniyar tube mata kaya yake yi.Da kyar ya samu ya cire kayar..Ita kuwa sai ashar take ta kundumawa harda kiran shi dan iska,zai yi iskanci da ita. Shi kuma yace tunda da matar shi zai yi,toh wannan bai shafe shi ba..
Kai a takaice fyade yayi mata.Ya sha yakushe2 da cizo amma sai da ya cimma burin sa.Ita kuwa ta sha azaba saboda sai da ta jigatu sosai ya bar ta.
Yana gamawa yaji duk yanayin shi ya canza,duk yaji kanshi wani iri.Wani irin tausayin ta da kaunar ta ya shige shi da ko da tace mai kashe kan ka,zai iya yi in dai har zai faranta mata rai.
"Ka cuce ni,ka cuce ni,Allah ya isa, shege..mugu..wayyo Mommy na"
"Haba amaryata kiyi hakuri na sa...."
"Fice min daga daki!"
Sum sum ya tashi har ya Kai bakin kofa zai fita sai ta kuma cewa,
"Shege dawo nan ka gyara ni,wallahi ka shiga uku kenan".Da sauri ya juyo jikin sa na rawa yazo ya na kokarin taba ta,cikin zafin nama ta watsa mai Mari.
"Wawa ruwa zaka hada min"
"Toh nagode,bari na hada miki",yace tare da shigewa bayi.
"Ai ka zama kuku na kenan tunda ka shiga hurumin da ba naka ba...wayyo Allah ya isa!!"...Haka dai take ta bala'i shi kuma tamkar yaron ta,sai jujjuya shi take yi.Ni kam nace oh Bilkisu da Ja'afar Allah ya raba Ku da dambe.Ashraf kuma Allah ya tsamo ka daga duniyar da ta tsunduma ka ciki..
########
"Alhaji naji yaran ga shiru,yau ba su Kira ba yadda suka saba"
"Haha,suna nan suna jin dadin su,kin manta lokacin da muka je mu ma",dariya tayi kana ta ce,
"Kai Alhaji har ka tuna min da baya.Ko zamu je ne kuma??"
"Hahha watarana zamu in mun yaye yaran nan"..kyalkyalewa da dariya suka yi kana Mami ta mike ta shige kicin domin duba abincin da ta sa a wuta.Ita dai tana ji a jikin ta cewa akwai abinda yake faruwa.Addu'a tayi wa 'ya'yan ta gaba daya sannan ta cigaba da aiki....
Wani club su Shu'uma suka kai Bilkisu.Karamin daki da yake gefen bar din suka shigar da ita. Lokacin ta soma bude ido tana cewa,
"Ruwa,Ruwa..."
Da sauri Shu'uma ta karbo kwalbar giya guda daya ta zuba a 'yar karamar kofi ta kai mata shi a baki,ta kwankwade shi tas.. "Meye wannan?",take tambayarsu yayin da take Kara shan wani giyar.
"Sha yarinya zaki ji dadi",cewar Shola..Haka ta cigaba da sha har ta bugu.Wani gaye suka kira daga dance floor..
"Shayo what's up now, wani dan aiki zaka yi min",cewar Shu'uma.Shayo shi ma dan Najeriya neh. Iyayen shi sun turo shi Dubai domin harkar business da su ke running a nan kasar Dubai..
"Ok, ya aka yi"...Nan ta zayyana mai abinda take so yayi mata.Cewa tayi ya kula da Bilkisu, karda ya bari kowa ya zo kusa da ita har sai lokacin da za su dawo,warning ta bashi sosai cewar karda yayi mata komai,yace toh..
Jan motar su suka yi sai Armani Hotels inda suka bukaci dakin da Ja'afar ya sauka.Ganin su da aka yi tare da shi,ya sa aka basu makullin dakin suka wuce ciki...
Rufe kofar suka yi sannan Shola ta ciro camera'n su Ja'afar da ya fadi a kasa yayin da suke ciccibar sa.Tube masa kaya suka yi suka fara jajjagula shi,kowane style suka yi,sai Shola ta dau hoton amma fa basu yi lalata da shi bah.Haka kurum Shu'uma take jin tausayin su ganin irin halin da ta sanya su ciki.Dukka abinda suke yi,Ja'afar bai sani bah saboda ba ya hayyacin shi.
Wuraren takwas na dare ya fara farfadowa,da gaggawa suka bar masa dakin da short note a gefen sa,
*_"I will be back soon you alone"_*
Yana farfadowa mike wa yayi da sauri yaji jiri na kwasan shi,sai ya koma ya kwanta.A hankali ya bude idanuwan sa domin ganin inda ya ke.Ya akayi yazo daki,shine abinda yake ta dawowa masa a kwakwalwa.
Yana tunawa,zumbur ya mike amma ina maganin da ta fesa mai yayi bala'in saukar mai da kasala.Kwanciya ya kuma yi yana tunanin ina zai ga Kissy'n sa.Sai wajajen karfe 9 ya dan ji karfin jikin sa ya mike yana dafa bango yaje ya watsa ruwa kana ya dauro alwala ya zo ya biya sallolin da bai yi ba dazu.
Yana idarwa ya daga hannu yana rokon Allah ya bayyanar masa da ita. Wuraren karfe goma ya fito daga dakin.
Cin karo yayi da ita. Wani gardi ya rike ta tana tafiya tana tangade,alamar a buge ta ke.
"Ga matar ka,she made my day a romantic one",yace tare da murmusawa ya wuce abinsa(Shayo kenan,kuma karashen aikin sa kenan da su Shu'uma).
"Ya anka yi neh you alone..hihi....ghoooor",ta karasa zancen tare da gyatsa cike da warin giya.
Fizgar ta yayi zuwa daki sai faman huci yake yi.Yana isa daki ya cillata kan gado.
"Meh nayi maaaah",ta tambaye shi tana lullumshe ido.
"Ina kika je??"
"Ni..ni..ni ba tare muka fi..fita bah...ji.ji..tambaya fah..ghooor",ta kuma yin gyatsa.
Mikewa yayi ya cakume ta a wuya.Tana son tayi magana amma ta kasa.
"Yaushe kika fara shan giya,when?when? Bilkisu when?tell me!",Kara makure ta yayi.
"Ke kika ajiye min note sin nan koh?kika fita da wannan gardin bayan ina ta Neman ki hankali a tashe"
"Eh..a'a..ni..na..na...",don tsananin haushi da kishi bai san lokacin da ya kwada mata mari a fuska bah.Firgigit ta dawo hayyacin ta.
"Wayyo yaya wani ya mare ni",tace cikin muryar kuka yayin da ta rike shi.
"Ke matsa min a nan!",ya daka mata tsawa,bata san lokacin da ta cire hannun ta daga jikin sa ba,tsabar tsoron da ya kamata..duk idanun shi sun kada sunyi ja tsabar kishi..........Toh fah!!
_*Najeriya*_
"Ka gama wanke wanken?"
"Eh na gama",ya amsa da sauri yana goge tafuka hannayen sa.
"Toh ni zan je gidan hajiya ta,karda ka kuskura na dawo naga ba abinci a dinning,kana ji na??"
"Eh..toh..amma.."
"Amma meh"Asmee ta katse shi.
"Don Allah so nake ki bar ni na je wajen Hajiya ta"
"Uhmmm.toh,zaka iya zuwa amma bayan ka kammala aiki fah!"
"Toh toh nagode",ya karasa zancen kamar wanda zai yi kuka don murna.
Rabon shi da ganin mahaifiyarshi tun bayan biki da tazo ganin ko lafiya,saboda basu kawo mata gaisuwa ba as usual. Rashin mutuncin da Asmee ta yi mata ya sa bata kara stepping ko da gate din gidan ba.
"Yawwa kuma karda ka kuskura ka ci abincin idan ka dafa.... Kuma karda ka ci a wajen hajiyar ka"..cewar Asmee a bakin kofa.
Kada kai yayi alamar eh sannan ya mike ya karasa sauran ayyukan da zai yi sannan yaje kicin ya fara dafa abincin.
Shi karan kanshi yana tausaya wa kan sa amma ya rasa mai ke damun sa.Kullum cikin addu'a yake Allah ya taimake shi.
Asmee ta mayar da shi kukun ta,dan aiken ta,mai yi mata wanki da sauran su..Ga ta da yawon tsiya kamar wacce ta ci kafan kare.Amma shi a su wa?ba ya iya musa mata ko kadan bare ma yace karda ta fita sai dai ita ta hana shi fita.
A takaice da zamar da shi mijin tace cikin mako daya da auren su...
*********
"You alone,meh ya faru?,why are you mad at me?",cewar Bilkisu tana hawaye.
"Oh tambaya ta ma kike yi?ina kika jeh bayan da naje siyan abin motsa baki mana"
"Kamar ya ina naje? I was standing there waiting for you!"
"Please save me that bullshit!,ki yi min shiru!ok kina jirana kika ce,ya aka yi na dawo kafin ke?!"
"Uhm..uhm..ni..ni"
"Ke..ke meh?!,na ce ke meh?!"
Shiru tayi hawaye sai ambaliya yake yi a fuskar ta..
"That means abinda yace gaskiya ne..You were cheating on me!,bayan taimakon da nayi miki na aure ki,na danne zuciya ta bayan wasu sun riga ni... "
"Please ka daina maganar nan please,ka san ban san kowa ba a nan,in fact no one knows me better than you,so plea...."
"Ya zaki ce na daina maganar, bayan kin san gaskiya nike fadi! Did I marry you as a vir...."
"Stop it!! Na ce ka daina!",ta daka masa tsawa yayin da ta sa wani irin kuka mai tausayi.
"How dare you shout at me?!",yace tare da wanke ta da mari kuma.(jama'a kun ga laifin sa?..duk cikin kishi neh,so ku yafe mai... #smile)
Faduwa tayi saboda gravity na marin, daidai kan cameran da su Shola suka ajiye ta fadi tare da sakin kara mai cike da tsananin azaba.Wani kara ta ji daga inda take a kwance.
A hankali ta dago ta dauka......
*********
Saleema ce tayi sallama ta shiga cikin gidan su.Dakin Umma ta nufa ta gaishe ta yayin da ta ajiye jakkan makaranta ta fito.
Dakin baba taje ta gaishe shi sannan ta wuce dakin Umma'n Bilkisu saboda ta shaku da ita duk da bata motsi.Kullum tana ganin baba yana zuwa shiyasa ita ma take yin hakan..
Da sallamar ta ta shiga,zama tayi kusa da Mama sai ta ga alamar hannun mama yana motsi.Da gudu taje dakin Umma..
"Ke lafiya zaki shigo min daki da gudu??"
"Umma,mama ce ta tashi..."
"Ke matsa can da shirmen ki dallah"
Fita tayi taje dakin baba,tana zuwa ta shige jikin sa tana ajiyar zuciya.
"Ya aka yi Saleema ta?"
"Baba,mama tana motsi"
"Meh kika ce?",cewar baba yayin da ya mike tsaye.
Kara maimaita abinda ta fadi tayi.Da sauri ya riko hannun ta suka shiga dakin...Zama yayi a gefen ta yace"mata ta Lami",sai ya ga ta juyo da kan ta a hankali,tana kokarin daga hannun ta......
*********
"Assalamu alaikum",cewar Ashraf yayin da ya shigo falon mahaifiyar sa.
"Wa alaikumussalam. Ashraf kai ne a gidan ga yau?",ta fadi mamaki kaf a fuskar ta..
"Ni ce mama,ina yini"..Kuka ta soma yi ganin yadda yaron ta ya canza cikin mako daya. Duk ya kode ya zama wani iri.
"Meh ya same ka Ashraf,meh yake faruwa? Da na San haka rayuwar auren ka za ta kasance da ban takura maka da cewan kayi aure ba"
"Umma ba laifin ki ba neh,kawai ki sani a addu'a.Nima na rasa mai ke damu na",yace tare da share hawayen da ya gangaro kan kuncin sa..
"In shaa Allah zan cigaba da yi ma.Allah ya kare min kai,ya warware ko ma mene ne yarinyar nan tayi ma"
"Ameen, nagode Umma"..Hira suke tayi na dan abinda ba za a rasa ba amma hankalin shi yana gida.Ya na tsoron Asmee ta dawo,baya gida.Sai kace ba ita ta ce ya je bah...
Minti talatin yayi ya wuce gida.Umman shi dai addu'a take ta yi masa har ya wuce...
*******
Daukawa tayi a hankali ta kai duban ta zuwa ga abinda ke playing.Wani rikitaccen kuka ta fara yi kuma.
"Ke Mallama lafiya??",
Mika masa tayi.Da karfi ya fizge daga hannun ta.Addu'oi ya fara jerawa yana salallami.Ga dai mata biyu a kan jikin sa amma shi bai ga fuskan su bah.
Cillar da camerar yayi kan gado ya rike kan sa da ke sara mai.Wannan wani irin al'amari neh?.
"Ni na yarda da kai,na san baza ka ci amana ta bah.Na san cewa wannan sharri neh aka yi maka amma meh yasa ka kasa yarda da ni?,nima ban san meh ya faru bah,ban san meh ya same ni ba.."
"I'm so sorry,nima kishi neh yasa na kasa sauraren ki..I'm so sorry,ban san meh zan yi miki ki yafe min bah,na san...."
"Shhh..ya isa haka.Ba komai ni na yafe maka. I understand you,kayi hakuri I never meant to shout at you",tace tare da zaunawa kusa da shi a kushin.
Tsananin mamaki ya lullube sa da yaga bata yi hushi da shi ba.Kai amma I'm such a fool,shine abinda yake fadi a ran sa.Ya kasa trusting matar sa..
"You alone mu koma gida gobe please saboda wanda ya hada abin nan,na san yana nan yana bibiyar mu har yanzu..please mu koma gida gobe",tace tare da kwanciya a jikin sa..
"Shikenan zamu koma gobe in shaa Allah, amma kin gama siyayyar da zaki yi ko kuma zamu je mall mu karasa da safe?"
"A'a mu dai mu wuce gobe da safen please"
"Toh shikenan kissy na.I Love You so much!"
"I Love You more!",peck tayi masa sannan ta mike ta cire kayan ta,ta shige bandaki domin watsa ruwa da kuma yin alwala don gabatar da sallolin da bata yi ba..A takaice cikin farin ciki suka kwana,har dan Dubai ma an samu Ina gani....hihi...
Wato abinda Shu'uma ta fesa musu ya sa sun fita hayyacin su har suka manta da abubuwan da ya gudana bayan ya je siyan abincin...
_Washegari suka shirya wuraren karfe goma suka kai airport.10:30am daidai jirgin su ya daga zuwa Najeriya....Ni dai fata na Allah ya sauke mu lafiya saboda a wurin injin jirgi na zauna.
_*A/N:Assalamu alaikum my sweet and lovely fans..na san nayi falling hands din ku cikin 'yan kwanakin nan,abubuwa suka yi min yawa shiyasa amma in shaa Allah zan kokarta na dinga turo 2pages kullum daga gobe domin na kammala novel din da wuri saboda nayi resuming sch so things will be difficult for me..Again,bayan wannan novel din,I'm afraid I'll have to drop writing novels aside saboda nayi concentrating a makaranta..Na san baza ku so nayi failing ba a makaranta koh?I know d answer is yesso,chill as you read this mind brightening chapter! Love you all*_
'.
Mun sauka a airport na Abuja,Najeriya lafiya.Direba yana jiran su Ja'afar already.Kayan su ya karba ya zuba a bayan motar.
Sun iso Niger state wajajen karfe biyu na rana.Daidai gaban gidan su yayi parking.Ya kwashi kayan su zuwa falo yayin da Ja'afar da Bilkisu suka riko hannun juna suna tafiya ciki suna dan hirarrakin su...
"Wow home,sweet home kissy...we are back!",yayi exclaiming yayin da ya zube a cikin kushin..Zubewa tayi a jikin sa itama tace "and no place like home....you alone I.....",murmushi tayi ta kasa karasa maganar..
"Gaya min ko kuma.....",rufe masa baki tayi ta kyalkyale da dariya.A nan suka fara wasannin su har suka wuce daki domin watsa ruwa....
*****
_Asibiti_
"Haba mallam,ya zaka yi wa diya ta haka,diya daya kankat da Allah ya bani a doron kasa kafin na fara wannan rashin lafiyar..uhm mallam?",cewar mama(mahaifiyar Bilkisu)..
"Saboda ke nayi haka.Sanadiyyar yarinyar nan kika shiga halin nan shiyasa na kasa yafe mata tsawon shekarun nan..",baba ya karasa zancen yana share hawaye..
"Haka Allah yaso mallam,amma ka daura laifi ka sa wa 'Yar ka da take bukatar ka,har tsawon shekaru goma sha takwas ka yi da yarinyar ga amma kace min ko kula ta baka yi..mallam baka kyauta min ba,ai wannan ba so bane"
"Ki yi hakuri maman Bilkisu",cewar Mami da ke zaune a gefen ta..
"Toh in ban yi hakuri bah Hajiya ya zan yi..Na gode wa Allah da ya ba wa 'ya ta suruka kamar ki..Nagode da halaccin da kuka yi wa 'ya ta Alhaji,Allah ya saka da alkhairi..."
"Ameen ameen.. ki daina yi mana godiya Mallama,ai da na kowa neh,baka san ko na waye zai rike ka nan gaba ba..Mu dai muna godiya wa Allah da ya karbi addu'ar mu ya baki lafiya...Bilkisu za tayi murna sosai...",cewar Alhaji.
"A'a ai dole na gode muku,Allah ya bar zumunci"...karar wayan Abba neh ya sa tayi shiru.
"Laaa Ja'afar neh,wa alaikumussalam my son,kun dawo neh?..ayya welcome back..lafiya kalau..eh toh muna asibiti...but karda ka gaya mata,Ku dai zo kawai..yawwa sai kun zo.."
"Ja'afar ne koh?"
"Eh shi ne,Mallama 'Yar ki ta na nan zuwa in shaa Allah",cewar Abba..
"Toh nagode,nagode,nagode..uhm"
****
"You alone bismillah koh?"
"Meh yasa kike zumudi neh kissy na,ki bari muje gobe mana",yace tare da zaunar da ita a kafar shi...
"A'a zuciya ta tana raya min cewa wani abin alkhairi zan tarar wajen Mami na,please ka tashi mu je, na dau tsaraban su ko..",tace tare da mikewa tana kokarin daga sa.
"Hahha..ji min 'Yar babyn ga, ni din zaki daga?",dariya yayi sannan ya mike tare da manna mata peck a kumatu..Hannun ta ya rike suka jera zuwa motar shi,ya ja su sai asibiti.
"A'a you alone,ina zamu kuma,wajen waye zamu je a asibiti"..
"Koma waye neh zaki gani in mun isa"...
"Please kar dai kace min wani bai da lafiya.."
"Hey kissy calm down mana, ki aminta da ni,zaki ji dadin abin da zaki gani"..
"Toh shikenan you alone, I love you"..
"I love you more and more sweetheart!"..Dariya tayi saboda yadda yayi stressing maganar..
Bakin asibitin suka yi parking motar sannan suka je reception suka tambaya inda dakin patient Lami Idris ya ke.
Nan take Bilkisu taji wani iri a jikin ta,wace ce wannan mai sunar Maman ta.Nomban dakin aka gaya musu, ya ja hannun ta suka wuce dakin.
Da sallama suka shiga dakin,ganin Mami da Abba da Baba da tayi yasa gaban ta ya fadi.Allah dai yasa ba mamar ta ba ce a ka kawo asibiti..
"A'a Ja'afar har kun gama honey moon din kenan?",Mami tace tare da mikawa Bilkisu hannun ta tana murmushi.
"Uhm..ina yini Mami".tace tare da karasawa gefen Mami tana murmushi...Juyowan da zata yi..idon ta ya hadu da na mahaifiyar ta...
"Maa.mam..maama?",cewar Bilkisu tare da karasowa kusa da ita kana ta taba ta domin tabbatar wa kan ta da cewar ba mafarki take yi bah...Sulalewa tayi ta fadi kasa sumammiya da mahaifiyar ta ta Kira ta da sunan ta....
Da gudu Ja'afar da Mami suka karasa wurin ta amma kafin su ankara sai ji suka yi an bangaje kofar dakin da karfi...
"Ina matacciyar???!!
Monday, November 6, 2017
Sunday, November 5, 2017
TUDUN DAFAWA 2
TUDUN DAFAWA Part 2
.
"Asmee,wannan yarinyar aminin Abba ce,jiya ya kawo ta gida,she would be living with us",ya karasa maganar cikin harshen turanci.."ohh,I see..toh meye sunan ta?",inji Asmee.."Bilkisu",ya amsa a takaice..
Kyalkyalewa da dariya tayi harda rike kirjin ta da hannu daya, dayan hannun kuma Samsung galaxy dinta ta rike dashi,"so funny!,'yan mata kika bari aka sanya miki sunan tsoffi?",ta karasa maganar tana dariyar iskanci.."please would you stop dt,its irritating!, ai kema sunan tsoffin gare ki,Assama'u","kai bros ka daina bana so Allah",tace tare fa shagwabe fuska."Toh ke ma ki daina bata so",ya fadi yana murmusawa..
"Toh bros,Mallama wai baki iya gaisuwa ba neh?koh nayi kama da kanwar ki ko tsaran ki neh?",da sauri Bilkisu ta sunkuyar da kan ta,idon ta cike da hawaye taf,"ina wuni anty","hhhh,so smart harda anty?.."please ya ishe ki haka nan! Kanwa ta,taso mu wuce",Ja'afar yace..
"Haba bros just kidding her n..","laaa bros kai ne a gidan mu yau?, wata yarinya tsarar Bilkisu ta sauko daga bene ta katse maganar da Asmee take yi.."Hey Zahratee baki je sch ba yau?,cewan Ja'afar,"a'a bros,wallahi bani da lafiya ne","subhanallah sorry Zahratee,Allah ya sawwaka Lil sister","ameen big bro,who is she bro,she is cute",ta tambayi Ja'afar yayin da taje kusa da Bilkisu ta tsaya tana mata murmushi..
"Friend na kawo miki, kinga school dinku ma za ta but ita a primary 3 za a sa ta,her name is Bilkisu,yarinyar friend din Abba ce","primary 3??!,suka fadi lokaci daya,"wannan katuwar yarinyar?",cewan Asmee.."hmm..daga Gurmana aka dauko ta,so she is just a fresher a school","ok,yanzu naji zance,Bilikisu suna na Zahra,ni kanwar yaya Ja'afar ce",cewan Zahra yayin da ta miko wa Bilkisu hannun ta domin suyi musabaha..Murmushi Bilkisu tayi sannan ta maida wa Zahra da martani...
"Toh lil sis sai kun hadu a sch gobe,mu zamu wuce kenan".."ok bro ka gaida min da Mami na",cewan Zahra.."Toh zata ji,nima ki gaida min da Mommy in ta dawo","toh zata ji,bye Bilkisu"..."oh ni baza a sallame ni bane?",cewan Asmee da ke tsaye a wurin tamkar zata fashe saboda sun share ta..."oh sorry na manta ki na nan,bye Assama'u",kwafa tayi kana taja tsaki ta hau bene abin ta su kuma suka fita daga falon..Zahra tayi musu rakiya har parking space,suka wuce.....
*Ubay bn Ka'b Islamic school* suka zarce kai tsaye,inda ya siya mata form na islamiyar 2-6,wato bayan ta tashi daga makarantar boko,drive zai garzayo islamiya da ita, sai 6 ya dawo ya dauke ta...Fitowar su ke da wuya daga islamiyar,tace "yaya shin ni za a sa a wa'ennan makarantun?,tambayar ta bashi dariya sosai amma murmusawa yayi kawai kana yace da ita,"eh can da muka je dazun,shine school din da zaki dinga zuwa,wannan kuma na islamiya"..
"Ayya Mami da Abba,ni ban san da wani baki zan yi musu godiya ba,sunyi min komai a rayuwa, yaya Allah ya saka muku da alkhairi, nima ina son ku yadda kuke so na",ta fad'i tare da share hawayen da ya gangaro mata akan kuncin ta..Tausayi ta bashi ainun,"ba komai kanwa ta,ke dai ki sa ido a karatu,kuma banda biye biyen kawayen banza",Toh zan kiyaye in shaa Allah yaya"...
"Kanwa ta wai me yasa ba kya son yin magana neh?",ya tambaye ta yayin da yake tuki,"ina yi mana yaya",inji Bilkisu harda dan dariyar ta.."wow,yau ne rana ta farko da naga dariyar ki,I love it!",cewan Ja'afar..Dariya ta kara yi saboda yadda yayi far da idanu,daga nan hira ta barke a tsakanin su har take bashi labarin kawar ta, Fatima da ke kauye..Amma bata gaya mai komai game da muzgunawar da ake mata ba...
*Alhaji Muhammad Isma'il*
.
Shine mahaifin su Zahra kuma mijin kanwar Mami,Hajiya Khadija..Yana aiki ne a CBN dake Abuja shiyasa baya samun zama a gida kowani lokaci..Kowani karshen mako yake zuwa duba iyalan sa kuma ba abinda zasu bukata da baya basu sai dai inda karfin shi bai kai ba..Yana da fara'a sosai,ga son talakawa da kuma taimaka musu.Shi amini ne ga mijin Mami.A bikin Abba da Mami, Alhaji Muhammad ya hadu da kanwar Mami....
*Hajiya Khadija*
Itace mahaifiyar su Zahra kuma mata ga Alhaji Muhammad sannan kuma kanwar Mami,wato mahaifiyar su Ja'afar..Hajiya Khadija kyakkyawa ce fara sol, ga ta da kyaun diri..Amma halin ta sai ita, idan tana son mutum,wallahi ko za a fadi aibun wannan ba zata ki shi ba,idan kuma ta qi mutum,ko za a fadi alkhairan sa so nawa ne,baza ta taba son sa ba..Gata da kyankyamin talakawa,a wurin talaka ba komai ba ne akasin Mami da ta dau kowa nata neh.Ita matron ce a asibitin gwamnati dake garin Minna.......
*Asma'u Muhammad*
Ita ce 'ya na farko ga Alhaji Muhammad da Hajiya Khadija. Ita fara ce amma ba sosai ba,tana da Kama da Daddyn su.Tana da kimanin shekaru 17 a duniya.Halin ta daya da na mahaifiyar ta,ga dagin kai da rainin wayo sai dai Allah ya jarrabce ta da bala'in son Ja'afar, shiyasa duk inda ta ganshi sai ta susuce ta zama tamkar wawiya..A shekaran ga ta samu _admission_ a FUT Minna inda zata karanta _Biochem_.....
*Zahra Muhammad*
.
Itace 'ya ta biyu kuma ta karshe ga Alhaji Muhammad da Hajiya Khadija.. Kammanin ta daya sak da na mahaifiyar ta sai dai ita halin mahaifin ta ta dauko.Akwai ta da son mutane da girmama na gaba,kowa nata neh..Tana da kimanin shekaru 12 a duniya,kuma tana jss3 a _*Galaxy international school*_.. Tana 9yrs tayi walimar saukan alQur'ani,yanzu hadda take yi a _Bilal bn Rabah_ kowani karshen mako..Wannan kenan!......
.
******** *Cigaban labari*
.
_''Hello,boy''_,cewan Ja'afar.."kai waye boy din ka,dan rainin hanks",cewar abokin shi,dayake Ja'afar yasa call din a _handsfree_ saboda yana tuki."Ashraf yane?", _"I dey oo steady!!_"ya su Mumcy da old man?,"lafiya kalau suke",inji Ja'afar.."mun samu admission fah!!","woah!!,yaushe ka duba mana??"cewan Ja'afar,"wallahi yau na duba,dukkan mu sun bamu courses da muke so harda su Ubaid da Sufyan"..
"Oh alhamdulillah!, _congratulations to all of us_,gaskiya naji dadin wannan news din",cewan Ja'afar.."Ok then,za a fara registration mako mai zuwa,dukkan mu zamu hadu ranar Monday muje muyi harda su payment na school fees cox beginning of next month zamu yi resuming which is 3weeks away"cewan Ashraf.."alright,sai mun hadu in shaa Allah",inji Ja'afar.."ya mutumiya ta ne wai?"..
"Tana nan dai yadda ka san ta,yanzu muka baro gidan su","oh my love,yarinyar nan tana birge ni sosai" cewan Ashraf."kai ba na son iskanci fah,ku karata can,bye"..Ja'afar ya yanke call din.."kanwa ta mu wuce gida ne ko na kai ki yawo kuma?","a'a ni dai muje gida,kila Mami ta dawo yanzu"..."toh as you say my sister".."A cuce waye yaya na?"cewan Bilkisu...
Kyalkyalewa yayi da dariya ganin bata gane turancin da yayi ba sai yace"nufi na shine,duk yadda kika ce,haka za ayi"..dariya tayi har sai da dimples dinta ya lotsa.."asi say ma sita,koh?",ta maimaita..Dariya yayi kana ya gyara mata sannan ta dinga maimaitawa har sai da ta iya..
"Bilkisu zan wuce makaranta nan da sati uku",dafe kirjin ta tayi kana tace "haba yaya?,tare zamu koh?,"ya zamu je tare kuwa,koh kin manta zaki fara zuwa makaranta neh?","wai har na manta,toh Allah ya bamu sa'a dukkanmu".."ameen kanwa ta,dan Allah karda ki sa muji kunya,kisa hankali a karatu sosai,be the best!!","be the best",ta maimaita maganar,yace"wow,kinyi kokari,kisa himma kinji koh?","toh in shaa Allah yaya"....Haka suka cigaba da surutun su har suka isa gida...
*********************
"Ke yaya wai meh yasa kike wa mutane haka ne?"cewan Zahra.."ke kuma asu wa da kike tambaya ta?"Asmee tace tare da watsa mata harara.."Allah ya huci zuciyar ki"Zahra tace tare da barin dakin.."mtsssw har Ja'afar ya dizga ni gaban village brat din nan,wallahi na sa mata karan tsana ta kenan,mtcchhhw",ta kuma yin tsaki kana tasa headphone dinta ta fara jin dabsy...
" _Hello,anybody home_?",cewar Mommy da ta shigo babu ko sallama.Zahra na jin ta amma tayi cim, bata amsa ta ba.."ke,ashe kina nan kina ji na,shine kika ba wa iska ajiya ta koh".."oh,sorry ma naga ba sallama kika yi ba shiyasa",Zahra tace tare da tsuke baki.."iyye,har karamar kwaro kamar ki ce zata fada min abin yi koh?u are stupid!",Mommy ta karasa zancen tana gallawa Zahra harara sannan ta wuce dakin ta..
Zahra dai halin mahaifiyar ta da yayan ta yana bata haushi amma ta rasa yadda za tayi.Mahaifin ta kadai ne gwanin ta kuma ba ya zama tare da su."Allah ya shirye ku",ta fadi tare da mikewa domin ta gabatar da sallar azahar...
.
*Kauyen Gurmana*
.
"Allah da gaske kake yi wai zamu koma birni??"cewan Umma yayin da take sa wa *Saleema* kaya.."eh wallahi,kinga shiyasa nace tsinanniyar nan annoba ce a gare mu,ji fa duka duka kwana biyu kenan da Alhaji yazo ya wuce da ita,gashi har alkhairi ya same mu,gwamnati ce ta bada takardun gidajen ga hakimi cewan duk wanda yake son gida a farashi mai sauki ya same shi,shine da ni,da Mal Auwalu,da Mal Musa muka siya,nawa da na Mal Auwalu suna kusa da juna neh,zuwa sati in shaa Allah zamu tattara inamu inamu mu wuce".
"Kai Mal amma naji dadin wannan zancen,sai dai wani hanzari ba gudu ba,wani aiki zaka cigaba da yi a birnin?","eh..toh,haka ne fah,zan yi magana da Alhaji ko da aikin masinja ne ya saman min"."toh madalli,amma dai a nan zamu bar waccan koh?",cewan Umma."waccan matar ka mana da bata da bambanci da......","kamar ya fa?ban gane ba.ke mai yasa idan ana zancen alkhairi sai kin dauko na sharri a ciki,haba meye laifin a wuce da ita can,'yar uwar ki ce fa.kuma lalura yasa take kwance haka nan,haba kiji tsoron Allah mana, mtccchw".Baba(Mal. Idrisu) ya karasa zancen da tsaki.Ni kam nace su Baba manya, har kana da bakin cewa wani yaji tsoron Allah, toh Allah shirya..
.
Umma kuwa tun da ya fara magana taga ran shi a bace yake, ta sha jinin jikin ta,"yi hakuri Mal ,subutan baki ne".."ke kika sani dai"baba yace tare da mikewa zuwa dakin mahaifiyar Bilkisu.."ki taya ni murna Lami,Allah ya azirta mu da gida sanadiyyar wucewar yarinyar da ta zamo silar kasancewar ki haka,ba zan taba yafe mata ba!!"........
*Billionaires quarters, Thursday*
Bilkisu ce na hango sanye da riga da skirt na kanti sannan da dan karamin hijabi kamar na jiya dai.Tayi kyau sosai.Sch bag ne sakale a bayan ta sannan da farin safa da bakin takalmi a kafarta.Sultee ne biye da ita sanye da uniform dinsu da ya kasance kamar kaftan,kalar baki da ruwan toka sannan da bakaken takalma da sch bag.Biye da su shine oga Ramlan..lolzzz. Yana wani takun kasaita da gayu,sanye yake da uniform iri daya da na Sultee sannan da sch bag irin wanda ake sakalawa a kafada....
Mami ce ta fito tana gyara saitin hijabin ta da gilashin ta a lokaci daya kasancewar sun makara har Abba ya riga ta fita..Ja'afar a gurguje ya fito shima ya shiga mota ya tayar..Ganin Bilkisu zata nufa wurin kofar seat na gaba,Ramlan yayi sauri ya shige gaban ta ya tsaya..Komawa baya tayi ta shige motar..Duk abinda ya faru kan idon Ja'afar aka yi amma saboda sauri suke yi,bai ce Kala ba duk da bai ji dadin abinda ya faru ba..Motar Mami ne ya fara fita sai na Ja'afar,kowa ya kama hanyar sa..
Sai da ya kai su Sultee tukun sannan ya kai Bilkisu itama.Wajen auntyn ajin su ya damkata tare da yi wa auntyn baya ni a kan ta sannan ya sallame ta ya wuce..Tana shiga ajin taga duk kananan yara ne sa'oin kanwar Fatima(8yrs)sai wata kamar tsaran ta da ta hango ta kujera na karshe.."class kunyi sabuwar kawa,da fatan za ku zama abokanai da ita, sunan ta BILKISU IDRIS",(dukka wannan bayanin cikin harshen turanci auntyn ke magana).."sannu d zuwa Bilkisu",('yan ajin suka fadi a harshen turanci).Murmushi Bilkisu tayi saboda bata san mai suke cewa ba.
"Ki bisu kuyi musabaha(handshake)",(Aunty Aisha ta fadi a harshen turanci tare da yi mata nuni da hannu)..Haka Bilkisu ta bisu daddaya tayi musabaha da su.Duk wanda tayi musabaha da,sai ya/ta fada mata sunansa/ta..Tana kaiwa wurin yarinyar nan,Aunty tace mata ta zauna a wurin.Zama tayi tare da yin musabaha da ita, yarinyar tace "sunana SAMEERAH NAJEEB".Murmushi Bilkisu tayi sannan suka maida hankali ga abinda Aunty Aisha ke rubutawa kan allo....
.
*_Lokacin break 10:00am_*
Bilkisu ce zaune a wurin kujerun shakatawa da ke karkashin wata bishiya tana kallon yadda kowa ke harkan sa..Sai ji kawai tayi an dafa ta,tana dagowa ta sake murmushi ganin wacce ta dafa ta..Zama tayi kusa da ita kana tace "Ashe da gaske bro yake yi,an kawo ki sch din mu",cewan Zahra..
"Eh wallahi",Bilkisu ta amsa a takaice."kun kai gida lafiya jiya?,"lafiya lau Anty Zahra".."wooahh,karda ki kara kira na da anty bayan ni tsarar ki ce,Zahra ma yayi min",Zahra ta fadi rai a bace."Toh kiyi hakuri Zahra",cewan Bilkisu."haba ko ke fah?",murmushi Bilkisu tayi."kinyi break ne koh?",Zahra ta tambaye ta."a'a bana jin yunwa","are you sure?",shiru Bilkisu tayi tana kallon ta,lokacin Zahra ta tuna ashe fa bata gane turanci,sai ta murmusa tace"kin tabbata ba kya jin yunwa?",a nan Bilkisu ta gane ma'anar _'are you sure?'_."eh bana jin yunwa"."toh shikenan"..Haka Zahra take ta jan Bilkisu da hira har ta sake jiki da ita,Zahra tayi mata alkawarin koyar da ita abubuwan da aka yi a classes da bata yi ba,a kowani break...
Suna zaune a wurin suna hira sai ga Sameera tazo ta zauna itama aka tsunduma duniyar hira da ita har Bilkisu ta ke basu labarin kawarta Fatima.Nan dai suka kulla kawance da juna dayake Zahra bata son 'yan ajin su saboda suna da jijji da kai,Sameera kuma yaran aji sun yi mata kanana..
Kullum suna makale da juna lokacin break.Da lokacin tashiwa yayi kuma zaka gansu tare a bakin gate har sai direbobin su sun zo daukan su...Haka rayuwa ta kasance wa Bilkisu, da safe ta na school,da an tashi ta wuce islamiya.Yayin da Ja'afar ya zama kullum yana nan ya na can batun registration din su..Sultan kuwa shine abokin hiran ta kuma mai koya mata abu in ya shige mata,sam bata da girman kai..Ramlan kuwa sai abinda ya karu na muzguna mata amma bata sanar da kowa sai dai taci kukan ta in yayi mata abu..Aunty Aisha kuma tana zuwa gida kowane asabar da lahadi domin koyar da ita bisa ga magiyan da Abba yayi mata da kuma alkawarin biyan ta dubu biyar kowane karshen wata...
*Bayan sati daya*
.
Ranar juma'a tana dawowa ta shige dakin ta saboda babu kowa a gida,direba kuma ya je kwaso su Sultan daga makaranta.Tube uniform tayi wanda ya kasance riga kalar sky blue da skirt navy blue da karamin hijab shima kalar sky blue,sannan ta tube bakin takalmin ta da farin safa dake kafar ta..Tawul ta daura ta shiga wanka,tana cikin wanka taji karar ana bude kofan ta da kuma muryar mutum,amma bata gane ko muryar mace ce ko namiji ba.Da sauri2 ta karasa wankan,ta dauro alwala ta fito gaban ta na faduwa...... *Wa zata gani???!!*
"Wayyo Fatima!!!",Bilkisu tace tare da rugawa da gudu ta rungume ta,da kadan towel dake jikin ta ya kwance..."Bilkisu kin gan ki kuwa??",cewan Fatima."zo zo zo,zauna, daga ina haka?",ta tambayi Fatima tare da karbar ledan da ke hannun ta.."Wallahi daga gida,ai mun dawo nan da zama mu ma,muna anguwar Bosso estate neh"."kai amma na taya ku murna,Allah ya sanya albarka a gidan, yasa ayi rayuwa mai alkhairi a cikin gidan,ameen"..
"Baba ne ya kawo ni ma",cewan Fatima."oh Baba,bari na sa kaya muje mu gaisa",tace tare da mikewa tana shafa mai a gurguje."Baban ki nike nufi fah,kuma muna isowa ya juya ya tafi abin sa"..jikin Bilkisu yayi sanyi da ta ji wai baban ta ne ya kawo Fatima amma ko tsayawa bai yi bah domin ya gan ta.Duk da hakan dai, ta ciro wani rigar kanti gown ta sa sannan taje kicin ta zubo musu abinci saboda ita da Mami sai sunyi abinci kafin su fita...
Tana kawo wa,taje ta dauko bottled water da kofuna sannan tazo ta zauna a gefen Fatima suka fara cin abincin."Shi baban meh yazo yi a birni,ko dai ke kika matsa mai ya kawo ki",cewan Bilkisu.."Ni? A su wa?!!,ai su ma sun dawo nan birni da zama,kuma gidajen mu na kusa da juna neh yadda muke a can dai,kar dai kice min ba ki sani ba??",cewan Fatima..
"Hmm,Fatima ya zan sani kuwa?,sanin kan ki ne tun da na zo birni ban kara leko kauyen mu ba duk da bai da nisa da nan"inji Bilkisu.."Toh Allah shi kyauta,nima sai da na hada da magiya kafin ya yarda ya kawo ni"..."Bilkisu kin fara zuwa sch ne?",murmushi tayi kana tace "eh na fara.......",nan ta fara zuba tana ta bawa Fatima labarin sch dinsu har da kawayen da ta samu,da uwa uba Ja'afar kuma..........
Mikewa suka yi,suka je suka yi alwala,Bilkisu ta sake wani alwala kuma..Bayan sun idar da sallah,Bilkisu suka cigaba da hira har sai da Mami suka dawo sannan suka sauka kasa,suka gaida Mami.Can Abba shima ya dawo.Sun yaba halayyan Fatima kwarai har yasa suka ce zasu bar Bilkisu ta dinga zuwa mata ziyara..
***********************************
*Bayan mako biyu*
Ranar litinin da yamma Ja'afar ya shirya tsaf,yaje falo sallaman su Mami da Abba. A yau ne zai wuce makaranta kasancewar ya gama registration kuma an fara lectures.Shi da abokanan sa zasu wuce,suna jiran sa a gareji..Ranan Bilkisu bata je islamiya ba.Taci kuka har ta gaji tamkar ba zata kara ganin shi ba.A karshe dai bayan iyayensa sunyi masa nasiha,suka ce da su Bilkisu su shirya su raka shi gareji..
.
Kuka tayi sosai a gareji kuma,har abokanan sa suna ta mata dariya,Ubaid har da cewa ko za ta bishi neh?,tsuke fuska Ja'afar yayi kana dukkan su suka kama kan su..Haka dai suka yi sallama kowannen su rai wani iri.Ramlan kuwa tamkar ya zuba ruwa a kasa ya sha domin mai kare 'yar iskan ya wuce...Tun a mota ya fara yaba mata magana amma ta ki amsawa saboda ta san mai zai biyo baya in ta amsa shi...
Bayan sati daya da wucewan Ja'afar,Mami da Abba suka yi tafiya zuwa kauyen su Mami da ke paiko.Nan fa Ramlan ya samu garabasan gallaza wa Bilkisu.Akwai ranar da zasu je sch kuma sunyi latti,sai yace ta je ta dauko mai juice a firij,tana shiga ciki yace ma direba su wuce saboda Bilkisu tace zata hau acaba taje.Shi kuwa direba bai san wainar da ake toyawa ba,ya ja motar suka tafi...Tana fitowa ta ga wayam,mai gadi yace mata ai yanzu suka wuce.Tamkar ta zube a wurin ta dinga kurma ihu taji amma ta kasa,Allah yaso Abba ya bata kudi kafin su tafi...
Fita tayi ta fara neman acaba,da kyar ta samu lokacin karfe takwas da minti ashirin,gashi ana basu punishment in sunyi latti.Suna isa ta biya dan acaba sannan ta karasa bakin get,manya2 buloli ne ta ci karo da,kamar ta ruga a guje ta koma gida,amma ya ta iya?,karasawa tayi ta shiga aka sasswade ta sannan tayi picking kana aka bar ta ta wuce class...
Kuka take tayi lokacin break,su Zahra da Sameera suna ta bata hakuri,da kyar tayi shiru.Duk haka ta yini ranan ba dadi,Ramlan yana ganin ta ya kece da dariya sannan ya taka kafar ta da yazo gittawa..Sultan shi dai sai dai ya bishi da ido sannan ya bawa Bilkisu hakuri....
.
Kafin Mami suyi tafi,ta yi ajiyan kudade masu yawa a wardrobe, haka Ramlan yaje ya kwashe kudin nan tas, yaje ya kashe na kashewa shi da abokin sa Shareef.. Sauran kuma ya je wani mini market dake kusa da su,ya siya snacks irin packaged one din nan ya je ya ajiye a dakin Bilkisu ta inda baza ta gani ba sannan ya kuma diba cikin kudin yayi squeezing ya sa a wardrobe din ta..
Mami ta dawo tana ta neman kudi amma wayam kudi tace dauke ni inda kika ajiye ni.Hauka kadai ya rage Mami bata yi ba ranan saboda kudin da aka bata ajiye ne a wurin aikin su na case din wata mata da za ayi running.Kudin da za a ba wa lauyan da zasu dauka kenan.Allah yaso lokacin Ja'afar yazo weekend a gida.Tuni Abba ya kira dukkan su falo..
"Ni ba barawo ba ne,mahaifiyar Ku ba barauniya ba ce,ta ya na samu barawo a cikin 'ya'ya na,wa ya shiga dakin mahaifiyar ku ya dauki kudi?!,dim!! gaban Bilkisu ya fadi wadda itama bata san dalilin faduwar gaban bah.."ba kwa ji na neh?!, nace wa ya dauka kudin a cikin Ku?!,look at how your mum is crying,who the hell took the money among you??!!!",shiru suka kuma yi.."Oh ba zaku yi magana ba koh??!..ok"..
Daki ya shiga ya dauko dorina,Ramlan yana ganin haka ya tsure,sai yayi saurin hada plan,"wallahi Abba kai ma ka San tunda muke nan gidan ba a taba yin sata ba sai yanzu,ple...","kai meh kake nufi??,kana son ka ce min Bilkisu ce ko meh, you're very stupid!!!..Bilkisu dai jikin ta sai bari yake yi."Ja'afar je ka duba dukka dakunan su",cewan Abba..
.
Bayan minti talatin,Ja'afar ya fito da kudi a hannun sa zuciyar shi cike da rashin yarda da bacin rai."Ab..Abba gda wanda na gani",yace tare da mikawa Abba kudin da ke hannun shi."a ina ka ga wa'ennan,tabbas wannan shine kudin saboda ni ban ba wa kowa irin kudaden nan ba kafin na wuce,a dakin wa ka gani?"..
"A..a..a dakin Bi..bi..Bilkisu na gan...",kafin ya karasa zancen Mami ta wanke shi da mari."har da kai za ayi wa Bilkisu sharri,yaushe ka fara biyewa Ramlan?!".."wallahi Mami a dakin ta na gani,kije ki duba yadda nayi scattering wardrobe din ta,a nan na gani"ya fadi hawaye na gangarowa kan kuncin sa...
Mami ba ta yarda da zancen Ja'afar ba,wucewa tayi zuwa dakin Bilkisu,lallai kuwa a nan ya gani saboda wani rafar kudin ma yana ciki bai hango ba,zarowa tayi zata fita sai ta hango leda a can loko2n gadon ta,tana budewa ta ga snacks cike da ledan.Daukawa tayi kamar wacce bata da laka a jiki ta fita zuwa falo..
Tim!! ta yar da ledan a gaban Abba,Bilkisu na gani ta fara zazzaro idanuwa,sai hawaye sharrr.Mami na zuwa dai2 wurin Bilkisu ta kwashe ta da mari. Ni kam nace hmm Mami rai ya baci, Bilkisun ki ce fa!."na dauke ki tamkar 'ya ta na ciki na amma kike neman ki tozarta ni a wajen aiki na?,meh zan ce musu,yarinyar da nike riko ta saci kudin da suka bani ajiya??,ban ga laifin mahaifinki ba da ya tsane ki,ke annoba ce!!"..Hmm Mami ta fita hayyacin ta ooo..
"Wallahi Mami bani na dau....",ki yi min shiru!,ko wata biyu ba ki kai ba da zuwa gidan nan amma har kin soma nuna halin ki,you are no more needed here,ki tashi ki bar mana gida,daman iyayen ki suna nan kusa oya a bar mana gida kuma Allah ya isa amana ta da kika ci as small as you are!!!"..Bilkisu dai sai kuka take yi tana ba wa Mami hakuri tana cewa bata san komai gami da abubuwan nan ba amma ko a jikin Mami...
"Please stop all this!!,meye haka wai??!",cewan Abba."ta bar gidan kawai that's all I know!!,sannan ta ja Bilkisu waje ta tura ta da karfi ta fadi.Ja'afar ya biyo bayan su yana hawaye,zuciyan shi na bashi cewan she is too innocent to do that..Hankade shi Mami tayi ta shige ciki..Ramlan kuwa wohoho dadi kashe shi.Ni kam nace karda kayi murna da yawa saboda in ka shiga hannu,baza ka ji da dadi ba..Sultee ma yana ta kuka ya ruga daki da gudu.Abba ya rasa nayi ma,da kyar ya ja kafafuwan shi ya zube a kushin..Duk jikin shi yayi sanyi,amma ya rasa nayi..
"Tashi muje",Ja'afar yace mata tare da miko Mata hannu,da gudu ta rungumeshi tana kuka,"yaya wallahi ba ni ba ce,yaya na shiga uku,babu mai sona,na rasa TUDUN DAFA WA,ina zan je??kowa ya tsane ni,kace Mami tayi hakuri,wayyo yaya na shiga u.....","shhhhh,ya isa bari zan kai ki gida,zanyi wa baba bayani kinji kafin Mami ta huce"..Ja'afar ya san halin Mami,in tayi hushi sosai,loosing control take yi kwata2,ya san zata yafe mata amma shin waye yayi mata wannan sharrin?,tabbas ba zai wuce Ramlan ba neh,amma why does he hate her that much da har zai kulla mata irin wannan sharrin,he needs to be interrogated.............
....
"Dakata dakata,meye haka?,nace ku dakata,meh annobar ga take yi a nan?",Baba yace a fusace.."Dan Allah Baba kwantar da hankalin ka nayi maka bay.....","kai Ku fita min daga gida!"cewan Baba."Ina son na ga Mama don Al...",amma bai bari ta karasa maganar ba ya hankade ta da karfi,"Ku fita nace"..."mallam lafiya?",cewar Umma da ta fito tana karkade zane...
"Ayyo Bilkisu ce,zo mana'ya ta",cewan Umma.."ke nace Ku fita".."haba mallam ka bar....".."babu ruwan ki a zancen nan,koma daki".Sum sum sum ta shige daki gaban ta na dukan uku2 saboda ganin yadda Bilkisu ta murmure.."Allah ba ka hakuri,tashi mu je kanwa ta"...Tana mikewa ta fadi sanadiyyar kashin kafan ta da ya goce saboda faduwa da tayi kansa sau biyu.Hannu ya sa ya dago ta,ta soma tafiya ta na dingishi,suna kaiwa wurin kofa,ta bige kafar ta,wani ihu ta saka kana ta kankame shi,"innalillahi wa inna ilayhi rajiun,wayyo kafa na yaya"...Daga ta yayi suka fita sai mota. A bayan mota ya kwantar da ita, sai ihun azaba take yi.Da gudu ya figi motar,sai wurin masu gyaran kariya......
"Haba wifey,meh yasa kika dau hukunci tun ba ki yi bincike ba,yarinyar nan tana ta cewa ba ita bace ta dauk.....","Abban Sultan ya isa please!"Mami tace tare da daga hannun ta tana kuka..
"Nima jiki na yana bani cewan ba ita bace,amma lokacin raina ya bace,I couldn't restrain myself, I was so stupid,na dau alhak...!!","shhhh,I understand, amma ki daina yawan yanke hukunci ba tare da kinyi bincike ba".."in shaa Allah na daina,gashi ban san inda yarinyar nan taje ba,na shiga uku,wayyooo Bilkisu na!"..Shiru Abba yayi kana yace "amma wane ne da wannan aikin??,someone must be investigated!",yace sannan ya fita..Ni kam nace, Ramlan! Sai ka yaba wa aya zakin ta,sai ka gwammaci kidi da rawa..
"Ya kafar yanzu?,"yana min zogi yaya",tace tare da share hawaye.Haka yake ta tuki duk jikinshi yayi sanyi yana tausaya wa Bilkisu..Daidai gaban get ya tsaya yana honk,tunanin abinda zai fadi yayi convincing Mami da Abba yake yi.Maigadi na bude get ya gaida shi yaja motar ciki.Bilkisu sai zazzaro idanu take yi,tana tunanin ina za ta je in Mami da Abba suka kore ta..
Sallama yayi ya shiga falo tare da Bilkisu da ke goye a bayan shi.Mami da Abba da ke falo mikewa suka yi suna kallon su kana Mami ta karaso gaban su."Mami dan Allah ku yi hak.....",abinda Mami tayi ya sa ya kasa karasa maganar da yake fadi.Bilkisu ta cire daga bayanshi ta dora ta a kafadan ta ganin katon bandage dake kafar ta..Zama tayi a kujera da Bilkisu a kan cinyar ta sannan ta rusa kuka..
"Ki yafe ni Bilkisu,ki yafe min,mene ne nayi haka,sanadiyya ta kika samu wannan ciwon,kaico na.kai....."."Mami babu komai,ba ki yi min komai ba amma please Mami ki yarda da ni ban dauka miki kudi ba"..ta karasa maganar tare da rungume Mami.Sai rizgar kuka suke tayi..Abba neh ya katse shirun,"kai Ja'afar jeka ka kira Ramlan da Sultan sannan kaje dakin Mamin ku ka dauko ledar da snacksa din nan ke ciki","toh Abba"...
Bayan sun fito gaba dayan su kowannen su ya zauna harda Ramlan da bai lura da Bilkisu ba saboda yana chatting,gyaran murya da Abba yayi shi ya sanya Ramlan dago kan sa.Ido hudu yayi da Bilkisu,nan take jikin shi ya fari bari,zazzaro idanu yayi jin abinda Abba ya fada."Ja'afar je ka wurin Hamisu ka tambaye shi wanda yazo ya siya wannan a wurin shi"..Mikewa Ja'afar yayi,nan da nan gumi ya keto wa Ramlan,sai zufa yake ta yi...
Bayan minti sha biyar ya dawo,saukan mari ya dawo da Ramlan duniyar da ya shiga."you are cruel,kai wani irin yaro neh?,meh ke damun ka,in iskokai kake dashi,to yau zanyi maka rukiyya da kaina",cewan Abba.Mami da Ja'afar da takaici ya cika su,shiru suka yi suna kallon su.."Kai Sultan je ka dauko min dorina a daki",da gudu Sultan ya ruga dakin mahaifin su."Abba kayi hakuri ba zan kara ba",yace tare da share zufan da ya jika fuskarshi.Ko kallon gefen shi Abba bai yi ba..Sultan na kawo dorina ya mike ya karba kana ya shiga da shi dakin horo dake gidan,kulle kofan yayi da sakata ta ciki..
.
Ba wanda yace ko kala a cikin su.Bilkisu kuma sai jimamin abin take yi a zuciyar ta.Meh yasa Ramlan ya tsane ta ne har da yi mata sharri,kodayake ta saba da tsana da tsangwama tun tana karama..Habawa ihu kake ji mallam, Abba yana cire aljanun jikin Ramlan..lolzzz.. Sai da yayi mai isar sa sannan ya bude kofar ya tura mage ciki kana us rufo da padlock..Ramlan na bala'in tsoron mage,yana gani us fara ihu yana zufa yana kiran Mami amma ba Wanda yayi ta kan shi,asali ma mikewa suka yi suka bar falon..
Can da dare Bilkisu tazo wucewa zata kicin,taji mutum yana cewa ruwa..ruwa,juyawan da zata yi sai taga Ramlan ne ta taga,duk ya canza ya zama wani iri... Kicin taje ta dibo mai ruwan gora mai sanyi ta kai meh, tana isa ya gan itace,jiki na bari ta mika mai, cafke hannun ta yayi kana ya watsa mata sauran ruwan da ya sha a jiki sannan yace,"mun zuba kenan ni dake,I will make sure you hate life".................
*Hmm,ba Bilkisu kadai ba,har sai da nima naji gaba na ya fadi da irin threatening din nan*
Bayan wata daya da faruwar hakan,Bilkisu suka fara midterm test.Wata malamar fine arts ta basu assignment akan suje suyi cardboard mat da kuma fure (roses) na paper..Tana isa gida ta sanar da Abba saboda ranar yana gida bai je duba shagunan ba.Nan da nan ya bata kudi yace ta siyo wajen Hamisu..Godiya tayi sannan taje ta zira hijabin ta ta fita siyo cardboard da water color....
Tana tafiya tana karatun Qur'ani dayake hadda da bita take yi a islamiya,sai ta hango motar gidan su,nan take ta sha jinin jikin ta saboda wanda ke cikin motar.Ba kowa bane face Ramlan...Sultee sai da yamma ake dauko shi saboda yana tsayawa a islamiya na sch wanda suke yi har alhamis..
Motar na kaiwa wurin ta,ta dauke idon ta da wuri,harara ya galla mata kana yace wa direba ya tsaya.Daidai inda take ya tsaya,"ke! Ina zaki?",yace mata yayin da yake saukar da gilashin motar."i....in..ina...ina son naje na siya cardboard paper neh",tace tana i'ina..
"Mtsssssw,mai ido kamar na aljanu kawai,Sule ja motar mu tafi",yace cikin isa babu koh girmama Sulen da ke da yaro sa'ar shi a gida...Sum sum taja kafs(lolzzz) dinta zuwa shagon Hamisu tayi siyayyar ta..
Tana isa gida,library ta shiga ta kama aikin weaving tabarma na cardboard paper.. Da kyar ta samu yankan yaje dai2..Awa uku taci tana hada shi,abin yayi kyau sosai da ta gama..A lokacin maghrib yayi sai ta fita taje ta gaida Mami a daki.."Abban ki yace kina nan kina assignment koh?",Mami ta tambaye ta..."eh Mami".."toh nima ayi min mai kyau in kun gama test,Allah shi baki sa'a,yayi miki albarka".."ameen Mami"..Daga bisa ni ta sallami Mami taje tayi sallah sannan ta koma library..
.
Sultee ta tarar a libraryn yana assignment.Ganin abinda take yi sai yaji sha'awar abin kana yasa hannu suka fara hada furen tare..Yayi kyau sosai.Bayan ta gama na assignment, sai tace bari suyi wa kowa da kowa dake gidan..Sultee yayi mata wani mai pink and light blue color, yayi kyau sosai sannan yayi wa Abba Red and green... Bilkisu kuma tayi wa Sultee dark blue and white sannan na yaya Ja'afar red and white,best color din shi kenan.Sannan tayi wa Ramlan Blue and black da ratsin white,maigadi kuma purple da white...
Raba ma kowa suka yi kana ta boye na Ja'afar a locker dinta yadda ba zai cikwuikwuye ba..Kowa na ta yaba kokarinsu amma banda Ramlan da yake ji kamar ya fashe don tsabar haushi..Can da dare ya tashi yaje library saboda ya gan Bilkisu a can ta bar assignment dinta..Zuwa yayi ya zuba duka paint din a kai kana ya yayyamutsa su sannan yayi murmushi yace "mutum sai iyayi"...
Washegari ta tashi confidently taje tayi aikin gida ta shirya,a lokacin ko waiwaya library bata yi ba.Sai da za ta wuce taje daukowa taga abinda kadan ya rage ta hadiye zuciya ta mutu..Tana fitowa taga sun wuce saboda ta tsaya tana kuka a ciki..Ranan a sch tun Anty nayi mata fada har ta gaji ta koma lallashin ta..A takaice ranan bata shiga shirgin kowa ba don takaici..Su Zahra ma da kyar ta gaya musu abinda ya faru..
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa ga Bilkisu da Ramlan muguuu..
*A gurguje plzzz....*
*Bayan shekara biyar*
.
"Wayyo dan Allah kuyi hakuri karda Ku min fyade..Al...llahu..ma ajirni fi musee..ba..ba..bati,wakhlifny khairan minha",take ta fadi yayin da samarin suka yi sheqeqe,ko a jikin su.."Wayyo Ku bar min yaya na,meh tayi muku",cewar Saleema yarinyar Umma..
Saleema tana bala'in son yayan ta tun da ta dawo gida da zama.Umma ce ta tasa Baba a gaba har sai da yaje ya dauko ta..Mami tace Sam baza ta yarda ba,sai da Abba yasa baki yace 'yar su ce,ta bari ya wuce da ita...Umma bata son yadda yarinyar ta ta shaku da Bilkisu amma babu yadda ta iya....Soyayya mai karfi kuma ya kullu tsakanin Ja'afar da Bilkisu.. Hakan ba karamin dadi yayi wa su Mami ba..Haka tana aji na karshe
Kenan a school yayin da Saleema take nursery 3..Ramlan yana IBB lapai inda yake karanta _Mass comm_.Sultee kuma yana zaman gida saboda ya gama school a 14yrs akace baza a iya bashi admission ba sai ya shiga 16yrs..Bilkisu da Saleema suna dawowa daga makaranta neh 'yan daba suka sace su zuwa wani gini da ba a gama ba a unguwar...
"Wayyo kuyi hakuri",cewar Bilkisu...B'arka mata vest yayi saboda sun cire long sleeve rigan ta sun cillar.."kai yarinyar akwai dukiya fa,ai dole mu cika aikin oga",wani cikin su yace yayin da yake kokarin cire wandon sa..daga bakin kofa suka ji wani yana cewa"kai! Ku dakata ni zan fara tukun"sannan yayo kan Bilkisu ya fizge skirt dinta cikin zafin nama sai ya..........
.......
*Wayyo Bilkisu, Wa zai kawo mata dauki???*
*Ku biyoni don sanin wa ya aika ayi mata fyade kuma wa ke shirin yi mata fyade!!!*
Ja'afar yana karyo kwana cikin anguwar su Bilkisu ya hango wata kamar Saleema tana fitowa daga wani gini tana kuka.Honk ya fara busa mata tun daga nesa amma ina?? Ko tsayawa bata yi bah sai ya sauka a gaban ginin domin yaga ko lafiya take gudu?...
"Allahuma ajirni fi musibatee,Bilkisu!!!!",ya Kira sunan ta tare da zubewa akan gwuiwansa ta gefen ta..Tana kwance jina jina,dukkan tsiraicin ta a waje... Wani kuka mai tsuma rai ya fara yi..
"Why?,why?,me kika yi musu suka yi miki..."bai ma iya karasa zancen ba,ya rike hannun ta yana jijjiga ta yana kuka..
"Kan uban can me zan gani haka??"
Da sauri ya dago ya kalli Umma dake tsaye tana wani karkade jiki kamar budurwar tunkiya..
"Umma kalli abinda suka yi wa...."
"Kai ja'iri yi min shiru,kun gama jin dadin Ku sannan kace wani wai wai wasu,Dallah ke zo mu wuce"
"Umma wasu n...
"Ke yi min shiru kizo mu wuce kuma sai babanku yaji zancen nan""
"Wallahi Umma nima ban san wanda yayi..."bata bari ya karasa maganar ba ta ja hannun Saleema suka wuce..
"Wato sharrin da Umma zata laqa min kenan,Allah gani gare ka"..Kallon ta ya kuma yi ya tuna cewan bata ko numfashi.Da sauri ya gyara mata sch skirt din ta sannan ya ciccibe ta zuwa mota...
Da gudu ya figi motan sai kofar gidan su Bilkisu. Yana shiga ya ci Karo da Saleema.
"Kanwa ta,je ki dauko min riga da zani da hijabin yayar ki"
"Toh yaya",tace sannan ta juya taje dakin.
"Anyi abin kunya ai dole ta kasa zuwa ta dauka da kan ta"cewar baba da ya fito daga dakin Umma.Umma tana biye dashi tana murgude murgude..
"Wallahi baba ba.."
"Yi min shiru ai ba yau na saba ganin Ku tare ba,sai ka dauke ta kuje anguwa kuyi ta shashancin Ku koh??.,yau ka kasa hakura har...."
"Baba ya isa! I can't take this anymore!,Saleema kawo min kayan nan"
"Eh lallai fa,mallam ai dole ya daga ma murya,tunda 'yar ka ta bashi kan ta"
"Yaya zan bika",cewar Saleema tare da gyara hijabin ta.Hannun ta yaja suka fita yayin da baba da Umma ke bin su a baya.
"Ke dawo nan"
"Ka dauke ta domin kaje ka karasa iskancin da ita koh,ke don ubanki baza ki dawo ba?!",baba ya karasa maganar cikin tsawa.Koh ta Kansu Ja'afar be bi ba,motarsa yaja suka kama hanyar Dr. Wahab hospital....
Da isar su aka basu gado a ER.Ja'afar ya rasa nayi,ya rike hannun saleema gagam.Saleema kuwa sai kuka take tayi tana cewa "yaya".Can ya zare wayar sa ya Kira Abba.
"Hello Abba"..ni kam nace Ja'afar an manta da sallama yau...
"Abba please kuzo Dr Wahab hospital yanzun nan"
"Lafiya son? Me ya faru?"
"Abba Bilkisu ce.sun..sun...kai Abba kuzo dai"
"Toh sai mun zo,just keep calm kaji??"
"Toh Abba",sannan ya katse kiran.
********
*_Bosso Estate_*
.
"Wallahi ba zai yiwu ba mallam,ka tashi muje gidan iyayen yaron nan"
"Toh sawo hijabin ki muje",yace kana ya juya ya shiga dakin mahaifiyar Bilkisu.
"Lami kin ga abinda annobar nan tayi koh?,tana so ta zubda mana da mutunci"
"Lami kiyi hakuri amma dole na aurar da yarinyar nan kafin ta karasa ni nima",ya karasa zancen rike da hannun Mama a hannun sa..
"Uh..uhm,mallam sai ka fito muje koh?",cewar Umma da ke matukar jin haushi in taga mallam yana magana da mahaifiyar Bilkisu.. Ni kam na ce mata hoo! Kishi harda wacce bata hayyacin ta,Allah ya ganar damu.
Fitowa yayi ya burga babur dinsa da ya siya kwanaki,Umma ta hau bayan mashin din sai gidan su Mami..
"Assalamu alaikum"
"Wa alaikumussalam, sannun Ku da zuwa",cewar Mami da take saukowa da hijabin ta a hannu..
"Habeebee ga su Umman Bilkisu sunzo"
"Sannun Ku da zuwa cewan Abba da ke saukowa daga bene"
"Yawwa Alhaji"
"Asibitin zaku kuma koh?",cewan Mami..
"Oh ashe har sun kira ku?",cewan baba.
"Eh",Mami ta amsa da sauri,"muje koh?"
"Ai batun wucewa bai ma taso ba",cewar Umma..
"Toh,da fatan lafiya dai koh?",cewan Abba da yake kokarin zama.
"Wallahi Ja'afar yaci amanar 'yar mu,fyade yayi mata fah",cewan Umma.
"What?!",Mami da Abba suka ce lokaci daya..
"Ke Mallama bama son rainin hankali fah,dan namu zaki yi wa sharri?",cewan Abba a fusace.
"Alhaji ina jin kunyar ka fah,ka bari tayi maka bayani mana",cewan baba.
"Bayanin banza,na san Ja'afar dina ba zai yi haka ba",cewan Mami da ta gama quluwa..
"Yi shiru Wifey,bari tayi bayani"
Zama Mami tayi kana Umma ta zayyana musu karya da gaskiya harda hawayen munafurci,har tana cewa da idanun ta biyu ta gansu a wannan yanayin.
Baba shi dai bai ce komai ba..Yadda Umma ta bada kagaggen labarin ta,ko za a sa maka wuka a wuya ne mutum zai ce gaskiya take fadi...
"Mu Ja'afar zai zubda wa da mutunci,toh in shi mutumin banza neh,mu ba mutanen banza ba neh,shi yasa ya kasa gaya min abinda ya same ta da na tambaye shi",Abba ya fadi a fusace tare da mikewa.
"Wifey zo mu wuce asibitin muga halin da innocent girl din nan ke ciki",mikewa Mami tayi ta bishi,su Umma ma suka bisu a baya.Duk jikin Mami ya yi sanyi,ta kasa yarda da cewan Ja'afar din ta zai yi haka.
*******
*_Dr Wahab Hospital_*
Suna isa suka hango Saleema da Ja'afar a bakin kofar shiga ER.Saleema tana hango su ta rugo da gudu tazo ta rungume Mami ta na kuka,
"Mami su ne..su ne.."
"Ke don uban ki wato sai da kika biyo shi bayan abinda yayi wa yayar ki koh",cewan Umma da ta ga Saleema za ta tona mata asiri.
Ja'afar da yaga Saleema ta ruga da gudu, sai ya kalli wurin yaga su Mami ne ke zuwa,sai ya taso yana share hawaye.
Yana isa gaban su Mami ya bude baki zai yi magana kenan kawai sai saukan mari yaji..
"Ashe kai dama yaron banza neh ban sani ba?"
"Ab..b.baa",Ja'afar ya kira mahaifinsa da i'ina.
"Meh tayi maka that you have to punish her this way??,why did you rape her??"..
"Rape her!rape her!!rape her!!",maganar dake ta ringing a kunnen sa kenan..Kawai zubewa yayi a wurin sumamme.
Mami na ganin haka ta kira nurses,Abba kuwa ko a jikin shi..Nurses maza suka zo suka dauke shi tare da baba da ya taimaka musu. ER suka wuce dashi shima,da yake sun san shi ya kawo Bilkisu,suna tsammanin mijin ta neh tun da sun gano cewan raunin da ta samu na saduwa neh,an shige ta sosai.Sai suka kai shi dakin da take itama..
Mami kam in banda kuka da addu'a babu abinda take yi.Ya zata yi,yaran ta biyu a lokaci daya sun shiga wani mawuyacin hali. "Meh yasa bamu yarda mun aurar dasu ba lokacin da yace yana son ayi auren",cewan Mami a zuciyar ta..
Abba kuwa sai basu baba da Umma hakuri yake yi yana kara jin takaicin abinda Ja'afar yayi.
Sai da likitoci suka ci awa biyu a kan Bilkisu ana dinka ta saboda ba karamin rauni taji bah,da ta farfado sai ta firgita ta suma kuma.A na ukun ne bata suma bah,sai kuka take tayi tana fadin "ka yafe min"..Can anjima aka fitar da ita zuwa special ward meh gado biyu a ciki inda aka mayar da Ja'afar da dadewa saboda ya farfado kafin ita.
Abba suna ganin an shigar da Bilkisu dakin,suka je su ma.Fashewa da kuka tayi da ta gan su Abba..Juyawa tayi ta bangaren Mami da Ja'afar.
"Mami kice yaya ya yaf...."
"Bilkisu zan kwatan miki 'yancin ki,bazan yarda Ja'afar yaci galaba a kan ki a banza ba",Abba ya katse ta.
"Ab..bb.ba,ban gane ba",cewan Bilkisu.
"Nufi na shine sanadiyyar fyaden da Ja'afar yayi miki,na yanke hukuncin daura meh aure da ke!!"
"What!!!",cewan................
"Hello,yaya gamu a gidan Ku amma only Sultan is at home,wai ance mai kuna asibiti"
"Waye bai da lafiya?"
"Ja'afar da Bilkisu?,toh Allah ya sauwake..bari mu garzayo can",Mommyn su Asmee ke waya da Mami..
"Mommy wai meh ya same su?",cewan Asmee..
"Bari dai sai mun je asibitin",cewan Mommy...
Zahra kam duk hankalin ta ya tashi da taji cewan an kwantar da su Bilkisu a asibiti.
Sultan ma mikewa yayi ya bisu..Suna is a Dr Wahab hospital suka shiga reception suka tambaya inda special ward yake aka kai su...
Suna shiga dakin kenan Abba yake cewa,"............nah yanke hukuncin daura meh aure da ke!!"
***********
"What?!!",cewan Asmee yayin da ta karaso ciki da sauri..
Lokacin Mami suka lura da isowar su.."A'a,har kun iso",cewan Mami.
"Eh wallahi, ya masu jiki?"
"Toh jiki alhamdulillah",Mami ta karasa zancen tana shafa kan Ja'afar tamkar karamin yaro..
Kowannen su suka gaida Su Mami, Abba,Umma da baba banda Asmee da take son jin karin bayani game da abinda kunnen ta ya jiye mata..
"Ke baki iya gaisuwa ba koh",cewan Mami da take jin takaicin halin Asmee..
"Ya zanyi gaisuwa bayan naji ana wani zance da ya tada min da hankali"
Da mamaki Abba ya juyo ya kalle ta kana ya tambaye ta cewan''wani zance kenan Asma'u"
Sunan da ya Kira ta neh ya kara kular da ita."zancen wai ko bros za a yi wa aure da wannan",tace tana wani murza idanu kamar mujiya..
"Eh za a daura wa yayan Ku aure da Bilkisu neh,Do you have any problem with that?",cewan Mami..
"Ya zaku yi min haka bayan kun san shi nike so,in fact shi nike jira shiyasa banyi aure bah",tace tare da sa musu kuka...
Kallon ta kowa ya ke yi bama kamar Bilkisu da Ja'afar bah..Shi Ja'afar yaji dadin zancen auren su da aka yi amma tunani daya neh ya makale masa a kwakwalwa..Shin wanene yayi wa Bilkisu irin ta'addancin nan?,so wani ya riga shi sanin matan shi kenan...
Bilkisu kuwa abubuwa da yawa ke yawo a kan ta?,daman yaya neh yayi mata fyade?kai bashi ba neh,suna da yawa fa,but would he accept me the way I am?,he doesn't deserve me.Na kasa kare mutuncin kai na..
"Why me?,why,why.....",abinda Bilkisu ta soma fadi kenan tana kuka.
"Shhhh..Bilkisu ke daina fadin haka nan kina nufin cewa *Allah bai isa dake kenan ba koh ko kuma kina da ja da abinda Allah ya nufa,Sam Sam wannan ba Kalmar da ya kamata ya fito daga bakin musulmi ba neh*",cewan Mami da ta rungume ta...
Zahra ma zuwa tayi ta zauna a gefen Bilkisu ta rike mata hannu tana mai murnar Bilkisu zata zama Inlaw din su amma ita ta kasa gane sauran zancen da ake yi,amma ohho dai happy she!!
Sultee shima zama yayi a gefen Ja'afar ya rike hannun sa.
"Congrats bro,ashe ciwon so kuke yi a nan",murmushi kawai Ja'afar yayi wa Sultee..
"Kai yi mana shiru ba ma son shashanci a nan,ke kuma Asmau idan munje gida zamu zanta da ke",cewan Abba da zancen Asmau da Sultee ya kara kular dashi..
"Toh mu zamu wuce,kun san mun bar mahaifiyar ta a gida,anjima zamu dawo mu dauke ta",cewan Umma da kwata2 bata ji dadin zancen auren su ba.Ta so Abba ya kore Ja'afar neh sannan ya tsani Bilkisu amma ko kadan bata ga alamar cikan burin ta ba,amma babu matsala tunda ta samu abokiyar adawa da su,wato Asmee...
"A'a ba sai kun dawo ba ma,zamu kai ta can gidan mu har taji sauki tunda sanadiyyar mu ta samu wannan raunin",cewan Abba..
Baba bai so hakan ba saboda ya so ne yaci kaniyar ta in sun je gida amma ba yadda ya iya."Toh",yace kawai sannan ya riko hannun Saleema da take gefen Zahra..kuka Saleema ta Fara yi..
"Ni dan caya da yaya.wayyo yaya Jara zan caya da yaya Bikitu neh",amma ina Baba ya finciko ta waje ya sata a gaban Babur,Umma ta hau baya suka yi gaba..
Duk Mami tana Lura da take taken su musamnan Umma,bata yarda da matan nan ba..
"Toh muma zamu wuce,sai mun leko Ku a gida",cewan Mommy fuska a daure..
"Toh mungode Khadija,jazaakumullahu khairan,sai kun zo "..
Ko amsa addu'ar basu yi ba,kofar fita suka nufa Mommy ta juyo ta kalli Zahra da koh motsawa bata yi ba daga inda ta ke.Watsa mata harara tayi kana ta ce,
"Ke kuma yaya haka?"
"Ayya Mommy ki bari na tsaya da ita please"
"Saboda kanwar uwar ki ce koh?"
"Aah Mommy meh yayi zafi haka,kiyi hakuri mu je",Zahra tace tare da sumbatar goshin Bilkisu ta sallame ta kana taje wajen Ja'afar shima ta sallame sa sannan ta sallame su Mami,Abba da Sultee.
Finciko ta Asmee tayi suka fita daga dakin.Baki galala Mami da Abba ke ta kallon su har suka fita..
Ja'afar kuwa dadi yaji da suka wuce saboda baya son irin kallon da Mommy da Asmee suke ta yi wa Bilkisu.Ajiyar zuciya yayi sannan ya juya ta daya bangaren ya fara barci..
Bilkisu ma dadi taji da suka wuce saboda sun takura mata da harara.Kara gyara kanta tayi a jikin Mami yayin da Abba da Mami suka ce mata sannu lokaci daya..
.
Mikewa Abba yayi yace zaije gidan kanwar sa da ke Farm center ya karbo musu abinci..
"Uhm Abba,Mahneerah tace zata kawo in 20minutes time",cewan Sultee yana dan soshe soshen kai kamar mara gaskiya..Mami dai ta gano inda dan ta ya dosa,murmushi kawai tayi..
"Ok ka sanar da su neh?",cewan Abba..
"Eh",ya amsa da..
"Ok bari naje na ga Alhaji Muhammad domin muyi magana kan yarinyar nan,naji kince Mommyn su Zahra tace ya na gari"
"Toh,a dawo lafiya",cewan Mami rai a bace.Ita dai duk da ta san yaron ta yayi laifi,amma bai kamata Abba ya yadda a hada shi da Asmee mara kunyar nan bah...
**********
Wata beautiful girl na hango tana tafiya tamkar dawisu..Kana ganin ta,ka ga yarinyar da tasha hutu amma.........da tarbiyya mai kyau.Sanye take da tiyobo hijab mint color sannan da black socks.Fuskar ta yasha ado..nikam nace da kin hada da niqabi ai..
Tana da slim face,sannan idanuwan ta dara dara,kwayar idonta grey color ne da black Wanda yayi mugun fito da kyawunta.Gata da long eyelashes sannan da bakin gira da karamin madaidaicin bakin ta da yasha lip glow.
Rike take da food basket tana shigowa ta reception din Dr Wahab hospital.A yadda na karance ta,shekarunta ba zasu haura 14 ba,sai dai tana da jiki mai kyau...
*Mahneerah!!*,naji Sultee ya kira ta da yake zaune a wurin yana jirar ta..Irin murmushin da ta sake yasa waya na ta fadi tsabar kyawun ta da yayi min shoki.............hahha
*Mahneerah Sadiq*
Itace yarinyar kanwar Abba dake zaune a farm center..Itace only sister na Abba,Hajiya Rahma..Kyakkyawa ce sosai,kamanninsu daya da Abba sannan tana aiki a wuri daya ne da Mami..Mijin ta Alhaji Sadiq Sadauki shine CEO na Jap.made Cars Limited.
Mahneerah itace only daughter na su kuma suna ji da ita sosai.Mummynta ta bata tarbiyya mai kyau duk da irin daulan da ta tashi a cikin sa..Ba abinda zata nema ta rasa a wurin iyayen ta amma wasu lokutan ana hana ta wasu abubuwan domain ta san ana rashi wani lokaci a rayuwa saboda,'yan Karin magana sunce ba kullum a ke hawa gado bah..
Mahneerah ta kasance yarinya mai fara'a,sam2 bata kyamar talakawa saboda haka ta taso taga iyayenta,suna kyautatawa jama'a..Ga ta da kokari a makarantar boko da islamiyya saboda har musabaqa take zuwa da quiz competitions..She is so nice to be with!!
*** *Cigaban labari* ***
"Ya Sultee",ta kirashi da funny voice din ta.Karban basket din abincin yayi daga hannunta sannan suka karasa cikin dakin da aka kwantar da su Bilkisu..
Har yanzu Bilkisu tana nan tana kuka saboda duk lokacin da ta yi yunkurin mikewa,sai taji kamar gaban ta zai yanke ya fado don azaba.Mami kam sai bata baki ta ke yi har su Sultee suka shigo dakin..
"Mahneerah ta,matso nan"
"Ina yini Mami",tace cike da jin kunya.
"Lafiya lau baby na,ya gida,ya Mummyn ki??"
"Lafiya lau,alhamdulillah, Mummy wai tana gaishe ku, tace zata shigo anjima da dare"
"Toh madalla,amma taje wajen aiki yau kuwa?"
"A'a,itama tana gida,Mami ya masu jiki?"
"Alhamdulillah Mahneerah,Ja'afar ma yana bacci"
"Anty Bilkisu,ya jiki??",Mahneerah ta tambaye ta tare da karasowa gefen ta.Daga mata kai tayi alamar da sauki..
Zama tayi a kujeran dake gefen Sultee kana Mami tace musu tana zuwa,ta fita waje..
********
Sai da Bilkisu ta kai sati daya a asibiti kafin aka sallame su da cewar zasu dawo a kwance dinkin.Ja'afar kuma yana nan yana zirga zirgan auren sa da Asmee saboda Abba yace tunda bai iya controlling din kan shi bah,za a aura masa Asmee da Bilkisu amma Asmee ce zata tare kafin Bilkisu saboda ba zai so ta kara jin rauni ba bayan na da.Ba yadda Mami da Ja'afar basu yi bah cewan Abba ya janye zancen aurensa da Asmee amma ya ce sam..
Hakan ya sa Ja'afar da Bilkisu a cikin damuwa duk da Ja'afar bai sake wa Bilkisu fuska kuma saboda itace silar abubuwan da ya faru cikin dan kwanakin nan..Abin na matukar damun Bilkisu yadda ya juya mata baya a lokacin da ta ke bukatan mutum a kusa da ita..
Zahra,Sameerah da Mahneerah suna zuwa wurin ta kullum,har Zahra da Mahneerah ma suka tattaro inasu2 suka tare a gidan Abba.Ba karamin dadi Mami ta ji ba saboda tana bala'in tausaya wa Bilkisu ganin Ja'afar ba ya kula ta..
A bangaren Ja'afar kuwa ya rasa wurin da zai sa kan sa,kwata2 ya rasa *tudun dafa wa*..Kullum cikin addu'a yake Allah ya tabbatar masa da alkhairi game da bikin nan.Asmee uwar rawan kai kullum sai ta Kira shi fiye da sau ashirin kamar zautacciya,kodayake ta zauce akan soyayyar da take yi wa Ja'afar din ta...An sa date na biki nan da two months domin Bilkisu ta samu ta rubuta exams saboda Abba yace ba ita ba school sai bayan ta tare zata fara zuwa makarantar jami'a.A yanzu dai za a cigaba da yi mata lesson har ta rubuta external exams..
*Bosso estate* ***
"Wai mallam haka cigaba da zuba wa Alhajin nan ido har sai yasa an daura auran nan?"
"Toh in bai aure ta bah,wa zai aure ta,haka kurum ya lalatata ya wuce?"
"Ni kam bai dace bah,ya aure ta suje su cigaba da iskancin su,haba mallam ka Kara duba zancen mana"
"Zancen banza zancen wofi,ba matar shi ba ce ko sunyi iskancin bare ai tsakanin mata da miji babu iskanci,bana son irin zancen nan"
"Toh Allah ya baka hakuri",cewar Umma tare da shigewa daki tana maganganu..
Mikewa Baba yayi ya shiga dakin mahaifiyar Bilkisu wato Mama."Lami kin ga 'yar ki koh,irin rayuwar da ta zabar wa kan ta ba mai kyau ba ne,saboda kwadayin kudi ta sake wa namiji jikin ta,ya lalata ta,kai yarinyar nan baza ta taba ganin haske ba a rayuwar ta",ya karasa zancen yana jin wani daci2 a zuciyar sa....
*One week kafin biki*
"Hehhe Amaryar yaya Ja'afar kin sha kamshi",cewan Mahneerah..
"Hmm,ke dai kyale,taji dadin ta,she is getting married @ 18,wallahi ance yafi dadi mace tayi aure at this age",cewan Zahra da ke gefe tana admiring yadda Bilkisu ta kara kyau tayi mulmul..
"Please girls,Ku bar zancen nan",cewan Bilkisu da sam2 zancen su ba ya mata dadi saboda gani take kamar Ja'afar ba ya son ta, so baza tayi enjoying auren ba kamar yadda suke tsammani..
"Hmm,ana so ana kaiwa kasuwa,mu dai a bar yin munafinci,na san Allah2 take yi taga kan ta in his arms dauke da dan babynmu a ci...",dukan da Bilkisu ta kai mata yasa Zahra ta kasa karasa maganar..
"Wallahi sai na rama"..Nan suka fara bin juna a guje suna dariya sai ji kawai tayi ta ci Karo da mutum...
"Tassssss!"kake ji kawai,karar saukan mari. Dagowa dukkan su suka yi a firgice domin ganin wanda yayi marin kuma wa ya mara... Ido hudu suka yi da Ja'afar da ke tsaye gaban Bilkisu yana huci...
"Ke wata irin yarinya ce,kina abu kamar baki san kin girma bah iyye??,wato jin dadin ki ma yayi yawa har da guje2 kike yi,ni ina can ina shan wahala saboda bakin cikin da kika cusa min,da auren Asmee zanji da koh kuma da.....",da sauri ta sa hannu kan bakin shi domin karda ya karatsa sauran zancen saboda ko da wasa bata son Sameera da Zahra suji wannan zancen..
A fusace ya cire hannun ta daga kan bakin shi sannan yayi nuni da ita yace "be careful!",sannan ya raba ta gefen su ya wuce...Zubewa tayi a wurin ta fara kuka mai tsuma rai.Su Zahra ma jikin su yayi sanyi,durkusawa suka yi a gefen ta suna bata hakuri..
"Ke,Dalla can da kukan munafuncin nan,ai yaya ma yayi kokari da ya yarda da cewan zai aure ki",cewan Ramlan da basu ma san ya shigo bah..
"Haba,Ramlan,maimakon ka bata hakuri shine kake kara yi gaya mata magana mara dadin ji ",cewar Zahra.
"Please kiyi min shiru,ba ki san cin amanar da yarinyar ga tayi mana ba,second hand crap kawai!!"
"Please Ramlan kayi min rai kayi shiru,karda ka fadi",cewan Bilkisu cikin shesshekar kuka.
"Dan Allah Ku yi min bayani,kun samu a duhu,what's going on??",cewan Mahneerah.Sameera kam shiru tayi kafin tayi magana ya yaba mata magana...
"Ki zo garden anjima da dare,i will tell you everything!",yace tare da yin wani shu'umin murmushi ya haye sama abin shi..Rike ta suka yi zuwa daki..Bilkisu kuwa hankalin ta ya tashi,bata son Ramlan ya fada musu halin da take ciki,dole ta nema hanyar bashi hakuri..
Wuraren karfe shida na yamma taje ta roke shi cewan karda ya fada masu, ya rufa mata asiri cox itama bata san yadda akayi mata fyaden bah.Cewa yayi ya ji amma taje ta dawo anjima ta same shi a garden,zai yi wata magana da ita..
Nan da nan tace toh,not knowing that akwai abu a kasa..Bayan an idar da maghrib yayi mata flashing alamar ta zo garden sannan ya kuma yi wa Zahra call itama..
Da sauri ta fita daga daki taje, dai2 Zahra na fitowa daga kicin da coffee da yace tazo dashi..Tana isa garden tazo gittawa a gaban shi sai yasa mata kafa ta fado a jikin shi,dai2 Zahra tana shigowa da coffee din a hannu...
"Bilkisu????!!",ta fadi tare da sake cups din coffee din a kasa ta juya da gudu. Kafin tayi yunkurin kwace kan ta,sai ga Ja'afar ya shigo..."Ramlan??Bilkisu??",yace tare da garxayowa inda suke cikin bacin rai....
*Toh fah,another wahala don come