"Ki shiyar insha Allah yau zan baki ajiyar Baby kinji dazu my friend yana cewa wai in baku kud'i Ku seyo mai babynda zasuke wasa tare".
.
Murmushi tayi cikin manna mai kiss a goshi tace .
" Allah Hamma
Dady nason yar uwa ko yanzu cewa yayi muje kasuwa mu saya wai ai gidan ya Auwal su yaransu 3 wai mukuma shi d'aya munk'i mu karo mai".
"Kin dai san ni ba rego bane Allah ne bai kawo ba muyi ta Addu,a".
" ni mako ba raguwa bace ka Sani sarai".
Kai tsaye bedroom din Khadija ya wuce a kan gado ya sameta konce
Daddy na gefe yana rik'e da hannun ta cikin gwaran cinsa yace.
"Ammi tashi Baby kasu my Friend saya mana"
"Wai kai wanne irin yaro ne mai nacin tsiya ancema
kai seyoka akayi bare a seyoma k'anin yau naji fitina da naci,
Wlh bakaji dad'i ba tunda ko halin naci irin na Abban ka ka kwoso maza fita kaban wuri".
" hi my friend"
lkci d'aya ya had'iye kukan sai kuma ya bud'e d'an hannushi ya d'aura kan hannun Mahmoud d'aya bud'e mai suka tafa cikin k'aunar yaron ya nuna mai kuma tunshi tare da cewa "kiss me my lovely boy"
cikin dariya sosai ya sumbaci kuma tunsa sannan yace.
"My Friend yau zaka saya mana baby ko?".
" insha Allah yau dinnan ko yanzu ko da dare zan sama mak'a k'anwa ko k'ani".
"Bari naje na gayawa Anty zamuje market mu samo yaro".
" jeka Allah yama albarka da kai da kannen ka masu zuwa gaba".
"Zaujee shine harda biye mai wai yanzu zaka zamo mai sai kace wasan yara".
" insha Allah yanzu zan baki ajiyar da dare na baiwa Abida".
" ni dai gsky bacci nakeji yanzu kuma na gaji ma kawai kaje gun Abida dan ni nafita girkin yau".
.
A hankali ya juyota rigingine sannan ya mata rumfa da k'irjinshi cikin yin piki-piki da ido tare da lasan lips enshi yace.
"Kiyi hak'uri kike daurewa ki zama jaruma kike d'aukar buk'a tun mijin ki wlh raunin ki na hanani rawan gaban hantsi ina gaya miki ba kyau mace take nuna gazawar ta ga mijinta".
" toh a hankali kuma awa d'aya ".
" in ankisa kiran sallan maggariba dai jam zaki huta tunda zanje nai sallah".
Mami da Adda Asabe da Fatima gaba d'aya suke k'aunar Khadija da d'anta bare sauran yan,uwa kam.
yaro d'an shekara 30 ya cika da haibar jiki da zuciya ga dukiya ga zuriyar sa ta yalwatu da kyewawan 'ya'yanshi masu kama da yayam larabawa
Yaro mai mata 2 da yara 5 Khadija nada yara 3 Ibrahim sai yan biyu mace dana. miji da ta kara haihuwa Amina takwarancyn Mami suna kiranta Meenal sai Aliyu wanda suke kira Haydar.
sai,
Autan su Aysha.
tana shiga Abida ta mike cikin sanyi ta cewa yaran.
"Kutashi muje Ku konta su Ibrahim da Haydar da Sani kam tuni suka fice suna good night Abbah
dan dama sun gaji,
Cikin sanyi ta sa hannu ta karb'i Aysha dake bacci kan cinyarsa ,
Sannan ta kalli Meenal dake mak'aleshi tana "uhum uhum ni a gun Abban zan kwana".
.
Cikin had'e fuska Khadija tace.
" maza bace min da gani yarin ya sam bakya girma kina shekara 7 amman kina abu kamar yar shekara 2".
Cikin tsoron uwar ta zame ta sauk'a tana kuka,
har sunje bakin k'ofar fita Mahmoud yace.
"Zo nan Meenal zo mamana zo gun Abban ki".
ta konta gefen shi cikin sanyi yace,
"Abida kije zan kawota in tayi baccin"
"Wonka fa?".
sannan ya zo ya ciccibi Meenal ya nufi d'akin Abida yana zuwa ya kontar da ita sannan ya dawo gaban ta ya d'an sunkuyo ya subbaci goshin ta cikin sanyi yace .
" Good night ".
kai kawai ta jinjina sannan ta shafa sajenshi cikin rad'a tace.
" I love you".
Murmushi yayi tare da cema ta.
"Me 2"
Sannan ya fice abinsa .
a hankali ya bud'e idon ya tsura su kan surar jikin ta,
Ita kuwa sai d'an tura baki tayi gami da zare after dress din jinta ta cillah kan kujera sannan ta zuge zip din rigar jinta ta d'an bud'e rigar sannan ta b'alle bel din k'ugunta wondon ya koma k'asa k'adan. sannan ta d'an juya gaban shi cikin salon Jan hankali.
cikin wani irin voice yace.
MI'WASMITI,
NAYI NADAMA,
Domin a yanzu na gane cewa
NAMIJI BAYA KAD'AN,
Nakuma tabbata Kaine
Noor la Noor a cikin rayuwa ta a yanzu da nan gaba" ```
"Ehh nasan wannan Amman yanzu me matsalar ki?".
" k'aik'ayi nakeji anan ta nuna k'irjinta ta ka sosa min kar nayi ma kuka".
har zuwa d'an wani lkci sannan ya d'an zame bakin shi
cikin rawan murya yace.
"K'aik'ayin ya tafi ne? ko sai munje bedroom?".
" Sai muje bedroom ".
Cikin kuzari ya ruggume ta ya nufi bedroom da ita suna shiga ya direta kan gado cikin rada yace.
" Baby na bari enje in rufe mana k'ofar k'afar d'akin
kar Aysha Ali Garkuwa ta shigo ta gammu bare ta samu abu rubutawa fans d'inta gobe,
Haka kuwa akayi yazo ya rufe musu k'ofar ban kuma ganin suba.............
.
Allah ya amsa mana niyar mu da aiyu KANMU na Alkhairi.
Ina mai Neman gafararku mace ko namiji babban ko yaro wacce nasani da wacce ban saniba Wanda nasani da Wanda ban sani,
Banyi littafi nan dan Na b'atawa kowa raiba Wanda banyi daceba kuma ya b'ata musu rai kuma toh a gafar ceni a daurani kan mizani na ajizanci irin na d'an adam
kuyi hak'uri insha Allah zan Baku goron sallan in Allah ya kaimu lkci
Byeeee sai mun had'e a goron sallan ku
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Na Aysha Ali Garkuwa
NAMIJI BAYA KAD'AN tirk'ashi lallai wani kayan sai amale bigi sai bigi babban goro sai magogin k'arfe.
Aysha Ali Garkuwa
Suna mai farin jini a duniyar gizo-gizo suna mai shekin imani da ilimi
Da akoi wannan rainakon a musulunci da Nana Khadija bata buk'aci Annabinmu Abin koyinmu ya Aureta ba abinda kuma muka sanine ya Aureta,
shine novel dinnan ya tunar damu.
Aysha Ali Garkuwa Allah ya miki albarka Allah ya k'ara d'aukaki Allah ya biyaki da jannatul Firdausi da wannan tunasarwa da kika mana.