ARNE Part Five (5)
.
Haka rayuwa ta kasance tsakanin faryal da kamil sai dai su hadu a waje amma ba gidan ba Domin kuwa run ranar haj mariya ta sa ido sosai akan kowanne daga cikin su Inaso ka bincika min waye saurayin faryal a garin nan""" khalid ya Fada ma guard din sa guda daya dake tsaye cikin office dinsa Ogah me za amasa in angansa,? just get his name da enda yake kabar min Sauran Ok sir yafada ya fice " Sake daukan wayarsa yayi ya cigaba da jera mata miss cols din da taki kulawa tun tuni Mikewa yayi ya ja tsuka straight ya dosa hanyar makarantr su, Bayan tsawon nemanta dayayi bai sameta Dan gefe ya nema ya zauna ya jira ko zata fito don' an tabbatar masa da bata tafi gida ba Daga nesa ya ganota tana tsaye tana waving kamil da har ya kusa ficewa a haraban schl din Minti daya bai kara a zaune ba ya mike ya Isa wajen, Cahkwamota taji anyi wanda yasata juya wa a firgice,. Ke dan ubanki kifada min waye wannccan kazami waywan da kike kulawa? Tas yaji an wanna masa mari Kul nasake ji. Sunan ubana abakinka,mahaukaci kawae Ta bishi da wani mugun harara ta wuce abunta Kamo hanneyenta yayi da karfi ya murdasu""" kika mare ni faryal yafada fuskan sa a damke " Kicin kicin din kwace hannunta tafara yi ga tsoro da yagama lullube ta Ka sakeni khalid you are hurting me Anki a sake ki ,come with me yai zan koya miki hankali yafada Yana janta har cikin motar sa ". kulleta yayi ya nufi hanyar fita shima Kuka faryal take tana dukansa amma ko ajikinsa, Har sanda sukayi nisa kafin ya tsaya,kashe ac yayi sannan ya dago fuskarta da ya gama jikewa da hawaye Khalid dangirman Allah ka maida ni gida, Wani murmushin mugunta yayi,not untill kin Fada min akan wani wawan ne zaki mare ni? Idan ba haka ba zan koya miki hankali anan, yafada yana kokarin kai fuskansa cikin nata Da karfi ta turesa ,na Fada maka ka kyaleni nace bana sonka Just shut up faryal,ya daka mata tsawa" duk wannan surutun ki is useless mahifiyarki bata gaya miki an bani ke bane? Meyasa zaki na kula wani Kin rainani ko? Yafada ranshi a bace kamar me shirin dukanta A dan tsorace tace what,Allah ya kiyaye wallhy ba wanda ya baka ni Mummy ai ba ita ke da iko akaina ba Shakureta yayi yahada bayanta da sit din motar
.
Hawaye ne kawae ke tsilala ba bakin magana wajen faryal Kinaji na ,bazan dauki wulakani da iskancin ki ba ""yanzu ba da bane got it? Kuma Tunda taurin Kaine dake namiki alkwari zan koya miki tarbiya da kaina nan gaba Naga alaman gidanku basu farsa miki baki ba Wani mugun kallo faryal ke binsa da shi And one last time yafada yana mata wani mugun kallon shima Kifada ma duk wanda ma yake rudin Kansa akan ki, haduwar mu dashi bazai yi kyw ba Tari ta farayi sosai kafin ya hankara ya sake mata wuyan ta Kuka kawae take yi batace uffan ba...domin kuwa ranta a hargitse yake da Bacin rai Bai saurareta ba ya ja motar ya kaita kofar gidansu Da hanzari tafara Kokarin bude wa taji GAM an kullee, Hannunshi taji a bayanta yana cewa baby am sorry kinji,kije gida ki huta Bata sanblokacin da ta joyo ba tana watsa masa wni zazzafan harara " Azzalumi': mugu ,allah ya tsine maka,tafada cikin wani sabon Kukan Bab...ka bude min Kofa khalid tafada a hatsale Ai Da sauri ya bude mata tafice Kallo ya bita da shi har ta mule gidan nasu kaga fuskarsa a lokacin wane maraya "kamar ba shi yagama shaketa ba .
.
Abokantakar zafar da siyama da ta sauya ta dawo shakuwa da soyyaya kullum manne take dashi Ranar jumuah da misalin karfe 6saura na yamma suka shigo gidan alhaj garba tare Siya,hope u had a good day with me? yafada yana kallon cikin idon nata Murmusawa tayu ta kamo hannayensa Zafar mu shi Shiga please, kullum Baka kaunar ka shiga ciki No cwety ba haka bane kinga is alrady late fa Uhm ban yarda ba amma ni ai ena Shiga gidnku ko ko yaushe ne bahaka bane ,am just in a haste Amma musamman zanzo Bai ma karasa zancen NASA ba " sukaji karar horn maigadi na kokarin bude kofar gidan Yawwa my dad,dama ka Dade Baku gaisa ba tafada tana yake Rusunawa zafar yadanyi ya gaishe sa Zafar ne dady,my boyfriend tafada tana dan murmushi Ohh"""" ayyah to shigo cikii mana yafada yana tallabo kafadan zafar Yes sir zafar ya ce nan suka jera zuwa ciki A zauna tare a valour .yace ya babanka I hope kuna lpya Lpya lau dady, Good " make your self comfortable, Yafada yana mikewa ciki Bai jima ba aka fara masa formalities na abinci kala kala Badin yaso ba don' dole ya zauna yaci abincin da aka jera masa shima .soyyayr su da siyama ta samu asali ne tun lokacin dayake england, don kuwa siyama a duniya batada amini dayake dauke mata kewar rashin uwa kamar zafar tun bayan rabuwarta da kamill Daga nan Abun ya zarce har aka furta ma juna kalman soyayya Zaf,tafada tana maida kallonta kansa Ya dai Hajiya enajinki,...zo muje kaga wani abu Dan zaro ido wajee yayi yace ae'na siyama" ko ena shiru agaidan nan What tafada tan dan yatsina fuska ;' CE maka akayi muna cin mutane, c'mon durling" tasoo , tafada tana Jan hanneyan sa Wani daki suka nufa tare wanda aka masa kwalliya tamkar kana gidan zinare ne Ko ena an masa adon kyale kyalen gold wajen sai sheki yakeyi Zauna mana "tafada ta mike zuwa wani wardrobe Wani akwati tadaauko me shegen kyw ta bude masa a gabansa A hankali yasa hannu ya dauko hotunan da yake ciki Wata kywawiyar mata CE yagani rike da karamar yarinya da ba sai an gaya maka siyaman bane " da kuma khalid a gefensu Your mum? Ya tambaye ta idonsa akan hoton Yes ,she died plane crash on her way to Casablanca run ena 4yrs Allah sarki" Allah ya jikanta ya mata rahma, Ameen zafar. Nan suka cigaba da fitar da pics kala kala Ciki kuwa harda hotonan alhaj garba lokacin yana yaro Wow dady fa thug ne da can a zamanin su"" zafar dubi wani makeken tattoo a kirjinsa!! ,siyaman tafada tana dariya Nan shima ya sa ido yace wow ,kinsan mutanen da bakamar yanzu ba Our parent wil go crazy in mutum yace zaiyi tattoo yanzu Said ace ka dawo dan iska Amma what does it stand for naga kamar zanen monkey? Yeah dad yace shida friends dinsa ne sukayi duk iri daya Kagane irin peer group haka Tabe baki yayi yace Ohh that's nice , ..
,
Agogonsa ya duba yaga already six ya dau hanyar gaucewa Baby let's get going,zanyi sallah na wuce gida . Dan hararsa tayi taje ta kulle kofar sannan ta jefa key din A bra dinta yana kallo Ufff siyama meye hakan ne wai?bani key din pls yafada yana mika mata hannu Dan hararsa tayi ta Dada daga boobs dinta tace "sai kasa hanu ka dauka zafar Haba siya na" kinsan bazan iya ba ai ko,to meye dalilinki na ajiye ni a gidankun enajinki Tamke fuskanta tayi kamr ba eta ba,tace just sit kawae Dan dolensa ya nemi waje ya zauna
.
Ya Dade yana lallaba ta ta cire tabasa haka taki fir har akayi maghrib In kaga na baka key din nan" toh kacire ne da hannun ka and don't touch my boobs tafada fuskarta a shake ' Yau na Shiga uku siyama ",shikenan , I surrender Mi kikeso nayi miki toh,? Tell me kinga dare nayi" kuma Yau fa kinsan tun safe Muke tare koo So? Ko banyi derseving time dinka bane zafar? Sake daure fuskan tayi ta juya masa baya baka gama cinye ranar ba ne " ai full day kace zaka min yau Dan mirmushi yayi sannan yace Toh naji madam,when zan tafi Babu rana tafada tana tura baki Dan shiru yayi sannan ya matso kusa da ita ya langwame fuska yana kallonta ,siyama what's is the problem? Juyowa tayi jin sassayar murynsa na kokarin kashe mata jiki, Take idanun ta suka cike da kwalla tace masa,I'm so lonely zafar" I missed my family, my mummy, I want a family," Nagaji da rayuwa nikadai":;; Dad hardly ka gansa a kasar nan" ko ya zo ma bai fi mu hadu few times ba sena Neme sa na rasa Zafar tun ena karama "gashi yanzu har na saba da hakan ta fada tana taro hawayen ta daya fara sauka Cikin sanyin murya ta sake cewa and Khalid is just like dad running from one place to another in search of fame dan dago kanta tana kallon cikin idon sa,don't I derseve to be happy? Kallonta shima ya keiyi a sanyaye "ga tausayin ta da ya keji na shigar sa Kai kadai ne kake sanyaya min rai na" just imagine yadda zan kasance ko yan zun nan in ka fice, Nika dai ce,no one will be here with me Sosai ta fashe da kuka a gaban NASA,har ta Neman isa kasa Shhhh yafada yana jingina ta a kirjinsa, a hankali yake buga mata bayanta kadan kadan kodan ta sassauta kukan data keyi Sosai tabashi tausayi,rashin uwa da family babban rashi ne komin arzikin mutum a rayuwa Dada shigewa jikinsa takeyi ta na kakkame shi cikin yanayi mai tada hankali da kyr ya samu yayi controlling dinta tabar kukan Siyama let's stop....zafar ya fada a raunane Kallonsa tayi da jajeyen idanunta tace Baka so nane,?"u hate to touch me zafar" da Sauri ya rufe matA baki da dan yatsan sa No siyama "ba haka bane,I love you so much more than anything else To meyasa kullum kake avoiding dina,?not even a kiss da ka ta min_ Oh C'mon love'kinsan Don' ena sonki ne siyama,let's not defile our selves tun yanzu kinji? I want to prove it to you that son da nake miki has nothing to do with your body kinji? Mikewa tsaye tayi a fusace tace Nooo ni ban yarda ba" ,yanzu na gama nuna maka sirrin gidan mu baki daya ,na nuna maka maka waye ni ba wanda na taba kawo shi nan Its a Secret room na family na .
.
Amma meyasa kai bazaka proving min ka yarda dani ba Siyama I know,wai meyasa kike ganin kamar bana sonki ne? Ba gashi ba tafada a zafafe ,Sauri kake ka tafi ka barni "'. baka son kazauna tare dani ";I have to beg u to stay" ta karasa cikin muryan kuka Hannu tasa a boobs dinta ta fito da key din,ta mika masa gashi ka bude Share kwallanta ta hau yi tace emmm thanks for keeping me busy today ta juya masa baya Jitayi an kamo waist dinta daga ta baya a hankali "juyota yayi tana fuskantar sa,numfashin su na gugar juna Sanyin labbansa taji akan nata sosai ya ke tsotsar bakin nata Lumshe idonta tayi etama ta biye masa sanda sukayi mai isarsu " kafin da kyr ta bude ido ta kallesa, I love you siyama,please trust me...kinji? Ya fada yana dada Jan ta kan kirjinsa Lamo tayi tana jin bugun zuciyarsa wani sabon kaunarsa ne ke ratsa jininta Da kyr suka rabu hakan wajen 9.30 saura ya fice ya nufi gida Kameel ne kwnace shima Tunanin mahaifiyarsa CE kawae a zuciyarsa take wani hawaye ke Neman saukowa kan kuncinsa. Mikewa yayi ya dauro alwala yasa hannu ya dauki qurani ya cigaba da karantawa Har bacci tayi awon gaba dashi Washe gari da safe khalid ya fito cikikn shirin fita office. A bakin mota guard dinsa ya tare sa "Ogah duk abunda kake so yana cikin nan guard ya Fada ma khalid tareda mika masa envelope Budewa yayi ba jira,tuni ya dakata ransa yaji ya mummunan baci a take" ganin hoton daya fado a cikin envelope din Wani busashen dariya yayi,I see Kammil ne dama?I knew it Yarinyar nan is so cheap da wannan shashashan zata na hada ni ? Amma bakomai tattara sauran information din ka ajiye bana bukatrsu yanzu Ogah amma yakama ka duba fa" guard din yace a dan tsorace Bari kawae Nasan shi ai gaba da baya,kake kawae Mumushin keta yayi yana ciza baki....... A ransa yana cewa ' "kamil the battle is just about to begin Tsakanina da kai zanga wa zai winning Muzuba
.
Gabanta ne ya hau dukan uku uku ,ganin sunan alhaji garba kan screen Hannu ta sa ta dauka hello alhaj,ranka Dade Hajiya Mariya? An wuni lpya Kalau,alhaji lpya kuwa naga ka kira da wannan lokaci Eh toh, kinsan dalilin da zai iya sa nakira ki ai "yaro Yazo min da korafi akan yarki tana wulaknta sa akan wani yaro. Anya Hajiya kina aikin ki da kyw kuwa? Da e"e na tace alhaji dan matsala aka samu amma insha Allahu ba za a sake ji ba ma Dama kinsan da hakane? Ah a wallhy alhaj, nima ban tabbar ba saboda faryal da ba enda take zuwa inba makaranta ba ena zataga wani saurayi? Kawae dai bazaka Sha bakin uaro bane Dan dariya yayi sannan yace Hajiya kenan "ai yaran namu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba Kedai nabaki dama ta karshe kiyi bincike ki warware matsalan nan nan da wata daya Inba haka ba to fah karkisha mamakin hukuncin da zan dauka akan Ku gaba daya da yarkin Ayi hakuri alhaji,kafin nan zakaji kykkwan labari na maka alkawari Toh Hajiya wannan ya rage naki nidai kywkkwan labarin kawae zan ji daga gare ki Nan ya katse wayarsa Sauke ajiyar zuciya Hajiya tayi ta nufi dakin faryal. bata ganta ba yasa ta juyawa domin zuwa gidan Hajiya shafa Kawata lpya naganki haka kuwa? Ena lpya fa alhaji yaji labarin kamil da faryal? Yanzu haka danake Fada miki wayarsa nagama ansawa yabani wata daya na kunce komai tsakaninsu Tab,amma anyi tsinannen yaro wallhy, faryal ma inbanda kyal kyal banza me zatayi da ShI? yaron da ba yida asali ma Gane min fa shafa,ke bar wannan agefe anemi abun yi tun yanzu kar abun yazo ya kufce mana a kukrarraen lokaci Dan shiru shafa tayi sannan tace,nikam mariya me zai hana muje gidan mallam zanah,ko rabasu yayi kowa ya huta Dafe kirji haj mariya tayi tana cewa A ah shafa ,banda malamai, alhaj yaji labarin nan kinsan ranar zan bar masa gida ko, ballantana Inda yasa yaron nan aransa "Idan nayi wani Abu ai na Shiga uku Gaskiya nemo wata shawarar Kai mutumiya ta akwae tsoro, To gaskiya kibani lokaci ko gobe ne sai na San me zamuyi akan su Yawwa ko kefa shafa, kinga Barin ykoma gida kinsan baisan nafito ba Tafada tana mikewa Sai naji ki, Saur i takeyi zata tafi schl Yau evening lectures ne da ita A bakin gate suka hadu da shi inda tayi kokarin komawa ciki da sauri amma ya damko ta sanda ya fitoda ita waje Da Allah malam sakeni tafada tana ture hannunsa Ke dan rainin wayo da kaamil zaki hada ni takara? Wani dariya ta fashe dashi,taja tsaki zata wuce Janyota yayi ya jillata gefe saura kadan ta zube kasa Nasan baka da hankali khalid basai ka dada bayyanawa anan ba kaje can gidanku na rash in tarbiya na azzalumai kayi ba anan ba Kai hanu yayi zai sake janyota zafar ya tare, Wani huci yakeyi kamr zai hade ransa Khalid me haka ka kyaleta ta tafi schl, Kai kuma asuwa?da Allah malam stay out of this .
.
A zuciye zafar yace masa innaki fa,akwae abunda zakayi ne? Wani mugun kallo ya bisu da shi kawae ya juya ya fita, don kuwa khalid a baki ne kawae ba'a yar hanu da shi..lol Are you OK? Zafar ya tambayeta da dan damuwa a fuskan sa Am ok yay zafar,karka damu. Toh shikennan Zo ki wuce
.
Haka khalid ya cigaba da sa bin cike akansu kamil da faryal Sannan Yasa ana bibiyansu duk yadda suke haduwa ya sani Ranar tun misalin karfe 4 na yamma aka fara ruwa Ruwa sosai akeyi kamil ma har bayan isha ko gida baisamu ya koma ba yana office yana ta aiki abunsa Karar waya CE ta hankarar da shi. Dan Murmushi ya sake kafin ya sa hanu ya danna yace Ruhi is missing me right? twinsoul kana ena ne,I'm stucked, motar driver yayi blocking akan titi . Gashi wai yaje neman mai gyara tun tuni ina kan titi. Kuma kaga tun dazu ana ruwa bai dawo ba am scared twinsoul dan Allah kazo tafada a shagwabe Wani kan titi kike?nan ta masa kwatance enda take din Ciki Minti 35 ya taho wajen Hangen motar yayi da kyar sabida iska da ruwan tazo da shi Ga duhu dare ya farayi Ta cikki ta bude masa ya shig yasa meta Am sorry ruhi,ruwan ya tsananta bana gani sosai,banzo da wuri ba ko? Are you ok? Yafada da fuskar damuwa I am fine,baga ka nan ba ta fada tana kallon sa da baby face. Dan lakace mata hanci Yayi yace Mutafi toh na kai ki gida nasan shima maybe ya rabe ne a wajen mechanics din kinga ruwan yayi yawa Toh muje ,ta fada itama tana kokarin bude motar Rigar suit dinsa ya cire duk da jikar ya mata lema da shi suka nufi bakin nashi motar Ganin yadda wuri. Yayi duhu ga ruwa na sauka kamar da bakin kwarya yasata kan kame shi sosai don' tsoro Dolensa ya tsaya ya dauke ta i chak ya wuce da ita motarsan ya rufe Gaba dayansu sun jika sosai ,harta bra dinta sanda ya nuna boro boro ta cikin rigarta A hankali yake tafiya dasu ,Barin ma faryaal data kan kame shi sosai, taki Barin jikin sa . Gaba daya hankalinsa baya jikinsa soboda dumin jikin ta dayake gogar nasa Twin soul mutsaya mana is dark,tafada kamar xatayi kuka Ok Barin nemi waje,dan wani fili ya samu yayi parking sannan ya jingina kansa kan sit shima Sanyi tafara ji sosai tana nemar fara karkrwa ruhi yadai ya fada yana tallabo fuskarta Narkewa ta farayi ajkin nasa da wani salo mai kashe jiki . gashi a yanayin da take kusan komai na jikinta a bayyane ne Balle button din jikkaken rigarsa ta Shiga yi ahankali shiko bai hanata ba har ta kammala,.wani dumi ta jiyo a jikin NASa tuni ta shiga goga fuskanta Akan faffadan kirjinsa Lumshe idanunsa yayi yanajin abubuwa na masa yawo har tsakan kansa a take . Lura da shiru yasa ta fahimci abunda takeyi ne yasa shi jikin wannan yananyi . dakata wa tayi sannan ta Kai kallonta tayi dai dai fuskarsa tana kare ma kyykwan halittarsa kallo A hankali ya soma bude idanunsa da suka rine sukayi ja Tallafo ta yayi ya hada goshinsa da nata .ruhi zaki kasheni ko? Kar ki sake min irin wannan kinji yafada yana murmushi Kokarin turo baki tayi tsam taji ta daura akan nasa Batayi wata wata ba ta fara aika masa sakonni kala kala na kisses Da kyr ya controlling kansa,ya daga ta Ruhi please_ yafada yana rungumota jikinsa cikin sanyin murya tace Twin soul toh ni xan kwanta tafada tana dada mikewa kan kirjinsa Daura Kansa yayi kan kafadan ta sukayi shiru bawan da yace uffan Kowannen su yana tunani kala kala aransa Basu hankara ba kuwa bacci ne mai nauyi yayi awun GabA dasu awajen basu da farkawa ba sai 6 na safe
.
Hasbi nallahu wa neemal wakeel faryal" ,tashi its 6clk .. Idonta ta bude kamr a mafarki take jin maganan sa Da sauri ta mike ta CE twinsoul safiya CE fa? Bai tsaya sauraren ta ba ya kunna mota a guje suka nufi gida Sallan safiyai tayi kafin ta fara kokarin shafa cream dinta Ban kado kofar taji anyi da karfi a tsorace ta juya,har cream din ta ya fada kasa ta maida kallon ta bakin kofar Tsayawa haj mariya tayi tana kare mata kallo inda ita kuwa sai bari take faman yi a tsaye Cikin sanyin murya tace mummy ena kwana Faryal INA kika kwana jiya? Tafada da normal muryanta Mummmyyy......ruwa ak...e...yi Faryal """hajiya ta kira ta cikin tsawa Ki Fada min ko naci ubanki. Yau kashe ki zanyi a gidan nan idan baki Fada min Inda kika kwana ba tafada tana jan hannayen ta gaba Kuka faryal ta fashe dashi sosai. Mummmy wallhy a mota na kwana Mota? Motar wa ? Wani ubankin ne ya baki mota da zaki kwana aciki ," Bayan na sa a dauko ki a enda driver ya ajiyeki ba a sameki ba Mumy wallhy har bayan isha ena wajen shiyasa........ Yi min shiru ai idan Karya zaki mun,ai bazaki ma ubanki ba ko Nan hajiy tafara yunkurin fita zuwa site din abba Da Sauri faryal ta kamo hannun ta mummy wallhy dagaske ne a mota na kwana na rantse miki mummy tafada tana kuka Fincike hannun ta tayi tace faryal motar waye? Ehm ummm emmmm..... Ke,kifada min kar na taka ki anan wajen motar wani shegen kika kwana Da kyr faryal ta sassauta kukan tace motar yay kamil ne mummy Wani wawan mari taji a fuskarta Na Shiga uku faryal? Me ya miki "me kuka yi? Mummy wallhy ba abunda mukayi na rantse....janta Hajiya mariya tayi ta hau jibgarta Ashe asiri na KiKE so ki tona a garin nan,me kika SANI da zaki bada kanki wa namiji Gardin banza, kwana da wanda ba muharraminki ba faryal? Mummy dan Allah kiyi hkiri wallhy ba abunda mukayi Ki min shiru dan ubanki, Yau sai na hadaki da ubanki Ihu faryal ta sake awajen tana rokon mummy data ke faman masifa tana bori Munafuka Niki sake min kafa ai Kin girma yanzu tunda kika san ki kwana da da namiji Karar wayanta ne ya dakatar da ita Shafa na gode allah da kika kira Meya faru mariya kukan waye haka nakeji kamar faryal An sameta ne? Bar shegiyar yarinya bayana take son gani? Wai ace faryal ta kwana a motar kamil,kiji min wannan badala fa Sallamewa haj shafa tafara sannn tace ,ke mariya ki nutsu kiji abunda zan Fada miki kije gefe Bayan minti 5 tasake shigowa hango faryal tayi ta takure a gefe ta hade kai da gwiwa tana faman kuka Wallhy ban gama dake ba faryal,.... Saura shi kuma munafiki azzalumi ma cucin yaron Yau zai gane kuransa,tana kaiwa nan ta fice Kuka faryal ta sake fashewa dashi,tana kokarin daukar wayanta da ke faman ringing Ruhi,ya dai inata kiranki shiru ? Wani matsanancin Kuka ta sake fashewa da shi, A daburce ya ke jero mata tambayoyi kala kala Da kyr ya samu ta bashi labarin abunda ya faru Innalihhi wa inna ilaihi rajiun,am soo sorry ruhi kiyi hakuri, Ni na jawo miki,ki yafe min kinji? Noo twinsoul..... ...shhhhhh ruhi kinsan ya zaayi? Ki kimtsa kanki ki je kiba mummy hakuri kafin nadawo muntafi bauchi da zafar Amma Gobe zan dawo ok? Ok tafada da disashhen muryanta, Kisha magani ruhi,take care for me kinji? I love you Love you too twin soul,bye tafada ta mike ta fara suturta jikinta Har bayan isha ranar bata leko waje ba Saboda Tsoro ne tam cikin ranta haka ta mike ta fita don' kamill ya takura akan taje din Da sallamrta ta Shiga har cikin bedrum din mummy galla mata harara tun daga kofa tayi tace Meya kawo ki? Tsugunawa faryal tayi jikinta na rawa tace mummy dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba wllhy ...nayi kuskure Murmushi haj mariya tayi sannan tace,toh ni INA ruwa na na Riga na Fada ma ubanki kijira shi yadawo Ku karata chan Ihu ta fasa ta fara birgima awajen,mummy dan Allah..... "ke kimin shiru karki sake ki Tara min jamaa'h Nan Hajiya ta kalleta a nitse tace faryal?
.
Zan baki dama daya tak, ki ceci kanki da shi munafukin saurayin naki daga sharinn Dana ke shirin kulla muku wajen ubanki Mummmy sharri kuma Eh,ai in na fada masa gaskiyar naki bazata kama hanakali ba ne enba sharrin zan fada ba wazai yarda baliga da valigi sun kwana waje daya ba abunda yafaru?? Bayan a ido na ranar kike rirrike sa Sunkuyar da kai faryal tayi ,mummy wallhy .."".ke ni banson jin wani rantsuwarki Inkin yarda da abunda na nzo miki dashi to in baki yarda ba Ga hanya out,,,sai ki jira hukuncin ubanki dake da shi din Ah a mummy koma meye ne zanyi dan Allah kar ki min sharrin Dariya abun ya ba ta amma tadake tace ban yarda ba ki wuce kawae kifita min na FASA baki damar ma Kuka faryal ta sake fashewa dashi tana rokonta Toh ya isa,zoki zauna nan a sanyaye faryal ta zauna kan kujera a gefen mirror Kimin alkwari zaki na kula khalid sosai .sannan zaki rabu da kamil shikenan Na miki alkwari Dake da shi kun kubuta har abada. Zaro ido faryal tayi Ta mike tsaye hawaye nabin kuncinta muryan ta na rawa tace mummy Na rabu da kamil? Wani harara Hajiya mariya ta galla mata, ah Ah faryal kije kuci gaba da shashancin ku Laifi nane da na baki Dama Kafin na rufe ido na bude kin bace min a daki "get out tafada cikin tsawa Faryal din ma bata San lokacin da tayi waje ba dan tsoro
.
Kallonta mummy ta tsaya yi ,... Sannan ta kau da kanta ta daure fuska Shiru faryal tayi ta rasa abunda ke mata dadi, Bude bakin ta tayi tace mummmy.... Ki fice nace miki kar na faffasa miki jiki anan Mummmy dan Allah ki zanca min zanyi kowanne amma wallhy bana son khalid mummy Karki so shi mana, shima kamil din naki daga yau mahaifinki bazai kara amincewa da shi ba A idonki za a masa koran kare Yau din nan ba jira Haba mummy don' Allah kiyi hakuri, kar ki rabani da shi ta fada cikin kuka Toh shikenan ai, ni dai na gama baki daman da zan baki ta shi ki tafi ki bani waje kawae Sha shashar banza toh wallhhy kisani faryal duk abunda ya faru daku kiyi kuka da kanki Da kyr faryal ta dafa zuwa cikin dakinta, ranar ko runtswa ko ena ba tayi ba duk ta kulla nan ta kunce can haka har Kiran sallah ya shigo Raka 'a biyu tayi Kafin tayi sallan ta Adduoe sosai tayi . . sannan ta mike zuwa dakin mummyn Kallo mummyn ta bita da shi dan har cikin ranta ta tausaya ma yanayin faryal din duk fuskar ta sun haura,jikinta sam ba kwari Me ya kawoki kuma? Ena wuni mummy ta fada a hankali Lpya lau enajinki_ Mummy Dama.....Dama Ehn dama me? Faryal Na amince zanyi abunda kike so,amma mummy dan Allah ki kyale yay kamil " ba laifin sa bane ,nice dama nace yazo ya dauko ni a schl din Ta fada tana share hawayen ta. Alhamdulilhhi,yawwa auta ta ko ke fa,ai in cewa kikayi kar na sake kula sa mai sauki ne awajena Muddin kin amince da komai Shiru faryal tayi,tana kan goge hawayen da suka ki tsaya mata a idanun taa Toh tashi kije ki kwanta ki huta my princess, Yau kika dawo cikkaken yarinya mai tunani da sanin ya kamata Itadai faryal bata CE uffan baa haka ta mike ta nufi dakinta a daddafe Daga wayar ta tayi taga misdcols dinsa har guda 3 da TeX mssg guda daya Sa hannu tayi ta kashe wayar gaba daya ta jefa sa kan cushion Wani Sabon kuka ta fara A hankali take furta am sorry twin soul, dole zan bi ta wannan hanyar na ceci mutuncin ka a idon abbah Sulalewa tayi kasa ta cigaba da rera kukan ta Karfe Tara na dare,ya fito kofar gidan hankalinsa a tashe tun safe Baiji muryn ta ba kuma bai ganta va Hasken mota ne daya doke sa a ido ya sashi tsayawa yaga waye ne da Daren nan Wani zafi yakeji a zuciyarsa wacce take nuna masa faryal dake fitowa daga motar khalid.,.. ganin yadda kamil din ya tsura musu ido yan binsu da kallo Khalid yayi amfani da hakan yafara Kokarin rike hannunta Gashi ya ci saa Sai ta mika masa hannun A lokacin ba gardama Duk da ma yasha mamakin rashin hanashi da batayi ba Wani murmushin ya sake" a ransa ya na farin cikin sauyawar al'amarin Faryal? Kamil ya kirata dab zata wuce shi ita da khalid KASA daurewa tayi ta sake hannun khalid din ta juyo Kasa kallon sa tayi saboda irin sauyawar da ta gani a cikin kwayar idanunsa Ena kika fito?. Na fita da khalid ne Ta fada tare da dauke kanta duk abunda takeji alokaci. Kokarin dannesa takeyi Tace yaya kamil gudnite Har ya bude baki zai yi magana...yaga tayi sauri ta wuce abunta Kallon mamaki yabi ta dashi, Kafi.n Ma ya lura da khalid dake gabnsa a tsaye Mr kamil yafada hade da fashewa da wani mugun dariya Look khalid just leave kamil ya fada ransa a bace ,a gidan namu? Haba kamil" Yanzu tsakani na dakai ai Kaine zancewa leave a gidan nan In karya ne ka tambayi faryal_ Tsaki kamil ya ja ya dauke kansa akan Khalid da ke faman masa dariya Har yar juya xAi baar wajen yaji ance And one last favour kamil" kaga ka bata mata rai kasa ta tafi baka bari munyi gudnite ba Pls tel her I have a great day today,_and I'm missing her already Blowing masa kiss yayi yace Hey not for you, for her Ya juya ya fice yana dariya ciki ciki Bari kawae kamil yake yi,gaba daya zafi yake ji a kirjin sa kansa na wani bugawa A fusace ya shige ciki ya nufi dakin ta Murdawa yayi yaji GAM an kulle ta ciki Dakin sa ya koma ya zauna Still layin ta ma ya dinga kira akashe Haka dai yayi tayi shika dai ba response hr bacci ta dauke sa shima
.
Da kyar ta tashi ta shirya zuwa makaranta ranar Duk yadda kamil ya so ya ganta haka taki Ranar har lati yayi zuwa wajen aiki son jiran ta ta fito Haka faryal ta dinga Share kamil,karshe ma wasan boya ta fara mishi Bayan wata daya da hakan ranar Musamman alhaji garba ya kira haj mriya ya yaba da sauyawar faryal akan khalid Sosai haj mariya taji dadi din kuwa har wani contract din yasa aka mata signing daga Abu Dhabi,a Dubai Domin a duniya yaran sa ne am na farko a muhimmaci kafin kowa,Alhj garba yakan iya komai akan khalid da siyama Riketa taji anyo da karfi sanda tadan yi kara ouucchhh Ruhi mena miki ya fada yana kokarin juyota ta fusknce shi Ka kyale ni yay kamil, stop it ta fada tana kokarin kwace hannunta, Bazan kyleki ba not until Kin Fada min komai what's happening? Dan Allah me namiki ke ki azabtar dani haka Kifi kifi da ido tayi tace bakomai ,look I'm not in the mood What ? Saboda me faryal? Rau rau da idonta tayi tace saboda yanzu........ yanzu khalid ne bani ba ko? Tell me angel why? Meyasa zaki na kona ni haka " kinki kibari ma mu hadu a month kenan yau haba faryal? Kifada min mana why are you hurting me angel? yafada kamar mai shirin yin kuka Duk maganan daya keyi idonta a kasa yake,saboda ita kadai tasan abunda take ji a ranta a lokacin Girgiza ta ya sakeyi,yace kifa da min mana Cijewa tayi ta dago kanta idanun nan a bushe tace Yay kamil nifa ba abunda ya faru... Imma akan tarayyar mu ne Its over between us please forget about me Ka daina Shiga hrkata pls .saboda bana... .shhhhh ya fada Yasa dan ytsansa a bakinta Faryal kar kice min baki sona please, Stop hurting me .....I know akwai dalilin dayasa kike haka meyasa bazaki Fada min ba I swear to you I will do anything to fight for us,I can't live without you faryal Kiyi hakuri pls,ya fada har jikinsa na rawa Kuka ne yaso yci karfin ta amma haka ta sake dannewa Da karfinta ta turesa daga jikinta, Nafada maka its over, ni khlid nake so yanzu Meyasa bazaka kyaleni ba tafada cikin masifa da zafin rai Faryal khalid kike so? Yes ta fada cikin tsawa ,kuma yau ya zamo na karshe da zaka na damu na....ai yanzu na warware maka it's over Ta wuce ta barshi tsaye awajen In banda its over da ta fada ba abunda yake maimaituwa a kwakwlwan sa, tsaye yake ko motsi ba ya iyayi Gefen wani empty lecture hall ta koma da gudu ta zube gwiwarta akasa tana rusa kuka sosai Im soryy twin soul,I know I'm hurting you Ba yadda na iya ne.... take fada eta kai awajen Da kyr ya tattara hankalin sa ya koma gida, Wani zazAbi ne ta rufe shi a take Haka rayuwarsu ta cigaba,har tsawon wata hudu ba abunda ya sauya Sai dai ma Karin rashin mutunci da khalid yake masa karara duk lokacin da yagan sa da faryal din Tun abun na damunsa har ya fara amincewa da shawarar jabir akan ya kyaleta tunda decision din ta ne Sanye da bakar wando yake Jordan hade da cool bright yellow polo shirt hadaden agogon wayar sa ya daura a hannun sa na hagu da Paris hand band masu kyw a dama Kallo daya kawae bazai isheka ganin kwalliyar tasa ba,domin kuwaa ya fito sosai duk da dan Raman da yayi kwana biyu amma kwarjini. Na nan a Tattare dashi Ba faryal ba har shi Khalid maida hankalinsa yayi yana kallon sa da yake tahowa ko kallonsu baiyi ba ya wuce Motarsa kirar Mercedes benz c class ya nufa ya yi hanyarr waje abunsa Sosai ranta ya sosu don' har cikin zuciyrta ta tsani taga ya fito zai je wani wajen gani take kawae wata zata gansa awaje ta kyasa Baby yadai,naga kin wani bata rai kamar mai shirin fashewa Niko? Tafada muryanta na dan rawa Yeah,kodai kishin tsohon Zuma ne ya taso naga kallonsa kike tun dazu Khalid just stay out of this...bani kake so ba and here I am....bana son wani surutu tafada tana dauke kanta Afuwan baby,yafada yana hada hannuwansa duka biyu Gobe zamu je shopping tare da su siyama is best ace we are all there koh,all couples out Ya fada yana kashe mata ido Ok Allah ya kaimu, Da rana misalin karfe 2.30 Zafar yA dai ,mummy tafada tana kallonsa da ya tsura mata ido Nemar waje yayai ya zauna kafin yce mum meyake faruwa? Aena zafar?
,
Faryal mana mummy I hope bakida hannu acikkn sabon salon soyyayr da ta keyi da wannan marar kunyan yaron Tohhhhh Ubana yazo kashe min warning Mummy ba haka bane, Yimin shiru malam,toh faryal din ne tayi rra'ayin haka Bata karasa maganr tata ba ma sai ga faryal ta shigo Yawwa baby na Fada masa da bakin ki Ni nace ki shirya da khalid? Kallonta yayi da niyyan Jin amsarta Dan shiru tayi sannan tace Eh yay zafar ra'ayi na ne Alhamdullhi to kaji , tashi kabar min Daki na Kallo kawai ya bisu da shi sannan ya mike ya FIta baice komai ba 5 pm da yamna siyama da zafar khalid da faryal suka shiga city mall ,babban super market ne wanda ba abunda babu aciki Shidai zafar sosai sauyawar faryal ya daure masa kai amma dai baida tacewa tunda mummy tace ra'ayinta ne kuma itama ta amsa da bakin ta Haka kawae take jinta wani iri ranar Baby yadai Khalid ya fada yan kallon ta Nagaji ne kahlid mu zauna please Nan suma su siyama suka jona su kan table a cikin wajen fannin ice creams Siyama ce tayi oda Aka ba kowa zabin sa Zafar da siyama da hirarsu kawae sukeyi duk da ma ba sosai yake amsa wa ba Don zafar ba ya yin khalid kwata kwata a rayuwrsa Haka itama faryal da duk hankalin ta a tashe yake kuma bata San dalilin ba Baby,baby Khalid ya kira sau biyu kafin ya lura da Inda take kallo Kamil ne rike da hannun wata yarinya da bata wuce 12yrs ba Tamkar jinin sa CE tsabar kaman da suka so suyi Da Sauri zafar ya mike ya nufi enda suke Tare suka jera da kamil da yarinyar suka nufo su siyama enda faryal ta daure fuska sosai kadan take jira ta fashe Sama sama suka gaisa da siyama ko binta gansu baiyi ba ya juya abunsa suka fice da yarinyar A fusace faryal tayi wurgi da ice cream din hannunta ba tare da ta San ta aikata hakan ba Baby are u ok? Khalid ya fada a zafafe Kallonsa tayi idonta cike da hawaye tace I'm ok nikan mutafi Ta fada tana mikewa Tabe baki siyama tayi tana jinjina ma kishin faryal din Zafar ko kansa Dada daurewa yayi Aransa yace toh kishin me faryal xata yi da kanwar jabir. Ba ta CE khalid take so ba?
Thursday, April 12, 2018
ARNE Part Four (4)
ARNE Part Four (4)
.
Da safe karfe 7.30 shiru faryal bata sauko ba Hajiya mariya dakanta ta fito ta kama hangar dakin NATA don ta duba ta Hangota tayi da karami. Coffee cup tana zaune da littafin Q/A na biology, Mummy ena kwana,tafada fuskarta ba yabo ba fallasa Ah,a rike gaisuwar ki,ena nice abokiyr gabarki a gidan nan faryal Mummy kiyi hakuri,nifa ba haka bane kawae abubuwa ne kinsan fa muna final exams Ke kinci gidanku, ki kalli tsakar ido na kimin karya? Ai ni nasan kina dawo wa dawuri fiye da ma normal school hours a da Ki Fada min meye namiki kwana biyu kike kin sakewa a gidan nan dani Wato salon ubanki ya dawo yace namiki wani abun ko? Saukar da murynta tayi,tace mummy ba wani Abu bane...kawae banason kinasa baki a maganan mu da khalid ne Khalid fa baida kunya,gashi baya girmama nagaba da shi Ke yi min shiru ,kaji maganan banza rike min tsuliya nayi kashi, Eyeeee lallai faryal kin girma,..kece zaki Fada min halin mutum ko nice zAn Fada miki,yaushe kika girma kikayi hankali da zakisan mai kunya da marar kunya Mummy wallhy bakisan halin khalid ba...nace kimin shiru faryal ta katseta Look girl,yaron nan kusan dai dai yake da ubanki a arziki,ballantana babansa Alhaj garba Nida nakeso soyyayarku ta daure ki huta nima na huta Mummy nifa bana sonshi Lahhh. hai lahhh kaji min yarinya.me kika sani akan so? Faryal Ashe bakida tunani?lallai ma rashin hankalinki sai Dada bunkasa take Toh ahir na sake jin bakin ki akan wannan magana Kuma in kinason mu shaida juna agidan nan to kibani hadin kai,muddin nafada miki magana bakiji to zami samu matsala dake,INA fata ba da gunki nake magana ba?
.
Cikin muryan kuka faryal tace naji mummy Tamike tafita.... Binta da kallo haj mariya tayi taja tsaki...wawiyan yarinya kawae zata jawo min tsiya inaganin arxiki Waya ta dauka ta kira haj shafa ,bayan minti 30 sai gata ta iso gidan nan suka nufi ware house office na baban khalid Yaune rana ta karshe a makaranta kowa na bakincikin rabuwa da juna anata faman Neman yafiya Siyama CE ta dafa ta ,hey faryal Dan yatsina fuska tayi sannan tace,wai meye ne Dariya abun ya bata amma saidm ta dake,yayanki ne zaiyi magana dake tafada tana mika mata wayar Da sauri karba ta koma gefe,hello faryal my sister, Ko amsawa batayi ba saboda kukan dayaci karfin ta.... Faryal,faryal..yake Fada sannan ta samu tace Yaya zafar Ohh my god waya taba ki haka faryal,kukan me kikeyi? Fadan hakan dayayi ma yasata kara fashewa da kukan kamar ba jiya jiya sukayi waya ba Cikin tashin hankali zafar ke tambayarta meya faru Dan control ta yi dakyr cikin shesshekar kuka tace,Yaya zafar dan Allah ki dawo mana,I'm so tired nagaji da gidan Dogon numfashi ya sauke ,yace haba faryal I called to congratulate you Yau ranar kammala schl amma kizauna kina kuka haka ? Zamu dawo ai just stay put ok?
.
A hankali tace ok ,nan ya dan dinga bata baki had ya mata alkwarin bata gift kafin dare Dariya tayi tace nidai zanga ya gift zai taho daga England zuwa abuja Toh zaki gani ai just be close by... Haka suka yi sallama ya mika wa siyama wayrta tabar wajen Zafar sis dinka har yanzu fushi take dani akan kamil, Murmushi yayai yace kyaleta she wll soon forget that.... Bayan shigar mummy da haj shafa ware house said ga alhaji garba da khalid nan tafe suma Da Sauri khalid ya taho wajensu,mummy har kin iso eh son To muje ga dad dina Ku gaissah kafin ya wuce Nan suka tashi suka isa Dad ga haj mariya mum din faryal ,she's one of the holders na company AbuZAYAL investment Ohh nagane ,haj barkanku fa yagaya min yana zuwa gidanki ,matar alhaj abdallh koh? Eh ranka ya Dade suka Fada tare suna yake Ahh bakomai ,em make them comfortable, ka kawo min takardun Nasu anjima Wani farinciki ne ya lullube su gaba daya barin ma shafa da yanzu ne NATA business din zai samu wannan daman Faryal ko ko bin ta kan mummy batayi ba dakinta ta wuni tana jiran surprise din da xAfar ya mata alkawari Karfe 9 na dare taji ring alert na video call Da kamar bazata dauka ba don' tunaninta bazai wuci khalid bane Jin mai kiran yaki hakura da kira yasata juya a fisace zata danna Chak ta tsaya ganin code din countryn daya nuna akan screen
.
Ta nemi hawaye a fuskanta ta rasa a lokacin wani farinciki taji na ziyrtan xuciyanta Da sauri ta danna ,masha Allah murmushin kawae taga yanayi inda ita kuma ta kafe shi da ido,kyw na musamman taga yayi gashi ya kara girma da kwarjini kamar badan 20yrs ba Wani kishi ne ya tukareta ganin yadda yadawo dole mata zasuna binsa Nan hawaye suka fara silala a fuskrta Angel.. .baki farincikin gani na ne? Don't talk to me tafada cikin kuka Murmushi yayi yace I know Angel,kimin duk abunda yadace nasan ban kywta ba da na kyale ta Amma ai tasan da ita nake kwana nake tashi ko? Bansani ba yay kamil,wannan wani irin rayuwace,u left me alone baka so na a cikin fushi take ta masa masifa wanda shikaran kansa ya dena gane maanan abunda take Fada Shiru yayi ya sa fuskan tausayi, sai hakuri yake bata Da kyr faryal tadaina bori ta saurare shi Magana sukayi cikeda kauna da kewar juna Ohh dama gift din yay zafar kenan,amma wallhy yaci nabashi kyawta Dariya kamil yayi yace gaskiya kam...
.
Ki kwanta faryal kinga past 12 Turo baki tayi zata sake sa kuka yace toh shikenan kinaso kar na sake kiranki ko faryal? Ba nafada miki avunda abba yace ba Da sauri ta gyda kai alaman Ah a.... Good girl,ki kula da kanki angel,for me? Of cous yay kamil and you too.... Haka har ta katse wayar badon son ranta ba ta sulale kan gado ta lumshe ido tana jiwo muryansa da fuskansa Haka har bacci yayi a won gaba da ita Washe gari kan dining suna cin abinci haj mariya mamaki ne ya rufeta ganin canjin yanayin faryal cikin dare zuwa safiya Wayarta ne yafara ringing,ganin sauyin fuskarta yasa haj ta CE Me haka faryal? Ki dauka mana Nan ta danna ta sa a kunne hello, My baby,....I'm sorry jiya ba time ban Miki congrat ba Angama schl saura akawo min ke ko? Batasan lokacin da tsaki ta kufce mata ba Nan ta katse wayar batare da tace komai ba Waye wannan haj mariya ta tambaya Emm mummy khalid ne fa Mtsw tashi kibani waje kar naci ubanki yr banzan yarinya A fusace faryal ta wuce sama Sallama Malm chief security yayi ya durkusa yagaida haj mariya, Yadai naganka da safen nan Dama aika ne na kawo ma faryal daga Khalid Ohh ok to ajiye anan Vudewa hj mariya tayi taga iv na graduation party musamman na faryal da cheque din 35million na kayan sawa da sauransu Ware ido tayi tana danna ma faryal din kira Ranar haka tasa ta agaba ita da haj shafa akayi shopping sharp sharp na designers aka gyra mata gashi aka mata make up Bayan isha aka zo da motar gidan su khalid aka tafi da ita wajen party Kamr zata fashe don'bakin ciki.wani zuciyan yace ta kira abba tafada masa komai amma wani yace tabari if not zata Shiga uku da haj mariya Cikeda baki kala kala mata da maza harda yan uwan alhaji garba su uku Iya tsaruwa wajen ya tsaru,siyama ma taci ado harta gaji da kyw, Bayan an kammala yan ciye ciye da rawa da perfmance da akayi na shaharraen mawakin nan davido...
.
Waje ya gauraya anata hidima Nan MC ya bada fili ma khalid donjin abunda zai ce Wanda yayi dai dai da shigowar alhaj garba wajen Nagode jamaa da kuka tayani farincikin wannan rana tare da sister na siyama .muna gode muku da taya murnan kammala karatun su Inaso nayi amfani da wannan dama na bayyana ma jama'ah Sarauniya ta wacce nake so nake kuma muradin aure kwanan nan Bawata bace illah faryal abdallh ..yafada yana murmushin yake Dum zuciyarta ya fara bugawa ga wani hasken da aka danna mata akai kowa kallonta Yau zaka gane kuranka khalid tafada cikin ranta tana mikewa zuwa Inda yake..... Karban MiC din Tayi tace Nagode daka bani damar zuwa nan wajeen.domin kuwa nasanar da jama'a I'm not ur Queen in any way ni ba sonka nekeyi ba, na tsaneka,kuma har abada bazan taba dawowa matarka ba... Ta wurga musu mic dinsu ta kama hanyar waje abunta Da zafin nama ya mike zaibita wake nan alhaji garba ya dakatar da shi ya ja shi zuwa ciki Nan fa guri ya kaure da kace kace kowa na fadan albarkacin bakinsa :
.
Calm down khalid,me haka ? Kyaleshi dad I told him yarinyar batada class,sai wani huci yake kamar zaki Da Allah malama kimin shiru karna FASA miki baki Harara siyama ta visa dashi. .of cous khalid ba baki ba ma kill me if u want Ena akan yarinyar da bata San kanayi bane Don't talk to me like that siyama raina a bace yake yanzunann can't u see Enough alhaji garba ya dakatar da musun nasu Son ka kwantar da hankalinka no one dares me and win...duk abunda kake so a duniyan nan zaka samu I promise Tare suka kalle uban nasu da ba alamar wasa a fuskan sa Dad me kake nufi yarinyar da ta yarfa ni agaban kowa da kowa. this girl has dissed me in front of everyone dad tace bataso na after all I have been tru saboda ita Kallonsa Alhj garba yayi yace khalid tell me kanasonta ko baka sonta Enasonta mana dad,but I mean to teach her a lesson Just live dat to me wannan tsakanina da iyayenta ne Daga Yau kadauka ka aureta an gama Daka tsalle khalid yayi ya damke baban NASA dad are you serious Tsaki siyama taja tafice abunta Yes my son .but ...... But what dad kafadi komai zan maka yanzun nan Are you sure? Yes enajinka dad Khalid i want you to live this country Zan tura ka las Vegas Kafin ka dawo I give you my words aurenka da wannan yarinya ba fashi Come on go and think about it gobe zanji amsa Dan shiru yayi kafin yace Yes dad,bakomai zan sameka goben Good jeka ka huta have fun Itako ko ajikinta kwnciya ma tayi tayi baccinta, ko bin ta kan haj mariya batayi ba karfe 2na rana alhaj garba da khalid suna tsaye yace Son u have made the right decision nikuma zancika maka alkwarinka kafin kadawo Sannan kuma Duk abunda na gindaya maka shi zakayi a Vegas kaji banason kuskure? Yes dad Barin wuce kar nayi late zan kira ka in na isa Nan sukayi sallama ya nufi sit dinsa dayake private jet ce Daukar waya yayi kira mint 5 saiga wani bakin karkarfan mutun ya shigo enda yake Mika masa envelope yayi yace masa ka nemo min komai gameda su Angama ogah.....family photon Alhj abdallh aciki da cheque na rabin kudin aikinsa Bayan wata daya,ba khalid ba labarinsa ko ajikinta don' itakam ma dadi takeji jin shi shiru Kallon post din sa a Twitter yasa ta Jan tsaki...maye kawai Ai nayi maganinka Ke,dawa kike magana ?
.
Mummy ,ba kowa tafada a dan tsorace Kwace wayar tayi taga suna khalid ne akan tweet din Wani mugun harara ta watsa mata Tashi ki fice min nikam ubanki na kira shasha Da Sauri ta sauka abunta don'tta matsu ita ma ta tafi makaranta tabar mummyn data sata agaba tun data ji labarin abunda yafaru tsakaninta da khalid ranar My princess baki Fada min Schl din dakike so ba Charab haj mariya ta karbe magana Alhaj ba enda faryal zataje,asata kusa da gida kawae ena kallonta Karamar yarinya kamar faryal har sai ka tambayeta ena zataje karatu salon tahadu da miyagun kawaye a dagula min tarbiyan ya....gaskiya alhj ban isaba bazan iya daukawa ba in wani Abu ya faru da faryal Ta Fada tana fashewa da kukan karya Sake baki faryal tayi tana kallon mummy Data dage tana share kwallan ban mamaki Haba mariya wannan ai bakomai bane,muna da hakkin yin hakan ma Amma yanada kyw Dama aji zabin NATA Ah a nidai banyarda ba yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halayensu ba Kawae tayi Turkish university ya isa tana zuwa tana dawo wa Me kikace princess,shiru faryal tayi ji take kamar ta rusa ihu awajen amma wani mugun idon da haj ta kalleta da shi Ya sata amsawa ba shiri,eh abba na amince nan ta shige ci:
Ogah Hajiya mariya ta iso, CE mata ta shigo nan aka kaita har Inda yake zaune shikadai Alhj an wuni lpya? Zauna mana Hajiya ai nan kamr gida ne Itadai gaba daya tsorone fam cikin ranta haka dai ta dake ta zauna Nan aka fara jera ma Hajiya mariya kayan alatu na abinci da shaye shaye wanda akayi musamman dan ita Bismllah Hajiya Cikin mamaki ta zauna tare dashi akan dinning Alhaji ena fatan lpya dai ko? Ahh ,dan gyran murya yayi yace bakomai hajiya Wata alfarma ne nake nema awjnki Kiyi hakuri ban nemi mijinki saboda naji yanada tsaurin ra'ayi sosai kuma banason na takura Koba haka bane haj? Dan shiru tayi tace ,hakane Alhj abdalla baida saukin kai sosai amma ba halinsa bane na asali Amma Alhj bangane alfarman dakake nema wanda baishafe Alhj ba ya shafe ni Kwantar da hankalinki akan mariya maganar yarki CE faryal Inaso kibani tabbacin Dana Khalid zai aureta shikenan Ena miki maganan nan a mtsayin business deal ne Ba inaso na baki doka bane Ku mata kunsan yadda kukeyi da yaran Ku Kin fahimceni? Dan dariya tayi,tace haba alhaji harka tsoratar dani Wannan maganan ai mai sauki CE Kabarmin komai a hannu na faryal batada mijin da ya wuce khalid Naji dadin zancenki Hajiya mariya,nikuma namiki alkwari zaki ji dadin wannan harkan muddin burin Dana ya cika Washe baki haj mariya tayi aranta tana hamdalan Business da alhaj Garba ainko wani iri ne zanyi ballanta wannan Riba biyu,tab Kafin Hajiya mariya ta fice a gidan sanda aka mata jaka daya na dollars acikin booth din ta hade da wasu pleasantries Faryal kuwa ana faman jigilar makaranta ta sami fannin medical physiotherapy Tsaye yake a bakin titi ya rufe fuskarsa da bakin sun glasses Dafa shi akayi Adan asirce, ya juya ya biyo shi suka Shiga ta baya Inda ba jama a sosai Mr kamil I'm glad this is the last piece of information I will be giving you...look man this shit is crazy and deadly. The police...... Shhhhhhh I know thanks Jordan,heere is your pay up Nan ya mika ma baturen nan envelope ya juya ya nufi gida Alhamdulihh dukannin vayani danake nema naga ma samu ,saura na fara binsu daya bayan daya don nayi alkwari Sai na ruguza alamarin duk wanda ya ke da hannun aciki ruguza rayuwta Dana iyaye na Nan ya dukufa aikin bincike da kyau yakaranta file din kowannensu Baisha wani wahalan sarrafa binciken NASA saboda kamil ya gabata fannin ilmin sarrafa computer kota wani hanya Bayan hour 4 ya fito daga sallah ishai_ nan ya cigaba da bin file din dayake downloading Ai kuwa yana tabawa yaga download completed.... Da hanzari ya zauna ya fara karanta wa Acikin su barayi shidan mutane hudu sun Riga sun mutu wanda duk ta hanyar kisan haya (assassination) ne Daya shine shaharraren dan siyasa ta kasar burtania da jamian tsaro suka kai shi prison sakamakon daukar fansa da wata yarinya tayi akansa bayan ya raping dinta ya kuma kashe mata iyaye Case din da yafara gani a news Dan jingina kansa yayi yace dayan yana las Vegas amma dan Nigeria ne Shaharren dan cacar casino ne....wanda kudi ma daya gansa sai da ya Sara masa...iya dukiya ya mallaka a rayuwarsa baisan ma adadin su ba Sai dai tsoron tsananta bincike yasa yake harkokinsa a asirce Babban matsalar shine bani da cikaken sunansa ...amma na tabbata shine gunner wanda ya so ya kashe ni da abba... Yana cikin nazarin ne alert ya shigo computers a Inda yayi hanzarin dubawa Tracker daya sa ne ta gwada masa present location na gunner is abuja...Nigeria Address ya fara kokarin dubawa amma yaga access denied Ohh what now,ya zanyi na gano sa? Gashi hotunar su na da ne a net ko yanzu ya kammanin su Yake oho Dan tunani yayi can yace Yes akwae tattoo but ya zanyi na ga tatto bayan a gefen kirjin su yake Haka ya hakura yA kwanta da tunanin abun a ransa....
.
Haka kamil ya cigaba da binciken sa batare da ya sanarda kowa ba, Sai dai haryanzu bai samu cikakken vayani akan wanda ya rage yake kuma nema ba Bayan shekara biyar gidan alhaji abdallah ba masaka tsinke yau kusan sati aka dauka ana tsare tsaren gidan domin dawowar su zafar da kamil Musamman Hajiya ta shirya abinci kala kala tasa kuma aka zanxa tsarin dakunan su komai da komai sabbi aka musu barin ma zafar datake ganin yanzu ya zama cikakken namiji zai hau kan harkokin dukiyar mahaifinsa Da yamma karfe biyar faryal dake neman cika shekaru 20 da haihuwa ta sauko cikin wata Riga da skirt na material baby pink mai ratsin silver stones ,ta parking dogon gashinta sai dai wannan karon sake shi tayi jelar ya Fada har gadon bayanta duk da Light make up ne a fiskarta amma tayi kyw sosai sannan ta rataye mayafinta putchia pink da takalmi da jakar vine a hankali take takowa zUciyanta fal da farinciki Ke wallhy zaki sa muyi latti, nafiso Dana yafara sauka a idon mummynsa haj mariya tafada tana kokarin turata gaba zuwa mota Kamr baza akai airport ba haka kowannen su yakeji, 5pm aka sanar da saukan jirgin Dubai, kasa zama faryal da haj sukayi sai hange hange suke Abba kuma hamdala kawae yake yarana sun iso insha Allah Kusan Rabin mutane jirgin sun sauko amma shiru ba zafar,da kamil Jitayi an damke ta ta gefe da Sauri haj mariya ta juya ido hudu sukayi da zafar wanda ya sauya ya dawo tamkar balabe suits ne ajikinsa farii da bakin Riga ta ciki mai dogon hannu Mummy yafada da karfi, wani farinciki ne ya lullube hj mariya tuni ta rungomu sa tana dariya aida gudu faryal ta karaso ta kankame shi itama dukansu uku kamar bazasu sake juna ba Abba tsaywa yayi yana kallonsu cikin sanyin rai da hamdaln ubangiji Karasawa yayi wajen nan zafar ya fashe da kuka yayinda yafada jikin abban nashi Shima alhaji. Daurewa yayi amma yayi kewarsa sosai musamman ma da tunda suka fara shi baije Inda suke ba Ina kaamil abba ya tambayeshi,yana........
.
Baiko karasa naganar NASA ba .....nan ta hangesa yana tahowa jaka ne a hannunsa yar karama kamar brief case Zaro ido waje haj mariya tayi tana mamakin da kokwanto anya wannan kamil ne? Sam ya sauya mata daga kamannin da ta sani saboda inka gansa ma zaka dauka dan gidan wani sarkin larabawa ne,farar designer jallabiya CE fara kat a jikinsa ya nade bakin sumansa da ja da bakin hularsu haraami...bakaramin kwarjini ne ya bayyana tattaree da shi ba Suman tsaye faryal tayi don' harga Allah son shi da tsoron shi Taji ya kamata a take Da murmushinsa ya tinkaro abba kamr bakomai aransa..abba na kai hannunsa don' ya tarbosa nan ya Fada jikin abba ya fara kuka kamr yaro karami Har cikin zuciyar sa yakejin son kamill din Kamilu Ashe baza a girma ba yafada yana dagosa Abba ,nayi missing dinku sosai,. Dan murmushi abban yayi yace,muma haka son I'm proud of you guys Naji dadin sakamakon Ku dukka, Mun gode abbah yafada yana juyawa Murmushi yayi ya dan rusna gaban hj mariya ena wuni hj, Hajiya mariya kam tsaywa chak tayi tana kallonsu itade har yanzu bata yarda shidin bane Wani bakinciki taji ya tokareta a lokacin, da kyr ta furta lpya tana yake Haka nan dai aka hakura aka tattara aka koma ta gida Isarsu keda wuya kowa yanufi dakinsa yayi refreshing ya sauya kayan jikinsa Wani sabon wankan faryal tayi itama .tubarkallah kowa yafito Ra's Ranar tamkar kwae haka ake tarairaya su a gidan abinci kam sanda suka gaji dan kansu suka bari Allah Allah take tasamu dama ta gana da kamil domin gani take kamr baza su hadu ba
.
Wayarta take ta nema bata gani ba,gashi kusan karfe 11.30 na dare duk hankalinta ya tashi saboda taso tayi amfani dashi ,musamman ma da ba abata dama sun gana da kamil dinta sosai ba Toh ni waya dauka min phone tafada ranta a dan bace Kodai na manta a palour ne,barinje dai na duba Tsaki ta danja ta bude kofar dakinta ta nufo waje Kan stairs tagansa zaune a bayan coriidor na fannin gurin haurawa sama Kansa akasa alaman waya yake latsawa Murmushi tasake aranta tana cewa wow ga abunda na ke nema anan ashe Nan ta cire takalmnta tafara saukowa a hankali zuwa wajensa Bai lura ba Hannun yaji a kan idanunsa an kullesu gam,sai dai kamshin turaren ta da laushin hannun yasa shi fahimtar muradin ransa a wajen Kamu daya yama dan hannayenta ya zare su duka ya jawota gabansa tana fuskrtan sa Zaro ido waje tayi tace what! Dama kaine ka daukemin waya koh? Wayace ka sacemun wayata ,ai baka damu dani ba, bayan ko kira na baka sonyii da katafi,ena kaaje chan ne ka sa mu wasu ka mance da ni ? tafada fuskarta ba alaman wasa sai wani murmurdaa vaki takeyi tana hararsa Dariya sosai ta basa yadda ta Dage tana masa Fada kamar dagasken satar yayi Mikewa tsaye yayi yazo dap Da ita ,tsit tayi don' ita har yanzu kwarjinin dake tattare da shi na sata taji kamar bazata iya kykwan tsayuwa agabansa ,murmushi ne mai dauke da sakonni kala kala na kewa da kauna A tare zuciyarsu ke bugawa yayin da gaba daya sun lume cikin kallon idanun junansu....
.
A hankali takai hannunta kan fuskrsa mai haske da laushin tabawa.... Shima a hankali ya kai bakinsa kan hannun nata hancinsa na gogan fatar hannun nata a lokaci daya Kamar kar ta bude ido takeji ,aranta cewa take in mafarki take bazata farka ba Iska taji ana hura mata a fuska , a hankali ta bude idanunta da suka fara sauyawa chak ta ci karo da narkakkun nashi idanun sa daya kasa daukewa akan ta Zuciyarta ne ke tsananta bugu,numfashin ta na nemar canza salo, Dan girar sa ya daga ya tabe baki yana murmusawa Hmmm Ta biyoni ne ko ? Marar kunya harda cewa na sace mata waya Turo baki tayi tace ni wayata zaka bani Ga wayarki hajiya ,kar asake karo min laifi Gwalo masa ido tayi sannan tace Waya kunna maka abunda na rife da password Ohh kin manta ba abunda za'a iya kullemin Yanzu? Nida abuna ma wazai hana ni budewa Cikin tsokana yake cemata Na duba ne Dama naga rivals dina da akamin bana nan yafada yana dan satar kallonta Dariya tadanyi tace,ina ka gansu? Ai sai kabani wayarka nima naga yan matar naka na chan masu hanaka kira ta Kuma dama da ka dawo ko oyoyo baka Min ba tafada a dan shagwabance Dariya yayi sosai kafin yace oyoyo? angel katuwa dake?da CE miki akayi ke baby CE da zan miki oyoyo? Daure fuskanta tayi tana kananun magan ciki ciki Nice ma zaace ma katotuwa koh Mekike cewa ne katuwa,zoki karbi wayar toh tunda zagi na kike a zuciya Yafada yana kallonta yana murmushi A fusace ta juyo zata nifi hanyar steps wai a dole taji haushi I'm sorry ruhi na yi hakuri Sassanyar dadaddar muryansan ne ya dakatar da eta Nan ta ja ta tsaya tana kallon karasuwarsa Inda take Jitayi ya rungumeta tsam ajikinsa i missed you ruhi, bakisan yadda nakeji ba ne kawae Some words are better left unsaid Dan dagota yayi ya nuna mata screen din wayarsa Hoton tane tsaye ta dafa glass door na airport dazu da suka fita Dazun Dana ganki a airport naso ace ke zan fara sacewa ba wayarki ba kin kara kyw angel, Hope dai ba a dama mun ke a schl din kun nan Dan turesa tayi ta jingina kanta akan stairs Ai nikam ba cewa nayi naga ma fushi dakai ba.5years fa tafada kamar zatayi kuka Shhhhh haba ruhi na nasan nayi laifi amma kinsan i need to fulfil abba s promise ko Kema kinsan kina tareda ni kowani lokaci, in har zan manta dake Ashe zan iya manta dakaina kenan Hannu ta mika masa ya karaso kusa da ita Kara kankame shi tayi tanajin yanda ya sanyaya muryansa yana cigaba da magana a kunnenta Shiru tayi ta kasa magana sai lumewa takeyi ajikin nasa Shikuma ya Daura kansa a kafadanta Ehm uhmm sukaji abayansu da Sauri ta sake shi duka suka maida kallon su bakin stairs .
.
Kaga blue moon lovers "dare yayi aje dai akwanta Wani kunya ne ya lullube ta da Sauri ta rabe jikin stairs da yayi hayar cikin gidan Wurga masa hankerchif kamil yay yace Kaifa wallhy kasamin ido zafar, Da Allah dakata malam "kace zaka zo lovey dubey dinka kabarni enata jiranka a dakin ka , Ba bacci kakeyi ba,na dauka tare zamu kwana ai,shyasa na barka I missed you fa bro,meyasa kataso? yafada yana kwale masa baki Yimin shiru da Allah"' kasan ma wadda kake fadan wannan ai .... endai bai isheka ba ne ai sai kajira gobe ka karasa fada mata Kar ka rude ni Dariya suka kyal Kayle dashi suka nufi da kin Kamil din tare Bayan sallahr asubahi abba ya umurcesu da su koma bacci su huta ,gaba daya satin ya basu Hutu su rabi gida kowa ya sake kafin aje next plan Yan uwa da abokan arziki haka suka dinga Turin shigowa ana musu maraba su enna salima da su kawu kabiru da matansa Mariya haka yaron nan yadawo? Ni na dauka balarabe ai kuka samu tacan kasashen Kedai bari shafa,Kudi wasa ne? Kudi kuma me kike nufi kamil din yayi kudi ne Hmmm ai sawa nayi adinga samin idon Akansa. Kinsan ba bazan sake alh ya dinga barnatar da dukiya ba Nan ne naga achievement din sa kala kala da awards kuma wallhy kudi yake caska a hannun turawan nan bana wasa ba Kinsan fa ya mugun kwarancewa a ilimin sanin computer Ni abunda ya tsaya min awuya ma shine,yanzu akwae companyn Samsung galaxies dasuka bashi contract zaiyi musu designing phone tracker na sabon tsarin zamani ..... Eyeeeeeee toohhhhh Me kuma wannan din toh mariya Kee shafa wallhy in sukayo signing dinsa to fa ya tsalleke wallhy Kamfanin wayace fa?
.
Kikasan adadin mutanen da zasu saya wayar kinsan bakaramin riba bane fa sai dai kiji ana kirga shi cikin billionairs nakasan nan kwanan nan Dafe kirji shafa tayi tace dan Allah? Shikuma dan namu fa? Ehh kinsan yanzu shi zaina lura da harkokin mahaifinsa amma ba nan ta tsaya ba shafa,so make nima na Daura zafar kan kamfanin da alhaji garba ya mayar karkashi na "GG investment' Bani mu kashe kawata gaskiya kanji na ja mariya Ai na dauka zaki sa ido ne Karen jeji ya wuce ma gida gata Toh alhamdulihhi ai ko naji zance......nifa tsoro ma yaron yafara bani sai kace dan aljanu anya alhaji ba gamo yayi ba da xuriyan aljanu? Ke da Allah ,shafa ni ba wannan bane yanzu ya za ayi da Maganin khalid dan gidan Alhaji garba? kinsan fa muna kan cin rabashe har mun fara giniga da dukiyar Alhj garba Uhmmmm hakane Kawata,toh me make ciki yanzu Gashi shima ance sati mai zuwa zai dawo kankat ya gama karatunsa a waje Dan shiru shafa tayi kafin tace Ai bakomai bane wannan mariya,ko eta faryal din tana da wani ne? Haba haba wani,, nida na dau alkwari zanba khalid ena zancen barinta da wani Uhm uhm mariya Ina fatan dai kina aikata abinda nake gaya miki akan ma nemartan dai Eh shafa duk sun tafi na koresu bakowa yanzu Amma kinsan meye Sam nakasa gane me tsakanin faryal da kamil tunda ya dawo fa Eyeeee kaamil kuma? Oh Allah ana wata ga wata Kamr ya mariya Ban fahimce ki ba Kawae naga yadda take shishige masa ne abun yana daure min kai wani lokaci anya yaran nan ba soyyaya suke a boye ba Ke zaki tsaya tamabya ne,ai bincikowa zaki yi kinsan bamuda mafita a hannun Alhaji garba muddin wani matsala ya kawo khalid ya rasa faryal Bayan sati biyu da dawowarsu kowa alhaj ya Daura shi kan companyn daya kamata ya kama aiki Duk da rashin samin lokacin da kamil da zafar suke fama dashi "faryal Sam ta dena bin driver inzata schl haka take jiran kamil yakaita sannan su dawo tare Ranan jumua da yamma Siyama CE zaune a falon ita da haji mariya suna gaisawa kicinkicin taji alaman Shigowar su faryal da kamil yasa ta mike ta CE ma siyaman toh bari na dubo miki shi zafar din ko Don kuwa har aranta dadin juyin mulkin nan taji zata hada zuriya da alhj garba ta da, ta ya... Toh mummy siyama tace tana duban kofa dake akejin motsin tafiyar Kamil ne yafara kutso kai ciki Ai ko batasan lokacin da ta mike tsaye ba zuciyarta na Neman zaucewa ganin yadda ya sauya kamanni Arrrmour Kaine wannan? Tafada tana nuna sa da hannu Shiko murmushi ya jefe ta dashi yace, siyama kenan u look great girma kenan Yafada cikin tsokana Mutsininsa yaji anyi da karfi sanda yayi ouchchh ....angel Ni mu wuce na gaji fa tafada tana narkewa ajikinsa Tabe baki siyama tayi aranta tana cewa,,,,, hmm yarinya da ba don ba don' ba wallhy saina dawo da tsohon zuma inga tafadin ki Ana cikin hakan zafar ya tinkaro zuwa wajen Bye siya talk later " OK kawae tace tana maida hararan da faryal ke fa man binta dashi Hey yan mata na zafar ya Fada yana murmushi ,da gudu ta zo ta rungume shi dama itakam gwana CE. Zama sukayi tare suka cigaba da hirar suu Itako farya tunda suka haura sama take kana nan magan ganu Nikam wai fushin na meye ne haryanzu faryal? Bakai bane? Tafada kamar zatayi kuka Ni? Mena miki ohh Allah yanzu fa muka shigo Ok baka SANI bako Tafada tana ware idonta waje,,,,, Yeah tell me ko na tafi na barki dodo ya cinye ki Da Sauri tace Ai gwara dodon ma akan wanda kake wani CE ma ""siya u look great, girma kenan c yh ltr " tafada tana kwaikwayon maganansa Dariya sosai tabashi abun ya matukar birgesa yadda take shake muryanta Ita kuwa kuluwa ma ta dada yi ta juya zAta haura sama Jawo ta yayi tsam tafada jikinsa A hankali ya sauke murynsa yace ......angel am sorry banace miki ke kadai bace a duniyan ya mace a ido na Koba kiyarda bane? Danja tayi daga jikinsa ta Dago kanta tace naji amma ni wallhy ban son tanace maka amour ka Fada mata hannunta sarke a cikin nashi tana wasa dashi Faryal.? Taji ankirata da wani murya " gaba dayan su sanda suka razana Me zan gani haka? Kinada hankali kuwa Ki wuce ki barnan kafin naci ubanki tafada a fusace Enda itama faryal din ta haura sama da sauri ta nufi dakinta Wani harara ta watsa masa ta bi bayan faryal din
.
Banko kofar haj mariya tayi" Cikin hanzari faryal ta juya tace,, Mummy ... .ki min shiru dan uvanki,wani uban kike masa harda wani rirrike masa hannaye Ohhh lallai fa,,,, wato shiyasa kika nace yadinga kai ki makranta don' kusami filin kuna shagalin Ku ko? A'ah mummy tafada cikin rawar murya To Fada min meye a tsakaninki da shi ........ kinsan Hali na sarai zan gaya ma babanki komai daga ke harshi Ku gane kuranku agidan nan Mummy dan Allah kiyi hakuri,wallhy ba wani Abu bane Bazaki Fada ba kenan? Kuka faryal ta fashe dashi Mummy INA son shi ne,shima yana so na Tas taji mari a fuskanta Kalleni nan faryal, Yau yazamo miki rana ta farko kuma ta karshe da zaki furta kalman so tsakaninki da wannan yaron kinji ko bakiji ba? Gyda kanta tayi alaman eh tana khannunta dafe da kuncinta Ficewa haj mariya tayi tabar ta tsaye a wajen Sulalewa kan gado faryal tayo sai kuka kawae takeyi ba kaukawtawa Da safe alarm din sallahn asubahi ne ya daga ta mikewa tayi ta janyo wayarta hade da ware idn ganin miss call da texes da kamill ya jera mata Murmushi tadanyi kafin ta sauko ta Shiga bayi Wanna tayi hade da alwala ,kafin ta tura msa sakon gaisuwa kamar yadda ta saba Baifi Minti 2 ba sai ga shigowar kirarsa Sallama tayi cikin sanyin murya ,shiru yadanyi jin yadda muryntar yake ratsa shi Haba Ruhi na kinsa har nabi nakasa bacci"mai ya hanaki daga wayata jiya ? Langwame fuska tayi kamar wacce take gabansa tace Twin soul bacci ne ya sace ni fa Oh alhamdullhi,na dauka ko akwai matsala ne naga kamar mummy na fishi da mu Uhm bakomai twin sou l Barin shirya na fito mu tafi ko OK ki shirya din.. yafada yana katse wayar Mikewa tayi tsaye a ranta tana cewa' mummy sai dai kiyi hakuri bazan iya rabuwa da twin soul ba nikam Yanzu nake jinsa, Karfe 5.na yammacin asabar. Laraba mai aiki ta shigo , Faryal ana Neman ki a falourn mummy Batayi wata wata ba ta fice ta nifi hanyar site din haj mariya da sallamarta ta shiga Zoki zauna faryal khalid ne haji mariya tace tana kmaida kallonta kan faryal din A take ta murtuke fuskan nan kamar taga mutuwarta Sannan ta zauna a takure batace uffan ba Toh my son bari naje ciki ko? haj ta mike ta nifi kasa Wanda yayi dai dai da lokacin Yana kokarin saukowa shima tagansa kai zo nan tafada da kakkauran murya tare da hade rai dan risinawa kamil yayi ya CE haj ena wuni? Rike gaisuwar kamil,bana bukatar gaisuwan munafuki mai neman lalata yara kanana,,,,, Dan shiru yayi baice komai ba Nidai INA maka last warning, kar na sake ganin ka kusa da yata faryal idan ba haka ba kaida wallhy kai da alhaj...... Ayi hakuri Hajiya Ko kallonsa bata sakeyi ba tafice abunta Wani shuumin kallo Khalid Kevin faryal din dashi Baby I'm speechless..... kinga yadda kika kara kyw kuwa Shine bazaki zo tarbana ba I know kinsan zan dawo jiya. not even a call or TeX tunda natafi Dariya ma ya bata,khalid am not sure Inda ni kake magana. Tafada fusknta a mirtuke Ena ruwana dakai dazan maka wadannan abubuwan pls? Hhhh baby kenan,kina nan yadda kike har yanzu I tot kin girma yanzu zaki bar yaranta and face reality Nidin nan fa mijinki ne kwanan nan "meyasa bazaki fara biyayya ba uhm baby Hehehe wani shewa faryal tayi " kace me? Su mijii manya Lallai tab.... Amma bada ni ba , and not even in your wildest dream khalid Mikewa tsaye faryal tayi tana kallonsa tace I belong to someone else shi ka dai , and u knw what? Ka kwantar da hankalin ka khalid he's better than you Ke Faryal ,,,,,ya kirata da kakkauran muryansa ,ke har a tunaninki akwae wani namiji better than me ne? Kinuma min shi go ahead girl uafada yana kokarin nufota Niko zan miki alkwarin. tabbatar miki that khalid GARBa is the only MAn for you Mtsw sai kayi kuma,all you can brag abt is riches, you disgust me khalid....tafada cki ciki Ni zan tafi tafada tan kallon waje I'm stucked here khalid sai anjima tafice Faryal,faryal ......
.
Yake kira ko ta juya abunta Dun kule hannunsa yayi yana furzar da iska a baki " ya fice Ko sallama baiyi ma kowa ba ya nufi hanyar waje, Karo suka yi da kamil dake kokarin shigowa cikin gidan Dada daure fuska Khalid din yayi Haka suka wuce tamkar basu San juna ba domin shi khalid Sam yaki jinin ganin kamil a fuska Har cikin ransa yakejin ena ma ace Yau kamil ya mutu yabar duniya Wajajen karfe 8 na daren ranar A hankali take tafiya harta kai bakin garden na back yard, zaune yake yana danna dannensa shikadai Farar riga CE sanye ajikinsa da farar three quarter sosai yayi kyw " Sai da ta tsaya ta gama kallonsa kafin ta karaso Twinsoul,ta fada tana kokarin zama tagaban sa, Just in time Angel,I'm so happy to c you" kamar kinsan kece araina yanzun Murmushi tadan yi tana kallonsa Riko hannunta yayi yace ruhi," meyafaru jiya? mummy tamiki Fada bazaki Fada min ba ko? Dan ja da baya tayi tace What ? No kawae ta CE min .....uhmm emmm" tace..... Girgiza mata kai yayi yace uhm uhm ,kar kimin karya ruhi,just tell me Kokarin kwakulo hawaye takeyi,tace twinsoul,idan nafada maka zaka dena bari na INA zuwa nan kullum Gashi kaga tahana ni binka schl yanzu ...I don't want us to be apart" nikam bazan iya ba Ok Dama ita ta hanaki bina yanzu? Ehhh tafada a hankali Amma kamil.... Shhhhh faryal kinsan bazamu saba dokan mummy bako, Aiko fashewa da kuka tayi,tanacewa Dan nafada maka ko ? Nooo angel c'mmon, look idan baki bar kukan nan ba ba abunda zan Fada miki yanzu Hannunshi yasa yana share mata hawayen yana cewa'. stop you're wasting your precious tears ruhi, ure too special to shed a tears ""na tsani kukan nan naki Dan tura baki tayi tace toh ni kafadamin ya zakayi dani,u know I can live witot seeing you OK fine,ZAmu na haduwa a schl kafin a tashi ko Uhm said wanne kuma tafada tana kallonsa Shikenan ruhi ,for now Yarfa hannunta takeyi tana cewa No,baza mu na haduwa a gida ba kenan ko me? Yes ruhi,bana son kisami problem da mummy Amma insha Allah na miki alkwari I will fight for us,zan tabbatar mata I love you and I wanna spend the rest of my life with you Com"on smile ruhi.... Murmushi tai tana kallonsa ,a hankali ta furta me too twin soul, Toh come let's get to bed kije ki kwanta kar mummy ta ga baki nan Ok tafada tamasa peg a kuncinsa, Shima mayar mata yayi a goshinta sannan ta wuce ciki
Share this
Tuesday, April 10, 2018
ARNE Part Three (3)
.
Alhamdullilh,kwana biyun nan haji mariya ta saduda ba kamar da ba,sai dai fa had yanzu akwae sauran abun aranta..... Duk lokacin da rashin kirkikn ta ya taso hka zata ci masa mutunci abunta Shafa atu CE tace mata ,karta shagala da dadin baki da wa'azin karya da alhaji yamata A fadin ta wai kar alhaji ya mutu ace zaa ba kaamil wani kaso daga ciki arziki da kaddarorin alhj koda sadaka ne..... Haji mriya da Allah ya Dora ma son kudin,Jim hakan yasata warware sauran imanin da yaso ya Shiga zuciyarta Sai dai ta barsa ya sake a gidan,amma bata yadda ta hada shi matsayi da yaranta ba...dole sai ta banbance su.
.
Bayan shekara daya makrantar su zafar cike take da many a manyan mutane inda motoci na alfarma ke famar zurga zurga Academic gown ne ajikin su kowa ya Sanya murmushi a fuskarsa,baka ramin kyw kuwa sukayi ba anata daukar selfie Siyama CE da kawayenta suka nufo su Dafa shi tayi tace amour I'm going to miss you,tana Fada tana nemar kwntar da kanta a gefen kafadarsa Dan tureta yayi yace ojh God siyama say nawa zance miki ki daina sa hannunki a jiki na ne,I hate it_common girl..yafada ya juya mata baya ya cigaba da abunsa da zafar Kallon kawayenta tayi sunyi kicin kicin suna mata dariya kaSA kasa Nan ta hantsile ta bar wajen da gudu Ko kallonta baiyi ba ballantana yasan me take ciki Kaamil meyasa kake ma siyama haka ne wai, Look zafar yarinyar ta gama fita min ne,ta takura min ko yawo bata bari yawuce min fa......think God ma zan bar schl din Yau Dariya zafar yayi ,hmmm karya dai ba kyw... Inajinka ranar kana ma faryal alkwarin bazaka sake kula siyama ba Dan Sosa kai kamil yayi yace ,tooooo gulma kenan....she's my sis ai anything for her....besides nifa ba son siyaman nan nake ba Ehmm hmmm nidai bazance komai ba What,me kake nufi zafar Ahh ba komai She's our sis yafada yana kyal kyalewa da dariya Toh ya isa ko,muje ma na dubata nasan tana chan tana ciye ciye...tohm let's go Marairece masa tayi a garden suna zaune ,yay kaamil nikadai zan na zuwa schl kenan.....I'm missing you already, Ware idonsa yayi yace missing me? Bayan gidan mu daya ko,.... Just concentrate on your studies banda kula wasu banda kuma Fada da kowa No Yaya kamil just tell me bakason na taba maka siyama.... Ohhh gosh haba Angel,u don't trust me? I do,tafada tana murmushi..... What's d smile for faryal? Ai ji nayi kace mkn angel Yau natashi daga litl sis din ne? Dariya tabasa ,a ransa yace to barin tsokaneta Wait,dama bakisan meaning din sunanki bake nan? Nidai na San sunanki nakira Faryal means Angel.... Oho dai tafada tana mikewa,ni bacci zanje Toh gudnite faryal sis Dan hararsa tayi ta wuce ni bazan amsa ba Toh shikenan gudnite angel......
.
Aikuwa dadi ya lullubeta da sauri tace gudnite bro tana kyal kyale dariya Kallonta yakeyi har ta kule kafin shima ya nufi dakinsa Bayan sallar da sati biyu had su faryal ana shirin komawa hutun jssce. Kafin nan siyama tasha zuwa gidansu yafi abunda yafi Duk da ma watarana sai dai suyi hirar su da zafar amma ba shi zai hanata sake dawo wa ba Tasaba da zafar kuwa domin shikne kullum vikin bata baki idan kaamil ya mata wani abun Gashi tunda haj mariya taji labarin abinda ke kawo ta kuma tasan waye ubanta Hankalinta ya matukar tashi son bakin ciki Amma bata nuna ba ,inbanda ma Jan siyama da takeyi ajikinta Hakan kuwa bakaramin sosa ma faryal rai yake ba..son aduniya ba wanda ta tsana kamr siyama
.
Bayan sati biyu faryal ta koma schl,amma har yanzu ba abunda take hada ta da kaamil Wasan boye ne ma tsakaninsu..Sam bata bari su hadu ballantana su shirya A schll kuma in banda wutar gaba ba abunda ke huruwa tsakaninta da siyama Barin ma siyama da Duk yabi yahadu mata da tana jin haushin wulakancin da faryal take ma yayanta khalid..kuma tadauka itace kawae silar da kaamil yace baya sonta Bayan isha I kowa ya hallara a Fallon alhaji abdallah,nan ya bude maganar sa da dan karamin waazantarwa kafin ya fito da envelope guda biyu da ga briefcase dinsa Wa zafar yafara mikawa,wannan admission dinka CE da visa komai da komai na ciki Yadda kake so,england kace ai ko? Da murna ya amsa ehh abba To gashi 6years program ne tareda masters degree six month fannin petro- chemical engineering Gaba daya faloun ya dauka da masha Allahu..nan kowa ya bayyana farincikkn sa ma zafar sannan aka gode ma alhaji Yawwa saura kai kaamil ga naka,Germany ko? A hankali ya gyda Kansa alamr eh To kaima gashi same thing 6yrs program da 6 month masters degree a fannin web design and computer engineering. Amma tafiyarku zai kai next week bayan an kammala walimar saukar ku Nan ma fa waje ya rude da kabbara, Fuskansu cike da farinciki da murna Godiya aka dinga ma alhaji ranar har sanda ya gaji ya basu waje Haj mariya da duk da ma abun ba harcikin ranta bane,amma ba ydda ta iya haka ta bisu da murmushi itama Faryal kuwa ma Zafar kawae tayi wa murna ko kula Inda yake batayi bllantama ta kallesa tace wani abu Duk da Baiji dadin hakan aransa ba,yaso ace faryal dinsa itace na farkon tayashi murna personally kafin wasu daga waje Ringing din wayrsa CE ta dakatar da shi, jabir ya akayi,yanzu nake shirin kiranka
.
Toh gashi ai na kira ka na siyama ruwa sai an tace Tsaki kamil ya ja toh zaka ruining min good mood dina kenan ko jabir dama haka kake Ohh really to fara Fada min naka kafin na gaya maka nawa albishir din Tab kaidai kafara enajinka, Anyways nasamu fa,and gues what am going to germany Dan Allah? Cikin farin cikin kamil ya tambaya...nima fa nan zanje Ai kuwa dariya suka kwashe dashi dukkan su Mutumina an sake hada mu , yeah amma ai ni medicine zanyi kaifa nasan computar ta ka zakayo ai mayen danne danne Dariya kamil yayi yace of cous ,Fada da karfi Dan hirarsu suka yi Inda kamil yadan gaya masa abunda ke faruwa tsakaninsa da siyama da faryal Kasan meye kamil kabari inna zo ranar saunkan ku zamuyi maganan kawae Nan sukayi sallama Kwanciya yayi ya rasa abunda ke masa dadi,wayarsa ya dauko daga inda ya jefa TeX ya sake tura mata kamr yadda yasaba Amma still shiru no reply, Haka yayi ta juyi daga bisani yayi wanka ya kunna karatun Qur'anin sa yana bi har bacci ta fara zuwa masa Zuciyarta na balaien sonta masa magana ko ta ma replyn TeX dinsa amma ena ,ta kudura aranta sai ya dan Dana abunda takeji in tagansa da siyama Writing pad kawae take yankawa tana rubutu tana zubawa cikin drwerta Ana sauran kwana uku walimar su zafar, Hangota yayi akasa tana zabga kuka ta rike cikin ta...dayake kofar dakinta a bude yake Ya na ganin abinda takeyi ayayin da yake shirin saukowa zaije wajen zafar Ganin kukan da takeyi tana rolling yasa shi dole Shiga dakin nata, Kokarin dagata yayi yace Faryal meya sameki,? Da kamr bazata amsa ba tace cikina ne yakemin ciwo A take ya fahimci menstral pain ne yake damunta Nan yace ena maganinkin? Dan dago kai tayi ta kallesa alaman ya akayi ya ganota Murda ta cikin yasakeyi ai ba shiri tanuna masa drwer Dayake hankalinsa duk atashe yake cikin hanzari ya sa hannu ya dauko inda wayannan writing pad dinta suka zubo kasa Mika mata yayi ya bata ruwa Sannan ya juya da niyyar tattra mata writing pad din Abinda yagani ne yasa shi tsaywa chak Da sauri ya dauka daya daga cikin su Inda yaga an rubutu" a day without u is like a day witou me,I lost my smile since d day i last see yours, I gues im not 100% living if am not being honest with you,I love you yya kamil I can't leave witou u my nurul qhalb..... Wani sanyi ne ke ratsa shi har cikin zuciyarsa, da saurii ya Sake daukan wani zai karanta har yafara ganin" ure d burning flame.......chak yaji ankwace A fusace tafara ,wai me haka yay kamil ,meyasa zaka kalla min abuna Far...ya.......... ni bana son naji komai daga bakin ka, Just leave me alone, And thanks for lying to me abt siyama , Ohh my goodness ,faryal what's is wrong with you? Everything ,tafada a fusace...nika ficemin a daki kake can dakinka da yan matanka suke zuwa Get out...tafada masa hartana bari hawaye tam fuskarta Wani sassanyar kallo yabita da shi mai dauke da sako kala kala Sannan ya sa Kansa ya fice baice mata uffan ba
.
Ranar jumua da safe wani makeken fili aka decorating a daya daga cikin gidajen alhaji abdallah dake garin abuja Hidima akayo sosai ,walima taci sunanta walima....mutane anci ansha masha Allah Sai godiya Dukkansu sun yi kyw sosai don kuwa tsadadden fararen yadi aka musu dinkin babban Riga ,tubarkallah Dayake suffar su kusan iri daya ne bazaka babbance waye ba dan gidan ba acikin su Sai dai duk da kywun zafar, abayan kamil yake,hasali ma yana daya daga cikjn abnda ya ke Dada hura wutar kiyayya a zuciyar Hajiya mariya tunda tafara ganinsa a asibiti Shima fari ne ammaa Arabian milk, yanda ball eyes dinsa ga wani sajen daya fara shatin kwanciya a fuskarsa.yanada dogon hanci,da fararen hakora..ga suman kanshi baki ne wuluk.barakallah. Faryal ma cikkn farin hijabin ta tafito ,a yau jitake kamr bazata iya daurewa bata ma kaamil magana ba Don kuwa tunda ya barta a daki take faman jin haushin kanta akan abinda ta masa Shima tundaga ranar ,ya fita hanyarta bayace mata uffaan , Gan tayi sun fice da abokinsa jabir Haka kawae ranta ya hau kuna jitayi kamr tayi tsuntsu ta bisu, Chan dai haka ta mike ta samu zafar dake famar waya da siyama sai dariya sukeyi....kai kace masoya ne Ina xuwa siyama ban mintuna biyu.... Noo zafar ,tace cikkn shagwaba Tsaki faryal take ja,a gefe tana kallonsa dayake famar llaba siyama, OK fine naji idan bankira after 3 min ba zanzo din shikenan? Yes tafada tana dariya Am here sarkin fushi,yafada ya na kallon faryal da ta tamke fuskarta Ni wallhy kabani haushi ma Yaya zafar nafasa maganan Tafada tana juyawa zata bar wajen Tsayawa yayi ya na rokonta haka fir taki, Chan bayan kamr mintuna 10 sai gashi ya fito shima zai fita Ai tama da gudu tazo ta davurce masa akan saita bisa dik enda zaije..... A tunaninta gurin su kaamil da jabir zaije don' ku ta kudira aranta sai ta ga enda yaje Hanyar wata villa garden taga ya kama ,nan tafara cewa ni ka sauke ni Harararta yayi yace ai baki isa ba tunda kika fito sai mun karasa,ai bani na kiraki va Parking yayi suka fito ,Nan ta je gefen wani 2sideways chair ta zauna, Muryan da takeji ne yasa gabanta dukan Tara tara Dan kasa kunnenta tayi, taji anacewa bakomai kaamil apology accepted, Bata bari an karasa maganar ba ta sa kanta cikin wajen Aiko ido hudu sukayo da kaamil ,kafar ta kasa daukarta ya yi Da sauri ta gaining balance tafice wajen tana kuka , Ko jiran zafar batayi ba ta tsaro a daidai ta Dariya siyama ta kwashe dashi,aikin banza To na bar mata kai sai ta dafa ta cinye tafada tana kara gaba
.
Kaamil Dama kuna nan ,e wallhy, munzo da jabir Kaine kazo tareda faryal? Ohh gosh ni har na manta fa,fitinanta wai sai tabiyo ni Kun hadu ne? Eh amma naga ta koma, Ohh kyaleta battada aiki,naga kwana biyun nan wani rigima take jii dashi To ya isa kuma ogah,ka kyale min sister ta sakata ta wala, Dariya zafar ya fashe da shi,kwaji da shi ai Kwana daya tal ta rage maka,gashi ba zuwa Hutu Tamke fiskar sa yayi shikam ,a yayin da zafar da jabir suka sa shi a gaba da tsokana Fitowar siyama ne yasa shi mikewa ,toh mu zamu tafi Kamil yace OK toh bakomai, nagode amour tafada da dan murmushi Da ka ganta kasan ba kalau take ji Nan jabir da kamil suka nufi hanyar gida suka bar zafar tareda siyama Hey,are u owryt,kinsan masoyinki zai zo shine kuma u asked me to come,yafada cikin tsokana Just stop it zafar,tafada hawayen na nemar kwace mata, Subhanallah siyama daga wasa,? No ba haka bane zafar, zuciyata tace ta kasa hakuri kawae Duk farinciki ya lullebe ni lokacin da mukayi waya da jabir yafada min da kamil zamu hadu But gues wat? Kamil hakuri kawae yabani ,tafada tana fashewa da kuka Yi hakuri siyama ,cmon stop the tears mana zakiyi zazzabi fa Na hakura zafar ,dole na kyaleshi kamil baya so na,no matter what tafada tana sharen hawayenta tace I'm going to move on , Da sauri zafar ya rike hannunta yace yes siyama move on,Allah ya zaba miki mafi alkhairi a rayuwanki Kinga you are still young fa,kinada lokacin da zaki zabi koma waye kike so a rayuwanki Thanks zafar,I really appreciate Just promise me bazaka kyaleni ba, kai kadai ne kake fahimta na ......I don't want to lose u too I promise siyama ,just chill ,kinga tashi ma mu tafi game resort let's forget about everything that hurts _let's have fun Murmushi ta sake tace cool,good idea Nan suka Shiga karada gari, Inda zafar yayi iya kokarinsa wajen tabbatar da siyama has a blast ranar An kammala komai ,kowa ya shirya an fiito Duk nasihar da zaa musu an kammala, Faryal data ki fitowa a dakinta in banda kuka ba abunda take..... Yau ne asalin takejin zafin rabuwa da su,ga kuma tsananin abunda takeji akan kamil Da kyar sanda abba ya sa baki kafin ta sagaita kukan nata aka nufi airport Maganan da sukayi da zafar ne ke dawowa cikin kwakwl warta,...wani haushin kanta takeji domin tunda zafar ya sanar da ita asalin labarin abunda yafaru tsakanin kamil da siyama takejin bata masa adalci ba Musamman ma kwana biyun nan da yake binta don su sasanta ba abunda bata mishi ba na bacin rai, Zaune yake a waiting area shida abba ,suna magana gaba daya idonsa ya sauya kala alamar maganan da sukeyi da abban ya taba shi sosai.....rungu mesa abban yayi yana Dada masa nasiha ayayin da kamil ya fara zubda hawaye sosai domin kuwa har cikin ransa yakejin matukar kauna da son Abbah na ratsashi Tamkar da da mahaifi in kaga yanayinsu Jin announcement da aka farayi ma passengers yasa suka mike da kyar aka raba haj mariya da zafar Faryal kam ba a magana,,,,don idanunta sunyi ja had sungaji sai jiri ma dake debarta ahankali Gashi ko magana bai mata ba ballantana ta bashi hakuri kamr yadda tayi niya Nan suka wuce su biyu zuwa seat dinsu domin kuwa a Dubai zasu sauka daga nan kowa ya wuce Kasan da zaiyi nash:
.
Bayan kwana uku da isarsu makaranta nan abba ya kira kowannensu.. Kanaji na kaamil,banda yawan kira gida saboda na lura in kuka sa maganan gida aranku bazakuyi karatu ba Zan aika ana zuwa duba ku,every after session saboda tsarina sai kun kammala komai kafin Ku dawo Toh ABBAH ,hakan ma yayi Allah ya kara daukaka ,insha Allahu zamuyi duk yadda kace Yawwa kamil Allah ya maka albarka Ranar tana zaune a dakinta,tana tunanin yayun nata da murmushin karfn hali a fuskanta,din kuwa jitake kamar an tsame wani bangaren rayuwarta ne da suka bar gidan Kwanciya tayi da baya,tana tuna fuskar kamil last ganin data masa a airport..... Mikewa tayi tasa hannu drawer ta zata dauki writing pad dinta Wani karamin envelope ya fado kasa Ganin rubutun ya sa ta Sauri tasa hannu ta dauka Budewa tayi, tafara karantawa,To my angel,am sorry! It Aches alots to know that I'm the reason you're upset this long, kiyi hakuri faryal,,,just want to let you know that your bro loves you much and am definitely missing you now and very second of my life....take care.... kaamil... Murmushi ta sake tareda hawaye,mikewa tayi ta rungome letter tana dariya,,,, Farinciki takeji,haka kawae na ziyartan zuciyan ta..... Bayan shekaru biyu, da wata shida faryal ana kokarin cika shekara 16_duk alaman girma ya fara bayyana ajikin natA tundaga kirjinta,round hips da curvy figure da ya fito sosai,sai kara kyw takeyi Anfara dawowa yan mata Duk lokacin nan zafar ne kawae ya kira gida,haj mariya kuma ko ta je ma bata biye wa takan kamil....haka shima kamil abba kawae yake kira su gaisa jifa jifa don' ko ya kirata batason dagawa Tun faryal tana fushi harta dena.... shima haka ya danne duk abunda yakeji aransa badon komai ba don' ya cika ma abba alkawrin da ya masa akan zaiyi karatu da kyw Khalid ne a falour yafi hour 3 yana jira, Mummy nifa nagaji ne,ace shi kullum yana bin mutum kamar wani maye Ke...bani son iyeyi tashi ki wuce kisameshi Inyaso kya gaya masa da bakin ki,marar hankali idonku ya Riga ya rufe bakusan abunda ya dace da Ku ba Tashi tayi Badon ranta ya so ba ta zura dogon riganta ta fito Haba baby,meyasa ke bazaki canza halikinki bane? Kullum sai na jira ki haba faryal Yaci ace na wuce wannan class din awajenki Wani harara ta watsa masa,kaga mallam nifa banazo bane kamin wani complain wannan ai kai ka sa kanka I came to ask you to please leave ni nagaji zanyi bacci What? Faryal lallai ma ,nagama bata lokaci abunda zakice min kenan Tsaki taja bata tanka masA ba OK,shikenan gobe zanzo akwai Inda zamuje so get ready.. Don na tambayi mummy ta kuma amince Wani kasalallaen dariya tayi,Khalid kenan Toh wallhy ba enda zanje kaima kasani ....iska ne kawae zata wahalar da me kayan kara Dan tabe baki yayi yace whateva, Nikam sai da safe Allah ya tura keya tafada ta mike ta nufi sama Bin bayanta da kallo yake ,shi duk abunda tamasa ma jiyayi ya ya dauke masa a ransa kallon siffar jikinta ya keyi har ta lume,.. .mumushi yayi yanacewa dole ki zama tawa faryal weda u like it or not ni zan fara saninki....and u will be mine forever
.
Karfe 9.30pm na dare Abinci yabiya siya a wani choklate candyfood restaurant a Germany, nan ya zauna jira amasa packaging.. ..ganin yadda hankalin mutane ya koma kan news yasa shima juyawa ya kalla Cikin harshen turanci wani yace,I've heard of this clan they are all over the world, Inda na gefensa ma kara dacewa ,they think they are too powerful buh thank goodness thy are now uncovered by the German CIA, Kara sa hankali kamil yayi,innalillhi yake maimaitawa aransa saboda abunda yagani ya tuna masa lokacin da aka kashe iyayensa ... Excuse me sir your package_baturiyar tafada tana mika masa ledarsa.. Bayan ya koma gida ne,ya zauna yana tunanin abu Wow,could it be wayanda suka kashe iyaye na ma yan clan din ne? Ance sukanyi kudi marar adadi daga karshe, definitely suna nan ana durza duniya dasu kenan Nan ya mike ya jawo tab dinsa,Shiga fannin bincike yayi na criminal investigation dayake ya kwarance aharkan computer bai sha wahala samin access ba nan ya typing ,the monkey clan kamar yadda yagani a news.... Nan yafara cin karo da sunaye kala kala na sauran kungiyoyi,kamar su scorpion kings,da lizardos, Da sauri ya hau kan monkey clans,20secnd alert yake dashi idan bai fita a shafin ba ...jamian tsaro zasu gano yayi hacking din su wanda hakan babban laifi ne a kasa Zuciyarsa fal da tsoro amma haka kaamil ya danna start button baiyi wata wata ba yayai downloading shafin da ya shiga Nan ya sauka ya kashe computer,zarewa yayi daga scanner ya Daura shi akan photocopy machine Mintuna 5 saigashi paper ya fito da zanen biri a gefen kirjin baturen Zare ido waje kaamil yayi zufa na keto masa hannayensa na bari Take wani zazzafan hawaye yafara zubo masa a kuncinsa Mummah ..........ya furta ,yana ganin hoton yadda abun yafaru kafin zuwan su alhaji abdullh wajen Waiwaye Rapheal run . Inada sauran ikon rufe idanunsu akanka Bazasu ganka ba maman sa tafada tana turesa gefe no mummah yafada cikin kuka, Damke shi tayi,my son zasu kashe ka fa,ka gudu anan zan tseretar da kai, no yasake cewa yana damke ta Raphael kanaso kaga ana wulakani agaban ka ne kamar yadda ake ma wayancan? Ta nuna sauran passengers mata da ake ta faman raping dinsu a filin Allah an ware kafafun su tsirara, Mummah bakin iya magic ba ? Ki mana tare nida ke da papa mu bace kafin suzo Amma bazan tafi nabarku anan ba yafada cikin kuka Raphael am weak now,banida isashen lokacin da zan tseratar da mu duka uku Amma kai zan iya,ka taimakeni ka rayu my son U don't deserve this Karkada mata kai yayai alaman a'ah Mummah I can't live without both of you Rungomosa duka iyayen sukayi ,raphael baban sa ya kira yana kallon idanunsa....kayi hakuri mu tsira tar dakai please my son Shut up ....sukaji an daka musu tsawa,wani sumbato da incantation maman Raphael takeyi irin na matsafar indiya, Da Sauri ta mike ta Daura ma raphael wani bakin dan kwali a hannunsa, a tsorace don' an hanasu kusantar juna dama Ke ,taji an damko dogon gashin ta Cike da tsoro take kallon matan motan su a jere da aka gama raping dinsu zaa harbe su Finciko ta yayi ganin Barin datakeyi don' tsoro Nan ogan su yabada hannu acire mata kaya itama,.... Sautin kukan baban raphael sukaji da karfi Shima nan aka bita kansa Kai,taso nan shima aka daga shi, Wani mugun kallo yamasa yace matarka CE wannan Ya nuna maman raphael dake tsaye haihuwar uwarta, Cikin matsanancin kuka ya amsa da eh Dariya gurin ya dauka da shi ,sukayi wani kara dukansu Gunner gama da shi, Ihu raphael yasaka ya zo ya rungeme mahaifinsa da ba abunda yakeyi sai kuka,shima rapahel din yana nemar zaucewa yana cewa papa,papa,.... Ku tsaya ,babban barawon yace, Ku daure mun su a zaune waje daya....zasu Sha kallo yafada yana kallon su cikin rashin imani Haka suna kallo kowa acikin su shidan ya zo ya hau kan mahaifiyar raphael,ya yi masha'arsa_gunner ne mutum na karshe dayayi raping dinta Papa da ya Riga ya Shiga shock idonsa kafewa yayai a zaune ,daga kanta aka fara harbe matan da suka farmasu a Daren, daga karshe aka ba gunner ixinin harbe mahaifin raphael Duk wannan a idon raphael ya faru......
.
Wanda hawaye sun kage a fuskarsa zuciyarsa ta bushe sai ido kawae yake cirewa Wani wawan dariya sukayi tareda karan da suka sabayi Me za'ayi dashi ogah,gunner yafada har yana bari Kabarshi kana ganin zai rayu ne?,mun Riga mun kashe shi.....bayida amfani a duniya,,,,zai mutu da tunanin mu.... Suka sake sake wani ihun jin dadi da nishadi Ana cikin haka saiga motar su alhaji abdullahi da Musa driver..... Sosai idanunsa suka sauya kamar wutar garwashi,sulalewa yayi kan gadonsa yana tsananta kukan Gaba daya sai yaji an tono masa ciwon dake ruhinsa da ya binne sa tun a asibiti Bai hankara ba agogo ya duba yaga karfe 2.56pm na dare ne Nan ya mike ya dauro alwala domin yayi sallar tahajjud.....kamr yadda ya saba
.
Da safe ringing waya ne ya tada shi, Video call ne Inda sunan xafar ya nuna kan screen Wani murmushi yA sake kafin ya danna answer button Allah ya kiyaye mutum daga cewa Barin siyo abinci sai shiru ko Hey zafar yafada a sanyaye,ba haka bane I'm just....sai kuma yayi shiru bai karasa ba Kamill lpyanka kuwa? Are you sick or what No,no yafada kamar marar gaskiya, Can kuma sai yace,kayi magana da faryal? Hmm nidai banyarda bakomai ba kamill...nasan baka so kayi magana ne kawae if not meyasa idonka suka haura kamar wanda yayi kuka.? Karatu nayi ,overnight... haba zafar yaushe kadawo cId ne kam.. Ina tambayarka ma bazaka amsa ni ba Toh naji,shes fine Amma yaci ace kuna biyana fa ban dawo muku dan aika ba Itama kullum sai ta tambayeni kai,although bance mata muna waya sosai ba Yarinya kamar mayya Tohh yA isa ni bance ka zaga min kanwa ba Kyal kylewa da dariya zafar yayi,da Allah min shiru kamil I know d secret. nasani fa.....kuna nan kuna kona kanku da soyayya dai Ya sake fashewa da dariya Tsumewa kamil yayi kafin zafar ya dena tsokanar sa akan faryal Nan suka danyi hirar su kafin suka yi sallama Bathroom ya shiga ya wanke jikinsa fes..ya yi shirinsa ya nufi makaranta Duk iya kokarin kauce tunanin abunda yafaru jiya dashi dayake,still abubuwan suna damunsa jifa jifa sai yanajin wani zazzafan bakin ciki na rufe masa zuciya Da kayr Hajiya mariya ta sa ta a gaba,ta Shiga motar da Khalid ya aiko dashi akan a dauketa Mummy don rainin hankali ya zaaayi shi bazai zi dakansa ba Ke kifice kar na saba miki Dazun nan ya kirani yace min zaije tarban mahaifinsa ne a airport Duk wani juye jyen da faryal tayi haka haj mariya taki fir sanda ta gaji ta fita ta bi driven Khalid Ba su tsaya ko ena ba sai wani hadden hotel amma private CE, Very important personalities ne kawae ke Shiga wajen,domin su kawai akayi Tabe baki kawae tayi ,tace a ranta ni CE zan Shiga nan wajen.. Yo ko abba ma sau daya ya taba meeting anan don' ance wajen na manya manayan kusosi ne Madamme we're here driver yafada So what,just call him..ni ba shiga zanyi ba Bata gama rufe baki ba ganinsa tayi ya nufota duk gaba daya hankalinsa nakan Surar jikin.....golden material lace ta dinka fitted gown long sleeve,tayi rolling da brown veil,da jakar lv mai hade da takalminsa Ko enan ta a rufe yake amma still kyawunta a bayyane yake karaara Wni shuumin murmushi yayi yace my baby, u killed it kin hadu yakamata na biya wannan wanka Look Khalid bana son iskanci, Shhhhhh baby sure driving me crazy in kika yi magana Dan kara masowa yayi kusa sannan yace...bakisan muryanki na romancing dina bako Wani dogon tsaki taja ta matsa daga wajen Hey kawo min cheque book ya Fada yana mata wani irin kallo Kudi ya rubutu kimanin million 20 ya mika mata Baby manage this. Hmm Khalid me ka dauke ni ne wai... Babe.....just shut up Khalid,ta dakatar da shi Cemaka akayi min rasa da zaka rainamin hankali da wani cheque din ka Daidaita tsayuwrsa yayi yace ok? In cash kike so I can double the amount nabaki., kinsan fa money wiil Neva be a problem U need it girl don't be shy Khalid banson iskanci da rainin wayo,wallhy Nafi karfin ka ma ballantana abun hannunka Ke faryal watch it, waya Fada miki don' inasonki bazan iya tarbiyantar dake ba Ki Bini ahankali fa Don' ko ubanki Nafi karfnsa ballanta ke kashinsa... A fusace ta juya zata fice tabar wajen Ido kawae yayi ma wasu gardawa nan suka taro ta mugun kallon suke binta da shi wanda yasata juyawa ba shiri suka ja suka kulle kofar gidan A tsorace ta koma badon son ranta ba ta Shiga motar tareda shi domin shirin fita Mika hannunsa yayi zai tallabo fuskarta Don't you dare lay ur filthy hands on me tabi shi da harara Wani makallalen dariya yayi yace calm down baby Look am sorry ,ki sake fuskanki kece bakiji dole na dinga koya miki respect... Shiru tayi tana kukan zuci,aranta tana cewa mummy son kudinki shike shirin zubar min da mutunci na wallhy Har aka iso bakin wani park cike da yan mata da samari wanda rabinsu kusan tsirara suke ana wanka a pool wasu suna zaune a shade da mata....
. Pool party Khalid ya hada da abokansa,musamman dan ya karyata masu cewa baya iya FitA da faryal Isowarsu wajen kowa ya juya kallonsa musamman ma abokansa Ahmed da tJ Khalid ne ya fara saukowa ya nufosu yana wani murmushi cike da kasaita Ahmed yace ena marar kunyan babyn taka take? Dariya tj yafara yi yanacewa ohh dama kana tunanin zai iya ne...yarinyar fa har yanzu jamai aji take Yakasa yin komai Enough guys lemme show you something Ai da sauri wani daga cikin yan party ya karbi mic Annoucemet.. announcement... annoucement.. Ladies and gents attention....yafada da funy voice Nan kowa hankalinsa ya dawo Kansu khalid Shikadai ya taka har zuwa kofar sit dinta ya bude motar Harara CE tafara tarbansa, fuskan nan a shake Heys baby take it easy mana,sauko muje friends are waiting Ya fara kokarin Kame hannunta....just leave me khalid zan maka rashin mutunci anan in baka kyale ni ba mahaukaci dan iska Tafada tareda Jan dogon tsaki Cije bakin sa yayi ya hade fuska yana kallonta, Look faryal,nabaki 5mints fito if not Kinga wadancan ya Nuna mata wasu karnuka masu manyan baki an daure su da chain Zansa su raka ki har zuwa wancan pool din Nan ya juya yayi tafiyarsa Bayan minti 4 saigata ta fito a hankali daga motar Tsayawa chak tayi tana maimaita innalihhi wa enna ilaihi rajiun ganin yadda aka chakudu maza da mata ba wani kayan kirki a jikinsu Sukuma kallonta kawae sukeyi sunah goshing kywun halittar ta My man,Ahmad yafada yana dafa khalid Wallhy hoto na karya kut ,this girl is damn she's on fire Murmushi khalid yakeyi Kansa na wani huruwa yana kallon ta yadda take tahowa, Karasowa kusa da ita yayi ,yace good girl Just behave ,if not kema kinsan sauran... Wani bakinciki takeji ya tokare ta Gaba daya friends dinsa suka zagaye su....anata neman shige mata Dakyar take amsawa wasu kam ma sai ya mata ido Baby tashi muje muyi rawa frdns suna su ki taka ,u know like couple dance Tasan inta CE A a zai sake kawo wani abun, Nan take tafashe da kuka Khalid nagaji,ciki na namin ciwo Ohh my gosh,meya sameki baby ko zamuje asibiti ne No,no gida zaka kaini nikam A rude ya kira driver aka sata a mota suka nufi gida Yana shiga cikin gida ta bude mota ta warware tafice tayi ciki abunta Shima cikin ya nufo Inda ya tarar da haj mariya Dan rusunawa yayi yace ena wuni mummy, Ahh khalid har kundawo ne Eh tace cikinta na ciwo ne Ayyah Allah sarki,ya baban naka ya dawo lpya ? Lpya lau mummy, Uhhm khalid ya maganan mu ne kam? Ohh mummy ai ba kida matsala gobe zaku zo warehouse office nan zanyi aiki ,ko bana nan zan bada sako Allah ya saka da alkhairi khalid,nagode dan nan Ahha bakomai mummy ai kin wuce haka Yafada yana murmushi ABBAH fa ? Har yanzu bai dawo ba Eh wallhy yana chan China almost 3month kenan ai yanzu Allah ya dawo dashi lpya,mmummy ni zan wuce To,to a gaida alhaji GaRBa Zaiji nan yafice.....yanufi gida. Kwanciya yayi, yana tunani aransa Faryal, oohhh faryal,na sameki Son? Yaji ance Wacece faryal kuma Ohh dad Kaine? Mikewa yayi ya zauna kusa da alhaj Garba Kallon dan nasa yakeyi yana jiran amsa Dan Sosa Kansa yayi yace,faryal yar gidan alhaji abdallah makaranta daya sukke da siyama Ohh OK, ya kamata nasan duk wanda kake tarayya dasu.... Toh dad,Dama enaso na shirya ma siyama graduation party ne nan sai nayi introducing dinta To my son, wannan ba matsala But ya maganan makarantar ka,kaki tafiya waje I don't know why Wannan kasar taku ba wani kwakwwaran educational standard Dad just calm down,zanyi masters ai a Germany in na kammala Just want to take care of some things Oryt toh shikenan,gudnite son yafada yana mikewa .