Batayi wani barcin
kirki ba saboda yanda ta k'agara gari ya waye, ga uban kukan da tasha da safe
duk idanunta sun kunbura. Gari na gama haske ta shirya wurin 11 tace ma Momie
taa tafi gidan Aunty Zainab, da yake tasan matsalanta da damuwanta kuma bata da
wani abokin shawara kamar Aunty Zainab ɗin
shiyasa momie bata hanata taje ta kwantar mata da hankali ba.
Napep ta tara ya
kaita gidan Aunty Zainab, tana sauka daga napep ɗin yana fitowa da motarshi daga gidan, ta juyar da
kanta gefe kamar bata ganshi ba, yayo kanta da mota kuwa har ya kusan take mata
k'afa sannan ya fito daga motar.
Yana nunata da ɗan yatsa yace "ina fatan
kinsan abinda ke faruwa, kuma baki amince musu ba" sai data gatsina sannan
tace "kaima kasani ai bazan taɓa
amince da auran ka ba"
"Yaa miki
kyau, don wallahi aka aura min ke gutsun-gutsun ina iya miki in jefar dake, don
ko kaɗan baki cikin kalar matan da
nake so"
Tsoki kawai
taja ta juya ta tafi don batason tsayawa magana dashi ma, wata tsanar shi ce ke
k'ara zo mata ta shige gidan Aunty Zainab kawai.
Tun daga ranar kullum cikin damuwa suke, babu wanda bai
kwanta rashin lafiya a cikinsu ba, k'iyayya sosai suke nuna ma junansu, anma
iyayensu sukai watsi dasu sai dai hidimar biki kawai suke.
Duk yanda suka so
a fasa auren sai da aka ɗaura shi su
duka babu mai so, a tunaninsu iyayen idan akayi auren daga baya zasu warware ne
suci gaba da son junansu, basu sanda babban kuskure ne suka tafka ba (inji rash
kardam).
A gurguje dai
Mu koma labari....
Ci gaban labari
A hankali majeed
Yace "miye mafita? Nifa tsakanina da Allah bazan iya zama dake a matsayin
mata ba" tace "nima haka wallahi, kuma indai zamu zauna a inuwa ɗaya sai munyi faɗa" yace "hakane ya
zama dole musan abunyi" tace "tohh me zamuyi?"
Yace "mu rabu
kawai kowa yayi sabgarshi, tunda kowa ɓangarenshi
daban" ta zaro ido "idan fa suka gano?" yace "tohh waye zai
faɗa musu? Kinga saima in samar
miki admission kici gaba da makarantarki" tace "hakane tohh
sakeni"
Ba wani tunani ko
damuwa a fuskarshi Yace "na sakeki saki ɗaya"
itama ba da wani abu a ranta ba tace "saki ɗaya ai ana komawa" kafin ta rufe "baki
yace "na sakeki saki biyu" tace "ai wallahi saki biyunma ana
komawa, ka cikashe kawai" Yace "na sakeki saki uku.
Wani ihun daɗi ta saki saboda tsananin
farin ciki, ta tashi tana tsallen murna, harta tafi ta dawo.
"Anma babu
ruwan kowa da harkar kowa? Babu aurenka a kaina, babu faɗa a tsakaninmu, ko nuna iko da shisshigi" yaja
tsoki yana juyar da fuska
"ke duk
wannan ya dama, salon kuma shegen surutunki ya kai ki faɗa ma wani"
"Anma haka
zamu zauna ba tare da kowa ya sani ba?
"nafa gaji
da ganinki wurinnan malama, babu abinda ke tsakanina dake, ki ɓacemun da gani"
Kamar ta maida mishi da bak'a, ta tuna idan tayi hakan faɗa ne zasu ci gaba, ta taɓe baki kawai ta shige ɗakinta, cikin ɗokin ta kira ibraheem ta faɗa mar.
Kiranshi ta dinga
yi anma tak'i shiga har ranta ya soma ɓaci
don yanda ta k'agara ta faɗa mishi
tasan sai yaa fita murna, cikin haka sai ga kiran hafsatul kiram babbar
Aminiyarta kenan.
"Ran Amarya ya
daɗe tare dana angonta"
"wacece
Amarya? Yanzu duk k'wak'warki dai bazaki kirani da wannan sunan ba" inji
majeeda.
Bayan hafsatul
kiram tayi dariya tace "Tohh ina angon naki? Na kasa hak'ura ne na kira
ki, duk da nasan kunanan tare yana jinya" ta faɗa cikin tsokana don tasan zata k'ular da majeeda.
"banson
iskanci fa hafsa, ina auren yake da har zai samu zuwa kusa dani ma?"
"saman kanki
mana, da aka ɗaura miki jiya".
"tohh
wallahi na saukeshi yanzunnan, karma ki ɓatan
rai ina cikin farin ciki?"
"kamarya
majeeda?" ta faɗa da
mamaki"
Da yake majeeda ta yarda da hafsatul kiram sosai, kuma tasan
duk rintsi bazata taɓa faɗama wani sirrinta ba, kuma tana
cikin son ta faɗa ma wani,
nan take ta kwashe komai ta faɗa
mata.
Shiru tayi kamar
wacce tayi suman zaune sai da majeeda tace "ko kin kashe wayar ne?"
"kin kashemin
bakin magana dai? Yanzu auren naku kuka kashe a washe garin amarcinki? Kuma
zaku zauna a gida ɗaya? Haba
majeeda kamar dai....."
"kinga
rik'e mamakinki da duk maganganunki, da kuma sirrina, kinsan don na yarda dake
ne na faɗa miki ko? Babu wani abin dana
sanin insha Allah"
"Allah ya
yarda, anma duk kin sakemin jiki"
"tohh a warware
lafiya, ki gaishe da Ya umar" bata jira me zata ce ba ta kashe wayar.
Layin ibraheem taci
gaba da neman, sai sintiri take a tsakar ɗakinta,
can taji taa fara ringing, ta samu kujera ta zauna tana jiran ya ɗaga anma har ta katse shiru.
Sai da ta mishi
kira biyu ana ukun ne ya ɗaga da alama
barci ya tashi.
"na kwanta
barci da tunaninki, banyi mafarkin komai ba bayanki, gashi na farka da
zazzak'ar muryarki, plz in fara jin sautin lallausan murmushin masoyiyah
ta" sai da ta mishi murmushin sabo da yanda kalamanshi suka mata daɗi tace, "ba murmushi na
kaɗai zaka farka dashi ba, harda
Albishir ɗin da zaiyi maka daɗi sosai"
"faɗamin da sauri masoyiyah, tunda
kafin ki faɗa ga tukuicinki" ya sakar
mata daddaɗan kiss a kunne
Ta rufe ido ta buɗe
cikin nishaɗi, "Yaimin daɗi sosae masoyi, karfa ka
sakani mantawa da albishir ɗin"
"sai in
k'ara miki wanda zai saka ki tuna"
"banma manta
bafa, anma duk da haka naa biyoka bashi, yanzu miye yayi mana katanga da zama
mallakin juna?"
"Auren ki da
majeed mana" inji ibraheem
"tohh k'ara
kwantar da hankalinka, don indai aurena ne yanzu....."
Maganar ta mak'ale mata saboda ganinshi tsaye a k'ofar
falonta, yana wurgo mata wani mugun kallo
Shirun da Ibraheem
yaji tayi ya saka ya dinga "hello, masoyiyah, kina jina?"
"ina jinka
masoyi zan kiraka yanzu," sannan ta katse kiran tana k'ok'arin dai dai ta
nutsuwarta.
Ta kalli majeed
tana mayar mishi da irin kallon da yake mata "Meya shigo dakai ɓangarena? Ka mantane sharaɗinmu na babu wanda zai shiga
harkar wani? Kuma bazaka zo inda nake ba"
"ke har kina
da bakin magana? Baki manta da sharaɗinmu
ba meyasa kike k'ok'arin faɗa mishi
sirrinmu?"
"ni ban
faɗa mishi ba ko kaaji naa faɗa?"
"kina shirin
faɗa dai, wannan ba k'aramar
magana bace da idan kin faɗa ma wani yaɗuwarta bazai kawo matsala ba,
har yaushe kike tare da Ibraheem da kika yarda dashi har zaki faɗa mishi wannan sirrin namu? Ke
kin kasa rik'e sirrinki ta yaya kike tunanin wani zai rik'e miki? Wallahi karki
kuskura ki faɗa ma wani wannan maganar"
Jikinta yaa riga da
yaayi sanyi, taama kasa maida mishi, ya juya ya bar ɗakin, taja tsoki "daman gulmace da sa ido ya
shigo dakai kenan" ta harari k'ofan tana murguɗa baki kamar yana ganinta, sannan ta tashi ta shige ɗakinta.
Yinin ranar bak'i
ta dingayi masu zuwa ganin gidan Amarya, kowah yazo sai ya zagaya gidan ana
lellek'a ɗakunanta, ba k'aramin haɗuwa da tsaruwa gidan yayi ba,
ga dukiyar da iyayenta suka zuba mata a ciki.
Ba ita ta zauna ba
sai 9 na dare bak'inta suka gama tafiya, duk taa gaji ga yunwa bata samu taa
girka komai ba, baba haule dai taa koma gida,
Kwanciyah tayi ta
jawo wayarta miss calls ɗin Ibraheem
ne babu iyaka, itama ta kirashi bai ɗaga
ba, ga yunwar dake yatsina mata y'an hanji, mik'ewa tayi kawai ta nufi kitchen
ta ɗaura girki, da yake an haɗa mata komi.
Fried cous-cous ta
dafa dai-dai cikinta, sai k'amshi ne ke tashi, tananan tsaye harya gama dahuwa
ta sauke ta jawo plate zata zuba kenan ta juyo wayarta na ringing a ɗaki, ta ajiye da sauri ta tafi
ta ɗauka wayar.
Ibraheem ne, ta
zauna gefen gado sannan da ɗaga kiran.
"Da fatan
ma'abociyar kyakkyawan murmushin nan tana cikin nishaɗi"
"sosai tunda
ina tare da muryan masoyinah"
"kawai ɗazun ina cikin ɗokin jin albishir daga gareki,
saiki yankemin waya, halan angonki ne ya kiraki?"
"shiya shigo dai, anma ai bai isa don
ina waya dakai in katse saboda shi ba"
"Hmm, kin
manta da mijinki ne? Kina kulawa dai don baniso muna shiga hak'k'ik aure da
yawa" sai can ya tuna kuma.
"Yauwah
aurenki yanzu ma... me kike cewa?" sai da ta ɗan daburce duk taa rasa me zata ce sannan tace
"yanzu ne yake k'ara damuna masoyi, anya bazamu gudu muyi aurenmu?"
"Aure akan
aure kenan? Nifa banda matsala da iyayena Masoyiyah jiran fitowarki kawai nake,
basai mun gudu ba kinji tawan"
"tohh"
kawai tace mishi a zuciyarta tunani take anya bazata faɗa mishi ba? Kuma sai taji tsoran kashedin da Majeed
yayi mata haka kawai ta fasa faɗa
mishi.
Majeed yana ɗaki
shima babu inda yaje, sallah ce kawai take fiddashi, sai juyi yake akan
gadonshi saboda yunwar da yakeji tunda rana, daya juya sai yayi tsaki
"Yanzu mutum ya tafi restaurant yana haɗuwa
da idon sani akama yi mishi surutun ya fara fita cin abinci"
Gani yayi zaman
bazai mishi ba, ya tafi kitchen ya duba ko zai samu abinci.
Cikin sa'a kuwa ya
hango tukunya saman cooker gas, ita ya fara buɗawa, abinci ya gani kuwa da zafinshi k'amshi sai
tashi yake, ya jawo plate ɗin daya gani
a wurin ya juyeshi tass sannan ya fito falo ya zauna ya fara ci.
Sai da ta gama wayanta da ibraheem daman yunwa duk taa
addabeta, ta fito ta wuce shi a falo ta nufi kitchen ko kallon inda yake batai
ba, shima ko sanin taa wuce baiyi ba.
Ta duba inda ta ajiye plate babu, kodai bata ɗauko ba? Ta janyo wani plate ɗin dai ta taho zuba abinci,
tana buɗa tukunya wayam babu komi,
fiddo idanu tayi waje cikin mamaki ta ɗauka
tukunyar tana girgizawa kodai bata gani dai dai bane, anma wayam babu komai.
Toh waye zai shigo
har gidanta ya kwashe mata girki? Kodai aljanu ne, can ta tuna fa ay ba ita kaɗai bane a cikin gidan, toh shi
kuma mezai dameshi da girkinta? Tunani dai ta dinga yi taga bazai mata ba, ta
fito daga kitchen ɗin can ta
hango shi ya saka plate a gaba yana kwasar girki.
Cikin jin haushi
tace, "Anma dai in ba'a kawoni da ɗaki
a gara ba an kawo ni da cous-cous ko?"
Baiko ɗago ya kalleta ba Yace
"Anma a gidana kike zaune, indai zaki zaunamin a ɗaki, dole ne kimin girki, bayan wannan babu wani
abu" ba tace mishi komi ba ta koma kitchen ɗin don yanzu batason magana tayi nisa tsakaninsu
yanzu zasu fara faɗa.
Bayan wata biyu...
Majeeda ce sanye
cikin doguwar rigar material, ta ɗaure
kanta da ɗan kwalin, ta jawo Abayarta
har k'asa ta saka, sannan ta ɗaura nik'ab
a fuskarta, ta janyo hand bag ɗinta
sannan ta fito waje. Driver nanan yana jiranta, ta buɗe sit ɗin
baya ta zauna yaja motan sai ALQALAM UNIVERSITY dake cikin garin katsina.
Kullum shigarta
kenan tunda ta fara shiga makarantar, kamar wata matar aure shiya saka har
yanzu batayi koda k'awa babu ruwanta da kowah.
Sai marece sosae
ta koma gidan, bata lura da motanshi ba ta saka kanta cikin falon, maganganu ta
fara jiyowa.
"haba Aisha,
ba nace karki zomin gida ba? Karki manta fa akwai banbanci tsakanin gidanmu da
gidana".
"akwai
banbanci, anma kasan ko inane zan iya zuwa don in ganka, tunda kai ba son zuwa
gidanmu kake ba"
"naji, anma
kincemin inzo banzo ba? Ki k'ara hak'uri mana lokaci kaɗan ya rage a fara maganar aurenmu"
"kullum haka
kake cewa, ni dai tunda nazo ka bari ko gaisawa muyi"
Wani abu ne ya tsaya ma majeeda har wuya, kamar ta kama
majeeda ta shak'e takeji, a ciki-ciki tayi sallama ta shiga ɗakin duk suka juyo suna kallonta, ta k'urama majeed
ido kawai, taa daɗe bata
ganshi ba, don tunda ya fara zuwa aiki ya daina zaman gida, girki ma idan taayi
a kitchen take bar mishi.
taa rigashi ɗauke idanunta, ba tare da tace
komi ba ta shige ɗakinta.
Ibraheem ya faɗo mata a rai, yanzu yaa daina
kiranta, ko kiranshi tayi sai yaga daman ɗagawa,
koya ɗaukama bazasu wani daɗe ba zai kashe wayan, shiyasa
itama ta daina damunshi, yanzu hankalinta akan karatun kawai ta maidashi.
Cikin ɗakinta haushin Aisha ne kawai
ya cika mata ciki, daganan tana jiyo maganganunsu tak'i tashi ta tafi duk da
maganar da majeed ke mata, tashi tayi ta tafi falon bayan ta cire hijabin
jikinta, ta gyara ɗaurin
kwallabin sannan ta fito.
Shiru suka k'arayi
suna kallonta, ita kam kamar ma batasan dasu ba, ta k'arasa gaban kallo ta
kunna, ta rik'o remote ɗin ta zauna
kallo.
K'asa-k'asa
Aisha taci gaba da mishi magana duk hankalinshi na kan majeeda, ta k'ure k'arar
ma yanda bazasu ji ba, duk a takure yake anma Aisha taa kasa ganewa, kawai ya
juya zai tafi ɗakinshi
itama ta mik'e zata bishi.
Majeeda ce tasha gabanta,
"kinfa
fara wuce iyaka malama, don tsabar rashin kunya ki biyo mijina har gidana,
kinga ban tanka ba shine zaki bishi har ɗaki,
ubanme zaki yo a ciki?"
"Akan mijin da
bai damu dake ba baya sonki kike tada jijiyoyin wuya? Abinda ranki ya baki shi
zamu yo"
"k'arya kike
wallahi ki shigo har gidana kina faɗamin
magana, banza mai k'wak'war namiji har gidanshi, ai naga mugun son da yake miki
ne ya saka sai dai ke ki biyoshi"
"laaah, ni
kike faɗa ma magana? Kana jinta fa
majeed"
Duk suka maida kallonsu ga majeed ɗin, "Da bakizo gidanta ba taa faɗa miki? Kinga muje in maida ke
gida"
Majeeda tsayawa
tayi tana kallonsu har suka fice, lallaima yaa fifita wannan banzar a kaina
kenan, har saida ta jiyo ta mata gwalo, haushi kamar ta fasa ihu.
Lallai don yaga
yanzu babu aurenshi a kaina ne harda shigomin da wata a gida, wallahi bazan
yarda ba nima sai na rama.
Bai wani daɗe ba ya dawo, anan ya wuce ta
inda ya barta, ya wuceta inda take tsaye yana tafiya da kakkausar murya cikin
gargaɗi yace, "babu ruwanki da
kowacece zatazo wurina, babu ruwan wani da harkar wani" ya wuceta sannan
ya k'arasa maganar.
Kwana biyu tayi
tana tunanin yanda zata rama abunda Majeed ya mata anma taa gaza samun mafita,
gashi kullum sai ya raba dare kafin ya shigo gidan, tunda safe kuma yake fita,
ita yaa maida ita er gadin gida duk da baiyi mata shamaki da fita ba.
Yauma da marece
sosai ta dawo daga lecture, suna hanya drivern ta ya ɗaukota, da yake hanyar gidansu majeed ne, hakanan
taji tanaso taje gaishe dasu, ta cema drivern ya biya da ita.
Ya ajjeta ta fito
har zata tafi kuma ta dawo "malam balah zaka iya tafiya, zan ɗan daɗe ne" yace, "tohh hajia" sannan ta
shiga gidan da sallamarta.
Zahra taci karo
da ita, aikam ta buga uban tsalle da gudu ta taho rungumeta "Oyoyo Matar
Yayanmu"
"Aifa sis
kamar a bakinki aka raɗa wannan
suna, ina umma?"
"tana ciki ki
shiga bari inzo"
"tohm naa
bari".
Ta yaye labulen ɗakin
Umma ta shiga haɗe da
sallama, ta ɗago tana amsawa tana ganin
Majeeda ce ta k'ara faɗaɗa fara'arta tana mata sannu da
zuwa, sai yanzu ne ma wata kunya ta k'ara nannaɗeta, ta duk'a har k'asa tana gaida Umma ta amsa
mata.
"Ina majeed
ɗin ko ba tare kuke ba?"
"Daga
makaranta ne yace Driver ya kawoni, anma zaizo ɗaukana Umma"
"Tohh Allah
kawoshi lafiya, kuna dai zaune lafiya ko?"
"Alhmdlh
Umma"
"ki faɗamin gaskia dai naaga duk kin
rame" wai taa rame fa, tace a ranta, tana tuna randa taje gida momie cewa
ta dinga yi taayi k'iba taayi haske, alamar dai tana mata zargin ciki ne da
ita, da yake momie ce sai ta ce mata "momie ni kece uwah ta farko da akama
ɗiyarta auren dole kuma tazo
ganin gida a ce mata tayi k'iba" momie tace "watau ma auren dole aka
miki ko? Kina nufin har yanzu baku zaman lafiya da mijin naki?" tace ma
momie, "ba haka nake nufi ba momie".
Umma ce ta katse
mata tunani "Yadai kikai shiru Majeeda? Indai da matsala ki faɗamun in tsawata mishi"
"ba wani
matsala Umma, kawai kwana biyu banji daɗi
bane" ta k'ak'alo k'arya.
"tohh Allah ya
k'ara lafiya kundai je asibiti ko?"
"Ai naaji
sauk'i Umma"
Zahra ce ta shigo
ta janye ta suka koma can ɗakinta da
fira, itama tsokanarta take kodai sun samu rabo,
"nikam sis
kamar Abinda kowa ke jira kenan, duka yaushe aka gama hidimar bikin ko hutawa
bamu yi ba?"
"Abinda
kowa ke jira mana kenan, in hutawa ne kam ai kinyi, anma burinsu Abba kenan
kullum ganin en jikokinsu" sai da
gabanta ya faɗi, tayi shiru tama rasa abin
cewa, tohh ta inama zata samu cikin tunda ba auren garesu ba?.
Haka ta yini cikin
gidan duk tayi sukuku kuma, har bayan isha'i taa rasa yanda zata tafi kuma
gashi tace ma Umma Majeed ne zaizo su tafi, yanke shawarah tayi kawai ta kira
malam balah, shi ɗinma ta
dinga kiranshi anma wayanshi a kashe.
Wurin 9 Umma ta lek'o ɗakin
Zahra, "wai ina majeed ya tsayane?"
"Umma
inajin dai wani abunne ya rik'eshi, anma zan tafi kawai kar dare yayi
sosai"
"A'ah ya zaki
tafi ke kaɗai? Ki mishi waya dai yayi sauri
yazo ku tafi" ita kam ko number wayarshi ma bata da, yama za'ayi yazo ɗaukanta.
Har 10 tayi ta rasa
dabarar da zatayi tabar gidan Umma, su duka suna zaune a falo, gabanta sai faɗuwa yake, tun farko ma meya
sakata yin k'arya.
Sa'a tayi wayarta
ta fara ringing, tayi saurin maida wayan silent sannan tayi kamar taa ɗauka sannan ta ɗan matsa daga inda su Umma
suke ta fara magana yanda zasuji.
"hi, lafiya
lau ya aiki?" ta ɗanyi shiru
sannan tace, "A'ah ya za'ai na tafi kace na jiraka?"
"Ayyah! Tohh
a dawo lafia, sai ka dawo gidan" tun kafin ta zauna Zahra tace "Halan
ina ya tsaya?"
"wai kinji
fa gaisuwar wani baban ɗan wurin
aikinsu sukaje Mashi, anma suna hanya kuma motan a cike take, yace inje a
napep" Umma tace, "Ayyah!Allah yaji k'an musulmi, sai kiyi sauri dare
na k'arayi, tace "tohh shknan Umma"
Zahra ce ta rakata har bakin titi, sun daɗe suna tsaida abin hawa duk da mutane a ciki gashi
batason hawan mashin, dak'yar suka samu wani mai napep ta shiga sukayi bankwana
da zahra.
Har ya tada zai tafi Yace "hajia ina
za'a kaiki?" tace, "G.R.A"
"kiyi
hak'uri hajia bazanje can yanzu ba ina ɗan
sauri ne" babu yanda ta iya ta fito daga motan gashi dare ya fara nisa
10:3., ta juya ko burbuɗin Zahra
babu, ga unguwar babu mutane.
Tsayuwar ta fara
gajia da ita ta ciro wayarta tana dubawa, ba don tana da abunyi da ita ba, sai
don kawai ta rasa abinyi gashi har lokacin ba wani motan da zata hau.
Wata haɗaɗɗiyar mota ce ja, mai shegen kyau ta wuce inda take,
sai kuma akayi reverse da motar aka dawo saitin da take, kaudar da kanta tayi sannan
ta matsa gefe. Kusan mintina biyar mai motan bai fito ba kuma shi bai tafi ba
ita kamar ma batasan da wani mota a wurinba.
Buɗe motan yayi ya fito da
takunshi na k'asaita, "Masha Allah" na faɗa saboda irin kyaun dana hango a tattare dashi,
harna kusan jefar da wayata kasancewar darene ina tunanin ko Aljani ne, dai dai
inda Majeeda take ya tsaya.
"Da alama
kina jiran Abin hawa, gashi kuma dare ya fara nisa zai miki wahalan samu"
kajimin mutum ko ina ruwanshi dani
"hakane zan
samu insha Allah"
"Zai miki
wahalan samu fa, kiyi shawara da zuciyarki idan harta amince miki zan kaiki har
inda kikeso, babu daɗi
kamilalliyar mace kamarki ta tsaya a titi a cikin darennan"
Maganarshi fa
hakane, idanma ya tafi ya zata samu wanda zai kaita gida? Kuma da alamar
natsuwa a tattare dashi ta san bazai cutar da ita ba, gaba tayi wurin motar
kawai ba tace komi ba, ya buɗe mata yaci
gaba da karanto addu'ah a ranta.
Har k'ofar gidanta
ya kaita "ajjeni nanma yayi" yayi parking ta fito tana mishi godia,
murmushi kawai yayi yaja motanshi, dai dai lokacin majeed shima ya sako
motanshi kuma yaga lokacinda ta fita daga motan.
Kamar wanda ake
hankaɗawa ya shiga gidan tana
dai-dai shiga ɗakinta yasha
gabanta,
"daga gidan
ubanwa kike?" na ɗauka
"gidan ubanka zatace"😄 tunda gidansu taje,anma sai tace
"gaishe dasu Umma mana, kana da matsala da fitata ne?"
"k'arya kike
tun ɗazu Umma tacemun kin taho,
wane ɗan iskane ya maidoki?"
"kash!"
ta dafe kanta da hannu ɗaya
"kaga nama mnta ban tambaya sunanshi ba, ragemin hanya yayi, babu ruwan
wani da harkar wani" shiru yayi yana kallonta yama rasa bakin magana, tohh
meyasa ma ya tanka mata? Shi ina ruwanshi kowa ma zata kula.
Ta juya ta barshi
anan zata shige ɗakinta,
k'afarta ta zamo bata ankara ba ta taho zata faɗo da sauri ya tare ta ta faɗa a k'irjinshi ta tallabeta da hannuwanshi,
kallonshi take cikin fargaba saboda yanda ta kusa faɗuwa, sai maida numfashi take, shima kallonta yake
cikin ido, wani irin yanayi da bai taɓaji
ba ya ziyarceshi wannan kallon da suke ma juna.
K'ara matseta yayi
a k'irjinshi, tsawon lokaci suna a haka kafinta lumshe kyawawan idanunta ta buɗe, idonshi dai-dai laɓɓanta ta buɗesu a hankali tace "da zafi" yanda ya mata
rik'on, sakinta yayi yana dai-daita kanshi, sannan ya juya ya tafi yana
waiwayenta, itama kasa motsawa tayi daga inda take ta k'ura mishi ido cikin
wani yanayi harya shige ɗakinshi.
Jiki a sanyaye
ta shige ɗakinta, ta kasa mantawa da
yanayin data motsa fuskar majeed ce ke mata yawo a sanda take a k'irjinshi.
Haka Majeed ma ya
kwanta barci da tunanin abinda ya faru, daya rufe idonshi yanayin yake dawo
mishi, koda ya buɗe kuwa bazai
daina ganinshi da majeeda rungume ba, juyi kawai ya dingayi a lallausar
katifarshi yana jiran lokacin da barci zai ɗaukeshi.
Hmm niko nace kome hakan ke nufi??
Da Asuba, ciwon
mara ne ya farkar da ita, tun cikin barci ta fara juye-juye harta farka, ta
dafe cikinta ko motsi batason yi, tanason ta ɗauko
maganinta anma ta kasa tashi saboda yanda ya matsa mata.
Dak'yar ta samu
ta mik'e ta jawo jikkarta ta fara laluben maganin sai dai kwalinshi babu ko ɗaya, kamar ta fasa kuka ga
wani irin azababben ciwo, haka tana duk'ewa ta samu ta haɗa ruwan zafi a toilet taje tayi wanka anma duk da
haka kamar ana k'ara tunzuro ciwon cikin gashi ita kaɗai a ɗaki.
Dak'yar ta iya
k'arfin halin kwaso kuɗi a jikkarta
ta fito mai gadi ya siyo mata, da yake a ɗan
duk'e take tafiya rik'e da cikinta ga azabar ciwo, bata lura dashi yana shigowa
falon ba ita kuma zata fita harta kusan kai mishi karo, da sauri ta dawo da
baya, kanta a k'asa tabi gefenshi zata wuce, shima gefen da zata wuce yabi suka
kusan haɗewa a tare, kuma kowannw ya
koma ɗayan gefen, da suka kasa
wucewa dai ya saka hannuwanshi biyu saman kafaɗarta, sannan ya juyar da ita ya wuce.
Wani irin murɗawa cikinta yayi anan ta duk'e-duk'e
rik'e da cikinta, ta daɗe a haka
kafinta iya mik'ewa tana ɗagowa suka
haɗa ido da majeed, duk ta
daburce tace, "yadai?" yaɗan
saki fuskarshi "ba komi", sannan ta juya ta wuce a wahalce.
Bata iske mai
gadi ba, da alama bai gidan gashi duk taa gama jigata, haka ta lallaɓa ta koma ɗakinta, tana faɗawa
gado ta saki kukanta marar sauti ga ciwon sai k'aruwa yake, ta dinga murgina
saman gado harta sauko k'asa.
"Ga
maganin" taji ya ambata, ta ɗaga
fuskarta tana kallonshi rik'e da laida a hannu, ya ajje robar faro da cup a
kusa da ita, ta mik'a hannu ta ansa maganin, irin wanda takesha ne da pad guda
biyu, ta ɓallo guda ɗaya ya mik'a mata cup ɗin ruwa ta haɗiye
dak'yar sannan tace "na gode" ta koma ta sulale k'asa tana jiran
ciwon ya lafa, a haka barci ya kwasheta duk taa k'udundune wuri ɗaya.
Tausayi ta bashi
ganin yanda tayi kwanciyar duk taa takura, lokaci ɗaya har taayi ramar dole, sai lokacin ya tuna ko
break fast batayi ba ya bata magani, da sauri ya tafi kitchen ya ɗauko flask da kayan tea ya
ajje mata.
Tananan kwance
inda ya barta tana barci, anma da alama batajin daɗin barcin ciwon cikin ma bai gama sakinta ba sai
rumtse ido take tana rik'e ciki.
Bazai juri
ganinta a k'asa ba, ya saka hannu ya tallabota, kamar yaa ɗauka jaririya, ya dire ta saman gado, tun lokacin da
yaa ɗaukota ta farka, anma ta kasa
buɗa idonta wani irin kunyarshi
maa takeji.
Megasa Yaya majeed
zaina taɓani koya manta yanzu babu aure
tsakaninmu? tunaninta ya katse saboda yanda mararta ta k'ara juyewa, tai wani
irin k'ara batasan lokacin data k'ank'ame hannunshi da hannu ɗaya ba, ɗayan
hannunta na rik'e a cikinta har lokacin da yake yana tsugune saitinta.
Wani irin tausayi
take bashi ganin yanda takeyi, fuskarshi kamar zai tayata kukan, ya kalli
hannunta dake sak'ale a nashi, zara-zaran yatsunta masu kyau sosai da taima ado
da jan lalle, baisan sanda yaci gaba da murzasu a hankali ba yana kallon
kyakkyawar fuskarta, sai runtse ido take, ga ciwon ciki, ga wani irin yanayin
da takeji hannunta rik'e a hannun majeed.
Kallonta yaci gaba
dayi, sai yanzu ne yake k'are mata kallo, ya saka hannu ya yaye mata
yalwataccen gashin kanta mai sulɓi
daya rufe mata fuska, fara ce tas, irin farinnan mai kyau, gashin girarta
gazar-gazar mai kyau kamar an zana mata shi, gata da manyan idanu masu kyau da ɗaukar hankali, girar idonta
bak'a wulik koda a rufe suke idanunta k'ara kyau suke, da dogon hancin ta wanda
ya dace da kyakkyawar fuskarta, idanunshi ne suka sauka a kan ɗan 'karamin bakinta (pink lips), ya tuna yanda take
motsashi idan tana mishi masifa, sai yaji ta burgeshi ma idan suna faɗa kyau yake mata.
Yanzunma motsashi
ta dingashi kamar zata tashi, dimples ɗinta
na lotsawa, a hankali yakai ɗayan
hannunshi zai shafi gefen fuskarta, kamar ance ta buɗa ido, ya sauka cikin nashi da sauri ya mayar da
hannun