Hutun mako na karewa suka wuce makaranta amma gaba daya
aisha humaira hanklin ta na kan masdook tun bayan daurin auran be kuma zuwa ba
kullum in sun yi waya da baffa ko abbi ko su mama yace aiki zai zo ko da
makarantar ne amma kasan ranta tasan ya fada ne kawai karya yake yi ita ce baya
son gani kawai.
Masdook,yusuf,nas,ni'imatullah,hanif zaune a tsakar falon
masdook suna hirar bayan rabuwa
Kai ango haka ake
yi sai ka bace daga murna?
Hmm kai ne kake
ganin abun murna a cikin wannan auran
Auran alakakai.
Kai mutumina baka
da kunya da kirki muna nan kake ci ma yar'uwar mu mutunci ko
To ace ban da hadi
da ita man
Aa meye zafi?
To ai karshen cin muntunci kenan
Ni'imatullahi yace
dana san da haka dana shiga na fita da fadanci na karbi auran aisha humaira
Kallon shi kawai
masdook yayi ya kyabe fuska ya dau lemo me sanyi ya sha ya ajiye ka makara kuma
ba .
Me aibun humaira
masdook kai ko.
Tana da kyau
diri
Ido hanci zukeke
Ga gashi ga haske irin matqn nan ne masu kyan jiki da tsari
tana da fara'a in ma yarinta ce ai zata daina lokaci ne kaima fa kayi nagani
Yusuf yace amma
hanif kai dan iska ne kai kuma ka tsaya ana tanka ma zubi da tsarin matar ka ko
kayi shiru ai da ni ne da tuni na make masa baki yayi jini
Aka sa darya ban da
ogan ya sha mur yana wani nazari na daban shi kadai yasan me yake tunani se
wanda yayi shi (Allah).
Ku kuna ta ma humaira campaign inji yusif ku barshi man ai
ido ke gani shi be hango ba amma ina tabbatar muku da cewa zai dawo yana a masa
sulhu in ya fada tarkon yar mitsilar yarinyar da ya raina.
Fatan ka kenan yusuf?
Sossai ma.
To xamu gani ai inda rai da lafiya ba
Yes we shall see.
*BAYAN SHEKARA UKU*
Wasu siraran hawaye ke yawo kan kuncin kyakyawar fuska me
dauke da murmushi kullum a yau kuma hawaye ke zuba kamar bazai kare ba
Ta gefenta ta riko
hannun ta tana rarashin ta haba kawata haba ban san ki da haka ba ni kawata
jaruma ce wadda tasan jaramunta da dauke kai kin hakura har shekaru uku balle
yanzu kuma?
Hmm bazaki gane ba
so dafi ne me wuyar warkewa so in ya kama ka baya cika ka so wuya ne dashi so
nauyu gare shi a zuciya musam irin wanda nake yi *son maso wani* amira only my
Allah knows yadda nake son hamma amma na rasa mesa baya sona har bakin jini na
ya ksi haka amira da za a kini?
Me aibuna na gyara?
Me nake yi mara kyau fada min na gysra?
Ta fada tana jijjiga ta tana kuks fada min amira fada min.
Na gaji wallahi Allah
na gaji na kasa sukuni
Duk sanda na runtse idanuna shi kadai nake kallo shi kadai
nake gani a ko ina na kasa cire shi daga raina am getting mad amira zan zauce
Rungumeta tayi haba
kawata ki daina damun ksn ki insha Allah komai zai zo karshe komai yayi farko
ai zai yi karshe ki daina damun kan ki focus in ur education ki bar hamma besan
me yake loosing ba
Kiyayar tayi yawa
amura good three years ace ban sa shi a idona ba
Na sani amma ki
kara hakuri shi ne ribar zama na duniya ki kara hakuri kin ji
Kema ur tym will come
zaki ce na fada miki .
Allah sa amma zan
koya wa kaina share alamuran sa a zuciyata.
Ko kefa ki daina
kuka kawai ki min murmushin nan naki dake nunan cewa yes wannan ce *Aisha
humaira* ta
Murmushi ta mata me
kayatsrwa
Point dinta ya loma ya koma ciki sossai karamin bakin ta ya
kuma tsukewa ta share hawayen ta sannan tace so ba karya bane ill make it
yes zaki iya.
Aiki ya gama kacame masa a office bashi da hutu sam sam
Ga wani gumi da yaji
yana zubo masa har rawar jiki yake yi saboda ciwo
Drower ya bude ya
dau maganin sa yaga wayam alamun babu kenan tsaki yayi ya juya dan dauko
wayarsa da kyar ya iya dauko wayar ya danna number abokin sa nas
Hello nas
Ya akai masdook
Nas dan Allah kazo office ko da lemun tsami ne
Ni ina zan ga wani lemun tsami ?
Ban sani ba kawai i need it.
Yq kashe wayar ba tare da ya kuma jin meze ce ba
Nas dake kwance a
quters ya mike ya duduba ko da akwai a fridge din sa yaga bsbu tsaki yayi ya
dau mukuli yayi waje
Masdook ko ciwon
ciki sossai ya ksma shi ga fanka ga ac amma duk da haka gumi yake yi ya kasa
sarrafa kan sa.
Kasuwa ya je ya samu lemun tsami ya yi asibitin.
A yadda ya same shi
ba karamin kaduwa yayi ba ya yi saurin tallafo shi aa masdook jikin ne har
haka?
Ina lemun ?
Ungo ya bashi ya dan lasa a bakinsa ya kuma zuqa ya
kwankwadi ruwa ya kwanta a kan kujera.
Yayi ajiyar zuciya.
Masdook wai kana son kan ka kuwa?
Ban gane ba nas
Masdook kasan cewa halin da kake ciki ya kamata ka samu
partner a kusa.
Hararar sa yayi ya juya masa baya kar ka soma nas kasan bazan
iya kiran wannsn yarinyar ba dan ba abunda zata iya min bata kai ba kuma ba
zata kai ba.
Ok naji amma zaks iya samo wata matar ko ka aura wadda kake
so.
Ina zan samu kawai
nas na fawalawa Allah komai
To Allah kiyaye amin.
Nagode na taimakon da kayi kuma kar ka fadawa ko da yusuf ne
Ok naji ta wuce.
Amma in fadama wani abu?
Uhm kawai ya fada.
Ka yi reconsidring din dangantakar ka da aisha humaira aure
ba fa wasan yara bane kuma kana bukatar ta tunda an daura auran ka daure kayi
kokarin ganin kun zama daya kaga tana sonka kar Allah ya ksma ka da hakkin ta.
Hmm nas nagode sossai .
*makaranta*
Sun shiga ss1 yanzu a science class amira da aisha suke.
Komai ya sauya musu
domin nutsuwa taxo musu sun rage wannsn shirman na yarinta musamman ma aisha
humaira da ta kara girma.
Kullum da son shi
take kwana take tashi a ranta amma hakan besa ta daina karatu ba illa ma da ys
bata kwarin gwiwar yin karatun a ganin ta dan bata da ilimi da wayewa yasa baya
son ta shi sa take ganin idan tayi karatun zai so ta.
*****************
*a gurguje kuyi hakuri ina dan yin labsrin da sauri ne hakan
ya kasance ne saboda wasu dalilai da dama*
Tafiya take yi kamar tana tsoron taka kasa hannun ta rike da
wata iriyar jaka ta gayu rataye a tsintsiyar hannun ta
Tayi irin daurin nan
na zamani me hawa hawa ta ci ado tasa irin takalmin nan me tudu ta saka
Gefenta amira ce
wadda na dinga kallon su yadda suka yi kyau suka canja gaba daya kamar ba
jikokin da'ada ba tsabar nutsuwa.
Fadima ta riko
hannun *aisha humaira* kinga sis mutumin ki ya iso fa
Dagowa daya tayi ta
masa kallo daya ta maida kan ta kan wayarta gaban ta bugawa yake yi amma ta
basar zuwa ysnzu ta san cewa hamma masdook bazai sota ba ta koys wa kanta
kokarin share shi ita ma kila nauyin zuciyarta ya ragu.
Hamma yusuf ya
yafito ta da hannu bata gani ba fadima ta tabota hamma yusuf na magana
Tsaki tayi tana
taunar cingum kamsr a kan ta a ka fara cin cingum.
A hankali ta karasa
gurin da suke inda kamshin turaren ta ya musu sallama
Gani hamma
Ungo ya mika mata leda gashi soveniers ne kuyi amfani dashi
a gun dinnar din ku bawa mutanen ku.
Tom hamma angode
Amma kina ji ?
Eh
Ki fadawa amira ta dan koma daga ciki mana kafin anjiman ban
son ana kalle min ita
Murmushi tayi to
hamma angama a mana afuwa mun yi laifi
Ta juya kenan yace
baki gs masdook bsne?
Na gan shi ta kara gaba dan inta kara tsayawa zata kasa
daurewa.
Masdook besan inda
zai sa yanayin da ya shiga ba amma yasan cewa lallai yaji wani abu a tare
dashi.
Mutuniyar fa ta koyi halin naka
Ni ina ruwana da ita?
Kai ko kake da ruwa
Hmn kai ka jiyo
Hhh kai kam ka ksms ka rike ta ka kyaleta mana masu so su
aura
Wani kallo ya masa
yana gyara tsayuwar sa
Ni na rasa tsayuwar
me suke yi ma a waje gaba dayan su .
Ni'imatullahi dallah kora yaran can cikin gida
Wane yara?
Gasu can man
Ya kalli yan'matan yayi dariya a ransa ysce wannan masdook
da manyance yake wallahi.
Wai ya zaka hana yanmata sha'anin biki ina aka taba kora
daga harkokin biki in ba a gunka ba masdook
Hararsa yayi sannan
yace ni da ma...
Se kuma yayi shiru
Karasa mana masdook matar ka ko?
Ban ce ba kar ka kaini inda ban je ba
To ma gani dai
masdook .
Bayan magrib suka
nufi gurin kwalliya su hudu harda amaryar
Inda sun sha ado da
kwalliya se walkiya suke yi
Kayan jikin su iri
daya sun sha dinki ya kama jikin su dake fitet gwon suka sa hill da roses
Ba karamin haskawa
humaira tayi tadan dosana mayafi kan kafadar ta
Da karamar purse a
hannun tq kalar sarkarta da takakmi
Angwayen sun sha ado
suma suna jiran amaren cikin mota da aka faka guda uku .
Masdook ni'imatullahi da nas sune ke jan motar jiran su
kawai suke yi su fito su tafi hall din dan su ake jira a gurin.
Fitowar su keda
wuya masdook ya maida hankalin sa gaba
daya kan humaira gsba daya ta tafi da imanin shi amma a fuska baxaka
gane ba ya ci kunu ya sha mur ya bata rai
Bude motar yayi ya
shiga a tunanin sa zata shiga motar sa ne sede abun mamaki motar ni'imatullahi
ta shiga gidan gaba fadima ta shiga motar da amaryar da angon suna motar
masdook.
Haka aka yi tafiyar.
Isar su keda wuya
kowa da wani a gefen ta suka shiga cikin tsari suna xama ya samu gu ya zauns
har kan sa ya fara juyawq ma shi saboda hayaniya banda matsayin yusuf a gurin
sa ai ba abunda zai kawo shi gun nan.
Can aka saka wakar kujerar tsakar gida ta ado gwanja kar
kusu kuga yanmata da maza yadda suka hade suna cashewa.
A xaune take amma
kidan ya tafi da ita bata ma san sanda ta shiga filin rawar tana cashewa wani
hadaddan guy ya mike cikin isa da salo yana mata liki a jikin ta ganin ya nace
mata yasa ta gyara tayi waje ta koma gurin inono ta zauna
Inono tace ke kam
anyi ysr kaniya kin shiga rawa kamar wata budurwa kuma mijin ki na nan
Inono ayi hakuri .
Kiranta fadima tayi
mikewa tayi ta isa gareta aka sha gabsn ta dagowa tayi da sauri dan ganin waye
wannan guy din ne ya sakar mata murmushi tsadadde
Kai tsaye yace ina
son ki sunana *ADNAN MUBARAK CIROMA*
Ina fata zaki ban hadin kai mu sasanta ksn mu waya sani ko
mune next za ayi...
Yi hakuri bawan
Allah ina da aure
Haba dai ki bsri
mana ai baxan yarda ba cewa kina da aure dan ki yafice ksn ki daga gareni ni
kuma na gani ina so.
Wallahi ina da aure
ga mijina ma can ta nuna masa masdook wands tun daxu yake kalllon su ya sha mur
ya dauke kai kamar baya gurin amma basarwa yake kawai ya rasa dalilin da ya sa
ran shi ke baci kan yarinyar da baya so kawai abu daya ya ke masa yawo a
kwanysr sa
*ina sonka kuma dole ka so ni*
Ya girgixa kan sa yana cewa *no* bazai yuwu ba.
Kinga zo dan Allah zo mu zauna kinji mu fuskanci juna in ba
haka ba zan biki duk.inda kika shiga Allah.
Jin haka ta tsorata sannan ta zauna kan kujera ya zauna
shima
Ko kefa sunan ki fa?
*Aisha humaira*
Nyc
Dan Allah kice kina sona zaki aureni kinji wallahi ban taba
haduwa da macen data sacen zuciya cikin yan lokuta ba kamar ki (love at first
sight)
Nagode adnan amma ka makaro ni zuciysta mutum daya keda ita
daga shi babu wani har abada ka fahimce ni ka yarda kuma duk wsnda zaka tambaya
a nan matsayina zai fada maka cewa matar aure ce
Oh God nima mijin
aure ni naga alama sona ne ba kya yi.
Murmushi tayi hmm
aisha humaira mutum daya zuciyarta tske so take kauna kamar yadda uwa ke san
danta haka nake son sa ba me maye gurbin sa a raina ina fata ka fahimta.
Nayi rashi hummy
nayi rashi amma ...kawai mutum suka gani a kan su ya tsaya yadan rankwafo ya ce
bawan Allah ko zaka iya bani aron matata?in kun gama gaisawa ?
Am sorry fa kayi
hakuri
Hannun ta ya kama ya
yi waje da ita inda ba hayaniya.
Cikin mota ya turata
ys kulle da key yayi gaba abunsa.
Ta dunga bugawa
hamma ka bude min kofa zaka rufe ni ksmar wata fursuna ka bude open the door.
Komawar shi keda wuya gun adnan ya koma ya nuna sa da yatsa
kayi na farko kayi na karshe ksr ka kums ko a hanys ne ka nuna kasan matata ya
kada ksn sa ys shiga cikin hall din sossai wajsn su nas ya zauna
Nas ya dafa shi ya dai man
Ba komai.
Da kyar ya tsaya aka gama kammala partyn
Humaira yake nema
gaba daya idan shi na neman ta amma be ganta ba
Nadiya ina humaira?
Sun tafi a motar hamma ishaq .
Yyi jim ya gyada kai
ya fice ba wacca ya dauka a cikin yanmatan harsu inono din be bi ta kan su ba.
Komawarta gida keda wuya ta yi wanka tayi sallar isha'i ta
sa wasu rikitatun kayan bacci dake mutuniyar bata son zafi ko takura musamman
manyan kaya ta baje kan gado ana hira amma hankalin ta na wani tunanin na daban
dadi take ji hamma masdook ya fara kula da lamarints amma haushi daya take ji
da beyi ba sai yanzu daya ga ta girma ta sauya kama mtsw dan rainin wayo kawai
Kedawa ke kuma
hajjaju?
Ban sani ba magulmata
Maida wukar sis bani na kar zomon ba rataya akw bani
Suka sa dariya gsba dayan su.
Har bacci ya fara
dauketa
Shigowa yayi cikin
kananun ksya ya canja kaysn sa ya shiga dakin da'ada ya zauna suka gaisa da'ada
ina humaira?
Humaira tayi bacci yanzu ai dan tun daxu ta shirya ta kwanta
kasan gajiyar biki.
To dama zan fada mata
wata magana ne
Amma tunda ta kwanta
bara na fada miki ki sanar mata kar na ganta gobe ba mayafi gun bikin nan kuma
kar ta kuma tsayawa da wani kato
To ayi hakuri insha Allah zata kiyaye
To seda safe
Allah tashe mu lafiya amin.
Dakin ta leqa taga
tayi bacci amma sauran na hira ku bazaku kwanta ba ku huta ga wani taron gobe
zaku yi.
To yanzu zamu kwanta.
***************
Da asuba ta tashi da
matsanancin ciwon ciki da kai ta dinga kwarara amai gashi ta galabaits hankalin
da'ada ya tashi ta kasa sukuni yar lele ba lafiya.
Mutsumutsu ta dinga
yi a kasan bandakin jini ko ya bata mata
jiki rabia ta kira wo inono aka taron mata a kai.
Gaskiya tana wahala
yarinysr nsn duk wata ace se mutum yayi kamar ya mutu
Masdook na dakin sa
yaji ana hayaniya fitowa yayi dan jin ba'asi
Meya faru kuma?
Humaira za a kai asibiti
Humaira kuma ?
Meya sameta
nima ban sani ba gashi dai zasu shiga mota da ita
Key ya zara yayi
waje da sauri amsarta yayi ya sa cikin mota ta gama galabaita bata gane kowa a
gun
Numfashi sama sama take kawai idanta ys lumshe ta suma a
gurin.
Rudewa mama hajja tayi shi kuma ya kara gudu har suka isa
asibitin aka shiga da ita emargency
Sai zarya yake yi a
waje ya kasa zama gu daya mama hajja da inono sun zauna jigum.
Jin kadan likitan ya fito ya ce wani ya biyo shi office din
sa ya zauna yana kallonshi
Gaskiya tana fama da
ciwo a cikin ta wnda shi yasa take shan wuya wajan aladar ta duk wata
To dr.me za ayi
yanzu ?
Ina tunanin better case ayi mata surgry a cire mata abun
insha Allah komai zai dawo normal
To dr yaushe za ayi
aikin?
Anytime from now in kun shirya
Ok
Amma waye zai yi
siging na yardar op din?
Ni
Wa kake a gunta
Mijin ta ne
Ok to anjima ka dawo munyi admiting nata
ai kasan proccess din komai dan se yanzu na gane ka
dr.masdook muhammad diko
Murmushi yayi kawai
ya fita.
Kai ya akai me likitan ya fada.
Cewa yayi za a mata aiki kar ku damu muje na sauke ku a gida
zan dawo anjima
Aiki kuma masdook
meya sameta hska
Bayani ya musu a nutse yadda hankalin su baxai tashi ba
Ya kai su gida ya yi
wanka again ya debi kayan ta biki dai ya tashi a alhinin yar so yar lele aisha
humaira ta da'ada matar manya masdook
Haka aka daura
auren ba wani jindadi dan dai ya zama dole ne da dagawa za ayi ma
Yana kimtsawa ya koma
asibitin bata farka ba har zuwa wannan lokacin
Kan kujera ya zauna inda ze dinga ganin movement nata
Kusan after minti uku
seya duba plus din ta sanan ya zauna
Wajan magrib bayan
anyi sallah dr.isa ya fara shirya aikin da zasu yi
Hannu masdook ya sa
aka shiga dakin op din da humaira shi ma bin su yayi dan is allowed .
Banda baffa da abbi
da baffa kabir ba kowa a asibitin.
Masdook ne ya fito yana cire gloves nurse na amsa ya dan sha
mur
Baffa ya ce ya dai?
Alhamdulilahi an samu nasara hutawa take yi an maidata dakin
hutu.
To masha Allah alhamdulilahi har naji dadi a raina bara na
kira su da'ada na sanar musu ko hankalin ta ya kwanta dan ta fi kowa damuwa dan
humaira komai ce ta da'ada.
Hmm a ransa yace baka ji tawa zuciyar ba abbi da ka tausaya
min fiye da kowa.
*
Washa gari ta farka lokacin fadimatu ce a dakin su msma na
waje a zaune kan kujera masdook kuwa ya komq gida ya dan kimtsa jikin sa ya
huta sai ya dawo
A hankali tw kira
sunan Allah tana kokarin mikewa fadimatu ta yi wuf ta mike ta yi wajebdan kiran
mutan gidan.
Da sauri suka shiga dakin gaba daya dan ganin ta
Tayi fayau ta rame
cikin kwana daya cuta da wuya (wayanda basu da lafiya Allah yw basu lafiya masu
shi kuma Allah ya kara musu).
Ya gama shiryawq kenan ya dau mukuli ya fita yaji alamar
sako a wayar shi dubawa yayi da kyau kuma fuskar sa dauke da mamakin ganin
sakon da number din
*ya kake habibi na
ina ka shiga ka manta dani masoyina ka manta da baya ka dawo mu fara sabuwar
rayuwa nasan ni kake so ba wannan yarinyar ba*
Tsaki yayi ya cigaba
da tuki abun sa
Haka ya tsaya a
supermakert ya yi yar siyayya su yougurt da abubuwan kwadayi dan yasan humaira
amma be siya za'ki ba dan yasan larurar ta.
*ya zaka min biris
duk yadda nake son ka ka manta baya nasan nayi kuskure amma ka yafe min ina
kewar ka*
Sitiyarin ya buga
yayi tsaki
*ban san ciwon kai
kar ki kuma damuna ina wuce guri na wuce har abada baki isa komai ba yanzu a
gurina ki fara koyo daraja iyayen wasu tukuna sannan na ga ko zan iya kara ki
rayuwata*
Tana kwance a kan gadon ta taga sakon ya shigo dubawa tayi
cike da mamaki tabdi jan lallai masdook ni xaka
wulakanta?
Dani kske zancan.
**
Hankalin ta kawai
masdook take son kalla shi take son gani ko taji sanyi a ranta
Soup inono ta bata a
baki ta amsa tana sha ta shagwabe mata fuska inono ni bani son wannan abun
Ki bani abinci me
kyau naci
Uwariyo ki sha soup kiji dadi a jikin ki abinci me nauyi ba
yanzu ba zuwa gobe ko jibi
Kai ni wallahi bani
son wannan gwara yougort da dan chips
Bakin kwadayi ysr
banza ki sha kina jina ko
Ana haka masdook
dikko ya shigo
Lumshe idanun ta tayi
dan kanshin turaren sa da ya ratsa dakin
Gaisawa suka yi da
ysn dakin sannsn ya ajiye ledae hannun shi .
Ya me jiki kuma?
Jiki alhamdulilhi da sauki gashi zata fara aikin za a dora
daga inda aka tsaya.
Me take so kuma?
Zaqi man
Nifa inono yought
nace ba zaqi ba ki barni na sha ko suger free ne
Ke kika san wani
sugerr me oho miki
Ta zumburo bakinta
hamma pls ka sa su bani ban san soup
Fadima!
Na'am hamma!
Bani ledar nan
Dauko masa tayi ta bashi ya dauko yought din zaunawa yayi
kusa da ita ya dinga batq a baki
Fadima ta kalli amira
suka kanne ido daya a tare suna murmushi kasa kasa.
Ya dan xubo mata
gefen baki ya sa hanki nasa ya goge matq bakin
Inono da mama suka
fita daga dakin haka ma amira da fadimatu suka bar dakin suma.
Hannun sa ta rike
alamar ta koshi
Ido ya bude mata ya
kuma sa mata a baki
Ta karba da kyar
tana gyada masa kai alamar aa ta koshi.
Kinga bayan zama a nan ina da wasu ayukan fa ki karba kawai
ki koshi ina da uzuririka da yawa dazan yi.
Hmm ta fada masa kawai tace ni na koshi nima ban ce ma ka
zauna ba a nan kana iya tafiya ba rike ka nayi ba.
Kallo ya bita dashi na mamakin humaira sossea ta canja masa
ko dama can haksn take garin ya mike ya zubar a kan rigarsa tsaki yayi ya shige
toilet
Dama ya bar wayar sa
a kan gadon
Sako ya shigo kamar
karta dauks se ta dauka ta duba
*pls masdook nace ka
yafe min wallahi na tuba ina son ka zan iya zama da kowa ma a ksn ka zan iya
zama da iyayen ka da so called matar ka*
So called?
Ni kenan lallai ma wannan koma wace zata san cewa hamma
masdook nawa ne ni kadai ba wadda ta isa shiga tsakanina da ita
Num tayi copying a brain din ta tayi sauri ta qjiye masa ta
kwanta abunta
Haka ya fito ya
karqci kallonta sannan ya fita.
Juyowa tayi a kufule tana kumbure kumbure abunta tsaki tayi
yafi a kirga ta riga tasan matakin da zata dauka kan wannan mayyar dazata
ruguza mata rayuwa tun kafin ayi zaman auren ma.
Kwananta biyu a asibiti aka bata sallama taso taje kai
amaryar amira amma dada ta hanata zuwa cikin yan kwanaki ta murmure tayi fes da
ita ta dada cikowa
Ranar da yamma suna zaune a kan tabarma ita da fadima da
ummu jamila suna hira
Ta dau wayar ta wannan
number ta danna tq kirawota harda shigewa uwar daka inda ba hayaniya.
Hello!
Ba rokon ki nike son yi balle tambaya ina miki warning ne
cewa ki tabbata kin rabu da mijina ki daina shiga harkar sa babu ke babu shi
kina shiga min rayuwa kar ki kuskura ki kuma kiransa ko da a waya na mun gode
da gaisuwar ma
Ke dakata waye mijin
naki?
*Masdook*!
Ohh kece dama banzar yarinyar data yi sanadin *(a sanadin ki
littafina na gaba insha Allah)*
Ke kikayi sanadin rabuwata da masdook amma ki sani sena
shiga rayuwar ki ta yadda bazaki iya fita ba sena ruguza farin cikin ki ta
yadda zaki daina dariya ki manta yadda ake yinta masdook nawa ne nawa ne kawai
ni kadai.
Shi kenan ni ina da
wani karfi guda daya kinsan me wannsn karfin nawa?
Shiru ya biyo baya
ok barq ma kawai na amsa miki
Karfin Aisha
humaira masdook shi ne karfina kuma matukar ina tare dashi matukar ina numfashi
to da son masdook nake numfashi ko wanne dakika da second duk wani jini dake
yawo jikin aisha humaira da son masdook yake diga tun bansan so ba nake son
hamma masdook shekaru goma sha daya ina *dakon son sa*
A raina amma bsn bari yq kubuta min ba to ta yaya zan bari
keda kika shigo rana tsaka na bari ki amshe shi a bagas?
Na fada miki ki
nisanta kan ki daga mijina snatcher kawai.
Ki nemo naki mijin masdook ya mijin aisha humaira ne.
Tq kashe wayar tana masifa kawai mutane su dinga bin mazan
wasu suna damun rayuwar su ni da na zaunadashi ne ma yace yana sona ai da da
sauki
Kuka kuma ya zo mata
ta juye hawayen ta idan abun ya cita wata ran tayi ta kuks ita kadai tq rasa
wanne irin so take ma hamma masdook wanda shi ba haka take a gunsa ba.
Hannayenta ta daga
sama ta kai kukan ta ga ubangijin kowa da komai dsn shi zai yaye mata shi kadai
zata dogara dashi ba mutum ba ya Allah ka dora masa sona yadda ka dora min nasa
Wallahi ina son hamma masdok
*(so me wuyar
sha'ani)*
Wayar ta yarda a kasa ta tarwatse a gun kan buuu ni wannan
yarinyar zata karqntawa karatun rashin kunya da wulakanci lallai ta nunan ita
din meson masdook ce amma nima nayi alkawri guda daya sena shiga rayuwar su
sena tarwatsa su sena yi kace kaca da wannan soyayyar .
Ta zauna tana saka
abunda zata aikata mata ta huta a rayuwarta taji dadi ko bata auri masdook ba
seta raba ta da masdook .
****
Kowa ya watse gidan ya yo tsit cikin wasu kananan kaya ya
fito se kamshin turaren sa ke tashi ta ko ina ga tsadaddan takalmi ya saka ya
dauko jakar laptop nasa ya shiga dakin dada dan ya mata sallama wucewa zai yi
kano.
Dada zan tafi !
Aa tun yau masdook?
Wallahi na bar aiki fa da yawa kin san aikin namu
To Allah kiyaye hanya
Amin.
Dada ina humaira?
Ina ga tana dakin ta
To bara naje mu
gaisa na wuce
To to
Ya shiga dakin humaira tana bandski lokacin daya shigo seya
ji dakin ya masa dan shi meson kamshi ne dakin ko banda kamshi ba abunda yake
tashi kums kal dakin ba kazanta .
Tana waka ta fito
daga toilet din
*yanzu ni da kai ba
shamaki bari ja da baya kar mi haka*
Tsayawq cak tayi tana mamakin ganin mutum a gurin
Zata koma ya daure
fuska
Ke ban san hauka mezan gani a jikin ki dazaki gudu a banza
in kin koma ma zan fada miki ne zan tafi yanzu in akwai abunda yake damunki ki
fada min ba sena tafi ba jarabar taki ta motsa miki bana nan kuma
Kallo ta bishi
dashi kallon me kake nufi ?
Kallon wacca jaraba kuma?
Kin sa min ido
kamar mayya kina kallo ina jiran ki ina da ayyuka masu muhimmanci da suka fiki
fa
Ta hararesa ba
abunda nike so Allah kiyaye hanya ya kiyayeka daga sharrin masharata kawai ta
fada
Ya bita da kallo
kawai yadda yaga jikinta me matukar daukar hankali
In ka gama kana iya
fita zan sa kaya ne ban san ana tsaya min a ka ko a takure ni da kallo.
Kunya ta kama shi
yayi waje da sauri abunsa.
Ta window ta leqa
har ya fice daga harabar gidan gaba daya.
Zan yi kewar
handsome look naka.
****
Wai ni baffa wannan yaran su yaushe zasu tare lokaci yayi fa
da ya kamata masdook yace wani abun
Haka ne amma tunda
banga ya motsa ba shi yasa bsn yi magana ba
Amma nags yarinyar zata fara makaranta a can buk idan
lokacin yazo ba sai kawai su karata su biyu ba.
Haka ne Allah ya taimaka yasa ayi a sa'a
Amin.
Ni fa dada yau
gidan amira zanje
Ni bsn hanaki ba amma ki tambayi mijin ki
Wai kice in tambsyi
mijina yana ina dazan tambaye shi?
Kawai ki bani kudin mota ko na je gun baffa da abbi ya bani.
Ni ba ruwana kinsan
halin masdook yana jin kin fita zai min wannan aikin nasa
To ina ruwan sa da fitata?
Ban sani ba
Wallahi dada sena fita kawai ki ban kudin mota kinsan banda
kudi
Nima banda shi mara mutunci
Dada dan Allah ki ban wallahi na riga nayi niysr zuwa kuma
na fada mata naga da fitar nake ba tambaye shi ba sede in tambaye ki kuma ki
barni se yau.
*so ba shi ne se
mutum yana son ka ba ya kasance so so yana faruwa ga kowa ko ka shirya ko baka
shirya ba idan Allah ya riga ya shirys maka ba yadda zaka yi one has to be self
content with what he have*
Ba wani jimawa suka yi ba suka sauka a katsina gouruba road
Wayarta ta zaro ta
kira num aminiyarta
Hello amira
Hello sis kina lafiya?
Wallahi alhamdulilahi ina kalau ya mijin naki da gidan ?
Wallahi komai alhamdulilahi
Kizo waje man ki
bude min kofa
Kee sis ban san
tsokana fa
Shi kenan bari mu koma tunda baki son ganin mu
Aa ina zuwa mayafinta ta zara tayo waje tana budewa taga sis
dinta ai da gudu ta rungumeta tana ihun dadi
Wayyo Allah na yar'uwa shigo daga ciki
Hamma kamal sannu da
zuwan ku naji dadi sossai yau kune a gidan
Dama ina ts zaman
kadaici kai amma naji dadi
Suna xama ta tara
musu abun makulashe a gaban su
Ya karfin jiki kuma?
Da sauki wallahi
To masha Allah.
Hamma sannu da zuwa
kune na farkon zuwa gidana
Uhm lallai kam ina
hamma yusuf din
Ya dan fita amma nasan yanzu ya kusa yana hanyar dawowa
To ai shi kenan.
Amira ta kasa zama yi wannan hada wancan ta gama hada musu
abu mai dadi sannan ta zauna
Jim kadan hamma
yusuf ya dawo suka zauna suka gaisa ya yi cikin daya falon da hamma kamal suk
barsu a anan.
Kee sis haka kika kara fresh cikin kwana biyu kawai me hamma
ya baki haka?
Hmm krdai bari kema zaki je gurin
Wallahi sis u look
take away sossai kika yi kyau kamar ba ke ba hamma ya iya kiwo
Hhh kai aisha
humaira
Wallahi da gaske nake miki fa to shi kenan godiya dubu.
Kin ban sha'awa sis kin yi kysu hamma na son ki kina son sa
kuna soyewar ku kamar ba ku ba amma ni da aure a kaina kusan how many years
wanda da me sona ne da tuni mun dan tara
Hmm aisha humaira
kenan bari cewa haka wallahi yana sonki tsabar tsantsar miskilanci ne
Menene alamar so ne?
*Kulawa*
Naga kulawa a tare da ke a idan hamma masdoo.
*damuwa*
Naga damuwa a idansa lokacin da baki da lafiya.
*kishi*
Naga kishin ki zallah a tare da shi lokacin bikina.
Sossai hamma na son
ki
Ki daina kare yayan
ki dan Allah ni na san baya sona
Wallahi baxan yi
kaffarq ba hamma yana mugun son ki kuma kema kin san da hakan nagani a idan sa
Ki daina bin zancan
idanuwan nan ki daina sauraran su in ba haka ba zasu yi decieving naki a barki
a ruwa.
Kinga mu canja topic
banda lokacin wannan zancan yanzu.
**
Kwance yake a kan gado ya kasa katabus kawai daya kulle
idanuwan sa surar matarsa yake gani
Idanuwanta ke masa
yawo a idan sa
Yadda take
tsiwa,murguda baki,masa rashin kunya burge shi yake yi.
Ya mike ys jingina
da bangon gadon nasa ya Allah meke faruwa?
So wata zuciyar ta bashi amsa
Ya juya da kyar no
bani son ta mesa zam dinga tunanin ta haka kawai
*Ni wacce ita a
guna*?
Matar ka,halalin ka,masoyiyarka.
Duk duniya ba wanda zai nuna maka so kamar ta *aisha
humaira*
Tana son ka mugun so tun kafin ta san ma'anar so take son
ka.
Wayar shi ya dauka ya kunna dan tun safe a kashe take
Data ya kunna ya
leqa watsap family grp nasu ya shiga an tutura hotunan bikin yusuf da amira
Suka gama budewa
gaba daya humaira tayi kyau wani hoto ne ya dau hankalin sa sossai wanda
humaira tayi ita kadai ta yi mugun kyau
Ga killar smile data
yi
Shi ma besan sanda yayi murmushi ba a cikin grp din ya dau
nuj ta.
Da niyar zai kirata
a waya.
Wanka ya fara yi yaci ado yayi kyau ya sha turarw yadda
kasan shi ne ma turaren ya dau tsadaddan takalmin sa ya saka ya dau key da
wayar sa ya kulle gidan nasa.
Mota yq shige abunsa ya juya mata kai yayi gaba
Cikin nutsuwa yake
tukin tamkar bashi da wata damuwa kwata kwata a tattare dashi
Hankali kwance yake
tafiya yana dan murnusawa.
Cikin hour biyu da rabi ya isa inda yake shirin zuwa ya
karasa layin su ya parker motar shi cikin yan dakika kadan ya parker motar ya
fito abunsa.
Bangaren su ya fara isa ya samu mama kwance kan kujera tana
hutawa
Salamu alaikum
Amin wa'alaikum sallam wa nake ji kamar masdook?
Mama ni ne
To amma nayi mamaki shekaran jiya fa ka tafi
Wallahi mama kawai na
dan dawo ne
To sannu da hanya
tashi tayi ta dauko masa ruwa me sanyi ta zuba mishi ya kurba
Kaje ksyi wanka tukuna se kazo ka ci abinci ka huta
Ai mama yau zan koma fa
Hba dai kamar ana korar ka tashi kaje kayi yadda nace maka
yaushe zan bari ka koma yau tsaka da yamma sossai.
Mikewa yayi yana dan murmusawa.
Da ya gama kimtsawa ya shirya yayi.cikin gida gurin su baffa
ya je suna zaune kan tabarba a tsakar gidan suna cin tuwon dawa miyar
busasshiyar ku'bewa.
Ya tsuguna ya gaida su dukka suka amsa faram faram
Aa masdook sannu da hanya ka sha hanys ko
Wallahi baffa ya aiki
Alhamdulilahi!to masha Allah
Baffa dama gun ku
nazo
To lafiya dai ko?
Baffa lafiys lou dama akan maganar aisha humaira ne
To bismillah
Baffa ina so cikin sati biyu daza su zo a yi kokari a yi
bikin nan ta tare a can ina da bukatar ta q can.
Eh to muma munyi wannan tunanin amma se muka ce mu bari
tukuna ta samu makaranta a can garin seta koma .
Baffa ,abbi duk
bazai zama wahala ba a gareni da ita yafi sauki a can in ta samu ai tana garin
To shi kensn masdook
zan yi wa da'ada da iyayen naku magana
To baffa Allah kara girma da arxiki
Amin amin!
**
Tsohuwa me ran karfe kin ci zamanin ki kina kuma cin na
wasu!
Ta murmusa kawai.
Kin wani kashingada kin yi wani fresh me sirrin ne tsohuwa.
Unbula ta masa
Yayi murmushi yana gyara zaman sa a kasan kilishin dakin
Da'ada ya kike ya gdan ?
Lafiya lou masdook ya aikin naga shekaran jiya muka rabu har
ka dawo ?
Kawai hutawa nake da yau zan koma amma mama ta hsna wai se
gobe ni ku nazo gani dama
Tayi murmushin manya
ta ce masdook lallai ka girma ko dai gun matar ka kazo ?
Ya sosa keyar sa yana
murmushin jindadi
Kai tsohuwar nsn da fassara kike
Yoh ai abun ne yazo
dani da kai zamanin mu daban bar gani na da hurhura a ka ina da sani tun farko
Uhm lallai ins matar
tawa?
Ai wannan ja'irar ban gants ba tunda tace min zata shiga
gari gun amira nace ta tambayeka a waya taki ban kuma ganin ta ba ko tayi
fushin ne tana dakin inono ko kuma tayi gun matar ismail.
To bara na duba ta.
Dakin inono din yaje suka gaisa rimi rimi ya tambayeta
matarsa itama ta fada masa.
Gida ya koma gun mama tana jan carbi a hannun ta zaunawa
yayi kan kujera dan ta karasa amma iya kaduwa ta gama ya gama kaduwa .
Tana gamawa ya tsuguno a gabsnta
Mama kin san inda
aisha take?
Uhm tana kastina
man.
Mama mesa kika bsrta
ta tafi
Da kamal na hadasu
ya kamata a ce yanzu sun dawo ma ko me ya tsaida su oho?.
Mama ni ban san fita wallahi
Yau naji ikon Allah
masdook me zan yi to?.
Mutum za a rike shi ne kamar marar yanci?
Mama ba hakq bane ban san fitar ta ne.
To masdook yi hakuri
ba za a kuma ba nayi laifi nayi iko da matar ka na daina.
Allah huci zuciyar ki mama kiyi hakuri ba haka nake nufi ba
Ya fice waje abunsa.