Wednesday, February 20, 2019
Ashe Hassan tun ranar da aka kama mu ya tattara yabar garin, Ya Umar harda biyan police akan su nemoshi amma ba'a ganshi ba.
******
Mama ta daina zuwa aikin rana, na safe kawai ta ke zuwa Ya
Umar ya siyo mana kayan abinci dai-dai na buk'ata, yana matuk'ar kulawa
da mu, duk wani d'an kud'in da yake samu na bautar k'asarshi da kuma
d'an bige-bigen da ya keyi a kan mu yake k'arewa.
Daga Ummi har mahaifinshi ba wanda ya nuna damuwa akan kud'in da yake kashe mana, sai ma dai dad'a goya mai baya da suke yi.
Ya Abdallah ma bai zauna ba, tunda dama ya jima da daina
zuwa school saboda rashin kud'in da za'a biya mai na zana waec d'inshi,
kullun zai fita yin dako da shi d'in ne muke samun na cefane kuma har
yake k'ok'arin siyamin duk wani abu na kwad'ayi wanda baifi k'arfinshi
ba.
A wannan lokacin ba ma yin kwana biyu Ya Abdallah yake siyo
mana nama asa a miya, Mama takan yimai fad'a akan yadinga ta ra kud'in
dan yasamu ya biya kud'in waec d'in, amma kullun Mama ta fad'a mai haka,
sai ya ce:
"Mamana ki daina damun kanki karki manta namiji baya tsufa
da karatu a hankali zanyi, amma na fiso na inganta farincikin ki dana
Farida"
Kullun ya fad'i haka sai mun zubar da hawaye, kuma Mama ba ta gajiya da Saka mai albarka.
***********
Akwai wata ranar jum'a da bazan ta6a mancewa ba.
Ya Abdallah ne ya fito daga d'akin kwanan mu sanye da kayan leburancin, kallonshi na yi nace "Ya Abdallah har zaka fita"
Fuskarshi k'unshe da murmushi ya ce "zan fita Farida Umar a mana addu'a domin yau na fita da kaza zan dawo"
Murna fal zuciyata nace "kai Ya Abdallah kace karna cika
cikina yau" dai-dai wannan lokacin Mama ta shigo d'aki ta kallemu ta ce
"wai me ake tattaunawa ne"
Na fad'a ma ta, murmushi Mama ta yi sannan ta ce "Bawan
Allah karka takura kanka da aiki fa kazo wani cutan ya kamaka kasan
halin da muke ciki"
Murmushi Ya Abdallah yayi kafin kuma yace "Mamana ki daina
damun kanki, addu'arki kawai nake buk'ata, yanzu dai fad'a min mai zan
taho dashi idan ina dawowa"
"Kullun a cikinta nake, bazanyi *SAKACI* da na yi a baya
wurin yi muku addu'a ba, kubewa zaka taho dashi d'an albarka" Mama ta
fad'a.
"Farida Umar mai kikeso na taho miki dashi" Ya Abdallah ya tambayeni, "Ya Abdallah ka tahomin da atile idan zaka dawo"
Ya ce "toh shikenan amma ga wancan farar yadin ki wanke min
don Allah ta fita kafin lokacin masallaci" na ce "angama har aron
dutsen guga ma zan d'auko na Ya Umar na goge maka"
"A'a Farida karki sa ke koda zancen wasa kice zaki zama mai
auro, mutum ya godewa Allah da duk abinda Allah ya bashi, nikam idan
kika wanke dakyau ya wadatar"
Murmushi Mama ta yi had'e da cewa " wallahi Abdallah idan
kana wasu maganganun sai naga kamar ba d'an shekara goma sha bakwai zuwa
sha takwas ba, sai naga kamar kawuce shekarunka, akwai ka da sanin ya
kamata"
"Sai na dawo Mama" Ya Abdallah ya fita, fitar da ta kasance
ta har abada fitar da bai sake dawowa ba sai gawarshi da aka kawo mana.
Tabbas munshiga tashin hankali mara misaltuwa lokacin da
aka shigo mana da gawar Ya Abdallah mota ta bigeshi, ruwan wankan juma'a
dana saka mai a murhu shi ne aka yimai wankan gawa.
Ba wanda baiji tsoron tashin ciwon Mama ba a wannan lokacin kasancewar ba wanda bai san irin k'aunar da Mama ta ke yimai ba.
Amma ga mamakin kowa shi ne Mama ko kuka batayi ba hasalima ita ta ke bawa jama'a hakuri.
Hakan da ta yi mutane da dama sunji dadi kuma sun yaba ma ta amma badda Ummi da Ya Umar domin sun san cewa ta na kukan zuci ne.
Ranar da Ya Abdallah ya cika kwana bakwai da rasuwa Baba ya
dawo, wanda rabonmu da shi wata biyar kenan, shi ne kuma yayi dai-dai
da watan Ya Hamid hud'u da sati biyu da rasuwa, sam Baba bai san da
rasuwar Ya Hamid ba balle kuma na Ya Abdallah.
Aranar munsha mamaki irin kukan da Baba ya ke yi yana da
yasani, tabbas a ranar mun tausaya mai ban ta6a sanin Baba ya damu damu
ba sai ranar, yana kuka yana cewa!
"Ku yafemin yarana, na cutar da ku cutarwa kuwa mai yawa,
ban ta6a yarda kun ra6eni ba, sam bakusan dad'in uba ba, na kasa d'aukan
nauyinku da Allah ya d'auramin bayan kuma Allah bai hane ni ba"
Kama hannun Mama yayi, ni kuma ya janyoni jikinshi, wannan
itace rana ta farko da mahaifina ya yafara rik'eni cikin kulawa, kuka
mukeyi mai ban tausayi, Mama idonta a bushe har wannan lokacin bata
zubar da hawaye ba.
Cikin kuka Baba yake cewa " Sakinatu na yi asara, ina
tsoron gamuwata da Allah, naci amanar da Lamido ya bani, na zalince ku,
ku yafemin ko zan sami sauki"
A ranar da daddare Mama ta sanarwa da Baba irin 6ata min
rayuwa da Hassan yayi, Baba yayi kuka yayi bak'in ciki gami da danasani,
haka yayita rok'on gafarar mu, a ranar dai Baba bai runtsa ba.
Washegari ya zowa Mama da maganar yanaso mu bishi zuwa
Bauchi, domin shi yanzu baya so yayi nesa damu dad'in dad'a kuma mutanen
unguwa sun sani agaba akan abinda ya faru ban isa fita ba.
Mama sam tak'i amincewa haka Baba yayi magiyanshi har ya
gama amma tak'i amincewa ta ce ita tafiso ya barmu anan, kasancewar baya
son ya kuma yin abinda zai shiga hakk'inta yasa ya hakura amma badan
yaso ba, sai dai yace dole zai canja mana gida wannan Mama bata hanashi
ba.
Kwanan Baba biyu da dawowa amma sam baya zama yana
cuku-cukun nema mana gida, Ummi ce kullun ta ke shigowa domin ta d'ebewa
Mama kewa sai kuwa Ya Umar da yana dawowa daga aiki mu yake fara
lek'owa kuma har wannan lokacin bai daina yi mana hidima ba baranma ni.
A ranar wata laraba ne, na tashi da wani azababban ciwon
ciki, Mama ta d'auka period zanyi shiyasa taje da kanta ta siyomin
peldine, nasha amma ciwon cikin k'aruwa ya keyi, haka na wuni ina abu
d'aya.
Ranar sam ba wanda ya rintsa a cikin mu ukun, da safe ne
kuma abun yayi tsanani domin jini ya fara zuba (bleeding) fiye da
tunani, ba abinda ba'asa ba don tare jinin amma ina harda guda-guda ya
ke fita.
Kan kace meye wannan na galabaita, ba shiri Baba ya je
gidan Ummi Ya Umar baya nan amma anci sa'an Alhajinsu na gari, shi ya
kaini asibitin a galabaice.
Dak'yar likitoci suka tsayar da jinin na zubar da jini
sosai amma sunce ba sai a k'aramin ba, wunin ranar haka likitoci suka
dukufa dubo abinda yake damuna.
Abinda suka gani a sakamakon gwajin nawa shi ne silar
komai, lokacin wani Dr ya shigo d'akin da nake da sakamakon, a sannan na
farka ina kwance jiki ba kwari, ya kalli su Baba hankali tashe yace .
"Kune iyayenta " su Baba da Alhaji sukace "eh likita don Allah sanar damu, abinda yake damunta"
Dr ya gyara gilashin idonshi sannan yace "ina mijinta?"
"Ras" gabana ya bada, cikin damuwa "Baba yace bata da miji a yanzu don
Allah ka sanar damu meye matsalar"
Dr yace "toh ina fargabar sanar daku akwai wani tsarin
iyali da y'arku ta keyi wanda ya janyo ma ta matsala babba, kuma ina
tsoron sanar daku mahaifanta ya samu matsala bazata ta6a haihuwa ba,
kuma ba lalle ne ta sa keyin al'ada (period) ba koma ta sa keyi toh fa
ciki bazai ta6a shiga ba, saboda yin wannan tsarin iyalin wanda ya wuce
k'a'ida, a yanzu dai munyi k'ok'arin tsayar da jinin"
Abinda likita ya fad'a shi yayi sanadiyar fad'uwan Mama,
cikin gaggawa akayi d'akin emergency da ita, adai-dai wannan lokacin Ya
Umar ya shigo asibitin koda yaji dalilin fad'uwar Mama, zama yayi a kasa
tamkar zaman y'an bori yana cewa mai yasa aka fad'awa Mama, ba wanda ya
iya bashi ansa.
Munga tashin hankali ranar ba yadda ba'ayi dani na kwanta ba nak'i nace dole naga Mamana haka aka barni.
Likitoci sun kai awa biyu a d'akin da Mama take kafin,
babban likitan ya fito yace "wai waye Farida" ban iya magana ba illah
d'aga hannuna da na yi, yace "toh ma za kije tana son ganinki" ya juya
gasu Baba yace sujira na fito.
Halin da naje na iske Mama ya kusan zautar dani, bazan ta6a manta wannan ranar ba.
Farida ta dakata saboda kukan da yasha k'arfinta, su Dr Jidda ma kukan sukeyi sosai.
SAKACI Part 13
Muna tsaye a bakin emergency, duk kan mu kuka mukeyi sosai
inka cire Ya Umar da ya dafe kanshi ba abinda ya keyi sai ajiyar zuciya.
Dr ne ya fito daga d'akin da Mama ta ke, dukanmu muka rufamai muna tambayarshi halin da Mama ta ke ciki, cikin damuwa yace
"ku biyo ni office"
Bayan Dr ya cire safar hannunshi gami da wanke hannun kafin kuma ya zauna, kasa hakuri Ya Umar yayi, cikin zak'uwa ya ce.
"Dr ya jikin nata please ka sanar damu" gyara zama Dr yayi gami da kallon mu sannan ya ce.
" Umar you are a Doctor cool down, zata iya farkawa zuwa ko wanne lokaci, sai dai fa akwai matsala"
A take gaba na ya yanke ya fad'i zama nayi jagwab ina cewa
"shikenan na shiga uku na gama yawo na kashe uwata"
Ya Abdallah ne ya ce "ke ki rufe mana baki ko ki bar nan wuri kafin na miki illa" ya fad'a cikin d'aga murya.
Ya Umar kuwa wani kallo ya aikomin dashi wanda yayi sanadiyar kad'awan hanjin cikina, toshe bakina na yi da hannu na.
Ya Umar ne ya sa ke cewa " muna sauraronka Dr"
Dr ya cigaba da cewa "gaskiya ina tsoron sanar daku mamanku
ta kamu da ciwon zuciya, kuma damuwa kad'an zai iya janyo zuciyarta ta
sake bugawa, wanda kuma zai iya zama sanadiyar rasa rayuwarta, don haka
dole ku kula idan kuna son ta cigaba da rayuwa, yanzu dai munci nasarar
ceto ranta"
Kuka sosai muke yi nida Ummi da Ya Abdallah, Ya Umar baiyi
kuka ba amma damuwar da na gani a ta re dashi ya tabbatar min da daurewa
kawai ya keyi.
Takardar magungunan da za'a siyawa Mama Dr ya bamu, Ya Umar
ya ce mai zamu iya shiga mu duba ta ya ce eh amma za'a canja mata d'aki
ma, yanzu ya je fara biyan kud'in.
***
Zaune nake a gaban Mama na sata a gaba ina kuka, a hankali ta rik'e hannuna ta na k'ok'arin bud'e idanunta.
Zaune nake a gaban Mama na sata a gaba ina kuka, a hankali ta rik'e hannuna ta na k'ok'arin bud'e idanunta.
Ganin ta bud'e idonta yasa na fad'a gaban gadon ina rok'onta gafara, ga mamakina sai ta ce "ki daina kuka kinji"
Cikin kuka na ce "Mama ni mai laifi ce, nayi kuskure, ki yafemin wallahi bazan k'ara ba"
Murmushi Mama ta yi wanda nasan na dauriya ne, kafin kuma
tace "Farida bakiga d'akin ba mu kad'ai bane, ko so kike ki tonawa kanki
asiri? Duk kibar wannan maganar har Allah ya bani lafiya mukoma gida
kinji" gyad'a kai na yi.
A hankali ta kira Ya Umar gami da nuna ni, ta ce "Umar kaje da ita a ma ta gwajin ciki da na k'anjamau"
"Dam"
Naji gabana ya fad'i, domin tunda abun nan yake faruwa ban ta6a wannan tunanin ba.
Fita ya Umar yayi ba tare da yayi min magana ba, sai Ummi
ce ta ce na ta shi na bishi, haka na cigaba da binshi jikina ba k'wari
har zuwa inda ake gwaji (LAB) d'in.
Da shike ba nisa tsakanin Lab d'in da asibitin, sanar dasu
yayi irin gwajin da yakeso a yimin, kafin kuma yaje ya biya kud'in ba
tare da 6ata lokaci ba suka fara aikinsu kasancewar sun san shi.
Ranar duk tsorona da allura haka na daure aka d'ebi jinina
don na tsorata da Ya Umar, bayan sungama gwajin suka bamu sakamakon,
wannan lokacin ma Ya Umar baiyi magana ba gani nayi ya fita nima na
bishi.
Jin sakamakon gwajin nawa yasa hankula da dama ya kwanta,
domin ba'asamu cututtukan a jikina ba, sanna ba ciki, amma sunce na dawo
bayan wata uku a sake yimin gwajin HIV.
****
Ni da Ummi ne muka cigaba da jinyar Mama, Ummi ba ta barina
naje ko'ina idan wani aike ne sai dai Ya Abdallah yaje idan kuwa baya
nan to ita da kanta ta ke zuwa.
******
Kwanan Mama shida a asibiti aka sallameta, a wannan
kwanakin na rame na lalace bani da aiki sai kuka, kuma ba wanda ya tayar
da abinda ya faru a cikinsu.
Ranar da muka dawo gida haka matan gida da makwabta suka cigaba da shigowa gaishe da Mama.
Bayan mun idar da sallah isha'i lokacin Ya Abdallah ya dawo daga masallaci, Mama ta dubeni ta ce.
"Matso nan Farida" ta nuna min gabanta bayan na zauna ta
dubi Ya Abdallah tace " bawan Allah (sunan da Mama take yawan kiran Ya
Abdallah dashi kenan) kaje falo ga abincinka can kaci zanyi magana da
Farida, kaima kuma anjima akwai maganar da zamuyi"
Toh yace sannan ya fita, Mama ta juyo gareni ta d'an
kalleni na d'an wasu dak'ik'u, ni kuwa na sunkuyar da kaina domin bazan
iya had'a ido da ita ba, gyaran murya Mama ta yi sannan ta fara magana
kamar haka!
"Farida inaso kiji tsoron Allah ki fad'a min gaskiyar duk
abinda na tambayeki idan kinaso na yafe miki, idan kuwa kika yimin karya
tofa babu tantama Allah zai kamaki kuma idan nazo na gane k'arya kika
yimin, ba zan yafe miki ba"
Cikin kuka nace "wallahi Mama zan fad'a miki gaskiyar duk abinda kika tambayeni" na k'arashe cikin zubar hawaye, Mama tace!
"Ki share hawayenki ba kuka nace kimin ba" share hawayena nayi sannan Mama tace.
" Yaushe kuka fara aikata zina ke da Hassan?"
"Ya kai shekara biyu, tun wani lokaci da yazo ya sameni ina
kukan yunwa yace na bishi na kar6a abinci, tun daga ranar ya fara wasan
ta6ani"
Mama ta girgiza kai sannan ta ce "Mai yaja ra'ayinki harki
ka amince mai, wanda a wannan lokacin ba kikai shekarun da sha'awa zata
rinjayeki ba, wanda kwata-kwata lokacin baki wuce shekara goma sha biyu
ba"
Ban 6oyewa Mama komai ba, Na fad'a ma ta komai.
Cikin wani irin yanayi Mama ta ce " mai yasa kika 6oye min wannan babban al'amarin, mai yasa baki sanar dani ba tun wuri"
Nace "na yi k'ok'arin sanar dake tun farkon lokacin da ya
fara ta6ani amma kika hauni da fad'a karshe kika gargad'eni, da ga baya
kuma shi ya dinga tsoratar dani......" Nanma na sanar da ita.
Hawayen da nagani a idon Mama da kuma kalaman da take fad'a shi ya tayarmin da hankali matuk'a!
"Ina tsoron gamuwata da Allah, ban rik'e amanar da ya bani ba, na yi sanadiyar lalacewar tarbiyar ku"
Ina kuka na ce "Mama mune da laifi mune muka kasa hakuri da
juriyar jarabawar da Allah ya aiko mana, Mama na tuba ki yafemin sannan
ki rok'a min Allah ya yafemin"
Cikin wani irin kuka Mama ta ce " na yafe miki Farida amma
tabbas nayi *SAKACI* wurin baku tarbiya rauni na ya hanani na nuna muku
illar aikata abubuwa da dama, wannan ne yaba wasu a waje damar d'auraku
akan gur6ataccen tulba, sannan suka baku fatawa wanda suka kasance na
k'arya da yaudara, ku yafemin yarana, Farida karki sake 6oye min duk
wani abu da ya shige miki duhu"
"Na miki alkhawari Mama na miki alkhawari"
Rungume Mama na yi ina kuka, mun d'auki tsawon lokaci muna kuka kafin Mama ta rarrasheni.
Cikin dare inaji Mama suna tattauna maganar da Ya Abdallah wanda shima ta yi mai nasiha sosai.
Haka washegari ma suka zauna da Ummi suka tattauna karshe Ummi ta kirani ta yimin nasiha mai shiga jiki.
Share this
Sunday, February 17, 2019
SAKACI Part 12
Har yau bazan manta halin da muka iske Ya Hamid ba, halin
da muka iskeshi yayi mugun d'aga mana hankali, yana kofar station
akwance cikin jini dak'yar nunfashinshi yake fita, ga k'uda sai binshi
suke da alama ya jima a haka, mutane na tsaye akanshi, ba wanda yaje
kusa dashi ballantana asamu mai taimaka mishi.
Rungumar shi Mama ta yi, cikin kuka ta ke cewa "kaga halin
da ka jefa kanka ko" yafiyar Mama kawai ya ke nema cikin mawiyacin
hali, ya ke cewa.
"Mama ki yafemin, ki nema min yafiyar ubangijina, na tuba Mama"
Ya Umar ne ya d'aukeshi Ummi ta taimaka mishi suka saka shi
a mota, hanyar asibiti Ya Umar yayi muna bakin asibitin kafin mukai ga
shiga ciki, Allah yayi ikonshi akan Ya Hamid.
Munga tashin hankali ranar, haka aka shirya Ya Hamid aka
mik'ashi gidanshi na gaskiya, duk hakuri irin na Ya Abdallah ranar sai
ya baka tausayi.
Haka muka cigaba da k'ar6an gaisuwa, ni da Mama da Ummi sai
Ya Umar da Ya Abdallah a waje ba wani cika akayi ba tunda ansan ba wani
k'arfi ne damu ba.
Baba kan bashi da masaniya domin ba wani d'an aiken da Mama
zata tura ya sanar dashi, shi kuwa Alhajin su Ya Umar baya gari, kuma
koda yana gari ma basa magana da Baban tun wani lokacin da Alhajin ya
kira Baba ya na mai nasiha akan irin ruk'on da yake yiwa iyalinshi.
Shi kuwa Baba ya rufe ido yayita fad'an maganganu na rashin kunya, k'arshe ma ya d'au gaba mai zafi tsakanin shi da Alhajin.
*****
Ranar da Ya Hamid ya cika kwana hud'u da rasuwa, muna zaune
da daddare bayan sallah magriba ni da Mama, ni ina ninke kaya, Mama
kuma na zaune.
Hassan ya shigo d'akin mu, na yi niyar guduwa don bana so
ko ganinshi nayi, zuwa wannan lokacin na tsane shi, tsana kuwa mai
tsanani.
kasancewar ina ninkewa Mama kayanta wanda na wanke mata a
yammacin ranar, ba yadda na iya haka na tsaya, domin nasan idan nace zan
shige dole Mama zata yimin magana.
Bayan sun gaisa, Mama ta d'au buta ta ce ta na zuwa, Mama
na fita yazo kusa dani ya zauna, ya cigaba da yimin kallon nan nashi na
yaudara kafin kuma yace.
"Tunda bazaki gaishe ni ba, ba damuwa dama ba wannan ne ya kawo ni ba"
Wata harara na aika mishi da ita, amma ya kau da kai tamkar bai gani ba, ya kuma cigaba da cewa.
" ina jiranki anjima" hawaye tab cikin idona nace mai "kayi hakuri rasuwa aka mana fa"
Ware hannayenshi duka biyun yayi had'e da cewa "lalle gobe
za'a sake zaman makoki" cikin tsoro na kalleshi, kad'a kanshi yayi
alamar tabbatarwa.
Shigowar Mama shi ya hanani cewa komai, amma idona tab da
hawaye, ina tausayin kaina, shin wannan wace irin rayuwa ce, k'arshe
kasa cigaba da ninke kayan na yi saboda fargaba, shikuwa cikin kwanciyar
hankali suka cigaba da hiransu da Mama.
Banyi bacci ba har wajen shabiyu na dare, sai share hawaye
kawai na keyi, sai da na bari Mama bacci ya d'auketa, na lek'a falo naga
shima Ya Abdallah yayi bacci tukunnan na fita cikin sand'a.
Ashe abinda ban sa ni ba shi ne, Ya Abdallah idonshi biyu
baiyi bacci ba koda yaga fitana yayi mamaki domin yasan ni matsoraciya
ce sam bana iya fita ko'ina da zaran dare yayi.
Tashi shima yayi yace bari yayi alwala yayi nafila ko
yasamu bacci ya d'aukeshi, sai dai yana fita sai yaga nayi harya waje,
lokaci guda hankalinshi ya tashi sai ya fara tunanin ko cikin bacci ne
na fita, bina yayi amma ga mamakinsa sai yaga na tura k'ofar d'akin
Hassan na shiga.
Mamakin abin ya bashi amma sai yace bari ya jira fitowa ta sai ya tambayeni, ya d'an jima a tsaye a wurin.
Lokaci guda yaji hankalinshi bai kwanta ba, bud'e kofar yayi a hankali abinda ya gani yayi mugun tayar mai da hankali.
Cikin gudu-gudu yaje ya taso Mama wacce tunda Ya Hamid ya rasu sai lokacin ta d'an samu bacci.
Cikin rashin fahimta Mama take tambayarshi mene ne, shikuma
yana cewa ta yi shuru yana jan hannunta, bai saketa ba sai a d'akin
Hassan.
Salatin Mama ne ya ankarar da mu, kafin kace meye Mama ta
yi k'asa ta fad'i, cikin tashin hankali mukayi kanta nida Ya Abdallah,
ganin Mama bata nunfashi nasa ihu ina cewa
"nashiga uku wayyo Mama kitashi"
Kafin kace meye wannan har matan gida sun fara fitowa,tsawa
Ya Abdallah ya daka min had'e da cewa " ki wuce kisa kaya tunda
hankalinki ya kwanta kin tonawa kanki asiri"
Komawa nayi nasa kaya ina kuka shi kuwa ruwa yake ta sawa
Mama amma sam bata farfad'o ba, mijin Ladiyon gidan mu ne yace "dole fa
sai an kai ta asibiti"
Ba tare da 6ata lokaci ba Ya Abdallah ya fita su Ummi ya
bugawa k'ofa Allah yasa Ya Umar bai tafi aiki ba shi ya d'auko motar
Alhajinsu.
Ya Umar ya na shigowa kan Hassan yayi gami da kamo ya
shak'e shi, mazan gidan sunyi iya k'ok'arinsu amma ba wanda ya iya
k'watan Hassan a hannunshi, idonshi ya kad'a yayi jazir, yana cewa.
"Saina kasheka maciyin amana azzalumi mazinaci, yau saika gane kurenka"
Ummi ce ta rik'eshi ta na kuka ta ke cewa "ba wannan zaka tsaya ba kazo ka taimaki Mama don Allah"
cikin wani irin 6acin rai ya tunkud'e Hassan har sai da ya bugu kafin kuma ya d'auki Mama cikin zafin zuciya.
Ya kuma juyo ya cewa Hassan "kai kuma zandawo gareka"
Share this
SAKACI Part 11
Bayan dawowan Ya Hamid Mama ta zaunar dashi tayi mai nasiha sosai ta kuma ce karya sake fita ko nan da kofar gida.
Kwana biyu kamar yaji fad'anta baya fita ko'ina, amma sai
ya fara wasu irin abubuwa tamkar mahaukaci, na tabbata rashin samun
kayan maye na kwana biyun da yayi ne ya maidashi hakan.
Haka muke sashi agaba muyita kuka, shima kukan yake yana kuma rok'on Mama akan ta taimakeshi.
Bayan kwana biyu kuwa muka nemeshi muka rasa, abinda yafi
tayar mana da hankali shi ne kwashe kayan abincin da yayi wanda Mama ta
siya harma da d'an kud'in da Baba ya bata da zai tafi, wanda mun san ba
kowa bane fa ce Ya Hamid.
Wannan shi ne ga samu ga rashi, ga k'arshen wata Mama bata
da albashi, munyi kuka ranar, kuma duk inda akasan za'aganshi bayanan,
haka muka kwana cikin tsananin damuwa, rayuwarmu ta koma gidan jiya.
A wannan lokacin ne kuma Hassan ya d'aukemin budurcina.
Haka kuma ya cigaba da mu'amala dani tamkar matarshi,
harzuwa wata rana da na kwana da ciwon ciki washegari da safe naje
fitsari naga jini nanfa na ringa kuka, kai tsaye d'akin Hassan na wuce
naje na fashe mai da kuka, da k'yar ya rarrasheni sannan ya tambayeni
mai ya sameni.
Cikin kuka nace " ba abinda kayi jiya bane inaga ya fasa min kayan cikina gashi sai fitsarin jini nakeyi"
A ta ke ya fahimceni, murmushi yayi irin tasu ta y'an
duniya, sannan ya zaunar dani, ya dinga fad'amin maganganu na k'arya da
yaudara.
Kasancewar bani da kawaye, islamiyya ma idan aka koremu
kud'in wata, sai mu kwana biyu bamuje ba, wannan shi ya sanya duk
maganar da Hassan ya fad'amin sukayi tasiri akaina, ak'arshe ya haneni
da karna fad'awa kowa, harda Mamana, sannan yace da nagama na fad'a mai,
na ansa mai da toh kawai.
Haka nayita 6oyewa ban bari kowa ya Sani ba, tunda Mama dama ba wuni take a gida ba.
Ranar da ya d'auke kuwa na fad'a mai, cewa yayi zaimin wani
abun da bazan k'arayin fitsarin jinin ba, tabbas na tsorata da fitar
jinin shiyasa na yarda.
Wata allura ya d'auko ya ce zaiyimin, rud'ewa nayi domin ni
sam bana son allura haka ya lalla6ani ya ce na tsaya bata da zafi, da
k'yar na yarda, tun daga lokacin kuwa ban sakeyi ba, kuma duk bayan wata
uku sai yamin wannan allurar.
****
Akwai wata rana muna zaune nida Mama ta na yimin kitso mukaji sallamar Ya Umar Mama ta na "oyoyo d'ana"
Da gudu na tashi zan rungumeshi amma sai naga yaja gefe, cikin sakewar fuska ya ce.
"wai yaushe Farida Umar zata girma ne"
Komawa nayi na zauna ina murmushi, Mama ta ce "kaima dai ka
fad'a, likita bokan turai yaushe a garin" ta fad'a da cikin sakewar
fuska.
Shi d'inma fuskarsa k'unshe da murmushi ya ce " d'azun nan "
Mama ta ce "shi ne Ummi bata fad'amin d'ana na hanya ba, kuma fa
shekaranjiya saida mukayi zancenka da ita, aikuwa har gida zan samu
Ummi"
Murmushi Ya Umar ya sakeyi sannan ya ce "Mama ai cewa ta yi idan ta fad'a miki zakiyita hidima ne"
Mama ta ce "kyale Ummi, to ina ruwanta tsakanin uwa da d'a, yanzu dai ya hanya, an kammala karatu lafiya?"
Ya Umar ya ce "munsha hanya, karatu kuma Alhamdulillah an kammala sai dai fatan samun sakamako mai kyau"
Mama tace "Allah yasa muga kyakykyawan sakamako"
Dukanmu muka ansa da "amin " sannan ya ce "Mama wallahi wannan dawowan nawa sai naga Faridana ta k'ara girma sosai"
Na ce " kai Ya Umar ? Na fad'a ina murmushi, shima murmushin yake kafin kuma ya ce " wai yanzu ajinki nawa ne ma"
" S.S 1 fa zanshiga yanzu" na fad'a, ya ce "kai Faridana
yaushe ma kika shiga school d'in gaskiya baici ace har kin kai S.S 1 ba"
Mama ce ta ce "hakane, gaskiya ta fad'a amma fa ta d'anyi
tsallake, batayi aji shida na primary ba sannam batayi aji uku na
secondary ba, a aji biyu ta zana Junior waec d'inta"
Gyad'a kai yayi had'e da cewa da alama dai Faridana mai hazak'a ce"
Mama ta ce "toh ba laifi amma kwana biyu kam tana wasa da karatuna".
Kallona ya keyi kafin kuma ya ce "wai hakane?" Sunkuyar da kaina nayi ba tare da nace komai ba, ya cigaba.
"lalle kuwa bake a tsarabata domin ni kinsani bana shiri da wanda baya son karatu, in dai kinaso mu shirya sai fa kin dage"
Cikin shagwa6a nace "na daina zan dinga dagewa, amma don Allah Ya Umar karka hanani tsarabar"
Daga shi har Mama dariya na basu, haka muka cigaba da hiran
mu, don ko abincinshi ma gidanmu Ummi ta aiko mai tare mukaci nidashi.
*********
Lokacin da Ya Umar ya dawo nayi k'ok'arin kauracewa Hassan amma abin ya gagara domin yayi min gargad'in da na tsorata dashi.
Cewa yayi bawai naga Ya Umar ya dawo ba duk ranar da nayi
k'ok'arin sanar dashi kokuwa nayi tunanin daina zuwa d'akinshi to
wallahi sai ya kasheni sannan ya kashe Ya Umar da Mama, wata bindiga ya
d'auko wacce alokacin na yi tunanin ta gaske ce, yace da ita zai
harbemu.
Tabbas bani da masoyan da suka zarce Mama da Ya Umar da na
rasa su gara na yi hakuri duk da a wannan lokacin ni sam banajin dad'in
wannan mu'amalar ga shi kullun sai kowa ya kwanta nake zuwa, ina tsoron
karna k'i zuwa ya kashemin su.
A wannan lokacin na koma mara walwala na kuma rame sannan
sam bana mai da hankalina a karatuna, ko naje aji ba abinda nake
fahimta, haka malami zai shigo har ya fita bansan abinda yayi ba, saboda
tsaban tunani da fargaban abun da ya ke min.
*********
Ya Umar kuwa ya fara bautar k'asa a Jos University Teaching Hospital (JUTH), bai fiye samun lokaci ba.
Akwai watarana ina zaune ni d'aya a d'aki Mama ta shiga
gidan Ummi, wani yaro d'an makwabtan mu ya shigo ya ce "farida wasu
mutane a waje sunce wai a musu sallama da Baban Hamid"
Na ce "su waye" ya ce shi bai sansu ba, amma dai yaga
d'ayan da kayan y'an sanda" ido waje nace "y'an sanda mai zasuwa Baban
mu" gyalena na d'auka gami da fita.
Ina fita naga matan gidanmu harda makwabta an fito gulma dama sun saba, kad'a kai kawai nayi ina mamakin irin halinsu.
Mutane biyu na gani a tsaye d'aya da kayan y'an sanda
d'ayan kuma shirt ce da jins a jikinshi, tsugunawa nayi na gaishesu
sannan nace kune kuke neman Baban mu"
Sukace "eh " nace baya gari amma bari na kira Maman mu" sukace to ma za nayi sauri.
Na samu Mama da Ummi harda Ya Umar suna zaune a tsakar gida, gaishesu na yi, Mama ta ce min.
"Ungo abincin nan ki d'ebi naki saiki barwa Hamida da Abdallah suma sud'an ta6a"
Ummi ce ta katse ta da cewa "kai Maman Hamid wato shiyasa
kika k'ici, nifa ke na bawa kici su ma ga nasu nan sannan ga buhun
shinkafa da mai can d'anki ya siyo miki an basu kud'n bautar kasa"
Albarka Mama ta yita sawa Ya Umar, "kin rufo d'akin" Mama
tace da ni, sai a sannan na tuna abinda ya kawoni, nace "Mama police ne
suke sallama da Baba suna k'ofar gida"
Dukansu suka rufamin baya muka fita, wato abinda police
d'in suka fad'a shi ya tayar mana da hankali, wai Ya Hamid sunje sata a
wani shago da asuba, garin su gudu shi aka harbeshi, yanzu yana kofar
station d'in.
Share this
SAKACI Part 10
Da safe bayan nasa uniform na shirya da zan fita sai na
tsaya a dai-dai kofar d'akinshi nayi sallama, ansawa yayi kafin kuma ya
min umarni da shiga, shi d'in ma kayan ya ke sawa da alama aiki zai
fita.
Tsugunawa nayi had'e da gaisheshi, zuwa yayi ya d'agoni gami da rungumata, ba tare da ya ansa ba.
Ganin yadda ya rik'eni yana kallona yasa nace "kawu Hassan
zan makara fa" sakeni ya yi kafin kuma yaje gefen katifarshi, naira
d'aya ya d'auko ya bani.
Kar6a na yi da sauri ina murna, sake kamani ya yi gami da
cewa "karfa ki fad'awa kowa na baki, idan an fita break ki sayi abinda
kikeso"
Godiya na mai sosai don nikam tunda nake ban ta6a zuwa da
koda sile biyar makaranta ba yau gani da naira d'aya, ai ji nake nafi
kowa ranar, ga shi dama ba wani abincin kirki mukaci da safe ba zallan
koko ne shi d'inma bashi Mama ta k'ar6a wurin mai kokon.
Koda na dawo daga school babu yunwa a cikina kasancewar nayi ciye-ciye.
Bayan magriba muna zaune nida Mama, Hassan ya shigo bayan
ya gaishe da Mama kafin ya zauna a gefe, nima na gaishe shi ya ansa
cikin sakewar fuska kafin kuma ya mik'o min naira biyar ya ce naje na
siyo mai fanta idan na siya na ajiye mai a d'akinshi.
Mama ta ce "toh ma za kije ki dawo karki tsaya wasa" na
ansa da "toh" kafin na d'au gyalena na fita, na barsu sunata hira da
Mama.
Koda na dawo ajiye mai na yi ina shirin fita ya shigo,
hannuna ya kama ya dawo dani ciki, zaunar da ni yayi a gefenshi sannan
ya ce.
"Za ki sha fanta?" Gyad'a mai kai na yi da sauri, tabbas ina son sha don rabona da sha tun Ya Umar bai tafi ba.
Cewa yayi "toh zan rage miki kinga ga tsire can ma sai muci tare ko?" Murmushi nayi wanda ya nuna tsantsan farincikina.
Katseni yayi da cewa " amma fa da sharad'in duk abinda na
umarce ki zakiyi shi, kuma idan kina yarda kullun zan dinga baki kud'in
break da irin wannan abincin, kuma inaso kimin alkhawarin bazaki fad'awa
kowa ba"
Nikam sam ban gane maganarshi ba amma dai idan zai dinga
bani abinci da kud'in break ai zan mai komai kuma bazan fad'awa kowa ba.
Katsemin tunani yayi da cewa "zo nan ki zauna" ya nuna min
gefenshi, ba gaddama naje na zauna, janyoni yayi muka kwanta akan
katifarshi ya cigaba da yimin abinda ni bangane ba amma ban hanashi ba,
ya d'auki tsawon lokaci yana wasu abubuwan da sukayiwa kwakwalwata girma
kafin kuma ya d'agani.
D'aukan fanta yayi ya sha kusan rabi kafin ya mik'omin tare
da naman naci sosai kuma naji dad'inshi, sai da na cinye tas na k'oshi
sannan na ce mai zan tafi.
Cemin yayi "karfa na yarda na fad'awa kowa, idan Mama ta
tambaye ni mai yasa na jima, nace shi ne ya ce na zauna ya ragemin fanta
da abincin, sannan ya ce gobe idan zanje school nazo na kar6i kud'i,
kafin kuma ya mik'a min wani sweet mai dad'i.
"toh"
Na ce mai had'e da yin godiya sannan na fita da murna ta.
Da Mama ta tambayeni, abinda ya cemin shi na fad'a, sai dai
abubuwan da yamin a daren yau sun tsayamin a rai inaso na tambayi Mama
meye hakan yake nufi amma ina tsoron kar ya daina bani kud'in da ya ce
da kuma abincin.
Duk yadda naso na kau da abun a raina ya ga-gara, k'arshe dai kusa da Mama na je na zauna sannan nace
"Mama nikam kawu sai ya....." Tsawa Mama ta dakamin sannan
ta ce "kin ganni nan bana son surutun banza da wofi fad'i ba'a tambayeka
ba kibarni kawai, idan kuwa baki daina yawan surutun nan ba watarana
zan cire miki hak'wara"
Tashi na yi na bar wurin na kuma ja bakina nayi shuru amma haka na kwana da abin a raina.
****
Abinda ya cigaba da faruwa kenan tsakanina da Hassan kullun
sai ya kirani ya ce wa Mama zai aikeni Mama ba ta kawo komai, watarana
da kanta ta ke aikana d'akinshi.
Haka kuma kullun sai ya bani kud'i, wani lokacin ya bani
naira d'aya da sile biyar, har naira biyu yana bani, da abinci kai harma
kayan zak'i, wannan yasa nake jure irin wasannin sa yake da jikina, har
zuwa lokacin da ya fara biyan buk'arshi ta bakina, duk ranar da ya
aikata hakan tofa wuni zanyi ina amai Mama ta d'auka tsutsan ciki ke
damuna har ta na cewa da zaran an biyata albashinta zata naima min
magani, kallonta kawai na keyi domin ni nasan inda matsalar ta ke.
Daga baya sai na daina zuwa wurin Hassan d'in ko ya kirani
bana zuwa, haka kuma na cigaba da jure zaman yunwa, har zuwa watarana da
ina zaune ni kad'ai a falo naji sallamar shi alokacin bazan iya tashi
ba saboda yunwar da nakeji domin har jiri nakeji.
Ya jima a tsaye yana kallona kafin kuma ya tsuguna a
gabana, tambayata yayi dalilin gudunshi da na keyi, ban 6oye mishi ba na
fad'a mai irin aman da nakeyi idan ya aikata abinda ya keyi.
Cemin yayi rashin sabo ne amma ba komai yadaina haka tunda
bana so, don shi baya so ya 6atawa matarshi rai, rufe fuskata na yi
saboda kunya, duk da a lokacin ba wani sanin meye aure na yi ba.
Naira biyar ya ciro a ajjihunshi ya bani gami da cewa naje
na siya wani abu naci, tabbas alokacin nayi farinciki da wannan kud'in
sannan duk wani alk'wari da na d'auka na daina zuwa wurinshi na watsar
da su, na cigaba da zuwa wurinshi amma ya daina wasa da bakina saidai ya
sunbace ni.
Wata rana da bazan ta6a mantawa da ita ba a rayuwata, itace
ranar da Hassan ya fara kawar min da mutuncina ta haryar turamin
yatsunshi, tabbas nasha wahala ranar, haka yayita rarrashina da zanbtafi
ya d'auko naira ashirin ya bani kud'in da banta6a rik'ewa ba kenan a
wannan lokacin ita kanta Mama idan ba albashi aka mata ba sai tayi sati
biyu bata rik'e ba.
Haka na dinga tafiya da k'yar na shiga d'akinmu tunda dama
baya bari na fita har sai ya lek'a yaga ba kowa a soron gidan tukunann,
yau d'in ma ba kowa domin ruwan a keyi.
Koda na shiga d'akinmu ban tarar da kowa aciki ba, neman
wuri nayi na kwanta, ban jima da kwanciya ba Ya Abdallah ya shigo, cemin
yayi " tun d'azu nake nemanki ina kikaje?"
Lokaci guda tsoro ya kamani, kar dai ace ya gane halin da nake ciki, cikin fad'uwar gaba na ce.
"daga gidan Ummi nake" gyad'a kai yayi alamar gamsuwa ba tare da ya sake cewa komi ba.
"Ina Mama ?"
Na jefa mai tambayar, a ta ke naga fuskarshi ta juye
yanayin damuwa, cikin sanyin murya ya ce "Ya Hamid ne aka kamasu, yana
can police station"
Tashi nayi da sauri gami da cewe "police station mai yayi aka kaishi can"
Azabar da naji ne lokacin da na zauna ita tasa nayi saurin komawa na kwanta.
Murya mai cike da damuwa ya ce "wai sata sukayi a kasuwa
Allah ne ma ya kare da y'an sanda zukaje da wuri domin niyar mutanan
wurin ma su k'ona su, amma kam sunsha duka akace don ni ban je ba"
Hawaye ne ya fara zubomin ina tausayin halin da muke ciki,
Mama ce ta shigo cikin tashin hankali na kalleta ruwa ya mata duka
idonta ya kad'a yayi jazir ga takalminta ma a tsinke haka take janshi,
wani irin tausayinta ne ya tsirga min.
Zama ta yi gami da dafe kanta, Ya Abdallah ne ya ce " Mama me ake ciki"
Cikin damuwa Mama ta ce "wai sai anbiya kud'in belin kafin
su sakeshi, shi abokin nashi ma na tarar da mahaifinshi acan har sun
tafi"
"Mama to ke kinada kud'in da zaki biya mai ne" na fad'a hawaye na zuba daga idona.
Mama tace "Farida Umar kenan sisin kobo bana maganinshi
amma naga Babanku a waje bari ya shigo na rok'eshi ko zai bayar" ta
k'arashe murya a raunane.
Koda Baba ya shigo Mama ta fad'a mai murmushi yayi sannan
ya ce "su rik'eshi har k'arshen rayuwarshi idan har sai na bada kud'ina
zasu sakeshi wallahi"
Yana gama fad'in haka ya shige d'aki abinshi dukanmu ba
wanda ya sake cewa komai, sai can Mama ta kalleni tace "Farida yunwa ko?
Kiyi hakuri komi mai wucewa ne, watarana sai labari" sam Mama bata gane
halin da nake ciki ba,tayi zaton yunwa nakeji.
Bata san rayuwata tashiga garari ba, washegari Mama taje
school d'in da ta ke koyarwa ta rok'esu da subata albashinta duk da ana
tsakiyan wata, sunsan halin da Mama ta ke ciki shiyasa suka bata.
Mama ta na kar6an kud'in taje tayi belin Ya Hamid daga can
ta wuce kasuwa ta siyo mana kayan abinci wanda zamu jima muna anfani
dashi da sauran kud'in, bata dawo gida da ko sisi ba.
Ranar munyi murna ganin muma ansiyo mana kayan abinci,
tundaga ranar ba k'ara zuwa wurin Hassan ba tunda daman don abinda zan
kashe yunwata nake zuwa, ga kuma abinda yayimin rannan wanda na tsorata
ainun, domin ranar haka na kwana wurin yana min rad'ad'i.
Share this
SAKACI Part 9
Sai da Farida ta yi kuka mai isarta, ba wanda ya iya rarrashinta a cikinsu domin su d'in ma hawaye su ke yi, Farida ta goge idanunta sannan ta cigaba.
**********
Haka rayuwa ta cigaba da gudana a gidan mu cikin yunwa da rashin kwanciyar hankali.
Ina da wata hud'u Innayo ta kawo ma su Mama ziyara ganin
halin da Mama ta ke ciki yasa ta samu Baba ta na mai fad'a amma ya
dakatar da ita cikin rashin kunya.
Innayo taji mamakin Baba kuma maganganun da ya fad'a sun ma
ta zafi, har ta d'aukan mai alkhawari ba zata sa ke tako inda ya ke ba,
Mama ce tayita bata hakuri shiko Baba ko a jikinshi.
Kud'i masu yawa Innayo ta ciro ta ba Mama ta ce na gadonta
ne wanda ya ke hannun Lamido amma karta yarda ta bawa Baba tayi tunanin
san'ar da zatayi, kafin ta yiwa Mama sallama ta tafi.
Mama ta samu Ummi ta nuna ma ta kud'in, ta kuma nemi
shawarta akan sana'ar da zatayi, Ummi ta bata shawarar fara siyar da
kayan anfanin gida, wanda ake anfani dashi yau da kullum.
Abubuwan da suka danganci kuka, magi, omo da dai sauransu,
domin sune zasufi tafiya da wuri, ta kuma cewa Mama zata had'ata da wa
ta ma ta awani k'auye wacce zata dinga saran kayan a wurinta.
Allah ya sawa Mama arbarka a cikin sana'arta domin ana samu aci abinci yanzu ko ba yawa za dai a ta6a a gidan.
Tun lokacin da na fara wayo na gane irin tsanar da
mahaifinmu ya mana domin su Kansu su Ya Hamid basa ta6a sakewa idan Baba
na gari dukanmu tsoronshi mukeji, bamu isa mu taka inda ya ke ba, domin
bazan manta ba, akwai wata rana, ina k'arama ya dawo daga tafiya naje
da gudu wai zanyi mai oyoyo ya tunkud'eni na fad'i, tunda lokacin da na
ganshi gudu na keyi.
Lokacin da na cika shekara biyar ne kuma komi ya lalace
domin d'an jarin Mama ya karye, duk mun cinyeshi a ciki, alokacin ne
abinda za'aci ya gagare mu.
Dama Baba ya kammala karatunshi, shekara biyu da suka
shige, ya kuma nemi aiki a Bauchi, cikin ikon Allah ya kuma samu aiki a
Mega Banka reshen jahar bauchin.
Kuma duk da haka Baba sai yayi wata hud'u biyar bai shigo Jos ba, ga shi ba wani nisa ba ne tsakanin Bauchi da Jos.
Aike ma sai yaga dama ya keyi, domin wani lokaci sai ad'au lokaci baiyi aken ba kuma da ya aiko kud'in ba wani yawa ne dasu ba.
Mama ta fara dillanci atamfofi, nan ma bashi ya fara hawa
kanta k'arshe ma aka daina bata kayan, a lokacin komi ya tsaya cak ga
shi su Ya Hamid sun isa shiga school amma ko zaman Islamiyya basu ta6a
yi ba, Mama ce ma take d'an koya musu karatu idan ta na cikin nutsuwa.
Nikam dama y'ar gidan Ya Umar ce, yawanci agunshi nake cin
abinci, domin tun ina k'arama na saba sosai da Ya Umar, Ya Umar yana
matuk'ar sona ko abinci idan aka saka mai tare dani yake ci kuma shi ne
mai koyamin karatu.
Tunda nafara wayo naji Mama da Ummi suna kirana da FARIDA
UMAR shi kuma su kirashi da Yayan Farida, akwai k'aunar mai tarin yawa
tsakanina da Ya Umar.
Ni kam ban san yunwa ba har sai bayan tafiyan Ya Umar
university a k'asar England, tabbas nayi kewarshi, ta 6angaren Ya Umar
kuwa da kyar ya tafi, bana manta irin kukan da ya dingayi, ranar da zai
tafi haka ya rungumeni yana kuka dak'yar aka rabamu.
Ya Umar ya soni tun bansan kaina ba, Ya Umar shi ne mai
hana kanshi abinci ni ya bani har sai na k'oshi, duk lokacin da yaga ina
kuka tofa idan hankalinshi yayi dubu ya yatashi, bayason ya ganni cikin
damuwa, wannan kenan.
****
Akwai wata rana da muka kwana bamuci komi ba ga shi har
yamma, Ya Abdallah kuwa ya gagara tashi ni kuwa kuka nake yi, Mama ta
samu a gaba ta yi tagumi domin bata da sauran dabara, hayaniya muka fara
jiyowa a tsakar gida kafin kuma muji kukan Ya Hamid da hanzari Mama ta
fita waje, abinda ta gani shiya tayar ma ta da hankali.
Domin matan gidan ne suka sa Ya Hamid a tsakiya daga mai
dungure mai kai sai mai zagin shi, wai sauran abincin da yaron Ladiyo ya
rage ta rufe to fa shi ne Ya Hamid ya d'auka yake ci, shi ne fa suke
cewa yayi sata, magana har waje ana cewa Hamid yayi satan abinci.
Hannun Ya Hamid Mama ta kamo kafin kuma ta bawa Ladiyo
hakuri, a dai-dai wannan lokacin Baba ya shigo koda yaji abinda ke
faruwa.
"kunsan mai ya ce"
Farida ta dubi su Dr jidda, girgiza kai sukayi, goge hawayenta tayi a karo na ba adadi kafin kuma ta ce.
"D'an iskan yaro 6arawo kana k'araminka ka iya sata, idan
abinda ka zabawa kanka kenan, to ina tabbatar maka sata itace ajalinka, a
kasheka an kashe banza, wallahi ba abinda ya dameni"
Cikin kuka Mama ta ce " mai yasa zaka dinga yiwa d'anka mugun baki? baka tunanin ya kamashi"
Da fad'a Baba ya ce "d'anki dai shasha, ina ke kinji kin gani sai kin haifesu? Toh wallahi baki ma fara kuka ba"
Yana gama fad'in haka yayi ficewarshi, kuka Mama ta ke
tamkar ranta zai fita, Ya Hamid na kuka ya durk'usa a gabanta yana ki
yafemin Mama wallahi yunwa nakeji shiyasa naci, shafa kanshi Mama tayi
ba ta re da tayi magana ba.
Ummi ce ta shigo cikin tashin hankali ta ke cewa
"Mai nakeji haka Maman Hamid, almajirina yanzu ya shiga ya ke fad'ami wai Hamid yayi sata, wai me yake faruwa ne?"
Mama na kuka ta mayar ma ta, fita Ummi ta yi ba ta re da ta
ce komai ba, cikin k'ank'anin lokaci ta dawo da abinci cikin kwano ta
sa mana a gaba yadda Ummi taga muna cin abinci saida ta zubar da hawayen
tausayi.
Kafin kuma ta ce "Maman Hamid ki shirya gobe zan kaiki
school d'in da k'anina yake shugabanci ko za'a sama miki gurbin koyarwa
tunda kinada takardar gama secondary school, don zamanki haka ba abu ne
mai yuwuwa ba"
Godiya sosai Mama tayiwa Ummi, ta kuma tabbatar samun kaman Ummi a wannan zamani sai an tona.
Ai kuwa an d'auki Mama aiki a makarartar, cikin ikon Allah
ta cigaba da kulawa damu ta kuma samawa su Ya Hamid gurbin karatu a
makarantar gwabnati, duk da hakan yasa kud'in da Mama ta ke samu baya
isan ta amma tasan ba wani gata da zata mana wanda ya wuce ta bamu
ilimi, mafi yawan lokuta haka Mama ta ke zama da yunwa mu ta bamu.
Haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya har izuwa lokacin da
nima Mama ta sakani a school tunda dama tuni ta samu a islamiyya, amma a
wannan lokacin Mama sai ta nemin aikin koyarwar rana saboda kud'in baya
isan mu wannan ne yasa idan Mama ta fita tun safe bata dawowa sai
yamma.
Yawanci lokuta nakanje gidan Ummi idan nadawo daga school
duk da gidan baya min dad'in kasancewar Ya Umar ya tafi jami'a, toh
Ummin ma ba mazauniya bace domin ta na fita aiki, haka dai nakanje idan
na gaji na dawo gida, haka zan zauna a d'aki har sai Mama ta dawo
kasancewar da na fita tsakar gida sai ansani kuka, don ma Mama
tsayayyiya ce akan mu don sun so suzamar damu bayi muyi aiki a bamu
abinci Mama tak'i sam tofa sai aka samu a gaba bamu isa fitaba sai yaran
gidan sun dake mu.
Rayuwarmu duk yawanci ta na tafiya ne a bashi domin albashi
Mama baya isa, mutane biyu ne kawai suke bawa Mama bashi a wannan
lokacin daga Ummi sai wani saurayi da ke gidanmu a d'akin soro mai suna
Hassan, ya na aiki ne da company Nasko.
Kuma Ya Abdallah yana fita yin wildbiro ko siyar da rake
idan ya dawo makaranta yawanci da d'an abinda ya samu ne muke d'an samu
ayi girki idan wata yayi nisa.
Hassan d'an d'akin Mama ne domin ya d'auki Mama tamkar
yayarsa duk wani shawara da Mama ya keyi, haka kuma idan ya samu kud'i
zai siyo su biskit da minti ya kawo min, shiyasa nake sonshi a wannan
lokacin.
Daga baya Mama ta fahimci Ya Hamid baya zuwa makaranta wasu
lalatattun yara ya kebi, Mama takan kirashi ta yimai nasiha tayi fad'an
bata san cewa abun yayi nisa ba domin ashe badda shaye-shaye da yaran
sukeyi harda sace-sace kuma tare da Ya Hamid suke komai.
A wannan lokacin Mama ta shiga wani irin hali, daga k'arshe
sukayi shawara da Ummi akan ta mai dashi makarantar kwana idan baya
ganinsu zai nutsu, amma abinda basu sani ba Ya Hamid yayi nisa domin
koda aka kaishi makarantar gudu yayi.
****
Akwai wata rana a rayuwata da bazan ta6a mantawa ba, ranar da itace mafarin komai!!
Wata yayi nisa bamu da komai a gidan asalima wunin ranar ba
muci komai ba ga shi kud'in da Ya Abdallah ya samu a dakon da yayi yasa
a ajjihunshi bai san ya yage ba duk kud'in sun zube.
Hassan ne ya shigo d'akin da sallama gani na ina rik'e da
ciki ina kuka ya sashi zuwa gareni yana tambayata mai ya sameni cikin
kuka nace mai "yunwa nakeji" cikin tausayawa ya ce zan iya binshi na
kar6i abincin, gyad'a kai nayi, hannu na ya kama muka fita Mama bata ce
komai ba.
Muna shiga d'akinshi ya d'auko abincin ya bani gami da cemin naje muci da Ya Abdallah idan mun cinye na kaimai kwanon.
Nazo ina murna muka ci abincin nida Ya Abdallah ba yadda
bamuyi da Mama tazo taci ba amma tak'i duk da yunwa da takeji amma ta
hakura.
Koda muka gama ci na d'auki kwanon na ce "Mama kawu Hassan
ya ce idan mungama ci na kaimai kwanonsa" gyad'a kai kawai mama tayi da
alama ta yi nisa a tunani, nidai na fita abuna.
Sallama nayi ya ansa sai da ya bani izinin shiga sannan na
shiga d'akin, yanayin da na ganshi ne yasani saurin sunkuyar da kai, duk
da k'arancin shekaruna nasan dai bai dace na ganshi haka ba, dagashi
sai d'an tawul d'aure a k'ugunshi.
Kamo hannuna yayi kafin kuma ya zaunar dani akan cinyarsa,
ya na mammatsa hannu na gami da shafani, sam ni bangane mai yakeyi ba
amma na dinga k'ok'arin tashi ya zaunar dani gami da tambayata na k'oshi
na ce "eh" ya ce toh gobe idan zan tafi school na lek'o zai ban wani
abu amma karna fad'a ma kowa na ce "toh" kafin kuma ya sakeni na tafi
bayan ya sunbace ni a goshi.
Ina shigowa d'aki na tarda Mama ta na tsintar abincin da
muka zubar a kasa ta na ci, bazan iya kwatanta muku yadda na keji ba
idan ina tunawa.Share this
SAKACI Part 8
Ummi ce ta shigo da sallama, da sauri mama ta tashi ta
rungumeta "ta na ga Ummi ga Ummi, oyoyo Hajiya Ummi mutanan saudiya da
India yaushe kuka dawo bani da labari"
Murmushi ne kwance saman fuskar Ummi, zama ta yi gami da cewa
"Jiya muka dawo, ai na aiko Umar aka cemai wai bakya nan"
Mama ta ce "Ummi kinganki kuwa? Kama alatsa jini ya fito" murmushi Ummi ta yi kafin kuma ta ce
"d'azu da safe Alhaji ya ke fad'amin sun had'u da Baban Hamid a masallaci y ke fad'a mai ashe Lamido sa'i yayi?"
Cikin damuwa Mama ta ce "wallahi Ummi, Lamido lokaci yayi" Mama ta k'arashe kwalla fal cikin idanunta.
Ummi ta tausaya wa Mama domin tafi kowa sanin irin k'aunar
da tausayin da ke tsakanin Mama da Lamido, a karshe tayi mai addu'a
sosai Mama na ansawa da Amin.
kafin kuma Mama ta tambayeta da "ina d'an nawa"
Ummi ta ce "sun fita da......." Bata kai ga k'arasawa ba
idonta ya kai kan wannan jik'on da ke gaban Mama, a ta ke fuskarta ta
sauya kafin kuma ta janyon kwanon alokaci guda kuma ta fara salati ta na
tafa hannayenta, sai a sannan ne Mama ta farga.
Cikin damuwa Ummi tace "Maman Hamid kamar jik'on wanke ciki nake gani" ta fad'a ta na juya kwanon kafin kuma ta sake cewa
"Wallahi shi ne, ba dai zubar da ciki kike shirin aikatawa ba, in kuwa hakan ne meye dalilinki?" Ta fad'a cikin fargaba.
murmushi Mama tayi wanda da ka gani kasan murmushi ne mai ciwo kafin kuma ta ce
" Ummi ina bukatar hutu kinga kuma ina karatu, sannan ina
ganin hidiman yara zai iya hanani karatu yadda ya kamata shi ne dalilina
na yanke wannan shawara"
Tabbas Ummi tafi Mama yawan shekaru da wayewa, ta san halin
da Mama ta ke ciki duk da Maman bata ta6a fad'a mata ba, kuma ta san
wannan ba shine dalilin da ya sa Mama tunanin zubar da cikin ba, amma
bata so ta takura ma ta da tambaya, cikin tausayawa Ummi ta ce.
"Karkiyi k'ok'arin aikata sa6o Maman Hamid, karkiyi abinda
Allah zaiyi fishi dake, Allah ba ya ta6a d'aurawa bawa abinda bazai iya
ba, Maman Hamid wannan arzik'in na haihuwa da Allah ya baki ya san za ki
iya ne, idan bazaki iya d'aukan nauyinsu ba Allah bazai baki ba, kuma
kowani yaro da arzik'insa ya ke zuwa, Maman Hamid kada tsoron talauci ko
wani abun yasa ki kashe kyautar da Allah ya baki"
Gyara zama Ummi ta yi sannan ta cigaba da ce wa.
" shin Maman Hamid bazaki godewa Allah da ni'imar da yayi
miki ba, wasu fa neman haihuwan suke ido rufe amma basu samu ba, ni nan
na isheki ishara kina gani tun daga kan Umar Allah baisa na na sake
haihuwa ba, koda kuwa 6ari ban ta6ayi ba, yau shekarun Umar goma, kina
gani duk inda akace ga magani sai naje, na ziyarci asibitoci kala-kala
amma haryanzu ba labari, dalilin hakan naje saudiya"
Maman Hamid na wa kawai kika sa ni akwai mutane da dama a
waje wanda basu ta6a haihuwan ba, amma mai yasa ke kike k'ok'arin
butulcewa ni'imar da Allah ya miki"
Sannan ta k'ara da cewa " banaso kiyi biyayya wurin sa6awa
mahaliccinki, ki dogara ga Allah, nasan halin da kike ciki, amma inaso
ki cigaba da hakuri watarana sai labari"
Kuka Mama ta dinga yi gami da istigfari, Ummi bata bar
gidan ba sai da ta tabbatar maganganunta sun ratsa Mama sun kuma
shigetatukunnan, bada 6ata lokaci ba Mama ta kwarar da maganin.
Ta kuma shiryawa fad'an Baba da kuma kowace irin azabar da zata fuskanta daga gareshi, addu'a kawai ta keyi acikin ranta.
Koda Baba ya dawo ta sanar da shi ta fasa zubar da cikin
zata haifi abinta ga mamakinta baiyi fad'an da ta ke tunanin zaiyi ba,
sai dai ya ce mata.
" Sakinatu kince ina kina son ki haife abinda ke cikinki?"
Mama ta gyad'a kai, ya cigaba da ce wa.
" toh kisani ba abinda ya dameni da abinda kika haifa kuma
karki kuskura ko da zancan wasa kiyi tunanin kwabona zaiyi ciwon kai
akan yaranki, Haram"
Ya na gama fad'an haka ya tashi ya fita, bai sa ke tayar ma ta da maganar ba.
Washegari kuwa yabar gari ba ta re da ya bar ma ta komai ba.
Tabbas a wannan lokacin Mama ta shiga wani irin hali domin
Baba bai sa ke yi musu aike ba, abinci sai dai ummi ta taimaka musu ko
kuma taje ta tsinko zogale ko Rama shine abincinsu harda gishiri cinshi
su ke yi.
A haka rayuwarsu Mama ta cigaba da gudana har lokacin da ta
haihu wannan karan ma ba abinda Mama ta tanada ga me da kayan haihuwa
gabshi wannan karan mace ta haifa, Allah ma ya sa a gida ta haihu ta re
da taimakon wata ungozoma, tabbas Mama ta sha gulma da habaici a wurin
matan gidan.
Abinda yafi damun Mama shi ne Baba na gari ta haihu kuma
bayan haihuwan ma ya shigo gidan amma ko kallonta baiyi ba balle abinda
ta haifa, da k'yar ta tashi taje gabanshi saboda tsananin yunwa da ke
d'awainiya da ita, ta ce.
"Don Allah kataimaka mana da abinda zamuci wallahi yunwa na keji ga kuma yarinyan nan ba ko wandon da za'a saka ma ta"
Tsaki Baba yaja kafin kuma ya tashi yayi hanyar fita, cikin k'aramar murya Mama ta sa ke ce wa.
"don Allah ka taimaka min badan halina ba wallahi har jiri nakeji"
Ba tare da ya juyo ba yace "zan turo muku da kayan abinci
amma batun abinda kika haifa karki sake kawo min maganar da ta dangance
su, wannan matsalarki ce ba tawa ba domin mun dad'e da wannan maganar"
Yana gama fad'an hakan yayi ficewar shi, haka yarinyar ta
cigaba da zama da zani har washegari, har sai da Ummi tazo ita ce ta
siyowa yarinyar kayan da aka saka ma ta.
Ranar suna da Mama ta tambayeshi sunan da za'a rad'awa
yarinyar da fad'a suka rabu ya ce ba abinda ya dameshi, sai wannan
lokacin mutuwar Lamido ta dawowa Mama sabuwa, aranar Mama tayi kuka
harta godewa Allah, k'arshe har washegarin suna ba'a rad'awa yarinya
suna ba.
Dama maganar yanka kam babu shi domin sauran ma Lamido ne ya musu.
Bayan Ummi ta shigo ne Mama ta ke fad'a mata ta kuma ce ta za6a ma ta suna, Ummi ce ta za6amin suna Farida ba mahaifina ba.
Farida ta k'arashe ta na kuka sosai, karshe magana ma gagarta yayi sai da ga bisani