Barka da zuwa shafin AYSHA ADAMAWA (Maman Sultan) Wannan Shafin na bude shine domin saka Littattafan hausa na soyayya, yake yake, hikayoyi. KU KASANCE DAMU DAN SAMUN NISHADANTARWA DA FADAKARWA. AYI KARATU LAFIYA.
"Jiya bayan sallar isha'i, mun fito daga masallaci nida
Alhaji, muka had'u da kawun shi Ahmad, bayan mungaisa, ya ce ya zo ne
akan batun aurenku, mukace muna saurarensa, yace dama suna so a d'aga
d'aurin auren"
"Nidai ban iya magana ba, ga Alhaji nan shi ne yace toh mai
yasa basu fad'a da wuri ba sai da aka gama gayyatan jama'a, sai shi
kawun nashi yace shi dai d'an aike ne"
"Alhaji ya sake cewa toh idan an d'aga har zuwa yaushe ne,
sai kawun nashi yace zuwa lokacin da suka kammala shirye-shirye amma
idan kin samu miji kafin nan toh fa kar a jirasu a aurar da ke"
"Tabbas alokacin da zan fad'i na tabbata zan rasa wani 6ari
na jikina, ni nasan na yi *SAKACI* tun farko amma ance danasani k'eya
ce"
"Waya na d'auko da zummar yin kira amma Alhaji ya ce wa zan
kira nace zan fara sanar da jama'a anfasa ne, Alhaji yace min waya ce
anfasa, tabbas gobe za'a d'aura miki aure"
"Nace anya Alhaji kaji abinda mutanan nan suka ce da kyau
kuwa, yace yaji, kuma abinda ya fad'a d'in ma ba fashi za'a d'aura miki
aure amma wannan karan ba da Ahmad ba, da Umar za'ayi"
"Nace wa Alhaji hakan ba zai yuwuwa ba, ba za asashi dole ya aureki ba sai dai idan ya yarda, zai aureki"
"Umar d'an albarka ne, yaron nan ana zuwa mai da maganar ya
amince ba gardama, ya kuma k'ara da cewa, basu isa su wulakantaki ba,
idan dama niyarsu kenan"
Baba ya d'an dakata kafin ya d'aura " Farida bani da abinda
zan sakawa bayin Allah nan dashi sai addu'a, sunyi min komai, kuma ina
rok'onki don Allah kiyiwa Umar biyayya, Allah sarki Sakinatu"
"Ki yafemin d'iyata ni ne silar komai, da badan na yi
*SAKACI* da baku kulawa ba da ba wanda ya isa ya wulak'antaki, ki yafe
min"
Hawaye ne yake zuba daga idanuwanshi yana gogewa, bayan Baba yayi shuru Ummi ta ce.
"kiyi hakuri Farida, nasan an tursasaki amma kiyi biyayya"
Saurin zuwa ta yi ta rungume Ummi gami da cewa "haba
iyayena mai yasa zaku dinga rok'ona bayan ni kuka rufawa asiri, ni kuka
taimakawa alokacin da kowa yake guduna"
"Mai yasa zakuyi tunanin zan bijire muku, wanda yafi dacewa
da ya bijire ya muku biyayya ni wace ce da zan bijire, ku yanke duk
hukuncin da kukaso akaina ni kuma zaku sameni mai biyayya agareku, na
yarda da kaddarata Baba kadaina damun kan ka haka Allah yaso"
Dukansu sai da sukayi hawaye, Ummi ta rungumeta ta na cewa
"Allah ya miki albarka d'iyata gidan yayanki shi ne gidan da za ki zauna
hankalinki a kwance ba ta re da an goranta miki ba"
Haka Innayo suka yi ta yiwa su Ummi addu'a, sannan a karshe suka sawa Farida albarka.
****
Lokacin da Mariya taji labarin auren babbar hauka ce kawai batayi ba, kuka ta ke tamkar mahaukaciya ta na cewa.
"Wallahi ka munafurce, saboda ni baka d'auken da mutunci ba Dr sai yau da za'a d'aura auren ne zaka fad'a min"
Cikin rarrashi Dr yace "Mariya bani da nufin 6oye miki, abun ne yazo a kurarren lokaci kiyi hakuri"
"Cike da rashin kunya ta ce " wallahi k'arya ne, ai dama
tunda naga ka gina wannan gidan harda yin wani shashi kace na iyayenka
ne, wai ni zaka munafurta"
"Kuma idan ba cin amana ba ka rasa wacce zaka aura sai ita,
tabbas nasan karshen zamana a gidan nan yazo, kuma Allah ya isa
tsakanina da ku"
"Mariya wa kikewa Allah ya isa" Dr ya fad'a cikin hasala, cike da rashin kunya tace "da duk wanda ya ke da hannu aciki"
Ba zai iya cigaba da sauraranta ba dan zai iya aikata
abinda baiyi niya ba, don haka yayi fitarshi ko bi ta kanta bai sake ba,
aikuwa fitan nashi da dad'a tunzurata.
A ranar ta tattara yaranta su uku ta koma gidansu.
Fad'a sosai akayi tsakanin Alhaji da abokinshi, shi Alhaji Sama'ila gani ya ke Alhaji ya wulakanta mai y'arshi.
Yace kuma ta yi zamanta bazata koma gidan Dr ba, ba yadda
ba'ayi dashi ba yace idan har anaso d'iyarshi ta koma toh fa sai dai a
warware wannan auren, shikuwa Alhaji ya ce tasha zamanta.
****
Da daddare aka kawo Farida d'akinta bayan tasha kuka sosai,
shashin da Dr ya gina a matsayin na iyayenshi idan suka zo Bauchi nan
ne aka sa Farida, bayan anyi mata jere.
Kowa sai yaba tsaruwa gidan ya ke, kwata-kwata mutanan gidan basu wuce wata guda da tarewa a ciki ba.
Gidan ba wani girma ne dashi na tashin hankali ba, gida ne
dai-dai misali amma ya tsaru matuk'a, yana d'auke da sassa uku, kuma
ajere suke, na maigidan shi ne a tsakiya, sai kuma d'akin masu aiki a
baya.
Bayan y'ankawo amarya sun tafi, ya rage saura amarya ita d'aya.
Har wurin karfa sha d'aya na dare ba ta ga idon ango ba,
toile ta shiga ta d'an watsa ruwa ko ta d'an ji dadi a jikinta, rigar
bacci kawai ta saka, ta gaji tana bukatar ta kwanta, aikuwa bata jima da
kwanciya ba bacci ya d'auke ta.
Ba ita ta tashi ba sai da asuba, taso ma ta makara don haka a gurguje ta shiga toilet ta d'auro alwala.
Bayan ta idar da sallah, ta jima ta na azkar d'inta kafin
kuma ta d'auko qur'ani ta cigaba da karatunta, sai da gari yayi haske
sannan ta ajiye qur'ani bayan ta yi addu'a.
Bayan ta fito daga wanka ba ta wani tsaya yin kwanliya ba,
powder kawai ta murza sai man baki, kafin kuma ta zura doguwar rigar
atamfa.
Da gyara gado ta fara gami da kintsa wasu abubuwa kafin kuma ta fito falo, wanda tsaruwarshi ya burgeta
"Falon ba wani girma ne dashi can ba, d'an madai-daici ne
amma fa ya tsaru, ba'a zuba mai wasu tarkace ba, duk yadda ka kalli
falon sai yabaka sha'awa.
Falon yana d'auke da d'akunan bacci biyu ko wanne da toilet
aciki, sai kitchen shima madedeci mai kyau, lek'awa ta yi ta ga komai a
kintse.
Wannan fa duk kayan da Dr ya siyamin ne bai san gidanshi za'a kawo ba, tabbas Dr ya iya za6e" ta fad'a zuciyarta.
Ledar da ta gani akan fridge d'in ne ya d'au hankalinta,
zuwa ta yi ta bud'e, gashashshiyar kaza ce a ciki, ga kuma ledar juice
da ruwa agefe, tabbas ya shigo bayan ta kwanta.
Cirewa ta yi a ledar ta juye akan faranti mai fad'i, sannan
ta sakashi a cikin fridge had'e da kunnawa, su juice d'in ma ciki ta
saka su.
Ta gama share gidan had'e da kunnna turaren wuta ko ina ya
d'au kamshi, shigowa yayi sanye da farar jallabiya, fuskarshi sai wani
shek'i ta ke, wannan kamshin na shi na ko yaushe ya na tare da shi.
Sunkuyawa ta yi had'e da gaisheshi, ya ansa da "lafiya" fuskar nan a tamke, kafin kuma ya ce
"Ya kika tashi, da fatan ba wata matsala?" "Lafiya lau, Alhamdulillah" ta ansa, ya sa ke cewa.
"Madalla, idan kina buk'atan wani abu sai ki kira ni a waya" ya na gama fad'an haka ya yi ficewarshi.
Kama baki ta yi gami da cewa "lalle akwai aiki ja agaba na,
toh yanzu haka zamu cigaba da zama da bawan Allah nan, tabbas ina
bukatar juriya da hakuri".
Ranar dai bata yi zaman kad'aici ba domin jama'a da dama
suna ta zuwa, shi kuwa gogan ba ta kuma sakashi a ido ba sai washegari
da safe.
Kullun da safe zai shigo yaga lafiyanta haka duk wani abun
buk'ata na gida da yasan za'a buk'ata ya na aiko ma ta, amma har wannan
lokacin ba sakewan fuska kuma ba wata magana ta fahimta da ta shiga
tsakanin su.
****
Kwanan Mariya hud'u ta dawo, ba ta re da anje biko ba, shi
kanshi Dr sai da yamma ya ga yaran, kuma bai lek'ata ba, halin ko
inkulan da ya nuna akanta ya dad'a sawa taji ta tsani Farida.
Satin Farida d'aya a gidan Dr amma har wannan lokacin bai
ta6a kwana a d'akinta ba, da yamma ta na zaune kallo ta keyi, wayarta ta
yi k'ara ta na dubawa ta ga number shi ne, ma6allin ansa wayar ta latsa
kafin kuma ta kara a kunnenta.
"kije elpis (asibitin shi) akwai marasa lafiya ki dubasu, idan kingama ki jirani akwai surgery da zamuyi" cewar Dr.
Dama ta gaji da zaman gidan don haka da murnarta ta shirya ta fita.
Bayan ta gama duba marasa lafiya ta d'an fito wani wurin da
sauran likitoci suke zaune ta zauna anata hira da ita, ganinshi ta yi a
gabanta fuskarshi a tamke ya na aika ma ta da harara sunkuyar da kanta
k'asa ta yi.
Cikin maganarshi ta isa ya ce "ki sameni a office" oh ita
ya zatayi da bawan Allah nan, tashi ta yi ta bishi jiki babu k'wari, ta
na addu'ar Allah yasa ba laifi ta yi ba.
*It hurt to think that you're not here anymore, ...it's has
been 10years since you left us UMMINA, but the memory of your humble
personality will remain a scar in our heart , Allah sarki uwa tagari
Allah yamiki rahma ke da sauran musulmai....Death change everything!
Time change nothing*
kuyi ma mahaifiyata addu'a da bakin Ku mai albarka.
*****
Ranar lahadi Ahmad ya dawo murna sosai masoyan nan suke, ranar da ya zo wurinta tamkar kar su rabu.
Ahmad matashi ne wanda ba zai wuce d'an shekara talatin da
takwas (38) ba a duniya, dogo ne fari, mai cikakkiyar kamala, siriri ne
mara jiki.
Su biyar mahaifansu suka haifa, kuma shi kad'ai ne namiji duk sauran mata ne.
Mahaifinshi Alhaji Ibrahim mai naira, ya mutu yabar musu
arziki, domin shi d'in d'an kasuwa ne, sannan ita kanta mahaifiyarshi
Hajiya Indo ba ta zauna ba, itama y'ar kasuwa ce sosai.
Ahmad ma kasuwancin ya keyi ba ma a gida Nigeria ba, yana saro kaya har daga k'asashen k'etare.
Wannan kenan.
Bayan dawowan Ahmad ansa ranar bikinsu shi da Farida sati uku masu zuwa, murna a wurin masoyan nan ba'a magana.
Shirye-shirye ake ba kama hannun yaro, Ummi da kanta ta gayyato kawarta daga Sudan domin a gyara ma ta amarya.
*****
Kwance ta ke akan gadonta, hankalinta na ga labaran da ta ke kallo a tashar BBC,
Iya ce ta shigo da sallama, Farida ta ansa, Iya ta ce "uwar d'akina Dr yazo yana falo ya ce na kiraki"
Gabanta ne ya bada rasss yau kuma da me yazo, karfi hali ta yi gami da cewa " Iya kice ina zuwa"
Sanin halinshi yasa hijab kawai ta zura ta fita, ya na zaune ya kame akan kujera, waya ce a kunnen shi.
Sai da ya gama wayarshi, sannan ya kalleta na d'an wasu dak'iku, kafin kuma ya ce.
"Banso ace na sa ke shiga wani abun da ya shafi rayuwarki ba, amma kiyi hakuri zan yi miki tambaya"
"Kina ganin za6in da kikayi hankalinki ya kwanta da shi,
kin tabbatar zai rik'eki amana, sannan baza ki fuskanci wata matsala
daga gareshi kokuma wani nashi ba, zuwa gaba"
Tabbas wannan tambayoyin nashi sun yi ma ta tsauri, ita
kanta ta na yawan yiwa kanta irin wannan tambayoyin, amma toh zata
cigaba da zama ne haka, sanin kanta ne rayuwarta ta jima da 6aci ba ta
da sauran wani jin dad'i.
"Yi hakuri da shishshigin da na yi miki, ga wannan" key ya ajiye ma ta a gabanta, ficewa yayi ba tare da ya jira cewarta ba.
Ba ta iya cewa komai ba, komai ya tsaya ma ta, lalle ta na bukatar mafita.
Ta jima ta na zaune a wurin kafin kuma ta janyo key motar da mamakinta ta ga wani key na daban wanda ba nata ba.
Ita a zaton ta key matar ta ce ko angyara tunda dama ya
aiko an kar6in key motar tun washegarin, "Allah sarki Ya Umar" ta fad'a a
fili.
Fita harabar gidan ta yi, mota ta hango an fakata sai d'aukan ido ta ke, kai tsaye can ta nufa da murna.
Motace mai kyau ta zamani, bud'ewa ta yi gami da shiga,
k'amshin shi na koyaushe wanda ya ke sawa ta shiga wani irin yanayi aduk
lokacin da ta shak'a.
Rufe idanunta ta yi a hankali, cikin wani irin yanayi, ita
sam ba ta gane wa kanta Ahmad shi ne wanda ta keso amma mai yasa aduk
lokacin da taga Dr koda kuwa k'amshin shi ta shak'a ta ke shiga wani
irin yanayi.
Ajiyar zuciya ta yi kafin kuma ta bud'e idanunta, a
hankali ta sauke su akan wasu takardu, da alama na motar ne, bud'ewa ta
yi.
FARIDA UMAR shi ya fito 6aro-6aro a rubuce, "ashe Dr zai
iya cigaba da anbata na da wannan sunan" wani lokaci Dr ya na bata
mamaki, idan yayi wani abun tamkar ba shi ba.
Ta na so ta mishi godiya amma ta na tsoron fad'anshi, haka
ta hakura sai dai text da ta tura mai ta waya, bai turo ma ta da ansa
(reply) ba, da ma batayi tsammanin reply d'in shi ba.
Su Baba da suka ga motar sosai sukayi farinciki a ta ke ya kirashi yayita samai albarka.
****
Ana sauran sati d'aya bikin, Hajiyar Sudan ta iso ta fara gyara amarya, dama tuni Farida ta d'auki hutu a wurin aikinta.
Amarya kam sai godiyar Allah ta sha gyara ciki da waje har ta gaji, tsayawa fad'an irin kyawun da ta yi 6ata lokaci ne.
Ranar laraba gida ya cika makil da y'an uwa, mutanan Wase
da na gombe harma da na jos sun fara hallara, sai hidima akeyi gwanin
sha'awa.
****
Wai mai yasa zuciyarshi ta keyi mai zafi ne, shin wai meke faruwa kar dai maganar Faridanshi ta zamto gaskiya.
"Kai ba haka bane, tayaya zanyiwa wacce nafi k'auna bakin ciki don ta cigaba, No tausayin halin da zata shiga na keyi"
Ya kasa zaune ya kasa tsaye, damuwa ta mai yawa, sam ya
rasa tudun dafawa, "Dr kiranka fa ake a waya" Mariya ta katse mai
tunani.
Cikin kasala ya d'auki wayar, ita kam kwana biyu ta rasa
gane mishi, sam bashi da walwala a y'an kwanakin nan, girgiza kai kawai
ta yi gami da fita.
****
Tun ranar da ya kawo ma ta key mota Farida bata sa ke sa Dr
a idanunta ba, ta na so ta gan shi ko dan ta nemi gafararshi amma abun
ya gagara sai dai kayan d'aki da ya aiko dashi na kayan su kujeru kayan
kallo da sauransu, a ranar Farida sai da ta yi kuka had'e da dana sanin
anbatar shi da munanan kalamai da ta yi.
"Tabbas Dr ya rik'e amanar Mama nikam na kasa rik'ewa" abinda Farida ta ke fad'a kenan ta na kuka.
Ranar alhamis da yamma labari ya riskesu cewan Dr ya yanke jiki ya fad'i a asibiti, hankalinsu ya tashi matuk'a.
Ta re da ita aka tafi asibitin amma suna shiga kallo d'aya
ya ma ta ya kau da kai bai sa ke kallonta ba, ita kam tasan Dr ya
tsaneta kuma ko ganinta baya son yi.
Zuwa ta yi ta durk'usa da gwuwowinta a gaban gadonashi ta na kuka ta ce
"Yayana ka yafemin na yi kuskure ka yafemin, bazan k'ara
ba, wallahi ni kad'ai nasan rad'ad'in da na keji idan na tuna yayana
yana fushi dani, kayi hakuri na tuba"
Ummi ce ta d'aga ta kafin kuma ta ce "Farida Umar karki damu Yayanki zai yi hakuri kwantar da hakalinki"
Shi kuwa Dr kau da kansa yayi bai sake kallon inda ta ke ba har suka tafi.
Likitoci sunce damuwa ce ta yi mai yawa, Ummi da Alhaji har
ma da Baba suka saka shi a gaba suna so ya sanar dasu damuwarshi amma
ya ce shifa babu abinda yake damunsa.
Da fad'a Alhaji ya ce " zaka raina mana wayo kenan, ka yanke jiki ka fad'i sannan ka ce ba komai"
"Alhaji ba komai fa gajiya ce ta sani na fad'i ba wani abu ba" sun jishi ne kawai amma ba don sun yarda ba.
*26.3.2016*
Jama'a da dama suka shaida d'aurin auran Farida da angonta.
kakaninta ne suka sata a tsakiya sai tsokanarta suke, ita
kam sam hankalinta baya wurinsu tunanin rashin samun wayar angonta ta
ke.
Tun jiya da safe rabonsu da yin waya ga shi ta gwada duk wayoyin shi a kashe.
Aunty ce ta zo ta ce taje su Baba suna kiranta a falo,
gyale Aunty ta yafa ma ta had'e da ruk'o hannunta jama'a sai yaba
kwalliyarta suke.
Zama ta yi a kasa gami da gaishe su, Alhajin su Dr ne, da
Ummi sai Innayo da kaka ta gombe sai kuma Baba da Aunty, dukansu da ka
kallesu kasan suna cikin farin ciki, Alhaji ne yayi gyaran murya, kafin
kuma ya fara magana kamar haka.
"Yau rana ce ta farinciki a garemu, mun godewa Allah da ya nuna mana wannan rana"
Ya d'anyi shuru sannan ya cigaba
"Farida duk wani d'a nagari yana biyayya ga iyayenshi a duk abinda suka umarce shi idan bai sa6a koyarwa addini ba.
A washegari Ummi tazo Bauch, ta ce ita bata ga dalilin k'in amincewar Dr ba, zanyi ta zama ne ba aure ai bai isa ba.
Shi kuwa ya ce "Ummi ni bazan hana Farida yin aure ba, amma badai wannan yaron ba"
Ni kuma nace shi nake so, Dr ya ce tofa sai dai na mutu banyi aure ba amma nasa a raina ba zan ta6a auran wannan yaron ba.
Cike da 6acin rai na ce " me yasa kake son kanka da yawa, wannan zalunci ne da mugunta" cike da 6acin rai Dr ya kalle ni ya ce
"Yau ni kike jifa da mugayen kalamai Farida"
Tsawan da Ummi ta yi mana yasa mukayi shuru, kafin kuma tace
"ashe mu bamu kai matsayin da zaku saurare mu ba"
Kai Yayan Farida kaga bana son fad'an rashin gaskiya, banga
dalilin hanata auren wanda ta keso ba, baka isa ba, kaji na fad'a maka"
Ba ta re da ya sa ke cewa komai ba yayi ficewarshi, Ummi ta cewa Baba ya nemi yaron ya sanar mai ya fito.
Baba kuwa yace shi a ganinshi tunda Umar baya so na hakura,
Ummi ta ce Umar yayi kad'an, aure ne ba fashi, idan shi bazaiyi ba zata
samu Alhaji.
Baba ya ce ba komai Ummi za'ayi ba sai anyi haka ba.
Baba da kanshi ya nemi Adamu, sai dai kuma ranar da muke sa
ran zuwan magabatanshi, da safe ina zaune a d'akina laptop ce a gabana,
naji alamar shugowar sako, abinda sak'on ya k'unsa yayi mugun tayar min
da hankali.
Wayar na d'auka na fita falo, Aunty ce da Baba suke ba Dr hakuri akan ya amince tunda na kafe sai Adamu.
Cikin ladabi ya ce "Baba ba wai bana son Farida ta yi aure ba ne, akwai abinda na ke jiye ma ta..."
Katse shi na yi gami da cewa "Ku daina bashi hakuri ai
burinshi ya cika ya je ya sanar da Adamu tarihin rayuwata, Adamu yace
ba zai auri macen da ta zubar da mahaifarta a titi ba"
Na k'arashe da kuka, dukan su jikinsu yayi sanyi, Dr ne yayi karfin halin cewa.
"kina tunanin zanje na fad'a mai wannan maganar, to meye ribata idan na fad'a"
"Kai kasan ribar ka, Umar bansan bakar zuciyarka ta zarce
tunanina ba, mugu azzalumi sai muntsaya agaban Allah, kuma na rok'eka da
Allah idan kai musulmi ne ba kafiri ba ka fita a rayuwata hakanan"
Ina gama fad'an hakan na yi ficewata ba ta re da na saurari Baba da ya ke ta min magana ba.
Tun daga ranar bama ga maciji da Dr kuma naji labarin har
kwanciya sai da yayi a asibiti Baba yayi-yayi naje na ba shi hakuri
nak'i.
Wannan ne silar 6atawa ta da Dr har zuwa wannan lokacin, amma bai fasa duk wata hidima da ya saba yimin ba.
****
Na san zakuso kuji meye dalilin da yasa duk wani saurayin da ya fito da niyar aurena k'arshe sai ya fasa .
Kawata wacce na yarda da ita, na amince da ita, na d'auketa aminiyata, itace ta ha'inceni "Mansura".
Ban san mai na mata taza6i ta k'untata rayuwata ba, ban ta6a yin k'awance ba sai akanta amma ta koyamin darusa da dama.
Dr shi da kanshi ya je ya binciko hakan, domin Ummi da
Alhajinshi sun d'auki fushi da shi sosai, Ummi ko gaisuwarshi ba ta
ansawa, wannan ne ya sa ya shiga tashin hankali mara misaltuwa.
Bayan da na samu labarin na yi k'okarin neman yafiyanshi
amma sam yak'i saurarata, tabbas nasan Dr mutun ne mai zuciya amma ban
san, abin zaiyi tsanani har haka ba.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, ban sa ke sauraran wani
saurayi ba sai acikin wannan shekarar da muka had'u da Ahmad d'ina abin
sona abin k'aunata, wanda ya amince na zama abokiyar rayuwarshi.
Wata rana naje F.W.A Store (Store mallakin masu Fikrah)
anan muka had'u da Ahmad, hakuri tausayi da nacinshi yasa na amince mai,
har kuma na kamu da soyayyarshi.
Sai dai wannan karan tun farkon had'uwarmu Baba ya sanar
dashi komai dangane dani, Ahmad ya tausaya min k'warai ya kuma ce idan
dai ta shi ne zai aureni ya kuma zauna da ni bisa amana.
Amma Baba ya ce ba'ayi haka ba dole ya sanar da magabatanshi, mahaifiyarshi ita kad'ai ta rage mahaifinshi ya jima da rasuwa.
Ansha wahala kafin ta yarda ya aureni, amma da sharad'in
sai ya had'a mata biyu tunda ni ba haihuwa zanyi ba, dukan mu mun amince
akan hakan tunda ni k'addara ta haka tazo dole na kar6eta hannu biyu.
Yanzu haka Ahmad na dawowa za'a fara shirye-shiryen biki.
Wannan shi ne tarihin rayuwata.
****
Jidda ta ce "kawata tabbas kin fuskanci jarabawa kala-kala Allah yasa kin cinyesu, na tausaya miki k'warai da gaske"
Maryam ta ce "Dakta Allah yajikansu Mama ya gafarta musu,
wannan labari naki Izna ce ga mu y'an baya ina rok'on Allah ya miki
kyakykyawan sakamako"
Duka suka ansa da "Ameen" kafin Jidda ta ce "amma fa kawata
sai yanzu na fahimci tsakaninki da Dr Umar, tabbas Dr masoyinki ne na
gaskiya"
Maryam kuma ta ce "wallahi Dakta ina miki sha'awar Dr, dama kuyi aure"
"Mu dage da addu'a Maryam ni kaina ina sha'awar hakan wallahi" Jidda ta fad'a.
"Hmm" kawai Farida ta ce, gami da cewa "Ku tashi muje muyi sallah.
Ranar farko da Dr ya fara ganinshi ya zo hira, naga 6acin
rai, domin korata yayi gida sannan ya cewa Adamu kar ya sake ganin
kafarshi a kofar gidanmu.
Wannan bai isheshi ba har sai da ya biyoni gida ya dinga
sirfamin kwandon fad'a tamkar wacce ta aikata sa6o, nikam saboda haushi
ma ko kulashi banyi ba.
Kuma na k'udiri aniyan duk maitar shi bazan rabu da Adamu
ba domin banga dalilin da zai dinga shiga rayuwata haka ba, ina shi ga
matarshi harda yara biyu (khalil da Ammar) ga cikin na uku, wato ni ce
zan zauna haka.
Haka ya gama fad'an shi ya tafi, yana fita kuwa na kira Adamu mukasha hiran mu, na kuma ce mai ya cigaba da zuwa.
Koda Mansura tazo na fad'a ma ta halin da ake ciki k'ara zugani ta yi akan karna yarda, na kuma na d'auka.
Sam ban sanar da su Baba ba, domin nasan duk bayanshi zasu bi.
****
Wata rana da yamma Adam ya yi min waya gashinan akan hanya, murna fal cikin zuciyata.
Ba tare da 6ata lokaci ba na shiga toilet na yi wanka gami
da tsantsara kwalliya mai d'aukar hankali, har mamakin kaina na keji
domin ban ta6a yin irin wannan kwalliyar da sunan zuwa zance ba.
Ina kan gyara d'aurin d'an kwalina wayarshi ta shigo d'auka na yi, ya sanar dani gashi a waje.
Turare na fesa gami da yafa gyalena, na fita, yana jikin
motarshi, ya na jifa na da wani mayaudarin kallonshi, bazan iya jure
irin wannan kallon ba, kallo ne wanda ya ke tuno min da mutumin da nafi
tsana a rayuwata.
k'arasawa na yi, ya min umarni da na shiga motar na ce a'a a tsayen yafi, bai min musu ba.
Muna cikin hiran ne na ke mai zancen turo magabata, na lura
duk lokacin da na mai zancen ya turo sai ya bada uziri, aikuwa hakance
ta sa ke faruwa cikin rashin jin dad'i na ce mai
"Gaskiya Adamu ban gane maka ba, karmu yaudari kan mu idan abinnan ba zai yuwu ba karmu 6atawa kan mu lokaci"
Nan fa ya fara rarrashina ya na min dad'in baki "Farida ina
tsananin sonki, ki daina saka damuwa a ranki ni d'in nan naki ne, akwai
abubuwan da nake jira ne amma da zaran sun kammala zan turo magabata
na"
Na ce "maganar gaskiya Adamu na fara sarewa da lamarin nan nifa gani nake kamar abin nan bazai yuwu ba"
"Ba ki yarda dani bane Farida, zo kiji yadda zuciyata ta ke bugawa, wannan shi zai tabbatar miki da irin son da nake miki"
kamani yayi yana k'ok'arin rungumeni, banyi aune ba naji ya
na k'ok'arin had'a bakinshi da nawa, ina k'ok'arin k'wacewa amma karfi
namiji da mace ba d'aya ba.
Wani irin fizga naji anyi min har sai da hannu na ya ansa, ban ankara ba naji anyi jifa dani a k'asa.
Shak'ar wuyanshi yayi, wanda da k'yar Adamu yake fitar da
nunfashi, ihu nake ina wayyo zai kasheshi, Baba ne ya fito a sukwane ya
rik'e hannun Dr yana
"Don Allah Umar ka sake shi kar kayi kisa, rok'onka na ke" tun kud'eshi yayi har sai da ya bigi motarshi.
A sukwane Adam yaja motarshi ya bar gidan mu, Baba ne ya
kama hannun Dr idanunshi sun kad'a sunyi jazir, Aunty ta ruk'o hannuna
muka shiga falo.
Baba ne ke tambayar abinda ya faru, Dr bai iya cewa komai ba, ni ce na fashe da kuka.
Dr ya ce "gwara ma ki yi shuru domin na sake ganin kafar yaron nan a gidan nan sai na karyashi kafin na mik'ashi ga hukuma"
Ga mamakinsu tashi tsaye na yi gami da ce wa "idan ka isa
shegiya nake, wai kai wani irin mugu ne da kanka kawai kasani, toh wlh
baka isa ba"
Maganar gaskiya naji zafin abinda Adamu yamin kuma nasa
araina dole na hukuntashi, amma kuma lokaci yayi da zan nunawa Dr na
gaji da mulkin mallaka.
Baba ne ya daka min tsawa, cikin 6acin rai Dr ya ce "Baba
kyaleta ai idan ba ta yi hakan ba baza ta nunamin ita ishashshiya ce ba,
toh ki gama duk abinda za kiyi amma wannan yaron kun rabu kenan"
Cike da rashin kunya na ce " ka ma isa, ka na wani abu tamkar ubana, toh wallahi ka ta6a shi sai kayi dana sani"
Tasowa yayi ciki karaji da niyan dukana, nima na tashi da hanzari gami da d'aukan kujera na ce "kana ta6ani ina sauke maka aka"
K'arar fad'uwar Baba ne da salatin Aunty ya ankarar damu,
lokaci guda mukayi kanshi, Dr shi ya kama Baba ya sashi a mota bayan ya
mai temakon gaggawa ya farfad'o.
A motarshi yasa Baba ni kuwa motata da Dr ya siyamin na shiga, na bisu a baya,domin ba zanyi gangancin shiga motarshi ba.
Washegari Baba yayiwa Ummi waya domin dukanmu mun kafe akan ra'ayin mu.
Sai bayan Isha'i Dr ya shigo gidan, nikam ina d'aki wani kunyarsu yanzu nake ji, Ummi ce ta k'wallamin kira.
Ba dan inaso ba na fita dan kawai bani da yadda zanyi ne, hijab d'in da na yi sallah shi na mayar na je kiran Ummi.
"Ummi gani"
Na fad'a cikin wani sabon ladabi da na samawa kaina.
Cikin sakewar fuska Ummi ta ce Yayanki za ki kawowa abinci"
"toh " nace had'e da bin hanyar da zata sadani da madafin.
Bayan na ajiye abincin ne, na bud'e fridge domin d'auko ruwa, na tsinkayi muryar Ummi ta na ce wa
" ka sanar da Baban Farida ko?" ta ke tambayar Dr.
Sai naji Dr ya ce " me kenan Ummi"
"ji mun sha-shanci dai, toh ina kata6a ganin anbada aure ba
ta re da sanin Uba ba, toh wa kake tunanin zai aurama Faridan" cewar
Ummi.
"Ikon Allah, Ummi ko dai tsufan ne tun yanzu, waye ya fad'a
miki zan auri Farida" Dr ya fad'a yana ajiye wayar hannunshi a k'asa.
Ummi ta ce "kaci gidanku, d'azun nan kace min setin akwati d'aya na Farida ne ina"
Girgiza kai Dr yayi kafin kuma ya ce "Ummi bazan iya yiwa
Farida wani abu ba sai da dalili? Nifa na siya ma ta ne kawai a
matsayinta na k'anwata"
Cikin muryar damuwa naji Ummi na cewa "ai na yi zaton duk
da ita za'a had'a har naji dad'i, toh itama Allah ya fito ma ta da miji
nagari"
"Ameen" Dr ya ce, gami da fara cin abincinshi, ba wanda ya k'ara magana a cikinsu.
Tabbas hankalina ya tashi da jin ansar Dr, amma ni banga laifinshi ba.
Ba yadda zanyi domin na riga na cuci kaina ba kuma namijin da zai so auran mace fanko.
Shiyasa na gadawa kaina dauriya, na kuma yi k'okarin kwantarwa da kaina hankali, tunda nasan bani da wata mafita.
****
Anyi biki an watse, da shike Dr ba mai son hayaniya ba ne, wannan ne yasa walima kawai yayi bayan an gama d'aurin aure.
Fannin amarya itama walimar ta yi, ba yadda Dr baiyi dani
naje walimarta ba, nak'i zuwa domin bana so naje wurin da za'a
wulak'antani.
Ko da aka gama bikin ko lek'a gidan amarya banyi ba, ba
yadda Dr baiyi dani akan nazo na rakashi siyan baki ba ranar da aka kai
amarya ba nak'i, na mai k'aryan kaina na ciwo amma yadda naga
hankalinshi ya tashi sai da na yi da nasanin fad'a mai hakan.
Da k'yar ranar ya tafi, ga amaryar ta dameshi da kira wai an barta ita d'aya.
****
Tun Dr ya na min uzirin rashin zuwa gidanshi har ya daina
ranar ya ce saina fad'a mai dalilina nak'in zuwa gidanshi, na rasa mai
zance mai k'arshe dai nace mai
"ai idan muka saba da ita zan dinga zuwa sosai"
Murmushi yayi ya ce "Faridana a rashin zuwa gidan ne zaku
saba, inaso kisawa ranki gidana gidanki ne, karki yarda ko da zancen
wasa wani dalilin ya hanaki iko da abinki, kuma ba na jin dadi, raina
yana 6aci da rashin zuwanki"
"Yayana ranka ya daina 6aci, na maka alkwawarin zuwa gidan har sai kai da kanka ka koreni"
Na fad'a ina dariya, shima murmushin yake had'e da cewa wa ya isa ya kori Farida Umar daga gidansu"
Tun daga wannan lokacin na cigaba da zuwa gidan Dr, duk da
matarshi ba wai ta daina nuna min tsanar da ta ke yimin ba ne, nidai ina
zuwa ne domin Dr.
****
Akwai wata rana da bazan manta ba na je gidan Dr da yamma lokacin Dr bai jima da siyamin mota ba.
Lokacin da na shiga gidan na samu Aunty Farida da d'ansu na
fari wato Khalil ta na bashi Indomie, yaron da gudu yazo gareni
kasancewar ya saba dani, wurgashi sama na yi na cafe, shi kuwa sai
wangale baki yake yana dariya.
Aunty Mariya ce ta zo ta fisgeshi a hannu na gami da cewa
"zonan kar ashafa maka rashin zuciya da naci, kamar yadda mutun ya dawo, sai bin mazan wasu"
Ta karashe da fad'in "ke don Allah kibarmin mijina ba aurenki zaiyi ba, haba Allah dai ya rufa mana asiri da bin mazan wasu"
Wannan maganar da ta fad'a a kunnen Dr, 6acin ran da na
gani a idanunshi ba zai misaltu ba, a lokacin zuciyata ta karye wani
irin kuka na fashe da shi kafin kuma na yi hanyar fita.
Kamo hannuna Dr yayi gami da rungumeni, abinda bai ta6a yimun ba tunda na mallaki hankalina.
Kallonta yayi cikin 6acin rai ya ce " sa'arki d'aya ke mace
ce amma da kinyi kad'an ki zagi Farida, na miki uziri a yanzu amma
karki manta akanta zan iya rabuwa da ke"
Ya cigaba da magana cikin zafin rai.
Sannan abu na k'arshe ke da Farida taso aure na ke kinyi kad'an da ki shigo gidana, wawiya ke d'in ba tallarki aka kawomin ba"
Ya na gama fad'a yaja hannuna muka fita, haka yayita rarrashina ita kuwa a ranar tayi yaji.
Koda su Ummi sukaji labarin abinda ta yi ba wanda ya goyi bayanta, Ummi kam ma ta d'auki abin da zafi sosai.
Sai daga baya aka sasanta ta dawo d'akinta, ni kuwa na
d'auke kafata, lokacin da ta sake haihuwa ne ma naje wannan ma tare da
Ummi mukaje.
Haka rayuwata ta cigaba da tafiya da dad'i ba dad'i.
*ABINDA YA FARA SHIGA TSAKANINA DA DR*
****
Bayan na kammala karatuna ina shirin zuwa bautar k'asa na
had'u da wani saurayi mai suna Adamu, tun bana saurarenshi har na fara
sauraranshi ba kuma wai don ina sonshi ba sai dai zuwa wannan lokacin
mahaifina yana yawan damuna da batun aure, nasan tabbas zamana a gida ya
na tuno mai da abubuwa da dama.
Wanda wani lokacin har ya ke zargin kanshi, wannan ne yasa har yanzu ya kasa samun cikakkiyar lafiya.
Dalilin hakan yasa na fara sauraran Adamu, har na ba shi daman zuwa gidanmu.
Sai dai akwai wasu abubuwa da Adamu ya kemin wanda ya ke sa
naji bazan iya aurenshi ba, shi mutun ne da ya ke ganin ta6a jikin mace
ba komai ba ne, ga maganganun batsa a bakinsa, sannan na lura yana da
son kallon mata wanda shi a ganinshi wata wayewa ce.
Sosai na ke nuna mai rashin dacewar hakan, sam bana yarda
ya ta6a ni, tabbas a wannan lokacin da inada wani saurayin na yi imani
zan iya rabuwa dashi.
Har k'aran shi nakai gun Ummi lokacin da tazo Bauchi
dubani, Ummi ta kirashi ta yi mi shi magana amma sam ya kafe ya kuma
rantse a gabana, sannan ya kuma ce.
"kar ki yi tunanin idan baki samu wannan shekarar ba, zan
hakura, a'a wallahi ko da zai zamo duk shekara sai kin zana jarabawar
nan ne ba zan gaji da kashe kud'ina ba"
Yana kuma gama fad'an haka yayi ficewar shi.
Ummi ce ta ce min "Farida kinfi kowa sanin halin yayanki,
kin kuma sanshi da kafiya idan zan baki shawara to fa kiyiwa yayanki
biyayya, bana so kema ki zamto mai kafiya kamar shi"
Sai a sannan Aunty ta ce "nifa banga dalilinki na k'in
amincewa ba, Umar fa gata ya ke miki, nan gaba za kiyi alfahari da
hakan, sannan kuma bakyaso ki zamto mai taimako ga addininki?"
"Farida"
ta kira sunana, d'ago kaina na yi na kalleta ba ta re da na ansa ba, cikin kwantar da murya ta ce.
"Inaso ki zamto mai kishin mata y'an uwanki, da'ace yau namiji ke duba mata ai gara muma asa mu mata, ace matan ma na musulmai"
"Shin ba za ki yi koyi da matan k'warai masu kishin
addininsu ba, Farida wannan karatu da za kiyi jahadi fa za kiyi, domin
Allah kad'ai yasan mutane nawa za su anfanu da karatunki"
Haka suka yita nuna min anfanin karatun, har naji zan iya, kuma na sawa raina zan jure duk wata wahalar da ke cikinshi.
Cikin ikon Allah na samu abinda ake buk'ata, na kuma samu
gurbin karatu a Abubakar Tafawa Balewa university (ATBU), wanda nake
karantar gynecology.
Tabbas karatu akwai wahala ba kuma k'aramar wahala nasha
ba, a haka ma Dr (Ya Umar) sosai yake taimakamin, domin wani lokacin
idan bani da lectures nakan bishi asibiti ina ganin yadda su ke gudanar
da aikinsu, kuma ina fahimta sosai.
Sannan duk abinda ban gana ba, dangane da karatuna wurinshi na ke zuwa ya k'aramim haske.
Ban sha wahala ta fannin zirga-zirgar makaranta ba, domin
Dr shi ya ke kaini ko'ina ya kuma dawo dani idan har ba shi da aiki,
domin zuwa wannan lokacin ya siya motarshi ta farko k'aramar Golf, idan
kuwa aiki yayi mai yawa, sai ya tura a d'auko ni.
Kasancewar a rayuwata ni ba mutun bace mai tara k'awaye
hasalima bani da k'awaye domin haka har na gama zaman Jos sai dai wanda
mukayi wasan k'asa da su.
Ko da na dawo Bauchi ma hakance, abinda ya ke gaba shi na
keyi, sai dai lokacin da na shiga university, na had'u da Mansura,
Mansura itace k'awata ta farko, daga kanta na fara kawance saboda na ya
bawa hankalinta da tarbiyarta.
Cikin k'ankanin lokaci muka shak'u da Mansura, sai dai sam Dr ba ya son kawance na da ita.
Mansura har gidanmu ta na zuwa amma ni sam Dr yak'i naje gidansu, tabbas bana son 6acin ranshi, shi yasa nake bin umarninshi.
Mansura ita ce mace ta farko da na fara ba tarihin rayuwata saboda yardar da na yi da ita.
A wannan lokacin samari da dama sun fito dan neman
soyayyata amma duk wanda ya fito haka kawai sai ya d'auke kafarshi ba ta
re da nasan dalili ba, anyi hakan yafi kashi hud'u, a hankali abin
yafara damuna har ya fara ta6a karatuna.
Daga k'arshe na yakice abin a raina na fuskanci karatun da ke gabana.
*******
Ina 300lv Alhajin su Dr ya umarce shi da yaje ya nemi
d'iyar abokinshi Alhaji sama'ila mai suna Mariya, suma y'an asalin garin
Bauchi ne.
Jininmu bai had'u da Aunty Mariya ba, sam ba ta k'aunata, sannan na rasa dalilin da yasa ta ke nuna min hakan.
So da yawa idan Dr zai je hira wurinta ta re muke zuwa da
shi, sai dai da k'yar ta ke ansa gaisuwata tun Dr bai fahimci hakan ba,
har yazo ya fahimta.
Ya nuna ma ta 6acin ranshi sosai, toh tun daga lokacin sai
ta daina nuna wannan halin a gabanshi, ni kam daga baya idan na fahimci
zai je wurinta sai na k'irk'iro da bacci koda kuwa ba naji.
Shima sai yayi zamanshi yak'i zuwa, haka ranar za ta yita
kiranshi awaya ta na tambayarshi dalilin k'in zuwan nashi, shi kuwa haka
zai sanar da ita dalilin fasa zuwan nashi, domin shi mutun ne mai
fad'an gaskiya, ko da kuwa kai ba zai maka dad'i ba.
Da farko idan ya fad'a ma ta sai ta d'au fushi dashi, shi
kuwa ko a jikinshi don so dayawa ma baya nuna ma ta yasan ta na yi, haka
zata ba kanta hakuri.
Domin na lura son da ta ke yimai yafi wanda ya ke ma ta,
lokuta da dama idan na rakashi hira wurinta duk hiran ita ta keyi, sai
dai ya bita da eh ko a'a, idan ya gaji ya ce mu tashi mu tafi, na lura
da hakan ba k'aramin 6ata ma ta rai ya ke ba.
Sannan duk abinda zai siya mata ta re yake siya mana sai dai kala ya ban-banta.
****
Wata rana bana mantawa ya ce na shirya muje jos domin kaiwa
Ummi kayan auranshi, bayan na shafe shekaru masu yawa ban sake waiwayen
garin ba, sam nak'i yarda, bana tunanin akwai kuma ranar da zan so
kafata ta k'ara takawa izuwa garin, garin da abubuwa da dama suka faru.
Dak'yar Dr yasa na bishi, amma koda muka isa halin da yaga na shiga yayi mugun d'aga mai hankali har sai da yace.
"Faridana da nasan bakya son zuwa Jos har haka, da ban takura miki ba, ki yafe min"
Ya fad'a yana had'a hannuwanshi alamar neman gafara.
Sosai na yi k'okarin danne duk abinda ya ke damuna, domin idan akwai abinda na tsana shi ne ganin tashin hankalin Dr.
Koda muka shiga gidansu ma, haka Ummi ta yita janyoni ajiki
ta na k'ok'arin mantar dani duk wata damuwa, sam bata barni na zauna
shuru ba.
Lokacin da na idar da sallah la'asar aka fara shugo da akwatuna, ina daga d'akin Ummi naji shugowan Dr.
Muryar Ummi naji ta na ce wa "Yayan Farida kamar akwati set
biyu na gani kuma kayan ciki kala ne kawai ya ban-bantasu, duka na
Mariya ne?"
Murmushi Dr yayi kafin kuma ya ce "a'a, set d'aya na Farida ne" cikin d'oki naji Ummi ta tareshi da cewa.
"Kace min mata biyu zaka h'ada yayan Farida"
Kafin ya kai ga magana wayar Alhajinshi ta shigo, alama yayiwa Ummi da ya na dawowa.
Ga mamakina sai naji Ummi ta d'au waya ta na kiran wata kawarta da ke Sudan akan ta na so tazo ta gyara ma ta d'iyarta.
Nidai ba naji abinda waccan ta ke fad'a na daiji Ummi ta na fad'a ma ta da zaran ta tabbatar da lokacin bikin zata sanar da ita.
Ranar farincikin da naga Ummi ta na yi abun sai da ya bani
mamaki, na kuma tabbatar Ummi mutum ce, tabbas bamu da abinda zamu
sakawa Ummi dashi sai addu'a
Jini na gani yana fita ta baki da hancin Mama ta na gogewa a
hankali, fad'awa na yi kan kafarta ina kuka, rik'emin hannu ta yi
sannan ta ce "kinsan dai bana son kukan nan, magana nakiraki muyi fa"
Cikin kuka na ce "Mama nasan kina jin jiki kuma nasan ni ce sila, Mama wallahi banyi ba a rayuwa, banyi ba mamaaaaa"
Na k'arashe cikin kuka, gogemin hawaye Mama ta yi kafin
kuma ta ce " ba kece sila ba Farida abubuwa da dama sun faru dani wanda
sunyiwa zuciyata girma, baki da laifi mune masu lefi, munyi *SAKACI*
wurin baku tarbiya"
"Mahaifinku bai so na haifeku ba, amma na dage sai na haifeku, ashe bazan iya baku tarbiyan da ya dace ba, ku yafemin yarana"
"Don Allah Mama kidaina fad'an haka, ba laifinki ba ne,
tabbas nauyi ne ya miki yawa Mama, Allah yafi kowa sanin nauyi ya miki
yawa"
"Wani tsarin iyali kukayi, inaso ki fad'amin gaskiya" Mama ta tambaye ni.
na ce "wallahi ni ban ta6a zuwa asibiti anyimin komai ba"
Mama ta ce "bai ta6a baki magani ko wani abun ba?" Na ce "nidai nasan yana yimin allura duk bayan watanni kad'an"
Girgiza kai Mama ta yi cikin takaici ta ce "Hassan ya cuceki Farida, amma ba komi kanshi yayiwa"
Ta d'anyi shuru sannan ta ce "nasan za ki fuskanci tsanani
arayuwarki zuwa gaba, gashi bazan kasance dake ba balle na rungumeki na
rarrasheki, amma zan baki shawara d'iyata, duk halin da kika tsinci
kanki ki koma ga Allah shi ne gatanki"
Tari ta yi wanda ya fito da Jini, ni nasa hannu ina goge ma ta had'e da cewa
"Mamana ba za ki tafi ki barni ba, wallahi duniya zata
yimin zafi idan na rasaki, babu Ya Hamid, babu Ya Abdallah sannan kema
kidinga irin wannan maganar Mama"
Shafa min kai Mama ta yi sannan ta ce "ki rik'e Ummi tamkar
uwa nasan itama zata rik'eki tamkar ita ta haifeki, sannan ki rik'e
Umar ya zama abokinki kuma abokin shawar ki, Farida inaso ki rik'e Umar
domin shi d'in masoyinmu ne, karki sake yarda da duk wani rud'in d'a
namiji kuma karki damu kanki akan aure mijinki zaizo gareki lokacin da
Allah ya tsara zai soki a yadda kike kinji"
"Sannan ki yimin alkhawari bazaki sa ke aikata sa6o irin wannan ba" na ce na yi alkhawari Mama"
Tace "toh jeki ki turomin Umar Allah ya miki albarka, Allah ya zama gatanki d'iyata"
Har na fita Mamana ta na anbaton kalmar albarka a gareni, ta kuma kasa d'auke idonta akaina.
Na tura ma ta Ya Umar bansan mai ta ce mishi ba, sannan su Baba da Ummi ma duk sun shiga.
Washegari da safe komi ya auku, wannan ranar ita na kira da
bak'ar ranar, wannan ranar itace sanadin d'aukewar duk wani jin dadina,
domin a ranar Allah ya amshi ran Mama.
Bazan iya kwatanta muku halin da na shiga ba, sai dai komi
ya tsayamin na wasu lokuta, sannan na jima ina ciwo, Baba ya aikawa
dangin mahaifiyata da dangin shi, duk kuwa sunzo, kakata ta yi kuka
sosai, haka ma Innayo.
Bayan anyi kwana bakwai da rasuwar lokacin da kakata tazo
tafiya taso ta tafi dani amma Ummi ta rok'eta akan ta barmata ni har
zuwa lokacin da zan k'are makaranta ta, ba yadda ta iya domin tasan irin
ruk'on da tayiwa Mama.
Baba ma yaso tafiya dani Bauchi amma Ummi ta ce yabari yayi
aure tukunnan don barina ni kad'ai a gida ganganci ne duba da yadda
nasa damuwa a raina, shima haka ya hakura ya barni amma duk ranar juma'a
sai yazo ganina.
Lokacin da Mama ta cika wata d'aya da rasuwa lokacin kuma
na samu saukin jiki saura na zuciya, Ummi ta umarceni da na fara zuwa
school da islamiyya, a wannan lokacin rayuwa ta yi min zafi ban isa fita
ba.
ko school naje ko Islamiya andinga cewa ga wacce bak'in
cikinta ya kashe uwarta rayuwa ta yimin zafi har takai bana fita, sai
kuma abun yaso ya ta6a k'wak'walwata na fara wasu irin abubuwa, wanda
duk tsangwamar da ake yimin ce ta janyo.
Ya Umar da Ummi ne ke rarrashi na amma sai suka ga abin yayi yawa, sai kuma suka fara shiga damuwa kada wani abu ya sameni.
Daga k'arshe Ummi ta samu Baba wata juma'a da yazo dubani
ta sanar dashi abinda ke faruwa, ya shiga damuwa mai yawa, yace wa Ummi
zai d'aukeni mu koma bauchi, Ummi ta ce amma a gaskiya dole ya nemi mata
ko don saboda ni, yace insha Allahu zai naima.
Haka ya d'aukeni muka koma Bauchi, bayan y'an watanni abokinshi ya had'ashi da Aunty.
Aunty y'ar kafin madaki ne da ke garin Bauchi, a bazawara
Baba ya aureta domin ta na da yara uku da suka haifa da tsohon mijinta
wanda suka rabu.
Ita ce ta cigaba da rik'ona tamkar ita ta haifeni.
*******
Bayan Ya Umar ya kammala bautar kasarsa nan ya samu aiki a SPECIALIST HOSPITAL da ke Bauchi kafin kuma ta koma ATBUTH.
A gidan mu ya fara zama, ba k'aramin dadi naji lokacin da
Ya Umar ya dawo gidanmu ba, domin yana d'ebemin kewa sosai, sannan ya
tsaya min a harkar karatuna sosai, domin daga farko naki karatun sam na
daina mayar da hankalina, bani da lokaci sai na kuka ko tunani, gani
nake bani da wani sauran anfani a rayuwata.
Ya Umar shi ya tsaya, tsayin daka wani lokaci har wayan
wuta yake tsoratani da shi, har dai naga Ya Umar fa ba gajiya zaiyi ba,
anan nasawa raina gara na yi mai biyayya, amma bawai don ina so ba.
Anan fa na dage sosai, ban zuba mai k'asa a ido ba, na dage
da karatun domin nasan ba wani abun da ya saura na rayuwarta a duniya
badda na dage da bautawa Allah sai kuma neman ilimi.
Duk wani abun bukata ba sai na nema ba, Baba da Ya Umar suna iyakacin k'ok'arinsu.
Ina SS2 Ya Umar yaje da kanshi yayi min register na WAEC da
NECO, karatu sosai mu keyi da Ya Umar, bani da wani lokacin hutawa,
cikin ikon Allah kuwa muka zana exams d'in, ba laifi result d'in NECO
yayi kyau fiye da na WAEC.
Lokacin da Ya Umar ya nema min form d'in JAM ya kuma ce wai
medicine zan karanta anan fa rigima ta, tashi domin ni na ce ba zanyi
medicine ba, shikuma yace ba gudu ba ja da baya.
Barka da zuwa shafin AYSHA ADAMAWA (Maman Sultan) Wannan Shafin na bude shine domin saka Littattafan hausa na soyayya, yake yake, hikayoyi. KU KASANCE DAMU DAN SAMUN NISHADANTARWA DA FADAKARWA. AYI KARATU LAFIYA.