Zagewa Yakumbo ta yi iya karfin ta ta rufe Haroun da
duka,ta na fad'in "mugu azzalumi wallahi Allah ba zai barka ba!" Ganin
ba ta da niyar dai na dukan Haroun Dawud ya yi yunkurin shiga tsakani.
Alhaji ya d'aga ma sa hannu dole shi ma ya ja gefe ya zubawa sarautar
Allah ido.
Alhaji Umar ne ya iya shiga tsakani,ya janye Yakumbon da ita ke dukan amma ta ma fi wanda ta ke dukan had'a zufa. Huda ce ta dad'a matsawa kusa da Haroun,ta ma rasa me za ta ma sa ta taimakasa ma sa,ganin yanda ya sha maka gun Yakumbo,gashi duk ta bad'e shi da kasa.......

Wata bakar jeep ce kirar Benz ta shigo farfajiyar gidan
biye da ita Mota ce kirar hilux,nan su ka faka,dake motacin duka tint ne
ba a iya ganin wanda ke ciki. Lokaci guda aka bud'e duka
motocin,Commissioner Adamu shehu wanda ya ke abokin Alhaji Shamsu tun
su na yara ne ya fito daga benz din tare da body guards din sa,yayinda
police har hud'u su ka fito daga hilux din.
Ganin su hankalin Mama ba karamin tashi ya yi ba. Bayan ya bawa Alhaji Shamsu,Alhaji Umar da Alhaji Hamisu hannu sun gaisa,Alhaji ya ce "me ya sa za ka zo da kan ka bayan cewa na yi ka turo yaran ka?" Ya na duban su d'aya bayan d'aya,in da idanun sa su ka tsaya kan Haroun,ya ce ."ka ce na tura yara na gidan ka,you shouldn't be expecting me to just stay back and do nothing,me ke faruwa ne Alhaji Shamsu?"

.
"Ga shi nan,ku tafi da shi" ya nuna Haroun da dan ya tsaya. Cikin rashin fahimta Commissioner Adamu Shehu ya ce " Saboda me ya sa za ka damka d'an ka hannun police?" Rai bace ya ce "wannan ba d'a na ba ne,daga yau na sallama shi na fitar da shi da ga cikin sahun 'ya'ya na....."
A razane Haroun ya d'ago ya na duban Alhaji,yayinda
Mama ta yanki jiki za ta fad'i,Ummi da Anty Salma su ka yi saurin rik'o
ta suna salati.
Shi kan shi aminin Alhaji ya girgiza da kalaman Alhaji,Alhaji Hamisu ne ya ja shi gefe su ka d'an yi magana,wanda daga bisani ya dawo gami da bawa police d'in umarnin su sa Haroun a mota. Nan fa sabon kuka ya farke,Huda har da karfin halin ruke hannun Haroun. Da kan sa ya banbare hannun ta daga cikin na sa,police su ka sa shi tsakiya har zuwa motar su. Commissioner Adamu Shehu ya shige ta sa, shi ne gaba,ta su Haroun na biye da su. Su mama na ji su na gani haka aka tafi da Haroun,kuma Alhaji ya hana ambatan ko da sunan Haroun ne a gidan,bare a yi maganar sa. Da wannan ya shige ciki,Alhaji Hamish biye da shi. Shi kuwa Alhaji Umar d'aukan Yakumbo ya yi ya maida ta asibiti. Sai tsinewa Haroun ta ke a hanya. Mama kuwa sai shigar da ita b'angaran ta aka yi. A takaice karamin zaman Makoki dai aka yi a gidan. Wannan kenan.

Sai da Habeebti ta cika sati guda da farfad'owa sannan aka mata d'inki,da test na HIV da kuma infections.An ci sa'a ba a same ta da ko d'aya ba,amma bayan wata uku za ta dawo a sake ma ta na HIV din bisa k'aida. A tak'aice dai sai da ta yi kusan wata d'aya ta na jinya,gashi kullum cikin kuka ta ke,tun ana lallashi sai da ya zamana sai dai kawai a zuba mata na mujiya.
Ranar da aka sallame ta rana aka sha daga,dan kuwa ta ce ba za ta
koma gidan Hajiya ba,sai dai a maida ita gun dangin Mahaifiyar ta.
Wannan shi ne wata sabuwa inji dan caca dan kuwa dangin mahaifiyar ta ta
ba su da masaniya kan lamarin. Dama kuma Yakumbo ta ce ba Aliya ba
gidan Hajiya har abada duk da Haroun ya nan hannan yan sanda sai ta ga
hukuncin da za a aiwatar kan shi sannan hankalin ta zai kwanta.
Dole ba a san ran ta ba,Bichi aka mai da ita,amma ta kudiri niyar komawa gun dangin mahaifiyar ta da ta sami dama.
Washagari da safe Habeebti ta fito daga wanka,ta yi zaune gaban mudubi,da ga ita sai towel. Kan ta take k'arewa kallo yayinda wani bak'in ciki ya tukare ta a k'irji. Ta rame sosai kamar wacce ta shekara ta na jinya. Ji ta ke dama mutuwa ta yi da ya fi wannan rayuwar da ta ke ciki,ta iya tsare mutumcin ta har tsawan shekarun ta a duniya,amma wuni d'aya dal wani wofi ya zo ya keta mata haddi. Duk duniya babu wanda ta tsana kamar Haroun,haka kuma ta tsani kan ta. Babu abun da ya fi d'aga mata hankali irin d'inkin da aka mata,da ko da yaushe ta ke jin shi,har gwara ma yanzu da ya fara warkewa,amma kam duk sanda ta shiga toilet har jin zare zaren ta ke.

Wani zazzafan hawaye ne ya gangaro daga idanun ta,ba ta damu da ta goge ba,idanun ta ya kai ga wayar ta jin ta na k'ara. Sunan Al'amin ne ya bayyana,tun jiya da ta kunna wayar ya ke ta faman kira da aiko sak'o txt massage amma ita ba ta d'auka ba,ba kuma ta ma sa reply ba. Ta na gani har wayar ta yanke,sai kuma ta jiyo Yaro daga tsakar gida ya na fad'awa Yakumbo ana sallama a waje. Yakumbo ta "amsa da waye?" Shiru ta ji,da Alama yaron ya fita. Ta tashi ta na tafiya a hankali dan da tayi motsi mai k'arfi ta na ji a jikin ta,gashi dama an ce kar ta cika gazargazar da yawa har sai ya warke.
Under wears din ta ta sanya,ta na kok'arin sanya doguwar rigar ta na
atamfa ta ji muryar yaro na fad'in "wai Al'amin ne ya ke sallama da
Aliya.." hannun ta a sama,riga a wuya ta tsaya cak ta na mai raba
ido,jin takun takalmi ta san Yakumbo ta nufo d'akin. Sauri ta yi ta
k'arasa sanya rigar. Fuska d'aure ta ke duban kofa ta na jiran shigowar
Yakumbo.
Ile kuwa sai ga ta ta d'aga labule,ta na mai yin sallama. A takaice ta amsa ma ta sallamar. Yakumbo ta dube ta ce "Habeebti kin ji sak'o daga waje ko?Sirikin na mu ne Al'amin" Kai tsaye cikin sassanyar murya ta ce "Yakumbo ki ce ba na nan,ba zan iya ganin sa ba....."
Yakumbo ta dan yi jim kad'an sannan,kamar ta na tsoran k'ara magana. Habeebti kuwa bakin gado ta zauna ta na kok'arin d'aura kallabi. Yakumbo ta nisa tare da fad'in "Na ce Habeebti ki taimaka ku gaisa....." Kukan da Habeebti ta sa ma ta shi ya sa ta katse maganar,dama ta san za a yi haka,dan haka sai ta fice ta ce da yaron ka ce ya shigo.
Daga d'aki ta jiyo muryar Al-amin,muryar da ta ke balain san ji,da ba ma ta san adadin missing d'in shi da ta yi ba sai yanzun da ta ke jiyo shi,haka kuma ta ke tsananin san saka shi a idanun ta,toh amma yanda ta ke yanzu ta fita ta ce ma sa me? Za ta ce ma sa yayi hakuri yanzu ita ba budurwa ba ce saboda dan gidan da ta ke zaune ya yi mata fyad'e ne har ta kwanta tsawan wata guda...?
.Ile kuwa sai ga ta ta d'aga labule,ta na mai yin sallama. A takaice ta amsa ma ta sallamar. Yakumbo ta dube ta ce "Habeebti kin ji sak'o daga waje ko?Sirikin na mu ne Al'amin" Kai tsaye cikin sassanyar murya ta ce "Yakumbo ki ce ba na nan,ba zan iya ganin sa ba....."
Yakumbo ta dan yi jim kad'an sannan,kamar ta na tsoran k'ara magana. Habeebti kuwa bakin gado ta zauna ta na kok'arin d'aura kallabi. Yakumbo ta nisa tare da fad'in "Na ce Habeebti ki taimaka ku gaisa....." Kukan da Habeebti ta sa ma ta shi ya sa ta katse maganar,dama ta san za a yi haka,dan haka sai ta fice ta ce da yaron ka ce ya shigo.
Daga d'aki ta jiyo muryar Al-amin,muryar da ta ke balain san ji,da ba ma ta san adadin missing d'in shi da ta yi ba sai yanzun da ta ke jiyo shi,haka kuma ta ke tsananin san saka shi a idanun ta,toh amma yanda ta ke yanzu ta fita ta ce ma sa me? Za ta ce ma sa yayi hakuri yanzu ita ba budurwa ba ce saboda dan gidan da ta ke zaune ya yi mata fyad'e ne har ta kwanta tsawan wata guda...?
Jin suna magana da Yakumbo ta tashi a hankali ta na bin bango,sai da ta zo bakin kofar ta tsaya,ji take kamar ta lek'a ta ga fuskar sa ko da sau d'aya ne.
Yakumbo ce ta ke masa bayani,ta na fad'in " Eh wayar ta ta ya jima a
kashe,da ke ta dan yi jinya ne...." "Ya Allahu,wlh sam ban ji ba ko
wajan kawayen ta da cousins din ta da mu ke magana da su,kuma na zazzo
gidan nan amma sai na tadda a kulle,dake can gidan da ta ke na Kano ban
sani ba,nan d'in ma dan nan mu ka kawo kud'i shi ya sa na sani,me ne ya
ke damunta?"
Nan fa d'aya,sai ga Yakumbo ta na kame kame,can dai ta ce "iye...naam.....toh cuta ce dai gata nan,yau ace wannan gobe wacan...." Duk da be gane abun da ta ke nufi ba,yayi tunanin gigin tsufa ne dan haka sai ya ce "Allah ya sauwake, ina ga gwara na zauna na jira ta tashi....." "Ah ah ka dai je ka dawo kannan ta tashi" Yakumbo ta yi saurin katse shi.
Jim ya yi,ji ya ke kamar ya tashi ya shiga d'akin da kan sa ya ga Habeebti. Kamar ta san tunanin da ya ke,ta ce "ka dai yi hakuri,ba daman na tada ta ne,sai dai ko zancen za ka yi da ni..." Ya na murmushi ya tashi,ya na fad'in "Yakumbo wake ta taki yanzu,bari dai na je na dawo d'in

kawai" da haka suna wasa da dariya su ka yi sallama da niyar zai dawo anjima.
Sai da ta ji ya fita sannan ta iya zama nan bakin kofa ta na kuka. Yakumbo ta shigo bayan ta raka shi har kofar gida,ya mata d'an ihisani. Saura kiris ta fad'i yin tuntube da Habeebti da ke zaune bakin kofa ta had'e kai da gwiwa ta na kuka.
Ta na sallallami Yakumbo ke duban Habeebti,cewa ta ke" za ki karasa ni ki huta,in ban da ke Habeebti ai mai san ka har abada mai san ka ne in dai san na gaskiya ne,wallahi ki ka ce wannan salon rayuwar za ki d'auka za ki sawa kan ki cutar da za ta kar ki har lahira,yaron nan ya zo tun daga wani gari amma ki ki ganin sa,ki shirya anjima zai dawo...."
.Sai da ta ji ya fita sannan ta iya zama nan bakin kofa ta na kuka. Yakumbo ta shigo bayan ta raka shi har kofar gida,ya mata d'an ihisani. Saura kiris ta fad'i yin tuntube da Habeebti da ke zaune bakin kofa ta had'e kai da gwiwa ta na kuka.
Ta na sallallami Yakumbo ke duban Habeebti,cewa ta ke" za ki karasa ni ki huta,in ban da ke Habeebti ai mai san ka har abada mai san ka ne in dai san na gaskiya ne,wallahi ki ka ce wannan salon rayuwar za ki d'auka za ki sawa kan ki cutar da za ta kar ki har lahira,yaron nan ya zo tun daga wani gari amma ki ki ganin sa,ki shirya anjima zai dawo...."
Shiru Habeebti ta mata har ta karaci surutan ta ta gama,ta fita. Sakon txt ne ya shigo wayar ta,ko da ta duba sai ta ga numbar Al-amin,ya tura mata da. "love you Aliya Habeebti" aje wayar ta yi ta na mai fad'in wallahi da zanga Haroun da sai na masa lahanin da zai kai shi har lahira!" Nan ta kara sa wani sabon kukan ta mai tsanar rayuwar da ta ke ciki.
Zuwan Al'amin har uku ranar,amma Habeebti ta k'i yarda ta gan
shi,ana hud'un ne ya dawo bayan magrib. sam ba ta san da zuwan shi ba,ta
na zaune falon Yakumbo kawai sai jin k'amshin turaren sa ta yi,kan ta
ankara sai ga mutum cikin falo,sallamar sa da shigowar sa lokaci
d'aya.
Yakumbo daga waje ta na " yi zaman ka nan falon kafin na
kira ma ka ita" amma ita kan ta Habeebti ta san da gangan Yakumbo ta ma
ta haka,ta san ta na falon dama.
Ganin shi tsaye gaban ta ba zato ba tsammani ya sa ta tashi tsaye da sauri,ganin yanda ya tsare ta da ido ya sa ta koma da sauri ta zauna ta na kwance kallabin da ke d'aure kanta,yayinda ta yi saurin yafawa jikin ta kamar mayafi,Allah ma ya sa doguwar rigar da ta sa tin d'azu ne jikin ta. Ganin be tanka ba,be kuma karasa shigowa ba ya sa ta dan d'aga ido ta kalle shi. Farar shadda ce sanye jikin sa,an yi ma ta aiki da koran zare,kan sa ko hula babu,kallo daya za ka ma sa ka tabbatar da damuwar da ke tattare da shi. Al-amin wankan tarwad'a ne,dogo kakkaura. Ya na da dogon hanci da tarin saje wanda ya ke k'ara ma sa kyau da kwarjini.
Ganin har yanzu idanun shi kan ta ya ke,ta yi k'asa da na ta idanun ta na mai fad'in "sannu da zuwa"da sassanyar muryar nan na ta. Be amsa ba,be kuma motsa daga in da ya ke tsaye ba,wanda hakan ya sa Habeebti tsarguwa,abun da ta ke gudu ne ya faru,shikenan har ya gane abun da ya same ta gashi ya tsare ta ido ya ma kasa mata magana......ba ta ankara ba sai ga hawaye na zuba daga idanun ta.
.Ganin shi tsaye gaban ta ba zato ba tsammani ya sa ta tashi tsaye da sauri,ganin yanda ya tsare ta da ido ya sa ta koma da sauri ta zauna ta na kwance kallabin da ke d'aure kanta,yayinda ta yi saurin yafawa jikin ta kamar mayafi,Allah ma ya sa doguwar rigar da ta sa tin d'azu ne jikin ta. Ganin be tanka ba,be kuma karasa shigowa ba ya sa ta dan d'aga ido ta kalle shi. Farar shadda ce sanye jikin sa,an yi ma ta aiki da koran zare,kan sa ko hula babu,kallo daya za ka ma sa ka tabbatar da damuwar da ke tattare da shi. Al-amin wankan tarwad'a ne,dogo kakkaura. Ya na da dogon hanci da tarin saje wanda ya ke k'ara ma sa kyau da kwarjini.
Ganin har yanzu idanun shi kan ta ya ke,ta yi k'asa da na ta idanun ta na mai fad'in "sannu da zuwa"da sassanyar muryar nan na ta. Be amsa ba,be kuma motsa daga in da ya ke tsaye ba,wanda hakan ya sa Habeebti tsarguwa,abun da ta ke gudu ne ya faru,shikenan har ya gane abun da ya same ta gashi ya tsare ta ido ya ma kasa mata magana......ba ta ankara ba sai ga hawaye na zuba daga idanun ta.
Ganin haka ya k'arasa gaban ta,ya zauna tare da fad'in"kukan na menene,ni da ki ka share Aliya ni ya kamata na yi kuka,shhhhhh maza goge hawayen nan,sam ba ya mi ki kyau...." Hanky ya mik'a ma ta. Ta karb'a ta na goge hawaye,ganin ta tsaya ya ce "d'ago na gani?" A kunyace ta d'an d'ago su ka had'a ido,murmushi ya mata tare da fad'in "ko ke fa yanzu ki kad'an yi min kama da mata ta Habeebti. Oya start explaining,me ya sa ba a fad'a min baki da lfy ba?me ya sa aka k'i d'aukan waya na,me ya sa ake gudu na?"
Murya can k'asa ta ce "Ban da lfy....."kai ya gyad'a mata,tare da
fad'in wannan na sani daga ganin yanda ki ka rame,abun da na ke tambaya
me ke damun ki?ni kuma menene laifi na?" Shiru ta yi ta na wasa da 'yan
yatsun ta,ganin ba za ta amsa ma sa ba ya kira sunan ta "Aliya" ta d'aga
ido ta na kallan sa. Ya ce "ba zan matsa mi ki ba,whenever you are
ready ma yi maganar owk?" Ta girgiza kai ta na kokarin kwakulo murmushin
dole. Nan su ka dan tab'a hira,amma gaba d'aya al'amarin Habeebti ya
d'aure ma sa kai,sam ta kasa sakin jikin ta,yau ko ruwa ba ta ma sa tayi
ba gudun kar ta tashi,gani ta ke da ta tashi zai gane. Ko da ya zo
tafiya ma ba ta raka shi ba,daga zaune ta ma sa sallama abun ta. Haka ya
tafi ya na sak'ar zuci.
Dangin Mahaifiyar Habeebti ne su ka iso Bichi jin abun
da ya sami d'iyar su. Sun zo ne da k'arfin su na akan lalle sai Habeebti
ta koma hannun su,kamar yanda ita ma Habeebti ke so. Amma nan su Alhaji
Umar su ka mu su fin k'arfi a matsayin su na dangin Uba,hakan ba
karamin ciwo ya mu su ba,Anty Talatu ce mai ikirarin mik'a k'ara
koto,Alhaji Murtala wanda ya ke shi ne babban Baffan Habeebti ya ce "ba
wannan maganar,ba dai Habeebti ba ce?Allah shi zai raya ta,dan haka su
bar ta kawai,d'aukan na ta a yanzu ai ba shi zai sauya komai ba,kaddara
ta riga fata".
.
Alh Sani wanda ran sa ya fi na kowa b'aci cewa ya yi kaddara da sakacin su ba,yanzu ya za a yi da yaran da ya kawo kud'in auren yarinyar nan? " Babu abun da ya fi sai a shedawa yaron dan wannan ba abunda za a buye ba ne" Alhaji Umar ne ya ba shi amsa. Girgiza kai Alhaji Sani yayi,kana ya ce "Allah ya sa a dace" su ka amsa da amin.
B'angaran mata kuwa ba masalaha,dan kuwa rabuwar rashin dad'i aka
yi,Anty Talatu ta fi kowa zaifi da nuna facin rai har ta kai ga Hajiya
Mario na zargin ta da rashin yarda da k'addara. Mai dan saukin Anty
Maijiddace,wacce ita ta ke bin mahaifiyar Habeebti. har jan Habeebti
gefe ta yi ganin tun da su ka je ta ke ta aikin kuka,ta ma ta fad'a,ta
na mai fad'in "ba ki yarda da k'addara ba ne Aliya?yanzu haka ki ke
rayuwa kullum cikin kuka?"Aysha Tafeeda wacce ta ke cousin din
Habeebti,kuma k'awar ta, ta ce "gaskiya dai kukan ya kusa ya yi yawa
Habeebti" Anty Maijidda ta kara da "na tsani kukan nan na ta wlh,an san
da ciwo,sai ki barwa Allah komai sai ki ga ya saka mi ki". "Toh" shi ne
amsar da Habeebti ta amsa mu su da shi. Haka ta na ji ta na gani su ka
tafi su ka barta gidan Yakumbo.
A daren ranar ne Al-amin ya zo mata sallama zai koma Kaduna,Alhaji Umar da Yakumbo su ka sheda ma sa gaskiyar abun da ya faru ba su buye ma sa komai ba. Ji ya ke kamar ya yi tsuntsu ya je ya sami Haroun ya masa abun da har ya mutu ba zai mance da shi ba kamar yanda ya aikatawa Habeebti. Jin ya na kulle sam be gam su ba. Tausayin Habeebti ne ya kama sa ya kuma ce da su Yakumbo wannan lamari yayi kad'an ya raba shi da Habeebti,san Habeebti yanzu ma ya fara,auran ta babu fashi. Wannan batu ba k'karamin dad'i ya yiwa su Yakumbo ba,albarka kam ya sha ba adadi. Amma sun ba shi shawarar ya je ya nemi shawaran iyayen sa shi ma.
Ranar gaba d'aya hirar sa da Habeebti nasiha ce,da kuma jadda soyayyar da ya ke mata. Har su ka yi sallama ya tafi. Ranar dai Habeebti ta yi kwanan farin ciki.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya,Haroun na can kulle,sai da Alhaji ya je da kan sa ya tabbatar da haka,sannan ya hana kowa zuwa ganin sa. Tun abun na damun Mama,har ta watsar ta danne cikin zuciyar ta.
Kusan watanni biyu ne su ka shud'e da faruwan al'amarin. Wata ranar
asabar ce r aka tsaida domin zana jarawabawar post utme a ABU. Dawud ne
ya je har Bichi ya d'auko Habeebti domin kai ta Zariya. Ta yi kyau cikin
shigar ta na material purple da hijabin ta iya gwiwa. Dawud ne ke ta
kok'arin ma ta hira,amma ta ki sakewa ta ma sa magana,sai dai ta amsa ma
sa da "um um-um" ko kallan sa sosai ba ta san yi dan sai ta ga kamar ta
na kallan Haroun.
Jin shirun ya yi yawa,ya ga kuma ta kau da kai gefe sai ya yi zatan ta yi bacci,dan haka sai shi ma ya yi shiru ya k'ara sautin karatun da ya ke ji ya na bi a hankali. Ji ta yi zuciyar ta na tashi,dama tun safe ta ke fama da jiri,tun ta na iya jurewa har ta kasa,ta ce da Dawud "Dan Allah ko kana da goro?" Jin tambayar na ta ya sa Dawud ya dan dara "Aw ashe idan ki biyu,kya bar Yakumbo a gida ki na tambayar dan samari goro?me ma za ki yi da shi?" Ya tambaya cikin zolaya. Amsa ma sa ta yi da "ina yawan jin zuciya ta na tashi ne lately,gashi ni kadai sai nai ta kunci raina ya ta baci na ba gyara ba dalili" dan juyowa yayi ya kalle ta,kan ya mayar da kallan sa kan kwalta,wani tunani ne ya tsarga zuciyar sa,ya yi saurin kawar da shi,daga bisani ya ce"Maganar kuncin zuciya ki na yawaita karanta Allahumma la sahala illa majaltahu sahalan wa antajalal hazna iza shita sahalan....kin iya adduar ko?" Habeebti ta gyad'a kai alamar eh. Ya k'ara da "ki na kuma karanta Hasbinallahu wani'inamal wakilu,450 safe da yamma,Allah zai yaye mi ki damuwaa ya kuma yassare mi ki" godiya ta ma sa sosai,ita dai fama ta ke da kan ta da za ta samu ta yi amai da ta sami sauki.

Haka ta yi jarabawar a daddafe,kan ta gama sai da ta
yi amai sau uku. Suna dawowa Kano kan ya wuce da ita Bichi sai da ya kai
ta asibiti,ta ga Doctor ya duba ta tare da mata test. Abun da Dawud dai
ya yi tunani ne ya faru,amma sai ya ki fad'a mata. Har sai da su koma
Bichi ya ke shedawa Yakumbo bayan sun keb'e.
.
Tagumi Yakumbo ta doka,ta ce "ai biri ya yi kama da mutum,wlh ba tun yau na san da haka ba,gaba d'aya alamu ya nuna oh ni Saratu ya zamu yi?Habeebtin ta sani ne?" Ya ce " sai dai ki fad'a mata daga baya" "Toh Allah shi ya san komai,Allah dai ya shige ma na gaba ni Saratu."
Sam Habeebti ba ta san abun da ke faruwa da ita ba,sai
da ta ji wata ya shude amma period shiru,gashi kullum cikin laulayi ta
ke,Hajiya kullum sai ta kira ta ji ya jiki,ita kan ta Yakumbo wani
lallab'a ta take,hakan ya sa ta gano bakin zaren,ta sawa Yakumbo bori
har ta tabbatar mata da gaskiyar magana.Habeebti dai juna biyu gare ta.
Ranar had'iyar zuciya na kawai Habeebti ba ta yi ba,ta sha alwashin
zubar da cikin,amma Yakumbo ta hana,haka ma su Alhaji Umar,wai idan ya
zo da ajali me za ta ce da Allah. Ita kuwa Habeebti gani ta ke tsabagen
ba a cikin su ya ke ba,haka ta na ji ta na gani za ta raini cikin shege
ta shayar ta goya? Da kanta ba za ta kawo abun da zai Zane ma ta bakin
ciki duniya ba.
Shi kan shi Al-amin da ya ji cewa ya yi zubar da cikin shi ne mafita tin da yanzu gudan jini ya ke be cika d'a ba bare ace an zubar an yi kisan kai., amma k'iri k'iri su Yakumbo sun ki yarda,kuma su ka ce in dai sun isa da ita lalle ta bar cikin nan ta yarda da hukunci ubangiji. Ana wannan yanayi result din Habeebti na post utme ya fito,amma percentage din ta be kai ba.
Sa'ilin da Habeebti ta koma hospital ne domin a sake ma ta HIV test wanda aka ci sa'a shi ma negative, Dawud ya biya da Habeebti gidan su bisa umarnin Hajiya.

Zaune su ke falon Hajiya,gaba d'aya ta kasa sakewa Allah Allah ta ke Dawud ya dawo su tafi,sai ga Mama,biye da ita Huda ce da Halima. Ita kan ta Hajiya ta yi mamakin shigowar Mama da raban da ta shigo tin randa wannan abun ya faru. Ga mamakin ta ba ta kula da Hajiya da ke zaune kujerar da ke kallan na Habeebti ba,sai ma zama ta yi kusa da Habeebti,su kuma su Huda bayan Mama su ka tsaya. Ganin haka cikin girmamawa Habeebti ta gaida Mama. Amsawa Mama ta yi,gami da ruk'o hannun Habeebti,ta ruke cikin na ta,kana ta ce "d'iya ta na zo neman alfarma wajan ki,na san an miki ba daidai ba,an zalince ki,amma ki duba darajar Allah ki sa baki a sako Haroun......." "Hajja Fadi ki ma dai na b'ata bakin ki,yaron nan ba za a sake shi ba!!" Fadin Hajiya kenan a fusace,ta k'ara da"idan ba ki sani ba yanzu haka yarinyar nan d'auke ta ke da juna biyu..."
Hannun Habeebti da tuni hawaye su ka wanke mata fuska ta saki da
sauri,ta na mai nanata maganar " juna biyu......." Hajiya ta gyad'a mata
kai "kin ji da kyau,ki na ganin za a sake shi ne ya ci gaba da rayuwar
sa bayan ta na cikin kunci,za ta kuma kasance cikin kunci har sai ta
haife ta raini abun da ke cikin ta? Ba wannan maganar......"
A rikice Mama ta koma yiwa Hajiya Mairo magiya,fad'i ta ke dan Allah ki taimaka min Hajiya Mairo,mu rufawa juna asiri,a fitar da yaran nan in ya so idan ta haihu kai idan ta kama ma zubar da cikin za a yi,a zubar a d'aura mu su aure......." Maganar ta Mama mutum biyu a wajen ta fi d'agawa hankali, Habeebti wacce ta san idon ta idon Haroun sai ta lahan ta shi,amma ace wai za a aura....."kai ba wannan ba maganar" abun da ta ke jaddadawa cikin ran ta kenan. Sai kuma Huda wacce jikin ta har rawa ya ke jin batun na Mama. Ita kuwa Hajiya girgizawa Mama kai ta yi ta ce "Aliya ba za ta auri lalatacce kamar Haroun ba,b'ata ma ta rayuwa da yayi be sa ta rasa sauriyin ta dan mutunci wanda zai aure ta ba......" Daga Huda har Habeebti sakin ajiyar zuciya su ka yi a tare. Amma me? Ganin Mama su ka yi ta na shirin kai gwiwowin ta k'asa ta na "idan ta kama na durkusa mi ki ne Hajiya Mairo..."kan ta kai k'asa Huda da Halima su ka yi riga rigan taro ta,Halima na fad'in "Wallahi Mama ba za ki durkusa a gaban su ba,su d'in banza su din wofi...."ji ka ke tas! Ayub ya d'auke Halima da mari,ya na cewa "uwar ta wa ce banza hofi dan baki da mutunci?.." wani marin ne ya sauka fuskar Ayub,cikin jin zafin marin ya d'aga kai su ka yi ido biyu da Dawud wanda shi ma shigowar sa kenan ya ga Ayub ya mari Halima,a fusace ya ce"wa ya ma ka tarbiyar dukan mace? Dama ashe ba ka da hankali? "Hajiya fa ta ke zagi ya Dawud..." "Get out!" Dawud ya fad'a cikin tsawatarwa da tuni Ayub ya kama hanyar waje,yayinda shi ma Dawud ya juya ya yi ficewar sa ba tare da ya k'ara tankawa kowa ba. Huda da Halima su ka ja Mama suna ba ta hakuri,yayinda Hajiya da ko ajikin ta tace da Habeebti "ki ma dai na kuka,hakkin ki ne sai an kwatar mi ki".

Ragon zubar da cikin Habeebti ya sa ta fara ganin canji gun Al-amin,da kullum kira safe,rana dare amma yanzu idan ta samu ya kira ta sau d'aya a rana ma ta godewa Allah,har ta gaji ta dan yi masa korafi,amma sai cewa ya yi aiki ne ya masa yawa. Ya za ta yi,tunda darajar ta ya ragu dole ta yi hakuri dama ta samu zai aure ta..tunanin da take kenan duk sanda ya mata ba daidai ba,sai ta hakura. Amma abun da ta kasa ganewa shin idan ta haife abun da ke cikin ta ya za ta yi da shi....? Ko b'angaran Al-amin ma damuwar sa kenan,shi ya sa ya tsani ganin Habeebti musammam yanzu da cikin na ta ya kai wata takwas da ka ganta za ka ga tulelen cikin a bayyane. Ko ya d'aga waya zai kira ta,sai ya ja tsaki ya aje.
Babban takaicin sa shi ne na kin zibda cikin,ya sha
kai mata magani da hannun sa tun cikin ya na jariri wanda za ta sha ya
zube amma shiru ka ke ji wai an shuka dusa. Akwai sanda ya tirsasa sai
da ta sha a gaban sa,amma taurin kai irin na cikin shege ko gizo bare ya
kai ga barewa.
Ganin yanda ko ganin ta ba ya zuwa yi sai Habeebti ta
masa uziri,ita ma ta kyale shi,after all ba ita ta d'aurawa kan ta ba.
Dawud ne me d'ebe mata kewa wanda duk weekend a Bichi ya ke yi. Haka ma
Anty Salma na yawan kiran ta,ta ji ya lafiyan ta. Kwanci tashi cikin
Habeebti ya kai wata tara. A yanzu kam kwata kwata Al-amin ya dauke mata
wuta,ko dan txt dinnan ma ba ya mata. Daran wata asabar,dare ne da ba
za ta mantawa ba. Har ta kwanta,amma sai ta nemi bacci ta rasa,dan haka
kawai sai ta kunna data din ta,ta shiga facebook,ta d'an fara dube
duben ta,hotan wani ango da amarya ta gani ana ta sawa ana mu su fatan
alkhairi. Ganin sun yi yawa ya sa ta tsayawa kan hotan ta bud'e,fuskar
wa za ta gani? Fuskar al'amin d'in ta ne da amaryar sa,sai a sannan ta
duba k'asan hotan ganin an sa "HML Al-amin and Aysha M.C" be sa ta gama
yarda da shi din ba ne. Haka ta rink'a duba duk posts din da ta ga da su
aka yi,ta duba profile din abokan sa sun kai goma....ta kai kusan minti
talatin ta na zaune shiru,ta ma rasa me za ta yi....can kawai sai
tsintar kan ta tayi ta na dariya sosai,ta na dariya ta na hawaye ta kira
wayar cousin din ta,Aysha Tafeeda. Bugu uku zuwa hud'u ta d'aga,cikin
muryar bacci ta ce "Habeebti ya dai?you never crash?" Jin Habeebti na
dariya ya sa Aysha wartsakewa,dan raban da ta ji dariyar Habeebti tun
iyayen ta na raye,bare wannan har da k'yakyacewa. Cikin kullewar kai
Aysha ta ce "Habeebti?lafiya kuwa me ya sa ki dariya haka?" Da kyar ta
ke jiyo muryar Habeebti daga na ta b'angaran saboda karfin dariyar da ta
ke,Habeebti ta ce " Aysha kunna wayar ki ki shiga facebook ki ga
Al-amin d'ina....." Cikin in ina ta na kok'arin kunna wayar da ta ke fb
din da shi ta ce " me ya-sami Al-amin-d'in---na ki?" Habeebti da har
lokacin ba ta fasa dariyar ba ta ce " Aure yayi,ya auri budurwa wacce ba
a mata fyad'e ba,ba a mata ciki ba,kuma ku ce bazan kashe Haroun ba?".
Ta dad'a kwashewa da dariya. "Innalillahi wainnailaihir rajiun!!!!!"
Fad'in Aysha tafida kenan jin kalaman Habeebti da kuma ganin zahiri,ga
Al-amin da amaryar sa ana ta mu su san barka. Fuska cike da hawaye Aysha
Tafeeda ta ce "Kuma shi ne ki ke dariya Aliya? Dan darajar Allah ki yi
kuka,ki yi hakuri ki yi kuka Habeebti,kuka za ki yi Aliya" ita kuwa
Habeebti zuciyar ta kyek'ashe,wanda hakan shi ya fi d'agawa Aysha
Tafeeda hankali da ta kasa hakura tuni ta aje wayar dan neman Anty
Maijidda....