Wayar Anty Maijidda Aysha Tafeeda ta nema,ta yi sa’a
ta same ta. Jin abun da ke faruwa Anty Maijidda ta shiga kiran
Habeebti,amma ta k’i d’agawa. Da sassafe su ka d'auki hanyar Kano,da
azahar sai gasu a Bichi,amma su ka tadda gidan Yakumbo a kulle da
kwad’o. Wayar Yakumbo ta nema,it ace ta ke sheda mu su suna asibitin
tun asuba,Allah ya sauki Habeebti lafiya,kukan jinjirin da ke tashi shi
ya tabbatar mu su da ba shakka ta haifo lafiyyan d’a,kwaran gaske.
Jiki sanyaye su ka garzaya asibitin da ke nan cikin Bichi ya ke. D’akin da Yakumbo ta fad’a mu su suka nema. Da shigar su suka tadda Yakumbo d'auke da baby,sai cilara kuka yake ta na ta faman jijjiga shi,sai Hajiya da ta ke ta yiwa Habeebti nasihan da d'au yaron ta bashi nono,amma kamar ana magana da dutse,sai ma juya ma su baya da ta yi kwance bisa gado. Ganin su Yakumbo har da hamdala,ta ce ‘’yauwa gwara da Allah ya kawo ku,ashe kuna tafe dama,kila ganin ku ya sa ta tausayawa yaran nan ta bashi nono,tun asuba ake abu d’aya sai dai a jik’a dabino da zamzam abawa yaro.’’ Tana magana ne yayin da ta ke k’ok’arin mik’awa Anty Maijidda babyn. Ba Anty Maijidda ba,hatta Aysha da ke lek'en yaran da ga nesa sai da ta matso kusa ta na fad’in ‘’Tabarakallau mashaAllah’’ tsabar baiwa na kyau da Allah ya yiwa babyn . Anty Maijidda ce ta k’ara da ‘’ wai wai wai sai ka ce d’an larabawa tibarkallah mashaAllah’’ ‘’Ai uban sa ne sak,idan ki kalli yaran nan ki ka kalli uban shi kadai ya isa mutum tsoran Allah’’ Yakumbo ta fad’a ta na mai tab'e baki. Anty Maijidda na jinjina kai ta d’an matsa kusa da Hajiya su ka gaisa a gaggauce kafin ta dan taba Habeebti,ta na mai magana cikin lallami,ta ce ‘’Aliya taimaka dan Allah ki ceto ran dan jinjirin nan ki bashi nono ya sha,kar kid'au alhakin sa akan laifin da bashi ya aika ta ba….’’ shiru ake ji,ko motsawa ba ta yi ba bare ta nuna ta san da ita ake. Hajiya ce ta fusata ta ce ku barta ta ruk'e nonan na ta,idan ya yi tsami ya fara ma ta ciwo ta san yanda za ta yi da shi. Bari na fita na nema ma sa madara" Ta tashi ta fita fuuu kamar wacce za ta tashi sama. Aysha ce da d'auki yaron ta sa shi a kafad’a yayin da ta fara kai kawo ta na girgiza shi. Yakumbo da Anty Maijidda su ka ci gaba da bawa Habeebti baki amma ta mu su kunne uwar shigo. Har ita ma Yakumbo ta fusata ta k'yale ta.
.Jiki sanyaye su ka garzaya asibitin da ke nan cikin Bichi ya ke. D’akin da Yakumbo ta fad’a mu su suka nema. Da shigar su suka tadda Yakumbo d'auke da baby,sai cilara kuka yake ta na ta faman jijjiga shi,sai Hajiya da ta ke ta yiwa Habeebti nasihan da d'au yaron ta bashi nono,amma kamar ana magana da dutse,sai ma juya ma su baya da ta yi kwance bisa gado. Ganin su Yakumbo har da hamdala,ta ce ‘’yauwa gwara da Allah ya kawo ku,ashe kuna tafe dama,kila ganin ku ya sa ta tausayawa yaran nan ta bashi nono,tun asuba ake abu d’aya sai dai a jik’a dabino da zamzam abawa yaro.’’ Tana magana ne yayin da ta ke k’ok’arin mik’awa Anty Maijidda babyn. Ba Anty Maijidda ba,hatta Aysha da ke lek'en yaran da ga nesa sai da ta matso kusa ta na fad’in ‘’Tabarakallau mashaAllah’’ tsabar baiwa na kyau da Allah ya yiwa babyn . Anty Maijidda ce ta k’ara da ‘’ wai wai wai sai ka ce d’an larabawa tibarkallah mashaAllah’’ ‘’Ai uban sa ne sak,idan ki kalli yaran nan ki ka kalli uban shi kadai ya isa mutum tsoran Allah’’ Yakumbo ta fad’a ta na mai tab'e baki. Anty Maijidda na jinjina kai ta d’an matsa kusa da Hajiya su ka gaisa a gaggauce kafin ta dan taba Habeebti,ta na mai magana cikin lallami,ta ce ‘’Aliya taimaka dan Allah ki ceto ran dan jinjirin nan ki bashi nono ya sha,kar kid'au alhakin sa akan laifin da bashi ya aika ta ba….’’ shiru ake ji,ko motsawa ba ta yi ba bare ta nuna ta san da ita ake. Hajiya ce ta fusata ta ce ku barta ta ruk'e nonan na ta,idan ya yi tsami ya fara ma ta ciwo ta san yanda za ta yi da shi. Bari na fita na nema ma sa madara" Ta tashi ta fita fuuu kamar wacce za ta tashi sama. Aysha ce da d'auki yaron ta sa shi a kafad’a yayin da ta fara kai kawo ta na girgiza shi. Yakumbo da Anty Maijidda su ka ci gaba da bawa Habeebti baki amma ta mu su kunne uwar shigo. Har ita ma Yakumbo ta fusata ta k'yale ta.
Har aka sallame su su ka koma gida Habeebti ba ta ko kalli yaran ba bare ta kai ga d'aukan sa ta shayar da shi. Da su ka koma gida ne Alhaji Umar da aka fad'a ma sa an yi haihuwar ya zo tare da matar sa,jin abun da yake faruwa na kin shayar da yaran da Habeebti ta yi ta wajan matar sa ya sa shi shiga har d'akin da Habeebti ta ke ciki ya rufe ta fad’a,ta in da yak e shiga ba ta nan yake fita ba,fad’i ya ke’’ Dan rashin imani kusan awanni bakwai da haihuwa amma kin ki shayar da yaro,da haka sai ki wulgar da shi ki tabbata irin matan nan da basu yadda da kaddara ba su ke kasha ‘yayan su da kan su….minti biyar kar ki k’ara ki tabbatar kin bawa yaro hakkin sa,shi ina ruwan sa?…menene laifin sa?…..’’ da wannan ya juya ya fice a fusace. Yakumbo ce ta d'au yaran ta d'aura mata kan cinya,Habeebti ta yi saurin kau da kan ta gefe,ganin haka ya sa Yakumbo ta ce ‘’ko sai na fitar da Maman da kai na na sa ma sa a baki?’’ jin haka Habeebti ta ce wallahi kar ki tab'a ni Yakumbo,kada wanda ya taba ni". Jan gefe Yakumbo ta yi,dan ta san tabbas Habeebti ba cikin hayyacin ta ta ke ba. Ganin Yakumbo ta ja baya,hannun Habeebti na rawa ta sa cikin riga ta na kokarin fitar da nono ta bawa babyn da bai fasa cillara kuka ba. Sai da ta d'au lokaci sannan ta daure ta iya kallan dan yayin da ta ke kok'arin sa ma sa baki..caraf kuwa ya karb'e ya fara sha yayinda Habeebti ta runtse idanun ta,ta na mai tawassali ga Allah,lalle shi ne zai yaye ma ta wannan bakin cikin da ya addabi rayuwar ta. Su hajiya kuwa ajiyar zuciya su ka saki,atlast Allah ya yi uwa ta shayar da dan ta. Ba ta wani jima ta na bashi nonon ba amma har ya fara bacci ta ciro shi,yaro sai tand'e baki yake da alama be koshi ba. Ta aje shi can gefe ta koma ta kwanta ta na mai gyara rigar ta. Aysha ce ta d'auke shi ta na ‘’Allah sarki wallahi daga gani be k’oshi ba’’ wani harara Habeebti ta watsa mata,tuni ta ja bakin ta ta tsuke. Su Yakumbo kuwa cewa su ka yi ba dai ta bashi ba,hakan ma sai a godewa Allah. Sai da bacci ya kwashe Habeebti Anty Maijidda ke fad'a mu su abun da ya sa suka d'auko hanya. Yakumbo ta tausayawa Habeebti,kana ta ce "shi ya sa ma na ko runtsawa ba ta yi ba,haka na tadda ta shakaf shakaf da gumi da hawaye,tun fa uku na dare da na fito zagawa bayi,duk a zatona ciwan nak'uda ne,ashe da biyu. Na ko fad'awa Karami sai a mayar ma sa da kud'in sa. Allah ya sa haka ya fi alkhairi" su ka amsa "Amin"
A daren ranar Dawud ya zo shi da su Akib da Aunty Salma,wacce ta Umarci
Dawud da ya taimaka ya yiwa yaran hud’uba da duk sunan da ya so.
Yakumbo ta ce da wani duk sunan da ya so bayan ga sunan uban sa…ai sai
ka masa da sunan uban sa kawai ya amsa’’
.
.
Bayan kwana bakwai Yaro ya ci sunan uban sa Haroun. Babu
zancen taron Suna,amma hakan be hana dangi taruwa ba,hatta b'angaran
dangin mahaifiyar Habeebti sai da su ka zo,bare kuma su Hajiya da Ummi.
Alhaji Hamisu ne da commissioner Adamu shehu tare da
Dawud wanda shi ya ja motar da kuma Akib su ka bak'unci Bichi,inda dama
Alhaji Umar ya san da zuwan na su,jin sun karaso ya ce za su iya shigowa
zaure,in da su ka tadda shi zaune tare da Baffan Habeebti Alhaji
Murtala da kuma mijin Anty Talatu,sai kuma wani Malami da Alhaji Umar ya
gayyato a nan Bichi.
Duka bisa tabarma su ka zauna,an fara gaisawa Alhaji Hamisu ya ce da su Dawud da ke shirin shiga cikin gida "ai ba ciki za ku shiga ba,ku ma ya kamata ku zama shedu,maza ku kwaso goro da alawar cikin mota"
"Toh" su ka amsa ma sa,yayinda Dawud ke mamakin rad'in sunan ma sai sun sheda?abun da ya kamata ace tun asuba a yi ma sallacin layi a gama. Da wannan tunanin cikin ran sa su ka kwaso goro da alawa,su kawo cikin soron. Diyar Anty Talatu Asmau,wacce su ke kira Asmee ce mai kimanin shekara bakwai ta zo wucewa,yaro da kwad'ayi,ganin kwalin alewa ga kuma baban ta a wajan ita ma sai ta ja tsaya abun ta.
Su Dawud ba su ankara da abun da ke shirin faruwa ba sai da su ka Alhaji Hamisu ya fidda bandir din kudi,sababbbi k'al yan dari biyar,sannan kwakwalwarsu ta fara aiki.Malam ne ya fara sallama gami da cewa "Toh a gurguje dai bara mu yi abunda ya tara mu anan,dama shi daurin aure ba ya yiyuwa sai abubuwa uku sun cika,waliyai,sadaki da kuma shedu,ina ga kuma duk akwai nan ko?" Aka amsa masa da "kwarai da gaske"
Malam ya ce "Ina waliyin yaro?" "Gani nan" Commissioner Adamu Shehu ne ya amsa ya na mai matsowa gaba. Malam ya ce "ina na yarinya fa?" Baffan Habeebti ya matso gaba ya na mai bayyana kan sa. Malam ya ce "toh bisimillah".

Commissioner Adamu shehu ne wanda ya ke waliyin ango ya
dauki kud'in da Alhaji Hamisu ya aje,kana ya ce " Ni Adamu Shehu,ina
nemawa dan mu Haroun Shamsu auren d'yar ku Aliya Nasiru bisa ga sunan
annabin mu Muhammad salllahu alaihi wasallam,tafarkin addinin musulunci
ga sadaki naira dubu hamsin" ya mi ka wa Waliyin Aliya kud'i.
Wanda shi kuma ya amsa tare da fad'in "Ni Murtala Hamza na baiwa Haroun Shamsu auren d'yar mu Aliya Nasiru bisa ga sunan annabin mu Muhammad salllahu alaihi wasallam,tafarkin addinin musulunci ga sadaki naira dubu hamsin,jama'a ku sheda"
Mallam ya dubi waliyin amarya ya ce "kun bayar?" Waliyi ya amsa da " mun bayar" ya dubi na ango ya ce "kun karb'a?" Waliyi ya ce "mun karb'a" Malam ya k'ara da "suturan ta da ci da sha,da kuma bada hakkin ta da k'are hakkin ta sun rataya a wuyan sa,jama'a ku sheda" nan fa aka yi salatin manzo tare da addu'a aka shafa. Aliya ta zama matar Haroun. Wanda idan aka d'auke wanda su ka d'aura da wanda su ka sheda ba wanda ya san da wainar da aka toya.
Cikin gida kuwa kowa na harkar gaban sa. Su Anty Talatu ne su ka sa faifai Al-amin na d'ibar albarka,Habeebti da ke zaune gaban mudubi fitowar ta daga wanna kenan,ta na jin su amma ba ta tanka ba. Can parlour kukan Haroun junior ne ke tashi,wanda ya ke hannun cousins din Habeebti,dan har yau ba nonon arziki ya ke samu daga wajan Habeebti ba,ga shi da tsotso,sai madara ake had'a ma sa da shi.
Asmee ce ta shigo da gudun ta,hannun ta cike da alawa,ta
fad'a kan cinyar Maman ta Anty Talatu,sai mai da numfashi ta ke. Anty
Talatu na duban ta ta ce "ummm d'iyar arziki ina aka samo swt haka?
Allah sa ba kud'in Yakumbo ba ne ya yi ciwo ba?" Asmee na juye juye ta
ce Abba na ne ya ban ni ma ya ce na sheda auran Anty Habeebti......"Tsit
ka ke ji,daga na d'aki har na parlour da iska ya kai mu su maganar
Asmee da dama irin yaran nan ne ma su surutun tsiya,ga murya,ba wanda ya
iya tankawa. Kukan Haroun junior kad'ai ke tashi,yayinda kowa idanun sa
na kan Habeebti da ta tsaya cak ta na duban Asmee.Wanda shi kuma ya amsa tare da fad'in "Ni Murtala Hamza na baiwa Haroun Shamsu auren d'yar mu Aliya Nasiru bisa ga sunan annabin mu Muhammad salllahu alaihi wasallam,tafarkin addinin musulunci ga sadaki naira dubu hamsin,jama'a ku sheda"
Mallam ya dubi waliyin amarya ya ce "kun bayar?" Waliyi ya amsa da " mun bayar" ya dubi na ango ya ce "kun karb'a?" Waliyi ya ce "mun karb'a" Malam ya k'ara da "suturan ta da ci da sha,da kuma bada hakkin ta da k'are hakkin ta sun rataya a wuyan sa,jama'a ku sheda" nan fa aka yi salatin manzo tare da addu'a aka shafa. Aliya ta zama matar Haroun. Wanda idan aka d'auke wanda su ka d'aura da wanda su ka sheda ba wanda ya san da wainar da aka toya.
Cikin gida kuwa kowa na harkar gaban sa. Su Anty Talatu ne su ka sa faifai Al-amin na d'ibar albarka,Habeebti da ke zaune gaban mudubi fitowar ta daga wanna kenan,ta na jin su amma ba ta tanka ba. Can parlour kukan Haroun junior ne ke tashi,wanda ya ke hannun cousins din Habeebti,dan har yau ba nonon arziki ya ke samu daga wajan Habeebti ba,ga shi da tsotso,sai madara ake had'a ma sa da shi.
Asmee da ba ta damu da canjin yanayin da aka samu a d'akin ba ta k'ara da "har da goro fa,wai angon Anty Habeebti ne ya siyo...Yauwa sunan sa ma d'aya da babyn Anty Habeebti,ya ma sunan Mama?yauwa HAROUN" ta fad'a ta na mai jaddada sunan kamar ta yi abun arziki......
A hankali Habeebti ta tashi,fuskar ta kunshe da murmushin da ya yi kama da na mugunta,ta ja hijabin ta ta zura,hanyar fita ta nufa ta na mai kwallawa Yakumbo kira
.
Jin kiran da Habeebti ke kwala ma ta Yakumbu da ta lek'a wajan ma su suyan ragon sunan Haroun junior,ta san labari ya isawar Habeebti. Ile kuwa sai gata nan ta fito, ba ta dai na kiran Yakumbo ba,su Anty Talatu ma ba su yi k'asa a gwiwa ba biyo Habeebti su ka yi dan jin ba'asi. Ganin haka Yakumbu ta amsa da sauri yayin da ta nufo Habeebti tun kan ta k'araso gare ta.
Cikin tsananin b'acin rai ta ke duban Yakumbo,ta na mai fad'in "na ji magana a bakin Asmee,yara ba sa k'arya,menene gaskiyar maganar....?" Nan fa Yakumbo ta fara kame kame ta ma rasa me za ta ce wa Habeebti. "Yara ba sa k'arya sai iyayen ki ne ma su k'arya ko?" Amsar da Alhaji Umar ya bata kenan wanda shigowar sa ya tsinci kalaman na Habeebti. Ya k'ara da "Eh aure mu ka d'aura mi ki,na lura ke ba ki san lallami ba,mu a matsayin mu na iyayen ki ba za mu iya sa ido mu na kallan ki da yaro ba hakannan siddan ba miji gare ki ba,tun da k'addara ta riga fata,shi wancan ya yi auren sa dole mu aurar da ke in da asirin kowa zai rufu,ga mahaifin dan ki....."
Tun da ya fara magana ta ke jin jiri na kwasar ta,kan ta na sarawa. Ba su ankara ba sai ga ta za ta fad'i,nan su Anty Talatu su ka yi saurin rik'o ta suna salati. Jikin Anty Talatu ta zube sumammiya. Anty Maijidda ce ta sa kuka,fad'i ta ke "gaskiya abunda aka yi wa yarinyar nan ba a kyauta ba,a rasa wanda za a aura ma ta sai wannan yaran da ya cuci rayuwar ta,ga shi ai ta fad'i idan ta mutu kowa sai ya huta" Alhaji Umar be damu da maganar da ta ke ba,bare ya rarrashi Yakumbu da ke ta faman kurma salati,fita ya yi da sauri. Kan ya dawo tuni sun cincibi Habeebti sun kai ta d'aki yayinda su ka cire ma ta hijabin jikin ta suna mai yayyafa ma ta ruwa. Da yardar Allah sai ga ta ta farfad'o,amma hannun ta bisa kan ta saboda azabar ciwan da ya ke ma ta. Kowa sai sannun ya ke ma ta,ga kukan Haroun junior da ya cika gidan,hayaniyar ba k'aramin dad'a d'agawa Habeebti hankali ya yi ba.
Muryar Alhaji Umar aka ji daga tsakar gida ya na fad'in "ya za ku mai da ita uwar d'aka,maza ku fito da ita asibiti za a kai ta" Daga dak'i Hajiya wacce ita kan ta ba ta san da batun d'aurin auren Haroun da Habeebti ba,kuma ba karamin ciwo abun ya ma ba ta ta amsa ma sa da " Ta farfad'o ai" "ko ta farfad'o din ya kamata ta ga Doctor,yarinyar nan ba lafiya gare ta ba,maza ku fito a kai ta asibiti" da wannan umarnin su Anty Maijidda su ka taya Habeebti shiryawa, wacce tun da ta farfado ba bu abunda ta ke furtawa sai "kai na,wayyo kai na"
.
Dawud wanda tun bayan d'aurin auren Habeebti ya fita hayyacin sa
ne ya kai su asibitin. Inda Doctor ya tabbatar mu su cewa jinin Habeebti
ne ya hau to the extreme level,any moment za ta iya collapsing,ya yi
mamakin jin ta haihu kwana bakwai da su ka wuce ba ta yi jijjiga ba. Ga
kuma migraine da Dawud ya sanarwa Doctor ta na da shi. Dan haka kwantar
da Habeebtin aka yi.
A hanyar komawar su kano,bayan komai ya lafa,Habeebti
na can kwance a asibiti,Alhaji Hamisu,Commissioner Adamu shehu sai kuma
su Dawud kamar dai yanda su ka taho,Hajiya kadai su ka bari saboda
jinyar Habeebti. Alhaji Hamisu ya kawo wa commissioner Adamu Shehu
maganar Haroun,tun da an sami masalaha,kuma ya na da iyali ya kamata a
sake shi.
Commissioner Adamu da fara'ar sa ya ce "Na ce da kai na d'aure shi ne dama?ai sanin rana irin ta yau za ta zo ya sa i made good use of him" Ba Alhaji Hamisu ba,hatta su Dawud sai da su ka kai duban su ga Commissioner,Dawud har da fad'awa dan rami. "Lura da hanyar nan fa Dawud" fad'in Alhaji Hamisu kenan,yayinda ya maida hankalin sa ga Commissioner, kana ya ce "ban fahimce ka ba Adamu,ka na nufin duk tsawan lokacin nan Haroun ba d'aure ya ke ba?bayan mun zo mun gan shi ne ka sake shi?toh da ma ka sake shi ina ya je?" "NDA short service...." Commissioner ya ba shi amsa a takaice. Shiru su ka yi na dan lokaci,kowa na ta shi sak'ar cikin zuci.

Dagabisani Commissioner ya tausaya mu su,ta hanyar
ba su bayani,kana ya ce" sanda aka fara case din yaron,dama ina da slot
har biyu na Nigerian Army da za a yi recruiting under short service.
Toh ga d'ana ance na k'ulle,kuma ba a ce da ni komai ba bayan wannan
umarnin,zaman shi a kulle is just a waste,and you knw me well Alhaji
Hamisu,ba na san asara musammam da na san sai an dawo an yi wannan
masalahar ta yau,saboda haka na tambaye shi qualification din shi,ya ce
da ni geography ya karanta,though ba wani result din arziki gare shi
ba,amma dai ya na da kwalin,ya na da tsayin,lafiyar,fad'in da duk abun
da ake buk'ata...."
Alhaji Hamisu ya nisa sannan ya ce "Ban tari numfashin ka ba Adamu,ta yaya ku ka sami takardun na sa?na ga dai kwal din sa aka tafi da shi?wani kasa a gidan ya d'auko ma ka ko yaya?" " Commissioner ya yi dan dariya ya ce dan ka Akib shi na sa ya d'auko min ya kamin har gida ba tare da ya san dalilin yin haka ba....." Wata harara Dawud ya watsawa Akib,da sai da hanjin cikin sa ya kad'a kafin ya bud'i baki ya ce " ku gafarce ni Baffa,amma sai na ga hakan kamar Aliya da danginta za su ga ba a aikata mu su adalci ba,mussammam yanda rayuwar Aliya ta kasance cikin k'unci da bakin ciki,za su yi tunanin dama mu na sane mu ka tura shi can inda ya ci gaba da gina rayuwar sa,ita kuma na ta rayuwar a dak'ushe...."
Alhaji Hamisu ya na mai jinjina kai ya ce "gaskiyar ka Dawud,na san shi kan shi Alhaji Shamsu ba zai ji dadin wannan maganar ba musammam.........."

"Kai rabu da shi....." Commissioner ne ya katse Alhaji
Hamisu,be gushe ba ya cigaba da fad'in " Wani Shamsu kuma shi da ya ce
ba shi ba yaro?ashe hannun ka na rub'ewa ka yanke ka yar?in fad'a mu ku
gaskiya ni mutum ne me san nawa,ina san kai na. Kuma su Aliyar da dangin
na ta ai abun bakin ciki su ne ace yau an aurar da d'iyar su ga wanda
be da future,ko kuna tsammanin Haroun da ya zauna har tsawan shekara
guda gidan yayi,in ya fito zai dawwama a Haroun din da ku ka sani ne?na
san masifar da kukan nan da matan nan ke yi har da na jin yaron ma ya na
gidan yayi,da sun san in da ya ke da ba su tada hankalin su haka ba,so
so ne fa,amma san kai yafi. Kai ina mai jaddada ma ka Alhaji Hamisu,ka
rubuta da babban baki ka aje, ba su ba,hatta ita yarinyar nan gaba sai
ta gode min,wallahi tallahi. Yaro dai nan da shekara d'aya za mu je
passing out parade inshaAllahu za mu sami second-lieutenant...."
Kai Alhaji Hamisu ya jinjina ma sa" Maganar ka gaskiya ne Adamu,Allah ya tabbatar da alkhairi." Ya na murmushi Commissioner ya amsa da "Amen,ka ma je ka shedawa Yayan nan na ka,idan ya na da magana ya zo ya same ni" dariya su ka sa su biyun,yayinda Dawud ya ke jin ran sa kamar ana rura wuta,shi kuwa Akib qula'auzai ya shiga karantawa cikin ran sa dan ya san masifar da zai sha gun Hajiya da ma Alhaji sai Allah.

Ga mamakin kowa,jin yanda ta kaya da Haroun Alhaji
Shamsu be yi masifar da kowa ke tsammani daga gare shi ba,sai ma wani
dan sanyi da ya ji cikin ran sa,Wato kam da gaskiyar Commissioner Adamu
Shehu,so so ne,amma san kai ya fi. Yanda Alhajin ya yi ne ya tunzura
Mama wacce Ayub na tsegunta mata,ta fasa kwanan Bichi,ta had'o kayan ta
sai gida. Ta yi masifa har ta gaji Alhaji Shamsu k'ala be ce mata ba,har
ta zarge shi da ya ba sane aka yi wannan abun,shi ya sa ma tsawan
lokacin nan ko maganar Haroun ba ya yi,dama yanda ya ke san uwar gidan
sa Hajja Fadi komai zai iya yi,ba dai an aura ma sa Habeebti ba,idan
aure be kawo shi ba,saki ya kawo shi.
.Hajja Fadi kuwa da 'ya'yan ta murna kamar zai kashe su, kanwar Hajja Fadi wacce su ke kira Maman Zahra har da rawa da takawa, Hajja Fadi sadaka ta yi da godewa Allah da ya k'arbi adduar ta. Bare kuma su Aunty Salma,da su Huda da ranar kasa bacci ta yi dan farin ciki,duk da ta na takaicin rashin zama matar Haroun ta farko ba,ba ta fidda ran zama ta biyu ba da ya fito daga camp da rai da lafiya.
In da ake farin ciki nan Kano a Bichi kuwa da aka fad'awa Yakumbo
abun da ya faru da Haroun cewa ta yi " Had'i ne,dama ana sane,toh amma
da jikar ta ta zama matar dan bursuna ai gwara matar soja" satin
Habeebti d'aya aka sallame ta. Sai da ta mummure sosai ta ke jin labarin
Haroun wajan su Yakumbo ta na shedawa Alhaji Umar. Murmushi ta yi na
mugunta,cikin ranta ta ce gwara da shiga sojan,dan kuwa akwai gagarumin
yaki gaban sa. Al-amin kuwa da aka mai da ma shi da kud'in sa sai ya
hau burin kunya,wai shi ba fasa auren Habeebti ya yi ba,so ya ke ya aure
ta a ta biyu. Sai da aka sheda ma sa ai ita yanzu matar aure ce kuma ya
ji bak'in ciki ya turnuk'e shi. Lalle wannan shi ne mugu dan masara.
Yakumbo ce mai rainon Harour Junior,idan ka gan shi wajan
Habeebti to yunwa ce ta kai shi. Kullum dad'a girma ya ke ya na
kyau,irin yaran nan ne ma su shiga rai. Bayan an raba gadon iyayen
Habeebti,ta sami dukiya mai yawa sai ta bawa baffan ta ya ci gaba da
juya mata kafin ta tsai da zuciyar ta kan abun da za ta yi da kud'in.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya,Dawud shi ne abokin
shawarar Habeebti. Tun ta na tsimayin bayyanar Haroun har ta fitar da
rai,dan kuwa shekara d'aya har da wata biyar amma shiru ka ke ji. Hana
rantsuwa rannan da ta je gidan Hajiya cikin yarda magana Huda ta fad'a
mata wai "za su je passing out parade din mijin ta Haroun..." Wannan
batun da Habeebti ta tuna ne ya sa ta tausayawa Dawud,wanda yanzu haka
su ke shirin zuwa Kano domin bikin auren sa shi da Huda.
.Zaune ta ke gaban akwaitin kayan ta,ta na zab'an kayan da za ta ci shagalin bikin da shi. Maganganun Dawud ta ke tunawa in da ya ke ce mata" wallahi biyayya kad'ai ya sa na yarda da auren nan da su Alhaji su ka had'a,da sun san wacece Huda da ba su ma soma ba....." Ajiyar zuciya Habeebti ta saki,kana ta ce "kowa da kaddarar rayuwar sa,shi kuma Dawud Huda ce tashi,Allah dai ya sa mu gama lafiya"
Bayan ta gama had'e kayan tsaf ta ja akwati ta rufe. Ta
shi ta yi ta nufi tsakar gida,sanye cikin riga da zani na leshi army
green,da ka gan ta ka ga dirarriya mace,musammam da ta haihu sai hips
din ta ya k'ara budewa sosai,gashi jikin ta ya yi kyau,timbinta ya koma
ba wanda zai ce k'atan d'an da ke goye bayan Yakumbo na ta ne.
" Yakumbo wallahi idan baki shirya shi ba har ya Dawud ya zo wallahi sai dai na bar mi ki shi,ranar wunin kya taho da shi" Habeebti ta fad'a cikin nuna k'ulewa. Da sauri Yakumbo ta sauko Haroun Junior ta na "ah ah sai fa kin tafi da shi Habeebti,kai sauko karka k'ara sa min bayan nawa jeka gyatumar ka ta shirya ka maza" Haroun Junior da tun ya na shekara d'aya ya yaye kan sa daga nonan da ake ma sa yanga,ya kuma yi k'afa,ga wayo gun sa har da na siyarwa,matsalar sa d'aya shi ne cizo,sai dai be ga yaro ba,amma ko bayan uwar sa yaro ya ke sai ya kai k'ananan hakoran sa ya yi cizo.
Jin an sauko shi da gudun sa ya yi wajan Habeebti ya na "beebti" sunan da ya ke kiran ta kenan jin ana kiranta Habeebti. Kafafun ta ya rungume yayinda ita kuma ta durkusa ta d'auke shi ta na fad'in ba za a je da kai taro ba saura ka bud'e hakora kai ta cizan yaran mutane......" Dariya ya shiga yi mata ya na tafa hannu kamar ya gane warning din da ta ke ma sa. Yakumbo ce ta bisu da kallo,har su ka shige ciki ta na mai tausayawa Habeebti.Tsakanin d'a da uwa soyayyace mai karfi,amma hakan ba ya hana Habeebti k'yarar Haroun junior duk sanda ciwan da baban sa ya d'ana mata cikin ran ta ya motsa,wani sa'in idan ya mata laifi irin na yara ta hau jibgar sa sai an ka ma sa d'auki,amma da anjima sai a ga ya koma jikin ta. Ta sha ana zaune lafiya ya na jikin ta kawai sai a ga ta tura shi gefe cikin hantara da tsana,idan aka mata magana ta ce ya fiya kama da uban sa. Ita dai Yakumbo yaran ya shiga ran ta.
." Yakumbo wallahi idan baki shirya shi ba har ya Dawud ya zo wallahi sai dai na bar mi ki shi,ranar wunin kya taho da shi" Habeebti ta fad'a cikin nuna k'ulewa. Da sauri Yakumbo ta sauko Haroun Junior ta na "ah ah sai fa kin tafi da shi Habeebti,kai sauko karka k'ara sa min bayan nawa jeka gyatumar ka ta shirya ka maza" Haroun Junior da tun ya na shekara d'aya ya yaye kan sa daga nonan da ake ma sa yanga,ya kuma yi k'afa,ga wayo gun sa har da na siyarwa,matsalar sa d'aya shi ne cizo,sai dai be ga yaro ba,amma ko bayan uwar sa yaro ya ke sai ya kai k'ananan hakoran sa ya yi cizo.
Jin an sauko shi da gudun sa ya yi wajan Habeebti ya na "beebti" sunan da ya ke kiran ta kenan jin ana kiranta Habeebti. Kafafun ta ya rungume yayinda ita kuma ta durkusa ta d'auke shi ta na fad'in ba za a je da kai taro ba saura ka bud'e hakora kai ta cizan yaran mutane......" Dariya ya shiga yi mata ya na tafa hannu kamar ya gane warning din da ta ke ma sa. Yakumbo ce ta bisu da kallo,har su ka shige ciki ta na mai tausayawa Habeebti.Tsakanin d'a da uwa soyayyace mai karfi,amma hakan ba ya hana Habeebti k'yarar Haroun junior duk sanda ciwan da baban sa ya d'ana mata cikin ran ta ya motsa,wani sa'in idan ya mata laifi irin na yara ta hau jibgar sa sai an ka ma sa d'auki,amma da anjima sai a ga ya koma jikin ta. Ta sha ana zaune lafiya ya na jikin ta kawai sai a ga ta tura shi gefe cikin hantara da tsana,idan aka mata magana ta ce ya fiya kama da uban sa. Ita dai Yakumbo yaran ya shiga ran ta.
Dawud ne ya zo d'auko su. Ganin sa Haroun junior har da tsalle da ke yawan zuwan da ya ke har sun saba. Yay ta rigima shi dai a wajan Dawud zai zauna,da kyar Habeebti ta samu yayi bacci bayan sun d'auki hanya.
Dawud ne ya saci kallan ta ta wutsiyar ido,shi kullum gani ya ke ta
na k'ara ma sa kyau,bakar mace ce mai kyau irin wanda turawa ke kishi da
shi. Ganin ta d'ago ya yi saurin mai da hankalin sa ga tukin da ya
ke,ji ya yi ta ce "Ango ka sha kamshi,ina su Halima amarya,na san Maryam
na nan kan nan na rawa amara k'irjin biki" "lalle kam" amsar da ya ba
ta kenan,yayinda ya ke ji ina ba Huda ba ce matar da iyayen sa su ka
zab'a ma sa,ya na mai bakin cikin rashin zab'in ran sa da ta kasance
matar wani a yau,wanin ma k'anin sa. Be san sanda ya sa hannu ya daki
sitiyari ba,wanda hakan ya tsorata Habeebti,cikin tausaywa ta shiga ba
shi hakuri da shawara,duk a tunanin ta tsabar bakin cikin auren Huda da
aka bashi ne ba,nan kuwa ba ta san har da ita ake rura wutar ba.
Cikin gida ma haka ta tarar,Huda saboda rashin san auren Dawud har jinya ta yi,amma aka k'i saurara mata. Abun da ke bawa Habeebti mamakin shi ne wai Haroun din da ta tsana karshen tsana shi Huda ta ke so akan Dawud,duk da ta san halin shi,ta san me ya aikata,gaskiya ne there is no accounting for love(shan koko daukan rai).
An sha shagali kan shagali,in da Halima ke farin cikin auren angon ta Saminu,ita kuwa Huda kamar makoki ta ke. Tun da aka fara bikin hankalin Habeebti be kwanta ba,sai dai rai da rai Haroun junior ya na hannun ta,dan da ta sake shi ya shiga cikin yara za ka ji kuka,abun da zai biyo baya kuwa shi ne "ina uwar wannan balaraben dan ne?" Ko kuma "wannan dan waye?jairi mai cizo" Wato Haroun junior ya yi halin kenan Tun Habeebti na fita da gudu ta na d'auke shi har ta gaji ta goya shi,nan ma sai rigima lalle sai ya sauko ya shiga yara yayi wasa,har Habeebti ta fusata ta sauko da shi ta sa yatsanta biyu ta nammake kumatun sa...zo ku ga kuka gun Haroun Junior kamar wanda aka jiwa ciwo. Nan mutane su ka yi wa Habeebti cha,har da me cewa "dan ba ta san ciwan dan ba ne,ta yi haka ma na gaban uwar sa" Anty Salma ce ta d'auke shi in da Habeebti ta dungurar da shi,ta na fad'in "ai maman ta shi ce,ya gajiyar da ita,yi shiru Junior" baki matar ta bud'e cike da mamaki,ta ce "kai amma sam ba su yi kama ba,ni ganin kamanin sa da maigidan nan na zaci d'an ki ne ko na Haroun,matar shi ta haihu ba a fad'a ma na ba, dan sai jin auren na sa kawai mu ka yi kamar daga sama." Haroun junior a hannun Anty Salma ta fice ta na fad'in "Allah sarki" ita kuwa Habeebti tuni ta bar wajan kafin a fara d'irga sh

Ranar da aka daura aure ranar aka kai amare. Kusa da
gidan akwai tagwayen gida da Alhaji ya gina wanda ake kyautata zatan ya
Gina ne dan Dawud da Haroun,nan Huda ta tare. Ta yi kuka kamar ran ta
zai fita. Ita kuwa Halima Tarauni aka kai ta.
Da misalin goman dare,bayan an dawo daga kai amarya,yan biki sun watse sosai musammam na b'angaran Hajiya,da ke ita namiji ta aurar. Dawud ya zo yi ma ta sai da safe. Nan ta zaunar da shi ta sake ma sa fad'a kan zaman auren. Duk abunda ake Haroun Junior na mak'ale da shi. Ko da ya zo tafiya yaro ba sai ya mak'ale ba,aka yi aka yi ya sauka ya ki,shi lalle sai ya bi uncle. Da kyar Hajiya ta b'anb'are shi,ta ce da Dawud ya yi maza ya tafi dan Allah ba ta da k'arfin ruke Junior. Ya na dariya ya fice,in da Hajiya ta aje shi ta na fad'in ga fili nan sai ka yi birgiman ka mai isar ka tun da na ga ji ka ke da k'arfi dan butar gidan ku. Nan kuwa yaro yay ta burgimar sa. Hajiya kuwa da gajiyar biki ya dame ta dan kishingid'a ta yi,ta ma bashi baya ya k'arata.
Habeebti ce sanye da doguwar rigar ta material ja,an ma sa ado da bakin stones,kunnan ta ko dankunne babu,ta cokalo daurin dankwali wanda ake ma lak'abi da ture ka ga tsiya,ba ta damu ta sa mayafi ba dan ta san mazan gidan sun gama shigowa,bare angon da ta san Haroun Junior na rigamar sa ne saboda tafiyar sa. Hannun ta ruk'e da ruwan tea d'in da ta had'o cikin kofi,daga kitchen ta ke ta nufo falon jin Haroun junior ya yi shiru ta Shigo ta na fad'in "an gaji an yi shiru kenan......"

Tsayawa ta yi cak ganin mutum tsaye tsakiyar falon,ga
Haroun junior rungume da k'afafuwan sa kamar yanda ya saba yiwa Habeebti
ko Dawud,a hankali ta d'aga idanun ta da su ka taho tun daga kan bakin
takalmin sa mai sheki,har zuwa bakin wandan sa,har ga bakar rigar
sa,inda ta ja ta tsaya a kan farar fuskar sa....tuni kofin da ta ruk'o
ya subuce ya fad'i wanda k'arar haka ya sa Hajiya da ta fara
gyangyad'awa ta yi firgit ta tashi ta na salati. Da fari idanun ta kan
Habeebti ya sauka ta na tambayar "lafiya kuwa?" Ganin ba ta da niyar ba
ta amsa ya ta ta waiga ta na "sai ka ce wacce ta ga faaataaalwaaaa" sai
a sannan ita ma ta gan shi ta tashi tsaye ta na fad'in Haroun uban me
ya kawo ka?
Haroun tsaye kamar wani gunki,ya k'ara kyau,girma,fad'i da kwarjini wane Dawud. Kan nan na sa ya sha kwalkwal da ka gan sa ka ga ma aboci saka kaki. yayi kusan minti goma tsaye falon,ba wanda ya san da shi sai Haroun junior da tun shigowar sa ya yi zaton Dawud ne ya dawo ya je ya rungume kafar sa ya na mai da ajiyar zuciya. Kallo d'aya ya yiwa yaran ya tabbatar shi ne dan da Habeebti ta haifa. Jin tambayar Hajiya ya sa shi sa hannu ya d'auki Haroun junior,ya sa shi kafad'a yayin da shi ma yaran ya juyo ya na mai duban su..tsabagen kama da ta gani sai da Hajiya ta ja za ta zauna,amma kalaman Haroun ne ya dakatar da ita,jin ya furta " ni ma nawa iyalin na zo d'auka....." Ya na magana ne idanun sa cikin na Habeebti,wacce idanun ta su ka bayyana tsana k'arara,cikin ran ta fad'i ta ke" kayya sai ka yi dana sanin dawowa cikin rayuwa ta HAROUN" Shi kuwa Haroun mai junior murmushi ya ke aika ma ta,cikin ran sa fad'i ya ke "ba a banza aka aurar da ke ga soja ba,rik'on mahaukaci sai sarki....."