Friday, February 22, 2019
"Please ka sanar dani Dr, ban gane ba" abinda Dr Umar yake fad'a kenan.
Dr Shamsudeen yace "Matarka nada ciki, Dr Umar, matarka nada juna biyu"
Kamar a mafarki yakejin maganar, cikin wani irin yanayi Dr
Umar yace "anya kasan abinda kake fad'a kuwa, na fad'a maka matsalar
matata, amma naji kana fad'a min abinda hankalina baze d'auka ba"
Sa ke kamo hannunshi yayi akaro na biyu yana mai nuni da
na'urar da ake scanny kafin kuma yace "zoka gani, ba karya nake maka ba
Dr umar, bama haka da kai"
Tabbas abinda ya fad'a hakan ne, gudan jininsa yake gani a
marar matarshi, tabbas shi ne, wata biyar da kwana goma gashi har abun
ya fara motsi, wannan ya nuna a watan da ya fara tarawa da ita a watan
Allah ya azurtasu.
" *Allahu Akbar* " shi d'inma yake fad'a, kafin kuma yafad'i k'asa yana sujjada ga mahaliccinsa.
Farida suman kwance ta yi, tabbas da bata gani da idanunta
ba da zata k'aryata, lalle ni'imar Allah ta buwaya, godiya ta ke ga
mahiliccinta ta na hawaya, lalle Allah ya mata kyautar da ba wanda ya
isa ya yayi irinta.
Ya azurtata alokacin da ta fitar da rai, "Allah na gode maka" abinda ta ke fad'a kenan ba adadi.
Kan kace meye Dr yayi waya yanata sanar da jama'a, ana
fad'awa Ummi itama fad'uwa k'asa ta yi ta na sujja domin godiya ga
ubangiji.
Shi kuwa Baba baza ka iya tan-tance tsakanin shi da Dr wanda yafi farinciki ba.
Tabbas duk wani masoyinsu sai ya tayasu murna, Alhaji ne yayiwa Ummi biza akan ta taho India domin kulawa da Farida.
Kasancewar likita yace mahaifarta ba karfi don haka bazata
juri zirga-zirga ba, sa'annan idan lokacin haihuwarta yayi baza abari ta
yi nak'uda ba za'a mata aikin acire abinda ke cikin.
Dakyar Dr ya hakura ya dawo Nigeria bakin aikinsa, sai da
Ummi ta nuna 6acin ranta sosai tukunna ya tafi, amma kuma tun da ya tafi
kullun yana ta re da Faridarshi a waya kuma duk bayan wata biyu yake
zuwa.
Dr yayi k'ok'arin kama musu hotel amma Dr Shamsudeen yace
yabari akwai d'akuna a gidanshi su zauna, mutumin sam bai mance irin
karamci da Dr yamai ba.
Yadda Mariya taga ana d'okin cikin taso ta sawa kanta
damuwa, toh amma daga baya sai ta cire komai aranta ganin ba dainawa
za'ayi ba, sannan kuma hakan da sukeyi bai tauyeta da komai ba kona
k'ank'anin lokaci.
**** ****
Ummi ce da Dr sun saka Farida a tsakiya sai rarrashinta sukeyi, ita kuma sai kuka ta ke wai ta na tsoro.
Haka dai dak'yar suka lalla6ata.
Allah mai kyauta da kari, Allah mai azurta wanda yaso alokacin da yaso.
Anfito da Farida lafiya ta re da yaranta y'anbiyu mata,
yara kam sai godiyar Allah, idan kaga Dr da Ummi aranar zaka d'auka a
ranar aka fara yimusu haihuwa.
Haka fannin Baba, bayyana irin farincikin da ya tsinci kanshi bazai yuwu ba amma kam yayi kuka yayi dariya, Allah kenan.
*******
Ummi na zaune ta na ninke kayan Ummi da Mama (sunan 'yan biyun kenan) kasancewar a washegari zasu dawo gida Nigeria.
Dr baya nan yana can yana cuku-cuku.
"Farida kinga ribar hakuri ko, Allah ya jarrabeki da
jarabawa kala-kala kinyi hakuri ba ta re da kin butulce ba, alokacin da
akace bazaki ta6a haihuwa ba nasan kin shiga wani irin hali, amma kika
jure "
"Sannan ya jarrabeki da jinkiri, daga 'karshe kika fara samun manema amma daga 'karshe sai su gujeki"
"Wanda kika amince dashi amma ana gobe d'aurin auranku suka
fasa, nan ma kin jure ba ta re da kin butulce ba, haka a zamanta kewar
auranki"
"Tabbas ke d'in me juriyace, da ma matan da suka samu kansu
a hali na jarrabawa zasu zama masu juriya kamarki da tabbas zasu zamto
masu sa'a"
"Domin ke kinga riba kuma riba ma har biyu kenan, kinada
lada awurin Allah gashi kuma aduniya ya azurtaki da miji irin wanda ake
cewa mijin marainiya, akarshe kuma ya azurtaki da yara biyu alokaci
guda, Allah ya albarkaci rayuwarki Farida"
Zuwa ta yi ta tsuguna agaban Ummi ta na hawaye tace
"Ummi kun bada gudunmawa mai yawa arayuwata, wallahi bani da abinda zan saka muku dashi sai addu'a, Ummina nagode Allah...."
"Shhhhhh" Ummi tace mata, kafin kuma tace "bana son wannan
hawayan naki, yanzu lokacinsa yawuce Farida, sannan ki rike godiyarki
bana so"
Rungume Ummi ta yi ta na fitar da hawayen farinciki, rayuwa kenan.
*****
Zaune suke a reception 'din filin jirgin sama, suna jiran
lokaci ya cika akirasu, Ummi na rik'e da Mama, Dr kuma na rungume da
Ummita a hannunshi na hagu, hannunshi na dama kuwa yana rungume da
Faridanshi .
Mutane biyu ne suka nufo inda suke, yar dattijuwan mace da kuma wani a gefenta da alama d'anta ne.
"Ina wuninku" cewar mutane biyun, Ummi ce ta iya ansawa itakuwa Farida mamaki ya hanata magana, tabbas Ahmad idanunta yake gani.
Dr kanshi mamaki ya hanashi magana.
"Farida karde wannan jariran naki ne" "Nata ne yau satinsu uku" Ummi ta bashi ansa.
"Amma da kince likitoci sun ce baza ki sa ke haihuwa ba, ya akayin hakan ya faru" wannan karan Dr ne yayi magana da cewa "Allah"
Juyawa yayi ga dattijuwan nan yace "Hajiya kin gani ko,
Allah ya azurta Farida da haihuwa ni d'in da kika hana na aureta har
yanzu shuru kingani ko"
Wannan dattijuwar da Ahmad ya kira da Hajiya ita tazo kusa da Farida had'e da kama hannunta ta na cewa
"kiyafe min, na hana ya aureki saboda ina tunanin bazaki
ta6a haifamin jikoki ba ashe na yi kuskure, Allah shi ne mai azurtawa,
ga Ahmad nan har yanzu shuru, ko 6atan wata matarshi bata ta6a yiba kuma
angwada lafiyanta kalau, kiyafemin don Allah"
"Ba komai na yafemuku Allah ya yafemana baki d'aya" cewar Farida
Karshe sukayi rabuwar arzik'i gami da jinjina halin karamci da yawan yafiya irin na Farida.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a tsakanin masoyan nan cikin farinciki da kwanciyar hankali.
*ALHAMDULILLAH*
Anan na kawo 'karshen wannan littafi na *SAKACI* kuskuren da na yi aciki ina neman gafarar Allah.
Gareku makaranta ina nemar afuwanku abisa tak'aita rubutun da na yi wanda wasu abubuwa ban fito dasu ba.
Wannan ya faru ne bisa ga 'karancin lokacin da na samu
kaina aciki, sannan nasan makaranta zasu ce mai yasa ban nuna makomar
"Hassan* ba, toh agaskiya *Hassan* da masu hali irin nashi Allah ne
yasan makomarsu da irin azabar da ya tanadar musu.
Ba abinda zance muku sai Nagode, Nagode, *I LOVE YOU ALLSAKACI Part 27
Alhaji abin da na gani ya tsorata ni, tabbas anyi wa
yarinyar nan sammi, shi kuwa yaron nan 'karfin addu'a ne ya ku'butar da
shi, yanzu zanyi k'ok'ari na karya wanda zan iya sauran kuwa dole se
munje gidan domin anyi birne-birne da yawa a cikin gidan"
Cewar Sheikh Muslim.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" abinda su Alhaji suke mai-maitawa kenan,
"Malam toh a gidan mijin nata ne akayi birne-birnen, kokuwa a ina ne?" Ummi ta tambayeshi.
"A'a agidan mahaifinta ne, yanzu ga wannan, ganyen magarya
ne da addu'o'in karya sihiri, ku shiga cikin gida zan sanar dasu yanzu
kije ki ma ta wanka dashi sannan ki bata tasha, sauran kuma sai kun
gama"
Farida na gama sha bayan an mata wanka ta fara wani irin bak'in amai, lokaci guda zazza6i ya rufeta.
Koda Sheik ya ganta yace ba damuwa hakan yana nuna sihirin ya karye kenan.
Alhaji yace "Shiek naji kace anyi birne-birne acan gidan mahaifinta yanzu meye abin yi"
Sheik yace "haka ne amma fa dole sai naje gidan da kaina sanna za'a tone su gami da karya dafin su"
Alhaji ne ya rok'eshi akan don Allah ya sallami iyalanshi suje bauchin haka kuwa akayi.
Sunyi k'ok'arin kiran Baba amma wayarshi akashe, na Aunty kuma bata d'auka ba.
Don haka kai tsaye gidan suka zarce.
Tun daga waje suke jiyo murya Aunty tana fad'a, ko
sallamarsu bata ji ba, abinda suka gani bayan sun shiga yayi mugun d'aga
musu hankali, shin dagaske ne ko kuwa gizo idanuwan su suke musu.
Baba ne zaune akasa Aunty ta na ta surfamai bala'i, kanshi a kasa tamkar yaron gida da ubangidanshi.
Shigowansu yayi dai-dai da kwara mai miyan da ta yi akanshi, cikin gi-gicewa yake cewa.
"wayyo Allah idona bana gani Aunty ki taimake ni" da gudu sukayi kanshi cikin tausayawa.
Cike da 6acin rai Farida tace "mai ya miki" ba ta re da ta bata ansa ba, ta yi hanyar fita cike da rashin gaskiya.
Sheik ne yace."Karku barta ta fita" da hanzari Dr yaje ya rufe kofar da key.
Sheik yace baiwar Allah zo ki zauna kifad'a mana duk wani sharri da kulla-kullen da kika yi"
Cike da rashin gaskiya tace "wani kulle-kulle kuma na yi, kokuma kunzo ne kumin sharri har gidana, toh wallahi bazan yarda ba"
"Akan me zaku zo har gida kuce zaku ritsa min mata ta wallahi ku fita min daga gida munafukai" Baba ya fad'a cikin hargagi.
Alhaji zaiyi magana ya katse shi da cewa "nasan kai
kashirya komai kuma wa ma ka d'auko nake jin muryashi kuka shigo min
gida, to ka kwashesu kubarmin gida"
Duk wannan maganar da yakeyi idanunshi basu bud'e ba, ga kuma rand'ad'in da suke mai.
Ran Alhaji idan yayi dubu ya 6aci zai sa ke yin magana.
Shiek ya sake katseshi da cewa "karka ga laifinshi ba cikin hayyacinshi yake komai ba"
Wannan ya fad'a ne cikin rad'a wanda Alhajin ne kawai yaji abinda yace d'in.
Sheik Muslim ne ya d'auko wani ruwa ya mik'awa Alhaji yace " maza bashi ya kur6a sannan ka shafamai ajiki zai rage mai rad'ad'i"
Shidai Alhaji yaga irin ruwan da akaba wa Farida ne amma sai yabi umarnin Sheik ya aikata abinda yace d'in.
Kasancewar shi Baba azaba ta dameshi a idanunshi har kuma baya iya bud'esu yasa ya yarda.
Cikin hanzari Aunty ta taso da niyar kwa6ar da maganin,
amma kafin takai ga hakan Sheik da yake ankare da ita yasa mata kafa, ba
ta re da ta idar da nufinta ba ta jita a kasa.
Sannan ya bita da wata gigitacciyar tsawa wanda ta sata nutsuwa ba tare da ta yi niya ba.
Hannu biyu ta ke rokon kar azubawa Baba wallahi zasu
kasheta, ba ta re da 6ata lokaci ba kuwa Alhaji yaba Baba yasha, Baba
yana cewa
"Kwantar da hankalinki Aunty da zaran idanuna sun bud'e
zanyi maganin........" Bai kai ga k'arasawa ba ya fara kwara wani bakin
amai tamkar zai fitar da hanjin cikinshi, Alhaji da Umar ne suka
rik'eshi.
Sai da aman ya lafa tukunna Sheik Muslim ya juyo ga Aunty yace "za ki je ki tone abinda kika birne kokuwa saina yi maganinki.
"Kana tunanin zan bi umarninka ne, toh wallahi kayi karya sai naga bayansu"
"mutanan da suka rik'eki amana kike ikirarin sai kinga
bayansu, anya akwai zuciya a k'irjinki kuwa, mai suka miki, mai suka
tsare miki" cike da damuwa Ummi ta ke tambayarta.
"Tabbas da zuciya a kirjina ita d'ince ma ta shawarce ni da abinda nakeyi"
"Sun rabani da farincikina, suna tunanin zan barsu da nasu
ne, kokuma suna tunani zan aureshi ne, na zauna dashi tsawon wannan
shekarun ba ta re da na sa ke haihuwa ba, kuma ace ban damu ba"
Ta k'ara da cewa "toh bari kuji na zauna dasu ne dan d'aukan fansa"
"Mai muka miki, na rik'eki tankar uwa mai yasa haka" Farida ta fad'a
"Idan ku kun manta bari na tuna muku, bayan auran mu dashi
na yi k'ok'arin kawo yarana gidan nan saboda tarbiyarsu da ta fara
lalacewa inaso na kawosu gabana domin na kula da su"
"amma sam yak'i amincewa yace yana tsoron kar asake 6ata miki rayuwa, tunda yarana mazane kuma sun kawo girma"
"Na yi magiyar amma yaki amincewa k'arshe yace sai dai na
nemi yardarki, koda muka miki maganar fashewa da kuka kikayi, nan kuma
mahaifinki yace sam baisan zancen ba"
"Kuna tunanin hakan yamin dad'i ne, sai kuma bayan an kwana
biyu sai ga Umar ya dawo gidan nan da zama, sai nace toh ko shi ba
namiji bane"
"Abun yamin zafi ba kad'an ba, daganan na k'udiri aniyar
d'aukan fansa ta dabara, na mallake Alhaji ba ta re da kowa ya sani ba,
sannan na yi k'ok'arin yiwa Umar asiri akan ya afkawa Farida"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" abinda su Alhaji suke fad'a kenan.
"Sai dai duk lokacin da malamina ya yi aiki akan shi sai muga haske ya baibaye shi, sam sihirin yakiyin tasiri a kanshi"
"ak'arshe na farrak'a tsakaninsu, sannan aka tura musu sha-shatau a harkar ibadar su, ta yadda asiri zai yi saurin kama su".
"Domin inaso na tozarta Farida ta yadda bakin ciki zai zama
silar mutuwar mahaifinta, lokacin da kuka munafurceni kuka had'a
aurensu, shi ne na tashi tsaye"
"Tabbas da Umar ya sake ya kusanceta da shida mazantarkarsa sunyi hannun riga, ita kuma alokacin zata bak'unci lahira"
"Toh amma sai yayi taurin kai, koda malamina ya duba sai yaga addu'ar da kuke mai ne ta hana sihirin yin tasiri akanshi"
"A wannan lokacin ba dan naso ba dole na 'kyale shi, randa
tazo gidan nan na k'arshe na bata maganin da idan tasha dole ne taje ta
nemi wani namijin.
"Na tabbata da zaran ta mutu shima dole ya bakunci lahira, kuma ko ayau kuka kashe ni na rama bakincikin da suka cusamin"
"Domin sai abinda naga dama yakeyi a rayuwarshi, abinci da magani sai naso yake anfanuwa dasu"
Kuka sosai Baba yake yi yana cewa "kije na sa keki, tabbas
nasan kin bani wahala iyakar wahala, amma me yasa kika nemi ki cutar da
Farida me yasa baki tsaya akaina ba, ni nasan alhakin Sakinatu ne yake
bina, amma mai yasa Farida"
"D'aga hannu sama yayi yana cewa "Allah na tuba ka yafemin tabbas naga rayuwa ina neman yafiyanka ya Allah"
Ummi ce tace " tabbas kin cika muguwa, mai yasa za ki cutar
da yarinyar nan, bayan kin san duk irin abubuwan da ta fuskanta
arayuwarta, Allah ya isa tsakaninmu da ke"
Aunty ko kallonsu batayi ba taje ta fito da akwatinanta
gami da cewa "sauran kayan nawa na aiko a kwashe mun" ta na gama fad'ar
haka ta fice.
Dr yace baza ta fita ba dole a mik'ata ga hukuma, Baba yace "barta Umar wallahi na yi imani duniya zata koya mata darasi"
Daga Ummi, Farida har Baba kuka sukeyi sosai Sheik Muslim
da Alhaji da Dr su suka tono duk wani sihirin da aka birne agidan,
d'akinta ma basu bari ba nan magungunan da aka samu ba'a cewa komai.
"Kai mutun mugun ice ne" cewar Alhaji, nan fa Alhaji da
kanshi yaba Sheik Muslim labarin irin gwagwarmayan da bayin Allah nan
suka shiga, ya tausaya musu matuk'a.
Bayan sun zauna ne Sheik Muslim ya fara magana kamar haka.
"Zan fara ta kanki Farida lalle kin fuskanci jarabawa arayuwa kuma kin jure, wanda muke miki zaton rahmar Allah a rayuwarki"
"Allah subhanahu wata alah yana jarrabar bawanshi yadda
yaso da kuma lokacin da yaso, ba kuma domin baya son ka bane, a'a yana
sonka, sai dai yana gwada imaninka ne"
"Tabbas kin jure irin jarabawar da kika tsinci kanki aciki,
kuma ladanki na wurin Allah kuma za kiga irin sakamakon da zai miki
imma ki fara gani tun aduniya kokuma sai anje lahira"
"Alhaji Sulaiman tabbas kayi *SAKACI* da amanar da Allah ya damk'a maka na iyalinka, ka kuma ga irin kamun da Allah ya maka.
Wannan na duniya kenan Allah kad'ai yasan na lahira, kaga
ahaka ma ka tuba ne da badan haka ba Allah kad'ai yasan a ina abun zai
tsaya"
"Yan uwa ina muku nasiha da duk wanda Allah ya dam'ka muku
amanarsu toh fa ku rik'esu hannu biyu, domin akwai ranar da za'a
titsiyeka a tambayeka irin rik'on da ka musu"
"Don haka sai mun jajirce, abu k'ank'ani shi zai zama silar
shigar da mu aljannah haka kuma abu k'ak'ani na zunubi zai kai mu ga
shiga wuta"
"Alhaji Muhammad kai da iyalinka kun birgeni matuk'a, duk
iyaye nagari ya kamata ace su kasance masu addu'a ga y'ayansu kunga
k'arfin addu'a ko, toh Allah ya shige mana gaba"
"Kai Umar ka d'auki iyalinka ku tafi, ka kuma rik'eta da
amana kekuma ki cigaba da kare hakk'okin Allah, Allah yasa muku albarka
azamanta kewarku"
Addu'a sosai akayi a gidan kafin kowa ya kama gabanshi
Rayuwa kenan, Aunty dai sai labarin rasuwarta sukaji, a
hanyarta tafiya ne, ta yi hatsari, adalilin shigewa 'kar'kashin babban
mota da ta yi, a ta Allah yayi ikonshi akanta, ko shurawa bata yi ba.
Lokacin da Baba ya samu labarin cewa yayi a wuce da gawarta
gidan iyayenta, ba yadda ba'ayiba yace ya yafe mata duk abinda tamai,
sai dai bazai yafe mata cutar da Farida da taso ta yi ba.
**** ****
"Rungumeta yayi sosai ajikinshi yana cewa "Faridana kinga yadda Allah ku6utar damu ko"
Kafin ta yi magana Mariya ta shigo fuskar nan tasha kuka.
"Dr ina buk'atar ka sauwak'a min, please ka bani takardata nagaji, gwara na barka da ita kafin hawan jini ya kamani"
Sa ke Farida yayi daga rungumar da ya mata, kafin kuma yaje
ga Mariya, hannunta ya kama suka fita, bai sa ke hannun nata ba saida
ya sadasu da falonta.
Zama yayi akan kejera kafin kuma ya zaunar da ita agefenshi, bai kai ga magana ba ta fashe da kuka.
Rungumeta yayi yana rarrashinta har ta yi shuru kafin yace "na miki laifi Mariya amma ina rok'onki da kiyi hakuri"
"Dr ni nasan baka sona kana zaune dani ne dan dole, kawai mu hakura da juna"
"Wa ya fad'a miki ina zaune dake ne dan dole, abinda nakeso
kisani ba'ayiwa namiji dole, kuma da zaran namiji ya gaji da mace bazai
zauna da ita ba"
"Zan can kuma kice bana sonki idan bana sonki da tuni
kinbar gidan nan, Mariya kece matata ta farko kuma uwar yarana, bana
rok'on Allah yabani ikon cutar da ke"
"Please ki kwantar da hankalinki, Farida kanwata ce, Mariya
tun Farida na 'karama muke ta re, bani da wata 'kanwa bayan ita, na
sha'ku da ita fiye da tunaninki"
"Farida mace ce mai kyawun halaye, Mariya, don Allah ki
rungumeta da hannu biyu bazan bari d'aya ya cutar da d'an uwanshi ba,
Mariya kizo muzama y'an uwanjuna"
"Please ki cire komai a ranki, ki kwantar da hankalinki"
Tabbas maganganu da ya fad'a sun shige ta kuma sun mata
da'di, dama kishi ne ya mata yawa amma Dr bai ta6a nuna mata wani abu
ba, haka kuma Farida hasalima duk abinda ta ke yi Farida bata ta6a tanka
mata ba.
Gaskiyan Dr ne Farida mace ce mai kyan hali, don haka dole
ta zubar da makamanta, ta rungumi mijin ta gami da zama lafiya da
abokiyar zamanta.
**** ****
Bacci ya fara d'aukanta taji tamkar hannun mutun ajikinta,
farkawa ta yi a firgice gami da kunna wuta, shi ta gani yana mata wannan
murmushin nashi mai tafiya da hankalinta.
"Kai Ya Umar bafa haka ake ba, kawai sai kazo ka firgitani" ta fad'a cikin shagwa6a.
"Oya zo ki koyamin yadda akeyi"ya fad'a yana janyota jikinshi.
"wai meye haka nifa ka tafi d'akinka" ta fad'a ta na ja da baya.
Rungumota yayi sosai har tanaji k'aran bugun k'irjinshi, cikin wata irin murya mai cike da kasala yace.
"Please Farida kizo kimin wallahi inbakiyi min ba mutuwa zanyi" kunya sosai taji, kai amma wallahi Aunty ta cuceta.
Rufe fuskarta ta yi da k'irjishi shima 'kan'kameta yayi a
jikinshi yana ra'da mata wasu manya-manyan kalamai a kunnanta wanda suka
rikita mata tunani, nan fa salo ya canja.
**** ****
Masoyan nan rayuwa suke mai cike da k'auna gami da tattalin
juna, idan kaga yadda suke tafiyar da rayuwarsu abin sai ya baka
sha'awa.
Mariya da Farida sun d'inke sosai ba mai jin kansu, mutunci
da girmama juna ne a tsakaninsu, basu da buri sai na kyautatawa
mijinsu, gami da tattalin yaransu, sosai Farida ta janyosu ajiki dama
kuma sun saba da ita.
**** ****
Dr ne ya shigo d'akin ganin bata falo yasa ya zarce d'akin kwananta kai tsaye, ta na cikin bargo, yaye bargon yayi gami da cewa.
"My Farida kar dai kice min baki shirya ba" murya canciki tace "Ya Umar kaina kamar zai tsage"
Subhanallah tun yaushe" ya fad'a gami da zuwa kusa da ita,
kafin kuma yakai hannunshi jikinta, jikinta yayi zafi sosai, hankalinshi
yayi matuk'ar tashi.
Baya son duk wani abinda zai damu Faridarshi.
"Faridana kinji jikin ki kuwa mai yasa baki sanar dani tun wuri ba"
Kayan aikinshi ya d'auko ya fara gwada ta, kafin kuma yace.
"kina da sirinji na d'ebi jininki ya kamata naje agwada dan na tabbatar da abinda yake damunki, zafin jikin naki yayi yawa"
Nuni tamai da hannu inda ta ke ajiye kayan aikinta, ba ta
re da 6ata lokaci ba ya d'ebi jininta gami da cewa "bari na turo miki
Mariya sai na dawo, zan taho miki da magunguna".
Duk irin gwaje-gwajen da ya kamata amata anyimata amma ba'asamu wata cuta a ta re da ita ba, malaria ne ma aka samu kad'an.
Farida na jinjiki an kuma rasa gane ainihin abinda ke
damunta takamai-mai, idan kaga Dr awannan lokacin sai ka tausaya mai,
Mariya ita ta ke kulawa da ita.
Tun ta na iya tashi har takai sai an kwantar an tayar,
gashi sai kunbura ta keyi daga bayan nan, hankalin kowa ya tashi, dole
Ummi ta dawo Bauchi suka cigaba da jinyarta.
Baba kanshi kullun yana hanyar gidan hankali tashe, ranar da Alhaji yazo dubata ya shiga damuwa matuk'a har ya ke cewa Dr.
"Umar rashin lafiyan Faridan nan ya dameni matuk'a anya
baza ka fita da ita waje aduba zuciyarta ba dubi fa yadda ta ke kumbura
gaskiya abun ya dameni"
Kuka sosai Dr yake tamkar 'karamin yaro, yana cewa "Alhaji bana so na rasa Farida, wallahi bazan iya rayuwa ba ita ba"
Alhaji yace "Umar karkayi sa6o fa, Allah baya barin wani
dan wani, zan cen ba zaka iya rayuwa ba ka daina, Allah zai iya d'auketa
yaga yadda za kayi don haka addu'a zakayi sannan ka nemi kud'i kayi
k'ok'arin fitar da ita k'asar waje ta na buk'atar taimako gaskiya"
Ya juya ga Farida da ta ke kwance da robar ruwa mak'ale a hannunta, yace "sannu Farida, yanzu me yake miki ciwo"
Dafe kanta ta yi da hannu alamar kan ne yake damunta, Ummi
ce tace "wannan ciwon kan na rasa irinshi wallahi, sam baya jin magani"
"Allah ya baki lafiya, ya tashi kafad'unki" ficewa Dr yayi daga d'akin domin sosai wa'dan nan addu'o'in suke kashe mai jiki.
**** ****
Acikin kwanaki k'alilan Dr ya kammala shirye-shiryen fita
da Farida India, shi da ita ne kawai zasu tafi kasancewar yadda ake fama
da rashin kud'i.
Ranar lahadi jirginsu ya d'aga, sai addu'ar dacewa daga masoya.
**** ****
Kasancewar Dr yasan likitoci sosai acan yasa basu wani sha wahala ba, sun samu kulawa sosai.
Dr Shamsudeen, babba likita ne kuma k'wararre a fannin
jikin d'an adam, ana matu'kar ji dashi a 'kasar India, shi ne kuma yake
duba Farida.
Tun bayan zuwan su jikin Farida ya matsa fiye da tunani har takai idan ka ganta sai ka tausaya mata.
Sosai likitoci suke bincike akanta amma har wannan lokacin ba'a samu wata cuta a ta re da ita ba.
Idan kaga Dr za kayi tunanin shima bashi da lafiya ne, ya rame sosai.
Dr Shamsudeen ya gama duba file 'din Farida, gami da tatta6a jikinta, kana ya juya ga Dr Umar.
Yace "Dr Umar maganar gaskiya bazan yaudareka ba, munyi
ikar 'ko'karin mu amma mun kasa gano ainihin abinda yake damunta, kana
gani a idonka akayi komai"
Ya cigaba da magana da harshen nasara, "agaskiya shawara d'aya zan baka a matsayinka na 'dan'uwana musulmi, ku dage da addu'a"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" kawai Dr Umar yake mai-maitawa cikin matsanancin tashin hankali.
Dr Shamsudden ya d'anyi shiru alamar tunani kafin kuma yace "amma inazuwa"
Ma'akatan lafiya yayi wa umarni da sukai Farida wani d'akin gwaje-gwaje.
Yafi awa guda yana aunata cikin gwanancewa.
Dr Umar yana gefe ya kasa ta6uka komai, damuwa tamai yawa, wai me yake faruwa ne ya kasa gane komai.
" *Allahu Akbar, Allahu Akbar* " abinda Dr Shamsudeen yake fad'a kenan, cikin farinciki, muryarshi har rawa ta ke.
Dr Umar ne ya taso cikin gaggawa yana cewa "me yafaru Dr, mene ne don Allah ka sanar dani"
Kamo hannunshi kawai Dr shamsudeen yayi ba ta re da yayi magana ba.
~Ummu Hanan~
Share this
SAKACI Part 26
D'agata yayi ajikinshi gami da cewa "kibar damun kanki Farida yi musu addu'a, ki kwanta sai da safe"
Wani abu ne ya tsaya mata a mak'ogwaro wanda har ta kasa yin magana.
Wai me yake faruwa da ita ne, "wayyo nashiga ukuna" fad'a ta ke cikin kururuwa.
Ga baki d'aya duniyar ta ma ta zafi wani irin shauk'i da
kasala ne yake d'ibanta, ita kam da badan ta najin tsoron Allah ba, babu
abinda zai hanata fita yawon bariki, ita kad'ai tasan yadda ta keji.
Bacci ya k'aurace wa idanunta, ta rasa tudun dafawa, ta na buk'atar mafita.
Toilet ta shiga da zummar ta yi wanka gami da d'auro alwala
ta kai kukanta ga mahaliccinta sai dai ta na shiga ruwan zafi ta fara
hamma alamar bacci.
Alwalar da bata yi ba kenan ta dawo ta kwanta.
Washegari haka ta wuni da ciwon kai, kuma ta kasa ta6uka
komai a wurin aiki har sai dai Jidda ta lura kawarta ta na cikin damuwa.
Bayan aiki ya mata sauk'i ta sameta ta na tambayarta abinda
yake damunta, ba taso ta sanar da ita, sai dai ta na bukatar mafita
saboda hakurinta ya gama k'arewa.
"Jidda ban san me yake damun mu ba nida Dr bansani ba jidda" ta k'arshe hawaye na zuba daga idanuwanta.
Cikin rashin fahimta Jidda ta ce " kawata bangane me kike nufi ba kiyi min gwari-gwari"
"Kinsan na fad'a miki zuwan mu Jos komai ya dai-daita ko" Jidda ta ce "tabbas anyi haka, toh yanzu wani abun ne ya sa ke faruwa"
"Jidda, Dr kwata-kwata yak'i had'a gado dani, ni kuma
nakasa hakuri, ni ban san me yake faruwa ba, wallahi ni nasan yadda
nakeji, har takai yanzu idan naga namiji a waje inaji tamkar naje na
rungumeshi"
"Na rasa gane kan wannan abun wallahi" Jidda ta fad'a cike da tausayi.
"Wallahi bariki zan shiga" "Innalillahi wa'inna
ilaihirraji'u, Farida karna sakejin wannan kalmar a bakinki, karki sake
aikata wani sa6on da yafi na baya girma"
Farida tace "Jidda ya zanyi wallahi hakurina ya k'are ina
bukatarshi, na rasa me yake damuna, kikaini asibitin mahaukata a dubani
Jidda"
Wani irin tausayin kawarta ne ya tsirga mata, wannan wace
irin jaraba ce take tunkaro su, asaninta da Farida bata ta6a yi mata
maganar da ta dangacin hakan ba, balle ta yi tunanin ta na daga cikin
jinsin da suke da yawan buk'ata.
Cikin sanyi murya Jidda tace "kawata karna sakejin kin
fad'i wannan maganar, dole mu samu mafita amma kafin nan yau kwananki ne
ko na Mariya?"
Farida tace "na Mariya ne" Jidda tace "yanzu sai zuwa jibi kenan zai dawo gareki ko"
"Eh" Farida tace, Jidda ta k'ara da cewa "yanzu abinda
nakeso dake shi ne ki yi azumi a wannan kwana biyun kinga na farko ga
lada sannan zai rage miki yadda kike ji"
Cike da damuwa Farida tace "wallahi Jidda yanzu bana iya
yin azumi bansan ya zanyi a watan Ramadan ba, mubar wannan maganar kawo
wata shawara"
"Farida abun yakai haka" Jidda ta fad'a cike da mamakin
kawarta, domin asanin da ta yiwa Farida ada mace ce mai rik'o da ibada,
yanzu me ke faruwa da kawarta ne.
"Toh karki damu yanzu dai kiyi hakuri zuwa ranar da girki
zai dawo hannunki, zo na fad'a miki yadda zakiyi na tabbata Dr bazai
ta6a tsira da wannan tarkon ba"
**** ****
A kwana biyun nan idan ka kalli masoya biyun nan zaka ga suna cikin damuwa, baram ma Farida da ta rame ta dawo wata iri da ita.
Lokaci guda ta dawo mara walwala.
Ranar da ta kar6i girki bayan ta tashi daga aiki ta aika mai sak'o ta waya tana sanar dashi zata je ta duba Baba.
Kasancewar kwana biyu ta kasa samunshi a waya, kuma idan ta
kira number Aunty sai tace mata baya kusa, hankalinta sam yaki
kwanciya.
Cewa yayi ta jirashi yazo suje tare, ba'a jima ba kuwa yazo, don haka a motarshi suka tafi tabar tata a asibitin.
Koda sukaje kofar gidan ya ajiyeta akan idan yazo d'aukanta bayan magriba ya shiga su gaisa da su Baba.
Da sallama ta shiga gidan amma ba kowa a falo, kitchen ta
fara dubawa, Babanta ta gani ya nad'e hannun rigarshi yana zuba abinci a
wormer abun ya bata mamaki.
"A'a Farida kece da yamman nan" Baba ya fad'a fuska a sa ke.
"Eh Baba, kai ne da kanka a kitchen" " eh wallahi Auntyn taki ce ba lafiya shi ne nake temakawa"
Cikin damuwa Farida tace "toh Baba kai da ba lafiya ba ina Iya ta ke"
Murmushi yayi gami da cewa " Iya ta tafi garinsu, kingan ni nan jikina yayi sauki sosai"
"Baba amma mai yasa ba'a nemo wata ba" farida ta fad'a gami da kar6an cokalin kwasar abincin.
"Farida naga kin rame, ko akwai abinda ke damunki ne" ya tambayeta ba ta re da ya bata ansar ta ta tambayar ba.
"Ba komai Baba, gaskiya yakamata asamo wata, dan wannan aiki ai banaka bane" farida ta fad'a cikin tausasawa.
"A'a Farida yaushe kika shigo" Aunty ce ta fad'a yayin da ta shigo kitchen d'in, "ban jima da shugowa ba" ta bata ansa.
Ita sam bata ga alamar rashin lafiya a tare da ita ba,
Allah sarki Baba yanzu yana k'ok'arin kyautatawa iyalanshi, bata mantawa
lokacin ta na karama ta na yawan ganin Alhaji na taya Ummi dafa abinci.
Amma ita yanzu sanin irin yanayin da yake ciki baza taso ya wahala ba.
**** ****
Bayan magriba Dr yazo d'aukwanta, kayan arzik'i sosai ya
kawo gidan, sosai ta yi farinciki, wannan ne ya goge kashi 80% na
haushinsa da ta keji.
Kafin su tafi Aunty ta sake kawo mata wani jik'o akan tasha.
"Aunty nikam abar wannan abun" " akan me za'a bari Farida, wayace miki yanzu ana zama" Aunty ta fad'a.
"Aunty nikam abarshi kawai ba yanzu ba, wallahi damuna yake nikuma ba wani abinda ke shiga tsakanin mu"
Murmushi Aunty ta yi gami da cewa" oh yaro man kaza, kar6i nan wannan shi zai juyo da hankalinshi zuwa gareki"
Ba dan taso ba haka ta k'ar6a ta shanye, amma tunkafin tabar gidan ta ke da tasanin sha.
Kwanciyar hankalinta d'aya irin yadda taga yana mata a motar nan, nan ne tasan yaufa ba ita kad'ai bace abun ya motsa.
Suna zuwa gida ta bud'e jakarta cikin wani irin salo tace "ka ganka ko"
"Me na yi " ya fad'a yana kashe mata ido, "ba kai bane kasa na manta key d'akina a asibiti cikin motata"
"Yau awaje za ki kwana kenan" "ni gaskiya a'a kazo mu koma na d'auko" ta fad'a cikin shagwa6a.
"No ba inda zan koma,kuma kema bazaki koma ba" ya sake fad'a, bubbuga kafarta take gami da cuno baki alamar shagwa6a.
Fita yayi ya zagaya ta inda ta ke. Batayi aune ba taji ya
d'auketa tamkar yarinya k'arama, sa ke lafewa ta yi a k'irjinshi tana
shak'ar kamshin shi.
"Farida na gaskiya ba haka ake ba, you're a doctor kina ba mutane shawara akan su rage k'iba but ke kinata hawa"
Turo baki ta yi gami da cewa " Allah ni sharri kakemin, ba haka bane" murmushi yayi ba ta re da ya sa ke magana ba.
Bai ajiyeta a ko ina ba sai akan gadonshi ya fad'i yana mai da nunfashi waishi ya gaji, muntsininshi ta yi.
"Faridana mugunta ne kuma, oya tashi kije kiyi wanka daganan ki d'auro alwala"
"Ni Allah nagaji sai da safe zanyi" ta fad'a cikin kasala, "ko kitashi kije kiyi kona d'auko ruwan cikin fridge na miki dashi"
Tashi ta yi tana dariya.
Bayan sun idar da sallah ita da kanta ta fad'a jikinshi, d'aukanta yayi ya d'aurata akan gadon.
Komawa gefe yayi ba tare da ya iya yin komai ba, bargo ya janyo gami da rufesu, kafin kuma yace.
"Kwanta kiyi baccin ki kinji"
Wani irin bakinciki taji ya taso mata, cikin dashewar murya
tace "ya Umar mai yasa kakeyi min hakane, nagaji, nagaji hakurina ya
k'are wallahi bariki zan shiga"
Tashi yayi cike da tashin hankali ya kunnan wuta, k'ok'arin bud'e kofa ta ke, daga ita sai tawul ajikinta.
Zuwa yayi da sauri yasha gabanta gami da cewa.
"Ina zakije daddaran nan" "bazan iya ba Dr zanje na nemi wani tunda kai kasa yimin" cikin damuwa yace
"Farida anya kinada lafiya kuwa, kodai kinsha wani abu ne" fad'awa jikinshi ta yi gami da k'ank'ameshi, ta na cewa
"Ban san me yake damuna ba, nidai ka taimakeni Ya Umar idan
ba haka ba wallahi ko wurin su Baba maigadi sai naje sunyi mun, wallah
idan ba'ayi min ba mutuwa zanyi"
"Kar na sake jin haka a bakin ki Farida ba kyau haramun ne, muje na miki"
Sam ya kasa aikata komai, cikin damuwa yace Farida na kasa wai shin me yake faruwa damu ne, nakasa yin komai me yasa"
Tureshi ta yi gami da tashi da sauri ya kamota yana kiyi
hakuri zan nemi mafita, "wallahi bazan iya ba ni ayau nakeso amin, kuma
sai naje anyi min"
Tabbas da gaske ta ke zata aikata abinda ta fad'a, to me yake damunta ne, zare key d'in d'akin yayi ya 6oye.
Tabbas ranar basu rintsa ba, yayi tunanin Faridan shi ta samu ta6in hankali ne, sunga tashi hankali ba karami ba.
Da asubar fari ya jata suka shiga mota Jos suka nufa ba wanda yayi sallah acikinsu balle wanka.
Karfe shida da rabi na safe suka isa, kai tsaye gidan Ummi suka nufa.
Daga Ummi har Alhaji hankalinsu yayi muguntashi cikin yanayin da suka ga yaran nasu, cike da damuwa suke tambayar yaran nasu.
Dr ne yace "Alhaji akwai damuwa" Alhaji yace "me yake faruwa ku sanar damu hankalinmu atashe yake"
Nan take Dr ya sanar dasu komai, cikin 6acin rai Ummi tace
"wato har yanzu bakabar bakin kishin nan naka ba, tabbas yau saika
sauwak'ewa yarinyar nan"
"Ummi ki rok'a min shi yazo yayi" Farida ta fad'a kafin
kuma taje ga Dr ta ne kamashi ta ne cewa, "Ya Umar ka taimakeni badan
halina ba"
Hawaye ne ya fito daga idanuwanshi yace "Ummi wallahi na
rantse miki da Allah ba kishi bane nima ban san me yake damuna ba, kinji
yanzu abinda ta ke fad'a ni kuma na kasa Ummi"
Alhaji ne yace "Ummi rik'e hannunta ku shiga ciki, zanyi magaba da Umar"
Bayan su Ummi sun shiga ciki, Alhaji ya juyo ga Umar yace.
"Umar yaushe ne ka samu wannan matsalar domin nasan da kanada lafiya tunda gaka da yara" Alhaji ya fad'a.
"Wallahi Alhaji har yanzu lafiyata kalau, idan ina tare da
Mariya hakan baya faruwa amma da nazo wurin Farida komai sai ya sauya
kuyi mana addu'a Alhaji bana so Farida ta jefa kanta a hatsari"
"Tashi muje" Alhaji yace da Dr, kafin kuma yayiwa Ummi waya da ta d'auko gyalanta su taho da Farida.
**** ****
Wurin babban malami sukaje, kuma babban limamin ne a wani babban masallaci, masani ne sosai a harkar addini.
Zaune suke agaban Sheik Muslim Anas, sannu ahankali Alhaji ya fayyace mai komai.
Kallonsu yayi sosai kafin ya juyo ga Alhaji yace "a gaskiya
Alhaji wannan al'amari akwai d'aure kai, amma fa ina tunanin sammu
akayiwa yaran nan, sai dai kasan sanin gaibu sai Allah, yanzu kuje gida
karku bari yaran nan su aikata komai ita kuma ku bata kyakkyawan kulawa,
domin komai na iya faruwa"
Zanyi istihara duk abinda ake ciki zan nemeku da safe, amma
zan dad'a jaddada muku ku kula dasu sosai kuma karku fad'awa kowa
abinda ake ciki"
Godiya sosai Alhaji yayiwa malam, kafin suka tafi.
**** ****
Da safe wurin karfe sha daya, kiran sheik ya shigo wayar Alhaji yace mai za yana kiransu da gaggawa.Share this
SAKACI Part 25
Ya na fitowa daga masallaci, kai tsaye d'akin kwanan Ummi
ya wuce, ita kawai yake so yasa a ido, sam jiya bacci ya k'auracewa
idanunshi, wani irin kewarta ya keji.
Kwance ta ke a kan gadon ta na bacci, duk rabin cinyoyinta a
waje kasancewar rigar baccin ta tattare, wani irin shauk'in kaunarta ne
ya ke d'ibanshi, a ta ke ya saukar mai da wata kasala.
Kujerar dressing mirrow ya janyo zuwa bakin gadon kafin kuma ya zauna, tallafe ha6arshi yayi da hannu biyu.
Kallonta ya ke tamkar idan ya d'auke idanuwanshi zata 6ace,
ji yake tamkar yaje ya kamata ya rungume abarsa, cikin wata irin murya
mai cike da shauk'i ya ce.
"Farida ina sonki, ina tsananin k'aunarki ba zan iya rabuwa da ke ba matata, domin kece farincikina"
Cikin bacci ta ke tajiyo maganganu, a hankali ta bud'e idanunta wanda suka sauka akanshi.
Da sauri ta janyo zani gami da rufe jikinta har ma da kanta, ya jima ya na zaune kafin daga bisani ya mik'e had'e da cewa.
"Idan kin gama ki sa meni a d'akina" daga haka ya juya ya tafi cikin tafiyarshi ta k'asaita.
**** ****
Sai da ta yi wanka, wannan karan ma ba ta yi wani kwalliya
ba gudun kar a fad'a mata maganganu marasa dad'i, sai da ta feshe
jikinta da turare kafin ta fita.
Kai tsaye d'akinshi ta nufa, sallama ta yi, sai da ya bata
izini kafin ta shiga, ba ta yi k'ok'arin zama ba domin yau kam baza ta
iya jure munanan kalamansa.
Sai dai kuma yanayin da ta ganshi a ciki ya bata mamaki tamkar ba Yayanta ba tagumi yayi da hannuwanshi biyu.
Ya d'an jima ahaka kafin ya d'ago kai ya kalleta, cikin sanyin murya ya ce "Bismillah zauna mana inaso muyi magana ne"
Ba ta re da gaddama ba ta zauna, amma shuru ne ya sa ke
biyo baya, ita kam tana mamakinshi mutun tamkar magana na bashi wuya da
kyar yake magana, itafa ta fara jin yunwa kuma ma bata so Ummi ta fito
bata ganta ba.
"Faridaaa nasan na k'untata miki ba kad'an ba na kasance mutun mara tausayi agareki, ki yafe min"
Ya d'anyi shuru, kafin daga bisani ya cigaba.
"Zuciyata ta kasa mance ranar da naga Faridana da na jima
ina tattali a k'irjin wani kazami, Farida why, mai yasa, na jima ina
tattalinki, duk wani kariya ina baki, me ya rud'eki da wannan kazamin,
wanda har ta kai kina jifata da mugayen kalamai akanshi Farida"
"Dr zargina kakeyi, Mai yasa zaka yi tunanin zan sake yarda
wani d'a namijin ya sa ke rud'ana ya 6ata min rayuwa, kasan yadda nake
ji a zuciyata kuwa"
Sha re hawayen da ya zubo ma ta ta yi gami da cigaba.
"Wallahi na rantse maka da Allah babu abinda ya ta6a shiga
tsakanina da shi, wannan ranar itace rana ta farko da ya fara kamani,
kuma a lokacin ina k'ok'arin kwatar kaina kazo, sannan ina rok'onka
gafara kayi hakuri da irin munanan kalaman da na fad'a maka"
"No Farida ni nafi cutar dake, na musguna miki na hanaki
walwala a karshe na rabaki da masoyinki ta hanyar auranki, ki yafemin,
sannan ki bani lokaci insha Allahu komai zai dai-daita"
"Kin amince za ki ci gaba da zaman aure da ni Farida?"
Shuru ta yi gami da sunkuyar da kanta.
A zahirin gaskiya bata da za6i, idan har tace lalle ta na so ta rabu da Dr, toh wazai aureta, sannan kuma ta yi musu budulci.
Sannan bata kyauta mai ba, shi da ya yarda ya aureta duk da
irin nakasar da ke ta re da ita, bai gujeta ba, dole ne ta jure duk
irin abinda za ta fuskanta arayuwar aurenta, tabbas sun mata karamci.
"Please Farida karki ce a'a, karki guji yayanki, ki amince
za ki bini ki cigaba da zaman aure da ni kinji" Dr ya katse ma ta
tunani.
Tashi ta yi da zummar barin d'akin, cikin hanzari ya tashi
ya sha gabanta gami da rik'e hannayenta a ta ke suka ji wani irin shock,
k'ok'arin zame hannunta ta ke daga nashi, amma ya sa ke rikewa gam,
gami da cewa.
"Noo karki tafi ba ta re da kin ban ansa ba, nasan bakya so na amma please ki bani lokaci"
Wannan magana tashi ji ta ke tamkar a mafarki, wai yau
yayanta ne yake mata magiya akan karta rabu dashi, "Allah nagode maka"
abinda ta ke fad'a kenan azuciyarta.
"Za ki cigaba da zama dani" ya tambayeta, d'aga mai kai ta
yi alamar "eh" gami da barin d'akin da gudu domin bata so ya cigaba da
bata kunya.
Da sauri ta fito daga d'akin, da Ummi ta ci karo, kunya ne
ya rufeta, a take ta hau kame-kame, murmushi Ummi ta yi gami da barin
wurin.
A zuciyarta ta na yan bad'on yara, suna so suna kaiwa kasuwa.
Ranar lahadi sukayi shirin komawa, sosai Ummi ta yi musu fad'a gami da nasiha mai shiga jiki.
Ummi ta k'ara da cewa "yanzu zakuje ku d'auki Mariya Ku wuce ko" cike da rashin jin dadi Dr ya ce
"Ummi wallahi bansan me yake damun yarinyar nan ba, na
fad'a mata lokacin da zamu tafi akan tazo kuyi sallama sai mu wuce amma
kina ganin har yanzu, tana wasa dani, ta biyo motar haya kuwa"
Ummi tace "a'a baza ayi haka ba kaga komai d'an hakuri ne,
kuma kai babba ne karka biye ma ta, idan zaku wuce kaje ka d'auketa
karka ce ma ta komai, nan gaba ko ance ta yi hakan baza ta yi ba"
Daga gidan Ummi kai tsaye gidan Auntyn Mariya sukaje Dr kam bai shiga ba waya ya mata ta fito.
Ta na zuwa ta bud'e kofar gaba wurin da Farida ta ke zaune gami da cewa Farida
"malama fita anan kin dai san wurin zama na ne"
Dr ne ya fito ya zagayo inda ta ke gami da cewa "haba
Mariya ba kiga nan kan hanya bane, please karki jawo mana idon mutane
tunda da zamu zo kekika zauna a gaba yanzu kiyi hakuri ki zauna a bayan
please"
Cike da tsiwa ta ce "wallahi wannan yarinyar ba ta isa na
bar mata wurin zama na ba, akwace min miji sannan gaban ma ahana ni
zama"
Tabbas ta fara kai shi bango, sam baya son ya ma ta abun da
zata ga kamar ya fifita Farida akanta, shi baiga wani abun fad'a akan
zaman gaba ba.
Lek'awa yayi ta widowo motar ya ce wa Farida "Faridana za
kiyi hakuri ki bar mata gaba ki koma baya, amma karki ga hakan a
matsayin tursasawa kiyi abinda zuciyarki ta amince da shi"
Murmushi ta yi gami da cewa "zan koma yayana ai da bayan da gaban duk d'aya ne"
Wannan abu ya 6atawa Mariya rai, don haka koda suka fara
tafiyar ma habaici ta diga yi wanda duk Farida ta ke jefawa magana, Dr
sam bai gane mai ta ke nufi ba amma ita Farida ta gane, banza ta bawa
ajiyarta har suka iso bauchi .
Yau tunda suka iso ta ke gyare-gyare domin ta na sa ran
zuwan mijinta gareta, hatta zanin gado yau sai da ta sauya, babu abinda
ba'a k'alk'aleshi ba.
Kasancewar ya ce ba sai sun dafa komai ba yasa ta na gama gyaran gidan ta shiga wanka, ta jima a ciki toilet d'in kafin ta fito.
Zama ta yi ta tsantsara kwalliya gami da feshe jikinta da turare, wata rigan bacci ta d'auko mai kyau ta sanya.
Ta idar da sallah kenan ya shigo, wani k'ayataccen kallo yake jifanta dashi.
Ita kanta yau ta na bukatar ta jita a k'irjin mijinta, "kinyi kyau" yace da ita,kuma har lokacin idanunsa na kanta.
Sunkuyar da kai ta yi ta na murmurshi, "Faridanaaa" ya fad'a cikin sanyin muryar da saida tsigar jikinta ta tashi.
"Bari na je na yi wanka" ya sake fad'a, "toh" tace dashi
yana fita ta janyo ledar da ya shigo da ita ta na dubawa, abincin da
yasan ta na so ne, "Dr ka jima kana kyautata min yau na maka alkhawarin
faran ta maka.
Ta d'an jira taga bai shigo ba kuma yunwa ta ke ji, don haka ta zuba abincin ta ci bayan ta rage mai nashi.
Ta jima ta na jiran shigowarshi amma bai shigo ba, har
bacci ya d'auketa a falon, wurin sha biyun dare ta farka, ranta yayi
matuk'ar 6aci.
Ita wai me Dr yake nufi da ita ne, haba itafa ba dutse bace
ta na buk'atar mijinta, daurewa kawai ta keyi a wannan y'an kwanakin.
Ranar kasa runtsawa ta yi kewar mijinta ya hanata sak'at, sosai ranta ya 6aci.
Ba ita bacci ya d'auketa ba sai karfe uku na dare.
Sawa kanta dauriya ta yi don bata so ta bada kai, koda ya
shigo da safe sam bai mata maganar rashin dawowanshi ba, ita d'in ma
bata kawo maganar ba.
Ranar ta re sukaje wurin aiki abun gwanin sha'awa, duk wani
motsinta a idanunshi, bini-bini sai ya biyota office wai yazo ganin
lafiyar matarshi, ita kuma ta biye mai.
Da yamma bayan sun tashi, ya d'auketa yace suje su gai da Baba, ba k'aramin farinciki Baba da Aunty sukayi da ganinsu ba.
Haka aka dinga tattalinsu, Aunty ce ta ja Farida d'akinta
ta ke cewa "d'azu munyi waya da Ummi ta ke fad'a min halin da kike ciki,
amma mai yasa baki fara sanar dani ba dota"
"Ayya Auntyna kiyi hakuri wallahi bana so na d'aga muku hankali ne Ummi ma dandai ta matsa ne" Farida ta fad'a.
Aunty ta ce "amma yanzu komi yayi daidai ko" Farida ta ce
"eh Aunty" wani kwalba Aunty ta d'auko cike da magani ta ce ungo maza
shanye mazan yanzu ba'a musu Sanya, ga wannan shiga toilet kiyi tsuguno"
Da dai kamar Farida bazata kar6a ba tunawa da jiya amma sai
ta yi tunanin watakila jiya gajiya ce tasa bacci ya d'aukeshi, kuma yau
kam taga k'aunarta fal cikin idanunshi.
Kafin su tafi sai da Baba ya musu nasiha sosai, ta tafi tana kewar Babanta wanda taga ya sake ramewa.
Suna tafiya a mota amma gani ta ke sam tafiyar bata sauri
wani irin shauk'insa takeji mai sauk'ar da kasala, bata ta6a shiga irin
wannan yanayin ba.
Koda suka isa ce mata yayi bari yaje yaga lafiyarsu Mariya, hannunshi ta kamo gami da cewa "zaka dawo"
Ce ma ta yayi "karki damu kije kiyi wanka yanzun nan ina zuwa my Farida, yau inaso naji matata a jikina"
Kusan awa biyu ta na jiranshi amma shuru, ta rasa me yake damunshi wai shin har yanzu bai hakura bane.
Ita kam gaskiya hakurinta ya gama k'arewa, ta kasa gane
ainihi me yake damunta, gaskiya yau bazata iya bacci ba, wani irin
tausayin kanta taji.
Kiran wayarshi ta yi har saida ta kusan yankewa ya d'auka, "Farida" ya fad'a muryarshi da alamun bacci.
Wani bakinciki ne ya tokareta wato shi baccin shi ma yake, kuka ne ya kwace mata.
Hankali tashe yake tambayarta, kashe wayar ta yi ba tare da ta bashi ansa ba.
Lokacin da ya shigo ta kifa kanta akan gadon ta na kuka,
zuwa yayi ya kamota gami da rungumota, fad'awa ta yi k'irjinshi ta na
kuka.
"My Farida kukanki na d'aga min hankali, na rok'eki ki sanar dani abinda ya sakaki kuka kafin zuciyata ta buga"
Ya fad'a hankalinshi a tashe, kukan ta cigaba da yi, kamo
fuskarta yayi da hannuwanshi biyu yana cewa "oya bani hawayen na shanye
Faridana"
"Bazan iya juran ganinsu suna zuba ba, please ki sanar dani, Farida ina cikin garari"
"Kallonshi ta yi gami da cewa "na tuna da Mama ne na karashe da kuka"
Rungumeta ya sa keyi tamkar zai maidata cikin jikinshi,
kafin kuma yace "addu'a za ki musu, na rok'eki matata ki daina tayar da
hankalinki ko kinaso zuciyata ta buga"
Girgiza kanta ta yi gami da kwantar da kanta a k'irjinshi, shima dad'a manne ta yayi a jikinshi.
Share this
SAKACI Part 24
Farida da Ummi na zaune a falo suna hira, duk rabin hiran ya ta'allaka ne akan nasiha wanda Ummi ta ke yi ma ta.
Dr Umar ne ya shigo falon, idanunshi na kan Farida, addu'a
yake Allah yasa ba ta sanar da Ummi ba, domin sam Ummi ba ta d'aga ido
ta kalleshi ba, balle ya sa ran za'amai magana.
Tashi ta yi had'e da barin wajen, har sai da ta shige d'akin Ummi kafin ya d'auke idanunshi daga kallon da yake mata.
Zama yayi a gefen Ummi gami da cewa "wash nagaji" yaji ba ta tanka mishi ba, ya sa ke cewa "Ummi Alhaji bai dawo ba ne"
"Ka ganshi ne anan" ta fad'a a hasale, tun daga nan ya sha jinin jikinsa, murya a raunane yace "Ummi wani laifi na yi ne"
Cikin fad'a ta ce "ban sani ba, na ce bansani ba, yau wai ni ce zaka ci amana Umar, wallahi kaban mamaki, bansan haka kake ba"
Murya a raunane yace "Ummi ki yafe min, wani abun akace miki na yi ne, kiyi hakuri ki sanar dani kar Allah yayi fushi dani"
Rai 6ace tace "na yi zaton kai mai rik'e Farida ne bisa
amana, Umar na yi zaton ko wani kaga yana k'unta ta ma ta sai inda
karfin ka ya k'are, mai yasa ka aureta kasan baza ka iya rik'eta ba"
"Ba komai bazan so Allah ya kama ka saboda hakkin baiwar
Allah nan ba, tabbas saki ba abu ne mai kyau ba sai dai ina maka tsoron
kamuwar ubangiji"
"Domin haka ina shawartarka da kaji tsoron Allah ka saiwak'e ma ta Umar"
Ummi na gama fad'an haka ta juya gami da cigaba da duba wasu takardu.
"Ummi wallahi ina sonta, ina sonta, Ummi kiyi min addu'a ban san mai ya ke damuna ba, na kasa mancewa"
Rabonta da ta ganshi yana kuka ta manta, tabbas ya na bukatar kulawarta, ya zama lalle ta taimaka musu.
Murya mai tattare da lallami Ummi ta yi magana "toh kai
wace irin zuciya ce da kai da ka kasa yafe ma ta, yarinyar nan ta nemi
gafararka, Umar karka zamar da kanka jahilin karfi da yaji mana"
"Ummi ban san mai yake damuna ba wallahi hoton yaron ya kasa fita a cikin zuciyata, Ummi Faridana ce fa"
Murmushi Ummi ta yi irin nasu na manya, lalle ba wani abu ba ne ya ke damun Umar sai kishi.
"Yayan Farida" Ummi ta kira sunanshi.
"Na jima da fahimtar kai da k'anwarka kuna tsananin k'aunar junanku, amma ku kanku kun kasa fahimtar hakan"
"Lokacin da kuka kawo girma na yi tunanin zaku fayyace wa juna halin da ko wannenku yake ciki, amma naga ba kuyi hakan ba"
"Sannan ko da Alhaji yayi maka maganar Mariya nan ma na yi
tunanin zaka fito da buk'atar zuciyarka, har zuwa randa ka kawo kaya, da
farko na yi farinciki dana ga akwatuna biyu amma jin bayaninka ya
sakarmin da gwuwa"
"Har izuwa lokacin da yaron na Adamu ya fito, fad'an da
naga kanayi nasan tabbas akwai dalili, sosai naji haushinka lokacin
domin kak'i ka fitar da sirrin zuciyarka"
"Bayan kunyi wanna tashin hankalin da ita sai na fara
k'aryata tunani na, amma randa ka taho daga Bauchi ba shiri, tafiyar da
baka ta6a irinta ba, nasan akwai damuwa, na yi k'ok'arin tambayarka,
amma kace ba komai"
"Ni nasan damuwarka ba zata wuce saka ranar auren Farida da Ahmad ba"
"Hankalina ya tashi matuk'a, wannan ne yasa bacci ya
k'auracewa idona, a daren naji ina buk'atar na sameka dan mu tattauna,
kai tsaye na shigo d'akinka a wannan daran.
Na yi sallama kafin na shigo amma naji shuru, kuma inajin
kukanka da surutanka, wannan ne yasa na shigo, na lura a wannan lokacin
sam baka cikin hayyacinka"
"Hankalina yayi mak'ar tashi da jin kalaman da suke fitowa
daga bakinka, anan na tabbatar da kana k'aunarta k'auna kuma mai
tsanani"
"Ban bari ka ganni ba na koma d'akina, hankalina ya tashi a ranar na samu Alhaji na fayyace mai komai nan fa muka dukufa addu'a"
"Allah ya ansa addu'ar mu, tun daga wannan lokacin
hankalina ya kwanta, duk a tunani na Farida ta samu kwanciyar hankali,
Umar ba zanso Ku rabu da juna ba domin kuna son junanku"
"Sai dai ba zan lamunci ganin Farida a damuwa ba, domin
haka nake rok'onka da ka sauwak'e ma ta, saboda ka kasa rage kishinka,
wanda hakan cutarwa ne a gareku"
Tamkar k'aramin yaro haka ya rik'e hanun Ummi ya na cewa
"Ummi dan girman Allah karki rabani da Farida wallahi ina sonta, zan iya
mutuwa akanta ki taimakeni"
Cikin hikima Ummi ta ce "ni kaina bana so na rabaku, sai dai maslaha nake nema muku domin wannan kishin naka yana cutar daku"
"Addu'a zakimin Ummi na rasa yadda zanyi ki rok'a min
Allah" sosai taji tausayinshi, itama dama ba taso su rabu domin ba wanda
zai rike mata Farida da amana sai shi.
"Zan yarda ku koma amma da sharad'i" "Ummi please banda sharad'i mai tsauri" ya fad'a yana rok'onta.
"Toh ai shikenan sai kaba ni takardar ta" Ummi ta fad'a ta
na k'ok'arin tashi, da sauri ya sha gabanta gami da sunkuyawa gwuwowi
biyu a kasa kafin kuma ya ce "wallahi na yarda da sharad'in"
"Da safe ka rarrasheta idan ta yarda, ta amince zata bika, to sharud'in zai biyo baya"
Ummi ta fad'a gami da tafiya d'akinta, daren ranar Ummi ta
rayashi ne da addu'o'i, ta rok'a musu Allah sosai wanda ta ke sa ran
addu'arta ta kar6u
Ya na fitowa daga masallaci, kai tsaye d'akin kwanan Ummi
ya wuce, ita kawai yake so yasa a ido, sam jiya bacci ya k'auracewa
idanunshi, wani irin kewarta ya keji.
Kwance ta ke a kan gadon ta na bacci, duk rabin cinyoyinta a
waje kasancewar rigar baccin ta tattare, wani irin shauk'in kaunarta ne
ya ke d'ibanshi, a ta ke ya saukar mai da wata kasala.
Kujerar dressing mirrow ya janyo zuwa bakin gadon kafin kuma ya zauna, tallafe ha6arshi yayi da hannu biyu.
Kallonta ya ke tamkar idan ya d'auke idanuwanshi zata 6ace,
ji yake tamkar yaje ya kamata ya rungume abarsa, cikin wata irin murya
mai cike da shauk'i ya ce.
"Farida ina sonki, ina tsananin k'aunarki ba zan iya rabuwa da ke ba matata, domin kece farincikina"
Cikin bacci ta ke tajiyo maganganu, a hankali ta bud'e idanunta wanda suka sauka akanshi.
Da sauri ta janyo zani gami da rufe jikinta har ma da kanta, ya jima ya na zaune kafin daga bisani ya mik'e had'e da cewa.
"Idan kin gama ki sa meni a d'akina" daga haka ya juya ya tafi cikin tafiyarshi ta k'asaita.
**** ****
Sai da ta yi wanka, wannan karan ma ba ta yi wani kwalliya
ba gudun kar a fad'a mata maganganu marasa dad'i, sai da ta feshe
jikinta da turare kafin ta fita.
Kai tsaye d'akinshi ta nufa, sallama ta yi, sai da ya bata
izini kafin ta shiga, ba ta yi k'ok'arin zama ba domin yau kam baza ta
iya jure munanan kalamansa.
Sai dai kuma yanayin da ta ganshi a ciki ya bata mamaki tamkar ba Yayanta ba tagumi yayi da hannuwanshi biyu.
Ya d'an jima ahaka kafin ya d'ago kai ya kalleta, cikin sanyin murya ya ce "Bismillah zauna mana inaso muyi magana ne"
Ba ta re da gaddama ba ta zauna, amma shuru ne ya sa ke
biyo baya, ita kam tana mamakinshi mutun tamkar magana na bashi wuya da
kyar yake magana, itafa ta fara jin yunwa kuma ma bata so Ummi ta fito
bata ganta ba.
"Faridaaa nasan na k'untata miki ba kad'an ba na kasance mutun mara tausayi agareki, ki yafe min"
Ya d'anyi shuru, kafin daga bisani ya cigaba.
"Zuciyata ta kasa mance ranar da naga Faridana da na jima
ina tattali a k'irjin wani kazami, Farida why, mai yasa, na jima ina
tattalinki, duk wani kariya ina baki, me ya rud'eki da wannan kazamin,
wanda har ta kai kina jifata da mugayen kalamai akanshi Farida"
"Dr zargina kakeyi, Mai yasa zaka yi tunanin zan sake yarda
wani d'a namijin ya sa ke rud'ana ya 6ata min rayuwa, kasan yadda nake
ji a zuciyata kuwa"
Sha re hawayen da ya zubo ma ta ta yi gami da cigaba.
"Wallahi na rantse maka da Allah babu abinda ya ta6a shiga
tsakanina da shi, wannan ranar itace rana ta farko da ya fara kamani,
kuma a lokacin ina k'ok'arin kwatar kaina kazo, sannan ina rok'onka
gafara kayi hakuri da irin munanan kalaman da na fad'a maka"
"No Farida ni nafi cutar dake, na musguna miki na hanaki
walwala a karshe na rabaki da masoyinki ta hanyar auranki, ki yafemin,
sannan ki bani lokaci insha Allahu komai zai dai-daita"
"Kin amince za ki ci gaba da zaman aure da ni Farida?"
Shuru ta yi gami da sunkuyar da kanta.
A zahirin gaskiya bata da za6i, idan har tace lalle ta na so ta rabu da Dr, toh wazai aureta, sannan kuma ta yi musu budulci.
Sannan bata kyauta mai ba, shi da ya yarda ya aureta duk da
irin nakasar da ke ta re da ita, bai gujeta ba, dole ne ta jure duk
irin abinda za ta fuskanta arayuwar aurenta, tabbas sun mata karamci.
"Please Farida karki ce a'a, karki guji yayanki, ki amince
za ki bini ki cigaba da zaman aure da ni kinji" Dr ya katse ma ta
tunani.
Tashi ta yi da zummar barin d'akin, cikin hanzari ya tashi
ya sha gabanta gami da rik'e hannayenta a ta ke suka ji wani irin shock,
k'ok'arin zame hannunta ta ke daga nashi, amma ya sa ke rikewa gam,
gami da cewa.
"Noo karki tafi ba ta re da kin ban ansa ba, nasan bakya so na amma please ki bani lokaci"
Wannan magana tashi ji ta ke tamkar a mafarki, wai yau
yayanta ne yake mata magiya akan karta rabu dashi, "Allah nagode maka"
abinda ta ke fad'a kenan azuciyarta.
"Za ki cigaba da zama dani" ya tambayeta, d'aga mai kai ta
yi alamar "eh" gami da barin d'akin da gudu domin bata so ya cigaba da
bata kunya.
Da sauri ta fito daga d'akin, da Ummi ta ci karo, kunya ne
ya rufeta, a take ta hau kame-kame, murmushi Ummi ta yi gami da barin
wurin.
A zuciyarta ta na yan bad'on yara, suna so suna kaiwa kasuwa.
Ranar lahadi sukayi shirin komawa, sosai Ummi ta yi musu fad'a gami da nasiha mai shiga jiki.
Ummi ta k'ara da cewa "yanzu zakuje ku d'auki Mariya Ku wuce ko" cike da rashin jin dadi Dr ya ce
"Ummi wallahi bansan me yake damun yarinyar nan ba, na
fad'a mata lokacin da zamu tafi akan tazo kuyi sallama sai mu wuce amma
kina ganin har yanzu, tana wasa dani, ta biyo motar haya kuwa"
Ummi tace "a'a baza ayi haka ba kaga komai d'an hakuri ne,
kuma kai babba ne karka biye ma ta, idan zaku wuce kaje ka d'auketa
karka ce ma ta komai, nan gaba ko ance ta yi hakan baza ta yi ba"
Daga gidan Ummi kai tsaye gidan Auntyn Mariya sukaje Dr kam bai shiga ba waya ya mata ta fito.
Ta na zuwa ta bud'e kofar gaba wurin da Farida ta ke zaune gami da cewa Farida
"malama fita anan kin dai san wurin zama na ne"
Dr ne ya fito ya zagayo inda ta ke gami da cewa "haba
Mariya ba kiga nan kan hanya bane, please karki jawo mana idon mutane
tunda da zamu zo kekika zauna a gaba yanzu kiyi hakuri ki zauna a bayan
please"
Cike da tsiwa ta ce "wallahi wannan yarinyar ba ta isa na
bar mata wurin zama na ba, akwace min miji sannan gaban ma ahana ni
zama"
Tabbas ta fara kai shi bango, sam baya son ya ma ta abun da
zata ga kamar ya fifita Farida akanta, shi baiga wani abun fad'a akan
zaman gaba ba.
Lek'awa yayi ta widowo motar ya ce wa Farida "Faridana za
kiyi hakuri ki bar mata gaba ki koma baya, amma karki ga hakan a
matsayin tursasawa kiyi abinda zuciyarki ta amince da shi"
Murmushi ta yi gami da cewa "zan koma yayana ai da bayan da gaban duk d'aya ne"
Wannan abu ya 6atawa Mariya rai, don haka koda suka fara
tafiyar ma habaici ta diga yi wanda duk Farida ta ke jefawa magana, Dr
sam bai gane mai ta ke nufi ba amma ita Farida ta gane, banza ta bawa
ajiyarta har suka iso bauchi .
Share this
SAKACI Part 23
Aikuwa da safe da ta bud'e fridge d'in ba farfesu ba alamarsa, tasan ba kowa ne ya d'auka ba sai Dr.
Toh kuma ita ai har zuwan wannan lokacin bata bud'e kofa ba, toh ta yaya ya shigo har ya d'auka.
"yana da wani key ne a hannunshi" zuciyarta ta ba ta ansa, haka ta cigaba da aikace-aikacents da mamakin Dr fal cikin zuciyarta.
Tun daga wannan ranar Dr bai sake yarda sun had'u ba, sai dai ya tura ma ta sak'o ta waya ya tambayeta lafiyarta.
Idan kuwa ranar girkinta ne, toh nan fa zai shiga kitchen ya samawa kansa abin ta6awa.
Lura da ta yi yana zuwa cin abincin cikin dare bayan ta
kwanta yasa ita kuma ta dage da dafa duk wani abinci da ta tabbatar yana
so, ta ajiye mai.
****
Yau ne hutun ta ya k'are, don haka murna ta keyi sosai, dama ta gaji da zaman wuri d'aya, ko ba komai yau zata samu canjin wuri.
Ta sha mamaki lokacin da Dr ya tura mata sak'o ta waya yana tambayarta k'arfe nawa zata tafi aiki, domin ta yi tunanin ya manta.
Karfe takwas ya turo da driver yazo ya d'auke ta.
Farida mace ce da kowa yake sonta saboda kyawun halayenta,
da son mutane gami da kyauta, shiyasa duk inda ta shiga a fad'in
asibitin nan ake martabata da bata girma.
****
Ta na daf da shiga ICU ta hangota, cike da farinciki Dr Jidda ta k'araso wurinta, rumgume juna sukayi cikin kewa.
Dr Jidda ce ta saketa gami da d'an ja baya kad'an, rike baki ta yi alamar mamaki kafin kuma ta ce.
"Kawata kinganki yadda kikayi fresh kuwa, fatarki sai wani
shek'i ta keyi, gaskiya aure ya k'ar6eki kawata kuma da alama ubangidan
nawa ya iya kiyo"
Ta6e baki Farida ta yi gami da cewa "nifa banga wani dad'i a wannan auren ba Jidda"
"Wai kina nufin Dr har yanzu bai bada kai ba" Jidda ta fad'a.
" Hmm, idan ya ta6a kwana d'aki d'aya dani kenan, nifa....."
Ganinshi a gabansu yasa maganar ta tsaya a mak'oshints ba
ta re da ta iya k'arasawa ba, cikin k'ank'anin lokaci ta shiga rud'ani.
Bai sa ke kallon inda suke ba, yayi wucewarshi, cikinsu ba wacce ta iya magana, sai daga bisani ne Jidda ta ce.
"Alllah dai yasa bai ji abinda muke fad'a ba"
"Ma had'u anjima Jidda" abinda Farida ta iya fad'a kenan, kafin kuma suyiwa juna sallama ko wacce ta kama gabanta.
****
Yau gaba d'aya ta yi wuninta ne cikin fargaba, ganin har
lokacin tashi daga aikinta yayi har wannan lokacin bata samu kiran Dr ba
yasa hankalinta ya d'an kwanta, kad'an.
Indomie ne a gabanta ta naci lokaci zuwa lokaci hankalinta
yana kan film d'in da ta ke kallon a TV, Sallama yayi had'e da shugowa,
kasancewar hankalinta na kan film d'in da ta ke kallo yasa bata ji
sallamar da yayi ba, balle kuma ta san da shigowar shi.
Gyaran muryarshi ce ta ankarar da ita, a ta ke zuciyarta ta
bada ras, lokaci guda kuwa ta tsahi tsaye cikin fargaba, wani kallo ya
ke jifanta da shi, kallo ne wanda ta riga tasan na 6acin rai ne.
Lokaci guda fargabanta ya dad'u fiye da baya, k'arasawa yayi ya zauna akan kujera.
Cikin yanayi na 6acin rai ya ce "ai bansan rashin
mutuncinki ya zarce tunanina ba, ban kuma san cewa Islamiyar da najima
ina kaiki na dawo dake duk runtsi bana miki wasa da ita ashe duk abanza
ne, babu abinda kike fahimta"
Wani irin murd'awa cikinta yayi har saida taji tamkar gudawa zai fito, "magana nake miki" ya fad'a cikin tsawa.
Sunkuyar da kanta ta yi ba tare da ta tanka mai ba.
" Na gode kinje kin tona min asiri awaje, tunda ke baki san laifin tona sirrin aure ba"
"Ba ma haka ba, ke don Allah ba abin kunya ba ne a gareki
ace auren fari amma kinje kina fad'awa jama'a mijinki ba ya had'a gado
da ke"
"Wallahi ban ta6a ganin jarababbiyar mace irinki ba, wacce ba kunya a idanunta"
Ya cigaba da cewa.
"Toh inaso ki bud'e kunnuwanki kiji ni da kyau, bazan ta6a
iya had'a jiki da ke ba, ko kina tunanin zan manta da irin kazantar da
kuka aikata ke da wancan kazamin da kika gama cimun mutunci akanshi ne"
"Allah ya sauwak'a, turrr da halinki wallahi"
Wani kuka mai zafi ta fashe da shi, cikin wani irin yanayi Farida ta ce!
"mai yasa ka aureni"
Cike da masifa ya ce "shak'eni sai na baki ansa, kuma zan
miki gargad'i idan kin d'auka kinsamawa kanki lafiya, wallahi kika sake
zuwa kika bud'e min sirrin gidana a waje, saina nuna miki other side of
me"
Ya na gama fad'an haka yasa kanshi yayi ficewarshi, kwanciya Farida ta yi ta na kuka mai ban tausayi gami da cewa.
Mama aure bai kar6emu ba, nima kinga yadda rayuwata ta
dawo, duniyar ta yimin zafi Mama, nima nasan nakusan zuwa gareki, Ya
Umar ba masoyinmu ba ne, Mama ya yaudaremu ne"
Kuka sosai ta keyi ta cigaba da surutai tamkar wacce ta zare.
Yana tsaye a k'ofar falonta ya na sauraran maganganunta,
wani irin zafi zuciyarshi ta keyi, ya rasa dalilin da yasa ya kasa manta
laifin da Faridanshi ta aikata mai.
Dukan bakinshi ya ke da hannunshi ya na cewa "banyi ba mai
yasa na kasance mai k'untatawa wacce nafi so fiye da rayuwata, why why?"
Juyawa yayi da nufin yaje ya rungumeta ya rarrasheta, amma
lokaci guda hoton ta ya hango ta na rungume a jikin Adamu, a take
zuciyarshi ta yi mai zafi, juyawa yayi gami da tafiya shashinsa.
Ko da ya koma shashinsa rasa abinda yake mai dad'i yayi,
wani irin tausayinta ya keji, mafita yake nema amma sam k'wak'alwarshi
ta kasa hasko mai komai.
Yana bukatar ya mance wannan rana daga cikin tarihin
rayuwarsu amma ya kasa, to wai shi ya zai yi ne, wa zai tunkara "
*ALLAH* " zuciyarshi ta bashi ansa.
Toilet ya shiga gami da d'auro alwala, sai dai lokacin da
ya idar da sallah sai ya rasa wace addu'a zaiyi me ma zai rok'i Allah,
komai ya tsaya mai, k'arshe hakura kawai yayi.
*** ***
Farida ma kwana ta yi ta na kuka gami da yiwa mutumin da ya
6ata ma ta rayuwarta Allah ya isa, domin tasan da badan hakan ba, ba
wani namijin da ya isa ya zageta, tabbas wata shari'ar sai a lahira.
Ranar dai duk cikinsu ba wanda ya runtsa har sai bayan sallar asuba.
Kasancewar bai kwanta da wuri ba yasa ya makara, d'akin
Mariya ya soma shiga, bai sameta a falo ba, jiyo hayaniyar Muhammad
(d'ansu na uku) a kitchen hakan ya tabbatar mai da suna kitchen d'in.
Don haka kai tsaye kitchen d'in ya nufa, da gudu Muhammad
ya zo ya rungume Babanshi, d'aukanshi Dr yayi yana mai wasa, kafin kuma
ya juyo ga Mariya wacce ko kallo bai isheta ba.
Ya lura tunda ya auri Farida sam ya rasa kulawa a wajen Mariya, ita kullun gani ta ke yana fifita Farida akanta.
"Ranki shidad'e baki ji shugowata bane" Dr ya fad'a, ta6e
baki ta yi had'e da cewa " ai gani na yi maganar tawa bata fiye zama mai
anfani ba, tunda kullun gani ake inada k'orafi, k'iri-k'iri za'a cuceni
ace kuma kar na yi magana"
Murmushi yayi gami da cewa "Hajiya Mariya kenan to yau ma na yi lefi ne"
"Dr ka maidani yarinya karama, duba agogo k'arfe goma kana
d'akin ta gaban goshin taka, ba labarin office, balle kuma mu musami
darajar azo aduba lafiyarmu, su khalil har suka tafi school basu sami
ganinka ba"
"Yi hakuri bank'i zuwa dubaku da gan-gan ba, ni kaina makara na yi" Dr ya fad'a,
Ciki fad'a Mariya ta ce " Ai ba sai ka fad'amin kwana
kukayi bakuyi bacci ba, nasan da haka, kuma cutar da akeyimin Allah na
gani"
Ganin idan ya tsaya ranshi ne zai 6aci yasa ya kama hannun d'anshi suka yi tafiyarsu ya barta ta nata sababi.
Kai tsaye shashin Farida ya nufa domin yana buk'atar
ganinta hankalinshi sam yak'i kwanciya, sanin da yayi jiya ya barta
cikin halin damuwa.
Goge kujerunta ta keyi, suka shigo, Muhammad ne yazo gareta cikin sakewan fuska ta rungumeshi ta na "oyoyo Alhajina".
So yake ya had'a ido da ita amma sam tak'i yarda, kallonta
ya ke sosai tabbas ta bashi tausayi duk da bata bata bari ya kalli cikin
idonta ba.
Amma idanunta sun kumbura wanda yasan ba tantama kwana ta yi tana kuka.
"Ina kwana" ta katse mai tunani ba ta re da ta kalleshi ba,
cikin sanyi muryar da ya bata mamaki ya ansa, sannan ya ce "kintashi
lafiya"
Tambayar da ya mata yafi mata kama da ta rainin hankali, domin haka bata ansa ba.
Ya d'auki lokaci mai tsayi yana zaune a wurin har taje ta
had'awa Muhammad tea ta dawo bai motsa ba, abun sai ya mata wani irin,
domin bai ta6a kwatanta hakan ba.
"Ki shirya ranar juma'a zamuje Jos mu gaishe su" ya katse mata tunani, gyad'a kai ta yi, alamar " toh"
Sai da ya tashi tsaye kafin ya ce "Alhaji na barka wurin Mamanka zaka taya ta hira ko" yaro ya gyad'a kai alamr " eh "
Ranar haka suka wuni da Muhammad, tabbas yaron ya d'ebe mata kewa.
Ita kuwa Mariya ba ta yi tunanin gun Farida Dr ya kai
Muhammad ba, ta yi zaton suna ta re ne, da tana da masaniya da tuni tazo
ta d'auke d'anta.
Sai da yamma da yaji hayaniyar y'an uwanshi suna wasa awaje, ya fita ya, daganan ne bai sa ke dawowa ba.
*****
Da wuri ta kammala shirinta ta na fargabar zuwa Jos d'in amma kuma ta na son taje ta ga Ummi.
Sanin Dr ya siyawa su Ummi gida a unguwar Ibrahim tayo,
yasa fargabanta ya ragu, domin ba taso ta kuma lek'a unguwar da al'amura
da dama suka faru acikinta.
Anayin sallah juma'a Dr ya umarcesu da su fito, Mariya dai gudun 6acin ranshi ne kawai yasa zata je amma bawai don tana so ba.
Ita a tunaninta salon a wulak'anta ta ne kawai yasa aka tsiro da tafiyar da ita.
Koda suka fito da saurinta ta wuce Farida harda bangajeta ta shiga gidan gaba, azuciyar Farida ta ce
"Hmm ke gaba ya dama da kinyi hakuri ma ni ba shiga zanyi ba"
Tafiyar kurame sukayi a motar ba wani mai magana d'an gara Farida ta biyewa yara suna ta ma ta surutunsu na yara.
****
Da gudu taje ta rungume Ummi, cike da farinciki Ummi ta ce "oh ni wai Farida Umar sai kin k'arasa ni"
"An zo wurin" Mariya ta fad'a a zuciyarta, yak'en dole kawai ta keyi amma ba karamin haushi sunan ya ke bata ba.
Sosai Ummi ta ke farinciki, duk motsin da Farida zata yi idanunn Ummi na kanta.
Cikin k'ank'anin lokaci aka wadatasu da kayan ciye-ciye da
na sha, sai da sukaci sukayi dam kafin suka tashi suka gabatar da sallah
la'asar.
Mariya ce ta ce "na fito ne ka saukeni a gidan Auntyn tawa" ta fad'a lokacin da ta ga yana shirin fita.
Fuska ba walwala Dr ya ce "sai da daddare "
"Don girman Allah ka kaini yanzu" zaiyi magana Ummi ta katseshi da ce wa
"A'a tunda ta had'aka da girman Allah ka kai ta"
Ba zai iya musu da Ummi ba yasa ya kad'a kai kawai gami da
ce wa "ba da yarana za kije ba" "toh" kawai ta ce domin tasan dole akayi
mai bawai don yana so ba.
Bayan sun tafi yara kuma ansa musu kallo, Ummi ta kamo
hannun Farida gami da ce wa " d'iyata me yake damunki ne, dubi yadda
kika rame"
Murmushi Farida ta yi kafin kuma ta ce "me kika gani Ummi ba fa komai, ni ba abinda yake damuna"
Ummi ta ce "Farida kalli cikin idona ni ba yarinya bace a
gabana aka haifeki don haka babu abinda za ki boye min, idan har kin
d'aukeni a matsayin uwa Farida ki sanar dani abinda ya ke damunki"
Hawayen da ta ke mak'alewa ne ya fara zubowa, cikin muryar kuka Farida ta ce "Ummi ki raba auren nan please"
Murya mai cike da damuwa Ummi ta ce "wani abu yayan naki yake yimiki, sanar dani Farida karki 6oyemin komai"
"Ummi ba komai nidai ki taimaka ki sakashi ya sakeni idan ba haka ba wallahi ciwon zuciya nima shi zai zama ajilina kamar Mama"
Rungumeta Ummi ta yi gami da cewa " shi d'in waye wallahi
bai isa ya wukantaki ba, bai isa ba wallahi dani ya ke, kwantar da
hankalinki Faridana wallahi Umar bai isa ba, ni zanyi magani komai, ki
manta dashi kinji, karna sa ke jin batun ciwon zuciyar nan"
Share this
SAKACI Part 22
A tsaye ta sameshi ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai safar
da marwa ya ke a cikin office d'in, fuskarnan a murtuke, gaggawan sauke
idanunta ta yi saboda wani kallo da ya ke jifanta da shi.
A ta ke zuciyarta ta fara bugawa da sauri-sauri, rawa jikinta yake tamkar mazari.
"Mene ne hujjarki ta zuwa ki zauna a tsakiyar wa'encan garadan"
Ba ta iya d'agowa ta kalleshi ba, bare kuma ta bashi ansa,
"magana na ke miki" ya daka ma ta tsawar da har sai da taji ta har
tsakiyar kanta.
Ba ta iya d'aga kanta ba ma balle ta ba shi ansa, cikin maganarshi ta k'asaita ya ce!
"Kinyi na farko sannan kinyi na k'arshe, ya kamata ace
kinsan ke matar aure ce, ni kuma da kika ganni nan ba sakaren namiji ba
ne, don haka idan kika sa ke mai-maita makamancin hakan, ke da aiki sai
dai kiga anayi, da fatan kin fahimci abinda na ke nufi"
"Kayi hakuri, hakan ba zai sa ke faruwa ba" ta ce da shi,
har cikin ranshi ta bashi tausayi, amma tunowa da abinda ya hana
zuciyarshi sakat yasa shi shiga wani irin yanayi, lokaci guda kuma
zuciyarshi ta yi bak'i.
Idan ba darajar iyaye ba yaushe hakan zai faru, Allah ya
gani bai ta6a aikata zina ba, yana mugun kyamarta, sannan bai ta6a
gajiyawa ba wurin rok'on Allah akan ya had'ashi da salihar mace.
"Kai Farida kin cuceni na jima ina inganta rayuwarki lokaci
guda ki wargaza komai, mai wannan yaron ya rud'eki a wannan lokacin
kika bashi kanki"
Ko zan hana kaina abu ke zan baki kawai don bana so wani ya sake rud'anki a karo na biyu, amma kin rusa min komai.
Kujera ya samu ya zauna ya fuzar wata iska mai zafi daga cikin bakinshi.
"Ki zauna na kammala wani aiki kafin mu shiga tiyatan" Ya fad'a ya na janyo jakar laptop d'inshi.
Zama ta yi gami da takurewa wuri d'aya domi ita sam yanzu ba ta sa kewa muddin yana wuri.
Ya kai kusan awa guda (1hr) kafin ya umarceta da su tashi su je dan gudanar da aikin da ke gabansu.
****
Basu suka bar asibitin ba sai karfe sha biyu (12) na dare,
Mariya ta cika ta yi fal, saboda a ranar ta kar6i girki, sannan ta ga
fitar Farida da ga gida, don haka ta kasa tsaye ta kasa zaune, zuciyarta
fal kishi.
"Don Allah AC bedroom d'ina da na falo ba sa yi ga zafi, ko zaka taimaka ka dubamin" Farida ta fad'a cikin sanyi muryarta.
"Tun yaushe ne ya daina yi" ya tambaye ta.
"Dama tunda nazo gidan bai ta6a yi ba" ta ansa mai, tsaki ya ja gami da cewa,
"Amma kullun ina tambayarki inda wata matsalar sai kice babu"
Ita dai ba ta ce komai ba, bud'e murfin k'ofar yayi yana
shirin fita, ita d'inma fitar ta yi, ta na aiyana irin zafin da zata sha
yau, domin zafin yau yafi na kullun.
Ga mamakinta taji ya na binta a baya, ko ba komai taji dad'i.
Ta na tsaye ta na kallon ikon Allah, ranta bai gama 6aci ba
sai da taga ya na bin Farida shashinta, tabbas tasan tunda Farida ta
shigo gidan k'arshenta yazo, ba ta shigo bama sai da ta kusa korarta, eh
toh korarta mana.
Sam basu lura da ta wurin ba, koda suka shiga kai tsaye
d'akin baccinta ta bud'e mai ya shiga, wata y'ar stool ta mik'o mai akan
ya hau kai.
"Wannan sai marasa tsayi irin ku" ji ta yi tamkar a
mafarki, idan kuwa ba mafarki ba ne, toh babu tantama kunnenta baiji ma
ta dai-dai ba.
"Wai tunanin me kike ina miki magana hankalinki baya nan"
ya fad'a da muryar da baza ta iya tantance wa da fad'a yayi maganar ko
akasinta ba.
"Banji mai ka ce bane" kafin ya kai ga magana sukaji ta banko k'ofar, lokaci guda suka kalleta.
"Toh maciya amana ranar kwanan nawa ma sai anci amanata ko
tsoron Allah bakyaji, toh wallahi na gaji da ganin bakin ciki, a cuceni a
hanani kuka ba zai yuwu ba"
"Ba ta re da ya tanka ma ta ba ya ratsa ta gefenta yayi ficewarshi, tabbas ta kula, kuma ta san hakan gargad'ine ya ma ta.
Juyowa wurin Farida ta yi hannunta a k'ugun kafin kuma ta
ce " wallahi dani kikeyi na miki alkhawarin sai kin fita kinbar gidan
nan, zanje na sa meshi sai dai ya za6a tsakanin ni da ke, munafuka"
Daga haka ta fice, Farida ko kallo Mariya bata isheta ba,
ita tasan ko giyar wake Mariya tasha baza ta tunkari Dr da wannan
maganar ba, idan kuwa ta yi gangancin fad'a zai bata mamaki, domin shi
ba'a mai gatse.
**** ****
Washegari da safe ya shigo lokacin ta yi wanka har ta gama gyaran gidan, ta shiga kitchen ta na had'a tea.
A tsaye ta sameshi sanye cikin light brown d'in riga mai
gajeren hannu, wandon kuma dark brown, kalar kayan sun kar6eshi matuk'a,
kasancewar kalar fatarshi ne.
Sumar kanshi a gyare, ya kwanta luf gwanin sha'awa, kai gayen ya had'u ta ko'ina.
Idan ka kalleshi za ka d'auka matashi ne d'an shekara talatin, ba zaka ta6a cewa ya kai shekara arba'in da biyar ba.
Dr akwai iya d'aukan wanka, kuma duk kayan da ya saka zaka ga ya k'ar6e shi.
Sannan shi mutun ne mai tsafta shi yasa kafin ka ganshi k'amshin shi ne zai fara yimaka sallama.
Tsugunawa ta yi gami da gaisheshi, ansawa yayi fuskar nan kamar ko yaushe.
"AC jiya yayi" ya tambaya a tak'aice "eh yayi" ta bashi ansa, kafin ya sa ke cewa,
"Ni zan fita ki shirya anjima zanzo na d'auke ki" "toh, Allah ya tsare" ta fad'a, "ba wani abunda kike buk'ata"
Ya sake tambayarta, da sanyin murya ta ce " eh babu" ta ansa.
Juyawa yayi yana wannan tafiyar nan tashi.
Zama ta yi ta rasa me ya ke ma ta dad'i a rayuwa, sam ba ta
kaunar wannan hali na ko inkula da yayanta yake nuna ma ta, k'arshe tea
d'in da bata sha ba kenan
Yau ne Farida ta kar6a girki kuma yau ta na da niyar ta
kyautatawa yayan nata shiyasa ta wuni gyaran gida, duk da gidan ba wani
datti ne dashi ba, amma sanin halin yayan nata da son tsafta yasa ta yi
k'ok'arin kimtsa komai.
Ta na gama gyaran gida ta hau na jiki duk ba ta da tabbacin
wanda ta keyi dominsa zai yaba, amma dai a ganinta bai kamata wannan ya
zama hujjarta na k'in gyarawan ba.
Shiga kitchen ta yi, ta na tunanin mai za ta dafa mai wanda
tasan zai yaba, tunowa da ta yi a rayuwar Dr yana son shinkafa da wake
da kuma miya, ko bayason cin abinci aka bashi wannan zai ci sosai.
Sannan kuma mutun ne mai son farfesun kayan ciki, ba tare
da 6ata lokaci ba ta nemi Isiyaku mai sharan gida da gyaran flawa, ta
aikeshi kasuwa ya siyo mata duk abinda ta ke bukata.
Cikin k'ank'anin lokaci gidan ya kaure da k'amshi, daf da magriba ta kammala komai gami da jerasu akan dining table.
Wanka ta shiga, gami da d'auro alwala, ta fito dai-dai an
kira sallah don haka kayan da ta ke sallah da shi ta zira had'e da
shinfid'a sallaya.
Ko da ta idar da sallah ba ta tashi ba azkar ta cigaba da yi kafin lokacin sallah isha'i ta tashi ta gabatar.
Kwalliya ta yi, wanda rabonta da ta yi irinshi ta manta,
tabbas ta san ta yi kyau, material ta d'auko mara nauyi, kasancewar
garin akwai zafi.
Doguwar rigace d'inkin fitet, ya kamata sosai dama gata masha Allah, ko'ina ya fito ba'a magana.
Kasancewar ita masoyiyar turare ne yasa ta fesa kusan kala
shida ajikinta, gasu masu sanyin k'amshi shi d'in ne kuma ya bada
k'amshi mai sanyi ga dad'i.
Kama gashinta ta yi da ribon kafin kuma ta kafa d'auri wanda ya mata kyau matuk'a.
Falo ta fita, zama ta yi akan kujera ta zaman mutun d'aya kafin kuma ta janyo wayarta, Ummi ta kira.
Cikin farin ciki suka gaisa da Ummi, Ummi ta ce "Farida Umar kinsamu
Yayanki kin manta dani ko"
Yayanki kin manta dani ko"
Cike da shagwa6a Farida ta ce "ni na isa na manta da
Ummina" Ummi ta ce "toh ba lefi da fatan dai kuna lafiya, ba wata
matsala ko?".
Farida ta ce "ba komai Ummina sai kewarki" murmushi Ummi ta
yi irin nasu na manya kafin kuma ta ce "karki damu d'iyata da nasamu
saukin aiki zanzo naganki"
Ummi ta sa ke cewa "yauwa kafin na manta, kina yawan yin wannan addu'o'in da na baki"
Farida ta ce " wanne daga ciki Ummi" Ummi ta ce " wanda na
ce ki dinga yin Istigifari, Salatin annabi da Lahaula wala k'uwata illah
billah, na fad'a miki duk wanda ya lazimcesu ba adadi insha Allahu
zaiga biyan buk'ata aduk abinda ya sa gaba, don haka ki dage kinji"
Farida ta ce "toh Ummi inayi amma zan k'ara dagewa, Allah ya k'ara girma Ummi"
"Ameen" Ummi ta ce da ga nan sukayi sallama gami da ajiye waya.
Dai-dai wannan lokacin ya shigo, hannuwanshi cikin ajjihun wandonshi, kallonta ya ke baya ko k'ifta ido.
"jibi mutumin nan inda ya samin ido, yanzu da ni ce na ke
mai irin wannan kallon da kaji bak'ak'en maganganu" ta fad'a a
zuciyarta.
Shima maganar ya ke a zuciyarshi "Wow, Allah na gode maka da ka azurtani da wannan zankad'ed'iyar matar"
"Sannu da dawowa" ta katse mai tunani, cikin basarwa ya ce
"ke me yasa baki san kalar kwalliyar da tafi dacewa da zamani bane, haba
abu sam ba fasali ya kamata kisan irin kwalliyar da za ta miki kyau,
mtsss" ya karashe da jan tsaki.
Shi kanshi yasan abinda ya fad'a ba gaskiya bane, amma gudun karta yi tunanin ta burgeshi yasa yayi haka.
Wani bakin ciki ne ya tokare ma ta mak'oshi, cikin sanyin murya ta ce "na kawo maka abinci ne"
Fitanshi yayi ba tare da ya tanka ma ta ba, ba kuma don baya jin yunwa bane sai kawai don tsare gida irin nashi.
Yau kam ma ta gagara yin kukan saboda bakin ciki, Qur'anin ta ta d'auko domin ta na bukatar abinda zai sanyaya ma ta zuciya.
Ba ta ajiye Qur'anin ba sai da ta ji ta samu sanyi a cikin
zuciyarta, abinci ta d'iba dai-dai wanda za taci sauran ta zuba a babban
wormer, hijab d'inta ta zura gami da fita.
Mai gadi taje ta bawa abincin, da murnarshi ya kar6a,
bud'ewa yayi yana kallo gami da saka ma ta albarka, juyawa ta yi domin
tafiya dai-dai wannan lokacin ya shigo gidan.
"Malam musa don Allah zo ka siyomin biredi" idanunshi ne ya kai kan abincin, atake yaji yawunsa ya tsinke.
"Malam Musa a ina ka siyo wannan abincin" ya jefa mai tambayar, kasancewar bai lura da ita ba yasa bai gane ita ta kawo ba.
"Alhaji ai yanzun nan dakta ta kawo mana" ya fad'a yana washe baki.
"yaufa za'ayita" ya fad'a acikin zuciyarshi.
"Aikuwa Malam Musa zan maka kwad'ayi domin tare zamuci, ban
san abinda aka dafa ba kenan, na ce na k'oshi na san kuma babu saura a
cikin gidan"
Ya fad'a yana shirin zama akan bencin da Malam Musa yake kai, Malam Musa ya ce,
"Toh Alhaji ai ba komai ni,zubamin nawa ma a murfin kawai" ya fad'a yana yaba irin kyawun halin mai gidan nashi.
Dr ya ce "a'a tare zamuci" "toh ayi haka" Malam Musa ya fad'a cikin farinciki,
Suna cikin ci ta dawo da kwanon farfesu a hannunta, ganin
Dr ya na cin abinci da mai gadi abun ya bata dariya kuma da ta mai tayin
abincin fa ko kulata baiyi ba, gimtse dariyarta ta yi.
Shikuwa kicin-kicin yayi da fuska ya ma cigaba da cin abincin sa tamkar bai ganta ba.
Itama sharewa ta yi sannan ta ce "Malam Musa ga farfesun kayan ciki nan idan zaka k'ara"
Malam Musa ya ce "ayya dakta kinga ni bana cin kayan ciki wallahi"
"Toh ka ajiye idan kaga almajirai sai ka basu" ta fad'a.
"Hoh yarinyar nan za ta kasheni wai sai ta sa naji kunya" ya fad'a a zuciyarshi.
"Kije ki ajiye a fridge zai yi anfani ko zuwa gobe ne" ya
fad'a fuska a murtuke, ita abun ma dariya ya bata, juyawa ta yi cikin
gida ta na dariya ciki-ciki.