Kuka ta ke sosai,cikin rarrashi ya ke shafa bayan ta,a
hankali ya ke fad'in "It is owk,it is alryt,i will never let go of you
again,my Habeebti" Gaba d'aya ta jik'a masa gaban riga da hawaye. Ta
d'ago ta kalle shi,da cikin muryar kuka ta ce "Junior......." Ta kasa
k'arasawa saboda kukan da ya ci k'arfin ta. Haroun ya maido da kanta
k'irjin sa ya kwantar ya na mai fad'in "Shhhh! Say no more,Junior mai
ceton iyayen sa ne inshaAllah,Allah zai ba mu wani,kukan ya isa"
Bacci Habeebti ta sha a hanya sosai. Ba ita ta farka ba sai da su ka isa gida,hanun ta cikin na sa,gaban ta na fad'uwa,kai tsaye su ka wuce bangaran Mama. A falo su ka tadda ta,ba ta yi mamakin ganin su ba,dan ta san a rina,nasihar anty Salma ya shige ta sosai,ita ce har da tambayar sun ci brkfast kuwa? Daga Haroun har Habeebti mamaki ne ya rufe su,cikin rad'a Habeebti ta ce da shi "Yaushe Mama ta sauko?" "Sanda na gane ba a raba hanta da jini,na yi kuskure saboda fushi,na ga ishara kan Dawud da Hajiya,ba na so Allah ya maimaita kai na,abun da hakuri be baka ba rashin hakuri ba zai ba ka shi ba,yanzu ku dubi yanda Dawud ya zama,gaba d'aya kan sa ya tab'u,ya koma kamar yaro d'an shekara uku,har gwara ace ba shi da yanda ya zama mara daraja haka,yara ne fa abokan wasan sa!kai Allah ya rufa mana asiri. Ku je kun ji,ku zauna lafiya,Allah ya sa mu ku albarka...." Dan Murna Haroun rungume Mama yayi,da za su tafi Mama har da had'a mata goma na arziki. Ita dai har su ka tafi ganin abun ta ke kamar almara. Haka shi ma Haroun a b'angaren Hajiya da ta ji dad'in dawowar auren na Habeebti,ita ce har da hira da Haroun,in da ya mata maganar Dawud,akan zai sami dama su fitar da shi waje. Hajiya ta ji dad'i sosai,har da sa ma sa albarka,ta kuma ce za ta je ta yiwa Mama godiya. Haroun ya ce ai ba komai,yiwa kai ne. Sai da su ka yi sallama da Alhaji,wajan la'asar za su tafi su ka hangi Dawud ya tara yara,su na ta wasan k'asa,jin yana kiran yaran da "Junior" sai da Habeebti ta zubar ma sa da hawaye,Haroun ya kawar da kanta,ya na goge mata hawayen kafin ya tada mota su ka tafi.
Sun jima nan tsaye kafin ya samu Habeebti ta yi shiru.
Kujera ya samu ya zauna,har yanzu Habeebti na jikin sa,ya ce "Ki yi
hakuri Aliya,kin ji ni shiru babu yanda zan yi ne,amma ban san rasuwar
Junior ba sai d'azu Akib da ya zo ya ke fad'a min" jin haka Habeebti ta
yunk'ura za ta tashi da fushi, Haroun yayi saurin dawo da ita,ta k'ara
yunk'urawa da niyar barin jikin sa,ya dad'a dawo da ita,a karo na ukun
kuwa da ta ga ya sake jawota sai ta fara kai ma hannun sa duka cike da
shagwab'a ta ke fad'in "ka rabu da ni dallah,ba dan ka ji rasuwar Junior
ba da ba za ka zo ba kenan?" Yana dariya ya ke k'ok'arin ruke hannun
ta,ya ce "Noooooooo kin san dole na zo my Habeebti,ni da ke mutu ka raba
takalmin kaza..." Habeebti na kokawar kwace hannayen ta biyu da Haroun
ya ruk'e da hannun sa d'aya,ta yi kicinkicin ta ce "Ba wani nan,you
don't miss me,ni inan ina ta missing din ka dare da rana,ka manta da
ni,I missed you,I missed you soo very much it drives me crazy....."
Irin kallan nan nasa da ya saba mata mai cike da lalaci
ya ke mata a yanzu,fuskar sa d'auke da murmushi mai k'ayatarwa,cikin
d'an mitinan da ya ga Habeebti gaba d'aya ji yayi an kwashe masa
damuwa,bare jin Habeebti da bakin ta tana masa furici irin wannan. Yanda
ya ke kallan na ta ne ya sa Habeebti nutsuwa,ta daina k'ok'arin
kwacewa,yayinda ta yi k'asa da na ta ido cike da kunya. D'ayan hannun na
sa ya sa,ya d'ago habarta,ya na mai sanya kwayar idanun ta cikin
nasa,cikin rad'a ya ce "Missing kawai?are you sure jst missing?uhm my
Habeebti? Don't you love?" Murya can k'asa ta ce "I do....I love you
Haroun,I love you Haroun with all my hrt"
Sai da ya lumshe ido na d'an sakanni,ya bud'e a
hankali,in da su ka k'ara yin ido biyu da kwawawan idanun Habeebti,jawo
ta yayi,yayi kissing goshin ta,kafin ya kara duban fuskar ta,ya na mai
fad'in "sake fad'a Aliya,pls say you love me....." Habeebti idanun ta
cike da kwalla,amma na farin ciki ta ce "I love you,my Haroun....." Cike
da farin ciki,ya sa hannayen sa biyu ya jawo fuskarta zuwa na shi,karaf
su ka ji k'arar an doka kofa.
.
Habeebti da ta san Yakumbo ce ta dawo tuni ta ja da baya
za ta tashi. Haroun da idan ran sa yayi dubu ya b'aci ya na mai sakin
ajiyar zuciyar bakin cikin koma waye ya katse masa lokaci mai tarihi a
rayuwar sa,ya ruk'e hannun ta. Tuni ta fara masa magiya ''Ka yiwa Allah
ka sake ni,ka sake ni kan Yakumbo ta shigo!" Kyememe ya k'i sakin ta,ai
kuwa sai gashi da yar sallamar ta Yakumbo ta d'aga labulai ta na fad'in
"Sarkin kuka ba dai ki na nan kina sanar ta ki ba..." Nan ta yi turus
ganin Haroun,hannun sa ruk'e da na Habeebti wacce ta kasa daga ido ta
kalli Yakumbo. "Kalu innalillahi wainnailaihi rajiun me zan gani ni
jikar Zainabu!" Yakumbo ta kurma musu ihu ta na mai tafa hannu ta shigo
falon. Fuska tsuke,Haroun ya ce "Me ko za ki gani kin sa ihu
kamar kin ga shed'anu,ku ji mu da tsohuwa,toh bud'e idanun ki da kyau,ni
ne Haroun ruke da Aliya!" A fusace Yakumbo ta masa dak'uwa tare da
fad'in "Butar gidan ku! Mara kunya kawai! Da ka ke maimaita min kai ne
ruk'e da Aliya,Aliyar matar ka ce?ba ka sau ta ba?Allah ya sa na dawo
ace barna ake min a gida!"
Haroun na dariya har da k'yak'yacewa ya ce "In ban da ke
da abun ki in ban ruke Aliya ba ke zan ruke?toh wai ma wata b'arna
abun da na riga na maida mata ta,auren b'arna ne ku ka auren ita?toh
gaskiya a daren nan ma za mu bar mi ki gida kowa ya huta,wanna tsohon
gidan ma Aliya ta ta fi k'arfin shi!"
Habeebti ta yi saurin tabo shi da k'afa,ya d'aga mata
gira,duk kan idon Yakumbo. Nan ta hasala ta na fad'in "Har wani ka dawo
da ita a rana a tsaka ka ce za ka tafi da ita! Wallahi ba ka isa ba dan
nema jemamme,ke Aliya wuce mu tafi,sauta na ce,ka sauta na ce!" Duk da
ya gane abun da ta ke nufi,ya kara ruk'e hannun Habeebti wacce ke
k'ok'arin kwacewa,ya ce " Ba zan k'ara sakin mata ta ba,toh idan na sake
ta ke zan aura?" Jin haka Yakumbu ta fara jan hanun Habeebti. Haroun
kuwa ya janye matar sa,sai ga ta jikin sa kwance,ya rumgumeta,ita kanta
Habeebti sai da ta tsorota,bare Yakumbo da ta fashe da kuka,ta saki
hannun Habeebti,ta na fad'in "Ni Dudu na ga ta kai na,haka duniya ta
lalace?me za a yi da yaran zamani,Allah ya isa ban yafe ba!" Da haka har
ta fice da sauri. Haroun ya saki dariya mai k'ara,sai a sannan ya saki
Habeebti da ta kai masa duka ta na fad'in "Me zai sa ka ma yar tsohuwa
haka dan Allah!" Ya na mai dariyar mugunta ya ce "Rama dukan da ta min
rannan na yi!" Da sauri Habeebti ta tashi ta na mai hararar Haroun ta ce
"Ka ji kunya wlh,kan yar tsohuwa ka ke ramuwa,ga shi ka sa ta kuka,kai
da Hajiya wlh! Yanzu ka tsokano min rigimar Yakumbo!" Ba ta bar mita ba
har ta bi bayan Yakumbo,ta na ji ya na kiranta ta masa banza. Dariya
kuwa yayi mai isar shi.
A dakin ta ta tadda ita,sai sharbar kuka ta ke. Ta yi
rarrashin duniya Yakumbo ta ki shiru,wai duniya ta lalace,gwara ta mutu
ta huta. A lalle sai Haroun ya zo ya bar mata gida. Habeebti ta ce "Yo
Yakumbo ki je ki kore shi mana,ya na can ya na mi ki dariyar k'yeta,wai
fa ya rama dukan da ki ka mai rannan!" Sai a sannan ta tuna,sai gashi
Yakumbo ta na goge hawaye,ta ce "Dan nema jemamme,ai tun da ya rama dai
ko?da irin bugun da yayiwa Dawud gwara wannan ai,bar shi ya kwana,tashi
ki koma wajan sa kafin ya zo ya k'ara min wata d'ibar albarkar"
.
Ko da Haroun koma gun Haroun sai cewa ta yi da shi ita d'akin Yakumbo
za ta kwana,shi ya iya kwana d'akin ta. Haroun ya tsuke fuska tare da ba
ta zab'in ko dai a daren su koma Kaduna, ko su nemi wajan kwana ko da
kuwa hotel ne a nan Bichi,ko kuwa ta yarda ta kwana da shi,ko kuwa shi
ma ya bita su kwana shi da ita da Yakumbo. Cike da takaici Habeebti ta
ce "like seriously?" Ya sha mur tare da d'aga mata gira ya ce
"Seriously,so choose wisely" baki zunb'ure ta ce "Wallahi ka fi Junior
rigima!" Cike da nuna lalaci ya ce "Wanda zan baki soon shi ma ba zai
kai ni ba,i promise...." Jin haka ta ja bakin ta ta yi shiru,saboda ta
san in da ya nufa. A haka ya taya ta su ka gama had'e kayan Junior,ta
kawo masa abunci,su ka ci tare. Duk wannan abun Yakumbo na kunshe cikin
d'aki,ta na so ta fito yin harkokin ta amma tsoran Haroun ya hana ta
sakat. Haroun na idar da sallar ishai ya ce oya zo mu kwanta. Habeebti
ta d'aga Kafad'a,ina ma laifin ta je gun Yakumbo,idan ta yi bacci sai ta
dawo. Da mitar shi na dama gun Yakumbo ta ke kwana a gidan?toh in kuwa
ta dad'e d'akin za ta gan shi shima. Da wannan ka shedin ya barta ta
tafi.
Yakumbo kuwa taki bacci,kuma baccin ta ke ji,amma dan
rigima da ta fara gyangyadawa sai ta yi firgit ta tashi zaune. Shi kuma
Haroun na nan ya na doka mata txt,wai kar fa ta bari ya zo fa,tam.
Habeebti dai na kallan ikon Allah gun Yakumbo da Haroun. Har Allah ya
taimake ta Yakumbo ta yi barci,sai da ta tabbatar mai ta yi nisa,sannan
ta tashi cikin sand'a ta fito,a tsakar gida ta ci karo da Mai Junior,dan
kuwa shi ma da har ya fito. Ganin ta ya d'auke ta cancarakas sai d'aki.
Har zan bisu na tuna an fa hana ni,dan haka na koma d'akin Yakumbo mai
cike da kamshin confo,na yi kwanciya ta,ko idan Yakumbo ta shafa ta jini
ta yi zatan Habeebti ce.
Washagari da asuba Habeebti ta koma d'akin Yakumbo,sai a
sannan ta tashe ta ta yi sallah. Sai da tambaye ta "Nan dai ki ka kwana
ko?" Habeebti ta amsa mata da "Gashi kuwa kin ga zahiri" ni da na ke
b'oye k'ark'ashin gadon Yakumbo cikin rai na nace ni kuwa na ga zahiri!
Haka Yakumbo su ka ta takun saka da Haroun,ta na masa kallan mara kunya
shi kuwa ya na mata kallan an sha da ke yar tsohuwa,har su ka zo
tafiya,ya bata na goro,sai gashi ta karb'a wai ba dan halin sa ba. Ya na
dariya su ka yi sallama.
.Bacci Habeebti ta sha a hanya sosai. Ba ita ta farka ba sai da su ka isa gida,hanun ta cikin na sa,gaban ta na fad'uwa,kai tsaye su ka wuce bangaran Mama. A falo su ka tadda ta,ba ta yi mamakin ganin su ba,dan ta san a rina,nasihar anty Salma ya shige ta sosai,ita ce har da tambayar sun ci brkfast kuwa? Daga Haroun har Habeebti mamaki ne ya rufe su,cikin rad'a Habeebti ta ce da shi "Yaushe Mama ta sauko?" "Sanda na gane ba a raba hanta da jini,na yi kuskure saboda fushi,na ga ishara kan Dawud da Hajiya,ba na so Allah ya maimaita kai na,abun da hakuri be baka ba rashin hakuri ba zai ba ka shi ba,yanzu ku dubi yanda Dawud ya zama,gaba d'aya kan sa ya tab'u,ya koma kamar yaro d'an shekara uku,har gwara ace ba shi da yanda ya zama mara daraja haka,yara ne fa abokan wasan sa!kai Allah ya rufa mana asiri. Ku je kun ji,ku zauna lafiya,Allah ya sa mu ku albarka...." Dan Murna Haroun rungume Mama yayi,da za su tafi Mama har da had'a mata goma na arziki. Ita dai har su ka tafi ganin abun ta ke kamar almara. Haka shi ma Haroun a b'angaren Hajiya da ta ji dad'in dawowar auren na Habeebti,ita ce har da hira da Haroun,in da ya mata maganar Dawud,akan zai sami dama su fitar da shi waje. Hajiya ta ji dad'i sosai,har da sa ma sa albarka,ta kuma ce za ta je ta yiwa Mama godiya. Haroun ya ce ai ba komai,yiwa kai ne. Sai da su ka yi sallama da Alhaji,wajan la'asar za su tafi su ka hangi Dawud ya tara yara,su na ta wasan k'asa,jin yana kiran yaran da "Junior" sai da Habeebti ta zubar ma sa da hawaye,Haroun ya kawar da kanta,ya na goge mata hawayen kafin ya tada mota su ka tafi.
BAYAN WATA TARA.
Bayan watanni tara, Habeebti sanye cikin rigar kakin
Haroun da gajeran wando,dan kuwa cikin da ta ke d'auke da shi ya tsufa
sosai,gaba d'aya kananan rigunan ta ba sa shigar ta,sai dai na Haroun
d'in. Shi kuma Haroun farar singilet ce jikin shi da wando
three-quarter,ya k'ara fari kyau da kwarjini,hankali ya kwanta. Kwance
ta ke jikin Haroun a dakin sa,cikin farin ciki su ke hirarrakin su. "My
Habeebti?"Haroun ya kira sunan ta,in da ta amsa masa da "Ummm"idanun ta
lumshe. Ya na mai shafa cikin ta ta ce "Allah ya sauke ki lafiya ki
haifa min Aliya Junior ko Haroun Junior.." murmushi ta saki gami da
k'ara kwantar da kan ta jikin sa,kafin ta ce "Am glad you are mine"
Haroun ya amsa mata da "And i u" shiru su ka yi,kafin Habeebti ta ce
"VIP" Sunan da ta ke kiran sa da shi kenan. Ya amsa da "Yes my Habeebti"
"Ya batun jikin Ya Dawud kuwa?" Jin ya yi shiru be amsa ma ta ba,ya sa
ta d'agowa ta na mai duban fuskar shi. Ganin Idanun sa lumshe tamkar mai
bacci ta ce "Ka na ji fa!" "Ki na fa damu na da tambayar Dawud,ah ah fa
yan mata!" Cewar Haroun,ya na mai tsuke fuska.
.
.
Kallan sa ta tsaya yi cike da mamaki,jin ya kwashe da
dariya,ya dawo da ita jikin sa,ta kai masa duka,ta na mai fad'in "Allah
harka bani tsoro,na zaci kishin ne ya motsa" ya na dariya ya ce "No tun
randa na gane kwakwalwar Dawud ta juye na dai na kishi da shi,jikin na
sa da sauki,amma psychiatris din sa ya ce ya riga ya yi losing memory
gaba d'aya,ko zai warke hardly ya dawo kamar yanda ya ke da. Kai
Habeebti ta girgiza kai cike da tausayawa,ta ce "Allah sarki,Allah ya
bashi lafiya" Ya amsa da amen. Kafin ya zame jikin shi daga na ta a
hankali,Habeebti ta d'ago ta na mai duban sa,ganin ya d'auko riga long
slip fara ya d'aura ba tare da ya sa butulan rigar ba ta ce "Ina zuwa
kuma"? Ya na murmushi "ya ce ba zance za ni ba,ops dat reminds me,auran
Huda fa saura wata d'aya" shiru ta masa,har sai da ya kai bakin kofa ta
ce "Allah ya sa a yi da mu,ko da wasa ban ji ba,Allah ya sa ba kai ne
mijin ba!" Juyowa ya na dariya ya ce "Ni ma dai ina kyautata wannan
zaton!" Ba shiri ta shiga jifan sa da filo,ya na kwaucewa cike da
dariya,ganin filollikan sun k'are ta fara rarumar wayoyin su,ya bud'e
kofa da sauri zai fice.
Tirus yayi ganin Neena da ni muna mu su labe. Cike da tuhuma ya ke duban mu,in da tuni na fara ja da baya,ita kuwa Neena kasa motsawa ta yi ganin ta gaban Haroun. Ya bude baki zai yi magana kenan ya ji saukar filo a bayan sa,tare da jiwo muryar Habeebti ta na mai kwalla ma sa kira. Kafad'a ya d'aga ya sauke tare da fad'in "Dax my wife for me! Ina zuwa i will get back to you za ku min bayanin ku su waye da dalilin laben da kuke min a gida" ya juya ciki da sauri,ganin haka na ce da Neena kin ga ki zo mu tafi,Haroun ya dawo ya same mu nan ba ta dad'i zai mana ba,ni kuwa ina tsoran hannun soja duk dai be kai zafin Captain Sulaiman na matar mu ba. Budar bakin Neena sai cewa ta yi "Ba inda zani Sidiya,dama ai sai da na ce mu zo musu a matsayin baki ba yan tsurku ba,ki ka dage sai kin yi gulsin karshe,ai ga irin ta ne kin jawo Haroun ya kama ni ina labe,ai ba girma wallahi,yanzu INA DARAJAR TA KE?"
Zani na tattare,na ce ko ba INAA DARAJAR TA KE BA?
Tirus yayi ganin Neena da ni muna mu su labe. Cike da tuhuma ya ke duban mu,in da tuni na fara ja da baya,ita kuwa Neena kasa motsawa ta yi ganin ta gaban Haroun. Ya bude baki zai yi magana kenan ya ji saukar filo a bayan sa,tare da jiwo muryar Habeebti ta na mai kwalla ma sa kira. Kafad'a ya d'aga ya sauke tare da fad'in "Dax my wife for me! Ina zuwa i will get back to you za ku min bayanin ku su waye da dalilin laben da kuke min a gida" ya juya ciki da sauri,ganin haka na ce da Neena kin ga ki zo mu tafi,Haroun ya dawo ya same mu nan ba ta dad'i zai mana ba,ni kuwa ina tsoran hannun soja duk dai be kai zafin Captain Sulaiman na matar mu ba. Budar bakin Neena sai cewa ta yi "Ba inda zani Sidiya,dama ai sai da na ce mu zo musu a matsayin baki ba yan tsurku ba,ki ka dage sai kin yi gulsin karshe,ai ga irin ta ne kin jawo Haroun ya kama ni ina labe,ai ba girma wallahi,yanzu INA DARAJAR TA KE?"
Zani na tattare,na ce ko ba INAA DARAJAR TA KE BA?
tsaya ki nemo darajar,ni dai na yi nan,na gama da wannan
bangaran kumaa,aje dai na ci walo. Tuni na cika riga ta da iska. Ban yi
nisa ba sai gashi ta biyo ni itama. Ashe dai ta na ji.lol.
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH