.
٨. Yanda Abdoul ya tafi haka shawaran da ya bata ya bi ta gefen kunnen ta don kuwa sabon soyayya suka fara da Hammad, duk tayi masa zancen aure yakan ba ta amsa da cewa "ai kawancenmu yafi soyayya mahimmanci kar ki bari zugin kewaye ya zama katangar biyan bukatar zukatanmu" a haka yake binta da daɗin baki har ta saduda. Ana cikin haka sai ya sauya salon soyayyar su ya zama hiran da suke na batsa ne, tun bata sakin jiki har ta kware a sarrafa kamai da kan motsa sha'awar su wanda hakan yasa yakan bata kula na musamman. Sukan kashe awanni suna waya har sai sun kai ga samun natsuwa, wata rana suna cikin irin wayar se ya ce mata "Baby ina so in na zo Niamey zaki ɗan min wasu abubuwan da kike kwaɗaita min a waya" Ya faɗi cikin sigar rarrashi. "Anya sweetyna kana so na kuwa, kasan dai bazan taɓa yin zina in saɓa ma Mahalicci na ba don faranta ranka" Ta ce a fusace "wa ya ce miki zina za muyi ai kin wuce ayi aron hannu da ke, wallahi iyakarmu romance, ba zan taɓa keta haddinki ba." haka yai ta faɗa mata kalamai masu nuna aminci da yarda har ta amince.
.
Washegari kuwa sai gashi, ta shirya da sunan zata shiga makaranta kamar yanda ya raɗa mata ta faɗi sai ga Abdoul ya iso gidan babu sanarwa ya zo mata sallama za shi karatu Kasar Faransa. "haka ba ko ɗan notice" Ta faɗi a zolayance "Na duba ne naga tabbas in ba wani kwakkwaran abu zai kaiki skul ba toh kina gida, shi yasa kawai na ga gara in zo yau tunda tafiyanmu ta nuna zuwa France" "aiko da ka taka zero, yanzu take shirin shiga makarantar wai an kira ta" faɗin haj Mas'ouda da ke shigowa falon. Kallonta Abdoul yayi alamun rashin yarda, murmushin yake ta sakar masa wanda ya tabbatar masa da zarginsa. "shin ina zata je tayi karya da makaranta" Ya samu kansa da tambayar kansa hakan. "Sai muje mu dawo kawai momma" Ya faɗi ma Haj Mas'ouda yana murmushi "Toh a dawo lfy, kaga sai kayi mata faɗan rashin tsaida miji, ta lake ma Hammad wanda sam ba aurenta a rayuwarsa." Ta ce fuskanta na nuna alamun takaici. "Momma lokaci ne..." gwaɓe mata baki da akayi ne yasa ta yin shiru.
.
Se dai a ranta tai ta surutun an sa mata idanu. Fita sukayi tana tunanin yanda zasuyi da Abdoul don ya sauke ta a inda Hammad ke jiran ta. Sake- sake kawai takeyi don har sun kai ga gate ɗin makarantar su sai wayarta ta ɗau kara. Kafin ta ɗauka yai saurin ɗauka ya amsa wayar kana ya sa wayar a handsfree "baby ina jiran ki tun ɗazu, na matsu naji ɗumin jikinki" aka faɗi a ɗayan ɓangaren. Da ace zata iya nutsewa a kasa da tayi don kunyar da ta shige. "se dai kaji azaban wuta don ubanka, kai rayuwar da ka zaɓa ma kanka kenan lalata yaran mutane toh Halima tafi karfin ka kuma ka fita hanyar ta ko in wulakanta maka rayuwa" bai jira amsar Hammad ba ya figi motar zuwa gida. Haj Mas'ouda ya zayyana ma komi nan ta fara kuka tana salalami "Halima me yasa zaki ɓata rayuwar ki haba nayi mamakin abin da yasa kika kasa rabuwa dashi ashe, ancen mahaifiyarki gsky ne da tace an gama kwakule ki. Tir wallahi da halinki" Ta faɗi tana shirin tsallaketa ta wuce. Kafafunta ta riko tana rokon ta, rantsuwa take mata akan ba abinda ya shiga tsakanin su asali ma wannan ne na farko nan dai ta kwashe yanda sukayi ta fada musu.
.
"Toh da kika tashi zuwa ki isko shi aka ce miki haka ne zai sa ya aureki? Sai ma ya kara tsanar aurenki. Kinga dai ni namiji ne, duk macen da na lagudata ta yarda ta aure ni wahala zata sha, kuma haka duk wani namiji yake, uwa uba ya sa ki a ɗiya mace to babu sauran mutunci tsakani. Zama ayi ta wayar batsa shi ke kai matasa ga aikata, zina, kuma da yake ce miki turmi da taɓarya ne kawai zina ina ya bar ayar Allah da yace kada mu kusanci zina, kinga kenan hatta karatun batsa, zantuttukan batsa, kallon batsa ana iya danganta su da kananun zina, kuma abin nisantarwa. Halima ki ji tsoron Allah ki tsoraci kwanciyar kabari, wuta gsky ne kuma azaban Allah gaskiya ne. Momma na wuce sai in na dawo" Ya karasa zancen yana mai da akalar zancen zuwa ga haj Mas'ouda. Godiya ta bishi dashi da albarka da tayi ta sanya masa. Nan ta bar Halima da bakin ciki da kunya.
.
Da kyar ta iya tashi ta sallaci magriba da isha'i sannan ta sa tuwon shinkafa da fakku (malohia murzazza) don taci. Jinsa take kamar maɗaci haka tai ta tutturawa har ta cinye kaɗan ɗin da ta ci.
.
Har zata kwanta ta yi tunanin ta ba Abdoul hakuri don ta san da wuya ya sake amincewa da ita. Nan ta iske missed calls ɗin Hammad fiye da talatin. Bayan ta tura sakon ban hakuri ga Abdoul ta kwanta tana wasikar jaki nan sai ga kiran Hammad ya sake shigowa, kamar bazata ɗaga ba don yana gab da tsinkewa ta ɗaga da sallamanta "Ni zaki wulakanta Halima? Nasan hana ki zuwa akayi amma ya akayi baki tsara su yanda mukayi planing ba, kin ban mamaki kuma ki rusa mana budget don wallahi zancen aurenmu yasa naso haɗuwar mu ba komi ba wallahi" Yayi shiru yana huci a tunaninsa zata ce wani abu sai tayi shiru wanda hakan ya kara harzuka shi. "kin ma maida ni mahaukaci ne ko, haka Allah ke abunsa, ya bani daman mallakar ki a matsayin mata nai wasa da wannan daman yanzu gashi kuma soyayyar ta dawo min kina min wulakanci" Ya faɗi kamar zeyi kuka.
.
"tsaya! tsaya! Hotel ne zakayi zancen aure dani, ina in har haka ne gidanmu yafi dacewa da muyi, ban taɓa haɗa makwanci da namiji ba kuma bazan fara akanka don kana min barazanar aure na zaka yi ba. Na kara gode ma Allah da ban saɓa masa saboda kai ba, wallahi kunyar da naji yau yafi min sau dubu akan wanda zanji ranar kiyama inda na cikata umurninka." Ta karasa tana mai shessheka. "haba Mon amour (masoyiyata) kin san Allah ɗaya ko to Je t'aime de tout mon Coeur (ina sonki da dukkan zuciyata. Kiyi min rai ki sake bani lokaci mu tattauna wallahi duk abinda zamu tattauna mai mahimmanci ne, akan zancen aurenmu ne. Ki taimaka min ba son ni ba" Ya faɗi cikin sigar lallashi da ban hakuri. "Na ji gobe ina gida kazo kawai" Ta faɗa a takaice. "wani irin kina gida, haba sweetyna kar kiyi min haka, in zaki samu fitowa ki same ni a hotel din. Don Allah ba don ni ba" abinda ya samu kansa da faɗi kenan bayan ya tattara natsuwarsa zuwa yanda bazai bayyana fushinsa. "bafa zan saɓa ma Mahalicci na don faranta ma abinda ya halitta ba. Kayi hakuri kawai kazo gida" itama ta faɗi kai tsaye ba tare da shakka ko tsoro ba.
.
"lallai duniya juyi juyi yanzu duk son da ake min an dena ne, sai ni kuma da Allah ya jarabta da sonki. Wai ba kiyi mamaki ba Halima, anya zan iya rayuwa babu ke, ki taimaka. Mana don Allah" Ya karasa da sumbatar iska, wanda yasan Halima na so kwarai da gaske koda ranta a ɓace yake da ya mata takan manta inda kanta yake. A mamakinsa sai yaji tace "Ni in bazaka zo ba muyi maganar anan shike nan, banyi mamakin chanzawarka ba don kana son gani na komi zaka iya" "shike nan kin zaɓi rabuwarmu akan ki zo, kin san dai babu abinda zan miki, just tattaunawa zamuyi akan mafitanmu" Ya nace akan son yardar da ita akan ra'ayin shi. "se da safe don na ga baka da niyyar gane annabi ya faku. Bazan saɓa ma Mahalicci na bafa" bata jira cewarsa ba ta kashe wayar. Buɗe kofar da akayi yasa tayi saurin share hawayen da ya gangaro mata. Har ga Allah tana son Hammad amma ya ta iya.
.
Rungumarta Haj Mas'ouda tayi tana share mata hawayen. "kin cika yar hallak Halima, ubangiji ya dubi hakurin ki ya baki mijin marainiya, kar ki sa damuwa a ranki, wani baya auren matar wani haka wata ba ta auren mijin wata. Don haka mata masu cewa zasu bada kansu don a auresu babban kuskure ne da suke tafkawa, in Allah beyi shine mijin ba sai dai bakin ciki ya kashe su don bayan asaran mutuncin su har da asaran masoyi. Kuma duk saurayin da kika ba shi kanki walau karami ko babban zina wallahi ranar da aka ɗaura aure duk son kan koma kiyayya, hantara da wulakanci zaki kwasa maimakon soyayya da tattali. Halima bakya mamakin meyasa auren yanzu babu karko wallahi maimakon mata su gina soyayya a zukatan masoyan su sukan gina sha'awa ne, tura ma samari kalamai da hotonan batsa wai da sunan su rike su har su aure su. Daga ranar da akayi auren kuma ya kashe kishin shaawarsa se ya fara gasa ta.
.
Ki cigaba da addu'ar zaɓin Allah ki aje son rai. Gara ki so mijin da kika aura da ki auri mijin da kika so. Kar kiyi gaggawa a aure, Allah ne mafi sani a dukkan Al'amura, Allah ya miki Albarka " Ta karasa tana lallashi ta, sannu a hankali ranta ya fara haske ta nemi bakin cikin ta rasa. Hamdala tayi ta nanatawa a zuciyarta akan gatan da Allah ya mata na samun mai ɗaura ta a hanya.