Sabon malamin ya bata punishment din wanki toilet din makarantar duka tare da share ko wane glass. ...tana kuka ta gama ko aji bata koma ba ta wuce gida ...
Hararansa tayi ...Kai baka san yarda ake cuwa ba ...ai murdeta zakayi ka mika masu da sun baka sae ka rugo da gudu. ..
Kaka ta rike baki tace. ..yanzu dan kaniyarki Meenalle wankan ne wahala ....to ai kuwa indae kina nan gidan ki dinga irin wannan wahalar ..tashi tun kafin na taso ...
.
*
Office dinsu ya nufa ...yana zuwa aka bashi takardar tafiya karo karatu kasar indiya nan da wata biyu ake so ya tafi ...Course din na shekara 5 ne suna so ya zama cikkaken Pilot ....Karba yayi yakoma gida ...dama Abba ya dade yana nemar mashi sae akace sae gurin aikinshi sun saka mashi hannu ...sae yau ya takardar ta fito suka saka hannu ....Mamarsa ya bawa takardar sannan ya kara fita da sauri ....
Dafe kanshi yayi tare da lumshe ido sannan yace ...Meenatou na nemeki bakyanan ..
..wani hamshakin mai kudine a cikin garin kaduna ...Sunyi aure da Rabi'at..Auren soyayya ...ko shekara basu datse ba Allah ya albarkacesu da Meenatou ...Mahaifinta yana mutuwar sonta amma matsakar uwar Alhaji Abubakar bata san danta ya haifi diya mace don tace dawainiyace da wahala haihuwar mace ...Tunda Rabi ta haifi Meena zaman gidan Alhaji Abubakar ya zame mata zaman makoki ...kullun mahaifiyarshi tana gidan ...wulakancin yau daban na jibi daban ...har Meena takai wata Takwas. ..sae Uwar Alhaji Abubakar ta kawo wata diyar kawarta tace sae ya aureta ....sannan ya saki mahaifiyar meena ko ta tsine mashi ...suna kuka suka rabu ...Sannan mahafiyarshi tace ko bayan ranta kar ya neme su idan kuma ya nemesu bata yafe mashi ba .....
Idanuwanta suka kawo ruwa ta duka gabanshi tare da kallon kasa ....
Dariya yayi ya shige masallacin kofar gidansu ....daya fito sae da ya shiga gida yayi wanka ya saka blue din shirt data fito da zaharin kyanshi tare da bakin jeans ...ya fito sae kamshi yake ...
suna hada ido suka lumshe ido tare ...tayi saurin bude idon tare da warosu ...Mai Kamshi ? ...ta fada da karfi ...bafa kai nake kwaikwayo ba hakanan nayi abuna ....
....
Uhmm Allah to ya fito masu da kudinsu ...nima da kyar kake biyana bare wasu ..uhmm .. ta tabe baki ...
....
.
Shiru tayi tana kallonshi ...a hankali tace Maikamshi ...
Zuciyarshi ta dafa tare da daura kanta a bisa tafi minti goma Sannan ta janye tana kallonshi ...idanuwanta suka ciko da kwalla ...tace ..Mai kamshi Ka dawo da wuri na dinga ganinka.. ...
Gab da zasu gama primary lokacin Meena ta gama fadawa kaf yan makarantarsu cewa gidan mamanta babansu luba ke zaune ...duk inda ta zauna bata da labari sae na babansu luba....sannu sannu magana ta koma kunnenshi ....ranar sae da yayiwa Rabi wulakanci sossae dan har cewa yayi zaya daketa ...da kyar maman su luba ta shiga tsakani ..
.
Shawarar ya dauka ...ya kuwa samu rabi da maganar ...daga farko taki amincewa ...amma daga baya daya sameta akan cewa ta nuna mashi bashi ya haifi Meena ba ...hakuri ta bashi amma ya tashi ya fice daga dakin ...tun daga ranar yake fushi da ita ...