Kofar gidan Alhaji Abubakar ta sauka ...bakin gate taga motarshi da alama yanzu ya Dawo ...
Yana hangota yayi saurin fitowa ya tareta ...Rabi dama kina raye ? ....ya tambayeta a rude ..
tambayar ta sosa mata rai ...saurin daga mashi hannu tayi sannan tace ..Muna Raye ko muna Mace abubakar wannan ba damuwarka bane ...nazone na tuna maka da amanar Da Allah ya baka tana bukatar taimakon Ubanta Abubakar ..Idan har kabar Ameenatu ta wahala a duniya daga ni har ita sae Allah ya tsayar damu ya mana hisabi ....Wata takarda ta fito da ita daga jikkarta ta daura mashi saman motar ta juya sannan tace ....Duk lokacin daka shirya daukarta ka nememu ta nan Abubakar ....Bata jira cewarsa ba ta haye adaidaitar da ta kawota ....
bata isa gida ba sae wajen sha biyu na dare ....gidan kaka ta wuce ta buga masu gidac...cikin bacci Meena taji bugun gidan da yake bata da tsoro ta fito ta tsaya jikin kofar tace ..
waye ke bugawa kamar barawo ...baka ga gidanmu bane ...to mugu idan ma kudin adashe na kazo nema to ban amso ba ...
Ki bude Ameenatou ....
Mama kene ...hala wani abu mugun babansu Luba ya maki ..kema dae Mama kawae kice ya fitar maki daga gida ...
Ameenatou nace ki bude ko ....ta fada da karfi ..
Da sauri ta bude tare da tsayawa tana kallonta ...amma mama banga wani ciwo a jikinki ba ....
Shiru tayi ta shigo tare da rufe gidan da sauri ...kaka ta tada ...ta kalleta a dan tsorace tace ...Rabi lafiya da wannan daren hakan ? ...
Da Sauki dae ...daga kaduna nake ...ta fada tana kallon meena dake zaune ta kura mata ido. .
Gurin wa kika je kaduna yanzu rabi ...
Gidan Abubakar Gwaggo can naje ..na tuna mashi da amanarshi ...na kasa Hakura gwaggo ko taimakeni ...idonta ya kawo ruwa. .
Da sauri meena ta matsa tare da dafa mamanta tace ...Mama Shi Abubakar din zai taimaki babansu luba ya sakeki ne ? ...
A a Ameenatu babanki ne ..shine mahaifinki ...ta fada da sauri ..
taba baki tayi ..su babana manya ni bana sonshi ..mai kamshine komae nawa...babana baya sona bai taba zuwa ya dubani ba ..amma mai kamshi yana sona ..ni bani da wani baba ...
Kina da Ameenatu babanki yana sonki karfinshi aka fi ....ta fada hade da dafa ...
Ba wani Mama ...baya sona ...nima bana sonshi ...ya taba zuwa ya kaini makaranta kamar yarda babansu sauran kawayena yake kaisu ...ko ya taba man kayan sallah ...Duka ba Ma'aruf yake man ba ...shike kaini makaranta idan an koroni ya har goyani yake idan ina kuka ya man komae ...shi kadae na sani arayuwata cikin maza ...sae ke da kakata ...kawae ki bar maganar babana ....kwanciya tayi bata sake cewa komae ba ...
.
Meenatou ...ya Fada Ahankali ...
Rufe idonta tayi sannan ta bude ...
Bara ki amsa ki ...ko bakya jina ...ya kara fada ahankali ..
Yaushe ka dawo ...ina son na ganka Mai kamshi ..dan Allah ka dawo ...ta fada cikin kuka ....
duk ya rude bai taba jinta ahaka ba koda take mashi kukan ya dawo kullun ba irin wannan kukan bane ...na yau yasha banban dana kullun ...asalin kuka take mashi mai shiga zuci ....
Zan dawo Meenatou ...zan dawo gobe kinji ko ...kiyi shiru please Meenatou nima na so nazo na kara ganin inga ya kika zama Meenatou ....Kiyi Hakuri gobe zan dawo ...ya fada cikin lallashi ...
Da gaske Mai kamshi ...ta fada cike da doki ...
Da gaske Meenatou..kin tuna Ranar da zamuje gidan Mama dake ...ya fada cikin wasa ...
Uhm na tuna Mai kamshi ..ina lissafawa shekara 3 da sati 5 yau ...ta fada tana murmushi kamar yana ganinta ...
sae da yayi dariya sannan yace ...kin tuna abunda kika fadawa kaka. ..
Aa ban tuna ba ...ta fada a hankali. ..
ya shafi sajensa yace ...a wancan ranar Meenatouta ta fadawa kaka cewa ta fira kirgar dangi ..to na tabbata ...
da sauri ta kashe wayar tare da rufe fuska ...Mamansa na ganinta tayi murmushi tace ...aa su mamana an fara kunya kenan .
Wayar ta kara ringing amma har ta tsinke bata dauka ba ....text ya turo ...dan lokacin Meenatou na js one. .kuma babu abunda ba zata iya karantawa ba ...
_Please Meenatou ki daga wayan baran sake cewa komae ba_
reply ta mashi tace ... _Uhm Uhm sae da safe Maikamshi_
Yana ganin text din yayi murmushi sannan ya tura mata
_Wow Meenatou ta fara hankali ...am Very Happy na kusa Furtawa Meenatou Sirrin Zuci ..._
tana karantawa ta yi murmushi tare da mikawa Mamanshi wayan ...kin karba tayi tace mata. ...
Jeki da Ita mamana taki ce ..dama bari mukayi ki gama primary sannan ....
tsaye tayi rike da wayar ta kasa koda motsin kirki ....
Babansu Luba ya shigo cikin dakin tare da nunata da hannu ....Dan Iskanci Rabi shine kika wucemu shekaranjiya ko gaisuwa babu ...sannan ma da zaki fita ubanwa kika tambaya .....
Ganin bata kulashi ba ya saka yace ...kuma ki shirya Musa yace yana bukatar matarshi nan da wata biyu ..kije ki sanar da innarki ku shirya duk abunda ake bukata na samo masu gida a kauye ...acan zasu zauna don bazan cuci yaro ba ace sae nan da wasu shekaru zai tare da matarshi ...tunda har ya nuna yana bukatarka ...don haka kuje ku shirya ni na gama koma ....
bata ce mashi komai ba har ya karaci fadanshi ya tafi don kanshi ....
*
Tun da asuba Meena ta bar gida ...inda take adashen kudin taranta ta nufa ..tana zuwa ta karbo kudinta sannan ta shige wani shago ....shinkafa ta sawo dan kwati ....Tare da gwangwani biyu na wake...Cefane tayo tare da namanta na dari biyu ...
To ka cire takalminka kaje kadаwo ...
girgiza kai yayi tare da sanya takalmi yana fadin ....Idan kaka ta gama baccin kice mata nazo muyi bankwana amma zan dawo ...
Da gaske dae komawar zakayi Maikamshi ...ta fada kamar zatayi kuka ...
Meenatou ba mungama wannan maganar ba tun dazu ...nace maki saura 1yr na gama na dawo baki daya ..mu zauna tare mu rayu a tare ko Meenatou ...karkiyi kuka kinji ko .....ya rike hannunta yana kallon cikin idonta ...
kanta ta sadda kasa tana kokarin hade hawayen dake neman zubo mata ....kwantar da kanta tayi bisa cikinsa tana shakar kamshinsa ....
Ji yayi wani sabon lamari na neman hargitsa mashi tunani ...yayi saurin janyeta tare da ficewa daga gidan
Zaman dirshan tayi gurin tare da hade kai da guiwa tana kuka .....
Lumshe ido yayi tare da ciro wani karamin abu mai shape din heart da envelope daga cikin jikkarshi ya daurawa Kaka bisa hannu tare da fadin ...Na Meenatou ne Kaka....ya fice kamar kwae ya fashe mashi a ciki.....
Kiyi Hakuri Meenalle zaya dawo kinji ko ...dan Allah ki bar kukan karki karya man zuciya nima ...ta fada lokacin da itama idonta ya kawo ruwa. ..
Kaka ta nunashi da hannu ...Kai Musa ko ubanka bai isa ya nuna man hannu ba bare kai ...
Lokacin da ya dawo hankalinshi ya fara nemanta yana sabbatun Sae yaci Uwarta ...babu inda bai duba amma bai ganta ba. ...
Watansu Biyu da aure amma Musa duk ya kare yayi baki dama abunka ga bakin ....fitinar meenalle ta bi ta dameshi kullun da irin muguntar da zata mashi sannan sau daya ya taba kamata ya daketa ...shima ya wahala gurin dukan don duk sae da ta yakuceshi ta cijeshi .....shi bai ma daketa ba kamar yadda ta wahalar dashi .....
Har labarin irin ciwon da taurin bashi ya sake mashi ba sae da taba yan kauyen ...
Don kar ya bata masu yara ...kauyen ya isheshi .... yaje har gida ya fadawa Malan sani halin da yake ciki ...
Kamar sakarae haka ya zauna yana kallonta har sae da ta gama sannan ta juyo tana kallonshi tare da watsa mashi harara. ...tace ..
.
Cikin wata biyu zaman ruhogi ya fi karfin Musa ..ga kuma wani bala'in son meenalle da yake ...ko mi tayi mashi baya iya ko da mata maganar banza ne ....abunda ta fada a wancen garin sae ma ya zama wancen garin da suka baro yafi mashi dadin zama ...dan a ruhogi cewa ta dinga yi ko rosu akayi saboda Musa dirawa yake gidan matan aure yana kwartanci ...sanna ga muguwar satar awaki da yake masu ...har cewa take wae ya dira gidan maigari ya shiga dakin amaryarshi mai garin ya saka aka mashi mugun duka ...sannan abincin mutane yake sacewa idan sun aje a waje kafin su shigar dashi gida ....
Daga nan gidansu mai kamshi ta shiga ...ta tarad da ba kowa gidan sun tafi Umara su duka ...sannan Ma'aruf kuma bai dawo ba ...haka ta dawo tana share hawaye ...anan gidan kaka ta kwana ...
aa tace mashi. .....sae gasu musa sun shigo .....nan dae aka bawa musa matarshi sannan aka ce su kaka su koma gida. .....