Alhaji Sadee ya kira Meenalle yace ta taho gida nan da sati biyu ...
Taji dadi sossae ko ba komae dama garin ta isheta ...
Ranar ta fito zata tafi asibiti ...taga motae Ma'aruf inda yake ajeta idan yazo gun Shamy ....
Hanya ta canza tayi uban zagaye ...ta fice daga School din ...Taxi ta tara ta kaita asibitin ..
Tana zaune doctor na mata bayanin yarda zata kula da lafiyarta idan ta koka gida ...kanta na bisa table din doctor din .
Magunguna ya rubuta mata ...wanda zatayi amfani kafin ta dawo ...mika hannu tayi zata karba taga an karba ....
Lumshe ido tayi ba tare da ta dago ba ....kujera yaja ya zauna kallon doctor din ...
Ya jikinta ...ya fada tare da kallonta ...
Alhamdulillah ...bata da matsala ...doctor ya fada ..
Lafiya lau kuma ta zo asibiti ...Ya kalleta. ..Fateema ki fadawa doctor abunda ke damunki ...
Babu komae ...ta fada ahankali ...
Doctor yace ...Tazo ne tana so ta koma gida shine na rubuta mata maganin da zatayi amfani dashi ...sannan bara tasha wani ruwa ba sae swan har tsawon wata shidda ....
Ido ya lumshe sannan ya mike. . tashi muje Fateema. ..
Ba musu ta mike suka fice tare da yi ma doctor din godiya. ...
Gaban mota ya bude mata sannan ya zagaya ya shiga .....kura mata ido yayi yana karantarta ...
Fateema. .....
Kamar tace mashi Meenatou dae ..amma babu dama ...sae dae ta juyo da fuskarta gefenshi idonta na rufe. ..
Ba da wata manufa ba ya kamo hannunta ya rike. ..Fada man meke damunki ...
Girgiza kai tayi idanuwanta suka ciko da kwalla ...
Babban yatsanshi ya saka ya share kwallan ...sannan ya tada motar hannunta na rike cikin nashi suka fice daga asibitin .....
Kafin ya maida ta makaranta jikinta ya hau rawar sanyi ...
Ya shafi wuyanta ...ya dauki zafi kamar wuta ...kwantar mata da sit din yayi baya ta kwanta ...sannan ya wuce da ita gidanshi ...tun kafin su isa ya kira Shamy yace ta tarad dashi gidanshi .....
Suna isa ya yi Parking ya fita ba tare da ya mata magana ba ya dauketa ya shigar da ita gidan ...dakin shi ya kaita ya kwantar da ita saman gadon ...
Sannan ya fita ya shiga kitchen ya hado mata coffee ....lokacin da ya dawo idonta a. rufe ...sae yayi zaton ko bacci take ...ja aje coffe din ya gyara mata kwanciya sannan ya rufe ta da bargo ya fita daga dakin ya koma falo ..
Yana fita ta bude idonta tare da tashi zaune ..tana kallon dakin ...duk kusurwar dakin hoton Meenalle ne ...wani photon ma bata san inda ya dauketa ba ....
Kanta ta daura saman cinyarta tana kuka ....hannu ta saka ta janyo pillown dake gefenta ....
Ribbon din da ta bashi tun tana yar yarinya ta gani cikin wani glass cover an Rubuta _*My Heartcherry*_.. _*They say you only fall in love once, but that can't be true... Every time I look at your Pictures, I fall in love all over again Meenatou*_
Glass din ta dinga shafa tana hawaye ...ita kadae .....Motsin magana ta taji ya saka ta yi saurin komawa ta kwanta ..
Tana jin lokacin da yake cewa Shamy ta shiga dakinshi friend dinta na ciki .....
Ta turo dakin ta shigo tana fadin ..Meena meke damunki . .ta zauna bakin gadon tare da dago kanta. ...
Ayya ...me kike wa kuka kuma ...dan Allah ki daina Meena ...tashi ki sha magani zaki samu sauki ....ta fada kamar zatayi kuka ..
Ma'aruf ya shigo yana tambayar ta farka ...amma sae ganinta yayi jikin Shamy tana kuka. ...
Bara ya iya jin kukan ba shi yasa ya juya da sauri ya fice daga gidan ....
Da kyar Shamy ta samu tayi shiru ta hada mata ta hada mata Coffee sannan ta bata maganin da Ma'aruf din ya bata ...ta koma tayi bacci ...
Shamy ta kira Ma'aruf din tace yana ina. ..
Ce mata yayi ...Ina Fateema ...
Da yake ta san Fateema yake cema mata ...sae tace mashi tayi bacci ..
Ya sake ajiyar zuciya yace gashinan zuwa. ......
ko da ya dawo ce mata yayi ta tsaya su kwana anan ta kula da ita ....
Murna tayi don ko ba komai yau zasuyi fira sossae da shi ...
Amma sae taga hankalinshi sam ba gareta yake ba. ...duk minti biyu ..zaya leka dakin yaga ko ta tashi ...
Meenalle kuwa ta dade da tashi amma taki bude idonta ...tana jin lokacin da suka shigo da shamy ya daga bargon tare da shafar wuyanta yaji ko zazzabin ya sauka ...
Shamy ta wani hade rai tana fadin Meye zaka wani tabata bayan ba aurenta zakayi ba ...ni bana son wannan wulakanci ..
Shima daure fuska yayi yace. ..bakya ganin bata lafiyane. .
Don bata lafiya sae ka tabata har da wani lumshe ido ..me kake nufi ...
Bai ce mata komae ba don baya son ganin fushinta ...sae towel daya mika mata tare da fadin ...please ki jikashi ki dinga goga mata a jikinta ..
Hararanshi tayi tace..tunda har ka iya taba wuyanta wannan ma bara ya maka wuya ba...
Kwantar da murya yayi yace. . Please Shamy kiyi mata mana. .friend dinki ce fa ...
Bafa zanyi ba ..ta fada kai tsaye ..
Ok ...to fita ...ya nuna mata kofa ...
Tsaye tayi tana kallonshi cike da mamaki ...tunda take bata taba ganin ya daure mata fuska ba sae yau ...kullun cikin lallashinta yake ...
Tsawa ya daka mata lokacin da ya fito daga toilet rike da bucket a hannu ...
Baki ji abunda nace maki ....Get out ...ya nuna mata kofa ...
Fita tayi a fusace tare da banko masu kofar ...shima karamin tsaki yaja ...sannan zauna gefen gadon tare da cire bargon .....
har ya kai hannu zaya daga mata riga ya tsaya cak yana kallon fuskarta ...mikewa yayi ...ya rasa ta yaya ma zai mata ...tana jinshi sae dukan hannunshi yake ...sannan ya mike ya fita daga dakin ...he decide yaje asibiti ya kira wata nurse tazo ta mata ya bata kudi
A falo ya wuce Shamy zaune ta kasa fita daga gidan ....tana ganin ta fito ta tareshi ...
am sorry Habibi ...
Lumshe ido yayi tare da kallonta bai ce mata komae ba ...
Kayi hakuri Please bara naje na mata kaji dan Allah...Please Hubby ...
Kofar dakin ya nuna mata tare da zama kujeran falon ....
Da Sauri ta shiga dakin. ..ta tarad da Meenalle zaune tana goga towel din a jikinta a hankali. ..
Tayi saurin amsa tana fadin ..Sorry MMA kawo na maki ...
A hankali tace. ..barshi ma nayi. ...
Sorry please ta fada tare da rike mata hannu ...
Komawa tayi ta kwanta ....rigarta ta cire sae dae ta kasa kwance belt din dake kirjinta na aikin da aka mata ...
Ma'aruf ta kira ya kwance sannan ya fita ya basu guri ...
Sae da tayi sati daya a gidan tare da shamy ...kula yake bata sossae idan ya shigo ya ga tana kuka ...ya dinga tambayarta meke damunta sae dae tace ba komae ....
Ranar da zasu koma ..ya shigo dauke da iv card na bikinsu ya mikawa Shamy ta gani ....
Wani Tsalle ta buga ganin designing din da aka masu da ratsin gold ...ta makale Meenalle tana nuna mata ...
murmushi tayi ta kallah tana karantawa
*Conjugal Bless* 💖
_MR MA'ARUF IBRAHIM_
*weds*
_SHAMSIYYA A MAMMAN_
_on 21 July 2017_
sae decoration din da aka bishi dashi da gold ana rubuta meenatou ...idan ba sani kayi ba bara kace mae aka rubuta ba ...zaka dauka kwarewace gurin wanda ya buga IV din ...
Wow yayi kyau ...ta fada tana waro ido ...
Murmushi yayi ya wucesu ...sae uban murna Shamy take. ...sae da ya canzo kaya sannan ya fito rike da ticket guda uku ya mika masu ....
Da nashi dana Meenalle Sae na amarya Shamsiyya ....
Meenalle ta kalleshi ido a waje tace Mr Ma'aruf ..ni ba gobe zan tafi gida ba ...
Gobe zaki tafi Fateema ..ya fada a hankali tare da bude coca cola ya zuba a cup ...
Da Sauri ta tashi ta je ta dauke cup din da sauran lemun tana kallonshi ...doctor yace ka daena shan lemun dake da gas a ciki ...
Lumshe ido yayi sannan ya bude su yana mata wani irin fitinanne kallo ...
Da sauri ta juya ta koma kusa da shamy ta zauna tare da daura kanta saman bayanta ....
Zo nan Fateema ....ya fada tare da mika mata hannu ...
Makale kafada tayi tana kallon shamy ...wacce ita hankalinta ma naga wayarta sae daukar photon IV din take tana turawa a social media ....
Ido ya lumshe yace ...me zaki bani tunda kin dauke nawa ...
Mikewa tayi ta je ta bude fridge ta dauko mashi lemun kankana da abarba da ta hada dazu ta tsiyaya mashi a cup ta mika mashi ...
Hannunta da cup din duka ya hade ya rike yana kallonta ...
Bata fuska tayi ya saketa da sauri tana yarfe hannu. ..
Tun da safe suka tafi Airport ...shi da Shamy suka zauna side daya sae Meenalle na gabansu ita da wata mata .....
Ko da suka sauka Meenalle har ta kira su Alhaji Sadee tace sun iso ..don haka tare motocinsu Ma'aruf suka iso da wadanda aka zo sauka Meenalle dasu ....
haka ta shige mota ba tare da ta kallesu ba ...har suka fice daga airport din ...sae lokacin ta sake kuka tare da fadawa jikin Mus'ab don tare suka zo ...
Bawan Allah duk ya rude ..duk da yayi aure
har da yaro daya baya. tafiyarta ......
Haka suka isa gida ...
Sae da ta huta sannan Alhaji Abubakar da Sadee suka kirata Falo ..
Alhaji. Abubakar yace ...da gaske Aminatu an maki aure ...
Gabanta ya fadi don tama manta da wani aure a rayuwarta ...daga masu kai a hankali ...
Alhaji Abubakar yace ...da yardarki aka maki auren ? ..
Nan ne tace aa ...bata san anyi auren ba sae dae kawae musa ya zo ya dauketa ..
Alhamdulillah ...Ya fada tare da tashi ya fita ...
Sadee ne ya. bude mata komae a ranar har da ba shine ubanta na Asali ba sae da ya fada mata ...sannan ta fada mahaifinta na sonta don ba yarda zayayi ne shi yasa har ya barta hannu. mamanta ..
Tabbas bata mu sa mahaifinta na sonta ba .don zaman da tayi tare dashi ya nuna mata so ..sae dae bashi da dalilin da zai banzatar da ita don Mahaifiyarshi ta umurceshi don Haka tace Ma Sadee ..yayi hakuri tacigaba da kallonshi a matsayin ubanta ..
Nan ya nuna mata matsayin da uwa ke da shi ga yayanta tare da mata waazi sossae har jikinta yayi sanyi ta cire kalmar da take fada cewa bata daukeshi uba na kirki ba ..
A Ranar ta dauke Abubakar a matsayin Ubanta amma ta kasa yarda da hajiyarshi a matsayin kakarta
Basu bar falon ba sae ga hajiyar ta shigo tana murna an fada mata Meenalle ta dawo
ta janyota jikinta tana fadin ...yaushe kika dawo yata ..
zare jikinta tayi ta fita daga falon ta barta zaune tana kallon Ikon Allah
Sadee lafiyar Aminatu kuwa ? ..ko wani abu kukayi mata
Murmushi yayi yace ...babu abunda ya sameta Hajiya ...
Anya kuwa Sadee ...ta fada tana taba hannu ..
Me kika gani ne Hajiya ..ya fada yana murmushi ..
Ahto ..naga yarda Meenalle ke nan nan dani amma yau ta nuna kamar bata sanni ba ...kasan Allah Sadee ..ina kaunar Aminatu ..da iyayenta zasu. bar man ita da ta zauna hannuna har na aurar da ita ..shin ni kau sadee baka san inda Rabi da diyarta suke ba ..idan nama abubakar maganar baya saurarena ..
Hajiya kenan . yanzu kuma jikkar har mace kina so ..?
jikinta yayi sanyi tace ..to tunda ita Allah Ya bani ba dole na rungumeta ba ?
Hmm Aa Hajiya ki tsaya ki gani ko Allah dae zai baki namijin ....yana gama fadar haka. ya tashi ya shiga ya kira mata matarshi ta fito ...
Sama Sama suka gaisa ta tashi ta tafi cike da tunani
Tun da safe Meenalle ta shirya tace wa Sadee zata je ta Gida gurin Mamanta ...
Direba ya saka ya kaita har zarian sannan ya bata kudi masu yawa ...
A Zaure ta tarad da Mamanta na waina ...ta rungumeta cike da murna ..suka shiga cikin gidan ...ta sake maman ta fada cinyar Kaka tana kuka ....
Yaro ya shigo wae ana kiran Meenalle ....
Kamar tace bata zuwa sae kuma taga kara taje kila drivern da ya kawota ne zaya juya ...dan haka ta dauki gyalenta ta fice ...
Sae da ta daga kai ta kalli Benen gidansu Ma'aruf kafin ta fita ...
Tsaye ta ganshi rike da robar swan yana waya ...sae murmushi yake da alama da shamy yake ...
Ajiyar zuciya ta sake ba tare da ta fita ba ...sae aikawa tayi tace wanda ke kiranta ya shigo tana zaure ...
Kamar mahaukaci ya shigo duk ya rame yayi baki ...sa sauri taja baya tana bata fuska ta nuna shi ...Kai ke nemana? ..
Washe baki yayi yana fadin ...kece Meenalle ...Meenalle ke kika koma haka ...Allahu Akbar ...kin ganeni ...nine Musa ..
Musa ta fada tana kallonshi sama da kasa ..sannan tace ...daga ina. ..
Baki ya washe yace...Musa dae Mijinki har kin manta ni ..gaskia an cuceni ...
Ido ta waro. ...oh wae Musa dan Sani na gidansu Luba? ..
Shi ma Meenalle ....bara naje na fadawa Baba kin dawo sae a janye karar sae mu koma ko ? ..
Dariya tayi tare da nuna shi da hannu. . ina jin har yanzu baka manta da ko wacece Meenalle ba ko .....
Bata jira amsarshi ba ta koma gida ta barshi tsaye ...
••°°••
Mamanta ta kalleta tace ...wa nene ya aiko kiranki ..
Mama wae Musa ne ..ta fada a hankali...sannan ta kalli kaka. tana goge hawayen da suke neman zubo mata tace ..
Kaka Maikamshi ya shigo ....
Daga mata kai tayi tace ..yazo Meenalle ..Kullun sae ya tambayi shin kin dawo Meenalle ..ko dazu da safe ya shigo ya gaidamu ....jiya ya dawo ma ..
Lumshe ido tayi a hankali tana kallon wainar da suketa lodawa a Coler ..wannan fa ta mecece..
Tsohuwar ta kaudar da kai tace ...gudunmuwa nakewa Maikamshi ta bikinshi ...aure zayayi ..jibi ake daura auren ma Meenalle ....
Kaka ta goge hawayen da suka zubo mata tace ...naso Meenalle ...naso ki zama matar Ma'aruf ...amma aka cucemu ...Yana sonki sossae. .
Tashi tayi tana fadin ...zan koma kaka.......
Da sauri ta fice daga gidan ta shige mota tace su koma kawae .....haka driver ya jata suka koma gida ba tare da tayi kwanakin da ta zo yi ba. ...
••°°••
Tana shiga gidan ta tarad da Shamy tazo ....suka rungume juna suna ihu ...
Shamy tace tazo daukarta ne ...ana ta hidimar biki amma babu ita ....sannan Mr Ma'aruf duk yabi ya damu baki zo ba ...gaskia ki shirya ..don ni na riga na tambayi dady da mommy ashe ba wanda kika fada mawa ...da banzo ba da bara ki zo ba kenan. ..
Murmushi tayi tace ..Shamy ai kinsan dole nazo bikinki ..
Harara ta sake mata tace ..Banga alama ...ni dae yanzu ki shirya muje ...
Duk wani abunda zata bukata sae da ta dauka ...sannan ta shiga tayi wa Mom bankwana suka shiga mota da yake shamy tare da driver suka zo ...suka koma zaria ....
••°°••
Tun a mota Shamy ta kira Mr Ma'aruf tace tare suka taho da Fateema ...
Yana tsaye ta bene ya kurawa gidan kaka ido ya waro ido yana murmushi ..yace da kun shigo gari ki kirani ..
Ok hubby ..ta fada tare da kissing din wayar sannan ta kalli Meenalle tace ..
Gaskia dole ki saki jikinki wannan bikin ..in ba so kike ki dagawa hubby hankali ba. .ni na rasa wane irin mutuncine tsakaninku ..karfa kiyi man snatching. ..
Murmushi Meenalle tayi tace ...kisha kurumin Shamy sanin kanki ne banda niyar maki snatching karki manta kidney dina daya tana jikinshi ..kuma silar hakan ne na hadaku ..kinga kuwa fadin kalmar snatching kamar butulci ne kika mani .....
Zatayi magana ta dakatar da ita .. please mu bar wannan maganar Shamy. ..
Shamy ta kwantar da kanta a bayanta tare da fadin ...Am so sorry Meena. ..
Lumshe ido meenalle tayi ..itama ta daura kanta saman cinyarta ..a haka har suka isa ...
Suna shiga garin ta kira Ma'aruf ta fada mashi sun iso ..yace su jirashi bakin gari ..zaya zo yanzu ..
*
Ko 15 Mints basuyi ba ya iso tare da kwankwasa masu glass din motar ..da yake side din Meenalle yayi knocking sae ta sauke glass din ...
Kamshinshi ya bugeta bata san lokacin da ta furta ..Maikamshina....
Saurin kallon bakinta yayi tare da fadin Me kika fada fateema ..
Lumshe ido tayi tare da bude kofar ta fito ..sannan tace ..Ango ina wuni ..
No ba haka kika fada ba ...abunda kika ce shi zaki maimata ..
Dan hararanshi tayi tace ...Cewa nayi ..sae Kamshi kake ...
A hankali ya lumshe ido tare da dubar Shamy yana fadin muje na kaiku ...shi ya tafi
Motarshi suka shiga ...Har gida ya kaisu ...Meenalle ta shiga ciki ta barsu a mota .....gidan ya cika da kawayensu ..har da soofy. ..sae murna suke ana labarai .....
Da daddare kowa yayi bacci aka bar Meenalle sae juyi take ...Soofy ta farka ta dade tana lura da ita ...sannan ta gangaro kusa da ita ta kira sunanta a hankali ...
Meenalle ta bude ido tana kallonta tace ...Bakiyi bacci ba ...
Soofy ta mike tare da jan hannunta suka koma falo ...zama sukayi sannan ta kalli Meenalle tace ...Meena meke damunki ..
Me kika gani Soofy ...ta fada tana kallonta ...
Meena komae ma na gani ...Mr Ma'aruf shine Ma'aruf dinki ko? ..
Da sauri ta rufe mata baki ...tace ...waya fada maki Soofy ..dan Allah ki bar wannan maganar ...bashi bane .
am not kid ...Meena...me yasa zakiyi haka ...kuma ba Shamy ce ta bashi kidney ba kice Meena ...duk wannan sirrin na meye ....Shin baki sonshi ne yanzu ....Dole zan fada mashi gaskia gobe ..
kuka ta sake tana fadin ..
aa Soofy. ..karki fada mashi dan Allah ...wallahi baya sona yanzu ...
Karya kike Meena ..har yanzu akwae kaunarki ..duk da bai san ke bace Meenalle amma ki kalli idonshi kaunarki ce ke cike dashi ...kuma sae na fada mashi ...
Cikin kuka ...wallahi Soofy baya kaunata naji yana fada ne ..ya tsaneni ..bansan me na mashi ba. ....
Ke dae kika sani ..ni zan fada mashi idan kinso idan zai aureki sae ki ki aurenshi
Soofy ni matar aurece ...ta fada a hankali
A masifance ta juyo tana fadin karya ne wallahi ...
Hannunta ta ruko tana kuka ...ki yarda dani Soofy ina da aure ..da banda aure da babu abunda zai hani bude *SIRRIN ZUCI* ...sun aurar dani ga wani ...wani wawa Soofy Wawa irin Musa ...Tabbas ina son Ma'aruf ..amma katanga babba ke tsakanina dashi ...sun dasa mashi tsanata ta yarda har yake furtawa ....ya zanyi Soofy ....ta kara fashewa da kuka. .
Tausayinta yayi balain kamata ...dukawa tayi tare da rungumeta a jikinta ...kiyi hakuri Meena...in sha Allahu dole musa ya sakeki ...kin sani mahaifina Justice ne ...zan mashi magana dole a bi maki hakkinki ...kiyi hakuri dan Allah
°°••°°
Karfe biyu dae dae aka daura Auren Ma'aruf da Shamy gaban dunbin mutane. ...Amarya baki yaki rufuwa haka ango ...Sae shirye shirye ake ..don bayan biki da kwana uku zasu bar kasar saboda karatunta da kuma aikinshi ...
Wajen karfe 9 ne akace a fito da amarya zaa tafi dinner ..
Amarya ta shigo hall tare da manyan kawayenta guda biyu ....
Chanchadi Mazakwae ...uhmm abun baa magana ..idan kaji ana Carai ..to wannan amaryar ta wuce anan ...Sky blue din gown ne a jikinta ...fuskarta na rufe da wani golding din net daga samanshi ya fitar da wani shape kamar an daura crown ......
Ango na zaune suka shigo ....lumshe ido yayi tare da jingina da kujeran da yake kai ..sannan ya bude su a hankali tare da sakin wani fitinannen kallo yana kallon right side din amarya ....
Sae lokacin na kalli inda yake kallo ....
Ido na waro sannan na lumshesu nima kamar yarda yayi ...Phone dina ta sulale ta fadi kasa ...duka glass din ya dargaje😒😥😥...bansan lokacin da nayi zaman dirshan ba ...ina kallo.. .sae da na lalubi wayar da niyar na fada maku me na gano ...sae lokacin na lura ashe ta dargaje 😒😒😒
*
Meenalle nagani tsaye rightside din amarya ...sanye da gown itama amma Pinch colour ....sae head maroon ...ta gaji da haduwa ..fatar har wani kyalli take. ....
Ma'aruf ya taso a hankali har ya iso kusa da amaryarsa ...hannnuta ya kama tare da matsawa kusa da Meenalle ...
Natural beauty ...ya fada mata dae dae kunnenta ....phone dinta tayi kara ....
Ta dan saci kallonsu ta dauke kai ..tare da ficewa daga hall din ....ta dauki sayar. ..
Aminatu ...gamu a bakin gate amma kamar baku ciki ko ? ...aka fada daga dayan bangaren ...
Muna ciki. mana ku shigo har zaa fara dinner ....
ki fito. ki shiga damu please ...ko mun shigo bamu san inda zamuyi ba ...don gurin da alama yana da girma. ....
Okey ..gani nan fitowa ta fada ...tare da juyawa ta kalli su Shamy ...Ma'aruf rike da hannunta ...wani abu ya tokare mata kirji ta fita da sauri ....
Daga can side din ta hango wata bakar jeep ....ta fito da wayarta ta kira number. ..kuna ina ...
Ki tsallako muna cikin jeep din dake tsaye gefe guda ....kafin tayi magana an kashe wayar ..
Tabe baki tayi ta tsallaka tare da knocking din glass din motar na gaba ....
Kofar baya aka bude ...wani kato ya fito ya toshe mata baki ya jata cikin motar suka hau titi da gudu ...
Hannun ta cire daga bakinta tare da jan uban tsaki ta gyara zama cikin motar tana watsa masu wani uban kallo ..
Da cewa kuka yi na fito kunzo sace ni ne da baku wahalar da kanku ba ....ta fada tana kallonsu ..
Torch light din wayarta ta kunna ta haska su daya bayan daya. ..sannan ta maida hasken ga na kusa da ita ..
Musa Sani ..ta fada tana kallonshi ....matsalata dakae wawa ne ...bakka ganewa ..dan zaka dauki yarinyar da kake tunanin matarka ce sae ka hado da wadannan jakunan ....? ..
Ke.....wani ya daka mata tsawa ...tare da nunata da hannu.
Hannun yaji an murde da karfi har sae da yayi kara alamun karewa .tare da angazashi baya ....daga lokacin bai kuma cewa komae ba ..
Meenalle ba tsoro ...haka ta dinga wankesu ..har suka shiga wani tsohon daji ...sae lokacin ta lura sun bar titi ....
Bata kuma cewa komae ba sae kallon ikon Allah da ta tsaya tana yi ....har suka isa wani dogon gini ..baraka iya cewa ga karshensa ba . ..
Daya ya sauka ya bude masu gate din suka shigar da motar ciki. ...
Ba wani babban gida bane ...duka kofarshi daya ta shiga ciki sae ta gate ..duka gidan arufe yake ...suka faka motar suka fito ...
da yake akwae hasken wuta ...ta bisu da kallo ..kamar mahaukata haka suke ko wane bakikkirin dashi sae mazurai suke ...
Ta hadiyi wahalallen miyau sai lokacin gabanta ke faduwa ....amma ta dake ta na hararansu ....
Mu shiga ciki Meenalleta ...Musa ya fada yana dariya ...
Murmushin ta sake mai cike da takaici ...tace ..ai ko bakace ba Musa kasan zan shiga sannan na zauna daku har sae kun gaji dan kanku ku mayar dani kuma na kwanta idan kai dan iskane kayi gigin zuwa kusa dani ...
Girgiza kai yayi yana wata dariya ..Meenalleta kenan ..kiyi hakuri ki soni muyi rayuwa a duniyata ..ki haifa man ya'ya kyawawa irinki ...
Wace duniyace gareka Musa...duniyar karnuka ..Sannan ba Ya'ya zan haifa maka ba ...Uwaye zan haifa maka. ...
Gaba yayi yana dariya ta bi bayanshi ...sauran suka take masu baya. ..har wani karamin daki ya kaita mai dauke da karamin gado sae wasu akwatuna guda uku ...
Meenalle ga lefenki nan ...wanda da ban baki ba ....akwae english wears a ciki kinsan ni mayan sune ....ya fada yana washe baki ..
Dariya ya bata sossae har tana rike ciki ...sannan ta nufi gurin gadon ta cire pillow ta aje a kasa ta kwanta ..tunda dama tayi isha'i ..
Tana kwance ya shigo tayi saurin tashi zaune tana kallonshi...kazar amaryace na kowa ..ya fada yana kallon kirjinta ...
Babu tsoro taja ledar ...tana dubawa ....je ka dauko plate ..ta fada ba tare da ta kalleshi ba ...
Da sauri ya mike yana fadin Meenalle har kin sauko zaki ci kazar amare ..kila dama dan ban nuna maki ita ba shi yasa kike zagina dazu ..
Musa baka gane ...ko dae Mamansu luba hada maka da nonon awakai lokacin da take shayar da kai....ta fada tana murmushi
Da kuwa ta cuceni yasin ...ya fada sannan ya fice daga dakin ...
Da Sauri ta mike ta rufe dakin da keys din dake jikin kofar ta koma ta harde kafa ta fara cin kazarta ...
.
Meenalle bude ga parantin ....ya fada yana buga kofar ...
Musa Aje akwanta sae Allah ya hada mu gobe ....ta fada daga cikin dakin ..
Haba Meenalle ke fa kikace na dauko ..ki bude dan Allah ...wallahi ni bama kazar zanci ba ..ke nake so...
ashe ma kai sakaraine .....ta nannade ledar tare da gyara kwanciya ..
Yayi lallashin duniyar nan ..amma taki ko kulashi ..daga karshe yace ...Meenalle ke yar iskace ko...kinsan ba tare zamu kwana ba kika cinye man kaza ko...to wallahi da safe sae na maki shegen duka ....ya bugi kofar da karfi ya wuce ....
Tana kwance taji alamar mota ta fita daga gidan ...ta mike ta leka ta taga ...taga sun fice sae mutun daya zaune bakin kofar an barshi gadi .....
Ta bude kofar ahankali tare da lekawa ...babu kowa sae falon dake gauraye da hasken wuta ...ta fito tana sanda ta rufe kofar shigowa ciki sannan ta shiga wani karamin daki mai shegen duhu. ...da wayarta ta haska taga duk kayan fadane aciki ..sae bindiga da bata wuce 5 ba kirar AK ....sae uwayen akwatuna da da buhu cike da kudade ....
Sae lokacin ta tabbatar yan fashine .. ..dakin da aka bata ta koma da kwanta ..
Su Musa suka dawo babu irin bugun duniyar da basuyi ba amma Meenalle bama ta sani ba tana baccinta ...
Da Asuba ta farka ta iske missed call kusan 76 ...50% duk na Ma'aruf ne ...sae Soofy itama ta kirata ...sae Mamanta ....
Mamanta ta kira ..tace fada mata duk abunda ke faruwa ...sannan tace mata ta kwantar da hankalinta ...ta dinga mata addu'a in Allah ya yarda zata dawo ....
Sannan ta kira Soofy ..itama addu'arta ta roka ta kashe wayar ...
Text ya shigo mata na Ma'aruf ne ... _Fateema ina kika shiga ne ? kina dae lafiya ko ,? ...._
Reply ta mashi _Na koma gida fatan Alkhairi kai da amarya_
Ta kashe wayar gaba daya ...cikin saa taga toilet acikin dakin ...ta shiga tayo alwala ..cikin akwatin da Musa ya nuna mata ta duba ko zata ga hijab ...amma babu ...sae Zanin atamfa ta dauko ta lulluba tayi sallah .....
Sae da gari ya waye sannan ta fita daga dakinta ...lekensu tayi babu wanda ya farka ..kamar matattu ...tsaki tayi ta bude kofar ...
Firgigi suka farka ...ko wane sae ya taso da zuciyarshi ...da sun hada ido da musa sae ya koma ya kalli kasa ...
Musa kuwa duk bala'in da yayi niyar ya mata sae ya kasa ...ya matsa yana washe mata baki.....ba kuma wani abu ya hana ya mata ba .aa tunowa yake da lokacin da suna kauye ..idan zai bugeta azabar da take mashi ...
••°°••
Tun kafin a shiga court Alhaji Abubakar ya sami Alkali ya mashi bayanin Musa ya sace Yarinyar ...Haka aka nemi Malan Sani shima bai zo kotun ba .....
Alkali ya aika a daukoshi ...yana zaune bisa dankali aka daukoshi sae masifa yake
Aka zo dashi office din Alkali ...aka tambayeshi ina Musa ....kada kai yayi yace bai sani ba ..
Juyin duniyar nan Amma Malan sani ya yace bai san inda musa yake ba ....
Nan take Alkali ya raba auren tare da tsare Malan Sani har sae Musa ya dawo da Meenalle lafiya ..idan kuma wani abu ya sameta to hukunci mai tsanani zai hau kanshi ...
Lokacin da labari ya isa gurin musa sae cewa yayi ...indae sae ya dawo da Meenalle zaa saki Malan sani sae dae ya mutu a daure ...
Ran Malan sani yayi bala'in baci ...ranar ya tsinewa musa yafi a kirga. .sannan yayi nadamar abunda ya dinga yi akan musa gashi yanzu ance ya maido Yarinyar a kwanceshi yace sae dae ya mutu a daure .....
••°°••
Ma'aruf da amarya aka koma india ...rayuwa suka bude mai kyau ...matsalar daya ce Shamy bata san yarda zata kula da mijinta ba ....illa iyaka ta dafa break ta ta fi school ...amma abincin rana dana dare sae dae ya sawo masu ...
Lokacin suna gab da fara exam amma babu Meenalle ..hankalin Ma'aruf yayi bala'in tashi ..har rigima sukayi da Shamy lokacin ...wae sae ya fada mata dalilin da yasa ya damu ....
Bai ce mata komae ba ...yaja har school din ya saki iyayen kudi sannan ya samu wata wadda ta riga ta gama school din aka sakata ta zaunawa Meenalle ...
Shamy ta shiga dakin Ma'aruf rike da cup din coffee ...bai san ta shigo ba yana rike da photon Meenalle ....ji yayi an fuzge photon tare da fasashi kasa ...
Lumshe ido yayi ba tare da yace mata komae ba ya duka yana tattara photon ..
kafa ta saka tayi wurgi da wanda ya tattara ....
Azuciye ya mike ya wanka mata mari ...tare da jan hannunta ya fitar da ita daga dakin ya saka key ...
Bugun kofar ta dinga yi kamar mahaukaciya tana bala'i ....har sae da ta gaji sannan ta yi shiru ...sae da tayi Wata ba tazo shinfidarshi ba ...haka bata mashi magana ba ...
Ma'aruf ba mai son hayaniya bane ganin abun nata bana karewa bane ya saka ya kirata da kanshi ya lallasheta ganin lokacin tana dauke da ciki .....
.
An baza ko 'ina ana neman Meenalle amma ko labarinta baa samu ...an kirata a waya an tambayeta ina take amma sae dae tace wallahi bata sani ba ....
Haka musa ma nemanshi ake ruwa jallo ..amma da yake munafukine ..suna da wani tsari indae ana neman su to basu taba haduwa da masu neman nasu ....
Kuma bai fasa shigowa zaria ba ....duk lokacin da yaso zaya shigo kuma ya fita ba tare da wadanda ke neman nashi ba sun ganshi ...ko da kuwa zaya wuce ta gabansu to shi kadae zai gansu ....
Meenalle kuwa tana can zaune ...duk tabi ta ishesu ....akwae ranar da suka bata girki ...Shinkafa da miya ...sae da ta juye masu quatern gishiri cikin miyar ....ranar Musa kamar yayi hauka don baya cin gishiri .....
Sannan babu shegen da ya isa ya nuna mata hannu ....komae tayi masu kuwa ...Musa ma ya taba gigin dukanta ranar da suka dawo daga fashinsu sa daddare suka iske kofar bude ...sukayi ta murna don sun saba kwana a waje ...ga sauro ..ga kunamu ....Suka shiga falon babu wuta su duka sukayi mamaki don babu inda zaka tarad ba da wuta a gidan ...
Gashi babu mai ko waya ...haka suka shiga cikin ...ko wane da ya shiga sae ya fito da gudu yana ihu rike da kafa ....
Zuwa can wuta ta kawo ...sae lokacin suka lura da cewa kwalbace farfashe a kasan gurin ....kuma sun tabbata Meenalle ta sakata ....
Musa ya shiga dakinta a fusace tana kwance ya fizgota tare da daura mata mari ....bai sauke hannu ba yaji kalan nata a fuskarshi. ..afusace ya cire belt ya zura mata...
Zafi da azaba bata san lokacin da ta murde mashi abun fitsari ba tare da aza mashi cizo a idon dama .....
A rude ya fito yana ihu rike da wando ....suka tareshi suna rikeshi ...wasu na Allah ya kara wasu na tausayinshi ....kafin safe ido ya kumbura ....
Sae da yayi sati baya fita ...don daga karshe ma zazzabi ya rufeshi ...tunda lokacin bai kuma gigin dukanta ba ...
kowa ta isheshi a gidan ...bayan ya warkene. ..yayi alkawarin ko zata mutu sae ya kwanta da ita ranar ..don haka suna gama fashinsu ya sawo mata kaza ...har wani karamin gidansu ya tsaya yayi wanka sannan suka taho ...
Da yake generator dinsu ya lallace ...babu wani shamaki suka kutsa kai cikin falon ....
Meenalle na tsaye bayan kaure rike da tabaryarta ...Musa ya kutso kai rike fa ledarshi .
.
ta daga tabaryarta iya karfinta ta buga mashi a goshi ...ya dafe gurin tare da sakin ledar ya koma baya da gudu ...
Lafiya oga ...wani ya tambaya ...
Saboda azaba da hannu ya nuna mashi cikin gidan ...ya daga labubalai ya shiga yana lafiya ....dukan da yajine ya bashi amsa ya yo baya dafe da goshi ga jini na zuba ...
Cikinsu babu wanda bai yi kokarin shigowa ba haka babu wanda baiji ciwo ba ...da Meenalle ta tabbata kowa ya samu rabonshi ta dauke ledar ta shige dakinta da gudu ta saka makulli .
Safe suna zaune kowane fuska a kumbure ta fito ta saka su gaba tana ta dariya ..
wani Sale cikinsu sae da yayi kuka ranar saboda takaici ...gashi sun san ita tayi masu wannan rashin kirkin amma babu halin magana ...
Bayan sati daya ne suka dawo suka iske ta kona masu duk abunda aka tara a gidan ...
Ranar sukayi Meeting musa baya nan suka sami Meenalle suka roketa tazo su fitar da ita cikin gari ...
Cewa tayi bata so bara ta tafi ba ...don bata gaji da zaman ba ..
Suka dinga hada ta da Allah ..Da kyar ta yarda ta shiga motar suka taho ....Har kofar gidan Kaka suka ajeta sannan suka juya da sauri ...