*A* office en D.P.O aka sauke su,da yake ya d'an shiga ciki yana zagayen duba masu laifi..
Suna nan zaune kusan 30 minutes sannan ya shigo,ganinsu da yayi yasa shi sakin fuskarsa,yana mai mik'a musu hannu,sunkuyar da kawuna sukayi k'asa alaman girmamawa kafin suka bashi hannu..
Bayan sun gama gaishe² ya kallesu su duka coz bai san abunda ke tafe da suba a wannan safiyar
"Ammm!me ke tafe daku?duk da dai nasan zuwan naku ba zai wuce kan yarinyar da kuka bada report na b'atanta ba"
"Yallab'ai ba b'ata tayiba saceta akayi"
ZUHRA tayi katsalandan d'in yin magana
'Dan murmushi yayi,kafin yayi magana BB ya rigashi duk da yayi maganar ne k'asa² ta yadda ita kad'ai taji me yace
"Tambayanki akayi da zaki yi magana?"
Bata kalleshiba ta d'an sunkuyar da kanta k'asa
"Ehhh!tabbas kina da gaskiya ba b'ata tayiba saceta akayi,shin kina da masaniyar yadda al'amarin ya faru ne,kuma mene ne alak'arki da ita wacce aka sace en?"
Sai da ta kalli BB tukun,ganin ya d'aga mata kai alaman tayi magana yasa tace
"Ehh!yallab'ai tabbas ni witness ce akan wannan case en,kuma ni Y'ar uwace ga wacce aka sace ta jini"
Kaf abunda ta sani na yadda al'amarin ya faru ta sanar da shi,sai dai abunda ta rage cikin labarin bata sanar da shi mahaifiyarsu ce tasa aka aiwatar da abunba,tana gama jawabi tayi shiru ba tare da ta sake cewa komai ba..
Dogon ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara magana
"Shin ko akwai wani abu da zaki iya ganewa game da mutanen da suka aikata wannan d'anyen aiki? misali:kamannin wani ciki,suturan da suka sa da kuma mota ko number motan?
Shin zaki iya gane wannan ko makamancin haka?tunda kinyi bayanin kuna tare lokacin da al'amarin ya faru"
Kanta ta d'an d'age alamar tunani
Fitowarsu daga gida zuwa aiken MAMA da yadda akayi al'amarin ya faru take tunawa,da sauri kuma ta d'ago
"Yallab'ai bazan iya gane kamanninsu da number mota ba,amma motansu k'irar CRV ne bak'i sannan kuma kayan jikinsu duk bak'ak'e ne,sun rufe fuskokinsu da bak'in handkey idanunsu saye cikin black glasses,wannan shi ne kad'ai abunda zan iya tunawa game da su"...
Shiru cikin office en yayi na d'an wani lokaci,baka jin komai sai kukan AC dake aiki...
"Ammmm!gaskiya wannan case en yana da matuk'ar d'aure kai,da kamar ace mun samu photon ita yarinyar da aka sace sannan kuma an gane fuskar ko da mutum d'aya ne cikin masu laifin da sauk'i,ina tunanin aikin da sai yafi zuwa mana da sauk'i,amma duk da haka abun bai b'aciba...
Yanzun akwai wani taimako da kuke buk'ata?"
Yayi tambayar yana kallonsu duka...
A hankali KHALEED ya d'an tab'a KHALEEL
"Uhmmm!kai baza ka iya magana bane?"
KHALEEL ya tambaya yana murmushin mugunta...
Harara BB ya sakar masa sannan yayi gyaran murya,hankalin D.P.O na kansa jin yayi gyaran murya yasan akwai magana a gurinsa
"Ehhheemm!yi maganarka muna sauraronka"
"Yallab'ai dama kan maganar photo ne idan muka samo zaku iya nemota kenan?"
"In sha Allah muna fatan samota duk inda take,saboda zamu baza photonta ne cikin garin nan,idan ma bata cikin garin nan zamu bada cigiya a kafafen sadarwa da yardar Allah zamu sameta"
"To Allah ya taimaka yallab'ai,amma akwai wata alfarma da nake nema idan babu damuwa"
"Fad'i maganar da kake son yi ina saurarenka"
"Dama Yallab'ai ina son ka taimaka mana da y'an sanda da za suyi mana bincike ne su kuma lura da al'amuran wasu mutane,saboda akwai zargi akan su ina tunanin da hannunsu cikin wannan d'anyen aikin"
"To! babu damuwa in sha Allah duka ai ba zai gagara ba,za ka bada address na inda suke idan yaso komai ake ciki zasu dinga sanar da kai"
Basu suka bar police station enba sai da suka tabbatar sun samu mafita akan yadda zasu b'illowa al'amarin....
Suka yi masa sallama...
Ta hanyan kasuwa yabi dasu,da mamaki KHALEEL yake binsa da kallo,sai dai bai kai ga tambayarsa ba yaga ya fice...
Cikin kasuwan ya shiga da tambaya ya samu store en,tun da akayi maganan photo zuciyarsa ke ayyana masa abubuwa da dama,shi ya sama yanzun ba tare da yayi shawara da kowa ba ya shiga siyan kayan zane abun mamaki kamar wani Artist haka ya siya kayan,yaran store en suka bishi da kaya fal hannunsu...
Cikin ZUHRA ko KHALEEL babu wanda yasan me yake shiryawa kamar yadda babu wanda yaga kayan da ya siyo aka zuba masa su a booth...
Ya sallamesu suka kama hanyan komawa store,shi kuma ya shiga motor en yayi mata key zuwa gidan su KHALEEL...
《《》》
Tun safe kowa cikin su biyu BABA ZUWAIRA da kuma KHUBRA suka kama hanyar sana'arsu...
'Bangaren KHUBRA babu wani damuwa da yake a ranta wanda har zai dinga damunta a wannan lokaci,burinta bai wuce ganin ta kafa kanta a rayuwa ba,shi yasa ta jajirce dan ganin rayuwarta ta inganta..
Can k'asan ramin ta gangara,gurin babu mutane sosai sai y'an tsirari da suke d'iban ruwa suma,har ta gama tana shirin barin gurin wata matashiya ta matso kusa da ita fuskanrta a sake,da sallama a bakinta dai² lokacin KHUBRA tana niyyar haurawa sama
"Sannu baiwar Allah"
"Yawwa sannu"
KHUBRA tana kallonta da mamaki ganin babu wanda ta sani a garin..
"Suna na HAFSAT ina zaune cikin garin ZAKIRAI,babana shi ne SARKIN KASUWA"
"Allah sarki na gode"
KHUBRA ta fad'a tana d'an murmushi..
"Kefa baki fad'amin naki sunan ba"
"Suna na KHUBRA"
"Amma ke bak'uwa ce a garin nan ko?naga ban san fuskarki ba"
"Ehhh!haka ne,ban jima da zuwa garin nanba"
"Allah sarki na gode sosai,sai mun sake had'uwa"
Kowacce ta kama hanyanta,da yake ita KHUBRA ta riga ta gama abunda ya kawota gurin,ita kuma HAFSAT zuwanta kenan shi yasa tafiyan nasu ya bambanta......
《《》》
"Oyoyo TAKWARA yau kam ina da manyan bak'i,yaushe rabona da ganin k'afarki a gidan nan,gaishe nima da kuke zuwa kun daina yanzu, ince ko HAJIYA MURJA ta hanaku zuwa??"
"Wallahi UMMI abunda na fad'a kenan lokacin da KHALEED ya sanarmin wai nan zasu yini"
Harara BB ya sakar masa ba tare da yayi magana ba...
"Ai kuwa dai gaskiya KHALEED ya fad'a,kai dan gidanku idan kaje a matsayin wa kake zuwa??"
"Aaaaa!UMMI nifa na fishi zuwa kinga kuwa dole na zama d'an gida,shi kuma idan ya zo nan bak'o ne"
"A'a ni d'ana ba bak'o bane a gurina,kai ne dai ka maida minshi bak'o"
"Yawwa UMMI gara da kika fad'a masa dama na fad'a masa ni ba bak'o bane a gurinki"
"K'warai kuwa ka wuce matsayin bak'o a gurina,bama kaiba ko da wani ka kawo gidan nan wanda ban saniba ai bazan kira shi da bak'o ba,saboda matsayinsa ya wuce haka"
"Lallai yau zuwanka yasa UMMI ta mai dani gefe kun had'emin head kai da UMMI,sauk'i d'aya Allah yaso nima ga k'anwata da yau ina jin sai nayi kuka"
Yanda yake maganar ya bawa kowa dariya cikin parlor....
Yini guda sun k'auracewa gidan MAMA,sai dare suka yi niyyan komawa gida,turaruka masu kyau da tsada UMMI ta bama ZUHRA,suka rako su har bakin mota,sai da suka ga fitarsu daga gidan sannan suka juya....
《《》》
Tun bayan fitarsu ZUHRA daga gida MAMA ta rasa abunyi,kallon y'ar lelenta tayi fuskarta duk ta soma tasawa saboda dukan da ZUHRA tayi mata...
"Kin ga irin abunda nake fad'a miki ai,duk lokacin da kika takali yarinyar nan da fad'a sai nayi miki magana,daga yau ai ba sai na sake ce miki komaiba,gobema kya k'ara"
"To ni MAMA me nace mata bayan itace bata da gaskiya dan kawai nayi magana shi ne ta zage nifa"
"Ni dai ai bance miki komaiba,amma dai kam wata rana zaki ci ubanki a hannun YAYANKU,kinsan ba a tab'a ZUHRA a gabansa"
Tura baki gaba ASHNA ta shiga yi dama gashi ya kumbure,abun dai sai wanda ya gani....
Yinin ranan MAMA tana zuba idon ganin ta inda su ZUHRA zasu shigo gidan amma shiru kake ji wai "MALAM YA CI SHIRWA".....
*8:40*
MAMA ce cikin parlor sai kaiwa da kawowa take,abun duniya duk yayi mata yawa,ita kad'ai sai surutai take,ga wayan a hannunta amma ta kasa kiran KHALEED bare ta tambaye shi ina suka tafi,ganin ta rasa mafita yasa ta nemi guri tana shirin zama,horn data jiyo shi ya bata daman sake mik'ewa ta nufi hanyan fita daga parlorn....
A haraban gidan suka had'u lokacin yana k'ok'arin fitowa daga mota...
"Kai daga ina kuke tun safe da kuka fita sai yanzu"
Babu wanda yayi magana cikin su biyu,suka kama hanyan parlor,binsu ta shiga yi har cikin parlorn yanayin fuskar BB ya hanata sake yin magana dan ko yanda ya had'e fuskansa za kayi tunanin bai tab'a sanin wani abu da ya danganci dariya ba,wannan yanayin da ta gani shi yasa ta kasa sake yin magana....
Ita ko ZUHRA suna shigowa ta kalli BB da ya zauna tana fad'in
"YAYANAH sai da safe"
Kansa ya kad'a mata ba tare da yayi magana ba...
MAMA sai kallonsa take amma ta kasa magana kan dole ta jaa bakinta tayi shiru,dan tana da tabbacin ko tayi maganar ba kulata zaiyi ba,tunda y'an miskilancin suka motsa....
Zaman gurin ne ya isheta haka ta tashi ba tare da ta samu abunda take nema ba,tana barin gurin shima BB ya mik'e da niyyar barin gurin har ya d'auka hanyan bed room ensa,ko me ya tuna kuma ya dawo,fita yayi har parking lot,booth ya bud'e duk kayan dake ciki ya fito da,d'iban kayan yayi a hankali ya shiga dasu bed room en...
Fito dasu ya shiga yi d'aya bayan d'aya ya baje komai,k'aton allon ya kafe a tsakiyan bedroom en nasa yanda ko da mutum ya tashi daga bacci da shi zai fara arba...
Toilet ya shiga ya sakarma kansa ruwa,ya jima k'asan shower kafin ya fito,ba tare da ya b'atawa kansa lokaci ba ya zira farin singlet da boxers,sai sprays da perfume's da ya bajewa jikinsa kamar ba gobe...
Bacci ya k'auracewa idanunsa ,dai² lokacin wall clock en d'akin ya nuna 10:30pm....
Idanunsa ya rufe yana tuna wasu moments nata,a hankali ya bud'e idanunsa masu haske ya sauke su kan allon da ya shimfid'a white card board paper...
Sake rufe idanunsa yayi bayan ya d'auki alk'alamin,cikin nutsuwa ya dad'a bud'e su,a hankali ya shiga zane saman paper en,abun gwanin sha'awa haka yake sarrafa hannunsa da yake d'auke da alk'alamin...
Bayan shud'ewar wani lokaci ya dakata yana k'arewa zanen dake kan board en kallo,dai² lokacin idanunsa sun gama k'ank'ancewa kallon zanen dake jikin paper yayi,ya saki wani k'ayataccen murmushi,shi kad'ai yake surutansa,bed ya nufa bayan ya gama sumbatan picture en ya kwanta,dai² lokacin 12:00am...
Bacci mai nauyi ya d'auke shi cike da mafarkin KHUBRA......
Da safe misalin k'arfe 11:00am ya fito cikin shiri hannunsa rik'e da paper ya fito sai k'amshi yake bazawa,har ya fita babu da wanda ya had'u haka ya fice daga gidan...
Direct police station ya wuce,sergent da suke kan counter suna ganinsa suka shiga gaidashi saboda sun ganeshi office en D.P.O suka raka shi,dan sun san basa rakiyar banza...
After sun gaisa da D.P.O ya shaida masa abun da ya kawo shi,take kuwa ya buk'a ci ganin pic en yarinyar da ya fad'a masa ya zo da shi,babu b'ata lokaci ya mik'a masa...
Duk abunda ya kamata shi D.P.O suka tattauna akan yadda za a yad'a photon cikin garin Kanon dabo...
BB ya masa godiya ya fito dan tafiya gida,wanda k'arshe ba shi ya bar station enba sai da D.P.O ya had'a shi da y'an sandan da zasu yi masa aiki suka gaisa,sannan ya wuce.....
《《》》
Kwanaki sun ci gaba da gangarawa b'angaren KHUBRA rayuwarta cikin nutsuwa babu wani abu dake damunta rayuwarta take babu takurawa...
Kulawan da BABA ZUWAIRA ke bata ko lokacin da take gida hannun iyayenta bata samu irinta ba,shi yasa ta saki jikinta sosai babu damuwan komai cikin ranta....
Duk lokacin da BABA ZUWAIRA ta kalli KHUBRA tana tausaya mata irin rayuwar da take ciki,duk da ta kafu akan sana'arta ta *GARUWA* wanda yanzun ta kai duk line da zata gifta cikin garin na ZAKIRAI an santa,duk inda ta gifta za kaji ana fad'in *KHUBRA Y'AR GARUWA*,wannan d'aukaka da ta samu kan sana'arta yana mata dad'i da yadda mutane ke yabon halayenta cikin garin....
Wannan kenan......
*~
Tun bayan zuwansa police station lokacin da ya kai photon da aka buk'ata,yake jiran jin sakamakon binciken daga wajen D.P.O amma shiru,har ta kai ga yau tsahon kwanaki bak'wai amma shiru kake ji....
_WAI MALAM YA CI SHIRWA...._
B'angaren Police kuwa da aka had'a BB dasu tuni suka fara aikinsu ba tare da sanin HAJIYA MURJA ko HAJIYA LAURA ba,dan ko kowacce akwai masu kula da al'amuranta duk zirga² da suke a idon hukuma suke aiwatar da hakan...
Shirun da BB yaji kwana biyu babu labari ne yasa shi kiran D.P.O yana neman k'arin bayani game da case en b'atan KHUBRA....
Cikin yanayin sarewa ya shiga kiran line en D.P.O,wanda cikin nasara ya d'auka ba tare da b'ata lokaci ba...
"Hello!yallab'ai barka da rana,ya aiki?"
Daga gefen D.P.O aka amsa masa
"Lafiya,Alhamdulillah!"
"Yallab'ai dama kira nayi na maka tuni naji kwana biyu shiru babu wani k'arin haske kan b'atan yarinyar nan"
Daga gefen D.P.O aka amsa da
"Ehhh!toh gaskiya nima dai abunda ya jima yana bani mamaki game da wannan case en shi ne,tun bayan da ka kawo photo da muka buk'ata aka watsa shi a kafafen sadarwa amma shiru har yanzun babu wani bayani da muka samu daga gurin al'umma,munyi nema munyi cigiya amma shiru har yanzun babu wani ci gaba,ina ganin dai kam sai mun k'ara hak'uri,mun kuma k'arawa abun lokaci muga yadda Allah zai yi ikonsa..
Amma har yanzun muna kan bincike da izinin Allah zamu sameta".....
Dogon ajiyar zuciya BB ya sauke kafin cikin kasala ya furta
"Allah ya bayyana ta"
D.P.O ya amsa da "Ameen"
Sannan ya d'ora da fad'in
"Ina fatan dai yaran da muka turo suna kan aiki,babu wata matsala da ake fuskanta"
"Ehhh!Yallab'ai babu wata matsala,aikinsu yana tafiya yadda ya kamata babu wata matsala"
"Ok! Babu matsala Allah ya bayyanata,amma a k'ara hak'uri"
"In sha Allah yallab'ai,na gode sosai"
Sukayi sallama,bayan BB ya ajiye phone en ya jima yana nazari kan wannan case en,shi kad'ai kuma ya mik'e ya zari car keys ensa ya fice...
《《》》
Tsaye take cikin super market en *JIFATU STORE* dai² b'arin y'an rugs tana dubawa...
Wayanta ne yayi k'ara a hankali ta bud'e jakarta ta fito da ita..
Rashin gaskiya ne yasa ta juyawa tana kallon yanayin gurin,babu kowa a arean da take shi yasa ta d'auki kiran ganin sunan dake lilo kan wayan...
"Hello HAJIYA MURJA kiyi hak'uri bana gida ne,shi yasa ban d'auki kirankiba,amma ki bari na k'arasa gida,yanzun ina *JIFATU* naje siyayya"
Daga gefen da aka kira cikin fad'a² ake magana wanda har wayan me magana ta farko tana amsawa k'asa²,ta yadda idan akwai wani a kusa zai iya jiyo abunda ake fad'a...
"Haba HAJIYA LAURA tun yaushe nake kiranki kink'i amsawa,idan abun nan ba mai yiwuwa bane yaci ace kin sanar dani,amma kin barni kara zube...
Waima dan Allah wasu sha³n kika sa suka yi aikin nan?"
"Haba HAJIYA MURJA nafa fad'a miki bana gida,kiyi hak'uri zan kiraki idan naje gida"
"Kinga HAJIYA LAURA dakata bana son jin wannan maganar daga bakinki kawai idan zaki tsaya muyi magana to idan kuma ba hakaba,wallahi zan zare hannuna a ciki duk lokacin da wannan lamarin ya kwab'e kada kiyi kuka da ni,kiyi kuka da kanki...
Kina da damar aikata duk abunda kika so,zab'i ya rage ga mai shiga rijiya....
Ko ki bani had'in kai muyi magana yanzun ko kuma ki kashe,duk lokacin da kikaga dama kya neme ni"....
Tana kaiwa nan tayi shiru tana sauraren jin me HAJIYA LAURA zata ce...
A gefen HAJIYA LAURA kuwa jin furucin na k'awar tata ya so ya bata tsoro amma ta dake tare da cizon leb'enta na k'asa,sai da tayi gefe da wayan sannan ta saki k'wafa....
"Babu damuwa muyi maganar yanzun"
Murmushin mugunta HAJIYA MURJA tayi sannan ta fara magana
"Ai ke nake sauraro naji baki cemin komai game da tambayan da nayi miki ba "
"Wane tambaya kenan?"
"Ce miki nayi wane sha³i ne suka yi wannan aikin?ina nufin wane gidadawa kika sa suka zo gidana ranan da aka sace yarinyar nan?"
Maganar HAJIYA MURJA ba k'aramin b'atawa HAJIYA LAURA rai tayi ba,haka ta danne tana bata amsa..
"Wasu yara ne da sukemin aiki,wani abu ya faru ne?"
"A'a kawai dai ina son sanar dake ne duk inda suke idan har suna cikin garin KANO to suyi gaggawar barinsa domin kuwa yaron nan ya tsananta bincike...
Sannan abu na gaba idan har sukayi abunda ya janyo aka kamasu to ki tabbatar musu da kada su sake suna na ya fito a cikin bakunansu...
Kuskuren dake cikin ambaton suna na dai² yake da rasa rai,na fad'a miki saboda haka ya rage naki,ko ki jaa musu kunne ko ki k'yalesu su aikata hakan"
Cikin sanyin jiki HAJIYA LAURA ta amsa,amma cikin zuciyarta cike take da tarin k'unci...
"Sannan abu na gaba ina so ki kula da duk wani al'amura naki,idanuna suna kanki,kuskure d'aya kikayi zaki ki hannun hukuma"....
Ita dai HAJIYA LAURA bata iya cewa komaiba,baya ga zuciyanta dake tafasa,wanda idan ka kalleta zaka iya gane tsananin b'acin rai da take ciki a kan fuskanya.....
Bayan sunyi sallama ne HAJIYA LAURA ta fara magana cikin b'acin rai ta furta
"Lallai HAJIYA MURJA wato ni take son mai dawa bagidajiya,to wallahi sai na koya miki hankali,zaki san dani kike zanc en"....
Cikin b'acin rai ta fice daga gurin ba tare da ta siya abunda ya kawota ba,ta kama hanyan komawa gida....
Zuciyarta tayi k'unci da maganganun da AMINIYAR tata ta gama yab'a mata,ita kad'ai take k'wafa idan ta tuna abun duniya duk ya isheta......
《《》》
"Hello!sir"
Aka ambata daga b'angaren mai kiran,wanda yake magana k'asa²,da alama kuma akwai wani babban al'amari a tare da shi da yake son sanarwa...
Bayan an amsa masa ya shiga koro jawabi...
"Yallab'ai akwai wata mata daga cikin assignment da aka bamu, yau nabi bayan matar zuwa *JIFATU STORE* dake kan hanyar *OBASANJO ROAD*...
Tabbas yallab'ai akwai wani al'amari a tare da matar,kuma daga dukkan alamu matar bata da gaskiya duba da yanayin yadda take magana a waya,da kuma yanayin data fito daga *STORE* en..."
"Cikin wane irin yanayi kaga ta fito?"
"Yallab'ai yanayin da ta fito yana nuna tana cikin tashin hankali"
"Shin akwai wani abu da ya faru? ina nufin wani abu ya faru da ita bayan shigarta gurin siyayyar?"
"Ehhh!yallab'ai bayan shigarta da kamar minti uku (3) naga ta d'auko waya a cikin jakarta ta hannu,to yallab'ai bayan ta amsa kiran wayan ne naga hankalinta ya tashi ta fito"...
"Lokacin da take wayan kana ina kai en?"
"Yallab'ai ina cikin gurin da ta shiga"
"Ok!ina fatan babu wanda ya kula da binta da kake"
Cike da ladabi Sergeant en ya furta
"A'a yallab'ai babu wanda ya gani"
"Da kyau aikinka yana kyau,abunda nake so da kai kaci gaba da bibiyarta,har mu tabbatar da gaskiyan abunda muke hasashe.
Allah ya taimaka"...
Daga haka sukayi hanging wayan...
Tunani BB ya tsaya bayan ya gama answering call en daga sergeant en,akan hanyarsa ta zuwa gidansu KHALEEL...
Da kyar ya katse abunda yake yama motan key zuwa gida,dan ji yayi bazai iya zuwa ba,hakan ne yasa shi canja shawara ya koma inda ya fito....
《《》》
Kwanaki sun ci gaba da giftawa kamar ana ingizasu....
Ta b'angaren binciken neman da akewa KHUBRA abu ya faskara dan ko zuwa wannan lokaci har an gama fidda rai,anyi cigiyan anyi neman amma shiru kake ji uwa an shuka dusa,wannan dalilin yasa BB yanke shawaran sawa a tsananta yin rok'on Allah game da matsalar duk da kuwa dama anayi amma yana da burin na wannan lokacin yafi na baya...
Haka kuwa akayi ko da ya tuntub'i KHALEEL bai yi k'asa a guiwaba ya amsa masa da fad'in
"Tabbas wannan ma shawara ce ya kamata muyi hakan,Allah dai ya bayyanata idan muna da rabon sake ganinta"
Suka amsa da amin cike da jimami....
《《》》
Zaune take cikin parlor ta hard'e k'afafunta d'aya akan d'aya,ta cije leb'e ta gama cika tamkar zata fashe...
Iska ta furzar mai d'umi tare da fizgo wayarta tana latsawa cikin fusata take magana..
"Haba BIGGY sau nawa zan sanar maka da ina nemanka,ko kuwa so kake sai raina ya gama yin duhu kafin ka zo?"
'Dan dakatawa tayi tana sauraren me zai fad'a
"To amma me yasa baka sanarmin da bakwa garin nanba ka b'oye??"
"Tuba nake ranki ya dad'e amin aikin gafara"
"Shi kenan amma magana nake son yi da kai mai matuk'ar muhimmanci,wanda bana son kowa ya sani,bayan ni da kai sai kuma yaranka,ka dai fuskanci me nake nufi ko?"
"Ehhh!HAJIYA amma idan babu damuwa kiyi maganarki yanzun kawai saboda bana son zuwa gidanki saboda tsaro...
Idan kuma wani aiki nema kiyi min bayanin yadda kike so ya kasance,za ayi miki duk abunda kike buk'ata"...
Jin furucin BIGGY ne yasa ta sakin murmushin mugunta kafin ta fara magana
"Toh! shi kenan,amma da san samu ne da ka zo gida ka same ni idan ya so sai muyi maganar,amma tunda ka sanarmin uzurinka na karb'a hakanma babu damuwa"....
Sai da tayi shiru na wasu y'an lokuta sannan ta soma magana
"Ka san me nake so da kai BIGGY?"
Daga gefensa ya amsa mata da fad'in
"A'a HAJJAJU"
"Ina son duk inda kuke ku je gidan dana saku aiki kwanakin baya,akwai wata yarinya da nake son ku satomin,amma idan kun sace ta kuyi nesa da ita bana son kuma a samu matsala kan wannan aiki,ina son kafin ku satota kuyi bincike sannan kuma ku tabbatar da babu wanda ya ganku...
Zan turo maka da photon yarinyar da zaku sato sannan ku tabbatar idan kun saceta kun sanar da ni a lokacin bayan kun d'aukota...
Ina fatan ka fuskance ni ko?ni kuma zanyi maka bayanin abunda zakuyi bayan nan,da fatan baka manta kwatancen gidanba"...
Dariya BIGGY yayi mai isarsa kafin yayi magana
"Amma HAJIYA ba dai yarinyar da muka sace ce ta dawo ba ko?"
"A'a wannan daban da waccan,wannan da nake son ku sato ina son 'DAUKAR FANSA ne akan mahaifiyarta,saboda ta nunamin ban iyaba shi yasa nake son ajiye mata DARASIN RAYUWA"....
"An gama ranki ya dad'e kamar anyi an gama wannan aikin,za muyi duk yadda kikace"
Sai da suka gama kitsa duk wata mugunta sannan sukayi sallama...
Zuciyar HAJIYA LAURA fal da farin cikin wannan al'amari tana zaune tana kad'a k'afa sai sakin murmushin mugunta take.......
_AYI DAI MU GANI...._
《《》》
*3 MONTH LEAP.*
KHUBRA ce rik'e da kuran ruwanta na sana'ar *GARUWA* k'afarta sanye cikin takalmin *FILLO SHOES* daga saman kanta ko ta kifa *HAT* na gargajiya,takalmin duk ya sha d'inki saboda gajiya da yayi..
Wani yaro ne ya gifo a guje daga wani k'aramin gida yana fad'in
*"Y'AR GARUWA* ki kawo ruwa gidanmu za a siya"
A hanhali taja hulan dake kanta baya kad'an tana kallonsa,fuskanta da d'an fara'a duk da yadda tayi duhu fatarta duk tayi wani iri abun tausayi...
"To amma zo nan"
Ta umarci yaron da yake shirin komawa a guje,jin ta kira shi ne ya matso..
Kunnensa ta d'an kama a hankali tana fad'in
"Suna nane baka saniba ka kirani da *"Y'AR GARUWA"* ko kuwa iskanci ne yasa kayi hakan?"
"A'a na sani"
Ya fad'a yana dafe gefen fuskarsa ta side en da ta rik'e kunnensa....
"Daga yau naji ka sake fad'in wannan sunan sai na mareka,kaji ni ko?"
Da sauri yaron ya gyad'a kansa alamar yaji kuma ya bi...
"Yawwa k'anina,maza to ungo wannan"
Ta sa hannunta cikin jakar dake d'aure jikin west enta ta fiddo da sweet....
Da murnansa ko ya karb'a yana tsalle,yana fad'in
"Daga yau idan ban sake fad'a ba zaki dinga bani alawa?"
"K'warai kuwa zan dunga baka"
"YEEEE!ya" fad'a yana tsalle "Idan zaki dinga bani har YAYA zan dunga ce miki kinji ADDA KHUBRA"
Murmushi KHUBRA tayi tana shafa kansa cikin so da kulawa..
"Maza to jeka gida gani nan zan kawo muku ruwan kaji?"
A guje ya juya ya shige gidan cike da murna...
Tana kallon shigewarsa ta d'an tsaya tana murmushi ita kad'ai tasan halin da ta shiga lokacin da taji yaron ya kirata da ADDANSA,wani siraran hawaye ne yayi layi akan fuskanta,da kyar ta tsaida hawayen nata tana mai goge su.......
~Ni da nake gefe cike da tausayin halin da take ciki "nace KHUBRA har yanzun kina nan da halinki na son kuka"...~
~My HULBATEEY kuwa hawaye naga tana sharewa kan tsananin tausayin yadda taga KHUBRA ta koma....
*~
*D* a kyar ta iya saita nutsuwarta ta kama hanyan shiga gidan da yaron ya fito d'azun,hannunta d'auke da robber 25 litters...
Da sallama ta shiga gidan,bayan sun gaisa da matar gidan ta shiga juye ruwan da ta kawo cikin mazubin da aka nuna mata,bata kai da gama abunda ya kaita ba,ta jiyo yaron nan yana fad'in
"Inna kinga alawana da ADDA KHUBRA ta bani d'azu"
Y'ar yank'wananniyar matar da aka kira da inna ta kalli yaron tana d'an murmushi
"Aaaaaa!aikuwa angode,Allah ya saka da alkhairi.....
Ina fatan dai kace ka gode ko?"
"Laaaa!inna na manta ban fad'aba"
Yaron ya fad'a yana rufe bakinsa da hannu..
Ran inna ne ya b'aci jin furucin yaron dake gabanta,cikin fushi² ta janyo rigarsa
"Sau naw nake fad'a muku duk wanda zai muku kyauta ku dinga cewa an gode,ko ban fad'a muku ba?"
"Dan Allah inna kiyi hak'uri wallahi mantawa nayi"
Kamar zaiyi kuka yake maganar
"Aii ba dainawa za kuyi ba,ina jin saina fara k'wacewa zaku shiga hankalinku,tunda bakwajin magana"
"Wollahi inna bazan k'araba"
"Maza wuce kace mata ka gode,kafin na sab'a maka"
Da gudu yaron ya matso kusa da KHUBRA dake shirin fita yana fad'in
"An gode ADDA KHUBRA"
Batayi magana ba sai murmushi da tayi kad'ai ta d'aga masa hannu,daga haka tayi waje tana sha'awar halayyan matar na ganin yadda tayi tarbiyyan yaranta.....
《《》》
Tun daga wannan lokacin da BIGGY suka yi magana da HAJIYA LAURA suke observation a unguwan na RIJIYAR ZAKI dai² area'n gidan na HAJIYA MURJA...
Sai dai da yake suna da wasu ayyukan na daban a kuma gurare da dama yasa har aka d'auki lokaci mai tsayi ba tare da sun gudanar da aikin da aka sasu ba....
Kamar wani mahaukacin gaske haka yake acting ta yadda kowa ya ganshi ba zai iya ganewa ba cewa mahaukaci ne na gaske ko kuwa na bogi ne?....
Haka yake zagaye line en tun asuba daya shigo cikin unguwan yanata buge² da son korar flies dake neman hawan masa fuska,a k'ok'arinsa na tabbatar da cewa shi mahaukaci ne,kayan jikinsa duk sun yage bayaga wata annakiyar daud'a da duk tabi jikin kayan ta lafe kai ka rantse dama a jikin kayan aka halicceta....
《《》》
Tun bayan wattani uku da suka wuce ne kuma al'amura suka tsaya cak,zuwa wannan lokaci gaba d'aya binciken da ake dangane da b'atan KHUBRA abun ya faskara a kamo bakin zaren,wannan dalilin ne yasa aka fawalla komai duk wasu lamura an mik'asu ga Allah...
Ta inda BB yaq sallami Sergeant da suke masa aiki ta inda suka koma ma'aikata suka ci gaba dqa aikinsu kamar yadda dama suke yi....
A dai² wannan lokacin ne kuma MAMA taso b'allowa BB ruwa akan lallai itafa tana son yayi aure duk dan ta mantar da shi maganar KHUBRA....
Jin maganar ta MAMA yasa shi neman mafita babu shiri dan kam tabbas tunda wannan al'amarin ya faru baya jin akwai wata y'a mace da ta isa ya kalleta bare har ya furta mata kalmar soyayya....
Cikin kwanaki k'alilan ya gama shirinsa cikin sirri babu wanda ya sanarwa zai yi tafiya...
Washe gari da safe ya shigo cikin sauri,a parlor suka had'u da ZUHRA tana fitowa daga kitchen...
"Yawwa CWEETY ansa wannan"
Ya mik'a mata leda en dake hannunsa
"Maza ki adana shi naki ne kinji ko?"
"Toh BB nah na gode Allah ya k'ara arzik'i"
'Dan murmushi yayi daga nan ya bar gurin yayi hanyan bedroom,abunda yasan yana da muhimmanci na daga documents ensa da visa en da yayi na barin k'asan ya d'iba ya gama sasu a envelop yana gama had'a kayan ya maida car keys ensa cikin drawer daga haka ya fito yana kulle d'akin....
Bedroom enta ta shiga da yake sauri take ta shirya time en tafiyansu school ya k'arato ne yasa ko bud'e ledan bata tsaya yiba ta sa cikin closet enta ta rufe....
MAMA na zaune cikin parlor su ASHNA suka fito cikin shiri zasu tafi school,lokacin suna mata sallama,daga haka suka fice cikin sauri dan time en suna gaf da makara...
Duk da ba flight en safe zaibi ba,yana son fita ya je gurin KHALEEL daga nan yake son wucewa,a tunanin BB yin hakan kad'ai shi ne mafita a tare da shi...
Da sauri shima ya fita lokacin har sun kaiga mota da driver zai kaisu,sai dai me suna zuwa driver'n yake shaida musu motan yayi faci kuma yanzun masu faci basu fitoba...
Yana gama maganan su ASHNA suka fice ita da ZUHRA,FATAHIYYA da KHALEEFA....
Ganin sauri suke ne yasa ZUHRA maida HANEEF ya sanar da MAMA abunda ke faruwa,komawa cikin gidan yayi da gudunsa ya fad'awa MAMA matsalan da aka samu,kamar yadda ZUHRA ta fad'a masa..
"Toh ai kuwa idan haka ne sai dai kuyi saurin tafiya ku samu NAPEP dan kada ku k'ara makara"...
Tun bayan fitowansu daga cikin haraban gidan ASHNA ke ta faman doka tsaki saboda tsaiwan da take...
Da gudun dai ya sake fitowa yana d'an haki ya mik'awa ZUHRA kud'in hannunsa..
"YAYA ZUHRA gashi inji MAMA ta ce mu nemi NAPEP wai ya kaimu kada mu k'ara makara"
"Toh!" tace ta kama hannunsa sukayi gaba,inda ASHNA da sauran suka mara musu baya,sai tsaki take takaici duk ya isheta...
《《》》
HAJIYA LAURA zaune cikin parlor ta hakimce kamar kowane lokaci k'afarta d'aya a saman d'aya tana girgizasu da gani zuciyarta fara tas take jinta duba da yanayin da dake shimfid'e saman fuskanta...
Wayanta dake ajiye gefe tayi k'ara,sai da ta lek'a fuskan wayar kafin ta d'auka da sauri ta kara a kunnenta tana magana lokacin ne kuma mood en fuskarta ya sauya kad'an
"Haba BIGGY me yasa kayi disappointing ena?
Kai da nake tsammanin zuwa wannan lokacin komai ya kammala game da aikin da nasa ku amma shiru mak'atau...
Me kuke jira ne kam har yanzun baku aiwatar da aikinba?"
Daga b'angaren BIGGY ya amsa
"HAJIYA ki k'ara hak'uri muna kan aiki ne har yanzun,matsalan kuma da aka samu yaran ba wani fitowa suke ba to jinkirin da aka samu kenan..
Amma har yanzu yarana suna kan aiki,a kowane irin lokaci za a iya aiwatar da aikin"
"To shi kenan ina jiran kiranka dai kada ka manta"
"Sai kin jini HAJAJJU"
Ajiye wayan yayi ya d'an waiwaya gefe kamar mai neman wani abu...
'Dayan wayan da ke ajiye yayi k'ara da sauri ya fizgota ya d'auka
"Hello!kai yaa?"
Daga gefen da aka kira aka ambaci
"Ogaa!yaufa dawa tayi nama yaran nan gasu nan sun fito amma ba tare da driver ba"
"Kace me!?"
"Oga ba wasa da gaske su na gani yallab'ai"
Da k'arfi BIGGY ya fara magana
"Ok!maza kabi bayansu kaji wane hanya zasu bi,mu kuma gamu nan zuwa yanzun"
Yana gama maganar ya kashe da gudu² ya fice daga gidan yana mai k'walawa ragowar yaransan kira..
A gurguje suka fito suna tambayansa
"Ogaa!lafiya kuwa?"
Key ya cillawa mai jan motan yana fad'in
"Maza kuyi sauri muje kada damar yau ta wucemu,yaran aka gani sun fito....
Yi sauri ka tada mota mujeee"
Cikin k'araji yake maganar wanda kafin su farga shi har ya isa bakin motar...
Tsawa yake dad'a doka musu,a guje suka shiga rububin shiga shi kuma mai jan motan ya tada motan suka fice a 360,sai unguwan LION'S WELL.......
《《》》
BABA ZUWAIRA zaune tsakar gida tana harhad'a kayan da zata fita gurin sana'arta...
Tsaf ta kammala shirinta,tana shirin fita daga gidan ta hau rafkawa KHUBRA kira da ta shige toilet har yanzun bata fitoba...
"Wai kam KHUBRA me kike yi ne har yanzu kink'i fitowa ki tafi"
"Gani nan fitowa BABA yanzu zan fito"
"Kin dai san sai kin dangana da rafi amma kin kama kinyi zamanki a band'akin,ko so kike rana tayi miki kam ai ya kamata ki fito haka ki kama hanya"...
Cikin sauri ta fito,ta ajiye bokitin hannunta a gefe tayi cikin d'aki...
Kallonta BABA ZUWAIRA tayi tana girgiza kai
"Allah ya kyauta....
To ni dai nayi gaba idan kin gama ga abincinki nan a rufe,sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya ya kuma bada sa'a"....
Tana daga d'aki ta amsa mata,ita kuma ta d'auki hijab enta ta fice daga gidan....
Cikin sauri itama KHUBRA ta gama shirinta ta fito daga gidan tare da kulle k'ofar da padlock k'arami...
Duk inda ta bi a hanyan garin kaga tana gaisawa da mutane kamar dama a garin ta tashi,wattani kusan biyar da zuwanta kenan amma babu wanda bai san sunanta ba,manya da yara dake cikin garin badan komai tayi wannan suna ba ko sai kan sana'arta ta *GARUWA* da ta rik'e da gaske babu wasa.....
《《》》
Gudun da motar keyi ne yayi yawa duk da haka basu sauraraba sai over taking wasu motocin suke inda suka saka ganye gaba da bayan motan,jami'an tsaron dake kan titunan duk sunyi tunanin gawane suka d'auko a motan,wannan dalilin yasa basu tsayar dasu har suka kusa *KABUGA UNDER PASS*....
《《》》
Tun bayan fitowansa daga gida da yake ya riga su ZUHRA fitowa shima a k'afa ya fito zuwa titi kuma da yake tafiyan na namiji ne duk da BB baya irin tafiyan nan da sauri² hakan bai hana masa isa main road en da wuriba...
Napep ya samu tare da masa kwatancen inda ya nufa,cikin sauri suka bar unguwan....
Unguwan shiru babu hayaniya,a bakin get ya tsaya,ya shiga laluben phone cikin pocket ensa line en KHALEEL ya kira,wayan ya jima yana ring ba tare da anyi answering call enba..
Kusan kira biyar ba a d'aukaba,har yayi niyyan juyawa ya kuma fasa,ya sake gwada kiran line en...
Cikin alamu na mai bacci KHALEEL ya d'auka phone en had'e da sakin hamma yana fad'in
"MAN yane? bacci nake yi ban san kana kiraba"
"Toh ai sai ka fito gani a bakin get"
Mikewa yayi ya zauna a saman bed en yana murza eyes ensa tare da tambayansa
"Kamar yaya kana bakin get gidan bak'onka ya zama yau da bazaka shigoba kayi parking a waje?"
"Noo! ba da mota nazoba,kawai ka fito kaga MALAM ina jiranka"
Yana gama magana ya katse ba tare da ya jira jin me KHALEEL zai fad'a ba....
KHALEEL dake shirin magana yaji BB ya katse line en,hakan ne yasa shi sakin tsaki,cikin takaicin rashin jiran jin me zai fad'a ya sauka a bed en tare da d'aukan jallabiyan dake saman bed side drower yayi waje,yana tafe yake saka rigan....
K'aramar k'ofan dake jikin babban get en gidan ya bud'e tare da lek'awa ya kalli gabas da yamma,ganin BB tsaye jikin wall en gidan ya fito gaba d'ayansa...
Hannu ya mik'awa BB yana d'an murmushi,shi kuma BB ya gimtse fuska saboda ya tsani jira,hakan ne yasa KHALEEL jan hannunsa sukayi cikin gidan....
Cikin bedroom en KHALEEL suka shiga nan suka zauna kan sofa en dake cikin d'akin....
Dafe pore head ensa yayi wanda hakan ya janyo hankalin KHALEEL ya dafa shi yana fad'in
"MAN lafiya kake kuwa?"
Sai da yayi tsaki tukun sannan ya shiga labarta masa abunda yake faruwa,da kuma hukuncin da yake shirin yankewa...
Shiru KHALEEL yayi yana nazarin me ya kamata ya fad'a wanda aminin nasa bazai ma hakan wata mummunar fussara ta daban ba........
《《》》
Tafiya suke har suka fito babban titin unguwan,suna tsaye suna sauraren napep da zai kaisu school en amma duk wanda suka tsayar sai yace ba can zaiba,suna tsaye wani mai napep ya yanko dai² inda suke ya tsaya...
"MALAM nan zaka kaimu MUSA ILIYASU COLLAGE"
"To ku hau muje"
Black jeap ce ta yanko a guje ta biyo one way dai² zasu shiga aka zuge murfin motan ta baya aka fizgeta,ba tare da motan ta tsayaba ta sake harbawa tayi gaba...
Ihunta shi ya dakatar da sauran da suke shirin shiga cikin napep en...
Mai napep da ganin haka ya fizgi machine ensa bai tsayaba shima gudun kada a kira shi shaida ya arce a 180..............
*~
*F*ATAHIYYA da sauran yaran dake tsaye ne suka fasa ihuu dan sunfi kusa da ASHNA,ZUHRA dake kusa da napep tana shirin shiga taga ya fizgi machine ensa ya k'ara gaba,da sauri ta dawo da baya har tana shirin fad'uwa....
Juyawa tayi da niyyar yin magana ihunsu duk ya rud'ata ta kasa magana sai raba ido da ta shiga yi tana neman ASHNA dake tsaye baya....
Tunda motar ta cilla kan kwalta bata sauraraba danko ko lokacin da ZUHRA ta waiwayo bataga motarba sai k'ura da ta bari a gurin.....
"Wayyo Allah sun sace YAYA ASHNA,shi kenan mun shiga uku"
Abunda ke fitowa daga bakinsu kenan cikin k'araji da gunjin kuka...
Jiki a sanyaye suka d'auki hanyan komawa gida dan sanar da MAMA halin da ake ciki.....
Suna tafiya suna kuka,ita kam ZUHRA da take bayansu ta sakosu a gaba sam ta kasa kukanma,tana tafiya tana fad'in
"Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un,allahumma ajirna fii musibatin wa-aklifna khairan minha"....
Abunda take ta maimaitawa kenan har suka shiga cikin gidan...
MAMA na zaune cikin parlor sai ganinsu tayi sun shigo sai ihu suke suna kuka...
Mik'ewa tayi cikin sauri bakinta har hard'ewa yake gurin tambayan ba'asin me yake faruwa...
Ganin babu wanda yayi magana cikinsu,ta shiga binsu d'aya bayan d'aya da ido,cikin k'araji MAMA ke fad'in
"Kaiiiiii!kuyimin shiru,ku sanar dani me yake faruwa"
Shiru babu wanda yayi magana cikinsu hakan ne yasa ta fasa k'ara tana dad'a fad'in
"Wayyoo!Allah kuyimin shiru nace.....
Ina ASHNATA?"
Ganin irin tashin hankalin da take ciki ne yasa ZUHRA matsawa jikin MAMA tana k'ok'arin rik'eta,cikin taushin murya ta fara magana a hankali kuma cikin nutsuwa
"MAMA ki zauna dan Allah zan fad'a miki abunda ya faru"
Figze hannunta MAMA tayi daga rik'on da ZUHRA tayi mata cikin surutun da bata sanma me take fad'aba ta shiga girgiza ZUHRA tana fad'in
"Maza sanar dani me ya sameta?me ya samu ASHNATA?"
"MAMA kiyi hak'uri ki zauna tukuna zan fad'a miki"
Kallonsu kawai MAMA take yi dan kam cikin wannan halin da take ciki tafi buk'atar su sanar da ita halin da ake ciki..
Jikinta babu ko mayafi ta nufi hanyar fita daga parlor cikin sauri tana sambatun
"Tunda bazaku fad'aba zanje na dubota da kaina".....
Da gudu ZUHRA ta mara mata baya inda sauranma suka rufa mata baya...
Iya k'arfinta ta bud'e murya tana fad'in "BABA kayi sauri ka rufe k'ofa kada MAMA ta fita"
Aiko cikin hanzari BABA dake zaune yana shirin kunna radio ya mik'e cikin sauri ya rufe k'ofan ko da ta k'araso gurin babu halin fita,juyawa tayi tana kallon ZUHRA da sauran YARANTA da suka iso suma a lokacin
"Kunk'i fad'amin abunda ya sameta ko?sannan kuma kun hana ni na fita nemanta,me kuke nufi kam??"
Duk maganar tana yine cikin hargowa....
"MAMA wasu sun sace YAYA ASHNA a mota"
FATAHIYYA ce tayi maganar,take ko MAMA ta dafe kanta dake barazanar fashewa,fuskarta ta shiga yamutsawa,bakinta kuma yana motsawa a hankali,ba tare da sautin da take furtawa ya fitoba ta sulale k'asa........
《《》》
"Kaga MAN bana son ka d'auki wannan matakin ina son kayi hak'uri ka koma gida,kayima MAMA bayanin da zata fahimta"
KHALEEL yayi maganar cikin alamu na mai rarrashi,hannunsa d'aya yana kan sholder en BB...
Ture hannunsa BB yayi daga jikinsa cikin fad'a² yake magana
"Ehhhh!dama mana dole kace haka tunda ba kai ne a matsayin da nake cikiba shi yasa kake tunanin zan koma gida ko??"
"A'a MAN sam maganata ba haka take ba,ina son dai ka tsaya ka fuskanci wani abu guda d'aya ne...
Sufa iya wajibinmu ne yi musu biyayya nasan kasan da haka,sai dai shaid'an yana neman yin nasara akanka,wanda nake son kayi gaggawar dawowa hanya...
Dan kam idan har ka bari shaid'an yayi nasaran sawa ka aikata abunda kake niyya to tabbas ka fad'a halaka...
Dan Allah BRO kayi tunanin maganata kafin ka yanke hukuncin da kake tunanin d'auka"....
Shiru KHALEEL yayi yana nazarin aminin nasa da yaga ya fad'a duniyar tunani,d'an tab'a shi yayi kad'an kafin yaci gaba da magana
"Tunani mai zurfi ba shida wani amfani,kayi k'ok'ari ka saita kanka,kada kayi saken da shaid'an zaiyi tasiri akanka"
"Haba MAN ta yaya MAMA zata wani d'aukomin maganar aure yanzun?bayan ni ban tab'a ce mata ina da wata yarinya da nake son auraba..
Duk wannan shirin na MAMA tana yi ne dan ta k'untatamin bayan RAYUWAR K'UNCI da ta dasa mana a baya wanda har yau babu wanda yasan takamaimai en gaskiyar al'amarin,amma a yau zan baka labarin GASKIYAR LAMARINMU ko dan ka fuskanci nufina......
Kamar mai nazarin wani abu ya d'an d'aga kansa sama kafin ya fara magana...
*"ASALIN LABARINMU"*
_"Shekaru ashirin da shida baya 26"_
"Iyayenmu sun kasance sunyi auren soyayya ne da juna kamar yadda labari da kuma yadda na taso na gani a shekarun baya kad'an,kamar yadda ka sani mahaifina sunansa *ALHAJI SAFWAN ABDALLAH* babban d'an kasuwa wanda aka sanshi kan kasuwancin man fetur a y'an shekaru da suka gabata wanda akewa lak'abi da *MAI DA AKWAI*...
Asalin Mahaifina d'an jihar JIGAWA ne cikin DUTSE,a lokacin da mahaifiyata take bani labari race min,"sunyi aurene irin na soyayya,kuma ita ta kasance d'aya daga cikin y'ay'an abokin kakana wato mahaifin ABBANA kenan,bayan sunyi aure da shekaru 3 Allah ya azurta su da samun d'a namiji wanda ba kowane wannan yaronba sai ni,sun raineni cikin so da kulawa duk da a lokacin mahaifina baiyi suna ba kamar yadda kowa ya sanshi daga baya...
Asalin sana'ar mahaifina ya gajeta ne tun iyaye da kakanni wato noma da kiwo,Allah ya sanyawa mahaifina nasibi ta yadda a gonar da kakana ya bashi yake noma bayan yayi aure,yana noma kayan amfani na masarufi,a duk lokacin da ABBANA yayi noma yana ajiye na amfanin gida sannan kuma yakan fitar da zakkah duk k'arshen shekara kamar yadda addini ya tanadar,ragowar kayan kuma yakan d'auka ya kaisu kasuwanni domin samun abunda zai b'atar....
Akan wannan d'abi'a tasa ne Allah ya had'ashi da aboki wanda ba kowa bane face ABBANKA,shi ya taimaki mahaifina har ya dawo cikin garin kanon dabo da zama ta hanyar bashi shawara akan ya dinga kai amfanin gonarsa da yake siyarwa kasuwannin garin kano saboda kasancewarta cibiyar kasuwanci...
Bayan mahaifina ya amince da shawaran da ABBANKA ya bashi ne,yaje neman sulhu da kakana alokacin kaka yak'i amincewa a kokarinsa na cewa duk cikin y'ay'an da Allah ya bashi babu wanda ya tab'a yin nisa da shi,amma ganin yadda mahaifina yake rok'onsa ne yasa ya amince tare da yi masa fatan alkhairi....
A lokacin mahaifina kan zo ya koma a duk lokacin da ya gama kasuwancinsa,sai dai bayan wani lokaci yaga zirga-zirgan yayi masa yawa,to alokacin ne kuma ya nemi shawaran KAKA akan yana son neman gida saboda yadda al'amuran kasuwancin nasa suka dad'a bunk'asa,ba a b'ata lokaci ba KAKA ya amince masa saboda yadda yaga Allah yana bud'a masa duk a dalilin kasuwancin da ya fara"...
"A gurguje nake son baka wannan *SARK'AK'IYAR LABARIN* fa.....
Bayan haihuwata da sukayi wanda ni asali an haifeni ne a garin DUTSE,JIGAWA STATE saboda haka dani suka dawo garin kano,tun daga ni basu sake samun haihuwa ba sai da na kai kimanin shekaru takwas da haihuwa inda a lokacin har na fara zuwa makaranta,sannan aka haifi k'anwata ASHNA inda itama tana da shekara d'aya a duniya MAMA ta sake haihuwan ZUHRA,bayan wannan lokacin ne Allah ya kawowa ABBANA bud'i bayan bin shawaran da Abbanka yazo masa da shi kan su had'a jari su fara harkar man fetur,cikin ikon Allah da nasara kuma Allah yasa musu nasibi cikin abunda sukayi niyya....
Bud'i ya dad'a zuwa musu wanda a lokacin ne kuma aka kuma samun k'aruwa a gidanmu na haihuwan FATAHIYYA,bayanta sai KHALEEFA wato mai sunan KAKA kenan ABDALLAH,bayansa sai HANEEF wanda aka sama sunan mahaifin MAMA kenan,daga Kansa ne kuma haihuwa ta tsaya"...
Kadafa kace ina yanke maka labarin ina yin hakane saboda nasan kasan hakan,sai dai ina son kaika k'arshen labari....
Tohh!a shekarun da suka gabata tun bayan haihuwan HANEEF ne kuma aka soma samun sab'ani tsakanin ABBA da MAMA tun lokacin da taji zancen yana k'ok'arin k'ara aurene ta tada hankalinta,idan baza ka mantaba a kwai wata k'awarta mai suna HAJIYA LAURA ko?"
Kai KHALEEL ya d'aga masa,ci gaba BB yayi da magana
"Wannan matar ita ce silar faruwar komai...
A lokacin MAMA ta sameta da maganar ABBA yana son k'ara aure,bayan da can baiyiba sai yanzu da yaga yayi arzik'i duk dan son ya wulak'an tata...
Nan ne itama HAJIYA LAURA ta shiga bata shawarwarin banza wanda MAMA ta biye mata sunata kitsa abunda za suyi,ana haka ne duk basu san da cewa ABBA ya dawo gidanba,kuma duk abunda suke tattaunawa yana saurarensu....
Jin maganar da suke hankalinsa yayi matuk'ar tashi wanda a k'arshe ya yanke shawaran samunta suyi magana ta fahimta....
Sai dai kash! a lokacin da ABBA ya samu MAMA kan maganar sai ta nuna masa itafa sam bata amince da maganar k'ara aureba,inda sukayi ta samun sab'ani wanda a k'arshe dai ABBA ganin ta dage yasa shi d'ebo duk wani kadara nasa ya zube mata ya kuma d'ora da fad'in "Ga abunda kikewa nan nasan dai duk auren da kike cewa bakya so nayi akan wannan abun kikewa ne ko?to gashi nan na baki,sai dai magana d'aya zan fad'a miki ki kulamin da yarana ki basu ilimi ta kowanne b'angare wannan kad'ai ya isheni,ni zan tafi bazaki sake ganinaba daga yau kin amince da wannan zab'in?
Bud'ar bakin MAMA kuwa tace "ehh taji ya tafi duk inda zashi,tunda tana ganin ai ya bar mata komai na dukiyar da ya mallaka....
Tun daga wannan ranar bata sake ganin ABBA ba ya kama hany ya tafi....
Idan baka manta ba ai ka tuna lokacin da akace ABBA yayi accident ko?"
Nanma kai KHALEEL ya sake d'agawa...
"Abunda ya faru a wannan lokacin duk shiri ne wanda MAMA da babbar aminiyarta HAJIYA LAURA suka shirya duk dan kada duniya ta zagesu akan abunda ya faru shi yasa suka b'atar da hankulan jama'a amma ABBA yaba raye,k'asar ya bari gaba d'aya"...
Shiru BB yayi yana dafe kansa,KHALEEL dake zaune ya hau fad'in
"Toh!amma ta yaya kai kasan wannan labarin?"
Sai da yayi wani murmushi mai ciwo tukun sannan yace
"A lokacin da akace ABBA ya rasu idan zaka tuna ai ba a kawo gawaba ko?
Toh bayan y'an zaman makoki sun watsene na samu MAMA kan maganar,akan lallai sai ta fad'amin abunda yake faruwa ita kuma tak'i bayan na takura matane kan zan sanar da hukuma idan har bata fad'aminba shi ne ta bani wannan labarin da kaji a yanzun"....
"Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un"
KHALEEL yake ta maimaitawa had'e da dafe kansa,ya rasa me ke masa dad'i.....
《《》》
Mik'ewa ZUHRA tayi a fusace daga kan MAMA da ta fad'i tana fidda hannu ta wankewa FATAHIYYA fuska da mari
"Ke wace irin sha³ ce da zaki fad'a mata wannan maganar bayan kina kallon yanayin da take ciki?"
Bata iya maganaba saboda tsananin b'acin rai da kuma haushin FATAHIYYA da take jin kamar ta rufe ta da mugun duka a guje kuma ZUHRA ta juya ta yanki hanyan cikin parlor,a wayan MAMA ta lalubo number BB..
Kira ta shiga danna masa amma sam yak'i d'aukan ko guda d'aya,ga phones en a gabansa,sai dai baya jin zai iya d'aukan kiran nata...
Ganin bashi da niyyan d'auka KHALEEL ya mik'a hannu tare da answering call en,yanayin muryanta ya tabbatar da ba lafiya k'alauba....
"Hello BB dan Allah ka dawo gida babu lafiya"
Duk maganar da ZUHRA ke yi bata fuskanci ko dawa take maganaba,sai da taji yayi magana
"Me ya faru?"
"Wayyoo Allah!dan Allah MALAM ina mai wayar?shi nake nema please"
Jin abunda ta fad'a yasa ya d'ago yana kallon BB tare da mik'a masa wayan..
Ko kallonsa BB baiba bare yasa ran zai amsa wayan,hakan da yayi ya tabbatar masa da ko kwana ne zasuyi a haka..
Hands free yasa wayan,cikin sheshshek'ar kuka ZUHRA ke fad'in...
"Hello!Hello!!
Dan Allah MALAM ka bawa mai wayar tun kafin mu rasata"...
Fizge wayan yayi a hannun KHALEEL cikin wani irin voice yake tambayanta
"CWEETY me ya faru kike kuka?"
Duk yanayin yadda yajita ya gama d'aga masa tunani..
"Hello BB dan Allah ka dawo gida MAMA ce ta fad'i kuma bata motsi"
"What!!!" ya fad'a yana mik'ewa...
Ko gama sauraren abunda zata fad'a baiba yayi hanyan fita,da gudu-gudu,shima KHALEEL cikin sauri ya mara masa baya...
Ko kafin ya fito har BB yayi waje,haka ne yasa shi saurin yiwa motan key ya fice daga gidan...
Fitowansa ya tarar har yayi nisa cikin tafiyan da bai saba irinta ba,sai dai da gani kasan yana cikin damuwa...
Tun kafin KHALEEL ya k'araso yake masa horn bai tsayaba,har ya k'araso kusa da shi,motan ya bud'e tare da masa magana
"MAN ka dakata hakanan da wannan tafiyan kazo mu wuce"
Juyawa yayi ya kalleshi cikin sakanni ya fad'a cikin motan,da mugun gudu suka bar unguwan sai gidan su BB.....
《《》》
Gudu suke shek'awa cikin mota, kamar wad'anda zasu tashi sama,duk da sun tserewa gurin da mutane zasu iya samunsu su cimmusu hakan baisa sun saurara ba...
Fizge² take yi cikin motan duk kan ganin ta kub'uta,sai kai hannunta take tana k'ok'arin jan handle en dake jikin k'ofan...
Mari BIGGY ya shek'a mata had'e da tsawa mai k'arfi wanda ta maidata cikin hayyacinta...
Kanta ta kifa bisa cinyoyinta ta shiga rera kuka,su ko na cikin motan suna saurarenta amma babu wanda yayi yunk'urin dakatar da ita,ratse hanyan suka dinga yi wanda k'arshe dai sai gasu a *NA'IBAWA FLYOVER* nan suka ci gaba da fella gudu babu sassauci....
Straight suka yanki hanyan *BAUCI STATE* ba tare da sun sauraraba..
Tun ASHNA na kallon hanya har ta b'ingire take bacci yayi gaba da ita ba tare da ta shirya masaba...
《《》》
Ko gama tsaiwa motan baiba ya fito dan baya jin zai iya tsayawa har BABA MAI GADI ya bud'e musu get..
K'ofan ya tura ya shiga,a nan yayi arba dasu duk sun lullub'e MAMAN ko isashshiyar iska bata samu,ba tare da ya kulasuba ya shiga maidasu gefe,yana yin arba da MAMA bai jira jin komaiba kuma ba tare da yayi shawara da kowaba ya shiga k'ok'arin d'aukanta...
KHALEEL da ya gama parking a gurin ya fito cikin sauri,kama masa MAMAN yayi suka sa a mota,ZUHRA tuni ta shige back seat kusa da kan MAMA suma suka shiga KHALEEL ya felli motan a 360....
*AKTH* suka wuce da ita direct babu jimawa aka shiga da ita EMERGENCY...
Sama da 2 hour's likitoci na kanta babu wani ci gaba da aka samu...
Zagaye gurin kad'ai BB yake hankalinsa duk ya gaza kwanciya,ZUHRA ko banda kuka babu abunda take,KHALEEL na kusa da ita sai hak'uri yake bata kan tayi shiru komai zai zama dai² amma abu ya faskara,saima k'aimi data k'arawa kukan nata...
Fitowan babban likitan yasa su mik'ewa,wanda bai tsayaba saima cewa da yayi su biyo shi office..
Binsa kawai suke har suka isa office en sai da ya tabbatar sun zauna tukun ya shiga magana
"Amm!kune wad'anda kuka kawo mara lafiyan ko?"
KHALEEL yayi k'arfin halin cewa
"Ehh!doctor"
"Ok toh amma yaya alak'arku take da ita?"
Nanma dai ya sake bashi amsa da
"Y'ay'anta ne"
Sai da DR en ya kallesu tukun,ya mik'a hannunta saman pore head yana share zufan da ya tsatstsafo masa da handkeey
"Am so sorry...
Gaskiya mara lafiyanku sai dai kuyi hak'uri...............
*~Wayyooo shi kenan MAMA ta auza,ta wula.......~*
*~#
*"S* ai dai kuyi hak'uri amma gaskiya mara lafiyan naku tana cikin mawuyacin hali wanda tun shigarmu har kawo lokacin dana fito bamu samu ta farfad'o daga dogon suman da tayiba...
Amma abunda ya d'auremun kai kuma abun damuwan shi ne akwai wani al'amari da ya faru wanda yayi matuk'ar tsoratar da ita da yayi sanadiyyar fad'awarta wannan hali,bayaga numfashinta da yake fita da sauri²...
Cikinku akwai wanda ya sanar da ita wani abune?ko kuwa kun san abunda faru da ita?"
A tare suka kad'a masa kai,alamar babu...
To gaskiya sai kun kiyaye ba ko wane irin lokaci ake sanar da mutum wani abu da ya faruba,matuk'ar tsoro ya bayyana a tare da shi ko a tashe shi daga bacci dan sanar da shi hakanba,dan kuwa yin hakan ka iya jawowa mutum matsalar k'wak'walwa,wanda ba a fatan hakan ya faru...
Sannan abu na gaba gaskiya muna buk'atar namiji babba,idan kuma kuna da wata da zata iya kula da ita to ya kamata ace kunzo da ita duba da har yanzun bata farfad'oba sai dai munyi nasaran saita numfashinta"....
Shiru sukayi dukansu suna nazarin al'amarin,a hankali BB ya d'ago kansa idanunsa sun soma sauya colour zuwa red,a kan ZUHRA ya saukesu,sam ya kasa magana sai kallonta kad'ai da yake yi,zuwa wannan lokacin damuwarsa ta dad'a ninkuwa fiye da kowane lokaci da ya wuce....
KHALEEL ne yayi k'arfin hali bayan dogon ajiyan zuciya daya sauke,sannan ya bud'e baki da k'yar ya fara magana,dan kam suna buk'atar k'arin bayani kafin du samu mafita kan nemo wanda zai zauna da MAMA
"ZUHRA me ya faru da MAMA ne kafin muzo gida?"
Sai da ta saita kanta ta kuma goge fuskarta da tayi kacha-kacha da hawaye sannan ta kallesu su duka ukun DR,BB da kuma KHALEEL en,wani sabon hawaye ne ya sake tahowa,suna shirin zuba ita kuma sai kokawa take yi da su gurin ganin ta hana hakan afkuwa...
"BB ASHNA"
Abunda ta iya fad'a kenan hawayenta suka k'arasa zubowa...
Wani uban tsaki BB yayi wanda yasa su kallonsa,tabbbas KHALEEL yasan mutumin nasa yana cikin matsananciyar damuwa...
Hannunsa ya d'ora kan sholder ensa yana d'an shafashi kad'an alaman rarrashi
"MAN take it easy,anything will be fine,ok?"
Bai kula shiba kamar yadda ko kallonsa baiba,saima k'ure ZUHRA da yayi da kallo wanda har yafi na farko,burinsa bai wuce tayi magana ba,amma ita ta kasa gane hakan dan ya gama damuwa yaji,k'arshe kuma sai kawai ta wani ambaci sunan ASHNA kuma tayi shiru,to shi ina ruwansa da wata ASHNA?yarinyar da sam ba ganin girmansa take ba,shi duk zaman gurinma ya isheshi saboda takaici,a fusace ya mik'e tare da hararan ZUHRA dai² lokacin ta d'ago idanunta suka sauka kansa yana cillo mata wata uwar harara.....
Shirin barin gurin da sukaga yana yine yasa su kallon-kallo,a hankali ta rik'o hannunsa tana kad'a masa kai....
Cike da fushi ya juyo
"Da Allah ni sakeni kin sa sai jiranki muke muji abunda ya faru kin tsaya jama mutane rai,ko an fad'a miki MAMA jiranki za tayi ki gama kukan kafin ta tashi??
To idan baki saniba daga nan zuwa kowane irin lokaci zata iya mutuwa"...
Da sauri ta d'ago ta kalleshi,dan tunda ya fara mata masifar ta sunkuyar da kanta,hawaye nabin fuskarta take fad'in
"Dan Allah YAYA kayi hak'uri zan fad'a"...
"Yi shiru ZUHRA ki sanar damu abunda ya faru kinga lokaci na dad'a k'urewa,kuma kinga DR mu yake jira yaji abunda yasa ta shiga wannan halin kafin musamo mafita....
Maza kinji fad'a mana me ya faru".....
Har lokacin BB na tsaye kamar wanda aka sama pause,ya kasa barin gurin kamar yadda ya kasa raba hannunsa dana ZUHRA...
Shi kuma DR yana zaune sai kallon ikon Allah yake tsakanin wad'annan mutane..
Abunda ya faru ta kwashe ta sanar da su tun daga shirin tafiyansu school har zuwa lokacin da MAMA ta yanke jiki ta fad'i....
"Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un"
Shi ne abunda ke fitowa daga bakunansu,ba iya su kad'aiba hatta da DR en shima abunda yake maimaitawa kenan...
Office en yayi tsiit babu wani sauti dake fita a cikinsa,sunyi shiru kowa da abunda yake tunani...
KHALEEL ne ya katse shirun bayan ajiyan heart da ya sauke tare da fad'in
"Dude gaskiya bai kamata muci gaba da zama a nanba,yanzun yaci ace mun sanar da hukuma b'atan yarinyar nan,tunda kaga wannan shi ne na biyu ya kamata ace mun dakatar da faruwar hakan".....
Ko kallo bai ishe shiba bare ya sa ran zai motsa daga inda yake,kallon mutanen gurin kad'ai yayi tare da ficewa cikin sauri kamar zai kifa...
A baya ZUHRA ta shiga binsa da gudu-gudu saboda yayi mata nisa sosai lokacin da ta fito.....
《《》》
Daf da zasu shiga garin BAUCHI ya d'auki waya yana pressing,number HAJIYA LAURA ya laluba tare da kara wayan a kunne...
Bata wani b'ata lokaci ba ta d'auka maganarta cikin isa da tak'ama
"Hello!BIGGY ya akayi kuma?ina d'azun muka gama magana?"
Yana dariya cikin wani irin voice had'e da shafa face en ASHNA dake tsakiyansu tana shek'a bacci yake fad'in
"HAJAJJU!Allah ya taimakeki, yau dai munyi nasara kan wannan yarinyar,dan yanzunma haka mun d'auki hanyar BAUCHI saura kad'an mu k'arasa"..
"Kaiii amma nayi farin cikin da na jima banyi irinsa ba...
Ammmm!yanzun ina zaku sauka kenan?"
Tayi tambayan tana jiran taji me zai ce da ita..
"HAJIYA ina ganin da mu kama hayan gida kawai kinga sai mu ajiyeta a nan har zuwa adadin kwanakin da za muyi"
"A'a BIGGY kada ku fara,taya zaku samu gidan haya a hannun mutanen garin da basu sanku ba,bayan wannanma idan aka ganku da yarinya me kuke so ayi tunani,kana dai sane da cewa mutane zasu sanar da hukuma muddin aka ganku da yarinyar nan.....
Abunda za kuyi kawai ku kama hotel a matsayinku na matafiya.....
"Gaskiya HAJIYA bana jin hakanma mafita ce,dan kuwa duk wanda ya ganmu da yarinyar nan tabbas zai gane satota mukayi dan kuwa yarinyar kayan makaranta ne a jikinta...
Ni ina ganin dai gaskiya ko dawowa za muyi KANO muna da gida kuma babu wanda zai san wani abu da yake faruwa"...
"To kai da kasan da haka har ka bari kuka bar garin ko ma?"
"HAJAJJU! wallahi na shiga wani shu'unin ne shi yasa na kasa tunawa,amma bari kawai mu dawo,tunda tahowarma ba wani amfani garetaba"
"Ehhh!toh amma BIGGY kana ganin dawowarku a wannan lokacin babu wata matsala da za a samu?"
"Babu hajiya,ina ganin tun kafin lokaci ya k'ure mana gara mu dawo kawai,ko ya kike gani?"
Cike da jin dad'i HAJIYA LAURA ke magana,tana sakin wani uban smiling
"A'a!tunda ka ce babu wata matsala dan kun dawoma babu wata damuwa kuyi hakan"....
Juyawa BIGGY yayi ya kalli ASHNA da ta zame ta jingina a jikinsa tana bacci,sai da ya lashe lips ensa garin tunani har baima san lokacin da HAJIYA LAURA tayi magana ba...
"Hello!hello!!
BIGGY kana jina kuwa?"
Yanayin yanda tayi maganar yasa shi dawowa daga duniyar da ya lula
"Ehhh!HAJIYA ina saurarenki"
"Yawwa to ina so ku kula da hanya,sannan kada ku kuskura kuyi saken da za a gane inda kuke...
Ina fatan dai ka fahimci abunda nake nufi ko?"
"Ehhh!HAJIYA za a kiyaye"
"Toh shi kenan sai na jiku,Allah ya kiyaye hanya"
Daga haka sukayi hanging kiran,kowa ya shiga duniyar tunani....
《《》》
Yau tun safe da ta tashi take jin jikinta na mata ciwo,wanda ta rasa dalilin faruwar hakan..
A haka ta lallab'a ta shirya,ko abinci bata ciba take shirin fita...
Kuran ta shiga kiciniya zata fita da ita BABA ZUWAIRA ta dakatar da ita
"Haba KHUBRA yanzu haka kika zab'i zama?"
Tsayawa tayi tare da juyowa tanama BABA ZUWAIRA kallon rashin fahimtar tambayanta,kafin ta bud'e baki tana shirin magana BABA ZUWAIRA ta rigata..
"Yanzu fisabilillahi ace ki tashi ba tare da kinci komaiba kuma ki hau shirin fita...
To waima idan kin tafi baki ci komaiba zaki iya aiwatar da abunda kika fita dominsa?"
Shiru tayi ta ci gaba da tsaiwa a gurin,sai dai wannan lokacin kanta na k'asa ta kasa magana...
Jikinta ne ya sake yin sanyj jin furucin BABA ZUWAIRA,inda nan take ta tafi tunanin rayuwarta ta baya..
"Lokacin da take neman abinci ido rufe ta sanya a cikinta,a lokacin da take daf da mutuwa,amma ta rasa mai taimaka mata,yau gashi a rayuwarta taci karo da inda ake mata fad'a idan zata fita ba tare da taci abinciba"...
Wasu siraran hawaye ta juya ta goge,sannan ta k'irk'iro murmushi lokackin da ta baro gurin da take
"Eyyah!BABA yau tun da na tashi ne bana jin dad'i shi yasa banyi tunanin cin komaiba"
Sai da BABA ZUWAIRA ta wurga mata harara kafin tayi magana
"Dama haka za kice,abu da ko zuba abincin kikayi ba wani cin na kirki kike ba,kina cin abinci kamar ana bawa kyanwa"
"Haba BABATA ina cifa da yawa"
Harara ta dad'a wurga mata
"Ke tafi can kya dai fad'awa wanda bai saniba,amma ba dai ni ba"
Dariya sosai KHUBRA tasa,ta jima tana dariyan wanda har tasa BABA ZUWAIRA tsayawa da abunda take tana kallon ikon Allah......
《《》》
"Dan Allah BB ka tsaya ka ji"...
ZUHRA ce mai yin wannan maganar lokacin da ta kusa taradda shi,k'in tsayawa yayi ita kuma ta ci gaba da bagging ensa kuma ba tare da ta saurara da binsaba...
Daga bayanta ta tsinkayo maganar KHALEEL
"K'yale shi kawai ZUHRA kada Allah yasa ya tsaya"
'Dan juyawa tayi kamar za tayi kuka
"Dan Allah YAH KHALEEL kace ya tsaya....please"
"K'yaleshi dan kansa zai dawo kinji"
Kanta ta d'aga alaman ta ji,sannan suka jera suna tafiya kowa da inda zuciyarsa ta karkata...
Dai² d'akin da aka kwantar da MAMA suka k'araso anan suka tarar da BB zaune ya dafe kansa da hannayensa duka biyu yayi shiru...
Tunaninsa bai wuce ta yaya zasu samo wanda zai kula da MAMA ba a zaman da za tayi a asibitin...
Yayi zurfi cikin tunani KHALEEL ya zauna kusa da shi yana kallosa,phone ya d'auko cikin contact nasa ya shiga bincike,nan ya lalubo number D.P.O,har ya gama magana da shi BB bai saniba...
Magana ya shiga yi masa amma sam bai san yana yiba har sai da ya girgiza shi,sannan ya kalle shi da rinannun idanuwansa da b'acin rai ya gama rine su
"MAN yanzufa ba lokacin tunani bane mafita ya kamata mu nema...
Waye ya kamata mu samu da zata zauna da MAMA?"
Shiru BB yayi ya kasa magana zuwa wani lokaci cike da jimami ya fara magana
"Irin abunda nayita fad'awa MAMA kenan lokacin da nake tambayarta danginmu...
Yanzun ga irinta nan,waye zai zauna da ita a wannan halin?duk dad'in k'awaye bai kai d'an uwaba,amma MAMA tayi watsi da danginta da dangin mahaifinmu"
Kallonsa kawai KHALEEL yake cike da rashin fahimta
"Kamar yayafa dude?"
Murmushi yayi mai ciwo kafin cikin jimami,takaici,haushi ya fara magana
"Tun bayan dawowarmu garin nan daga DUTSE dai² da rana d'aya MAMA bata tab'a komawa garin nanba,y'an uwanta da suke ganin tana cikin rufin asiri zata taimaka musu,k'arshe duk wanda yazo sai dai ya koma yana k'unar zuciya,saboda MAMA korarsu takeyi bayan ta ci musu mutunci"
"To amma duk da haka MAN ya kamata mu hanzarta nemo wanda zai zauna da itan"
Duk sunyi shiru sun kasa tsai da matsaya akan wanda zasu samu ya zauna da MAMA a wannan yanayin da take tsakanin *RAYUWA DA MUTUWA*.........
*~
*K* allon da taga BABA ZUWAIRA nayi mata ne yasa ta gimtse dariyar tata,tana d'an murmushi ta k'arasa kusa da ita ta zauna tana dafa k'afarta
"Allah kuwa BABATA ina cin abinci dayawama bakiga nayi kiba ba,kuma nayi k'arfi....
Kallifa kiga yadda nake iya d'aukan wad'annan robber en"
Kallonta kad'ai tayi ba tare da ta iya maganaba saboda yadda taga ta hak'ik'ance akan maganar ne yasa tayi murmushin yak'e wanda akance "yafi kuka ciwo"...
Kafin ta samu k'arfin guiwar yin magana
"Kayya dai KHUBRA wannan ba bigiren k'arfi bane,banda abunki ina kika tab'a ganin mace tayi irin wannan sana'ar?
Baya ga hakama su kansu mazan bakiga yadda suke wahalaba,kuma duk da haka ba kowa ne yake juran wahalar da wannan sana'a take da ba..
Ni kaina dan dai tun farko ina tsoron rasa ki,abu na biyu kuma tausayinki da rashin sanin hannun da zaki fad'a yasa ban musanta miki sana'ar nan da kika ce ita kike so...
Amma har ga Allah wannan sana'a bata kwantaminba"...
'Dan murmushi tayi ba tare da ta sake cewa komai akan abunda BABA ZUWAIRA ta fad'aba ta hau fad'in
"BABA bani abinci naci sai na tafi kinga dama ban shirya da wuriba,kada rana ta yimin a hanya"
Itama BABA ZUWAIRA ganin KHUBRA ta bagarar da maganar yasa tayi shiru bata sake cewa komai ba,saima abincin da ta mik'o mata...
Duk wani motsi da abunda take yi tana cin abincin,idanun BABA ZUWAIRA na kallonta...
Ita kad'ai tana cin abincin kamar bata so tana yi tana yatsina face enta kamar wacce akawa dole haka take cin abincin...
Da kyar take iya had'iyan abincin kamar mai shan magani....
Kai BABA ZUWAIRA ta gizgiza tana kallonta da tausayawa,yau kam ta rasa dalili da yasa y'artata take wannan abun
"Jikin ne yake damunki?"
Tayi tambayar tana dad'a k'ureta da ido..
'Dago idanunta tayi ta kalleta tana kad'a mata kai
"Wollahi BABA kwana biyu ina jin jikina babu dad'i,kuma na yau sai nake ji yafi na ko wane lokaci"
"Ayyaahh!sannu,amma toh me yasa kike son fita duk da bakya jin dad'i kam?
Ina ganin dai yau kam ki hak'ura da fita,idan Allah ya kaimu gobe sai ki je ko?"
Shiru tayi bata sake magana ba,har BABA ZUWAIRA ta gama shirinta,sai da tazo fita ta kalli KHUBRA
"To ni dai zan fita,kuma abunda na fad'a miki d'azu kiyi zamanki a gida gobe idan Allah ya kaimu kya fita,kin ji ko?"
"Toh BABA Allah ya kiyaye hanya,Allah ya bada sa'a"
"Ameen".....
Ta amsa mata....
Har ta juya zata fita daga gidan ta juyo tana fad'in
"Afffff!na manta kinga anjima kad'an zan aiko yaro ya kawo miki magani....
Me ma kikace yana damunki?dan na samu a sayomin a gurin d'an lafiya jari ennan"
"Wallahi gaba d'aya jikina ke min ciwo,cikin k'ashina kamar ana saramin da adda"....
"Ashsha!sannu y'ar nan Allah ya yaye miki kinji....
Ni na tafi sai na dawo"...
"To Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen..."
BABA ZUWAIRA ta fad'a tana mai ficewa daga gidan gaba d'aya.....
《《》》
Damuwar da yake ciki a yau ji yake kamar a kowane motsawar second k'ara masa ake yi...
Duniyar tayi masa d'umi wanda ya rasa inda ya kamata ya sa kansa dan yaji sanyi....
Hannu yasa ya dafe kansa ta kowane gefe,inda KHALEEL ke zaune kusa da shi shima yayi shiru kamar wad'anda akace musu MAMA ta wula.....
Shiru kowa da abunda ke damunsa,kome BB ya tuna yayi saurin mik'ewa
"MALAM bani key"
Wani kallo KHALEEL yayi masa na jeka na gaji da kai,kafin yayi masa magana
"Me zaka yi da key kuma? ko nace ina zaka?"
"Kaga kawai ka bani ina ruwanka da inda zani?"
"Niko nake da ruwa da inda zaka...
Kasan dai babu yadda za ayi na baka key yanzu koh?kana cikin wannan halin za kayi driven en ko me?"
Tsaki yayi daga haka kuma bai sake kula shiba yayi shiru,sai kansa da yake juyawa side zuwa side....
ZUHRA dake tsaye ta kallesu tana shirin magana sai dai tana jin tsoron abunda zata fad'a kada taja BB yayi mata fad'a irin na d'azu...
Har tayi shiru kuma ko me ta tuna ta sake kallonsu tana fad'in
"YAYA KHALEEL dan Allah ka maidani gida babu kowa sai su HANEEF kafin MAMA ta farfad'o sai na samu nayi girki,nasan yanzu haka suna can da yunwa"
Shiru babu wanda yayi magana,sai dai abunda ta fad'a yasa KHALEEL en kallon BB yaga ko zai yi magana...
Ko tari baiba bare su sanya ran zaiyi magana,hakan da yayi yasa KHALEEL mik'ewa yana yin gaba,itama ZUHRA ta mara masa baya...
Har sunyi nisa a tafiya,ya d'ago yana kallon gurin amma bai gansuba,hanya yabi da kallo can daga nesa ya hangosu,a hankali ya mik'e zuciyarsa duk babu dad'i...
So yake yaje gida dan akwai abunda yake damunsa,shi yasa yayi saurin barin gurin....
Har sun isa gurin da sukayi parking motan ya iso,babu wanda yayiwa magana cikinsu ya bude back seat ya zauna had'e da jingina kansa da jikin seat en....
Motan shiru babu wanda yake iya cewa wani komai har suka isa gida......
《《》》
Misalin k'arfe 9:00pm ASHNA ta farka,har lokacin gudu suke shek'awa kan titi basu sauraraba,kallon gefe da gefenta tayi ta kalli yadda duk suka wani kafeta da ido,uban tsaki tayi wanda yasa guy en dake gefenta ya kalleta cikin magana irinta k'auraye
"Kee!ya dai?kinawa mutane tsaki"
Bud'ar bakin ASHNA sai cewa tayi
"Dallah ina ruwanka dani ko kaji na kulaka da zaka wani yimin shishigi?kun kama kun wani sato to waima gidan wace uwar zaku kaini?? Banzaye b'arayin y'ay'an mutane kawai.."
Furucin da tayi ba k'aramin kaishi k'ololuwar b'acin rai tayiba,take ya d'aga hannu da niyyar kifa mata mari sai dai me,tun kafin hannusa ya sauka kan fuskarta ta matsa jikin BIGGY tana fasa k'ara...
Kallonta BIGGY yayi duk ta cukuikuyeshi idanunta a runtse,kamar wacce za a zarewa rai..
Dariya gaba d'aya yaran nasa suka sa dan gaba d'aya drama'n da akayi suna jinsu,banda BIGGY da ya sake d'aure fuska yana hararan yaran nasa..
"Da Allah kuyiwa mutane shiru"
Ko gama rufe bakinsa baiyiba suka shiga taitayinsu,kallon wanda ke kusa da ASHNA yayi
"Ka maida hankalinka jikinka tun kafin ranka ya b'aci...
Daga yau kada ka sake k'ok'oarin aikata abunda kayi niyya kaji dai na fad'a maka"....
"Sorry OGAA hakan bazai sake faruwa ba"
Juyawa yayi ya kalli ASHNA da take murgud'a ma yaron nasa baki ya sake juyawa yana kallon window....
Tafiya ta mik'a inda basu suka isa gidanba sai misalin 12:00am,babu wanda ya kulata duk suka fice suka nufi cikin gida...
Sai BIGGY dake bayanta,haka ya tusata a gaba har cikin gidan,a ransa yake raya "anya kuwa zai iya hak'uri da chik ennan?"...
Shi kad'ai yana biye da ita yana kallon yadda take tafiya duk motsawan da zatayi duk da ba wani jiki ne da itaba amma shi kam tafiya take da imaninsa...
Ji yake kamar tayi ta tafiya yana binta a baya a haka har zuwa tsayin wani lokaci....
《《》》
Bayan shigansu gidan suka tarar da babu kowa cikin parlor,kitchen ZUHRA ta wuce dan yin girkin da tace za tayi,nan ta bar su BB da KHALEEL...
Jin shigowansu yasa su HANEEF,KHALEEFA da kuma FATAHIYYA fitowa zuwa parlor a tunaninsu tare da MAMA suka dawo...
Sai dai fitowansu suka tarar da BB su biyu cikin parlor babu MAMA...
"YAYA ina MAMAN take?"
FATAHIYYA tayi tambayar tana yamutsa fuska alamun damuwa shimfid'e saman fuskarta...
Tsawan da ya buga mata yasa tayi baya cike da tsoron yadda taga ya mik'e yayo kanta...
Dank'ota yayi yana zare jajayen idanunsa
"Dan uwarki ba kece fitinanniyar da duk kika jawo muka shiga wannan halinba"...
Yadda ya matse mata wuya yasa KHALEEL yin sauri ya fiszeta daga hannunsa yana fad'in
"Haba MAN me kake shirin aikatawa kenan?
Please!! Dan Allah kabi komai a sannu mana kada ka k'arawa kanka wata damuwar"
"Dan Allah ka kyaleni da wannan y'ar iskar yarinyar,idan ba saita musu zama akeba basa ganewa,gara na raunata ta ko zan samu zuciyata tayi sanyi"
"Haba mana to idan ka hukuntata hakan zai dawo da MAMA yadda take ne?"
A fusace BB ya bar gurin yana watsawa FATAHIYYA mugun kallon zamu had'u...
Shigansa bed room en ya hau safa da marwa a d'akin ya rasa me yasa a y'an kwanakin nan yake fama da mugun zafin zuciya...
Kansa ya dafe tare da fad'in
"Ya Allah ka kawomin mafita"
Zama yayi ya sake yin shiru,shi kad'ai kome ya tuna kuma ya sake mik'ewa da sauri ya shige bathroom....
Cikin k'ank'anin lokaci ya gama abunda yake yi ya fito duk abunda yaje yi yana yi ne cikin gaggawa,yana shirin fitowa KHALEEL ya shigo..
Binsa da kallo yayi a lokacin ne kuma kiran sallan Azhur ya katse su...
Babu wanda yayiwa wani magana haka KHALEEL en shima ya shiga toilet en...
Yana gama abunda zai yi ya fice daga gidan....
Fitowan KHALEEL ya tarar baya nan dama yayi tunanin haka tunda yaganshi yana gaggawan fita..
Da sauri-sauri KHALEEL ya shirya,cikin closet en BB ya bud'e wasu kayan ko amfani dasu ba ayiba,nan ya d'auki wanda yake ganin zai iya sawa a lokacin ya fice cike da gaggawa kada abunda yake tunani ya faru.....
Tada sallah da yaji anyi dai² lokacin da ya fito shi yasa shi tafiya masjeed en amma zuciyarsa tana cike da damuwan Allah yasa KHALEED ba tafiyan da yayi niyya yayi ba,in dai kuwa haka ne an samu matsala babbama kuwa...
Da wannan zullumin a ransa ya isa masallacin,sai dai yana shiga ya hangoshi a sahun gabansa..
Hakan da ya gani ne yasa shi yin hamdala ya dai²ta sahunsa da na kusa da shi ya kabbara sallah...
After an idar da sallah suka fito,gida suka nufa KHALEEL ya kalli side en BB
"Kafa sa naji tsoro wallahi dana fito ban ganka ba"
"Ohh!ni wai kake magana akai?
"To idan ba kaiba dawa nake?"
"Na sani ko ba dani kake ba"
Kai ya kad'a yana jinjina k'arfin hali irin na KHALEED da yake iya rainawa mutane hankali amma a fili sai ya bar zancen haka tare da sako zancen
"Ya kamata fa muyi tunanin abunda ya kamata muyi tun kafin dare yayi... Zuwa yanzun yaci ace mun nemo wanda zai ringa kula da MAMA saboda jinya ce sai mun sami mataimaki....
ZUHRA yarinya ce baza ta iya jinyan MAMA ita kad'aiba,ko dan school ensu bai kamata musa musu ido ace baza su ba dan MAMA tana kwance....
Yawwa!! Gaskiya ina tunanina ya kamata mu nemo HAJIYA LAURA dan ita kad'ai take da masaniya kan b'atan ZUHRA da kuma sace ASHNA da akayi a safiyar yau"....
A fusace BB ya kalle shi
"Ina ruwana da wata ASHNA taita b'atama mana ni babu abunda zai d'agamin hankali..
Ai duk laifin MAMA ne ya jawo haka ta faru,kuma ina tabbatar maka da sakamako MAMA ta fara karb'a tun a duniya"....
"Nasan da haka amma dai ya kamata kayi tunani hausawa suna cewa 'Hannunka baya tab'a rub'ewa ka yanke ka yar'....
Shirun da yayi yasa KHALEEL samun daman tunasar da shi abubuwan da yake shirin mantawa,a lokaci guda duk jikinsa ya dad'a yin sanyi,kana kallonsa zaka gane hakan a tare da shi veins en kansa duk sun bayyana ya dad'a zama quit da shi....
"Ya kamata naje"
Abunda ya furta kenan da yasa KHALEEL binsa da kallon mamaki
"Ina kuma kake cewa za kaje?"
"KHALEEL baza ka ganeba amma ya zama dole na nemi sulhu da dangina haka kuma dole ne na shirya MAMA da danginta idan har ba so take ta tashi cikin wad'anda Allah zai yanke rahamarsa daga garesu ba"
Kai KALEEL ya kad'a
"Tabbas wannan shi ne abunda za kayi ka tseratar da MAMA daga fushin ubangiji da take ciki,Allah ya bamu ikon abunda mukayi niyya....
Amma taya ya zamu billowa lamarin tunda yanzun MAMA tana kwance cikin mawuyacin hali,dole dai ko za muyi tafiyar nan cikin kwanakin nan sai mun samo mai zama da ita"
Tunanin hanyar da zasu bi BB yake dai² lokacin da suka shigo haraban gidan...
"Ina ganin muje mu nemi shawaran UMMI kan wannan al'amarin,za ta fimu sanin abunda ya kamata"
Sai lokacin KHALEEL ya tuna ashefa UMMI bata san ya fitoba,kuma gashi bai kirataba bare ta san halin da ake ciki....
"Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un"
Abunda ya fito daga bakinsa kenan da ya jawo hankalin BB kansa cikin dauriya yana fad'in
"Lafiya kake kuwa?"
"Inafa lafiya...wallahi na manta tun fitowarmu UMMI bata saniba
Ina da tabbacin yanzun haka hankalinta a tashe yake tunda bana gida...
Sannan kuma ban kirata na sanar da ita halin da ake cikiba"
Cikin nuna damuwa yake maganar dan kuwa yasan idan har UMMI ta duba bata ganshiba tabbas hankalinta dole ya tashi musamman ta kira shi taji bata same shiba,a nan kam hankalinta sai yayi k'ololuwar tashi...
Hannunsa yasa ya dafe kansa ya rasa me ya kamata yayi,haka kawai ya nufi inda yayi parking yana shirin yiwa motan key BB ya dakatar da shi
"Amma dai ai ka jira mu tafi tare ko?"
Kasa yin magana yayi sai k'ok'arin tada motan da yaci gaba da yi,shi kuma BB ya koma side en mai zaman banza ya zauna suka bar gidan.....
《《》》
Bai barta ita kad'ai ba har sai da ya dangana da ita da bedroom en da yake ganin nan ya kamata ya ajiyeta,sannan ya fito ya jaa mata k'ofa'n ya rufe ta waje...
A parlor yaransa suka baje suna jiran dawowarsa dan suna ganin ogan nasu ya fad'a tarko,duba da ganin yadda ya kafe yarinyar da ido duk sai wani tsare gida yake...
Fitowarsa yasa su shiga taitayinsu suna jiran jin me kuma yazo da shi a wannan karon...
Sai da ya zauna tukuna ya kallesu yana fad'in
"Kai kufa maida hankalinku jikinku,sannan kunga yarinyar nan baba so wani cikinku ya shiga harkarta...
Kun dai gane abunda nake nufi ko?"
Dariya suka sa dukansu wadda tasa ran BIGGY ya b'aci ganin suna neman maida shi wani sauna...
Wani uban ashar ya k'unduma musu wanda yasa suka nutsu daga dariyar da suke
"Wane irin iskanci ne zai sa ina magana kusani a gaba kuna dariya....
Wato ga wawa yana magana ko?
Allah ya baku sa'a inga wani d'an iska ya shiga harkarta,wallahi saina fasa kan mutum da alburushi".......
*~
*U* MMI cikin parlor sai kaiwa da kawowa take abun duniya duk yabi ya dameta saboda rashin ganin d'an lelenta yasa ta shiga damuwa,musammanma yau da bata san inda ya nufa ba,ita dai tasan a tsawon tasowarsa bai tab'a fita irin hakaba ba tare da ya sanar da ita inda za shiba....
To amma yau kam me yasa ya mata haka,bayan rashin sanar da ita da baiyiba ya fice kuma sai kiransa take amma shiru...
Babban tashin hankalinta bai wuce ganin yadda take kiran wayan ba a d'aukaba,wannan shi yasa ta shiga damuwa sosai...
Tun safe har zuwa wannan lokacin hankalinta ya kasa kwanciya,zuciyarta sai kawo mata tunani take iri-iri wanda sam basu da dad'in ji...
Dalilin da yasa ta shiga addu'ah kenan tana nema masa kariya daga mahalicci...
Haka ta tashi tayi sallah,har ta idar ta gama addu'o'in da za tayi tana jiran ganin ikon Allah,duk jinta take cikin damuwa sosai da har ta kasa cin abinci....
Parlor'n shiru babu abunda ke tashi sai k'ira'ar SHEIKH-MANSHAWIIY cikin tashar nan ta SAUDI-QUR'AN...
Ta yi shiru tana sauraron karatun sukayi sallama a bakin parlor'n had'e da shigowa,kowanne fuska babu annuri...
Da sauri UMMI ta shiga fad'in
"Al-hamdulillah!!
SON ina ka shiga yau tun safe?kasa hankalina duk ya tashi sai nemanka nake...
Ina kaje kam duk layukan wayankama suna shiga baka d'auka?"
Shiru yayi yana dad'a yin k'asa da kai,sai shigewa bayan BB yake,kamar wanda yake tsoron fad'in abunda aka tambayeshi...
Shiru UMMI tayi tana kallon ikon Allah tare da rik'e hab'anta...
Wucewa BB yayi ya zauna saman cuitions en dake parlor'n,cikin sanyin murya yake gaida UMMI datake binsu da kallon mamaki...
Ta k'asan idonsa yake kallon UMMI da take tsaye itama har lokacin bata zauna ba,kuma ta kasa barin gurin...
"Wai daga ina kukema tukun duk kun wani yimin shiru kunk'i magana...
Na tambayeka kai kuma kak'i bani amsa ko?"
"Kiyi hak'uri UMMI wallahi uzuri ne yasa muka fita bamu sanar dakeba,amma in sha Allah bazai sake faruwaba"
BB ya fad'a yana hararan KHALEEL da ya kasa zama,sai yanzu da BB yayi magana tukun ya matso kusa da UMMI..
"Allah UMMI ba da niyya nayiba matsala ce tasa muka fita bamu sanar mikiba,kuma daima lokacinfa bana jin kin tashi...
Yawwa UMMI kin hak'ura ko?"
Cike da shagwab'a yayi maganar yana had'e hannunsa alaman ban hak'uri...
Murmushi tayi tana matsowa inda yake,ganin tana murmushi shima ya shiga murmusawa..
Kunnensa ta rik'e ta d'an murd'a kad'an...
"Argghh!UMMI wallahi da zafi,zafa ki ciremin kunne,dan Allah kiyi hak'uri,nayi miki alk'awari baran sake ba"....
Duk maganar yana yin tane dafe da side en fuskansa da ummi ta rik'e idansa a rufe....
Shikam BB yana zaune yana kallon ikon Allah....
Sakin kunnen tayi tana fad'in
"Gobema idan ka tashi fita kada ka fad'amin kaji ko"
BB ta kalla tana murmushi,sai dai yanayinsa kad'ai ta karanta tasha jinin jikinta kan yadda ta ganshi,zama tayi lokacin shima KHALEEL ya zauna yana murza kunnensa dan da alama har lokacin bai daina masa zafiba.....
"KHALEED lafiya kuwa kake na ganka cikin damuwa,anya kuwa babu wani abu dake damunka"...
Ta d'an yi shiru na wasu sakanni kafin taci gaba da magana,sai da tayi masa nasiha mai shiga rai da ta dad'a sanyaya masa jiki da har yake jin kamar zai yi kuka a lokacin....
KHALEEL yayi gyaran murya yana fad'in
"UMMI gaskiya ba lafiyaba dan kam yau al'amura duk sun dad'a cakud'ewa".....
Nan ya kwashe komai ya sanar da ita daya faru a safiyar ta yau....
Salati take ta zabgawa ta dafe bakinta da hannu,sai juya zancen take tana kad'a kai....
Sun jima parlor'n shiru babu mai magana zuwa wani lokaci sannan UMMI taja ajiyan zuciya tare da kallonsu
"Yanzun waye kuka bari a gurinta?"
Kallon-kallo suka shiga yi tsakanin su biyun,basu bata amsaba sai da ta sake mai²ta musu tambayan...
"Amm!UMMI ai babu kowa gurinta yanzun muma dawowarmu kenan,ZUHRA kuma tana gida mun barota za tayi abincin da za a tafi da shi hospital en"
"Too!Amma kuma labarin ita ASHNA fa ina fatan dai kun sanar da hukuma halin da ake ciki ko?"
BB ne ya shiga kad'a kai alamar a'a,har za tayi magana KHALEEL ya tari numfashinta
"Ehh!UMMI na sanar da D.P.O d'azun ta waya,amma lokacin naso ace zuwa muka yi,sai dai kuma muna hospital shi ne dalilin da yasa bamu jeba"
"To Alhamdulillah tunda hukuma sunsan da b'atan nata,ammafa ni wannan al'amari yana d'auremin kai...
B'atan y'an mata biyu lokaci guda,kuma tazaran sace ta farko da ta biyu duk a cikin shekara d'aya...
Kaiii!Allah yayi mana magani,ubangiji ya tseratar damu daga sharrin masu sharri"
Duk suka amsa da amin,sannan KHALEEL ya gyara zama yana shirin korowa UMMI labarin abunda ya kawosu a yanzun...
"UMMI to amma mufa zuwa mukayi ki samo mana wacce zata zauna a asibitin,wa kike tunanin zamu samu ya zauna da MAMA?
Ina nufin kisa a samo wata matar da zata yi jinyan MAMA har zuwa lokacin da zata samu sauk'i...
Kinga ko da biyanta nema sai ayi idan zamu samu hakan"
Yayi shiru yana jiran jin amsan da zata bayar...
Murmushi tayi irin nasu na manya duk da bana tsammanin zata wuce 45 year's...
"Lallaima yaran nan wato kuna so a samo wata matar daban tayi jinyar MAMA ko?"
Shiru babu wanda ya iya amsawa saima kallonta da suke suna kuma kallon junansu....
"Ina ganin babu buk'atar nemo wata mata da zata yi wannan aikin,ni aikin me nake da ya wuce zaman gida tunda Allah yasa DADDYNKU baya nan bari na kirashi na sanar masa halin da ake ciki sai mu wuce,yanzun babu kowa a gurinta bai kamata a bar mara lafiya shi kad'ai ba,ya kamata ace mun hanzarta sai na kula da ita zuwa lokacin da Allah zaisa ta samu sauk'i...
Daga nan kuma sai ku koma gida ku d'aukomin su ZUHRA da kayansu,bai kamata ace an barsu su kad'ai a cikin gidaba tunda ba wani girmane da su ba,ni zan kula dasu zuwa lokacin da HAJIYAN zata samu sauk'i,in sha Allah kuma zan kula da HAJIYAN,Allah ya bata lafiya mai d'orewa...
Su kuma Allah ya bayyana mana inda suke idan da rabon mu sake had'uwa da su"...
Ta k'are maganar fuskarta da annuri shimfid'e samanta
Suma maganar ta UMMI kam tayi musu dad'i sosai wanda har suka rasa bakin magana...
Cike da jin dad'i sukema UMMI godiya cike kuma da jin dad'i mara misaltuwa.....
"To amma UMMI akwai fa wata sabuwar matsalar"
KHALEEL ya katse musu maganar da suke dai² lokacin
Da mamaki take kallonsa
"Matsala kuma ta me kenan?"
Bayanin tafiyar da zasu yi zuwa DUTSE suka yi mata da manufar da zata kaisu...
"To amma yaushe kuka shirya yin tafiyar?"
Tayi tambayar tana son sanin lokacin da suka yanke tafiyar
"UMMI ai mu da a gobema muke son tafiya,tunda dai ance da sanyin safiya ake kama fara koh??"
"Gaskiya ne to Allah ya biyaku da samako mafi kyau kan wannan niyyar taku"
Taji dad'i sosai da bayanin da sukayi mata ta kuma yi musu fatan alkhairi cikin abunda zai kaisu,da addu'o'in samun nasara,daga haka ta mik'e ta shiga shirin tafiya hospital gurin MAMA......
《《》》
ZUHRA har ta gama abunda za tayi a kitchen en ta fito,babu kowa cikin parlor sai FATAHIYYA kad'ai dasu HANEEF...
"Ina su YAYA KHALEEL suka shiga kuma?"
Tayi tambayan tana jiran jin amsan da zasu bata...
FATAHIYYA kam kasa magana tayi dan da ganin alamu taji matsa a gurin BB..
Rik'on da yayi mata bana wasaba,shi yasa har yanzun tana nan tana faman murza wuyanta,danma Allah ya taimaketa KHALEEL na gurin ya kai mata d'auki da kam sai tafi haka jin jiki....
"YAYA ZUHRA sun fita,amma kamar dai masallaci suka tafi"
"To ama kuma idan masallaci ne ai ya kamata ace zuwa yanzun tuni sun dawo tunda gashi har ana sallan la'asar nefa"
"Amma YAYA ZUHURA bakya ganin ko sun jira suyi la'asar enne kafin su dawo"
KHALEEFA ya fad'a
"Ehhh!to kumafa haka ne....
Maza kuje kuyi sallah kuzo kuci abinci kunji ammafa ayiwa MAMA addu'ah kunji ko?"
Cikin sauri suka tashi suka nufi yin sallah,da yake sun san warning en da BB yayi musu kan rashin yin sallah,idan aka bashi labarin ba suyi sallah ba su da shi...
Shi yasa tana yi musu magana suka yi saurin tashi dan yin sallah....
Bayan lokaci mai tsayi suna zaman jiran BB ya dawo dan tafiya hospital en,amma shiru har bayan salla'n Maghreb....
Sai bayan da aka idar da sallah'n ishaa sannan suka shigo gidan shima a gurguje suka shigo,nan KHALEEL yayima ZUHRA bayani dan shi kam BB ko tsayawa baiyiba ya shige ciki...
Haka suka shige kowa dan had'a kayan da yake buk'ata sannan suka fito lokacin KHALEEL har yayi waje,a parlor BB ya tadda su nan ko ya tsaya kansu fuska a d'aure ya jaa musu kunne kan duk wanda aka ce masa yayi wani abu na badai-daiba to ya kuka da kansa dan kam zaima yaro hukunci dai-dai da abunda yayi...
Jikin FATAHIYYA ya sake yin sanyi dan ita kam tana tunanin wannan fad'an na BB da ita yake ba kowaba shi yasa ta dad'a sunkuyar da kanta k'asa uwa wata munafuka...
Har suka bar gidan babu wanda yake k'wak'wk'waran motsi cikin motan haka suka isa gidan su KHALEEL inda zasu soma sabuwar rayuwa da babu MAMA cikinta......
《《》》
'Dakin take k'arewa kallo tana yamutsa face,ko gama shiga d'akin bata yiba ta ji an rufe k'ofan d'akin...
Tab'e baki tayi taci gaba da abunda take na daga yamutsa fuska haka har ta isa bakin mirror en d'akin...
Kan stool en gurin ta zauna tana d'ora kanta kan k'afarta duk ta wani takure kamar wacce take jin mugun sanyi...
Kusan awa guda bata ji motsin kowaba hakan yasa ta sauka daga kan stool en saboda ta gaji da zaman gurin..
Can wani space da ta gani tsakanin closets da bango ta shige ta dad'a takurewa sai yanzun data ga dare yayi sosai wani tsoro ya shigeta duk tunanin gida da MAMA shi yafi damunta,ko wane hali su MAMA suke ciki da sukaji labarin an sace ta...
Wannan tunanin da tayi shi yasata sa kuka mai tsuma zuciya tana yi tana surutai ita kad'ai
"Wayyoo!!! ni shi kenan bazan sake ganin MAMA ba da su ZUHRA,wayyoo!!! Allah sun sace ni ba zasu sake barina naga MAMANA ba"
Tana tsaka da kukan aka turo k'ofan had'e da shigowa,dube-dube ya gamayi cikin d'akin amma bai gantaba kuma dai ya tabbatar da ya kulle d'akin tana ciki....
K'arasa shigowa yayi cikin d'akin bayan jiran da yayi da magana yaji shiru,ya nufi door en toilet amma wayam babu kowa...
Can tsakanin closets da bango ya hango k'afafunta da yake d'akin akwai haske,gurin ya nufa yana mamakin me kuma take yi a nan?
K'arasawa yayi gurin da take da niyyar yin magana sai dai me tun kafin ya isa ya fara jiyo kukanta da ba'a ji sosai sai an matso kusa da ita...
"BEAUTY me ya sameki kike kuka?"......
~Tofa wata sabuwa inji y'an chacha,su ASHNA kuma an koma BEUTY ammafa ba a bakinaba a bakin BIGGY~...
《《》》
"Haba KHUBRA me kuma ya kaiki kwanciya da wannan al'murun ke dama da ba lafiyaba ai sai ki jaa jikin naki ya dad'a yin zafi"
Shigowar BABA ZUWAIRA kenan gidan ta tarar da KHUBRA kwance tsakar gida saman tabarmar kaba....
'Dan d'ago da kanta tayi kad'an ta kalli BABA sannan ta sake maida kanta ta kwantar saman hannunta da tayi matashi da shi.
"Sannu da dawowa BABA"
"Yawwa y'ar nan,kinga na ce zan aiko miki da magani shiru gashi da gani jikin naki ke damunki...
Yau kam ISAH bai fito da wuriba shima sai yanzu da zan taho na biya naganshi...
Shi ne yake shaidamin gona yaje dubawa,Allah dai ya taimaka na samo miki maganin,yi maza ki tashi ki sha kinji idan aka jima an yi sallar ishaa sai ki kwanta kinji ko,Allah dai ya baki lafiya"
Duk maganar nan da BABA ZUWAIRA ke yi hankalin KHUBRA ba a kanta yake ba,tunani ne iri² duk zuciyarta ta cunkushe,jinta take a wannan lokacin tana so tayi kuka ko zata samu sauk'in rad'ad'in dake damunta a zuciyarta,a cikin kwanakin nan tana yawan yin mugayen mafarkai da wani mutum da har zuwa yanzun ta kasa tantance waye ne,sai dai duk lokacin da zata ganshi cikin muguwar damuwa take ganinsa wannan dalilin da yasa mafarkin ya tsaya mata a rai,yawan mafarkin da take da shi yasa ta shiga damuwa da ta haddasa mata ciwon jikin da take fama da shi cikin satin....
Sai da BABA ZUWAIRA ta tab'ata sannan ta tashi ta zauna had'e da karb'ar maganin tana juyashi a hannunta...
Da kyar ta samu tasha maganin sannan ta tashi da nufi yin sallah....
Tun misalin k'arfe 8:30pm tayiwa BABA ZUWAIRA salamma ta shige d'aki,ita ko BABA'N a lokacin tunaninta duk jikin ke damunta,ta dai bita da fatan samun sauk'i fuskarta duk alamun damuwa da halin da y'ar tata ke ciki...
Ko da ta shiga d'akin bayan ta kwanta nan ta shak'i kukanta har ta godewa Allah...
Sai bayan ta gama kukan ta tsaya tunanin menema wai yasata kuka haka?
Tana wannan tunanin bacci ya d'auketa cike da mafarkai iri-iri....
《《》》
Gari na wayewa suka hau shirin barin garin,misalin k'arfe 10:00am suka yiwa UMMI sallama suka mik'i hanya bayan d'umbin nasiha da suka sha a gurinta sannan ta musu fatan dawowa lafiya...
Sai da suka biya suka ga jikin MAMA,sai daifa har zuwa wannan lokacin MAMA bata sanma wanda yake kanta ba,bare ta samu damar yin magana.....
Daga nan suka d'auki hanya sai garin na JIGAWA DUTSE......
乛乛乛乛乛
*T* afiya ta mik'a a b'angarensu BB,inda babu wanda ke wata magana hakan ne yasa tafiyan nasu ya zama kamar na kurame...
K'arfe 1:15pm Motansu ya parker k'ofar wani madaidaicin gida,ginin gidan dai² na talaka dake cikin rufin asirin ubangiji,a cikin garin na DUTSE unguwan shiru babu hayaniya,fitowa BB yayi ya tsaya yana tunanin ko ina ne gidan daga cikin jerin gidajen?...
Sun shafe tsawon lokaci suna jira a gurin ba tare da ganin kowaba,sai zuwa can wani d'an dattijo ya fito daga zauren d'aya daga cikin gidajen,da alamun shima kamar gona zai tafi duk da wannan tsufan nashi...
Ganin mota tsaye bakin k'ofar gidan ya d'an kalli motan da mamaki a tare da shi...
Da sauri KHALEEL ya kalli BB
"MAN ya kamata fa mu tambayi wannan datijjon tun kafin mu rasa wanda kuma zamu tambaya"
Kallonsa BB yayi tare da murmushin k'arfin hali,sannan ya sake bud'e motan motan karo na biyu ya fita cikin sauri..
Matsowa yayi kusa da dattijon yayi masa sallama fuskarsa da fara'a,shima dattijon ya mayar masa da murmushin tare da amsa masa sallaman da yayi masa...
Bayan BB ya gaida shi ya amsa masa,sai kuma shiru ya ratsa tsakaninsu,tunanin BB ta ina zai fara masa bayanin abunda ya kawosu,shi kuma dattijon yana kallonsa ne irin na rashin sanin nan...
"Samari daga ina haka?sai dai kuma ban shaida kaba"
Sai da BB ya sake yin wani murmushin kafin ya fara magana
"BABA daga kano muke,to dama akwai wani gida da muke nema kuma dai gaskiya BABA gidan ne ya b'ace mana,saboda shekarun da yawa"
Murmushi dattijon yayi irin nasu na manya kafin ya tambayi BB
"'Dana wane gidane kuke nema haka?"
"Ehhh to BABA gidan MALAM ABDU MAI AL-MAJIRAI muke nema,ko nan ne unguwan da yake?"
Murmushi dattijon ya sake yi masa tare da gizgiza masa kai
"K'warai kuwa nan ne unguwan da yake gama gidan da kuke nema nan kusa da kai"
Ya fad'a tare da nuna k'ofar gidan da ya fito yanzun
"To amma wa kuke nema a gidan shi kuke nema ko wani daban kuke nema?"
Sosai BB yaji dad'in samun gidan da suka yi ba tare da sun sha wata wahalaba,fuskarsa d'auke da jin dad'in hakan ya furta
"BABA yana raye ne ko kuwa?"
"Sosaima kuwa d'an nan,sai dai ya jima yana jinya dan a halin da ake cikima yana kwance ne sai dai a tayar da shi saboda k'afafunsa da suka samu matsala"
"Eyyyahhh!Allah ya bashi lafiya....
Amma BABA idan da hali muna son ganinsa ne dan shi muka zo garin nan"
"To to kada ka damu yaro,bari na shiga na sanar masa da yana da bak'i tukuna"
Da sauri BB ya amsa da
‘’To BABA mun gode sosai‘’
Sai da ya ga shigan dattijon tukun ya juyo,ta saitin window en da KHALEEL yake ya tsaya tare da knocking..
Sauke glass en yayi yana kallonsa
"Yahh!ina fatan dai munyi nasara"
"Sosaima kuwa Allah ya taimakemu wollahi,ashema a k'ofar gidan muka tsaya"
"Kaiiii!ammafa naji dad'i sosai wollahi,to amma KAKA yana raye kuwa?"
Sai da yayi wani k'ayataccen murmushi kafin ya amsa
"K'warai kuwa,sai dai kuma ance bashi da lafiya yanzun hakama"
Yanayinsa ya d'an sauya lokacin da ya fad'i hakan,shima KHALEEL en yanayin da yake kan fuskarsa kenan lokacin da yaji hakan...
"Allah dai yasa ba wani seriuos ciwo ne da zaisa ya kasa fuskantar dalilin zuwanmu ba"
KHALEEL ya fad'a yana sauraron yaji me BB zai ce kan hakan..
"Ameen kam dan wallahi har murnan da nake ya soma b'acewa,gaskiya ina cikin damuwa yanzun haka da naji wannan maganar"
"Tohh!Allah yasa dai babu wani abu da zai mayar mana da farin cikinmu baya"
Suna cikin maganar dattijon ya fito yana waigawa yaga ina saurayin ya nufa kuma,bayan ya barshi tsaye a k'ofar gidan....
A jikin motan ya hango shi ya jingina,k'arasowa yayi da murmushi a fuskarsa
"To samari zaka iya shiga yana sauraren zuwanka"
Kallon KHALEEL yayi da yake k'ok'arin fitowa daga motan,sukama juna murmushin k'arfin hali sannan sukabi bayan dattijon zuwa cikin gidan....
Mata ne da k'ananan yara wad'anda bazasu iya aikin gonaba sunata aikace-aikace a tsakar gidan,gaisuwa kam su BB sun shata musamman da aka gansu da shiga data bambanta da yanayin y'an garin...
Haka sukaita wucewa har suka isa turakar mai gidan,shigansu suka tarar da wani DATTIJO da yafi wanda ya rakosu tsufa a kwance k'afafunsa sun kumbura sosai suna tsatstsafar da ruwa ta jikinsu...
Da tausayawa suke kallonsa wanda duk mai raunin zuciya idan ya kalli k'afafun sai yayi masa hawaye,inda tafin k'afar tasa yayi wani irin sai wata irin sab'a yake kamar jikin maciji.....
Kallon yanayin da yake ciki yasa jikinsu dad'a yin sanyi,dan har sun yanke tsammani da cewa wannan dattijo zai gane duk wani bayani da zasuyi masa a wannan lokacin,sai dai kuma maganarsa ta basu mamaki matuk'a...
"Marhaban lale"
Juyawa sukayi suka kalli juna da mamaki,sannan kuma suka kalli dattijon dake kwance...
Guri suka samu suka zauna,nan dattijon da ya rakosu shima ya samu guri ya zauna daga gefen wannan dattijo dake kwance...
"Samari daga ina haka?ban shaida fuskokinkuba"
Sai da suka sake kallon juna sukayi murmushi tukun BB ya juya ya kalli dattijon tare da fad'in
"BABA mu bak'i ne daga garin KANO,sai dai kuma ba lallaine dama ace ka ganemu ba"
K'ura masa ido dattijon yayi da alama akwai wani abu da yake son karanta akan fuskarsa da har yasa yake masa irin wannan kallon k'urilla,yanayin kallon da yake masa ne yasa shi yin shiru yana binsa shima da ido had'e da murmushi...
"Yaka nan zo maza,matso kusa dani kaji zo?...
Ina ji ajikina wannan yaron duk inda ya fito jini nane shi duk inda ya fito"
Da mamaki suka sake kallon juna shi da KHALEEL,inda KHALEEL en ya d'aga masa kai alamar yaje gurin dattijon...
Matsawa yayi kusa da dattijon,shi kuma sai k'ok'arin mik'ewa yake ya zauna,da sauri d'aya dattijon da ya rakosu ya mik'e ya kamashi ya zaunar...
Hannunsa ya mik'a ya rik'o BB yana dad'a kallonsa...
"Tabbas ko tantama babu wannan yaro duk inda ya fito jinin SAFWAN ne....
Allah sarkin hikima,yaro ina ka baro SAFWAN en?
Yana raye ko kuwa ya mutu ne?
Iya tsawon wannan lokaci SAFWAN ya watsar damu sam yak'i zuwa ya ganmu duk tsayin wad'annan shekaru,ina ya shiga haka?"
Ganin bai bashi amsaba yasa shi sake fad'in
"Yaro ka sanar dani ko dai da gaske SAFWAN en ya rasu kamar yadda nake mafarki?"
A lokacin da yayi wannan maganar idanunsa har sun kawo ruwa,wanda suke shirin zubowa,saboda rashin sanin amsar da za a bashi...
"A'a BABA yana raye"
BB ya fad'a wanda fad'ar hakan yasa KHALEEL ya kalleshi,zuciyarsa cike da tunanin
‘’Too kaji mutumin nan yana neman b'allo mana ruwa,idan har ABBA yana raye a wane bigere yake rayuwa,ko kuwa yasan inda ABBAN yake da har ya fad'i haka?‘’
Saurin katse tunaninsa yayi ya sake maida hankalinsa kan abunda BB zai fad'a...
"Too Alhamdulillah da har kuwa yana raye,amma me ya faru tsawon wannan shekaru ya kasa zuwa ya ganmu bayan yasan muna raye kuma muna cikin garin nan,idanma ace bana raye shin ba ga y'an uwansa nanba da suke ciki d'aya,ko kuwa shi kenan ya yanke zumunci da mu?"
Jin maganar BABA ABDU yayi kamar zubar wuta a jikinsa,cikin zuciyarsa yana jinjina kalaman da zai sanar da BABA a wannan halin da yake....
Sai da BB yayi k'arfin hali sannan ya fara magana,duk wani labari daya shafesu tun daga barin garin har zuwa wannan lokacin da yake zaune a gabansa bai b'oye masaba ya sanar da BABA ABDU,amma banda labarin b'atan ASHNA...
Al'ajabi da mamakin abunda ya faru cikin labarin da BB ya sanarma da BABA ABDU yasa shi kuka yana fad'in
‘’Lallai wannan al'amari daya faru tabbas muk'addari ne daga Allah,Allah ya tsara haka sai ya faru daku a rayuwarku,babu kuma wanda ya isa ya tsallake K'ADDARA.....
To amma ina ita mahaifiyar taku da sauran y'an uwanka da kace suna nan?
A wane hali suke yanzun?kuna tare gaba d'aya a guri d'aya ko kuwa?"
Duka tambayoyin BABA ABDU ya jerowa BB ba tare da ya jira ya amsa wasu ba....
"Ehh!BABA muna tare dasu can garin kano,sai dai kuma ita mahaifiyar tamu a halin yanzun bata da cikakkiyar lafiya,wanda ta kaiga har bata iya shaida wanda yake kanta"
"Subhanallah!wannan wane irin ciwone haka ya sameta?"
"BABA muma dai gaskiya bamu san wane irin ciwo bane,tun da likita ya shaida mana suna buk'atar ganin wani babba daga zuri'ar mu dan suyi magana dasu,to mu kuma babu kowa a tare da mu,shi yasa muka yanke hukuncin nemanku mu sanar muku halin da muke ciki"....
Dattijon dake gefe ne ya mik'e tsaye cikin fushi
"Wato da can baku neme muba sai yanzu da al'amura suka gama cukurkud'e muku kuka lallab'o gurinmu....
To kuma tashi ku d'ebi tsummokaran jikinku ku k'ara gaba mu ba abunda zamu iya yi muku a halin yanzu,muma fama muke da namu mahaifin kun dai ga halin da yake ciki...
Saboda haka maza ku tashi ku koma babu abunda zamu iya yi muku a halin yanzu,ita mahaifiyar taku zata iyayi muku komai ai na rayuwa ciki kuwa harda samar muku wasu dangin uban‘’....
Jikinsu duk yayi sanyi da jin furucinsa,suna sauraron yadda yaketa fad'a..
Shi kuwa BABA ABDU yana zaune yana kallon ikon Allah yadda d'an nasa yake ta fad'a kamar zai ari baki...
Murmushi yayi ya sake kallon d'an nasa da ya kasa yin shiru har zuwa lokacin,ganin bai gane me shirun nasa yake nufiba ne yasa shi yin magana
"Ya isa haka KHALEED"
Kallon-kallo sukayi tsakanin KHALEEL da BB,sannan kuma suka juya suka kalli mutumin dake fad'a ganin yayi shiru a lokacin,suka sake kallon BABA ABDU...
"Banda abunka KHALEED ina kai ina fad'a ga wad'anda basu da laifi?ko ubangiji idan muka masa laifi yana hak'uri damu ya kuma gafarta mana....
Kuma ubangiji baya tab'a kama bawa kan laifin da ba nasaba"
"Kayi hak'uri BABA raina ne ya b'aci shi yasa‘’
'Dan murmushi yayi sannan yayi gyaran murya
"Allah sarki MURJA Allah ya bata lafiya,shi kuma SAFWAN idan yana raye Allah ya bayyana mana inda yake"
Gaba d'ayansu suka amsa da ameen...
"Da gani dai wannan da yake zaune kusa dani shu ne KHALEED ko?"
KAKA ya tambaya yana murmushi shima,duka suma suka murmusa tare da amsa masa,juyawa yayi ya kalli KHALEEL
"Shi kuma wannan abokin nawafa?
Ya tambaya yana y'ar dariya
"KHALEEL suna na KAKA"
"Ahhhh!IBRAHIM KHALEEL kenan...
To Allah ya muku albarka da kuka zo nemanmu bayan lokaci mai tsaho".....
"KHALEED kasa a kira sauran y'an uwanka da mutanen gida yanzu ina son ganinsu"
BABA ABDU ya fad'a yana kallon d'ayan dattijon dake tsaye har lokacin,da sauri ya fita don aiwatar da sak'on BABA....
Bayan wucewar wani lokaci cikin turakar ta d'inke da jama'ar gidan manya da yara kowa ya matsu yaji me BABA zai sanar musu haka mai muhimmanci da ya tarasu gaba d'aya....
Sai da yayi gyaran murya yana jingine jikin pillor sannan ya kallesu d'aya bayan d'aya ya fara da fad'in
"Alhamdulillah da Allah ya nunamin wannan rana da na jima ina sauraron zuwanta a tsayin rayuwata...
Dalilin daya sa na taraku a nan ba komai bane face sanar daku wani muhimmin al'amari game da SAFWAN da iyalinsa,wanda wasu daga cikinku sun sanshi wasu kuma basu saniba"......
Take BABA ABDU ya jaddada labarin SAFWAN da iyalinsa ya sanar dasu da duk wani abu daya faru dashi bayan barinsa garin kamar yadda BB ya sanar da shi,yana gama basu labarin turakar tasa kowa dake ciki ya d'auki salati,masu kuka nayi masu jinjina lamarin nayi...
Bayan wani lokaci aka samu kowa yayi shiru sai jimami da kowa keyi da abunda ya faru...
BABA ABDU ya kalli BB dad'an murmushi a fuskarsa yake fad'in
"Kaga wannan?" ya nuna dattijon daya rako su d'azun
"Sunan sa KHALEED shi ne babba cikin y'ay'ana,sannan wannan shi kuma sunansa SULAIMAN,sai kuma wannan AYUBA kenan,sannan sai mahaifinka,daga shi kuma sai k'anwarsu da ta rasu shekaru bak'wai da suka wuce wato FALMATA"...
Wad'annan kuma ya nuna matan dake gefensa matansu ne,haka yayita nuna masa su d'aya bayan d'aya yana gabatar dasu a gurinsa,sannan shima ya gabatar da shi a matsayin d'an uwansu da basu saniba sai wannan lokacin....
Hira sosai tsakanin mutanen parlor'n anata dad'a gaisawa,sannan BABA ABDU ya sallamesu kowa ya fice aka barsu daga shi sai su BB zaune cikin turakan nasa...
Nan da nan aka tashi girki na musamnan a gidan saboda zuwansu,tarba da karamci kam sun samu gurin mutanen gidan wanda basu tab'a tunanin samunta daga gurin mutanenba.....
*2 DAY'S LATER.*
Kwanaki biyu kenan da zuwansu garin wanda suke sa ran a washe gari za suyi haramar barin garin idan Allah ya kaimu ko dan sanin yanayin da jikin MAMA yake a halin da take ciki ko an samu ci gaba ko kuma akasin haka Allah shi ne masani...
Farin ciki kam suna cikinsa tun daga zuwansu garin har zuwa wannan lokacin,kullum cikin hira suke da KAKA da kuma su BABA KHALEED suna dad'a basu labarin zamansu da ABBANSA,wani abun idan sun fad'a sai dai suyi dariya wani ko har da k'walla saboda rashin tabbas akan ABBA'N yana raye ko akasin haka.....
Yau tun safe suke shirin komawa KANO kamar yadda suka sanar da KAKA dama kwana 3 suka zo da niyyan yi....
Sai da ya had'asu yayi musu nasiha sosai kan su rik'e zumunci...
Sunyi masa godiya tare da alk'awarin dawowa nan da wani lokaci ba mai nisaba...
Sosai yaji dad'in hakan,sannan yayi musu alk'awarin da sun koma zai turo su BABA KHALEED suzo su dubasu...
Sunji dad'i sosai da yadda aka karb'esu,sannan sukayi sallama dasu suka d'auko hanyan dawowa KANON DABO......
《《》》
Kimanin kwanaki biyu (2) KHUBRA bata samu ta fita gurin sana'ar taba kamar yadda ta saba...
Duk jikin ya takura mata da ciwo a kwanakin da yasa ta kasa fita,dalilin da ya sa BABA ZUWAIRA ta dad'a sa ido kenan kanta tana dad'a bata kulawa ta musamman saboda yadda take ganin jikin nata....
Yau ta tashi jikin da sauk'i sosai har tana iya yin komai da kanta....
Tashinta da sassafe ta share gidan ta gyara ko ina sannan ta shiga tayi wanka,ta fito kenan daga toilet en BABA ZUWAIRA itama ta shigo gidan d'auke da robber a kanta...
Sororo ta tsaya kallonta tana kuma kallon gidan,dan tana da tabbacin ita tayi wannan aiki...
K'arasowa tayi cikin gidan tana son yin magana...
"Sannu da dawowa BABA"
"Yawwa y'ar nan"
Ta fad'a tana bin KHUBRAN da kallon mamakin yadda ta ganta,bayan a kwance ta barta ta yaya kuma yanzun zata ganta ta mik'e kamar ba itaba...
"Sannu kin tashi?"
"Ehhh!wallahi BABA,ai jikin da sauk'i sosai har ina jin yauma zan iya fita"
Da sauri BABA ZUWAIRA ta katse ta tana fad'in
"Haba haba KHUBRA me zai hana ki k'ara hak'uri zuwa jikinki ya sake warwarewa,in yaso sai ki fitan ko kuwa?"
Cike da tab'ara irin ta y'ay'an fari kuma na k'arshe ta hau buga k'afa tana fad'in
"Ni wollahi a'a ban yardaba,nafa samu sauk'i sosai"
Kallonta BABA ZUWAIRA take tana sake bud'e ido tana kallon ikon Allah
"To ai shi kenan tunda kin dage Allah ya bada sa'a,kuma Allah ya k'ara sauk'i kinji"
Tsalle ta hau yi sosai tana ta murna BABA ta amince mata zata koma gurin sana'ar tata....
Cikin zumud'i ta hau shiryawa,yau da yake ita take son fitan bata b'ata lokaciba tayi ta gama shirinta,sannan tayiwa BABA ZUWAIRA sallama,dai² lokacin itama ta gama shirinta tana jiran al-majiran da zasu d'ibar mata kayan abincin zuwa bakin kasuwa....
Tafiya take cike da kuzari had'e da karsashi saboda yau kam tana jinta cikin k'oshin lafiya,sai dai d'an abunda ba a rasa ba da yake damun zuciyarta....
Har ta k'arasa bakin rafin ta d'ebo ruwa,ta kuma juyo don komawa cikin gari,tana tafe ta kare kanta da hat ta gargajiya saboda rana da ake tsulawa ga zafi.....
Yayinda wani gefen na sararin samaniya ya had'a hadari wanda yake ta gangamowa lokaci guda har garin ya had'e,da alamun yau kam za a iya dacewa da ruwan sama....
Wani iska ne ya taso mai k'arfin gaske,wanda sakamakon haka yasa wasu daga cikin mutane suketa guje-guje,bayan k'uran ya lafane kuma wani iskar cike da yanayi mai dad'i ya sake tasowa...
Cikin nutsuwarta take tafiya tana kuma ci gaba da tura kuranta ita d'aya a hanya....
Wani bak'in PRADO ne ya yanko kan kwaltan da mugun gudu sosai,dai² kafin motan ya k'araso inda take aka tsaya,tare da jan brake da k'arfi wanda ya bada wani mugun sauti ji kake KUUUUUUUUUUUU!!!...............
*_~KEEP FOLLOWING.....~_*
*~#
*T* ana daga gefen titin tana ci gaba da tafiyanta wanda jin k'aran motan da tayi baisa tayi yunk'urin tsayawaba saima ci gaba da tayi kamar ta samu sak'on k'in tsayawar.
Yanayin yanda garin yake ne ya bata damar k'ara sauri saboda wasu irin thunderstorm da ke tashi akai-akai.
Tsayawan da motan yayi a dai² lokacin hakan ya farune sakamakon motan dake fidda hayak'i bayaga engine en motan da ya d'auki zafi,fitowa suka yi suka bud'e gaban motan ko dan su samu hayak'in ya sarara,wannan dalilin shi yaja musu tilas suka tsaya a gefen hanya'n.
Bayan motan suka duba cikin irin galan da masu mota ke zuba ruwa saboda gudun ko ta kwana irin wannan a tafiya.
Shiru sukayi suna kallon juna,saboda rashin ruwan a tare da su sannan suka kuma maida hankalinsu kan hanya'n da yarinyan nan tabi,can nesa dasu sosai suka hangota dan kam tsakaninsu da ita da tazara mai nisa.
"MAN wai ya zamuyi ne kam kanafa kallon yadda garin nan yake dad'a had'ewafa kuma ka tsaya anan kana wani kallona"
Harara BB ya bankawa KHALEEL dake magana,yanayin yadda yayi masa ne yasa shi shek'ewa da dariya,sai da yayi mai isarsa sannan ya kama hanya cikin sauri don tsayar da ita tun kafin ta b'acewa ganinsu.
Cikin sauri yake bin bayanta wanda da k'yar ya samu ya isa bayanta a dai² lokacin da take k'ok'arin karkatawa ta shiga hanyan da zai sadata da cikin gari.
Sallama yayi mata yana daga bayanta dan yasan hakan dai shi ne kad'ai abunda zaisa ta tsaya.
Cikin sa'a kuwa ya samu ya tsaya tare da juyowa don ganin waye ne mai maganar duk da tasan hanyan babu mutane sosai,duba da yanayin da aka tashi da shi a garin.
Idanu KHUBRA ta bud'e sosai ganin fuskar dake tsaye gabanta,tunani ta d'an tsaya yi kanta d'age a sama tana son tuna inda tasan fuskansa.
Magana yake yi wanda sam ta kasa bashi amsa saboda yadda ta lula duniyar tunani,har sai da yayi magana da d'an k'arfi sannan tayi firigigit da dawo duniyar da take tare da fad'in
"Ammm!kace mene?"
Shiru yayi yad'an tsaya yana binta da kallon mamaki da kuma tunanin inda yasan mai wannan muryan,kallo sosai ya k'ureta da shi sai dai bai gano komai kan fuskartaba,dalilin daya katse shi kenan daga tunanin da yake.
Yana shirin yin magana BB ya iso gurin yana fad'in
"MAN lafiya ka zo ka zauna ka wani shanyani a jeji bayan kana ganin yadda garin yake"
Shiru yayi lokacin da ya k'araso ya gansu tsaye suna kallon-kallo tsakanin su.
Kallonsu yayi sun kafe juna da ido,a hankali KHUBRA ta maida kallonta kan BB da isowarsa gurin kenan,dad'a fiddo idonta waje tayi da sauri kuma ta maida kanta k'asa had'e da dafe chest enta jin yadda zuciyanta keta skipping kamar zai fito waje.
Tun daga sama har zuwa k'asa BB yake kallonta a zuciyarsa yake magana
"Ina nasan mai wannan kamannin?anya ko itance ko kuwa mafarkine nake yi?"
Sake kallonta yayi da yadda take tsaye jikinta na vibrating da gani kasan akwai abunda ya bata tsoro wanda yasa ta shiga yanayi irin na rashin gaskiya haka,da sauri ya katse shirun ta hanyar magana da ya sasu kallonsa
"Ammm!baiwar Allah taimako muke buk'ata"
Ba tare da ta kalleshiba ta furta
"Taimako akan me kenan?"
Sake kallonta yayi yanzun kam ya samu shaida ta biyu da take bayyana masa hasashen da yake yi akanta,abu d'aya yake nema don tabbatar da gaskiyar lamarin.
"Muna buk'atar ruwane zamu sa a mota,mun d'an samu matsala ne so motan yana can kan hanya"
Har lokacin duk maganar da yake yi yana yine idanunsa na kanta,yayin da ita kuma duk take jinta a takure saboda yadda take jin idanunsu a kanta.
KHALEEL ya koma kamar wani idol yayi shiru yana sauraren muryanta dake masa yawo cikin kansa,so yake ya tuna inda yasan wannan muryan,yayin da a b'angaren BB shima hakan take dan shi kam gani yake a yanzun yana da yak'inin itance da kashi 50%,babban abunda yasa bai gama amincewa da itanceba ganin yadda wannan take b'aka,ga yanayin suturan dake jikinta sannan ya tsinceta cikin yanayin da baya tunanin KHUBRA zata shiga.
Duk sunyi shiru har sai da yayi k'arfin hali tare da danne zuciyarsa kan lallaifa wannan ba waccan KHUBRA'N da suke tsammani bace,kawai dai yanayin halittane da kuma su d'in da suke cikin yanayi na rud'u yasa suke ganin kamar itan ce da gaske.
Kautar da tunanin yayi tare da fad'in
"Amm!ina fatan dai ba zaki damuba dan da d'an tafiya tsakanin nan da gurin da mukayi parking"
"A'a babu komai,muje kawai"
Ta fad'a tana juya akalar kuran nata da niyyan komawa bayan garin inda suka bar motan nasu.
A baya suka shiga binta tana tura kuran nata,duk wani motsi nata akan idanunsa hakan yake yana ankare da ita,suna tsaka da tafiyan ne wata matashiya ta taho kanta d'auke da robber yellow da alama daga rafi take ta gansu suna tafiya,kallon mamaki tabisu da shi kafin tayi magana
"A'a KHUBRA ina kuma zaki nufa haka bayan kin d'ebo ruwan kike k'ok'arin komawa"
Cak!KHUBRA ta tsaya a gurin kamar anyi pausing enta ba tare da ta k'ara one step forward ba.
"Shi kenan HAFSAT kin tonamin asiri,wayyyo Allah ka kawomin d'auki"
Abunda ta furta kenan k'asa-k'asa idanunta a runtse ba tare da tayi tsammanin wani cikinsu zaiji me ta fad'aba.
A hankali ya furta
"ALHAMDULILLAH ALAA KULLI HALIN!
ALHAMDULILLAHIL-LAZIIY BI NI'IMATIHI TATIMMUS-SALIHAT!!!"
Yanzun kam ya gama samun shaidan da ya bayyana masa itan ce dai wacce yake hasashe d'ari bisa d'ari yanzun ya tabbatar da hakan.
"Amma to ya akayi ta koma haka ne kam?"
Yayima kansa tambayan ba tare da tunanin samun amsa daga gare shiba.
Matsawa yayi a hankali ya d'auke hat en dake kanta tare da sake k'ureta da kallo,ko tantama baya yi yanzun kam daya ga fuskarta ya gama yin amanna akan yak'ininsa gaskiya ne.
"Why KHUBRA zaki nuna baki ganemuba a yanzun?me yasa?me yasa za kiyi haka??"
Cike da tsawa ya k'arashe maganar tasa.
Kuka ne ya kufce mata wanda daga ji kasan mai yinsa cike yake da fargaba da kuma tsoron halin da take ciki,ta jima tana kukan wanda su dake tsaye gurin suka kasa magana sai kallonta kawai da suke yi,ganin bata da niyyan dainawane yasa KHALEEL yin magana
"Ina tunanin yanzu kam ba kuka ne abunda ya kamata kiyi ba,godiya ya kamata kiyiwa Allah da yayi sanadiyyar had'uwarmu,kafin mu wuce gida kuma"
"A'aaaa!! babu inda zani........ni kam babu inda zani........bazan biku ko inaba.........kawai kuyi tafiyanku ku k'yaleni a nan.........bazan biku ba!"
Ta fad'a lokacin da kukanta ya dad'a tsananta,tana ta kuka mai tsuma zuciya.
HAFSAT dake tsaye har lokacin duk abunda ya faru akan idonta,duk wani furucinsu da maganganunsu ya tabbatar mata da akwai wata alak'a tsakanin wad'annan samari da *KHUBRA Y'AR GARUWA* ,cillli tayi da robber dake kanta take ta felle k'afafunta ta yanki hanya sai cikin gari,gudu take shek'awa wanda ba ita ta tsaya ba sai gaban BABA ZUWAIRA dake ta hada-hadar sallamar customer's,cike da haki take maganaa
"BABA kiyi sauri ga KHUBRA can a bayan gari da wasu samari sai kuka take yi kuma"
Ambaton sunan KHUBRA da tayi shi ya dakatar da ita daga abunda take yi ta mik'e tsaye cikin firgici dafe chest enta
"Y'ar nan maza sanar da ni inda kika ganta tun kafin wani abu ya sameta"
Cike da rud'ewa take musamman jin ance KHUBRA'N tana kuka shi ne babban tashin hankalinta saboda tunanin BABA ZUWAIRA a wannan halin samarin tareta sukayi zasu mata "FYA'DE".
HAFSAT a gaba BABA ZUWAIRA a bayanta yayinda tayi k'wallo da kayan abincin ta marawa HAFSA'N baya sunata faman fakaka sauri kamar wad'anda zasu tashi sama..
Kukanta take tuk'uru yayin da ta kuma jajirce kai da fata ba inda zata bisu itakam,suna tsaka da wannan tak'addamar su BABA ZUWAIRA suka iso gurin,har kuma lokacin ta kasa yin shiru daga kukan da take yi.
"Y'ar nan ina fatan kina lafiya"
BABA ZUWAIRA ta fad'a tana shafa jikin KHUBRA'N dake tsaye.
Da sauri KHUBRA ta k'ank'ameta tana sake sakin kuka
"Ni bazan bisuba,a nan zan ci gaba da zama gurinki"
Maganarta ta d'aurewa BABA ZUWAIRA kai cike da mamaki ta d'agota suna kallon juna ta kuma furta
"Yi shiru ki sanar da ni,ina ne baza ki bisu ba?"
"Gida zasu maida ni,ni kuma ba zan bisu ba,ni gaskiya a nan zan ci gaba da zama gurinki"
Kallonsu tayi d'aya bayan d'aya,sai yanzun ta soma d'aukan haske game da lamarin nasu da kuma inda maganar KHUBRAN ta nufa,cike da jin dad'in Allah ya kawowa y'ar tata k'arshen wannan rayuwar k'uncin take fad'in
"ALHAMDULILLAH!Lallai Allah shi ne abun godiya a kowane irin yanayi,Allah ya amshi rok'onmu da addu'o'inmu da muka jima munayi,Allah mun gode maka"
Idanunta d'auke da k'wallar farin ciki take ta magana,kafin talli KHUBRA
"Bai kamata muci gaba da tsaiwa a nanba,muje gida tukun sai muyi magana ina ganin hakan zaifi"
Fuskarta d'auke da wani irin expression da ba zai fassaruba suka mik'i hanya da niyyan komawa cikin gari,inda KHALEEL yayi saurin zuba ruwa a motan ya biyo bayansu dan su kam har sunyi gaba basu tsaya jiran shiga motaba....
《《》》
Shigowanta gidan kenan daga hospital,shima daga dukkan alamu ta dawone dan yin wasu uzurorin kafin ta koma.
Wayanta ne ya shiga kuka a parlor saboda nan ta ajiye hand bag en da ta shigo da shi yanzun,tana shirin shiga kitchen kasancewar gidan babu kowa duk yaran sun tafi skul saboda yau en ta kama monday ne shi yasa take ta komai cikin sauri duk dan ta kammala kafin dawowarsu.
Kukan wayan da ta jiyo shi ya fito da ita daga kitchen en cikin sauri ta d'auka dai² lokacin da kiran ya zama missed,d'an janye key en tayi sannan ta duba number da aka kiratan da shi,kafin tayi wani yunk'uri wani kiran ya sake shigowa cikin sauri ta d'auka
"Assalamu alaikum!SON mutanen DUTSE ince dai ba cewa za kayi kuna hanya ba ko?"
Sai da yayi wani murmushi mai cike da sauti wanda yake nuna yana tattare sa tsantsar farin ciki sannan ya amsa mata
"UMMINAH barka da safiya da fatan duk kuna lafiya"
"Lafiya k'alau muke SON ya mutanen gidan?"
"Wallahi suna lafiya UMMI duk suna gaidaku"
"Muna amsawa kun samesu lafiya dai ko?"
"Ehh!to lafiya k'alau dai za ace,amma dai kam UMMI KAKA ba shi da lafiya kuma ya jima cikin ciwon,ya jikin MAMA?"
"Too HAJIYA MURJA dai kam da sauk'i za ace,ammafa har yanzun tana nan kamar yadda kuka tafi kuka barta,bata san waye akanta ba ni kam wannan ciwo nata yana bani mamaki wollahi,yanzun jiran dawowarku nake muji yanda za ayi gaskiya ciwonta baya buk'atar a zuba ido hakanan,tunda nan en babu wani ci baba da ake samu"
"To UMMI in sha Allah muma muna nan kan hanya nan da anjima kad'an,yanzunma akwai wani abu ne mai muhimmanci da ya tsaidamu,amma idan mun k'araso za kiji labarin koma mene ne wannan abun"
Sai da tayi murmushi sannan ta ce
"To SON Allah ya kawo ku lafiya kuma Allah yasa muga Alkhairi"
Su duka sukayi dariya sannan ya amsa da "Ameen" yayi mata sallama akan sai sun k'araso...
《《》》
Yau tun da ta tashi jikinta yayi zafi saboda zazzafan zazzab'i data tashi da shi,kusan sati uku kenan tana fama amma ta kasa fita taje asibiti ko dan samawa kanta sauk'in ciwon dake damunta..
Shigowar babban mutumin kenan ya shiga cire kayansa kamar ko wane lokaci da hakan ya zame masa d'abi'a,da duk inda yaje ya dawo tofa yana shigowa zai hau tub'ewa kamar wani k'aramin yaro dake son mahaifiyarsa tayi masa wanka.
Saman gadon ya shiga haurowa yana shafata kafin ya d'age gefen duvet en data rufu da shi,cikin jikinta ya shiga k'ok'arin shigewa,ita kuma sai dad'a matsawa baya take saboda a yanzun kam bata jin zata iya tab'uka komai a rayuwanta,sosai ya manna jikinsu da juna duk uban zafin da jikinta yayi hakan bai hana shi fara abunda ransa ke soba,cikin wahalalliyar murya ta bud'e baki iya k'arfinta
"Dan Allah ka k'yaleni yau kam bana jin dad'i gaba d'ayafa kana jin yadda jikina yayi zafi ko wanka na kasa yi saboda rashin k'wari da jikina ke fama da"
Duk maganarta hakan baisa ya saurara mataba,saima shinshinata da yake yana wani fiddo da harshensa kamar kare tare da sakin wani irin numfashi.
"Kinsan dai a yanzu kam yadda nakai wannan matakin ba zan iya jurewaba,babu wani hak'uri da zan iya yi a halin yanzu,kawai dai kiyi hak'uri ki bani had'in kai mu ragewa juna zafi"
Ko d'aya cikin maganganunsa babu ko guda d'aya wanda ta iya ganewa saboda ta kai mak'ura gurin wahala,shi kuma duk da haka bai d'aga mata k'afa ya kyaleta ba,saima dad'a k'ok'ari tare da himma da yake gurin ganin ya cimma burinshi na biyan buk'atarsa.
Ba shi ya kyaletaba sai bayan da ya tabbatar da he is well satisfied,sannan ya sauka a kanta had'e da cilla mata damin kud'i
"Ga shinan kije kiga likita,ni fita zanyi idan kin dawo muyi waya"
Daga haka bai jira jin komai daga bakinta ba ya shige toilet en hotel en,har ya gama shirinsa ya fice MA'U na kwance ta kasa tab'uka komai kuma bata d'aga kai ta kalle shiba,da k'yar ta iya lallab'awa ta yi wanka shima jikinta sai kyarma yake haka dai ta shirya ta fice tare da kulle k'ofan ta nufi hospital...
《《》》
Lokacin da ya gama waya da UMMI yayi dai² da isowarsu k'ofar gidan,yana kallonsu suka bud'e gidan suka shiga,hakan ne yasa shi fitowa shima ya kulle motan sannan yabi bayansu.
A tsakar gidan ya tarar da su suna zaune kan tamarma sunyi jigum-jigum.
Guri ya samu ya zauna,sannan suka gaisa da BABA ZUWAIRA wacce KHUBRA ta kanainaye kamar wani yace zai tafi da ita duk ta hanata sukuni.
"Samari duk da dai ganinku nayi sama ta ka,hakan ba zaisa nayi saurin yanke hukunci ba,nasan dai duk inda akaje aka dawo kuna da alak'a da KHUBRA kuma alak'a mai k'arfi,duba da ganin yadda kuke kama da juna"
Kallon-kallo akayi tsakaninsu su uku kowa na burin gano abunda BABA ZUWAIRA ke fad'a a tare da d'an uwansa hatta da kuwa ita kanta KHUBRA dake kwance sai da ta d'ago tabi su KHALEEL da kallo.
"Tabbas ku en y'an uwane na hak'ik'a ko ban tambayaba nasan ku yayunta ne"
Tana magana da fara'a akan fuskarta tana kuma binsu da kallo,tun kafin BB yayi magana KHALEEL yayi tsalle ya dire da fad'in
"K'warai kuwa mu yayunta ne,tun bayan b'acewarta da muka yi neman bamu sametaba wanda ya had'a da jami'an tsaro a ciki,kaf cikin gari sai da aka dubata amma ba a ganta ba,ashema tana kusa-kusa damu kawai dai Allah ya nufa hakan dai sai ya faru"
Yayi shiru yana kallon BB daya kafe shi da kallo,ita kuwa KHUBRA kanta ta sauke k'asa tana sauraron maganganunsu.
"To ALHANDULILLAH tunda dai yau Allah ya nunamin wani naki KHUBRA kuma in sha Allah a yau ba sai gobe ba zaki bi danginki ku koma gida,saboda dama zamanki tare da ni ba shi ne mafi a'ala ba,ki zauna tare da danginki shi ne babban kwanciyar hankali kuma kema da su duk zakufi samun nutsuwa saboda kuna tare da juna.
Ni da kike tare da ni Allah ne ya had'amu kuma ina fatan Allah ya sake sadamu cikin amincinsa da alkhairinsa,yanzu zan baku labarin yadda akayi na samu KHUBRA da kuka ganmu tare"
Take ta shiga labarta musu yadda akayi suka had'u da zamansu tare tun daga ranar da ta fara ganinta kawo yanzun da suke zaune suna sauraronta ba tare da ta b'oye musu koda wasali ko harafi ba.
Jikinsu duk yayi sanyi kan irin wahalar da ta sha da irin rayuwar da tayi duk da kuwa sun ganta kan sana'ar tata,kallon tausayi had'e da al'ajabin yadda ta juri wahalar sana'ar suke binta da shi kafin daga bisani suka sako maganar tafiya da KHUBRA'N.
Haka BABA ZUWAIRA ta shiga d'aki ta had'a kayan duk data san na KHUBRA'N ne ta fito,tana d'an matse idonta da k'walla ta tarun mata.
Mik'ewa sukayi cikin shirin barin gidan,nanfa KHUBRA da BABA ZUWAIRA da suka ga dai tabbas tafiyar nan zasu yi,suka k'ank'ame juna suna kukan rabuwa da juna a lokacin da d'ayansu bai tab'a tsammanin faruwar hakanba.
KHALEEL ne ya ja BB gefe yana fad'in
"MAN baka jiba"
'Dan matsawa BB yayi jikin KHALEEL tare da kallonsa yana d'aga masa kai
"Gaskiya a shawarana ina ganin rabasu yanzun akwai damuwa duba da yadda suka shak'u da juna,ina ganin me zai hana mu tafi da su duka kaga ta wani b'angarenma BABA'N zata mana amfanifa ko kuwa me kake gani?"
Shiru BB yayi yana hasashen maganar KHALEEL en sannan kuma ya d'an daki kafad'ansa
"Yeahhh!ka kawo shawara mai kyau kawai muyi hakan"
Komawa gurin da su KHUBRA suke tsaye sukayi har lokacin suna manne da juna,KHALEEL yana y'ar dariya yace
"Ina ganin BABA da kun daina kukan nan haka nan,saboda mun yanke shawaran tafiya dakune duka"
Da sauri KHUBRA ta d'ago kanta ta kalleshi,shi kuma ya kad'a mata kai dan ya fuskanci so take ta tabbatar da abunda ya fad'a.
Aiko da sauri ta shiga gogewa BABA ZUWAIRA hawayenta itama ta goge nata tana dariya,cikin sauri ta shiga d'akin ta d'ebowa BABA ZUWAIRA kaya sannan suka d'unguma suka fice daga gidan,sai da ta shiga mak'otanta tayi musu sallama,tukun ta dawo inda ta barsu a k'ofar gidan jikin mota,daga nan suka shige tare da d'aukan hanya sai cikin gari wato cikin k'waryar KANON DABO.......................