*B* ayan k'ura ta lafa komai kuma ya dai-daita an gama jimamin abubuwa da suka gabata sannan kuma an shaidawa ABBA'N KHUBRA labarin yadda ta rayu a gurinsu a matsayin y'ar aiki da kuma matsayinta yanzun a gurinsu,daga nan kuma suka gangara kan mak'asudin zancen daya kawosu garin.
Sosai yayi farin cikin abunda suka sanar masa,daga nan ya shaida ma ABBA'N BB cewa
"Duk abunda kaga ya dace ka aikata SAFWAN ba sai ka neme niba idan ya so daga baya naji hukuncin daka yanke,saboda KHUBRA y'arka ce kuma bayan haka kuma kuna da hak'k'i akanta a matsayinku na iyayenta kuma dangin mahaifiyarta..."
Wannan karramawa da ABBA'N KHUBRA yayi masa yaji dad'inta,take kuwa shima ya yanke nasa hukuncin inda yace
"To Alhamdulillah! da Allah yasa al'amura suka kasance haka,gaskiya nafi kowa farin cikin faruwar hakan,amma magana biyu gareni zan fad'a yanzun kuma ba ga kowa ba sai kai MALAM BUBA"
Nan suka sake maida hankali gurin ABBA don jin me kuma zai fad'a
"Ina ganin a yanzu tunda abubuwa da dama sun faru zan nemi wata alfarma a gurinka..."
ABBA'N KHUBRA ya kalleshi yana murmushi yace
"Fad'i duk abunda kake so ni kuma in sha Allah idan baifi k'arfina ba zanyi maka"
Murmushin shima ABBA yayi sannan yace
"Ai nasan baifiba ma,amma dai bari mu gani.......Ba komai zan fad'a ba dama illa ina so nace maka.....tunda Allah yasa yanzun baka da kowa a garin nan mai zai hana bazaka bimu mu koma can birni tare ba,kaga kaima zakafi samun kwanciyar hankali ace kana ganin y'arka a kowane lokaci,behind ma kuma yanzun ba iyali gareka ba,sannan banajin a garin nan kana da wani d'an uwa ko kuwa me kuke gani...?"
"K'warai wannan maganar da kayi nima Allah ne yasa ban yitaba amma nima hangena kenan"
ABBA'N KHALEEL ya fad'a yana murmushi
Ga ABBA'N KHUBRA kuwa yaso musawa buk'atar tasu ganin yadda suka jajirce yasa shi amincewa..
Kowa ka kalli fuskarsa cikin mutanen gurin babu komai samanta face farin ciki da annashuwa.
Bayan wucewar wani lokaci komai ya lafa an kuma gama yanke shawara game da hukunci,shirin tafiya ya kankama in da ABBA ya kammala had'a kayansa aka sasu a mota,gaba d'aya sun mik'e da niyyar kama hanyan komawa inda suka fito..
Suna shirin fita ZUHRA ta kalli ABBA tana fad'in
"ABBA ai kunyi mantuwa..."
Duka suka juya suna kallonta da neman k'arin bayanin mantuwar da sukayi
LADIYO ta nuna musu dake cikin rumfa sai kallonsu take da fuskar munafukai musammanma KHUBRA data koma kamar baturiya dan kyau data k'ara,sai lokacin LADIYO ke nadama game da dana sanin bata aikata abunda tayiba duba da yadda KHUBRA'N ta koma,lokaci guda ta bayyanar mata a matsayin y'ar dangi mai cikakken asali,komawa tayi wata kalar tausayi ganin irin kallon da mutanen gurin ke mata.
A fusace ABBA'N KHUBRA yayo kanta yana fad'in
"Bak'ar munafuka al-gunguma kinzo kin ficemin a gida ko kuwa saina raunataki"
Wani ice ya rarumo faskare guda ya dumfarota da shi,da sauri ABBA'N BB ya rik'e shi yana murmushi had'e da girgiza masa kai
"Haba MALAM BUBA me zai kaika aikata abunda ko a baya baka aikataba,kana so ne ka k'arasa gawar da ba taka bane?...."
Da sauri kuma ya tsaya harara ya aika mata sannan ya jefeta da icen,aiko nan ta juya da niyyar guduwa d'aki icen ya sauka a tsakiyar bayanta ji kake timmm,wani ihu ta kurma su ko su ZUHRA,ASHNA,FATAHIYYA me za suyi inba dariyaba,tsabar mugunta harda rik'e ciki,BB ya kallesu yana fad'in
"Dillah ku rufawa mutane baki,ko meye abun dariya a nan kuma ohooo...."
Kyal-kyalewa KHUBRA tayi da dariya dan ita sai a lokacin da yayi magana tata dariyar tazo,nan ta shiga dariya saboda mugunta irinta KHUBRA baya ga hawaye harda durk'usawa a k'asa tasa hannu ta dafe gefen cikinta..
Kallonta yayi yana dad'a d'aure fuska,lallaima yarinyar nan ta raina shi,banda iskanci shi zai musu magana ta tsaya tana masa dariya,lallai ko zata bawa mutanen garinsu labari idan suka had'u..
Lower lip nasa ya cije yana kallonta k'asa-k'asa fuskar nan a had'e kamar bai tab'a dariyaba,ZUHRA data kalli yanayinsa da sauri ta dunguri KHUBRA tana nuna mata BB,d'an bakinta ta murgud'a k'asa-k'asa tayi magana
"Ina ruwana to da shi....."
Abunda KHUBRA bata saniba tsaf BB yaga abunda sukayi kuma yaji maganar da tayi,kwafa yayi had'e da girgiza kansa..
"Kinzo kin fice ko kuwa sai na danganaki da gaban mai gari?..."
"Wollahi MALAM ban san ina zaniba bani da kowa sai MA'U ita kuma ban san ina takeba a fad'in duniyar nan,dan Allah ka rufamin asiri dan sonka da manzon rahama kada ka koreni,idan ka koreni ina zani.....?"
"Ke dallah dakata ina ruwana da inda zaki?? ni yanzu bani da alak'a ta kusa ko ta nesa dake,tun wuri kuma ki zo ki fice kafin na fusata jikinki ya kuma gaya miki ina fatan kinji dai abunda na fad'a miki....."
Kuka wiiwii take tana bashi hak'uri amma bai biya ta kantaba,nan suka fice daga gidan,haka LADIYO ta k'ullo y'an kayanta ta fito tana kallo MALAM ya sawa gidan pad lock ya rufe gidan,sannan suka d'au hanyan komawa....
Maimakon su d'auki hanyan KANO sai gani suka yi BB dake driving ya yanke hanya,cikin garin DUTSE ya nufa,babu wanda yayi magana cikin iyayen da suke zaune,a tunaninsu a kwai abunda zaiyi a garin,basu tsinci kansu a ko inaba sai k'ofar gidan KAKA,parking yayi sannan suka fita gaba d'aya da masu son tambaya duk sun yi shiru,jikin ABBA'N BB da kuma ABBA'N KHUBRA duk yayi sanyi saboda su kam ko daga mafarki suka tashi aka kawo su nan sun gane ko ina ne,su kuma y'an matan babu wacce tayi tunanin wani abu game da gidan da suka zo.
BB da KHALEEL na gaba,basu tsaya shawara ba suka shiga gidan su KHUBRA na bayansu har cikin gidan,su ABBA na waje suna shawaran yadda zasu fuskanci KAKA dan dukansu masu laifi ne a gare shi,har basu sanma y'ay'an nasu sun shigeba.
Da sallama suka shiga kamar zuwansu na farko haka tsakar gidan yake cike da mutane sunata aikace-aikacensu game da hirarraki irin na mutanen k'auye,bayan sun gaisa da matan gidan kai tsaye suka nufi turakar KAKA dan sun san kam yana nan kamar yadda take a wancan lokacin,da shigarsu cikin turakar suka tarar da KAKA na karatun AL-QUR'AN saboda hadda gare shi,sai da ya kai aya sannan ya amsa musu sallama'n da sukayi,nan BB da tsokana yace
"Sadak'allahul-aziiym tsoho mai ran k'arfe,ashe a kwai tsohuwar hadda bata guduba..."
Dariya KAKA yayi sannan yace
"Yo an fad'a muku haddar da mukayi irin taku ce ta yanzu,mu gwagwarmayar da mukayi ai ko rabi baza kuyiba....Idan kuma ka musa to mu gwada mu gani waye zai nasara..."
Gaba d'aya suka sa dariya har y'an matan sannan suka gaisa,kallon y'an matan yayi yana murmushi kafin yayi magana su ABBA suka shigo da yake ABBA'NSU BB ne a gaba hakan yasa KAKA baiga na can bayaba,kallon ABBA yayi yana murmushi sannan ya fara magana
"Idonka kenan ko SAFWAN..."
Sunkuyar da kai ABBA yayi k'asa ba tare da yayi maganaba
"Kayi hak'uri BABA ka kuma yafemin dan Allah,komai daya faru nima ba a son raina ya faruba...."
"Ai shi kenan Allah ya yafe mana baki d'aya...."
Gaisuwa ta musamman akayi ga kaka,nan KAKA ya sake kallon BB yana fad'in
"ABOKINA wad'annan y'an matan kumafa ?"
Dariya BB yayi dan yasan da shi yake
"Baka sansuba ko...?"
"To banda abunka da na sansu zan tambaya ne.....?"
Gabatar masa da su yayi a matsayin jikokinsa da bai saniba sai yanzun....
Dariya KAKA yana kallonsu duka,ABBA ya kalleshi yaga yana kallon KHUBRA,d'an murmushi yayi yace
"BABA ka santa ne....?"
"Gidanku SAFWAN ni kuma na zama abun tsokana ne kam a gurinka?"
"A'a BABA naga kana kallonta ne kamar ka santa..."
'Dan murmushi ABBA yayi sannan ya kalli KHUBRA dake murmushi ya kuma kalli KAKA yace
"To tunda ka santa fad'i wace ce....?"
Bud'ar bakin KAKA yace
"Yo wannan kam duk wanda ya kalleta ya ganka ai yasan y'arka ce ba sai an tambayaba....kuma har mene abun wahala anan da zaku sani gaba kai da d'anka daga zuwanku,ce muku akai bazan ganeba ne...?"
Dariya suka sa mishi saboda paul daya buga gurin fad'in ko wace ce
"Haba BABA ka dai sake kallonta sosai dawa take maka kama"
Sake kallonta BABA yayi sannan ya kalli ABBA yace
"Nifa bana son shegantaka yo to dawa take kama idan ba da kaiba...."
Sai da suka gama wana shi sannan ABBA yayi gyaran murya,duka suka juya suna kallonsa
"BABA dan Allah duk abunda zaka ji a yanzu ina so ka maida shi ba komaiba,kayi hak'uri ka yafewa wad'anda suka maka laifi,nasan kasani sai dai tunatarwa dan Allah BABA..."
Murmushi KAKA yayi masa ba tare da yayi maganaba,kallon KAKA ABBA yayi sannan ya kalli KHUBRA a hankali yace
"BABA wannan da kake gani tabbas y'ata ce amma bani na haifeta ba.....jikarka ce ta wajen y'arka FALMATA....."
KAKA dake kwance idan zai tashi sai an taimaka masa jin an ambaci FALMATA bai san lokacin daya mik'e zauneba da kansa.
"Ka ce me SAFWAN...? Shin kam yaushe na fara wasa da kai kamar haka?..."
"BABA sam cikin maganar da nayi babu wasa a ciki,jikarka ce y'ar wajen FALMATA..."
Kallonta KAKA yake tabbas ga kammani nan,sai dai kuma abunda yasa yace y'ar SAFWAN ence kaf gidan kuma kaf cikin y'ay'ansa su biyu suke kama da juna,ko wasu tagwayen da ake haifarsu identical baza su nuna musu kamaba..
Hawaye KAKA ya shiga yi na tausayinta yana mik'awa KHUBRA'N hannu,da rarrafe ta isa kusa da shi sosai ya rik'eta ita ko data samu abunda take so nan ta kwantar da kanta kan laps en KAKA feeling so happier take jinta saboda kasancewarta y'ar dangi kuma gata tare da su.Kanta KAKA yake shafawa lokacin daya goge fuskarsa,nan kuma aka shiga maida zancen abunda ya faru baya,sai a lokacin KAKA ya hango ABBA'N KHUBRA dake zaune da tun shigowarsu kansa na k'asa sai yanzun daya d'ago KAKA ya kula da shi..
"Idonka kenan kaima ko ABUBAKAR?...Shi kenan kuma tun daga waccan ranar baka sake dawowaba...na sani dukanmu munyi ba dai-daiba daga mu har kai,kuma sai daga baya muka gane kuskuren da muka aikatawa yarinyar da bata jiba bata ganiba,tabbas dukanmu munyi laifi kuma sai Allah ya saka mata hak'k'inta da muka d'auka....ki gafarta mana JIKATA....."
Yanayin da KAKA yayi magana shi yasa jikin ABBA yin sanyi duka sai yaji ya muzanta a gabansa,nan ya shiga neman yafiyarsa....
Bayan nan kuma ABBA ya tambayi KAKA shin ko FALMATA tana nan ko kuwa wani auren ta sake yi..
Sai da KAKA ya matse idanunsa sannan ya shiga basu labarin tun daga ranar da ABBA ya dawo da ita gida da kuma irin yadda suka yi gwagwarmaya gurin karb'ar KHUBRA da yayi ya kaiwa mahaifinta,a lokacin da yake cikin fushi...sannan ya d'ora da fad'in
"To tun daga wannan ranar ne kuma ta shiga damuwa saboda abunda na aikata akan y'arta d'aya tal,daga lokacin ta sakama kanta damuwa sosai wacce a k'arshe duk bamu fargaba,sai da ciwo yaci k'arfinta bayan shekaru data shafe tana tare da ciwon har ciwo yaci ya cinye jikinta,yau kimanin shekaru bakwai (7) kenan da rasuwarta...Sai dai kafin rasuwarta ta bar min wasiyyar ko da zaka zo wani lokacin in sanar maka cewar ta yafe maka abunda kayi mata,kuma itama tana neman ka yafe mata."
Kowa dake cikin parlor'n sai da yaji mutuwar MAMA'N KHUBRA,tare kuma da nema mata yafiyar mahalicci...
An yafewa juna an kuma maida abunda ya wuce ya riga ya wuce,sannan an rungumi juna,dangi ya dad'a had'uwa bayan d'umbin lokaci da aka d'auka a tarwatse,tsintsiyar data tarwatse ta koma cikin mad'aurinta....
Sai yamma lokacin duka gida an had'u kowa nata murna da farin cikin ganin d'an uwansa,KAKA ya sake gabatar da su a matsayin y'ay'a da jikokinsa da ba kowa ya sansuba...
ABBA'N KHALEEL ne ya matsala kusa da KAKA nan ya sanar da shi dalilin zuwansu garin,na neman auren KHUBRA da KHALEEL yake son yi,sosai gidan kowa yayi murna da jin hakan,bayan an gama magana aka dank'a alhakin yanke ranar auren ga KAKA a matsayinsa na SHUGABA,yaji dad'i sosai bai yi wata-wataba ko ya dank'ara yanke lokaci nan da makonni takwas wanda yayi dai-dai da watanni biyu kenan masu zuwa.....Nanfa murna ta dad's k'aruwa fiye data farko.
BB kam jin wannan maganar da kuma hunkuci na KAKA ba k'aramin tada masa da hankali yayi ba,da k'yar yayi ta maza ya danne damuwarsa a lokacin,har aka gama duk maganar da za a yi kansa na k'asa dai-dai da sau d'aya baiyi kuskuren d'agowaba bare wani ya fuskanci yanayin da yake ciki..
Wajejen Maghreeb sukayi sallama da kowa kan zasu koma,bakin KHALEEL kam sam yak'i rufuwa saboda farin cikin da yake ciki a yau,bayan sunma mutanen gidan sallama kan zasu koma amma zasu dawo bada jimawaba,har bakin mota su OLD KHALEED suka rakosu sai da sukaga barinsu a line en sannan suna koma gida cike da murna da far in cikin al-amarin d'aya wakana a wannan rana.
KHALEEL ne ya amshi driving tunda a zuwa BB ne ya kawosu garin,godiya BB yayiwa Allah daya sa ba shi zaiyi driving ba,dan yana da tabbacin idan shi ne to babu makawa kam k'arshe sai dai su tsinci kansu a jirkice gefen k'walta.........
Tafiyar yau ta zama tarihi a garesu gaba d'aya family'n kowa na farin cikin yadda tafiyar ta kasance idan aka cire BB da wani gefe na zuciyarsa babu komai cikinsa face tsantsar k'unci,idanunsa da take jin sun masa nauyi ya rufe kamar mai bacci duk wani yanayinsa KHALEEL yana kula da shi,shi kam sababbin halayen da aminin nasa ya bijiro da su a kwanakin suna bashi mamaki matuk'a,shiko BB gani yake hakan da yayi shi yafi masa,a gurinsa kam cewa yayi wannan itace MAFITA a tare da shi....
*TAMBAYOYI......*
_Game da littafin *Y'AR GARUWA*.._
1-Shin a cikin wannan littafi wane ne jarumi & jarumar ku??
2-Wane mutum ne yafi burgeka/burgeki??
3-Wane mutum ka/kika fi tsana a ciki???
4-Wane mutane kukafi so a cikin wannan littafin???
5-Mene ne kuskuren mabuciyar a cikin labarin nata??
6-Shin yaya matsayin wannan littafi yake a gurinku???
7-Idan akace ka/ki bawa wannan littafi mark,mark nawa kuke ganin zai karb'a daga gurinku??
8-Shin kuna son wannan littafin ko kuwa??
_Sai munji daga gareku......_
*Comment for more page's....* 💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA.~*
*_#®EAL $MASHER._*
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*23/ʝųlყ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~__________________________~*
_Naga comments enku kuma naji dad'in hakan sosaifa,sai dai k'orafinku gareni akan *MAMA'N KHUBRA* mafi yawancinku amsarku iri d'aya ce *"BAI KAMATA NACE TA MUTUBA"* sai dai abu d'aya nake son tunasar damu shi ne,itafa mutuwa wajibice akan ko wane bawa,walau ka shirya ko baka shiryaba,tabbas idan lokacinka yayi dole ne ka amsa kiran mahalicci,kuma wannan novel en da kuke gani ba wai zance muku true life story bane,just na k'irk'ire shi ne amma kumin afuwa tunda haka ya faru,dama tun farko haka na tsara labarin so ina ganin ba abun damuwa bane dan an rasa mutum d'aya a cikin labarin,sannan hakan shi ne solution ga MAMA'N KHUBRA dama su kansu ahalinta coz koda ace tana raye tofa kada ku manta abunda aka mata k'azafinsa ba zai tab'a gogewa ba,kunsan k'azafi a kwai ciwo sosai,so ina neman afuwanku..._
_Fatan Allah yasa muyi kyakyawan k'arshe....Ameen._
*Really luv u fan's..* ♥
*~__________________________~*
*DON ALLAH INA ROK'ONKU DA KU DUBI GIRMAN ALLAH DA YANAYIN YADDA NAYI MAGANA DA MANYAN BAK'AK'E,DAN ALLAH KUYI HAK'URI DA YA'DA JITA-JITA AKAN WAI ANYI KIDNAPPING SIS ENA,SISINA TANA NAN CIKIN K'OSHIN LAFIYA KUMA BABU ABUNDA YA SAMETA CIKIN HUKUNCIN ALLAH TANA NAN SAIMA K'ARIN LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI DA TAKE DA'DA SAMU FIYE DA BAYA,MASU YI DAN ALLAH KUYI HAK'URI HAKANAN,DAN BAMU SAN DAME ZAMU JIBA DA SAK'ONNINKU KO KUWA DA CIWON MAGANAR KIDNAPPE EN,INA FATAN ZAKU FUSKANCI NUFINA...MUN GODE.*
_Stay wealthy *CWEET SIS HABIBA IDREES (HUBBEEY)* nd now i turn ur name into *INDO K'AFAR.........* 😉💔
*~__________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
5⃣1⃣
*S* ai misalin k'arfe 10:00pm suka iso gida,a gida'n UMMI suka fara yin branch inda ABBA'N KHALEEL da KHALEEL suka fara sauka,bayan sun musu sallama kuma BB ya amshi driving,ikon Allah kad'ai ya kaisu gida,yana yin parking bai tsaya jiran fitansu ba ya fice a motan ya nufi cikin gidan.
Yanayin yadda yake tafiya kad'ai ya isa yasa a gane akwai matsala a tattare da shi,saboda yadda yake tafiya a durk'ushe dafe da side en k'irjinsa na hagu.
Da yake kowa a gajiye ya dawo saboda zaman motan da suka d'iba coz tafiyan yini guda akwai wahala,babu wanda ya lura da yanayinsa kowa ya shige nasa gefen.
ABBA kad'ai aka bari tare da ABBA'N KHUBRA,shima bayan daya nuna masa gefen da zai zauna sukayi sallama ya wuce shima.
Gidan shiru daga dukkan alamu mutanen gidan sun jima da yin bacci,hakan ce kuwa ta kasance dan wasu kam a lokacinma basu san inda kawunansu sukeba.
HAJIYA MURJA na d'aki ta kishingid'a,tana nan ta jiyo shigowansu gidan da motsinsu amma sai bata yi yunk'urin fitaba,har zuwa lokacin da ABBA ya shigo,nan ne tayi masa barka da dawowa,da mamaki ya kalleta yana fad'in
"A'a dama bakiyi bacci bane madam?...da naji gidan shiru haka nayi tsammanin ko har kunyi bacci nema..."
'Dan murmushi tayi kafin ta bashi amsa
"Uhmmmm! ta yaya zan iya bacci yanzun bayan ban san a wane hali yarana suka kasanceba..."
Teasingly ya kalleta da salon tsokana fal saman fuskarsa lokacin yana shirin zama kusa da k'afafunta
"Ke dai fad'amin gaskiya y'ay'anki kikafi damuwa da su ko kuwa mijinki....?
Baki bud'e take kallonsa
"Wane irin kuma miji y'ay'an dai...."
Dariya sosai maganarta tasa shi wanda ganin yanayin yadda yake yasa ita da kanta itama sai data dara
"Tohh! tunda kince haka let's see the truth....."
"Wane irin gaskiya kuma kake buk'atar gani a wannan maganar....?"
Winking yayi mata
"Ahhhh! ya wuce na nemi wani d'akin na kwana,tunda ni ba a buk'ar sanin nawa damuwan..."
Cikin sauri ta katse shi
"Aaaaa! nifa ba haka nake nufiba,kawai dai nace haka ne saboda kaga su yara ne ba wani girma garesuba,bayan haka ma kuma basu tab'a tafiya dogo kamar hakaba...."
Duk maganar da takeyi tana yi ne da kanta a langab'e kamar wata yarinya,koda yake za a iya ce mata yarinya,ammafa a gurin mijinta.
Cike da nishad'i suna tsokanar juna suka kwanta,bacci mai cike da kwanciyar hankali kam wannan family sun same shi,musamman b'angaren ABBA'N BB,ABBA'N KHUBRA,KHALEEL,dama sauran tawagar tafiya except one person.
A b'angaren BB kuwa tun daya samu ya shige bed room nasa,yayima Allah godiya kan bed ya zube zuciyarsa kamar zata faso chest ensa ta fito,duk lokacin daya tuna abunda ya faru a yau sai yaji zuciyarsa na masa k'aik'ayi ji yake inama bai san KHUBRA da KHALEEL ba a tsahon rayuwarsa da ya fi masa alkhairi sama da wannan al'amarin daya faru..
Da k'yar ya samu bacci ya d'auke shi shima sai gabanin salla'n asubah,bacci yake amma duk wanda ya kalleshi zai iya gano babu komai cikin baccin nasa face zallan wahala....
《《》》
Tun daga ranar da BIGGY ya yankama yaransa warning dai-dai da sau d'aya babu wanda ya kuma kuskuren yi masa shaye-shaye,tun daga ranan suka shiga hankalinsu,saboda tun kafin wannan lokacin suka san halinsa bare kuma yanzun da suke ganin ya canja wasu sabbin halaye dan yanzun ba kamar da bane..
Ranar Mondy kamar yadda aka buk'aci yaje *REVENUE OFFICE* en,aiko ya shirya da takardunsa a envelope ya fice,bai jira d'aukan motaba don a cewarsa idan suka ganshi a mota da matsala danko yana da tabbacin ba zasu tab'a bashi offer en aikinba.Babban dalili kenan da yasa BIGGY yake faman yawo a NAPEP.
Cikin hukuncin Allah aka masa interview ya kuma samu nasara inda suka mik'a shi b'angaren accountant da yake fannin *ECONOMICS* ya karanta,kuma babu laifi result ensa yayi kyau.
Aiki yake ka'in da na'in,babu damuwar komai a tare dashi hakane yasa shi bayan samun wannan nutsuwar da gyara halayensa da yayi ya yanke shawaran ziyartar danginsa,bayan zuwansu garin nasu ya tarar da baffaninsa na cikin matsananciyar buk'ata da rashi,taimako ya basu wanda su da kansu sai da wasu cikinsu suka zubarda hawaye saboda suka banzatar da rayuwarsa a bayan rasuwar mahaifansa wanda gini ya zubowa lokacin da suke tsaka da bacci,daga lokacin kuma da rik'onsa ya koma hannun kishiyar mama'nsa wacce ta azabtar da dashi na tsayin wani lokaci bai sake samun kulawa daga gurin dangin mahaifin nasa ba bare ya san muhimmancin su gare shi,wahalar yau daban ta gobe daban har ta kai da tana sa shi y'an sace-sace da haurawa gidajen mutane yana kwasowa yana kawo mata,ganin babu abunda take bashi ko da ya sato mata goal ne kuwa shima daga bisani ya gudu coz ko abinci ta girka rabonsa a ciki k'anzo ne,babba'n dalili kenan daya sashi guduwa don neman na kansa kuma ya tsaya da k'afafunsa ta hanyar ci gaba da wannan sana'a,wanda a lokacin daya baro k'auyen nasu ya kammala makarantar primary har ya shiga k'aramar secondary,bayan dawowarsa birnin kano'n dabo kuma bai zauna hakaba sai da yayi duk wani k'ok'ari da zaiyi ya maida kansa makaranta babban gata kenan da BIGGY yayiwa kansa a rayuwarsa ta baya.
Yasha sa albarka gurin dangi da suka guje shi abaya,wanda kafin ya dawo bakin aikinsa sai daya sanarwa baffanin nasa buk'atarsa ta zuwa nema masa aure cikin wani sati,babu musu bare jan lokaci duka suka amsawa buk'atarsa tare da yi masa alk'awarin zuwansu cikin weekend,ba don komaiba kuwa sai dan ganin yanzun yana cikin rufin asiri sannan kuma shi zasu mora ba shi zai moresu ba..
_Duniya kenan...._
《《》》
A safiyar ranar ta lahadi gaba gidan basu iya tashi da wuriba kasancewar akwai gajiyar tafiya tattare da su wannan dalili yasa gidan yake shiru,misalin k'arfe 10:00am suka fara fitowa d'aya bayan d'aya.ZUHRA data riga su tashi ta nufi d'akunan baccin nasu tana tashinsu,gurin KHUBRA ta dawo data bari a bed room coz su tare suke kwana suke tashi tun bayan bayyanarta komai nasu tare suke yinsa.
"Yawwa CWEETY ki tashi kinga yanzun ABBA yace yana son ganinmu duka a parlor.."
Juyi tayi tana bud'e idanunta da suka mata nauyi coz baccin bawai ya isheta bane,da kyar ta tashi ta shirya,a parlor ta tarar da su sun hallara suna shirin yin break fast.
Kusa da ZUHRA ta zauna ABBA ta fara gaisarwa sannan MAMA,sai kuma sauran y'an uwanta data tambaya lafiyarsu da yadda suka tashi.
Fuskokinsu babu alamun damuwa suke break,ABBA ya kalli yaran gaba d'aya cikin so da kulawa
"Ina BB ne kam...? Gaba d'aya kowa yana nan banda shi ko baccin ne bai sake shiba har yanzun...?"
Dariya sukayi duka gurin
"ABBA kaima ka koma ce masa BB ne?"
ZUHRA tayi tambayan tana dariya dan tasan ABBA da tsokana ya fad'i hakan
"Aaaaa! to nima ba dole na koma fad'in haka ba,nima ai naga BB ena ne ko....?"
Yayi tambayan yana kallon MAMA da take dariyan drama'n nasu
"To ai ABBA baka san me yasa muke fad'an hakaba...."
Kallonta yayi yana murmushi
"Ku rik'e dalilinku nima na rik'e nawa....Kuma dai duk da haka nima da BB zan kira shi ko kuna so ko baku so.."
All family en they were happy da wannan moment's da suka tsinci kawunansu aciki,MAMA ma ba a barta a bayaba dan ABBA ya sanar da ita komai game da matsayin KHUBRA a gurinsa,sai yanzun idan ta kalleta take jin kunyar abubuwan da suka aikata mata ita da su ASHNA lallai ta dad'a tabbatarwa da ubangiji baya bacci kuma duk wanda ka zalunta yana gaggawa tare da saukar maka da naka isharar,ta kuma dad'a godewa Allah daya sa KHUBRA'N ta bayyana ba tare da wani yaci zarafinta ba,da ace wani abu ya sameta to tabbas bata san kuma da wane ido zata kalli ABBA ba saboda gungun laifuka da ta aikata,ita kam wannanma kad'ai ya isheta hujja da zata kafa idan taga wani mai irin halinta.Har yau kuma tana dad'a neman afuwar Ubangiji kan laifuffukanta.
Bayan sun gama break aka koma hira,suna tsaka da hira KHALEEL yayi sallama,ZUHRA ce ta dunguri KHUBRA cikin rad'a take mata magana
"CWEETY ga oga nan ya zo ina fatan zaki bashi kulawa ta musamman"
Uwar harara KHUBRA ta maka mata,d'an bakinta ta dad'a tsukewa tana kallonta k'asa-k'asa ta furta
"Bafa nason iskanci kin sani..."
"Dillah wane iskanci,madam idan zaki zage ki bashi kulawa to idan kuma ba hakaba to y'an matan zamani sayi miki k'afa d'aya...."
Still tayi tana kallon ZUHRA da bakinta a bud'e
"Heeyyy! beb ki rufe bakin kada flies su cike miki shi..."
"Uhmm! Allah ya baki lafiya dan naga kina buk'atan addu'ah..."
Aiko ZUHRA ta amsa da ameen tana mata gwalo,bata sake kulata ba duk yadda taita tsokanarta,ganin tak'i biye mata yasa ta mik'e ta nufi bed room enta,cikin closet enta ta bud'e tana duba wani gown nata da take mutuwar so,a jikinsa leda en ta fad'o,da sauri ta tsuguna tana d'auko ledan tunanin inda ta same shi take,can kuma ta tuna yadda akayi ta mallakeshi ita sam ma ta manta da shi sai yanzun data gani ta tuna da tsawon lokacin daya d'auka a ajiye,d'an bud'ewa tayi tana fiddo kwalin ciki phone ne sabo mai maituk'ar kyau,zaroshi tayi duka tana dad'a dubawa,daga bayansa wani farin paper ya fad'o da mamaki ta d'auka ganin kamar letter ne ciki nan ta shiga ware shi a hankali kuma ta shiga bin kalmomin dake rubuce
*DEAR CWEET SIS.*
_"Am so sorry lil sis! nasan hukuncin dana yanke baza kiji dad'in saba sai dai babu yadda zanyi hakan ya zamemin dole,ba komai yasa na rubuta miki wannan short note enba sai kan wani dalili nawa......na yanke hukuncin tafiya don barin k'asar saboda samun nutsuwar zuciya ba don komaiba sai dan soyayya da take neman salwantar da ruhina....sai dai kash na makaro saboda wadda nakeyi dominta bata sanma ina yiba,behind kuma wani ya rigani,ina rok'onki daki tayani da addu'ah sannan kuma kada ki bawa kowa labarin abunda ya faru duk da nasan a lokacin da zaki samu wannan sak'on nayi nisa da ku......ga phone nan ko da wani abun ya faru a gida zamu dinga magana dake,idan na sauka a inda naje zan nemeki,ina muku fatan alkhairi...na barku lafiya.._
_Ur's BB..._
Ai ZUHRA na idar da karatun wasik'ar hankali tashe ta fice daga d'akin bata zame ko inaba sai hanyan bedroom ensa tana rafka masa kira,har ta shiga bata dena kiransaba,kaf d'akin ta kalla babu kowa ciki hankalinta a mugun tashe ta zube a gurin tana sakin kuka..
"Me yasa BB zakamana haka....ko mai yayi farko ai yana da k'arshe,ni kam bazan tab'a bari ka rasa farin cikin kaba,indai har akan soyayya zaka tafi ka barmu na tabbata wannan abun yafi komai muhimmanci a tare da kai....."
Kuka sosai take ta kife fuskanta da hannayenta biyu,dafa ta akayi ta baya a d'an tsorace ta d'ago tana kallonsa ganinsa gabanta yasa tayi saurin goge fuskarta paper en ta mik'a masa,karb'a yayi yana dubawa,bayan ya gama dubawa kafin tayi magana sai gani tayi kawai ya d'aga paper ya yagashi,sai da yayi masa gutsi-gutsi sannan ya rabu da shi..
"BB me yasa.......?"
Da sauri ya dakatar da ita,ta hanyar d'aga mata hannu alamar tayi shiru,shirun kuwa tayi itama tana binsa da kallon mamaki,tafiya ya soma yi har ya isa bakin bed ensa ya zauna,tana kula da yanayin yadda yake tafiya da gani kasan dauriya ne kawai yake yi,da tausayawa take fidda wasu sabbin hawayen cikin kuka ta fara masa magana
"YAYANAH! me yasa bazaka fad'i abunda ke damunkaba ka b'oye mana, shin baka tunanin akan ko zamu iya nema maka mafita...kana ganin hukuncin da kayi yayi kenan?please dan Allah kayi magana kaga ina jin tsoron kada wani ciwon ya kamaka please.....!"
Murmushin k'arfin hali yayi
"Noo! CWEET SIS babu abunda ke damuna yanzun kam wancan letterma k'arya ne a da ne yanzun kam babu wanda nake so ko yake sona,wancan lokacin ne kawai kuma kema ki kwantar da hankalinki dan wacce nake so en tuni har iyayenta sun mata aure kinga ko bashi da amfani na fad'a,abunda kawai nake so dake ki tayani addu'ah Allah ya yayemin abunda ke damuna...."
Sosai ta gama yarda da maganar daya fad'a cikin wani yanayi na tsananin tausayi take kallonsa idanunta suna dad'a kawo ruwa
"Shi kenan BBNAH amma sam ban so akace haka ya faru da kaiba na so ace ka samu ABINDA RANKA KE SO (SAWWAMATEEY),Allah ya maka canji mafi alkhairi....amma! Amma ai ka fasa tafiyan ko?"
A fili ya amsa da ameen ya kuma tabbatar mata d'aya fasa tuni,a zuciyansa ko fad'i yake "Lallai yaro yarone yanzun ta yarda da abunda na fad'a kenan"
"Amma YAYANAH meya sameka kake tafiya ahaka da alama wani abu kuma na damunkafa...me yasa baka je kaga DR ba kake zaune da rashin lafiya?"
Tambayan nata ya zo masa a bazata shi yasa sai da ya d'auki wasu minutes kafin ya iya bata amsa
"Sorry CWEETY na bige ne a toilet yanzun shi yasa kikaga haka"
"Eyyahhh! sannu YAYANAH nayi tunanin ko wani abun ke damunka daban shi yasa na damu...."
"Noo! babu komai kam ki kwantar da hankalinki yanzunma idan na gama abunda nake yi zanje naga DR ko da wani matsalan da ban wanda ban san da shiba.."
"Yawwa YAYANAH barin je to sai ka dawo Allah ya kiyaye hanya"
Kallon tausayi yabita da shi har ta fice karo na farko kenan da yayi mata k'arya shi kam sam ya rasa dalilinma daya sa yayi mata hakan sai kuma yanzun yake jin haushin kansa da faruwar hakan.Har ya kammala shiryawa ya fito still tafiyan shi bai koma normal ba,duk wanda ya kalleshi zai gane hakan a tare da shi,kaf sai da suka kalleshi ganin yadda yake tafiya a duk'e kamar wani tsohon daya shekara d'ari.d'an dakatawa yayi ya gaida ABBA da MAMA,daga bisani kuma ya mik'awa KHALEEL hannu fuska babu yabo bare fallasa,sauran kuma suka gaida shi,amsawanma da kyar yake yi,ya kama hanyan ficewa daga parlor
Maganar ABBA ta dakatar da shi wanda yasa shi dole ya juyo ya kalleshi fuska a dame
"SON me yake damunka kake tafiya haka....?"
Kafin ya bashi amsa ZUHRA data b'illo daga corridor tace
"ABBA bigewa yayi a toilet yanzun nima muka gama magana da shi..."
"Eyyahhh! Allah ya kiyaye....To amma ina zaka je kuma kana irin wannan tafiyan?"
"ABBA hospital fa yacemin zashi yaga DR ko da akwai wani abun daban da yake damunsa ko...?"
"Ehh to hakanma yayi Allah ya kiyaye gaba"
Da ameen suka amsa duka nan BB ya sauke ajiyan zuciya mai nauyi saboda shi da kansa yasan Allah ne ya taimakeshi da ZUHRA tazo at the right time kuma tayi saving ensa a hannun ABBA da bai san me zai biyo baya ba,side en da take zaune ya kalla sun wani had'e kai da ZUHRA suna matsa phone,a hankali ya juya da niyyan ficewa daga parlor'n again KHALEEL ya sake dakatar da shi ta hanyar fad'in
"Lemme help u MAN,muje tare hospital en"
Ganin yadda idanu suka masa yawa yasa bai k'i amsan tayin KHALEEL enba amma kam da niyyansa yace bai so sai dai ya mazeee suka fita tare inda KHALEEL yake driving ensu har sukaje hospital suka dawo,sai dai duk k'ok'arin KHALEEL na sanin matsalan aminin nasa hakan bai faruba dan BB ya hana DR fad'an matsalan a gaban KHALEEL kawai ya ce masa ya bashi maganin da yake ganin shine zai masa maganin rashin lafiyansa,after kuma suka kamo hanyan dawowa duk motsinsa yana kula da shi kam sam bai yadda da abunda ZUHRA ta fad'a yana damun KHALEED enba kawai dai yayi shiru ne,ko da suka dawo gida BB ya kalli KHALEEL tare da fad'in
"Thnks!..."
Daga haka ya fice bai kuma magana yayi bedroom a nan ya duba prescriptions en nasa,aiko nan ya tsorata da ganinsu.....
《《》》
Kwanaki suna ta dad'a wucewa inda ya zama a lokacin har family en BIGGY sunzo sun kuma gana da iyayen BEAUTY'NSA a take babu b'ata lokaci 3ple ABBA suka tsaida rana dai² da bikin KHALEEL da KHUBRA wanda KAKA ya tsaida da kansa...
Musamman BB ya d'auki hanya bayan dawowansu daga DUTSE inda ya koma don ganin jikinsa da kuma maganan kaishi a duba lafiyan k'afan nasa,tunda yajema da BAFFA'N nasa da maganar ya kalleshi da fuskar damuwa yake fad'in
"Kayya dai takwara nan da kake ganinmu babu maganin da bamu kawo masa ba amma yak'i amfani da shi,shi nan BABA da kake gani magani ko wane iri ne ba sonsa yakeba,shi yasama kaga mun zuba idanu muma tunda babu yadda za muyi..."
"To amma BAFFA kam ai wannan ciwon nasa bana a zuba masa ido bane...ko kuwa bai damu da lafiyar k'afafun nasa bane?"
"Ehhh to nima dai abunda na kasa ganowa kenan,da yake ku y'an zamani ne la'alla idan kayi masa wani dabaran ma samu ya amshi maganin a wannan lokacin,amma muma kanmu ciwon nasa na damunmu kawai dai babu yadda za muyine kuma yak'i yarda akaishi asibiti a duba k'afar..."
"Shi kenan in sha Allah komai zai zo da sauk'i,bari na masa sallama a yau nake son komawa kuma gashi yamma ya kawo jiki..."
Koda suka koma gurin KAKA sallama kad'ai yayi masa sannan ya kamo hanyan dawowa gida,tun daga lokacin ya k'udire niyyan nemo masa magani daga na asibiti har zuwa na gargajiya dan bai san da wanne za a daceba saboda masu iya magana kan ce "idan dama yak'i to sai a koma hagu"
Neman magani yayita yi bayan dawowarsa sai daya tabbatar ya samu magungunan daya aminta dasu sannan ya kama hanyan komawa garin,da taimakon Allah ko bayan gumurzu da suka sha da KAKA ya amince ya karb'i prescriptions en dan kafewa yayi akan magungunan suna kisa shi ko haka kawai bai shirya mutuwa yanzuba.....
_Kunjifa KAKUS da gigin tsufa...._
Lokaci baya jira sai dai a jira shi,haka yake inji masu iya magana kuma su kan ce "duk abunda kaga bai zoba to tabbas ba a sa masa lokaciba" k'warai kuwa dan ko idan har ansa masa lokaci sai ya zo kuma harma ya wuce.
Biki nata dad'a matsowa ko wane gefe suna shiri babu ji bare gani,zuwa wannan lokaci duk wanda yaga ASHNA da BIGGY sai ya so sake kallonsu saboda soyayya,shak'uwa gami kuma da yarda da juna dake tsakaninsu,b'angaren su KHALEEL kuwa ba a cewa komai saboda sanin su nasu tsarin ba irin na kowa bane abun dai sai wanda ya gani,biki na k'aratowa amare da angwaye hidimomi sai dad'a shan kawunansu suke haka lokacin yaci gaba da kusantowa..........
*COMMENT FOR MORE PAGE'S......*
💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*24/ʝųlყ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
5⃣2⃣
*Y* au gaba d'aya abunda yayi saura a kwanakin da suka rage musu baifi kwanaki goma ѕhα hud'u ba,duka gidan ya dad'a hautsinewa,kowa ka gani ba shida lokacin zama aikace-aikace da hidima duk sun sasu gaba,hatta da su kansu amaren ba wani lokacin zama garesu ba,yau suna nan gobe can.
Cikin mota suke tafe sai surutu suke su uku KHUBRA,ZUHRA sai kuma ASHNA,shi kansa KHALEEL da yake driving hiran nasu har hawan masa kai yake saboda yawon da suka sha yau gashi duk ya gaji,ba shida burin daya wuce su isa gida ko Allah zaisa ya samu nutsuwa.
Daf da sallan isha suka iso gida,yana ajiyesu ko bai tsaya hiraba yayi musu sallama gami da juyawa,su kansu da yake a gajiye suke da shigansu gida,basu tsaya ko inaba sai d'aki,a kan bed ZUHRA ta zube tana fad'in
"Wash! wallahi duk joints d'ina ciwo sukemin haka wannan yawon raba I.V en yake....tabbb wallahi idan na tashi aure bazan iya wannan wahalarba,gara mutanen kada su zo."
ASHNA dake zaune kusa da ita ta kalleta tana fad'in
"Lallai yarinya ce ke,ta ina zaki wani sakowa mutane zancen aurenki bayan samarinma koransu kike,kenan wai gaki malama to waima ni da wane suna zanna kiranki ustaziya ko me....?"
"Ke kika sani kuma wannan,ni rabani da SAMARIN BANA (ASY KHALEEL) ba komai a cikinsu sai k'arya kamar ragowar yak'i....Fatan dai Allah ya zab'a mana mafi alkhairi.."
"Wollahi kin gama magana tunda kika nemi zab'in mafi alkhairi,da sannu zaki ganshi wollah...."
KHUBRA ce tayi maganar dan duk hiran da suke bata sa bakiba sai lokacin,saboda lokacin da suka shigo tana k'ok'arin cire kayanta,shirin shiga wanka ta gama nan ko tayi hanyan toilet..
Mintuna k'alilan ta fito jikinta jik'e gada ita sai towel iya cinyanta,sai k'arami data d'aure kanta ta gaba ya bada shape na harafin V.
"Ha'aaa! ya kuma naji kunyi shiru ko har kun gama hiran ne?"
Ta tambaya tana coge k'afa d'aya,ASHNA dake faman chart ta juyo tana kallonta
"Uhmm! nikam abunda nake yafi min wannan firan da kike magana"
Dariya tayi dan tasan me take nufi,batayi maganaba ta wuce tana fad'in
"To ai sai ku tashi kuyi wankan dan ni ina gama abunda nake kwanciya zanyi.....wallahi dana shiga wankan nanma kamar kada na fito saboda dad'in ruwan da naji...."
"Kina iya komawa ai in yaso sai muyi using wani toilet en.."
Hankalinta na kan waya tana chat take bada amsa,da sauri ko ASHNA ta kalleta ehfa tunda ke baza kiyi wankanba ai kya fad'i haka dubi irin gajiyar da muka kwaso amma nice haka,bari kiga ke idan kin gama chart en kyayi nan da talatainin dare"
Wayan ta ajiye tana shirin core kayanta,kafin tayi yunk'urin mik'ewa ai har ZUHRA ta dire a guje ta shige toilet en,baki ASHNA ta saki KHUBRA ko me za tayi mata ba dariyaba,tana cikin dariyan aka bud'e k'ofan hankalinsu duka ya tafi kan k'ofa suna son ganin waye haka babu knocking ya danno musu kai..
FATAHIYYA ta shigo tana fad'in
"BRIDE AUNTIES.....Ashe kun dawo amma ko ku nemeni..shi ne kuka gudo nan kuna hira babu ni..."
"Allah sarki k'anwarmu yi hak'uri kinji shigowanmu kenan muma.."
"Kai AUNTY KHUBRA shigowa'nkufa kenan kika ce bayan gashi nan har wanka kikayi kinga kenan kun jima da dawowa...Shi kenan ai tunda kuna nuna min triberlism dama ni nasan ba wani damuwa kukayi da niba....wa ya sanima ko idan kunyi aure zaku neme ni..."
Fuskanta a shagwab'e tayi maganar cike da nuna damuwa
"Yi hak'uri kinji....me zaisa mu kuwa bazamu nemeki ba,k'arewa ma ni dake tare zamu tafi kinji..."
KHUBRA tayi maganar tana rik'e hannunta..
"Su tafiya tare manya,ai ga hanya nan zaku iya abunda yafi hakama...Amma ko dai angon a ranar zai ce ku koma inda kuka fito.."
Yanayin da tayi maganar yasa su darawa dukansu,dai² lokacin kuma wayan dake saman mirror ta hau ruri,kallon gurin KHUBRA tayi had'e da tab'e baki,banza tayi suka ci gaba da hiransu har kiran ya katse,zuwa can aka sake kira nanma wayan sai ring yake
"Haba sis kina jifa ana kiranki kuma kin share kamar ba ke ake kiraba..."
ASHNA tayi magana cike da tuhuma kuma take kallon KHUBRA'N da tayi kunnen uwar shegu kamar bada ita take ba.Ganin bata da niyyan motsawa yasa ita ASHNA'R nufan gurin da wayan yake ta d'auka tana duba mai kiran,YAH KHALEEL ta gani a rubuce saman phone en sai lilo sunan yake
"Ungo ni YAH KHALEEL ke kirankima ashe kika wani share kamar bake ba,nifa wannan gulmar ne banso idan zaki amsa ki amsa,mata tana so sai wani kaucewa kike...Allah yasa ayi ai auren nan naga yadda zaki yi..Ni wallahi har so nake naga yadda zaki koma idan anyin auren..Zaki ci gaba da yi masa duhun kai ne ko kuwa ya za ayi nema ohoon muku..."
Ita dai KHUBRA shiru tayi mata bata tankaba sai wayan data karb'a ta ajiye gefenta ba tare da tayi tunanin d'aukaba,saima hira da take k'ok'arin sako musu.
FATAHIYYA ta kalleta lokacin da kira na uku ya shigo wayan nata
"AUNTY da kin d'auka kinji me zai ce miki...Kinga yanzun kada kisa shi tunanin ko wani abu ya faru..."
"Ke kyale shi ai yasan a gajiye nake ni kuma yanzun baran iya d'aukaba.....Dan yanzun yana ganin na amsa zai tsare ni da surutu ni kuma gaskiya bacci nake ji...."
"Aifa shi yasa naga kinyi baccin yanzun..kina nan kin wani yi gwaraf a gaban k'anwa zaku dasa surutu shi ne harda wani cewa bacci kike ji....Allah dai yana kallonki kuma sai dai ki tunasar da wani wulak'anci babu kyau.."
Ita dai FATAHIYYA tana kallonsu idan wannan yayi magana ta juya ta kalle shi idan wannan ya amsa sai ta sake juyawa,rashin d'aukan wayan da KHUBRA tayi yasa FATAHIYYA d'auka a hankali ta furta
"Hello! YAH KHALEEL ina wuni....?"
"A'a FATAHIYYA ya kike...? Ina AUNTY'NKI fa?"
"Lahh! YAH KHALEEL damafa gani nayi kana kira ita kuma tana shigowa tayi bacci.."
"Ok! to shi kenan na gode k'anwata,da safe mayi magana da ita dama kiranta nayi naji lafiyanta,amma tunda tayi bacci shi kenan kada ki tasheta,na gode sosai.."
Sallama sukayi ta ajiye wayan,sai lokacin hankalin KHUBRA ya kwanta saboda tunda ta d'auki wayan hankalinta bai kwantaba sai da taji sunyi sallama kuma duk abunda suka fad'a taji tunda wayan a handsfree ta sata.
Ajiyan heart tayi ASHNA kam shiru tayi musu amma lamarin na KHUBRA na bata mamaki musamman da auren ya dad'a gabatowa..
Bata kuma kulasuba har suka gama abunda za suyi k'arshe kuma kowacce ta kwanta.Ita dai tana kan waya suna chart da nata prince en kuma tana cikin garin ciki........
*ONE WEEK TO MARRIAGE....*
A gurguje ya fito daga mota ya nufi cikin gida dan dama a kwai abunda ya shigo dashi yanzun da yake ta sauri kada wani ya tsaida shi.
Karo suka yi da sauri ya d'ago dan ganin me ya faru haka,kallonta ya tsaya yi ganinta yake kamar cikin mafarkin daya saba a y'an kwanakin da auren nan ya matso,sam baya son abunda zai had'a shi da ita bare ya kawowa ransa wani tunanin ko yasa damuwanta a ranshi,sai daifa hakan da yake ba k'aramin azabtuwa yakeba,duba da yadda rashin ganin nata ya dad'a jefa shi cikin wani hali,ganin da ya mata a yanzunma duk da a rashin sani hakan ya faru,sosai ta dad'a yi masa kyau musamman da bai gantaba cikin y'an kwanakin da suka wuce,kamar an dasa su zuciyarsa sai sak'a masa abubuwa da dama take a kanta,cikin sauri ya d'auke kansa tare kuma da ci gaba da tafiya abunsa..
Kallonsa kawai tayi ta tab'e baki sannan ta juya tana tafiya abunta zuciyarta na fad'in
"Anya ko YAH ba wani abu ke damunsa ba?...Ko kuwa dai ni kad'ai nake ganin haka?....To amma idan har ba gizoba naga ya rame sosai ba kamar yanda na sanshiba...."
Da sauri kuma ta d'age kafad'a tana fad'in
"Kai to ni ina ruwana ma da damuwa'rsa....Shi ya sani ko wani abu na damunsa...Can ta matse masa ni banda damuwa...Allah yayi mutum sai d'an karen nunk'ufurci..."
Hanyan guarding ta nufa tana shiga ta nemi guri ta zauna,bata jima ba a gurin ko ZUHRA ta shigo gurin
"Ki ce nan kika yo yau kuma nan kika tuno bayan da kin daina zuwa"
"Ehh fa na gaji da zama cikin d'aki ne kawai shi yasa na yanke shawaran zuwa nan nasha iska....
"Wallahi dai kam nima haka nan nake jin zuwa nan yau shi yasa na fito ban kuma yi tunanin kina nanba..."
Suna cikin hiran motan KHALEEL ta kunno kai da sauri KHUBRA ta kwanta a k'asa saman grasses en tana rufe ido,dan ita kam bata son surutun KHALEEL a yanzun sam bata shiryawa jinsu ba,a nan ya tarar dasu shima ko ya zauna,mafi yawanci hiran tsakanin KHALEEL da ZUHRA ne dan dama ita ce abokiyar kuma y'ar rakiyar zance duk lokacin da yazo hira.Ita kam KHUBRA ko magana yayi mata amsanta tsaf sai mutum ya k'irga su saboda yadda take magana a tak'aice..
Labari suke sai dariya suke duka ta window ya hangosu su uku a cikin lambun,da yake lambun yafi kusa da window ensa shi yasa yake iya jiyo sautin dariyarsu.
Yanayinsu gwanin sha'awa haka nan yau kuma yaji yana sha'awar fita zuwa gurinsu ko ya rage damuwan dake ransa.
Suit en dake jikinsa ya zare ya sauya kayan dake jikinsa zuwa masu sauk'i sannan ya fice zuwa gurinsu dan a lokaci ji yayi ba zai iya fitanba.Tun kafin ya k'araso fuskarsa a sake ba kamar kwanakin da suka wuceba ya iskesu,ganin fuskarsa a sake wanda shi kansa KHALEEL ganin canji a tare da shi sai da yayi mamaki abu d'aya ya hana shi nuna hakan murnan da yake na ganin aminin nasa ya sakko yasashi jan bakinsa ya tsuke ko a fuska kuma bai nuna masa komaiba,hira sosai da suka jima basuyi ba suke wanda k'arshe suka gangaro kan maganar program's da za ayi a bikin,lokacin da KHALEEL yayi maganar sai da BB yaji wani iri kan maganar dinner da yayi,kawai dai ya danne ne,zuciyarsa na masa k'una,maganar KHUBRA ta katse masa tunani wanda har sai da ya d'ago ya kalleta
"Ni kam dan Allah wai dole ne sai anyi wad'annan bidi'o'in..."
Kallonta sukayi su duka suna mamaki
"To banda abunki CWEETY ai hakan shi zai nunawa duniya irin farin da muke ciki..."
Tab'e baki tayi tana fad'in
"Tabbb ni kam wallahi da da yadda zanyi da nayi dan kawai na hana wannan abun....Dan ni kam har ga Allah ba so nakeba"
"Saboda me zaki ce haka CWEETY...?
Sai data kalleta sannan tace
"Saboda bana son hayaniya ne kawai shi yasa,na tabbata lokacin zanyi ta fama da ciwon kai"
KHALEEL kam sam bai so hakan ba amma saboda jin abunda ta fad'a yasa yace
"To ai ina ganin hakan ba abun damuwa bane,abu ne da za ayi na k'aramin lokaci kuma ba dad'ewa za ayi ana yiba,so ina ganin babu wani abu da zai faru in sha Allah...."
BB kam bai ce komai ba game da muhawaran da suke saima waya daya ci gaba da dannawa kamar baya gurin,hiran ya koma tsakanin ZUHRA da KHALEEL dan ita ta maye matsayin BB na babban aboki da za ayi shawaran da shi itama amarya tana gefe tayi musu shiru kamar bata gurin......
Tun da suka shiga satin komai ya dad'a kachamewa musamman da kwanaki kad'ai ya rage musu a fara biki.
A lokacin duk wanda ya kalli KHUBRA babu lallai ya shaidata saboda kyau data k'ara akan nata,fita ko a cikin satin babu mai yinta tsakaninsu kullum suna d'aki daga su sai halinsu MAMA kad'ai ke da ikon ganinsu sai ko mai gyan jiki dake zuwa kullum tana gyaresu wanda gaba d'ayan su akewa sai dai na amaren yafi na sauran,a haka sauran kwanaki suka soma cimmusu.
Kamar yadda yake a tsare bayan kamu da walima ta mata zallah da za'a gudanar a shagulgulan bikin,sai d'aurin aure wanda daga shi sai dinner da za ayi bayan nan kuma za a wuce da amare gidajensu.
Duk wannan budirin da ake har lokacin BB baiyi kuskuren d'aukan invitation card enba bare ya gayyaci wani aboki ko wani mutum mai muhimmanci a rayuwarsa nasama da aka bashi tunda ya amsa ya bud'e closet ensa ya cillasu,tun daga ranar ko bai sake bi ta kansuba,hasalima duk lokacin da KHALEEL zai kirashi akan zaizo suje rabon card en sai dai ya bashi excuse akan aiki ya rik'e shi office,duk naci da magiya babu irin wanda KHALEEL bai masaba amma sam yak'i rakashi,kan dole ya hak'ura ba dan ya soba sai dan babu yadda zaiyi da shi.
Tun daga ranar da sukayi haka da shi ko ta k'arshe bai sake nemansa daya raka shinba sai dai duk inda zashi ya kama hanyansa shi d'aya,wasu daga cikin abokansu ko har tsiya suke masa idan sun ganshi shi kad'ai,sai dai ya fake musu da BB aiki ya tsare shi a office amma sun san babu yadda za ayi su ganshi shi kad'ai...
Haka har ranakun biki suka fara shigowa....
Kamar yadda aka shirya haka aka soma gudanar da events en ba tare da k'arya ko nuna su wasu bane,duk k'in KHUBRA na rashin son shiga taron jama'a abun ya gagara,kan dole take aiwatar da komai ba dan ranta na soba,duk inda ta juya jama'a ne daga ko wane sashi.A hankali saboda hayaniya da k'aran kayan kid'an wajen suka soma damunta nan ko ciwon kai yace bisimillah...
Duk yadda take ji ajikinta d'auriya kad'ai take amma sam tak'i nunawa mutane hakan.
*23/SEPTEMBER,2018.*
Rana bata k'arya akace sai dai uwar d'iya taji kunya,a yau ne dubban jama'a suka taru a babban masallacin na *UMAR BIN KATTAB* dake *ZARIA ROAD* dan shaida d'aurin auren,d'aurin aure mai cike da tarihi..
Shiga ta alfarma na hango manyan mutanen uku wanda duk ya gansu a wannan lokaci tabbas sai ya san sun bayyana a gurin,manyan ALHAZAWA da a wannan lokaci tarihinsu da labarinsu ya baza birni da k'auye cikin lokaci k'alilan,wanda dama dayawa daga cikin mutane sun san da su a wancan zamanin na baya sai a wannan lokaci labarinsu yafi yin shura...
Fuskokinsu kad'ai mutum zai kalla ya shaida tsantsan farin ciki dake shimfid'e samansu,jama'a sai gaisawa suke da su suna musu fata da kuma sanyawar alkhairi.
Da misalin k'arfe 10:30am KHALEEL na hango cikin shiga wacce take bayyana eh lallaifa wannan young man en akwai wani abu dake faruwa.
Kallo d'aya tak ya isa mutum ya gane hasken dake tare da shi a ranar wanda a dai² lokacin ya juya yana kallon BB daya koma kamar ba shiba,shigansu iri d'aya komai dake sanye jikin d'aya tabbas idan ka kalli d'aya zaka ganta ba aikin kowa bane sai BB dan shi yayi iya yinsa na ganin ta faru,kallon juna suka yi,sannan suka yima juna murmushi kafin suka fice a tare,BB ke driven inda ango KHALEEL ke gefensa
"Wai MAN lafiyarka k'alau kuwa...."
Kallonsa yayi ta cikin bak'in glass dake fuskarsa kafiin nan kuma ya furta
"Me ka gani kuma...?"
"Yo to kai d'in ne ai kake bani mamaki...cikin lokaci k'alilan kamar wani mai shafar jinnu..yau a ganka kana d'aci gobe kuma ka sake rikid'ewa ka koma ba kaiba"
Dariya yayi "To waya sani ne ko na koma cin wahainiya...kasan idan mutum na ci rikid'ewa yake yau ka ganshi a wannan siffar gobe kuma ya sake komawa wata"
Kallonsa kawai KHALEEL yayi ya furta
"Allah ya kyauta..."
"Ameen...!"
"To amma shi wannan glass enfa daka toshe da shi kamar wani sabon makaho,na lafiya ne kuwa?"
Banza ya masa yayi kamar bazai yi maganaba,can kuma kamar wanda aka tilasta ya furta
"Idan baka son ganinsa ba dole aka maka sai ka kalle niba ai...Duk ka wani dami mutane da surutu dama kasan daka tashi karatu ka zama *JOURNALIST* dan naga yanzun abunda kafi k'auna kenan...Mutum sai d'an karen surutu kamar ya had'iya farrot,Allah yasa kada ka koyawa k'anwata wannan zancen..."
Dariya sosai maganar da yadda BB yake da face ensa ya bashi,KHALEEL jinsa yake yafi kowa dace a wannan ranar saboda aminin nasa ya dad'a sakin jiki da shi dan yau kam gashi harda su tsokana,suna ta faman tsokanan juna suka isa masallacin inda ake jiran k'arasowarsu.....
*11:00am*
Aka fara addu'ah sannan bayan gubatar da siga da akayi a cikin massalacin wanda duk abunda ake BB na wajen masallaci yak'i shiga sai KHALEEL en kawai ya shiga,aka fara sanar da d'aurin auren inda mai sanarwar ya fara sanarwar da d'aurin auren ta cikin abun magana kamar haka...
_AN 'DAURA AUREN *IBRAHIM-KHALEEL* DA AMARYARSA *KHADIJATUL-KHUBRA* AKAN SADAKI NAIRA NA GUGAN NAIRA HAR NAIRA DUBU 'DARI BIYAR........_
Ai jin wannan sanarwa take idanun BB dake cikin glass suka soma kawo ruwa,a lokacin kam ya gama tabbatarwa da kansa ya masifar yiwa kansa,ya cuci kansa cutar da baya tsammanin akwai wata cuta da zaiwa kansa kamarta,yasan yayi k'auron baki inda yanzu gashi nan abunda ya jawowa kansa.....Ya tabbata kam yanzun hak'uri ya zame masa dole.
Gefen k'irjinsa ya dafe saboda yadda yaji yana masa zafi lokaci guda tsaiwa ta soma neman ta gagare shi,a daddafe ya nufi mota shi kad'ai yasan me yake ji a guje kuma ya fizgi motan tare da bar in gurin..............😱😱😱😱
_Wayyoooo Allah ínα masoya KHALEED (BB) ku kαwσ αgαjí kαdα wani abu ya same shi........_
_mσvє fσwαrd tσ thє nєхt pαgє..._
*COMMENT FOR MORE PAGE'S*
*~#TEAM KHUBRA-KHALEEL.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*©® 2018*
*25/ʝųlყ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
_rígíjí gαвjí....wαní kαчα ѕαí αmαlє...mαí kαmαr zuwα kαn αíkα....ídαn вα kαчí kα вαdα gurí dσmín вαnα ч'αr uwα kumα αвσkíчαr αíkí tα zσ dα wαní ѕαвσ mαí tαfє dα ѕαвσn ѕαlσ......_
_kαdα kují ínαtα zuвα ѕurutu gαmє dα в'αв'αtu вα kσwα nαkє nufí вα fαcє *AUNTY MAIMOUNATH O.G* dσmín kuwα вαnαmα tα dαwσ muku dα ѕαвσn nσvєl nαtα mαí cíkє dα dαrαѕí,ílímí,fαd'αkαrwα tαrє kumα dα k'αчαtαrwα ku nєmí nσvєl єntα mαí tαkєn *MEELAT TAMU*..._
_dαurє kα/kí nєmí nαkí α duníчαr ❄ domin kαdα α вαku lαвαrí........kαdαfα ku mαntα dα ѕunαn...._
*MEELAT TAMU.!*
*MEELAT TAMU.!!*
_ku nєmα ku ѕhα kαllσ tαrє dα kαrαtu,kαdα ku ѕαkє α вαku lαвαrííííí..._
*~__________________________~*
_jínjínα tαrє dα gσdíчα gαrєkí mαruвucíчαr zαmαní *HALISSA ADAMOU* ч'αr mutαn nígєr mαвucíчαr *MARAYUMA Y'AY'A NE* kí jímα kíчí k'αrkσ tαwαn αllαh чα k'αrα míkí lαfíчα dα níѕαn kwαnα mαí αmfαní.. *SMASHER & HUBBEEY* nα gσdíчα dα kαrrαmαwαrkí gαrє ѕu.αllαh чα вαr zumuncí._
*~__________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
5⃣3⃣
*K* asa controling temper ensa yayi wanda shi ne babban dalilin da yasa shi baro gurin ko tsayawa jin sauran d'aurin auren baiba ya baro gurin,bai zarce ko inaba sai gida wanda ikon Allah kad'ai ya kai shi,gidan a cike yake da jama'a amma sam BB bai iya gane abunda ke gaban sama bare kuma magana da ake masa da bai sanma suna yiba bare ya iya basu amsa.
Bedroom ya shige nan ko ya shiga watsi da kayan jikinsa d'aya bayan d'aya har ya gama raba jikinsa da kayan ya rage daga shi sai singlet da wandon kayan kifewa yayi a k'asa take wasu hawaye masu matuk'ar k'una suka shiga tsere a saman fuskarsa,a wannan yanayin duk wanda yaganshi dole ne ya tausaya masa saboda ganin garjejen saurayi majiyin k'arfi yana kuka da hawaye dole abun ya baka mamaki game kuma da tsoro coz irin su ba komai ke sasu yin kukaba.
Damuwa ta tarun masa gami da dana sani wacce bata da amfani,a dai-dai wannan lokacin da kowa ke cikin farin ciki da wannan ranar mai cike da tarihi,amma sam a gurin BB babu wannan labarin sai yanzun ya tabbata da ya tafka kuskure game kuma da asara wacce ba zai tab'a samun hanyan da zai gyaraba.
Babu abunda yake banda wani irin haki mai ban tsoro idanunsa sun canja launi zuwa jaa mai duhu,kwanciya yayi nan k'asa dafe da k'irjinsa da yake jinsa kamar zai tarwatse saboda azabar ciwo da yake masa....
*GURIN 'DAURIN AURE.*
Bayan fitowar su KHALEEL lokacin an gama d'aurin aure,Nanfa yayi ta dubawa bai ga BB a gurinba duk yadda yaso ya ganshi abun ya faskara,ko da ya tambaya wad'anda suka ga fitarsa sun sanar masa ya jima da fita,ko da yaji haka k'ok'arin kiransa yayita yi amma wayoyin sai ringing suke ank'i d'auka,duk k'ok'arin da yayita yi babu amsa,hak'ura yayi amma kuma hankalinsa baya tare da shi,kawai dai jama'an da suka kewaye shi ne yasa bai tafi nemansa ba dan yasan ba k'aramin abu ne yasa shi barin gurinba kuma har ya hana shi d'aukan kiransa.
Haka suka wuce gurin reception daga nan,har akayi aka watse abokai da y'an uwa sunata musu Allah ya bada zaman lafiya,ana gamawa ko bai zarce ko inaba sai gidansu BB,direct d'akinsa ya nufa dan yasan can ne kad'ai zai sameshi.
Abunda ya gani ya matuk'ar bashi mamaki game da tsoro wanda baiyi tsammaniba,magana ya shiga yi masa a hankali BB dake kwance k'asa ya d'ago rinannun idanunsa ya kalleshi da sauri kuma ya maida kansa ya kwantar wanda gaba d'ayan veins na kan sun gamaa bayyana.
"Hasbunallahu wa-ni'imal wakeel....!
KHALEED lafiyar ka k'alau kuwa,me yasa kake son zama cikin damuwa? me yake damunka ne kam...?"
Banza yayi masa saima kulle idanunsa da yayi dan bai shiryawa jin maganganun KHALEEL enba yanzun da yake cikin wannan halin
Jiki a sanyaye KHALEEL ya nemi guri ya zauna,a zuciyarsa ya furta
"Ya kamata na sanar masa yanzun ko kuwa....?"
Da hanzari kuma cikin tausayi ya kalli BB yana fad'in
"Tashi za muyi magana yanzun..."
Banza ya sake masa,hannunsa dafe da kansa da yake barazanar tarwatsewa,hakan da yayi masa yasa shi sake kallonsa,duk k'ok'arinsa na ya kwantar masa da hankali yasa shi kuma magana dan ya kore masa damuwan hakan ya faskara dan Sam yak'i bashi had'in kai,wayansa ya shiga pressing cikin apps nasa ya binciko app na *MAHEER MU-AQQILIIY* sauka ne complete amma a app yake nan ya kunna tun daga fatiha suke sauraro tare a lokacin da kuma suke zaman kurame,yini guda sallah kad'ai ke tada su,itama nan suke yinta cikin d'aki babu mai fita,weeding pics da ake da amarya da ango saboda tarihi a wannan ranar kama sam amaryar KHALEEL bata sashi a idanuntaba,dan ko suna can zaman makoki shi da aminin nasa...
B'angaren AMARYA KHUBRA ko tun bayan da aka dawo da labarin an d'aura aure ta dad'a lafkewa kan bed dan ko dama tuni take fama da matsanancin ciwon kai wanda ya saukar mata da zazzab'i mai zafin gaske.
Da k'yar aka samu ta iya shiryawa shima sai da taimakon ZUHRA,tana kwance ZUHRA na gefenta labarin d'aurin aure ya riskesu,jikinta ko ya sake rikicewa,tana kwance cikin duvet amma kana hango yadda jikinta ke vibrating kamar wacce aka jonama shocking.
Duk k'ok'arin da MAMA take akan samun su KHALEEL a waya hakan ya faskara kan dole ta kira line en ABBA,shi enma dai suna tare da mutane lokacin da take kira dalili kenan daya sa bata same shiba,k'arshe dai sai magani aka bata haka da k'yar da sid'in goshi zazzab'in ya sauka sai ciwon kan da yak'i tafiya coz dama haka ciwon kai yake mata baya saurin tafiya idan ta fara.
Shirin dinner ake sai daifa har lokacin babu ANGWAYE bare kuma AMARE duk iya kaiwa ruwan da za ayi anyi akan shirya KHUBRA amma sam ta kafe akan ba inda zata,k'awayensu ASHNA da ZUHRA da su suka zama k'awayensu duka a gurin,haka suka shirya suka d'auki hanyan tafiya dinner,ZUHRA aka bari gida dan ta kafa ta tsare akan babu inda itama zata idan babu KHUBRA a wajen,har aka dawo daga dinner suna d'aki ZUHRA na kula da ita,yini guda babu wani abu da taci duk k'ok'arin da MAMA tayi akan taci wani abu amma ta gagara yin hakan kan dole suka kyaleta kowa ya sa mata ido sai sannu da take karb'a daga bakin mutane da dama.Wajen 9pm aka fara dawowa daga gurin dinner dan d'aukan amare a lokacin ne kuma MAMA ta sake shigowa gefen da su KHUBRA suke,a kan idanunta ta shirya duk jikinta a sake kamar wacce bata da laka har ta kammala,kayansu tunda aka fara biki iri d'aya da ASHNA.
Kusa da ASHNA aka zaunar da ita nan nefa ta d'ago idanunta da suke masu kama da an tsoma a man gyad'a tabi mutanen da kallo,KAKA ne zaune saman sofa sai sauran BAFFANINSU da kuma ABBA'NTA da ABBA'N BB,sai sauran y'an uwanta ZUHRA,FATAHIYYA,duk taurin kai da nunk'ufurci irin na BB da yake wannan kiran na manya ne sai daya halarta,cikin wani shigan daban sai k'amshi yake bazawa kamar sabon ango,fuska a d'aure kamar wani BOSS yake zaune gurin,ganinsa a gurin ya tabbatarmin yanzun kam da sauk'i jikin nasa sai dai har lokacin ba wani sosaiba sauk'in saboda yadda yake tafiya a hankali kuma cikin dauriya yake saboda bai son a gane halin da yake ciki.
Bayan dogon lokaci da KAKA ya d'auka yana musu nasiha mai ratsa jiki,sannan sauran iyaye suka d'ora nasu,bayan nan kuma KAKA yasa akayi addu'a wanda ya dad'a sanyaya musu jiki daga bisani kuma akayi musu fatan zaman lafiya sannan aka fita dasu kowacce sai kuka take,a haka aka dangana da kowacce d'akinta.
Amare sai muce Allah ya bada zaman lafiya...
BB ne ya mik'e zai fito daga parlor'n KAKA ya dakatar da shi ta hanyar fad'in
"To MALAM sauran kai ko naji ance ko budurwa baka da,ko dai a k'auye zan bada kai sadaka ne...?"
Murmushin k'arfin hali yayi ba tare da yayi magana ba har KAKA ya gama jansa da tsokana wanda k'arshe shima ya biye masa,daga bisani kuma KAKA yayi masa nasiha sosai,shi dai sai mamaki yake ko mene dalilin wannan nasihar ta KAKA oho,haka har ya samu KAKA ya sallameshi,yana fitowa ko KHALEEL na kiranshi babu yadda zaiyi kan dole ya d'auka saboda yanzun ba kamar da safe ba jikin da sauk'i kuma tunanin da yayi ne akan rashin dacewar abunda yakewa KHALEEL en ya rinjaye shi,dalilin kenan daya yanke shawaran sakin jikinsa d'aukan wayan yayi,KHALEEL ne ya fara magana cikin sanyin murya
"MAN! kana ina ne yanzun...?"
Shiru yayi na d'an lokaci kafin ya iya yin gyaran muya sannan a tak'aice ya furta
"Gida......"
"Ok Zaka iya rakani ko kuwa....?"
Jim ya sake yi kamar kuma bai gane mai KHALEEL en yake nufiba ya furta
"Ina kenan..?"
Cike da zolaya ko KHALEEL ya ce
"Sai da kai zanyi..."
"Uhmmm! kaima kasan na wuce haka ai"
"Banda kuri dai.."
"Haba wane irin kuri kuma kaima kasan gaskiya ai"
Sai da KHALEEL yayi dariya sannan ya furta
"Kawai dai ka shirya yanzun zan zo zaka raka ni wani waje ne mu dawo..."
"Haba MAN ina zamu kuma a wannan lokacin kai da kake da amarya bai kamata ka barta taita jiranka ba kaga dare na dad'a yi,ka bari zuwa wani lokacin ka je koma ina zaka.."
"To wai kam ina ruwan ka da maganar amarya ko kuwa shi kenan babu wani uzuri da zai taso min yanzun nayi kafin na wuce gidana...?"
Banza BB yayi masa cikin sanyin murya kuma kamar wanda bai son magana yace
"Za kayi ka bari d'an air kawai..."
Sarai KHALEEL ya jishi kawai dai baison BB en yace ya fasa rakashin ne yasa yace
"Naji...ni dai gani nan a hanya zan zo na d'aukeka.."
Yana gama fad'an abunda zai fad'a ya datse kiran ba tare da yaji amsan da BB zai bashiba,cikin k'ank'anin lokaci kuma ya k'arawa motan wuta zuwa gidan su BB en.
A harabar gidan ya tadda shi tun da suka gama waya ya kasa barin gurin har lokacin kuma yana jin chest ensa ba daidaiba duk da dai ya bawa kansa hak'uri amma kam yana jin zuciyarsa na k'aik'ayi kawai dai k'arfin hali yake.
Yana daidaita parking BB na isowa kusa da shi cikin shiga kamar ta d'azun yanzunma haka suke har mamaki BB yayi daya ga KHALEEL sanye da irin kayansa wanda suka kasance kyauta daga gurin ABBA'NSA,bai tambaye shiba ya b'oye mamakinsa ta hanyar d'auke kansa daga kan KHALEEL en ya shiga motan suka bar gurin.
Tafiyan babu wani nisa daga gidan su zuwa inda suka je en,a bakin wani gida KHALEEL ya tsaya sannan yayi horn,bud'e masa k'ofar get man en yayi nan ya danna hancin motan ciki,farfajiyan babu laifi akwai girma dan ko yanayin gurin zai tabbatar da hakan duba da yadda motoci da dama suke a parke a gurin,fita sukayi tare da kama hanyan shiga gidan KHALEEL na kan gaba sai BB dake bayansa,shi dai binsa kawai yake ba tare da yayi masa tambayan komai game da inda suka zo enba,har suka k'araso kusa da inda taron abokan nasu suke a cikin parlor.
A nan ne kuma mamakin BB ya kasa b'oyuwa duba da yadda suka tarar da wasu daga cikin abokansu ke zaune,mamakin dake kan fuskarsa ya kautar sannan suka gaisa nan ko suketa masa tsiyan basu ganshi gurin reception ba da sauri KHALEEL yace
"Ammm! da yake ai kunsan k'anwarsa ce amarya to kuma bata ji dad'i ba shiyasa ya tafi ya wakilce ni a gurin..."
"Eyyahhh! gaskiya ne aiko yayi maka babbar karafa.."
Daga haka suka yi musu fatan alkahiri sannan suka yi sallama da su ba tare da sun jira ganin amarya ba suka kama hanyan maida jama'ah zuwa gida.
Parlor'n ya rage daga KHALEEL sai BB suna zaune can BB ya kalleshi
"Ko mene ne ma'anar yin hakan da kayi...?
A nawa tunanin ba sai kamin haka zan san kana son na rako kaba,idan ka sanarmin gidanka zan rakoka zan gagara yi maka hakan ne...?"
Banza shima KHALEEL en ya masa saima dad'a nutsewa da yayi cikin cousion yana turo hulansa saman giransa,wayansa a hannu yana danne-danne,zaman kurame suka ci gaba da yi inda yake ankara da BB daya gama cika kamar zai fashe saboda haushin banzan daya masa bai bashi amsaba.
Jin gidan yayi shiru yasa KHALEEL ya mik'e tare da gyara zaman cap nasa yana fad'in
"Muje ko naji alamun babu mutane a gidan..."
K'wafa yayi sannan ya mik'e yabi bayansa,ta nan cikin parlor'n suka bi wani k'ofan daban,sai gasu a wani k'ayataccen parlor'n fiye da wanda suka baro,a nan BB ya nemi guri ya zauna KHALEEL ya juyo cikin d'an alamu na kamar yayi mantuwa ya kalli BB
"Sorry MAN d'an jirani nan nayi mantuwafa.."
Kallonsa yayi sannan yaja wani uban tsaki,KHALEEL dai bai jira jin me zai fad'a ba ya fice da sauri.
BB na zaune yaji alamun tashin mota a fili ya furta
"Lallaima GUY ennan koi d'an rainin hankali..."
Kiran KHALEEL en ya soma yana zaune har lokacin a gurin,shi kuma KHALEEL yana ganin kiran BB yayi murmushi game da k'in d'aukan kiran coz time en ya isa bakin get ko fita baiyi daga gidanba,sai da ya tabbatar da ya fice sannan ya tsaya gefen hanya ya fiddo wayansa,dai² lokacin kiran BB ya sake shigowa da sauri ya d'auka ko kafin yayi magana BB ya rigashi
"Wane irin iskanci ne wannan zaka ajiye ni ka fice...Ko kuma ka maidani mai tsaron gidanka ne...?"
Dariya sosai KHALEEL yayi iya son ransa har saida BB yaji haushinsa
"Idan ka gama gasamin maganar to ka shiga ciki matarka na jiranka..."
Yana fad'in haka ya datse kiran,cikin rashin fahimta BB yake son tambayansa,anya kuwa yaji dai² ko kuwa dai kunnensa ne yake yaudararsa,kafin yayi magana yaji an katse wayan,k'ok'arin sake kira yayi amma KHALEEL yak'i d'auka har ya gaji da kira dan kansa ya bari..
Ganin bai sake kiraba KHALEEL en ya tafa masa text kamar haka...
_Am sorry friend naso yi maka bayani tuni sai dai kak'i amincewa muyi maganar shi yasa ni kuma na yanke shawaran yi maka haka,tabbas nasan a yanzun kana cikin shock da maganar da na maka,sai daifa tabbas abunda na fad'a babu k'arya ko zolaya a ciki,dama kai na rako ba wai ni ka rakoba,ina maka fatan alkhairi kai da amaryarka *KHADIJATUL-KHUBRA*.Na barka lafiya aci amarci lafiya._
*UR'S KHALEEL.*
Dai² lokacin daya samu sak'on bayan ya gama karantawa mik'ewa yayi tsaye kamar wanda aka tsikara yana nanata sunan *KHUBRA* da ya gani rubuce...............
*COMMENT FOR MORE PAGE'S......* 💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*©®2018*
*26/ʝųlყ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~__________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
5⃣4⃣
*S* till yayi a inda yake har lokaci he ain't believe abunda yaji kuma ya gani gaske ne,cap nasa yayi removing ya cilla saman cuition shi kad'ai sai kaiwa da kawowa yake cikin parlor,zuciyarsa tak'i samun nutsuwa da abunda KHALEEL en ya sanar masa,nan ko ya shiga magana a fili
"How za ace haka ya faru bayan akan kunnena naji d'aurin auren wannan kawai shirme ne na sani irin na KHALEEL babu yadda za ayi haka ya faru,am not believing any more...."
Waya ya sake dannama KHALEEL,ganin kiran BB yasan da akwai damuwa kan dole ko ya tsaya gefe still yayi yana sauraron maganganun BB da yake yinsu cikin fad'-fad'a
"Heyy! MR MAN u have to came and take me up here right now.....
Banda shirme irin naka taya za a d'aura maka aure da yarinya naji kuma akan kunnena ka maida ni wani sauna....Idan ma baza ka dawoba to zan bar maka matarka cikin gida,and ni kuma na san inda dare yamin..."
"Ka gama fad'an....?"
KHALEEL ya tambaya cikin coolness tone
"Ohhh! abunda za kacema kenan...wato ka mai dani wani tamkar ban san abunda nakeba shi ne harda cemin na gama fad'an....?
To ban gamaba kuma Allah ka ji na rantse babu abunda zai hanani tafiya,idan ka gama ka dawo ka tarar da babu kowa...."
Yana kaiwa nan ya datse wayan ko sauraron me KHALEEL en zai fad'a baiba kuma har lokacin yana tsaye sai huci yake.
KHALEEL jin da yayi BB ya kashe wayan yasa shi saurin yin tunanin ya kamata ya tura masa wani evidence da zai zauna cikin gidan kada ya bar yarinyar mutane ita d'aya a gidan,da saurinsa ko ya tura masa sak'o ta email,sannan ya jaa motansa ya k'ara gaba.
Dai² lokacin da yake sintiri tsakiyan parlor hannunsa d'aya a dunk'ule yana naushin iska sak'on ya shigo,da sauri ya isa kusa da phone en yana dubawa,email nasa ya shiga cikin sauri saboda ganin sak'on ta email yake,nan ko ya tarar da sak'on audio da kuma na video's wanda da gani babu tambaya kasan a gurin d'aurin aure ne.
Cikin hanzari ya shiga playing nasu d'aya bayan d'aya yana kuma sauraro har dai² lokacin da aka soma sanar da d'aurin auren kamar haka
_An d'aura auren *IBRAHIM KHALEEL* da amaryarsa *KHADIJATUL-KHUBRA* akan sadaki naira na gugan naira har naira dubu d'ari biyar..._
Wani uban tsaki BB yayi a dai² nan yana fad'in
"Banda d'an iska ni zai rainawa hankali kamar ba a gabana aka fad'i hakaba...."
Kafin ya sake magana yaji mai sanarwar yana fad'in
_"Afwan..! Afwan..!! Afwan..!!!_
_Y'an uwa a gafarceni nayi makuwa gurin sanar da wannan d'aurin auren,ina fatan kuma za amin afuwa dan kuwa ba *KHALEEL* zan ambataba gurin fad'amin ne aka samu sab'ani sai yanzun aka sanar dani gyaran dake cikin wannan maganar tawa,a maimakon KHALEEL dana ambata *KHALEED* ne angon,wannan auren na *KHALEED* ne da amaryarsa *KHADIJATUL-KHUBRA*_
_Sai kuma auren *IBRAHIM-KHALEEL* da amaryarsa *FATIMA-ZUHRA* akan sadaki dai-dai dana y'ar uwarta,aure na uku kuma shi ne na *ABUBAKAR-SADEEQ* da amaryarsa *ASHNA* sadakinta kwatankwacin na y'an uwanta lakadan ba ajalanba...._
Dafe baki BB yayi yana fad'in
"Ta yaya akayi haka ya faru? kenan bayan na bar gurin akayi haka ko kuwa yaushe ne hakan ya faru...?"
'Daya bayan d'aya ya dinga binsu yana playing har yazo na k'arshe,again bai hak'ura ba ya sake kiran KHALEEL,shima cikin isa ya d'auka yana fad'in
"MAN! lafiya kake kirana kuma dai² lokacin da zan shiga gidana? ko kuma har yanzun shaidan basu gama gamsar da kai bane...?"
Murmushi kawai yayi yana fad'in
"Noo! kawai dai na kasa yarda ne...!"
"To tunda baka yarda ba ai shi kenan ka jira gobe sai su ABBA su maka bayanin yadda akayi haka,ni nayi iya nawa sauran nasu..."
Yana kaiwa nan ko ya kashe wayan gaba d'aya dan yasan idan ya barta haka BB zaita damunsa da kira,dai² ya shigo parlor aiko ya juya ya kulle k'ofofi tare da addu'an neman kariya daga mahalicci...
**********
B'angaren amarya KHUBRA kuwa tun bayan da suka futo daga parlor lokacin za a sasu mota ta rik'o ZUHRA akan itafa lallai sai dai k'afarta k'afar ZUHRA zasu tafi,ganin zata jik'a musu aiki da dabara aka sata cikin mota sannan aka ce to ta matsa ZUHRA ta shigo,da yake babu wayo nan ko ta matsa aiko tana yin haka aka rufe k'ofan sannan driver'n yaja yayi gaba.
Kuka babu irin wanda bata yiba dan an taho da ita babu ZUHRA dama kuma ba wani cikakkiyar lafiya gareta ba,haka ko bayan da aka kawota da d'aya da d'aya duka suka zare jikinsu suka gudu,aka barta daga ita sai halinta,kukanta ta shak'a bayan taji gidan shiru a nan inda ta gama kukan take kwance jikinta duk ya dad'a yin zafi tana saman bed jikin ta ya ko dad'a rikicewa ....
Nan parlor yaci gaba da zama ya kasa yanke shawaran abunda ya kamata yayi,har 12am yana nan shi bai bar gurinba kuma bai daina kiran number KHALEEL ba duk kuwa da yadda wayan ke sanar masa a rufe take,wani zuciyan ne ya bashi shawaran kiran UMMI baiyi tunanin komaiba ko yaddana mata kira ba tare da yayi tunanin dare yayi ko akasin hakaba...
Cikin magana irinta mai bacci UMMI ta d'auka tana fad'in
"KHALEED SON lafiya kuwa ka kirani cikin wannan lokacin.....ina ita KHUBRA'N ko kuwa jikin nata ne ya sake rikicewa...?"
Murmushi yayi mai k'ayatarwa ko tantama babu yanzun kam ya soma gasgata maganar KHALEEL,sai dai tambayan da yake ta damun kansa shi ne *TA YAYA HAKA YA FARU?*.
Murmushi yayi ta saki abunsa kamar ba wanda yake jinya ba d'azun,kan cuition ya kwanta had'eda kashe wayan ba tare da yayi magana ba,yana juya lamarin a ransa,lallai a yanzun kam ya tabbatar da komai hukuncin rabbi ne ba tare da dabara ko k'arfinsa ba ya bashi abunda ya jima a ransa a kuma lokacin da babu zato bare tsammani, ai kam ya tabbatar a yanzun yafi kowane d'a namiji sa'a,a duniyarsa gani yake babu wanda zaiyi dace kamar nasa.
Tunawa yayi da maganar KHALEEL ta d'azu da abokansu suke tambayan basu ganshi gurin d'aurin aureba,sannan kuma maganar UMMI ta sake fad'o masa inda take cewa
_"KHALEED SON lafiya kuwa ka kirani cikin wannan lokacin.....ina ita KHUBRA'N ko kuwa jikin nata ne ya sake rikicewa...?"_
Cikin hanzari ko ya mik'e yana bin hanyan da zai sadashi da d'akunan baccinsu cikin damuwa coz bai san halin da take cikiba a fili ya furta
"Is she ill...? Amma tun yaushe ne hakan ya faru...?"
Dai² lokacin ya iso kallon gefe da gefensa yayi coz bai san a wane room take ba,kallon doors yayi ya d'an tsaya tunani can kuma sai ya kalli wanda yake bud'e a hankali ya d'aga k'afafunsa ya nufeshi...
*GIDAN KHALEEL...*
Bayan ya gama tura masa abunda zai tura daya kashe phone ensa ya kulle k'ofifi,hanyan bedrooms en ya nufa yana fad'in
"HABIIBTIIY!!!.....Ina kika shige ne..?"
Shiru yaji babu amsa nanko ya nufi cikin bedroom enta,zaune saman bed ya hangota sai dad'a jan vail enta take tana dad'a rufe jikinta,da alama da ba gurin take zauneba,dariya yayi yana fad'in
"Ohh! kunyana kuma ake ji yau..? i think yau kam babu wannan a tsakaninmu tunda burin da muka jima da shi yanzun Allah ya nuna mana ranar da muketa jira...So ina ganin kamata yayi ace munyi godiya ga Allah daya nuna mana hakan cikin rai da lafiya gami kuma da kwanciyar hankali..."
A hankali ta d'an motsa kamar zata janye vail en sai kuma yaga sab'anin haka
"Ohhh! wato sai kin bani wahala dai kenan ko..?"
Har lokacin ZUHRA ta kasa masa magana,ta kuma k'i d'agowa ta kalleshi,saman bed en ya isa yana ajiye ledan dake hannunsa,a kusa da ita yayima kansa masauki,fuskanta ya shiga lek'awa yana fad'in
"Haba mana duk kalaman da nake GAM DA KATAR (ZEEY BUGAJE) dasu a kullum kuma yauda nake tsammanin ganinsu a zahiri bayan tsawon lokacin da muka d'auka bama tare,sai naga sab'anin haka,shi kenan tunda baki son ganina bari na koma inda na fito...Dama na had'u da wata d'azun so kinga saina tafi zance gurinta ko?"
Yana gama fad'in haka ko ya shiga k'ok'arin mik'ewa da niyyan zai fice,a zahiri kuma yana kallonta yaga wane reactions zata bayar da jin maganar tasa,alama yayi kamar zai fice,aiko nan ZUHRA ta dire k'afafu tana bugasu k'asa cikin tab'ara tana fad'in
"Ni wallahi a'a,kuma idan ka fita nima saina bika duk inda zaka..."
Dariya ya kwashe mata da,sai da yayi son ransa,ita kuma ganin yana mata dariya gashi dama tunda ta mik'e tayi cilli da mayafin,tsayawa tayi kallonsa yadda yake dariya take kallo sai taga ya k'ara mata kyau fiye da yadda ta sanshi.Tsayawa tayi tana kallonsa bata k'i su dawwama a hakaba.
Ankara yayi da irin kallon da take masa,nan ya matsa kusa da ita,waist enta ya rik'o yana matso da ita jikinsa,da sauri ta kalleshi coz batama san ya akayi yazo kusa da itaba,jinta da tayi a jikinsa shiya farkar da ita,duk'owa yayi dai² kunnenta yake fad'in
"MADAM wannan kallonfa haka,bayan gani kusa da ke,ko mafarki kike yine wata ta k'wace miki ni...?"
Kai ta sake d'agawa ta kalleshi jin abunda ya fad'a,a hankali ta tab'e d'an bakinta ta sake kauda kanta,mutsu-mutsu ta shiga yi saboda tana son ya saketa,shi kuma hakan da tayi yasa shi dad'a rik'eta sosai
"Please YAH ka sakeni..."
Maganar yayi escaping daga bakinta ba tare da ta shiryama hakan ba.
"Nak'i...Ina son jina jikinki ne yasa..it's been long da nake son mu kasance tare sai dai aikin UMMI ya hana mu kasancewa kusa da juna....Buh Al-hamdulillah alaa kulli haliin...Yau kam komai ya zama tarihi,tunda gamu yanzun a matsayin abu guda.."
'Dan murmushi ta sake yi tana sauke kanta k'asa dan ita kam yanzun tunda ya fara mata wannan maganar take jin kunyarsa...
《《》》
Shigansa d'akin ya hangota can saman bed ta duk'ule guri guda,jikinta sai karkarwa yake da alama dai kam tana cikin mawuyacin hali,da d'an hanzari ya isa kusa da ita nan ya birkitota ta juyo suna fuskantar juna sai dai nata idanun a kulle suke,jikinta sosai yayi zafi fiye da tunanin mai tunani saboda hatta da kayan dake sanye jikinta hucin jikinta ana jinsa jikin kayantan.
Tsayawa yayi dafe da hab'ansa yana tunanin me ya kamata yayi mata wanda zai sauke mata zazzab'in,a hankali ya kad'a hannu sannan ya nufi toilet,bowl ya d'auko a toilet ya d'ebo ruwa,dawowa yayi ya d'ora shi saman side drower sannan ya nufi wall-drop,k'aramin towel ya d'auko ya dawo kusa da inda dake,nan ko ya soma tunanin me zaiyi kuma..?,Ganin yana b'ata lokaci kuma gashi har lokacin jikinta na a yana yin daya taddata yasa a hankali ya haura saman bed en har lokacin ya kasa believing da abunda yake shirin aikatawa,hannunsa sai rawa yake kome ya tuna kuma yayi saurin janyota had'e da soma rabata da kanyan jikinta daga ita sai pant da bra ya barta,bowl en ya janyo nan ya sa towel en cikin ruwan ya matse,goge mata jiki ya shiga yi sai rolling eyes nasa yake a kanta,ganin batama san me yake yiba,har yayi ya gama bata san halin da take ciki bama bare tasan waye a kanta yasa ya kauda tunanin dake ransa .
Kwantar da ita yayi yaja duvet ya rufeta da shi,sannan ya tafi maida kayan da yayi amfani dasu,ruwan ya zubar ya wanke bowl en sannan ya maida shi muhallinsa,fita yayi a d'akin ya nufi d'ayan bedroom en,sai da ya gama shirin kwanciya ya tuna da halin daya barta,da sauri ya diro daga saman bed en dan a time en har yayi addu'ah ya fito ya nufi d'akin nata dan ya duba halin da take yanzun kafin ya kwanta.
Zafin jikin kam alhamdulillah da sauk'i sai dai har yanzun tana nan a dunk'ule kamar d'azun da alama kuma sanyi take ji,tsayawa yayi ya rasa me zai yi kuma,d'an gajeran tunani yayi tunawa da wani india'n film,d'an murmushi yayi daya kalleta had'e da shafa kansa ya haura saman bed en,sai daya tabbatar da ya dai-daita zamansa saman bed en sannan a hankali ya zuge zip na pyjames ensa a hankali yasa soft hands ensa ya janyota,cikin jikinsa ya sata sannan ya maida hannayensa ya zagayeta da dasu,a hankali ta sauke wani wahalallen ajiyan zuciya,shi kansa BB jinta kwance cikin jikinsa sai da yaji bak'on al'amari a tare da shi.Ranan kam da kyar ya iya bacci saboda ya tsinci kansa cikin yanayin da ya kasa tantance na mene ne,farin ciki ko kuwa akasin haka....
《《》》
*GIDAN SADEEQ BIGGY.*
Aifa a wannan dare bayan watsewar y'an kai amarya ango ya shigo shi d'aya ba tare da ya yarda kowa ya rako shiba,haka ya tadda sahibar tasa ta hakimce da alama kuma zuwansa kad'ai take jira..
Bayan sun gabatar da komai cikin ilimi,wanda ita kanta ASHNA sai da angon nata ya bata mamaki jin yadda yake rero k'ira'a,after kuma yaita zuba addu'a ita dai a zuciyarta take fad'in
"Allah na gode maka daka sa mijina yake da ilimin addini,amma abun mamaki dama haka yake da ilimi...? A da kam nayi tsammanin bashi da komai,ina masa kallon irin mutanen da suke fama da k'ungurmin duhun jahilci.."
Kallonsa ta sake yi a karo na biyu ganin sun had'a ido yasata saurin sunkuyar da kanta,a haka suka gama duk abunda za suyi a wannan dare sannan suka kwanta,kwanciyarsu babu jimawa ta tsinkayo hannun BIGGY a jikinta yana murzarta,nan ko jikinta ya hau rawa dama kam tasan da kamar wuya ya d'aga mata k'afa a yau,tana tunani shi kuma yana ci gaba da aikin da yake gabansa,a haka har ya samu daman da yake buk'ata bai tsaya b'atawa kansa lokaci ba ko ya amsheta da hannu biyu-biyu.....
Ko a gidan KHALEEL ma hakan ce ta faru tsakaninsu,wanda a wannan dare ZUHRA kam tayi kuka iya yinta,KHALEEL duk ya wani dad'a rikice mata a haka har ya samu abunda yake nema a tare da ita,sai bayan da ya samu nutsuwa tukun ya koma lallab'ata kamar kwai yana kuma sa mata albarka sai sumbatu yake zuba mata,bayan komai ya lafa kuma ta koma tausayawa KHUBRA a ranta take fad'in
"Allah sarki CWEETY yanzun kam nasan babu lallai BB ya mata komai saboda nasan idan har yaganta a yanayin da muka rabu tabbas zai tausaya mata bazai mata komai..Allah ya baki SISTER'NA"
A haka suma bayan ya tsaftacesu suka kwanta cike sa so da k'aunar juna yana rad'a mata maganganu masu dad'i da kwantarwa da mutum hankali......
《《》》
Sai da gari yayi haske sannan KHUBRA ta farka,jinta jikin mutum ta shiga k'ok'arin zare jikinta saboda haske da take gani cikin d'akin ya tabbatar mata da an jima da yin salla'n asubah..
Motsinta ne ya farkar da shi,a hankali ya bud'e idanunsa ya saukesu a kanta,d'an murmushi yayi ganin idanunta a kulle kuma sai k'ok'ari take ta tashi,fuskarsa ya gintse sannan ya saketa,da sauri ta mik'e ta fito a cikin duvet en,k'afafunta ta zuro k'asa tare da bud'e idanunta,kallon jikinta tayi ganinta daga ita sai pant da bra yasa ta k'walla k'ara had'e da saurin yayibo bargon ta b'oye ciki.
Murmushi yayi ta zubawa,yana kallon yadda ta shige tak'i fitowa,mik'ewa yayj ya fice a d'akin jin an rufe k'ofa tayi saurin lek'owa tana duba d'akin ganin babu kowa tayi wurgi da bargon,a guje ta shek'a had'e da rufe k'ofa harda murza key,sannan ta dawo a bakin bed ta zauna tana maida numfashi,hakan da tayi niko nace
_"Ehh! lallaifa KHUBRA kin samu sauk'i...tunda gashi harda su gudu bayan ihu.._
Tunawa da bata yi sallah ba yasa tayi saurin tashi tayi hanyan toilet,wanka ta fara yi sannan ta d'auro alwala ta fito,doguwar riga ta zura ajikinta tayi sallah,bayan ta idar ta jima tana addu'o'i.
Knocking k'ofan da akayi yasa ta dafe chest enta tana jan numfashi da sauri kamar wacce taga abun tsoro..
Muryansa yasa ta dad'a fiddo ido waje ko a mafarki kam taji shi zata gane waye bare kuma ido biyu,dafe bakinta tayi idanunta sun dad'a bayyana tace
"BB kuma....? me ya kawo shi da wannan safiyan kuma...? Ina YAH KHALEEL en ya shiga bayan fitansa daga nan...?"
Ita kad'ai ta rasa mai bata amsa,kuma har lokacin batayi yunk'urin yin maganaba,sai data tabbatar da ya bar gurin sannan ta matso jikin k'ofan,a hankali ta bud'e tana lek'awa.
"Yeehhhh! AUNTY AMARYA..."
FATAHIYYA dake tsaye ta fad'a,a d'an tsorace KHUBRA ta kalleta
"Wallahi har kin bani tsoro..."
Dariya tayi mata sannan ta bud'e k'ofan tana juyawa ciki bayanta ta biyo dai² lokacin suka gaisa a hankali tace
"Ina ZUHRA'N kuma naganki ke d'aya.....Ko kuma dama keda BB kuka zo....?"
Kallon rashin fahimta tayi mata bakinta bud'e take fad'in
"AUNTY kika ce mene...?"
"Ohh! da baki ji me nace bane kam?"
"A'a naji mana kawai dai tambayoyin naki ne suka sani mamaki.."
Kallonta KHUBRA tayi tana fad'in
"Mamakin me kuma kan wannan y'ar tambayan...?"
"Amm! to ai AUNTY naji kina tambayana ne kamar baki san komaiba..."
Idanta tayi blanking sannan tace
"Kamar yayafa....?"
"Ehhh! Naji kina tambayana YAYA ZUHRA.."
"Ehh! laifi ne dan na tambayeta gani nai bata zoba kuma bayan ita yafi dacewa data zo en..."
Dariya sosai FATAHIYYA tayi sannan ta kalleta tace
"Hala kam AUNTY baki san tana gidanta ba itama ko...?"
A tsorace KHUBRA ta kalleta "Gidanta fa kika ce..?
Wane irin gida kuma kike nufi?"
"Uhmmm! gida dai na aure kuma irin wannan da kike ciki..."
Jikinta duk ya dad'a shiga shock da jin maganar FATAHIYYA amma sai ta daure tana fad'in
"To amma waye angon kuma ya akayi ni ban san da haka ba..?"
"YAH KHALEEL ne...."
Ta bata amsa a tak'aice.
Ai tuni ta dad'a fiddo idanunta waje tana kallonta,ckin tsoro murya na cracking ta furta
"Ni kuma wa nake aure kenan....?"
A dake ko FATAHIYYA ta furta
"BB mana...!"
Ai jin haka take yasa KHUBRA tayi freezing a gurin hannunta a saman chest baki kuma bud'e..............
*COMMENT FOR MORE PAGE'S........* 💃💃💃💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*©®2018*
*30/ʝųlყ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~___________________________~*
🎂🎂🎂
_All I got you for your birthday was this post. Hope you enjoy it! Try not to read it all at once._
_May God shower his choicest blessings on you. wishing you happiness, good health and a great year ahead._
_Once more Happy birthday wish you fruitful years *HAFSAT M.U.(REAL HEARFSEY)*._
*Happy Birthday sweet sis.* 🎂🎂🎂
🎁🎁🎁
_Here is my gift for u..._ 😉
*~___________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
5⃣5⃣
*I* danunta sun dad'a bayyana a fili saboda tsantsar tsoro da fargaba da suka taru suka mata yawa,a bakin bed en tayi ragwaf hannayenta tallafe da kumatunta,nan ta tafi duniyar tunani,d'an tak'aitaccen tunani tayi a hankali kuma ta kalli FATAHIYYA tana fad'in
"Wato shi yasa tunda aka fara hidiman biki komai namu ya zama iri d'aya,ashe da walakin aka ce 'goro a cikin miya'....To amma me yasa za ayimin haka bayan ga wanda ke sona kuma a auramin wani daban...?"
Kafin ta bata amsa BB ya shigo cikin bedroom en,fuskar nan a gintse kamar ba shiba,ya kallesu dukα tunanin KHUBRA a LOKACIN yaji abun da ta fad'a shi yasa tsilli² jin baiyi maganaba yasa ta saki ranta amma zuciyan tafa a lokacin banda skipping babu abunda take yi,sai k'amshi yake zubawa da ka ganshi zaka tabbatar da lafiya ta samu,a hankali ya juya yana daidaita zaman hulan a kansa ya furta
"Idan kun gama ku sameni parlor.."
Daga haka bai k'ara koda wasalin 'a' ba ya fice,a hankali KHUBRA ta tab'e baki kanta na k'asa tun shigowarsa SAI ajiyan zuciya da take,FATAHIYYA ce ta kalleta taga yanda take kamar a takure cikin salon tsokana tace
"AUNTY kijefa kuyi break ni kam sai dana gama nawa sannan na fito,so ni kam a k'oshe nake...."
Hararanta KHUBRA tayi kafin ta mik'e zata fita,da sauri ko ta rik'o hannunta tana fad'in
"AUNTY ince dai ba a haka zaki fita gurin YAYA'N ba ko...?"
"Mene to dan naje a haka..?"
"Haba dai kingafa face naki ko lip stick babu bare kuma powder,ke kam dai ai kya gyara face naki kafin ki fita,amarya ai da kwaliyya aka santa..."
"Ke ni da Allah kyaleni wane kwaliyyan zanyi kuma,ko dan ba auren so.....!"
Kafin ta k'arasa FATAHIYYA ta katseta tana fad'in
"Tabbbb! lallai AUNTY za kiyi wasa da damanki,ko kinsan da yawa y'an mata damar da suke nema kenan ko da basu son namiji zasu zauna da shi musamman ace yana da y'ay'an banki,bare kuma ace mijin yana da kyau....Kamar dai naki mijin...To wallahi AUNTY kiyi a hankali da mijinki dan idan y'an mata suka d'ora idonsu akansa sai dai kiji labarin ya canja salo,garama ki kamashi da hannu biyu-biyu ko da kuwa baki sonsa a hankali zaki fara sonsa..."
Tunani ta d'anyi cikin y'an dak'ik'u,tabbas tasan duk abunda FATAHIYYA ta fad'a mata gaskiya ne,ko ba komai kuma d'an uwanta ne na jini,ko da ace babu soyayya to tabbas akwai y'an uwantaka,kenan ya zama dolenta ta kula da shi kamar yadda zata kula da kanta ko fiyema da haka..
A fili kuwa sai tayi murmushi ta kuma godewa Allah daya sa Y'ar uwarta ta bata wannan shawaran,a ranta ta k'udiri niyyan ko da bai sonta to lallai ita kuwa zata koya masa yadda zai so ta,a hankali cikin sanyin jiki ta mik'e ta nufi gaban mirror kallon kanta tayi ta ciki tabbas ita da kanta ta san mai kyau ce,amma ai ana cewa idan kana da kyau to ka k'ara da wanka,cikin y'an mintuna ta fente fuskarta cikin simple make-up,har ta tashi zata fita again FATAHIYYA ta sake dakatar da ita,closet ta bud'e nan ta ciro mata riga da sket na wani holland mai kalar ja da adon kore,babu musu ta sauya kayan sannan ta feshe mata jiki da turaruka iri daban-daban ta kuma d'aura mata head tie en,das ya zauna kamar ashobe a kanta,duk wanda yaga wannan kwalliya ji zai inama ya saceta ya gudu saboda kyau da tayi,ita da kanta data kalli kanta a mirror sai da tayi murmushi saboda yanzun kam tasan tafi yin kyau sosai,musmman jan kala data sa daya had'u da farar fata,plat shoe ta zira sannan tayi hanyan parlor ta bar FATAHIYYA nan tana ta yaba kyau da tayi kafin ta fita ko sai da ta gama kyasa mata pictures sannan ta barta tana danna phone..
Kwance yake saman cuition da phone a hannunsa sai murmushi yake zubawa,da ganin alamu kasan yana cikin yanayin da yake jin dad'insa,tun kafin ta bayyana a gabansa k'amshinta ya iso,a hankali ya lumshe idanunsa yana shak'an sanyayyen k'amshin turarenta,idanunsa a haka har ta bayyana cikin parlor dai² zata wucesa ta kalleshi ta sake tab'e baki ai ko nan suka yi four eyes da shi,fuskarsa ya d'aure ganin abunda tayi,zata wuce ya dank'o hannunta had'e da fizgota,kansa ta fad'o take ta runtse eyes nata chest enta na harbawa da sauri-sauri,yanda tayi yasa shi kallonta sannan ya d'an saki fuska,dai-dai kunnenta ya kai bakinsa cikin wani irin salo ya furta
"Kina jin tsoro a kamaki kinyi laifi,amma kuma kin iya yin laifin ko...?
Nan gaba idan na sake kamaki kin min wannan abun zanyi maganinki..Kin jini ko..?"
A hankali ta d'aga masa kai alamar ta ji,idanunta har lokacin a kulle,eyes nata yake so ta bud'e ta kalle shi amma abu ya gagara,baya ga maganar ta daya ke son saurare,a hankali zuciyarsa ta bashi shawaran sata magana,rasa me zaiyi mata yayi wanda zaisa tayi magana.
A hankali ya kai bakinsa dai-dai kunnenta yana hura mata iska ciki,da sauri ko ta bud'e idanunta tana kallonsa,hakan da tayi yasa shi d'aga mata gira,da sauri ta girgiza masa kai alaman babu komai,ci gaba yayi da abunda yake,cikin voice nata mai nuni da wanda ke magana yana cikin wani hali ta furta
"YAYA ka bari..."
Kallonta yayi yana murmushin gefe
"Ohhh! da kina da baki kika d'aga min kai kaman wata lizard,ko kina ciwon hak'ori ne...?"
"Ni lafiyata k'alau..."
Ta k'are tana murgud'a masa baki,bata k'are abunda take son fad'a ba,ta tsinci d'an mitsitsin bakintan na futsara a nasa,sai da ya tsotse lip bam nata data sa tas,dan kansa kuma ya sake mata baki,sai dai har lokacin tana rik'e a jikinsa ai ko ganin yak'i sakinta har lokacin ga kuma tarin kayan kunya daya barta da shi yasa ta b'oye face nata a jikinsa,tana maida numfashi da d'aya da d'aya.
Tana kwance jikinsa shi ko babu abunda yake sai sakin smiling jinta a jikinsa yafi masa komai a duniya,bai k'i su dawwama a haka ba,da sauri kuma ya dakata da murmushin da yake saboda wani tunani da zuciyarsa ta bijiro masa da shi
"Shin ma wai kai da kake wannan zumud'in ka tabbatar da yarinyar nan na sonka ne ko kuwa kai kad'ai kake kid'anka kake kuma rawar....Wannan rawar kan da kake idan kuma yarinyar ba wani sonka take bata,shi kenan ka yada girmanka?"
'Dan sassauta rik'on da yayi mata yayi,a zuciyarsa ya furta
"Ya Allah ka taimaki bawanka a dai² lokacin da baiyi tsammani ba......Ya Allah ina rok'onka a karo na biyu kasa ba ni kad'ai ke fama da dakon soyayyanta ba..."
Kallon mamaki KHUBRA ta bishi da shi tana fad'in
"Ni ka sake ni na tashi,ka wani rik'e ni bayan kuma sai maganar kana son wata kake,to idan za kayi maganarka sai ka bari kayita kai kad'ai amma ka denamin ni dan ban son ji ni..."
Ta k'arasa tana ture shi,kallonta yayi yanda tayi magana yasa shi sakin murmushi wato dai maganar da yayi a zuciyarsa a fili yayita kenan.
Baya ga haka kuma mene ne dalilin daya sa ta fad'in haka,fuskarta kad'ai zaka kalla kasan ranta a b'ace yake,dan ya kauda zancen yasa ya saketa da sauri ko ta mik'e tana gyara riganta daya d'anyi squeezed ta gaba,cikin sauri ta bar gurin,shi dai kawai ya bita da kallon mamakin kalmominta.
Har ta b'ace masa sannan ya sauke idanunsa yana murmushi lallai zai sha fama,dan kam ya tabbatar za tayi bak'in kishi da ganinta.
Tunawa yayi da dalilin da yasa ta fito,gashi yanzun kuma ya koreta.Lallai ya zama dole ya kirata,sai yanzunma ya tuna da jiyafa ba wani lafiya gare taba a haka kuma suka kwana,amma yau ji yanda tayi masa kamar ba itaba,bedroom en nata ya nufa,nan ya hangota kwance ta juya baya,FATAHIYYA nata fama da waya a hannu,ganin shigowansa yasa ta tab'ota da sauri ta juyo tana kallonta,ganinsa cikin d'akin tayi saurin kauda kanta daga gurin
"Kin taso kinyi break ko kuwa sai na maimaita miki warning da na miki..."
Banza tayi da shi ita ko FATAHIYYA da sauri ta fice a d'akin,ganin tak'i kula shi yasa ya k'araso inda take cike da isa ya d'agota,sai da ya tsaidata a kan k'afafunta sannan ya furta
"Oyaaah! muje muyi break sai na baki labarin abunda kike son sani..."
"Na k'oshi ni..."
"Da kika ci mene zaki fad'i haka...Maza wuce muje kafin na sab'a miki.."
Bakinta ta kyab'e za tayi masa tab'ara,bai tsaya sauraronta ba ya kama hannunta suka fice..
Har suka kammala break fast bata sake kula shiba,shi ko duk spoon d'aya da zai kai bakinsa sai ya kalleta yayi murmushi,a haka har suka kammala,ita ta fara ture plate nata tana yamutsa face,yana kallonta bai ce komai ba har ya kammala,tattara kayan tayi sannan tayi kitchen shi kuma ya koma cikin parlor,da sauri FATAHIYYA ta tadda ita a kichen amsan kayan tayi taba fad'in
"Haba AUNTYNAH ina nan kuma wane aiki za kiyi,kije ki huta bari na wanke kayan..."
Murmushi kawai tayi tana mamakin halayen FATAHIYYA a yanzun kamar ba ita ce mai d'an banzan jin kannanba a da,da sauri kuma ta juya zuwa parlor.
Tsaye ta same shi yana dad'a gyara cap nasa,tab'e baki ta sake yi da sauri kuma ta rufe bakin saboda tuna abunda yace d'azun tana kuma kallonsa,juyowa yayi yana kallonta dai² tana shirin zama cikin cuition.
"Ammm! zan fita ga FATAHIYYA nan ku zauna tare zanje gida na dawo ba jimawa zanyi ba kinji...?"
Kallonsa tayi tana mik'ewa tsaye
"YAYA nima zani kaji....kaga jiya dama banga ZUHRA ba yanzun sai ka kaini gurinta..."
Dariyar rainin wayo yayi kafin ya rik'o hannunta ya zaunar
"Haba BABY waye ya fad'a miki amarya tana zuwa gida a irin wannan ranar..? kiyi zamanki nima ba dad'ewa zanyiba kinji...?"
Baki ta kyab'e za tayi kuka,shi dariyama take bashi duk wani abu na yara ta iya
"Noo! kada kiyi kuka kinji yanzun zan dawo,barima nayi sauri naje ina son mu had'u da KHALEEL ne kinji...?"
Kai ta kad'a masa tana cuno baki,sakinta yayi da sauri kuma ya fice dan ya tabbatar idan ya biye mata to ko babu inda za shi,yana fita harabar gidan ya daidaita tafiyansa daga saurin da yake yi,KHALEEL ya kira yana fad'in
"MALAM ai sai kazo ka d'auke ni ko,tunda kunmin auren dole kuma name ne na wani yimin wulak'anci bayan kuma na karb'i matar da kuka had'a baki kuka auramin...?"
KHALEEL dake driven jin abunda BB ya fad'a yasa shi sakin baki da mamaki shimfid'e saman fuskarsa ya kashe wayan,sai da ya zo bakin get sannan ya kirashi,yana d'auka ya furta
"Idan kaga dama ka iya fitowa mu wuce ko...?"
Daga haka ko bai bashi damar yin magana ba ya kashe,bakin get en ya fito yana ganin motan babu magana ya bud'e ya shiga ba tare da ya kula shiba ya rufe k'ofan yana gintse fuska shi a dole ga wanda akama auren da baya so.Kallonsa KHALEEL yayi ya d'auke kai kamar ana fisgar maganar daga bakinsa ya furta
"MR pretender ka gama yanzun....?"
Kallon sa yayi cike da son tambayansa,gane hakan da KHALEEL yayi yasa ya furta
"Ciwon SO mana...ba shi ya kwantar da kaiba ne...? ko an fad'a maka bamu san halin da kake ciki bane..?"
"Allah ya sawak'e ciwon so kuma kamar wani mara abun yi zan kwanta ciwo kuma a hakama wai na so.."
Dariya sosai KHALEEL yayi
"Ehh! lallaifa ka samu lafiya tunda ka samu ABINDA RANKA KE SO ai dole kayi wannan maganar..Amma tunda hakane yanzun muje gurinsu ABBA kaga tunda baka son auren sai a warware tun tafiya bata yi nisa ba ko....?"
Yamutsa fuska BB yayi sannan ya furta
"Ka makara kuma ai dan ni a tsarina babu saki...Kuma ko bayan hakama ni yanzun ai na riga da na karb'a tunda babu yadda zanyi,ko ba haka nace maka ba...So no need kuma ace za a warware zanyi taimako..?"
"Kutt!!! wai K'anwar tawa kake cewa zaka taimakawa...?"
"Yeahhh! Itanfa.."
"Haba MAN kaima da kanka kasan ta wuce haka wollahi kai dai kawai ta taimaka maka dan karka mace akan so,kama rufawa kanka asiri kayi shiru haka nan,dan kana ci gaba da magana zan nad'e komai na sanar mata,sannan kuma zan bata shawaran ta baka wahala ne ko me kazo da shi kada ta yarda..."
Dariya sosai sukayi daga haka kuma BB ya canja musu firan..Haka har suka iso gidan iyayen nasu.
Gidan a cike da jama'a y'an biki da basu k'arasa tafiya ba,bayan sun gama gaisawa da su,suka wuce babban parlor inda su ABBA suke tattaunawa da su OLD KHALEED da kuma KAKA da k'afarsa tayi kyau kamar ba shi yayi muguwar jinya ba..
Kowa yaga BB sai yayi dariya a cikinsu,shi dai kam bai iya cewa komaiba har sukayi shirin ficewa bayan sun gama gaishe-gaishen suka kama hanyan komawa gida,a hanya ne BB ya kalli KHALEEL yana fad'in
"MAN nifa har yanzun ka sani a duhu wallahi kuma kak'i warwaremin yadda wannan al'amarin ya faru.."
'Dan murmushi yayi kafin yayi parking gefen hanya ya furta
"Zaka iya tuna wata rana da muka je gurin UMMI akan maganar auren KHUBRA da nake sonyi a wancan lokacin...?"
Kallonsa kawai BB yayi ya girgiza masa kai
"Baka tuna ba ko..?"
Nanma kai ya sake d'aga masa
"Toh! idan baka mantaba kamar yadda na fara fad'a maka yanzun tun a wannan ranar dana jema da UMMI maganar wacce mukayi a gaban idonka,yanayin yadda kabar gidan shi ya bamu tsoro,a take UMMI tasa nabi bayanka amma ina fitowa na tarar har ka shiga mota wanda a k'ok'arinka na yin reverse har ka daki round about amma ko kulawa baka yi ba,in tak'ai ce maka zance har biyoka nayi a baya,sai da na tabbatar da ka isa gida lafiya sannan na koma,a nan na shaidawa UMMI duk abunda ya faru...Kasan abun da ya bani mamaki a lokacin?
Bud'ar bakin UMMI bata furta komaiba sai cewa tayi KISHI ke damunka kuma ba kan komaiba ne sai kan wannan maganar da nayi mata,tun daga lokacin UMMI tayi ta bani baki akan nayi hak'uri da maganar KHUBRA,da tarin shawarwarin da take bani yasa na mata alk'awarin na janye neman auren,sai dai kuma abunda yasa bamu nuna a fili ba shi ne ganin yadda a fili kake nuna halin ko in kula da lamarin yarinyar bayan kuma a gefe kana fama da dakon soyayyarta,wannan dalilin yasa muka shirya maka wannan drama daka gani.
A ranar d'aurin aurema nasan zaka ce to kuma me yasa aka fara sanar da d'aurin aure da sunana ko? to gaskiya wannan kuma ba daga mu bane daga mai sanarwar ne dan dama a yadda muka shirya mun barshi a kan sai a gurin d'aurin aure za kaji komai...
Mistake en da aka samu yasa ka bar gurin ba tare da ka tsaya kaji d'aurin auren ba,wanda yanayin da na tarar da kai bayan gama d'aurin auren yasa nayi niyyan sanar maka da duk wani shirin da muka yi maka,sai dai kak'i saurarona,dalili kenan daya sa al'amura suka zo a haka...ina fatan yanzun ka fahimta..."
Kallonsa kawai BB keyi fuskarsa d'auke da wasu irin expressions yama rasa me ya kamata ya sakawa da aminin nasa da shi,a hankali ya rik'o hannunsa sosai
"Ban san da wane irin kalmomi ya kamata nayi maka godiyaba,kamin abunda ba zai tab'a gogewa daga zuciyata da rayuwataba,bani da bakin da zan iya gode maka,na gode na gode sosai d'an uwana...Allah ya baka mace ta gari wacce zata kula da kai.."
Da sauri KHALEEL yana murmushi ya furta
"Tabbas ya bani sai dai fatan Allah ya bamu zuri'a ta gari..."
Sai da suka gama hiran yadda al'amura suka wakana sannan suka yi gaba,sai da ya sauke BB a gida kafin ya wuce nasa gidan.
A parlor ya tadda su suna fama da kallon wani adventure film a MBC 2,nan ya zauna shima tun shigowansa da suka amsa sallama KHUBRA ko kallonsa bata sake yiba,har after asr prayer FATAHIYYA na gidan sai wajejen 5 sannan tayi niyyan tafiya gida.
Driver'n daya kawo musu lunch shi ya dawo da dinner sannan suka tafi da FATAHIYYA,gidan yayi mata shiru babu abokiyar hira,sai BB dake kwance yana faman chat,ita dai bata da aikin daya wuce idan ta kalleshi ta tab'e baki ta kuma juya taci gaba da kallonta..Har bayan Maghreb suna a haka wajejen 10 kuwa suka sake sa wani film mai suna *DRAG ME TO HELL* film en abun tsoro musamman yadda a farkon film en inda ake marin iyayen yaron da malamar dake masa addu'a saboda yadda yake yi kamar mai iskokai,yadda aka cilloshi daga saman stairs bayan nan kuma k'asa ta bud'e wuta na ci ta ciki take kuma yaron ya nutse...
KHUBRA dake wani cuition en daban,bata san lokacin data koma kusa da BB ba,yana chat lokacin yaji mutum a kusa da shi,kallonta kad'ai yayi yaci gaba da abunda yake yi,kallonta take ci gaba da yi idan taga abun tsoro saita sake shigewa jikinsa,shi kuma yak'i kulata dan bai sanma me ake a channel enba,maganar da suke da KHALEEL ya d'auke masa hankali kan maganar makaranta da yake ganin ya kamata ace an sa KHUBRA'N.
Dai² gurin da yarinyar ta farka lokacin da wani k'waro ya shige mata hanci ta farka a bacci,har ta koma ta kwanta taji abu kusa da ita juyawan da za tayi tayi arba da wani irin halitta...Take ko suka kwala ihu tare da KHUBRA data gama cukuikuye BB,wanda ihunta yasa shi kallonta da kuma cikin parlor'n,TV en ya kalla take ya gano dalilin daya sata yin hakan,murmushi yayi yayi switching TV en,sannan ya mik'e da ita a jikinsa saboda yadda ta rik'e shi ya tabbata ba zata yadda ya kyaleta ita d'aya cikin parlor ba....
*~TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_.®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*©®2018*
*31/ʝųlყ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
5⃣6⃣
*H* anyan bedroom enta ya nufa ita dai tayi luf a jikinsa,k'wak'warran motsi ta gagara yinsa bare yasa ran zasu rabu,sai da ya tabbatar da ya zaunar da ita a saman bed sannan ya mik'e da niyyan fita,hakan KHUBRA data gani shi yasata buga wani tsalle daga inda take,aiko nan ta rik'e shi cike da son tayi kuka ta fara magana
"YAYA ina kuma zaka tafi...?"
"Bedroom nawa zan wuce mana,wani abu ne ya faru kuma..?"
Ya tambaya kamar bai san komai ba,kame-kame KHUBRA ta soma fuskarta cike da damuwa,duk wani abu da take idanunsa na kanta,shi kad'ai yake sakin murmushin mugunta,jira kad'ai yake tace ba zata iya zama nanba,ai ko take ya jiyota tana fad'in
"Dan Allah YAYA ka tsaya a nan,baran iya zama ni kad'aiba kaji...?"
Idanunta duk sunyi rau-rau wanda k'iris take jira ta fashe masa da kuka,a hankali ya fara magana
"A'a BABY ni kuma nawa d'akin waye ne zai kwana ciki...Ki kwanta kinji babu abunda zai faru,kinga jiyama na tsaya inda kike saboda na tarar dake baki jin dad'i...kinga yau kuma tunda kinji sauk'i saina tafi nawa room en ko...?"
Hakan daya fad'a shiya jawo hawaye suka fara tsere a saman fuskarta,cikin sheshshek'ar kuka take magana
"Dan Allah YAYANAH kaji kagafa ina jin tsoron wannan abun na can..."
"Haba mana BABY idan kikayi addu'ah babu abunda zai sameki kinji ko,maza je kiyi wanka ina jiranki kafin nan sai na wuce..."
"A'a wollahi ni bazan iya shigaba ni kad'ai sai dai ka rakani....Dan Allah YAYA kaji zaka kwana a nan...?"
Shiru yayi yana kallonta har lokacin kuma hawayen basu daina zubowa daga idanuntaba
"Lallai ashe haka take da d'an banzan tsoro...? in dai kuwa haka ne to tabbas babu wata wahala da zai sha gurin shawo kanta.."
Hannunsa ta dad'a k'ank'amewa jin yayi shiru bai ce komaiba while her eyes continuously shading tears,a hankali ya d'an kalli yadda ta cukuikuyeshi sannan ya d'aga mata kai yana fad'in
"Ehmmm! muje dai kiyi wanka tukuna sai muyi maganar latter.."
'Dan murmushi ta saki,da kansa ya goge mata face nata sannan yaja hannunta zuwa toilet,ko da suka shiga bayan ya rakata yana k'ok'arin fitowa nan fa KHUBRA ta kafe akan itafa lallai sai dai ya jirata nan cikin toilet,rarrashi babu irin wanda bai mata ba akan ta hak'ura ya jirata cikin room en amma ina sam tak'i amincewa
"Ni kam BABY ban san me kuma kike so nayi mikiba..Nace zan jira ki fito.."
"Ni dai gaskiya a'a idan baraka tsaya ni nanba Allah zan fasa wanka'n ma gaba d'aya.."
Cikin zuciyarsa yake fad'in "lallai na had'u da rigima,banda abunta ta ina zan iya jiranta a nan...?"
"YAYA nifa tsoro nike kada su biyoni nan..."
"To banda abunki ai canma zaki na ganina ba sai na tsaya nanba..kiyi wankanki babu abunda zai sameki ko ina nan ko bana nan.."
Yana fad'in haka ya juya zai fice,take ta doka tsalle ta mak'alk'ale shi tana sakin sabon kuka
"Allah kuwan nama fasa wankan gaba d'aya..Shi kenan dan bani da kowa sai kace zaka barni nan salon suzo su d'auke ni nima..Kuma Allah saina fad'awa ABBA su zo su maidani gida tunda haka ne..."
Sake baki yayi yana kallon sabon salon tab'aran nata,komai nata cike da yarinta take yinsa,shi kam bai san kuma ya zai mataba,amma kam tabbas bai iya jiranta cikin toilet en kome za tayi kuwa.A kaikaice ya kalleta har lokacin tana faman matse idanu,fuskarta duk ta sauya tayi ja saboda azabar kuka data sama ranta fitina.
"Haba mana duk abun bai kai nanba ta ina zaki fad'awa ABBA akan wannan d'an maganar shi ne zaki kai musu k'arana....?"
"To ba kaine kace baraka jiraniba nayi wankan.."
"Haba mana sai kace k'aramar yarinya zakiyi wanka gabana ko baki jin kunya tane...?"
"Ina ji amma wollahi baran iya zama ni kad'ai cikiba...Sai dai ka zauna ka jirani..."
"Lallai BABY kina da rigima ta ina namiji kamata zan tsaya kallonki kina wanka a gabana...Da sake wollahi 'wai an bawa mai kaza kai' idan kuma bani kike so nayi miki wankan ba to kam ya zama tilas ki kyaleni nayi waje..."
"Tabbbbb! Allah ya sawak'e ta ina zan wani tsaya k'ato da kai ka wani yimin wanka,yo to ko ina jinya ai bakamin wankaba,k'arshe kam sai dai wollahi a bari idan na samu sauk'i nayi...Gara nayita zama da datti..."
Bud'e baki yayi yana kallon yadda take zuba mishi fitsara,harda su murgud'a masa bakii,hannunta dake sak'ale da nasa ya dank'a sosai har sai da tayi y'ar k'ara
"Ba dai kin iya fitsara ba,zan gyara miki zama soon....Kin ce ko kina jinya babu maiyi miki wanka ko...?"
"Eh en to da akwai ne...?"
Murmushi ya saki ganin har lokacin bakinta yak'i mutuwa,duk da irin yadda ta rintse idanunta kan zafin rik'on da yayi mata
"Oyaahh! sake min hannu na fice wanka kuma kada kiyi,ki fito haka nan kiga yadda zanyi dake..."
"Allah baran sake maka hannu ba...sai ka jirani tukuna.."
"Kin san Allah idan baki sake mun hannuba zan miki abunda baki tunani yanzun..."
Tab'e fuskanta ta sakeyi tana sakin kuka,cikin muryan kukan kuma take fad'in
"Allah sai dai kayi koma mene amma kam ban sakinka yau...Salon ina wanka kawai su zo su d'auke ni,ni wollahi a'a babu inda zaka..."
Murmushin mugunta ya saki,kafin tayi wani k'wak'waran motsi ya sureta bai direta ko inaba sai cikin bath tube,duk mutsu-mutsunta da ihun da take masa akan ya kyaleta bai sauraretaba sai daya rabata da kaf kayan jikinta fuskarsa a d'aure yake magana
"Kin tsaya ko kuwa saina mareki ban fad'a miki kiyi wankan da kanki ba kika k'i...?"
"Wayyoo! MAMA dan Allah ka kyaleni zanyi na yadda ka fita wajen zanyi da kaina,dan Allah kada ka kalleni ka rufe idonka..."
Duk maganar da take idanunta a rufe suke hannayenta a saman chest nata tana k'ok'arin rufe jikinta..Ko ta kanta baibiba saima hannunta daya ke k'ok'arin b'amb'arewa daga inda ta musu matsuguni duk da babu abunda suka rufe daga jikinta da take son b'oyewa.
Baki ya tab'e suna kuma ci gaba da kokawa da ita akan abunda yake niyyan yi.
"Kin san Allah...."
Kafin ya k'arasa ta bashi amsa
"Da ce maka akayi ban sa shi ba..."
Da mamaki ya kalleta
"Lallai wato bakinki bazai mutuba ko...?"
"To dama ance maka zai mutu ne ai shi da mutuwa sai ranar dana daina numfashiiiiiii....."
Kafin k'arasa bashi amsan yasa yatsansa ya d'alle mata bakin fitsaran
"Saboda kin raina ni yasa ina magana kina bani amsa ko kuwa...?
Shiru tayi tana murza bakinta dayake mata zafi coz taji shigan abunda ya mata,baki ta kyab'e za tayi masa kuka
"Kin min shiru ko saina k'ara miki wani...Duk ranar da nayi magana kika sake bani amsa makamanciyar wannan Allah sai nayi maganinki.."
"Nifa ba wani abu nace ba..."
"Kin min shiru ko kuwa...? Na tambayeki ne da zakiyi magana...?"
Bakinta ta kame tana k'unk'uni k'asa-k'asa wanda sautin magana sam baya fita
"Zagina kike yi ko..?"
Idonta ta bud'e da sauri ta marairaice fuska
"Allah ya baka hak'uri ni ba zaginka nayiba fa...amm! dan Allah YAYANAH kaji ka bari zanyi da kaina..."
Wani mugun kallo ya watsa mata yana fad'in
"Ina wasa dake ne kam..?"
Kai ta girgiza masa
"Idan na sake jin bakinki akan wannan maganar Allah zan sab'a miki.."
'Dif tayi ta maida idonta ta kulle,tana ji tana gani haka ya shiga dirzarta yanayi yana kallon fuskanta yaga ko ta bud'e idon amma still suna kulle sai chest enta dake harbawa da sauri-sauri,wankan da baifi 15 minutes ba sai da aka b'ata sama da one hour ana abu d'aya guri d'aya kawai yake wankewa idanunsa tsaye kyam a guri guda ya kasa kauda su,gajiya tayi dan da farko dama cewa tayi barata sake magana ba,ganin abun nasa ba na k'are bane ta furta
"YAYA nifa na gaji wannan wankan yak'i k'arewa kamar an kawo maka y'an matan duniya ka wanke.."
Murmushi yayi shi kad'ai kuma ya furta
"An kusa gamawa ai..."
"Tabbb! inafa aka kusa abu da har yanzu a gurin...."
Bakinta tayi saurin dasawa pad lock jin b'aramb'aramar da take shirin yi.
"Kin ce mene...?"
"A'a fa babu komai...Dama ina son cewa bacci nake ji ne.."
"Ohh! na zata suma kike ji ai,ashe a bacci kad'ai aka tsaya...da kinyi da kanki ai baraki jima haka ba...Ko da yake dama haka kike so ai tunda nayi miki da kaina shi kenan hankalinki ya kwanta..."
Haushin maganarsa taji sosai dan tsabar wulak'anci ita zai kalla ya fad'awa haka...amma saita gimtse ta fasa magana saboda kada ta jawowa kanta wani abun dan kam bata manta d'alle mata baki da yayiba d'azun ba jimawa.
Da k'yar ta samu Allah dai ya taimaketa ya d'auraye mata kumfan ya nad'eta a towel,d'aukota yayi ya fito da ita,a kan bed ya direta yana fad'in
"Ki jira na fito yanzun.."
"YAYA ina kuma za kaje to...?"
A kaikaice ya kalleta yanafad'in
"Zanyi wanka ne yanzun ina fitowa"
"Wayyoo! Allah na dan Allah YAYA ka tafi dani wollahi ni tsoro nake ji..Baran iya zama nan ni d'aya ba.."
Kallon ta kawai ya tsaya yi,lallaima yarinyar nan tana son jefa shi cikin bala'i idan ba neman fitinaba irin nata ta yaya zai tafi da ita cikin toilet,bayan tarin fitinar data ke neman jefashi wanda ba don ya kai zuciyarsa nesaba da yanzun a toilet tuni labarin ya canja salo.A fili kuwa sai cewa yayi
"A'a ki dai jirani nan zan bar miki door en a bud'e shi kenan..?"
"Aaaaa! ni dai a'a gaskiya.."
Fuska ya had'e yana kallonta cikin alaman kamar ransa ya d'an soma b'aci yace
"Shi kenan ai sai ki taso,amma kam ki tabbata idan har k'afarki ta taka cikin toilet ennan to ina mai tabbatar miki da sai dai kiyi min wankan...Zab'i ya rage naki ko ki zauna nan ko ki bini ki kuma yimin duk abunda nasa ki.."
Da sauri ta kalleshi tana komawa tana zama,gira ya d'age mata yana fad'in
"Yesss! haka nake nufi,zaki bini har yanzun...?"
Da sauri ta kad'a masa kai alamar a'a,shiko murmushi yayi a zuciyarsa yana fad'in
"Da kin ce eh ai da kuwa kinga d'anyen kai"
A fili kuma ya furta "Kin ceci kanki yarinya.."
Ita dai kanta nak'asa har ya bar gurin ya shige toilet a yayin da ya bar k'ofan a bud'e tana jiyo motsinsa.Tagumi ta buga idanunta na kan door en har ya gama abunda yake ya fito d'aure da towel,d'agowa tayi ta kalleshi ganinsa daga shi sai towel yasa tayi yin ihu,da sauri ya iso ya rik'e shoulders enta yana fad'in
"Lafiya kikema mutane ihu da daren nan..?"
"Ni kasa kayanka ka wani fitowa mutane a haka.."
Wani uban tsaki ya ja shi a tunaninsa bai kawoma abunda yasa take ihu ba kenan,amma ya ya iya da wannan shugabar rigimar tasa,kan dole ya lallab'ata tayi masa shiru amma ta dage sai ya tashi ya sa kaya,sai daya juya mata baya sannan ya fara magana
"Ke wollahi ban tab'a ganin mutum mai rigima irin kiba,sai kace ke ba towel en ne a jikinki ba zaki dasa ma mutane rikici da wannan daren.."
Bata kula shi ba har ya gama maganarsa shi kad'ai coz a lokacin ma abunda ya hanata tanka masa saboda kada ya korata nata d'akin,ita kuma tsoro bazai barta ta iya kwanciya ita d'aya ba.Har nata bedroom en ya rakata ta d'auka abunda take buk'ata sannan suka dawo tare,yana kwance saman bed yana fama da waya ita kuma ta juya a nan ta shirya cikin riga dogo mai laushi turarukansa ta feshe jikinta dasu dan ba abunda zai sata fita yanzun,har ta gama ta hauro saman bed en daga gefensa ta kwanta,da sauri ya kalleta yana matsawa gefe
"Heyy! MADAM da fatan dai ba nan zaki kwantaba ko..?"
Marairaicewa tayi kamar za tayi kuka
"YAYA toh ina zan kwanta..?"
"Can zaki koma a can zaki kwanta.."
Ya mata nuni da cuition dake can gefe,da sauri ta kalleshi kamar za tayi kuka tana fad'in
"Dan Allah kayi hak'uri wollahi baran iya kwanciya canba,kaga ina jin tsoro sosai..Dan Allah kaji.."
Dad'a d'aure fuska yayi yana magana like serious
"Kinga MALAMA gara dai kiyi nesa da ni,ni babu abunda zaisa na kwana tare da ke a guri d'aya."
Kuka sosai tasa masa tana ta faman begging ensa,juya mata baya yayi alamar babu wasa a cikin maganarsa ita kuma tak'i dainawa,a hankali ya juyo yana fad'in
"Ok! shi kenan an gama ya isa haka kukan.... Shugabar masu kula ta duniya... Idan kin yaddafa amma ko ina da sharad'i.."
Da sauri ta matso tsakiyan bed en tana fad'in
"Allah na yarda koma mene ne ba zan maka musuba kaji.."
"Kin tabbata...?"
Nanma ta sake d'aga masa kai da eh
"Ok c'mon..."
Da sauri ta shige jikinsa ganin yadda ya bud'e mata hannu,hannunsa ya mayar ya rufe,yana sauke wani wawan ajiyan zuciya,a kunnenta ya rad'a mata
"Kin ce kin amince da sharad'ina ko..?"
Kai ta sake girgizawa
"Ok...! Duk abunda kikaga nayi ban son magana,kin gane ko..?"
Again ta sake girgiza masa kai
Daga haka bai sake magana ba yayi musu addu'ah,ita dai KHUBRA tana kwance jikinsa babu damuwan ko wani abu da zai je ya dawo,yayin da a b'angaren BB jinta a karo na biyu a cikin jikinsa jiyoyin sha'awa suka fara motsawa,a hanakli ya fara shafa bayanta yana dad'a shinshinar jikinta.Cikin alamun bacci ta ce
"YAYA ka bari nifa bacci nike ji.."
A kunnenta ya rad'a mata
"Baran iyaba BABY ba na fad'a miki ban son magana ba.?"
"To ni ka kyaleni na ce banso dai ko..?"
Tana maganar tana kuma ture hannunsa dake yawo cikin riganta.
Da k'yar ya iya bud'e idanunsa da suka masa nauyi baya ga colour da suka soma sauyawa.Tuna yadda suka yi yasa ya mirgina gefe yana fad'in
"Ok! tunda baki so maza tashi ki koma d'akin ki..."
Jin haka yasa ta tuno yadda yarinyar film en ke shan wahala da sauri ko ta furta
"A'a a'a! na yarda.....Amma dai dan Allah YAYA ka bari Allah babu dad'i abunda kakemin kaman tafiyar tsutsafa nake ji a jikina.."
'Dan murmushi ya sake dan yana ganin yadda take maganar
"Ok...! tunda baki so ai na baki zab'i zaki iya komawa d'akinki.."
"A'a ai na fasa tafiya baran iya kwana ni d'aya ba.."
"Ok! toh zo nan.."
Babu musu ta sake shigewa jikinsa,idanunta runtse kamar wani zai kamata,tana ji tana kuma gani yaci gaba da sarrafata son ransa................
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*©®2018*
*2/ɑմցմՏԵ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
5⃣7⃣
*A* hankali cikin nutsuwa yake aika mata sak'onninsa wanda yasa lokaci guda jikinta yayi mugun sanyi,cikin dabara yake juyata side zuwa side,komai da yake yi yana yinsa ne cikin nutsuwa coz yana gudun kada su samu matsala.
Soyayyarta game da tausayinta su suka narka masa zuciya wanda sune sinadarin da yasa yake lallab'ata tamkar tsoka d'aya a cikin miya,yanayin jikinta da kuma halittun da Allah ya wadatata dasu wanda ya sake yin tozali dasu su suka k'arasa rud'ashi game kuma da birkita masa lissafi,wad'anda sune sukayi jagora na rusa duk wani plan nasa na son ya bita a sannu,cikin zafi-zafi ya koma aika mata da sak'k'onninsa masu girma wanda suka sa KHUBRA kasa jurewa,da farko ta so ta musa ma buk'atarsa kamar yadda a farko tayima kanta alk'awarin bazata hana shi hak'k'insa ba da Allah ya d'ora mata,sai dai kuma yanayin y'an aikensa su suka sa ta bada kai bori ya hau.Cike da so da kuma k'auna wanda zuciyarsa ta kasa kiyasta adadin hakan a tare da ita,duk kuka da kiran da KHUBRA kewa y'an gida kan neman taimako babu abunda yasa BB ya d'aga mata k'afa face k'aimi da azama daya sake k'arawa na ganin ya cilla kwallonsa a raga,bayan komai ya lafa yana rungume da ita cikin jikinsa hawayenta har lokacin suna ci gaba da sauka saman chest nasa,da sauri ya mai data k'asa yasa hannunsa yayi cupping face nata,harshensa yasa yana d'auke mata duk wani hawaye dake biyo fuskan nata,cikin kunnenta kuma yana rad'a mata how he luv's her,ita kam KHUBRA a wannan lokacin damuwarta yadda jikinta ke mata azaba,amma kuma wani b'angare na zuciyarta,na tare da shi kalamansa na dad'a narka mata ilahirin gangar jíkíntα,sαí dαí kumα wαní bígírє dαgα zuciyarta na tunatar da ita girma da kuma lokacin data shafe da soyayyarsa data jima a mak'ale cikin zuciyarta tun a wancan lokacin na baya wanda duk ranar data tuna rabuwarta da shi ta k'arshe cikin mafarkinta dai dai tayi murmushi mai ciwo,sai gashi yanzun ta same shi a gaske tunanin da bai tab'a zuwa zuciyarta ba kenan murmushi tayi a lokacin mai cike da sukuni,idan har bata mantaba tun bayan zuwanta gidansu ZUHRA bata sake mafarki da shiba,a she a lokacin'ma suna kusa da juna,sam BB bai san mai ke gudana a tare da itaba a lokacin shi dai kam burinsa a lokacin bai wuce ya kafa gwamnatinsa ba duk kuwa da yanda yake da yak'inin kalamansa na tasiri a tare da ita,da sauri ta dawo duniyarta tana sauraren kalaman da suke mata yawo cikin jini da b'argo na jikinta,a wannan lokacin duk wata y'a mace da zata saurari kalaman dake fitowa daga bakin BB to tabbas babu makawa sai ta fad'a TARKON K'AUNA koda kuwa ace bata tab'a tsintar kanta cikin soyayya ba,halin da take tsintar kanta a wannan lokacin da BB yasan halin da yake jefa zuciyarta to da tabbas babu abunda zai sa bai k'ara k'aimi gurin ganin k'arasa narkar da ilahirin zuciyarta ba,ji take a lokacin inama tana da bakin magana to kuwa da tabbas babu abunda zai fito daga bakinta sai dai tace
"Ya barshi haka nan tun kafin zuciya da gangar jikinta ya gama yin melting saboda girman kalaman da yake amfani dasu..."
Sai dai kash babu bakin magana bare wannan kalamai su fito daga bakinta,haka taci gaba da saurarensa.
Duk da ganin irin sa'ar da tayi a matsayinta na wacce tayi dace da salihin miji hakan ba zai hanata kukaba saboda ta gurzu a hannunsa,duk fitsara irin tata data ke ji da ita a lokacin kam tayi k'us babu baki sai kunne.Wani wawan ajiyan zuciya ta shiga saukewa akai-akai,tausayinta duk ya cika shi ganin irin halin da ya jefa abar k'aunar tasa,rarrashi kam ya shashi a cikin wannan dare mai cike da d'umbin alkhairai wad'anda baki ba zai iya lissafasuba.
Kiraye-kirayen salla'n asubah shi yasa shi yunk'urin mik'ewa ya gyara mata kwanciyanta dan a lokacin kam tuni bacci yayi gaba da ita cike da wahala take baccin idanunta sun shige ciki saboda kumburi da suka yi,fuskarta ya shafa sannan ya ja mata duvet en ya rufeta,ya nufi hanyan toilet sai sakin murmushi yake shi kad'ai,sai daya tabbatar ya tsarkake jikinsa,ya kuma tanadi ruwa mai zafi irin wanda ba zai cutar da mutum ba,sannan ya dawo baccinta har yayi nisa,bai saurara mataba sai daya kaita har cikin bath tube,jinta cikin ruwan daya ratsata wani sabon azaba ya ziyarceta data ji shi from head to toe,take tayi wani uban zillo tana shirin fitowa,da sauri ya maidata ciki yana fad'in
"Easy baby..."
Sabon kuka tasa masa,murya dishii-dishi ta soma fad'in
"Bayan tarin muguntar da kayi min bai isheka ba saika had'a da k'arasa ni....Wannan ma ai mugunta ne kawai ka kama kana wani dafani kamar ka samu ganda...kuma Allah sai ya sakamin kan muguntar da kamin.."
Yana jinta sai murmushi yake yana kuma bata hak'uri dan yasan shi ne mai laifi.Cikin kuka take ci gaba da fad'in
"Ai dole ka sani gaba kana bani hak'uri tunda kasan ka gama da ni,inba muguntaba ai sai dana ce maka ban so amma ka wani dage...harda wani cewa sharad'i ashe sharad'in mugunta ne bana komaiba..."
Sai da yayi murmushi sannan ya sunkuya cikin kunnenta yake fad'in
"Yanzunma ki gama min fitsaran ina da k'arin sharad'i..."
"Wallahi a'a babu wani sharad'inka da zan sake saurara...haka kawai naje ka kashe ni..dan wollahi ina jin yanzu'nma bazan k'ara iya tafiya ba,shi kenan na zama gurguwa..."
Tana fad'in haka ta sake kecewa da kuka harda sheshshek'a,dariya ya saki yana shafa bayanta,da sauri ta doke hannunsa dake yawo a bayanta cikin kuka take masa masifa
"Ni ka bari bana so,ai dama da haka ka cuce ni d'azunma..."
Zallan futsara take zuba masa,amma sam BB bai ga laifinta ba a lokacin coz yasan shi ya janyo wannan rikicin nata.Sai daya wanketa tas a karo na biyu sannan ya barta ta k'arasa,yana jinta duk magananun da take idanunta a kulle suke ta kasa had'a ido dashi,a nan jikin wall na toilet en ya tsaya jiranta dan kam yana da tabbacin wannan sarauniyar rakin bazata iya fitowaba tunma dama can ta fad'a masa kad'an ya rage mata ta zama gurguwa.Tunani ya fad'a yadda daren ya kasance a gare shi,murmushi kad'ai yake saki idanunsa rufe kamar mai bacci.
Bayan ta gama tana k'ok'arin mik'ewa taji azabar data fi k'arfinta babu shiri ta koma ta zauna tana sakin kuka,cikin kuka take fad'in
"Wayyooo! Allah na MAMA shi kenan na zama gurguwa,wayoo ni shi kenan baran sake tafiya ba..."
Kukanta ne ya dawo da shi duniyarsa da sauri ya koma,baiyi mata magana ba ya d'auketa yayi waje da ita a kan bed ya direta ya juta ya fice a d'akin,bedroom enta ya isa kai tsaye ya d'auko mata jallabiyya da hijab ya dawo,shi da kansa ya sa mata sannan ya d'auketa ya dire a kan pray mat daya shimfid'a,fuska babu fara'a haka ta cunkushe ita a dole ga wacce akayiwa laifi,jam'i ya jasu raka'atanul fijr suka fara gabatarwa sannan suka sallacci asubah,ya d'an jima yana musu addu'a wanda sam bai kula da abunda KHUBRA keyiba,sai bayan daya k'are tukuna yana juyowa ya ganta kwance da alama kam baccinta take a lokacin d'an murmushi yayi sannan ya mik'e ya d'auke pray mat en,cak ya d'auketa a gurin ya maidata saman bed,sannan ya gyara mata kwanciya,kusa da ita ya haura ya kwanta tare da sata cikin jikinsa suka koma bacci....
《《》》
Kulawa ta mussaman KHALEEL ke bawa ZUHRA wadda bata tab'a tunanin samunta daga kowa ba,cike da so da k'auna suke nunawa juna kulawa,kwanaki biyu da aurensu sun koma matsayin abu guda duk inda d'aya yake to tabbas zaka samu d'ayan a tare da shi..
B'angaren ASHNA da SADEEQ ma ba'a cewa komai dan kam soyayya ko wasu turawan sai dai su d'aga k'afa coz babu abunda zasu fisu,idan har ka shiga wannan gida to tabbas ba zaka so ka fito ba saboda soyayyarsu mai cike da burgewa da mutunta juna babu raini...
《《》》
Sai around 11:00am ta farka idanunta ta shiga bud'ewa a hankali har ta kammala bud'esu tas a kansa zaune kusa da k'afafunta,kallon da yake mata yasa tayi saurin mayar da su ta kulle saboda tabbas kam baza ta iya bud'esu ba matuk'ar yana gurin,d'an murmushi yayi ya dawo kusa da ita,hannunta ya rik'o cikin nasa,sai da yayi kissing hannun sannan ya d'ora fuskarsa akai,tana jinsa tayi masa banza dan kam tana jin haushinsa har yanzun,ga kuma nauyin bud'e idonta da take gabansa gudun kada su sake had'a ido da shi.
Tunanin maganganunsa ta soma yi na jiya da yaketa faman rera mata acikin kunnenta,ita kad'ai take zancen zuci tana fad'in
_"Uhmmm! KHUBRA kenan ke yanzun kuma har kin yarda da abunda ya fad'a...? ko kuwa kin manta gurzar daya miki kamar ya samu kayan wanki da sukayi uban datti,ji fa irin wahalar daya baki,idan har da yana sonki ne kamar yadda ya fad'a to da lallai babu abunda zaisa ya miki irin wannan muguntar,kawai ki share duk wani abu da zai fad'a miki...dai dai me kina ganin kamar kalamansa gaskiya ne a gareki ko ko din kina sonsa ne yasa kike tunanin gaskiya ya fad'a miki...?_
D'an k'aramin tsaki ta jaa,dai-dai lokacin wayanta dake saman mirror ya fara kuka,shi da kansa ya d'auko mata wayan ganin mai kiran nata yasa yayi murmushi yana fad'in
"Ga CWEETY'NKI nan tana kiranki.."
Hannu ta mik'a masa nan ya d'ora mata wayan kan hannunta tare da jan hancinta,d'an k'aramin k'ara tayi duk da yanayin muryanta da baya fita
"Wayyoo! Allah YAYA zaka ciremin hancifa.."
Y'ar dariya yayi mai sauti yana fad'in
"Ko na cirema ai nawa ne ko..?"
"A'a naka ai gashi nan a fuskanka.."
"Ohhh! ba nawa bane kenan kike nufi ko mene...?"
"Ehh mana naka ai yana kan fuskanka ma.."
"Ohh! kina nufin abunki ba nawa bane ko..?"
"Ehh en inda naka ne ai da bakamin abunda kayiminba da dare..."
Murmushi ya sake yi mai sauti dai-dai fuskarta ya sunkuya yana fad'in
"Ki gama gayamin magana son ranki anjima na kamaki sai nayi miki fiye da haka...Kin san wani abuma kuwa...to bazan barki kiyi bacci ba yau,kwana zamuyi ina sauke miki gajiyan dake jikinki...Kin gane ko..?"
"Tabbb wollahi ba dani kake ba,sai kace wata inji..."
Da sauri ta toshe bakinta,tana dad'a k'udundunewa cikin duvet,sanin babu komai jikinta daga ita sai towel,shima gaba d'aya ya gama nad'ewa zuwa can saman cinyoyinta wanda kad'an ya rage aga komai na daga halittanta.
Bata ankaraba taji ya d'age duvet en,ihu ta saki tana k'ok'arin ja shima yana ja,kukan shagwab'a tasa masa tana fad'in
"Dan Allah YAYA ka bari kagafa babu komai jikina..."
"Ehh dama ai banson ganinki da komai,yanzunma ina son checking enki ne naga babu matsala...."
Dai-dai kunnenta ya rad'a mata cikin murya da yake kashe jikin mai sauraro
"Kinga dole na dubaki saboda anjima da dare bana son wani abu yamin shamaki daga d'and'anon zumanki..."
Hannu tasa ta rufe kunnenta duka shi kuma ya fice yana mata dariya,da kyar ta bud'e idanunta sai lokacinma ta tuna da ZUHRA ta kirata bata d'aukaba ta biye masa,tana dubawa ko taga cikin rashin sani ashe ta d'auka daga can gefen da aka ji batayi maganaba aka kashe,har fiye da mintuna uku,da sauri ta dafe kai a fili take fad'in
"Wayyoo Allah na Allah yasa baki ji komai ba"
Kiranta ta shiga yi cikin shak'iyanci ZUHRA take fad'in
"Amarya bakya laifi....ko da kin kashe d'an masu gida.."
Cike da tsiwa KHUBRA ta tari numfashinta tana fad'in
"Ai wollahi babu abunda zaki fad'amin...Yanzun ace harda had'in bakinki acikin wannan abun dake faruwa,ko ba komai ai na wuce haka a gurinki,amma shi ne kin san wannan maganar kiyi min shiru...babu komai na gode tunda kin san BB'N naki ba sona yake ba Amma kika wani yi shiru aka had'ani da shi,shi kuma YAH KHALEEL dama yaudarana yake ban saniba ashe.."
"A'a CWEETY kada kiyi saurin yanke hukunci kan abunda baki saniba,ki bari kiji komai da yadda al'amura suka wakana,na tabbata ke da kanki zaki fuskanci abubuwan da suka faru a baya..."
A tak'aice ta bawa KHUBRA labarin yadda BB ke sonta tunma kafin a saceta,har zuwa yadda aka shirya komai duk dan asa shi ya fito fili ya nuna da kansa,amma abu yaci tura,wanda daga k'arshe kuma hakan ya kaishi ga fad'awa mummunan yanayi,idonta ta runtse cike da tausayin irin halin da ya shiga akanta,ashe dama akwai lokacin da zata samu wanda zai sota har haka? ita kam ta tabbatar dalilin daya sata sakin jiki da shi a kwanakin nan ba komai bane illah tsoron fad'awa fushin ubangiji da kuma tsinuwar mala'iku,dalili kenan daya sata take k'ok'arin dasama zuciyarta soyayyarsa ko ta wane hali,sai gashi ta tsinci dami a akala,shi tunima ya gama macewa a soyayyarta Wanda bata saniba sai yanzun,lallai ko babu abunda zata yi masa a wannan hali face biyayya sau da k'afa...
Hawayen da suka biyo fuskarta ta shiga gogewa dai-dai ZUHRA na mata tsiyar hiran da suke d'azun da BB,sai gashi ya dawo hannunsa d'auke da d'an k'aramin tray samansa kuma thick tea ne da toasted bread,hangota tana goge fuska hannunta dafe da phone enta dake jikin kunnenta har lokacin ya tabbatar da kuka take,da sauri ya k'araso wayan ya zare daga hannunta yakai kunnensa yana fad'in
"Heyy! MADAM me kika fad'awa matata take kuka cikin wannan safiyar...? idan kinsan kuka zaki dunga samin ita idan kin kirata to a hak'ura da kiran kin gane ko...?"
Yana gama fad'an abunda ke bakinsa ya kashe dai-dai lokacin kuma yana zama kusa da ita,d'agota yayi ya jinginata a jikinsa,dad'a narkewa tayi a jikinsa tana fashewa da sabon kuka,kansa ya dafe yana fad'in
"Ya salaam..!"
patting bayanta ya shiga yi,yana hura mata iska cikin kunnenta,nan da nan tayi shiru jin gaba d'aya vains nata sun soma saki,ta koma sakin ajiyar zuciya
"Watoo abunda ta kira tamin kenan..ta saminke kuka hankalinta ya kwanta,zan gamu da ita tabbas sai na sab'a mata..."
Da sauri ta rufe masa baki da hannunta tana girgiza masa kai cikin sanyi take fad'in
"A'a YAYANAH...ko kad'an kada ka mata haka..ni nasan ba dan haka tayi ba,sai dan wata manufa ta daban...ko kad'an ba abunda kake tunani bane,dalilin kukana ba yana nufin abunda ta kira tayi ba kenan,hasalima ta kirani ne dan ta sanar dani wani muhimmin sak'o da ni kaina ban san dashiba...
Kayi hak'uri YAYANAH sam ban san abunda ya faruba kenan,kuma ko da wasa babu wanda ya sanar dani,ina...ina...so...so..n...ka...nima fiye da yadda kake tunani...tun tasowata na rayune da soyayyarka,da ita na girma..tun ban san kaina ba har nazo na mallaki hankali..sai dai ko kad'an ban tab'a nunawa kowaba,gudun abunda zai faru.."
Shiru tayi tana maida numfashi d'aya da d'aya,matar dake kunyar bud'e ido ta kalleshi sai gata idanunta cikin nasa tana falassa asirin zuciyarta..
Mamakin kalamanta yake sosai saboda baiyi tunanin faruwar hakanba,sai gashi tana sanar masa da soyayyarsa ta rayu..Yana tunanin ta katse shi dai-dai lokacin data ci gaba da fad'in
"A lokacin da nake rayuwa cikin k'unci da tsanani soyayyarka ce kad'ai abunda ke k'aramin k'arfin guiwar ci gaba da rayuwa,badan hakaba da tabbas ban kawo yanzu'n ba,a lokacin da bani da kowa bani da komai sai zallar soyayyarka dake gudu cikin jinina,bana tare da kowa nawa amma idan na tuna da soyayyarka sai naji na zama mai cikakken gata,ina jina a matsayin wacce take da kowa...Dan Allah YAYANAH kaci gaba da sona har k'arshen numfashi,kada ka nunamin halin maza..."
Ta k'arasa tana sake rungumeshi had'e da sakin sabon kuka mai tsuma zuciya,gaba d'aya ilahirin jikinsa ya saki jin irin maganganun dake fitowa daga bakinta kamar a mafarki,komai sai zuwa masa yake da sauk'i ba kamar yadda yayi tunaniba,ajiyan zuciya yayi yana fad'in
"It's ok baby me,bana son kukan nan naki,ina jinsa ne har k'asan zuciyana..."
Da sauri ta shiga gogewa tana girgiza masa kai had'e da murmushi mai burgewa.Murmushin shima ya saki yana janyo tray en dake kan bedside drower,babu musu ya shiga bata tana amsa,sai dai kuma fuskarta da take yamutsawa kamar mai had'iyan magani,duk wani abu da tayi shi kam burgeshi take had'e kuma da k'ara masa kyau.Duk duniya babu abunda yake so sama da ita,tausayi da kuma soyayyanta da suke dad'a taso masa daga can k'asan zuciyarsa su suke dad'a tasiri a lokacin a kansa.
A haka har ya gama bata tea en da toasted bread,murmushi tayi masa tana shafa gefen fuskarsa ta furta
"Na gode YAYANAH..."
Hannunsa yasa saman bakinta ya rufe yana girgiza mata kai,cikin sanyin murya ya furta mata
"Babu godiya acikin abunda ya zama wajibina..."
Har ya mik'e zai fita ya juyo yana fad'in
"Baby get ready idan na dawo zan miki wanka...."
Ta gane dalilin da yasa ya fad'i haka duba da yadda ya mata winking,fuskarta tayi saurin b'oyewa,cikin sauri ya fice da tray en a hannunsa yana dariya,itama dariya tayi tana jin zuciyarta wasai,dawowarsa cikin d'akin tayi saurin b'oyewa cikin duvet har kanta tana tuna abunda zai mata yanzun kuma dan kam ta tabbata sai ya aikata abunda ya fad'a
"Ehheem! MR'S KHALEED SAFWAN kin shirya ko kuwa yanzunma babu k'aton da zai miki wankan...?"
Dariya tayi mai sauti tana fad'in
"Ehhh! babu..."
Kafin ta k'arasa ya sureta yayi hanyan toilet yana fad'in
"Haba yarinya....zancen babu wani k'ato da zai miki wankama ai bai tasoba,tunda anyi abunda yafi wanka ko....?"
B'oye fuskarta tayi cikin jikinsa sukayi dariya dukansu.ko a toilet enma shiriritarsu suka tsaya yi,sai da suka b'ata lokaci a ciki ana gumurzu tsakaninta da BB,shi yana wani aikin daban ita kuma tana masa raki haka suka fito,sai daifa akwai tarin tambayoyi a zuciyar BB da yake son yi mata kan maganarta na d'azun...................