Idanuwansa kawai data kalla ya tabbatar mata da yaji kome take fada.
Tsaye yake har lokacin ya kafa mata idanuwan na nasa da suke bala.in yi mata kwarjini.
Ji take har iskar da take yawo a dakin tsaye take cik. A hankali ya tako ya qaraso inda take.
Yanayin yanda zuciyarta ke dokawa ta dauka fitowa waje zatai tsabar kidimewar datai.
Bata taba kawoma ranta zai kamata ba. Ko kuma zata ma ji abinda take ji yanzun idan har ya kamata.
Baiko kalleta ba. Harya karaso. Hannu yasa ya zare earphone din daga kunnenta.
Wayar yazo dauka takai hannu wajen. Ya hada da wayar da hannunta duka ya riqe. Jikin bangon wajen ya turata. Kalar riqon dayai mata a wajen ne yasa batai kiciniyar qwacewa ba.
Idanuwansa har sun sauya saboda bacin rai.
Bai taba zaton zaiji kishin wata ya mace bayan huddynsa ba.
Da huddy baisan kishi kalar wannan ba. Saboda yasan shi kadaine a zuciyarta.
A yanzun ma bazaice ga kalar dacin da yake ji a ranshi ba. Yama kasa mata magana.
Kallonta kawai yake. Kuma taqi yarda su hada ido. Kanta a kasa da bayanannen tsoro.
Ya matsa kusa sosai yana sake hadeta da bangon.
Tana jin hucin numfashinsa kan fuskarta saboda kusancin da sukai amman taqi yarda su hada ido.
Hannunsa yasa ya dago mata haba. Tako sauke idanuwan nata cikin nasa. Saurin rufe su tai gam.
Abinda take gani cikin nasa idanuwan ba zata iya daukar shi ba. Ya mata girma.
Dai dai lokacin wayarta ta soma ringing.
Karba yai daga hannunta ya duba 'ammar' yagani rubuce jiki da hoton heart qato tsakiyarsa rubuce da 'true love'.
Wani numfashi yaja ya fitar dashi. Yakan jima ranshi bai baci ba. Yana duk abinda yasan zai guje masa faruwar hakan. Saboda bai iya shi ba.
Dagawa yai ya kara a kunnensa.
Hannunshi daya na riqe da husna. Ya janyota ya matseta a qirjinsa sannan yace
"Hello"
"malam kaba mai wayar abinta"
Aka fada daga dayan bangaren.
"Mafi munin kuskure da inaji kaf zuri.arku basu taba yinshi ba shine waya da matar aure. Matar kuma ta ishaq"
Yanayin muryarshi ya tsorata kafafuwanta har kyarma suke. Badan rikon dayai mata ba dole ta zauna.
Ammar kam ranshi ya soma baci yama akai wayar husnar shi taje hannun mutumin daya fi tsana a duk duniya.
Dan haka yace
"kaine kai kuskuren auren yarinyar da ta jima da miqamin zuciyarta. Ba zata taba sonka ba"
Murmushin takaici prince ishaq yai. Yanajin wani sabon ciwuka suna budewa a zuciyarshi.
"kai kana sonta kuwa?"
Ya bukata da bala.in karfin hali.
"Ina sonta son da ba zaka taba iya mata shi ba"
Ammar ya fada cikin bacin rai.
"Zan iya yarda ka shaqu da ita amman baka taba sonta ba. Daka na sonta ba zaka taba janta zuwa halaka ba.
Ni ba qaramin mutum bane akwai dalilai da dama dazai hana na dauki hukunci akanka.........."
Katse shi ammar yai da fadin
"malami bama son dogon surutu ka saketa mana tunda bata sonka ni take so"
Zuciyar prince ishaq har wani daci take ga sabbin raunukan dake ciki suna kara budewa. A hakan ya daure.
Cikin kanshi yana lissafa watannin aurensu kamun yace
"Zan sake ta! In har bata soni ba nan da *WATA BAKWAI 7*
Be a man karka sake kiramin mata har sai wa.adin nan ya cika if not wallahi kaf danginku babu mai gane kurkukun da zan kaika!"
Kamin ya bashi amsa ya kashe wayar.Tura husna yai kan gadon dakin ya bude wayan yana qoqarin ciro sim din.
Sai lokacin ta taso.
"Make shirin yi haka?"
Bai kulata ba ya zaro sim din ya karya.
"Gentle ka bari kai baka san darajar so bane?"
Ta fada tana goge hawayen da suka zubo mata.
Ko inda take bai kallaba. Saboda baisan me zai iya mata ba.
A yanda yakejinsa komai ma zai iya yi. Wayar ya doka da bango ta tarwatse.
Ya tsaya ya dafe kanshi da hannuwansa duk biyun. Yau shine wani yake fadawa maganar da duk ranshi yaso.
Yau shine aka tozarta. Tozarci mafi muni. Abubuwa da yawa sun faru da rayuwarsa.
Sai dai babu wanda ya taba darajarshi irin nayau. Bai isheta ba ta hada masa da zagi cewar baisan darajar SO ba.
"Akanme zaka fasamin waya? Saboda me? Kasan yanda..........."
Bata qarasa ba ya dauketa da wani irin mari da saida taga wani haske da wasu kana nan taurari.
Ta dafe kunci tana kallonshi. Komai ya tsaya mata.
Muryarshi a dake yace
"Da aurena akanki husna? Da darajata zakina waya da qato cikin gidana!
Qarqashin ikona. Saboda bakisan daraja da haqqoqin aure ba ko?
And you dare have the guts to question me?
Wallahi bansan tsanar da kikaimun tai girma haka ba"
Tsugunnawa tai a wajen tana wani irin kuka.
Ya qare mata kallo kawai yana dana sanin wannan auren.
Tun farkon shi yasan babu komai sai fitina a ciki. Da karin matsaloli a wajen shi.
Fita kawai yai yana doko qofar da qarfi gaske.
*
Tunda husna take bata taba zaton akwai randa zataji kunyar wani dan adam kwatankwacin tayau bama.
Taji ta muzanta.
Maganganunsa sun sosa mata rai shisa taso tai tabarmar kunya.
Sam marin dayai mata bai dameta ba. Domin ta cancanta yai mata fiye da wannan hukuncin.
Ta jima da sanin cewar abinda take bashi da kyau saidai ta kasa dainawa.
A kwanakin da suka wuce ta daina kiran ammar saboda tanajin kaman bata kyautawa aurenta.
Saidai shi inya nemetan bata iya share shi. Bata san ta inda zata fara ba.
Me zata soma gyarawa? Laifukan zunuban da suke kanta taji sun wani danneta lokaci daya.
Da sauri sauri take maida numfashi. Tunanin mutuwa da kwanciyar kabari ta ziyarci zuciyarta.
Tunanin yanda ta biye son zuciyarta da tunzurar shaidan ta aikata laifi mai girma.
Astagfirullah ta shiga jerowa tana wani irin kuka. Bata san da wanne irin ido zata kalli prince ishaq ba.
.
Falon kasa ya sauka. Baya son ya shiga dakinshi dake cike da hotunan huddy yaga abinda kaddara ta ja masa.
Fuskarshi na cikin hannuwan shi yana maida numfashi. Bai taba zaton akwai ranar da zai daga hannunshi wa mace ba.
Saidai kuma bai taba zaton abinda ya faru yau zai taba faruwa ba.
Hakama ciwon da yake jin zuciyar shi nayi. Yasan ya tsaneta a farko fine. Saboda yana dauka auren kwadayi tayi dashi.
Amman wannan bai isa ta hukunta shi ta wannan hanyar ba. Asalima yanzun abinda yake ji game da ita shi kanshi bazai fassara shi ba.
Baisan abinda ya kamata yayi ba. Jikinshi har wani kakkarwa yake.
*
Saida tai kukanta mai isarta sannan. Ko fuskarta bata damu data wanke ba.
Ta riga da ta gama yanke ma zuciyarta. Zuwa zatai ta bashi hakuri.
Zuwa tai wucewa zuwa bangaren shi. Kaman ance ta kalli kasa ta hango shi.
Jitai zuciyarta ta sake karyewa. Da wanne idon zata kalle shi? Me ma zatace ne.
*
Yanajin zuwanta. Bai dago daga yanda yake ba. Saboda baya son ganinta sam sam a yanzun.
Tsugunnawa tai gabanshi a kasa. Ya bude fuskar shi ya sauke jaijayen idanuwanta akan ta.
Kasa hada ido tai dashi saboda wani kwarjini da kunyarshi data cika mata zuciya.
Kafarshi tazo rikewa ya matsar da sauri yana fadin.
"Don't..... Please ki tafi kawai"
Girgiza kai tai tasa hannu tana goge hawayen daya zubo mata.
Cikin kuka tace.
"Dan girman Allah kayi hakuri. Ka yafemun......"
Ji yake kaman tana goga masa gishi a sabbin ciwukan dayaji.
"Dan Allah ki kyaleni. Just leave me the hell alone!"
Duk da ba hayaniya yake ba. Muryarshi a dake take.
Bude baki zatai ya katse ta da fadin.
"Kibarni husna, laifina ne dana kasa sauke hakkokin ki da Allah ya doramun. Na biyewa son zuciyata. Hukunci na ne wannan........."
Da alamaun gajiya sosai a muryarshi. Ga tunani ya masa yawa. Shima ya gane kuskuren daya aikata.
Ko da baya son husna bai kamata dan yana gudun karin matsala yaki sauke hakkokin da Allah ya wajabta masa ba.
Bai kamata ace yaki duba darajar ibadar da take cikin aure. Shisa Allah yai masa wannan jarabawar. Ya kuma dora masa wani azababben kishin husnar.
Yanda husna ta yanke ma zuciyarta duk abinda zaiyi zata jure ta bashi hakuri.
Zata sake gwadawa wayar shi dake ajiye jan table din wajen ta shiga ringing.
Ko kallonta baiba harta tsinke. Ta kara daukar wani ruri.
Ya duba likitan Nas ne. Dagawa yai yana addu.a Allah yasa ba wata jarabawar bace.
Karawa yai a kunne yai shiru. Dakyar ya iya amsa sallamar da doc din yai masa.
"Nas ya bude idanuwan shi. Saidai baiyi magana ba. Nasan zakaso ka sani......... "
Baima bari ya karasa ba. Ya ajiye wayar ya lumshe idanuwan shi yana mika Godiyarshi Ga Allah madaukakin Sarki Mai Ikon rayuwa da mutuwa.
Husna ya kalla badon ya daina jin bacin rai ba. Ko abinda ya faru ya wuce. Sai don girmab labarin daya samu yanzun ya danne komai. Hakan yasa yace mata.
"Nas ya bude idanuwan shi"
Fuskarta ta goge tana hamdala. Mikewa tai muryarta can kasa tace bara in dauko hijab.
"Kiyi me?"
Ya tambaya yana mata wani kallo daya sata jin ta tsani kanta da abinda tayi. A rauna ne tace.
"Muje wajen Nas....."
Girgiza kai yai sannan yace.
"Believe me, after dazun Nas bazai so ganin ki ba..... "
Wasu hawaye suka zubo mata. Ta goge su tace.
"Ban roke ka karka hukuntani ba amman ka dubi girman Allah karkai mun hakan da haramtamun ganin Nas"
Wuce ta yazo yi saboda yanda take neman karya mishi zuciya. Hannu ta riko masa tana fadin.
"Allah idan bakaje dani ba. Ko ta katangane zanbi inba a budemun gate ba"
Taso ta bashi dariya ya share. Hannun shi ya kwace yace.
"Fine. Karki batamun lokaci"
Kusan da gudu ta wuce shi ta hau sama. Ya girgiza kai murmushi na kwace masa.
A wannan lokacin ne yasan ko da baya son yarinyar nan gaba daya. Ya soma sonta.
Saboda jiyai ya yafe mata. Har zuciyarshi ya yafe mata. Rokar musu gafara yake wajen Allah na laifin da su duka suka aikata.
*
Har sukaje asibitin ko inda take bai sake kallo ba balle tai tunanin zai mata magana.
Saidai sanda suka je Nas din harya koma bacci. Canjin da zaka iya gani an samu da idanuwa shine da kan shi yake numfashi. Babu taimakon komai saina Allah.
Zama sukai. Prince ishaq can nesa da ita. Sai take jinta duk wani iri.
Mumyn Nas ya fara kira ya sanar da ita da kanshi ci gaban da aka samu.
Sannan ya kira umman shi. Sun jima suna waya da ita sannan ta bukaci ya bata Husna su gaisa.
Kallonta taga yayi sannan ya tashi ya karasa inda take a dake ya mika mata wayar yace.
"Umma nason magana dake"
Gabanta taji ya fadi. Hannu na rawa ta karbi wayar. Tai sallama ta gaishe da ita a ladabce.
Zata iya jin fara.ar umman ta cikin muryarta tace
"Ya mai jiki kuma"
A sanyaye ta amsa da.
"Alhamdulillah umma"
"Allah ya kara sauki. Dan Allah ku kula. Ki rike amana, kinga kalar rayuwar da baban yake fama....."
Wata kunya taji don amana ta dade da watsar da ita. Ta daure tace.
"In shaa Allah umma. Mungode Allah ya kara girma"
Ta amsa da amin tai musu addu.a sosai sannan ta kashe wayar ta mika masa.
Karba yai ya koma inda yake ya zauna.
*
Yau ko da kamala ya kawo musu kayan ciye ciye. Kowa daban daban yaci.
Basu koma gida ba sai dare da doc ya tabbatar masa allurai da magungunan dake aiki jikin Nas ba zasu bari ya farka dan ranar ba.
Saboda kwakwalwar shi na bukatar wadataccen hutu.
Suna isa gida suka hau sama. Yana shirin nufar bangaren shi tace.
"Gentle......"
Bai juyowa ba amman ya tsaya da tafiyar da yake. Hakan yasa ta fadin.
"Dan Allah ka yafemun. Nayi kuskure mai girma. Ka yafemun..... "
Yanajin tayi shiru yaci gaba da tafiya abin shi. Yana son sosai ta gana kuskuren abinda ta aikata. Ya kuma yarda da ita cewar ba zata sake ba kamun nan ya soma goge mata wannan yaron a zuciya.
Ta lumshe idanuwanta ta bude su hadi da sauke wani dogon numfashi. Bakomai zata ci gaba da kokari tunda ita ta aikata laifi.
Dakinta ta wuce itama. Rigar jikinta kawai ta sake dan sunyi isha.i a asibiti. Ta kwanta.
.
Allah sarki rayuwa. Bata taba zaton zata juya da ita ta wannan fannin ba.
Wasu hawaye masu dumi taji sun zubo mata.Sai yanzun girman laifin datai yake dawo mata.
Ina hankali da iliminta ya tafi take waya da namijin da ba muharraminta ba da aurenta.
Inalillahi wa ina ilaihi raji.un. Wasu maganganu suka dawo mata a daren da za.a kawota gidan prince ishaq.
"Husna baki taba bijirewa umarni na ba sai akan auren nan. Ba don bama son yaron da ke kike so bane muka hana shi ke. Sai don mu mun hango abinda baki hango ba. Aure an daura. Ki dauka hakan shine alkhairi a rayuwarki. Inhar kikai abinda kika kaso auren nan Allah ya isa tsakanina dake!!!"
"Ya Allah"
Ta furta tana sake juyi kan gadonta maganganun babanta na dawo mata.
Ta rasa yanda akai komai ya juya mata haka. Lokaci daya farkon abin ya dawo mata.
*
Husna itace yarinya ta uku cikin yaya biyar da Alhaji abdullahi da matarshi Haj. Baraka suka mallaka.
Babbar yarsa mace ce wato haj.fatima. Tana da aure harda yara uku.
Sai namijin dake bi mata Aminu. Da shima yana da aure.
Sai husna. Akwai tazarar shekaru kusan bakwai tsakanin su da aminu.
Maheer sai autarsu aisha.
Baban su dan kasuwa ne. Estate guda gare su da gidaje ashirin cif a ciki. Family dinsu ke cikin wajen gidaje goma sha biyu. Sauran ne kawai baki.
Sun samu wadatacciyar tarbiya da ilimi na addini dai-dai misali.
Husna tagama secondary school da shekaru sha bakwai tai Nasarar samun gurbin karatu a kano poly inda take diploma dinta akan computer science.
*
Ba zata manta haduwarsu ta farko ba da ammar.
Kaya tai loading harda system cikin wata jaka. Tun daga gida mamansu tace mata hannun jakar bazai dauki nauyin data loda masa ba tai gardama.
Aikam tai sa.a hannun jakar ya tsinke. Kasancewar bamai zip bane komai yai kasa.
System dinta kadai ta iya tarewa. Komai ya watse kasa.
Jitai kaman ta saka kuka dan takaici. Bama tasan ta inda zata soma tattara su ba.
Ta tsugunna ta soma da maths set dinta.
Kaman daga sama taji ance
"Dole kiyi bari wannan books din sun maki nauyin dauka"
Dagowa tai suka hada ido. Murmushi ya qwace mata. Shi ya tayata ta tattara komai.
Haduwarsu ta biyu islamiya zataje anan ne taji sunan shi yaji nata har sukai musayar number.
*
Ammar kam shine babba gidansu sai kannensa maza.
Babansu ba wani mai hali bane. Rufin asirin Allah. Lokacin da ya hadu da husna yana level 2 bawani girman kirki ne dashi ba.
Cikin watanni biyu sukai wata irin shakuwa taban mamaki saboda duk wani abu da yake bukata a wajen mace husna ta hadashi.
Ba fara bace can. Tana da wani hasken fata mai kyau. Da manyan idanuwanta tubarkalla. Bakinta da hancinta kaman ita ta zaba.
Yakan mata tsiya wani lokacin cewan tsayinta bazai wuce damtsen hannun shi ba. Dan kuwa gajera ce da jiki madaidaici.
*
A shekaru biyu da dori da sukai da ammar duk wani wanda yake tare da ita yasan shi.
Duk wani buri na rayuwarshi husna ce. Duk wani mafarki na har abadanta ammar ne.
Lokacin data hada diploma dinta ne babansu ya bukaci yaron da take so ya turo manyan shi.
Labarin ya daga musu hankali saboda ammar a lokacin yake shekarar shi ta karshe a karatu.
Yana da gidan da zasu zauna. Saidai bashida sana.ar da zata rike su.
Ko da magabatan shi suka zo basu boye ma baban su husna ba. Sun sanar dansu bashida wata sa.a saidai yana matakin karshe na karatun shi.
Sam babansu husna bai musu alkawari ba. Asalima yabar magana ne kan cewar in har yarshi ta samu tsayayye nasu dan bai samu sana.a ba zai aurar da ita.
Babu kalar tashin hankalin da basu shiga ba. Husna ke karfafa masa gwiwa cewar saita kula wani ne za.ama ganshi a aura mata.
Saidai batasan me kaddara ta rubuta mata ba.
*
Lokacin da ammar ya tafi bautar kasa ne. Kasancewar estate dinsu yana kusa da gidan wazirin kano.
Husna ba zatace tasan wata alaka dake tsakanin babanta da wazirin kano ba data wuce makwabta ka.
Asali ma basu ko taba shiga gidan ba. Saidai su wuce shi in hanya ta kama.
*
Bata san da kaddarar data hada babanta da wazirin kano ba.
Alaka ce data samo asali sanadin makaranta. Tare sukai primary school.
Lokacin da mai martaba yazo masa da bukatar a samo ma danshi yarinya mai hankali.
Ba sai yar sarauta ko yar wani mai kudi ba. Yarinya yar babban gida. Yar manyan mutane.
Wazirin yaranshi duk mazane. Macen shi yarinya ce dabata shige shekara goma ba a lokacin ne yaima baban husna magana akan nema ma prince ishaq auren yarshi idan ya amince.
Yaji dadi sosai da wannan girmamawa da yai masa dan haka ya amsa shi.
*
Husna ba zata manta wani yammacin ranar juma.a ba. Kwance take suna waya da ammar.
Kasancewar yanzun sai suyi sati biyu ma zuwa uku basuyi waya ba. Wani kungurmin kauye ne yake bautar kasa.
Sai yahau abin hawa tafiyar awa daya da wani abu ya shigo gari dan ya samu network yaji muryarta.
Aisha ta shigo dakinta tace mata tazo babansu yana kira. Kaman zasu sakama juna kuka sukai sallama.
Tun a hanya ta rasa me yasa take jin gabanta na wani faduwa.
A haka ta karasa falon babansu ta gaishe dashi. Mamanta ma tana nan.
Bayan sun gaisa a ladabce babanta ya sa magama a nutse.
"Husna kasancewar ina da tabbaci akanko yasa na amsa neman aurenki jiya da dare. Yau din nan zasu kawo komai. Idan an dade wata biyu..........."
Tun daga wajen kalmar "Aurenki" kunnuwan husna suka daina jin wani bayani.
Komai ya daskare mata. Zuciyarta na wani mata nauyi. Lumfashinta taji yana shirin daukewa.
Cikin tashin hankali tace.
"A.a baba.... Wallahi bana son shi.... Mama karku mun haka......."
Daga ranar tashin hankalinta ya fara. Babu kalar haukan da batai ba amman a banza. Aka kwace mata wayoyi duka.
Wata biyun nan da yan kwanaki shi ya rage musu su cimma burinsu ita da ammar............!
**** ****
Wani nauyi da zuciyarta tai mata ga numfashinta na fita sama sama yasata tashi zaune.
Addu.o.i take karantawa dan Allah ya bata karfin halin hana zuciyarta maidata rayuwarta ta baya.
Mayar da ita watanni biyu na rayuwarta da suka fi kowanne kunci.
A haka bacci ya kwasheta da mafarkai kala kala.
.
Da safe tunda tai sallar asuba ta kasa bacci. Ta saba a wannan lokacin ko basuyi waya da ammar ba zai mata text kamun ta koma bacci.
Wanka tai tasa kaya. Kwalliyar datai bamai yawa bace. Ta koma ta kwanta.
Tuno ammar kawai wani zafi zuciyarta take. Saboda kuskuren da sukai ta aikatawa.
Kalar kalaman da suka dinga gaya juna da igiyar aure akanta da ta dabaibayega ga barin ko da daga murya ne ga namijin daba muharraminta ba.
Ballantana kalamai masu zafi. Batai kokarin tarbe hawayen da suke zubo mata ba.
Qwanqwasa kofar dataji anayi ne ya katse mata tunanin da take.
Hawayen dake fuskarta ta goge sosai ta dai daita muryarta sannan tace
"shigo"
a hankali.
Turo qofan yayi. Harya tako yazo bakin gadonta ya zauna bata dago ta kalle shi ba.
Batai zaton shi bane saboda tasan laifin datai masa. Da ka yanda ko kallonta baya sonyi duk jiya.
"Hussy......."
Ya kirata da wani yanayi da saida taji yarr a jikinta. Dagowa tai ta kalle shi.
Fuskar shi dauke da mamaki yace
"kukan me kike?"
Wasu hawayen taji suna shirin zubowa. Kamin tai wani abu ya tallabi fuskarta da hannayensa.
Baya son kukan nan ko kadan. Yace
"Everything is gonna be okay.....banson kukan nan kinaji!"
Daga mishi kai tai alamar eh. Ya lumshe idanuwansa ya bude su.
Cikin taushin magana yace
"hussy banson ana amsamin magana dakai, idan na miki magana ki bude baki ki amsa ni"
"Kayi haquri"
Ta fada muryarta na rawa.
Sakin mata fuska yai. Duk yanda yake jin son ce mata ya yafe mata ta daina damuwa ya danne.
Kwali ne gefe bama ta kula da shi ba. Ya dauko ya dora akan jikinta.
Ya soma magana
"Kiyi hakuri da daga hannuna danai akanki. Ki yafemun...."
Bude baki tai zatai magana dan bataga me yasa yake bata hakuri ba ya daga mata hannu alamar ta saurare shi kawai. Yaci gaba da fadin.
Kiyi hakuri da wannan wayar. Akwai sim da komai a ciki. Nasa a kawo miki irin ipad dina.Cikin week din nan.
Munyi alqawari da Saurayinki.......!
Yanda ya ja kalmar saurayinKI din saida yasa ta dan razana. Kamin ya ci gaba da fadin
"so zaki iya daraja dokokin Allah dayake kanki na aure badanni ba dan banda wannan mutuncin a idanuwanki har zuwa lokacin da alqawarinmu zai cika"
Shiru husna tai wasu hawayen nason zubo mata. Idan har tace baida daraja a idonta karya take.
Tayi shiru ne kawai dan tasan yanzun bazai yarda da duk wani abu dazai fito bakinta ba. Kuma bataga laifinshi ba
Jin tayi shiru ta sadda kanta qasa yasa shi saka hannu ya dago da habarta.
"Kar hawayen nan ya zubo fa"
Ya fadi. Wata sumba mai taushi ya manna mata a kunci. Sannan ya sakar mata fuska.
Jin wani dumi da wajen ya dauka yasa husna kai hannu ta shafa ta tabbatar babu abinda ya samu wajen.
Yana kallonta gira ya daga sama cikin alamar tambaya sannan yace mata.
"Gogewa kikai?"
Kai ta girgiza masa. Da sauri tace.
"A.a" saboda ta tuno kashe dinshi.
Daure fuska yai. Tai raurau da ido kaman zatai kuka.
"Ki shirya zamuje wajen Nas"
Bai jira amsarta ba ya tashi ya fice. Ta sauke wani numfashi. Dan tun jiya wani tsoro tsoronshi take jima.
Yanzun sai taji ya rikita mata lissafi duk ta daburce. Hannu takai zata sake taba kuncinta ta fasa.
*
Wajen Nas suka wuni. Yauma kaman jiya bacci yake yi har dare da suka taho bai farka ba.
Wani sha mata kamshi yake. Tunda yabata wayar magana bata sake hadasu ba.
Fuskarshi normal. Kawai dai batajin dadin yanda yake shareta. Sai takejin lefinta like a fuskarta.
*
Suna hawa sama ta soma takawa zuwa bangarenta ya kira sunanta. Wani yarr taji.
Muryarshi ta wani kara budewa ganin ta juyo yace.
"Zo"
A hankali ta taka inda yake ta tsaya. Matsawa yai kusa da ita sosai ya hade space din data bari.
Kan kirjinshi take sauke numfashi. Zuciyarta na wani irin dokawa. Kanta a kasa.
Saida yadan kwanto kanshi sannan ya sumbaci kuncinta. Cikin kunne a hankali yace mata.
"Ki kalle ni"
Yanayin yanda take ji da yanda yai maganar ne ya sata kasa musama umarnin shi.
Idanuwanta ta sauke cikin nashi da suka wani shige ciki. Wani irin dumi taji gaba daya jikinta ya dauka da tasan ba zazzabi bane.
"Good night"
Ya fadi muryarshi tana wani amsawa cikin kunnuwanta.
Kamun ta gama sanin me yake faruwa yabar falon.
Kujerar wajen ta kama ta zauna. Tana maida numfashi. Batasan meke damunta ba. Tadai san kafafuwanta ne basu da karfin kirki.
Takai mintina goma a wajen sannan ta iya tashi ta koma dakinta da wani yanayi da ya dasa mata.
*
Juye juye kawai yake kan gadon shi.
Rabon dayaji wannan yanayin harya manta.
Hussy.....huddy ya rasa meye hakane yakeji.
Bai taba zaton cewar zai sake samun soyayya ba sai yanzun.Abin har tsoro yake bashi.
WATA BAKWAI 7 kawai ya dauka.Alqawari abune mai girma.
Bacin raine ya saka shi ya dauki alqawarin da yake jin bazai iya cika shi ba.
Abinda yasan ya zama dole a gare shi yanzun shine ya koyawa hussy soyayyarshi.
Hakan abune mai matuqar sauqi a wajensa. Duk da kishi yana damunshi.
Yana kishin ammar da yasan ta gama furtawa kalamai da baya son zuciyarsa ta soma qiyasta masa.
Yanzun daya ganta. Yanayin yanda ta nuna rauni. Idanuwanta....komai nata ya kasa jurewa. So kawai yake yajita a jikinsa.
Addu.a ya dinga yiwa huddynsa. Tabarshi da kewarta da yasan har abada bazai daina ba.
Sai dai yanzun yana jin ya karbi rashinta a abu rubutacce.
Yanzun yakan mata addu.a fiye da da. Kuma yana godiya ga Allah daya bashi damar sanin ta a rayuwarsa.
Ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe idanuwansa. Ya so huddy so mai yawa.
Ya tuna wani lokaci can baya.
*** ***
Hawaye yaji suna bi masa fuska. Why? Meyasa za.a canza wannan tsarin a zamaninsu.
Bai taba son sarauta ba. Babu komai cikinta sai wahala da rikici.
Duk ya gama sakankancewa akan mulki bazai taba juyowa kanshi ba. Duk a ture wannan ai bashi bane babba da za.a nada shi a matsayin magaji.
Dafa mishi kafada yaji anyi.
Hannunta ya fita daban dana kowa.Don yakanji tabawar da duk zata masa har ranshi.
Juyowa yai ya kalleta.
Hannu tasa tana goge mishi hawayenshi.
"Yaya kana so nayi menene? Ka daina. Komai ya faru akwai dalili. Hikimomi na Ubangiji suna da yawa sosai. Sun wuce tunani. Ba zamu taba fahimtar hakan ba. Sai dai muyi qoqarin gode mishi da addu.a ya kawo mana komai cikin sauqi"
Baya taba nuna rauni a gaban mutane. Amman huddy dabance. Duk da qarancin shekaru irin nata in tana wani abun har mamakinta yake
Janyota yai ya zaunar da ita gefen shi. Yanda yakeji a kanta yanzun yasa sai dole yake bari jikinsu na haduwa.
Idan ita da karancin shekaru a tattare da ita. Shi babu.
A hankali yace
"huddy ba zasu fahimta ba. Bana son nauyi. Bana son mulkin nan saboda yana da rikici sosai. Zasu iya komai kan shi. Bana so wani abu ya sami........."
Kamin ya qarasa ta rufe mishi baki da hannunta. Cikin idanuwanshi ta kalla sannan tace
"Allah yasa zabin dayai maka shine mafi alkhairi a lahirarka da duniyarka. Allah ya daukaka ka. Daukaka mai daraja yayana. Karkaja da Ikon Allah. Ka gode masa kawai"
Alhamdulillah! Ya furta a fili. Duk da hawayen da yakeji bai hana shi murmushi ba. Allah ya kai Rahma kabarinki hudisa.
Zai iya rantsewa yanajin muryarta cikin kunnuwanshi tana masa dariyarta kan abinda yakeji game da hussy
Da murmushi a fuskarshi Bacci ya dauke shi cike da mafarkin hudeesa da husna.
.
Da wuri ya shirya yau saboda zuwan su mumyn Nas.
Ya fito zuwa babban falonsu.
Wayarshi ya dauko.Ya kira num din husna dayai save tun jiya.
Ringing biyu tai ta dauka. Cikin sanyin muryarta tai mishi sallama.
Ya amsa
"kin tashi lafiya?"
Ya buqata.
"Alhamdulillah"
"Ina babban falo"
"Owk tam barin fito"
Bai amsa ba ya kashe wayar. Ya sauke wani numfashi da baisan dalilinsa ba.
*
Shigarta simple cikin doguwar riga irin ta mutanen sudan pink wacce tai matuqar karbarta.
Har inda yake ta qarasa.
Ta samu waje ta zauna.
"Ina kwana ta furta a hankali"
Sai lokacin ya dago ya kalleta.Ta mishi wani irin kyau daya kasa fadi.
"Hussy"
yaja sunanta. Saida taji wani iri kaman ko yaushe. Indai zai kira sunan ta haka.
Muryarsa na shigarta har bata son tasirin da take mata.
"Mun gaisa yanzun fa"
Yace da yanayin gajiya a muryarsa.
"Hmm yaushe zamu tafi wajen nas?"
Ta tambaya tana sauya maganar. Tunda ta samu yau ya soma mata magana ba kaman jiya ba.
"Sai su mumynsa sun qaraso"
Ya amsa a taqaice.
Jingina tai da kujerar sosai. Kowa yai shiru.
Can ya nisa yace
"hussy kiban labari shirun nan ya isheni"
Yakan bata mamaki haka rannan wai ta bashi labari. Ita kam wanne labari zata bashi. Dan dai yau bata son su wuni irin jiya. Tana son yadan mata magana ta samu damar da zata sake bashi hakuri.
"Wanne irin labari kake so?"
Ta ce tana maida hankalinta kansa.
Gyara zama yai ya kalleta yace
"ko wanne iri ma"
Yanda yai da fuska ya bata dariya sosai.
Ya sake wani tabare fuska. Saita tsinci kanta da son ja masa hancinsa da ya burgeta.
Wani irin kallo yake mata data kasa fahimta.
Shikuma abubuwa da yawa ne suke yawo a zuciyarsa. Kewar huddy. Yana mamaki yasan soyayya.
Amman akan hussy ya rasa ma ko meye a yanzun. Dan wannan ya girmi so.
Yakanji yanayi da dama kan huddy. Amman ba koyaushe yake kallonta yaji yana son jin duminta jikinsa ba. Sai in ita ta taba jikinsa.
Amman hussy. Ko kallonshi tai da idanuwanta din nan a cikin kwanaki kadan da suka wuce sai yaji jikinsa ya dauki dumi.
"Dariya ko? Zo nan"
Ya fada yana nuna mata gefen shi.
Da sauri ta hadiye dariyar ganin yanda fuskarshi ta sauya babu alamun wasa.
Idanuwansa ya zuba mata yana mata wani kallo.
Duk sai takejin ta daban.
Ga kunya da taji ta rufeta babu dalili. Ammar yakan kalleta sosai haka. Batare da taji komai ba.
Amman prince ishaq. Kominsa dabanne. Shi kanshi dabanne.
Da ta tsane shi amman yanzun tsanar sake kala take a hankali.
Bata taba zaton cewar zata rasa kome take ji game dashi ba.
Muryarsa tafi komai tasiri a kanta.Qamshinsa intaji sai taji kaman harda duminsa.
Hakan nasa ta son jinta kwance kan faffadan qirjinsa.
"Zakizo da kanki ko ni inzo?"
Maganar shi ta katse ta. Dakyar ta matsa kusa dashi inda ya nuna mata.
Kafarshi daya ya maida kan kujera ya gyara zama yanda zai fuskance ta.
Yana son yanda manyan idanuwantan nan ke fitowa waje inta tsorata.
Da sauri tace.
"Dan Allah kayi hakuri"
"Inyin hakuri dan kinmun dariya?"
Ya bukata yana kallonta.
"A.a kayi hakuri dan girman Allah. Ka yafemun"
Sarai tun farkon maganarta yagane me take nufi.
Shiru yai kaman yana nazarin me tace. Bayan tun shekaranjiya ya gama yanke hukunci.
"Dan Allah..... "
Ta sake fadi muryarta na rawa. Dan tana tsoron me zatace ma Allah inta mutu a yanzun. Laifinta mai girma ne.
"Fine.... "
Yace yai shiru. Ganin bashida niyyar sake cewa wani abu yasata fadin.
"Haba mana gentle. Fine fa kawai kace"
Wani juya mata idanuwanshi yai a yangance yace.
"You need to sweat a bit more....fine for now"
Batace komai ba. Zata dauki fine din a yanzun. A hankali zai furta ya yafe mata da kan shi.
"Uhum ina jinki"
Ya fadi yana sake gyara zama.
Muryarta a hankali tace.
"Nikam wallahi na rasa labarin dazan baka. Film? Littafi?"
Daga mata kafada yai alaman duk wanda yai mata.
Muryarta a nutse ta soma bashi labarin "Knock knock by james hardley chase"
Tunda ta fara idanuwanshi ne kafe kan labbanta. Yanayin yanda suke motsawa da duk kalmar da take fada.
Idan kaganshi zaka rantse wani abu yake karanta daga labban nata.
Kula tai kaman ma ba sauraranta yake ba. Fuskarta kawai yake nazari. Hakan yasa tace.
"Wai kana ma jina ne?"
"Inajinki mana. Massino ya zauna daram kan power yana controlling duka unions"
Tai mamaki dan bata ma zata yanaji ba. Langabe kai tayi tace masa.
"Zan karasa maka anjima. Bakina ya gaji"
Baice mata komai ba kallon fuskarta kawai yake. Labbanta da bai taba karema kallo ba ya zuba ma ido.
Ba karamin ja mishi hankali sukai ba. Hannunshi yakai yasa yatsan shi ya zagaye yana dangwalo man dake lebenta.
Husna ta wani daskare waje daya. Banda bugun zuciyarta da take ji har cikin kunnuwanta.
Kallon yatsan yai. Da man daya dangwalo a jiki. Ita kuma shi take kallo.
Ga mamakinta a nashi leben na kasa ya shafa sannan a hankali kaman mai gwada wani abu ya tsotse leben daya shafa ma man.
Wani dumi taji jikinta ya dauka.
Kawai so yake ya dandana labbanta kuma wannan ba lokacin daya kamata bane.
Babu yanda za.ai ya hada bakinshi da yarinyar da bata son shi. Ko ya yake ji akanta kuwa.
Hakan ya sashi dandana kalar man da yasa yaga labbanta sunyi wanu pinkish kala mai haske.
Zakin dayaji me yasa shi yamutsa fuska. Kallon ta yai cikin ido yace.
"Zaqi.... I mean man dake lips dinki"
Harshenta tasa ta laso kaman bata taba sanin yanda man leben yake ba.
Wani numfashi yaja dayasa kallon shi sosai.
Ringing din wayarsa ya katse su daga duniyar da suka shiga.......!
.
Wayar ya dauka. Mumyn Nas ce hakan ya tabbatar mishi da isowarsu.
Dan haka yace ma hussy ta dauko alkyabbarta ta saka su jira qarasowarsu.
Sai bayan ta fito ne ya kalleta yace
"me kikaci?"
"Bana jin yunwa"
ta fadi.
Lokaci daya fuskarsa ta sauya zuwa yanda ta saba ganinsa farkon aurensu kamin ta san fara.arsa.
"Muje dining room din"
Ya umarta. Yanayinsa ya nuna mata ba zai karbi wani uzuri ba dan haka tai gaba yana binta har suka qarasa.
Zama yai yace mata
"Maza ci wani abu da sauri kamin su qaraso"
Babu yanda zatai haka dolenta ta danci plantain da dankalin turawa.
Ga kunyarsa da ta tsinci kanta ciki saboda kallon da yake mata.
A hankali tace
"kai ba zakaci komai ba"
"Na sha malt banjin saka ma cikina wani abune"
Ya furta yana miqewa.
Binsa tai a ranta tana fadin. Wato shi baya son sakama cikinsa wani abu. Sai ita yai ma dole.
Suna fita babban falo sukaji sallama.
Tare suka amsa.
Da fara.ar prince ishaq ya qarasa ya tarbo su yana fadin
"mumy sannunku da isowa"
Cikin sanyin murya husna tace musu
"barkanku da isowa"
Mumyn nas ta kalleta tace
"Ma shaa Allah. Sannu in-law"
Dan bata taba ganinta ba. Sanda akai auren tana england dubo kanwarta da akaima dashen koda.
"Ku qaraso ciki mana"
prince ishaq ya fadi.
Yana shirin juyawa yaji an taho da gudu ana fadin
"yayaaaaaa"
Kamin ya qarasa juyowa ta ruqunqume shi kaman zata karya shi.
Ya lumshe idanuwansa ya budesu a hankali. Wanni aikin sai auta.Baisan da ita za.azo ba.
Wani son kanwarshi yaji ya cika masa zuciya fal. Yayi kewarta sosai.
"Auta saikin karya shi ke yaushe zaki natsu ne bakya ganin antynki tsaye"
mumyn nas ta ke fadi tana murmushi.
Auta ta sake prince ishaq tana dariyarta cikin tabara tace
"mumy ai na dade banga yaya bane shisa. Laaaa antyyy wlh kin hadu"
ta qarasa wajenta tana riqo mata hannu.
Shafa kanta husna tai tana murmushi farat daya yanayin yarinyar harya shiga ranta.
Tai bala.in kama da nasir. Waisu haka suke da shiga raine? Ta tambayi kanta.
*
Bayanda prince ishaq baiba ko hutawa su danyi. Mumyn Nas taqi tace suje asibitin dan da sun ganshi ba jimawa zasuyi ba komawa zasuyi.
Husna tace
"Haba mumy da wuri haka na dauka zaku kwana ne ai"
Wai ai kam yau zamu juya in-law. Ba zamanmu nasir yake buqata ba. Addu.a ne. Tunda duk gaku anan din. Da munga yanayin jikin nasa zamu koma in shaa Allah"
Haka suka haqura tunda mumyn nas sam taqi jinsu. Suka nufi asibitin.
*
Suna bayan mota zaune ita da prince ishaq kasancewar mota daban daban ce data su mumyn Nas tace mishi
"kana ganin ya kamata auta taga Nas kuwa. Kaman shekarunta sunyi qanqanta taga tashin hankali har haka"
Dan autar kam duka bata fi shekaru bakwai ba.
Murmushi yai. Hannunta ya riqo.Ya hada yatsun su waje daya. Yace
"ki yarda dani hussy a rayuwa irin tamu auta taga abubuwa da yawa. Wannan ba komai bane."
Saita tsinci kanta da sake riqe hannunta cikin nasa sosae. Tana mamakin hargitsi dake cikin sarauta.
Lallai mutane na kuskure kan mulki. Daga nesa saikaita sha.awarsa har kana jin dama kaine matsayin.
Sai yanzun take lura babu komai cikin mulki musamman na sarauta banda rashin kwanciyar hankali da tarwatsar farin ciki.
*
Har suka qarasa asibitin suna riqe da hannun juna saida suka fito ne sannan.
Nas yanata bacci a fadar likitansa. Daqyar ma suka barsu suka shiga gabaki daya da sunce ba.a son hayaniya ta tashe sa anfi so ya farka da kanshi saboda magungunan da ke aiki.
Sunkai mintina ashirin zaune shiru kawai.
Kamin mumyn nas ta miqe.
"Allah ya bashi lafiya"
ta furta a sanyaye.
Su duka suka amsa da amin.
"Is he gonna be okay?"
Auta ta tambaya muryarta can qasa.
Tsugunnawa prince ishaq yai yanda tsahonsu yazo dai dai.
Ya dafa kafadunta cikin taushin murya yace mata
"we don't know yet. Amman muna masa addu.a."
Husna ta faki ido tadanyi qasa ta mintsine shi a baya.
Yaji zafi ya dake kawai ya miqe.
Ta riqo hannun auta da idanuwanta suka cika taf da hawaye. Tajata jikinta. A hankali tace
"karki damu zaiji sauqi in shaa Allah. Kinga bacci yake. Daya tashi zan kira mumy a waya ku gaisa."
Kai kawai auta take daga ma husna saboda kukan da yake neman cin qarfinta.
Hada ido sukai da prince ishaq ta galla mishi harara. Duk shi yaja.
Wannan yar yarinyar saboda Allah.
*
A wajen mota sukai sallama da su prince ishaq aka tafi a mayar dasu airport subi jirgin dazai koma kano qarfe 12.
Saida suka shiga mota su kadai sannan ta juyo ta kalle shi sosai a dake tace
"meke damunka?"
"Me nai maki zaki mintsine ni"
Ya buqata shima a dake.
"Saboda me zaka fada ma auta cewan ba lallai bane nas ya tashi. Baka ga tai qaranta ba?"
Husna take fadi ranta a bace.
Shi sai yaga ta qara kyau yanda ta dage tanata masifa. Baisan sanda dariya ta kubce masa ba.
Ta sake hade rai duk da kyau da taga ya qara mata. Inyai dariya takan bayyana farin cikin a fuskarsa da wani kwarjini naban mamaki.
Bata san lokacin data ja mishi hanci ba. Ya ture hannunta yana fadin
"oww hussy da zafi fa"
Ammar! Zuciyarta ta furta a hankali.
Dannewa tai ta kalli prince ishaq dake gabanta. Tace
"abinda kai baka kyauta ba sam"
Da yanayin muryarta yace
"ni bazanyi qarya ba"
Dariya ya bata sosai.
Ya tsaya yana kallonta. Komai nata yasha ban ban dana huddy.
Komai da yake ji a kanta dabanne da yanda yaji akan huddy.
A lokaci daya kuma su dukansu sunyi tarayya a zuciyarsa wajaje daban daban.
.
Mintsininta yai a cinya bata zata ba. Tako saki wani qaramin ihu.
Dan taji zafin mintsinin.
Da sauri ya rufe mata baki yana zaro ido.
"Shh hussy bamu kadai bane a motar fa akwai driver"
Yake fadi cikin sanyin murya. Duk da akwai iyaka tsakaninsu.
Ta rausayar dakai gefe tace
"amman kasan da zafi aiko?"
Kallonta yai ta qasan idanuwansa
"umm qaramin wanda kikamin ne"
ya fadi yana daga mata gira.
Dariya tai sosai. Ta rasa yanda akai yake yawan sakata dariya.
Tasan ammar kan sakata dariya amman ba kaman wannan ba.
Yanayin yanda yake canza fuskarsa zuwa yanayin abinda yake so ne yake burgeta.
Yana sa ta manta da damuwar da takanji a yanzun.
Kewar ammar tana nan daram. Sai dai shi din ya cika wani gurbi da bata son da zamansa ba ma.
Kallonta yake yanda tai zurfi cikin tunani. Zaiso sanin me yake yawo cikin kanta saidai shiba mutum bane mai yawan bincike.
Muddin abinka bai shafe shiba yakan baka wajen da kake buqata kai taka rayuwar.
Hannu yasa ya tallabo habarta ta sauke idanuwanta cikin nasa.
Tsoro,shakku da fargaba da wani yanayi da baison meye ba cike da idanuwanta.
Sauke su tai a hankali daga nasa idon zuwa fuskarsa.
Gara ta kalli komai a yanzun da cikin qwayar idanuwansa da take fisgarta zuwa wata duniya mai zurfi.
Hada goshinsa yai da nata. Tana jin hucin numfashinsa kan fuskarta.
Ta rufe idanuwanta. Bata son yanayi ko daya da take ji a jikinta.
In batai wasa ba prince ishaq zaisa ta manta kanta bama ammar kawai ba.
Lokaci daya taji zuciyarta ta fisgeta zuwa wani lokaci. '
*** ***
"tawan wlh kewarki ta dameni na ma kasa zama lectures"
Na samu na gudo gida fa.
Murmushi tai
"haba nawan abinda zaka dawo ka sameni saika gudo. Bana son kana saka wasa kaga dai shekarar qarshe kake."
Dariyarsa yai mata cikin muryarsa mai sanyi yace
"haba kin fiyemin lectures din yau. Inban ganki ba ba fahimtar komai zan ba"
Hmm ammar.......!
*** ***
Bata son ta furta ammar' a fili ba sai wani irin dilla taji mai zafi kan lebenta daya dawo da ita hayyacinta.
Owww ta fadi tana ture shi.
Lebenta ta taba da dan yatsa ta dawo dashi zuwa dubanta dan zatonta yai jini.
Tana shirin yin kuka ta kalli prince ishaq da saida ta tsorata da yanayin fuskarsa.
*
Wani abu yaji ya tokare masa wuya mai daci dashi bai fito ba shi bai koma inda yake ba.
Qirjinsa yai wani zafi. Yana tare da hussy har tunaninta zai kaita kan 'ammar.
Hannuwan shi yasa ya janyo gab dashi sosai.
Goshinsa ya hade da nata yana kallonta. Numfashi yake maidawa a hankali yana son controlling abinda yake ji.
Da aurensa akanta takejin tana da iko ko damar da zatai tunanin wani. WATA BAKWAI 7!!! Kacal yake dasu ta so shi.
"I am sorry" ta furta tun kamun abinda take gani a fuskarshi ya fito fili.
Muryarta ta katse mashi tunanin da yake. Hannunta ya kamo ya dora saman qirjinsa.Ya hada da nasa ya danna.
Tanajin yanda zuciyarsa ke dokawa. A dake yace
"kinsa tana bugawa a bangaren da nai zaton ya jima da daina aiki. Zaki iya taimakawa yanayin raunin da ke jikinta. Ki danne son 'ammar'......"
Yanda ya fadi son ammar saida jikinta ya amsa. Yaci gaba
"sorry na dillar maki lips ko?
Ya qarasa yana yatsina fuska.Ta gyada kai alamar eh dan har lokacin wajen yana mata zafi kuma ta tabbata sai jini ya kwanta.
Ta sake saka dan yatsa ta taba. Duk yana kallonta.
"Good"
ya furta ya dora da
"inkinzo fadin sunanshi a gabana ki dinga tunawa dan zan maki wanda ya fishi a gaba"
Goshinta ta cire daga nashi. Wato wanda yafi wannan ma. Naushin masa kafada tai da qarfi tako ji kaman ta naushi dutse saboda taurin muscles din dake tattare wajen.
Ta lanqwashe yatsu. Wayyoo owwhh take fada tana yarfe hannu.
Yai dariya dai dai lokacin da motar ta tsaya alamar sun qara so gida. Bude masu qofa akai suka fito.
Husna riqe da hannunta tana murza yatsunta har suka qarasa can cikin gidan. Ya wani basar kamar bashi ya gama dariya cikin mota ba.
*
Cikin gida suka shiga.
"Gentle"
Ta fadi. Ya juyo yess! Saita rasa me ma zata ce masa saboda yanda ya kafa mata idanuwan shi din nan.
Ta kasa sabawa da kalar kallon da yake mata. Kodan koyaushe daban take ganinsa.
Intaso ta gane yanayin kallon anjima bada irinsa zai dubeta ba.
"Ina jinki hussy"
ya fadi a qagauce da son jin me zatace.
A daburce tace masa
"ina son inje saloon ne daman a wankemin kaina and......."
Daga mata gira yai data soma sabawa dan yana yawa yin hakan duk da ma.anarsa yawa gareta a wajensa.
Duk ta daburce kaman mai koyon magana. Daqyar ta hadiye miyau ta ci gaba da fadin
"Ina son inje wajen kausar in babu damuwa"
Sauke ajiyar zuciya yai.
"Ki kira kausar ta turo address dinta a kaiki.Masu tsaro zasu rakaki.
Su jira ki gama ko yaushe ne su dawo dake gida"
"Saloon dinfa?"
Ta tambaya tana shagwabe mishi fuska.Ya girgiza kai
"Ki haqura ba yauba. Saboda dalilai da yawa"
"Amman......."
Ta soma yanda ya zuba mata idanuwa yasata yin shiru. Ta rasa me yasa yake bala.in mata kwarjini haka..
"Good Banson gardama..." Bata sake cewa komai ba harya wuce sashinsa.
*
Itama nata bangaren ta wuce. Kan gado ta kwanta. Yanayin komai da suke ita da prince ishaq na dawo mata. Wani abu na mata yawo cikin zuciya.
Ga ammar ta kasa daina jin kome take ji a kansa. Abinda yake bata mamaki yanayi kala daban takeji akan su shida prince ishaq.
Shin wanne ne so a ciki? Ko dai qauna, so da kuma shaquwa abubuwane daban bata sani ba wai.
Tabbas basukai tsayin lokacin da a tunaninta zasu shaqu da prince ishaq ba. Qaunarsa fa? Tsana na juyewa zuwa qauna ne.
Son shi fa? Um to zuciyarta na mata wasi wasi saboda indai yanda takejin ammar a zuciyarta shine so to wani abune daban kan prince ishaq.
Abu can cikin zuciyarta manne da qamshin sa kawai intaji yakan tuna mata abu da yawa. Sai ta tuna wani lokaci can baya.
Tana kwance kamar lokaci irin wannan a dakinta. Ammar ya kira wayarta suna hira yace
"tawan kamar yan gidanku basa na.am da soyayyarmu. Ina tsoro har raina"
Duk da itama ta soma tsoron hakan kuma tasan dalilinsu yafi nata qarfi bai hanata son ammar dinba.
Cikin taushin murya tace
"ba haka bane nawan kaima kasan dalilinsu kuma in shaa Allah zamu samo maganin matsalar kafin abin yai nisa ko?"
"Hakane tawan ina tsoro ne kawai. Jiya nai mafarki ana daura aurenki amman da wani bani ba"
Dariya tai mishi
"nawan mafarkine fa Ba komai ba. Ka manta kawai. Me kake yanzun?"
"Um waqa nake ji da wayana na kiraki kuma."
Ya amsata.
"Wanne waqa?"
"Cikin zuciya tana quna da so tai bankwana rabamu da juna soyayya a rai ya bugan naji zafi"
ya soma raira mata waqar fitaccen mawaqin nan hussaini danko.
Indai waqane kam muryar ammar daban take. Tason waqar jin yai shiru yasa tace
"uhm nawan da dadi ka ci gaba"
"Hmm"
ya fadi ya dora da
"waqar ta tunamin da yanayin da muke cikine shisa"
Jin ya fadi hakan yasa ta dora dan shiya koya mata jin waqoqin danko
"na yarda dakai kadai daya ke saka mini shauqi. Zancen da kake yasa na sarqe ka har a mafarki. Rabani dakai yakan sa na kashe kaina in rufe daki. Zamanmu dakai a zuci nakai ya yarda na mallaka mata kai"
Sai lokacin yai dariya
"tawan wlh ina shan dariya sosai in kikai waqa a tsayen nan kuma ko a jikinki"
Itama dariyar take sam duk yanda ake fadin muryarta nada dadi bata lanqwasuwa indai wajen waqane.
Haka ammar zaice tai mishi waqa kawai dan yaita dariya yakance tawan a haka nake sonki da kominki.
Hawayen da suka bi mata fuska ta goge. Taya zata manta ammar ne a ranta. Sunyi wata irin shaquwa.
A ko ina na rayuwarta yana ciki!
Saidai yau take shirin yi masa sallama. Dan ta karbi aurenta da zuciya daya. Ta na fatan Allah ya yafe kata kuskuren data aikata.
Bathtub ya shiga ya sakarwa kansa ruwa masu matsakaicin sanyi.
Ko zai daina jin abinda yake ji. Zuciyarsa wata iri ce mai saurin shaquwa.
Yana da kishi sosai. Har yanzun qirjinsa zafi yake. Rabon da ya ji haka an kai wata biyar.
Tunda radadin rashin huddy ya soma sauqaqa zafin qirjin ya rage.
Yakanji shi in yana tunaninta koda kuwa zaiyi murmushi ne.
Amman ba irin nayau da yaji sunan ammar kan labban hussy ba.
Ya dauki lokaci mai tsayi cikin kwamin wankan kamin ya fito.
Towel ne kawai jikinsa ba tare da tunanin komai ba ya qarasa zuwa dakin baccin nasa yai tsaye jikin mudubi yana goge gashinsa da qaramin towel.
*
Wanka ta sake yi ta shirya cikin atamfa lemon mai dan duhu. Kwalliya tai sosai.
Ta zo kiran kausar ta tuna babu lambar a ciki tana wayarta da prince ishaq ya fasa.
Mantawa tai randa suka zo asibiti duba Nas ta karba.
Amman tace mata zasu dawo ai ta karba tare da address din gaba daya.
Ta yanke shawarar ta kira ta fada mishi abar zuwan sai wani lokaci bai dauka ba.
Wajen kira shidda. Data share shi saita kasa haqura. Haka kawai taji ta damu tasan ko lafiya.
Kamin kwakwalwarta ta gama natsuwa tabi shawarar zuciyarta ta fito daga dakinta ta nufi shashinsa.
Duk da bata bata takawa wajenba. Wani dan karamin falo ne a ciki. Kawatacce.
Tabi dan lungun da tasan zai kaita bedroom dinsa. Ta qwanqwasa taji shiru ta tura da sallama ba.a amsa ba.
Dakin baccinsa gabaki daya kalar blue ne mai haske kaman na sararin samaniya.
Da digon taurari yellow mai haske jikin komai. Harta da furnitures din. Kallon dakin kawai ya saukar mata wata natsuwa ta bangaren da bata fahimta ba.
Kan gadon ta zauna daga gefe. Hatta zanin gadonsa irin kwalliyar gare shi. Tasa hannu ta shafi pillow din sa. Ko ina qamshinsa yake.
Komai neat a tsare sai dakin ya wani burgeta.
A nutse take qare ma dakin kallon. Idonta ya sauka kan bangon dake fuskantarta.
Qaton hoton mahaifiyarsa ne da mahaifinsa. Dukansu sanye da shiga ta alfarma.
Daga gefe ma wani hotonne na mahaifinsa da mumyn Nas shima yai kyau. Ta maida kallonta kan hoton Nas har guda biyu.
Tai murmushi a ranta tana masa addu.ar samun sauqi.
Dayan bangon ta juya cike yake da hoton wata kyakkyawar yarinya da duka shekarunta ba zasu qarasa goma sha shidda ba.
Daya dayafi kowanne girma sanye take da riga da wando na pakistan ta yafa mayafin kan kafadarta.
Gashin kanta ya sauka saman kafadarta. Idanuwanta ba kan mai hoton yake ba.
Da alama wani take kallo can tasa hannu tana qoqarin rufe bakinta da dariyar da take.
Sai husna ta samu kanta da yin dariya itama. Yarinyar a hotuna ne amman tana ji kaman tana qoqarin yi mata magana ne.
Duka hotunan hankalinta yana wani waje ba kan hoton ba. Motsi taji dan haka ta juyo.
Cik komai ya tsaya mata. Prince ishaq ne daga shi sai towel daure a qugunsa. Sai dan qarami da yake goge gashinsa.
In tace jikinsa mai kyaune. To a nata ganin kaman ta rage masa daraja ne. Komai nasa.
Tsayi da qirarsa yanda take misalta namijin da zatai rayuwa dashine a can duniyar tunaninta.
Abin mamaki yau gashi a gabanta. Bugun zuciyarta taji ya tsaya.
Har iskar wajen ma. Shi kawai ta zubawa idanuwa tana kallon yanda Allah yai namiji a wajen.
*
Jikinsa ya bashi ana kallonshi. Ya juya cike da mamaki ya fito da idanuwa.
Lokaci daya mamakinsa ya juye zuwa nishadi ganin yanda husna ta zuba masa idanuwa.
Har fitowa yaga idanunta sun qara irin yanda ka keyi inkaga wani bangare na abunka dayafi dayan barin kyau.
*A duk lokacin da wani zai karramaka. Baka da abinda zaka bashi sai dai fatan alkhairi. Allah ya albarkaci rayuwarki UMMIE JAY. Allah ya karramaki fiye da yanda kika karramani! "Masoya ina godia da sakkoni da fatan alkhairi. Ina kaunarku fiye da yanda kukeson prince ishaq.*
Duk ihun da kwakwalwarta take mata a banza dan zuciyarta kan prince ishaq da kyawunsa take.
Allah ya qera namiji a wajen. Bata taba zaton namijin da take mafarki a zuciyarta akwai shi bama.
Da komai da yanayin jiki. Girma da tsayi haka take son taga namiji.
"Hussy"
ya kirata da wani yanayi a muryarsa.
Hakan ya dawo da ita hayyacinta a kunyace ta sadda kanta qasa.
"Lafiya dai ko?"
Ya buqata.
Duk da bata kalli fuskarsa ba taji murmushin dake cikin maganarsa.
Cikin sanyin murya tace
"na kiraka ne baka dauka ba shine nazo na duba ko lafiya"
Takawa yai har zuwa inda take ya zauna gefen gadon. Kallonta yake sosai.
"Ina wanka ne hussy shisa"
Tana jin hucinsa a kusa da ita da qamshin da ba zata ce sabulai bane. Abin wanka ne ko na wanke kai. Wani fresh kamshi mai saukar da kasala.
Duk ya hautsina mata lissafi so take kawai taji duminsa. Tana kuma so ta taba damtsensa da wata tsoka take dunqule.
Cikin rawar murya tace masa
"abar zuwa gidan kausar na duba banga number inta a wayana ba. Shine zan fada maka daman"
Hannu yasa ya dago mata fuska taqi kallon shi.
Miqewa tai da niyyar barin dakin ya riqo mata hannu.
"Gentle inka gama shiryawa ina falo"
ta furta tana qoqarin qwace hannunta.
Muryansa a tabare yace
"ke zaki tayani shiryawa tunda kinzo"
Sai lokacin ta kalli fuskarshi sosak ta fito mishi da idanuwa tace
"haba mana gentle kamin haquri ka shirya kam"
Ita kadai tasan me take ji gashi yaqi ya sake mata hannu.
Wayarshi tai qara,hamdala husna tai saboda sakar mata hannu yai ya dauko wayarshi.
Hankalinsa gabaki daya kan wayar dayake yi ya koma.
Hakan yaba husna damar lallabawa ta fice daga dakin.
*
Falonshi ta zauna harya fito. Suka hada ido tai mishi murmushi.
Ya wani yatsina fuska hadi da fadin
"shine kika gudu ko?"
Dariya ya bata.
Ya zagayo ya dauki pillow din kujera ya jefa mata tasa hannaye ta kare tana dariya.
"Ka kyaleni ka cika rigima"
ta fadi muryarta da alamun dariya.
Wani dogon numfashi ya fitar dayasa husna tambayarshi
"yadai?"
Saida ya fuskanceta sannan yace
"nagajine kawai, nagaji da komai ina son zama normal kaman kowa."
Tai shiru saboda batasan meya kamata tace mishi ba.
Shima shirun yai dan bai tsammaci amsa daga wajenta ba.
Yai maganar ne kawai danta tsaya mishi a wuya.
"Hotunan huddy ne a dakinka?"
Ta tambaye shi cikin sanyin murya. Idanuwanta kan fuskarsa.
Tana kallon yanda tambayarta tasa ya rufe idanuwansa na yan daqiqae sanan ya bude su.
Da dukkan alamu tambayar ta taba mishi zuciya.
Hakan yasa husna fadin
"kayi haquri ban........"
Katseta yai da fadin
"karki damu,hotunantane"
*
Tare sukaci abinci. Shiru kowa da abinda yake tunani a zuciyarsa.
Bayan sun gama ne suna zaune a falonsa take tambayarshi ko zasu koma wajen nas ne.
Yace mata
"sai gobe in Allah ya kaimu"
"Allah ya kaimu"
ta amsa mishi. Yatsine fuska tai yace
"yadai?"
"Gashi na ya isheni bana iya gyarawa da kaina ko a gida saloon nake zuwa ko mamana ta tayani mu gyara"
Idanuwansa ya kafa mata yanayin yanda take maganarta yana burge shi. Murmushin sa yai.
"Muje ki wanke in tayaki"
Ta fito da idanuwa tana dariya
"gentle ina ka iya? Ka taba yine"
"Sai muyi downloading ingani"
Ya fadi muryar sa babu alamar wasa.
Hakan ya sake bata dariya.
"Lallai barshi i will manage har lokacin da zanje saloon"
Yasan zai iya sa a dauko hair stylist ta gyara mata har gida. Bazai yi bane sabo da yana son ta soshi kuma bashida wani wadataccen lokaci.
So ba abu bane dake shiga lokaci daya. Musamman nashi a zuciyarta dake dauke dana wani.
Hade fuska yai kaman maganarta ta taba mishi zuciya.
"Ni ko?"
Ya fadi yana tabare mata fuskarshi me kyau. Ta sake yin dariya. Tashi yai.
"Ina zaka?"
Ta buqata bai kulata ba ya kama hanya. Hannunshi ta riqo ta rasa me yasa jikinshi yake mata dumi haka. Sai kace yana zazzabi.
Juyowa yai ya daga mata girarsa duk biyun.
"Zo ai downloading din kagani sai mu gyara tare"
ta fadi tana kallon idanuwanshi.
Murmushin sa yai mata daya kai har cikin idanuwanshi ya samu waje ya zauna sukai downloading yanda ake wanke gashi.
Sai daya gama kallo tsaf
sannan ya juyo yace
"kinada duk kayan nan na ciki? Ko nai waya a kawo"
Ta girgiza kai
"tace dryer ne babu irin nasu sai karami na riqewa a hannu...sai clips in nan suma babu"
Wayarshi yake dannawa.
"Me zakai?"
Ta tambaya. Zan wayane akawo. Kamun ta sake magana harya ce
"Hello....."
Hakan yasa tai shiru tana kallonshi yana bada umarnin akawo duk wani kayan da za.a samu a saloon.
Saida ya gama tsaf ta ce
"gentle yanda kake fadar nan sai kace saloon zamu bude"
Murmushi kawai yai. Ba ai awa dayaba aka kawo kayan.
Hadiman gidan suka dauke suka kai bangaren husna. Saida suka gama tsaf suka koma nasu wajen sannan prince ishaq ya miqe tsaye yace ma husna muje.
Sai da taji gabanta yadan fadi. Yau akwai rigima kenan gashinta ba wani mai tsaho bane can saidai warwarewarshi ne aiki tunda rubber ne.
Takan godema Allah data biyo jinin fulanin babansu ta bangaren gashi. Kanwarta taita cewa daman ita. Dan nata gashin dakyar yake parking.
Haka tabi bayanshi har toilet din bangarenta. Duk da ta rage zama da hijab sosai in tana tare dashi.
Cire dankwalinta a gabansji ba karamar wahala yai mata ba. Sai taji gaba daya kunya ta rufeta.
Da kanshi yaje ya dauko stool din dake dakinta yana fadin ta zauna akai kamun su siyo nasu kujerun wanke kan.
Ta zauna wajen abin wanke kai. Prince ishaq yazo ya warware ribbon da ta kulle gashinta dashi.
Ya dauko comb ya soma tajewa.
Tai mamakin yanda yake bi a hankali kaman ya sabayi daman.
Fuskarshi take kallo ta cikin mudubin toilet din yanda ya nutsu sai kace yana wani muhimmin aiki.
Sai taji wani yanayi a zuciyarta data kasa fassarawa.
Shampoo yasa ya soma cakuda mata gashi. Wayarshi dake ajiye gefe ta soma ringing.
Ya share ya cigaba da abinda yake yi harta yanke.
Yatsun sa yasa cikin gashinta ya yamutsa hakan yasa tsikar jikinta tashi.
Kula yai da hakan yace
"da zafi ne?"
"A.a"
ta fada dakyar muryarta can kasa saboda wani yanayi data tsinci kanta cikinsa.
Haka ya wanke gashin tas. Yasa oil ya fara daukar abinda ake maqale gashi yana kallon su.
"Hussy"
Ya kirata.
"Naam"
ta amsa tana goge kunnuwanta da towel.
"Ya ake maqala wannan abin ma?"
Dariya tai sosai tace
"ba zaka iyaba kabarshi"
tana kokarin karbar clip din daga hannunshi.
"Um um"
ya fadi yana janyewa ya dora da
"ni fa sai nayi ki fadamun yanda zansa kawai
Ta kula prince ishaq ba karamin dan rikici bane. Dole a haka daqyar tare suka maqala clips din.
Ya dan koma da baya ya kalleta kinyi kyau ya fadi. Tai murmushi a kunyace.
Dryer ta shiga suna dan hira da prince ishaq din kadan kadan.
Har kanta ya bushe. Clip daya ya cire yako hado da gashinta ouchh! tai yar qara tana kai hannu wajen.
"Sannu sannu da zafi ko?"
Yake fadi yana shafa mata wajen.A hankali yabi ya cire clips din duka.
Tana miqo mishi kalar man dazai shafa mata. Ya gama suka taje kan tsaf tasa abu ta daure.
Sannu da aiki gentle. Ta fadi tana kallonshi duk ya wani burgeta. Sauke numfashi yai yace mata
"yawwa kinga kin huta da zuwa saloon ko? Tunda na iya"
Dariya tai kawai dan tama rasa me zata ce mishi. Suka dawo falonta. Ya dauki wayarshi ya duba.
Ya kalli husna yace mata
"Zan fita"
"Allah ya tsare ya dawo dakai lafiya"
Ya amsa da
"amin"
Miqewa yai kaman zai tafi ya dawo ya sumbaci kuncinta sannan ya wuce.
Ta lumshe idanuwa tanajin qamshinsa daya cika wajen. Har lokacin tana jin hannuwansa cikin ko ina nakanta.
Zuciyarta tai mata wani nauyi mai wuyar fassarawa.
*
Har tai sallar isha.i bataji dawowar shi ba. Haka kawai sai taji ta damu tasan wanne hali yake ciki.
Ta dauki wayarta ta kirashi wayarshi a kashe. Tai ta trying bata samu ba.
Hakan yasa ta shiga tai wanka ta fito tai shirin bacci ta kwanta.
Amman zuciyarta dauke take da damuwa musamman da ta sake kiran lambarshi taji wayar a kashe.
Tashi tai ta koma bangarensa ta kwanta falonshi kan doguwar kujera. A zuciyarta tana fatan Allah yasa lafiya. Bata san lokacin da bacci ya sace taba.
Ji tai ana taba mata fuska a hankali ta bude idanuwanta ta sauke su kan prince ishaq dayake mata wani kallo da ba zatace ga fassarar shi ba.
A kunyace ta sauke idonta tana fadin
"ka dawo? Inata kiran wayarka shiru"
"Chargy na ya kare ban sani ba sai yanzun nagani"
Ya bata amsa. Miqewa zaune tai duk kunyarshi ta rufeta saboda yanayin kayan dake jikinta.Shikam ko a jikinsa.
Tashi tai tace mishi
"saida safe daman dan inji shigowarkane yasa nazo"
Kallonta kawai yake baice mata komai ba harta fita daga dakin.
Yanda yake ji a zuciyarsa idan ya tsayar da ita komai zai iya faruwa.
A hankali yake son ya saka mata sonshi a zuciyarta. Baya son gaggawa a rayuwarsa.
Daqyar ya iya tashi ya qarasa ciki ya rage kayan jikinsa ya watsa ruwa. sai juye juye yake kan gado ya rasa abinda yake masa dadi.
Ga jikinshi ciwo yake sosai. Ba saba wannan zirga zirgar yai ba. Kasa bacci yai ga yunwa na damunshi.
Ya mike ya fito wajen dakin. Da niyyar zuwa ya duba abinda zaici ya fito amman zuciyarsa da kafafuwansa bangaren husna suka kaishi.
Saida ya tura dakinta a hankali tukunna yasan me yake. Saidai bazai iya juyawa ba koda yaso. Karasawa yai.
Bacci take hankalinta kwance. Ya zauna gefenta ya zuba mata idanuwa kawai zuciyarshi dauke da wani nauyi da ya rasa na menene.
Hannu yasa ya shafi gefen fuskarta. Hakan yasata bude idanuwanta cike da bacci ta sauke su kan fuskarshi.
"Gentle"
ta fadi muryarta ta mishi dadi yanayin yanda taja sunanshi.
"Yunwa nakeji hussy"
yace mata yana langabe kai.
Ga mamakinsa lokaci daya ta mike.
Takai hannu ta kunna normal wutar dakin dan marar haske ce bata ma kashe ba bacci ya dauketa.
Sai lokacin ya kalleta sosai. Tana murza idanuwanta. Gashinta duk ya hargitse wani ya zubo gefen fuskarta. Dariya yai a hankali.
Ta harare shi
"ni ko gentle? Zaka nemo mai kawo maka food tunda dariya kakemun"
Ta fadi tana komawa kwanciyarta. Dariya yaci gaba dayi yace
"Yi hakuri hussy taso ki rakani in samu abinda zanci"
Yanda yai da fuska yasa ta kasa mishi musu. Ta miqe zaune tare suka shiga kitchen. Sai tarin snacks. Don haka ya dibi cake da apple sai fresh milk. Su yaci husna na zaune tana kallon shi.
Kominshi a nutse yake yinsa. Yanayin taunar abincin ma zaka rantse yanga yake kuma ta kula haka halittarsa take. Saida ya gama tsaf ya sa mata rikici saita rakashi yai brush.
Dole ta bishi nasa bangaren yai brush ya dawo dakin baccinsa.Miqewa husna tai ya riqo hannunta.
"Ina zakije?"
Ya tambaya. Hannunta take kokarin kwacewa tace
"bacci nakeji zanje in kwanta"
Girgiza mata kai yai alamar a.a sannan yace
"nan babu wajen kwanciya?"
Fito da idanuwa tai ta langabar dakai gefe guda tana fadin
"gentle bana son rikici ka sake ni in tafi"
Janyota yai da duk karfinsa ta fada jikinshi.
Yasa hannuwa ya rungumeta sosai yana sauke numfashi.
Saida ta hadiye yawu yafi sau uku kamun ta samu muryar ce ma
"bacci nakeji"
Cikin kunnenta yace
"hussy........ Yanayin yanda yaja sunan da muryarshi suka saukar mata da kasala. Ga zuciyarta dake dokawa.
Ki kwanta anan. Magana take shirin yi ya cizar mata kunne cikin sigar data sa duk wasu kalmomi suka bace mata. Shiru tai.
Jin haka yasa prince ishaq gyara kwanciyarshi sosai. Itama ya gyara mata tata kwanciyar.
Tanajin shi yana karanto addu.o.in tsari da saida ya burgeta.
Ya tofa ko ina na daki. Ya sake yin wasu ya tofa musu shi da ita.
Bata ganin fuskarshi yanayin yanda ya kwantar da ita. Bayanta ne a kirjinsa. Sumba ya manna mata a wuya hadi da fadin
"sleep well hussy"
Yaja blanket ya lullubesu. Bacci mai nauyi ya dauke shi. Husna kam zuciyarta dokawa take da wani irin yanayi da bata saba jin shi ba. Koya tai motsi saiya sake riqeta a jikinshi.
Ta jima batai bacci ba kuma ba zatace ga abinda ya hanata bacci ko kuma ga abinda take tunani ba.
Tana da tabbacin koma meye yana da alaqa da prince ishaq. A haka har bacci ya dauketa........!