After three weeks
Tun ranan da rigima ta had'a Jaleelah da Raheemah Abdul bai sake kiranta ba bayan kiran da yayi mata akan jin dalilin da yasa ta zagi mishi mata. Ita kuwa Jaleelah then a schl har sun fara biyan kudin external exams lessons da zasu fara in two weeks time. Sosai ta mayar da hankalinta ga karatu unlike yadda take yi idan zasu yi end of term examinations. Kuma har lokacin ba wanda yasan ita matar aurece hatta Ni'imah da kuma Aneesah dake ta kokarin shisshige mata akan tana son uncle dinta.
Da yammacin ranan saturday suna zaune suka buga whot`whot kiran Raheemah ya shigo wayarshi, bai yi gaggawan dauka ba sai da ya tsaya kallon Jaleelah ita kuma bata boye mishi kishinta akan yin hakan ba. Ganin yadda ta kure su da idanu yasa ya kasa maganar kirki daga bisani ma yace mata zai kira ta anjima. Tab'e fuska tayi ba tace mishi komai ba suka cigaba da buga game d'in.
Washe gari wuraren karfe goma na safe ya samu daman kiranta bayan ya farka daga bacci, shima d'ari d'ari yake yi don yasan Jaleelah na juyawa taji bashi a side d'inta zata farka ta fito nemanshi. Gudun ma kar ta ganshi da wuri yasa ya fita zuwa back yard ya sami wani block ya zauna akai sannan yayi dialling number d'inta. Ita ta fara magana da tayi picking voice dinta so weak, tace "my Abdul", ya amsa mata da "my Raheemah", tace "Abdul ka tsane ni... Abdul ka tsane ni... Abdul ka tsane ni.. Me nayi maka pls?", yace "Raheemah ya za ayi na tsane ki? You are my first love and last, ya za ayi kice haka?", tace "ga matarka can masoyiyar rayuwarka"
Yace "this is something different baby, mata ta daban, ke daban"
Tace "I know mana, ba sai ka fada ba, kaga yanzu ai nasan matsayi na a wurinka", cikin yanayi na tausayi take maganan.
Shi kanshi yasan bai kyauta ba, amma he had no choice saboda shi taimakonta yayi, shiru yayi yana nazarin yadda zai wanke kanshi daga laifin da yyi, tace "Mommy nata expecting ganin iyayenka sai taji shiru, ashe da walakin goro a miya"
Ya shafa kanshi yace "ba haka bane, da aure na ko good four months ba ayi ba, we are still in the third"
Shakar majina tayi wanda ya tabbatar mishi da hawayen da take yi, tace "I've been sick, nayi tunanin ma zaka neme ni amma naji shiru tunda kayi aure yanzu ko?"
Yace "a'a, I don't know what came in to my head.. Please kiyi hakuri kinji?", bata amsa shi tace "yanzu ba labarin auren mu ko? Don sincerely speaking bana tunanin zan iya aurenka Abdul, ka yaudare ni, kuma kayiwa kanka"
Ya tari numfashinta yace "how can I ever be disloyal to you? Kin taba yarda zan yaudareki Raheemah? Baki san fa ya akayi nayi auren nan ba"
Tace "kuma bana so na sani, bani da sha'awar saninsa"
Yace "Raheemah Allah ne kawai ya kaddara zanyi aure, I was not ready for it, ba zan rantse miki akan karya ba, amma Wallahi taimakon yarinyar nan nayi, ba a son raina na aure ta ba kuma ni ba sonta nake yi ba, I just respect her for the sake of being my wife, kuma kinga hakkina ne na kare martabanta a matsayinta na wacce take karkashin iko na"
Murmushi tayi mai hade da kunar rai, tace "maza. Maza kenan, namiji kudan zuma, ga zaki ga harbi, namiji rumbun kashi rumbun karara, namiji hawainiya, namiji fa ba d'an alkawari bane, sau nawa ina jin irin haka? Na nawa kuma? Na nawa? Ai haka kuke kuma ni ba zan taba yarda ba"
Tausayi ta koma bashi, yace "wallahi Raheemah aure na kaddara ne, kuma ai da kinji ana fadi a gari cewa I'm married saboda to ba a son raina nayi ba not everybody knows my status has changed to Married, billahil Azim Raheemah taimakonta nayi za a aura mata wanda bata so naje a matsayin wanda take so saboda ina tausayawa rayuwar da zata iya tsintar kanta a gaba. She's only a secondarian, karamar yarinyace, shekarun nata nawa ne? Just 17, ni ba son ta nake yi ba, But believe me you're the one I love. Pls understand me"
Bata nuna damuwarta ba tace "lokacin shan magani na yayi. We talk someday, ka gaida Madam ko?", ko jiranshi ya bata amsa bata yi ba ta katse wayar. Mahaifiyarta dake zauna a gefenta yayinda take wayar ta kalle ta tace "yanzu sweetheart what is your move? Namiji fa ba dan goyo bane"
Tace "Mom ai ba shi bane autan maza, kawai na hakura da shi, dama Sultan ya matsa min akan shi fa lallai dagaske yake yi"
Mom tace "amma ban taba sanin ke shasha bace sai yau, yo to karamar yarinyar ce zaki bari ta ci galaba akan ki? Sa'ar Muneefah? Ai ko Muneefah nasan ba zata barta taci galaba akan ta ba bare ke, aure fa sai kin aure shi, kuma dama ki shirya sanar mishi cewa ya turo iyayenshi ayi magana matukar dagaske yake yi, daga baya ita kuma yar shilan dake gidan ta nemi hanyar fita"
Tace "ko Mom"
Girgiza mata kai tayi tace "kwarai kuwa daughter"
Murmushi tayi suka kashe sannan Mom ta fara bata magungunan da kanta.
Ajiyar zuciya yayi Sannan ya furzar da iska daga bakinshi. Hawayen dake zuba daga idanuwanta ta goge tana tsaye a jikin window da ya fita zuwa back yard tana rike da curtain tana kallonshi. Tana ganin ya mike tayi saurin shigewa bathroom. Ko nightie dinda ke jikinta bata cire ba ta sakar ma kanta shower me sanyi hawaye na cigaba da kwaranyowa daga idanuwanta. Tafi 30minutes a tsaye tana kuka sannan tayi wanka ta fito that took her almost an hour. Bata dauki lokaci me tsayi ba wurin shiryawa. Material lace ta saka tayi light make up sannan ta fita zuwa duba shi. Kamshin abinci ta shak'a yayinda tayi stepping cikin sitting room d'in. Wuri ta sama ta zauna saboda ba abinda ke mata dadi, ya kira aurensu auren kaddara, to me zata je kitchen din tayi masa? Tunanin Raheemah tayi tayi da furucin AbdulHakam akanta. Idan ya auri Raheemah ai sam bai yi laifi ba saboda ita ce budurwarshi, kuma tasan itama haka zata kalleshi da idanun da take kallon Khaleefah a matsayin namijin da take so ya kuma yaudare ta.
A gabanta ya ajiye tray din da ya dauko, cups biyu ne da plates biyu, tea da omelettes and bread. Kallon tray din tayi sannan ta dago ta kalleshi. Murmushi ta sakar mishi tace "kayi kokari"
Yace "sosai kuwa my Ameerah, bana so ki tashi kiji yunwa"
....Ameerah....
Tace "in tambaye ka?"
Yace "to journalist, mene ne?"
Tace "what's the wisdom behind calling me your Ameerah wai?"
Kallonta yayi for a moment yace "amma ai da farko sai da na fada miki, saboda ke mata ta ce"
Tace "princess fa kenan"
Yace "ofcourse"
Tace "to ai ba zaka nada mace ta zama gimbiyarka ba sai dai idan kana son ta"
Bai kawo komai a ranshi ko irin ta jishi yana wayar ba, cox he was pretty sure bata ji shi ba tunda lokacin da ya shigo karar ruwa yaji a bathroom wanda ya tabbatar mishi da ta jima da shiga wankan, yace "to waya ce miki na tsane ki"
Murmushi tayi cikin zolaya tace "I thought so", amma deep down she meant it.
Murmushi yayi yace "zan cire miki lower lip idan baki idan kika sake fadar haka, sauko kiyi breakfast", tace "okay. Dama ina so ma zan fita"
Bai ko kalleta ba yace "na hana"
Hade gira tayi tace "and why?"
Yace "yau weekend nasan maza na nan ana zaman majalisa zasu kalle ki", tace "to mene ne a ciki? Ko so na kake yi?"
Cikin fushi ya dago ya kalle ta yace "meya sa sometimes baki da kunya Jaleelah? Idan kin raina ni saboda ni mijinki ne atleast remember one thing"
Lumshe idanuwanta tayi ta bude ta katse shi, tace "it is always on the uppermost of my mind"
Yace "to it will be better".
Shi a ranshi yana nufin ta tuna abu daya cewa shi ba sa'anta bane kuma ko ba komai ita sa'ar last born dinsu ce ko don wannan ya kamata ta girmama shi, ita kuwa a side dinta taimakonta da yace yyi shi tayi tunani.
Plate din omelette and bread ya dauka da cup din tea dinsa ya fita zuwa main parlour ita kam kasa cin nata tayi, gaba daya sai taji bata da appetite.
Bin sa tayi main parlour din ta zauna daga gefenshi, tace "I'm sorry"
Bai ko kalleta ba yace "sorry for your self"
Haushi taji yadda ya bata reply din in I don't care manner, tace "I know I'm a burden in your life huh?"
Ajiye bread din da zai kai bakinsa yayi ya mayar da dubanshi gare ta, yace "how?"
Tace "na sani ne ai, I usually feel it.. Kayi hakuri, watarana if I have a way insha Allah I'll leave your life, I'll go somewhere where I won't enburden anyone. Nasan ka taimake ni kuma kaima kamar yadda ka taimake ni haka nima watarana I'll help you leave your pretty life"
Shiru yayi yana kallonta har ta gama, yace "ni na tab'a fad'a miki cewa you're a burden to my life?", girgiza kai tayi alamar a'a tace "ai ba sai ka fada ba"
Ya ja numfashi yace "to ki bar irin wannan maganar kinji? Kinga idan kika rabu dani baki san wanda zaki aura ba"
Tace "insha Allah zai zamto mai so na ne"
Cigaba da cin abincinshi yayi yace "ina kike so kije?"
Tace "gidansu Fadeelah"
Yace "yin me kuma?". Tace "aurenta ya kusa, next week ne so I won't be able to attend the events, shine nake so naje na ganta"
Yace "okay ki bari sai anjima bayan sallar la'asar"
Ta amsa masa da to sannan ta tashi ta bashi wuri.
Basu sake haduwa ba saboda da ta koma bacci tayi sai da lokacin sallar azahar ta farka, kuma ko da ta farka bata Ganshi ba har akayi la'asar. A cikin mota ta same shi data fito zata tafi, yana zaune yana ta shafa waya, daga gefe ta tsaya tace "na tafi"
Kanshi na a sunkuye yace "OK", bai sake cewa komai ba bayan haka.
Sai bayan sallar magrib sannan ta dawo gida bayan doguwar hirar da suka yi da Fadeelah, sai kuma ranan bikinta zata sake lek'awa saboda ta fara exra lessons after schl hours. Idan suka tashi 2pm sai su fara lessons d'in 3pm su tashi 5:30pm kuma soon zasu fara WAEC.
Da daddare ta dafa indomie suka ci amma kowa da plate dinsa. A hankali take cin abincin har tayi ta gama sannan ta tashi ta kai plate da cup din kitchen ta koma bedroom tayi taking shower sannan tayi shirin bacci. Kwallafawa tayi a ranta dole dole ita watarana sai ta bar rayuwar AbdulHakam, tunda ya riga ya taimaketan ai ya kamata ta karawa motarta wuta kuma yanzu, kawai tayi deciding ba zata taba hada shekara a gidanshi ba, immediately after NECO zata tafi, lokacin ta fara preparing shiga higher institution. Zata tafi ta barshi ya auri wacce ranshi yake so tunda dama suma ba son junansu suke yi ba.
Duk da haka bata taba denying dinsa ba, yadda ma take mishi biyayya ba wanda zai taba kawowa akwai wani quduri a ranta ba, har polishing takalmansa take yi saboda cigaba. Biyayyarta har yawa take yi saboda ji take yi kamar ta goye shi. Shi kuma yana so ya faranta mata ya tambayeta me take so, rasa abin zaba tayi tace kawai ya kaita Panama Castle sai kuma the next day su tafi *BilHam light* suyi hotuna ayi musu da enlargements kuma ya yardan mata.
Har suka fara rubuta WAEC bata canja qudurinta akan tafiyarta ba, duk da yadda yake petting dinta, she knew she would missed all these romantic scenes. Kuma har lokacin Raheemah bata ce wa Abdul ya turo iyayenshi ba, tana jira sai ta kimtsa tukunna yadda da tayi magana zai turo at once, don yanzu bata kallonsa a matsayin mai aure saboda karamar yarinyar da bata kai ta yake aure ba.
Wata ranan wednesday, ranan paper biyu garesu, zasu je su dawo for afternoon paper. A restroom suka je suka zauna ita da Ni'imah domin hutawa, Ni'imah tace "Jaleelah kawai mu wuce gida, yanzu 11:30am har sai yaushe ne zamu ci abinci? Ni wlhy yunwa nake ji"
Jaleelah tace "to ki zo mu je gidan mu ko indomie ce sai na dafa mana"
Zaro idanu tayi, tace "waye zai bi ki premier cresent kamar wani banza?"
Yar dariya tayi tace "ke fa mutum ce wlhy, ba nan nake nufi ba, Yarwa Close ne, ai ba nisa"
Tace "yaushe to kuka yi relocating zuwa wani Yarwa Close?"
Tace "ke dai idan zaki je to, idan kuma ba zaki je ba to"
Tsaki tayi tace "tolotolo kawai, mu tafi"
Hararta Jaleelah tayi suka fita daga rest room din daga nan suka bar haraban schl din gaba daya.
Tun daga hanya Ni'imah keta yiwa Jaleelah tambayoyi akan gidan wa zasu a Yarwa Close har sai da ta kare tace mata "gidansu Faruq"
Ni'imah tace "ko kuma gidansu Khaleefah ba"
Tace "ai yafi karfin zuwanki yarinya sai dai ko dai na su Faruq d'in"
Ni'imah tace "wai ni kam ina Khaleefah? Abu kamar anyi ruwa an d'auke?"
Jaleelah tace "to bari kiji, kar kije ki kashe min aure, ki rabani da maganar Khaleefah"
Ni'imah ta kyalkyace da dariya, tace "anyi new catch kenan"
Tace "ke fa yar iskan yarinya ce, nace miki ina da aure kina fada min wani new catch, a'a newest catch ne"
Dariya ta sake yi tace "amma ke kuwa katuwar agwagwa ce, ki rasa wanda zaki raina ma wayau sai ni"
Jaleelah tace "to muje gidan ki gani, hala gidan mijinki za mu je ke da ba katuwar agwagwa ba"
Ni'imah da ta dauki abun a wasa tace "eh muje ai za a gani, ke dai kawai kice kina son aure"
Tsaki tayi bata kuma tanka ta ba har Napep din ya isa inda ta fada mishi za su.
⚜Mijin Jaleelah⚜
32
By Linah Shams✍🏼
A main parlour ta sauke ta, ita dai idanu kawai take binta dashi don har lokacin bata yarda ba. Jaleelah ta juya ta kalleta, tace "marhaba da zuwa gidan Jaleelah Naseer matar AbdulHakam", Ni'imah ta ballaqa mata harara tace "karya dai ba kyau", tabe baki tayi tace "dalla matsa nan, ke har kin isa na miki k'arya, to zo mu je ki gane ma idanuwanki abinda zasu isheki sheda"
Binta tayi a baya suka shiga inner sitting room inda ta ganewa idanuwanta enlargements din hotunasu da su kayi da su ke makale a kowa ne side din parlourn, da mamaki Ni'imah ta kalleta, tace "Anjayjay dagaske kike yi?", tace "to ko ma dai wasa ne ai gashi kinga evidence kuma the society isn't blind, iyayena ma haka"
Samun wuri suka yi suka zauna, Ni'imah tace "girlfriend kin bani mamaki, ashe zaki iya yin aure ban sani ba"
Murmushi tayi tace "ke ai shine lokacin nan dana shiga damuwa a schl har na naida ma kowa magana, kuma ke banza ce nasan ki da kaikayin baki sai kije ki fada ma wasu ni kuma bana so kowa ya sani, Mrs Kiyawa ce kadai ta sani, sai ke"
Shrug tayi tace "amma wannan kamar uncle din nan naki me zuwa daukanki"
Tace"ke kifa daina cewa uncle dina, MIJI NA dai"
Tace "eh, amma kin san yan class din mu nawa suka fola ma guy din nan? Harda miss Aneesah fa"
Kwafa tayi tace "Allah ya basu sa'a, saura kuma dama naji labari a schl cewa inada aure"
Ni'imah tace"ke kin fa yi na iya kudinki, kije ki kawo min abinci don ni yunwa nake ji"
Da rokon Allah Ni'imah ta samu Jaleelah ta dafa mata indomie, da cewa tayi sai dai ta shiga ta dafa da kanta.
Sai da suka yi sallar azahar suka huta sannan suka fito gidan. Trekking sukayi zuwa bakin hanya don samun abun hawa da zai mayar da su schl duk da sun so su makara.
Kwanci tashi kwana nesa. A haka ne har suka kammala exams dinsu saura jiran sakamako, sai kuma Jamb da ta rubuta cikin ikon Allah ta samu fiye da marks din da ake buk'ata, sosai tayi farinciki. Tana so ta karani Economics a Ahmadu Bello University, Zaria.
Bayan ta kammala exams din WAEC da kwana tara, wanda ya zo on a Saturday, Abdul ya buk'aci data koma Kano saboda yadda Umma ke kira kullum tana tambaya yaushe zata dawo, haka ma Inteesar da yaran Aunty Safiyya. Ko da ya same ta da batun komawarta nuna masa kin amincewarta tayi, lallashin duniya yayi mata amma taki yarda, ya tambayeta "yanzu to ya kike so a yi? Zaki cigaba da zama a gida ne kullum idan na fita ki kirani kice ke tsoro kike ji?"
Tace "a'a ni gidan mu nake son komawa"
Yace "amma ba nan bane gidanki ko? Ga gidan da ya kamata ki zauna can a Kano"
Ta sake cewa "a'a ni gidan mu nake son komawa"
Yace "amma fa ke kika yiwa Umma alk'awari da kin gama exams zaki koma"
Tace "to ai saura NECO, ban riga na gama ba"
"Sai nan da two months zaku fara NECO kuma kema kin sani"
Tace "eh na sani mana amma ni gidan mu fa zan koma"
Cikin fushi yace "to ba zaki ba, Kano zaki koma" daga haka ya wuce ta ya bar bedroom din. Yana fita ta daga waya ta kira Mommy, cikin girmamawa ta gaishe ta sannan tace "Mommy da zan zo gida ne fa"
Mommy tace "lafiya dai ko"
Tace "lafiya k'alau, da ina so na dawo ne shine yace wai a'a bazan zo ba sai dai na koma Kano"
Tace "to Jaleelah me zaki zo kiyi a nan? Tunda mijinki yace ga yadda yake so ba sai kiyi masa biyayya ba, last week ba kin zo ba? Ko so kike kullum kiyi ta bin hanya?"
Tace "Mommy ba haka bane"
Mommy tace "koma dai yaya ne ne ki daure kiyiwa mijinki biyayya ki tafi can din, Allah yayi albarka"
Ta amsa mata da amin daga nan suka yi sallama.
Kifa wayar tayi akan cinyarta tana tunanin abinyi, sai ta ji kawai tana so taje taga gidan Fadeelah duk da ba abinda zata fada mata. Data san yadda ake neman sanadin da zai sa namiji ya kori mace ta tafi gidansu da yau sai ta nema a wurin AbdulHakam don kawai ta sawwak'e mishi taimakon da ba a son ranshi yake yi ba. Tubure mishi tayi akan dole dole sai taje gidan Fadeelah da daren ranan bayan ta kirata ta shaida mata zuwansu, ran Abdul yayi matukar baci amma yaga ranshi kara baci zai yi idan bai kai ta gidan Fadeelah ba saboda yadda take nema ta dinga yi masa kuka every second. Hakanan yaje ya kaita suka sha hira shi kuma yana waje yana jiranta har ta gama sannan ta fito, Fadeelah tayi mata godia sosai don da wuya su sake haduwa sai an dade don ita Jaleelah washe gari zata wuce Kano ita kuma cikin kwanaki masu zuwa zasu bar k'asar.
A daren ranan ya sata ta hada kayanta saboda yadda ta bashi haushi. Ita kuwa ko a jikinta haka nan ta hada ta koma tayi kwanciyarta ko sai da safe bata yi masa ba tana jin haushinshi, how would he be so selfish shi kullum sai dai taje gidansu amma ba zata je gidan iyayenta ba.
Washe gari da wuri suka fito gida kamar an kore su, ba irin rokon da bata yi masa ba akan ya barta taje ta yiwa Umman Fadeelah sallama amma ya hanata. Hakanan ta hakura ta shiga mota and embarked on the journey. Driving dinsa yake tamkar ba mutum a cikin motar don tunda suka shiga bai sake ko kallon side dinta ba. Ita ma haka, shiru ta masa.
Sai da suka kusa Zaria sai ga call d'in Raheemah, don ya k'ara b'ata mata rai sai da ya samu gefen hanya yayi parking sannan yayi picking. Gaisuwa irinta masoya suka yi, sannan Raheemah tace "Abdul wai kana Kano ne?"
Yace "a'a, but I'm on my way, wani abu ya faru ne?"
Tace "eh a'a, it's urgent dai amma"
Yace "to shikenan Insha Allah gani nan zuwa"
Daga haka suka yi bye. Yar murmushi ya saki sannan ya kalli Jaleelah data jinginar da kanta da backrest ta rufe idanuwanta, yace "wayarki fa?"
Banza tayi masa kamar tana bacci, ya sake cewa "wayarki fa?" Nan ma bata amsa shi ba, yace "dake fa nake yi", da weakness cikin voice dinta tace "pls let me be....!"
Bai sake ce mata ko uffan ba haka itama har suka isa Kano. Gidan iyayenshi suka wuce kai tsaye don ba abinda zai kai shi gidansu. Farincikin Umma baya boyuwa don rungumeta tayi tana ta mata sannu da zuwa, tana jin dadin treatment din. Dakin Inteesar ta wuce da kayanta ta ajiye sannan ta koma parlorn Umma. A gefenta ta zauna kusa da kafafunta ta gaishe ta with a toothy grin haka ma Umman. Sannan tace "Umma Abba fa?"
Umma tace "ai baya nan yanzu, yana Kasuwa"
Tace "okay, to Inteesar fa?"
Tace "na aike ta ne, yanzu zaki ga ma ta shigo" gaba daya ma ta manta da Abdul da suka zo tare sai da taji sallamarsa. Cikin ladabi ya gaida Umma.
Suna cikin gaisawa sai ga Inteesar ta shigo da sallama, sallamar da bata karisa ba data hango Jaleelah, wani ihu ta saki taje da gudu ta rungumeta, nan take suka bar parlourn suka koma dakinta. A kan gado suka zauna, Inteesar gaba daya ta kasa rufe bakinta saboda tsabar murna, tace "dama ina ta expecting zuwanki", tace "ai fa, ya Jamb dinki? Ke gaba daya ma wayarki bata da amfani"
Tace "battery din ne ke da matsala amma Umma tace zata siya min sabo ai"
Tace "to auta"
Zamansu suka yi a nan suka b'arke da hira kamar zubar kanya.
Abdul ji yake yi kamar ana mintsininsa a gidan duk ya kosa yaje yaji kiran me Raheemah tayi masa. Bai had'a two hours ba ya mik'e ya nufi dakin Inteesar, daga bakin k'ofa ya tsaya ya d'aga labulen ya kalli Jaleelah, yace "ke zo zan wuce", banza tayi mishi ta cigaba da surutunta, Inteesar tace "Ya Abdul na kiranki fa", d'ago kai tayi tace "aww" sannan ta tashi ta wuce suka fita tare zuwa compound, a bakin motarsa suka tsaya, yace "zan wuce", tace "Allah kiyaye hanya"
Yace "ba wani abinda kike buk'ata?"
Tace "babu"
10k ya k'irga ya mik'a mata, yace "in case idan kina son wani abu"
Girgiza masa kai tayi tace "a'a ka barshi nagode ma"
Kallon ta yayi for some seconds, yace "ai ba roko na kika yi ba, ni na ga dama na baki"
Tace "I don't need your money, kawai ka tafi Allah ya kiyaye hanya"
Kwafa yayi yace "kin ma kanki ai" Daga haka yayi shigewarsa mota mai gadi ya bude masa gate yayi tafiyarsa itama ta shige ciki wurin Inteesar, tasan dai gidansu Raheemah za shi kuma it no more bothers her to know that.
Tana dai jin zafin hakan, ji tayi kamar ta fadawa Inteesar amma sai ta basar saboda kar ta gane kishi take yi bugu da k'ari kuma ta tsani labarin yarinyar. Hakanan ta boye damuwarta suka cigaba da hira, nan ta kira Umman Fadeelah ta shaida mata tafiyarta sun tafi da sassafe ne shiyasa bata shiga tayi mata sallama ba, sannan ta kira Mommy da Mrs Kiyawa suka gaisa.
Ko da ya isa gidansu Raheemah tarba ya samu na musanman, abincin kala kala akayi domin shi da drinks. Sai da ya fara shiga ciki ya gaisa da Ummanta sannan ya dawo parlourn bak'i inda ya saba zama su yi hira.
Cikin kwalliyarta na english wears ta shigo parlourn ta zauna tana facing dinshi, tace "barka da zuwa honey"
Yace "barka dai baby"
Tace "ya hanya?"
Gyara zama yayi yace "mun baro ta... You look gorgeous"
Murmushin jin dadi tayi tace "thanks honey, it's for you"
Yace "I appreciate.. Amm, I'm on a hurry, kuma kin ce there's something urgent shine na biyo na ji kamin na wuce"
Tace "okay, dama a gida ne a kayi min magana, aka ce nace maka ka turo"
Kunnuwansa nauyi suka yi masa kamar an aza masa dutsen dala, he looked confused, yace "in turo fa kika ce?"
B'ata fuska tayi tace "eh mene? Ko ka fasa auren nawa ne kuma?"
Murmushi ya kirkiro yace "no no no no.... I'll see to that"
Tace "dama shine maganar, babban albishir kenan"
Murmushi mai fassara biyu yayi yana girgiza kai yace "yea sure sure baby". Tayin abincin tayi masa amma gaba daya ya nemi appetite dinsa ya rasa saboda badak'alar da zai fuskanta, ruwa kawai ya iya sha ya tashi yace mata zai wuce dama ya riga ya fad'a mata he was on a hurry. Har bakin motarsa tayi masa rakiya tana wani takwarkwasa don tsabar jin dadi shi kuwa gaba d'aya ya d'imauce.
Tunanin wa zai tunkara da maganar k'ara aurenshi yake yi, na farko dai ya san ko giyar wake ya sha ba zai tari mahaifinsa da maganar ba, na biyu kuma ko star yake sha ba zai je ma Umma da maganar ba bare kuma yadda take nunawa Jaleelah tsantsar so. Buga stir wheel yayi da k'arfi saboda b'acin rai. He has been yearning to get married to her amma yanzu gashi lokaci yayi kuma abun yana nema ya b'aci.
Nan take ya d'au wayarsa yayi dialing numbern Khaleel bugu d'aya biyu ya d'auka, ko gaisawa basu daman yi ba yace "baban Timah kana gida ne?"
Yace "a'a lafiya dai ko?"
Ajiyar zuciya yayi yace "lafiya ba lafiya ba, ina so zamu yi magana ne"
Yace "to yanzu dai ina Kasuwa wurin Abba ne, kana ina ne kai sai na zo na same ka? Ko zaka zo ne?"
Yace "a'a it will be safer idan kai zaka zo. Mu had'u a kusa da Lujaina Bahrain's palace, na kusa karisawa wurin"
Khaleel ya amsa masa da "to" yayi hanging up.
Sai da ya kusa 7mins da isa sannan Khaleel din ya zo, yana hango shi yayi gaggawar fitowa daga motarsa suka koma motar Khaleel d'in. Khaleel ya dube shi yace "ya akayi?"
Abdul yace "wlhy wani al'amari ne ya ta so min, ni ban san ya zan yi ba yanzu, na san ba kowa bane zai fuskance ni"
Khakeel yace "ina jinka, mene ne?"
Yace "aure nake so zan k'ara"
With mouth agape Khaleel ya kallesa, yace "aure? Aure fa kace AbdulHakam, to watanka nawa ne da yin auren?"
Yace "ka gani, abinda ba kowa zai fahimta ba kenan"
Yace "to fahimtar da ni"
Abdul yace "kaga wannan yarinyar Raheemah, ita ce wacce na fara so, almost seven years muna tare tunda tun tana JSS muke tare, har lokaci ya zo ta kammala secondary schl d'inta na nuna mata ya kamata yanzu ace munyi settling to start a family, sai tace iyayenta ba zasu bari ba sai taje tayi degree ta kammala, Cyprus, haka nan na yarda na amince idan ta kammala ta dawo sai muyi auren, but before then sai na had'u da wannan yarinyar Jaleelah, we were never for once in love and aren't, ita kaga taimakonta nayi na aure ta duk da bana tunanin sai na baka labari saboda shi labari ne mai tsayi, to make things short, tausayinta ya rufe min idanu na aureta time din gaba d'aya na mance da wata Raheemah. To daga baya muka cigaba da courting har ta dawo ta san ina da aure ta zo tayi fushi, yanzu shine ta hakura tace na turo iyayena"
Numfasawa Khaleel yayi yace "yanzu what are you up to?"
Yace "shine ai Nima ban sani ba"
Yace "amma su duka biyun kana son su?"
Yace "a'a. Ita fa Jaleelah na fada maka taimakonta nayi".
Khaleel yace "shikenan idan akayi taimako ba a so?"
Yace "bro forget, ni na fada maka Raheemah ce warce nake so"
Yace "then bai kamata ka k'ara aure ba yanzu d'an Alhaji"
Abdul yace "and why?"
Khaleel yace "saboda ba zaka iya yin adalci a tsakaninsu ba, dama dai duka kana son su ne to shine zance may be ka iya kamanta adalci a tsakaninsu, but if you still insist you can still move on and get married again"
Abdul yace "to ai shine ban san Wanda zan tunkara ba for now, nasan su Umma ba zasu tab'a approving ba, shine nake tunanin ya zanyi yanzu"
Murmushi Khaleel yayi yace "kai dai kawai kace kana neman me goya maka baya ba wai wanda zai fuskance ka ba, and I got your back"
Murmushi shima yayi yace "thanks"
Khaleel yace "abin da zai fi maka sauki yanzu shine kaje ka sami Baban Tarauni ka fad'a masa halin da ake ciki, I will talk to dad anyway, itama Umman zan yi mata maganan ko kuma na roki safiyya tayi mata, you know this women stuff sai su"
Godiya yayi masa sosai sannan suka yi sallama Abdul ya kama hanyar gidan Baban Tarauni.
⚜Mijin Jaleelah⚜
33
By Linah Shams✍🏼
Babban rashin sa'a Abdul ya tako don kuwa anyi rashin sa'a Baban Tarauni baya nan yayi tafiya, yaje Jigawa sai nan da kwana biyu zai dawo. Haka nan ya juya ya dauki hanyar Kaduna yana ta tufka da warwara a zuciyarshi har ya isa Kaduna.
Da daddare bayan ya sha black tea yayi shirin bacci ya tuna da Jaleelah, he missed her. Sai ma da ya kalli gadon yaga yayi masa mugun fad'i. Murmushi yayi ya haye gadon sannan ya daga wayarshi ya kirata, lokacin suna tsaka da hira da Inteesar a bedroom din Umma, fuska ta tab'e data ga call din sannan ta sa wayar a silent suka cigaba da hira. Gajiya yayi da dialling number dinta ya kira Inteesar da Allah ya taimake shi tana da chaji. Saboda dad'in surutu sai da call din ya kusa tsinkewa sannan tayi picking tana fad'in "Hello Ya Abdul", ya amsa mata da "na'am auta ya kike?"
Tace "lafia lau"
Ya tambayeta "ina Jaleelah? Ko tayi bacci ne?"
Tace "a'a gata nan, a bata ne?"
Yace "eh bata mana"
Ta mik'a mata tana fad'in "ga Ya Abdul", sai da tayi tsaki a k'asan mak'ogoronta ta amsa wayar tace "ina ji"
Yace "ina kika shiga ina ta kiranki ba kiyi picking ba?"
Matse lips dinta tayi tace "hira nake yi da Inteesar"
Yace "yayi miki kyau, lafiyarki k'alau dai ko?"
Tab'e fuska tayi tace "ka damu ne?"
Yace "ni dai ban san yadda aka yi irin wannan mugun rainin ya shiga tsakanin mu ba Jaleelah"
Cikin damuwa tace "to Ameer dan Allah ka damu dani ne? Baka damu dani ba to ba gashi na zo inda aka damu dani ba? Umma tana kula dani kaga ma Inteesar ita ma tana so na, whatelse?"
Yace "to... Yanzu kuma me ya kawo wannan labarin?"
Tace "a'a kawai dai ina so ne kasan akwai masu so na"
Yace "ni bana son ki kenan kike nufi?", tace "wannan kuma kai zaka fad'a ai Ameer"
Yace "to, dama na kira naji lafiyanki ne a matsayina na mijinki", dariya tayi tace "to Mijin Jaleelah, sai da safe"
Yace "to ki gaida Umma"
Kallon Inteesar da ta kafe ta idanu tayi tace "amshi wayarki", ta amsa tana fad'in "ke yayan namu ne kike ma wulak'anci?"
Jaleelah tace "eh shima haka yake min, d'azu fa tad'i zashi da ya zo ya kira ni da zai tafi"
Inteesar tace "to meya sa baki fad'a min tun d'azu ba? Ai wallahi dana had'a shi da Umma"
Tace "manta dashi yaje yayi auren, ai ita yake so"
Tace "to ke fa?"
Tace "manta shi dan Allah muyi hiranmu"
Bayan sun gama wayar da Jaleelah ya kira Raheemah suka fara hira, har da na sanin kiranta yayi saboda yadda ta kwazazzabe shi akan maganar turo iyayensa saboda har lokacin he wasn't saying anything. Yace mata "baby ba zaki gane bane yanzu, komai fa a hankali ake yi, we can't rush in to this marriage"
Tace "which rush again? Shekarun mu nawa muna tare?"
Yace "amma kin san dai ban dad'e da yin aure ba, yanzu sai na san yadda zanyi sannan zan fad'awa iyaye na, that's even if they might approve of it Raheemah"
In I don't care manner tace "then sai ka fada musu taimakonta kayi mana may be su fahimce ka"
Girgiza kai yayi yace "it doesn't seems reasonable, ki bar ni nayi abubuwa na a hankali baiwar Allah"
Tace "as you wish"
Sai to 1am sannan suka yi sallama kowa yaje ya kwanta.
Bayan kwana biyu Safiyya taje gida domin isar da sak'on da Khaleel ya aike ta duk da tasan ba amsuwa zai yi ba. Sai da tayi hiranta ta gama sannan ta kalli Jaleelah da Inteesar tace "zan yi magana da Umma Hajiyoyi, zaku iya bamu wuri?"
Jaleelah ta fara mik'ewa sannan Inteesar suka fita daga parlourn suka koma parlourn gidan.
Aunty Safiyya ta kalli Umma tace "Umma an aiko ni ne"
Umma tace "wa kenan?", tace "yaranki ne wlhy", tace "wasu yaran? Wa'innan da su ka fita ko suwa?"
Tace "a'a, Ibraheem ne da D'an Alhaji". Umma tace "wani abu ne ya faru?"
Tace "a'a, d'an Alhaji ne dai ya zo da wata gurguwar magana"
Umma tace "eh ina jinki", tace "to, wai d'an Alhaji ne yake so zai k'ara aure shine Ibraheem ya aiko ni wai inzo inyi miki magana"
Umma ta kalleta a hagungunce tace "ai shiyasa nace d'an Alhaji ya fara hauka ban sani ba, kinga gashi yanzu ya shafa ma wannan yaron, to ko kema sun shafa mikin ne?"
Dariya tayi tace "a'a wallahi Umma, nima ko kadan ban goyi bayan wannan al'amari ba, abun ma ai ba tsari, yaushe yayi auren?"
Tace "dan Allah Safiya kar ki sake tara ta da maganar nan, wannan rashin hankali ne ba komai ba. In banda sakarci me ya ja mishi wannan tunanin?"
Aunty Safiyya tace "Umma kema kya gani"
Korafi suka yi tayi akan k'arin auren da zai yi daga bisani Aunty Safiyya ta koma gidanta.
Da daddare Umma ta je ta sami Abba ta fad'a mishi sak'on Abdul, shima b'arob'aro ya nuna rashin yardansa.
AbdulHakam duk ya k'osa weekend ya zagayo yaje Kano gidan Baban Tarauni ya shaida mishi damuwarsa saboda yadda Raheemah take nuna masa naci kamar mayya.
Ita kuwa Jaleelah dashi take kwana dashi take tashi a ranta, she really missed him.
Ranan friday bai samu zuwa Kanon ba sai washe gari saboda wasu uzururruka. Gidan Baban Tarauni ya wuce kai tsaye ba tareda b'ata lokaci ba.
Baban Tarauni shine babban gidansu Abba, duk da ba uwa d'aya suka had'a ba amma suna zumunci mai k'arfi
A compound din gidan ya tarar da matansa tana ta kai komo. Da fara'arta suka gaisa sannan ta fara mishi tsiya, "kai kuwa AbdulHakam ina matar wai? Ko so kake sai dai mun je barka sannan zamu ganta"
Murmushi yayi mai bayyana hakora yace "a'a gwaggo ba haka bane, Baban na ciki ne?", tace "eh yana nan, ka shiga". D'akinsa ya nufa ya shiga da sallamarsa. Baban Tarauni dake kishigide akan pray mat ya tashi zaune yace "d'an Alhaji da kanshi ba sak'o ba", murmushi yayi ya sami wuri ya zauna yace "sannu Baba", ya amsa masa da "yawwa", sannan ya gaishe shi cikin girma da arziki. Rasa ta inda zai fara magana yayi saboda nauyin maganar, yace "Baba. Kasan shi Allah ne da kanshi ya halattawa namiji auren mace fiye da d'aya"
Baban Tarauni yace "eh wannan tabbas haka yake"
Yace "to shine baba... Dama dai, dama ina so zan k'ara aure ne"
Kallon mahaukaci yayi mishi for a while sannan yace "amma sai naga kamar kwanakin baya akayi aurenka"
Yace "eh ba a jima ba"
Baban Tarauni yace "shine zaka k'ara aure da wuri haka?"
Yace "da haka nake so saboda wasu dalilai na"
Kamar yadda ya bawa Khaleel labarin Raheemah da Jaleelah haka ma ya sake fadawa Baban Tarauni, shi sosai ma ya natsu yayi masa bayani yadda zai fuskance shi, bayan ya gama bashi labarin komai Baban Taraunin ya dube shi yace "to yanzu ya kake so ayi?"
Yace "ina so ne kayi min jagora, ka sa baki saboda nasan Umma da Abba ba zasu tab'a yarda ba"
Yace "Ashe kaima ka sani, yanzu da kaje ta tattago sabon aure, kana tunanin zaka iya adalci a tsakanin yaran mutane? Shi fa adalcin nan babu ruwanshi da wanda kake so da wanda baka so, kana ganin zaka iya adalci a tsakaninsu?"
Yace "insha Allah Baba"
Yace "to shikenan, zanyiwa Mahaifin naka magana, amma idan bai yarda ba shikenan, iyakar abinda zan iya yi maka kenan d'an Alhaji"
Yace "to shikenan Baba, nagode, ni zan wuce", ya fad'a yana saka hannunsa a aljihu, wallet dinsa ya ciro yayi masa ihsani saboda yaji dadin taimakonsa ya mik'a masa, godiya baban Tarauni yayi sannan Abdul ya tashi yayi masa sallama ya fito daga d'akin, a tsakar gida ya had'u da Gwaggo Tani yayi mata sallama ya fice daga gidan. Yanzu half his worries had subsided.
Gidansu Umma ya nufa domin zuwa duba Jaleelah, kwana biyu yayi kewarta don haka ma tunanin d'aukarta su koma gidansu yake yi saboda ma it's something usual. Da sallamarsa ya shiga parlourn gidan inda daga Umma sai Jaleelah dake zaune bisa rug tana yanka aleyeho da spring onions. Dukansu suka amsa masa sallamar nan da nan annurin dake fuskan Umma ya kau. Wuri ya sama akan sofa ya zauna, Jaleelah da kanta ke d'uke ta cigaba da abinda take yi bata ko d'ago ta kallesa ba tace "ina wuni?", ya amsa mata da "lafia qalau", daga haka bata sake ce mishi komai ba.
Gaishe da Umma yayi ta amsa mishi amma a d'aqile take amsawa. Bayan sun gama gaisawa tayi masa shiru bata sake yi mishi magana ba har sai da ya sha jinin jikinsa.
Bayan Jaleelah ta gama yanka veggies d'in ta mik'e ta wuce kitchen inda Inteesar take tana duba girki, binta yayi da idanu yana waigawa suka had'a idanu da Umma, bata ce mishi komai ba amma irin kallon data yi mishi ya ishe shi ishara. Sai ma kunyanta ya kamashi, ya fake da tambayar "ina Inteesar?"
Bata amsa mishi ba ta shi kwala mata kira sai gata ta fito daga kitchen d'in, sai da ta gaishe shi sannan tace "gani Umma", tace "ga me nemanki nan", ta fad'a tana cuno shi da baki, Inteesar tace "gani ya Abdul", da hanzari yace "a'a ba komai, dama naga ban ganki bane"
Tace "ina kitchen ne", daga haka ta wuce shi ta koma wurin Jaleelah.
A gefenta ta tsaya tana kallonta tana wanke veggies din, tace "ga fa mijinki can ya zo", shiru tayi mata, ta sake cewa "d'an Alhaji fa ya zo"
Tace "to ko d'an Hajiya ne me kike so nayi masa? Ko so kike yi naje na d'auke shi na Goya shi ko me?"
Tace "kije ki sake wanka ki yi masa kwalliya"
Banza tayi mata ta cigaba da had'a miyar har ta gaji tayi mata shiru.
The silence was eery and weird, gaba d'aya he was not comfortable don ko kallonshi Umma tak'i yi. Tashi tayi tace mishi "ka same ni a d'aki na" gabansa ne ya fad'i, yau akwai matsala kenan, he never thought har Khaleel ya samu damar yi mata maganar ko ya aika Safiyya kamar yadda yayi mishi alk'awari. Sai da ya d'auki kusan 2mins yana nazari sannan yabi footstep d'inta. A zaune a gefen gado ya same ta shi kuma sai ya zauna a kan carpet, sunkuyar da kanshi yayi ya na jira yaji me zata ce, ta fara da cewa "sai naga kamar kwanaki na kira ka da mara hankali ko?"
Shiru yayi yana jin lafazin nata wani gwandandan, tace "ashe dagasken ne kai k'atoton mara hankali ne, wai ni kuwa ma dan Allah baka shan komai d'an Alhaji" sai a sannan ya d'ago ya kalleta, yace "Umma shaye shaye fa?", tace "eh shi nake nufi", yace "wallahi bana shan komai Umma, ko sigari"
Da sauri tace "yi min shiru, da ina maka kallon mai hankali Ashe baka da shi, to yar gidan wace ce ka roro kake so ka aura?"
Kansa a sunkuye yace "Honourable Adda'u Bello", Umma tace "kai ka san shi, to bari in fada maka, wannan aure ba mai d'auruwa bane, ubanka ma yana nan yana jiranka ne dama, tunda ni ka raina ni shine kamin aike, to ai ba ni kad'ai na haife ka ba"
Kasa magana yayi kansa na masa juyi, yayi yunkurin yin magana tadakatar da shi, tace "tashi ka fita min a d'aki", sumi sumi ya tashi ya fita daga side d'in gaba d'aya ya koma d'akin Izuddeen yayi kwanciyarsa yana tunanin da wasu idanuwa zai kalli Raheemah ya fad'a mata cewa iyayenshi ba zasu yarda ya k'ara aure ba yanzu.
Sai after magrib sannan suka kammala girkin tuwon shinkafa da miyan ganye. Bayan sun gama setting suka je suka yi alwala su kayi sallah a d'akin kwanansu sannan suka koma parlourn Umma don a can suka ajiye abincinsu. Tare suka ci a plate daya ita kuma Umma nata daban, bayan sun gama suka kwashe plates d'in suka koma kitchen don yin wanke wanke, a can Inteesar ta tambayeta "wai kin kaiwa mijinki abinci?"
Jaleelah tace "for God's own sake ki kyaleni mana Inteesar, da me kike so naji? Miji miji miji!!! Haba". Inteesar ta ja bakinta tace "to, Allah baki hak'uri, amma dai kema kin san ya kamata"
Tace "to a ina na ganshi? Ko gidan bakonshi ne? Da nice nake kai mishi abincin? Ka ji wani kinibibi"
Tace "to zan had'a ki da Umma ince kin ki kai ma d'an Alhajinta abinci"
Tace "je ki fad'a", da dariyarta ta fita ta barta a kitchen d'in tana wanke wanke.
Bayan ta kammala ta fito lokacin an fara kiran sallar isha, nan suka yi sallah sannan suka koma suka zazzauna ko wacce sai shafa wayarta take yi.
Ko da Abdul ya had'u da Abba bai ce masa komai ba, faran faran su ka gaisa. Abban jira yake yi sai shi da kanshi ya tunkare shi da maganar sannan zai nuna mishi rashin amincewarsa. Hira suka yi saboda ya kasa shiga d'akin Umma sakamakon yadda take daure mishi fuska. Sai around 9:30pm sannan ya shiga part d'insu. D'akin Inteesar ya wuce kai tsaye yaga ba kowa a ciki sai ya wuce parlourn Umma. Can ya same su ko wacce nata shafa wayarta ba k'akk'autawa, daga ciki ya shiga ya kalli Jaleelah, yace "ke ta so mu wuce"
Banza tayi masa ya sake nanata kanshi, ta waigo ta kalle shi da gefen ido tace "ka tafi kawai"
Duk a kunnen Umma suke maganar, yace "ba zaki ta so bane ina magana kina fad'a min in tafi kawai"
Umma ta fito ta harareshi har sai da gabanshi ya fad'i, tace "ba inda zata"
Wani dad'i Jaleelah taji a ranta, Umma ta k'ara da fadin "babu inda zata tunda a nan ta zabi zama, ka wuce kayi tafiyarka", ba yadda ya iya hakanan yayi musu sallama ya tafi yana jin zafin yadda Umma tayi mishi, and sincerely speaking yana matukar kewar matarshi gashi ta hana ta bishi. Duk da itama tana kewarshi amma bata tunanin yadda yake missing dinta ita tana missing d'inshi, tana so ta bishi amma ta fi so for now ya gane wane ne mai taimakon wani a cikinsu, shi da ya taimake ta ya aureta ko it a da take taimakonshi ta fannoni da dama and being a loyal wife, a iya saninta she had never failed him.
⚜Mijin Jaleelah⚜
34
By Linah Shams✍🏼
11:15pm
Rike kugunsa yayi yanata faman safa da marwa shi kadai a cikin bedroom din. So violently ya dauki wayarsa ya k'ara dialling number wayarta, har ya kariki ringing bata yi picking ba, "this is the fifth time I'm calling", ya fad'a a zafafe sannan ya sake dialling, dariyarta tayi mai isanta sannan tayi picking tayi muryar bacci, tace "kai kuwa dan Allah ka bar ni nayi bacci mana, haba mana, gaba daya ka hanani sukuni", bata jira yayi magana ba tayi gaggawar disconnecting. Mamaki ta bashi aynun, don ko kadan bai ji haushi ba sai mamakin ta ya sha, yasan ba Wanda ya ja mishi sai Umma, da yanzu suna tare and cuddled up.
Tana yanke call din ta ja duvet ta rufe jikinta, rufe idanunta tayi tana imaging dinta a side dinsa right away, she really mished him. Da tunaninsa tayi bacci.
Washe gari da safe bayan ya je ya gaida su Umman bai ko nemi Jaleelah ba ya bar gidan ya fita yawonsa kar zafin yayi masa. Sai after 11am ya dawo gidan saboda yana so bayan sallar azahar ya tafi.
Tsit gidan yayi masa kamar ba kowa. D'akin Inteessar ya fara zuwa first yaga ba kowa sannan ya zarce d'akin Umma, nan ma ba kowa, kitchen ya lek'a ya ganta a tsaye tana goge goge. Tana daga kai suka had'a ta sunkuyar da kanta, murya kasa kasa ta gaishe shi ya amsa mata, sannan ya tambayeta "ina Umma?", tace "bata nan", ya sake tambayarta "ina taje?", tace "na manta su nan garin"
Ya tambaye ta "yaushe zata dawo?"
"Da yamma"
"To Inteesar fa?"
"Tare suka tafi"
Murmushi yayi yace "to ke meya sa baki bisu ba?"
Tace "bana jin zuwa"
Yace "yayi kyau, kin kusa gamawa ne?"
Tace "eh, mene ne?"
Bud'a hannayenshi yayi yace "ah ba komai, gida zamu tafi, kiyi sauri"
Tab'e fuska tayi ta kalle shi, tace "akan wani dalili? Ni ba inda zani ina nan, kawai idan zaka tafi ka tafi, besides, ba yau zaka koma Kd ba?"
Zare mata idanu yayi yace "ina ruwanki? Idan na ga dama yanzu zaki had'a kayanki mu koma can tare"
Tace "to ni me zan maka idan na bika?"
Karisawa yayi cikin kitchen ya tsaya a kusa da ita, yace "Umma ce ta auro ki ko ni?"
Turo mishi baki tayi tace "to ni me zan yi maka?"
D'aga mata gira yayi yana jinjina kansa, ya rik'o hannayenta duka biyun da k'arfi, yace "I came all the way for you but see how you're treating me a trash!", had'e giran sama dana k'asa tayi tace "wlhy ba don ni ka zo ba, ka dai san wacce ka zo dominta, pls... Ka rike min hannu da zafi", yace "kina jin zafi ne?"
Naranara tayi da idanu tace "wlhy akwai zafi, pls mana"
Yace "this is just nothing compare to the pain I feel"
Fizge hannunta tayi ka karfi ta raba ta side d'insa zata wuce ya rik'e ta, kamar zata yi kuka tace "dan Allah ka bari bana son irin wannan wasan"
Jawota baya yayi ya yi hugging dinta, a saitin kunneta yace "you are missing me right?"
Murmushi tayi, tasan she really does, tace "why should I?", yace "saboda ni mijinki ne". Jan numfashi tayi ta fara kokarin kwace jikinta amma ya k'ara matse ta kamar za a kwace ta, yace "wai me ke damunki Jaleelah? Don't you know that I'm your husband?"
Tace "aiki zanje nayi"
Patting din bayanta ya fara yi, yace "ke baki san aikin miji yafi lada ba?"
B'ata rai tayi tace "time is going fi sabilillahi ka wuce ta tafi inda zaka, nace maka ina da abubuwan yi"
Bai ji haushi ta ya tallafo fuskarta su kayi four eyes, da sauri ta kawar da idanunta, yace "I can see you miss me too", cike da tsiwa tace "I don't"
Yace "zanyi maganin rashin kunyanki yau kuwa"
Fincikar hannunta yayi tana biye dashi suka wuce d'akin Inteesar, a bakin kofa ya tsaya ya tunkud'a ta ciki, cikin fad'a yace "d'auko hijab d'inki"
Kuka ta tsaya zata fara ya daga mata tsawa ai ba shiri ta ja hijab dinta yana tafe tana biye dashi, bai ko sake juyawa ya kalleta ba ya shige motarsa hakanan ta bud'e gidan baya zata shiga ya waiga ya kalleta rai a b'ace, yace "who's your driver?"
Hakanan ta koma ta shiga front seat ya tada motar, suna zuwa kusa da gateman din ya tsaya yace mishi "malam dan Allah ka kula da gidan, yanzu zamu dawo"
Yace "to yallabai, a dawo lafiya"
Haushinsa gaba d'aya ya mamaye mata zuciya. Dukansu har suka isa gidan fuskarsu a murtuk'e kamar abokan gaba.
1:07pm
A gaban wardrobe ta tsaya tana ta kokarin zipping riganta. Ganin ta kasa ne ya sa ya tashi yaje ya fara zipping mata har lokacin bata bar kuka ba. A hankali ya shafi ruwan daya diga daga gashi kanta ya sauka a kafadarta, yace "kukan na mene ne?"
Banza tayi mishi a ranta kuwa tace "mugu".
Juyo da ita yayi ya kare mata kallo kanta a sunkuye, yace "I'm sorry.. I didn't mean to be cruel, nasan idan ba haka nayi miki ba you won't let me, kiyi hakuri ki bar kuka haka"
Da kanshi ya share mata hawayen sannan ya d'auko mata hijab da d'an kwalinta ya bata yace "kiyi sauri kar Umma ta dawo, kar ta b'ata min rai".
Hand to hand suka isa motar ya bude mata ta shiga sannan yaje ya bude gate ya fita ya dawo ya rufe suka wuce gidansu Umma. Allah ya taimake shi bata dawo ba.
Direct d'akinsu ta wuce taje ta kwanta, a gefenta ya zauna yana kalle mata fuska ta juya mishi baya ta rufe idanunta. Bata san sanda bacci ya kwashe ta ba. Muryar Inteesar ta jiyo tana fad'in "to hamshak'iya mandiya, yau duniyar dadi take miki", a hankali ta bude idanunta and squinted, yar tsaki taja tareda yin mika hade da kalmar shahada, tace "yaushe kuka dawo?"
Tace "dawowar kenan, me kika dafa?"
Lumshe idanu tayi ta gyara kwanciyarta, tace "Umma tace iya abinda zan ci zan dafa"
Kwafa Inteesar tayi tace "to ai sai ki tashi na baki labari da zafi zafinshi kamin ya huce"
Da sauri ta tashi ta zauna, tace "meya faru?"
Kallonta tayi tace "kin ma yi sallah?"
D'aga kai tayi taga it was past 3:20pm ai da sauri ta sauka daga gadon ta shige ban d'aki, bata d'auki good five minutes ba ta fito tayi haraman yin sallah. Ko da ta idar bata tashi akan pray mat din ba har sai da ta gabatar da sallar la'asar bayan tayi evening azkar dinta.
Duk da labarin da aka ce za a bata was uppermost in her mind, d'akin Umma ta je don yi mata sannu da dawowa ta tarar da ita tana sallah. Wuri ta sama tayi zamanta har sai da ta idar da duk abunda take yi, tace "Jaleelah", tace "na'am Umma, sannu da dawowa"
Tace "yauwa ya gidan?", tace "lafiya k'alau Umma", tace "kin ci abinci kuwa?"
Tace "eh naci indomie"
Tace "to madalla". Daga nan ta tashi ta wuce wurin Inteesar dake backyard tana wanke hijjabanta. A kan dutse ta zauna tace "Inteesar gani"
Inteesar tace "yauwa, dama yanzu nake cewa a raina kin ki zuwa ki sha labari"
Tace "ai gani na zo"
Tace "to, kunninki nawa?"
Murmushi tayi tace "kunni na biyu", tace "to k'ara d'aya ki sha labari"
Tace "na k'ara"
Sai da tayi gyaran murya tace "wato ina fad'a miki bayan munje gidan k'anuwar Umma sai muka je gidan Gwaggo Habi, ai kin san ta ma k'anuwar Abba"
Jaleelah tace "eh na san ta mana, ba maman Marfu'ah ba?". Tace "eh ita, ai kuwa ina fad'a miki dai, da muka je take tambayar Umma wai dama d'an Alhaji zai k'ara aure ne? Umma dai tace mata ita ma haka taji amma bata san ko ya tabbata gaskiya ba"
Wani irin muguwar faduwa gabanta yayi daya hanata boye damuwarta, tace "aure fa kika ce zai k'ara"
Tace "eh wlhy, nima haka naji shine duk na k'osa na dawo na fad'a miki"
Takaici yasa hawaye suka taru mata a ido, tasan baya son ta amma how won't he atleast give some time?. Idanuwanta rufewa suka yi ta tashi ta bar wurin tana tafiya Inteesar na kiranta amma ko waige.
Bedroom d'insu ta shige harda locking ta sha kukanta ma'ishi har sai da tayi bacci a haka. Sai magrib da Inteesar ta zo tana knocking sannan ta farka da matsanancin ciwon kai. Da k'yar ta iya tashi ta bud'e kofar sannan ta koma ta kwanta. Inteesar tace "lafiya dai?"
Girgiza mata kai tayi alamar eh ta cigaba da kwanciyarta.
Inteesar taje tayi alwala tayi sallarta amma Jaleelah na kwance har akayi isha, idanuwanta har nauyi suke mata. Bayan Inteesar ta idar da sallolinta ta tashi ta fita zuwa d'akin Umma.
Daga ciwon kai zazzabi kuma ya rufeta. Sai gurmususu take tayi a d'aki ita d'aya tana ta jiran shigowar Inteesar amma shiru. Wani irin weakness ya sauka mata da har bata so tayi motsi mai k'arfi. Yunkurin aman da ya taso mata ya zo mata da k'arfi, da gudu ta tashi ta shiga bathroom ta fara kwarara shi sai ga Inteesar ta zo kiranta ta ci abinci. Da sauri ta karisa tana mata sannu sannan ta juya taje ta kira Umma. Da fad'in subhanallahi Umma ta k'arisa ta rirrik'eta tana mata sannu. Da kanta ta d'iba ruwa ta zuba mata a baki tana fad'in "kuskure bakin", ta kuskure ta zubar, Umma tace "ya gama fita?", ta girgiza mata kai alamar eh hawaye ta kwarara daga idanuwanta, dama it is in her nature to cry duk lokacinda bata da lafiya da raki. Umma ta rik'eta ta wuce da ita bedroom dinta ta kwantar ta ita akan gado sai rawar sanyi take yi, bargo ta ja ta rufeta dashi tana ta mata sannu. Ciwon karuwa yake yi da duk wani fitan numfashinta, duk yadda ta so taga ta b'oye kukanta kasawa tayi, tun tana yi a hankali har sai da sautin kukanta ya fara fita a hankali tana fad'in Mommy Mommy!. Umma ta matsa kusa da ita ta d'an ka bargon, tace "jikin har yanzu Jaleelah?", nan ma girgiza mata kai tayi, Umma ta zauna sai lallashinta take yi ta daura kanta bisa cinyarta, dama ita the more ana lallashinta the more she break into tears, abu fa sai cigaba yake yi ta dafe kanta tana ta fad'in Umma kaina, zan mutu.
Inteesar kasa sukuni tayi taje ta je ta kirawo mata Abba. Ai nan da nan yace su tashi a wuce asibiti bai kamata su zauna a gida ba haka. Hakanan suka shirya suka tafi dukansu, Abba kadai aka bari a gidan saboda Izuddeen ya kaisu.
Bayan sun sami ganin likita yayi mata 'yan gwaje gwaje aka yi admitting dinta, amma kamin nan sai da ya so ganin mijinta Umma tayi representing dinsa suka gana da likitan suka yi wasu maganganu masu muhimmanci. Ranan Inteesar ta kwana da ita a asibitin ita kuma Umma ta koma gida.
Shi kuwa AbdulHakam tun da ya isa Kd yake ta dialling numbern Jaleelah amma bata picking. Lokacin da yaje yi musu sallama Umma tace mishi tana bacci kuma bai isa ya tashe ta ba. Har rok'onta yayi amma tace ba zai ganta ba, yadda tayi fushi dashi bashi da niyyar zuwa Kano next weekend saboda irin abubuwan da take mishi, har ji yayi dama ya sani bai kai ta can ba ya gayyaci Inteesar ta koma gidansu ta dinga taya ta kwana ko ya d'auko Marfu'ah ko wata a dangi. Umma har mantawa tayi dashi bare ta kira ta fad'a mishi halin da matarsa take ciki.
Kwana uku suka yi a asibitin kullum Umma tana can tare da su. Inteesar kuma ke kwana da su, 'yan dubiya kullum suna hanya har akayi sallama. Tun AbdulHakam na kiran wayar har ya gaji ya daina, itama Inteesar wayarta a kashe, kuma yasan idan ya kira Umma ba zai sha da dadi ba. Hakanan yayi deciding ya kira yayarsa Safiyya taje ta rokan mishi Umma ta daina fushi dashi, in dai sake auren da zai yi ne bata so to ya fasa. Nan ne take shaida mishi rashin lafiyar Jaleelah gashi har an sallame ta daga asibiti yau kwana biyu. Bai yi niyyar sake zuwa Kano da next weekend ba amma ya zama mishi dole, friday din ma abinda yasa ba zai je ba ana auren Sha'aban kuma sune manya abokai.
Ranan saturday ma hidindimu suka yi masa yawa har yamma bai sami damar tafiya ba sai da suka gama abubuwan da zasu yi sannan ya d'auki hanya.
Ita kuwa Jaleelah kamar jinjira haka ta koma don motsi d'aya sai tace Umma ko da kuwa babu abinda take so, ita kuwa Umma tayi ta biye mata, Inteesar ko da yaushe tana side d'inta, abokiyar hira ba lafiya.
Ranan by 5pm Allah yayiwa Baban Tarauni isa gidansu AbdulHakam domin fuskantar iyayensa da maganar da yaje mishi da ita, kuma yana da yaqinin dole sai sun yarda anyi yadda yake so saboda yadda Abba ke yi masa biyayya a matsayinsa na makwafin mahaifinsu.
Sai da ya kira Abban ya shaida mishi zuwansa saboda haka ba zai fita zuwa wurin business dinsa ba, sannan ya shaida masa da shi da Zainabu yake so ya gani tafiyar ba tashi bace shi d'aya.
A parlourn Abba suka had'u su ukun; Baban Tarauni, Abba da Umma. Gaisuwa suka yi sannan suka yi hiran yaushe gamo, ita Umma duk ta k'osa yayi ya sallameta ta tafi wurin d'iyarta mara lafiya tasan tana can tana kiran sunanta, ko Mommy Umma ta hana a kira a fad'a mata a cewarta sh'es also her mother not her inlaw.
Baban Tarauni ya fara magana "tafiya nayi lahadi mik'ak'k'iya tun daga gidana zuwa gidanku saboda in isar muku da muhimmin sak'o", dukansu suka kasa kunnuwa suna jinsa, ya cigaba "wannan sak'o kuwa shine d'ana na wurinka, d'an Alhaji, AudulHakamu yana so ya k'ara aure, da na so na kiraku ku zo ne sai ayi maganar, amma naga kamar idan na zo da kaina zaku fi d'aukan sakon da muhimmanci"
Wani abu Umma taji ya tsaya mata a wuya, shi kuwa Abba kallonsa yake yi ko kiftawa babu, Baban Tarauni yace "baku ce komai ba?"
Umma zata yi magana Abba ya dakatar da ita, yace "shi AbdulHakam din ne yace yana son ya kara aure?"
Baba Tarauni yace "ina ce abinda kuka ji na fada kenan"
Umma tace "munafiki ai shiyasa yaki zuwa hutun karshen mako"
Abba na d'aga wayarsa ya nemi numbansa ya kira, ya dauka ya fara yan gaishe gaishe Abba ya katse shi, "kana ina?", yace "naje gaishe da Hajiyarsu Munawwar ne", Abba yace "na baka minti ashirin ka shigo gida", ya yanke wayar bai jira ta cewarsa ba.
[4/1, 10:06 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
35
By Linah Shams✍🏼
A gefen baban Tarauni ya zauna, sai da d'akin yayi tsit na kusan 20secs sannan Abba yace "kace kana son k'ara aure ko?"
Kasa magana yayi, Abba ya sake cewa "kayi shiru". Shiru ya sake yi bai ce komai ba, cikin fad'a Umma tace "ba da kai ake magana ba?"
Cikin in'ina yace "eh eh"
Abba yace "ka bani kwararan dalilai guda uku da kake so ka k'ara aure, idan kuma baka da su to baka da dalili", Baban Tarauni yayi saurin taran numfashinshi yace "saboda Allah ne ya halasta mishi, ko zaka haramta abinda Allah ya halasta ne?"
Girgiza masa kai yayi yace "Yaya Bak'o ai da ka barshi yayi magana, don wannan rashin hankali ne tsagwaranta"
Yace "to, a matsayina na wanda ya isa ya fad'a aji na goya masa baya ya k'ara wannan auren, aka ma yi auren mace biyu a rana d'aya bare bayan wata sama da biyar? To ka fad'a musu da kanka wannan mata taka taimakonta kayi"
Umma tace "ban gane ba"
Abba yace "ai dama ba abinda ba zai ce ba, dole aka mishi ko me?"
Baban Tarauni yace "to ita dai wannan yarinya rufa mata asiri yayi ya aureta, idan kuma kun k'aryata ni ku kirata ku tambaye ta, wannan yarinya kuma da yake so ya aura ita ce wacce suka jima suna son junansu"
Gaba d'aya Abba ya karaya da al'amarin sa, yace "yanzu me kake so ayi?"
Yace "so nake ku yarje masa ya k'ara aure"
Abba yace "to yaje yayi, Allah ya bada sa'a, shikenan?"
Yace "tabbas, ita uwar tashi fa?"
Umma tace "ai d'a naku ne, ni bani da ta cewa kuma", ko minti biyu bata k'ara ba ta tashi ta fita ta barsu saboda duba Jaleelah. Abinda take tunani shi taje ta tarar, Jaleelahn nata kuka tana kiran sunanta, cike da damuwa ta karisa ta zauna a gefen gadon ta janyota jikinta tana share mata hawaye, tace "jikin har yanzu?", girgiza kai tayi hawaye na sake ambalowa daga idanuwanta, Umma tace "to me kike so? Gashi kinki cin abincin Jaleelah", tace "fresh cow milk nake so", Umma ta dubi Inteesar dake gefe tayi tsumi tace "je ki kira min Izz", a hanyar fita d'akin suka ci karo da Abdul ya matsa mata ta fita sannan suka gaisa tayi wucewarta, da fargaba ya shiga ciki da sallama ya zauna a edge din gadon. Dukansu babu wacce ta kalle shi bare tayi mishi magana, a hankali yace "amm Jaleelah ya jikin?", bai zama lallai yaji ba don motsi kawai tayi da bakinta. Shiru ya biyo baya sai ga Inteesar da Izz sun shigo, sai da ya gaishe da Abdul sannan yace "Umma gani, wannan yarinyar tace kina kira na"
Tace "eh, dama kasan Jaleelah bata iya cin abinci sosai shine tace fresh nono take so nace to ka zo ka siyo mata"
Cike da tausayi ya kalli Jaleelah dake kwance kan cinyar Umma yace "sannu sisto"
Gyd'a mishi kai kawai tayi, Umma tace "bud'e drawer'n can ka d'auko min purse d'ina"
Abdul ya tari numfashinta "Umma to bari na siyo mata mana"
Galla masa harara tayi Izz ya mik'a mata purse d'in ta zari dubu d'aya ta bashi, tace "sai ka siyo mata da fruits, naga tana ci, ka tabbata ka samo da kankana"
Amsa yayi yace mata "to" ya fice itama Inteesar ta fita, Abdul ya dubi Umma yace "Umma", a zafafe ta kalle shi tace "lafia?", yace "dan Allah kiyi hakuri, idan baki son auren nan wallahi zan fasa", muguwar fadi gaban Jaleelah yayi, cikin fad'a Umma tace "rufa min baki, idan ka sake min magana akan wani batu game da aurenka sai naci maka mutunci wlhy, tukunna ma, me kake min a d'aki?"
Yace "na zo gaishe ki ne sai na duba ta"
Tace "ita wa? Ca nake ka gaishen nin kuma ka ganta, to tashi ka fita, daga yau idan kaga dama kar ka sake zuwa, ba da gaisuwarka nake rayuwa ba, ita kuma dubiyarka ba zai sai ta warke ba, hala yau ne kasan bata da lafiya".
Idanuwansa suka kad'a suka yi ja sosai, yace "Umma don Allah kiyi hakuri"
Cikin tsawa tace "tashi ka fitar min daga d'aki"
Kamar zai yi kuka hakanan ya fita. Amma that didn't save him, da ya shiga motarsa saida yayi kuka sannan ya ja motar ya bar gidan, yana driving idanuwansa na d'igar da kwalla har ya isa gidansu na Kano. Kasa fita yayi daga motar bayan yayi parking sai da ya sha kukansa.
Bayan fitarsa Jaleelah ta d'an d'ago kanta ta kalli Umma sannan ta sake mayar dashi cinyarta, tace "Umma meya sa kika kore shi?", Umma tace "dad'i miji ko?"
Kunya Jaleelah taji tace "a'a Umma, ki daina fushi da shi mana, ki barshi ya k'ara aurenshi ai ita yake so"
Umma tace "wani irin zancen banza ne haka? Abinda kema ya saki ki fada kenan? Haka yake cewa yayan ubanshi da ya gayyato zuwa nema mishi auren"
Tace "ai dagaske ne, ni taimako na yayi, ita kuma.... Ita yana son ta ne"
Sababbin hawaye ne suka fara zarya daga idanuwanta har sai da tausayinta ya cika Umma, tace "wannan wane irin taimako ne da ko da yaushe yake ikirarin yayi?"
Bata b'oye mata komai ba, tun daga ranan da suka had'u da yadda ta d'auke shi abokin shawara da kuma labarin da yake bata akan Raheemah, da labarin Khaleefah da yadda suka rabu, da yadda iyayenta suka yi treating dinta da maganar auren da za ayi mata da kuma aurenta da Mijin da ya bayyana mata shine bata b'oye mata ba.
Numfasawa Umma tayi tace "amma ai auren taimako ba hauka bane, ai ba dole aka yi masa ba", baki Jaleelah tayi ta bata saboda yadda Umman ta d'au zafi.
Washe gari da safe around 8am bayan tayi breakfast da fruits as usual kuma tayi wanka ta shirya cikin material riga da skirt, ko body lotion ta kasa shafawa ta hawaye gado saboda jikin ta ba k'arfi amma taji sauki sosai.
Da sallamarsa ya shiga parlourn Umma, yaci sa'a ta amsa mishi. Kusa da ita ya durqusa har k'asa ya gaishe ta, rai dai ba a sake ba ta amsa mishi ba sannan ya mike ya nufi hanyar bedroom dinta tayi gaggawar dakatar dashi, tace "ina zuwa kuma malam?"
Shafa kansa yayi yace "Umma.. Zan duba ta ne"
Tace "kasan yarinya ta bata da lafiya, ba zaka shiga ka barbad'awa rauninta land'an ba", yace "Umma dubata kawai zan yi"
Kawar da kanta tayi tana fad'in "kuma kayi sauri"
Da sauri ya wuce ya shige bedroom d'in, sai da ya tsaya daga k'ofa ya k'are mata kallo, ta rame sosai kuma tayi fari, duk kasusuwa sun fito mata a k'irji amma ta k'ara kyau da fresh, a hankali ya taka zuwa gaban gadon yayi kneeling ta side din da take, runtse idanuwanta tayi ya rik'o hannun hannunta yana caressing, softly ya kira sunanta "Ameerah", ita ma tace "Ameer", rungumeta yayi yana jin zafin rabuwa da ita, he would have been by her side. Ita kam hawaye ta fara yi mara dalili, a hankali ya dinga share mata hawayen, shima ji yake tamkar ya taya ta, yace "kin ji sauk'i?"
Ta girgiza masa kai alamar eh sannan tace "Ameer kana cin abinci?"
Murmushi yayi yana shafa cheek dinta yace "eh"
Tace "are you.. I mean are you okay?"
Yace "no"
Da damuwa a voice din ta tace "but why?"
Yace "I'm missing you.. So much", yayi ajiyar zuciya "everyday I wish I can come back from work and see you. I'm missing your precious presence wife"
Murmushi tayi tace "what if I'm dead?"
Da Sauri yasa palm dinsa ya rufe mata baki, yace "ki daina fad'in haka, do you want to break my heart? Idan kika mutu ya kike so nayi?"
Tace "ba komai, ba sai ka k'ara aure ba". Wani iri yaji yace "forget that wife, wani irin ciwo aka ce miki kina fama da shi a hospital din?"
Tace "da fever dai, amma ka tambayi Umma"
Twitching left eyebrow dinsa yayi yace "ai Umma ta daina so na, ke take so"
Yar karamar dariya tayi tace "not all dear, she loves you"
Dai dai nan Umma ta shigo d'akin, bata ko kalle shi da kyau ba tace "tashi ka zo ka wuce, ai kasan bata da lafiya"
Yace "amma Umma..", kamin ya karisa maganarsa ta katse shi, "nace dai ka zo ka fita", jiki ba kwari ya tashi ya fita yana tausawa matarshi.
Daga nan yana fita ya kira Mustapha ya sanar masa da zuwanshi.
Bayan ya isa aka yi masa masauki a parlourn baki harda breakfast, suka gaisa da Mustaphan sannan yace "ina Ilham dear fa?"
Yace "kana so ka gayyato ta ta hana mu sukuni kenan"
Yace "ta taya mu hira dai"
Yace "to sai dai idan a baka ita ka kaita wurin Jaleelah"
Murmushin second daya yayi yace "tana can gida ma bata jin dad'i"
Mustapha yace "aa Ya Subhanallahi! Meke damunta?"
Yace "ni dai tace min da fever ita ma she don't know what is actually wrong with her"
Yace "I don't get you, ba taje asibiti bane?"
Yace "taje mana", yace "to kuma tace bata San me ke damunta ba", Abdul yace "eh Umma ce kawai ta sani, kuma yanzu muna takun sak'a ne shiyasa ma ni ban tambayeta ba"
Yace "me kayi mata?"
Kwafa yayi yace "wlhy aure zan k'ara duk shi ya kawo haka, kullum sai ta danganta ni da hauka. Yanzu fad'a ke had'a ni da ita ya kuma rabani da ita"
Mustapha yayi tsaki, yace "ai gara da ta alak'anta ka da haukan, wace ce zaka aura?"
Yace "wace kuwa idan ba Raheemah ba", jinjina kai Mustapha yayi yace "Abdul kaji wani abun amai ko? Dama har yanzu kuna tare?"
Yace "eh"
Mustapha yace "Allah ya baka sa'a, shine kawai abin cewa, amma kwananka nawa da aure?"
Yace "guy it doesn't matter, yarinyar nan fa ba Auren soyayya muka yi ba taimakonta fa nayi. Ga wacce nake muradi nan"
Kallonsa yayi cike da mamaki, yace "dama dai ba da zuciya d'aya ka taimake ta ba, if not miye na fad'a min bayan na sani? Kuma idan ba fad'a kayi ba waya san abinda ya faru? Ko bata maka biyayya ne"
Murmushi yayi yace "don biyayya fa akwai biyayya, amma ga wacce muka jima muna son junan mu ai", yace "to mene ne Abun yi?", yace "kasan Umma tana matuk'ar ganin mutuncinka, so nake kaje ka bata hak'uri daga nan ka jiyo min abinda ke damun yarinyar nan, saboda her phone is always off"
Yace "to shikenan, amma ita yarinyar da baka so ne kake so a tambayo maka lalurarta?"
Yace "eh cox no matter what she's my wife, tana da haqqi a kaina"
Tab'e baki yayi yace "a dai juri zuwa rafi.."
Hira suka yi har almost 11am sannan ya fita suka gaisa da Afaf matar Mustapha sannan ya wuce. Fruits ya tsaya ya siya tuli a hanya da fresh milk. Gidansu Umma ya koma don yi musu sallama, saboda zamansa a Kano bashi da amfani as long as ba zai ko zauna a gefen matarshi ba bare ya kula da ita.
Bayan ya bama Umma fruits din yace mata ya son ganin Jaleelah, tace masa tana bacci kuma bai isa ya tashe ta ba sai dai ya tafi ko ya jira har sai ta tashi. Dole yana so ya koma Kd da wuri saboda uzururrukansa da yake so ya gabatar, hakanan ya hakura da ganinta yayi musu sallama ya tafi.
Da yamma sai ga Mustapha ya zo, lokacin Jaleelah da Inteesar na bedroom din Umma suna hira ita kuma Umman tana parlournta tana zaune ita d'aya. Fara'a ta fara yi data ganshi har ya zauna suka gaisa. Sai da suka jima kad'an suna hira sannan yace "ya jikin Jaleelah?"
Umma tace "ahh da sauk'i alhamdulillah"
Yace "to Allah ya k'ara sauqi", ta amsa mishi da "amin"
Yace "wai ciwon me take yi ne?", murmushi Umma tayi tace "zazzabi ne kawai sai ciwon kai", yace "to... Allah ya k'ara afuwa"
Tace "amin"
Shafa Kansa yayi yace "amm Umma", tace "shikenan kuma wannan shafe shafen ya kama Ku", yace "ba haka bane, dama na zo bada hakuri ne"
Umma tace "me kayi Mustapha?"
Yace "a'a na wurin Abdul ne"
Tsaki tayi tace "wannan yaron daga gani ya fara hauka"
Mustapha yace "Umma a dai yi masa hakuri"
Tace "to ai ni bance komai, aure ne yace yake so ya k'ara nace yaje yayi, a kaina matar zata zauna? Ita wannan tunda yace taimakonta yayi sai ya sakar min wlhy sai na sama mata mijin da yafi shi, wannan ma shine sulhu"
Yace "a'a Umma hakurin dai shi yafi"
Tace "ai tunda zai auri wacce yake so, to sai ya sake ta ita, ba zan yarda yaje ya dunga k'untata mata ba tunda banga alamar zai iya adalci ba, kullum sai yace taimakonta yayi, taimako hauka ne?"
Yace "nima Umma sai da nayi masa maganar haka"
Umma tace "to ai shikenan, ya zo ya bata takardanta, tana gama idda ni nayi mishi alkwari sai na aura mata wanda ya fishi komai"
Hak'uri yayi ta bata amma sam tak'i yarda, hakanan ya tashi ya lek'a bedroom d'in ya gaida Jaleelah da jiki sannan yayi wa Umma sallama ya tafi.
••°••
Hawaye ne yayi ta ambalowa daga idanuwanta Inteesar na aikin lallashinta, saboda duk hiran da Umma da Mustapha suka yi duk a cikin kunnuwansu suka yi, har sai da Umma ta lek'a ta tambaye su lafiya, Inteesar bata b'oye mata dalili ba. Umma ta zauna da kanta ta dunga rarrashin ta har sai da ta hakura, ta dunga bata dadad'an kalamai har sai da tayi shiru.
Sai after nine sannan Mustapha ya kira AbdulHakam ya shaida masa sak'on da mahaifayarsa ta bada a matsayin amsan neman hakuri. Saboda tashin hankali ranan yadda yaga dare haka yaga rana don kasa runtsawa yayi.
[4/2, 9:57 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
36
By Linah Shams✍🏼
_🙏🏼sorry for the inconvenience. My salutations💞💞_
Da safe kasa ko kai ruwa bakinsa yayi yana ta jimamin maganganun Umma. To 7am lokacin gari yayo shaa ya fara neman numbern Jaleelah amma switched off, na Inteesar ma haka, nan ya nemi numbern Izz ya kira shi, da kyar ya jira suka gaisa, yace "dan Allah alfarma nake so kamin guda d'aya"
Izz yace "Allah yasa zan iya"
Yace "zama ka iya, pls ka kaiwa Jaleelah wayarka zamu yi magana ne and it's urgent, pls bama sai kayi hanging up ba just kawai ka tafi"
Ba musu ya wuce zuwa kaima Jaleelah wayar. Kicibis suka yi da Umma a hanyar shiga parlournta, tace "ya ya?", cikin ladabi ya gaishe ta sannan ya fara kokarin wuce ta, tace "ina zaka a nan?"
Yace "wurin Jaleelah". Umma tace "lafiya dai ko?", yace "ahh lafiya k'alau, Ya Abdul ne ke son magana da ita a waya"
Tace "ba zata yi ba d'in. Zo ka wuce, hala ita k'anuwar uwarsa ce da zai kira ya dame ta da farkon safiyar nan, yo to ko Uwani ai ba zai kirata yanzu ya dame ta ba, wuce ka bani wuri"
Wuce ta yayi ya fita zuwa compound sannan ya kara wayar a kunninshi, yace "ka dai ji abinda tace ko?"
Yace "eh thanks"
Zama yayi kan sofa ya rasa me ke yi masa dad'i a rayuwa, and he desperately wanted to talk to her.
Sake kiran Izz d'in yayi yace "to ka kaiwa Inteesar mana sai ta bata"
Yace "ka dai san halin Umma, tunda ta ganni yanzu she'll be suspecting all my moves. Ka kira ita Umman mana"
Murmushin takaici yayi ya yi hanging call ya tashi ya fara shirin fita, Sam ya ma manta bai yi breakfast ba.
Jaleelah kuwa babu irin kulawar da bata samu a wurin Umma tamkar ita ta haifeta, amma for now ita tafi so ta koma wurin Mommy, Umma kuma tace a'a ai duka gida ne.
4:17pm
Bayan Abdul ya dawo daga sallar la'asar yana zaune a office d'insa, tunani ne yaci k'arfinsa saboda gaba d'aya hankalinsa ya fita daga jikin sa. Knocking table d'inda akayi ya sa ya d'ago da rinannun idanunsa don yaga ko waye, sai da ya sake murza idanunsa a karo na biyu instead of ya bata welcoming words yace "me kike yi a nan?"
Guests' seat ta zauna a kai ta hard'e k'afafuwanta, tayi shrug sannan tace "I just came to check on you husband"
Furzar da iska yayi daga bakinsa yace "and why? With whose permission?"
Kwabe fuska tayi tace "and is that a fault? Kai baka iya zuwa ka duba ni ba and ni na zo dubaka but you're like complaining? Oh my gosh!!"
Neman inda zai sa kansa yaji dadi yake yi, yace "not at all, amma kin San office dina isn't a joint or a park, ba wurin shakatawa bane, wurin aiki na ne, so please just wait for me outside, I'll show up after 5pm"
Da mamaki ta kalle sa, zata yi magana ya nuna mata hanyar k'ofa yana fad'in "please..."
Tab'e baki tayi ta tashi ta fita shi kuma ya fara clearing table d'in saboda baya son yabar wani file zuwa gobe. Sai quarter past five sannan ya fito kuma koda ya fita bai nemi inda take ba saboda throught out cikin zullumi ya wuni kuma yaki fadawa kowa damuwarsa. Tana hangoshi ta k'arisa inda yake, tace "Abdul, you take an offence?"
Tab'e baki yayi ya girgiza mata kai, yace "not at all, I'm just worn out"
Tace "to, zan biyo ka tare da driver"
Zare idanu yayi ya d'aga sautin muryarsa, yace "to where?", tace "your home", daga haka ta wuce shi ta shiga motarta da driver ya kawo ta tayi masa umurni da bin bayan Abdul.
A tare suka isa compound dinsa drivern Raheemah ya je ya rufe gate din ya tsaya a parking lot Abdul kuma ya wuce ciki Raheemah na biye da shi. He was just wondering.
Duk inda ya cire k'afa nan take sa nata har suka isa inner sitting room. Zama yayi ya ajiye car keys dinsa a kan center table ita ma ta zauna a gefenshi. Jinginar da kansa yayi da backrest yana tuno Jaleelah, da ta na nan da yanzu ita zata cire mishi takalmi da socks yadda ya gajin nan. Rufe idanuwansa yayi yana jin wani twinge of pain tun daga tsakiyar kansa har cikin idanuwanshi.
Raheemah karewa d'akin kallo tayi tana kallon enlargements din hotunan Abdul da Jaleelah da akayi hanging a ko wane angle, wani bak'in kishi taji da ya rufe mata zuciya, a fusace ta kalli Abdul wanda har yanzu idanunsa a rufe suke, tace "my Abdul", ba tareda ya bude idanunsa ba yace "my Raheemah", tace "kace min taimakon yarinyar nan kayi", yace "eh" still idanunsa a rufe, tace "but this must be a lie! You are only fooling me Abdul"
Sai a sannan ya bude idanunsa ya kalleta, yace "me ya faru?", tace " komai... Komai ma. Idan ba wa'inda suke son junansu ba ya za ayi suje su d'auki hotuna suna dariya?"
Yace "ba inda ba zanje na nuna hoton nan ba naji wani d'arr a raina saboda mata ta ce, muharrama ta, kuma halas d'ita, hey look... I'm seriously tired and need some rest, mata ta ba damuwarki ba ce, baki da matsala da ita, ba zamanta za ki zo yi ba zamana za ki zo yi, now tell me, me ya kawo ki Kaduna?"
B'ata fuska tayi tace "kwana biyu baka zo ba shine na zo na duba ko lafiyanka k'alau"
Yace "good, yanzu ai kin ganewa idanunki, and... Meya sa ba zaki jira na zo ba? Ai tunda kika ga ban zo ba you know I'm engaged"
Yar gajeruwar tsaki tayi tace "yunwa nake ji"
Yace "akwai restaurant a bakin hanya idan zaki tafi ki tsaya ki siya abinci"
Tace "God forbid! Girki zan yi", dariya ma ta so ta bashi, yace "a ina? A kitchen d'in mata ta?"
Tace "ofcourse yes"
Tsaki yayi yace "you are not serious, ki tashi ki tafi gida", tace "Abdul. Kora ta kake yi?"
Yace "not at all, dare zai miki ne a nan kuma kinga ke mace ce"
Tace "to mene ne? Ba sai na kwana a nan ba?", har saida tasa ya tauna harshensa saboda son ya bata amsa da wuri, yace "are we spouses?"
Tace "but we are getting married"
Yayi kwafa da murmushi yace "but atleast I'm not an idiot.. Now ki tashi ki tafi gida before it gets late"
Haushi taji ta tashi ta d'auki handbag d'inta ta fita fuuuu kamar zata tashi sama ya bita a baya, tun daga nesa take kwalawa drivern ta kira "Lukman! Lukman!" Da Sauri ya bayyana, kamin ta karisa tace "je ka bude gate ka zo mu wuce"
Abdul yayi kokarin riko hannunta don ya dakatar da ita amma ya tuna ba muharramansa bace ai sai yayi gaggawan ja da baya yana ta kiran sunanta amma tayi masa banza ta shige mota, Lukman ya zo ya ja ta suka fita ya fito ya rufe ma Abdul gate din suka k'ara gaba.
Cikin hut ya shige ya zauna, shi yanzu ba takanta yake yi ba takan matarshi yake yi, she's even sick amma ko jin muryarta baya yi. Kamar dazu da safe yanzu ma numbern Izz ya kira ya roke shi ya kaima Jaleelah wayar. A main parlour yaga Umma, ya wayance yace "Umma ina wannan yarinyar?", tace "tana d'akinta tana guga"
Yace "to bari na ganta, aiki zan sa ta"
Yana shiga d'akin ya Tarar da ita tareda Jaleelah, ya roki Inteesar tayi excusing dinsu, mikawa Jaleelah wayar yayi, yace "sisto gashi nan, Ya Abdul zai kira ki, kar ki bari Umma ta ji ki" ta amsa tace "to" tare da Inteesar suka fita zuwa compound saboda ta bar Jaleelah tayi wayar a tsanake.
Kamin ta kai ga dialling sai ga call din Abdul din, tayi picking tana fadin "hello", wani farinciki ya mamaye zuciyarshi, yace "Ameerah", ta amsa da "na'am", yace "ya jikinki?" Tace "alhamdulillah I'm getting better"
Yace "sosai my Ameerah?", tace "eh", yace "to Alhamdulillah, you know what?"
Tace "till you tell"
Yace "I'm missing you", emotionlessly tace "lallai"
Yace "Jaleelah... Please, zan roke ki ne"
Tace "toh? Mene ne?"
Yace "please save me, kar ki yarda Umma ta raba mana aure dan Allah, wallahi tace sai na sake ki yanzu and I don't know what to do"
Tace "to... Meya sa zata yi haka?"
Yace "saboda kawai na fada mata I helped you and married you"
Wani irin zafi zuciyarta tayi mata kamar bakery, tace "amma ai gaskiya ka fada mata"
Yace "ni yanzu ba shi ya dame ni ba, dan Allah kar ki bari ta raba mana aure"
Sai da tayi hawaye taji dadi, tace "nasan Umma ba zata tab'a yin abinda zai cutar dani ba, idan tace a raba za a raba, just let go"
Zuciyarsa ta karaya, yace "please Jaleelah"
Tuno yadda yake ikirarin taimakonta da kuma alwashinta na barin gidansa tayi, a ranta tace "it's time!"
Cikin fad'a ta fara mishi magana "then amfanin me zanyi maka idan ba a raba auren ba? Ka taimake I've heard and thanks. Let this help get over! Kullum I almost practically worship you amma you never appreciate me, kullum taimakonta nayi taimakonta nayi, I don't want to hear it anymore!!!!! Where have I failed you? So kake na zauna na cigaba da bauta maka kana kara fadawa duniya abinda ba Wanda ya sani, remember then ko best friend dita na kasa fada mata halin da na shiga sai kai, but at the end look at what's happening.... Almost Kowa a danginka ya sani. Kafi so na zauna da kai na dinga dafa maka abinci kana ci, na cire maka takalmi, na cire maka socks and uniform na hada maka ruwan wanka and sometimes bath you, nayi dressing dinka like a baby, nayi maka wankin inners and Polish your shoes, nayi feeding dinka sannan na fada maka sweet stories... Now to make it sweeter, I sing lullaby to lull you to sleep. Me kake so na maka wanda ban maka ba? Have I ever denied you? Not once. Kawai tunda zaka auri wacce kake kauna may be kayi appreciating efforts dinta, kuma ni ban taba tsanar aurenka ba, I only feel jealous saboda nasan komai, and for your own information, gidan mu zan koma immediately na gama holiday dina"
Yayi kokarin Kare kanshi, yace "Jaleelah ba haka bane, I seriously..."
Bata jira ya gama magana ba tayi disconnecting. Sai da ta share hawayen fuskanta sannan ta tashi ta fito parlour zuwa kai ma Izz wayarsa. A nan taga Umma a zaune tana tsintar wake, kunya taji kamar ta hak'a k'asa ta nutse, tace "Umma sannu da aiki"
Tace "yawwa"
Cikin Sauri ta fita ta kaiwa Izz wayarsa sannan ta koma d'akin Umma tayi zamanta.
Kansa chaji ya d'auka ga wani jiri da yake gani, a daddafe ya samu ya koma ciki ya canja kaya ya kwanta zuwa magrib. Sai after isha ya dawo daga masallaci, then ne ya tuna ko ruwa yau bai sha ba. Kakkauran tea ya had'a ya sha sannan ya sha ruwa, amma ko fifteen minutes ba ayi ba ya amayar dasu. Take ciwon kai mai tsanani ya kama shi gashi ba mataimaki, Allah ya taimake shi ya sami paracetamol yasha ya kwanta.
Washe gari daya tashi pain din yayi subsiding. Amma sai da ya tabbata yaci wani abu sannan ya bar gida.
Ranan Friday nayi yayi shirin tafiya Kano. Zai je ya rarrashi Jaleelah ya kuma ba Umma hakuri, and still, zai soke neman auren Raheemah ko Umma zata daina fushi da shi.
Sai da yayi sallar la'asar sannan ya shiga gidan. Tunda ba mutane ne da yawa a gidan ba Umma da Jaleelah kadai ya Tarar a parlourn Umma.
Gabanshi sai fad'i yake yi daya shiga, hakanan yayi na maza ya kirkiro murmushi ya gaishe da Umma, Jaleelah kam ko kallon tsiya bata mishi ba bare na arziki. Umma tace "gashi ka zo a daidai lokacin da nake son ganinka d'an Alhaji", yadda tayi maganar ka rantse kace ta sauko ne, yace "to Umma"
Umma ta dubi Jaleelah, tace "ke Jaleelah"
Ta d'ago da kai tace "na'am"
Tace "je ki d'akin Inteesar ki samo min Biro da takarda". Gaban Jaleelah ya buga da k'arfi, tace "Biro da takarda?"
Umma tace "eh kiyi sauri"
Ta tashi ta wuce d'akin Inteesar don samo abinda aka aike ta.
[4/3, 1:48 PM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
37
By Linah Shams✍🏼
Kasa figuring abunda take ji a ranta tayi, bak'inci ne ko farincikin rabuwa? Hakanan ta d'auko takardan da biron ta fito ta mika ma Umman sannan ta sami wuri ta xauna. Satan kallon fuskokinsu Umma tayi, tayi murmushi a ranta sannan tace "yawwa, d'an Alhaji ungo nan"
Mik'a hannu yayi ya amsa yace "na mene ne Umma?"
Tace "Mustapha bai fad'a maka sak'o na bane?"
Gabansa ya fad'i, yace "sak'on me Umma?"
Jinjina kai tayi tace "tabd'i! Zaka rubuta ko kuwa?"
Confusedly yace "Umma me zan rubuta?"
Ita dai Jaleelah ganin abin take kamar wasan Hausa, Umma tace "ca nake zaka auri wacce ranka ke so kuma kake muradi, ita kuma wannan ko oho ko?, to ba zaka je ka kashe min yarinya ba, rubuta mata saki in gani, idan ta kammala idda zan aura mata mutumin da ya fika, kuma ba zan aura mata mahaukaci mai suffan masu hankali kamar kai ba, rubuta in gani"
Nan fa maza suka koma mata, hawaye ya fara yi, Jaleelah kuwa tashi tayi ta koma bedroom ta haye gado ta fara rera nata, Umma tace "jiranka fa nake yi, rubuta min in gani"
Cikin rawar baki yace "Umma dan Allah kiyi hak'uri kar ki raba mu"
Tace "d'an Alhaji taimakonka fa zanyi, tun da ba son ta kake yi ba taimakonta kayi yanzu ba sai ka sawak'e mata ba?"
Idonsa na zubda hawaye yace "wallahi Umma ina son mata ta". Cikin tsawa tace "rufa min baki munafiki, a gidan uwar wa kake son ta? Ba wanda baka fada ma taimakonta kayi ba saboda cin fuska da rashin sirri, sake ta nace ko inci ubanka"
Idonsa na hawaye ya rubuta takardan ya ninke sannan ya mik'a mata, hamdala tayi ba tare ta bude takardan ba tace "daga yau zata fara idda, ni rokon iyayenta ma zanyi su bar min ita nan", daga nan ta tashi ta fita daga parlourn ta wuce d'akinta. Hawayen fuskansa ya share ya tashi ya fita daga gidan. Bakin ciki ya dabaibaye masa zuciya. Direct Kaduna na nufa ya koma gida.
A sitting room dinsu ya tsaya yana kallon hotunan da suka d'auka tare suna dariya akayi musu enlargements. Lumshe idanuwansa yayi hawaye na fita, yace "I love you Jaleelah... I never know I'm in love, and it's still not late to prove my Love for you..."
Akan kujera ya kwanta duk rintse idanuwa ita yake gani, but ya za ayi ace har ya fara k'aunarta bai sani ba?.
Abin duniya gaba d'aya ya ishe shi, ga fushin Umma da Abba ga rashin matarsa, call din Raheemah ya shigo wayarsa, wani takaici ya sake kama shi, he loves her too kuma matukar yak'i aurenta bai mata ihsani ba, amma kuma ba zai iya jure fushin iyayenshi a kanta ba, bayan call din yayi disconnecting yayi dialling, tana picking ya yanke kiran saboda ba ya cikin mood din da zaiyi mata hira.
Tunanin komawa Kano yayi gobe yaje ya sami Abba ya labarta masa cewa ya soke auren Raheemah Umma ta bashi matarshi gashi tana gab da dawowa saboda an kusa fara NECO. Kasa hak'uri yayi ya tashi ya sake d'aukan keys ya bar gidan ya sake daukan hanyar Kano. Saboda yadda yake gudu kamar zai tashi sama a awa d'aya da rabi ya isa Kasuwa a tank'amemen shagon Abba dake sayar da laces, atamfofi, shadda da yadudduka inda yaran shagonsa ke kai komo yana making order. Ciki ya nufa wurin Abba, amma kamin ya ganshi sai da ya tsaya ya gabatar da Sallahr azahar sannan yayi la'asar ya fito ya wuce wurin sa. Abba kam sai farinciki yake yi daya ganshi don shi zuba masa ido kawai yayi ya yi yadda yake so. Bayan sun gaisa ya zauna akan stool, he didn't hesistate to mention his problem, yace "Abba dama na zo muyi magana ne"
Abba yace "to ai da ka bari na dawo gida ko d'an Alhaji"
Yace "har fa na zo d'azu na koma saboda dai muhimmancin maganar shine na dawo"
Yace "to ina jinka"
Yace "dama dangane da maganar k'arin Auren nan, shine Umma take ta fushi da ni kuma tace na saki mata ta, dan Allah shine na zo ka bata hak'uri ni na fasa auren, na hakura da k'ara auren"
Dariya Abba yayi yace "yaro kenan, to so kake na zama k'aramin mutum ko me? Jiya jiya aka je aka nema maka auren yarinyar nan, yanzu za a fara da gabatar da abubuwan al'ada, an kai maka nuna kai shine zaka dawo kace ba ka so? Ai hakanan zaka yi hakuri ka rungumi kaddara, ni babu hannuna a cikin wannan maganar, sai dai idan zaka je ka sake samun uban d'akin naka ya shige maka gaba Ku koma kuce kun fasa, amma ni babu hannu na a cikin wannan al'amari"
Dafe kanshi yayi yana jin bakin ciki. Ajiyar zuciya yayi yace "to Abba ka bata hak'uri"
Yace "a'a babu ruwa na, tsakanin d'a da mahaifi sai Allah, kaje ka same ta da kanka kuyi magana"
Yace "to shikenan Abba", ba wai don zaije yayi mata maganar ba. Sallama yayi mishi ya tashi ya sake dauko hanya ya koma Kaduna a gajiye.
••°••
Da sauri Inteesar ta saki ledan hannunta ta k'arisa kan gado wurin Jaleelah, tallafo ta tayi tana fad'in "Jaleelah mene ne? Jikin naki ne?"
Share hawayenta tayi ta girgiza kai alamar a'a. Inteesar ta sake cewa "to mene ne?"
Ta sharce kotsanan hancinta tace "Ameer ya sake ni yau"
Saboda mamaki kasa rufe bakinta tayi tace "saki? I mean... Ya sake ki wai?"
Ta girgiza mata kai tace "eh". Rungume ta tayi tace "so bad. Amma, bari naje naga Umma"
Ta tashi ta fita zuwa d'akin Umma, ko sallama bata yi ta kutsa ta zauna a gefen Umma, tace "Umma wai dagaske ya Abdul ya saki Jaleelah", tace "eh ya rubuta mata takarda, ni nama manta ban bud'e na karanta ba"
Tace "to Umma laifi tayi masa?"
Umma tace "a'a aure ze k'ara shine ya sake ta"
Takaici yasa ta tashi ta fita tana surutai ta koma d'akinta. Lallashin Jaleelah ta dinga yi daga baya Jaleelah ta tashi ta fara had'a kayanta a trolley dinta, a cewarta ita gobe zata koma gidan iyayenta. Tare suka shirya kayan Umma ta lek'a kiran Inteesar tayi mata blending ta ga Suna ta aikin had'a kaya, Umma tace "lafiya dai ko?"
Inteesar tace "tana had'a kayanta ne saboda tana so zata koma gida gobe"
Umma tace "Jaleelah zo nan"
Rike mata hannu tayi suka wuce bedroom dinta directly, a gefen gado suka zauna. Kallon ta tayi a ranta tace "dama iskanci ke damunku, kuna son junanku kuna kaiwa kasuwa"
Tace "kar ki damu zaki zauna a nan, idan ya gane cewa taimako ba hauka bane zan barki ki koma d'akin ki, kuma kinga jibi likita yace mu koma asibiti, bai kamata ki dinga zirga zirga ba ko don cikin ki, kar ki sawa ranki damuwa ya zo ya shafi lafiyarki"
Da mamaki tace "Umma ciki kuma?"
Tace "eh, saura kije ki fadawa wannan yaron ki sa yayi ta min zarya a gida ba dare ba rana. Kina ji na?"
Saboda kunya kasa amsawa tayi, tace "ki tashi kije kiyi sallah"
Ta tashi ta fita tana jinjina Kalmar ciki kamar yau ta fara ji.
After two weeks
Abdul bai sake komawa Kano ba saboda yana shayin haduwa da Umma. Ya sha kiran Izz yace mishi yaba Jaleelah tak'i amsa gashi yau saura kwana biyar su fara NECO exams dinsu dole zata dawo Kaduna kuma yasan da wuya Umma ta barta ta dawo gidan shi. Ranan Monday zata koma Wednesday su fara exams.
Deciding zuwa Kanon yayi da weekend saboda dole yana so ya ganta, may be idan ta yarda zata koma Umma itama ta yarda.
Duk yadda ya so ya ganta ranan Friday bai samu ba, haka ma ranan Saturday. Sai ranan Sunday da yamma ya kira Izz yace ya kai mata wayar, yace mishi ya zo idan yana so yayi magana da ita Umma bata nan kuma sai da daddare zata dawo, idan ma d'aukarta zaiyi ya d'auke ta su tafi.
Jiki na rawa ya d'auki car keys dinsa ya fice daga gidan. A compound ya same ta tana zaune a balcony. Tun daga nesa data hangoshi ta murtuke fuska, hakan bai mata ba ta tashi ta gudu zuwa bedroom din Umma. Har ciki ya bita ya janyota, ba tareda b'ata lokaci ba yace "je ki dauko hijabinki"
Ta buge mishi hannu tace "bazan d'auko ba. Ka fita ka bani wuri", yace "look, I'm not here for jokes, ki je ki dauk hijab"
Hararshi tayi from head to toe ta sama wuri ta zauna, ficewa yayi daga d'akin zuwa nasu d'akin. K'arar ruwan da yaji a bathroom ya tabbatar masa da cewa Inteesar ce a ciki. Cikin sauri ya Bud'e wardrobe ya janyo hijab d'in da ya gani bai San me shi a cikinsu ba ya fita ya koma bedroom d'in Umma. Janta yayi suka fita tana turjewa tana bige mishi hannu har ya sata cikin mota. Izz kam na daga d'akinsa ya bud'e window yana kallonsu. Hon yayi gateman ya bude musu gate suka wuce. Gidansu suka nufa tana ta masa ihu da kwaratsi har suka isa.
Ya fita ya bud'e mata k'ofa suka wuce ciki yana rik'e da ita don k'in tafiya tayi. Suna isa main parlour ta fizge hannunta da k'arfi ta juya zata fita, ya sake rik'e ta har sai da suka isa bedroom yayi locking sannan ya sake ta. B'acin rai ne k'arara bayyane a fuskanta. Yana matsawa daf da ita tana ja da baya har suka k'ure space din. Cikin tsiwa tace "what the hell do you think you're doing? Let me go"
Da k'arfinsa yace "never! I will never let you go"
Tace "you had already, saboda haka ka mayar dani gida ko in tara maka makwabta"
Yace "let's talk serious wife"
Kallonsa tayi ido cikin ido kawai sai ya rasa me zai ce mata, yayi shiru shima yana kallonta cikin ido. Hawaye ya cika mata idanu, suna zubowa ta share tana rissinar da kanta, yace "Jaleelah"
K'in amsawa tayi, yace "are you still mad at me?"
Banza tayi masa, yace "kin tsane ni?"
D'ago da kanta tayi ta kalle shi. Yace "you are still my wife Ameerah"
Tace "never.. Ka sake ni, I'm no longer your wife. Ka zo ka bud'e min k'ofa zanje na sha magani"
Yace "Jaleelah ban sake ki ba, you are my wife and will forever be. Ni ban sake ki ba. Ki tambayi Umma"
B'ata rai tayi "you can't play such silly games with me, ni bani da lafia, ba abinda zan iya maka, ka mayar da ni gida"
Yace "I missing morethan just your body. Ni ba abinda kike tunani ya kawo ni ba, please kawai ki ce ma Umma zaki koma gidana, besides ni ban rubuta miki saki ba"
Kallonshi tayi ta yi tsaki, tace"ba zan ce ba, nace ka mayar da ni gida. I once promise you that I'll leave your life, and this is the right time to. Tun da.. Tun da.. Ni baka so na and you never appreciate me"
Kuka ta fashe da yayi saurin hugging dinta, a hankali yake fadin "I love you Jaleelah, I love you"
Cikin kuka tace "you just want a house girl amma baka so na", ya tallafo fuskanta yana kallon yadda hawaye ke bulbulowa daga idanuwanta, yace "aswear I love you... I came all the way to tell you this, to announce my feelings for you"
Kuka ta cigaba da yi yayi hugging dinta a kirjinsa.
Sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru tana kokarin janye jikinta daga nashi, hannayenta duka biyun ya rik'e, yace "please, can you still be my wife?"
Kasa magana tayi ya sake repeating same question. Shiru d'akin yayi na kusan sakwanni goma. Abdul ya saki mata hannayenta, cikin yanayi na tausayi yace "it's fine. Whatelse?"
Juyawa yayi zai fita yana unlocking k'ofar taje da gudu tayi huggin d'insa ta baya "I love you Ameer.. With all my heart and soul"
Juyawa yayi ya yi hugging dinta yana jinta har cikin ransa. He has been feeling it this way amma bai tab'a tunanin it was love ba.
A hanyarsu ta komawa gida yake tambayarta, "wai ciwon me kike yi?"
Murmushi tayi da ta tuna warning d'in da Umma ta bata akan kar ta fad'a mishi ciki ne da ita ya zo ya fara damunsu. Yace "kin yi shiru"
Tace "a'a ba komai".
Yace "dama ana ciwon ba komai ne? I never know"
Murmushi tayi tace "ciwon so ne kawai"
Dariya yayi yace "to shikenan tunda ba zaki fad'a min ba"
Tace "to why not ka tambayi Umma"
Ya d'an b'ata fuska, yace "ai ta daina so na, ke ta ke so yanzu"
Tace "wani abu da baka sani ba shine, she loves me for Allah's sake and for your sake, she loves for the sake of love"
Yace "dama haka zaki ce"
Time din suka isa gidan. A parlour ta had'u da Inteesar, tace "daga ina haka? Daga jirani nayi wanka sai kika fita"
Tace "naje siyo malt ne kuma ban ma samu ba"
Wuce ta tayi tana fad'in "gama malt din can a tsakar gida ai"
Tayi saurin shan gabanta tana dariya, tace "bafa tare muke ba"
Dariya tayi tace "ni matsa min ko in bi ta kanki, wai ni zaki ma k'arya"
Tace "tare muke, kirana yayi wai na roki Umma na koma Kaduna"
Kwafa Inteesar tayi tace "namiji kenan, buhun tasono. To se ki je ki rok'e tan"
Jaleelah tayi dariya tace "Allah shirye ki, amma ni ba rokontan da zanyi"
Daga haka suka yi parting kowa ya nufi inda zashi.
Har bayan sallar isha Abdul bai tafi ba yana zaman jiran Umma ta dawo ya roke ta gobe ya dawo ya d'auki matarsa. Sai to 9pm sannan Allah yayi mata dawowa. Yana ganin wucewarta ya tabbatar ta shiga ciki ya fito daga motarsa ya shiga. Jaleelah da Inteesar kuwa tunda suka ji sallamarta suka fito suna mata sannu da zuwa suka rungume ta, "to ya isa haka kar Ku kada ni", ta fada tana cire hijabin dake wuyarta. Jaleelah ta amsa da handbag din ta wuce ta kai mata d'aki Inteesar kuma taje kawo mata ruwa.
Da sallama ya shiga parlour. Mamakin ganinsa Umma tayi ta amsa sannan ta d'auki tumbler d'in ruwa tana sha. Lokacin Inteesar ta kawo mata abinci. Jaleelah kuwa tunda taji muryarsa sama sama tak'i sake fitowa. Inteesar tayi serving dinta ta wuce d'akinta.
[4/5, 10:25 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
38
By Linah Shams✍🏼
Cikin girmawa ya gaishe ta, rai a sake ta amsa mishi. Shiru ya biyo bayan gaisuwar na d'an wani lokaci, Umma nata cin abincinta, yace "Umma dama wurinki na zo", tace "amma dai kana gani abinci nake ci"
Bai sake cewa komai ba sai da ta kammala, yace "to Umma"
Tace "ka jira sai nayi sallah"
Ba yadda ya iya sai da ta je tayi sallah, ga sallarta ba dai dadewa ba. Bayan ta idar ta fito ta zauna har lokacin ko sitting position bai canja ba saboda ladabi, tace "ina jinka", tare da zama, gyara zama yayi yace "dama Umma naga ranan talata za a fara NECO, shine nake so dan Allah ki bari gobe na zo na d'auki Jaleelah"
Tace "a'a zan roki Alhaji ya bada motarsa Izz zai kaita har kofar gidansu"
Yace "Umma to mene ne amfani na?"
Tace "yo kuwa to mene ne amfaninka?, ko ka manta tana idda ne? Aww, kar dai kace min ka mayar da ita ne"
Da damuwa a voice dinsa yace "Umma ni ban sake ta ba ai", tsaki tayi tace "idan ka shirya tafiya ka wuce ba sai kamin sallama ba", daga nan ta tashi ta wuce shi ta shige d'akinta. Kuka ne kawai baiyi ba, ga mari ga tsinka jaka. Tun safe yake jiranta har dare amma kuma bata yarda da kudirinsa ba.
D'akinsu Jaleelah ya leka ya gansu a kwance akan gado kowa yayi shiru.
Sunan Jaleelah ya kira tayi kamar tana bacci, Inteesar ta d'an tsikareta ta bud'e ido kamar mai baccin gaske, Inteesar tace "mijinki na magana", d'aga kai tayi ta kalle shi, ya yafuto ta da hannu ta tashi ta karisa inda yake suka fita.
Cikin mota suka shiga, cikin gidan baya. Tace "mene ne?", yace "Jaleelah ki taimake ni ki sa baki Umma ta barki mu koma gida tare, gobe zan zo na d'auke ki"
Tace "so kake ace nayi rashin kunya? Tunda dai bata yarda ba ai shikenan", yace "kin san dai nayi hakuri da yawa, dan Allah fa"
Hamma tayi tace "to ni dai ba zan iya mata magana ba, why not kayi mata da kanka mana?"
Yace "how many times? Kullum magana d'aya nake mata amma it seems ko tausayi na ma bata yi"
Tace "saura kwana nawa ma ayi aurenka?"
Yace "it's none your business"
Hangame baki tayi ta kalleshi, tace "Allah ya baka hak'uri"
Haushi ya fara ji, yace "this is only because I care!!!"
Tab'e fuska tayi ta bud'e motar ta fice wanda ya faru a kan idanuwan Abba. Sai yaga Abdul ya fito ya shiga driver's seat ya bar gidan.
Numban Umma ya lalubo ya kira taje ta same shi a part dinsa, bayan ta zauna yace "kamar d'an Alhaji na gani ya fita"
Umma tace "eh shine, wani abu ne?"
Yace "kwarai, ya zo ya same ni wai kin sa shi ya saki matarshi". Umma tace "wato k'arata ya kai, kuma ai bai yi sakin ba, da yake ya raina ni I love you ya rubuta da wasu kalaman soyayya ya miko min, har yanzu bai san na karanta ba"
Abba yace "to meya sa zaki yi haka Hajiya?"
Tace "naga kamar basu da hankali ne shine nake so na gogewa kaina shakku. Kullum kiran taimakon nan yake yi, kullum. Ashe yana son ta sakaran"
Abba yace "to da sauki ma, ita matar tashi ta dunga zama a nan kenan?"
Tace "a'a gobe nake so ta koma amma nafi so ta sauka a gidan iyayenta"
Abba yace "haba ke kuwa, ga gidan mijinta can inda take da daraja"
Umma tace "ba wai na k'i maka bane, tana da ciki ne mai kimanin sati Biyar, to likita yace banda motsa jiki da yawa sai cikin ya fara kwari, to idan taje can gidan nashi wa zai dinga mata aiki? Gara dai taje inda za a kula da ita, kaga bayan ta gama jarabawar sai ta koma can gidan na sa"
yace "to shi bai san tana da juna biyun bane? Ai da sai a sama mata mai aiki"
Umma tayi murmushi tace "so kake yi ya dinga zuwa min gida kullum kenan, dama a hakan ya lafiyar giwa bare kuma tayi hauka".
••°••
Washe gari after 10am Jaleelah ta fara shirin komawa gida. Amma Kamin nan sai da Umma ta kira Mommy ta shaida mata dalilin da ya sa zata sauka a nan gidan, bacin a Kd zata rubuta exams din da sai dai idan ta zo ganin gida Mommy taga cikin. Tsaraba ta hada na musamman ma Mommy.Sunyi kewar juna da Inteesar har ma da Umman. Izz ya kaita gida kamar yadda Umman ta buk'ata don ko AbdulHakam bai San tana hanyar dawowa ba ga kuma bacin ran daya ke ji idan ya kirata yaji switched off.
Har kofar gida ya kaita sannan ta shiga ta fadawa Mommy zuwansu tare. Sai da ya shiga suka gaisa sannan ya fito ya dauki hanyar gida.
Mommy kuwa sai ina zata saka da ita take yi. Komai sai dai ta sa Hadiyya tayi mata ita kuwa tana zaune.
Sai bayan sallar la'asar sannan ta samu caji ta bude wayarta, Umma ta fara kira ta fada mata komawarta lafiya, sun dan jima suna hira har da Inteesar sannan call din yayi disconnecting. Bayan nan ta kira numbern oga at the top, AbdulHakam, shi kuwa lokacin a matse yake ya tashi daga wurin aiki ya wuce Kano, yau yayi bearing in mind dinsa komun dare sai Umma ta bashi matarsa, idan ta kama yayi kneel down a gabanta yana mata kuka ne ma zai yi indai har zata bashi ita sai kuma ga call. Saboda tsabar kosawa da kansa ya yanke kiran sannan yayi dialling. Sai da ta ja mishi aji daidai misali sannan tayi picking. Da kyar ta iya gaishe shi sannan tace "dama uniforms dina nake so"
Yace "uniform? Me zaki yi dashi a Kano kuma?"
Tace "ina gidan mu ai tun d'azu"
Mamaki yayi, yace "gidanku? Yarwa close"
Yar gajeruwar dariya tayi tace "to gidan babana nake nufi"
"What? But ke kinga ya kamata ki sauka a can?"
Tace "sosai ma, ai a nan Umma tace na sauka till further notice"
Yace "but.. But.. Meya sa haka?"
Ta tab'e baki tace "ka kira Umma. Nima ban sani ba, dan Allah ni dai ka kawo min uniform dina da stockings, kaga gobe ne ma zanje na amsa exams card dina"
Wani irin tukukin bakinciki yaji, yace "none of my business, ki zo ki dauki uniform din da kan ki"
Marairaicewa tayi tace "dan Allah mana, kaji?"
Tsaki yayi mata, yace "I doubt if you truly love me, a hakan?"
Ita ma d'aukan zafi ta fara, cikin tsiwa tace "I don't love you then idan haka kake tunani, now, my uniform!"
Tsaki ya sake yi yayi disconnecting call din, rashin kunyarta ya soma isan shi.
Tun da ya san tana Kaduna gaba daya yaji bai damu ba saboda ko yanzu ya so ganinta zai iya zuwa, kuma yasan iyayenta ba zasu hanashi ganinta ba kamar yadda Umma ke masa. Sai a sannan hankalinsa ya dawo jikinsa har ya samu damar waya da Raheemah, wacce tun tana k'orafi har ta gaji, amma yanzu tunda matarsa ta dawo kusa ya tabbatar mata da zuwansa next weekend su sha hira.
Ranan through out basu sake waya ba har washe gari da safe. Cikin Mufti ta shirya ta fad'awa Mommy zata school dinsu amso exams card. Mommy ta sa driver ya kaita inda zata. Bayan sun je school din ta amsa card din taje suka gaisa da Aunty Maryam, tayi ta mata tsiya wai ta k'ara b'ul b'ul, tace "Aunty Maryam ba zaki gane bane, bafa abinda kike tunani bane", dariya tayi tace "haba Jaleelah, jiya ba yau ba ne fa, ke dai fad'i gaskiya"
Kunya taji tayi dariya tace "ki bari har gida zan zo insha Allah", ta amsa mata da "amin".
Bayan ta fito direct ta sa driver ya kaita base wurin Abdul ta amsa keys zata je gidan ta dauko uniform dinta tunda shi bazai iya kawo mata ba.
Sai da suka shiga cikin base din sannan suka fara tambaya, Group Captain A.M Jafar. Da taimakon masu kwatancen ta isa office dinsa ko knocking babu ta murda knob din ta kutsa kai. Sai akayi rashin sa'a yana tare da b'akuwa, ko kallon bak'uwar bata yi ba k'arisa har side dinsa kamar zata shige mishi, cikin kunakunai tace "ina kwana"
Sosai yayi mamakin gainta, yace "daga ina haka? Baki iya sallama bane? Amma ai kin iya knocking ko?"
Bata tanka shi ba ta sake cewa "ina kwana"
Yace "ban ganshi ba, kinji?"
B'ata fuska tayi tace "dama keys d'in gida na zo amsa"
Satan kallon fuskar bakuwar ta sa yayi sanna ya kalli Jaleelah, yace "a wani gida kika sauka?"
Tace "gidan babana"
Yayi shrug yace "to ai kin ji inda ya kamata ki duba uniform dinki"
Had'e rai tayi tace "dan Allah da driver na zo, ka bani na wuce, zan sa shi ya dawo ya kawo maka tunda nasan baka fito da spare ba"
Kallonta yayi k'ikam yana yi, tace "kaji?"
Yace "ki je waje ki jirani ina tare da bakuwa"
Juyawa tayi da zummar kallon bakuwan ta roketa afuwa sai bargon mamaki ya lullube ta, ta dube shi tace "ina bakuwar?"
Hararata yayi yace "ban sani ba", girgiza mishi kai tayi tace "bari naje na kira Umma may be idan ta kira ka sai ka bani", daga haka ta wuce tayi ficewarta, ba shiri ya tsallake Raheemah dake zaune tana kallon ikon Allah ya bi bayan Jaleelah. Da ta ji karar footsteps dinsa sai ta k'ara sauri zata je ta shige mota ya sha gabanta, b'ata fuska yayi yace "wai what's wrong with you?"
Idonta shaye da toka tace "something I need to ask you"
Ta zagaye shi zata wuce ya sake shan gabanta, yace "look kar kiyi distracting mana attention"
Slight sigh tayi tace "even morethan that"
Hannu yasa a aljihu ya ciro mata keys din ya mika mata, da kamar ba zata amsa ba daga baya kuma ta amsa, yace "I'll come after isha"
Kawar da kanta gefe tayi tace "dama har an d'aura auren naka ne? I never know"
Yace "zan buge miki baki, what's your own business?"
Kamar zare mishi idanu tayi, tace "it's my business saboda mijina ne, MIJIN JALEELAH!"
Gudun kar ya ja ta ja su jawo mutane yasa ya sassauta muryarsa, yace "fine, yanzu dai ba sai kin kira Umma ba, ga keys nan kije ki dauki abin da kike so"
Ta gefen ido ta kalleshi, tace "bye" ta wuce shi shima ya wuce ya koma ciki yana addu'ar Allah yasa kar ta fadawa Umma cewa taga Raheemah a wurin aikinshi, ko shi baya son tana zuwa kamin tayi tarnishing image dinsa a idanuwan mutane.
Gidan suka nufa bata tsaya wata wata ba ta shige cikin bedroom ta kwaso uniform dinta da sets din kaya da wasu tarkace ta zubo a jaka. Duk ta kosa ta koma gida saboda jikinta taji ba dadi amma kuma babu abunda yake damunta don ba zata iya cewa ga inda yake mata ciwo ba.
Sitting room dinsu ta fito tana kallon enlargements dinsu tana murmushi kamar an mata kyautar kujeran makka, amma all of sudden murmushinta ya koma ciki yayinda taga pink headscarf akan kujera. Komawa tayi da baya ta tsaya ta kalli scarf din tana tantama for a minute or so sannan ta durkusa ta dauko shi. Gida ne dai ita daya ce mace a cikinsa sai mijinta kuma wannan scarf din ba nata bane, kuma ranan da zata tafi Kano bata tafi ta barshi a wurin ba. Mamaki ne fal cike da ranta, duk yadda ta so da kiyaye zargin mijinta a ranta abin faskara yayi, d'aukan scarf din tayi yayin da body weakness dinta yayi doubling kansa ta sa a cikin jaka ta fice ta rufe gidan. Da har gidan Umman Fadeelah ta so ta shiga amma a yanzu yadda take jin jikinta ba zata iya ba.
Kamin su isa gida tuni ciwon kai ya saukan mata har amai ke ta so mata. Suna shiga gida ko bi takan jakan kayanta bata yi ba ta fice da gudu ta wuce Mommy dake parlour bata zame ko ina ba sai toilet ta shiga kwara amai Mommy ta bi bayanta shi kuma driver ya shigo mata da kayanta. Mommy ta rike ta har sai da aman ya gama fita sannan ta wanke mata baki ta goge mata jikinta ta fito da ita ta kwantar da ita, sannan ta koma toilet din ta wanke inda ta b'ata ta dawo tana mata sannu. Fresh cow milk da fruits din ta ta saba ci ta nacewa Umma shi zata siyo mata. Allah ya taimake ta driver din bai tafi ba ta bashi sako yaje ya siyo mata ya kawo.
8:30pm
A parlour ta jiyo muryansa suna gaisawa da Mommy ta sake lafewa cikin gado. Tsanar kadai ta kusa fara yi. Ta ma rasa haushin wa zata ji a cikin su uku. Shi da ya kasa kamewa kuma ta ganewa idanuwanta Raheemah a office dinsa, ko Umma da ta kekasa kasa ta hana su zama tare ko ita da ta bijire masa ko spending weekend daya basu taba yi tare ba tunda taje hutu?
Tana ta aikin judging bata ma san lokacin da ya shigo ba.
Kawai jin hannun mutum a fuskarta tayi, tayi firgit ta kalle shi, murmushi ya sakar mata, yace "ya jiki?"
Juya masa baya tayi ta b'ata fuska, ya sake yin murmushi yace "sarkin zuciya, ya jiki?"
Duk sanda taji sautin muryarsa sai taji bakin ciki, duk fadin Kaduna ya rasa inda zai kai budurwanshi sai gidansu kamar wani me karancin ilimin addinin.
Riko hannunta yayi ta fizge so violently, yace "oh my gosh! Jaleelah", cikin zafi ta juya ta kalleshi, duk azaban ciwon kan dake damunta be hanata yi mishi rashin kunya ba, tace "you're such a shameless infidel that I never know, a worst perfidy"
Ji yayi kamar ta caka mishi mashi a kahon zuciya, yadda bacin ransa ya bayyana yafi nata, cikin kakkausara murya yace "don't dare... Don't ever woman! You are crossing your limits, kar ki fara kice zaki kira ni mazinaci, ki tsaya a matsayinki na matata"
Cikin kuka da d'aga murya tace "and that's what gives me the audacity to"
Shima kamar yadda ranta ya b'aci haka ya b'aci, ta d'aga pillow ta dauka keys din ta jefa mishi, yace "ki koyi girmama kanki, idan ba haka ba zan sauke miki duk rainin wayon dake kanki, yarinta ba hauka bane and I can't stand it"
Tace "then go fuck yourself!!!"
"What?????", ya kusa second biyar yana kallonta so flabbergasted sannan ya tsugunna ya dauki keys din ya fita. Hakanan ya kirkiri murmushi daya hadu da Mommy a parlour yabi su Hadiyya da 1k sannan yayi musu sallama ya tafi.
Maama'astouh💞
[4/7, 10:09 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
39_40
By Linah Shams✍🏼
Washe garin ranan Mommy da kanta ta kaita schl saboda ta kwana zazzabi amma da safen ta d'an ji sauki. Sai da taje ta sami principal tayi masa bayanin lalurarta amma bata fada mishi juna biyu ne da ita ba, ta dai yi making emphasis akan a d'an dinga barinta tana fita idan zata yi amai sai kuma gautan d'acin data siya mata ta bata. Mrs Kiyawa tayi ta kula da ita har suka yi practical suka gama dama shine paper'n farko. Bayan sun gama ta kira Mommy tace ta zo ta d'auke ta ta kaita asibiti saboda jikin yaki mata dadi. Mommy ko bi takan Mijin Jaleelahr bata yi ba taje ta d'auke ta suka wuce asibitin suka ga Dr, prescribing drugs aka mata ba allura suka koma gida.
Yadda Mommy ke kula da ita yasa ta rage damuwa akan AbdulHakam Wanda har yanzu bai sake kiranta ba ko zuwa inda take. Da dare tana kwance akan jikin Mommy call ya shigo wayar Mommy, tana daga wayar taga mai kira tace "Jaleelah ga mamarku tana kira", murmushi tayi tace "ai da yanzu a jikinta zanyi kwanciyata". Mommy tayi picking call d'in suka gaisa da Umma sannan ta tambayi lafiyar Jaleelah, Mommy tace "ga dai ta nan, d'azu ma sai da muka sake zuwa asibiti"
Umma tace "subhanallahi, to yaya jikin yanzu?"
Tace "ah da sauk'i, ai ga ma ta nan", Mommy ta mik'a mata wayar suka gaisa da Umma irin gaisuwar d'a da mahaifi sannan suka gaisa da Inteesar, tana so tayi mata gulma amma ba hali, ita tana gaban Mommy ita kuma tana gaban Umma.
Washe gari Mommy ta sake kaita schl din still amma bata shiga ba, da akayi closing ma taje ta d'auke ta. AbdulHakam bai tashi kiranta ba sai da akayi kwana biyar, shima ya kira ne yaji lafiyarta ba don komai ba saboda ya sami labarin bata da lafiya a wurin Izz, bama zai je dubata bane kamin ta fara tunani negatively akansa, Mommy ma sai baza idanu take yi taga ta inda Mijin Jaleelah zai b'ullo. Ko da ta ga call din ba ta d'auka ba at first sai da ya sake kira, bata ce komai ba haka shima bai ce komai ba har sai da suka yi 20secs a haka sannan ya sauke girman kai yace "ya jikin naki?"
Da k'yar ta iya ce mishi "lafiya"
Yace "good. Sai da safe"
Daga haka ya yanke kiran. Kwanciya tayi tana jin zafin call din, da shi ai gara babu. Wani wawan tsaki ta saki ta tashi ta koma d'akin Mommy don rage damuwa.
Gajiya yayi da jiran ranar da zai ji an kira shi ance ya d'auki matarshi, yasan may be tafadawa iyayenta ya sake ta, amma ai Umma ai ta san komai. Lambanta ya zak'ulo ya kira, bayan gaisuwa yace "Umma dan Allah wai yaushe za a bani mata ta?"
Umma tace "d'an Alhaji wai yaushe ka koma haka? Saboda rashin kunya yau an sa maka ranan aure shine zaka kira ni ka tambaye ni matarka? Ni kanuwar uwarta ce ko na ubanta?" Mamaki ne ya cika sa tatil, yace "Umma sa rana kuma? Nifa Jaleelah nake nufi?"
Tace "dama Jaleelah matarka ce?"
Shiru yayi yana nazarin me zai ce, tace "zaka sake kirana ka tambayeni matarka sai na tabbata na ci maka mutunci d'an nan"
Yace "Umma ni ba ita nake nufi ba, Jaleelah nake nufi"
Tace "rufa min baki Mara kunya, yarinyar da bata da lafiya ne kake kirana kace min yaushe za a baka saboda ka je ka kai ta asibiti?"
Yace "to ni Umma ai ban san bata da lafiya ba"
Tace "to ai yanzu ka sani, kuma dama ka san can ba gidan ubanka bane bare ka dinga musu zarya a gida kamar yadda kake min, ka kama kanka"
Kasa maganar kirki yayi yace "to Umma sai da safe"
Tace "mu kwana lafiya" tare da datse kiran.
Jingina yayi da kujera yana tunani, wai an sa mishi ranan aure, yasan watakila tsiya Umma take masa amma saboda yayi clarifying doubts dinsa ya kira Raheemah, bugu d'aya biyu tayi picking tana fad'in "baby love"
Yace "sweetheart ya kike?"
Tace "I'm cool honey, ina fata kaima haka"
Yace "yea sure. Yanzu nake samun labari"
Tace "name ba?"
Yace "wai an sa mana rana"
Mamaki tayi, tace "oh wai nufinka baka san yau an sa mana rana ba?"
Yace "I'm not so sure, saboda ni ba wanda ya kira ni ya fada min", tace "to yau an sa mana rana, three months aka diba"
Kwakwalwarsa ta yamutse, yace "ina laifin 7months?"
Tace "haka Dad yace yake so ayi, yace ko kwana daya aka k'ara sai dai a fasa auren"
"Raheemah ina da abubuwa da yawa a gabana, ya kamata ace an kara kwanakin aure saboda na shirya da kyau"
"Wane irin shiri? Seven years muna tare baka shirya ba amma ka iya shiryawa auren kaddara"
"Auren kaddara kika ce, pls let's find a way out, Raheemah ban shirya ba"
Tace "everything is left over to you, kasan halin Dad idan yace yana son abu yadda yake so haka za ayi, Abdul idan ba zaka iya aure na bane sai ka fada min"
Yace "haba not at all, gaskiya bani da financial means din yin aure for now", duk fad'a mata yake yi saboda ya kaucewa auren don yayi masa kusa da yawa, tace "I thought gida biyu kake dashi, d'aya nan d'aya kuma can Kaduna, to what's left? Dama wurin zama ne babban abin ji, though bana tunanin zan iya zama a d'aya daga cikin gidajenka"
Yace "saboda me?"
Tace "ka riga ka saka wannan kazamiyar yarinyar a ciki, so gaskiya ba zan iya shigarsa ba, and sai maganar lefe, idan ba zaka yi ba Dad zai yi, sai ka kawo sadaki kawai and ka nema min inda zan zauna"
Yar dariya yayi, yace "Raheemah kenan, to ai talauci ne bai kai nan ba, gida ne shima bani da halin nema miki wanda zaki zauna a ciki sai dai ki zabi daya ko Kano ko Kaduna, and, kudina ba na yin lefe bane akwai abubuwan da nake so nayi da su, sadaki dai insha Allahu akwai shi"
Tace "then fine! Amma bear in mind ni ba zan iya zama a either of your houses ba"
Yace "then baki so na kuwa, saboda banida inda zan kai ki bayan nan, dukiyata ba na k'arya bane, abi komai a sannu baby"
Ajiyar zucci tayi tace "Mom na kira na, sai anjima"
Yace "to bye".
D'akin Mom ta tashi ta tafi ta zayyana mata k'in amincewarta akan zama cikin daya daga gidajenshi, sai dai ya siya mata wani, kuma yace shi bashi da kudin da zai yi lefe for now so ta na so ta fadawa Abba yayi lefen, Abdul din zai kawo sadaki, Mom tace "ai ko yaki ko ya so sai anyi auren nan, duk ya gama soki burutsunsa"
Raheemah tace "amma nifa Mom honestly speaking ba zan iya zama a wannan gidan ba, gidan da ya fara zama da wata banza"
Mom tace "ke dai ki bari ayi auren first, wanne kike so?"
Tace "sai na zauna a nan Kano kusa da ke"
Mom ta ja numfashi ta sauke, tace "amma baki da wayau yarinyar nan, to a Kaduna zaki zauna ita tsinanniyar yarinyar da ya aura ya fake miki da cewar auren taimako dana kaddara ne sai ta dawo nan ta zauna, then we shall see idan dagaske taimakonta kawai yayi ko kuma duk bilhu ne"
Shiru tayi kamar me nazari, sannan tace "yesss Mom! Kuma hakane fa, idan na zauna a nan sarai zai mayar da ni dussa. Sai ranar daya ga dama sannan zai waiwaye ni ita kuwa tana can da miji"
Mom tace "owwho... Kema kya gani, yanzu ki fada masa cewa ke lallai lallai a Kaduna kike so ki zauna idan ba haka ba ya shanya ki a nan yayi gaba"
Tace "to best Mom"
••°••
Tun da ta jiyo sallamarsa daga compound ta tashi ta koma d'akinta, saboda haushinsa take ji sosai, ko bata dauke da babynsa ai ya kamata ace at least ya kula da ita by the virtue of been his wife amma ko kiranta baya iya yi. Mommy kam kallonta kawai tayi su Hadiyya suna amsa sallamar. Afdal da Yaseen suka fita da gudu suna masa oyoyo suka shiga cikin parlour tare.
Zama yayi suka fara gaisawa da Mommy da fara'a sannan Hadiyya ta gaishe shi, sai da suka dan taba hira sannan ya tambayi Mommy ya jikin Jaleelah, tace ya shiga ai tana ciki. Ya tashi ya nufa d'akin ya shiga da sallamarsa, bata amsa masa ba tana tsaye daga bakin wardrobe tana buttoning rigan barcin ta. Ya karisa ciki ya zauna a gefen gadon, yace "ya jikinki?"
Juyowa tayi round ta kalle shi, sannan ta koma d'ayan side din gadon ta kwanta, tana kwanciya wayarta dake kan dressing mirror ta fara ringing, ta tashi ta dauka sannan ta dawo ta zauna a inda ta tashi, Sisi Intee ce me kiran, da murmushi tayi picking suka gaisa, Inteesar tace "ina ta expecting call din ki naji kin kira kina fada min latest news"
Ta kalmashe kafa tace "name?"
Shi kuwa AbdulHakam sai kallonta yake yi, ta k'ara mishi kyau, may be ko don kwana biyu bai zo ya ganta ba ne, daga d'ayar bangaren Inteesar tace "na sa ranan Ya Abdul mana, an sa musu rana dashi da wannan budurwar tashi"
A razane Jaleelah ta d'aga kai tana kallonshi, tace "to zan kira ki d'an anjima kadan"
Tace "to" tare da hanging up. Irin yadda take kallonsa yasa ya tambayeta "lafiya?"
Murmushin takaici tayi tace "ta b'ace"
Yace "meya faru?"
Tace "pls bacci zan yi, dama sakon sa maka ranan aure ka zo sanar min kuma na sani, kawai ka tafi"
Yace "Jaleelah... Wai what on God's green earth do you think you're doing? Kullum sai na fad'a miki yarinta ba hauka bane"
Cikin sanyin murya tace "sai yawan shekaru ne hauka?"
Buga kafarsa yayi a kasa, yace "meya sa kika koma haka?"
Ta d'an harareshi tace "kai ka mayar dani haka"
Ya d'an yi murmushi yace "if that's the case, yanzu me zan miki?"
Tace "just stay away from me, stay away from my life, besides ni ba matarka bace anymore, bana Son ka bana son ganinka, just leave......"
Zuciyarsa gaba d'aya ta karaya, yace "if that will make you happy, I'll surely do it, zanyi duk abinda zai sa ki farinciki"
Cikin tsiwa da raini tace "thanks for that, ka yi tafiyarka kawai, insha Allah ina haifan babyn nan zan kawo maka kayanka, and that's all"
Kamar bai jita da kyau ba, yace "baby?? Which one is that?"
D'aga masa gira tayi tace "ohh.. Ka gani ko? Now, I take a part of you in my womb, da Zarar na haihu zan baka babynka kaga baka da sauran damuwa dani, saboda ma banida muhimmanci a rayuwarka you don't even know what I'm going through bayan babynka ne a jiki na"
Mamaki da farinciki ne suka ziyarci zuciyarshi at once, kamar me koyan magana yace "but... But.. But you never tell me"
Tace "dama kana da lokaci na ne da har zaka San halinda nake ciki, ni kawai ka kyale ni, ya ishe ni haka. This shouldn't be a gospel, ka tashi ka tafi ni bana son ganinka ni bazan iya rayuwa da kai ba anymore"
Idanuwanta sun rufe tana ta antaya mishi ruwan rashin kunya taji saukan lafiyayyen mari, kamin ta bude idanu wani ya sake diran mata har sai da ta amshi lafiyayyu guda biyar. Hakan bai ma Mommy ba ta rufe ta da duka, igiyar rechargeable dake jikin socket ta finciko ta shiga dukanta da shi, taga kamar ma ba dukanta take yi ba ta yardar ta shiga dukanta har sai da ta kai kasa, dukanta take yi tana hanbarinta har sai da Abdul yaga abin ya fara wuce iya misali sannan ya taimake ta ya amshe ta daga hannun Mommy, ran ta gaba d'aya ya b'aci shi kam yana rike da ita a jikinshi tana ta shesshekan kuka.
Cikin fada Mommy tace "da aka daura auren ki abinda na fada miki kije gidanshi ki dinga yi kenan? Saboda iskanci da fitsara kamar wannan mutumin ne zaki dinga kallon kwayoyin idanuwansa kina fada masa duk abinda ya fito daga bakinki? Ba a banza naga baya zuwa ba munafuka ashe shiyasa idan ya zo kike dawowa nan saboda ki dinga mishi rashin kunya kamar sa'anki, to zanyi maganinki wallahi, bazan d'auka ba"
Cikin shesshekan kuka da jan majina tace "kiyi hakuri", daka mata tsawa tayi har cikin kwakwalwarta, tace "bashi hakuri ko in kakkaryaki a cikin gidan nan", ba yadda ta iya hakanan tace "yi hakuri". Mommy tace "a haka ne zaki bashi hakuri kafadarki had'e da na shi? Tsugunna har kasa"
Kamar yadda ta umurceta haka tayi, kneel down tayi a gabansa ta rike kafafunsa sannan ta bashi hakuri ya tsugunna ya tallafota suka mike tare, Mommy tace "kayi hakuri kaji AbdulHakam? Ai ban san haka take maka ba kai kuma baka tab'a fad'a min ba", kasa magana yayi ya sunkuyar da kai, ta kalli Jaleelah da har then kuka take yi a rakube a gefensa tace "dama ki had'a kayanki ki bi mijinki, ki bar min gida"
Ta fad'a tare da jefar da igiyar rechargeable din hannunta ta fice.
Share mata hawayen fuskarta yayi sannan ya sake mayar da ita kirjinsa ya rungumeta yana jin radadin zubar hawayenta. Sun kusa five minutes a haka sannan ya ja ta suka zauna a gefen gado yana ta patting dinta amma ya kasa ce mata komai saboda he felt guilty.
Yace "to ki dauko trolley din mu kwashe kayan, kinji?"
Bata ce mishi komai ba ta tashi ta sauko da trolley din kayanta sannan ta bude wardrobe ta kwaso ilahirin kayanta ta zube su a kan gadon. Tare suka ninke wa'inda ba gogaggu ba suka zuba, ko eye pencil bata bari ba ta kwashe kayanta kaf sannan ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta fito, duk da hawayen dake zuba daga idanuwanta bai tsaya ba.
Zumbulelen hijab ta dauka ta sa, ta d'auki handbag dinta da travelling bag shi kuma yaja mata trolley suka fita parlour, har gaban Mommy ta tsugunna, kukanta ya koma sabo, ta rike kafafunta tana kuka, tace "Mommy dan Allah kiyi hakuri, dan Allah"
Mommy tace "tashi ki tafi nayi, Allah yayi miki albarka, ki daina abinda kike yi kina ji na? Mijinki ne ba sa'an wasan ki ba, ki san irin abinda zaki fada mishi, kin ji ni?"
Tayi nodding alamar eh, Mommy tace "to tashi ku tafi, Allah yayi albarka", sannan ta tashi Abdul ya risina yayiwa Mommy sallama sannan suka fita, ita kam Hadiyya sai cije cije take yi wai Mommy ta daki mata yar uwa.
Da kanshi ya bude mata motar ta shiga sannan ya bude boot ya sa trolley din ya zagaya ya shiga suka bar gidan. Har suka isa gida bata bar kuka ba shi kuma yana jin nauyin bata hakuri, saboda a kanshi ne Mommy tayi mata irin wannan kafirin dukan, rokon shi ma Allah yasa bata tab'a lafiyar babynsu ba.
Bata jira fitowarsa ba ta fita shi ma ya fita ya dauko mata trolley din yabi bayanta ya bude musu kofa suka shiga. A sitting room tayi branch, ganin haka yasa shima ya saki trolley din a nan ya koma gefenta ya zauna, yana tunanin ta yadda zai fara bata hakuri, ya riko hannunta yana caressing, sofly yace "are you okay?", rufe idanuwanta tayi still bata bar hawaye ba, yasa hannu ya share mata hawayen, a hankali yace "I'm sorry Ameerah" tayi shiru ba tace komai ba, yace "do you still insist we go on our separate ways?"
Tayi mishi nodding alamar a'a sannan ta bude idanuwanta gami da gyara zama, tace "dan Allah saki nawa ka min?"
Da confidence dinsa yace "ni ban sake ki ba Jaleelah, wallahi, idan ma baki yarda ba ki kira Umma, I just wrote I love you, and nothing else, kawai tana so ta dinga b'ata min rai ne but ni ban sake ki ba", ta jinginar da kanshi a kafadarta, tace "to meya sa zaka kawo mace gidan mu? Gidan auren mu"
Shi sam ya manta da zuwan Raheemah kuma baya tunanin da akwai evidence na fadin haka, yace "Jaleelah kina zargi na ne? Ban taba kwanciya da wata mace ba tun kamin nayi aure sai yanxu ne da nake da aure Zan yi haka?"
Tace "to shikenan I'm sorry, amma nasan ka kawo wata gidan nan, don't argue me", har yayi tunanin ko wani ne a Layin ya gansu shine ya kira ya bata labari, yace "what are you thinking of me?", bata amsa mishi ba ta janyo handbag dinta ta bude, ta fito mishi da scarf din da ta gani ta mika mishi, da mamaki ya kalli scarf din, bai san sanda yace "it's for Raheemah" ba
Wani zafi taji a zuciyarta tashi a fusace zata wuce ya riko ta ya zaunar da ita.