Surutu take ta faman zubawa kanuwarta mai bi mata, Hadiyyah, bata damu ba data na sauraronta ko bata sauraronta ba, ita dai ta amayar da abinda ke cikin ta shine damuwarta, Hadiyyah sai dai tace mata eh ko a'a, ko u'um, a haka suke tafe suna trekking zuwa high way don taran commercial vehicle zuwa makaranta, Hadiyyah bayan particular answers dinta data ke bata ba ta canja su ba, har sai da suka kusa kaiwa high way zasu yi crossing, lokacin wani me navy blue peugeot406 ya zo ya wuce su ya hau kan high way ya nufi inda zashi, sai a lokacin Hadiyyah tayi magana tace "Jaleelah me motan nan fa khaki yake sawa", ba tareda ta kalle ta ba hankali a kwance tace "ina ruwanki? Motarshi tinted amma har kin hango shi, mtchw", tace "wlhy dagaske nake fada miki, khaki yake sawa", ba tareda wata damuwa ba Jaleelah tace "toh how does it affect me? Ya sa barrack idan yaga dama", Hadiyyah tayi banza da ita, tasan idan ta biye mata zata iya 6ata mata rai kamin su kai makaranta. Sukayi crossing hanya suka tari mini bus suka shiga, wanda zai sauke su a kasan flyover daga nan su sami keke napep ya kai su schl dinsu dake Kumasi road. Jaleela na ss2, hadiyyah kuma na jss2. Suna shiga schl sai ga Ni'imah ta fito daga class da sauri, da yake akwai windown dake facing schl gate din, ta hango su through there, tana karisowa suka rungume juna cikin murnan sake ganin juna, bayan musabahan da Ni'imah da Hadiyyah sukayi, sai Hadiyyah ta kama hanyar upstairs, a can class dinsu yake, a secondary section ajinsu Jaleelah ne kadai yake downstairs, saboda sunfi ko wane class yawa a schl din, su 54 ne a ajinsu, inspite of it been a private school, sabanin sauran azuzuwa masu dauke da students in few, daga 30 and below. Ni'imah da Jaleelah sunata fara'awa junansu, Ni'imah tace "ammata how ws ur weekend?" Jaleelah tace "tws lazy girl", tace "always, evry weekend is lazy to u, Allah ya shiryeki, yasu mama?" Tace "lau lau, yasu Ruqayya da Ihsan da Muhammadu Ghali?" Tace "suna nan qalau, baki ce ya Faruq ba", Jaleelah ta murguda mata baki, cikin tsokana, tace "sai dai sarkin garinsu", suka fashe da dariya, tace "kin manta ne, toh ni bari na tambaye ki, ya Khaleefah?" Ta harareta, tace "ban san shi ba", Ni'imah tace "ke dai kika sani, u cnt argue it, kina son shi fiye da tunanin me tunani, that's the fact". Jaleelah bata so su cigaba da maganar Khaleefah, tace "ke mu tafi class, classes will soon start, Ni'imah tayi dariya, tace "ai dole kice a tafi, saboda baki son gaskiya, mu dai 'yan bayan khaleefah ne, nan bada jimawa ba zamu kai ki Sokoto", Jaleelah tace "Allah ya kiyaye hanya, sai kin dawo". Suka kama hanya suka wuce class, sukayi suspending hirarsu zuwa dan wani lokaci. Bayan an gama first period, Ni'imah ta matso daf da Jaleelah, tace "wai kun sake samun misunderstanding da Khaleefah ne?" Jaleelah tace "ki barshi, ya cika rainin wayau ne, I don't know y, khaleefah ya raina ni, ina yi mishi abu kadan sai yaji haushi, sai kawai kiji mu a break". Ni'imah tace "ai sai da na ayyana a raina, kun fiye rikici dake da shi, and dis x true love", Jaleelah tayi tsaki, tace "ke kika ga true love, kina ji wai yana fada min zai auri wata cousin dinshi, Allah dai yasa wasa yake min, wai gayen nan saboda rainin hankali, har yake fada min hankalinshi a kwance, kiji ikon Allah fa", Ni'imah tace "toh mene ne a ciki? He's 30years, u r 17years, sai yaushe kike tunanin zaki aureshi, ko so kike yi yayita zama a haka yana jiranki, while sa'anninsa suna can suna making family?, ke kuma gashi kince ba daga gama secondary zaki yi aure ba", Jaleelah tace "and so? Na tabbata a irin son dana ke wa khaleefah da nice zan iya jiranshi, anya ma wai yana sona kuwa? Cox I cnt believe what's happening, kuma mumun ce min yayi yana nan zuwa ya ganni a karshen month din nan, best day ov my life, at last zamu ga juna dani da Khaleefah, shekarun mu biyu kenan muna dating" Ni'imah tace "dagaske zai zo?" Tace "haka dai yace min, Allah dai ya kaimu", tace "ameen, me kike shirya mishi?" Tana rufe baki sai ga malami ya shigo, yama danyi jinkiri, Jaleelah tace "ki bari during break zan fada miki". Suka mayar da hankalinsu ga karatu, bayan dan jawabin da malamin yayi yasa su suka firfito da note book dinsu, yayi musu dictating note. Jaleelah duk ta kosa ya fita ta fadawa Ni'imah abinda take shiryawa cweerienta, sai dai tun kamin period din ya kare sai ga next teacher ya tsaya yai kikam a bakin kofa, yana jira ayi ringing malamin dake ciki ya fita shi kuma ya shiga. Motsi daya biyu sai Jaleelah ta duba time dinda ke hannunta, which seems to be interminable. Bayan malamin ya fita, class rep dinsu yabi bayan malamin don kiran malami na gaba, sai akayi rashin sa'a ranan he's absent, good news kenan a wurin students, "teacher's absence" nan da nan Jaleelah tayi completing note dinta, ta dawo da dubanta ga Ni'imah wacce take ta jiranta ta kammala note din, tace "muna magana, me ma kika tambaye ni?" Tace "ban sani ba, kina sane kike tambayata", tace "ke fa mutum ne wlhy, sai nace ma na fasa fada miki", tace "kar Allah yasa ki fada, dama baki ga dama bane, dalla wai me kike shirya masa ne??"
Jaleelah tace "for now dai ba wani abu, akwai dai wani riga da skirt da aka dinka mana nida kanne na, atamfan ba laifi tana da 'dan kyau, last week din nan na fara sawa, so na aje ta ita zan sa idan zai zo, na za6i mayafin da zai shiga dashi, har naga haduwan da zanyi ranan, hatta cosmetics da inner wears din da zan sa ranan na aje su a side daya kar a sama hitch, amma ina so na siya sabon takalmi, cousin kuma tace zata mai girki, kin san I'm not that familiar with cooking, ba wai don ban iya ba, kawai dai na tsani girki ne, idan akwai aikin gidan dana tsana to shine girki, gidan su kaka zan je na aje shi, na siya sabon perfume, just for my Khalee", Ni'imah tace "ai na riga na fada miki, u cnt argue it, kina son khaleefah fiye da tunaninki ke kanki, bama tunanin wani ba", tace "na sani, ba sai kin fada min ba, okay? Hal fahimti?" Tace "ke shut up!! Ban son iyayi, ya isa haka, yanzu dai ki tabbata kin shiryawa Khaleefan mu better, kin gane dai ko?" Tayi murmushi, tace "can't wait to see him!!!", ba wanda yake saka musu baki idan suna hiransu, Jaleelah ta daura kanta bisa desk tareda lumshe idanuwanta, "I love u khaleefah, u my one and only.... Habibiy, looking forward to ur arrival!". Ni'imah ta kura mata idanu, yau tana ganin ikon Allah, akan mutumin da bata ta6a gani ba amma duk tabi ta rude, gashi ya girmeta da kusan 13years, kiris ya rage ya haifeta, haduwan facebook amma duk ta rude a kanshi, a wurinta khaleefanta ya fiye mata kowa kyau, duk kudin guy, haduwarsa, kyawunsa, darajansa, da ficen family name din mutum, bai isa Jaleelah ta kula shi ba, khaleefah ya fiye mata kowa ne namiji. Matukar ke kawarta ce toh sai kin san khaleefah, a gidansu hatta mamanta tasan sunan Khaleefah a bakinta, bata iya kwana ba tace ma wani Khaleefah kaza Khaleefah kaza ba, har sai da mamanta ta gaji ta fara mata fada sannan ta rage, amma fa bata daina ba, tana ciki.
Aka share wannan month din Jaleelah ko waya basuyi da Khaleefah ba, sakamakon dan karamin sa6anin da suka samu. Khaleefah yana fama da girman kai da alfahari, ita kuwa jaleela tana fama da fadin rai da gadara, gani yake tunda shike gaba da ita itace ya kamata ta kira shi tayi apologising, ita kuma gani take mace tana da martaba, don haka shi ya kamata ya kirata ya bata hakuri, idan ba haka ba sai dai su rabu, gashi anyi 1month bai kirata ba itama ba ta kirashi ba, ko sun hadu a facebook kowa sai dai yayi sha'aninsa, ita kuwa Ni'imah kusan kullum sai ta tambayi zuwan Khaleefah, tana son abinda Jaleelah take so, amma sai dai tace mata he's busy, amma yana nan zuwa, hakan kuma bai sa Ni'imah ta daina tambayar zuwanshi ba, amsan ta daya ne, he's busy, amma yana nan zuwa. Ita kanta Ni'ima tana mamakin irin soyayyar Jaleelah da Khaleefah, kuma ba ayi musu sulhu, da kansu suke shirya kansu.
[4/4, 8:21 PM] +234 803 829 7611: ⚜Mijin Jaleelah⚜
2
Linah✍🏻
Sai da suka share wata daya da kwana tara sannan Khaleefah ya cire girman kai ya kira Jaleelah, lokacin data daga wayarta taga call din Khaleefah ne taji wani farinciki ya mamaye zuciyanta, har sai da gabanta yayi faduwan mamaki, cikin hanzari ta daga wayar, cike da farinciki, amma kuma bata nunawa Khaleefan ba "ha..l..llo" kai zaka ce baza tayi magana ba, khaleefah yayi shiru na kusan 3secs, sannan yace "ya kike?" Itama sai da tayi shiru na kusan 3secs, sannan ta amsa mishi "lafiya qalau" maganar ta a ciccije, yace "Jaleelee kin share ni, kin ture gomnatin khaleefah", tace "Khaleelee har kana da bakin fadin haka, ban fadi haka ba sai kai?" Yace "eh dama toh ya za ayi ki fadi haka, bayan its ur fault, idan nace kinyi laifi sai ki dinga tuhumana kina so sai na fada miki abinda kika yi sanka sanka, filla filla, muyi ta muhawara, yanzu haka zamu yi auren ki dinga yi min musu?" Jaleelah ta 6ata fuska "musu kuma?" Yace "ofcourse, musu mana, ban isa in fada ki ji ba" abin ya bata haushi, ohh wato nufinshi ma bata da wadatacciyar tarbiyyan da zata yi mishi biyayya kenan, 'wannan ma harda iyayena ya zaga ba ni kadai ya zaga ba' tace "malam bafa sa mana ranan aure a kayi ba, so for that matter ba zaka dinga gindaya min sharruda ba, saboda mene ne zan dinga making small mistakes ka dinga yi min fada kamar wata 'yar cikinka, ya kamata ka gane akwai babban banbaci tsakanin auren zumunci da auren bare, niba wannan so called fiancee din taka bace da kake zagewa ka dinga karantawa rainin wayau" "what? Jaleelah! Khaleefah ne fa" cikin kuna kuni tace "toh mylove.. Ai kaine... Dunno what to say, m sorry, kaji?" Dama abinda yake so yaji ta fada kenan, shi yafi karfin ya fadi haka, yace "its okay mylove, there's no need to say sorry, yanzu dai ya kike?" Tace "qalau qalau" yace "toh, dama zan fada miki nan da 3months aure na fa, anyi postponing" mtchew, tace "naji, Allah ya sanya alheri, zan iya ce maka sai an jima" yace "Allah ya kaimu Jaleelah, na gane ba wai Jameelah bace baki so saboda kishi, nine baki so" cikin fushi, Jaleelah tace "duk yadda ka fada haka ne, idan ka ga dama kace m ur worst enemy, or ur best, duk abinda ka fada haka ne, bye" ta fada tareda yanke wayarta, tana ta zuba tsaki, amma fa tana son Khaleefah, duk iya misunderstanding din da zasu samu ko da bayan 5months ne sai sun shirya. Amma dai yau Jaleelah ta shaqa abinda Khaleefah yayi mata, idan ya kuskura ya fara auren Jameelah toh ita kam baza ta aure shi ba, ai rainin wayau ne tayi soyayya dashi lokacin da yake single ta kuma aureshi bayan ya auri wata, tufiakwa! Bata ta6a ganin Khaleefah ba shima kuma bai ta6a ganinta ba, sai dai suyi chatting a facebook da whatsapp suyi exchanging pics, a haka kuma suna masifar son junansu.
Bayan faruwan haka da 7days, Jaleelah da yar kanuwarta, Hadiyyah suna tafe suna hira just as usual, Jaleelah nata zuba kamar kurna, bata da matsala da a saurareta ko kar a saurareta, amma ka'idane sai ta bata labari. Suka isa highway don crossing sannan su sake crossing dayan hannun, tun daga nesa Jaleelah ta hangi wani guy fari mai 'dan tsayi, kamar yadda ta saba ganin Khaleefah a pics dinsa, sai dai wannan yafi Khaleefah haske, da sauri ta dafa 'yar kanuwarta, tace 'Hadiyyah kalli Khaleefah, gashi can dashi da wani guy a jingine da wancan vibe din" Haddiyyah tace "na ganshi, dama kunyi dashi zai zo ne?" Tace "a'a, ina tantamar ko shine ma, cox rabonda muyi waya mun kwana biyu, bana tunanin shine, amma fa da kamar wuya idan bashi bane", suka tsallaka hannu na farko, guy din yana ta binsu da idanu, Jaleelah kuma bata fasa surutun ba, ta cigaba da abinda ta keyi tareda kawar da kanta gefe, jikinta ya riga ya gama bata Khaleefah ne da abokinsa, ta tabbatar da hakan ne kuwa bayan sun tsallaka, suka tari mini bus suka shiga, shigarsu keda wuya shima ya shiga motarsa, abokinsa ma ya shiga seat din gaba, sukayi U-turn suka wuce, dama akwai wani U-turn kusa da wurin, ya koma cikin gari. Girman kai ya hana shi yayi mata magana, ya ganta 'yar karama, duk da haka kuma yana sonta, ita kuma fadin rai yayi mata katutu, ko kallon inda yake batayi ba, hasali ma juya ma side din da yake baya tayi. Tana zuwa schl ta cewa Ni'imah "yau fa naga wani kamar Khaleefah na a hanyan mu na zuwa schl, da wuya in ba shi bane" Ni'imah tace "toh kun dai yi magana ko?" Tace "nice zan mishi magana? Zai mutu kuwa, garin mu fa ya zo, sannan ya kasa min magana sai nice sakarya sai na mishi magana" Ni'imah tace "dani ce kuwa dana yi mishi magana, nace malam ai kuwa naga kamar na sanka" Jaleelah ta ta6e baki, tace "ji sokonci, mtchw" Ni'imah ta dan duketa a kafada, tace "sokuwa kawai!!" Dukansu suka yi dariya.
[4/4, 8:21 PM] +234 803 829 7611: ⚜Mijin Jaleelah⚜
3
By Linah Shams✍🏼
Bayan 3days, a hanyar Jaleelah da Hadiyyah na zuwa highway suka sake ganin me peugeot406 din nan, ya zo ya wuce su, yana zuwa 'dan gaba sai yayi parking, Jaleelah na ganin motarshi ta wuce tace "la Hadiyyah ga mutumunki", tayi murmushi, tace "ai faaah! Wai mutumina, daga ce miki khaki yake sawa shike nan ya zama mutumina" Jaleelah tace "eh mana, wani yace ki dinga kalle kalle" dai dai lokacin suka isa inda motar tasa take, suna isa yayi winding glass din motarsa, yace "are you going my way?"
Jaleelah ta dan kalleshi, sannan tace "yes", yace "shall we...?" Ba tareda ta sake cewa komai ba ta kai hannu zata bude kofar gidan baya, yace "no, yu get in to the front seat", ta zagaya ta shiga, ya bude mata ta ciki, ta shiga da sallamanta, ya amsa mata, sannan ta gaishe shi cikin harshen hausa, although shi da turanci yayi mata magana, sai ta mayar da harshen hausa, ga mamakinta kuma sai taji ashe ya iya, bayan sun hau kan highway sun fara tafiya, yace "I'm Abdul-Hakam, my nieces and nephews usually call me 'uncle abdu', and that becomes my other name 'uncle abdu' Abdul-Hakam Muhammad Jafar, I relocated to your area a couple of months ago" idanun Jaleelah na kan highway, tace "welcome" yace "thank you, I've been seeing you two together, are you sisters?", tace "eh, kanuwata ce" yace "toh ke ya sunanki?" Tace "Jaleelah, kanuwata kuma Hadiyyah"
Yace "nice, Aunty Maya Memorial School right?" Tace "eh", yace "toh bari nayi dropping dinku, sai na wuce wurin aikina", suka cigaba da tafiya, a inda yake ta ba su Jaleelah labari game da rayuwar karatunshi, yana ta basu courage, sun 'dan yi hira, sannan yayi dropping dinsu a bakin school din ya wuce. Jaleelah taji dadi sosai, yayi musu kirki.
Sir khaleefah kuwa yana can yana jiran kiran Jaleelah ta bashi hakuri, ita kuma tace ba yadda za ayi ta sake kiranshi, shi zai kirata ya bata hakuri, ya 6ata mata rai. Soyayyar Jaleelah da Khaleefah sai su. Yana can yana shirye shiryen aurenshi da Jameelah, itace za6in da iyayenshi suka mishi, amma shi harga Allah Jaleelah yake so, yana da burin aurenta.
Yau 3weeks kenan da haduwarsu Jaleelah da Uncle Abdu, amma har yau basu sake haduwa ba, da kusan kullum sai sun ganshi idan zashi wurin aiki, amma yanzu kuma sun daina ganinshi tun bayan daya basu lift. Sai dai Jaleelah ta ta6a ganin motarshi ta zo ta wuce ta layinsu da yamma, amma tasan bai gane ta, kuma bai zama dole ya rike fuskanta ba, haka itama, bata kalli fuskanshi ba bare idan ta ganshi a gaba ta gane shi, motarshi da plate number dinshi ne kadai take ganewa, amma ko sa mata wuka za ayi ba zata gane shi ba idan suka hadu a hanya ba, hakan yasa ko kallon side din da motar take bata yi ba ta cigaba da tafiyarta.
[4/4, 8:21 PM] +234 803 829 7611: ⚜Mijin Jaleelah⚜
4
By Linah Shams✍🏼
Jaleelah da Khaleefah sun share kwanaki masu yawa ba tareda sun yi magana ba, kuma a haka da daya zai kira daya so zasu yi, sai dai kowa jiji da kanshi ba zai bari ya kira dayan ba. A haka harsu Jaleelah sukayi first term sukayi hutu, sai da sukayi resuming sannan Khaleefah ya kirata, wani farinciki mara misaltuwa taji yayinda call dinsa ya shigo wayarta, hannunta na rawa ta daga wayar ta kara a gefen left ear dinta "ha...l..llo" ya amsa mata da "hum", tace "mylove.... I missed yhu" shima haka ya fada mata, sannan yace "Jaleelee wai kin daina so na ne?", tace "me ka gani mylove?", yace "you don't care about me anymore, ko ki kira ni kice min HML", Jaleelah ta zaro idanu waje, tareda 6ata fuska, duk da ba wai yana gani bane, tace "wai dagaske ka keyi kayi aure Khaleelee?" Yace "Jaleelah me zai sa na miki karya, wlhy nayi aure last week, ko na ba amaryar wayan ku gaisa ne? Cox na riga na fada mata muna yin aure zan aure ki", tace "har kana wlhy? Nifa duk a zatona wasa kake min", yace "kin ta6a jin inda akayi wasa da aure, na bata wayar ku gaisa ne?", wani mummunan kishi ya ziyarci zuciyanta, tace "Khaleefah!" Yace "na'am Jaleelah", tace "matarka tana bukatar shan zagi?" Yace "what do you mean?", tace "kar ka kuskura ko a mafarki kace zaka bani matarka mu gaisa, don zata sha zagin da tunda uwarta ta haifeta bata taba sha ba! Ko don kaga ni karamar yarinyace shiyasa ka raina ni irin haka, bari kaji Khaleefah, ni Jaleelah nayi maka alkawarin duk dadi, duk sanyi, duk tsanani, duk wuya, duk so, duk kiyayya, duk tsanani bazan ta6a aurenka ba! Over my dead body!! Allah sai ya saka min, you wasted my time knowing that you are not going to marry me. Bye!" Ta fada cikin tsawa tareda hanging, tana aje wayar Khaleefah ya sake kiranta, zata so ta amsa, tana son shi fiye da tunaninta, amma ya zama dole ta kiyaye shi, ita ya 6ata mata lokaci amma yaje ya auri wata, yana mata karyan cewa wai dole iyayenshi suka mishi ya aureta. Bayan three missed calls din da yayi mata sai ga text message dinsa ya shigo wayarta, sai da ta kusa 5mins sannan ta dauki wayar ta bude, ta fara karanta sakon kamar haka
““Jaleelah bance dole ki aure ni ba, kuma bance dole ki cigaba da so na ba, amma ki sani, kamar yadda nine first love dinki, haka ya zama dole na zama mutum na farko da zai fara dandana dadinki, yadda ni kika fara so, ya zama dole dani zaki yi loosing virginity dinki, matukar kikace ba zaki aure ni ba. Ba wanda ya isa yamin shishshigi a harkan rayuwarki, saboda ni na raine ki a soyayya, so be informed””
Ta gama karantawa cike da raini irin wanda ke tsakaninka da mace idan kace kana sonta, ko da kuwa kai ka yankewa kasa cibi, ba ruwanta da fada maka maganan banza, tayi mishi reply da “zan ji zan gani. Ba kuma zan aureka ba, Mara mutunci sakarai nitwit! I regret ever knowing you aswear”. Tana turawa tayi deleting both nashi da nata harda contacts dinshi, hatta pictures dinshi da ilahirin messages din da ya turo mata da Wanda ta tura mishi kaf ta goge su tare da chat dinsu na social media.
[4/4, 8:23 PM] +234 803 829 7611: ⚜Mijin Jaleelah⚜
5
By Linah Shams✍🏼
Nan ta dasa aikin zaman jiran reply dinsa, amma har garin Allah ya waye bai kirata ba kuma bai bata reply ba, idan har kasan Jaleelah da yawan fara'a da faran faran dinta da barkwanci to ranan zaka gane cewa she isn't in mood. Gaba daya sai shan kunu take yi, wai saurayinta yayi aure, takaici ya kamata, tana zuwa school ta fadawa Ni'imah, amma Ni'iman ce mata tayi kawai ta hakura ta aure shi idan ta kammala secondary schl, Jaleelah tace ta riga tayi alkawari ba zata ta6a auranshi ba, lokacin tana cikin fushi, amma tayi nadama, she's to keep her words now, ba zata auri Khaleefah ba, Ni'imah ce mata tayi Allah yasa haka shine mafi alheri. Amma kuma taki fada ma kowa cewa Khaleefah yace zai yi disvirgin dinta, gani take abin kunya ne ta fada ma wani, she rather keep her mouth shut.
Washe gari da safe, bayan sun isa bakin highway ita da Hadiyyah, sai ga wata prado wacce ta sha tint ta zo tayi parking a gabansu, duk a zatonsu wani ne aka bama lift zai sauka a nan ko kuma mai motan ya tsaya yin wani abu, ko kallon wurin ma basu yi ba, sunata hira abinsu, wasu guys ne suka fito su hudu, suka tsaya zagaye da inda suke su, fuskansu a daure, sun sha sun glasses, dayansu yace "wace ce Jaleelah a cikinku?", cikin rawar murya Jaleelah tace "nice, gani nan, anything?", kasancewar suna kusa da motan ne, na kusa da motan ya bude mata gidan baya, yace "get in!", tace "and why?", tana rufe baki ya ciro bindiga ya seci Hadiyyah dashi, yace "choose one, loss your sister or get in", ba musu Jaleelah ta shiga motar, ta juya ta kalli Hadiyyah, tace "as long as I'm alive, bazan ta6a bari wani abu ya cutar dake ba, matukar ina da daman da zan iya hana hakan, your prayers sis!" Nan kuma ta fara hawaye, kamin ta sake magana wani ya shiga ya zauna a gefenta na dama, daya kuma ana hagu, daya kuma a seat din gaba, sai fourth one kuma a seat din driver, suka hau kan kwalta suka mike hanya. Motar taji tint, ba wanda zai ganta bare ya taimake ta, glass din motar duka a rufe suke. Sai da suka kusa 45mins suna tafiya sannan wanda ke zaune a seat din gaba ya ciro wayarsa ya fara shafawa, cikin wasu 'yan mintoci ya mikowa Jaleelah wayar, tareda fadin "ko kin san wannan?" Tana gani gabanta ya fadi, Khaleefah ne, saboda raini da kayan da yaje inda suke hawa mota dashi ya dauki hoton saboda ta gane shi, tace "eh", yace "alright, wurinshi zaki", gaban ta ya hau dukan uku uku, tana hawaye tace "dan Allah kar ku kaini wurin Khaleefah, don soyayyarku da Allah, Khaleefah kashe ni zai yi, ku taimake ni, nasan you've sisters at home, ba zaku so a musu abinda Khaleefah yake shirin yi min ba", wanda ke 6arayin damanta yayi mata tsawa "shut up! Bloody fool!!" tayi tsit, tana tunanin yadda haduwanta da Khaleefah zata kasance, dagaske yake yi zai keta mata mutuncinta? Ko dai yana so ne kawai ya ganta? Allah kadai masani, nan ta hau yin addu'o'i iri iri tana rokon Allah. Bayan nan ne sai na seat din gaban ya miko wani kyalle, na left side dinta ya amsa, na seat din gaba yace mishi "yi aiki da wannan", nan take ya kulle mata idanu da kyallen.
[4/4, 8:23 PM] +234 803 829 7611: ⚜Mijin Jaleelah⚜
6
By Linah Shams✍🏼
Hankalinta duk ya gama tashi, wani tsautsayi ya sata ta fadawa Khaleefah maganar banza? Bakinta ya ja mata, dama ta sani tace ya bawa matar tashi su gaisa, da yanzu ta kai schl, Hadiyyah fa? Allah kadai masani. Ta shiga wata duniyar tunani, bata san sanda suka isa wani makadeden gida ba wanda bata san a wani unguwa yake ba, ba kuma tasan yanda akayi suka isa ba saboda idanuwanta a rufe suke. Bayan motar ta tsaya cik, suka bude mata kofa suka ce ta fita, kamin nan sai da suka bude mata idanuwanta, sannan ta fito, tana fitowa sai drivern yace "Shayo, lead her in", ba tareda an umurceta da tabi bayan Shayo ba ta bishi, suka dinga shiga sako da lungu suna wucewa, tana tunanin yadda zata yi ta ba Khaleefah hakuri, wata zuciyar kuma tace kar ta bashi, zai rainata.
Atlast dai suka isa cikin wani bedroom, Shayo yace ta shiga ciki, tana shiga ya mayar da kofan ya rufe, kafafuwanta suka fara rawa, hannayenta har wani zufa suke fitarawa na musanman saboda tsabar tashin hankali.
Karan ruwan da taji a toilet din dakin ya tabbatar mata da cewa Khaleefah ne a toilet din, duk ta kosa ya fito ta bashi hakuri ya barta ta tafi gida, tasan by now hankalin gida ya tashi, an nemeta ba a ganta ba, tasan Ni'imah ma hankalinta zaiyi mugun tashi saboda sunyi sabo da juna.
Tayi nisa cikin tafiyarta a duniyar tunane tunane, sai dai ji tayi ance "Madam sama wuri ki zauna mana, amaryan Thabit", da sauri ta kalleshi, tareda komowa cikin hayyacinta, Khaleefah ne, daga shi sai towel daure a waist dinsa, sai kuma wanda ya sagala a kafadarsa, ya wuce kan gadon ya zauna, ya dubeta, yace "Mrs Thabit, come over hah!".
Tsira mishi idanu tayi, ya sake nanata maganarsa, sannan tace "Khaleefah let me go!" Yace "you are free to go, je ki", ya fada tareda yin shrug, ta juya ta murda hannun kofan, amma anyi locking, gabanta ya buga da karfi, idanunta suka kada suka yi jaa, tace "look Khaleefah, dan Allah ka zo ka bude ni, bana son irin wannan wasan" ba tareda ya amsa mata ba, ya mike ya nufo inda take, yana tafiya majestically, yayinda take ta komawa da baya, a haka har sai da ta kai jikin bangon daki, Khaleefah ya zo daf da ita, yace "you are in hand Jaleelee", tasa hannayenta ta ture shi, ba wai don tafishi karfi ba ya matsa baya, fuskansa cike da dariyan cikar buri, yace "Jaleelah kenan, kina tunanin akwai abinda zaki iya yine? Wannan dan karamin bakin nan ai shi ya ja miki" yayi pointing bakin nata, "Nifa na riga na fada miki, kamar yadda ni na fara sonki haka ni zan fara shiganki, kin fahimta?" Tace "zan dai fahimta, dallaah malam ka zo ka dube min kofa, ko ce maka akayi ni yar iska ce?" Yayi wurgi da towel din dake kafadarsa so violently, sannan ya sake komawa inda take, tun kamin ya karisa ta tsugunna har kasa, tace "Khaleefah look here, I'm on my knees, dan martaban iyayenka kayi hakuri ka barni na tafi" bai ko bi takan abinda take fada ba ya daga ta tsam, ya direta akan gado, yana ajeta ta tashi da sauri zata dira, ya rungumota, yayinda ta fara kokarin guduwa ya turata baya sannan ya fadi a jikinta, ya fara kissing dinta kota ko ina, ya janye hijabinta yayi hurgi dashi, tanata ihu tana fadin "Khaleefah!! Noooo, don't do dis to me!!! Please"
[4/4, 8:23 PM] +234 803 829 7611: ⚜Mijin Jaleelah⚜
7
By Linah Shams✍🏼
Shi kaam ko saurarenta baya yi, tanata dukanshi amma ina.. Yayi nisa, har cizonsa sai da tayi, amma kamar bashi ta ciza ba, nan kuma yafa kokarin 6alle buttons din schl shirt dinta, ta dinga kokarin dakatar da haka, amma batayi nasara ba. Khaleefah yayi ta squeezing dinta dai dai da son ranshi, idan ya gaji ya tsotse ta, idan ya gaji yayi squeezing br***st dinta, ko yayi romancing dinta, fuskarta tuni ta 6aci da hawaye da majina, ba zaka ce Jaleelahn data tsaya ta gama ca6a ado bace da zata fito daga gida, tun tana ihu har ta gaji ta koma yin addu'o'i, yanata kokarin janye mata skirt Allah ya bata sa'a ta kucce masa, tana kokarin mayar da kayanta yayinda Khaleefah ya zauna yana mayar da numfashi yana kallonta.. "Ohh God! You're hot babe!!!" Ita kuwa Jaleelah banda kuka ba abinda take yi, tana gama mayar da kayanta ta tsugunna ta dauki hijab dinta, ta dubi Khaleefah, tace "bazan ce maka Allah ya isa ba, amma Allah sai ya bi min hakki na akan ka" yayi dariya, yace "Jaleelah look, bakinki ya ja miki, wlhy banida mata, I was kidding you girl, sai kika dauka da zafi kika fada min magana, and I can't bear leaving you like this, full virgin? Oh no babe!, come here love, let's make it, bafa inda zaki" tace "gaba tafi baya yawa Khaleefah, duniyace, akwai Allah", yayi mika, yace "Jaleelah! Kin san wane ne ni kuwa? You have no clue who exactly am, ke karamar yarinyace, and you arer lovable, na so ace kin kwantar da kai kinci arziki, amma kin kasa" tace "kai ne matalauci faqiri, bakayi arzikin da zan kwantar da kai naci ba", yace "au bakin ki bai mutu ba har yanzu? Lallai bakiji damk'a ba, amma bari na ta so miki" yana rufe baki sai ga Shayo ya bayyana a dakin, yana fadin "excuse me sir, someone is here for u" kamin ya rufe baki ta bangaje shi da karfi ta bar dakin, ta bayyana a wani babban parlour, yayinda Khaleefah ke ta fadin "run after her! After her!" da gudu tabi ta wata kofa, ta dinga shiga tana fita tana shiga tana fita har ta bayyana a fakadeden tsakar gidan da aka kawata shi da flowers amma tashin hankali bai barta ta kalli komai ba. Bayyanarta a compound din yayi daidai da lokacin da wata mota ke shigowa, idanun Jaleelah suka rufe, ta dumfari gate din da gudu ta fice, kafafuwanta ko takalmi babu, yayinda guys din Khaleefah suka bi bayanta, amma sun kasa ci mata, gudu take kamar akan iska, basu barta ba har sai data fara shiga ghetto area, sannan suka juya, abin ba nasara, hakanan suka hakura suka koma wurin Sir Khaleefah na Jaleelah, sun sha masifa, saboda haka ne yace zai cire 25% daga cikin payment dinsu.
To 12:15pm
Jaleelah ce zaune a dakalin wani gida, ta gama gajiya saboda gudu, ga yunwa, ta fito gida ba tareda tayi breakfast ba cox sun so su makara. Schl bag dinta na wurin Hadiyyah, bata da ko sisi a tare da ita bare ta sa dan ci wani abu idan ta gani. Layin kamar ba mutane, ba wanda ya zo ya wuce tunda ta zo ta zauna, gashi ana neman 2pm.
Hadiyyah kuwa tun bayan wucewansu Jaleelah da mutanen Khaleefah ta koma gida tayi reporting. Ta kuma shaidawa Mummynsu sakon da Khaleefah ya turowa Jaleelan, sai yayi abducting dinta, ta tambayeta a bisa wani dalili yace zai dauke ta, amma Hadiyyan sai cewa tayi itama bata sani ba, Jaleelahn bata fada mata ba. Amadadin Mummynsu ta tausayawa halinda 'yar tata ta shiga, amma sai ta hau fada "ba yadda ban yi da ita ba ta daina wannan soyayyar facebook din, taje ta kare ta yayibo aljani, bata da zance idan ba na wannan guntun Halifan ba, yanzu wa gari ya waya? Wannan fa rashin kunya ne ma irin nata, ta rasa yadda zata yi ta bishi su gudu shine suka hada baki ya zo ya dauke ta sai ace an sace ta ko? zamu gauraya dani da ita, wato tana nema ta zubda mana da mutunci a idon duniya, shine ta bishi can suje su sheke ayarsu, jiya fa ba yau bane, zata dawo da kafafuwanta ta same ni" nan ta kira mahaifinsu ta fada mishi, Jaleelah fa ta bi saurayinta sun gudu, abin ya mishi zafi, ji yake kamar a mafarki, toh guda nawa Jaleelan take? Da har ta san tayi eloping? Lallai zai yi maganinta matuqar ta kuskura ta dawo gidanshi, kuka in dai aure take so toh ta kwana gidan sauki, idan ta dawo bayan ta amsa queries dinsa zai mata auren, kamin ta dauko mishi abin kunya! Da faduwar girma ai gara karayan arziki.
[4/4, 8:23 PM] +234 803 829 7611: ⚜Mijin Jaleelah⚜
8
By Linah Shams✍🏼
Har past 4pm Jaleelah na zaune a wajen, ba wasu mutanen kirki da suke wucewa ta wurin bare ta sami wani ya dan taimake ta, ana haka ne sai ga wani dattijo ya zo wucewa, Jaleelah ta daga jajayen idanuwanta suka yi four eyes, cikin ladabi ta gaishe shi, ganin bai ta6a ganinta ba a unguwar tasu gata kuma sanye da uniform ya jefa mata tambayar "kun ta so makarantan kenan?" Jaleelah tace "a'a baba, ban ma ko sami daman zuwa ba ma" ta fadi hakan ne don ya tambayi bahasi ya dan taimaka mata ta koma gida, yace "lafiya baki je makaranta ba?" Tace "wani ne ya sa aka dauke ni daga hanyar makaranta aka kaini wani gida, shine Allah ya taimake ni na kwaci kaina na gudu, gashi banida kudi bare na koma gida, ga yunwa", cikin tausayi dattijon yace "ya Allahu! Toh fa! Mutane me suka dauki duniyar? Mece ce ita? Guda nawa take? Yanzu a wani unguwa kuke?"Ya fada tareda saka hannunsa a aljihu, Jaleelah tace "premier cresent" ya zaro N500, ya mika mata sannan yace "yi maza gida yarinya, na san ana can ana cigiyarki, kya samu kici abinci a hanya" Jaleelah tace "nagode baba, ta ina ne hanyan?" Yace "ki mike hanyar nan kawai, zata kai ki har babban kwalta" Jaleelah tayi mishi sallama tareda godiya sannan ta wuce. Taje bakin highway ta tsayar da wani me napep, bata san wace unguwa bace nan, ce masa kawai tayi "Malam premier cresent, nawa zaka kai ni?" Yace "ki bada N650" da sauri tace "haba Babana, zan dai baka N300" da kyar ya yarda ya kaita a N400, hakanan ta shiga, har sai da suka fara kaiwa kusa da arean su sannan ta fara gane gari, duk ta kosa ta isa gida taga Hadiyyah. A dai dai kofar gidansu mai napep din ya sauke ta, cike da farincikin dawowa gida ta shiga gidan, dakin Mummy ta fara wucewa, idanuwanta suka yi mata tozali da Hadiyyah a kwance tana kallo, ta mika tankalinta kacokan ga TV, da sauri Jaleelah ta karisa kusa da inda take, tace "Keeee!!!" Fuskarta cike da murna, Hadiyyah ta tashi zaune, tace "laaa Jaleelah! Ya akayi suka barki kika dawo?" Jaleelah ta zauna a gefenta, tace "wannan labari ne mai tsawo, wlhy yunwa kadai nake ji, Mummy fa?" Tace "ai Mummy na nan tana jiran dawowarki, tace zaku gauraya, tana can a kitchen" tace "me nayi mata kuma? Kin fiye zolaya, abin ayi min murna na dawo gida shine kike zolayata" tana idar da maganarta Mummy ta bayyana a parlourn, Jaleelah ta tashi da sauri ta nufi inda take cikin fara'a, ba tareda Mummyn tace mata ko uffan ba ta ja hannunta suka nufi bedroom dinta, tasa key ta rufe kofan, ta cirewa Jaleelah schl hijjab dinta, ta janye skirt dinta yayi kasa, ta ja riganta da karfi ta gaba, buttons din suka rabu da rigan, ta fincike shi gefe, jikin Jaleelah ya rage daga skin tight din da take sawa beneath her skirt wanda bai wuce iya gwiwa ba sai vest din dake jikinta, tana ta kallon ikon Allah, tace "Mummy lafiya? I'm okay fa, ba abinda ya faru", bata amsa mata ba, ta bude chest drawer ta ciro dorinanta mai baki daya, ta shiga watsa mata ko ta ko ina, ta fara kuka tana bata hakuri, amma taki daina dukanta, tayi ta zananta tana zaginta, tayi mata lilis, ta dauki almost an hour tana dukanta, sannan ta kyaleta, ta fita ta barta a dakin, Jaleelah ta kwanta a kasa tana kuka, gunin ban tausayi. Tafi 15mins a kwance a wurin sannan ta tashi ta bar dakin ta koma dakin kwananta ita da Hadiyyah, can ma ta kwanta taci kukanta son ranta, sai bayan sallar magrib sannan ta tashi ta shiga toilet. Ta yo wanka tayi alwala sannan ta fara rattafa salloli, sai afta isha sannan ta tashi akan sallayan. Bayan nan ne kuma Daddynsu ya dawo, kamin ya fara aiwatar da komai sai da ya tambaya "ina Jaleelah?" Aka ce mishi tana dakinsu, nan yasa aka kirata, sai daya mata kafurin duka sannan ya kyaleta, sannan yace mata "kuma daga yau kin bar sake jerawa da Hadiyyah don ba zaki sake zuwa makaranta tareda ita ba, bazaki lalata min d'iya ba ki goga mata shashancin da kika je kika koyo, and for ur own information, zan miki aure kwanan nan, indai ba zaki iya kama kanki daga maza ba, ki fadawa dan iskan yaron da kika bi ya turo iyayenshi a daura muku aure ku tafi can ku karata, idan kuma bai turo ba toh ni zan hada ki da wanda naga dama, kuma bazan hada ki da 'dan mutunci ba na cuce shi, da mara mutunci zan hada ki me kama dake, tashi ki bani wuri! Stupid as u are!!" Jiki na rawa ta tashi ta bar dakin tana hawaye "idan mafarki nake yi zan so na farka daga wannan mummunan mafarkin!" Cewar Jaleelahn. Ranan ta kasa cin supper dinta saboda tsabar bakin ciki da takaici, idan da ce mata akayi Khaleefah zai iya yi mata haka da sai ta karyata, saboda tsabar son da take mishi to zata iya zagin mutum in dai a kan Khaleefah ne, bayan ko ganinshi bata ta6a yi ba sai sanadiyyar wannan incident din, sai dai kuma ta ganshi a hoto.
[4/4, 8:23 PM] +234 803 829 7611: ⚜Mijin Jaleelah⚜
9_10
By Linah Shams✍🏼
Jaleelah ta gwadawa Khaleefah so, shine first love dinta, gata teenager, hakan yasa Khaleefah yake juyata yadda yaga dama, idan yace kar ta fara ta fita yau, toh ko kofar gida ta bar lekawa, ko da kuwa unguwa zasu tafi duka gidan, idan ya hanata magana da mutum hanuwa take yi, yau idan Khaleefah yace tayi blocking dinka a facebook sai tayi, komai mutuncin da kuke yi. Yanzu ne data dan kara girma take iya bijirewa umurnin sa.
Washe gari da safe, suka yi shirin schl, bayan sun gama shiryawa Daddynsu ya kira Hadiyyah yace ta jira driver ya zo, shi zai dinga kaita makaranta henceforth, ita kuma Jaleelah ta cigaba da bin commercial vehicle, idan ta ga dama daga can ta shiga duniya, she's free. Zaka yi mamaki idan da zaka bude zuciyar Jaleelah 'har yanzu son Khaleefah take yi, ba taki ace ya kirata su shirya ba'.
Abdul-Hakam ne tafe a motarsa, yana driving cikin nishadi, ya zo dai dai da inda ya tsaya ya bawa su Jaleelah lift, sai lokacin ya sake tunawa da su "Allah dai yasa they are doing okay, tun ranan da muka hadu na basu lift har yau ban sake ganinsu ba, Allah dai yasa lafiya", yana ida zancenshi call ya shigo wayarshi, MyRaheemerh, shine sunan dake ta kai komo a screen din wayar, ya kalli wayar yana mai murmushi, ya na jira kiranta ya gama ringing ya kirata, haka kuwa akayi, parking yayi a gefen hanya, sannan ya kira MyRaheemerh, sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta daga. "Hello sweerie" Abdul yayi murmushi, sannan yace "dearie ya kike?" Tace "lafiya qalau, ina fata hubby na yana cikin koshin lafiya" yace "alhamdulillah, ina hanyane ma, zan tafi wurin aiki", cikin kulawa Raheemah tace "toh muje na raka ka, ko baka son rakiya ta? "Yayi murmushi yace "ai ko ina zani ina tare da ke", taji dadin jin hakan daga gare shi, tace "wow! Dear gobe fa zan koma, how I wish I can see you once more" yace "I wish so also dear, but bana tunanin it's possible" cikin shagwaba tace "dan Allah ka zo, pls kaji?, kaga Daddy yace idan na tafi bazan sake dawowa ba har sai na kammala karatuna, nan da six months kenan, ba zuwa nayi two days na koma" yace "Raheemah it will hardly be possible, sai after 5pm nake isowa gida, yaushe na dawo na shirya har na zo Kano, sannan na koma? Think about it dear" ta dan yi murmushi, tace "na gane nufinka, ka hadu da wacce fuskarta ta fi tawa kyau a idanuwanka, that's why baka damu da ganina ba yanzu, wata ta riga ta kwace min kai, kuma laifi na ne" ta fada cikin zolaya, yace "how is that your fault?" Tace "da na yarda an daura mana aure tun tuni da shikenan, amma yanzu kam ai kaga laifi na ne" yace "kema kinga laifin naki kenan, kar ki damu dearie, ai kamar gobe ne in Allah ya yarda" tayi murmushi, tace "kar ka manta fa you promised to marry me Abdul" yace "its always on my mind Raheemah, in sha Allah" tace "toh, ni dai gobe kamin 5pm bana tunanin ban bar 9ja ba, shikenan yanzu ba zan ganka ba, anyway, bye, anjima sai muyi magana, okay?" Yace "its okay, bye" suka yi sallama tareda hanging call. Sannan ne Abdul ya hau kan hanya don tafiya wurin aikinshi kamin ya dauki lokaci mai yawa ko ya makara.
* * *
Bayan wucewar Hadiyyah da driver ne Daddy ya bawa Jaleelah transport fare da break money dinta, sannan ta kama hanya ta fito gida, tana tafiya tana hawaye, wani bakin cikin duniya ya taru ya tattare mata a zuciya, tafiya take tanata tunane tunane, hankalinta sam bashi a jikinta, bayan ta dan yisa da tafiyarta akayita mata hon kamin a kariso inda take, amma bata ji ba, Uncle Abdu ne, har ya zo kusa da ita yana mata hon, still bata ji ba, kuma tana tafiya gashi tana dumfaran high way ne, sai da ya sake mata hon sannan ta waiga ta kalli side din da motar take, yayi winding glass din motar suka yi four eyes yayinda hawaye ne kadai ke tsiyaya daga idanuwanta, ya bude mata kofar seat din gaba ta ciki, ta shiga sannan ta rufe kofar. Cikin ladabi tace "ina kwana?" Yace "lafiya qalau, kin tashi lafiya?" Tace "lafiya qalau, yasu Hajiya" yace "suna nan lafiya qalau, although dai ba a nan take ba, tana Kano, a can suke, nan gidan yayana nake zama kamin na gama nawa a Yarwa close, ina Hadiyyah?", tace "ta wuce" da sauri yace "yau kuma?" Ta girgiza kai alamar eh, yace "it seems you are not okay Jameelah" ta tsani sunan nan, sunan wacce ta zama barrier tsakaninta da saurayinta wanda kusan koda yaushe tunaninsa yana kwakwalwarta, bata iya hada good 15mins ba tareda ta tuna dashi ba, gashi kuma ya kirata da shi, nan ya sake tada mata da takaici, tace "Uncle Abdu Jaleelah, not Jameelah", yace "noticed, meke damunki kike tafe kina kuka? in akwai abinda ke damunki kamata yayi kije ki samu wani ku tattauna and sort a way out, ba ki dinga tafiya kina tunane tunane ba, wani abun Allah ya kyautan ka iya samunki" tace "da wa?" Yace "your friends and family man" tace "I trust no one anymore" cikin zolaya yace "harda Uncle Abdu?" Tana ganin girmanshi, duk da sau daya ta ta6a ganinshi, alamunshi sun nuna yana da kirki, hakan kuma ba wai ya tsame shi bane, amma fa hardashin, tace "noooo.....!" Yace "toh, meke damunki?" Tace "nothing..... It's not that much serious" yace "but it is... Ina jinki, kuma sai kinyi min alkawarin gaskiya zaki fada" gabanta yace durum! Gaskiya kuma? Bata tunanin zata iya fadawa wani abinda ya hadata da Khaleefah, saboda a ganinta abin kunya ne ta tsaya tana fadi, jin tayi shiru yace "ke fa nake saurare" tace "okay........" Jaleelah ta cire jin kunya ta fadawa Uncle duk yadda sukayi da Khaleefah ba tareda ta 6oye mishi wani abu ba, cox akwai abinda sai ka fadama wani sannan ka samu relief, tana yi tana kuka, hatta haduwarsu a facebook bata 6oye mishi ba, sai da ta bayyana mishi komai, yanayin yadda yake lallamarta ne yake kara bata courage wurin fada mishi komai, ta karishe fadin abinda ya faru a gida tsakaninta da iyayenta cikin kuka mai tsanani, tareda fadin "kuma Daddy yace aure zai yi min!!" Uncle Abdu ya juyo da sauri ya kalle ta, yace "aure? why? Toh wa zaki aura? Khaleefahn?" Tambayoyi ne da bata bukatar ta amsa mishi, saboda amsoshinsu suna cikin labarin, kuma ba abinda ta 6oye mishi, tace "yes.. Ba Khaleefah zan aura ba, wai zai hada ni da mara mutunci irina, ba zai hada ni da 'dan arziki ba ya cuce shi, Uncle Abdu believe in my words.. Wlhy I'm a virgin, ni ba 'yar iska bace, ni ko hannun namiji ban ta6a rikewa ba saboda wani dirty thoughts, amma yau gashi Daddy na kira na mara mutunci, I really don't know whatelse to do" ta jingina da seat din tareda maida kallonta sama, cikin tausayi yace "kar ki damu Jaleelah, ki dinga yin addu'a, idan Mummy da Daddy basu san komai ba ai Allah ya sani, kuma shi ba azzalumi bane, amma dai ki daure kiyiwa Mummy magana, zata fi fuskantar ki" "Mummy bata magana da ni anymore" yace "Hadiyyah fa? Ki mata magana sai tayima Mummyn" tace "nope, an raba mana daki, Daddy yace kar ya sake ganina tareda ita, wai kar na lalata musu yarinya, tun jiya bamu sake yin magana ba," yace "Ya Salam! I'm sorry, yanzu baki magana da ita?" Tace "sai dai idan zata tambayeni, amma babu hira, dakin mu ma ba daya ba, gashi ina jin tsoron kwana ni daya a daki, but I've to endure it, jiya na kwana cikin tsoro" yace "ki dai dage da addu'a, yanzu dai from now on ki dinga fitowa 6:55AM zan dinga daukan ki da safe, da rana kuma sai ki dawo da kanki, is it okay?" Ta girgiza kai da sauri, tace "thank you. Thanks a lot, yayi" suka cigaba da magana yana bata shawaran ta dage da addu'a a haka har suka kai AMMS. Yayi dropping dinta tayi godiya ya wuce.
[4/4, 8:23 PM] +234 803 829 7611: ⚜Mijin Jaleelah⚜
11
By Linah Shams
Jaleelah ta shiga school fuska a murtuke, idanuwanta sun kumbura sunyi jaa, daga ganinta kasan she isn't in mood. Ta shiga class, direct seat dinta ta wuce, bata tsaya yin musabaha da classmates dinta ba kamar yadda ta saba, ta zauna ba tareda ta kalli kowa ba, Ni'imah wacce ke wani row ta zo seat din da sauri ganin qawallinta ta zo, cikin fara'a ta bata hannu suka yi musabaha, Jaleelah ta koma gefe ta jingina da bango, Ni'imah ta zauna, tace "Jaleelah ya dai?" Tayi shiru kamar bata jita ba, Ni'imah tayi tsaki, tace "kar ki fada" shima shiru tayi bata amsa mata ba, ta kwantar da kanta akan desk saboda bata son damu. Ni'imah itama ta shareta, bata ce mata komai ba, malamar da zata dauke su first period ta shigo, kowa ya tashi ya gaisheta amma Jaleelah ta cigaba da kwanciyarta taki tashi, malamar tace kowa ya zauna ita kuma Jaleelan ta tashi, sai tayi pretending kamar tana barci, Ni'imah ta dan duki bayanta, Jaleelah ta dago da kanta, ta kalli Ni'imah, tace "mene ne?" Cikin harshen Hausa, hakan kuma ya sabawa dokar makarantasu kuma yayiwa malamar tasu zafi. Ni'imah tace "Aunty" ba tareda ta mata bayani saboda tasan ta fahimci sakon da take son isar mata na cewa malama ta shigo, sake mayar da kanta kan desk din tayi ta rufe idanu. cikin fushi malamar tace "hey look up!" Jaleelah ta dago ta kalleta, tace "stand up and remain like that" ta tsira mata idanu kamar bada ita tayi magana ba, "are you deaf or dumb?!" Ta cigaba da kallonta, tace "then get out of my class" ko motsi taki yi. Malamar ta aika aka kira mata sargent, tayi tunanin tun kamin zuwanshi Jaleelahn zata mike ta bar class din saboda yadda kowa ke masifar jin tsoronsa amma ta cigaba da zama, bayan ya shigo, ta nuna mishi Jaleelah, tace "give her ten good strokes" Jaleelah ta cigaba da zama, Ni'imah ta fita daga seat din, ya fara dukan Jaleelah, amma sai nunawa tayi kamar ba ita yake duka ba, yayi mata guda goma kwarara, amma ko alamun nadama babu a fuskanta balle tayi kuka, abin ya chaki malamar, hakanan ta kyaleta tunda bata da niyyar barin class din, ta 6arayin Jaleelah kuwa, bakin cikin da take ciki yafi bulalan schl, don haka an dade ba a duketa ba. Ranan through out ba wanda ya isa yayiwa Jaleelah magana ta amsa mishi, hatta principal sai da ta zo ta tsaya mata, amma taki motsi, har suka fara tunanin ko jinnu sun shafe ta ne, hakanan suka haqura suka rabu da ita. Akayi closing ta fita ta bar class din, ko kallon side din da Ni'imah take bata yi ba. Ta fita wajen school taga Hadiyyah a tsaye, ta manta sam Daddynsu ya hanasu wata mu'amula, taje kusa da ita tace "Hadiyyah" tana rufe baki Hadiyyan ta wuce ta bar wurin, sai lokacin ta tuna da rule din Daddy, ta fara hawaye, ta tari napep zuwa wurin Fly over daga can ta hau mini bus ta tafi gida, tana tafe tana hawaye a haka har ta kai gida, ta shiga daki ta rufe kanta, sai da tayi kuka ma'ishi sannan ta tashi tayi sallar azahar, tana idarwa bada dadewa ba aka kira sallar la'asar, shima tayi, ta kwanta ta cigaba daga inda ta tsaya. Bacci ya kwashe ta, sai afta six sannan ta farka.
Washe gari da safe, bayan ta kammala shirin tafiya school taje wurin Daddy ta amsa transport fare da break money dinta, tana ta sauri ta fita kar ta 6atawa Uncle Abdu time, tana kaiwa dai-dai junction sai gashi ya iso. Ranan da kanta ta bude kofan front seat suka gaisa, cikin fara'a ya kirkiro zance gudun kar su zauna shiru shiru. Ranan kamin yayi dropping dinta sai da ya amshi phone number dinta, saboda kubcewan tsaro ko idan dayansu yayi latti, sannan ta mishi bye bye ta shige school. Bayan ya kama hanyar tafiya wurin aikinshi ya fara tunanin Jaleelah, 'daga gani salihan yarinya ce, shi yasa hankalinta ya tashi da aka ce za a aurar da ita ga mara kirki, abin tausayi, gashi iyayenta sun ki tsayawa su ji asalin abinda ya faru, suna blaming dinta akan komai. Allah dai ya sa a aura mata mai mutunci, Allan kuma yayi mana za6i mafi alkhairi, shine kawai abin cewa' da tunaninta ya isa wurin aikinshi.
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
12
By Linah Shams
A school kuwa Jaleelah ta tsayar da magana da kowa, hatta Ni'imah, bata magana da kowa, aminiyarta ce, amma a halin da ake ciki ta cire yardanta akan kowa, mai yihuwa idan ta fada mata abinda ya faru ta kasa rikewa taje ta fadama wani, gashi kuma abin kunya, ai kuwa da Ni'imah ta shiga uku ta gama lalacewa a wurinta, amma dai maganin ayi kar a fara, gara kar ta fada mata balle har taje ta bada labari. Sai dai ta zauna a seat tayi ta kallon kowa cikin annashuwa, ita kuwa tana cikin matsanancin hali, za a mata aure, zata auri wanda bata sani ba, Khaleefah kuma bai yi aure ba, but he's yet to, 'toh ko dai na kira Khaleefan ne na fada mishi baba yace ya turo in dagaske yake yi?'.
* * *
Uncle Abdu ne zaune a parlourn apartment din da yayanshi ya bashi a gidanshi, yana ta conference call da best friends dinsa; Basheer, Munawwar da Mustapha, yakan dauki kusan 60secs ba tareda yace komai ba, sai dai yayi ta saurarensu, "nifa Munawwar ko, wlhy totallyn yarinyar nan bata min ba, bata min bane....! Ni ban san ya akayi ba Abdul-Hakam ya maqale mata" cewar Basheer kenan, Mustapha yace "Malam, idan zaka je ka nemi mata kaje ka nemi mata, cox wannan yarinyar ba mata bace, muna mata ce, gaba daya she lack manners", Munawwar yayi dariya, yace "zaku je dauko yan matan amarya ai nan bada dadewa ba, ko ya AbdulHakam?" Yace "kwarai kuwa, nan bada dadewa ba, tunda nan da 5-6months zata kammala karatunta ta dawo gida, sai aure kuma" Basheer yaja tsaki, yace "malamai ni nayi nan, sai anjiman ku, dana san idan aka hada conference din nan maganar wannan doluwar zaku yi da banyi picking ba", yana rufe baki Munawwar yace "nima dai bari in sata, bye guys" Mustapha kuwa ko sallama bai musu ba ya dira daga kan layi, bada jimawa ba conference call din ya kawo karshe. Shi kuwa Abdul yana son Raheeman shi sosai, ba wanda zai zauna mishi da ita, shi zai zauna da kayanshi, amma ba zai iya rabuwa da ita ba, duk da yasan she is somehow immoral. Nan yaji muryarta kadai yake son ji, yayi deciding ya kirata su dan yi hira, ya lalubo contact dinta yayi dialling, call din na shiga tayi caraf ta dauka
"hello dear" ya amsa mata da "ya kike wifie?" Da sauri tace "lafia qalau" kamar tana jira yayi magana, yace "kawai sweet voice dinki naji ina son ji" tace "toh I'm sorry ka bari anjima I will call U, yanzu ina cinema ne" cinema? Wacce aka tura makarantan? Yace "dake da wa kuka je?" Yana jira yaji an lissafo suna irin su Fatima, Zainab, Khadeeja, Salma and so on, sai yaji tace "da Muslih ne da Nawas, da Victor" yace "Jaleelah har yanzu baki daina yawo da maza ba?" Da sauri tace "Jaleelah kuma?" Yace "oh sorry I mean Raheemah" tace "dama wacce ke ranka kenan, toh ka bata shawara ta kaurace ma rayuwarka, haduwana da ita ba zai yi kyau ba" yayi dariya, yace "kin fiye kishi Raheemah, sunan ne kawai ya zo baki na" tace "toh, bye dai, talk later" bata jira ya amsa mata ba tayi hanging call din ta cigaba da abinda take yi.
Sanin kan shine Raheemah tana da matsaloli da yawa, babban burinshi shine suyi aure, in Allah ya yarda bayan aurensu zata daina duk shirmen da take yi, shine fatan shi.
Bayan 3days, da safe, ranan Hadiyyah ta riga Jaleelah wucewa school, Jaleelah taje ta amshi kudin data saba amsa a hannun Daddy, ranan shima ya dan yi lattin fita, bayan ta fita ta dan fara tafiya sai ga Abdul, yayi parking ya dauketa, a daidai lokacin Daddynsu Jaleelan ya fito daga gida, ya hangeta ta shiga motar, "wato har yanzu tana bin dan iskan yaron nan" abin yana daure mishi kai, duk dukan da ka mata a gida bai hanata binshi ba, mafita daya ce kawai, ya gaggauta aurar da ita, main desire dinta ya girmama. Ya tsaya yana kallon motan cike da mamaki har suka 6ace mishi.
Bayan gaisuwar da ya shiga tsakanin Jaleelah da Abdul ba abinda ta sake ce mishi, shine daya ga shirun ya fara yawa yace "Jaleelah na kusa aure fa" tace "MashaAllah, Allah ya sanya alkhairi, yaushe ne?" Yace "ba a riga an sa rana ba" cike da mamaki tayi dariya, tace "wani aiki sai kai Uncle Abdu, ko rana ma ba a sa ba, a ina zaku zauna?" Yace "bana fada miki ina aikin gidana ba, toh yanzu na kammala, wasu 'yan abubuwa kadan ne suka rage" tace "toh Allah ya tabbatar da alkhairi, ya sunan Auntyn?" Yace "Raheemah, soulmate dina" tayi murmushi, tace "Allah ya sanya alkhairi" ya amsa mata da "ameen". Suka dan taba hira kamin su isa bakin school dinsu yayi dropping dinta ya wuce.
Da dare, Daddy yaje ya sami Maman su Jaleelah, ya shaida mata cewa "Jaleelah fa har yanzu bata daina bin shaidanin yaron nan, yau ma da safe shi ya kaita makaranta, da idanu na guda biyu na gan su, I don't know what exactly is wrong with this girl" Mummy tace "hakanan za a aura mishi ita a rabu lafiya" yace "hakan shine kawai mafita, muma mu huta, tunda auren take so, in ba haka ba ina ga the next time da zan sake laying hands dina a jikinta zan kusa nakasa ta"
Bayan anyi haka da kwana biyu, Daddy ya sake ganin Jaleelah a motan Abdu da safe, sun hadu a kan highway, yana hangensu suna hira harda dariya. Da ya koma gida bai cewa Mamansu komai ba, don ya san idan ya fada mata abubuwa ba zasu yi kyau ba, sai ya nuna kamar bai ganta ba, washe gari ma ya sake ganinta, nan ma ya nuna kamar bai ganta ba, jiran lokaci kawai yake yi yasa guy din ya turo iyayensa a daura auren, ko da kuwa ba lokacin zasu tare ba. Ita kuwa Jaleelah tana nan jiya e'yau, kullum cikin damuwa, fargaba da zullumi, iyayenta basu hira da ita, sun hana Hadiyyah magana da ita, sai dai ta zauna ita daya a daka kamar maiya, kuma wannan abun ya faru gaba daya akan Khaleefah ne. Abdu kadai take hira dashi had tayi dariya.
Ranan Wednesday Jaleelah ta kwana da zazza6i mai tsanani, ta kasa fadawa kowa bata da lafiya, ko tsoron da take kwana a cikinsa duk dare ya isa ya haifar mata da zazza6i, ga kuma damuwar data ke ciki. Abdul-Hakam kadai ta fadama bata da lafiya da suka yi waya a daren ranan, yayi yayi da ita taje ta fadawa Mummy bata da lafiya amma taki, har ta gaji tace masa zata je, not knowing that ba inda taje, hakanan ta kwanta, baccin ta rabi da rabi saboda azaban ciwo a haka had gari ya waye.
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
13
By Linah Shams
Da safiyar Thursday
Ta kasa ko tashi tayi wanka tayi shirin school, da kyar ta samu tayi alwala tayi sallah a kwance, lokacin tafiya school yayi amma shiru bata fito ba, hakan yasa Daddy yaje har dakinta ya duba ta, ya ganta a kudundune cikin blanket, daga bakin kofan ya tsaya, yace "baki da lafiya ne?", tace "eh" muryarta kasa kasa tana rawa, yace "sai kije ki shirya mamanku ta kai ki asbiti" yana gama fadin haka yasa kai ya fita ya bar dakin, yana fita sai ga call din Abdul-Hakam ya shigo wayar Jaleelah, tana rawan sanyi ta kai hannu tayi picking, ga mura ya toshe mata hanci, muryarta sai tayi dadi, tayi pressing button din amsa kiran, ta kara wayar a kunni, "Assalamu alaikum" ya amsa mata da "Ameen wa alaiki salam",
"ina kwana?"
"Lafiya qalau, ya jikin?" "Alhamdulillah", ta ja wani dogon numfashi tareda huro iska daga bakinta, har sai da yaji karan, yace "kin yiwa Mummy magana kuwa?", tace "a'a, yanzu haka ma kana waje kana jira na ko?" Yace "wlhy kam, nasan dai jikin ne shiyasa ban ganki ba", tace "yau ba zani school ba, yanzu zamu tafi asibiti da Mummy", "Allah sarki... Allahumma yashfiki" tace "ameen" "anjima zan kira ki in Allah ya yarda" "Allah ya yarda" "ameen, bye" " 'alright, bye", tayi hanging call din.
Bayan ta kammala shiryawa cikin lace dinta ash mai kwalliyar pink da purple hijabinta wanda bai wuce giwanta ba ta fito parlour ta zauna, tana tafiya kamar zata fadi, ba wani karfi a jikinta, bata dauki 10mins da zama ba sai ga Mummyn ta fito daga dakinta, tana tafe sauri sauri, "oya tashi mu tafi" ta fada fuskarta a daure, yayinda tayi gaba ta fita ta bar parlour ta wuce inda motarta take, Jaleelah na biye da ita, ta shiga seat din gaba ta zauna tayi dunkum, ta rasa meke mata dadi a rayuwa, tayi loosing appetite dinta, bata jin cin komai, ko ruwa bata jin sha, amma zata so taji voice din Khaleefah. Tunda suka shiga motar ba wanda yace ma wani uffan, ita dai Mummy hankalinta ta mika shi ga driving, ko nuna akwai mutum a cikin motar bata yi, a haka suka isa asibitin.
Bayan sunga doctor ne ya shaida musu cewa ya kamata a kwantar da Jaleelah, za a sa mata drip. Mummy bata yi musu ba tace ayi admitting dinta. Suka je aka daurawa Jaleelan drip, bayan sun kammala komai, Mummy ta kama hanya ta bar asibitin, tace mata ba zata iya zama a asibiti ba, tana da yara a gida, amma kamin ta tafi sai da ta sami wata nurse tace ta dinga duba mata ita, kamin nan sai da suka yi negotiating.
2:45PM Abdul ya kira Jaleelah ya tambayeta ya jikin sai take fada masa an ma yi admitting dinta, ya fada mata in Allah ya yarda yana nan zuwa ya duba ta kamin ya wuce gida. Bayan Mummy ta koma gida ta kira Daddy ta fada masa an kwantar da Jaleelan, yace in Allah ya yarda da yamma in ya tashi daga wurin aiki zai wuce asibitin ya duba ta.
Da misalin 5:20PM AbdulHakam ya isa Lafiya Clinic don dubata, wata nurse tayi leading dinsa zuwa ward din. Jaleelah na kwance tana kallon sauran patients din dakin, ana ta zuwa gaishe su 'yan uwa da abokan arziki, ita kuwa tun safe da akayi admitting dinta banda wannan nurse ba wanda yake zuwa duba ta, tana cikin wannan tunani ne taji anyi sallama anata gaishe gaishe, tana waigawa taga Abdul ne ya shigo, hannunsa dauke da wata leda, tun kamin ya iso take ta faman murmushi har ya karisa inda take, ya zauna akan wata kujeran roba dake gefen gadonta, cikin fara'a tace "Uncle Abdu ina wuni?"
Yace "lafiya ba lafiya ba" da sauri tace "me kuma ya faru?" Yayi murmushi, yace "toh Jaleelah bata da lafiya, ya jikin naki?" Tayi murmushin jin amsar shi, tace "Alhamdulillah, I'm getting better" yace "MashaAllah, Raheemah tace a gaishe ki da jiki" tace "ina amsawa, ka fada mata wuri na zaka zo ne?" Yace "eh a'a, ban ce mata wurin Jaleelah zani ba, na dai ce mata zani wurin wata kanuwata ne gaishe ta a asibiti" tayi dariya, tace "meyasa baka ce mata wurin Jaleelah zaka ba" da sauri yace "kai... Jaleelah kina so na shiga trouble ne?" tace "hum! Uncle Abdu yana tsoron matarshi" yayi dariya yace "ai dole, my one and only Raheemah" "Allah da ya barku tare"
"ameen".
Bayan sun gama 'yar hirarsu sai ya bata ledan, yace fruits ne ya siya mata, tayi godiya, to 6PM suka yi sallama ya tafi.
Allah ne bai sa zasu hadu da Daddy ba, don yana fita suka shigo tareda wani nephew dinsa Murayyan. Bayan gaisuwa da kuma ya jiki? Ba abinda ya sake hadashi da Jaleelah, a tsanake ya tsaya kare mata kallo, duk tayi baki ta rame a cikin kwanaki kadan, sai dai sam yarinyar bata tausayin kanta, don da tana tausayin kanta da bata kara shiga sabgan yaron nan ba, bayan barazanar da yayi mata na aurar da ita hakan ma bai sa ta shiga hankalinta ba, ba zai taba zaba uba mai shiga haqqjb diyarsa ba tunda har ta nuna auren take so hakanan zai mata don ba sai ta fito fili ta fada mishi cewa aure take so ba, bai yi 10mins ba ya tashi suka tafi. Kasancewar nurse din da aka sata ta dinga kula da ita a asbiti yar unguwarsu ce yasa Mummy ta bata abinci da dare tace ta kaima ta can, in taji zata iya ta kwana da ita, idan kuma ba zata iya ba ta dawo gidan iyayenta ta kwana, gobe sai taje ta duba ta, ita kuwa Miss tace gara ta kwana a gidansu, dama dai ranan da take da night duty ne sai ta dinga kula da ita sosai. 9:35PM dot nayi Jaleelah ta dauki wayarta ta kira Abdul ta mishi godiya da kuma jin ya koma gida lafiya, sun dan yi hira sannan suka sauka akan layi.
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
14_15
By Linah Shams
Hadiyyah tana missing sisternta so much like kilode, tana ji tana gani an hanata magana da ita, su hudu ne kacal a gidansu, mata biyu maza biyu, yanzu sai dai ta dinga magana da Afdal da Yaseen, ba kuma ta jin dadin hira dasu.
Washe gari da safe ta so ta bi Mummy su je asibitin tare, amma ta hana ta, tace ta bari sai gobe weekend sai su tafi dasu Afdal, amma for now ta shirya ta tafi school, hakanan ta hakura ta tafi goben sai taje, ita kuma Mummyn ta shirya taje mata da breakfast ta duba ta. Iyayen Jaleelah suna matukar son ta, 6acin rai ne kawai ya sa suka juya mata, shima ba wai don basu sonta bane anymore, sai don ta gane kuskurenta, mace ya kamata ta kasance mai kamun kai da kiyaye abinda zai iya zubda mata da mutuncinta da martabanta. A school kuma ba wanda ya san Jaleelah bata da lafiya, idan aka tambayi Hadiyyah sai dai tace tana gida, amsar kenan. Daddy da Mummy sun yi shawara akan zuwa duba ta, idan Mummy taje da safe, sai daddyn yaje da yamma, Murayyan dake zaune a gidansu kuma ya dinga kai mata lunch da dinner, ita kuma Mummy ta dinga kai mata breakfast.
Washe gari da safe kamin Abdul ya tafi wurin aiki sai da ya kira Jaleelah, sannan daga baya ya kira Raheemah suka dan ta6a hira. Ya shaidawa Jaleelah zuwanshi anjima da yamma in Allah ya yarda. Ba wanda ya isa ya kira Jaleelah tayi picking sai Abdul, cox iyayenta ma ba kiranta suke yi ba, bayan call din Abdul bata amsa na kowa. Ta ji sauki sosai, ji take yi kamar likita na shigowa yace yau za ayi discharging dinta, ba inda yake mata ciwo yanzu. Mummy, Yaseen, Afdal da Hadiyyah suka je asibitin da safe duba Jaleelah ranan saturday, bayan gaisuwa da ya jiki Mummyn bata sake tanka mata ba, Hadiyyah kuwa kamar ba wacce suke hira suna dariya ba, bayan sannu bata ce mata komai ba, Afdal ne kadai yake ta dan surutan shi tana taya shi, da yake shine last born.
Ta side din Khaleefah kuwa, mahaifinshi ya sa shi gaba, zai aura masa Jameelah, wacce a da ya nuna ya aminta da aurenta, a yanzu kuma yana nema ya bijire ma hakan. Wutar soyayyar Jaleelah ce take ruruwa a cikin zuciyar shi take cin shi ba sassauci, ya rasa da wasu idanu zai kalli Jaleelah?, da wani murya zai kirata yayi magana da ita?, bai mata adalci ba, kuma bai sake kiranta ba, ya kamata ya kirata ko don yayi apologising, yasan yayi mata laifi, amma baya tunanin zai iya magana da ita, kunyar abinda yayi mata yake ji. Hakan yasa yaje ya sami wata Auntynsa kanuwar mahaifinsa, ya girmeta da 4years, she's 26years kenan, ya shaku da ita sosai, in dai sirrinshi kake bida toh kaje wurin Suhairah, Khaleefah ya yarda da ita sosai, ya kuma amince da ita. Yayi mata bayani one after the other, cewa shifa Jaleelah yake so, ita yake so ya aura, kuma ko da zai auri Jameelah toh sai ya fara auran Jaleelah, ya bata labarin duk abinda ya faru ba tareda ya 6oye mata abu daya ba, ta nuna damuwarta da kulawanta a gareshi, ta tambaye shi "yanzu me kake so ayi? So kake yi ace ma Yaya Basheer ka fasa auran Jameelah? Kar kasa kanka a tashin hankali, kasan halin Daddynku farar sani" yace "na sani Suhairah, yanzu dai zan baki numbernta, dan Allah ki kirata kisan abinda za ayi, I can hardly do without her" tace masa toh ya bata numbern, zata kirata, ya fada mata numbern ta rubuta, da yake ya haddace. Khaleefah yayi hailing dinta, saboda yana so tayi mishi deal sannan yayi mata godiya ya ware.
Da misalin karfe uku na rana, Suhairah tayi deciding ta kira Jaleelan, duk ta kagara taji muryan wannan Jaleelan da Khaleefah yake nema ya tayar da hankalinshi akanta. Sai da tayi mata 5missed calls bata dauka ba, da yake ta daina amsa call din kowa in ba na Abdul ba, bare kuma taga sabon number. Ganin bata dauka ba yasa Suhairah tayi mata text da:
“Mara mutunci, ai dole kiki dauka”
Yana shiga Jaleelah ta daga wayar ta karanta, duk a tunaninta Ni'imah ce, saboda tayi ta kiranta bata yi picking ba, may be shiyasa ta sake number, sai tayi mata da reply:
“Toh banza na, zaki fara ko? In kin ga dama call me, nima idan naga dama nayi picking, mumulic baby”
Suhairah bata yi wata wata ba ta dannawa numbern Jaleelah call, ita kuma da yake jira take yi yana shigowa ta kai hannu tayi answering
" 'yar duniya ya kike?" Sai taji wata murya ta daban
"da wannan shegen rashin ladabin naki ne ya maqale miki dama, banda zagi ba abinda kika iya, mara kunyar yarinya"
jikinta yayi sanyi, tace "baiwar Allah ko dai kin samu wrong number ne?"
Cikin fada fada tace "ba kece Jaleelah ba?" Tace "eh nice, lafiya malama?" Tace "baki nemi lafiya ba tunda kika hana Khaleefah yayiwa mahaifinshi biyayya ya auri yarinyar daya za6a mishi, kin hure masa kunni ko? Ke wato 'yar duniya, toh bari kiji, idan kika kuskura kika auri Khaleefah kin dinga ido hudu da tashin hankali iri iri har ki gaji ki bar gidanshi, kin rasa mashinshini shine kika manne mishi, kazamiya kawai, irin tsiya da talauci, kaf dangin mu ba wanda yake son ki dai dai dana second daya sai shi daya nace miki kamar wani maye, wato kunga arziki da ke da uwarki shiyasa kuka je kuka neme shi, toh ta Allah ba taku ma, irin asiri da mugun abu" Jaleelah ta jirata ta gama amayar da abinda ke bakinta, ba tace ko uffan ba tayi hanging, abin yayima Suhairah ciwo, wato ta mayar da ita mahaukaciya kenan, irin ma bata da time dinta. Jaleelah abin bai wani bata haushi ba, saboda tasan daga ji Suhairah bata da cikakken tarbiyya, duk da tana gaba da ita bai kamata ta kirata ta zage ta irin haka ba, ta aje wayar a gefe ta kwanta.
5:30PM nayi sai ga sallamar Abdul ya zo gaishe ta, cikin fara'a ta tashi zaune. Abdul ya sama wuri ya zauna suka gaisa, bayan sun danyi wasu hirarraki, Jaleelah ta fadawa Abdul kiranta da 'yar uwan Khaleefah tayi, duk yanda suka yi sai da ta fada mishi, yace hakan yafi kyau da bata amsa mata ba. Bayan sun gama magana sai ga call din Raheemah ya shigo wayar Abdul, ya jira call din ya gama ringing sannan ya kirata daga baya, Jaleelah sai kallonshi take yi, irin salon da yake amfani dasu wajen yin magana da Raheemah, sun fi 15mins suna hira sannan suka yi sallama, yace mata idan ya koma gida zai kirata, yanzu yana asibiti ne, tace a gaishe da me jiki. Ya fadawa Jaleelahn tace tana amsawa. Abdul ya mike, yace ma Jaleelah shi zai wuce, sai kuma sunyi waya, tayi mishi godiya, sukayi sallama. Yana zuwa dai dai bakin kofan suka yi crossing da babanta da Murayyan zasu shiga, Abdul ya matsa gefe ya basu hanya, bayan sun shiga ya gaishe da baban Jaleelah, bai san mahaifinta bane, shi dai kawai girmamawa, yaga na gaba dashi. Daddy yayi mamakin ganin Abdul a asibitin, wai me hakan yake nufi? Bacci kadai ke raba su? Anya ma tana zuwa makarantan idan aka tura ta? Toh fa yau za a yita ta kare. Ranan koya karfin jiki bai iya cema Jaleelah ba, saboda takaici, a daddafe suka hada 10mins suka fita. Bayan sun shiga mota, sun dauki hanyar gida, Daddy yace ma Murayyan "kasan wannan mutumin kuwa?" Yace "wane Daddy?" Yace "airforce din nan da muka gani cikin asibiti" yace "eh, amma ban ta6a magana dashi ba, ina dai ganinshi" yace "kasan gidansu?" Yace "eh Daddy, lafiya?" Yace "sako zan baka, kuma saura inji a gari ana yamadidi" yace "in Allah ya yarda Daddy hakan bazai faru ba" yace "toh idan mun koma gida, kaje ka same shi, kace mahaifin Jaleelah ne ya aiko ka, yace idan yaga dama ya gama lalata mishi yarinya toh ya turo ayi musu aure, idan ba haka ba na sake ganinshi tare da ita, wlhy sai nayi mummunan 6ata mishi rai, haka zaka fada mishi, bance ka kara ba kuma bance ka rage ba, ko uwar gida bance ka fada mata ba" yace "toh Daddy, muna komawa gida?" Yace "eh, a hanya ma zan sauke ka kaje ka fada mishi sako na" yace "ohkay toh", suna zuwa layin gidansu Daddy ya sauke Murayyan, shi kuma ya wuce gida, gidansu Abdul a can kasa layinsu yake.
Murayyan yana tafe yana tunanin taya ya zai yi ya fadawa Abdul sakon Daddy, amma ai da kunya, but ya zaman mishi dole ya isar kamar yadda Daddy ya umurce shi, kuma abin ya isar ne ai, cox yana nema ya 6ata mishi cousin. Bayan ya isa bakin gate din gidan, ya tsaya yayita knocking sannan mai gadin gidan ya fito, bayan sun gaisa Murayyan yace mishi yana neman wani airforce ne, mai gadin ya bukaci da Murayyan din ya shiga, amma yace a'a, ya dai fadawa mutumin ana son magana da shi a waje, ya shiga ciki wurin Abdul suka fito tare. Gefe suka koma, Murayyan ya gaishe shi, sannan yace "kai ne Abdul right?" Yace "eh Allah dai yasa lafiya", yace "dama baban Jaleelah ne ya aiko ni, yace a fada maka idan kaga dama ka gama lalata mishi yarinya toh ka turo magabatanka, idan kuma ba haka ba ya sake ganinka tareda ita toh sai yayi mummunan 6ata maka rai" gaban AbdulHakam ya buga da karfi, hankalinshi ya tashi, ce ma Murayyan kawai yayi "okay" ya wuce cikin gida ya barshi a tsaye a waje, shima yana wucewa ya wuce gida don isar da sako. Abdul ya koma daki ya kasa zaune ya kasa tsaye, brain dinsa is no more functioning, "idan na ga dama na gama lalata mishi yarinya" abinda ya dinga nanatawa kenan a fili for a thousand times. Abin yayi mummunan 6ata mishi rai, wannan maganar kadai ta gama 6ata mishi ina ga kuma sunyi arba da mahaifinta? Ai mutuncin ba dole bane, ba ita kadai bace yarinya mai fara'a da kirki ba a premier cresent. Abdul yayi deciding ba abinda zai sake hada shi da Jaleelah, ko a ina suka hadu, koda kuwa a birnin sin ne.
Da dare wuraren 9:20PM, Jaleelah tana ta expecting kiran Abdul amma bata gani ba, may be ya gaji ne ko yana aiki, ko kuma yana can yana hira da Raheemanshi, ta dauki wayarta tayi dialling numbernshi, kiran farko bai dauka ba, bayan 6mins ta sake yi for the second time, ta kara bashi 5mins sannan ta sake kira, nan ma bai yi picking ba, data yi na uku sai tace bari ta barshi haka, may be he's busy. Sai ta tura mishi text:
“Slm Uncle Abdu, I just called to say hi and you weren't able to pick or call me back. Do have a restful night”.
Duk calls din a kan idanshi suke shigowa su yanke, ba zai sake picking call dinta ba, kuma ba zai sake kula ta ba. Text message din na shiga wayarsa ya dauka ya karanta, ba abinda yayi mishi dadi a ciki, dai dai da harafi daya bai mishi dadin karantawa ba, yayi deleting text din, sannan ya koma yayi deleting din numbernta, hatta call history dinta sai da ya goge shi da duk wani happy moment ko happy jumaa text din da ta tura mishi sai da ya goge su, yayi dana sanin haduwa da ita, tunda yake bai ta6a ko kissing mace ba bare zina, amma yau ana tuhumar shi da lalata diyar mutane, daga mutunci!. Abdul ya kasa fadawa kowa sakon Baban Jaleelah, ranan through out kasa bacci yayi saboda bakin ciki. Amma koma mene ne, zai nemi su Basheer a waya, tunda ba states daya suke ba, Mustapha yana Jos, Basheer yana Katsina, Munawwar kuma yana Kano, dukansu asalinsu 'yan Kano ne, aiki ne ya kaisu states din, sai dai Munawwar da yake gida still, shi a can yake aiki.
Washe gari da safe, bayan AbdulHakam ya fito daga wanka, yana fitowa wayarsa ya dauka, saboda yana ji tana ringing lokacin da yake bathroom. Ya duba missed call din, duk da bai haddace numbern Jaleelah ba yasan numbernta ne, tayi mishi 5missed calls, sannan ta tura mishi text daya, ya bude ya karanta kamar haka:
“U ain't picking Uncle Abdu, yau za ayi discharging dina”
Yana gama karantawa yayi deleting, ya dai ce "Allah ya kara lafiya" a fili. Sannan ya koma ya cigaba da shirinshi, ita kuwa Jaleelah tanata jira taga call din Abdul yana mata murna, har lokacin daya saba kiranta ya zo ya wuce, may be kwana biyu he's busy ne, abinda take tunani kenan. Ba ayi discharging dinta ba sai da yamma da Daddynta ya zo, ya biya bills aka sallame su, suka dawo gida. Tun kamin ta bar asibitin ta kira Abdul two times amma bai yi picking ba "toh fahh...! What's wrong?" Ta tambayi kanta "Allah dai yasa lafiya" bayan sun koma gida, tun kamin tayi komai sai da ta turawa Abdul text:
“Uncle Abdu na dawo gida yanzu”
Sai yanzu ta lura duk texts din da take tura mishi bai ta6a bata reply ba, kuma idan yaga missed call din ta bai ta6a kiranta ba, may be Raheemah ta hanashi ya dinga amsa kiranta ne, wannan kuma ya rage nata, tunda ba soyayya suke yi ba, harkan mutunci ne ya hada su. Jaleelah tayi deciding in dai bai kirata ba ko bai mata reply ba toh ba zata sake contacting dinshi ba.
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
16
By Linah Shams
Jaleelah ta dauki kwana biyu ba tareda ta nemi Abdul ba, abin kuma na ranta, duk ta kagara da taga call dinshi ya shigo wayarta, may be sai next week monday idan zata tafi school.
Ta side din Abdul kuwa, yana nan yana nazari game da abinda mahaifin Jaleelah ya fada akan shi, bai kamata ace yayi concluding shi kadai ba, ya kamata ace ya nemi Basheer, Munawwar ko Mustapha, Basheer wani murdedden mutum ne, ba ko da yaushe yake fahimtar abu da sauri ba, yanzu sai ya mishi Allah ya kara, sai dai shi kuma Mustapha bai kai Basheer murdewa ba, shi kuma Abdul yasan wata kila tambayar shi zai yi 'toh wa ya aike ka?', har ma gara Munawwar, ya 'dan fi saukin kai. Nan da nan ya dauki wayarshi yayi dialling numbernsa.
Munawwar ya fara magana bayan yayi picking call din "senior man ya dai?"
Abdul yace "lafiya qalau, ya gida?" Cikin muryar mazaje Munawwar yace "Alhamdulillah, komai yana tafiya normal and good, ya nan side din ku fa?"
Yace "da godia, lau lau, Hajajju fa? Hope tana lafiya" yace "ahh lafiya qalau", yace MashaAllah" Munawwar yace "ya ya dai? your voice sounds somehow, lafiya?" Abdul yace "to be honest with you ba wani lafiya"
yace "me kuma ya faru? Hala wannan wawuyar daka makale mawa ce take nema ta saka cikin wani hali"
yace "a'a, ba ruwanta, wata yarinya ce daban kuma" da sauri Munawwar yace "AbdulHakam me kake nufi? Me kake nema ka zama? Wata yarinya daban fa kace, wato tara chics kake yi" yace "haba haba haba... Ba haka bane"
yace "toh ya ne?" Yace "yarinyar muna good time da ita, a hanyar fita kullum nake ganinta ita da sistern ta, har ya kai ga na fara basu lift, muka zo mu ka saba, mukan yi making calls da texts, amma bama chatting, so sai tayi laifi a gida, aka ce toh ta daina jerawa da sis dinta zuwa schl, ta dinga tafiya ita daya, ka gane ba, shine sai jiya jiyan nan dad dinta yayi aike, wai idan naga dama na turo iyayena idan na gama spoiling masa yarinya, may be yana gani na ne sa'adda nake bata lift, may be he's suspicious of me, kuma yarinyar kamar zata yi hali na gari" Abdul yayiwa sakon baban Jaleelah kwaskwarima ne saboda baya so kowa yasan hakikanin abinda ya faru, tunda duk fadin duniyar nan daga Allah, sai Jaleelah da Khaleefah sai shi suka san abinda ya faru, Munawwar yace "well idan kaga ta maka sai ka tura, idan bata maka ba a matsayin mata sai kayi gaba, tunda ba wai soyayya kuke yi ba, ka jira wannan sokuwar ta kare karatun ta dawo"
Abdul yace "Munawwar akwai wa'insu abubuwa behind this, babanta yace zai aura mata wani ne na daban, ita kuma bata so, ina tausayawa halin da zata shiga ne nan gaba" yace "ni har gobe shawara mai options zan dinga baka; in ta maka toh, in bata maka ba toh, the ball is in your court so everything is left to you" cikin muryar damuwa yace "toh Munawwar ya zanyi da Raheemah?" Yace "well... Wannan kuma wani abu ne na daban, ai zaka aureta daga baya, ba wai ba zaka aure ta ba, amma yarinyar da kake magana akanta in kasan natsatstsiya ce kawai kayi magana daga gida aje a nema maka" yace "toh, zan yi tunani, idan na gama zan fada maka, but pls kar ka fadawa Musty da Basheer, kasan su murdaddun halittu ne" yayi dariya yace "toh, duk ranan da ka shirya sai a fada musu" suka yi sallama tareda hanging up call din.
Shi dai Abdul bai gamsu da shawaran da Munawwar ya bashi ba, bashi da wasu abokan shawara sai su, a wannan yanayi kuwa yasan Basheer da Musty ba wani fahimtar shi zasu yi ba, kuma he's far from home da yayi magana da Ummanshi, and baya tunanin zai iya magana da yayanshi Yusuf a yanzu. Zai yi tunani ya hada da abinda Munawwar yayi suggesting.
* * *
Ranan monday tayi, Jaleelah duk ta kosa ta ga Uncle Abdu, tunda bai sami daman
kiranta ba kuma bai sake zuwa asibitin ba. Cikin sauri tayi ta shiri, har ta riga Hadiyyah gama shiryawa, a daddafe tayi breakfast ta shirya ta fito parlour, then 10mins to 7AM. Cikin sauri taje ta gaishe da Mommy sannan ta fita, Sai da ta jira Daddynsu ya fita sannan ta amshi kudi, har 7AM ta wuce lokacin, cikin sauri sauri ta dauki schl bag dinta ta sa sandals ta bar gidan, kamin ta tafi tayi tunanin zata ga Abdul a junction yana jiranta, amma taga bata ganshi ba, may be ya jira ta bai ganta ba ya wuce, tunda yanzu it's past 7AM, hakan yasa ta cigaba da tafiyarta, rabonta da ta hau motan haya da safe in zata schl har ta manta, sai dai da rana. Tana cikin tafiya kawai taga motan Abdul ya zo ya wuce ta, "ko be gane ni bane?" Ta tambayi kanta, abin ya bata mamaki, anya Abdul ya gane ta? Bari dai tayi mishi uzuri, wata qila bai gane ta bane ko ma bai ganta ba. Bata kawo wani abu a ranta ba ta tafi schl, ba laifi ranan tayi concentrating akan karatunta, ta kuma rage turnuke fuskanta.
During break, Ni'imah ta zo ta zauna a gefenta, ta dawo daga schl shop, ta ajiye duk abinda ta siyo a saman desk, tace "Jaleelah Bismillah", ta girigiza mata kai alamar a'a, tace "why no?" Jaleelah ta 6ata fuska, tace "nothing". Ni'imah ta matsa daf da ita tace "Jaleelah idan nayi miki laifi ne ki yafe min, kinji? Ramadhan is fast approaching" Tace "baki min komai ba" tace "toh meyasa kika daina magana da ni? Da tare muke yin break, amma yanzu mun daina, idan na kira ki baki picking, in nayi sending miki text baki replying, idan na miki magana baki son amsawa, unlike before, tare muke yin komai, idan abu ya dame ki kina fada min, but now.... Dunno why! May be you are starting to hate me!!" Ta fada tareda dan matsawa gefe, Jaleelah ta riko hannunta, tace "never! I can never do such a shameful act!! Ban tsane ki ba Ni'imah, u r nice, bazan ta6a tsanarki ba, kima cire wannan tunanin a ranki", tace "then if not, meyasa kika guje min" ta sunkuyar da kanta, bata son ta fadama kowa abinda ya faru, abin kunya ne a ganinta, idan wani ya yarda ba bin Khaleefah tayi ba, wani ba zai ta6a yarda ba, tunda kowa ya san ta nuna mishi so, tayi mishi makahon so, kome yace tayi tana yi, haka zalika kome yace ta bari tana bari, wanda sau tari a gidansu akan hanata, amma taki hanuwa, kamar yawan surutun ta, da tana da jarababben surutu, ba yadda Mummy bata yi da ita ta rage surutu ba, ga fada da masifa, amma taki bari, Khaleefah kuwa na hanata ta hanu, shiyasa wasu zasu iya tunanin binshi ta yi. Tace "ba zaki yi ss3 ba?" Ta girgiza kai alamar eh, tace "toh I promise to tell U what's happening to me, amma sai mun shiga ss3 ko kuma idan mun gama", Ni'imah tace "as U wish, amma pls ki daina gaba da ni, I use to feel so disgraced" Jaleelah tayi murmushi, ta dan yi punching dinta a arm din ta, tace "c u", Ni'imah tayi dariya ita ma, tace "I really missed all these crazy things we did", daga nan kuma sai suka fara hira, amma not as before, Jaleelah har yanzu bata dawo normal ba, don akwai abubuwa masu faruwa yanzu da nan gaba.
Bayan schl hours, Jaleelah ta dawo gida, tana ta azar6a6i ta dauki wayarta ta kunna, shine abinda ta fara yi data shiga gidan, ko sandals dinta bata cire ba bare socks ko uniform, duk a tunaninta zata ga text message din Abdul yana mai sanar da ita dalilin daya sa ya ganta ya ki daukanta dazu da safe, amma ko text din MTN bai shigo mata ba bare na wani. Tayi tsaki ta tambayi kanta "toh meya sa ma na damu da shi? Ni da bani da lafiya ai ma kamata yayi ace ya zo har gida ya duba ni, so for that matter, kar Allah ya sa idan ya ganni ya sake yi min magana bare dauka na", ta kashe wayar tayi jifa da ita kan gado sannan ta koma ta fara yin abubuwan da zata yi. Kullum tunaninta wanda Daddy yace zai aura mata, gashi yace ba zai hada ta da 'dan arziki ba, ita abinda yafi damunta kenan, kuma yace nan bada dadewa ba, bata tunanin zai barta ta kammala secondary schl.
Washe gari, Jaleelah tasa a ranta ma ba zata ga Abdul ba, amma kuma sai tayi mamaki, ta sake ganinshi, kuma ya wuce ba tareda ya mata ko hon ba. Abin ya daure mata kai, "ko dai zan tura mishi text of apology ne? May be nayi offending dinsa unknowingly, Allah ya hana!! Ba text din da zan tura mishi, toh meya sa ma na damu da shi, mtchw.. I'm stupid wolla!" Ta fada a sarari tana tafiya. The following day ma ta sake ganinshi, ta tabbata yana ganinta, koma mene ne shi ta shafa ba ita ba, da har zai iya ganinta ya wuce ta ba tare da yayi ma ko hon ba, shiyasa mutane suka zama abin rashin yardanta.
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
17
By Linah Shams
Ranan Abdul ya kasa sukuni a wurin aiki, baya jin dadin yadda yake treating din Jaleelah, bata san laifin data yi masa ba shi kuma bai sanar da ita abinda ya faru ba, amma kuma ai ba laifinta bane, mahaifinta ne ya 6ata mishi rai. Yayi concluding a zai dauke ta gobe idan ya ganta a hanya. Yana ta kokarin ganin ya san yadda zai yi da shawarwarin da Munawwar ya bashi. For sure baya jin dadin hakan, Amma in Allah ya yarda zai kawo karshen hakan, kamin Basheer yaji ya mishi dariya.
Ita kuwa Jaleelah tana ta kokarin cire kowa a ranta, musanman Khaleefah, ta so shi sosai a rayuwa, yanzu kuma gashi zata rasa shi, kullum sai ta roki Allah ya cire mata son Khaleefah, sallah biyar addu'a biyar. Har yanzu Mummy, Afdal, Daddy, Hadiyya da Yaseen basu kula ta sosai, har da Murayyan, dama shi tun asali ba wani maganan kirki suke yi ba, sai dai tayi ta buga sha'anin rayuwarta ita daya, babu abokin magana ko na shawara, dama Abdul ne, kuma shima yanzu ya daina ko magana da ita, 'ko ya fara yarda da abinda su Mummy suke tunani a kaina ne?' Ta tambayi kanta.
The next day, Jaleelah ta shirya da wur wuri zata tafi schl, amma sai da Daddy ya 6ata mata lokaci, duk da haka kuma ta riga Hadiyyah fita gida. Tana ta tafiyanta a natse, fuskarta ba yabo ba fallasa. Bata wani yi tafiya mai nisa ba zuwa highway taji hon, na farko dai bata waiga ba, sai da motor ta zo daidai inda take tafiya aka sake mata hon, Abdul ne, ta waiga ta kalli motar, yayinda shi kuma yayi winding glass din motar, Jaleelah ta gaishe shi, Abdul 6ata rai, yace "in dai a waje ne toh bazan amsa ba, ki shigo daga ciki mana", a hankali ta dinga girgiza kanta na kusan 6secs, sannan tace "A'a", yace "mene ne a'a?", tace "ba sai na shigo ciki ba", yace "Kamar ya kenan?", ta kalle shi da sauri ta kawar da kanta, tace "bari na wuce kar nayi latti, sai anjima", da sauri yace "toh y not ki zo na kai ki mana?", tace "a'a barshi na gode" ta fada tareda fara tafiya, Abdul ya kira sunanta, amma ko waige, a ranta tana cewa "u should either be real or be gone, mu'amala da ni ba day schl bane da yau idan ka zo da safe anjima da rana kuma ka tafi, gobe kuma idan kaga dama ka zo ko kar kazo", Abdul yaja motar shi, yaje dai dai inda ta tsaya, a side dinta akwai wasu mata guda uku, ya bude kofar motan ba tareda ya sake ce mata wani abu ba, matan suka juyo suna kallon motan da me motan, Jaleelah taga idan bata shiga ba kamar tayi embarrassing dinsa ne, hakanan ta shiga ta rufe kofar suka wuce, bayan sun hau highway sun dan fara tafiya, yace "hm, Jaleelah", tace "na'am", yace "have I offended you?", tace "I'm the one to ask this", yayi wata murmushi, yace "why?", yana sane itace ya kamata ta tambaya, kuma yasan abubuwan da yayi ba tareda ta amsa mishi ba, tace "idan ka ganni sai ka wuce, ko hon babu na nuna sanayya ma, idan na maka text baka replying, idan na kira ka baka picking, and u won't call me back", ya rasa me zai ce mata don ya kare kanshi, saboda baya so ya fada mata abinda Dadddynta yace, yace "abubuwa ne sai a hankali kwana biyu Jaleelah.... Ai nasan kin gane", tace "hum, zan dai gane, hala Aunty Raheemah ce ta hanaka magana da ni", yace "gaskiya kina da saurin fahimtar abu, ita ce din fa, ni kuma daga baya naji I can't continue that way", tace "uhm... Ai banga laifinta ba, sometimes nima haka nake ma Khaleefah", da sauri yace "iyyeh, y not yanzu?", murmushi kawai tayi ta share zancen, suka dauko wani magana na daban.
Tun daga ranan Abdul ya koma ya cigaba da kiran Jaleelah, yana tura mata texts iri iri na happy moment, good morning, happy jumaa, good night, wata rana ma harda na afternoon, idan ta samu dama sai tayi replying, tunda yanzu da kanta take recharging wayarta. Ta side din Raheemah kuwa tana nan suna zuba love da ita da Abdul, ba abinda ke ranta irin ta kammala karatunta ta dawo Nigeria, ta kagara da taga ta auri Abdul, sai dai har yanzu bata daina chilling dinta ba a makaranta, wanda hakan ke yiwa Abdul matukar ciwo da tara mishi bakin ciki, but son ta ya rinjayi ganin laifinta a zuciyarsa. Burinshi suyi aure ya sauya mata rayuwarta, don rayuwar da take yi bata girma da mutunci bane, tarbiyyanta yana da nakasu, ta taso cikin shagwaba da dukiya, ga gadara da alfahari, ga rashin ladabi da na kamun kai, amma a haka shi fa ya ji ya gani, sai ya aure ta, in Allah ya yarda kamin su yi auren ma zata canja, shima dawowarta kasan kawai yake jira.
Jaleelah ta cigaba da relating ta Ni'imah cikin kwanciyar hankali, sai dai surutunsu da rough play dinsu ba irin na dama bane, saisa saisa suke yi yanzu.
* * *
After 8days, su Jaleelah lokacin sun fara qualifying exams din su da kwana uku (Ramadhan); da yamma, duk da a gida an hana Hadiyyah zuwa in da Jaleelah take sai dai dole, amma sai da taje wurinta ranan, Jaleelah na kwance tana playing games a wayarta hankalinta kwance, da sauri Hadiyyah ta shiga ta zauna a gefenta, Jaleelah ta tashi zaune, cike da mamakin ganinta a dakinta, tace "lafiya Hadiyyah?", tace "na zo in kwankwasa miki ne, yanzu yanzun nan naji Mummy na fadawa wannan kawar nata Hajiya Talatu wai an sa ranan auren ki, nan da 2months, bayan sallah", kafafuwan Jaleelah suka kage, ji tayi kamar ba a jikinta suke ba, ga wani zirrr da take ji a cikinsu kamar ta taka shocking, tunaninta ya tsaya cik, kirjinta ya shiga dukan uku uku, bakinta ya tsaya a hangame, idanuwanta ko kifawa basu yi, Hadiyyah tace "amma fa ban san ko wane ne zaki aura ba, ban ji wannan ba, ni dai ina ji tace an sa ranan auren Jaleelah na wuto nan da sauri sauri nace bari in fada miki, kafin kiji ashanan tashi", Jaleelah tace "Hadiyyah dan Allah kice mafarki nake yi, dan Allah", ta jinjina kai, tace "ba mafarki kike yi ba, u r awake, kuma matukar kina da rai da lafiya na tabbata sai anyi auren nan, ba wanda zai janye, kin san ba kowa yake zuwa ma Daddy da kalan nashi suggestion din ba", saboda tarin takaici ko hawaye Jaleelah ta gaza yi, tunani ya mamaye elahirin zuciyanta, ganin bata ce komai ba yasa Hadiyyah ta mike tsam, tace "toh ni nayi nan, idan na sama wani information zan zo na fada miki, okay?", ta girgiza kai alaman eh, tace "its okay", Hadiyyah ta juya ta bar dakin, ta bar sis dinta cikin fargaban wane ne mijin da zata aura?, wa aka ce za a aura mata? Wa zata fadawa taji sanyi a ranta? Wayarta ta dauka ta hau duba contacts dinta, a cikin cousins dinta ba wanda yasan abinda ya faru da ita, kuma mai yihuwa basu da labarin sa ranan aurenta da aka yi, ta zo kan numbern Ni'imah, tayi tunanin kiranta ta fada mata, sai kuma ta fasa, saboda in dai tana so ta fahimci abinda zata fada mata toh dole ne ta fede mata biri har wutsiya, sai ta bata labarin farkon abinda ya faru. Ta ganrara ta kai kan numbern Uncle Abdu tayi dialling, amma bai yi picking ba, yana gama ringing da 5secs sai ga call dinsa ya shigo wayarta, hannunta na rawa ta kai hannu tayi picking
"Uncle Abdu!" Yanayin yadda ta kira sunanshi ya nuna mishi cewa ba lafiya, yace "me ya faru Jaleelah? What's wrong?" Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, hankalinshi ya tashi, ya sake cewa "Jaleelah what's wrong? An miki wani abu ne a gida? Tell me", tana sheshshekan kuka tace "an sa min ranan aure, nan 2months" Abdul yayi relax, yace "yaushe?", tace "nima ban sani ba, yanzu Hadiyyah ta fada min", ya numfasa, sannan yace "kiyi hakuri, just pray for the best, ki roki Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, idan kuma ba alkhairi bane Allah ya rugurguza al'amarin, kin ji?", baya ganinta amma hakanan ta girgiza kai, tace "eh eh, zan yi Inn Shaa Allah, thank you!", yace "never mind, yanzu dai ki zauna kiyi tunani, wa kike ganin Dad dinki ya hada ki dashi, ko da a cikin mutanen da kike full time dasu ne, koma kuwa da baku magana, just develop interest in been with him right?", tace "toh, thank you", ta jira shi yace "welcome" tayi hanging kiran. Sai lokacin ta sake samun chance din yin kuka, ta kwanta ta fara yi babu ji babu gani, yanzu aure za a mata? She's just 17, mates dinta na zuwa schl amma ita tana gidan wani tana zama? Lallai. Sha'anin miskilancinta da daure fuskanta, da rashin walwala ya koma sabo.
Tun daga ranan ta daina faran faran din data koma yi a schl, har Ni'imah sai da ta fahimci haka, idan ta tambaye ta meke damunta, sai dai tace mata "never mind", idan abin yayi mata yawa kuma sai ta je empty class ta zauna taci kukanta ma'ishi. Rubuta exams din kawai take yi, amma ba hope
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
18
By Linah Shams
Jarabawan ma rubutawa kawai take yi, domin halinda take ciki ba zai barta tayi koda karatun arziki ba. A duk lokacin da suka yi waya da Abdul sai ya kwantar mata da hankali da kuma bata shawarar dagewa da addu'a, shi ka dai yake sama mata natsuwa. Ita kuwa Ni'imah tun tana tambaya har ta gaji ta daina, don kullum amsa daya take samu a wurin Jaleelahn. A haka har suka kammala examinations din su suka tafi hutu.
***
Rayuwa ta karawa Jaleelah ba dadi, kullum tana kunshe a daki tana tunane tunane, sam rayuwar bata birgeta, bata ganin abin sha'awa a cikinta, ga zullimin wanda zata aura ga kuma fushin iyaye da take ciki, ko hakan ya isa yasa ta kasa cin ma nasara a rayuwarta. Duk da yanzu mum takan sake mata haka ma mahaifinsu unlike before. A haka har sukayi resuming ss3
Ana saura 15days auren Jaleelah da 6oyayyen mijin da zata aura, tana zaune a main parlour ta tsirawa t.v idanu taji vibration wanda yayi notifying dinta shigowar new text message, duk a zaton ta text din MTN ne, ta kai hannu ta dauki wayar tare da bude text din, wanda ya haifar mata da faduwar gaba, nan ta mayar da hankalinta kacokan wurin karanta text din a hankali.
Text din Khaleefa ne me kunshe da sako kamar haka:
"My most dearing one, nasan na miki laifi mai girma sweetheart, ko da baza ki yafe min ba zan so na furta kalaman neman yafiya na a gare ki.. Jaleelah Please ki yafe min, wallahi hakan ba hali na ba ne, sharrin shedan ne."
Shiru tayi tare da yin lamo a cikin seater, ta rasa wanin reply zata bashi, ta lumshe idanuwanta yayinda tunani iri iri suka ziyarci zuciyanta. Vibration ta ji wanda yayi daidai da shigowar Mommy parlour, da sauri ta tashi ta nufi bedroom dinta, daga ganin tafiyarta kaga mara gaskiya. Mommy ko kawar da kanta tayi kamar bata san tana yi ba.
Tana shiga ta fada kan gado "dama nasan Khaleefa na ba haka yake ba, he's such a gentle man, ni kam na yafe mishi, the love of my life." ta fada a fili tare da rungume wayar a kirjinta. "ya kamata na sanar da uncle" shine tinanin da ta fara yi, tunda abokin kuka shi ake fadawa mutuwa. ai kuwa bata yi kasa a gwiwa ba ta nemo numbersa ta doka mishi kira, har ya tsinke bai dauka ba. Ba a hada minti daya ba sai ga kiranshi, hannunta na rawa ta dauka
"hello uncle"
"na'am amarya" cewar Abdul. Nan da nan ta dan tsuke fuske tamkar yana kallonta, tace "uhm kasan mene ne?", yace "a'a"
Murmushi tayi sannan tace "yanzun nan text din Khaleefah ya shigo, wai he's seeking for my forgiveness"
"toh... sai kika masa reply dame?"
"ban kai ga bashi reply ba, amma dai na yafe masa, ina so komai ya zama ya wuce mu cigaba da rayuwar mu kamar yadda muke yi a baya"
da sauri yace "amma something must be wrong with you, kin manta aure za a miki? And you're going through hell saboda shi"
Cikin kunkunai tace "eh Uncle Abdu amma idan muka shirya ai zan iya cewa a bar wancan ga nawa"
Gajeruwar tsaki ya saki sannan yace "look, ki rabu da wannan guy din, yaushe kika fara zama mara jin magana?"
Shiru tare da sunkuyar da kanta tamkar yana kallonta, tace "uncle kayi fushi ne?"
"ofcourse yes"
Tace "then i'm sorry"
Banza ya mata tare da hanging kiran. Bata wani ji haushi ba saboda tana so taga sun shirya da Khaleefah.
***
Bayan kimanin kwana biyu da Khaleefah ya tura mata text ya tsiri kiranta, kuma taji dadin hakan sosai. Kullum cikin waya suke da text, hakan kuwa ya canja mood din ta ta koma normal self dinta tamkar ba abinda ya taba faruwa sannan ya kuma mantar da ita batun ranan dake kanta. Har saida Abdul ya fahimci haka kuma bata boye mishi komai ba, sosai take sakin jiki ta fada mishi duk wata damuwarta, fada yayi mata ba kadan ba sannan ya gargadeta akan kada ta sake waya da Khaleefah, ko shima da tayi aure zai rabu da ita.
Nazarin maganganunshi tayi sannnan ta daina kula Khaleefah kamar yadda ya umurce ta, aikuwa hankalin Khaleefah idan yayi dubu ya tashi.
* * *
Five days more
Ranan Monday kenan ana saura kwana biyar auren Jaleelah, kuma bata kara daga wayar Khaleefa ba balle ta sanar dashi, gradually taji ta ma fara tsanarshi, idan ta cigaba da mu'a'mula dashi ribar me zata ci? Na farko akwai wacce za a bashi a gidansu sannan kuma kowa baya sonta a gidansu kamar yadda Suhaira ta shaida mata, sannan shine sanadiyyar shiganta fushin iyayenta da kuma auren da za a mata.
Bayan ta dawo daga schl taci abinci ta zauna tana hutawanta ita kadai a daki call din Khaleefah ya shigo, tsaki tayi sannan ta dauka cike da fushi
"Hello" cikin tsiwa ta fada, a hankali ya amsa mata da "ya kike?" "Lafia", jim yayi sannan yace "Queenie nayi laifi ne?"
"And are you asking?"
"Yes I have, saboda naji kin dauke wuta at once"
"To bari kaji, for your own information, aure zanyi on saturday, this coming saturday I mean, so save the date"
"Queenie, what did I hear you say?"
"Aure zanyi, and you know what? You caused it all"
Cikin muryan tausayi yace "haba Jaleelah, do I deserve this?"
"And how do I deserve rape from you" da karfi ta fada mishi cikin fada yadda yafi kama da tsawa, hakan yayi daidai da isowar Mommy kofar dakin zata fada mata fa fito ta kula mata da gida zata shiga makwabta, ai sai ta tsaya
"Look here Khaleefah, sbd kai iyayena fushi suke dani, everybody is blaming me for crime I never commit, ni nasan bama so na kake yi ba, da kana so na da baka daukeni ba"
Gaba daya ta jagwalgwala mishi lissafi, "Jaleelah I thought you've forgiven me"
Tsaki mai tsaho tayi "I'm yet to", muryarshi kamar zaiyi kuka yace "to ya kike so inyi? I'm currently at KD just to see you, gobe insha Allah zan zo"
"Wannan shine karya Khaleefah, wallahi ba zaka sami ganina ba"
Mommy ta gaji da tsayuwar hakan yasa ta tura kofan ta shiga tareda kiran sunanta, hakan yasa tayi cutting call din tare da amsawa, "ki fito ki zauna a parlour ki kula min da gida kamin su Afdal su dawo daga islamia zan shiga gidan Maman Hassan, idan kin jini shiru ki daura min miya da ruwan tuwo"
Abin sai ya bata mamaki, tace "okay mommy sai kin dawo"
Kuka ne kawai Khaleefah bai yi ba bayan ta katse wayar, a gidansu Suhaira ya sauka hakan yasa yaje ya sameta ya fada abinda ke faruwa, farinciki ne ya cika zuciyarta saboda ita loyal fan din Jameela ce, amma a zahiri ta nuna mishi tsantsar damuwarta, a nan ya fada mata washe gari da yamma idan Allah ya yarda zai je ya ganta ko da kuwa ba zata mishi magana ba, infact ko da ba zata fito ba sai yaje layin gidansu.
Mommy na fita Jaleelah ta daga wayarta ta kira Abdul, for the first time da yayi receiving call dinta, don Kadan ya rage ya fara jin haushinta akan sha'anin Khaleefah. Gaishe sa tayi cike da girmamawa shikam a dakile yake amsawa,
"Kasan mene ne?" Ta tambaye shi,
"Sai kin fada"
"Khaleefah wai yana nan zuwa gobe kuma..." Bai jira ta idar ta maganarta ba ya katse ta "how stupid of you!" Ya daka mata tsawa, ji tayi tamkar a mafarki wai uncle Abdul na mata tsawa "don't dare call me again with the intention of telling me something about this ugly dude, rashin wayonki ya fara yawa and I can't help it anymore"
Cikin rawar murya tace "ba haka bane"
"ko ma mene ne matsalarki ce kinji, kin gane ko?" A fusace yayi hanging call din yayinda bakin ciki ya taru mata a zuciya.
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
19
By Linah Shams
Washe gari da safe bayan tayi shirin schl ta zauna a gefen gadonta tana sa socks, sai lokacin ta tuna time din da take wanka an kira ta, ta daga pillow dinta ta dauko wayar tayi unlocking, missed call din Khaleefah ne sai text guda daya, shima nashi ne, budewa tayi ta karanta "I will be coming later today" hannunta na rawa tayi mishi reply da kar ya zo yayi haquri, sake turo mata da text yayi na neman afuwanta amma shifa dole sai ya zo don tafiyar ta tace. A meeting mode ta sa wayar ta saka ta cikin aljihun gaban riganta. Tana gama shiryawa ta wuce dakin Mommy ta gaishe ta, nan tace mata idan ta tashi daga school ta biya gidan kawarta a Sultan road ta amso mata sako, sannan ta kara mata transport fare tareda ja mata kunni akan kar ta dade duk da cewa tafiyar nada dan tazara daga school dinsu. Har mamakin yadda Mommy take mata yanzu take yi. Tana fita ta ci karo da motan Abdul yayi parking a gefe yana jiranta, da wucewa ta so tayi amma ta tsaya ta fara gaishe shi, harararta yayi sannan yace "ki daina gaishe ni a waje", bata fuska tayi sannan tace "ai sauri nake yi", a yanzu ya riga da ya fara jin haushinta, ji yake kamar ya mareta, cikin fada yace mata "my friend will you get in!", turo mishi baki tayi kamin ta zagaya ta bude side din gaba ta shiga, cikin kunkunai tace "ina kwana"
Tayar da motar yayi suka fara tafiya sannan yace da ita "it's not by force, rike gaisuwarki", haushinshi ya kamata, shi ba ubanta ba ba komai nata ba amma sai fada yake mata tun jiya, amma kuma bata ga laifinshi ba, laifinta ta gani da ta sake mishi fuska. Har suka isa school dinsu ba wanda ya sake ce ma kowa komai, ko da ta fita daga motar tayi mishi godia bai amsa mata ba ya wuce, hakan kuwa ba karamin zafi ya mata a zucci ba.
Tana shiga school ta zarce class dinsu ta wuce seat dinta ta zauna, yau aurenta saura kwana hudu a lissafinta, Allah yasa barazana ce kawai Daddy yayi mata, adduar da tayi tayi kenan har aka yi closing. Ana tashi ta tari me mashin ya kaita har bakin kofar gidan Aunty Balaraba, da wuri ta isa gidan don bata dauki 15mins ba a hanya, 3o'clock suke closing, ta so ace by four tana gida, amma sai da ta tsaya zaman jiran Aunty Balaraban da sam ma bata gidan, sai da ta dawo ta bata saqon, ganin an fara kiraye kirayen sallah ne ya sa ta tsaya ta gabatar da sallar la'asar sannan ta fito daga gidan. A bakin hanya ta tsaya ta jiran me mashin, tafi 5mins a tsaye ba ko dayan da ya zo ya wuce, wayarta ce ta fara vibrating, tana fiddo ta daga pocket din ta taga Khaleefah ne, da kamar ba zata yi picking ba daga baya ta dauka
"Yaya dai?" Shine abinda ta fara furta masa
"Ina hanya shine na kira na sanar dake"
Dariyar rainin wayau ta mishi sannan tace "journey mercy",
"Gidanku fa zan zo"
Tsaki tayi sannan tace "and how does it affect me?"
Kwafa yayi sannan yace "wai kin fara tsanata ne?"
"Kwarai kuwa. I hate you. I hate you with passion"
Wani irin kara ya saki mata a kunne wanda hakan yasa tayi gaggawar kashe wayarta, a cewarta zai kashe mata dodon kunni. A haka har ta sami mashin ya kaita bus stop ta sami mini bus ta wuce gida.
A hanya go slow ya fara haduwa tun daga nesa take hango shi, ga zafin ranan da ake yi, kowa na cikin bus din sai complain din zafi yake yi banda Jaleelah wacce sam bata k'aunar hira a motar kasuwa. Kowa ya kosa motar tayi gaba don ya gane ma idanuwansa dalilin afkuwar go slow din, tun kamin su isa alamu ya nuna accident a kayi.
* * *
Da sauri ta shigo dakin domin jiyo ringing din wayarta da tayi, Yaya Basheer ne sunan da yake ta kai koma a screen din wayar, da hanzari ta dauka "ashe ke mahaukaciya ce ban sani ba?"
Mamaki ne ya bayyana a fuskarta karara "Yaya me nayi?"
Cikin fushi yace "ubanki ki kayi, ina Khaleefah yace miki zashi?"
Cikin in'ina tace "premier crescent"
"Me yaje yi?"
Da sauri tace "ammm nima ban sani ba"
"Oh really? Idan na zo gidan zaki fada min, don na sami labari ke ke tunzura shi akan bijirewa umurni na na hada shi aure da yar uwarshi kike cusa mishi son wata, zan ci mutuncinku dake dashi, zai dawo ya same ni"
Hanging call din yayi ba tareda ya saurareta ba, jiki na rawa tayi dialling number dinsa, yana shiga ringing biyu aka dauka, but kamin tayi magana aka fara yi mata wanda hakan ya tabbatar mata da cewa bada Khaleefah take magana ba, ranta ya baci cikin fada tace "ba me wayar muyi magana"
"Baya kusa" ya bata amsa
"Abeg ina yake?"
Ajiyan zuciya yayi sannan yace mata "he's involed in an accident"
A razane tace "what!!!! Ina yake yanzu? Yana ina?"
"Relax madam, a kusa da Sams annex hatsarin ya auku right away"
Bata iya bashi amsa ba ta fita da gudu don shaidawa jama'ar gidansu.
Bedroom din mahaifiyarsu ta fada inda kaninta da yayanta da matarsa suke zaune suna hira, "lafiya" Halima ta tambayeta, ko kallonta ba tayi tace "Maa Khaleefah yayi accident a kusa da Sams annex" da sauri ta mike tana sallallami yayinda sauran mutanen dakin suma duka suka mik'e. Nan da nan yayanta ya fita suka bishi a baya duka, motarsa ya bude ya shiga suma suka dunguma suka shige banda Maa dake cikin dakinta cikin tashin hankali.
* * *
Ranshi ba karamin baci yayi ba sanadiyyar ganin wannan go slow din, ya kwaso gajiya ga kuma yunwar da yake ji bugu da kari ga bacin ran da yarinyar nan ta sashi ya kwana ya wuni a cikin shi.
Lokacinda suka isa wurin da accident din yayi daidai da lokacinda aka ciro shi daga motar. Jikinshi yayi kaca kaca da jini wasu suna ya mutu wasu suna yana da rai, da hanzari driver dinsu yayi parking domin taimakawa. Fitarsa ke da wuya yan bus din duka suma suka bi bayanshi, motar ta dade sai Jaleelah dake maqale a gefe. Zafin motan ya isheta hakan yasa ta fito daga waje itama. Matsawa tayi kusa da mutane taga me hatsarin duk da tana tsoron me idanuwanta zasu hango mata kada taje ta kasa bacci, karaf taga Khaleefah ne kwance cikin jini. Tuni tayi kukan kura ta dunga bangaje mutane ta isa inda yake a kwance, mutane sai suka koma kallonta, durkusawa tayi ta tallabo kanshi dake zubar da jini ta dauranshi akan ciyarta tana kuka mai sauti "my love are you okay? Please talk to me!"
Murmuring words ya dinga yi sai dai ba wanda ta iya ji. Tuni uniform dinta ya baci ta jinin dake fita daga jikinshi, "my love please say something" gani kawai tayi an janyeshi daga jikinta, da sauri ta dago taga ko wanene, bata ankara ba taji saukan lafiyayyen mari a fuskarta. Hakan kuwa yayi dai dai da isowar AbdulHakam spot din accident din, da saurinshi yayi parking ya fito daga motan shi, yana isowa wata matashiyar mace na wanke wata student da mari, wacce sai da ya hanga yaga Jaleelah ce, "what must she be doing here?" Ya tambayi kanshi, kamin ya karisa ya hango Jaleelah ta nufi bawan Allah da yayi accident ta riko hannayenshi, yana isa kusa da su Suhaira na kara wanke ta da mari a dalilin sake taba Khaleefah da tayi, Abdul shima bai yi kasa a gwiwa ba wurin dauke Suhairan da mari "how dare you?!" Kasa magana tayi ta dafe kuncinta saboda radadi, ita kuwa Jaleelah sake reverse tayi ta rike Khaleefah yayinda ake ta kokarin sa shi a mota, Abdul yaja hannunta so violently yace "let's go!" Fincike hannunta tayi ta koma inda Khaleefah yake tana fadin "he's dying! Happened all because me! Na shiga uku" ko bata fada mishi ba yasan Khaleefah ne, komawa yayi da baya ya fizgo ta sannan ya sauke mata lafiyayyen mari ita ma, sai da taga taurari masu wutsiya. Jan ta yayi zuwa mota ya bude front seat ya tunkuda ta ciki sannan ya rufe ya zagaya ya shiga.
Kukan bakin ciki ta dunga yi har suka isa layin gidansu ba tareda yace mata uffan ba haka ita ma, bude motan tayi da karfi ta fita ta rufe mishi ko godia bata yi ba. Tsaki yayi sannan ya ja motarsa ya wuce cike da jin haushinta.
Tana shiga gida sukayi kicibis da Mommy a falo, cike da al'ajabi take kallonta, tace "meya same ki Jaleelah?", karisawa tayi kusa da ita tace "accident akayi a hanya shine jini ya bata min kaya"
"How manage?"
"Na dauki wani baby ne"
"A gabanku accident din ya faru?" Mommy ta tambaye ta, "a'a wucewa muka zo yi shine driver din mu ya tsaya"
"Allah ya kyauta to, yanzu idan kika kasa iya bacci da daddare fa?"
Tayi nara nara da idanu "Nima mommy abinda nake tunani kenan"
"Ina sak'o na?" Ta tambaye ta, bude jakarta tayi ta fiddo mata da yar karamar bakin leda "gashi tace gobe za ta aiko miki da dayan" ta fada tareda mika mata.
"Je ki sa min a cikin chase drawer to" ta umurce ta. Ta wuce dakin ta ajiye a inda ta fada mata, kamin ta fito Mommyn ta shiga dakin, "ki shiga ban daki kiyi wanka, bari in dauko miki kayan canzawa", cike da farinciki ta ajiye school bag dinta a kan gado ta rage kayan jikinta ta shige.
Koda ta fito Mommy har ta kawo mata kayan canjawa, vaseline ta shafa sannan ta sa kayan, a gefen gadon ta zauna tana tuna when last tayi wanka a bathroom din Mommy, hamma ta fara yi hawaye na zirarowa daga idanuwanta, lumshe idanunta tayi ta matsa ta janyo pillow ta kwanta, tunane tunane ta dinga yi kamin bacci yayi awon gaba da ita.
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
20
By Linah Shams✍🏼
Sai da aka fara kiraye kirayen sallar magrib sannan Mommy taje ta tashe ta tace mata taje tayi sallah. Saukowa daga gadon tayi tana tana squeezing idanunta sannan ta dauki schl bag dinta, hamma tayi tareda duba inda ta cire uniform dinta taga bata gani ba, "Mommy ina uniform dina?" Ta tambaye ta, tace "Hadiyya ta wanke miki", "is it really mommy?" Ta tambayi kanta amma a fili tace to tareda fita zuwa dakinta. Gaba daya ta manta experience dinta na ranan. Tana shiga ta nufi bathroom tayi alwala ta fito ta gabatar da sallar magrib. Nan ta cigaba da zamata kan carpet sai a sannan ta tuno da Khaleefah, "ohh" tayi exclaiming tareda dafe forehead dinta. Tiryan tiryan ta shiga jero abinda ya faru in her mind, waya sani ma ko Khaleefahn ya rasu? Tausayinshi taji sosai. Sai kuma ta tuno lokacin da Abdul ya mareta har saida ganinta ya dauke for almost three seconds, shafa kumatunta tayi tareda yin kwafa.
Tashi tayi ta bude schl bag dinta ta ciro wayarta, "10 missed calls!" Ta fada tareda mamaki, gaba daya kiran Abdul ne har da texts guda biyu, duka texts din rokonta yake tayi picking call din. Sabon haushinsa ta fara ji nan take ma ta rufe wayar gaba daya ta saka ta cikin wardrobe.
Shi kuwa Abdul tunda ya koma gida yake ta tunanin marin daya mata, bai so hakan ba amma ita tayi forcing dinsa, yana janta tana jan kanta. Kuma he can't help seeing her touch any man. Hakanan yayi deciding ya kirata ya bata hakuri duk da still haushinta yake ji. Ko kanuwarsa wacce shekarunta be wuce na Jaleelahn ba bai taba marinta ba bare wacce ba abinda ya hadasu. Gajiya yayi da kiranta ya tura mata texts sannan ya sake kira amma taki dauka, hakan kuwa ya tabbatar mishi da taji haushin abinda yayi mata ba k'ank'ani ba.
Bayan sallar isha Mommy na zaune a parlourn Daddy bayan yaci dinner dinshi, Mommy ta muskuta tace "dama ina ta so muyi magana sai yanzu na tuna", yayi sipping pineapple juice din dake kan stool a side dinshi yace "ke nake saurare", numfasawa tayi tace "akan yarinyar nan ne"
"Wace kenan?" Ya tambayeta
"Jaleelah"
"Meya same ta? Bata da lafiya ne ko me?"
"A'a lafiyarta qalau, akan zancen aurenta ne, zai fi kyau idan aka fasa. Saboda munyi kuskure sosai, bamu bincike ta ba bayan ta dawo. Kuma wallahi she's innocent"
Kaikaicewa yayi ya kalleta "so kike na zama karamin mutum ko me? Yau saura kwana uku auren yarinyar sannan kice na fasa? Ki sake tunani, tunda dai an samu wanda yake sonta ai sai a aurar da itan, kuma ko tayi laifi ko bata yi ba she is ripe for marriage, shekarunta sha bakwai ai ta isa aure"
"Amma baka ganin an tauye ta? she is just seventeen and a final year student!" Ta fada da alamun bacin rai, "whatever! Ko mamanta ma a gidan mijinta takammala secondary schl kuma hakan bai hanata cigaba da karatunta ba".
Sosai ran Mommy ya baci, laifinta ne a matsayinta na mahaifiyarta da bata zaunar da ita taji asalin abinda ya faru ba ta biyewa Daddy suka yi gaban kansu.
Shiru ta mishi ba ta sake cewa komai ba.
* * *
Washe gari da wurwuri AbdulHakam ya fito gida saboda yana so yaga Jaleelah ya bata hakuri saboda marinta da yayi jiya. Ya jima a bakin layinsu kamin ya hango ta tana zuwa. Murtuke fuska tayi don bata tunanin zata iya shiga motarsa yanzu, saboda a dalilin dan lift din daya ke basu ne har ya samu daban wanke mata fuska da mari. Ko da ta isa inda yake bata nuna alamun ta ganshi ba tayi wucewarta, da sauri ya bude motar ya fita ya bita, "haba Jaleelah sai ka ce baki ganni ba?"
Banza ta mishi ta cigaba da tafiyarta, ya sake cewa "gaba kuma kike yi da ni?" Juyawa tayi ta kalleshi tareda bata fuska, kunkunai tayi mishi amma bai ji komai ba "anyway, daga yau in Allah ya yarda kin daina gani na, dama shiyasa na zo da wuri and to wish you a happy marriage life in advance", tsayawa tayi tareda kare mishi kallo, kwayoyin idanuwansa ta kalla yayinda zuciyarta ta fara bugawa da karfi, wani voice taji na mata whisphering "his voice oozes sadness...." A hankali tayi mumbling "thank you" yayinda hawaye suka circiko idanuwanta, ta juya ta cigaba da tafiyarta, kallonta ya tsaya yi har ta dan yi nisa sannan ya koma ya shiga motarsa. Yana isa kusa da ita ya tsaya yace mata ta shiga, da farko k'i tayi sai daya roke ta. A hankali yake driving din kamar ba zai yi ba saboda tayi magana amma taqi, a haka har suka isa bakin schl dinsu, sai sannan yace mata "thanks for the good times, I really appreciate it, and I'm sorry for what I did yesterday, I couldn't control my temper, I wish you'll acknowledge it. I'm sorry you won't see me as a stranger henceforth, and.... Not even tomorrow. Happy marriage life in advance once again, Allah ya bada zuri'a dayyiba"
Kasa amsawa tayi, tayi still kamar ruwa ya cinyeta, hakan yasa yace mata ta tashi ta shiga makaranta kar tayi latti. A hankali ta fita motar kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, sai da ta kai bakin schl gate din ta tsaya ta waigo hawaye cike da idanunta, ganinshi tayi a waje yayi folding arms dinshi yana kallonta, wani kyau ya mata da kwarjini kamar ranan ta fara ganishi. A hankali hawayen dake idanuwanta ya shiga zirarowa yayinda Abdul ya fara nodding alamar kar tayi kuka, murmushi ya mata tareda raising eye brows dinsa alamar itama tayi murmushi, murmushin tayi and waved him bye. Toothy grin ya mata tareda komawa cikin motarsa.
* * *
During Break
Zaune take a seat dinsu ita kadai, fuskarta ba yabo ba fallasa amma da ka ganta ka ga wacce tayi zurfi a duniyar tunani. Ji tayi an girgiza ta da karfi that startled her. Da sauri ta juya taga ko wanene, classmate dinta ce Shafa'atu Rabi'u, kallonta tayi fuskarta dauke da alamar tambaya sai taji an kira sunanta, waigawa tayi taga English teacher dinsu, Mrs Maryam Kiyawa, yakuto tayi da hannu alamar ta zo, mikewa tayi ta karisa inda take suka fita daga waje saboda ajin was too noisy.
"What are you thinking about?"
Murmushi ta kirkiro tace "nothing Ma"
Tab'e fuska tayi tace "is your note complete?", girgiza kanta tayi, tace "okay let me have it". Nan ta juya ta koma ajin ta kawo mata note din.
"And what has been wrong with you?" Ta sake tambayarta, "I've been observing you since and you aren't your chirpy self"
Murmushi ta sake kirkirowa tareda cije lebenta, malamar ta sake cewa "if you need someone to talk to you can always count on me, okay?"
Sunkuyar da kanta tayi tana fidgeting fingers dinta sannan tace "but promise never to tell anyone, pls ma, not even a staff"
Girgiza mata kai tayi tareda riko hannayenta, "feel free with me"
"Aure za amin and, ban san ko wa za a aura min ba, shiyasa"
Da mamaki take kallonta, "yaushe ne auren?"
"This coming saturday"
Tausayinta taji ya kamata, "anjima idan kika koma gida zan kira ki kinji? Just relax your mind and chill out, damuwarki ba zai hana komai ba, I promise to help you.." Murmushi tayi tareda yi mata godia sannan suka rabu kowa ya wuce inda za shi.
Mrs Maryam Kiyawa ba wata babba bace, shekarunta twenty six tana da aure da yara guda biyu, Hauwa(Maijidda) da Surumbai. Sun kasance da Jaleelah tamkar kawaye tun sanda ta fara koyar dasu a ss1 inda sab'ani ta hadasu, Jaleelah tayi mata tsiwa ta hukunta ta, tun bayan faruwar haka suka fara mutunci, sauran staff har ciwon baki suke mata wai tana hira da student dinta kamar wata kawarta, tunda idan hira tayi musu dadi har tafawa suke yi. Kuma suna yawan yin waya kamin wannan incident din.
Bayan ta koma class ta zauna ta fara tunanin rayuwarta, komai gani take tamkar a mafarki, dagaske ne zata yi aure ranan Saturday tunda taga kayan siye siyen da akayi mata, su duvets and kitchen utensils da curtains. Kamar yadda Mrs Maryam ta fada mata damuwarta ba abinda zai hana, harma gara ta koma yin addua ta rungumi kaddara. Amma dole tana so tayi magana da Mommy tunda taga yanzu tana sake mata, hakan yasa duk ta k'agara ayi closing.
A daren ranan AbdulHakam yayi relocating zuwa gidanshi a Yarwa Close, shi sam ba zai ya sake ganin Jaleelah ba a yanzu saboda ya mareta, kuma duk sanda ya ganta sai ya tuno marinta da yayi wanda ke bata mishi rai. Ba yadda brother dinshi baiyi dashi ba ya zauna zuwa wani lokaci amma yaqi yarda.
Da sallama ta Shiga dakin, Mommy dake zaune akan sofa ta amsa mata. Daidai kusa da kafarta ta zauna a kasa akan rug, Mommy ta dube ta tace "lafia?", tace "eh lafia lau"
"To mene ne na zama haka kamar zaki shige min cikin jiki?" Ta sake tambayarta. Hawaye ta fara yi wanda tuni yayi breaking heart din Mommy, "na tambayeki lafia kince lafia qalau yanzu kuma kin fara min kuka, baki da lafia ne?"
"A'a" kawai tace mata, "to mene ne?"
"Mommy wallahi ni ba bin Khaleefah nayi ba, wallahi fada muka yi ya aiko aka dauke ni kuma Allah Mommy bai yi nasara akai na ba na gudu, wani mutumi ne ma ya taimake ni ya bani N500 na hau napep amma wallahi Mommy ni bani na bi Khaleefah ba, dan Allah kice ma Daddy kar ya min auren nan" ta karise zancen tareda rushewa da sabon kuka. Ta jigina kanta da knees din Mommy ita kuma sai patting dinta take yi a baya, "meyasa to baki fada ba tun da wuri ba?", cikin kuka tace "ai baku tambayeni ba. Gashi yanzu kuma zaku aura min mara mutunci inji Daddy", patting dinta ta cigaba dayi tace "insha Allah ma ba mara mutunci bane, kiyita addu'a that's all. Kinji?", nodding tayi sannan Mommy tace "to tashi kije kiyi koyawa su Yaseen homework dinsu, kar kisa damuwa a ranki, kinji?, and daga yau kin gama zuwa schl, idan time din rubuta external exams yayi za a biya miki kiyi a wani schl, okay?" Girgida mata kai tayi tareda wiping hawayen dake fuskarta ta fita. Suna cikin yin assignment din Aunty Maryam ta kira ta, sun dan yi hira sannan tace mata akwai abubuwan da zata kawo mata gobe a schl, nan ta ke shaida mata ita fa ta gama zuwa AMMS daga ranan, Aunty Maryam tayi mata alkawarin kawo mata abubuwan bayan auren nata. Godia ta mata sosai kamin su kayi sallama.
Tun daga ranan Mommy ta fara bata 'yan stuffs na mata kuma take janta a jiki sosai fiye da da. Hakama su Hadiyya komai ya koma normal, sosai Mommy ta kwantar mata da hankali akan auren amma bai sa taki damuwa akan waye mijin ba. Babu wani event din da a kayi sai dai ana gobe daurin auren akayi Walima a compound din gidansu Wanda ya amsa sunansa Walima. Yan uwa fa an taru da abokan arziki an taya Mommy murna duk da kaf danginsu ba Wanda yasan dalilin auren ko cikin kawayenta ba wanda ya sani. Iyaye mata a wurin na ta encouraging aurar da yara da wurin kamar yadda za a aurar da Jaleelah, babu wacce Jaleelah ta gayyata sai Aunty Maryam kuma ta sami daman halarta. Sai dai bata kawo mata abubuwan ba sai bayan biki.
10:15PM
Tayi tsammanin Abdul zai kirata amma ko text dinsa bata gani ba. Hakan yasa ita ta zauna ta tsara text kamar haka ta tura masa "Aslm. Greetings from Premier Crescent. Fata na kana cikin koshin lafia, just want to seize this opportunity and say a big thanks to you.. Thank you isn't what I'm suppose to say, it's all I have to say to show my gratitude, but if you have any other method that you'll insist and I am capable of, I won't fail you, just say it, I'll insha Allah comply. Thanks for once being an uncle that cares for me, a mother that listen to me, a father that scolds me, a brother that advices me, a sister that loves my happinees and a friend I always lean on. You are my uncle, father, mother, brother, a sister and a friend. I'll be forever thankful for your gifts. Yours ever loyal, Jaleelah Naseer"
Shigowar text din yayi daidai da gama wayar shi da Raheema, yayi matukar jin dadin sakon, ya bata reply da "a thank you is not what I deserve. I don't even need it. Be a loyal wife to your husband and be patient in all circumstances, then I'll be forever thankful dear. Yours ever sincere AbdulHakam".
A daren ranan sai da tayi yawa da Khaleefah tayi mishi ban kwana, yaji sauqi sosai don har anyi discharging dinshi daga Viva hospital inda aka kaishi a halin da ake ciki ma ya koma Sokoto, dukansu sai da suka yi kukan rabuwa da juna musanman Khaleefah. Hakanan shima zai rungumi kaddara ya auri zabin mahaifinshi kamar yadda ta bashi shawara, ko don samun 'ya'ya na gari suma suyi mishi biyayya.