_Washe gari_
Amakare Asma'u ta tashi kasancewar bata kwanta da wuriba,, ta tashi da addu'a abakinta, ganin yanda haske ya gauraye d'akin yasata zaro idanu waje, ta kalli agogo k'arfe 7:06am, zummbur tatshi Dan gabatar da sallah, agaggauce tayi sallar, tana idarwa saiga doctor Al-Ameen ya shigo, suka gaisa ya tambayeta mai jiki?.
Da sauk'i doctor, Asma'u tafad'a tana d'an murmushi.
Shima murmushin yayi ya ce, "Alhmdllh, yad'an duddubashi sannan Yakuma kallon Asma'u, Hajiya insha ALLAHU nanda awa d'aya zuwa biyu zai iya farkawa.
Alhmdllh doctor, mungode sosai.
Karki damu hajiya, mugodema ALLAH kawai, fita yayi.
Ita kuma ta tsurama ya Umar daketa barcinsa idanu cikeda shauk'in so.
_ya Umar bak'ine kuma k'yak'yk'yawa masha ALLAH, bazamu kirasa dogoba haka kuma ba gajere bane yana dai tsaka tsaki, yanada cikar hallita mai k'yawun haiba dan bai kasance siririba, yanada d'an jikinsa dai-dai misali, mutumne mai yawan hak'uri da kawaici, bakomaine abin magana awajensaba, bashida yawan hayaniya amma akwai yawan fara'a ga wanda yasani, bayason raini arayuwarsa, yanadason 'yan uwansa da mahaifiyarsa, so ya Umar dai yakai akirasa cikakke kuma nutsatstsen namiji abinson kowace mace._
Asma'u tasaki wani k'asaitaccen murmushi Wanda batasan tanayiba, gsky tana bala'in son ya Umar, harma tana ganin tafi kowa sonsa aduniya.....
Da sauri tad'ago danjin an dafa kafad'arta, Rafi'a tagani, sukaima juna dariya, Rafi'a ta ce, " haba Anty Asma'u irin wannan tafiya haka?, ya Umarfa nakine.
Murmushi Asma'u tayi, ta ce, "wai yaushe kikazone?.
Nakai Minti biyar akanki wlhy, amma ko kad'an bakisan da shigowataba, kina cikin shauk'in so.
Kai wai Rafi'a yaushe kika koyi rashin kunya ne?.
Hhhhh daga fad'ar gsky auntynmu, wai ni inama Anty Lubna ne, kobatasan bashida lfya bane?.
Wlhy Rafi'a ban saniba nima, rabonta da gidan tun washegarin randa kukaje datazo itada iyayenta.
Tofa ALLAH ya k'yauta, kardai ace itama butulcin zata masa?.
Asma'u ta ce, "Hmmm Rafi'a kenan, aii mutanen duniya sun wuce yanda kike tsammaninsu wlhy, yanzu jiya kinsan kuwa mina Tatar a asibitinnan bayan dawowata daga saida waya?, bakiga mun canja likitaba?.
Nagani, kuma tunjiya naso tambaya amma tashin hankalin halinda ya Umar yake ciki ya hanani tambaya, miya farune?.
Asma'u tashare hawayen fuskarta sannan ta ce, " lokacin Dana dawo a waje na tadda su ya Umar, makwafcinmu ya tallafesa yana kwance ak'asa, da hanzari nak'arasa garesu Dan azatonama ya Umar ya rasune, cikin kid'ima na tambayi koya mutu?."
Makwafcinmu ya CE, "a'a da ransa, wai Doctor jafarne yafito dasu waje saboda mun dad'e bamu dawoba.
Kaina kawai na jinjina Dan bak'incikinsa bashine agabanaba, lfyar ya Fharuk nake dubawa, na ce, " babu damuwa mu maidashi nasamo kud'in.
Dak'yar ya Fharuk yad'agamana hannu alamar a'a karmu maidashi, na marairaice murya INA fad'i haba ya Umar daka dai daure mun maidaka tunda lfyarka Muke nema.....
Makwafcinmu ne yakatseni da fad'in gaskiya Hajiya koni ban goyi bayan hakaba, Dan bakiga wulak'anci da cin zarafin da likitancan yamanaba, mutane sukaita kallonmu, dazaki amince akwai wani d'an uwana shima likitane anan dasai na kirashi.
Da Saudi nace kirashi kawai.
Bayan yakirashi babu dad'ewa saiga Doctor Al-ameen, cikin mamaki ya ce, "wannan ba Alhaji Umar bane?.
Mukace shine, agaggauce makwafcinmu yabashi labari, ran doctor Al-ameen ya 6aci matuk'a, babu 6ata lokaci yasa aka kawo gadon d'aukar Mara lafiya aka d'auki ya Umar, namatsa kusadashi INA MASA godiya, na ce, " ammafa bamu biya kud'in komaiba.
Harya fara tafiya yajuyo gareni ya ce, "haba Hajiya aiba kud'i yakamata mufara damuwa dasuba lfyarsa, kije ki ajiye mufara fuskantar matsalarsa, wlhy Rafi'a har kukan dad'i nayi danjin furicin likatannan.
Rafi'a ta share hawayen fuskarta itama ta ce, " ALLAH sarki ya Umar kana ganin rayuwa, bakomai ALLAH yana tareda masu hak'uri aii, ALLAH yabaka ikon jurewa.
Asma'u ta ce, "Ameen dai Rafi'a.
Rafi'a ta ce, "ga abinci nan inji mama.
Wayyo mama munsata aiki.
Baki Rafi'a ta ta6e ta ce, " kebar Maman nan itama haushi take bani, inaji inama ace ba ita ta haifemub......
Da sauri Asma'u ta rufe bakin Rafi'a, a'a karki fad'i haka Rafi'a, duk lalacewar mahaifi mahaifine, mubita da k'yak'yk'yawar addu'a kawai kinji.
Rafi'a batace komaiba saima hawaye dasuka cika mata idanu.
_Bayan 3h..._
Zuwa sannan asibitin yacika da dangi,harsu inna sunzo, amma duk doctor ya tsaidasu awaje Dan yana saran farkawar Ya Umar.
Cikin ikon ALLAH kuwa agogo na nuna k'arfe 10:00am sai ya Umar yafarka, dagashi sai Harri's a d'akin Dan Asma'u taje gida tayi wanka, cikin gaggawa Harris yafita zuwaga likita, yana sanar masa suka iso tare, bak'aramin farinciki Dr Al-ameen yayiba Dan ganin Ya Umar ya farka cikin hankalinsa, Dr al-ameen yad'an k'ara duddubashi sannan yafito yasanarma su mama.
Gaba d'ayansu suka shiga d'akin ya Umar na zaune jingine jikin gado, mama tazauna akusadashi tareda kamo hannunsa ta ce, "Umarina sannu kaji?.
Murmushi yamata, Dan bayason yin magana, suma su Rafi'a, Anty sa'a, Anty Saratu, inna, mufida, hasiya, Fatee dadai sauran 'yan uwa suka shiga yimasa sannu, kansa kawai yake iya d'aga musu, aransa ya ce, "ko ina wannan yarinyar?.'"
Bayan kamar minti talatin doctor yashigo ya ce, "suyi hak'uri sukuma bashi waje ya huta, duk fita suka kumayi akabar Harris kad'ai, doctor ya ce, " kataimaka masa yaje bayi danyayi wanka sannan yaci abinci yasha magani.
To doctor mungode sosai.
Doctor nafita Harris yataimakama Ya Umar yarakashi har cikin bayi, saida yaji yafara wankan sannan yafito waje indasu inna suke.
Babu dad'ewa Asma'u tadawo, abinda tafara tambaya shine ya Fharuk yatashi?.
Mufida tayi dariya, ta ce, "Asma'u amaryar ya Umar, yatashi yana nan zaune kekad'ai yakeson gani.
Fuska Asma'u tarufe tana dariya, ALLAH yasoma mama da inna sunacan zaune agefe su kad'ai, Anty sa'a ta ce, " jeki kigansa kinji ma'u, k'yale Mufida.
Ba musu Asma'u tashiga d'akin, babu kowa Dan haka ta kakka6e gadon tagyara sannan tazauna jiransa.
Tana nan zaune aka bud'e k'ofar bathroom d'in, d'ago idanunta tayi sai suka had'a ido da ya Umar, tai saurin kauda kanta Dan ganinsa dagashi sai tawul, cikin tafiyar mara lfy dabayajin k'arfi yak'araso kan gadon, saida ya zauna sannan ya kalleta, kanta ak'asa ta ce, "ya jikin?.
Kallonta yakumayi tareda fad'in da sauk'i, yayd'an tsaki wai ina Harris d'in?.
Asma'u ta ce, " yaje gida yadawo."
Shiru yayi, zuwacan kuma ya CE, "sakama k'ofarnan key zan shirya kar wani yashigo, jikin Asma'u a sanyaye tamik'e amma saita fara k'ok'arin fita, ya ce, " ina zakije kuma?.
Uhmm dama zanjiraka awaje, idan ka kammala saina dawo, yad'an d'aure fuska sannan ya ce, "dawo.
Babu musu Asma'u tadawo tazauna inda take ada.
Man shafawa yamik'a mata, kar6a tayi tana mai satar kallonsa, duk yayi wani cid'in-cid'in da fuska, ya ce, " d'an shafamin mannan hannuna duksunyi sanyi saboda k'arin ruwa..
Yanda yake magana a cikunshe babu alamar wasa yasa Asma'u mik'ewa da mai ahannnunta, ta lakata amma saitata murzashi Dan takasa ta6a jikinsa, ganin yanda taketa mulmula man takasa ta6ashi saiya mik'a mata hannunsa, cikeda kunya tafara shafa masa, jitake tamkar k'asa tatsage tashiga ciki Dan kunya, shikam gogan naku ko a jikinsa shi dad'inma shafa man yakeji, jiyake tamkar tana masa tafiyar tsutsa, idonsa a lumshe harta gama.
Tashi yayi yana shiryawa, Asma'u kam tazauna kanta ak'asa.
Saida yagama shiryawa sannan tajawo kulolin abinci tazuba masa, yana zaume yana kallonta harta gama, tad'ora masa filet d'in abincin a bak'in gado, shiru yayi bai d'aukaba baikuma yi maganaba, ganin haka yasa ta ce, "ga abinci.
Fuska ya yatsine dawane hannun zanci?, nacemiki hannuna yanamin ciwo.
Cikeda mamaki take kallonsa, wannan wane irin sabon salone daga ya Umar kuma?, yana nufin itace zata bashi abincinma?.......
Yakatsemata tunani da fad'in jeki kiramin mama ko inna subani tunda ke bazaki iyab.....
Bata bari yak'arasaba ta d'auki abincin tamatso tana bashi, yanda take basa abincin takasa kallonsa saita bashi dariya, amma baiyiba yadaure ya gimtse, tana cikin bashi abincin aka kwankwasa k'ofa, tashi tayi taje ta bud'e, su mamane da matan anguwarsu sunzo dubashi.
Babu kunya yamik'ama Asma'u filet d'in abinci wai tacigaba da bashi, wayyo ALLAH Asma'u tamkar zata fasa ihu, babu yanda zatayi tacigaba da bashi harya k'oshi, tazuba ruwa a cup tamik'a masa, yanzudai kar6a yayi yasha da Kansa...........
*_Luv you all_*
*_(((S)))......2017_*
[11/28/2017, 3:27 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
*Amma saga yau na sakad'a Xoxo da hajja ce & zeety, 🤔kona had'a da Rano?, umm baradai nabarta kawai.*🤥
_muhud'u writer's Asso..... Kenan._😜😂
*_page→20-22_*
..........Alhmdllh jikin ya Umar yana yin k'yau, yaji sauk'i sosai, saidai abinda ba'a rasaba.
Dangi kam balaifi suna d'an zuwa ganinsa, musamman wad'anda zuciyarsu bata manta da d'umbin alkairinsaba sanda yakeda kud'i.
'Yan uwansa dai suna mamakin rashin zuwan Lubna asibitin, kuma duk Wanda ya tambayesa saiyayi kicin-kicin da fuska alamar baya buk'atar maganar, ganin haka kowa ya daina tambayarsa Lubna.
Yauma duk suna asibitin har kawu kabiru da babansu Asma'u, 'Yar hira akeyi da raha irinta family idan an had'u, ya Umar kam shiru baya cewa da kowa k'ala, Harris ya kalli ya Abubakar ya nuna masa ya Umar da baki (zind'e kenan, kuma babu k'yau😏.)
Baki ya Abubakar yata6e shima suka had'a ido da matarsa Haleesat.
Asma'u duk tana kula da abinda sukeyi, hakama Anty Sa'a, hawaye yacika idon Asma'u tamik'e ahankali tafice.
Ya Umar dake kallon duk wani motsin kowa, har abindasu ya Abubakar sukeyi masa, yabi Asma'u data fita tana kuka da kallo, ahankali yalumshe idanunsa yanamai jin tausayinta, shima sakkowa yayi daga gadon yanufi hanyar fita.......
Inna ta ce, "Umar ina zuwa kuma?.
d'an shafa kansa yayi, idonsa ak'asa ya ce, " inna zand'an tattaka ne, na gaji da kwanciyarne".
To aii dakayi magana sai ko Harris ya taimaka maka, kaida bakajin k'warin jikinka".
A'a inna yayi zamansa zan iyama, nafison nayi dakaina.
To shikenan, jeka, idan kagajidai kadawo kaji.
Kansa ya jinjina mata tana murmushi, sannan yafice.
Asma'u na zaune akujerun dake jere a tsakkiyar reception d'in asibitin, kanta a duk'e yake shiyyasa ya Umar baiga halin datake a cikiba, takawa yayi zuwa gareta.
Da sauri tad'ago danjin mutum ya zauna a Kusada ita.
Had'a ido sukayi da ya Umar, sai kawai tad'auke kanta, tamaida k'asa tana k'ara share hawayen dasuka silalo mata yanzun, girgiza kansa yayi tareda kamo hannunta ya rumtse anasa, yaarrrrr tsigar jikinta ta tatashi, yauce rana ta farko da ya Umar yata6a rik'e hannunta amatsayinta na matarsa, ta rumtse idanunta harda cije le6e.......
Bata gama dawowa dai-daiba taji muryarsa na kuwwar fad'in Husna!.
K'ara rintse idanunta tayi sosai takuma kasa amsashi.
Shima baya buk'atar amsar tata Dan haka yacigaba da fad'in, Husna shin bazaki zama jaruma baneba?, kina ganin rayuwa zata cigaba da tafiya komai da kuka?, Husna bamusan randa rayuwa zata canja bafa, kenan hawayenki basuda ranar k'afewa?, kinga d'ago ki kalleni.
Shiru Asma'u takasa d'agowa, amma tana sauraren dukkan maganganunsa.
Ya kuma fad'in husna kalleni mana.
d'agowa tayi cikeda kasala, suna had'a ido tayi azamar janye nata, yad'aga baki zaiyi magana Anty Sa'a tak'araso wajen.....
A'a d'an k'anina mikuma kukeyi anan wajen?.
Baice komaiba saidai nuna mata Asma'u da kanta ke k'asa yayi.
Anty Sa'a tad'anyi murmushin takaice tareda zama Kusada Asma'un suka sakata tsakkiya itada ya Umar.
Itama dafa kafad'arta tayi, cikin sigar lallashi ta ce, "Asma'u kik'ara zama mai hak'uri da jarumta dukda nasan kinadasu, kicigaba da yima mijinki kuma yayanki addu'oin fatan alkairi, kizama mai k'arfafa MASA gwiwa kinji?.
Karki sake damuwa da abinda wasu suke masa barema harya sakaki kuka, ALLAH daya basa shiyya kar6i abinsa badan baya son Umar ba, sanda ya azurtasa baiyi shawara da kowaba, hakama yayin amshewa, suma basufi karfin ya kar6e daga garesuba.
_antambayi Mazon ALLAH (s,a,w) waye talaka?._
_sai ya ce, "Wanda zaitashi ranar k'iyama babu komai na aikin alkairi a gidauniyar ayyukansa._
To Ashe talaucin duniya bashine talauciba, dukiyar duniya ba itace arzik'iba, Dan *_KARAYAR ARZEEK'I_* ta riski Umar ba hakan na nufin ALLAH baya sonsa baneba, ya jarbceshine Dan kawai yaga nauyin imaninsa, wannan itace *Kaddararsa* Dan haka bashida ikon tsallakewa, inhar d'an Adam bazai iya gujema kaddarar ranar mutuwarsaba, to tabbas bai Isa gujema duk wata k'addara a yayin rayuwarsaba, kibar kuka kinji.
Jin jina kai Asma'u tayi, cikin raunin murya ta ce, " Anty sa'a ngd da tunatarwarki agareni, ALLAH yak'ara bamu jarumtar cinye jarabawarsa, Ameen ya rabbi Asma'u, ALLAH ya albarkaci rayuwar aurenku.
Murmushi Asma'u tayi, azuciyarta ta ce, "Ameen Anty Sa'a".
Ta juya tad'an kalli ya Umar, muryarta kasa-kasa ta ce, " ya Fharuk kayi hak'uri da d'aga hankalinka danayi harka taso kafito, insha ALLAH wannan shine na farko kuma na k'arshe.
Mik'ewa yayi yana fad'in ni bakimin laifin komaiba dama.
Daga Asma'u har Anty Sa'a da kallo suka bishi harya shige d'akin dayake jinya.
Asma'u tajuyo tana kallon Anty Sa'a, kanta a langwa6e ta ce, "ya Umar yanada wuyar sha'ani anty".
Murmushi Anty Sa'a tayi tareda fad'in duk taurinsa kece zakisakashi yayi sanyi k'anwata, nakumasan zaki iya saboda jarumtarki...
Itama tana kaiwa k'arshe ta tatashi tabar wajen.
Da kallo Asma'u tabita harta shige, ta sauke ajiyar zuciya tana wani murmushi da juya maganar Anty sa'a a zuciyarta, indai hakane to tabbas zata zama zaruma wajen maida ya Omar sanyi kamar yanda Anty Sa'a tafad'a, tabbas tanason ya Umar sosai kuma zata zauna dashi aduk halin dayake ciki, itama mik'ewa tayi tashiga d'akin
Da sallama tashiga, wad'anda sukaji suka amsa, tanemi waje kusada Fatee ta zauna, data d'ago ido saita kama ya Umar na kallonta, Anty sa'a na kallonsu tana dariya ciki-ciki.....
_____________________
Kwana biyu tsakani aka sallamai ya Umar suka tattara sai gida, duk dangi sun musu rakiyya zuwa gidan nasu.
Wani abun mamaki tundaga babban falo suka fara gani, kaf abinda ke falon an kwasheshi babu komai sai agogon dake manne abango, kallon-kallo aka koma kowa yayi cirko-cirko kamar zakaru na shirin fad'a, Asma'u ce tayi k'arfin halin d'aga k'afafunta tashiga cikin falon sosai tana kalle-kalle.
Babu Wanda ya iya cewa Uffan aduk taron, Dan Ya Umar baibama kowa damar hakanba, hasalima d'akinsa yashige yabarsu anan, a falon nasama abin mamakin ya tarar Dan nanma komai babu sai agogo dawata kujera guda d'aya dayakan zauna domin hutawa, sai tebiri agefenta Wanda yakan d'ora abubuwa, dak'yar yaja k'afarsa zuwa cikin bedroom d'in zuciyarsa cikeda tunani kala-kala, nanma dai bata canja zani ba Dan babu komi sai katifa da jibgin sutturunsa akai, saikuma tarkacen daba'a rasaba, jin hajijiya na neman d'ibarsa ya dafe bangon d'akin, cikin zuciyarsa yake tunanin wayayi masa wannan aikin?, badai za'a danganta ta'asarnan da 6arayiba Dan babu abinda 6arawo zaiyi da katakai, zuciyarsa tafara rawa akan ina Asma'u tasamu kud'in biya masa asibiti?, can wata zuciyar ta ce, "ita ta saida kayan gidan kenan?. Damm gabansa ya fad'i yay shiru batareda iya koda kwakwkwaran motsiba, yama rasa wane tunani zaiyi akan Lamarin........
A 6an garen Asma'u madai tunani take yaushe ya Umar yay cinikin kayan gidansu?, kanta bai ida kwancewaba saida tashiga nata d'akin, babu komai an kwashe sai katifa, hattada akwatinanta na lefe ankwashesu kaf, sai kayan datazo dasu daga gida aka zube a katifa, innalillahi wa'inna ialaihirraji'un kawai take iya amabata, yaraf tazube bisa katifar tana sauke numfashi, wai miya shiga kan ya Umar ne haka?, Dan kawai *KARAYAR ARZEEK'I* ta riskeka sai komai daka mallaka yazama hajar rabawa a kasuwa?, haba wannan wace iriyar rayuwace?.......
6angaren dangima dai kowa lamarin yagirmi tunaninsa, amma babu halin magana, dansu duk tunaninsu su ya Umar sun saida kayan gidanne dan nema masa lfy, wannan yasa tausayinsu ya d'arsu a zukatan wasunsu, Anty sa'a ma kasa zama tayi ta tattara 'ya'yanta suka tafi tana kuka da tausayin k'anin nata, ganin haka sauran sukaima Asma'u sallama suma suka tattafi.
Daga Asma'u har ya Umar sun riski kansune a halin shiru da zargin juna, kuma har zuwa yammaci babu Wanda ya iya neman d'an uwansa balle tambaya agareshi, ganin agogo ya nuna 3:45pm yasaka Asma'u tashi tafito da k'yar saboda jin cikinta yafara kiran Ciroma tasan kuma ga ya Umar ma hakane.
Kicin tanufa da nufin dafa musu komi yasamu su zirarama hanjinsu, mamaki al'ajabi da tsinkewar zuciya duk suka risketa alokaci guda, wayam babu komai akicind'in koda kuwa cokaline, hakama sitod'in babu alamar kwayar gero acikinsa, ta nisa tareda sauke numfashi, tama rasa abin fad'a Dan haka tafito zuwa d'akin ya Umar.
Tofa. ta ambata yayinda tayi tozali danasa d'akin shima wayam, ta hard'e hannayenta ak'irji tana k'ara raba idanu akan komai, shin kuka zata fasa kokuwa kururuwa?, da sauri tafito zuwa d'akin Lubna, nanmadai an kwashe komai ko tsinke ba'a bariba, nasu d'akunan yafi dama-dama tunda anbar musu katifu da agogunan kallon lokaci.
Ayanzun kam ba tsinkewar zuciyace kad'ai ta risketaba harda tsinkewar 'Yar hanji da daskarewar jini, da k'yar taja k'afafunta takoma d'akin ya Umar, masu iya magana kance ta inda aka hau aii tanan ake sauka.
Bedroom d'insa takutsa kai batareda neman iziniba bare tsoron shiga, babu kowa ad'akin saidai k'arar ruwan wanka daga bathroom d'insa, wannan yasa tazauna abakin katifar tanabin tulun kayansa dake jibge bisa katifar da kallo...............
*_luv you so much my sweet fan's, ALLAH yabar zuminci, inata godiya da k'aunarku gareni, wlhy nima ina matuk'ar k'aunarku aduk inda kuke alkairin ALLAH yakai muku😻😻😻😻❤❤❤❤❤❤🤝💋._*
*_(((S))).......2017_*
*_Luv you all_*
[11/29/2017, 2:40 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
_Na gaisheku my Deexerh da Billy S Fari & Deejerh, alkairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke, ina alfahari daku._😻😻🤝💋
*_page→23-24_*
.......Yana fitowa tamik'e zumbur tamkar wadda aka tsikara, da sauri tafice a d'akin, shikuma ya rakata da kallo, baice komaiba ya zauna yana shafa mai, duk jikinsa babu k'arfi yake jinsa, jallabiya kawai ya zura yafito domin tafiya masallaci sallar la'asar.
Afalonsa ya tadda Asma'u, harzai wuce saikuma yajuyo ya kalleta, itama shi take kallo, amma suna had'a ido tajanye nata, ya ce, "lfy kuwa?".
Tashi tayi tsaye tana tura baki gaba, muryarta na rawa ta ce, "ya Fharuk miyasa zakayi haka?".
Kallonta yakeyi sama da k'asa Dan baisan inda maganar tata ta dosaba, hasalima shiyya dace yamata wannan maganar saboda saida kayan gidan datayi.
Ganin kallon dayake mata yasaka jikinta yin sanyi. shima juyawa yayi yafice abinsa batareda yasake cewa komaiba.
Dak'yar ta iya jan k'afarta takoma d'akinta, itama sallar ta gabatar, tana nan zaune akan sallayar cikinta na k'ugin yunwa taji alamar shigowar mutum, kafin tayi wani yunk'uri k'amshin turarensa ya sanar da ita shine, sosai yake bin d'akin da kallo, jiyayi wani haushi yakuma turnik'e zuciyarsa, to aii 6annar tayi yawa, kujerun babban falo kad'ai zata iya saidasu sama da dubu d'ari biyu, amma shine hardana d'akinsa Dana d'akinta?, afusace ya ce, "k! Waimike damunkine?.
Asma'u tad'ago tana kallonsa, tuni tsoronsa ya tasirantu azuciyarta Dan ganin yanda idanunsa suka kad'a sukayi jajur.
Muryarta na rawa ta ce, "yaya babu abinda ke damuna fa"......
Wata Uwar harara ya galla mata wadda tasakata saurin tsuke bakinta, Yakuma Daka mata tsawa ubanwaye yasakaki saida kayan gidannan!?.
Cak jikin Asma'u yatsaya daga rawar dayakeyi, sosai take kallonsa dakuma mamaki, shi Kansa ya lura da hakan.
Ta d'auke idonta daga kansa tana fad'in niban saida ko cokaliba agidannan, nima kuma d'azu maganar danaje yimaka kenan, dai-dai da kicin ba'a bar komaiba hakama d'akin Anty Lubna babu komai........
Shiru yayi yana kallonta, zuwa can kuma ya ce, " to idan bake bace wanene?, kinsandai 6arawo bazai saci katakai yabar kayan sakawaba?, shin inama kika samu kud'in biyamin asibiti?.
Zuwa yanzun kam zuciyar Asma'u tafara tunzura, Dan haka tafara maganar dad'an karsashi, wayata nasayar nayi hidimar asibitinka, Dan alokacin banida abinda yawuce wayar saikuma kayan lefena Dan sukad'ai na mallaka agidannan, sukad'ai kuma zan bigi k'irji nace nawa, ko a shekaranjiya danazo gidannan komai yana nan, na tabbata duk Wanda yay wanan aikin ajiya yayishi.... Fuuuuu tashige bathroom batareda tajira cewarsaba.
Cikeda mamaki yabita da kallo, dama yasan tuni Asma'u tanada tsiwa daga bayane tabari saboda tana shakkarsa, fita yayi zuwa d'akin lubna danya gaskata maganar Asma'u.
Ilai kuwa babu komai acikinsa, kamarma ba'a ta6a ajiye wani Abu daya danganci mutumba, can jikin k'ofar window ya hango wata farar takarda, ahankali yataka ya zareta tareda bud'ewa, anutse yafara karanta takardar, baikai da zuwa k'araheba yasaketa awajen yana ambatar addu'ar da akeso musulmi yayi yayinda al'amura suka tsananta a gareshi.
↓
*_“Allahumma laa sahla illaa maa ja'aaltahu sahlan wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlan”._*
_(ya ALLAH! babu wani Abu mai sauk'i, sai abinda kasanyashi yazama mai sauk'i, kuma kai kana Sanya tsanani idan kaso yazama sauk'i)._
Haka yayta maimaita wanan addu'a ahankali nutsuwa tafara zuwa agareshi, d'aukar takardar yayi yafice daga d'akin Yakoma nasa.
Asma'u dake la6e tana kallon duk abinda ke faruwa takoma baya da sauri Dan ganin zai fito, koda yashiga d'akinsa saiyayi wurgi da takardar a katifar, shima yafad'a saman kayan ya kwanta domin samun sauk'in zafin da yakeji.
Asma'u nanan zaune afalo shiru saiga Rafi'a da abinci, sosai tayi murna da hakan, bata 6oyema Rafi'a damuwarta tasanar da'ita komai. sosai lamarin ya girgiza Rafi'a.
Asma'u tamik'e takaima ya Umar abincin, tadad'e akansa tana masa magana amma ko motsi baiyiba bare tayi tunanin zai amsata, hakan yasa tadire abincin tafitowarta.
++++++++++++++++
Haka rayuwar gidan tacigaba datafiya cikeda k'unci da damuwa, babu mai shiga harkar wani acikinsu, gaisuwa kawai take had'asu saikuma kaimasa abinci Wanda Rafi'a tajuri kawowa kullum bada sanin mamaba.
Ranar yashirya fita, tsaf yafito yanata zabga k'amshi, idan baka saniba bazaka ta6a cewa yana cikin wata damuwaba, fuskarnan fayau sai Annurin hak'uri ketashi, saidai duk Wanda yasan ya Umar ya kalleshi a yanzu yasan ya rame sosai, sai dogon hancinnan dayay ziri-ziri, jin k'amshin turarensa ya yawaita awajen yasaka Asma'u dake kwance d'agowa tana kallonsa, tashi tayi zaune.
Shima sai binta yakeyi da kallo, gani yake dukta canja masa, kamarma tayi bak'i, tausayinta ya d'arsu azuciyarsa, zama yayi abakin katifar kusada ita, cikin taushin murya ya ce, "Husna bakida lafiyane?.
Kwalla suka cika mata idanu, kanta ak'asa ta ce, " a'a lfyta k'alau".
Shiru yayi yana nazarinta, zuwa can yasauke numfashi, d'aya daga cikin wayoyinsa yazaro saga aljihu, yacire sim Cart d'insa sannan ya kalleta, ina cim cart d'inki?.
Yana nan, tafad'a kanta ak'asa.
"d'akkomin".
Tashi tayi tamkar kazar da k'wai yafashema aciki, yabita dakkalo sanye take cikin sket da Riga na shadda ruwan ak'asa mai turuwa, ada kayan sunmata kad'an amma yanzu data rame sunmata yawa.......
Katse masa tunani tayi da mik'a masa sim Cart d'in, baice komaiba ya kar6a ita kuma takoma inda takeda ta zauna.
Saka sim Cart d'inta yayi a wayar ya sassaita mata abubuwa sannan yamik'a mata yana mik'ewa.
Galala take kallonsa da waya a hannu, ganin haka ya d'ora mata bisa cinyarta, ya ce, " zanje wani waje yanzu Dan inaso nafara Neman aiki.
Muryar Asma'u a sanyaye ta ce, "ALLAH yatsare yabada sa'a".
Amin yafad'a yanamai jin dad'in addu'arta har cikin zuciyarsa.
Tunda yafice taketa juya wayar a hannunta tana murmushi, aranta ta ce, " ko wayarnan takai nawa?, Dan tabbas daga ganinta an sayeta da kud'i masu nauyi. Ta sumbaci wayar tana murmushi tareda shak'ar daddad'an kamshinsa dake tashi a jikin wayar, ahankali tafurta ALLAH yabarmu har Abadan my Umar Fharuk!, abinsona, farincikina, Nusfulhayat d'ina, hawaye suka gangaro abisa fuskarta.......
Kamar wadda akaima magana akunne tamik'e zummbur tanufi d'akinsa, takardar ranar tafara bulayin nema, amma duk inda take zatonta babu ita, tacije le6e tana yarfe hannun jin bak'in ciki, harta kama hanyar fita saikuma tadawo, bai k'yautu ace tacigaba da Barin d'akin da kayansa akan katifarnanba, komawa tayi tazauna ahankali tafara ware gogaggu da wankakku wad'anda babu guga, harma damasu daud'a aka had'a awajen, zagewa tayi sosai tagyara d'akin tsaf, tad'akko zanin gado ta shimd'a, kamar ance tad'an d'aga katifar saiga takardar ranar, wani murmushi jin dad'i tasaki, ta d'auki takardar ta ajiye gefe saida tagama gyara komai tsaf sannan tafice zuwa d'akinta cikeda son ganin abinda takardar ta k'unsa.......
Ya Umar kam koda yafita ak'ofar gida sukaci karo da makwafcinsa, hannu yabasa suka gaisa, ya Umar yamasa godiya sosai akan taimakon daya masa ranar, babu komai d'an uwa aii anzama d'aya, amfanin makwaftakar kenan.
Hakane gskyarka ngd sosai ALLAH yabar zuminci, saidai bansan sunankaba.
Murmushi makwafcin nasa yayi ya ce, "hakane. Ni sunana Muktar".
Masha ALLAH malam Muktar, nikuma sunana Umar Fharuk.
Masha ALLAH Umar, daga yau ina fata zamu zama abokan juna, matanmmuma zasu zama k'awaye.
Babu damuwa Muktar ALLAH yabarmu tare, suma saimuyi k'ok'arin had'asu.
Sund'an dad'e suna hira, sannan Muktar yamasa sallama yakoma wajen aikinsa, dama yayi mantuwane yadawo d'auka.
Ya Umar ma mashin ya tsaida yahau suka nufi inda zaije........
*_(((S))))......2017_*
*_Luv you all_*
[11/30/2017, 3:19 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
*_page→25-26_*
........Jikin Asma'u har rawa yakeyi wajen bud'e takardar, ta jingina da k'ofa bayan ta rufe tafara karantawa.
*↓*
*_hii Umar Fharuk_*
_Hummm abin mamaki da al'ajabi._
_hhhhh Umar nasan abinda zaku fara ambata kenan kaida matsiyatan danginka da Mayyar matarka a yayin da kuka shigo kangon gidanka kuka tarar babu komai a cikinsa, hhhhhh to kasan wacece ta shirya wad'annan abubuwan mamakin da al'ajabi kuwa?. nice nan Lubna, nayi hakane saboda bazan ta6a barin kacigaba da morar wani Abu daga dukiyarmuba, bazan ta6a barin wannan shegiyar matar taka jin dad'in rayuwa da kaiba wlhy Umar, nice nan na kwashe komai nagidannan kuma nayi k'yauta dasu, Ku k'arata acikin talaucinku dama ahaka kuka taso kuma ahaka zaku k'are, Dan matiyaci ko'a tulun manshanu kasakashi haka zaifito bai dangwali komaiba, nasoka tamkar babu wani namiji aduniya, mahaifina yamaka gata tamkar shine ya haifeka, amma saboda butulci irin na talaka karasa dami zaka sakamin saida wata abar banza wai kishiya, tom ga fili gamai dokinan, saura kuma sukuwa ko?, ALLAH yabada sa'ar cin gabbaza mukan nagaba yayi gaba nabaya sai labari, abinda yasa zan barka katsira da gidan dakake cikima saboda yazama tukuyci wa tsaron dukiyar mahaifina dakayi abayane kawai, afrah da amrah kam kasaka aranka baka ta6a haihuwar wasu 'ya'yaba aduniya, nikam kamanta dani hakan zaifi yimaka sauk'i._
_wassalam matarka ada😜._
Ajiyar zuciya Asma'u tasauke, k'irjinta har wani d'agawa yakeyi sama saboda bugawar da zuciyarta takeyi da k'arfi, tadafe k'irjin tareda lumshe idanunta hawaye na zurara akumatunta, wani tausayin ya Umar ne yaketa walanked'uwa azuciyarta, ashe dama duk abubuwanan saboda ita yake faruwa dashi?, haba Anty Lubna miyasa zakiyi hakane?, gara'ace kin rabani da ya Fharuk da'ace kin cutar dashi da k'untata rayuwarsa sabodani, inason ya Fharuk banason wani Abu dazai ruguza duk wani cigabansa, ya ALLAH ka kawoma wanan bawa naka d'auki, tazame ta zauna k'asa da6ar tamkar wata mai shirin hawa bori.
Tadad'e a wajen tana kuka kamar wadda akace inna ko baba sun mutu, ganin babu sarki sai ALLAH tamik'e tawanke fuskarta, hijjabinta ta d'auka tasaka tafito.
Hartaje k'ofar fita saikuma ta fasa, komi ta tuna?, dawowa tayi tazauna a tsakar gidan tanabin k'adangaru daketa guje-guje da kallo.........
Ya Umar kam yanacan yanata bulayin Neman aiki, duk inda yasan yanada wata alfarma ada saida yaje, amma k'alilannema acikinsu suke Nuna sun ganeshi, wasuma nunawa sukeyi basuta6a ganinsaba, murmushin takaici kawai yakeyi yatafi, har yamma lik'is babu wani cigaba saima wahalar kishirwa da yunwa data addabesa, ganin magriba takawo kai yahau mashin yanufo gidansu.
Atsakar gida ya iske Mufida da Rafi'a suna hada-hadar girkin dare, Rafi'a dake wanke naman kaji tad'ago tana kallonsa da murmushi, yaya Sannu da zuwa.
Yauwa Rafi'a, aiki kukeyi?.
Eh yaya INA yini.
Lfy lau ya makaranta?.
Alhmdllh yaya.
Mufida itama ta gaisheshi.
Amsa mata yayi itama cikeda kulawa, Dan itama yanzu tausayinsa takeji tunda ya kwanta a asibiti.
Ya ce, "mamafa?".
Tanan ciki itada ya Abubakar.
Okey shima yazo gidanne?.
Eh yaya.
Cikin falon yashiga da sallama, ya Abubakar da mama suka d'ago suna amsa MASA babu yabo babu fallasa, durk'usawa yayi yana gaida mama, ta amsa MASA kadaran kadahan, hannu yamik'ama ya Abubakar shima suka gaisa, suna gama gaisawa ya Abubakar yamik'e, to Mamana bara nawuce gida saikuma gobe, babudai abinda kike buk'ata ko?.
A'a Sadiq d'ina bana buk'atar komai wlhy kawadatamu dakomai saidai nace ALLAH yayi maka albarka yak'ara arzik'i.
Ameen Mamana saida safe.
ALLAH yakaimu ka gaidamin 'yan jikokina da d'iyata.
Zasuji insha ALLAH.
saida yaje bakin k'ofa sanan ya ce, " o Umar sorry fa namanta kananan bamuyi sallamaba Ashe, saida safe konace saiwani jik'on danku kunyi wuyar gani yanzu.
Ya Umar dakansa ke a duk'e tun d'uzun yana sauraren tad'in Nasu mama, ya d'ago idanunsa dasuka fara canja launi zuwaja saboda 6acin rai, yasan sarai habaici ya abubakar yamasa amma ko kad'an fuskar jarumin naku bata nunaba, fuskarsa shimfid'e da murmushi ya ce, "babu damuwa ya Abubakar saida safe agaida iyalin, ficewarsa yayi batareda ya amsaba.
Ya Umar yadawo da kallonsa ga mama datake k'irga kud'in da ya Abubakar yakawo mata yanzu sai murmushi takeyi ana dangwalar yawu da k'ara Tisa k'irgar, baice komaiba yamaida Kansa k'asa yana jiran takammala.
Saida tagama tsaf sanan yad'ago ta kalleta, gabad'aya fuskarta ta canja yanzu babu walwala, amma kuma idonta na kan ya Umar d'in.
Muryarsa a raunane ya ce, " mama dama Nazi nasanar dake yanda mukayi da Lubna ne.
Baki mama ta ta6e amasife ta ce, "Umaru kaini rabani dawata lubna tunda kud'in ubanta basu ammfaneka da komaiba, idanda su wasu mutanene arzik'ine Aida sun taimakeka kodan ganin halin masifar dakake ciki, amma mutanannan sunyi funfurun fus saboda bak'in ciki irinna mai arzik'i dabayaso talaka yasamu, wace irin wahalace bakaima ubantaba fisabilillahi amma yamzu suka watsar Sakai, kofa dubaka basuzoyi asibitiba harkayi kwanakinka kagama jinya....
Shidai Umar tunda mama tafara sababinta baice komaiba kansama na k'asa, saidai zuciyarsa tana mamakin halin *_MANTA ALKAIRI_* irinna mahaifiyarsa, koba komi iyayen Lubna sun taka rawar gani akansa, kuma har gobe yana ganinsu da mutunci bakuma zai manta da karamcin dasukai masaba a baya......
Jin mama tayi shiru yagane tagama NATA, muryarsa a tausashe ya ce, "tom mama kiyi hak'uri amma bawannan maganarce dama kawoniba.
Tsaki mama tayi ta ce, " kaji zancen banza to miya kawoka!?".
Saida ya had'iye wani yawu k'irjinsa yana dukan uku-uku ya ce, ''mama na saki Lubna tunkafin na kwanta a asibiti".
Ba mamaba har Mufida da Rafi'a dake k'ok'arin shigowa saida suka daskare awajen, maganarsa ta razanasu.
Cikin tsawa mama ta ce, "Umaru bakada hankaline!!?, kokuwa kafara shaye-shaye bansaniba!!?".
d'ago jajayen idanunsa yayi yana kallonta, cikin girmamawa ya ce, " wlhy mama bana shan komai, amma idan kin bani dama zan fad'a miki dukkan abinda yafaru harna saketa.
Wani huci mama tasauke harda hura hanci ta ce, "ina jinka.
Ya Umar ya sauke ajiyar zuciya sanan cikin nutsuwa yafara zayyanama mama komai, Rafi'a da Mufida sai hawaye sukeyi, mama kanta jikinta yayi sanyi, wani k'auna da tausayin d'an nata suka ratsata, tabbas tana matuk'ar son 'yayanta mafisifar son kud'i da hange-hangene kawai suke dakusheta, ya Umar yayi shiru ayayinda yakai karshe, zuciyarsa sai zafi takeyi da rad'ad'i, jiyay k'irjinsa yafara nauyi, addu'arnan ta yaye bak'inciki da tafiyar da k'uncin zuciya yafara ambata.....
*↓*
*_“Allahumma inni abduka ibnu abdika ibnu amatika, naasiyatin bi yadika, maadhin fiyya hukmika adlun fiyya k'adha'uka as'aluka bi kullis min huwa laka sammaita bihi nafsaka au anzaltahu fiikitaabika au allamtahu Ahdan min khalk'ika awista' asarta bihi fii ilmil gaibi indaka an taja'ala k'ur'ana rabii'a k'albii, wa nuura sadrii, wa jalaa'a huznii wa zahaaba hammi”._*
_(ya ALLAH ni bawankane kuma d'an bawanka, kuma d'an baiwarka, makwarkwad'ata a hannunka take, hukuncinka zartaccene akaina, kuma k'addararka gareni mai adalcice ina rok'onka dakowanne suna Naka, Wanda ka ambaci kanka dashi, koka saukar dashi acikin littafinka, koka sanar dashi ga wani daga halittarka, koka ke6ance kanka da saninsa acikin ilimin fake da ke wurinka daka Sanya alkur'ani ya zama kaka ga zuciyata, da haske ga k'irjina, da kwaranyewa ga bak'in cikina, dakuma mai tafiyar da damuwata)”._
*↓*
*_“Allahumma inni a'uzu bika minal hammi wal huzni, wal ajzi wal kasali wal bukhli wal jubni, wadhal'id daini wa galabatir rijaali”._*
_(ya ALLAH! ina neman tsarinka daga damuwa da bak'in ciki, da gajiyawa da lalaci, da rowa da ragwantaka da nauyin bashi, da rinjayen mazaje)._
Ahankali k'irjinnansa yafara rage nauyi, zuciyarsa yafara sanyi, wata nutsuwace tafara riskarsa babu abinda yakeyi sai sauke ajiyar zuciya, da sauri Rafi'a tabud'e firij ruwa tad'akko batareda ta nemi kofiba ta mik'a masa, shima bai tsaya tambayar kofinba ya 6alle murfin yana kwankwad'awa cikinsa, saida yashanye ruwannan tas sannan yadire gorar, dama k'aramar gorace, kansa yad'ora jikin kujera yana sauke numfashi ahankali, bayan wasu 'yan mintuna nutsuwarsa tadawo gaba d'aya, har bak'in cikin da mutane suka cusa masa d'azu wajen neman aiki dukya kwaranye, saima wani nishad'i da farinciki daya mamayesa.......
Maganar mamace ta sauka a kunnensa, cikin tausayawa ta ce, "ALLAH ya k'yauta, saikadage yanzu kafara neman aiki da takaddunka, dama kaine kak'i aii tuni, yanzu da aikin kayarda ya samama maka alokacin daya baka za6i aikaga da haka bata faruba ko?........
Kallon mama yakeyi k'ur da mamaki wai ita har yanzu batayi laushi bane?, wai sai yaushene mahaifiyarsu zata daina wanan masifaffen son kud'in nata da hange-hange, (wata zuciyarsa ta ce, " addu'a kawai zakucigaba da mata").
Yananan zaune harta gama surutanta, jin ankira sallar isha'i yamik'e yamata sallama.
Awaje yatadda k'annen nasa mata duksunyi tagumu, yata6a Mufida dake kusadashi, "k! Lfyarku kuwa?".
Figigit suka dawo hayyacinsu, babu komai yaya. Okey tomni nawuce saida safe.
Lah yaya munfa kusa gama abinci katsaya kaci mana.
No ngd saida safe... Yafad'a yana fita.
Rafi'a da Mufida suka bishi da kallo cikin tausayawa.
Kai tsaye gidansa yanufa, baishigaba saida yayi sallar isha'i a masallacin anguwarsu sannan yashiga gida. Tun a tsakar gida yaga canji Dan yau gidan yasha gyara, yana shiga abban fallo wani k'amshi mai dad'i yabigi hancinsa, dukda babu komai afalon sai agogo amma yasharu tas sai k'amshi ke tashi, jin tafiyar abayansa yasakashi d'agowa da Sauri..............
*_(((S))).......2017_*
*_I Love you all my sweet fan's_*💋
[12/2/2017, 4:11 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
*_page→27-28_*
........Asma'u ce sanye cikin doguwar riga ta atanfa, kayan sunyi bala'in zama ajikinta d'as, taci kwalliya ta alfarma sai bulala k'amshi takeyi, cikeda yanga tak'araso gareshi, shikam tsaye yake gingiringin tamkar wani gunki, harta k'araso gareshi amma bai motsaba.
Cikeda mamaki Asma'u take kallonsa, miya samesa haka?, kokuwa kwalliyar tatace batayibane?, shiga tayi bin jikinta da kallo tamkar mai Neman wani wani Abu, can tad'ago tana kallonsa itama, ya Fharuk lfy kuwa?.
Firgigit yadawo hayyacinsa tareda sauke wata nannauyar ajiyar zuciya!, 'yan kame-kame yafara na basarwa, no. babu komai yafad'a yana nufar d'akinsa.
Binsa da kallo tayi saikuma ta tab'e baki, kadaiji dashi tayi maganar tana masa gwalo😜.
Ya Umar nashiga d'akinsa yazube bisa katifar datasha d'an karan gyara, lumshe idanu yayi yana murmushi, yadad'e baiji farinciki irinna yanzuba, a 'yan watannin nan yama manta shi macene kokuwa namiji?, kwata-kwata bayajin wata sha'awa ko son kasancewa da mace, damuwa ta mantar dashi farinciki da nishad'i, yaukam Asma'u ta tunatar dashi koshi waye, Dan kwalliyarta tasakasa begen wani Abu, babu k'arya yarinyar tanada jiki irinna mata masha ALLAH, hannu yakai yashafa sumar Kansa wadda ba gayubane yasakashi tarata, a'a damuwace kawai da rashin lokacin kai, tashi yayi zaune yanamai bin ko'ina na d'akinsa da kallo, komai tsaf kamar ba d'akin daya zama bolaba acikin kwana hud'u dasuka wuce.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda furta *_“Alhamdllh alaa kulli hallin”._*
A gaggauce yatashi yacire kayansa, wanka yashiga sauri-sauri ya kammala Dan yana burin sake ganin Asma'u da k'yau, baiwani d'auki dogon lokaciba yagama shiryawa cikin wando iya gwiwa da k'aramar Riga mara hannu, turare yafesa sanan yasaka silifas yafito babban falon dayake tamkar zaure, babu kowa afalon Asma'u takoma d'akinta, shima d'akin nata yanufa, tana a falonta zaune kan tabarmar data shimfid'a waya taketa latsawa tana kallon hotunan ya Umar sannan yana Umar Fharuk d'insa, tana murmushi, Dan sanda akayi hitunan yana wasa da nairane, shikansa yana son hotunan sosai, yad'an dad'e tsaye yana k'are mata kallo, ganin batasanma yanayiba yay mata gyaran murya.
Jikinta har rawa yakeyi wajen 6oye wayar.
Baice da ita komaiba yazauna kan tabarmar, saida yazauna sanan yamik'a mata hannu alamar tabashi wayar yagani.
Idanu ta kwalalo masa waje, ya Fharuk bafa wani Abu baneba. Uhm nasani, kibani dai. Marairaice fuska tayi tamkar zata FASA kuka Dan batason yaga mitake kallo, ALLAH ya bawani abun ashsha bane hotuna nake kallo.
Hotunan waye?, yay maganar cikeda cin magani.
Uhm uhm namunefa nidasu Hasiya da Fatee....... Batama bari ya tanka ba tamik'e tafita Dan kawo masa abinci.
Binta yayi da kallo, dukda bai yarda da itaba.
Yana nan zaune tashigo da tiren abinci, kallon tiren yayi dake d'aukeda komai sabo, kuloli Kofi cokula filet duk sababbi, kallonta yayi da k'yau yanzukam fuskarsa amatuk'ar d'aure take, ayatsine ya ce, "wad'annan abubuwanfa INA kika samu kud'in siyensu?.
Ad'arare ta kallesa muryarta na rawa ta ce, " uhm ya Fharuk sauran kud'in wayarnanne dama nabama Fatee tasiyo mana saboda naga ko kofin shan ruwa babu agidannan, dama sonake ka kammala cin abincin namaka bayani amma kayi hak'uri nayi Abu batareda Neman shawararkaba.
Ahankali ya furzo huci daga bakinsa yana kauda kai daga gareta.
Jiki a sanyaye tahad'a MASA abincin agabansa, tuwon masarane daya tuk'u da k'yau saikuma miyar k'u6ewa d'anya dataji d'anyen kifi da daddawa sai k'amshi ke tashi, a jok d'in kam zo6one shima sai k'amshin kayan yaji yakeyi.
Tunkafin yafara cin abincin k'amshin yawunsa keta tsinkewa, sosai ya k'agara yafara saka lauma, amma jinkai da k'asaita irinta mazaje yasakashi mazewa harda kauda kai gefe.
Cikin sanyin Murya Asma'u ta ce, "ya please kaci abincin, Dan ALLAH kada kamin horo akan hakan."
Tausayi tabashi Dan muryarta har rawa takeyi, amma baice komaiba, hannunsa takama tasaka acikin ruwan data aje arobar wanke hannu, Fes ta wanke hannun yana jinta, bai ankaraba yaji hannunsa acikin miyar, kallonta yayi da sauri, ta langa6e kai gefe tamkar zata FASA ihu, kona baka da kaina?, tayi maganar hawaye na zurara akumatunta.
Kad'an yarage ya fashe da dariya amma saiya gimtse ya antaya mata hararama.
Tashitayi tamkar Mara laka tashige bedroom, shikuma yaraka bayanta da murmushi, tana shigewa yafara saka lauma yana lumshe ido saboda dad'in da tuwon kemasa.
Saida yaci yak'oshi sanan ya wanke hannunsa, tuwon yad'iba a filet yatafi d'akinta danyasan itama bataciba, kwance take akan katifa rubda ciki da alama ma kuka takeyi, aransa ya ce, "idon kuka kenan".
Zama yayi abakin katifar yana ambatar sunanata, Husna tashi kici abincin. shiru tamasa batayi koda motsiba.
Ganin haka yakamo hanninta yana murzawa ahankali, zumbur Asma'u ta tashi zaune tana muzurai, wani yarrrr! Taji yayinda yake Mirza tafin hannunta, batareda yace mata komaiba yad'ora filet d'in abincin saman cinyarta, maza kicinyeshi tas.
Fuska ta shagwa6e tana turo baki nima na k'oshi tunda kaima bakaciba, ido d'ya yad'age yana kallon shagwa6a, saikuma yayi murmushin gefen baki yana fad'in waya gaya miki banciba?, saida nakusa cinyewama nakawo miki sauran.
Ya Fharuk da gsk?.
Kansa ya jinjina mata.
Bismillah tayi tafara cin tuwonsa, shikuma cikin dabara ya d'auki wayarta yafara bincike, ganin hotunansa take kallo d'azu yasakashi sauke ajiyar zuciya, tayi sagare tana kallonsa Dan mamakin wannan ajiyar zuciya, saida tagama tsaf taje ta wanke hannu sannan tadawo ta zauna abakin katifar hannunta d'aukeda kud'i masu d'an yawa har kashi biyu.
Naminene?, yafad'a batareda ya kar6aba.
Zan maka bayani aii.
Yau bayan fitarka Inna tazo gidannan, takawo mana kayan abinci, sannan tace nabaka wad'annan kud'in tanuna masa kashi d'aya acikin kud'in, wad'an nan kuma na sauran wayatane, saidai kayi hak'uri nata6a wasu aciki.
Amma ya Fharuk nayi wani tunani. Mizai hana shagonnan na k'ofar gida kazuba kayan provisions acikinsa har muga abinda ALLAH zaiyi akan Neman aikin naka.
K'yawawan idanunsa ya tsura mata yanamai kallonta cikeda so da tsananin k'auna, tun Asma'u tana yarinya yake sonta amma wasu abubuwa suka hanashi nunawa dakuma soyayyar Lubna data rud'eshi kasancewarsa mutum maison wayayyar mace. jiyake tamkar ya rungumeta. amma bazaiyi hakaba Dan gudun karta rainashi.
Jin yayi shiru gashikuma ya tsura mata idanu ta ce, "ya Fharuk! Mike faruwane?. Ko shawarata batayi daidai baneba?.
Ajiyar zuciya ya sauke, a'a Husna shawararki tayi, amma kibari zanyi tunani. Kud'in inna kuwa gsky bazan amsaba, za'a maida mata abinta, idanni har ban bataba, amatsayinta na uwa agareni, tom baik'yautu na kar6a daga garetaba.
Humm yaya kasandai halin Inna sarai, wlhy na tabbata bazata amshi kud'innanba, tunda har tayi niyya. Amma kagwada kagani, Dan kunfi kusa.
Hararta yayi, kokina kishine?.
Asma'u tazaro idanu waje, ya Fharuk nikam kishinmi zanyi dakai? bayan inna tabamu labari tunkan tasamemu kaine d'anta, yanzukuwa danta samemu bazata ta6a had'a soyayyarka da tamuba. Tokaga idanma nayi kishin, ainayi abanza. Ammafa inad'anyi kad'an. ‘tayi maganar tana dariya damasa gwalo.’
Shima murmushin yayi, yamik'a hannu zai cafkota ta zulle. Filo yad'auka yajefeta dashi, wlhy nakula yarinyarnan kinrainanifa.
Hannu tasa takare kanta daga filon, cikin dariya ta ce, "ALLAH niban rainakaba." ‘ashagwa6e take masa magana.’
Shikam yayi sagade yana kallon yanda takeyin dariya k'yawawan fararen hak'oranta suna burgeshi.
Saida tamik'e tsaye sannan tad’auki filon itama ta jefa masa, ta antaya da gudu waje.
Lalala nikika jefama fillo? Lallai yau jiki magayine. Yay maganar yana mik'ewa yabita abaya da filon.
Tana ganinsa tafita babban falo da gudu tana dariya, zagaye falon sukaitayi yana tilla mata filo, itakuma tana gudu.
Sunkai wasu mintina ahaka har Asma'u tagaji sosai tafara bin bango tana haki.
Taku biyu ya damk'ota, zille zille tafara tana fad’in ya Fharuk natuba, ALLAH bazan sakeba.
Zaki gayamin hakane idan kika horu, gaba d’aya yad'auketa yakoma d’akinta.
Sai fad'in yayi hak'uri takeyi ALLAH bazata sakeba.
Ahaf yarinya zancen kikeso kuma, aii daga yau idan ance kimin rashin kunya bazaki sakeba kuma.
Wayyo na Inna plss, narantse bazan sakeba.
Ko saurarrta baiyiba yajefata bisa katifarta.
Zuwa yanzukam da gsk tsoronsa tafara shigar Asma'u, kardai mutumin nan yace mata wani Abu zai mata, nashiga uku ni Asma'u, wlhy tsoro nakeji, atsorace ta yunk'ura zata tashi ya damk'ota da sauri suka fad'a saman katifar atare..........
_“kuyi hak'uri da wanan wlhy murace taketa nuk'urkusata, ga ciwonkai🤧, da k’yar na iya wannanma.”_
*_(((S))).......2017_*
*_Love you all_*
[12/5/2017, 5:34 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
_Wayyo mura🤧🤧🤧🤧🤧🤧🤧🤧._
*_page→29-30_*
........Humm miye labarin Lubna ne? Su Lubna anagida hankali kwance, tak'ara k'yau da k'iba tamkar ba itaba, hakamasu Afrah sunyi 6ul-6ul dasu, an maidasu wata had'ad'd'iyar makaranta ta 'ya'yan manya.
Lubna duk inda taso zuwa takeyi, gakud'i ga Hutu, babu ruwanta dawani maganar iddah sai kula samari takeyi yara k'anana. (Dan mamanta ta ce, "bazata auri mai mataba, saidai saurayi d'anyen jini). Tako hau kan wannan magana tayi d'ane-d'ane. dukda ta ce, ''ita yanzu aure baya gabanta. Karatuma zata koma."
Gantalin zuwa biki kuwa itada Suhaila sunmaidashi tamkar cin gwaza, Lubna tabiye mata sosai tamkar wata budurwa, ko bak'i akayi a gidan ba'a cewa Afrah da Amrah 'ya'yan Lubna ne, Dan basaso ace tata6a aure barema harta haihu.
Dad bazama yakeba sosai Dan haka baisan wainar da'ake toyawaba agida, Ameer da Safwan yayyensu suma dai samma kal, Dan duk taron kwara da ama ne, babu mai tada wani suma shaid'anun kansune, Neman mai gyarasu sukeyi barema su gyara wani.
Ayanzu hakadai cikin hidimar shirye-shiryen bikin Ameer d'in sukeyi, zai auri d'iyar wani babban k'usa a gwamnati, shirin biki takeyi na garari na d'angata.
Duk suna zaune afalo dad ne kawai babu Dan yaje k'asar Chaina, akwatinane guda 30, set biyar kenan, kowanne da kalarsa, dank'are suke da kayan alfarma na garari, kayan lefen Ameer ne dasukaje gabad'aya gidan har k'asar Dubai suka had'osu, jiya da daddare suka dawo, shine yau ake duba abunda babu, kayane na garari babu na k'asa da dubu d'ari biyu, kayan sakawa kawai na less, shadda, atanfa, material, dadai sauran yayi, kala d'ari hud'une, banda su jallabiya, k'ananun kaya..etc, kayan shafa kam da takalma jakunkuna aiba'a magana, barema azo kan yari, sark'ok'in zinari goma sha biyu, 'yar dubu d'ari biyar itace k'arama. Humm masu karatu! Mahaifinsu Lubna fa bak'aramar dukiya ya taraba, suma 'ya'yansa babu Wanda bashida hannayen jari a ciki da wajen k'asarnan, saidai kuma acikinsu babu mai aikinyi Dan bama su nutsu sunyi karatunba, kasuwancin kuma bazuwa sukeba bare su koya, to anrigada antara musu.
_wlhy 'ya'yan many an k'asarnan basa karatu ko kad'an, 'ya'yan talakawa muke maida hankali muyi karatu komai wuya komai dad'i, amma da zaka karad'e madafun ikon k'asarnan zakaga duk 'ya'yan masu fad'a ajine awajen, akuma many an kujeru, mu 'ya'yan talakawa mune ak'asa k'alilanma kenan acikinmu da'aka d'auka aikin, shiyyasa kullum k'asarmu tana cikin masifu iri-iri, tomasu rik'eda k'asar duk basusan ciwon kansuba ballantana su taimaki na k'asa dasu, basusan ana talauciba bare su taimakawa talaka, basusan komaiba saibin k'asashen duniya suna shek'e ayarsu yanda suka gadama da karuwan kafirai._
ALLAH yasa mudace.
Lubna tad'aga wata sark'ar zinari tana fad'i kai 'yan uwa sark'arnanfa tawuce dani wlhy, dolene nakoma Dubai kafin biki nima nasaka ayimin.
Harararta Ameer yayi, ya ce, "kefa dad'ina dake kenan, babu yanda za'ayi mutum yayi Abu mai k'yau saikinyi copy copy, ai abin kunyane ma ace aga amarya da sark'ar k'anwar ango ma da ita."
Safwan ya ce, "bar yarinyarnan kaji, aidama agidan wancan k'aban take har a yanzu dabata samu yanda takesoba."
Cikin shek'ewa da dariya Suhaima ta ce, "bro's kubarta, wlhy badan ceton da momy taima baby ba dayanzun k'ila mun fara bata kwancen kaya."
Duka Lubna takaima Suhaima, tana fad'in bakinki ya sari d'anyen kashi muguwa kawai. Kuma wlhy duk Wanda Yakuma had'ani da Umar zamu kwashi 'yan kallo agidannan, natsaneshi! Na tsaneshi wlhy!." ‘tayi maganar tana hawaye.’
Safwan dake Kusada ita yaruk'o hannunta, sorry babyn dad! Karki damu bazamu sake fad'aba kinji, sark'a kuwa dakud'inama zan saya miki.
Murmushi tamasa tana mai share hawayen fuskarta.
Daga nan Suhaima da Ameer ma suka bata hak'uri, murmushi mom tayi tana cigaba da birkita kayan Dan bincikawa.........
____________________
Koda ya Umar yajefa Asma'u kan katifa shima saiya fad'a Kusada ita. Idonta cikeda kwalla tadubeshi, pls ya Fharuk natuba, ALLAH bazan sakeba.
Ido d'aya yad'age yana kallonta da d'ayan, yamatso daf da ita tamkar zai shige jikinta, k'amshin turarensa na matuk'ar dukan hancinta, gadad'in k'amshin da turarensa kemata ga fargabar abinda zai mata, tad'an runtse idanunta danjin bai tankaba.
Jin hannumsa akan k'irjinta Yakuma firgitata, tawaro idanunta yayinda shikuma ya ida kai hannunsa kan kunnenta na dama, Wanda dama shiyakeso ya damk'o.
Jin anmurd'a mata kunni da k'arfi yasakata sakin wata kasalalliyar k'ara tareda ruk'o hannunsa tana shiii da baki. Wayyo ya Fharuk wlhy akwai zafi, sheeeeeee! Plss natuba wlhy.
Shikam murmushinsa kawai yake saki tana k'ara Murza kunnen saboda salon mugunta, saida ya tabbatar taji gargad'insa sanan yasaki kunnen yatashi yana wata dariyarsa wadda Asma'u batasanma ya iyaba.
Ficewarsa yayi, itakuma tana rik'e da kunnenta dakemata rad'ad'i da zugi, jitake tamkar tarushe da kuka, afili ta ce, "mugu d'an masa, ALLAH yasakamin.
Yana shiga d'akinsa yafad'a kan katifarsa fuskarsa shimfid’e da murmushi. Lumshe idanunsa yayi tamkar mai barci, tabbas abaya yayi soyyaya da Lubna, kuma har yana ganin bazai ta6a son wata 'ya maceba bayan ita, saboda yasameta wayayya yanda yake buk'ata. Ya burkita kwanciyarsa zuwa rubada ciki tareda k'ara k'an k'ame filo ak'irjinsa, shikad'ai yasan miyakeji.
dannidai bilyn Abdul bazan saniba🤷🏽♀........
Washe gari dawuri Ya Umar yashirya cikin shadda milk color, d'inkin zamani, tamasa k'yau aynun, idan bakasan yana cikin wani haliba saika d'auka irin masu kud'innanne ko 'ya'yan masu kud'i da Hutu ya huda, duk wannan bitada k'ullin da ya Umar yashiga hakan bai canja kalar fatarsaba, tana nan lumi da ita, sai shek'i da Annuri ketashi, gakuma gashi daya kwanta luf luf afatar tasa.
Fitowar Asma'u kenan daga wanka yashigo d'akin, dasauri taja hijjab tasaka.
Shima kauda kansa yayi gefe, zanje nagaida Inna, kokinada sak'o?.
Kallonsa tayi sosai da mamaki, yaukuma wani sabon salonne akazo dashi?. Ganin kallon datake masa yasashi juyawa yana fad'in tunda bakida sak'on saina dawo. ‘batareda yajira amsartaba yafice abinsa.
Ta6e baki Asma'u tayi, afili ta CE, "hummm ya Fharuk kai zumane nalura saida wuta, indai banda Neman magana yau kafara zuwa gaida inna? Kata6a fad'amin zakaje? Bare sallamar saika dawo?....
Cigaba tayi da mitarta tana shafa mai, saida tagama tsaf tasaka kaya sannan tafara shirin gyaran gidan.......
Agidan inna kam bayan ya Umar yashiga ya gaida baba sukad'an ta6a hira sannan yashiga d'akin inna, tana zaune tana karyawa, Fatee nagefenta tana yankan d'inki Dan bayan ta kammala secondary d'inta sai baba ya ce, " tashiga wani makaranta nan kusadasu na koyon d'inki tunda basuda k'arfin dazata cigaba da karatu kafin kuma ALLAH yakawo mata miji, sosai tadage a makarantar takoyi d'inki acikin wata shida, zuwa yanzukam takware harma kawomata mutane sukeyi.
Inna ta washe hak'ora tana fad'in lale dakai yarona.
Shima fuskarsa shimfid'e take da murmushin yaje Kusada inna yazauna yana fad'in yauwa innata, nasameki lfy?.
Lfy lau Umaru ya iyalin naka?.
Lfy lau suke inna, tamace agaidaku.
To ina amsawa.
Fatee ta ce, "ya Umar ina kwana?.
Lfy lau Fateema tela, ya d'inkin? Kinadai k'ok'ari ko?.
Eh wlhy Yaya inayi sosai, yanzuma kayan gidansu zaliha naketa d'inkawa na ankon bikin kareema nanda next week, kusan kala 20 kenan na d'inka na manya da yara.
Masha ALLAHU, amma kinyi k'ok'ari, kuma naji dad'i, inason mitum mai k'ok'ari akan Sana'a komin k'an k'antarta, ALLAH yak'ara bada sa'a.
Ameen Yaya ngd sosai, ina Anty Asma'u?.
Tana gida nabarota tace agaisheku.
Muna amsawa da k'yau.
Inna Hasiya fa? Tana inane?.
Hasiya tana islamiyya kasan malama za'ayi wanan waje Umaru.
Da k'yau Inna, aii anason Haka, itama ALLAH yacika mata burinta.
Ameen Umaru yacikamana gaba d'aya.
Ya Umar yagyara zama yana fad'in inna dama akan kud'in jiyane dakika kaima Husn........
Hannu inna tad'aga masa batareda ya k'arasaba, kaga Umaru nidai banbaka kud'innan Dan wani abuba, nabaka amatsayina na uwa agareka, tsakanin uwa da d'akuwa aii babu jayayya ko?.
Ya Umar yad'aga mata kai.
Tacigaba dafad'in to Indai kasan hakane bana buk'atar jin komai daga bakinka, kaje kasamu sana'a koda k'aramace kafara ALLAH yasaka albarka acikinta. Kokad'an banaso kacigaba da wahalarmin da kanka awajen Neman aiki, ALLAH yabada nasara akan duk abinda aka saka hannu.
Ameen inna, ngd sosai dakasancewarki uwa agareni, lallai nayi dace dasamu uwa tagari mai share hawayena, ngd sosai inna, ALLAH yak'ara tsawon kwana da lafiya, ng......
Kaga godiyar ta isa haka, ALLAH yayi muku albarka gabad'aya.
Ameen suka amsa shida Fatee daketa zuba murmushin jin dad'i.
Inna mikuka dafa yunwa nakeji?.
Umaru kokone da Alala da Fatee tayi, Fatee maza tashi ki kawo masa.
Amma ita lalatacciyarnan tana ina kafito baka karyaba tabarka?.
A'a inna balaifinta baneba, nine, nayi sakkon fitowane da wuri saboda nabiya wajen wani abokinane kafin nazonan dayace zaimin hanyar aiki, amma koda najema saisukace yawuce Abuja tun ajiya, dama yamin k'aryane kawai irinna 'yan boko.
Karka damu Umaru inna tafad'a tana kwafa, komai zaizama labari wataran, kama ture batun samun aiki karungumi 'Yar sana'ar da ALLAH yaza6a maka, inada yak'inin wataran sai sundawo suna nemanka da kud'i kagagara ganuwa agaresu.
Shikenan inna nahak'ura, yanzudai munyanke shawara nida Husna............nan yazayyanema inna komai akan maganarsu tajiya da Asma'u tamasa.
100/100 inna tabada goyon baya tareda addu'ar alkairi.
Yadad'e agidan, Dan har shabiyu sanan yatafi.........
_____________________
Tundaga ranar suka shiga gyaran shagon dake k'ofar gidansu kamar na 'yan tireda, cikin kwana hud’u aka zuba komai, dukda kayan bawani yawane dasuba amma Alhmdllh sund'an k'ayatar.
Tun aranar suka fara ciniki kasancewar dama babu wani shagon tireda a anguwar, sai idan anje can k'asan layinsu ko baya.
Tunda safe ya Umar kezuwa yabud'e saboda masu sayyar safe, idan Asma'u ta kammala break taje takai masa shagon tunda da k'ofa tacikin gidan.
Hakama da rana, da daddarema haka, zuwa 11:30 saiya rufe yashigo gida.
Tsakaninsa da Asma'u kam babu komai sai gaisuwa da girmamawa, ita tsoronsama takeyi, aganinta tunda yafara mata gargad'in ranar to aii zuwa nangaba duk abinda yazo zuciyarsa zai iya mata.
Yaukam antashi da muku-mukun sanyi, wanan yasaka Asma'u tashi da zazza6i mai zafi da mura.........
*_(((S)))).....2017._*
*_luv you all_*
[12/6/2017, 4:15 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
*_page→31-32_*
........Tunda tayi sallar asuba takoma ta k'udundune a bargo.
Shikam ya Umar tundaga masallaci baima dawo gidanba yana shago, agogo ya kalla dake cikin shagon har 9:37am amma Asma'u bata lek'oba, sallamar wani saurayi tak'atse masa tunani, ya amsa yana mik'a masa hannu suka gaisa, saurayin yace abashi Sabulun wanki, d'akkowa Ya Umar yayi yabashi, saikuma ga wasu yara, doledai ya hak'ura yacigaba dabama mutane abinda sukeso, haka shagon yake wuni cikin shige da fici namasu siyayya.
Har 11 tayi baisamu damar shiga gidanba, gashi Asma'u ma bata lek'oba, yanaji azuciyarsa badai lafiyaba.
Can zuwa 11:30 mutane sukad'an lafa saiya rufe shagon yashiga gida.
Har yanzu Asma'u nak'udundune abargo, sai rawar sanyi take faman yi da sambatun zazza6i, dama ita haka take indai tana zazza6i tatayin sambatu kenan.
Da sallama ya Umar yashigo, ganin Asma'u a kwance cikin bargo sai gabansa yafad'i, k'arasawa yayi cikin d'akin sosai yana fad'in lafiya kuwa?.
Asma'u dabatasan yanayiba sai rawar sanyi takeyi tana sambatu dakiran baba, inna, Fatee, Rafi'a, hasiya, kuzo kutaimakeni, wayyo ya Fharuk zan mutu kazo plzz.....
Ganin yanda take abirkice yak'arasa da sauri yazauna bakin katifar, husna lafiya kuwa? Yay maganar yana yaye k'aton bargon data lilli6a ajikinta, wani hucin zafin zazza6i yabigeshi, da sauri tarik'o hannunsa tana fad'in wayyo Yaya rufeni sanyi nakeji sheeeeee!!!!.
Lilli6eta yayi tareda fad'in sannu, amma miyasa baki fad'aminba tun d'azun? Haba mutum yata zama da ciwone?.
Mik'ewa yayi zai fita tarik'o hannunsa tana kuka, wayyo ya Fharuk kaina kamar zai fashe, k'irjinama haka, kataimakeni wayyo.
Tausayi tabashi sosai, dawowa yayi yazauna akusada ita, tad'ago da dak'yar tad'ora kanta saman cinyarsa, kokad'an bataso yatashi data Kusada ita, (dama itakam wanan salon zazza6inta kenan, saitaji wani akusada ita). Ya Umar yad'an rintse ido danjin yanda zafin zazza6inta ya ratsamasa jiki, tausayinta yakuma kamashi, kanta yashafa ahankali, husna kikwanta zanje nama muktar maganane kozai samo mana doctor d'in dazai dubaki.
Uhm uhm Yaya banason allura wlhy, kabarni kawai.
Yaya zan barki husna! Kinta6a ganin anbar mutum cikin ciwone? Kiniji yanda jikinki yayzafi kuwa?........
Kafin tace wani abu sai sukaji sallaman Rafi'a.
Ya Umar ne ya amsa, tatsaya ak'ofar d'aki danjin muryarsa, jin shiru nawani lokaci ya ce, "shigo mana."
K'arasowa tayi cikin d'akin, ta gaida ya Umar sanan ta tambayi miya sami Asma'u?.
Batada lfyne, yauwa shiga nan makwaftanmu kima muktar magana kozai samo mana doctor dazaizo gida?.
To Yaya, ammafa masu sayen Abu suna jiranka a k'ofar shago.
O!. kinga kar6a key d'in, idan kinmasa magana saiki bud'e ki zauna, kafin nagama.
OK, tana kar6ar key d'in tafice da sauri.
Mintina k'alilan saiga Muktar yazo, dak'yar ya Umar yasamu Asma'u tabarsa yatashi, fitowa yayi wajen Mukhtar, hannu yabasa suka gaisa sanan yamasa bayanin ga doctor Al-ameen nan zuwa.
OK Abokina ngd sosaifa, ALLAH yabar zuminci.
Abokina aii babu godiya tsakaninmu, munrigada munzama d'aya, ciwon madam kodai munsami baby ne?.
Dariya ya Umar yayi yana fad'in abokina baby kuma? A INA?. Hhhh babu wani baby abokina, zazza6ine kawai wlhy.
To shikenan ALLAH ya k'ara sauk'i, cikinma muna addu'ar zuwansa nan kusa.
Murmushi kawai ya Umar yayi batareda yace komaiba.
Babu dad'ewa saiga doctor Al-ameen ya iso, suna gaisawa ya Umar yamasa iso zuwa cikin d'akin Asma'u. Har yanzun kuka takeyi da surutanta, ya Umar yazauna Kusada ita, yayida doctor Al'ameen ke a zaune bisa wani tum-tum da lubna bata d'aukaba, Mukhtar kam na tsaye daga k'ofa.
Tambayoyi yamata tana basa amsa, amma fad'i take pls doctor kada kamin allurafa.
d'an dariya doctor Al-ameen yayi, ya ce, "madam kina tsoron allurane?."
Kanta ta jinjina alamar a'a, cikin muryar Mara lafiya ta ce, "doctor banasone kawai."
Gashi kuma dolene amiki ita, Dan teiport nadamunki sosai. K'an k'ame hannun ya Umar tayi sosai tana fad'in pls Yaya kace karyamin banaso. Harararta yayi danshi surutun yafara bashi haushi, yanada kishi sosai.
Magun guna yabata sanan ya ce, "zai mata alluran dabata so d'in. Hawaye tafara zubarwa Rana k'ara k'ank'ame ya Umar tamkar zata koma cikin jikinshi. Kamo hannunta yayi yamik'ama doctor Al-ameen Wanda yake rik'e da igiya dansan d'aura mata yanemo jijiya. Igiyar ya d'aura mata, cikin sa'a aka samo jijiyar. Hawaye takeyi sosai Rana k'ara k'ank'ame ya Umar.
Tana ganin yanufota da allurar yak'ara sautin kukanta, taso tabama Umar dariya amma saiya gimtse, doctor da Muktar kam saida suka murmusa. Wata uwar harara da ya Umar ya galla matace tasakata nutsuwa waje d'aya, amma hawayen basu daina zubaba. Tanaji tana gani akamata allurarnan, har aka gama tana k'ank'ame da ya Umar.
Doctor ya kalli ya Umar ya ce, " Alhaji insha ALLAH zazza6in zai sauk'a, taci abinci tasha maganidai, ammafa idan har zuwa yamma akwai Matsala saika kirani.
Okey doctor ngd sosai ya Umar yafad'a yana bashi hannu, saida suka rakashi har motarsa sanan ya Umar yadawo Muktar kuma yashiga gidansa.
Babu dad'ewa saiga matan Muktar Sadiqqa tashigo gidan, lokacin ya Umar na k'ok'arin had'ama Asma'u shayi.
Gaisuwa sukayi da ya Umar, ta tambayeshi mai jiki, sanan ta ajiye kular abinci data kawo. A'a Maman Faisal abokina yatadoki ko?.
Lah babu komai wlhy, aii kawai kama koma shagon saina lura da ita, abincima nanan na ajiye a shop d'in. A'a aii hidimar tayi yawa Maman Faisal. Wlhy babu wani yawa Indai ba rainawa kayiba.
Mik'ewa ya Umar yayi yana dariya, ni na' Isa?, aii sadai nace ALLAH yasaka da alkairi yabar zuminci kawai.
To Ameen.
Yana fita saddiqa tashiga hidimar bama Asma'u abinci, saiga Rafi'a da ya Umar ya kar6eta ya ce, "tashigo gida.
Atare suka gyara gidan tsaf, bayan Asma'u taci abinci Saddiqa tasakata tayi wanka tasha magani, sanda tafito angyara d'akin tsaf, saikawai tasaka wasu kayan takuma kwanciya sai barci.
Saida suka gama komai sannan Maman Faisal tawuce gida, Rafi'a kam saida tamusu abincin dare takuma gyara gidan tsaf sannan tawuce gida Dan tanaso taje islamiyya.
Ya Umar yanata zagayata danyaga yajikin, amma har yamma bata farkaba.
Sai bayan isha'i daya shigo yataradda ta tashi.
Kintashi?.
Kanta tad'aga masa, har yanzun tana cikin bargo. To yajikinnaki?, da sauk'i amma har yanzu inajin sanyi wlhy.
Zai daina shima, tashi kiyi sallah ko?.
Nanma kanta ta jinjina sannan ta yatsina fuska, yaya dama akwai ruwan zafi sainayi dashi, bazan iya da ruwan sanyiba. OK bara naduba ko Rafi'a tazuba a filas.
Rafi'a tawucene?.
Eh tun d'azun tawuce, tanason zuwa islamiyya tace.
Batace komaiba, shima yafita yakawo mata ruwan zafin, dakansa ya taimaka mata zuwa bayi, tsayawa yayi kanta yak'i fita.
Tajuyo tana kallonsa kamar zatayi kuka, kafita to.
Gira yad'age sama tareda d'an langa6e kansa gefe, bazaki iyayi agabana baneba?.
Gyad'a kanta tayi cikeda shagwa6a.
Murmushi yayi, ya jingina da bango harda hard'e hannu ak'irjinsa yana kallonta. Ta marairaice murya tana k'ank'ame jikinta, yaya sanyi nakeji wlhy, kuma zanyi fitsarin atsaye...
d'an zaro idonsa yayi waje, ya CE, "da gsk?."
ALLAH kuwa.
Murmushi yayi mata sannan yafice batareda yace komaiba.
Tana idar da sallan takuma zuwa zata kwanta, rik'o hannunta yayi yana fad'in no zauna ki huta.
Wayyo ya sanyi fa.
Toni wannan sanyi namiyene? Dayak'i tafiya. Bara nakira doctor namasa bayani......
Kafin Asma'u ta ce, wani Abu saiga Faisal (babban yaron Muktar), rissinawa yayi ya gaidasu, yayma Asma'u sannu, sanan ya ce, "uncle Abba ya ce, "kakawo key d'in shop yazauna, kaikuma kazauna wajen aunty.
To yarona ALLAH yayimaku albarka kaji, gashi kacemasa ngd.
Rissinawa yayi yakar6a yafita.
Shikuma yashiga kiran doctor. Bayan sun gaisa yaymasa bayanin harfa yanzu Asma'u tanajin sanyi.
'Yar dariya doctor yayi, ya ce, "wanan aikinkane Alhaji, indai babu zazza6in to Alhmdllh, maganar sanyi kam tana buk'atar d'umin jikinkane kawai.
Da sauri Asma'u da ya Umar suka kalli juna Dan yasaka wayarne a Hans Free.
taja bargo ta kwanta, shikuma yad'auke idonsa daga kanta yamaida hankalinsa akan maganar doctor.
Okey doctor babu damuwa ngd sosai, saida safe.
ALLAH yakaimu Alhaji, agaidamin da madam.
Okey zataji, agaida iyali.
Koda ya Umar ya kammala wayan baikalli Asma'u ba yatashi yafice, itako tak'ara k'udundune kanta a bargo, tamkar wadda ake shirin sacewa.
Waje yaje wajen Muktar, saida sukad'anyi magana ta mintuna sannan yadawo gidan.
Kaitsaye d'akinsa yanufa, yay wanka tareda shirin barci tsaf sannan yakoma d'akin Asma'u.
Harma tafara barci ita.
Yad'an dad'e akanta yana k'are mata kallo cikeda tunani kala-kala tamkar bayason abinda yay niyyar yi agareta na bata taimakon da doctor yabashi shawarar.
Tsawon mintuna sannan yazauna abakin katifar tareda d'aga bargon yashiga ahankali.
Jawota yayi ya manna da jikinsa, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke tareda rinmtse idanunsa. Itakam sai kawai tagyara kwanciyarta danjinta cikin wani lallausan jiki, gawani d'umin mai dad'i da k'amshi. Barcin yaci k'arfinta shiyyasa ko farkawama batayiba.
Amma ga mutumin naku ba haka baneba, jinsa yakeyi tamkar bashiba, tuni yasan shi mutumne mai yawan buk'ata shiyyasa yake tausayin fara kusantar Asma'u, amma yazaiyi? Zuciyarsa takasa daurewa, akwana biyunnan hak'uri kawai yakeyi. Yanason kasancewa da matarsa amma yana gudun karkuma ta rainashi. Yakuma k'ank'ame ta sosai tamkar za'a kwaceta daga gareshi, jin anrik'eta tamau yasakata motsawa, shima saiya sassauta mata.
Addu'a yamusu ta barci, tanata barcinta amma shi yagagara yin nasa saboda kwad'ayin kasancewa da ita................
*_"ngd duknaga sak'on gaisuwarku, harma damasu kirana, harma wad'anda basu sami damaba, dukna gode ALLAH yabar zuminci, nama warke, ammafa ina jiran kazar😋😋🤷🏽♀😄"_*.
Luv you all💋💯
*_Luv you all_*
*_(((S))).......2017_*
[12/9/2017, 8:40 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
*_page→33-34_*
.......Haka yakasance yana gadinta har asubahi baisamu wani barcin kirkiba, itakam bamatasan yanayiba, barcinta tasha sosai, musamman datajita cikin wani ni'imtaccen jiki mai yalwataccen k'amshi, ga d'umi na musamman dayafi bargon data wuni aciki.
Kiran sallar asubahine yasakata farkawa, akuma lokacin wani barci mai dad'i ya d'auki ya Umar kasancewar baisamu yiba farkon dare, ahankali ta bud'e idanunta tanamai ambatar addu'ar farkawa daga barci, saukar numfashin datakeji ahankali visa gadon bayanta yasakata juyawa ta sauke idanunta akan fuskar ya Umar daketa barcinsa. Sosai tawaro idanu waje, azuciyarta ta ce, "la'ila. miya kawo ya Fharuk nan? Kardai tare muka kwana? Nabani wannan abin kunya har ina. Tana k'ok'arin zame jikinta ya Umar yafarka. K'ara rik'eta yayi danjin zata bar jikinsa, kokad'an baiyima zaton asuba tayiba.
Jin haka Asma'u ta ce, " ya Fharuk asuba yayifa." 'Muryarta narawa tayi maganar.'
Bud'e idanunsa yayi shima, ahankali cikin muryar barci ya ce, "Asmah da gsk asubahi tayi?."
Kanta ta iya d'aga masa kawai, amma takasa magana.
Yunk'urawa yay yatashi zaune shima yana binta da kallo, kauda idonta tayi daga kansa tashige bayi. Shima saiya tashi yafita zuwa d'akinsa.
Yana dawowa daga masallaci yalok'o d'akinta, tana zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani, saida takai k'arshen surar sanan tatsaya, dama takusa kammalawa. Kanta ak'asa ta ce, "ina kwana."
Ya ce, "Lfy lau, yajikin naki?.
Alhmdllh. Nama warke.
Masha ALLAH, har sanyin kindainaji kenan?.
K'asa takumayi da kanta Dan kunya, haka kawai yau taji tana matsanancin jin kunyarsa, kokad'an bataso su had'a ido, musamman idan ta tuna cewa aguri d'aya suka kwana, manne da juna kuma..........
Katse mata tunani yayi dafad'in, kinyi shiru, ko har yanzundai kinajin sanyinne? Idan kinaji kuma to sainak'ara baki d'umin jikina.
Tusa kanta tayi cikin cinyoyi, kai ya Fharuk kabari plss.
Hummyim toni minayi kuma?.
Shiru tayi tana k'ara k'ank'ame kanta acikin cinyoyin nata.
Ganin haka ya Umar yamik'e abinsa, shikenan bara naje shago kinsan 'yan makaranta da saurin fita.
Kanta ta jinjina amma bata d'agoba ta ce, ''ALLAH yabada sa'a.
Ameen yafad'a yana fita...........
____________________
Akwana ukunnan sosai ya Umar ke kulada Asma'u, wanan karonkam sunci gari, Dan har mama saida tazo dubata, hakan yayima ya Umar dad'i sosai, dazata tafi yahad'a mata abubuwa sosai.
Dukda batawani d'auki shagon da muhimmanciba tamasa godiya tawuce.
Bayan tafiyar mama saiya shigo gidan, Asma'u nazaune akan katifarta tana canja zanin gado, canjama filo riga takeyi.
Yay sallama. d'ago k'yawawan idanunta tayi tasauke akansa, gira yad'aga mata tareda sakin wani sassanyan murmushi.
Itama murshin tamasa sannan tajanye idanunta tacigaba da abinda takeyi.
Harta wuce?.
Uhm tawuce, yafad'a yana zama bakin katifa. Ya ce, " lallai kekam 'yar gatan mamace, yau har tana zuwa dubaki?.
Ya Fharuk kenan, dama can ni 'yargatan mamace koka mantane?.
Ban mantaba my Asmah Husna!.
Murmushi Asma'u tayi danjin wani salon suna daga yayan nata.
Kwanto da kansa yayi saman filon data d'ora akan cinyarta bayan tagama saka rigar, ya hard'e hannayensa a k'irji tareda lumshe idanu.
Itadai Asma'u tana kallon ikon ALLAH, Tunda tayi zazza6in nan take ganin sabon salo wa yayan nata, ta tsurama k'yak'yk'yawar fuskarsa ido, sosai ya Umar ya had'u, gashi bak'i sosai, kuma bak'insa mai k'yaune, kwanakin baya yarame amma yanzu saitaga yamata k'iba, kodan hankalinsa yafara kwanciyane?.
Hannu takai ahankali zata ta6a girarsa dake matuk'ar burgeta sosai, girarsa tanada yawa, tayi kamar zata had'e dajuna, kasancewarsa bak'i kuma bai hana bayyanartaba.
Bud'e idanu yayai ahankali danjin motsin hannu akan idonsa. Da sauri Asma'u tasa hannu tarufe fuskar tata. Yayi murmushi mai sauti. My Asmah miyafaru?.
Babu komai fa.
Hummm k'arya babu k'yau.
'Yar dariya tayi, batareda ta ce, "komaiba". ‘zuwa can kuma ta ce, " Yaya bazakaje shagobane?.’
Bud'e idonsa yayi sosai tareda d'age gira d'aya yana wani murmushin gefen bak'i, ya ce, "kingaji daganinane?."
Lah a'a bafa haka nake nufiba.
To mikike nufi?.
Uhm damafa dankar mutane suyita jirankane, jibafa har 9:48.
Juyawa yayi yana kallon agogon shima, saikuma yadawo da dubansa kanta, karki damu akwai mutum a shagon.
Akwai mutum?. ‘Asma'u ta tambaya cikin mamaki.
Tashi yayi zaune sosai, yad'auke filon daga cinyarta yagyara asaman katifar sosai ya kwanta. Itadai binsa kawai takeyi da kallon mamaki. Bata ankaraba taji yajawota, ta fad'o jikinsa. Kafin tayi wani yunk'uri ya rungumeta tsam tamkar za'a kwaceta.
Tuni jikin Asma'u yafara rawa, tamarasa mizatayi ta kwaci kanta. Gogan naku kuwa abubuwa yake mata masu nuna tsananin k'yauna da bege agareta. Tun tana iya yunk'urin hanashi harta Gaza komai sai kuka ahankali damasa magiyar yayi hak'uri bafatada lfy. Kokad'an bai saurari furicin nataba, sosai cukirkud'ata ya cigaba dayi yanda yakeso.
Saida yayi mai isarsa sanan yasaketa yana maida numfashi. Itakam kuka takeyi sosai, ganin yasaketa tatashi da hanzari tabar masa d'akin. Binta kawai yakeyi da kallo yana zuba murmushi tamkar wanda yasamu abinda yakeso..
_____________________
Tsawon kwanaki hud'u kenan tsakanin Asma'u da ya Umar ana 'yar wasan 6uya, ko kad'an bata yarda su had'u dan harga ALLAH tsoronsa takeji, shago kam ko lek'e bata lek'ashi.
Yauma suna zaune atsakar gida itada maman faisal tana mata kitso (dan Asma'u ta iya kitso sosai), hirarsu suketa zubawa irinta mata, maman faisal tana tambayarta kozatasha wani magani takawo mata?.
Anty magani kuma? Maganin miyene?.
Dariya maman Faisal tayi sannan ta ce, "magani dai na mata.
Asma'u bata fahimci zancen na Maman Faisal ba ko kad'an, dan haka tayi dariya, kai anty saddiqa mu mata har wani magani ke garemu daban?.
Maman Faisal tajuyo tana kallon Asma'u da k'yau danson gaskata maganarta. Banganeba Asma'u! Kina nufin bakisan miye maganin mataba? Kina matar aure.
Asma'u dake kallon maman Faisal tad'an yatsine fuska, wlhy Anty saddiqa kiyarda dani bansaniba.
Jinjina kai kawai Anty saddiqa takeyi cikeda mamakin furucin na Asma'u. Dama har yanzu akwai matan dabasusan ire-iren wad'annan abubuwanba arayuwa kenan?. Idan akayi la'akari da yanda mata suka lalata kansu dashan magunguna yanzu, wasuma cutar dasu sukeyi amma sun gaza ganewa, dolene duk wadda tanuna bata saniba ayi mamaki.
Asma'u dai tacigaba dayima maman faisal kitsonta, sauraren k'arin bayani kawai takeyi daga gareta. Jin tayi shiru ta ce, " anty Saddiaqa kigayamin dan ALLAH, miye maganin mata?.
Bak'aramar dariya tambayar tabama Maman Faisal ba, dan haka tadara, saidatayi dariya sosai sannan ta ce, "Asma'u nabaki dama kitambayi Umar nasan zai fad'a miki miye maganin mata.
Shiru Asma'u tayi tana tunani azuciyarta, mizaisa anty saddiqa ta ce, " ta tambayi ya Fharuk? Shimiye had'insa da wanan maganar? tunda maganin mata akace.
Badai takuma cema Anty Saddiqa komaiba, amma ta k'udiri aniyar tambayar ya Fharuk d'in kamar yanda anty Saddiqa tafad'a mata.
Maman Faisal kam tayima Asma'u gatsene dantaga shin rainamata hankali tayi (tasan maganin Matan) kokuwa batama San miye ma'anar shan maganin matanba. Amma amamakinta saitaji Asma'un tayi shiru batace komaiba.
Itama daganan wata hirar takawo mata, ta watsar dawaccan maganar gefe kawai.
Bayan sun kammala k'itson sukad'anyi hira har yara suka dawo daga islamiyya, sunsan babu Inda mamansu take zuwa sai gidan Anty Asma'u, Dan haka suka shigo Nanal.
Oyayo 'yan islamiyya antaso?.
Eh Anty INA yini.
Lafiya lau yarana, ya makaranta?.
Lafiya lau.
Daga nan suka gaida mamansu ma.
Maman Faisal ta ce, "kunga kuje gida acanja kaya, Faisal kacanjama kowa kajiko, karfa Ku hargitsa kayan.
To mama, Faisal yaja k'annansa suka fita.
Asma'u da Maman Faisal kuma sunata hirarasu.
Suna nan zaune saiga ya Umar yashigo, da alama dai akwai abinda yazoyi cikin gida. Da Sauri Maman Faisal taja hijjabi tasaka.
Shi koma Inda take bai wani kallaba, yadai amsa gaisuwarta sannan yakalli Asma'u da ak'alla yad'au tsawon kwana Biyar bai gantaba, tun randa abinnan yafaru basu sake had'uwaba.
Itama kallo d'aya tamasa ta d'auke kanta daga gareshi.
Yana shigewa Maman Faisal ta zunguri Asma'u.
Asma'u kitashi gafa mijinki yashigo.
Yatsine fuska Asma'u tayi, yo Anty nimizan masa? K'ilama wani abun yazo d'auka.
Idanu Maman Faisal tazaro waje, Asma'u bangane mizaki masaba? Mijinkine fa? Yashigo gida amma bazakije kiji matsalarsaba?. Anya kinada wayau kuwa? Kamar yanda nake tsammani?.
Hummm Anty kenan inada wayau mana.
Inafa kikaga wayau tunda bakisan yazaki kula da mijinkiba. Bara kigani natashi idan Dan ganina zai hanaki bama mijinki kulawa.
Da Sauri taruk'o hannunta, lah wlhy Anty Bahaka bane, yihak'uri kizauna Dan ALLAH, kinad'an d'ebemin kewa kuma kice zaki gudu? Nidai yanzu fad'amin mikikeso nayi to?.
Maman Faisal ta sauke ajiyar zuciya, tana mamakin wai dama haka Asma'u take? batada wayo, ta girgiza kai tareda fad'in yanzu kije kikaimasa ruwansha, sannan kiji miye matsalarsa.
Shike nan Anty zanje, amma kimin alk'awari bazaki tafiba?.
ALLAH babu Inda zanje, jeki kidawo.
Da azama Asma'u tamik'e, kicin tashiga tad'iba ruwa a jok sannan tanufi cikin falonsu.
Ganin babu kowa anan tashiga d'akinsa da sallama k'irjinta na dukan tara-tara.
Gabantane yafad'i yayinda tayi tozali da Ya Umar tsaye yana goge jiki da Alama wanka yayi.
Taisaurin kauda kanta daga gareshi, zuciyarta na faman tambayarta wankan mi ya Umar yayi yanzu da yamma haka? d'azunfa babu dad'ewa yayi wanka?.
Ganin mutum agabanta yasaka rawar jikinta k'aruwa, jok d'in ruwan haryana girgiza.
Ya Umar ya jinjina Kansa kawai yana kallonta, ruwan hannunta ya kar6a kafin ta zube masashi akan katifa, Dan yakula arikice take sosai.
Tana bashi takama hanyar fita. Dasauri ya ce, "wai saurin mikikeyine haka?.
In INA tafara namarasa gsky, u...u....um....dama zanjene Anty Saddiqa tana jirana awaje.
Hum Kodai kinason guduwa saboda kina tareda dodo? Miyasa kike tsorona yanzun Husna? Konamiki kama da abin tsorone?.
Azuciyarta ta ce, " sosaima wlhy". ‘amma afili sai ta girgiza MASA kai.’
Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai, kokad'an babu walwala afuskarsa, ya ce, "jeki kawai.....
Aibama tabari ya k'arasaba tafice da Sauri har tanayin tuntu6e zata fad'i. Tayi saurin tare Bango sannan tafice.
Ya Uamar yacije le6ensa da k'arfi yana naushin iska, yamatse hannayensa da k'arfi yana magana afili kamar wani sabon kamu.
Gashinan Umar dama abinda naketa gudan maka kenan, gashinan tanajin tsoronka, guduna takeyi, dama abinda Yasa ban nemi komai daga garetaba Kennan.
Jiba wai d'an abinda naimatannan yasa har tafara guduna. Wayyo nikam miye fafita!!.............?
*_Luv you all_*.
*_((((S)))).........2017_*
[12/11/2017, 8:57 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
*_page→35-36_*
.......Haka yayta zagaye d'akin yana surutai, saida yagaji Dan kansa sanan yashirya cikin wankan k'ananun kaya yafito sai baza k'amshi yakeyi. Idan kaga ya Umar saika d'auka irin matashin saurayinnan ne dabai wuce 26 ba, yanada tsafta Da son k'amshi sosai.
Atsakar gidan Yakuma tarar da su Asma'u, wadda tun d'azun tadawo wajen Maman Faisal.
Saina dawo yafad'a yana k'ok'arin ficewa.
Adawo lafiya sukafad'a suduka, shikuma yafice.
Yana fita Maman Faisal tashiga yima Asma'u fad'a (Dan ta girmeta gsky, zata iya zama sa'ar Anty saratu ma). Haba Asma'u yanzunan mijinki zai fita bazaki masa rakkiyaba? Idanfa kika saka wasa wata zatazo ta kwace miki miji. Nakula kinada sakaci sosai. Hakamafa d'azun abirkice kika fito, kamar wadda taje wajen dodo. Kodai akwai matsalane?.
Girgiza kai Asma'u tayi, Dan aganinta baikamata tabama Anty Saddiqa labarin abinda yafaru itada ya Umar ba.
Maman Faisal tacigaba da fad'in to gsky ki gyara kinjiko. maza sunason ana kula dasu tamkar kwai a cokali. Indai kinama namiji haka to tabbas zai koma miki tamkar jinjiri wlhy.
Hakane anty amma wlhy ya Umar daban yake, yacika tauri dayawa. Wani lokacinma dolene kiji matuk'ar tsoronsa.
Hummm Asma'u kenan, duk taurin namiji mace saita sakashi laushi. Shawarar dazan baki ki fara karatun Hausa Novels, insha ALLAH zaki k'aru matuk'a da ilimin zama da miji. (Musamman idan kin had'u da buk d'in marubutan dasuka san Kansu) akwai wasu buks dana karanta na bilyn Abdul, na tabbata zaki k'aru acikinsu.
To a ina zan samu?.
Bak'yayin charting?.
Inayi da, amma yanzu banayi.
Tom Indai ba mijinki ya hanakiba kikoma yi zan baki no. d'inta.
To Anty ngd sosai.
Maman Faisal tamik'e dak'yar saboda tsohon ciki datakedashi, haihuwa yau ko gobe, bara naje gida, nasan sunacan sunamin 6arna tunda sukak'i dawowa.
To Anty ngd.....
..................................
Su Lubna anata hidimar biki, shiri sukeyi na garari Dan bikin namasu akwaine babu k'arya.
Komai awadace yake tafiya, party kam aii anshirya yafi kala 10, su Lubna sune amarori k'irjin biki.
Yau kamu Dan haka sukaci uwar kwalliya nawani sky blue d'in less itada Suhaima, sai walk'iya sukeyi, idan kagansu kai kace sune amaren, bakowa zaiga Lubna ya ce, "ta ta6a aureba bareba harda yara biyu.
Harabar gidan suka fito inda abokan Ameer suke birjik, duk sunci wankan bak'in wando da yellow d'in Riga, wanan shine kwalliyar kamu na maza.
Matankuwa yellow d'in wando da bak'ar riga. Sudai su Lubna basu sakaba.
Wani abokin Ameer ya ce, " kai yarinyar canfa tawuce dani wlhy, wai k'anwar Amee CE?.
Inaganin k'anwarsace, ammafa in k'aramar tafimin k'yau, kasanni ko aure zanyi banason yar 20+ gsky. Nafison daga 16 zuwa k'asa.
Dariya abokin yayi, ya ce, "humm aikai mugunta kakeji.......
Wucewarsu Luban tagabansu tahanasu cigaba da hirar. Sukam basusan sunayiba, sun wuce sun barsu da k'amshinsu.
Mota suka shiga, Lubna tajasu suka bar gidan.
Kaitsaye hall d'in daza'ayi kamu suka nufa. Dangin amarya Suma sunyi shirinsu sosai, amarya tad'auki k'yau, naira tayi kuka agidannan. Su Lubna sai nan nan akeyi dasu, sukuma suna fankama da Nuna isa, su adole dangin miji.
Babu dad'ewa su Ameer suka iso. Ba awani tsaya 6ata lokaciba aka fara gudanar da kamu Wanda yak'ayatar.
Sai wajen 9pm aka tashi, ansha casu kam babu k'arya. Idan kuga yanda Lubna tadage tana rawa saikusha mamaki......
____________________
Tunda Anty Saddiqa tafad'a mata idan tana sakaci wata zata kwace mata miji tashiga damuwa, tana matuk'ar son mijinta, tanajin ya Umar yafi sauran maza awajenta, idan akace wata zata iya kwaceshi agareta takanji tamkar an soki zuciyarta da mashi.
Wasu zafafan hawaye suka gangaro bisa kumarunta. Bata sharesuba, saima cigaba da matso wasu datayi.
Duvanta takai ga agogon d'akin, karfe 9:23pm amma har yanzu ya Umar bai dawo gidanba, tun fitar d'azu da yamma. Tana mamakin ina yajene har zuwa wannan time d'in?.
(Zuciyarta ta ce, ''yaje tad'i.") Rushewa tayi dawani kuka mara dalili....
Ni dariyama tabani aradu😂.
Tana nan tana kukanta saitaji motsin bud'e k'ofa, da sauri tad'ago tana kallonsa. Ya Umar ne sanye cikin kayan barci, da'alama ma yadad'e da dawowa gidan.
Shima kallonta kawai yakeyi amma fuskarsa ko kad'an babu walwala. Cikin d'akin yak'araso, yaja tum-tum yazauna har yanzu idanunsa akanta. Itadai nata na k'asa, ga hawaye sha6e- sha6e a fuskarta.
Ahankali ya firzo huci daga bakinsa yana mai kauda kansa daga gareta. Ko kad'an bayaso yaga mace na kuka. Shi mutumne mai tausayi sosai musamman akan mata.
Yakuma dawo da kallonsa gareta, kukan mikikeyine? Ko har yanzu bakida lafiyar?.
Shiru tamasa, bata d'agoba, bakumata tanka masaba. Dan zuciyarta wani irin zafi takeji, gani takeyi kamar da gsk daga tad'in yake.
Cikin d'an fad'a-fad'a ya ce, "wai bakijinane!!?.
Da sauri tad'ago takalleshi, ganin yanda yakuma tur6une fuska sai tsoronsa yakuma kamata. Bakinta na rawa ta ce, "bakaine kaje tad'iba."
Tad'i!?. ‘ya Umar yafad'a cikin sigar tambaya da mamaki.’
Itama kanta tad'a tana wani kumbura baki.
Siririn tsaki yayi, amma batajiba. Ya ce, "kewaye yagaya miki naje tad'i?.
Gabantane yafad'i, dan kuwa dai zuciyartace ta sak'a mata, bawanine yafad'a mataba.
Shima ganin haka sai kawai ya girgiza kai. Yakuma yin k'aramin tsaki tareda fad'in kinga ni bar wannan banzan shirmen naki gefe, magana nazo muyi. Tashi kije ki wanke fuskarki kidawo.
Ahankali tamik'e kamar wadda kwai yafashema aciki tashiga bayi. Fes tawanke fuskarta sanan tadawo gareshi.
Saida sukaja wasu 'yan mintuna sannan yay gyaran murya:- inaso kibani hankalinki nan muyi magana. Kanta ta jinjina masa alamar to.
_d'azu fitar danayi naje office d'in su muktar ne, dama tun kwana hud'u daya wuce munyi magana, ya ce, " nabada takarduna zai kaima ogansu yanemamin aiki. Dafarko ban aminceba Dan narigada na fidda raina ga aikin. Amma saiya nace sosai da magiya da kawomin hujjoji akan fa'idar Neman aikin harna amince.
Jiya yakai takardun, yaukuma ogan nasu saiya buk'aci ganina. Shine Muktar yakirani ina shago yasanarmin. Wanna dalilin yasa nashirya naje.
Tom saidai kuma abinda yagirgizani shine ogan su muktar abokine ga dad (mahaifin Lubna) akwai dangantaka mai k'arfi a tsakaninsu ta kasuwanci gsky, Dan sanda ina k'arkashinsa yasha aikena awajensa.
Abu na biyu kuma shine Alhaji Ahmad mai kano yad'aukeni aiki ak'ark'ashin kamfanin nasa, ya ce, "kuma yana buk'atar bayani daga gareni akan abinda yasa muka rabu da mahaifin Lubna.
Yabani dama daga nan zuwa gobe, idan nafad'a masa yace zuwa Monday zan fara aiki.
Yakika gani nafad'a masa gsky?, kokuwa na hak'ura da aikin kawai?. Ban fad'ama kowa maganarnanba saike, koshi Muktar baisan yanda mukayiba.
Asma'u tasauke ajiyar zuciya sanan ta gyara zama. Yaya nidai abinda nake gani kafad'a masa kawai, Dan ALLAH yagani bacin amana ko cutarwace taravaku da mahaifin anty Lubnar ba, yanzu kuma aiki za'a d'aukeka idan kayi kuma za'a biyaka, kaga kuwa guminka zakaci bawai a k'ark'ashin wani zaka zaunaba.
Kuma ina ganin koda kafara aiki tom nikuma saina cigaba da lura da shagon harmuga abinda ALLAH zaiyi.
Sosai ya Umar yagamsu da bayaninta Dan haka ya jinjina mata kai alamar gamsuwa, gawata k'aunarta na ratsashi, wani lokacin idan tayi Abu tamkar wata babba. Idan shirmen yamotsa kuma sai an sauke masa cikin tirela😂.
Asma'u tayi murmushi mai kwantar da zuciya, ya Fharuk natayaka Murna, ALLAH yabada nasara da sa'a.
Ameen Husna ngd.
Filo yajawo ya kwanta.
Gaban Asma'u ne yafad'i, karfa asake irin ta ranar.
Kamar yasan tunanun datakeyi saiya mik'e zaune yana fad'in yau baza'a bani abinci bane?.
Da sauri Asma'u tamik'e, Dan danan tacika gabansa da kulolin abinci, tashi yayi zaune tazuba masa komai.
Yanzukam babu laifi yad'an saki fuskarsa, Dan yanacin abinci yana satar kallonta. Sukan had'a ido lokaci-likaci, ganin haka ya Umar yad'auke idonsa gaba d'aya daga kanta yamaida ahankali kan cin abincinsa.
Kamar daga sama yaji Asma'u ta ce, "ya Fharuk inada tambaya?."
Idanunsa masu haske yad'ago yana kallonta, saida ya had'iye abincin bakinsa sannan ya ce, ''ina saurarenki?."
Shiru nawani lokaci tanata juya maganar a zuciyarta, kamar tayi kamar kartayi, can wata zuciyarta na angizata akan ta tambayesa da ace tazauna cikin duhu.
Jin tayi shiru yace yadai? Kokin fasane?.
A'a. Dama inason tambayarka minene maganin mata?.
Sosai ya ware idanunsa akanta. Aransa yace mike damun kan yarinyarnan?. (Inhar bai mantaba Lubna ta ta6a fad'a masa kayan k'arin ni'ima sune ake kira Maganin mata. Dan yata6a rutsata tana sha saiya tambayeta maganin minene wannan?. Dayake Lubna macece da batada kunyar Abu kai tsaye, musamman ga mijinta, sai takecemasa maganin k'arin ni'imane)..........
Ganin yayi shiru yadaina cin abincin, kuma gashi ya tsura mata idan ko k'yaftawa bayayi saitasha jinin jikinta. ad'arare ta ce, "ya Fharuk akwai matsalane?.
Girgiza mata kai kawai yayi yacigaba dacin abincinsa, Dan aganinsa dawata manufa daban tamasa tambayar, ashema k'aryar gudunsa takeyi, tasan komai, tana raina masa hankaline kawai.
Wani d'an murmushin gefen baki yayi, shikad'ai yasan miya kitsa wa zuciyarsa.
Asma'u kam tayi gum, Dan sosai tasha jinin jikinta akan tambayar.
Harya kammala cin abincin babu maicewa da d'an uwansa k'ala.
Bayan ta gyara wajen ta kwashe kwanikan tadawo d'akin. Inda tabarsa anan ta iskesa.
Ya ce, " kinason amsar tambayarki?.
Kanta ta jinjina da sauri.
Yalumshe idanunsa yana wani murmushi na musamman Wanda Asma'u bata ta6a gani daga gareshiba.
Zan baki amsar tambayarki amma nima zan tambayeki Abu biyune, idan kinsani bazan amsa mikiba. Idan baki saniba zan had'a duka nabaki amsa, amma bayauba, zan baki amsar Abu d'aya a daren yau, biyun kuma saida safe.
Bata kawo komai arantaba ta ce, "to ina saurarenka.
Mizakiyi da maganin mata?. Na biyu:- miyasa kika tambayeni.
Gefen wuyanta ta Sosa Dan batasan amsar dazata bashiba.
Ganin haka ya ce, "shikenan, tashi kiyo alwala zan baki amsar farko dakika tambayeni...............