<<1>>
Cikin shagwaba ta fito daga bedroom ta nufi wurin mahaifiyar tata dake kwance kuyangu namata tausa ta kanga jikinta jikin maihaifiyar ,cikin girmamawa kuyangu suka gaishe ta sannan suka tashi suka basu wuri. Cikin jin dadi umma tashaqi kamshin jikin autar ta ta lumshe ido tace "auta wannan kamshi haka Ina zaki je?"
Murmushi tayi tanafadin "ummana wurin safina zan shiga amma bazan jima ba zan fito",
" haka zakice ai ,kafin naganki kila sai anyi kiran sallah issha'i'",
Ta mik'e tana fadin "Allah umma bazan dadebafa, ammafa in hira tayi dadi...uhm....uhm.."
Umma tayi dariya "aifa kya fadi gaskiya, keda safina dai naga ranar aurenku dai dole ba miji daya zaku aura ba karewar abota kenan"
"Kai umma ,ni dai na tafi" tafita tana dariya
Umma tarakata da "agaishe min da tawa aminiyar .
Cikin natsuwa ta ke tafiya harta dangana da gidan waziri , a falon farko tayi sallama nan ta taradda momy na kishingide jikin tuntun tana hutawa ,ta fadada murmushin ta " a..ah autar kece da safiyar nan"
Ta russuna cikin girmamawa ta gaishe da momy ,sannan tagaya mata sa'kon umma,
"Ina amsawa ,nasan dai wurin 'kawa kikazo to tana dakinta kishiga",
Dariya tayi sannan ta wuce dakin safina.
Taradda da ita tayi kwance tana latsa system ,ta Dada mata duka abaya " to uwar chatting kullum kina online Dan jaraba",
Safina tajuyo ta ware ido ta zubawa safiyya idanu "wallahi sai na rama",
Ta bita da zata rama da sauri safiyya tayi zillo tayi falo a guje, " haba cwt kiyi hakuri bansan kinji zafiba wallahi",
Safina ta dauki pillow ta wurga mata ,safiyya ta kwace tana dariya ,haka suka dinga guje guje a falon momy (lokacin ta bar falon),sai da safina ta gaji sannan suka koma dariya suka hakura.
Safiyya na kwance a kan gadon safina tana sauke numfashi tace "ke nifa nazo ne na fadamiki ranar Saturday zamu wuce fa",
Safina ta waro ido " kai cwt wayafada miki",
"Allah jiya naji mai martaba yana gayawa umma",
Safina ta Daka tsalle " wuuh lallai, sun yarda kenan",
"To ai naji umma ta bashi baki tace ai akwai su yaya sufyan acan ba matsala",
" aikuwa kice nafara shiri, amma fa kinsan su yaya sufyan da takura" tafadi hakan tana Dan yamutsa fuska,
Safiyya ta tabe baki "kedama kika sansu kenan, nikuwa da ko a titi muka hadu bazan ganesu ba",
" ai dashike duk dawowansu bakya gida amma _yhu will soon know them_",
Safiyya tayi murmushi "ai naji kullum maganar mom kenan _twins_ din ta,gaskiya tana ji dasu fa ",
Safina ta muntsileta " au to nice ba'a jidani kenan?",
"A ah nifa banceba, keda kike autaress",
Sukayi dariya dukkansu,haka suka cigaba da hirarsu cikin wasa da dariya har sai da akayi magriba sukaci abinci sannan suka wuce gidan sarki
Sarki Abubakar mai kudi shine ke sarauta a garin gombe , sarki mai halin dattaku da karamci ,sarki mai jama'a da gaskiya ,matarshi daya tilo mai suna Maryam (umma) mahaifiyar yaransa uku na farkon su shine Ibrahim Khalil dan shekaru 27 Wanda yaci sunan maihaifin sarki medicine take karanta a India yanzu haka yana shekararshi ta karshe sai ta biyu aunty amina yar shekara 21 inda take karanta nursing a jami'iar ahmadu bello dake kaduna, sai auta safiyya wacce tagama secondary school yanzu haka zata fara karatar law a turkey, dukkansu sun taso cikin tarbiyya da kuma gata na iyaye , Babban aminin sarki shine wazirinshi kuma amintar tasu tun sun a kanana Dan haka koda aka Nada Abubakar a sarauta ya dauko aliyu ya bashi wazirinsa ,basa taba yanke hukunci sai tare Dan haka ko gidajensu kusa take da juna ,cikin ikon Allah matansu suka zama aminan juna ,in yau basuga junaba to gobe daya zata biyo daya gida , Aliyu sunnan matarshi Fatima inda suke kiranta da momy itama yaranta uku , yan biyu ta fara Haifa Wanda aka haifesu tare da Khalil , sufyan da safwan suma shekarunsu 27 ,shi sufyan ya gama degree dinsa a law yanzu haka shekararnan zai kare masters ,yay in da safwan ke shekarsa ta karshe a karatunsa na medicine suna turkey dukkansu Dan kuwa tunda suka kare jss 3 aka maidasu turkey suka cigaba da karatu ,basa wani kama sosai Dan kuwa kowanne halinsa daban,sufyan miskili ne na karshe gashi baki fiye hayaniya ba,shiyasa lokacin da ya cewa mom law zai karanta tace _naga yadda za'ayi miskili yayi law_ shidai sai kawai yayi dariya, shikuwa safwan akwai faran faran da mutane, sai kuma autarsu wato safina wacce take sa'ar safiyya kuma cwt aminiyar ta ,tare suka taso tare suke makaranta kuma tare suka kare kuma tare zasu tafi karatu yanzu turkey amma ita safina pharmacy zata karanta. Kubiyo mu danjin yatakene.....
[3/7, 11:13 PM] +234 703 962 5239: *MACE KADARACE MAI TSADA*
© _UMMU SABREENA_
_ND_
_AUNTY AYSHA_
_January 2017_
<<2>>
A safiyar Asabar misalin karfe 10 na agogon Nigeria, ayarin sarki Abubakar ne da wazirinsa Ali ne a filin jirgin sama dake gombe anata bankwana da safiyya da safina dake ta matsar kwalla za'abar gida ,momy ce ketaba su hakuri da addu'a ita dai umma murmushi takeyi duk da batason abinda zai sa tayi nisa da autar ta ,amma ba yadda zatayi tunda mace ce dole gidan miji zata tafi wata rana, haka dai suka daga badan sun so ba ,
Misalin karfe biyu na agogon Turkey ,su safiyya suka isa masu Wanda mai martaba yasa su safwan suka tanadar musu , suna yin sallar kowacce tabi lafiyar gado, sai misalin karfe hudu da kwata kowaccensu ta tashi , suka gabatar da sallar la'asar sannan suka jika cornflakes suka sha , safiyya ta cema safina bari ta fita cikin garin tayi musu siyayya, "ohk nakira su yaya safwan sunce gasu nan zuwa",
" to cwt nidai gaskiya sai na fita ,in sunzo kice nadan je na siyo abu ",
" kai cwt keda bakisan gari ba",
"To ai ba dadewa zanyi ba, kusa da schl din kawai zan je kozanga abin dadi nasiyo mana",
Ta dauki mayafinta ta daura akan doguwar rigar data fito da asalin kyawunta ta saka sannan ta fita .
Ta na tafiya a hankali cikin natsuwa har ta isa cikin schl din, tadinga bin makarantar da kallo , can ta hangi wani zaune da jarida a hannunsa yana karantawa , taga kowacce tazo wucewa sai ta kalleshi sannan ta wuce , gaskiya gayen ya hadu shiyasa kowacce sai ta bishi da kallo, kuma ta kula mutumin kamar Dan Africa ne, ta tsaya itama tana kallonsa tana nazarin fuskarsa , aikuwa dagowan dazaiyi suka hada ido dashi ya yi mata wani kallon banza Wanda saida tayi Dana sanin kallonsa, sai yayi mata tsaki ya mike yabar wurin , abin ba karamin bata was safiyya rai yayi ba , Dan kawai ta kalleshi shine zai wulakantata , cabdi Jan ,wallahi sai ta rama ko za'a mutu.
Cikin bacin rai ta bar wurin ta nufi hanyar komawa gida ba tare da tasiyan musu komaiba, ta tsani ayimata wulakanci kuma batason ta wulakanta kowa,
Cikin zafin rai ta tura dakin tashiga tafada jikin safina tana kuka, safina duk ta rikice tana tambayanta abinda ya faru, sai da ta nisa sannan ta bawa safina labarin abinda yafaru
"Yanzu cwt Dan kawai anyimiki kallon banza shine abin kuma , haba kar kibani kunya ma"
A hakilce safiyya tace "amma cwt harfa tsaki yamin ,Dan kawai na kalleshi, ni..ni..ni wallahi fa sai na rama ba dai a cikin makarantar yake ba",
Safina ta gwalo ido " ke cwt in lecturer nefa?",
_"Aiko shine director sai na bi hakkina ,ni baisan banacikin Wanda zanga ana wulakanta mata a duniya nayi shiru ba ,balle kuma ni a wulakanta ni, ke nifa fada Nike da maza Wanda basusan darajan mata ba, shiyasa fa tun INA karama nake son karantar law, Dan kuwa inshahallah sai na kwacewa mata hakkinsu da ake takewa ta hanyar yima kananan yara fyade da kuma safararsu da akeyi zuwa garuruwa da kasashe",_
"Ai fa lallai cwt kinada aiki amma pls kiyi hakuri ki kyale mutumin nan",
" ai INA ,wallahi cwt _I will teach him a lesson_, sai yasan cewa _MACE KADARACE MAI TSADA_",
safina ta fashe da dariya hard a tafa hannaye ta dauki towel ta shige wanka, tana fadin autar umma ba dama"
Wanshekare da wuri suka shira suka shiga makarantar, dashike safiyya ta Riga safina gama daukan lectures Dan haka tasamu wani wuri ta tsaya tana jiranta ta fito, wulga idonta dazatayi ta hango shi tsaye yana magana da wani hannunsa dauke da kwalban coke ,tayi wani shu'umin murmushi tanufeshi cikin san'da ta isa gabanshi ,cikin dubara ta fizge coke din dake hannunsa ta wankeshi dashi Wanda yayi sanadiyyan bata farar T-shirt din dake jikinshi , ta kalleshi " karyar wulakanci kenan",
Aikuwa duk 'yammatan dake binsa da kallo suka sake baki hard a maza Wanda mamaki ya baibaye fuskokinsu ,
Shi kuwa yana rasa ta INA zai fara ,gashi tayi gaba abunta, kawai sai ya bar wurin cikin sassarfa , cikin kunar rai yake tuku ,wai shin ma wacece wanannan yarinyar ,kuma wani wulakanci take tutiyan yamata, shidai a tunaninsa babu abinda ya taba hadashi da ita.
Koda ya isa gida Dan uwansa safwan yadamesa da tambayar maiya bata mishi kaya kuma yadawo ranshi a bace , sabida tsabar miskilanci sai tace mass ai coke ne ta zube mass a jiki amma a ranshi fadi yake _"i will teach her a lesson"_
Topah!!!
[3/7, 11:15 PM] +234 703 962 5239: *MACE KADARA CE MAI TSADA*
_NA UMMU SABREENA_
_ND_
_AUNTY AYSHA_
_January 2017_
<<3>>
Bayan sallar magriba su safiyya na zaune bayan sungama cin abinci kenan sukaji sallama, dayake safina ta dauki muryar su dan haka cikin zumudi ta mike zataje ta bude musu kofa, sofy ta riko ta "ke cwt dagajin sallama sai kije kibude kofa bakisan kosuwaye ba",
Ta fizge hannunta tana murmurshi "cwt su yaya sufyan nefa, ai nagane muryarsu" ta fadi hakan tana mai kokarin fita daga dakin.
Safina ita tayo musu jagora har dakin dasuke , sai tsokanarta yaya safwan keyi wai su auta anzo Turkey, hannun su a sarke da juna suka shigo su ukun yayinda safina ke tsakiyarsu da sallamarsu suka shiga lokacin safiyya tana toilet taje wanko hannunta ,
"Ita safiyyar ne?" Cewar safwan dayake bin dakin nasu da kallo
"Naji karan ruwa a toilet tana ciki",
Safina ta dan kalli ya sufyan tace "ya sufyan naga kaman ranka a dan bace kabarni nida ya safwan sai hira muke, ko anbata maka raine babban yaya" ta karisa maganar tata cikin zolaya
Cikin dariya safwan ya karbe zancen nata ta hanyar fadin "aikuwa dai auta momy kema dai kya gani , tunda ya dawo yake hada rai na tambayeshi yaki ya fada min, kila miskilancinne yau ya tashi",
Sufyan yayi murmushi yace" kyaleshi autar momy, kawai dai bana danjin dadi ne",
Bude kofan toilet ne yasanyasu dukka suka kallo kofan, Alokaci guda kirjinsu ya buga sabida abinda idanuwansu ya nuna musu , "to wannan kuma biyo ni yayi har gida ya kuma wulakantani , ko kuwa dama sun san juna da cwt safina ne?",
safwan ne ya katse ma sofy tunanin datakeyi "karaso mana safiyya kinyi tsaye kamar baki sanmu ba",
Murmushi ta kakalo sannan tasamu wuri gefe guda ta zauna kirjin ta na dukkan ukku ukku, amma ta maze ta gaishe su,
Sufyan ya kalleta ta kasan ido amma sabida miskilanci irinnasa sai yayi fuska ya amsa gaisuwar , zuciyarsa dauke da tambayoyi iri iri.
"Lallai safiyya kema kin girma, dan Allah sufyan kalleta kamar ba ita bace lokacin dazamu taho turkey ta kankameka tana kuka ba sai ta bika, lallai autocin nan sun girma" cewar safwan cikin zolaya.
Safina ta fashe da dariya sabanim safiyya ds kirjinta ya sake bugawa
Nan suka dan taba hira wanda duk yawancin hiran tsakanin safwan ne da safina, sai da aka tada sallar ishha'I sannan suka wuce masallaci sannan suka aje musu shopping din dasukazo musu dashi , har mota suka rakasu sannan suka dawo, itadai safiyya daurewa kawai takeyi amma duk ta rasa ta ina zata fara .
Snacks ne da drinks sai takeaway da suka kawo musu da ice-cream , safina ce ta ci sosai ita sofy ice crean din kawai tasha.
Tun a mota yake fadi a ranshi "lallai wannan ba sofy daya sani ta kankanuwa bace, dan kuwa in hakane ta yada tarbiyyan umma da mai martaba dan kuwa yasan ba hakan suka ginata da rashin kunya ba, dama tunda yaganta yake ganin kamaninta da umma ashe safiyyar umma ce, lallai ma yarinyar nan, to zatace bata sanshi bane koda a hoto dazata mishi wannan rashin mutuncin?"(amsa na gun ummu sabreena. Ku biyomu).
Ta bangaren safiyya hakan ta kansance dan kuwa tama rasa wani tunani zatayi, aiko da tayi abin kunya , kila ma yagayawa safwan abinda tamishi , wata zuciyar tace "anya zai gayamishi kuwa yanda ta fuskanci hanlinshi a zuwansu na dazun gaskiya miskiline, kai allah dai yasa kar cwt safina taji zancen nan ko umma da ta shiga uku ", wata zuciyar tace mata "ai dan baki dan shi bane", haka dai tagama sakesakenta har bacci ya kwashe ta .
Umma da momy kullum sai sunyi waya da su sofy da safina , haka mai martaba yana yawan kiransu , safwan yana ziyartarsu every sunday amma shi sufyan ba every week yake zuwa ba , ya kance masa zai shiga schl,
Safwan yayi ta mishi tsiya yana fadin "to *allazhi boko*"
Shidai sufyan sai dai yayi murmushi yace "waya kai yan medicine allazhi boko",
Tunda sukazo gidan su har yanzu basu kara haduwa ba gashi , dama ita safiyya bata sonma su hadu, takanji dai suna waya da cwt safina .dan ko zagayawa zasuyi gari to safwan inyanada tym shi yake kai su.
Akwana a tashi har shekara daya da rabi su sufyan sun gama komai na karatun su domin kuwa jibi zasu koma gida. Dan haka gidan mom sai shirye shiryen dawowan twins akeyi . Har fadar sarki tasan zasu dawo .sukuma su soffy anata exams kuma suna karewa zasu dawo hutu.
Ranar dazasu dawo harda mai martaba akeje tarbosu, kuma direct gidan mai martaba sarki aka wuce..
Sai da zuka gama kwasan gaisuwa da albarka wurin sarki da umma sannan suka nufi wurin momy, kai kuxo kuga murna wurin momy kamar tazuba ruwa a kasa tasha, abinci ne ta shirya musu sai wanda suka zaba , tana tsakiyarsu ita da daddy ali suna ci ana hira,
"wai twins ina kuka baromin auta na ne" cewar mom datake kokarin zuba coconut juice a tambulan,
"ai nasan kila sai sunyi kuka kamar su biyosu" dady Ali yafadi cikin murmushi.
Safwan ya dauki tissue ya goge baki yace "ai kuwa mun barsu suna jarabawa ne amma ai suna samun holiday zasu taho suma"
sufyan ya katse musu zancen "wai khalil ya dawo kuwa?",
"eh last month ya dawo naga har ya fara aiki ma ai, jiya da yazo gaidani yake fadamin" inji mom .
"Ai nasan yanaji kun dawo zaka ganshi, ina tsammanin baiji labari bane shiyasa" cewar dad dayake kokarin mikewa.
Hakan suka zauna sunata hira tsakanin mom da twins dinta gwanin ban sha'awa ,inkagansu zakace kakarsu ce.
Da yamma da khalil ya dawo shima wurinsu yazo suka shashance sunata hira nan yaci dinner sai karfe 11 na dare sannan ya koma fada.
Satinsu biyu da dawo safwan da sufyan suka fara aiki shi safwan a asibitin dake fada sannan kuma every tueday yana zuwa federal hospital dake cikin gombe nan ma sun daukeshi aiki anan.
A safiya jum'a bayan sundawo daga sallahr juma'a suka biya gidan sarki sannan suka shiga wurin mom ,
Da daddare mom na gefen dady Ali ya kalleta yace
"Kinsan dai ke kikacemin yaran nan nabari sugama karatu kafin namusu maganar aure to gashi dai sungama. Kuma jiya mai martaba yamin maganarsu su da khalil akan yakamata ace yanzu sunyi aure domin duk sa'oinsu nada yara",
"To insha'allah zanmusu magana gobe in Allah yakaimu"
"Ki tambayesu in sunada wacce sukeso to ace musu zasu turo magabatan su zuwa sati mai zuwa"
"Insha'allah zan musu magana, Allah yamana zabi na alkhairi"
"Ameen ameen"
Dashike weekend ne suna gida basu suka farka ba sai 9 na safe. Ko da suka fito basu tadda dady Ali agida ba shi ya fita , mom ce a falo tana jan carbi a hannunta .
Tunda suka dunfarota take murmushi, kama suke sak da maihaifinsu shi sufyan yafi safwan kauri ne kadan da fadi amma safwan ya fishi haske dan shi haskenta ya dauko , shi sufyan chocolate colour ne kuma yanada tsawo ga fadi, fuskar nan zagaye da sajen da ya fito masa da cikar sa na da namiji gashin sa kwance a kai kamar balarabe sai dimple a fuskar wanda indan yayi murmushi yake kara masa kyau .kama suke amma a fizge kuma halayensu ta bambamta amma kuma suna matukar son juna dan kuwa tun suna kanana in wani ya taba daya, to sai daya ya rama masa ko su hadu sumaka duka tare amma kuma idan fada ya hadasu to momy takan sha wahala kafin ta rabasu dan shegen zuciya irin ta sufyan , dan akwai lokacin da dukkan ninsu suka dauko wuka , sai da sukaga momy na kuka sannan suka bari amma duk sunjima junansu rauni ,
ranar sai da daddy Ali ya musu dukka sannan yace karya sake gani . Wanshekare kuwa dakansu sukaje suka bawa momy hakuri dan kuwa sun tdani suga abinda zai batawa momyn su rai nan dai ta musu fada dama insunyi fada to ranar zakiga sun koma kaman basu ba.
"Mun kwana lafiya momy" sufyan ya katse mata shirun ta hanyar gaisheta da kuma zaman dayayi kusa da ita.
Murmushi tayi sannan ta shafi sumar kanshi "alhamdulillahi",
Safwan kuwa yana gaida ita ya wuce dining area ya fara zubawa kanshi abinci .
Momy tanata mishi dariya tana fadin "wannan likita da cin tsiya kake"
Shiko sufyan sai da yagama latse latsen shi a waya sannan ya tashi yanufi dining din.
Saida sukayi nak sannan suka dawo wurin mom, itama gyra zama tayi sannan tafara magana......
[3/7, 11:20 PM] +234 703 962 5239: *MACE KADARA CE MAI TSADA*
_©UMMU SABREENA_
ND
_AUNTY AYSHA_
_january 2017_
<<4>>
_gaisuwa da jinjina gareku lubabatu maitafsir(momyn cute amah) tareda Brr. Jamila Danja.Love yhu bohot bohot_
"Jiya daddyn ku yamin magana akanku, tun kunada shekaru 25 yacemin shi aure zai muku , na bashi hakuri yabarku ku gama karatu tukun , to yanzu yace namuku magana idan akwai wacce kukeso to kuyiwa iyayenta magana cewan zaije suyi magana kuma sannan zaiyi bincike akan halayenta",
Tunda momy tafara magana sukaui 'kuri da idanu suna kallonta, shidai safwan a zuciyarshi fadi yake _to muda ba'anan muka tashi ba ina zamuga wata mu sota, ko dayake ai gwanda ma ni akan sufyan_ sai kuma ya fashe da dariya shi kadai tuno sufyan da ko mata bai son kallo balle da akai ga maganan soyayya domin ko yamai maganar mace yanzu sai suyi fada yace shifa karatu yakeyi ba soyayya ba.
Momy da sufyan suka kalleshi ganin dariyar da yakeyi , mom ta dan daure fuska tace " kai safwan bafa wasa nake muku ba , meye abin dariya kuma?",
Ya dan sosa keya "mom bakomai kawai na tuna wani abune",
"To kunake sauraro ko akwai wacce kukeso nasani?",
Sufyan dai baice mata komaiba idonsa na kallon kofa, shifa yafiso a hankali zai nemo yarinya mai natsuwa data kwanta mishi kuma baya son wacce take gaba da secondary school wato jami'a, yafison wacce tagama scec. Tsarinsa kenan, momy ta kalleshi "kai sufyan yanaji kayi shiru?",
Ya motsa dan karamin bakinsa a hankali yace "momy ni gaskiya kawai kicewa dady ya bani nan da ko shekara daya ne zan nemo a hankali",
Momy ta fara afa hannayen ta tana salati " a ah lallai baka da seti sufyan, kai ana maganar sati mai zuwa kana zancen shekara mai zuwa, to wallahi bada ni ba, so kake mahaifinku ya dauke ni mara hankali ko, yace ni nike biye muku , kai kuma safwan da?",
"Ai nima dai momy ina ganin kawai shawarar sufyan zanbi, ki dan rokan mana daddy mana plsss",
Momy ta dauko pillow a gefenta ta kai masa duka dashi "aifa baku da kunya, to nidai ba abinda ya dameni, zaku gamu dashi indai dadyn ku ne kunsan halinsa , duk abin da ya biyo baya kar kuyi blaming dina,Ku tashi Ku ban wuri",
sum sum suka mi'ke suka bar dakin, kai tsaye dakinsu suka nufa , suna shiga sufyan ya zari mukullin mota zai fita , safwan dai sai dariya yake masa kasa kasa Dan yasan halin sufyan sarai.
Tafiya yake aciki mota ya ma rasa mai zaiyi ,kai tsaye office dinsa ya nufa, "shifa atsarinsa ba yason macen dataciga wayewa shiya yake son just wacce ta ida secondary , domin baisan ya dauko mai kyawun Dan maciji Mara tarbiyya, mata mafi yawancinsu na wannan zamani basa amsa sunan na mata,kuma basa rike darajar da Allah ya musu, mace kamar _gold_ take amma yadda yake ganinsu yanzu bazakace ko fatiha zasu iya karantawa ba ,sai dai ayita bokon amma ba ilimin addini ,aje gidan miji amma basu sa menene hakkin miji akansu ba , Matan zamanin nan basu San cewa su *_kadarori me masu tsada ba* shiyasa yakeso ya tsaya ya neman ma 'ya'yansa uwa ta gari ,amma zaije yasamu daddy ko sarki Dan kuwa yasan inyasamu sarki shikenan zai rokar masa daddy",
Da wannan tunanin ya wuni, ko da daddy Ali yaji abinda twins sukace , baice mata komai ba ranar da daddare yaje yasamu mai martaba a fada da zancen
"To Ali nima dama koda nayiwa Khalil magana yafara kawomin kabali da ba'adi, shine nace ko zan fito mana da wata shawara?",
Daddy Ali ya muskuta ya ce"sarki duk shawaran dakake fito mana dashi bata taba zama ta banza ba , Dan haka ina maraba da duk shawarwarin ka",
Sarki yayi murmushi yace " tunda dukkansu alamu ya nuna cewa basu da wani tsayayye mai zai hana shi _sufyan_ a hadashi da _safiyya_, shi kuma _safwan_ ahadasa da _aminatu_ sai _khalil_ a hadasa da _safina_, ta hakanne zamu gina zamuncin mu har karshen rayuwarmu",
Daddy Ali ya washe baki" Allah yaja da ran sarki wannan shawara taka tayi, kuma hukunci da ka yanke yayi,amma ranka ya dade su auta da suke karatu fa acan turkey?",
"Jiya da mukayi waya da ita tacemin jibi zasu dawo wato Monday, ina ganin tunda hutun nasu watanni biyu ne sai ayi auren cikin hutun, sukuma zansan yadda zamuyi sudawo nan kasar da karatun, tunda bazai yiwu mata na wata kasa ba uwa tana wata kasa ba miji ba na wata uwa duniya, zansa ayo musu transfer zuwa Nigeria, ita kuma aminatu dama wannan shekaran zata gama",
Daddy Ali yayi dariya yace"insha'allahu abinda sarki ke shirin kullawa alkhairi ne,Allah ya shige mana gaba",
"Amin amin Ali, ai kai awurina ba aminini bane kazama dan'uwa, ubangiji nake fata ya hadamu agidan aljanna",
"Amin amin ranka shi Dade", Daga nan suka Shiva hiran fada, sai wurin karfe goma daddy Ali ya wuce gida ransa fes.
Koda sarki ya gayawa Umma zancen itama tayi matukar farin ciki ,balle kuma momy kamar ta Suba ruwa a 'kasa tasha,amma sun gargardesu da karsu fada musu domin sarki da kanshi zai tarasu.
Tun da duku dukun safiya momy ta shigo wurin Umma suka fara tattauna zancen, (kunsan mata da son biki)
A safiyar Monday su sofy aka dira a Nigeria, zokagansu kaman ba 'yan Africa sunyi fresh abinsu sai kyalli suke sunyi bul bul abinsu kamar lubiee(mom amah).
Itama anty Amina ta dawo Dan haka gidajen biyu ya kaceme da murna, su auta andawo gida sai zubama iyaye shagwaba ake, kwanansu uku da dawowa mai martaba ya kirayi kowa da kowa fada, Umma da mommy suna zaune waje Daya, sai sory da safina a gefensu, sai aunt Amina a gefe guda na su mai martaba , sai mazan uku a gefensu na hagu.
Daddy Ali shi ya bude taro da addu'a taro sannan mai martaba ya fara jawabi
"Ina mai farin ciki taramu a wannan taro mai albarka sannan kowa yasan taron dazaisa mu taru dukkanmu to taro ne mai mahimmanci, kuma mai albarka , acikin shekarar nan sufyan ,khalil da safwan suka kare karatunsu sannan itam aminatu ta kare nata a shekarar nan su kuma safiyya da safina suna kan yi ,kuma insha'allah cikin shekarar nan zamu 'kulla alkhairi,
"Nida babbanku Ali muka zauna mukaga ya dace mu cigaba da kulla zumuncinmu har jikoki da kuma bayan ranmu, domin kuwa no dashi ba aminai bane kawai face kuwa 'yan uwan juna kuma kuma hakan mukeso kudauki kawunanku
"Sakamakon haka muka yanke shawaran hada Ku aure , (safwan da aminatu)(sufyan da safiyya) sai (khalil da safina), wannan magana nun Riga min gama ta Dan hakan bama Neman shawarar Iowa acikinku",
Ba Wanda ya dago ido acikinsu sabida kowa yasan wanene sarki, sai za'ka'kura safiyya ta mike cikin kuka take fadin "ni wallahi ni aka cuta, ni gaskiya bana sonshi,gwara ahadani da kowa amma banda ya sufyan",
Da Sauri kowa ya dago kai yana kallonta,umma ta taso zata duketa momy ta rike yayinda safiyya tayi cikin gida da gudu.
"Lallai yarinyar nan!!!
[3/7, 11:27 PM] +234 703 962 5239: *MACE KADARA CE MAI TSADA*
©UMMU SABREENA
ND
AUNTY AYSHA.
january 2017
<<5>>
umma a harzuke take fadin "momy ai da kin barni na bita, ita kadai ce mara kunya mai bakin ba'ayi mata dai dai ba, shi yana namiji bai ce bai sonta ba sai itace zatace bata sonshi",
"haba umman safiyya ki yi hakuri yarinta ne fa, insha'allahu komai zak zai zama normal",
shima daddy Ali hakuri yabawa umma yace mata karta damu ai yarinta ne,
mai martaba yace " duk wanda zake bin zabi na iyayensa to bazai taba tabewa ba kuma yadinga ganin alheri kenan a rayuwarsa dan haka ina mai rokon allah ya sanya muku albarka ya kuma hadaku da zuriya dayyiba" kowa ya amsa da amin ", yasanya lokacin biki nanda wata daya, sannan ya sallami kowa.
Tunda ya fito da yakejin kansa na sarawa
"lallai shi aka cuta ba ita ba, yo shi ina zai kaita, gaskiya yarinyar shi aganinsa tafi karfinsa, ji yadda a turkey ta rufe ido ta tsula masa rashin mutunci batasan girman na gaba da ita ba ,wallahi ko ya daure ya aureta to ya cuce kansa, dan tun abinda tamishi yakeji ya tsaneta, bazai iya wulakanta jinin mai martaba ba amma dai.......to....",
zufa ta karyo masa ya mirgina akan gado fuskarsa na kallon sama,
safwan ya shigo dakin a hankali yayi sallama amma sufyan bai san ma ya shigo ba, yamatso kusa dashi ya dafashi sannan ne sufyan ya sauke aajiyar zuciya "
lafiya kuwa sufyan, wannan tunani haka?",
ya sauke numfashi idanunsa a rufe yace "bakomai amma ni gaskiya hukhncin da su mai martaba ya yanke gaskiya ni akafi cuta, wannan mara kunyar za'a hadani da ita, ban fada maka ba, ranar da kaga nadawo gida kayana ya baci da coke fa ita ta watsamin a turkey",
safwan ya kwalo ido waje "bangane ita ta watsama ba?",
"eh ranar ina cikin schl kawai ta fizge coke din a hannuna tamin wanka dashi, wai ta rama wulakancin dana mata, nidai a iya tunani na ba hakan nasan ba abinda ya shiga tsakanina da ita na wulakanci , kaga kuwa yanzu akwai matsala",
safwan ya dafa shi yace
"eh gaskiya kuwa akwai problem but kasan yanzu dai tunda aka rigada aka yanke hukuncin nan to ta zauna kenan, tunda itama ta furta a gaban kowa bata sonka mai zai hana kuyi auren, idan kaga ta cigaba a haka to sai ka kara aure kanemi wacce kakeso idan kuwa kayi sa'a ta canza halayenta dan dai sofy tana karama ba haka take ba",
sufyan yayi dan murmushi "hmmm to nima gaskiya hakan nai tunani, kai kuwa nasan meena bata da prblm",
safwan yayi dariya "bafa a shedan mata sai ka zauna dasu , ai kaima kayi sa'a wannan cancadediyar budurwa haka", sufyan ya tabe baki"kyan dan maciji dai .
Umma tana komawa cikin gida direct wurin safiyya ta nufa aiko ta taradda ita a daki ta hade kai da gwiwa gashin kanta duk ya rufe mata fuska "ai lallai samun wuri kikayi auta, da har mahaifinki zai yanke shawara ki mike gaban mutane ki watse shi , bansanki da irin wannan halin ba, ni dai asanina sufyan tun kina karama yake wahala dake, mutumin daya girma cikin gidannan , ohoo yanzu kin girma ko , to zamu gani damu dake waya haifi wani",
a hankali ta dago da kyawawan idanuwanta da suka rine zuwa ja tace "nifa umma ba haka nake nufi ba",
"to me kike nufi da kalamanki na mun cuceki, ko ya taba miki wani abunne? Yaro salihi da girmama mutane",
safiyya ta turo baki" kawai ni fa bana sonshi ne", "ke soyayya ta shafa, su sauran akace miki san juna suke? Ita safina mai yasa batayi magana ba, kece mara kunya ko , dan haka abinda nake so dake kije anjima kibawa sarki hakuri kafin ranki yayi mummunan baci",
ta fito fuuu... safiyya ta bita da ido ta daura hannu kai "oh ni wai za'ayiwa auren dole da wannan dan wulakanci to yasin za'aga tsiya. Da daddare haka taje tabawa mai martaba hakuri akan ta amince shi da umma, tanaso tashiga wurin cwt safina amma tanajin kunyan momy akan abinda tayi dazun.
wanshekare , Karfe 4:30 na yammaci safwan na kan computer dake falon momy , ita momy na gefenshi da fruits a gabanta tanaci sai ga sufyan ya shigo,
kusa da ita yaje ya zauna yana fadin "wash momy nagaji", tayi dariya sannan ta kwalawa safina kira data kawo masa ruwa . Safina tazo takawo mishi sannan tazauna tana mishi sannu da zuwa,
momy cikin zolaya tace "Auta yau banga sirikar tawa ta shigo gunki ba, ko kunyan angon nata takeji",
safwan mai zaiyi banda dariya shida safina , shiko sufyan murmushi kawai yayi baice musu komai ba. "Ai kuwa umma nasan kunyarki takeji" inji safina data tsagaita datata dariyar .
Momy ta kirayi safwan ya dawo kusa da ita sannan tace musu " kun daiji hukuncin da mu iyayenku muka yanke akanku dan haka banason naji wata baraka ta fito daga gareku domin dukkanku babu wanda muka masa zabi na banza, ku mazan kune kukafi mace hankali. Mace kuwa kullum cikin hakuri ake da ita, manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi yayiwa maza wasilci da su riki mata da alkhairi ko bayan raina ku rike 'ya'yan sarki da mutunci dan daurewar zumuncin mu, yanzu kunga dai yadda aka sanya bikin cikin kankanin lokaci dan haka duk abinda kuke bukata kuyimin magana akan bikin, ita dai auta bata da matsala dan kuwa dama khalil ya dade yana kamu",
ta karasa zancen nata da dariya, da sauri safina ta bar falon da sauri itama tana dariyan .
Momy ta kallesu tace "inaso yanzu kuje ku gaida umma sannan ga sako ku kaiwa kowacce acikkn sirikannawa"
ta dauko wasu turaruka masu kyau ta mika ma kowannensu , dukkansu suka gwalo ido domin sunyi nacin tabasu turaren taki
,"lallai momy har kin fara nuna mana bambamci tun kafin ayi auren", inji sufyan
"momy ko jiya nace kibani turarennan zan siya kika ki ,kikace kinaso amma.......",safwan ya fadi yana dariya .
momy tayi dariya kunsan yanzu nayi sababbin yara watsar daku zanyi.
Safwan yace "amma momy ai da tsohuwar zuma ake magani ko", "ni dai ku tashi kuban wuri kutafi inda na aikeku",
tare suka mike suka nufi dakinsu, sufyan ya faki idon safwan ya tura nashi turaren a jaka ,a zuciyarshi yace "naga wacce zan kaiwa wani turare",
sai da suka shiga wurin mai martaba sannan suka nufi cikin gida, umma suka samu a falo tana kallo , sallamarsu ita ta katse mata kallon ta dago cikin murmushi
"maraba da yan biyuna", cikin dariya suka karaso cikin falon suna gaida ita
"ya momyn taku?", " tace a gaisheki" "ina amsawa. Amina da taji shigowan su ta fito sanye da hijjabi ta gaidasu ,dukka suka amsa cikin murmushi umma tace "aminatu ki kaiwa safwan din ruwa falon sama ko?",
"to umma ta fita shikuma ya bita a baya ,
fitan sa keda wuya saiga safiyya ta fito kanta ba ko dan kwali, bakar riga ce ajikinta irin mai net dinnan amma wurin kirjin anyi kwalliya da wani jan yadi,rigar iya cinya sai skin tiet baki da kadan ya rufe gwiwanta, bata san da mutun a falon ba da haka kai tsaye ta shigo ta nufo wurin umma
" umma kinga dan dubamin bayana kaman gurji ya fito min ko",
umma ta dan bata fuska "ke baki ganin bako ne bazaki gaidashi ba",
sai a sannan ta kai duban ta ga sufyan wanda kallo daya ya mata ya kauda kai
"au... ina yini ya sufyan", "lafiya alhamdulillahi", umma tace " wucemin dagani kije ki sauko kayan kirki ki dawo ",
a hankali tabar falon ta sako bakar after dress wacce ta sauko mata har kasa sannan tadawo,
tana shigowa umma tabar falon
[3/7, 11:29 PM] +234 703 962 5239: *MACE KADARA CE MAI TSADA*
©UMMU SABREENA
ND
AUNTY AYSHA
_January 2017_
<<6>>
Kan kujera ta kame ta zauna nesa dashi , ganin haka ya sanyashi mikewa shima ya zauna a saman kujera ya kalleta a wulakance yace
"ke bawai dan kin ganni gabanki ba zaki dinga wani fadin rai, kindai san hakan nan don kaina bazan zo wurin kiba , dan kuwa baki kai matsayin dazan bar abunda nakeyi nazo wurin kiba, dan bana hulda da marasa kunya irinki, dama ingaya miki yadda kika furta cewa bakya sona nima kisani bana sonki ,zandai aureki ne dan kawai kece zabin iyayena, dan kuwa baki da qualities din macen danake so, haduwar mu ta farko dake data biyu batayi kyau ba naso haduwar mu dake ta uku kar tayi kyau but kisani haduwata dake na hudun bazata yi kyau ba"
tunda yake magana ta juya kai tana karkada kafa tana kallonsa sai da ya kai aya sannan tace "kagama! To bari kaji, ka kalleni da kyau ni bana cikin irin matan da maza irin ku ke wulakantawa, kuma ko na aureka bazan taba daukan wulakanci irin naka ba, yadda kake a shirye nima haka na shiryawa zaman mu dan haka.." ta mike tsaye ta tako gabansa "haduwar mu dakai na hudu zamuga waye zaici galaba" ta fita a falon , binta yayi da mugun mamaki , tafdi jan zatasan wanene sufyan. Umma ce ta fito tana fadin "ah..ah ina take ne", da sauri yayi murmushi " ai tafiya zanyi ita ta shiga ciki dama jira nake ki fito muyi sallama", umma tayi dariya "to sai anjima ka gaida min da momy"
fita yayi yana murmushin da shi kadai yasan ma'anar sa, sai da akayi kiran sallar magriba sannan safwan ya dawo ya taddashi a falonsu ,
cikin murmushi yace "yaushe kadawo ne baka jirani ba?",
idanunsa nakan wayar hannunsa yace "ba dole nadawo ba naga kanacan amaryarka ta rike ka",
safwan yayi dariya "kai mutumina ai mun sha soyayyar mu wallahi, soyayya fa dadi ne da ita tun balle ka hadu da mai sonka, nida my dear har mun dai daita ,gaskiya nayi sa'a",
sufyan ya mike domin wucewa masallaci "to sarkin love ai sai kaje kayitayi",
safwan yayi dariya sannan ya mike yabi bayansa.
Wanshekare da safe safiyya ta shirya ta nufi gidan momy wurin safina .
Tana shiga taci sa'a momy bata falon dan haka kai tsaye dakin safina.
Taradda ita tayi suna waya da khalil, ta dada mata duka a baya "wai cwt baki ganni kwana biyu ba shine ko ki zokiga ko lafiya",
safina tayi mata nuni datayi kasa da muryarta ,
safiyya tayi dariya tajirata har ta kashe wayar sannan ta juyo gareta ta bata fuska "ai ni wallahi cwt fushi nake dake",
safiyya ta tsugunna kusa da ita " fushin me kuma cwt meyafaru?
", ai kema kinsan meyafaru , sabida tsabar cin fuska shine zaki mike kice bakison ya sufyan a gabana",
safiyya tayi dariya "allah ba haka bane, kin gane ni tsoronsa fa nakeji(kai sofy karya) shiyasa amma kiyi hakuri ai yanzu na yadda",
safina ta dariya tace "to matar yaya",
suka fashe da dariya dukkansu ,suna cikin hira momy ta kwalawa safina kira, da sauri safiyya ta ce mata" dan allah kar kice mata nazo",
safina tayi dariya" au tun yanzu har kinfara yar kunya ne da momyn bansani ba?",
"no ba haka bane kawai dai nasan tsiya zatamin ban zo na gaida itaba na taho wurin ki",
" ba abinda zatace miki wallahi, gwarama kizo muje tare ki gaida ita,dan jiya tagama cigiyarki",
Tare suka nufi sassan momy,tana ganin sofy ta fara murmushi "dama nake cewa auta tashiga ta dubomin ke lafiya,sai kuma gashi kinzo", safiyya ta gaisheta a kunyace sannan suka wuce, koda suka koma hiran schl kawai suke da kuma shawarar da sarki ya yanke akansu na dawo dasu Nigeria sucigaba da karatu, safina dai bataso ba amma safiyya tace mata tayi hakuri bayadda suka iya , sai yamma safiyya tabar gidan a kofar gidansu suka hadu da sufyan yadawo, da sauri safina ta isa wurinsa tana masa sannu dazuwa, ita kuwa yar mulkin tana tsaye a gefe tana karkada kafa , sai da taga safina ta juyo tana kallonta sannan ta furta " sannu da dawowa",
can kan mokoshi ya amsa "yawwa sannu" sannan ya shige abinsa ciki .
safina tayi dariya tace "ku kuma taku salon soyayyar kenan! mulki mulki da shan kamshi dan kun ganni",
safiyya ta harareta bata ce mata komai ba, itama safina dama ba jiran amsarta take ba , dan kuwa tasan halin ta wani lokaci in mulkin nata yatashi sai tayita surutun ta ita kadai amma taki kulata.
Duk gidajen biyu shirye shirye akeyi ba kama hannun yaro , bikin kuwa ba inda bai zaga ba cewan sarki zai aurar da 'ya'yan sa dukka, dagajin haka kuwa kasan biki ne da naira zatayi kuka, kuma biki ne bana wasa ba, amare kuwa sai gyra su akeyi ciki da waje, inka gansu kamar ka sace su ukun ,ko wacce sai sheki takeyi,momy ita taje dubai dukka ta sayo musu kayan daki, sannan ta hadowa twins akwatinan su kowanne sake da kayan azo agani ,su dai safina da khalil kullum cikin zuba soyayya suke a waya safiyya tayi ta musu tsiya wai kar su cinye kansu kafin a daura, yayin da safwan shima kullum like da aunt meena a waya sabanin safiyya da sufyan domin ita tun da ta gansa a kofar gida ita da cwt safina to basu kara haduwa ba ,ko wanne cikinsa harkar gabansa kawai yakeyi.
Da shike duk a gidan sarki za'ayi komai dan haka duk baki gidan suke sauka, kawayen amare sun cika gidan da 'yan uwa da abokan arziki tun ana sauran kwana biyu fada ta dauka kide kide da hawan daushe, kuma ranar akayi hawan angoncin, in kaga yadda angon sukayi kyau kamar taurari dukkansu sunsha alkyabba da rawani ,ga dawakai sun sha kwalliya, kl ina ka duba sai hasken camera ke tashi.
wanshekare kuma akayi kamun amare a fada kowaccensu tasha alkabba sunyi kyau da lallen hannunwan su da kafa, ansha hotuna iri iri, ba ma irin lubiee da tasha selfie, su amiraty ansha asobin kamu, haka dai aka tashi lafiya .
Wanshekare misalin karfe 11 na ranar asabar aka daura aurensu dukka akan sadaki kalilan dan neman albarkan aure, garin gombe ya dauka kide kide da busa ,cikin gida kuwa mata sai guda suke ,maroka nata faman kirari suda fadawa, amaren kuwa sai wadda ta gansu sunyi kyau har sun gaji. su umma da momy kuwa sai fama ake da baki, ita dai safiyya daurewa kawai take domin umma ta ja mata kunne akan kar taji kuma ta gani , "aure dai zata yadda a daura amma a shirye take ta wulakanta duk wanda zai wulakantata".
Da daddare aka fara tafiya dinner, wanda angwayen suka shirya, su brr. jummala anci gayu dama kawar safiyya ce tun shekaran jiya akazo gombe daga zazzau, khalil shi ya fara zuwa ya tafi da safina, sannan safwan yazo ya wuce tare da aunt meena, sai da sukayi minti sha biyar da tafiya sannan gogan ka yazo, da wata mota da duk wanda suke bakin fada sai da suka bi motar da kallo dan kuwa sabuwace dal ranar ya fara using nata, sai abokansa a wata motar dake bayansa,
suka fito sukace bari suje su rakashi fito da amarya yace " ku barshi da kaina zanje na fito da amarya ta",
Dama tunda taji Kurarin fadawa tasan ya iso, dan haka ta sanya alkabbanta akan leshin dake jikinta , sai zuba kamshi take wanda hakanne ya tabbatar da cewa amarya ce ta gaske, tana mikewa kuyangu da kawayenta biyu suka rufo mata baya ana zuba mata kirari "taka alafiya jinin sarauta, zara cikin taurari, amarya agidan sufyan",
yana shigowa murmushi ne dauke a fuskarsa wanda har sai da beauty point dinsa ya lotsa, wanda yake rikita 'yammata dashi , ya balle kudi ya rabawa kuyangu sannan ya kalle kawayenta yace
" kuyi gaba abinku,ni kadai zan fito da amaryata(kujmin pretender)",
aikuwa kowacce tayi gaba shikuwa ya wani riko mata hannu suka fito ya rada mata a kunne "nagaya miki cewa haduwar mu na hudu ba zatayi kyau ba ko, to sa'arki daya yau ne but kijira abinda zai biyo baya.
Tunda suka fito hasken camera keta tashi. ko ita safiyya dataga mota sai da ta kara kallo, ya shiga bangaren mai tuki ita kuma ta zagayo zata shiga amma ta kasa, dan kuwa ta rasa ta inda ake bude motar, tayi kasake tana jiran taga ya bude mata amma shiru,
a zuciyar ta ta furta " ta nan kuma kabiyo hmmmm funny guy",
Gashi duk jama'a idanunsu na kanta amma ace takasa bude mota, sai da yagama jan ajinsa sannan ya danna wani abu mota ta bude murfin yayi sama, shiga tayi bata ce masa komai ba sannan yaja motar suka bar wajen.
yasan sarai akwai sanyi garin amma ya kunna musu a.c dan tsokana amma taki mishi magana dan kuwa naga alama yau mulkin ne ya tashi.
kamshin turarenta da nashi shi kawai ya gaurye motar sai kuma numfashin kowannen su da ke fita a hankali har suka isa wurin.
Suna fitowa masu video da hoto suka musu cha, ko sauran amaren da angwayen sun san cewa su sufyan sunyi matukar kyau .
dan kuwa sunyi matu dacewa da juna , haka dai aka sha dinner akaci aka sha sannan aka goge wuya . karfe goma aka wuce da safina tare da amina gidansu take nan cikin garin gombe, yayin da safiyya sai wanshekare dan kuwa kaduna za'a kai ta dan nan aka maida sufyan din, cwt &cwt ansha kukan rabuwa ido yayi bulubulu
wanshekare karfe 1 aka wuce da safiyya kaduna garin gwamna
[3/7, 11:32 PM] +234 703 962 5239: *MACE KADARA CE MAI TSADA*
NA UMMU SABREENA
ND
AUNTY AYSHA
_january 2017_
<<7>>
Gidane mai kyau domin idan ka kalli gidan sai kara , dan madaidaici gwanin ban sha'awa.wadan da suka kawota ana gama sallar la'asar suka juya gombe, a ka barta ita daya acikin gidan
"Ta goge hawayen daya gangaro mata a kuncinta cikin zuciyarta take fadin _a dauko ka cikin gidan iyayen ka cikin gata da so da kulawa azo a jiyeka cikin gidan mutumin da bai san darajar ka ba.mtsww_,"
Mikewa tayi daga kishingidan datake akan gado ta lalubo wayarta ta danna nombar wayar cwt safina , bugun farko aka daga, safina ta fara mata dariya "amaryar ya sufyan ya akayi ne",
Safiyya tayi murmushi a zaunan datake "lallai amarya wannan dariya haka, uhmm ya amarcin",
"Ke zan tambaya amarci keda kikazo yau niko tun jiya nagama amarci",
Safiyya ta yi dariya "wallahi cwt bazakiyi hankali ba kila sai kin fara aje mana 'ya'ya"
"Ni dai ina ya sufyan, shi ne ko ya kirani ko, ko har ya zama mijin tace ne sai yadda kikayi dashi?".
"Ai keya kamata nawa tsiya, ya khalil inata jiranshi yau ya zo muyi sallama yaki lekowa, kina nan kina mishi kisisina".
Duka su biyun sukayi dariya , sai da suka sha hirar su sannan daga bisani sofy tayi hanging off din kiran.
Ta mike ta nufi falon. Gaskiya ba karya tsarin dakunan ta summata kyau , falon babba shine main falon gidan sai dakin ta wanda shikuwa bedroom ne babba da toilet a ciki sai kuma daga bangaren ta wani dakin shima a gyare sai kuma dayan dayake facing dinta but shi a kulle yake, tana tsammanin nan ne dakinsa, ganin garin ya fara duhu ya sanya ta kunna burner na turaren wuta ta fara turare gidan domin ita akwai son kamshi, aikuwa gidan ya dinga kamshi.
Ana kiran sallar magriba ta shige dakinta tayo alwala tayi sallah nan ta zauna tana azkar har aka kirayi isha'I sannan tayi , tayi safa'I da wutiri sannan ta nannade dadduman , ganin tafara jin yunwa yasan ya ta je kitchen ta saka ruwa a gas, nan da nan yayi zafi ta hado kayan tea ta wuce dasu dakinta , nan ta hada tea din tasha sannan ta fara shirin kwanciya bacci, riga da dauko pink mai kyau acikin akwatinta , rigar ta kai mata har gwiwa sannan anyi kwalliya da stones fari ajikin rigar ta saka sannan ta haye gado tayi kwanciyarta.
Kamar a mafarki takejin magana a cikin dakin, tun tana karyatawa har ta gasgata domin magana ne hade da kukan mutun da dabba, safiyya sarkin tsoro dama ga duhu tama manta inda wayarta take balle ta dauko ta haska , cikin tsoro jikinta ya soma kyarma tana zuba ihu dan a tunaninta aljanu ne , ihu take ba kakkautawa tana neman agaji. Cikin bacci yakejin kaman ihu ,a hankali ya kunna ya wuta ya kara saurarawa ,ihu ne sosai ,da sauri ya fito daga bedroom dinsa ya nufi falo , cikin dakinta yajiyota tanata kuka da karfi ita azo a taimaka mata zasu kasheta, da sauri ya shiga dakin ya lallubi fitilan dake gefen gadonta ya kunna, tana ganinsa da sauri ta daka tsalle ta rarumeshi ta kankame tana kuka "dan allah ka fitar dani wallahi ni dai bazan iya zama anan dakin ba aljanune aciki",cikin sanyi jikin yadda ya rungumeshin ya kalleta " aljanu kuma, ki bude idonki mana ninefa bawani aljanu ", ta kara rufe idonta ta kankameshi "uhm...uhmm.. allah magana nakeji acikin dakin nan, ni dai dan allah ka fitar dani", cikin mamaki ya fara tunani sannan ya gano cewa jiya ya bar akkun shi a dakin nan kuma ya mance ya fita da ita da safe . Dariya ya fara yi kasa kasa can kuma ya daura fuska "to kin wani cakumeni, ki sake ni mana naga ko menene", a dan tsorace ta salube a kan tiles ta bishi da kallo ya mike ya leka karkashin gadonta , sai gashi ya fito da akku a hannunsa , ya gwalo idanuwanta tama rasa abin cewa , ji tayi yana yiwa akkun magana a hankali "baka san nayi aure bane kake tsorata min mata, karka sake kaji" sai kawai taga ya akkun ya amsa da "to bazan kara ba", ya juyo yana kallonta ya wani hade rai "ki tashi ki cigaba da baccin ki", sannan ya fita , ta bisu da kallo sannan ta sauke ajiyar zuciya sai a sannan ta tuno abubuwan da tayi ,itama dariya abin ya bata . Tunda sufyan na karami yakeson akku ganin ta daya tabayi a gidan wani abokin daddy Ali dan haka yacewa daddy shima sai an siyan masa ,dan haka daddy ya siyan masa , tare da akkun sa ya taso kuma sunyi matukar shakuwa da da akku duk wanda ya taba akku to sai sunyi fada dan kuwa suntaba kare jini biri jini da safwan akan ya duketa har yaji mata ciwo , da kyar mommy ta raba ,koda zai tafi turkey tare da ita suka tafi shi ya koyamata magana kuma kowa ya sanshi da akku. Da asuba ta farka tayi sallah sannan ta koma bacci, sufyan ya dawo daga masallaci wuraren karfe 6 da rabi , tuno wa'azin da daddy Ali yamasa akan cewa " matar shi ya kamata kullum ya dinga tabbatarwa da tayi sallah, hakkinsa ne ya dinga koya mata bautan Allah dan haka ya yanke shawarar ya dubata ko tayi sallah asuba dan shi a tunaninsa tana nan tana bacci dan bai ta mishi kama da mai natsuwa da hankali ba, ya tura kofan a hankali ya shiga can ya hangota kwance tsakiyar gado ta lulluba da blanket tana ta baccinta , yace a ransa "dama nasan za'a rina", ya karisa bakin gadon hannunsa sarke a kirjinsa yana fadin "ke! Kinyi sallah kuwa", sarai taji shigowarsa amma ta mishi banza, sai da ya kara maimaitawa hade da bubbuga gefen gadon sannan ta bude ido tana kallonsa duk da yamata kyau da kwarjini domin sanye yake da riga jallabiya fara kar sai ya koma kamar balarabe amma cikin tsiwa tace "ni ba yanzu nake sallahr asuba ba sai rana ta fito dan haka ni ba yanzu ake tashi na a gidanmu ba", taja bargo ta kwanta, tayi mugun bashi mamaki amma dayake bamai son hayaniya bane yasa ya fita a ranshi yana fadin "lallai yarinyar nan ba matar zama bace . Tun daga ranar ya fita harkarta , da safe zatayi breakfast dinta ta kule daki , da rana ma takanyi girkinta wank lokaci kuma sai dare, gayu kuwa sai wanda ya gani ba abinda ya dameta da wani miji can dan ita sai ma taji tsayuwar motar shi ko tashin mota da safe take tunawa da shi , kusan kullum tana waya da umma da mommy kuma tana cemusu ai komai lafiya . Satin su biyu mai martaba ya kira sufyan cewa jakadiya na nan zuwa yau zata musu sati guda, sarki yayi hakanne ya tabbatar da ko suna zaune lafiya kamar yadda suke fadi , yace mata duk abinda ta gani tazo ta fada masa . Ranar da tazo safiyya tanata murna dan dama tagaji da zama ita daya . Da daddare tare sukayi abinci. Ganin safiyya bata warema sufyan nashi ba yasa jakadiya tace " a ah ..autar umma ina na mai gidan naki", safiyya ta wayance "jakadiyya kinga fa bai cika son tuwo ba anjima zan dafa mishi indomie , jakadiya tayi dariya "au to incd inta nice karkiji kunya ta ,ni kamar uwa ce a gareki kuma ni zan baki wasu shawarwarin yadda zaki kama mijinki hannuwa biyu biyu a kwana kinnan ", safiyya tayi dariya sannan suka koma falo dan kuwa ta gane jakadiya aiko ta akayi tayi spying zaman su ita da sufyan. Kuma tasan duk abinda tagani shi zata gaya , kuma in tagane irin zaman dasukeyi har umma taji to ranta zaiyi mugun baci ,gwara ta san abinyi , wayarta taji karan shigowar text dan haka ta duba taga nomba ne _jakadiya tazo gidan yau kuma nasan tazo ne taji ya zaman mu yake dan haka we will pretend kaman muna zaune lafiya_ tana gama karantawa tayi murmushi dan kuwa ta gane sufyan ne ashe yasan dazuwan jakadiyan , dama tunanin abinyi take . Jin karan tsayuwar motarsa yasanta mikewa domin ta tarbo sa ....
[3/7, 11:35 PM] +234 703 962 5239: *MCE KADARA CE MAI TSADA*
©UMMU SABRENA
ND
AUNTY AYSHA.
_january 2017_
<<8>>
Sallama yayi da zakakkiyar muryarsa , a hankali safiyya ta karisa wurinsa ya ansa briefcase din dake hannunsa tana mai fadin
"sannu da dawowa" , murmushi ya mata wanda ya bayyana kawawan hakoransa a wajen
"yawwa, kina lafiya",
itama murmushin ta maida masa sannan suka karisa tsakiyar falon , sufyan ya zauna a gefen kujerar da jakadiya take zauna suka fara gaisawa
"duk sunce agaishe ku ai", sufyan ya ce mata muna amsawa. Safiyya ta wuce dakinsa domin aje masa briefcase dinsa
"gaskiya dakin yayi ba karya sai bin dakin take da kallo gashi ko'ina tsaf tsaf kamshi mai sanyi sai tashi yakeyi , gaskiya daga ganin sa akwai tsafta tunda dai ita ba ta taba shiga dakin ba sai yau, ajiyewa tayi sannan ta fito ta taradda shi sunata hira da jakadiya,
dan haka ta kariso ta bayan sa take cemasa "a kawo maka abincinne?"
. Bai kalli inda take ba don tun kallon daya mata data tarbesa dazun yakejin wani abu na masa yawo tundaga kansa har kafa domin sanye take da wata jar atamfa riga da sket wanda ya zauna mata ajikinta cif cif gashi sai zuba kamshi take wanda kullum yake shakansa a cikin gidan "noo ki barshi coffee kawai zansha",
ganin haka ya sanyata komawa wurin jakadiya sunata hira shima jefi jefi yakan sa musu baki, karfe tara nayi jakadiya ta soma hamma dan haka ta mike ta nufi dakin safiyya, da sauri itama ta bita abaya , ganin jakadiya nayin safa'i da wutiri ya sanyata shiga wanka ,minti biyar ta dauka ta fito , humra kawai ta shafa ta sannan ta saka rigan bacci doguwa wata dark blue ta koma kusa da jakadiya zata kwanta
"a ah autar umma nifa ba sai kin tayani kwana ba tafi wurin mijinki nayafe zan kwana ni kadai",
safiyya ta hadiye yawu da kyar domin jakadiya ta juya mata baya aikuwa ta turbune fuska kamar zatayi kuka
"haba jakadiya ni..ni..ni kawai ki barni mana dan dai yau kawai, hira nakeson muyi ",
jakadiya ta mike daga kwancen datake ta rike baki "autar umma so kike gobe goben nan mai gidan naki ya ce na barmasa gida.
Ni tashi ki tafi wurin mijinki , bari ma na baki sakon momy tace na baki ", mikewa tayi ta bata wata zuma mai kyau sannan ta gaya mata yadda zata na using dinta, hakanan ba yadda ta iya ta mike ta dauki hijjabi iya gwiwa ta saka sannan ta fita . Sai da tayi kusan minti biyar a kofar dakinsa sannan ta kwankwasa , zaune yake a gefen gado yana danne danne a system dinsa dan kuwa satin nan yanada wani case mai zafi ne, bai dago ba yabada umarni cewan a shigo , bude kofan tayi ta shigo a hankali kamar wacce batason taka kasa ,dago kai yayi yana kallonta ta kasan ido sannan ya dauke kai
"yasan jakadiya ce ta korota amma ya ce mata "lafiya kika wani shigo min daki bako sallama , ko angaya miki dakin nan na marasa tarbiyya ne irinki" ,
jingina tayi da kofan itama ta hade rai "kasan haka nan ba abinda zai kawoni dakinka dannafi karfin nazo wuri wanda baisan darajar mace ba",
mikewa yayi ya nufota da sauri ta gwalo ido ita akwai tsoron duka , hannuwanta ya riko ta murdesu ta baya sannan ya kama dan mitsitsin bakinta fasa kara tayi tana ihun zai kasheta , cikin zafin rai
"ni zaki dinga ma rashin kunya ko, rannan kinmin na kyaleki shine yauma zaki kuma, kafin kidinga furta kalma kidinga sanin waye a gabanki , mara kunya kawai , sa'arki daya kike ci amma da sai na miki lagalaga a gidannan ,
sake mata baki yayi aikuwa ya kai masa cizo a hannun sannan tayi sauri ta mike zata gudu , riko hijjabin jikinta yayi da sauri tacire hijjabin ta bude kofan ta fita falo tana fadin "Allah ya isar min, mugu kawai", bai bita falon ba dan haka yacigaba da abinda yakeyi har karfe goma da rabi sannan ya kwanta , tanan falo har karfe 11 lokacin ta tabbatar yayi bacci sannan a hankali ta murda kofan dakinsa ta shiga , can karshen gado taje tayi kwanciyarta har bacci ya kwasheta ,
karfe uku ta farka ta gansa yana sallah, har zata mike tayo alwala dan kuwa tasaba tashi ta yi sallah Duke dare sai ta tuno bata sallah dan haka ta cigaba da baccinta .
Saida aka kirayi sallah asuba sannan ya mike ya fice masallaci.koda yadawo ya tarrada bata nan dan haka ya kwanta ya cigaba da baccinsa kasancewar bada wuri zai dawoba.
Tana fita taje tashiga bayi tayo wanka sannan ta tsaftace jikinta,jakadiya na kwance tana lazimi, safiyya ta matso suka gaisa "autar umma mai za'a dafa muku ne yau",
safiyya tace "kawai jakadiya a fere doya sai ki soya da kwa sai asa ruwan tea",
mikewa sukayi dukka jakadiya ta nufi kitchen yayin da safiyya ta fara gyran dakin.
suna zaune suna breakfast itada jakadiya yavshiryo da nufin fita, bai gansu ba dan haka yayi niyyan fita .jin muryar jakadiyavyayi tana gaisheshi "ranka shi dade an tashi lafiya",
tsayawa yayi yana murmushi "alhamdulillahi jakadiya, ya bakunta",
itama dariya tayi tana fadin "lafiya kalau",
sannan ya fice, yana fita jakadiya ta kalli safiya , "naga bai karya ba ya kuma fita?",
"jakadiya azumi fa yakeyi, ki daina damuwa da ya sufyan in yana bukata dakanshi zai zo muci,yau azumi azumi yake kinsan yau litinin",
tunda yamma tayi safiyya ta fara aikin waina itada jakadiyya,gidan sai zuba kamshi yakeyi, dalilin karyar data zabgawa jakadiya cewan sufyan na azumi dan haka taketa shirya masa kayan shan ruwa, sannan sukayi zobo mai dadi, suka jera a dining table, bayan anyi sallah magribavsa gashi ya dawo , dakinsa ya nufa direct, wanka yayi ya shirya sannan ya fito falon jin hirarsu. safiyya ta bishi da kallo dan kuwa ba karamin kyau ya mata ba .gashin nan kwance luf luf ,jin jakadiya na mishi sannu da shan ruwa ya sanya shi ganewa kila soffy tace mata yana azumi ne, safiyya ta fadi a hankali "ga abincin ka a dining kona kawo maka nan ne?",
"no bari naje can din",
mikewa tayi taje tafara zuzzuba masa.tunda yaga abincin miyansa ya tsinke, ya wani lumshe ido yana tunanin yasan dai ba soffy tayi abincin nan ba kila jakadiya ce ta dafa dan wannan mara kunyar ba abinda ta iya. iya ba yafarayi yana ci ba kakkautawa, sai da ya cinye abincin tas sannan ya kora da zobon .safiyya na daga dan nesa dashi tana chatting da safina a wayarta. juyowan dazatayi taga yaclamushe wainar tas. ita abin mamaki yabata dama yana cda ci haka.aiko dai yaci albarkacin jakadiya amma da ba abinda zai sa ta mishi girki.
kwanan jakadiya hudu ta koma gida d dunbin tsaraba. kuma tunda ga wannan lokaci zaman ma'auratan guda biyu ya canza yakoma yadda yake.
sarki yavsamarwa safiyya da safina transfer zuwa ABU Inda suka cigaba da zuwa. ita safina da shike khalil yanada gida a zaria dan haka ya baro gombe ya dawo zaria.yayin da safiyya ke zuwa ranar sunday sannan ta koma ranar friday .abota ta dawo sabuwa tsakanin safiyya da safina kullum a schl suna tare.
[3/7, 11:38 PM] +234 703 962 5239: *MACE KADARA CE MAI TSADA*
NA UMMU SABREENA
AND
AUNTY AYSHA
```January 2017```
```<<10>>```
Bayan sunyi breakfast ne dukkansu sannan suka shirya domin tafiya asibitin, mota biyu sukayi , motar daya sufyan ke janta dayan kuma safiyya ke jansu matan, suna isa dakin nan suka zauna aka gaisa, safiyya ta aje musu flask din abincin data kawo sannan ne sufyan yacewa mazan dasu taso suje su gaida yan sauran gadajen. Kowani gado sukaje sufyan kan aje musu dubu daya sunata godiya har suka isa gadon karshe,
"Yatinyace wacce bata wuce shekara goma sha biyar ba tanata sumbatu hade da kuka matar ta ke gefenta tana rirriketa tana tofa mata addu'oi tana kuka itama.
Sufyan da khalil suka karaso cikin tausaya suke cewa matar "Allah ya bata lafiya",
"Amin mungode"
Safwan ya kallesu yace "ku kira likita mana tunda naga kaman jikin ya tashi",
Matar ta goge kwallan daya zubo mata sannan tace, lokacinne safina ta karaso itama jin kukan yarinyar
"Tunda muka zo jiya haka taketa sumbatu da surutai, likita kuma sunce aiki za'ayi mata amma sai mun aje dubu arba'in sannan",
Safina ta girgiza kai cikin tausayawa take fadin" Allah sarki ina mahaifinta fa",
Safiyya itama ta biyosu tazo ta tsaya kusa da cwt dinta
"Mahaifinta ya rasu ai tun tana karama",
Safiyya ta tambayi safina cewan meke damun yarinya kuma ina likita , nan safins ke ce mata "ai wai operation za'ayi mata kuma ance sai sun bada 40k .
Safiyya a hankali take furta "hajiya kar ku damu indai 40k ne zan biya bari likitan yazo, amma a ina za'ayi mata aikin , meke damunta?",
Matar ta fashe da wani kuka mai cin rai " fyade akayi mata",
Safina ta gwalo ido "fyade kuma.innalillahi wa inna ilahi raji'un.garin yaya?",
Su sufyan kuwa daskarewa dukayi a wajen, khalil ya shiga girgiza kai "kai mutane basu da imani, wannan yar yarinyar",
Matar ta kallesu da idanuwanta dasuka koma ja sannan tace " mahaifinta ya rasu tun tana yar mitsisuwa , dan haka rayuwa tamana kunci da zafi, duk abinda mahaifinta ya bari duk yazo ya kare, ganin haka yasa na baro rigar mu ta fulani dake kafanchan na shigo cikin gari neman aiki, a hakan nasamu aiki a gidan wata hajiya, matar mai mutunci amma mijinta dan siyasa ne. Dan su daya mai suna faisal. Mahaifinsa ya rigada ya sangarta yaron sabida shi kadai garesu. To jiyan da safe na aiketa bagaren faisal din ta kai masa abincin sa na karin safe .nace inta dawo ta yi wanke wanke Ni kuma sai na shiga sasan hajiya kulu. Can kaman bayan minti sha biyar sai najiyo ihuta.
Da sauri muka fita nida hajiya kulun . Dashike ihunnata daga bangaren faisal mukeji dan haka nan muka fita .
Cikin dakinsa muka dinga jin ihunta da sauri na nufi wurin inata bubbuga kofan dakin. Hajiya kulu itama ta biyoni tana jijjiga kofan dakin hade da kiran sunansa , kuka nasaka nida mahaifiyarsa ina fadin
"Hajiya ki taimaka danki zai kashemin ita, ita kenan min a duniya, yau na shiga uku ni lubabatu",
Hajiya fadi take "ka bude ka bude amma yaqi har muka dena jin ihunta",
A sannan ne ya bude kofan ya bar gidan lokacin da Hajiya kulu ta saura sasanta ta dauko guduma dan balle kofan. Yana fita da sauri na shiga dakin shine na sameta a sume jini na bin kafafunta , ko da hajiya ta dawo shine ta dauki mota ta kawo mu nan.
"To tunda takawo mu tasa aka bamu gado bata dawo ba har yanzu",
Safwan ya girgiza kai cikin tausayawa yace "to ke yanzu mama bazaki iya zuwa gidan kifadawa mahaifinsa ba ",
"Ai tunda kaga hajiyar bata dawo ba to nasan da hadin bakin alhaji wurin karewa dansa",
Safina sarkin kuka sai hawaye take "lallai mutane basu da imani, kai Allah yasaka muku",
Sufyan ya numfasa sannan yace "insha'allahu mama zan iya iya bakin kokarina wajen na kwatowa yarinyar nan 'yancinta kuma shi faisal kotu ce zata rabamu dashi",
Khalil yace "kwarai da gaske dan kuwa ni nagane gidan alhajin datake nufi, azzalumi ne kuma macuci,",
Nan suka yita bawa inna luba hakuri, likita na zuwa safiyya tamasa magana akan cewa zata biya kudin. Zuwa dare zatazo sannan suka wuce.
```8:00pm```
Da daddre safiyya da safina sukaje asibitin suka kaiwa inna luba abinci lokacin Amira tanata bacci , inna luba nata godiya sannan suka dawo gida.
Kafin su kwanta kowa yanata jimamin abin a ransa sannan kowannensu yaja matarsa suka wuce dan su kwanta.
Wanshekare da safe dukkansu sai da suka biya asibiti. Dan kuwa ranar zasu koma gida. Lokacin Amira ta farka tana kishingide inna na bata tea. Nan aka gaggaisa safiyya ta matso ta shafi fuskar Amira tana fadin "sannu kinji. Ya jikin naki?:,
Murmushi kawai tama , inna ce ta amsa "ai jiya bayan tafiyanku aka mata aikin. Jikin alhamdulillahi tunda gashi ta sha tea ma",
Safina tayi murmushi" yarinya kyakkyawa da ita , kai Allah ya saka miki",
"Amin amin cewan aunty amina datake zaune a gefe.
Khalil kudi yabawa inna shida safwan sannan suka wuce.
Sufyan daga nan office ya wuce yayin da sofy ta nufi gida a motar ta a zuciyarta tana saka wani abu
[3/7, 11:42 PM] +234 703 962 5239: *MACE KADARA CE MAI TSADA*
©UMMU SABREENA
AND
AUNTY AYSHA
_january 2017_
<<9>>
Hutun da suka samune ne dakkunsa na karshen shekara yasanyasu kiran sufyan cewan suna nan zuwa. dashike shine babba duk cikin khalil da safwan. aikuwa ranar da suka iso gidan ya kacame domin ranar juma'a sukazo. dukkansu suna zaune a falo anty amina da dan cikinta na wata biyar wanda fito ya mata cas, duk inda ta motsa safwan ya ce mata "lafiya", sufyan da khalil nata mishi tsiya. ita dai aunt amina sai dai tayi ta dariya , safiyya da safina suna kitchen sunata hada musu abinci da drinks . safina ta dan kallo safiyya tayi murmushi "cwt naga kin wani cicciko ne, kodai da bayani ne",
safiyya tayi far da ido tana fadin
"ke ni bani da wani ciki bansan gulma ke dai kawai kicemin kin kamu",
safina tayi dariya " haba amaryar ya sufyan duk wannan ji dake da yayanawa yakeyi bazaki aje mana kid ba",
a zuciyan safiya take fadin "allah ya rabani da hada jiki da wannan dan rainin wayaun balle akai ga wani ciki" amma a fili tace " sai kin aje mana twins sau uku sannan zan baku guda",
safina ta dinga dariya a haka har suka kammala abincin sannan suka dinga kaiwa falo. safina isa wurin ya khalil tana fadin
"habibi na barka da yunwa ko,sorry bari na zubo mana muci tare",
murmushi yamata "karki damu cwry ni ,dafatan dai autar umma bata wahalarmin dake ba ko",
ai sufyan yayi maza anshe zancen "iyyeh ko dai kunzo kun cika mana gida zaku wahalarmin da mata", (kunji pretenders)
safiyya ta kalleshi ta ksan ido ita dai tanason kallonsa inyana magana sabida dan bakinsa na mata kyau.kodan bata saba ganinsa yana dariya bane oho. safina ce ta katse mata tunani ta hanyar fadin
"nidai ni da mijina kawai zan zubawa munci tare", ta mike ta dauki plates ta zuba musu.
safwan ya saki baki "wai ni yaushe safina ta zama haka jama'a.
khalil ya katse shi "no kar ka tasamin mata agaba. kajimin wani zance.kaima taka ta mike tasa maka mana.ka wani kwantar da ita kamar zaka mai data ciki
"cant yhu see ita lalura gareta, ay dayake ma dakaina zan sama tare muci,"
safina ta ce barsu kaji ya safwan bari na sanya muku. tare ta sanyawa aunt amina da safwan sannan ta hada nata dana sufyan.
matsowa tayi kusa dashi tawani marairaice fuska " dear ko nabaka a baki ne",
murmushi ya mata wanda shi kadai yasan ma'ar sa "banaso kisha wahala dear, barshi zanci da kaina",
tare suka fara cin abincin. bakajin komai sai karan cokula da kuma a.c daketa aiki a falon. yanda suke cin abinci zaka dauko masoya ne sabida yadda sukayi matukar dacewa da juna amma kowa ta ciki na ciki.
Da daddare dukkansu suna zaune a falo yayinda su matan suna bedroom din safiyya. aunt amina ta fito musu da wani abun a cikin jaka tace " gashi nace na kawo muku kuyi using yanada kyau, sannan ta fito musu da sabulun wanka na magarya da kuma humra. kowaccen su ta shafa aiko dakin ya bude da kamshi .
aunt amina ta kai kallonta ga safiyya tana dariya "anya autar umma bakida ciki jifa yadda kirjin ki da hips suka cika.kodai boye mana kike",
shagwabe fuska tayi "wallahi aunty banida komai fa shekaran jiya nagama period ",
"ohk amma gaskiya ya sufyan ya iya raino .wannan amarci haka",
safina tayi dariya tana fadin "aikuwa. dai ana ba'aso ba'aso amma gashi kamar ta maida shi ciki",
safiyya ta bita zata duka da sauri safina tayi falo tana dariya. safina na zuwa ta shige bayan khalil tana cigaba da dariya sai ga safiyya ta biyota har falon wai saita duketa .
khalil ya kalleta yana fadin "lallai auta .yanzu matar tawa zaki duka agabana",
safiyya ta shiga bubbuga kafa " wai yaya khalil kasan abinda taminne",
safina ta leko kai tace "wai dannace _tana batason ya sufyan da amma yanzu kamar ta maida shi ciki shine tabiyoni_",
sufyan dake kishigide jikin kujera ya kalli safiyya ta wutsiyar ido sannan ya miko mata hannu alamun tazo garesa "kyalesu kinji dear, ai tokanar ta tayi ",
safiyya ta isa gareshi ya rungumota wanda hakan yasanyasu duk ilahirin jikinsu ya amsa, kamshin jikinta ya shaka wanda sanyashi lumshi ido , da sauri ta murgina gefen sa ganin yadda idanunsa suke a rufe ya sanyata a hankali ta furta " ya safwan aunt amina tana dakinmufa kaje kuyi sallama dan zamu shiga mu kwanta . aikuwa safwan dake danna system a gabanta ya watso mata kallo "ai duk inda matata zata kwana nima nan zan kwana haka nan kuje ku murkusheta ita da babyna",
khalil yayi dariya "to dama waya cema karka kwana kusa da taka matar. uhmm ni kunga dama ga dakin dazamu kwana can . ya nuna dakin dake gefen na safiyya.
safiyya tayi rau rau da fararen idanuwanta "yanzu maimakon kubarmu mu kwana tare muyi hira shine duk zaku kwashe su ko, bakomai",
ta lallubo tattausan hannun sufyan tana fadin " dear tashi muma mu wuce namu dakin tunda waremu zasuyi",
sufyan yayi murmushi a zuciyarsa yake fadin "lallai yarinyar nan shu'uma ce, sai kace irin dagaske dinnan. ohk shima zai nunamata dan duniya ne irinta,
mikewa yayi hannusu a sarke yana fadin " sai da safenku"
A Duk lokacin da jikinsu ya hadu to kowannensu sai yaji ajikinsa . shidai sufyan yana gwammace nesanta kanshi da ita sabida duk lokaci da jikinsa danata suka hadu yakan tsibci kansa a wani yanayi na daban. shidai yana kokarin kare kansa daga zina domin 'yammata dayawa suna kawo masa hari. sanin halinsa ne yasanyashi yawaita yin azumin nafila .na farkovdai bazai iya kusantar safiyya ba sabida batada qualities din macen dayakeso. a ganinsa batada ilimin addini kwata kwata.to matar da tace ita bata sallahr asuba sai rana ta fito.gaskiya sarki yayi sakaci da tarbiyyan soffy.zai dai llalaba da ita harta gaji ta nemi saki dakanta. dan haka yaketa kokarin kanewa har sai ya samo maccen dayake so.
suna zuwa corridor ya sake mata hannu. tsaki taja sannan taja ta tsaya har yayi gaba sannan ta bisa a baya. yadda tasaba kwanciya can karshen gado taje tayi kwanciyarta. basuce da juna komai ba . karfe uku ya kejin kaman kartu daga gefensa, yana farkawa ya hangota a kan dadduma. danye da hijjabinta data taba bari tun zuwan jakadiya da kur'aninsa tana rero karatu cikin suratul hud.kasa gasgata kunnansa yayi ya kara kallan itada batasan ma yana kallonta ba. lafewa yayi a gado yama kasa tashi yau balle yaje ya dauro alwala
_"dama safiyya tana karatun alqur'ani , dama tasan Allah take wannan tsula tsiyar tata, lallai kuwa_
ya lumshe ido yadda kira'arta ke tashi cikin muryarta mai dadin saurare. saida taji ankirayi sallah assalatu sannan ta mike taje ta kwanta. koda yadawo daga sallah asuba ty taradda da ita ta gama sallah kenan zata mike. ko kallon inda take bai yiba ya wucewarsa ciki.
kitchen ta wuce tana tsaki a ranta"dan wulakanci kawai,ai wallahi ka gamu da dai dai kai",
sai karfee shidda sannan safina ta fito domin tayata aikin gidan . dan kuwa anjima zasuje asibiti dan gaida matar abokin ya safwan. maizaifaru???
[3/7, 11:45 PM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```NA UMMU SABREENA``` ```AND```
```AUNTY AYSHA```
``` January 2017```
```<<11>>```
Karfe goma na safiyar laraba safiyya ta nufi asibitin dasu inna luba ke kwance. Jikin amira kuwa ta warke sai dai dan har tana takawa. Sunata hira da safiyya nan take tambayan Inna wani unguwa ne gida alhajin datayi aiki, inna ta ce maga unguwar sarki ne nan tamata kwatancen gidan. Amira natama safiyya godiya dan kuwa inna ta bata labarin taimakon da suke musu.
Da Rana sufyan ya nufi asibitin yacewa su Inna luba cewan ya shigar da karan Faisal kotu , kuma za'a Fara zaman kotu ranar litinin wato gata.suna ta mishi godiya sannan ya wuce .
Alkali ya aikawa da alhaji da sammaci cewan ana karan dansa a kotu cewan yayiwa yar aikin gidan fyade. Alhaji ya shigo a hargitse yana nunawa hajiya kulu takardan, ya zauna yana huci
"lallai matar nan ni zata tozarta yadda ake ganina da mutunci, duk irin taimakon danake Mata da rufa mata asirin danayi, to wallahi Dani suke magana, sai na wulakanta ta itada 'yar tata",
Hajiya tacigaba da cin fruits din datakeyi batace masa Kala ba , ganin haka ya harzuko kanta
" dama na kula bason yaron nan kike ba, jibi Ina magana kinyi banza Dani! Ga mahaukaci ko?",
Ta ajiye tufan datake hannunta itama a zuciya tace
"Aifa sannu mai 'da!, lokacin da nake kokarin na dinga hanashi wasu halayen nasa na banza bacemin kayi ina takura masa ba,
Kar kamanta fa har rigima muka so muyi ta kan Ina dora Faisal akan hanya ta gari, ranar da abinnan ya faru na fada maka me kace?,
Cewa kayi ai yarinyar ce bata da tarbiyya, ita ta Kai masa kanta, to ni ko na godewa Allah da suka kaisa kotu, nan zasu koya masa hankali, menene Faisal bayayi agidanan, ka taba kwaba masa?!",
Alhaji ya watso mata kallon banza " bakinki ya sari danyen kashi, ke kanki kinsan bani da mutunci. Banida tausayin duk Wanda ya shigo cikin rayuwata, sai nasa an shafeta itada matsiyaciyar 'yarta a doron duniya dakuma lawyer da suka dauko, ke kuma ki kiyayeni!, fuu ya fita yana surutai .
Hajiya kwalla ta zubo mata "wannan wace irin rayuwa ce. Kwatakwata ace baka da iko da 'dan daka haifa, Kai itadai alhaji ya cuci rayuwarta",.
Safiyya dataje asibiti wanshekare ne Inna luba ke cemata " ai sufyan ya Kai su Faisal kotu, batace musu komai ba ta wuce Gida dankuwa ita duk harkan da tahada da sufyan bata marmarin shiga ciki.
Faisal ya kalli abokinsa abdulhamid yace " nifa abinnan duk ya dameni , Dan kuwa inba munsami lawyer maikyau ba to za'a iyayin nasara akanmu. Kaga jibi nefa za'a shiga kotu,"
Abdul yayi murmushi "kar kadamu frnd, ni aganina indai akwai kudi ba problem, ka ganni nan ban dauki mace abakin komai ba sai kayan hutawa, banga laifinka ba Dan ka yi amfani da wannan yar yarinyar kuma fa maid din gidan Ku kace ko?",
" eh ,I think she is 15",
Abdul yayi dariya harda buga kafa
"Lallai kayi kokari, kaga ni bana harka da less than 20yrz, amma kar ka damu tunda Ina nan, akwai wata lawyer da nayi aiki da ita last week kan wani case, gaskiya lawyer akan baki gashifa macece amma gwana ce",
Faisal ya Dan tashi yana fadin " haba abokina ka hadani da ita mana yau, sai muje Dan kuwa in kudi ne kasan akwai su",
Abdul ya dafashi "cool down! Yanzu ka shirya Zan Mata Waya mu hadu office anjima, karka damu zata zo",
Faisal yayi dariya " ai nasan kai bana wasa bane mutumina",
_3:00pm_
Safiyya ta fito daga cikin motar ta, sanye take da wani less blue mai ratsin pink ajiki, da hajjabi Wanda ya saukar Mata gwiwa sai flat shoe blue shima ammasa kwalliya da pink ajiki, Abdul na hangota ya was he baki yana fadin
"Barka dazuwa lawyer",
Murmushi tayi kadan sannan tasamu wuri tazauna" barkanka dai ya aiki',
"Lafiya lau, jiya ai na baro Lagos na shigo kd, ya Gida ya oga",
" suna lafiya",
Abdul ya juya ya kalli Faisal sannan yace da ita "wannan amini nane Faisal",
Gyada Kai tayi kawai shi kuma Faisal yace " Ina gaisuwa lawyer ",
" ya Gida ya yara",
Dariya yayi yace "banyi aure ba tukun amma muna kan hanya",
Abdul ya kalleta " kinga brr. Wallahi wani case ne ya tasomin, abokina ne by mistake yayiwa yar aikin gidansu fyade,
Da sauri safiyya ta dago ta kalleshi tana nazarin abinda Abdul ke fadi, Abdul ya katse mata tunani
"To shine uwarta takaishi kotu, munaso ne Dan Allah ki kare mana shi akan cewa sharri suke mishi",
Safiyya ta kallesu can ta numfasa tace " yasunan yarinyar?',
Faisal yace " sunanta Amira, aiki suke tare da mamarta a gidanmu",
Nan safiyya ta gano wacce Faisal ke nufi amma ta basar. Ajiyar zuciya ta sauke "bakomai yanzu yadda za'ayi kabani nombar wayarka zuwa gobe in allah yakaimu zamuyi waya , karka damu", dukkansu suka washe baki ,faisal ya kalleta "to barr. Kaman nawa zamu fara baki?". Murmushi tayi tana kallon abdul "no karku damu da nawa zaku bani. Bana bukatar ko kwandala daga wurinku. Dan kuwa kudin basu ne a gaba na ba, shi abokin naka ai ya sani". abdul. Yayi dariya sannan yayi mata godiya sannan ta wuce . Tafiya take a mota amma hankalinta ya kaisu kashi biyu, Tasan cewa zaluntar amira akayi kuma sufyan ne mai gaskiya but zata ansa case dinne kawai dan ta nuna mishi shi ba abakin komai ba yake a wurin ta. Ba wai zata amsa case din bane dan tayi nasara. No a ah zata ansa ne kawai dan ta goga da sufyan a kotu, bawai zata ansa case din bane dan ta zalunci su inna luba. Kawai zata ansa ne dan ta nuna masa baikai matsayin namiji ba a wurinta. Zata ansa ne dan wata manufa tata ta daban. Wanshekare safiyya ta kirayi faisal ta tambayesa wani kotu ne za'ayi zaman. Nan ya fada mata ina ne sannan tace masa su hadu gobe. _8:00am_ na safiyar litinin mutane ne keta fitowa domin shiga cikin kotun dake rock road . Sufyan yayi parking motarsa sannan ya fito cikin hanzari . Dubawan dazaiyi kawai yaga motar safiyya daga gefensa da hagu. Bai gasgata abinda yake gani ba ya budewa Amira da inna luba motan suma suka fito. Sanye yake da kayansa na lawyers wanda sukayi masa kyau, kai tsaye wurin zamansa ya nufa sukuma su inna luba suka samu gurin cikin mutane suka zauna. Alkali ya shigo kowa ya mike . Dashike kansa a kasa yake bai kula da ita wurin ba sai da aka gabatar da case dinsu sannan alkali yace kowani barrister ya mike ya gabatar da kansa. Shi ya fara mikewa " sunana barrister sufyan aliyu kuma nine lawyer wanda suke kara", mikewa tayi a hankali take furta "sunana barr. Safiyya abubakar maikudi kuma nice lawyer mai kare wanda ake kara. Dagowa yayi cikin kaduwa dakuma daure kai ya zuba mata daradaran idanuwansa .nan idanuwansu suka hadu da juna.......
[3/7, 11:47 PM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
_january 2017_
```<<12>>```
sauke idonta tayi ta zauna hade da gyara pashminan dake kanta, ganin ta maze ya sanyasa shima kauda kansa daga kallonta .
shiya fara mikewa sannan ya bukaci ganin inna luba.
"Munaso kifadawa kotu cikakkan sunanki da kuma matsayinki ga Yarinyar da akayi fyade",
inna luba ta gyara tsayuwarta tace "sunana lubabatu sani kuma ni mahaifiyace gareta", "shin menene matsayinki a gidan alhaji dandano"?, "ni ce mai yiwa hajiya kulu aiki ni da yata amira",
"shin ko zaki iya fada mana mai yafaru ranar da abinnan ya faru", inna luba ta numfasa tace " ranar nagama girki sai na raba nace ma amira ta dauka ta kaiwa faisal nasa bangaren, sufyan ya katse ta " waye shi faisal din?", "faisal shine 'da daya tilo ga alhaji dandano da matarsa",
uhmmm cigaba muna sauraronki . Inna ta cigaba " bayan ta dauka sai na ce mata idan ta dawo tayi wanke wanke ni zan wuce sasan hajiya, bayan kaman minti biyar da hawana kawai sai mukaji ihunta nida hajiya, da sauri muka fito muka nufi sasan faisal sabida daga nan mukejin ihun nata, muna zuwa na fara bubbuga kofan tare da kiran sunanta, hajiya ita kuma tazo tana kokarin bude kofan tana kwala masa kira amma bai bude ba, tun inajin kukanta sosai har nazo banaji, ihu hade da kuka na fara ina fadin "hajiya karya kasheta ita kenan min a duniya".
hajiya da sauri ta cemin bari ta je ta dauko karfe wajen baba maigadi dan a balle kofan , ta wucewa sai gashi ya bude kofan ya fito ya tsallakeni a durkushe ya wajen ya wuce ko a jikinsa, nidama batashi nake ba ta 'yata nake, da sauri na shiga sai ga hajiya ta dawo tana fadin ina faisal din a rikice hade da kallon Amira dake kwance a kasa jini na bin kafarta kaman matacciya , ban amsawa hajiya abinda take fadi ba domin ji nayi numfashi na na barazanar daukewa "fa...fa..fyade yayi mata hajiya! Wayyo nashiga uku ya kashwmin 'ya",
da sauri itama hajiyar tana hawaye shine tace mun na dauko ta mu tafi asibiti da sauri, mota taje tafito dashi ta kawo mu asibiti amrullah dake dutsimma .
Bayan ta ance za'amata aiki sai tace bari taje gida ta dauko kudi.To tunda ta kawo mu har dare bata dawo ba.
Sufyan ya girgiza kai yana fadin" inna shi mahaifin nashi baizo ba?", " bawanda muka kara gani daga gidan, shiko alhajin ina muke ganinsa dama!",
"ya mai shari'a ko da wadannan maganganu na wannan baiwar allah ya isa ace kotu ta duba zancenta kuma ta daukan mata hakkinta akan zaluncin da faisal yayi mata, Nagode ya mai shari'a",
komawa yayi yasamu wuri ya zaunan sannan alkali yace " ko lawyer mai kare wanda ake zargi sunada tambaya? Abdul ya mike yana fadin "eh inadashi ya mai shari'a.
Matsawa yayi kusa da inna yana fadin "malama lubabatu dama yar taki ita take kai masa abincin kullum ko kuwa ranar ne kawai kika aiketa?". Inna tace "eh ita kullum take zuwa kai masa",
abdul ya gyada kai yana fadin "da take kai masa abincin ta taba zuwa ta ce miki ya taba yi mata maganar banza ko ya taba gigin taba mata jiki ko wani abu makamancin haka?",
" gaskiya nidai bata taba cemin ga wani abu a tsakaninsu ba", abdul ya juya " ya mai girma mai shari'a. " inaso wannan kotu mai adalci ta dubi wannan kage da akeso ayiwa wannan bawan allah akan cewa yayi ya amira fyade cewa sharri ne domin idan da Ace dagaske ne ai ba tun yau take zuwa kai masa ba kuma ba wani abu dake shiga tsakaninsu dan haka kotu ta dibi wannan zance nacewa zamewa tayi ta buge da kwalba acikin tiles, nagode ya mai sharia, alkali ya kalli sufyan yana fadin "ko lawyern mai kara yanada wata shedar",
sufyan ya mike yace " eh inada ita, inason ganin amira", amira ta fito cikin natsuwa ta nufi inda aka tanada dan ta tsaya",
sufyan ya kalleta yace " munaso muji sunanki", sunana fatima amma anfi kirana da amira", sufyan ya ce " shekarar ki nawa amira?",
"shekarata 15",
sufyan yayi murmushi yace "ko zaki gaya mana abinda ya faru tsakaninki da faisal?",
"eh ranar inna bayan ta gama girki na dauka domin na kai masa daki kamar yadda nasaba sai in jera masa a dining table, sufyan ya katseta
"ko baya dakin kina shiga ki ajiye masa kenan",
amira ta gyada kai "ko baya nan nakan ajiye masa na fito, to ranar ina shiga bayan nagama jera masa zan wuce shine ya taremin hanya wai na harareshi bayan nashigo , sai nake mamaki dan kuwa ni tunda na shigo ban kalli inda yake ba, kawai sai ya fincikemin hijjabin dake jikina nikuma tsora yasa nafara ja da baya zanfara kuka, shine yace wai ba abinda zai min kawai yanaso yaga kwalliyata ne, haka ya dinga bina ina matsa har yayi nasarar kamani, ya toshemin baki muka fara kokawa, dayake karfin mace da namiji ba daya ba nan yayi nasarar yimin fyade, ta goge hawayen daya zubo mata ,kotu ta dauki hayaniya yayin da faisal da alhaji suka fara mazurai , abdul ya mike ya kalli amira yace
"malama amira mecece ribarki indan kin yiwa mutum sharri alhalin bashi ya aikata miki abu", amira ta zuba mishi idanuwanta "ba ribar dazanci inhar zanyiwa mutun sharri a duniya amma kuma ubangijin daya haliccemu yasan gaskiya nafada",
abdul yayi dan murmushi yace "ya mai girma mai shar'a inason faisal ya fito domin ya gaya mana gaskiya abinda ya faru, nagode ya mai shari'a. Faisal ya fito sannan abdul yace masa
"zamuso kagayawa kotu cikakken sunanka dakuma alakar ka da amira", "sunana faisal usman dandano kuma tsakanina da ita shine ita aiki suke a gidanmu",
abdul yace "munaso muji gaskiya lamari akan abinda ake zarginka dashi",
faisal ya gyara tsayuwarsa sannan yace "ranar ta kawomin abinci nikuma na shiga toilet kawai sai naji ihunta, ina fitowz naganta kwance cikin jini ta zame ta bige da center table, shine nayi sauri na isa gareta ganin jinin dayake zuba kuma gashi tanata kuka mai karfi yasa narasa abinyi dukda inajin bugun kofa, sai daga karshe ne na iya bude kofan na fita da sauri dan dauko mota mu wuce asibiti",
abdul ya kalle shi yace "ya mai sharia kaji shi faisal taimakonta yaso yi amma dayake mutane yanzu basu da amana dama suna rike dashi a rai shine za'a ce yayi mata fyade, inaso wannan kotu mai adalci tabiwa faisal wannan sharri da bata mishi sunana da akeso ayi ,nagode yamai shari'a.
"Ko lawyern masu kara yanada tambaya ga faisal", sufyan ya mike "inadashi ya mai shari'a",
sufyan ya kalli faisal tsaf sabida hango rashin gaskiya a idonsa
"malam faisal mai yasa lokacin da mahaifiyarka suke kwala maka kira baka bude ba a lokacin?",
faisal yace " eh bakaji nace nima lokacin a rude nake ba, sai daga baya nayi dabaran inbude inkaita asibiti, ko kafin nadawo mai gadi yacemin sun wuce da ita", to menene yasa baka bisu asibitin ba?"
Faisal ya dan daburce "eh ..eh ai koda nadawo naji kaina na ciwo dan haka nace bari wanshekare sai inje",
"to meyasa ka baka koma ba?" "Ai sai kuma muka wayi gari dady bashida lafiya dan haka muma hankulanmu ba'a kwance yake ba.
Sufyan ya kalli alkali yace "ina rokon wannan kotu mai alfarma data bani lokaci domin gabatar da wasu shedu kwarara wanda zasu tabbatar mana cewa faisal fyade yayiwa amira Nagode yamai shari'a.
Alkali yayi rubuce rubucensa sannan yace "kotu ta daga wannan zama sai farkon watan nan dazamu shiga na october. Kotu!!!