Alim dai mamakin sa'ido na yan kauyen yakeyi Bai Saba ganin hakan ba Sam,
Sabo da haka ya dage dole sai ya ganar da tsohon nan gaskiya kar ya kala masa sharri
Alim ya kwallo da karfi Baba tsoho ka fahimceni mana matata ce pls ka gane,tsoho dai ya kara haskesu yace kai ni nan dan zamani ne harda hada dan turancinsa kalleni da kyau noti a small boyi ni big ne zaka mai Dani gara, uwarka ka yiwa ba ni ba shegen yaro,
Tsaki Alim yaja tare da dafe kai Amana tace ka kyaleshi kaima kasan fa ba ganewa zaiyi ba,
Tsoho yace kinyi da uwarki Abinda yasa muke yiwa irinku Wa'azi Ku tuba Ku daina saboda idan Allah ya tashi kamaku sai a hada da mu na gari wanda bamuji ba bamu gani ba wlh baza mu yarda da Ku a cikin garin nan ba,indai na isa sai nasa an koreku daga garin nan muna ji muna gani Ku jawo a kifar da garin ko ayi mana girgizar kasa,to Ku sani billahillazi la Ila ha illahuwa saina nemi me gidan nan wanda ya baku haya ya koreku ya tasheku da gidan nan,mu Malam Salisu dake kasanku mutumin kirki ne.Amana ce ta janye Alim,haka tsoho ya gama surutunsa ya tafi.
Kitchen Amana ta shiga Alim ya bita ciki suka fara girki tare,Alim Bai iya komai na girki ba kawai batawa yakeyi,
Garin yanka Alaiyafu ya yanke a yatsansa sai jini shar....Amana kamar itace ta yanke kwace wukar tayi ta kama yatsan toilet ta kaishi ta wanke masa hannun ta sa masa hydrogen ta manne masa da plaster,
Kallonta kawai yakeyi ji yakeyi kamar ya hadiyeta ya huta yanda take matukar Kula dashi.lips ta cuno masa shi kuwa ya miko nasa ya manta kiss,murmushi sukayi taci gaba da aiki a kitchen yana zaune a gefe yana kallon ta idan ta juyo suka hada Ido sai ta cunno masa lips ta turoshi sosai shi ma ya miko nasa sai muahhhhhh..... zuba masa kunun Aya tayi da ta hada yana tasha tana aikinta
Waist dinta ya rungumo ta baya da hanu daya daya hannun kuma yana Shan kunun ayarsa,
A hankali yake magana ayi sauri a gama girkin nan,mene kake sauri yunwa?hmm kema fa kin sani tun kafin ki bar lagos rabona dake nazo nan kina period da kyar nake manage,kin gama kin hana min abina har kinyi kusan 4 days da gamawa ya karasa kamar zaiyi kuka.duk sai taji tausayinsa domin iyakacinsu romancing yana so haka zai hakura saboda tace tana Jin zafi kuma karyar Amanace kawai wai itama dan aji ta ja masa amma ko ita watarana tana so musamman Idan ta kalli kyakyawar surar Alim dinta me tsananin kyau da haduwa.
Bayan ta gama girki abinci suka ci tayi gyare gyarenta,fitowa tayi ta shiga bedroom dinsu Alim ta gani ya fito a wanka yana shafa Mai ba komai a jikinsa,
Amana dai wani yarrrrr yarrrrr take ji a jininta ,nan take taji tana matukar bukatarsa,sha'awarsa taji wacce bata taba jiba a rayuwarta, tsayawa tayi tana ta kallonsa kamar mayya,tongue dinta ta zaro ta lashi lips dinta sai lumshe Ido takeyi tana ta kallonsa,sai ta fara sosa wuya idan ya juya har dogon wuya takeyi wajen leko kirjinsa etc
Yana kallonta ta mirror amma bai Kula ta ba domin ta dan bashi haushi dazu a kitchen yace yana bukatarta ta shareshi ko kulashi ba tayi ba,
Rigar wankansa ya mayar harda kara daureta ya rufe jikinsa kirjinsa kadai ya bayya,Matsowa tayi tana soshe soshe Him.... uhmmmmm...uhm kallonta yayi tare da lullube jikinsa da towel yace lfy?
Uhmmmmm ba komai,dayan Bed room din ta wuce tayi wanka tare da sako wasu shegun kayan bacci masu Jan hankali tasha kyau tana bulbula kamshi,
Saman bed ta hango shi shima cikin shirin baccinsa ya mike kafafu sai danne danne yakeyi a system,
Jiki a mace tana karairaya hadi da lumshe Ido tana fari,Alim ya kalleta sama da kasa sai da ya girgiza ta gama tafiya da imaninsa,
Sha'awarta ta dawo masa sabuwa fil amma ya daure ya shareta,gyaran murya tayi hade da Zama kusa dashi tana ta binsa da kallo tana ina ina tace um.um..ta sosa kanta taci gaba baza...baza...kayi bacci yanzu ba?
Alim ya kalli yanda take kallonsa idanunta sun canja tsab ya ganota yasan me take so amma ba tare da ya kalleta ba yace kwana zanyi ina aiki yau,
Magana tayi tace to..to..to naga Alama tana ta zaune taki kwanciya sai satar kallonsa takeyi,
Kashe computer yayi Amana na ganin haka tayi Hamdala a ranta,bai kwanta ba sai ya zauna cure a bed din,Hannunta ta mika a hankali ta kama wasa da kafarsa,
Dauriya kawai yakeyi,gajiya Amana tayi matsa jikinsa cikin sigar shagwaba tace am in...in....the...mood kaji kayi wani abu sweet mana,ta kare zancen tana shafa hannunsa,matsawa yayi gefe yace dazu da nace I need u me kika ce min?sai yanzu zaki neman da yake bukatarkice I hope zan iya miki yanzu amma na gaji kin makara
Jiki a sanyaye ta Mike zata bar dakin tare da cewa ahhhh.....ok.....never mind ta fara tafiya ya fisgota ta fado kansa flat ya mata ya fara kissing dinta dama Amana jiran kadan takeyi ba bata lokaci suka gigita Kansu kamar mayunwata,Sosai Amana ke enjoying din abinda Alim ke mata ta bada hadin kai ta dage tayi iya yinta,ta gama baje basirarta a kan Alim,ta mishi abubuwa masu rikita hankali wanda ya Sha mamakinta yanda ta tafiyar dashi,gata gwarzuwa ce akwai juriya da jajircewa na ganin ta bawa Alim abinda yake so ,shima hakan take
Yau su Alim harda kwallar dadi da farin ciki,bai taba Jin makamancinsa ba,Amanansa ta dabance sai da yayi round 3 ya kyaleta hakanma kawai kyaleta yayi dan kar ya shiga hakkinta Bai sani ba domin Amana Idan zaiyi sau 100 baza ta nuna masa alamar ta gaji ba sai ta daure,duk da cewa itama tana da karfin sha'awa kuma uwa uba tana Jin dadin harkar kasancewar mijinta ya hadu ta ko ina,style iri iri sunyi shi,tasha sambatu wajen Alim itama haka,saida suka nutsu ya shiga sa mata jerin Albarka,wanka sukayi tare da tsarkake jikinsu sai nafeela da sukayi da adduoi suka fada Bed hade da manne juna sai bacci.
Sulemanu Harka jiki yaki dadi duk yanda za ayi anyi masa ana ta kashe kudi amma kafunsa sunki doruwa,sai ma kara lalacewa sukayi yanzu kullum sai an fitar dashi an Shanyashi a rana a kofar gidansa,
Yauma yana kwance a tsakar gida sai numfarfashi yakeyi ya tambayi Badriyya ke ina Amana ta ke zaune a garin nan?Badriyya tace Baba nima ban sani ba tana dai zuwa dubaka kuma ta ebi kayan sawa ta tafi,duk kusan ta kwashe kayanta na sawa,
Baba yaga bashi da kudi kudinsa ya kare gashi ba fita yake ba ba lfy,ga ba Amana ba mijinta babu me bashi domin ko sanda Amana na lagos har kudi take tura masa.
Baba ya kwalla kara yace Wannan kwai gantalalliyar yarinya akan wannan shegen yaron ta bar gidana saboda nace baza ta koma ba,
Indai Namiji ne gata gashi na yafe mata taje tabi mijinta akan haka harda barin gidana,to ni dai na yafe mata ta koma dakinta yarinyar kirki ta gari bani da kamarta ga biyayya tafi kowa Jin tausayi na da bin umarnina,matansa da yaransa ya Tara ya fada musu dalilin barin gidansa da Amana tayi,babu wanda ya kulashi sai Umman Amana tace Baka kyauta ba kayi butulci,nan dukka gidan Akayi caaaaa akan Baba,yace to kuzo Ku dakeni Ku huta
Isa yace Baba matar da kake zargi itace Umman Alim wlh ba ita bace Baka ganeta ba,ni naga matar ganin idona,Babar Alim fara ce waccen kuma Baka ce,
Ka bari ayi bincike tukun amma mijin Amana mutumin kirki kalli yanda ya mai damu mutane,
Nan Sulemanu Harka yace to latso min waya ka kira min Amanata,Hamza ya fara kira amma bata shiga har Number Alim duk basa shiga,
Da dare Alim Zaune a saman kujera Amana na kasa magana ya mata honey yau mu dan fita mu zaga gari mana,
To bari mu shirya ko,wanka sukayi fes dasu suka hade cikin shiga me matukar kyau sannan suka kulle wajensu suka fito,da yake akwai wuta ko Ina da haske ba laifi,
Sunzo tsakar gida su shiga Wajen Sa'adatu suka gaisa sai ga Yarta budurwa Iklima ta fito sai kallon Alim takeyi taga baiwar cikar zati
Mum gaba daya ta rasa sukuni sabo da rashin Alim,gashi Abba yaki saurarar zancenta yace karyane dansa yana nan lafiya,
Su Nura ma shareta sukayi kowa ya kama harkar gabansa,matar Nura shanawa sukeyi da mijinta saboda Mum tana cikin damuwa bata kulasu,Matar Nura ke Kula da Aabid sosai.Mum kuwa kullum kuka takeyi harda Jin haushin Abbansu Alim shi ya cuceta ya tura mata da yaro aiki wani state.
Amana na kallon yanda Iklima yar Sa'adatu take kallonsa ta faki idon kowa ta dallawa Iklima harara,radawa Alim tayi tashi mu tafi tare da tamke fuska wai haushi,a hankali yace mu dan zauna ayi hira ko ma Saba dasu,Amana tace pls kaga ni Bana son wani sabo,mu kadai zamu dinga rayuwarmu.
Me za
Muyi a wajensu dama mutuncin makwaftaka yasa muka shiga,
Sa'adatu ce ta fito dauke da lemo da ruwa amma Amana tace sun koshi tafiya zasuyi,Sa'adatu tace da kun zauna munsha hira?Amana tace zamu dawo watarana ai,Alim yace to Mene mu zauna mana Amana cikin Jin haushinsa tace ko second Biyar bazan kara ba tashi mu tafi kawai ai yawo zamuje.muje to ya Mike sukawa matar sallama Amana tasa Alim a gaba kamar danta,suna fita Iklima tace Mama wlh wannan matar tasa masifaffiyace kuma kamar itace mijin yanda take abu ta gama mallake bawan Allah, wa ya sani ko asiri ta masa da ganin Alama,Sa'adatu cikin fada tace ina ruwanki dasu ki iya bakinki,Iklima tace ai naga ta gama mallakeshi wlh har ya bani tausayi.
Alim suna fita Amana tace Allah ya taimaki yarinya watarana ta gwada min hauka kamar yau ta gane shayi ruwane da kanta kamar kwallon kwakwa,Alim yayi murmushi ke ki kwantar da hankalin ki ke kadai ce ba Kari don ta kalleni sai me ni kinga na kalleta ne?to me yasa zaka ce mu zauna?nufina mu dinga zumunci,to bazamuyi dasu ba karma ka jawo na koresu daga gidan nan.
Sorry sarkin zuciya ni dai ki huce kar mu koma gidan ki hanani Harka,da wasa Amana ta dalla masa harara sunan Babane fa Harka,sorry na manta I swear
Dariya Amana tayi tare da rungumeshi tsam haba dai ai kome zaka min bazan hanaka komai ba,ba wannan shirmen ai sai kace yarinya marar tunani,idan ana Jan fada haka ai aure baya lasting duk fadan da zakuyi da mutum matukar baza Ku raba makwanci ba to dole a shirya da wuri bare har ya kai ga saki,kiss ya manna mata tare da shafa wuyanta a rungume da juna suke
Suna tsaye sai ga Baba tsoho yana takawa da kyar ya dawo daga masallaci ya kara biyowa ta wannan lungun me duhu,wannan karan tsohon masifa yakeyi a hanya sosai,Alim yace laaa ga tsohon nan na ranar nan mun ga ta kanmu
Tsoho Ashe yaji me Alim yace yace bakuga ta kanku ba sai Allah ya damkeku da kansa,
Yau ba ta Ku nakeyi ba domin kun Zama Bala'i sai sadaka,
Amana tace Malam me aka maka yau kake fada?yace kedai bari karuwai wlh wasu yarane suka bata min tsoho ya fara basu Labari wai wasu Samari ne a masallaci kullum sai sun dagashi bayan an idar da sallah saboda bashi da karfi da kyar yake tashi ma,
Kawai sai rannan matarsa ta haihu gobe suna shine ya bada Sanarwa a masallaci gobe za a rada suna matarsa ta haihu samarin nan suna jin haka suka saki dariya tare da cewa ah....tsoho Ashe kana da karfi yanzu har matarka ta samu ciki ta haihu ta wlh baza su kara dagashi ba sai dai idan ya kasa tashi ya kwana cikin masallaci tunda har yasan zai iya wata ciki,ai kuwa su Alim suka dinga dariya,Amana tace Baba dai dai sukayi wlh gwara haka,
Tsoho yace ai gwarani ba dan iska bane irinku,karuwai shedanu,Amana tace wlh Tsoho muna da aurenmu fa,yace ban yarda ba ko sama da kasa zata hade bazan yarda ba kuna da auren zaku dinga bin lungun masu shegen duhu ba kunya ba komai,
Da Allah kar Ku kara min takaici wai yanzu ace yaronka Bai jawo ma magana ba wasu a titi na kwararo su dinga sawa zuciyarka na tafasa.
Dariya suka karayi tsoho yace kwayi da wani marasa mutunci.
Alim ne ya zaro kudi masu yawa ya mikawa tsohon Baba ga wannan ka siyi rago ko
tsoho yace wuuu...rufani ka sayani dannan niiiiii na karba kudinku na haramci inma cin hanci ka bani wato dan na dinga rufa muku asiri kuna shekewa to ni Bana karbar cin hanci,bazan rufa muku asiri ba,zan karba na gode kuma amma kar kusa rai zaku zauna lafiya a unguwar nan sai na sa me gidan ya koreku,tsoho ya karbe kudinsa yana godiya,wata mata tazo wucewa Ashe tasan Amana nan suka gaisa sosai,tsohon nan har ya fara tafiya ya dawo yace Delu wato ke kike daure musu gindi ko har gaisawa kukeyi?Delu tace kaji tsoho da sa Ido to har duwaiwai na hada na daure musu karewarta,tsoho yace Bana ja'in ja da matar wani yayi tafiyarsa yana masifa wlh sai ya tonawa su Amana Asirinsu.
Delu tace tsohon nan sai hakuri ta wuce,su Alim suka tafi yawonsu sosai suke Jin dadin yanayin.
Saude ce zaune a wani rubabben dakinta dake kauyensu tana waya tana faman sheka dariya,ba a Jin me suke fada sai dariya r Saude kawai kake ji.
Alim da Amana sun Dade suna zaga garin har 10 na dare sannan suka dawo gida hannunsu rike da ledar da suka siyo gashashiyar kaza da yogourt.
Suna shiga cikin gidan Amana tace ayi rige rigen zuwa Palo,ai kuwa Alim yace 1,2,3 go suka zura da gudu Amma Alim ya Dade da shiga Palo sannan Amana ta karaso ciki tana nishi tare da kukan shagwaba ni... ban yarda ba Allah,dariya sukayi gaba daya suna ta faman haki,ta fara masa rigimar sai ya goyata,haka ya goyata har saida ta fara bacci a bayansa sannan ya samu lfy,
Dole ya tasheta suka ci namansu da wanka sai bacci,
2:30 Alim ya farka da rigima ya fara tashin Amanarsa Babyna Baby,cike da maganar bacci tace naam mene?cikin kulawa tayi magana tana mayen bacci ruwa zaka Sha?yace ae Mikewa tayi zaune zata bar kan bed ta kawo masa ruwa,cike da sha'awa yace honey naki nakeso fa,dukan wasa ta kai masa sukayi murmushi nan suka karashe Daren suna ta faman raya
sunna.
AsmaBaffa
Ina godiya masu sharhi kune nawa.
✳CIRANIN AMANA✳
150-155
Official
By
AsmaBaffa
ZAUREN QUEEN MERMU DA TASKAR FIDDAUSI SODANGI WANNAN PAGE NAKUNE. TNX ALL.
Bayan 3months Mum Alim ta shiga damuwa,zuciyarta dankare da bakin ciki,haka Sulemanu Harka komai sai dai ayi masa baya iya komai ya rame yayi baki ya tashi daga aiki,gashi Bai yiwa yaransa abinda ya kamata ace iyaye sunwa yayansu ba,bai sauke hakkinsu ba,ya gama zubar da mutuncinsa duk da cewar suna masa komai da ya dace amma basu damu dashi ba ko ya mutu ko yayi rai harkokinsu sukeyi domin mazan ma sun koma state din da suke business wasu kuma sun dawo Kano da kasuwanci duk cikin tallafin Alim gashi Hamza Babban yaya da kb sun samo matan aure a city har an musu engage,
Badriya ma maganarta da Huzaifa tana tabbata sai karfi takeyi,
Alim ne yayi shiri da safe da wuri yace zaije banki ya curo musu kudi,cikin shadda dakakkiya yake dinkin fited yasha kyau har bakin titi Amana ta rakashi ya shiga taxi drop ya wuce
Ta dawo ta gama komai na gidan tana Jin zazzabi kadan kadan har ta kwanta tana tunanin rayuwarsu ita da mijinta,
Gaba daya jinta take bata da lafiya kawai hijab dinta tasa ta tafi hospital sabi da ta tsorata this mnth bata ga period ba,kuma Alim yace mata indai unguwa ta kama da lalura to ko baya nan taje kawai ya yarje mata,
Karamin asibiti taje a cikin garin saboda yana da girma garin nasu,ana aunata ciki ya bayyana a jikinta wata daya,magungunan da aka rubu ta mata ta siya ta wuce da result a hannunta tana ta murna,ta matsu Alim ya dawo ta bashi labari,
Kasa hakura tayi tun a hanya ta danna masa kira a waya cike da nishadi shauki na kwasarta tace my Man yaushe zaka dawo? Alim yace nan da 3-4hrs na biya ta wani waje,
Amana ta saki murmushi tare da furta Allah dawo min da kai lfy,murmushi Alim yayi cike da zallar
Kauna ta gaske sannan a hankali yace Ameen sai na zo me zan kawo miki?anything kawai cewar gogar,sallama sukayi ta koma gida tare da bajewa a 3seater.
Alim Bai dawo ba sai 9pm ya kwankwasawa yayi tare da murda handle,Amana ta fito daga kitchen tasha kyau da sauri ya jawota jikinsa yayi hugging dinta yana murmushi sannan ya mika mata ledar hannunsa,
Wani dan kyakyawan saurayine ya fito fit daga bed room din su Amana yana sweetheart kin barni ina t faman jiranki kiyi sauri muyi abinda za muyi kafin dare yayi nisa ina da aikin yi ....kamar gaske saurayin nan ya tsaya cak yana hangame baki yace dama cutata kikeyi kin San kina da aure kika ce nazo,
Da gudu saurayin nan ya nufo Amana tare da kwasheta da wawan mari yace kin cuceni Allah ya isa ban yafe ba nayi tarayya da matar aure.
Ya bude kofa ya fice fit,Yana barin gidan wata dalleliyar mota ta tsaya gabansa ya shige suka bar garin gaba daya.
Alim kamar gunki haka ya tsaya yayi poster sai hawaye da suke ta bulbula kamar famfo daga idonsa,Amana kuwa da ledar da Alim ya mika mata da result na ciki na hospital ta saki a kasa,
Kafin kace me ta sume sharab a wajen,
Alim kuwa innalillahi kawai yake maimaitawa sannan ya shige bedroom ya tattara nasa ya nasa kaf,ya fito ganin Amana har yau a sume sharab a kasa kallo daya ya mata ya tsugunna tare da daukan result din hospital dinta ya duba hawayensa ne suka karu kamar ba Namiji ba ya zauna ya dinga rusa kuka,
Yana why....why.....na bar yan uwana da iyayena duk sabo dake,Mum dina ban San wannan Hali suke ba,sai yanzu Alim ya gane kuskuren biyewa shawarar Amana da yayi sabo da so ya rufe masa Ido,Mum dinsa tana can cikin bakin cikin rashinsa har cuta tayi sabo da son da take masa,ta dauki cikinsa,ta raineshi amma yanzu ya gujeta duk da Mum Nada babban laifi amma uwa uwa ce baza ka biyasu abunda suka maka ba,sune sular zuwanka duniya Harka hadu da wata,
Amma yayi fushi da Mum dinsa ya barta saboda matarsa kuma yasan dole tana cikin wani hali tunda duk tafi kaunar Alim cikin yaranta,
Kuka sosai Alim yakeyi,ashe Amana dai Amanarsa take ci,yana ta shirme akanta yana biye mata,bai taba zatan zata aaikata haka ba,tunani yayi sosai da karfi ya furta no.no...nooooo...baza tayi haka ba,
Amma Sam zuciyarsa ta hanashi tunani bare wani bincike,ji yayi ya tsani Amana gaba daya baya kaunar ya bude Ido ya ganta,sambatu yakeyi sosai idonsa jajir jijiyoyinsa sun tashi rada rada ji yake kamar ya kashe Amana ya huta,
Ya yarda a gaban ko waye zai iya zubar da mutuncinsa kan Amana domin ya faranta mata,
A titi,a lungu,a kwararo,a bainar jama'a duk saboda yayi proving dinta yanda yake sonta,dan yasa taji duk duniya ba kamarta tafi kowa sa'ar miji,har ana ce masa kwarto sabo da ita,
Abinda watsatsun yan mata keyi a boye a titi yayiwa Amana shi tana matarsa amma duk wannan Bai hanata neman maza ba,
Ashe makaryaciyace,ta yaudareshi,mikewa yayi da niyar tafiya
Amana ta ja dogon numfashi ta farfado,zumbur ta Mike tare da rike rigarsa tana kuka wiwi kamar ranta zai fita,da kyar tace pls....ka...sau...rareni...dan Allah wallahii ban sanshi ba,kayi tunani da bincike sharri aka mana kasan muna da makiya,hannu biyu Alim yasa yaci kwalar Amana tare da girgizata da karfi ya makata jikin bango ya shaketa sosai tana ta kakari,... sannan yace ohhh makiya ko......da karfi yace makiya Mum ce makiya ko?Amana ta kasa magana sai hawaye nan Alim ya jefar ta kasa ta zube rigip,juyawa yayi tare da cewa kar ki sake ki nemeni,kar naga kafarki a gidanmu bana son ganinki na tsaneki,
Inda kika San zamu hadu kar kibi ta layin coz idan na ganki cikin karaji ya karasa I will kill u.
Result din ciki kuma ki haihu ayi DNA test idan har nawa ne zan karba.ya bude kofa baram ya kara makota ya bar gidan,
Direct airport Alim ya wuce ya bi flight sai Lagos inda akafi wayo.
Amana kuka takeyi tana salati sallah tayi tayi addua sosai hawaye kuwa yaki tsayawa a idon Amana,bata San wannan tsinanne ne ya hada mata wannan sharri ba.
Tattara nata ya nata tayi itama cikin dare tana zabga kuka ta bar gidan ko su Sa'adatu bata yiwa sallama ba,tana fita ta fara tafiya a kasa wani Almajirin kusa da gidansu ya biyota yana dan Allah Anty ki bani sadaka dare yayi banci komai ba,wani takaici ne ya kara kama Amana ta kara harzuka ta hayayyakowa Almajiri da masifa cikin kuka kai dalla karka dameni ka kyaleni naji da matsalata,da wannan matsalar dana shiga gwara na kwana 3 banci komai ba,dallah matsa ta furta tare da tallafewa Almajiri keyarsa ta jefa masa Dari Biyar,
Tana yin gaba ta hadu da karamar kanwarsu Zaliha ta siyo sugar a kanti na gobe da safe,Zaliha tace Amana kece da dare yau me ya sameki Baba yana ta nemanki har ya rasu ma naga su ya Haladu suna ta kuka da Umma,ai Amana kafa tasa tayi short da Zaliha,
Ta kara gaba,Zaliha ta gama kukanta ta bi bayan Amana suka shiga gida,tun daga tsakar gida taji kukan su Haladu da gudu ta fada dakin Baba,Baba ne a kwance yana ta suma yana farfadowa ya suma yafi sau saba'in gashi yace Baza a kaishi asibiti ba,an tafi dashi yace duk wanda ya kaishi asibiti Bai yafe masa ba,haka aka dawo dashi,
Amana kan Baba tayi tana kuka ta cakumeshi tana Baba dan Allah karka tafi ka barmu muna sonka Baba,
Farfadowa Baba yayi tare da damke hannun Amana ya fara magana da kyar Amana...ta....da yan uwanki Ku yafe min ban muku tarbiyar kirki ba na sabawa Allah da yawa kin min Wa'azi naki ji ga yanda duniya tayi min juyin wainar Asabe,ki rokar min matana iyayenku su yafe min,gwaggo uwar gidan Baba tana sheka kuka tace mun yafe maka Allah Baka lfy,
Sauran matan ma suka ce sun yafe suma ya yafe musu domin irin zagin da tsinewa Sulemanu mijinsu da suka dingayi kullum a maimakon suyi masa addua,
Tari Baba yayi yace Amanata ki koma dakin mijinki na yafe miki ki yafe min kin Sha wahalar rayuwa na turaki Cirani saboda kina min Wa'azi kaico na,
Badriyya tace Baba mun yafe maka dan Allah kar tafi ka barmu muna sonka,muma munyi maka laifi sosai bamuyi ma biyayya ba,Sakina cikin kuka tace Baba wa zaimin kayan daki idan ka tafi wayyo gashi na samu miji gatana ya kare bango ya fadi,kayan daki Baba gashi ko secondary ban gama ba,Sadiya wacce ke Aure a Gaya lg tace Baba gashi su Hamza sun fara kudi Amana ta auri me kudi karka tafi baka dangwali dadi ba Baba,
Kb ne yace baku da hankali Ku ta abin duniya kukeyi ko,Baba ne ya fara tari ba ji ba gani sannan ya lafa,Amana ya damko yace ga Amana nan na daura mata nauyinku gaba daya saboda nayi Imani duk abinda zan muku Amana zatayi muku shi domin tafi kowa hankali,kyauta,da son zumunci,Amana ke ce wakiliyata ki rike min Iyalina ki maye gurbina,ga yayyenki Maza da sauran Ku hadu kuyi zumunci Ku tallafi juna,ku Manyan maza abinda Allah ya hore muku Ku tallafi yan uwanku Ku hade kanku babu yan Ubanci duk da nasan dama bakwa nuna yan Ubanci Ku kara akan Nada,
Ku Zama masu hakuri,juriya,hankali da nutsuwa duk fitinar da kukeyi da kuyi kokari Ku daina saboda nasan kun daina Amma a kara jajircewa duniya ba matabbata bace,hakuri da yafiya shine komai Ku rike wannan komai akayi muku banda daukan fansa Ku Zama masu yafiya da kawaici,a tsare mutunci, amma kar Ku bari a rainaku ko ubanye Ku taka masa birki.
Baba ya kara Suma ya farfado ya Dora da nasan Amana da saurin zuciya kike dan Allah ki dinga salalawa ga maza nan zasu tayaki Ku Kula da kanku,ga takaddun dukiyata nan nayi rubutu na fitarwa da kowa gadonsa yana nan rubuce a cikin littafin nan,Amana nafi yarda da ke me adalci ce dauki ki rike a hannunki,Amana dai sai kuka kawai Baba sai nauyi yake Dora mata Bai San ma Alim ya gujeta ba a lokacin da take bukatarsa.
Baba yace Ku kuma matana wacce taga zatayi aure to tayi aurenta amma ta barwa yayana a cikin yan uwansu ban yarda a rabamin kan yayana ba su zauna tare su so junansu zumincinsu yayi karfi,
Kuci gaba da min addua ko Allah zai karbi tubana ya yafe min,na barku da alheri.
Nan Baba tari ya turnukeshi yana ta murkususu Bai kara minti biyu ba yace Amana ki tallafi zuri'ata tayi kyau,ta gyara,abinda banyi ba kiyi musu kiyi iya kokarinki ki bar sauran ga Allah,
Gaba dayanku Maza da mata Manyan Ku tallafawa Amanata Ku Kula da kan....k...luf Baba ya cika Allah ya karbi rayuwarsa cikin wannan dare,
Sunyi kuka sunyi Addua mutane sun girgiza da wannan mutuwa,
A daren aka hada gawa akayi komai,washe gari Aka fito da gawa akayi mata sallah aka dauka akayi hanyar Makabarta a hankali akaji kamar makara na motsi, a tsaya a tsaya a kace Makarafa na motsi dubban jama'a suka fara guduwa sun firgita,
Liman da wasu tsirarine suka karasa kan makara tare da yayan Sulemanu suka duba Gawa sai akaga Baba ne yake motsi yana magana Badai asibiti zaku kaini ba a mai Dani gida ko na tsine muku,yana makyarkyata yace ina Amanata iceko tana Kula da Iyalina,ina su Hamza kai ...kuna tallafa mata kuwa,matana fa sunyi aure?karfa su auri kowa ina son matana ina kishinsu, idan sukayi aure to nima za a bani Hurulein
Ina littafin da dukiyata take ciki ne Ku raba kuwa?na bawa Haladu buhun masarata Biyar,Amana a bata sabon injin murzar taliya dana siyo rannan hhh
Ai su Hamza murna da gudu suka suri Baba suka koma gida ana Bai mutu ba Bai mutu ba,gawa taki rami gawa taki rami Allah wlh sai Baba.
Suna dawowa karfe Biyun rana Baba ya kara margayawa wannan mutuwar gaske ce domin Har doctor suka dauko ya auna ya tabbatar musu ya rasu, haka suka kara sabon kuka da komai aka kai gawar Sulemu Harka aka binne.
Amana kuka kamar ranta zai fita sauran kuwa har sun fara Hakura,Amma Amana itakam ba iya kukan mutuwa take ba,kukan rabuwa da masoyinta takeyi,ga nauyin da Baba ya daura mata,ga kuma ko secondary bata gama ba,bare ace tayi karatu tunda ba miji ta nemi aiki ta cikawa Baba Burinsa,
Ga cikin dake jikinta gashi Alim baima yarda nasa bane,ga bakin cikin sharrin da aka mata ga mutuwar uba duk ita kadai,shi yasa gaba daya ta kusa zarewa,yan uwa duk sun hadu da aluma masu zaman makoki ana ta yiwa Amana nasiha an zata kukan mutuce kawai,mutane sai ace Allah sarki Amana duk tafi shiga damuwa ai sun shaku da Babanta duk yafi sonta dole tayi kuka mutuwar tafi taba ta,
Tun Amana na kuka ita kadai a daki har ta fito waje ta kalli bishiyar da Baba ke Zama sanda tana Budurwa tazo ta wuce tana bouncing tace ai sai Baba Allah bar mana tsoho,yanda Baba ke ji da ita komai Amanansa,
Alim dinta ta tuno ta tabbatar da suna tare da tuni ya lallasheta ya sata nishadi da tuni ya zame mata gurbin uba,amma yanzu Babu me lallashinta,ya tarairayeta ya bata farin ciki ya tallafi danginta da iyayenta,shine gatanta,iyaye kuma duk lalacewarsu katanga ne,nan take Amana ta kurma ihu a kofar gidan ga maza masu zaman makoki su Hamza suna ciki,Amana ta fadi a kasa ta fara burbuwa tare da cewa wayyo Allah Bango ya fadi katanga ta rushe,gatana ya kare,gatana wayyo gatana,duniya kin juyamin Baya,kin juya min up side down,wayyo uwata wayyo Ubana...mijina...mijina shikenan nima.
Su Hamzane cikin hawaye suka riketa tare da danne kirjinta saitin zuciyarta domin wani numfashi yakeyi zuciyarta zata buga,
Da kyar aka samu numfashinta ya dawo normal,magana ta fara Ya Hamza a haka rami nima a binneni,nima dan girman Allah ku harbeni,zuciyarta ta nuna tace ku fasa min nan da Bullet,
Haladu dauko wuka a samu wani ya yankani dan Allah masifar danake ciki tafi karfina,
Kb da Isa ta kamo tace dan Allah ku farke min ciki mene Amfanina,kuka ta kara fashewa dashi,haka suka shigar da ita gida Amana ta fita daga hayyacinta,
Zazzabi tayi sosai sai hakuri ake bata,yau Kwana hudu da rasuwar Baba,Amana ta dan gana ta daina Kukan rashin Baba sai na Kukan rashin Alim,amma duk da haka idan taga abokan Baba da wani abu daya shafi Baba sai kuka mutuwar ta dawo mata sabuwa.
Kamar yau Huzaifa Badriyya ta fada masa rasuwar babansu dole ya taso Abbansa da kanwarsa Saddiqa suka taho ta'aziya,bayan sunyiwa su Hamza sai suka jera Baban su Huzaifa a gaba,Huzaifa da kanwarsa Saddiqa suna baya haka suka shiga har cikin gida domin Yiwa mata ta'aziyya,Amana tana ganinsu haka mutuwar Baba ta dawo mata sabuwa ta dora hannu aka tare da kwallawa da karfi wayyo wasu suna da Uba mu bamu dashi wayyo Ubanmu...ga wasu yan gata da Ubansu nan ma da kyar aka lallasheta,sai kuma tashin Alim ya fado shima,ganin Huzaifa suna yanayi da Alim sai ta fara Hawaye,
Tana ta kallon su Huzaifa kamar bata sansu ba,
Huzaifa bai sai me ya faru ba,yace Madam sai hakuri na sanarwa mutuminki yace min yaji kin yayanki ya fada masa dashi Akayi ta'aziyya zuwansa ukku ma,
Cak Amana ta tsaya da Kukan wato har ta'aziyya yazo ko nemanta baiyi ba da gaske ya hakura da ita,nan hawaye masu zafi suka zubo mata,
Ta kara wajen Haladu tace wai Alim yazo ta'aziyya?
Haladu yace dashi aka raka Baba har makabarta a mutuwarsa ta karshe, dashi akayi sadakar Uku,cewa yayi kar mu fada miki bai son ganin kukanki,
Amana a ranta tasan dan kar ya ganta ne ya tsaneta,
Amma kuma taji wani irin dadi da farin ciki tare da da ran Allah sa ya dawo gareta watarana,nan kuma tayi dariya hadi da hawaye,Amana bamu sanki da kuka ba ko ya kukace readers?
Huzaifa ne ya fito zasu tafi Su Abbansu na Mota da kanwarsa shi kuma Huzaifa sun tsaya a soro suna ta hira da Badriyya cike da so yana lallashin Badriyya,Amana ta hangosu a cikin mutane a fili ta furta ni bani da masoyi babu me lallashina sai kuka tare da tuna yanda Alim ke ji da ita.Ummanta ne suka fara mata fada sosai,kamar akanki aka fara mutuwa Allah ya hana Yiwa mamaci kuka haka,idan ma ganinki wani abu to ki sani Baba ba dawowa zaiyi ba kukanki ba gata bane a wajensa,masifa kike kara masa,daki Amana ta fada taita Kukanta.
Kwanan Baba Bakwai da rasuwa yau Alim yasa Abbansa,da Nura tare da dan autansu suka je sukayiwa yan gidan su Amana ta'aziyya,
Lokacin Amana ta kule a daki tana ta zazzabi da kuka,sai jin labari tayi Alim ne ya hana a tasota,wai zai dawo.
Ga abinci sun kawo musu Mota guda da kudi masu yawa sannan suka tafi,
Haladu ya ce Amana kai mijinki na sonki kinga yanda yake barka kuka kamar mace ke kyace babansa ne ya mutu,kb yace ai wannan Kukan Uba bai cancanci ayi masa ba sai dai Uwa,Isa yace kutmar Uba guy nan mace ne,kb yace a macen ma ta gaske,Hamza yace mamakin danayi mutum kai ba ubanka ba amma kafi yayan cikinsa kuka,
Haladu yace kai Burauba naga kuka wajen yaron nan kasan yaran masu kudi yayan Hutu ne inda kaga mace haka suke basu saba da gwagwamarya ba,wai guy nan daga cewa Amana ta suma tana kuka ta rame tayi duhu kawai ya barke da kuka shima yo ko uwatace ai bazanyi kuka ba bare mata,akan wata mace ka kama kuka,
Hamza yayi dariya yace ai kabewa ne,Isa yace ai mugun tumatir ne wlh.ammafa yana son Amana da ka ambaci sunanta za kaga ya kafe ka da ido ya shiga wani hali sai kwalla kuma kwal kwal,
Kb yace ai da ace ban san Amana ba da cewa zanyi asiri tayiwa guy nan,Hamza yace gaskiya Uwarsa ta haifawa Amana da Allah ya tsare ta haifawa Wata da,
Suna tsaye suka ga Amana yif tayi kasa ta sume saboda tsananin tunanin Alim,surarta sukayi Sai asibiti.
Kwananta uku aka sallameta tare da garga din Likita cewar a kiyaye damuwa zata mata illa kwanan nan,
Suna dawowa gida aka rufarwa Amana da nasiha cikin kuka tana share ido tace ku nutsu na baku labarin mece damuwata,
Kaf Amana ta kwashe ta fada musu tun farkon Haduwarta da Alim da irin zaman auren da sukeyi da soyayyarsu,da Mum Alim abinda take mata,da kuma gidan da ta zauna tare da Alim a garin,da sharrin da aka mata,sai rasuwar Baba,mata har Amana suka taya kuka,sun san Baza ta aikata haka ba,Hamzane yayi magana Lallai ko waye aka masa haka dole ya yarda kar kuga laifin Alim,
Da gani har yanzu yana sonki sai yanzu muka gane dalilin da yake barka kuka,
Zamu tayaki da addua Allah ya bayyana gaskiya,Haladu yace Insha'allah zai dawo da kansa wajenki ki raini cikinki Allah raba lfy,Umma tace shi yasa kike ta kuka haka,gwaggo tace Allah ya shige gaba,sauran matan sukace Ameen,Amana sai hawayene ke sintiri a fuskarta,ana ta mata Nasiha,Badriyya tace wlh ko Saude ko Mum ne zasu kala miki wannan sharri na sani Allah zai saka miki.
Alim kuwa kwana yakeyi ba barci saboda tunanin Amanarsa tsananin sonta,da abinda kuma ya gani wai kwarto fasiki Amana taci Amanarsa,shima yayi kuka yayi bakin ciki yana wani Hali ya rasa inda zaisa kansa,shike nan cikin zazzabi,baya cin abinci,duk ya rame sosai,kamar yau yana kwance a gidansa domin tunda ya dawo gida bai taba ko kwana a gidansu wajen Mum ba,yauma kwance yake zaman bed zazzabi ya rufeshi a hankali ya furta I missed u me yasa zaki zalunceni,bayan ina sonki zaki ha'inceni?why Amana.haka yayi ta sambatu,
Mum tayi farin cikin ganin Alim dinta gashi ya dawo shi kadai ba tare da tsinanniya Amana ba. cewar Mum
Abba da su Nura sun tambayi Alim ina matarsa sai yace ya dan barta a gidansu ta huta Sabo da rasuwar Babansu zai dinga zuwa can yana da gida a garin nasu a ciki ya sata.
Aabid kuwa yana gidan Nura sunyiwa Mum wayo sun daukeshi.
Amana ta gargadi Badriyya kar ta fadawa Huzaifa komai tsakaninta da mijinta.
Kwana biyu laulayi Amana ta fara sosai zazzabi,kwadayi ga yawan sha'awa da takeji kuma sha'awa r Alim kadai take ji,s ai ciye ciye kullum na kwadayi yan uwanta Maza da mata su suke kula da ita sosai,kafin tace tana son abu sunyi mata,sai abinda take so suke kawo mata,kowa lallabata yakeyi dan hankalinta ya kwanta,ta rame sosai sai fari data kara kwal kwal da ita,
Yanzu bata da matsalar komai sai ta rashin Alim,sha'awarsa,sai nauyin da Abba ya dora mata har yau bata sauke ko daya ba,
Sati Uku da rasuwar Baba sai kuma wata sabuwa Umman Amanace ta bijiro da wata tsiya rigima sabuwa fil ta baro.
AsmaBaffa
Readers a dinga Afwa idan anga mistake,ba lallai Allah ya hada komai abinda kake so ba,idan kunga abinda bai muku ba kuyi hakuri story a haka yazo,kuma ku dinga nutsuwa a ko wanne acting da akayi a wannan novel ko wanne page akwai sakon dayake isarwa a dinga gane abinda ake rubutawa ana masa kyakyawar fahimta ta gaske.na gode kwarai
✳CIRANIN AMANA✳
155-160
Official
By
AsmaBaffa
ANTY SUMEE INA GAISUWA WANNAN PAGE NAKINE.MARAICIN SO FANS INA GODIYA KWARAI.
Umman Amana ta tsiro da wata tsiya Inda kwata kwata take ta jin haushin Amana saboda taga yanzu bata da kudi,bata Auren me kudi komai sai dai su Hamza suyi mata,yan kudin da take dasu duk ta karar dasu a gidan tana yo musu cefane idan mazan basa gida gashi ta biya sauran yara kudin makaranta,gashi mutane da yawa sunzo wai suna bin Sulemanu Harka kudi kafin ya mutu ya ranta,sabo da haka kudin bashin da ake bin Mamaci dubu dari tara akayi lissafi,
Gashi sauran mazan gaba daya sana'arsu batayi karfi ba ga kula da gida,
Gashi wanda sukayi aure ma ko wacce rurowa sukeyi a gidan ake tallafa musu,ga yara masu tasowa cincirundo,shawara suka hadu iya manyan gidan babu kudin da za a biya Bashin mamaci kuma ya zama dole,Amanace ta bada takaddun gidan da suka zauna da Alim aka siyar dashi aka biya bashi,
Sauran canji akayi bukatun gida,bayan kwana biyar wani yazo yace shima yana bin bashin dubu dari biyu Amana ta bada sarkar Gold dinta har guda Hudu da Alim ya siya mata nan ma aka siyar aka biya,bayan sati biyu wasu suka kara zuwa wannan yace dubu hamsin,wani ashirin wani talatin,haka mutane suka dinga zuwa su Hamza suka nemo sukayi karo karo aka gama biyan bashin Baba kaf,kowa na gidan a gida tattalin arzikinsa yayi kasa basu da wani karfi,gwara ma su Hamza ba laifi,dole suka jinginar da maganar aurensu.
Kullum Umman Amana haushin Amana takeji wai ta kwashe kudinta ta biya bashin Baba ita kadai arzikinta duk ya kare ita bata bata ko kwandala ba,kuma Amana yanzu da su Hamza take shawara har meeting sukeyi,
Amana ga halin da take ciki ga kuma Umma kullum cikin hantararta da zaginta takeyi tana jifanta da muggan kalamai,idan readers baku manta ba Umman Amana ko koko safe a da bata bawa Amana sai dai ta siya,ganin Amana Allah ya buda mata ta samu kudi tana auren me kudi shine Umma ta sakko take kula da Amana,yanzu Amana Babu ba mutunci,dama ita Umma me bata shine nata,idan kana bata to a cikin yayanta kiri kiri zata dinga nuna banbanci.
Yauma gaba daya family na mirgayi Sulemanu sun Hallara a babban palo ana shawara,banda iyaye a meeting din,
Amana zaune take a tsakiyar Palo ta darararrashe ta sangale kafafu zaman masu ciki sosai ta rame idan kunga Amana za ku sha mamaki ta rame sosai,kana ganinta sai ka tausaya mata Sabo da Amana kullum sai tayi Kukan rashin Alim tayi addua tayi ba dare ba rana,
Da addua aka bude taro Hamza yace da Amana sayyada a cika mana da addua kinfi kowa Ilmi,ai kuwa akayi addua sannan aka kawo littafin wasiyyar Baba daya bari na gadon kowa gwara a bawa kowa hakkinsa dama Umman Amanace tace wlh sai an dakko an raba gado domin duk anyi tunanin Sulemanu ya tara dukiya ne a boye shi yasa har yayi littafi guda ya raba gardamar gado,
Page din farko na littafin aka bude ga abinda aka gani da Babban baki ya sa wani abokinsa ya rubuta masa domin Harka baiyi boko ba Badriyya ce me karantawa.ga abinda ke rubuce.
AMANATA INA KAUNARKI,Amana na jin an karanta haka ta fashe da Kukan tuna Baba,NI SULEMANU HARKA BABAN AMANA NA BAWA A CIKIN DUKIYATA DA ALLAH YA MALLAKA MIN NA BAWA AMANA SANIYATA WACCE NAKE KIWATAWA A GIDAN ABOKINA ME GARI,SANIYAR BATA HAIHUWA ITA KADAI CE ABINDA NAFI SO A CIKIN DUKIYATA,SABO DA HAKA SANIYA TA AMANACE KAR TA SIYAR DA ITA TA YANKA TA IDAN ALLAH YA BATA HAIHUWA TA DAGARGAJI DADINTA.dariya kowa yayi harda Amana me kuka,
Page 2. HAMZA NA BAKA TINKIYATA DA RAGO KA YANKAWA AMARYARKA RANAR BABBAR SALLAH ASHA DABGE,hhhhhh nan ma aka dau shewa da tafi tare da cewa Allah yaji kan Baba.
Page 3. KABIRU KB DAMIN GERO SHIDDA KA SIYAR KA KASHE KUDIN,
ISA KUMA WAYATA TA CELLULA DA AMANA TA SAI MIN,
HALADU KUWA BUHUM MASARA BIYAR,
BADRIYYA TOLO TOLO GUDA UKU,
SAKINA BARGONSA NA BACCI DA RADIO DA YAKE JIN LABARAI,DUK SUNA GIDAN ABOKINA ME GARI IDAN BAI BAKU BA KU SHIGAR DA KARA.
MATAN AURE KUWA KO WACCE A BATA RIGARSA DA WANDONSA DAYA DAYA,
SAURAN YARAN GIDAN KUWA KAI KUNCI UWAKU GABA DAYA GA SU AMANA NAN DUK ZASU KULA DAKU KAR KUCE BAN BAKU KOMAI BA CIKIN KAYAN SAWATA KUMA A RABA MUKU DAYA DAYA KOMA ME ZAKUYI DASU KUYI.
second to the last page kuwa na matansa ne,
KO WACCE CIKIN MATANA NA BATA KYAUTAR IYA DAKIN DA TAKE CIKI TA ZAUNA HAR IYA RAYUWARTA,SAURAN GIDAN KUMA KAR WANDA YA SIYAR GABA DAYA NA YAYA NANE,WACCE TAGA ZATAYI AURE TO BA BATUN SIYAR DA DAKI DOLE SAI DAI CIKIN YAYAN WATA KO WANI YA SIYA
LAST PAGE KUWA FATAN ALKHAIRI DA ADDUA YA ZAZZAGAWA IYALINSA,
Gaba dayansu sai da sukayi hawaye na tunowa da Baba,Umman Amana kuwa wani uban tsaki taja tare da cewa aikin banza akan wannan ya bata lokacin to wlh ni yola state zan koma cikin city wajen yan uwana su rikeni mahaifina,duk kun hanani ci gaba a garin nan.
Dan haka wanda yaga yana da kudin siyen dakina ya siya ya bani ko na kira wani a waje bare ya siya,
Amana hawaye da takaici ya isheta,tace Umma zan siya,Umma saida tayiwa Amana kallon banza sannan taja tsaki tace naji dumus,Kb Amana ta kira gefe tace kb ku samu a siyi dakin nan banda kudi hanuna kun san komai dai,kb yace akwai ragowar kudin gidan ki a hannuna ina ga zai siyi gidan,
Amana ta dawo cike da Ladabi tace Umma nawa kudin dakin? Umma tace sannu azagwai uwar Iya, wa ya sani ko da gaskene abinda kika aikata nasan ubanki kika gada shi kwarto ke kuma fa
?ai dole ayi gadon tsiya,wannan mijin naki yaron kirki Amana amma sai da kika nuna hali ya sako ki gaki ga gidan nan ai ki zauna,
Muna zaman lfy yaro na mana kyauta kika watsa kanki ya sakoki ga ciki dan Allah baki ji kunya ba?
To ko kin sayi dakina dan ubanki dole ki bini mu tafi yola na dinga dora miki talla,mene amfaninki wai ku masu Uba ko?
Amana dai bala'in da take ciki kadai ya isheta ta saba da hali Ummansu tunda yanzu bata da kudi,
Shi yasa Amana kamar ba ita ba duk tayi laushi tubus ta gama karaya da lamarin duniya,cike da ladabi tace to Umma amma Baba yace in ba aure ba kar mu rabu da yan Uwa, da karfi Umma tace iyyeeeeeee to wlh sai kin bini,sana'a za muyi mene amfaninki,
Nan Umma tayi kudin daki Amana ta siya sannan Umma tace dauko kaya mu tafi,kowa dake gidan yaji ba Dadi,nan Mutuwar Baba ta dawo musu sabuwa kowa kuka,
Musamman Badriyya da suka shaku da Amana ga bikin Badriyya da Huzaifa ya kusa,domin Huzaifa ma har tallafi yake kawo musu idan yazo sai Badriyya tace suna tare da Alim a lagos ita kuma Amana ta boye kanta,Sakina da Badriyya rana daya za ayi bikinsu saboda mazajensu masu hali ne sunce sun dauki nauyin komai na biki.
Amana bata so bin Uwarta ba amma gudun bijirewa iyaye dan kar ta maimaita yanda ta bijirewa Baba ta bar gidan da ita da Alim duk da cewa iyayen sune masu laifin amma duk da haka saida masifa ta afka musu shi yasa taji tsoron bijirewa Ummanta
Duk yan gidan ne suka taushi Amana suna ta kwantar mata da hankali,Badriyya da Haladu harda kuka yanda Amana ta fita daga hayyacinta gaba daya,
Haka tana ji tana gani tare da sharbar kuka ta hada kayanta tas tabi Ummanta,amma abin mamaki Umma ta bar kannen Amana wajen su gwaggo wai su rikesu Amana tallafa mata za tayi da talla.
Tun a tasha,Amana kuka kawai take shike nan an kara nesantata da Alim,kuka kamar ta kashe kanta,Umma tace kiyi kukan jini ma ke kika jawa kanki,
A mota ma kuka takeyi ana ta kallonsu,to Amana ko wa zai taimaka miki oho.yanzu ba kudi basu Hamza ba Alim baki da kowa sai Allah.
Yanda Amana take wannan halin haka Alim ya shiga sanadiyyar rashin Amana kusa dashi ya yarda itace rayuwarsa,shima ya rame sosai da kyar yake fita ma,yan uwansa da iyayensa sun rasa gane kansa,yayin da Mum ta Nemo masa wata yar kawarta Zainab wai Abba yayi masa aure ko zai samu nutsuwa,Abba kuwa ganin halin da Alim ke ciki sai ya yarda,
Har zance Mum tace sai yaje wlh,Alim yana zuwa yaga Zainab wata tambadaddiya marar tarbiyya nan take yaci mutuncinta tun daga sama har kasa yayi tafiyarsa,wannan dalilin yasa aka dage biki sai nan da 6mnths,
Saude kuwa ana can Ana Wainar siyarwa tare da ci gaba da kulle kullen tsiya.
Ranar da Amana tabi Umma suka tafi ranar da yamma Alim yazo gidan shi da Huzaifa,dalili kuwa ranar kawai yaji ba abinda yake so ya gani a duniya irin Amana,
Waya yayiwa Huzaifa wai yana so ya gaisar da iyayen Amana mata yayi musu alherin saboda yanzu basu da miji,ai kuwa Umma bata da rabo Alim Mota guda yasa aka kawo gidan ta kayan abinci,sai kallon yan gidan yakeyi,sai ya faki ido ya share Hawaye,gaba daya suma sunga ya rame,inda
Su Hamza suka birgeni ba wanda yayiwa Alim maganar Amana ko kadan,sai Baza ido yakeyi yaga Inda Amanansa zata bullo yayi tozali da ita ko bai mata magana ba zaiji sanyi kuma zai rage radadin sonta da yake daminsa,
Amma duk da haka yana cike da bakin cikin Amana taci Amanarsa ta zalinceshi gashi yana sonta Amma dole ya hakura da ita,maybe ma ta manta dashi tana ta rayuwarta cikin Jin dadi,a hankali ya furta Allah sarki ni..a fili .
To Alim dai yana ta baza idanu Ba Amana ba labarinta,tunowa yayi da Badriyya mutuniyarsa me handling case dinsa,
Komawa yayi wajensu ita da Huzaifa yace sorry frnd zanyi magana da kanwata for some few minutes,
Sun kebe waje daya shi da Badriyya Alim yace Sis wannan yarinyar fa? Badriyya tace wa kenan a hankali yace Aman...kasa karasawa yayi saboda yanda zuciyarsa ta kare,takaici yake son taso masa haka ya daure,
Badriyya ta lura da hakan sai tace oh...Amana ai sun bar gidan na....kafin ta karasa Alim yace Badai aure tayi kan aure na ba?Badriyya tayi dariya kamar bata San komai ba tace haba aure ba aure ba kawai Ummanta ce ta takura mata sai sun tafi Yola garinsu tayi mata talla.
Talla?Alim ya kwala da karfi yace to wlh bazai yiwu ba Sam,nan ya fara fada ni nake da iko da abata,
Badriyya batace komai ba sai tace ai na tausaya mata in ka ganta baza ka ganeta ba ta rame sosai kullum cikin kuka take tace wai sharri akayi mata aka rabaku gashi tana da ciki har ya fara girma,kasan me Baka ga bakar wahalar da take Sha da cikin nan ba,yanzu Amana ko maganar kirki ta daina sai da dalili,
Fiya fiya fiya Alim ya kama fyalla sauri kamar zai tashi sama,mota ya bude tare da fadawa ciki ya dinga bakin ciki da share kwalla na tausayin Amana har ya gaji yace ko mene ke kika jawo,ke kika jefa mu cikin masifa...nan take zazzabi ya rufeshi da ciwon kai mai tsanani cikin motar ya kudundune saida Huzaifa ya kaishi asibiti sannan suka koma gidansu Kano kenan.
Amana sun sauka lfy,wani gida suka shiga da Alama nan ne gidan su Umma,gidan Bulo ne ko siminti babu,daki biyu ne rak,ba mace a gidan iya Baban Umma ne kawai wato kakan Amana kenan,shi kadai yake rayuwa saboda tsabar masifar tsohon,masifaffe ne number daya,sabo da haka mata basa Zama da shi,haka Umma ta masa bayanin Amana da ita,zasuyi Sana'a,
Malam Nuhu yace to gwara da kukace zakuyi Sana'a ni dai kwandalata bazan kashe muku ba,gida dai gashi nan Ku zauna a waccen dakin baya Ga wannan ba zan yi muku abun sisi ba,
Amana dai tunda ta gaisheshi kala batace ba,tana rakube a bango kamar marainiya,tana tunanin Umma Babanta ta gado, Umma ce ta dan sai musu abinci har Malam Nuhu sukaci dan kadan dashi baifi mutum daya ba,
Amana kuwa bata cin shinkafa da miya amai takeyi da tashin zuciya amma Umma tace iskancine wlh baza ta sai mata komai ba,ga yunwa tana ji gashi bata da ko sisi,haka taci abincin tana ci ta fara Amai sosai Ai kuwa Malam Nuhu ya fara sauke Bala'i wannan iskanci ne wannan?yanzu haka ma cikin shege ne kuka gudo min nan za a cuceni, Umman Amana tace Haba Baffa da kai fa aka daura mata aure.
Amana ta ebu ruwa zata kuskure baki ta wanke hannu datt
ijon yace karki bata min gida kimin asarar ruwa ubanki ne ya sai min?kai gaskiya ubanku ya Sha wahala daku to wlh baza a zo a hanani walawa ba a gidana,
Amana kwalla ta share tare da tsugunawa tace kayi hakuri,kallonta yayi tsab yace iyye ke baiwar Allah yaushe kika daina harkar niganci da jagaliyar ne?Allah da iko yaushe haka ta faru?amma wanda ya aureki kamata yayi a bashi kyautar sarkin hakuri,yo ni da nine yausheeeeee tabbb,badan halin ki ba ebi ruwan kadan amma ki shiga bayi ki wanke hannu da baki ba a tsakar gidana ba bar ganin gidan ba siminti ba a lalata min gida,hakan Amana tayi ba tare da tacewa Malam kala ba,saboda tasan ma idan tayi magana to bakar magana zatayi domin ta kai wuya saboda halin da take ciki ga duniya ta bata darasi shi yasa bata cewa komai,kun San shi karatun duniya dole sai ka jishi,kuma ba iya kunne ne ke ji ba duk gangar jiki ce ke karba sosai.Amana sarkin zuciya ji take kamar tayi ta dukan Malam har ya suma,dan darajar Umma ta kyaleshi amma da sai ta nuna masa ita wace
Washe gari Umman Amana ta siyo gero ta fara kunun siyarwa ba na markade ba na daka su surfa ita da Amana su daka ayi Amana ta dauki katon botikin paint a kanta ta fita can wata majalisa,bata so gudun fushin Umma ta hakura, Amana kar A manta fa,dama can ta Saba da sana'a talla ne kawai bata taba yi ba amma duk aikin wahala tayishi kuma gata da zafin nama ba bata lokaci tunda tasan dole tayi ko dan abinda zasu sa a bakin salati bare ma ta San Umma ba kyaleta za tayi ba kuma bata son yi mata musu heeeee su Amana anji jiki fa da dane na tabbata Umma baza ta iya juya Amana ba,sai gashi yau Amana har mamakin wai ita Amana akewa abinda aka ga dama,da ace da dane har Baban Umma Malam Nuhu zata ci Ubansa. duniya kenan.
Amana kam yau satinsu Biyu da zuwa Yola,suna zuwa har gidajen sauran yan Uwan su Umma suna zumunci,
Amana tana zaune da waya a hannunta zata kira Hamza Umma ta kwace wayar kawo siyarta zanyi na kara jari,Amana shuru tayi ta zare sim dinta ta mikawa Umma dalleliyar wayarta sannan ta fashe da kuka sabo da wayar taka rage zafi da ita wajen kallon hotunansu tare da Alim sai taji sanyi a ranta ta samu nishadi to yau Umma ta kwace wayar ma amma duk da haka ba iya sim ta cire ba komai na wayar ta mayar kan Memory ta zare Memorynta ta hade ta daure a Leda tasa a bag dinta,
A banza Umma ta siyar da wayar Amana duk tsadarta,yayi dai dai da Alim wanda ya kasa hakura da Amana,ya shiga matsanancin Hali kullum sai ya Sha maganin bacci yake iya bacci kawai ya yanke shawarar kiran Amana ko muryarta zaiji ya rage zafi,canja new Sim yayi tare da dan nawa Amana kira amma ya makara wayar bata shiga,Badriyya ya kira itama ta gwada bata zuwa,yace Badriyya pls bani Address din inda suke a Adamawa,Badriyya tace wlh duk gidan basu sani ba amma dai gwaggo tasan sunan local government da suke a can da unguwar amma bata San wanne gida bane,tsaki Alim yaja yace kinga Illar rashin Zumunci wannan ba zumunci bane yanzu idan wani abu ya sameta kuma baza Ku sani ba، ya kamata ace ko kishiyoyi a dinga zumunci ana sanin asalin inda kowanne ke zaune Sabo da irin wannan. yanzu wannan me yake nufi kenan kuna Uba daya baku san inda yar uwarku take ba ku bakwa shiga harkar kowa gashi abin har yan Uwa na jini ma wannan ba dai dai bane,
Haka Alim ya dage ya dinga bala'in da masifa ya dinga saukewa Badriyya kwando kwando yana ta nuna mata illar rashin zumunci wasu kuma zumuncinsu ma sai suna Uwa daya Uba daya da iya su suke zumunci.Sai da ya gama yana huci kana yace hadani da gwaggo ta fada min Unguwar da lg din,
Bayan an fadawa Alim komai sai kuma ya fara jin dadi da nishadi kamar wanda akace masa ga Amana a gabansa,
Amana ce suke ta daka geron kunu,sanye take cikin kayan da ta saba dasu wata falkekiyar riga tshirt saboda cikinta ya dan fito sai jean trouser fari tayi kyau ba laifi Sabo da yanzu yawan addua yasa ta dan rage damuwa duk da cewar kullum sai tayi Kukan rashin Alim,amma yanzu ta danyi kiba kadan Sabo da cikin ya sata yar kiba da kyau yanzu,
Yanzu ma tana dakan geron ta tuno Alim sai hawaye tana yi Hawaye na bin kuncin ta,Malam Nuhu dake gefe yana jin radio ya mike yau ga kwarzababbiyar yarinya yar iska ke zan koreki fa daga gidana kullum cikin kunci da kuka ko uwarki aka yimiki iyeeee nace Ubanki aka miki? Ke kenan a gidana kullum cikin shigar yan iska kike kina nuna tsaraici,shi yasa ma ga badayanki zubin karuwa shaddar kasuwa ce dake wannan anya jikata tace ba musaya akayi ba,Umma dake wajen Murhu haushin Babanta taji yana zagin yarta sai taji tausayin Amana kuma,mikewa tayi tace ajiye dakan muje ciki muyi magana ba musu Amana ta shige daki tsoho ya dauki Salati yace Hauleeeee Hauleeeee yau ni Ubanki zaki nunawa kin haihu niiiiiiiiii....sai ya saki kuka.
Umma daki ta samu Amana kwance bisa tabarma tana sharbar Kukan takaici tayi rashin Uba da miji yanzu da Ubansu ya na raye duk Lalacewarsa ai gidansa zata zauna,a da suna ganin Baba bai musu rana ba bashi da amfani a garesu sai gashi tun ba a je ko ina ba mutuwarsa tasa sun ga rashin Uba babban wani abune a rayuwa,
Da da Mahaifa sai Allah Umma ce ke lallashin Amana tace kiyi hakuri kinji tashi ki siyo abunda kike so yau kici kinji,Amana bata ce komai ba,Umma ta rasa abinda zata cewa Amana ta sata nishadi Umma gani take yau kudi zata kashewa Amana sai tace Amanan Baba ko za kici mitimis?saida Amana tayi murmushi,Umma taci gaba zan kashe miki kudi ko mene fadi kinji,shuru Amana tayi tare da goge hawaye,Umma tace Aya fa? Dan tamatsitsi?dabino?awara?gurasa?ko dan silif zaki siyo flour kiyi? Amana tace ni kaza nake sha'awa dan Allah Umma ki sai min a ribar da muka samu,Hangame baki Umma tayi tace yo ina kudin kaza yake ke Amana wannan ai zalincine da mugunta har Kaza fa?
So kike ki karya jari canja wani kinji yar Baba,Amana kuma a duniya kazar take son ci,haka tasan Umma ba siya mata zata yi ba,sai ta hakura tace Umma to ki siya min kasar calabar da Aya.
Umma tace ko kefa zauna da kaina zan siyo miki ma,A mana insha'allah sai mijinki Alim ya dawo da kafarsa ya nemeki har ki ja masa aji da yanga ko?kyalkyal Amana ta kyalkyale da dariyar Jin dadi tare da furta ai Sai Umma,Amana sai nishadi Umma bata taba birgeta ba irin yau,tunda Umma ta ambaci Alim ta gamawa Amana komai a duniya.
Umma kuwa mamakin Yarta takeyi yanda take matukar son Alim haka,
Umma tace tab Amana ni kuwa me Alim yake miki ne kike sonsa haka?ko kanki bakya so haka,Amana cike da fara'ar da ta Dade rabonta da yin irin ta ta fara magana Umma baza ki gane ba komai Alim yi min yake Umma komai da kika sani,Umma tace komai? Amana tace komai Umma bazai fadu ba ina fada miki Umma Mijina karshene a komai da kika sani wasu suka rab....sai kuka wiwi Amana ta fara,sannan tana murmushi sosai ga hawaye tace Umma Allah uban giji ya daidaita ni da mijina,Umma Alim mutum ne,Mijina yayi Umma nayi dace,hawaye ya kwararo mata taci gaba da sambatu Umma Alim abin so ne dan ina Jin kunya ne da kullum sai na dinga baki labarinsa abubuwan da yake min.
Umma harda kwalla tace kullum zan dinga tayaki da addua yata.
Fita tayi da kanta ta siyowa Amana Aya da calabar harda Rabin kaza gashashiya sai da Umma ta siyo mata,Amana bata zata ba Allah sarki Uwa me tausayin yayanta.
Nan Amana ta zauna a tabarma ta dinga Garza,
Umma na kallon ta da tausayi.
Kusa da gidan da Amana suke makwaftansu akwai wani Deeni kwaro tantirin dan iskan gari ne,tunda yaga Amana ta fita tallan kunu yaji a duniya Bai taba sha'awar mace ba irin Amana,a ransa yace ko hannun Amana ya shafa sosai to ko ranar ma dan ta shi ya mutu,
Sabo da haka duk unguwar ake ce masa na me Kunu ko hannunta ka shafa sai ya karasa musu da ko yau namutu.
An fara Zafi sosai a Adamawa nan su Amana suka dawo suna kwana a tsakar gida,Amana tana can karshen gidan kan tabarma ta shige cikin net dinta sabo da sauro
Umman Amana ma tana tsakar gidan farkon gidan cikin Net,haka Malam kuwa yana can cikin daki,
Cikin tsakar dare Deeni kwaro ya taka katangar gidan ya dane tare da lekowa a hankali,sai yaga mata biyu saboda duhu gashi baya so Amana ta farka tayi ihu ya kasa shafa jikinta,haka ya shiga gidan ta saman Katanga sadab sadab ya shige cikin Net din Umman Amana ya zata Amana ce, kawai ya ya kara shigewa jikin Umma sosai ya fara shafa jikinta,Umma cikin bacci taji ana shafata ta manta Sulemanu Harka ya rasu cikin magagin bacci tace uhhmmm......Sulemanu....Sulemanu a'a....a'a mene haka Sulemanu,kaji jarabar taka ko,Da gudu Deeni kwaro ya fito fit kamar walkiyya Umma ta dawo hayyacinta ta jawo rigarsa baya ai kuwa Deeni kwaro ya cire rigar cikin zafin Nama ya barwa Umma a hannunta ya tsallake ta Katanga ya fece,
Umma ta fara kuka da kurruwa Sulemanu ya jawo mana yayiwa matan wasu wlh dole ayiwa nasa wani tsohon zan samu na aura kafin wani ya min Illa ohhh yau na gane da saurana Ashe saurayi haka na bi na ai sai aure,
Tashin Amana tayi tace tashi dan Ubanki mushe kina can wani zaimin fyade,bazan iya zaman nan ba wani satin zamu koma gidan Babanki gwara gidan Mirgayi wlh ina gama takaba zan samu sakarkarin dattijo na aura domin ubanku ya jawo mana sai mun tsare mutuncinmu.
Amana sabo da murna harda tsalle da kyar ta iya bacci sabo da murna zata koma wajen yan uwanta,murnar Amana dayace tasan dole bikin Huzaifa da Badriyya Alim zai zo ko don Huzaifa to dole ta ganshi ko taji sanyi.
Malam Nuhu kuwa dadi yaji zasu bar masa gidansa wani satin.
Alim duk abin duniya ya masa Zafi shirye shiryen bikin Huzaifa sukeyi kuma shine kan gaba shi ya tsaida dashi zuwa Adamawa neman Amana.
Washe gari Amana ta tashi fes cikin tsananin murna,karin Jin dadi n Amana Umma tace ta daina talla kudin da suke dashi ya ishesu har su koma gidan Baba Mirgayi.
Yau Amana ta fita siyo kayan miya a hanya garin tsallaka kwalabati kafarta ta goce ta fada katon Kwalabati marar ruwa cikinta ya bugu sosai nan take cikin ya juya sai jini ya yanke mata sosai yake ambaliyar fita daga kasanta,Amana ihu takeyi tana wayyo Allah dana dana zai mutu na shiga uku dana wayyoooo dana kar ka tafi me kama da ubansa,kai nake sa rai zan haifa na dinga ganinka kamar babanka 'yata ko dana me kama da Alim dina,
Gudan jinin Alim,zarota mutane sukayi da kyar ta kara dafe cikin taci gaba wayyo dan Halak dan Alim,wlh Alim ne yayi cikinka mijina Alim a gidan aurenmu,Ka tallafamin kaine shedata da zan wanke kaina wajen babanka,
Deeni kwaro ne ya taho da gudun tsiya masoyiyarsa ta samu matsala yace mahaukata kun tsaya my love tana gabanku shinfide cikin wani Hali kun kasa kaita asibiti sai kallonta kukeyi kuna kallon daga inda jinin ke fitowa kuna Jin dadi kuna kissima surart a zuciyoyinku,to gurin yafi karfinku,daga wanda yayi mata cikin sai nine kadai zan San wajen nan,
Amana dai ta fara fita daga hayyacinta sai nishi takeyi tana Dan Alim...shedata...dan Alim
Habawa ai tuni Deeni kwaro ya Sureta tare da tare napep sai asibiti.
AsmaBaffa
Tnx alot readers.
CIRANIN AMANA
160-165
Official
By
AsmaBaffa
Dukkan yan AsmaBaffa fans club godiya gareku da jinjina.love u all
Da sauri Deeni ya shiga da Amana cikin wani private hospital nan danan akayi emergency da ita likitoci suka rufa a kanta,komawa Deeni yayi tare da sanarwa Umman Amana da Malam Nuhu,a sukwane suka rufta asibitin,Umma sai kuka takeyi tana ohhh na jawo miki,na jawo miki masifa Amana Ashe kaddarace ta kawoni na daukoki nan Adamawa,
Deeni ne ya biya kudin asibiti da komai da aka bukata domin Deeni kwaro akwai neman kudi baya talauci..
Duk iya kokarin da likitoci sukayi dan ganin Cikin Bai fita ba amma abu yaci tura domin tun kafin ma a kara so asibiti ciki ya zube,dan haka suka mata wankin ciki,sai allurai da magunguna na Karin jini da sauran abubuwa,Deeni Kwaro kuwa maltina carton 3 ya kai da madara peak ta ruwa kwali biyu,sai kuma kullum da kalar naman da yake kaiwa asibiti wajen Amana.
Amana kuwa bata magana sai yanda akace da ita,da ance yi zata yi bari zata bari,kai ko gabas kace kalla zatayi,arewa,kudu,
Sai hawayen da basa tsaya a idonta,tasan yanzu ita da Alim sai a darul salam dama da cikin ta dogara idan ta haifa dole zaiyi ko kama da Alim sai ya San da gaske shine Ubansa to gashi ya zube.
Umma kuwa ko a asibitin gasa Amana takeyi sosai tana gyara ta cike da tausayi,
Satinsu guda aka sallamesu,Deeni kam yayi Namijin kokari,sai yanzu ya gane lallai son Amana yakeyi,kuma yaji labarin tana da aure,hakan yasa ya tattara soyayyarsa da kwadayinsa ya kara gaba dan karma ya dinga ganin Amana yana Jin wani abu ya koma daga gida sai wajen aiki,sanadin hakan Deeni kwaro ya daina halayen banza ya samu shiriya Sanadiyyar Amana me Kunu,Amana ma batasan yana yi ba,sunje dai har gidan su Deeni sunyi Godiya sosai,sai lokacin Maman Deeni ta basu labarin Deeni da komai har shiryuwarsa sanadin Amana,ai nan take ya birge Amana ta dinga yi masa fatan alkhairi,Amana ta bashi Address dinsu na gidan Baba.Deeni dai ya karba kawai amma bazai je ba tunda Amana Nada aure, kuma ga kunyar shiga net din Umman Amana da yaya satin Amana biyu cif da yin Bari yanzu kam Umma gyarata tayi sosai a saboda Shan madarar rakumi da sauran Abubuwa yasa Amana ta maida jikinta tayi sumul sumul tayi kyau na ban mamaki sabo da kayan da Umma ke bata tana ci da Sha na gyara,
Itama Amana saboda kullum cikin sa rai take zata hadu da Alim dinta yasa take yarda da gyaran sosai,kai ba kace Amana ta taba aure a duniya ba yanda ta kara komawa kuma gashi kullum dai sai tayi kukan rashin Alim amma a hakan ba laifi ramarta kadan ce ta rashin mijin ta.
Saura kwana Uku su koma gidan Baba Sulemanu Umma ta samu Amana tace na dauki Number Hamza dake littafi jiya na ari wayar Malam na kira shi mun gaisa sosai duk sunce a gaisheki,bikin Sakina da Badriyya Saura kwana 5 biyar a fara kinga zamuje a dai dai,Badriyya tace na fada miki ta kai miki dinkunanki cikin Kano za a yo miki,wai ya cikinki na basu Labari ya zube da abinda ya faru,sunyi jaje sosai,
Murmushi Amana tayi tace Umma bari naje gidan su Nusaiba ayi min dilka da halawa,Malam Nuhu shi ya bawa Amana kudin,Amana kuwa gaba daya kwana Ukun nan a gidan gyaran jiki take yini,ko ina ta gifta kamshi take bari me dadin gaske,skin dinta tayi smooth sai sheki da kyalli takeyi,duk wannan Alim takewa tanaji wai ko zai ganta ya ganta bata lalace ba ya ganta har yanzu fa za a je da ita,yaga bata ci baya ba,kuma duk sabo da tsaro bata San ya ta Allah zata kasance ba ko Alim zai yi tunani ya daina zarginta ya maida ta wajensa kunga kenan a shirye take,dama kuma kun San Amana bata son raini akwai son har kar wanka da gyara hade da tsabta.
Umma tace kinga gobe zamu tafi ko zakiyo lallen bikin?Amana tace a'a Umma salon ya goge ma da wuri kenan ai sai naje can zanje har cikin Kano city ayi min na kece raini,
Duk sabo da Alim Amana ake wannan cakarewa.
Ta wani bangaren Amana tana Jin haushin Alim sosai yanda ya manta da ita duk zaman da sukayi,ya kasa tunani akan abinda ya gani,ya zargeta,har ya yarda zata iya cin Amanarsa,
Uhmmmmm Amana ta furta a fili tace Namiji kenan me manta alkhairi,ka shekara kana aikin me kyau rana daya ta baci ba mutunci...wai ni Alim zai yarda Ina bin maza,wai Alim ya gujeni ya manta Dani,lallai a duniya anything is possible shuru tayi tana ta tunani,
Maybe idan Alim ya ganta ma ko kallonta bazai yi ba ya manta da rayuwarta,wani Hawayene ya zubo mata masu Zafi,ganin Umma na kallonta yasa tayi sauri ta fada daki ta kwanta tana ta shesheka har bacci ya kwasheta.
Alim kam bangarensa sai duai domin yafi Amana shiga kunci yaje Har Adamawa ya gama bulayi baiga Amana ba ya dawo ya dage da addua sosai na tabbata da Alim Bai rungumi addua ba shima da tuni ya haukace ya zare.amma a haka idan ka ganshi sai ka dauka bashi da matsala haka Addua take da yawan karatun Qurani yan uwa mu dage da Addua karatun Qurani shine magani.Alim gaba daya sun rankaya sun taho Kano bikin Huzaifa aboki kuma dan uwa.
Baban su Huzaifa part guda ya warewa Amare da kawayensu haka angwaye da abokai nasu daban duk cikin gidansa sabo da Amare Sakina da Badriyya ba a cikin Kano suke ba su kuma angwaye a cikin birni suke saboda dinner kala uku da angwaye suka shirya yasa Abba yace Amare da kawayensu su taho gidansa angwaye ma haka har mijin Sakina sabo da shima sanadin zuwa zance suke haduwa da Huzaifa har zumunci ya kullu tsakaninsu tare suke shirye shiryen komai,Alim kuma shi ya shirya musu party har kala biyu,Abban mijin Sakina ma ya shirya musu daya.don haka duk shagalin biki gidan su Huzaifa za ayi shi,daurin aure ne kawai za aje gidan Amare a dauro,su kuma iyaye mata suna can zasu Kula da jamaarsu ta gari.
Alim sabo da zaman mutuncin da sukayi da Amana da kuma sonta da yakeyi yasa kaf mazan da matan gidan da yara yayi musu dunkuna na alfarma manyan mazan kala Uku uku yaran kala biyu biyu,har iyaye har Umman Amana ya bayar da nata a Dinka a ajiye mata,Amana kuwa ya Dinka mata har kala Goma da takalma da jakankuna da mayafai tsakaninsa da Badriyya sukayi sirri yace tace wai Huzaifa ne ya Dinka mata itama kar ta fada shine,Badriyya tace to bakina kanin kafata,a halin yanzu Huzaifa yasan Alim da Amana basa tare amma duk ya tambayi dalili ba wanda ya fada masa har Badriyya kawai sai ya kyaleta.
Kayan abincin biki kaf Alim ne ya saukewa su Hamza shi da kudin kayan dakin Amare,amma Sam Angwaye sukace kar a kawo Amare da cokali sunyi komai nasu.
Alim ya karbi kudin ya siyawa Hamza da Kabiru kb fili kato guda biyi a Na'ibawa Kano,sun Hamza harda kukan dadi za a koma City,
Yacewa su Haladu ma za a basu nasu suyi aure shi kuma Huzaifa yace zaiyi tallafin Gina gidajen nasu,Ishaq Saurayin Sakina yace shi kuma zai zuba musu furniture,wannan murna kawai sukeyi suna cewa duk A sanadin Amana suka hadu da wannan alkhairi,Ciranin Amana ciranin alkhairi,ta yo musu hanyar arziki gaba daya gidan,domin ta hanyar su Alim kadai Alkhairi ke fado musu,
Allah sarki Amana ana nan ana Jin dadi ta sanadinta ita kuma tana can ma ba ita ke Jin dadin ba haka ikon Allah yake.
Saura kwana biyu a fara biki misalin karfe biyar Amana da Umma suka kwado Sallama cikin gidan Baba Sulemanu,
Kaf gidan suna nan ana ta shirye shirye,nan kowa ya tashi da ihu ana rige rigen rungume Amana,Mazan kuma suka tafa tas tas da Amana suna ta kashewa ana dariya,da karfi Amana tace surprise no going back sai ihu yeeeeeee,Amana ta rike kugu tare da juyawa ta furta look at me ? Ya kuka ce heeeeeee wlh a basu wuta,Amana tace ai da girma ya fadi gwara na kwana da yunwa,nan suka hargitse da murna yara da manya Amana ta dawo gaba daya,kowa sai cewa yake I missed u Sis,yaran gida suka hada baki we missed u Anty Amana,murmushi Amana tayi tana daukansu daya bayan daya tana ajiyewa,
Nan fa aka fara labarin bayan rabuwa daga nan suka bawa Amana labarin komai na yadda suka shirya biki,suka bata labarin yadda Angwaye da iyayensu suka taimakesu sosai da kawo agaji,a karshe suka fara bata labarin kaf alkhairan da Alim ke musu,suna fada mata Amana kuma bata San sanda Ruwan Hawaye ke bulbula a idonta ba,
Yana yin wannan taimakon a danginta amma Bai taba tambayarta ba lallai badan ita yakeyi ba don taimakon Allah yakeyi,ba komai hakan ma an gode masa cewar Amana.
Lallashinta akayi sosai harda su Gwaggo,Umma kuwa tuni ta sa kayanta a dakinta ta yi sallah ta huta ta fito wajen kishiyoyinta sukayi hira sannan ta basu hakurin abinda tayi,sannan tayi musu godiyar Kula da yaranta da sukayi,
Gwaggo tace ba komai ai daki har yau nakine tunda yakice ta siya,mukan munji dadinmu arziki sai bunkasa yakeyi ta hanyar mijin Amana nan suka bawa Umma ma labarin,umman Amana ta saki baki tare da cewa ohhh....rashin rabo ya sa na tabi ina ta Shan wahala,iyyyeeeee kuce sai cin jar miya da zaki,Inna tace ah mu sai Sam barka Allah ya kai gaban Annabi,wannan yaro Allah masa Albarka,Hajiyayye kuwa daya matar ta shanye hannu tare da bugar cinya tace ai dadi ya barki baki ga yanda muka canja ba harda dunkuna naki yana wajena kala Uku Alim Bai manta dake ba harda ke,
Umma ta rike haba tace oh kinjiiii na gudu na bar ladana,to ai ta faru ta kare yanzu mun dawo kenan,gwaggo tace af wa yagaya miki barni gabas take gane min hanya yar uwa cewar Hajiyayye.
Amana kuwa Badriyya ta jawo akwati guda na kayan Alim da ya dinkawa Amana,Badriyya kuma ta cika alkawari tace Huzaifa ne yayi mata Amana tayi mamaki tayi godiya sosai.
Tace dan Allah ki fada masa idan kunyi waya to kawai Badriyya tace,
Badriyya a cikin wayoyinta biyu ta bawa Amana daya tasa sim dinta da memory wayace me kyau,sosai yanzu gidan Sulemanu suka kara nutsuwa suke zumunci,suka samu zaman lafiya ba a ware kowa.
Dama sai ba wani wasu zasu gyaru,ranar da wani ke kukan babu wani shi kuma ranar yake samun nasa kudin.
Sai yaba kyan da Amana tayi akeyi,kowa kallonta yakeyi har yan uwanta mamaki sukeyi,Amana ta kara gogewa ta Zama mace sosai,
Wannan bacin ran da ta shiga yasa ta Zama miskila,bata magana irin da,ba fada ba masifa,amma duk da haka me Hali baya fasawa watarana sai an dan gwadashi,
Alim kam rashin Amana da halin da yake ciki yasa ya tashi daga miskili, shuru shuru, mararar magana, ya dawo kasurgumin masifaffe number daya,abu kadan zaka masa ya zage yaci mutuncinta,ko maganar arzikice sai ta koma fada a wajensa,kullum cikin hade rai da bakin ciki yake,
Ko Aabid yanzu tsoronsa yakeyi da yayi abu zai ci Ubansa,Duk yan gidansu basa ma ganin fara'arsa,bare Mum da yake gani ita ce ta jawo komai.
Mum kuwa bata zo Kano biki ba sabo da bata son dangin miji,tace ranar yini zata zo a flight ta koma da yamma.
Ana gobe Amare zasu dawo Kano a fara biki angwaye tuni ma sun fara zuwa domin wasu duk daga kasar waje suka sauka,sai na wasu state duk sunzo,Alim yana cikinsu sun cika a Palo yana kwance a 3seater baya magana duk hirar da sukeyi,bacci kuwa ya daukeshi Bai Dade da bacci ba ya fara mafarkin Amana,Yana ta dariya a mafarki yana washsh....Amana zaki kasheni,sai yayi dariya yace my wife I love u,do u know what? Can yayi shuru sai sukaji yace I missed u,
Mika ya karayi ya ci gaba da mafarkinsa yana ta furta I love u.......I missed u......sai hawaye zirrrr zirrrr ta idonsa suna ta gangarowa yana I missed u kuka na kara yawa,sai yi yake ta yi,yayan Huzaifa Ahmad ne ya danawa Alim duka tashi banza na mamajo,zumbur Alim ya tashi yana taba fuska alamar Bai San ma yayi mafarkin ba,sai da ya nutsu ya tuno mafarkin Amana ya kara yi dama kullum aikinsa kenan,da masifa yace mene haka zaka tashe ni,Ahmad yace to dan iska kaje can wajen Amana ka sauke gajiyarka da kwadayinka zaka zo nan kana mana kukan banza da wofi,mayen mata kawai manniru,kwana dayan ma baza ka hakura ba,me yasa Baka taho da ita ba kasan Baka iya Zama saida ita,Alim ya cika tam amma ganin mutane sai ya share zance sai tsaki da yaja kawai yana turo bakin shagwaba kamar mace,Ahmad yace Allah....sannu Ayu....mu zaka kawowa iskancin shagwabarka nan to bada mu ba kaje can gaban Amanan ka mata, Huzaifa yace pls Babban yaya a kyaleshi haka.
Gobe dai za a fara party daya dan haka Amare da kawaye yan makaranta hadaddu Sabo da Badriyya duk kawayenta yan cikin birni ne bata kula na kauye,Sakina kuwa nata duk yan makarantar boarding schl dinsu ne,sai da suka zabo gogaggun yan wanka da masu kyau hadaddu su suka gayyata dinner saboda kar a lalata musu party,tuni Ishaq ya turo abokansa aka ebi Amare da kawayensu da wasu manyan ma da zasu dinna,Hamza ma yana da Mota yanzu zai tafi da kb,Isa da Haladu, Alim ne yace dole sai sunje dinner har dinkin dinner ya musu.
To fa Badriyya da kawayenta da sauran yan Uwa yan mata suna cikin kano gidan su ango Huzaifa,suna part dinsu maman Su Huzaifa rakanas ta dauko musu me lalle da kwalliya,dama Amare sun kashewa jikinsu kudi sunyi gyara sosai,Amana ta rasa me zata siyawa Amare gudun mawa kawai ta je gidan Me gari aka bata Saniyarta ta gado ta sa aka girba saniya da wuka,aka gyarata ta karbi motar Hamza aka zuba nama a buhun huna,ta figi motar Hamza sai cikin birnin kano,wani waje da akeyin kwangilar hada take away takai tace ayi dambun nama lafiyye a zuba a abin take away unique color na alfarma,
Zoben Gold na Alim da ya taba bata ta cire ta ba dashi jingina hhhh jinginar zobe huuu Amana aka bata kudin da niyar idan ta samu kudi zata basu su bata zobenta zoben Alim ne baza ta iya siyarwa ba,baza ta iya rabuwa dashi ba,haka ta karbe kudi ta biya masu dambun nama,computer Laptop dinta ta Nemo ta siyar da ita nan ta kara figar kyakyawar motar Hamza ta tafi Saloon da lalle cikin city,
Sai dare aka gama mata,a daren sabo da rashin tsoron Amana ta koma garinsu Wudil,
Amana fa ta fara daukan haske shining kawai takeyi,ga lalle ga gashi yasha gyara,washe gari Badriyya sai waya take radowa Amana tayi sauri tazo a fara kwalliya da ita,Amana kuwa kwalliya ta cancada kai kace yaune party, Hamzane yace kiyi amfani da matata Amana kije da ita kawai ni zamu yi Amfani da ta friend dina tafi tawa girma sosai kinga muna da yawa kuma zan kai su little Zaliha ma.
Tnx Bro cewar Amana.
Akwatinta guda tasa a bayan Mota,t a cokala takalmi me shegen tsini cikin kayan da akace na Huzaifa ne a cikinsu tasa wata arniyar atamfa baka da green,dinkin riga da skert yayi mugun da Meta fam,da kyar take mitsi a ciki,ga takalmi da gyale siriri na daukan magana malam,ta sha kyau kamar a sace ta kamar wata yar shugaban kasa,
Dama ga tafiyar Amana tun asalin ta takama da gadara ce,
Sai zuba kamshi takeyi gashin ta glass a fuskarta brown yayi mugun mata kyau gashi sake a gadon baya.
Wajen masu take away ta nufa tuni an gama mata komai nata na take away yayi kyau shi kanshi plastic da marfinsa da aka zuba dambun naman a ciki abin kallo ne,Bare ledar da aka sa plastic din a ciki wai wai,buhunan take away ta zuba a Mota,sannan ta sa kati a wayarta,sai canjin kudi sababbi dal dal yan dari dari da ta canja rapa biyu,ta zuba a pose din dake hannunta
Direct gidan su Huzaifa ta nufa da motarta,
Yan mata da samari sai sintiri sukeyi a gidan,wasu tsakanin mata da mazan ma har sun saba da juna sai shagali akeyi tare,musamman aka dauki dj aka sa a tsakar gida zai dinga kida kwana da yini har a gama biki,Alim duk wacce ta shige sai ya kalleta ko Amana ce ,amma Amana shuru,ko yaushe yana tsakar gida ko zai ga tazo amma shuru,Shine ya kutsa wajen Badriyya wai lallai sai ta kira Amana tayi sauri tazo ayi mata kwalliya,Badriyya shine fa take ta faman kiran Amana,
A waya.
Dama in baku manta ba Amana tasan gidan su Huzaifa,Alim yana zaune a farar kujera a tsakar gida gindin bishiya ga dj na tashi wasu na rawa wasu na hira,wasu matam gulmar Alim sukeyi ga wani me kyau ga haduwa kamar bature,wasu suce dan india ne,musamman kawayen su Asiya da kannen su Huzaifa yan iyayin tsiya yan kwalliya da daukan wanka,har fada sukeyi wai ina marar mutunci matar yaya Alim ne,gwarzuwa me tuko Mota from lagos to kano,sun ga Alim ba fara"a yanzu shi yasa basa tambayarsa Amana,wasu yan matan kuwa cewa suke mutum baya kula kowa sai ya dinga fitowa yana wayon kallon yan mata,
Wasu sukace munafukin banza ba fara'a baya kallon ko wacce da mutunci kamar yaga kashi to uban waye ya sa ya fito waje.
Amana ce ta danna uban Horn a kofar gidan,me gadi ya wangale kofa,ta shararo motar cikin gidan da Alim tayi tozali.
Sorry masu karatu bakuwa nayi yau shi yasa ban gama typing da wuri ba,n asan kun jirani,gashi ku karba na wullo muku.........
AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳
165-170
Official
By
AsmaBaffa
INA GAISHE KU MAKARANTA CIRANIN AMANA.
Da Alim tayi tozali ya harde a kujera ya tsirawa gate ido,tuni gaban Amana yayi mummunan faduwa,da kyar ta iya parking din motar sannan tasa hannu a saitin kirjinta ta dafe tana maida numfashi ga mugun sabon Son Alim da ya taso mata,tunani ta shiga na abinda ya faru a baya, Hawaye ke neman kwace mata a hankali ta maida kukanta tare da furta ah...Oh God ....bazanyi kuka ba...karki yi kuka Amana ke me dauriyace,amma duk da haka saida hawaye kadan ya fito tasa yatsa tare da dauke hawayen,sai da ta daidaita kanta sannan ta bude kofa tare da zuro kafarta daya waje,bata ma son ta kalli bangaren da Alim yake bare ya mata wani wulakancin tunda yace duk hanyar da zata hadasu kar ta sake ta bi ta wajen,sannan yace mata ya tsaneta,amma kuma dole sai ta wuce ta gaban su Alim sannan ta shiga cikin gidan part din Amare,
Alim kuwa kalle kalle yakeyi yanda Amana zata bullo bai kawo itace a Mota ba domin bata da Mota amma sai kallon motar yakeyi yana tuna inda ya san motar,
Alim a ransa yace wannan kamar motar Hamza,gashi wata kyakyawar kafar mace ya hango kamar ta yar India,takalmin kawai ya gani ya gane takalmin da yasiyo ne a London ya kaiwa Badriyya ta bawa Amana,wannan kenan Amana ce tazo da motar Hamza tunda dama yasan Amana ta iya driving,yes itace Alhmdllh cewar Alim.
Amana kuwa kasa fitowa tayi saboda da gudun kar tayi kuka,amma haka tayi shahada ta fito gaba daya da kyar saboda yanda dinkin ya tamke mata ko ina cip cip,tuwon mazaunan nan gasu sunyi dam sosai,
Ko mayafi bata yafa ba yana hannunta saboda taga cikin gidane kuma tayi ne Sabo da Alim yaga fa ba ta tashi takeyi ba wai irin ta manta dashi ma wanka take dauka shiga takeyi yanda taga dama,bayan kwalliyar duk dan shi akayi,shi kuwa Alim yaga duk kayan da ya siya matane a matsayin na Huzaifa,sai farin ciki ya lullubeshi,ga wani kyau na ban mamaki da Amana ta karo,da gogewa tare da zama hamshakiyar wata yar budurwa,
Ka rantse bata taba aure ba,
Nan take kishi ya tasowa Alim za a kalli Amana ga maza,to wai ma ina cikin dake jikinta tambayar Alim,ko ta zubar dashi lallai ma yarinyar nan zanyi maganinta,
Yana ta magana a zuci ji yake kamar yaje da gudu ya rungumeta,yama rasa inda zaisa kansa,Amana kuwa juyawa tayi tana fito da buhun hunan take away,da akwatinta,mayafinta na rike a hannunta tana ta tunanin Alim,ji take kamar taje itama ta rungumeshi yanda taga ya kara kyau da haduwa yar ramace kadan jikinsa ita ma sai kayi masa farin sani za kace ya dan ragu kadan,Amana a ranta tace uhmm dan gayu wannan uban daukan wanka da yayi haka kamar zaije dinner,
Ya wani zo ya zauna cikin mata sai kallonsa akeyi,awai dan a kalleshi an fada masa kowa ce zata soshi dan yana da kudi da kyau ya wani zo sai tallar kansa yakeyi,salon wai ace ana sonsa tsaki taja a hankali,kaji fa Amana to ina ruwanki.
Buhu buyu ta dauka tana tafiya das das kowa mata da Maza sai kallonta akeyi,Alim kuwa dafe kai yayi yana hadiyar yawu,yace lallai yarinyarnan kalli yanda take wani bawa mutane show kalli Maza sai kallonta akeyi lallai zan gyara mata zama wannan ai tangal tangal ne da aure kaji Alim to ina ruwanka da ita kaida ka tsaneta,
Garemu matan Aure,zawarawa,yan mata,karki bari mijin ki ya dinga dawowa yana ganinki bakya daukan wanka kamar zaki party,bazawara da budurwa ko kun rabu da mijinki ko saurayi ki sani bafa mantawa yayi dake ba ko ya daina sonki yana nan yana sa miki ido yana bibiyar halin da kike ciki,kinci gaba ne ko kin lalace,namiji yana bakin ciki yaga sun rabu da mace taci gaba,tafi da haduwa kyau da komai da komai,yafi so yaji ance ai naga wance rannan baka ganta ba ta lalace ta rame ta fige,duk kwalliyar wance tab ai kasa ganeta nayi a hanya,ta dawo abar tausayi,ko kuma shi wanda kuka rabu ya ganki da kansa,kin lalace murna zaiyi ba zai damu ba,cewa zaiyi ma wa ya gaya mata,da tana jin dadi a gidana tayi min kaza na kori shegiya gwara haka gashi ai yanzu ta dawo abar tausayi,ai Baza ta samu kamata ba,tayiwa kanta,yanzu ni aka bani wannan me zanyi da ita,ai gidansu wuya suke sha etc.idan kuwa ya ganki kinci gaba,idan yana sonki sai yayi dana sani tayu ma ya dawo yayi ta naci ki koma,ya rude a kanki zaman da kukayi tare ya dawo masa,ko labari yaji saiya nemi ya ganki face to face ya ganewa idonsa,idan budurwace sai yaji takaici ko bai aure ki ba,idan matar aure ce zai kara dinga kaunarki,dan karamin neman aure sai kiji ya fasa,ko ya auro ma yasan kin fita,kowa yana son gyara,tsafta,kwalliya etc duk da cewa suma mazan suna da matsala,amma mata shine ur eye woooo a kara dagewa a daure a cire kyuya da son jiki kiyi iya yinki,
Amarya Sakina ce ta fito ita da ango Ishaq wai yazo kawo mata abinci ta kasa cin abinci shine yazo da take away sai da ya tabbatar taci ta koshi ta rakoshi zai tafi kafin zuwa after magrib dinner party,
Da Amana suka ci karo,dariya Sakina tayi oyoyo Anty muna ta jiranki ba dadi ba kya nan,to banza take away na tsaya daukowa laaaaa hado mana kikayi? Yeah cewar Amana,Nan Sakina ta dinga godiya Suka gaisa da Ango shima harda godiya,
Sakina ce tayi magana to ki mayar cikin motar kinga ko an kai ciki sai an kara fitowa fa dasu dole ga mutane,Amana tace af hakanefa na manta kinsan ni ba kawaye ne mata dani ba,sannan bikina ban samu gatan haka ba ban san ya abin yake ba,bari na maida,ango dai tuni ya hau mota ya tafi,Sakina ta dauka bari na tayaki...Amana tace commot abeg Amaryace ke ba aiki ai,matsa ko na makeki,Sakina ce ta radawa Amana ga mijinki can kamar zai cinyeki da kallo,kinga kalli yadda yake ta muzurai,kamar kishi yakeyi fa,Amana tace zan mareki Sakina ban son shirme na fasa kaiwa motar ebi ki kai ki zuba,
Kai Amana saurin zuciya da fushi yana nan dai,kyaleta Amana tayi ta koma ta kai kayan cikin Mota da kanta ta dauko trolley dinta ta juyo kenan taga Alim a bayan yana huci kamar zai daketa har ta tsorata sai ta tsinci muryarsa yace gyara parking din motarki zan fita da tawa,Amana itama a fusace tace duk filin nan bai Isa ka dauki Mota ba sai na gyara parking?Alhmdllh Alim ya furta a ransa saboda dadi hade da sanyi da yaji a ransa Amana tayi magana yaji muryarta,
Cike da masifa ya kara cewa ko bazaki janye bane?Amana shuru tayi don taga kamar zai daketa yanzu kuma bata fada,kawai sai ta shiga motar ta janye ta can lungu ta fito a fusace fuuuuuuu ta ja akwati ta wuceshi.
Badriyya sai murna takeyi Amana tazo Sakina har ta fesa mata Labarin Alim da take away na Amana da ta musu,
Bayan Amana ta huta saiga Asiya kanwar Alim tazo tana cewa Badriyya wai ina matar Ya Alim ne?
Da sauri Badriyya ta nuna Amana dake kwance saman gado tana faman tunanin Alim,
Anty Amana ina yini cewar Asiya Amana ta amsa cikin fara'a da sakin fuska,Asiya suna kama da Alim sai take ganinta kamar Alim,kallon Asiya takeyi tana ta murmushi tana jin sanyi a ranta,sai suka fara hira, har muryar Asiya kamar ta Alim,Amana sai hira take kakalowa,Asiya tace muje wajen su Abban Huzaifa da Mama ku gaisa da sauran dangi,Amana ba musu ta yafa mayafinta tare da kara gyarawa suka wuce,da dan Auta Kanin su Alim suka ci karo Asiya tace Bro kaga matarfa ya Alim na san baka santa ba lokacin kana schl,Amana a ranta tace wannan yama fi kama da Alim dina,gaisawa sukayi sosai yana ta tsokanar Amana ashe matas ce ma,gaskiya na iya zaben me kyau,suna tsaye saiga Nura ma Babban yayansu shida matarsa da yarsa sun dawo daga shopoing,Asiya tayi sauri ta nuna musu Amana suka gaisa harda hira sosai da sosai saboda Nura akwai nutsuwa, Amana a ranta ta ce lallai ai wannan Nuran ma sunfi kama sak da Alim. matarsa ma sai jan Amana take da barkwanci,tambaya Amana tayi wai ina dana ne Aabid?
Nura yace yana wajen Maman Huzaifa yana ta bacci,ok kawai Amana tace taja Asiya suka wuce cikin part din su Huzaifa,Da sallama suka shiga palo da Alim suka fara hada ido yana saman kujera yana cin snacks da Icecream a gefe,
Huzaifa Ango yana gefensa,mama tana zaune tana jira lallenta ya bushe,ga sauran yan Uwa mata nan gaba daya cike dam a palon amma Alim yana ciki yana cin abu sunki tashi,,tsugunawa Amana tayi har kasa ta gaishe dasu kaf cikin mutunci,Mama da fara'a ta tarbeta tana yata sai yau kika zo muna ta jiranki,dariya Amana tayi,Alim a ransa yace wayyo ta kasheni da murmushinta,
Tambaya Amana tayi ina Abba da yar tsohuwa kaka kenan idan masu karatu baku manta ba,Tace tsohuwa tana daki da bakin ta har danki Aabid yana wajenta,Abba kuma yana sama ke Asiya rakata ta gaida kowa,
Sun mike sunje ko ina sun gaisa da kowa cikin mutunci sun dan dade suna hira da kaka tsohuwa Aabid bacci yakeyi,kowa na dangi sai da aka nuna masa Amana suka gaisa
Fitowa sukayi amma still Alim yana palon kusa da Mama,Huzaifa kuwa ya koma jikinta ya nanike ya kwanta a cinyarta,kowa ya shigo sai anyi dariya Ango kamar Amarya me jimamin rabuwa da gida,
Mamace ta kalli Amana dake shirin fita tace zo yata,dawowa Amana tayi tare da tsugunawa har kasa,duk wanda yasan Amana a da sai yayi mamakin canjawar halinta yanzu har Alim,Mama tace zaki dawo dakina da kwana ne? Da sauri Amana tace a a zan zauna wajen frnds,Haushi Alim yaji a ransa yace da kin dawo nan ai nafi ganinki,Huzaifa yace Anty tafi son cikin yan mata,hararar wasa Amana ta cilla masa,
Yana dariya yace to mene na harara,kowa yayi mamaki ana cewa matar Alim ce amma anga basuyi magana da juna ba sai kallo da yake binta dashi kamar maye yana shan Icecream,
Mama ta fuskanci kamar da matsala tsakaninsu Amma sai kowa ya share tunda ba wanda yasan komai akai,Mama tace to ga dakin mijinki ko can zaki zauna dan iyayi dakinsa shikadai ne ko angon ma su biyu ne amman wannan marar kunyar Mama taja kunnen Alim tace dakinsa daban kullum yana cikinmu,yaki bari mu sake,dariya akayi banda Alim da Amana, Umma duk bata sani ba Alim ne ya tura Asiya ta kawo Amana su gaisa da danginsa shi yasa ya dawo palon ya zauna Sabo da ya kara ganinta,
Mama tace zauna yata,Amana kallon dakin tayi kaf ba space kujera 2seater ce kawai ta rage me dama dama,itama Alim ne a kai ya wani kwanta,Mama tace zauna kusa da wannan kwadayayyen Alim kenan,Amana bata son tayi musu,gashi bata so a gane halin da suke ciki da Alim tunda shima ya boye,Mama tace gyara musu su zauna mana, Asiyace taje ta fara Zama sannan ta jawo Amana ta fada kujera suka sa Alim a tsakiyarsu,
Tofa an Dade ba a hadu ba.
Jikinsu ne ya gogi juna,wani uban shock ne da faduwar gaba ya shigi masoyan biyu,
Haushi Alim yaji kar ma tace ya damu da ita,itama Amana haka,Alim ya matso jikin Amana ya bangajeta da kafada tayi gefen kujera haushi taji a ranta tace dan yana Jin haushi na sai ya bangajeni,gyara Zama tayi,ya kara bangajeta,Amana a ranta tace kai Kai kai da Zafi fa Bai isa ba saina Rama wlh ina ruwana dashi,Amana ta matso itama sosai ta bangazo Alim Bai zata ba ai kuwa ya rikita jikin Asiya,
Asiya tana kallonsu tayi murmushi,Alim a ransa yace halinta Ashe yana nan,nan ya samu ya kara turota tare da kara hade rai,Amana ta kyaleshi ganin mutane kara bangazota yayi,Ai kuwa ta samu ta sa hannunta iya karfinta ta turashi jikin Asiya tana nishi da cijewa,kuma sunyi mukus suna ta faman ture turen juna,haka suka dingayi sai kallonsu yan biki keyi suna dariya,mitsini Alim ya kwanyawa Amana a cinya da sauri ta sosa waje tasa kafa ta take masa kafa tare da murzawa,Alim yaji Zafi amma ya cije, hannu yasa ya yakusheta a wuya har wajen yayi danja kadan,Mama tace wai me kukeyi haka Ku tashi ku barmin Palo iya shege a cikin bakina sai ture ture kukeyi da yakushe yakushe, Ku fice Ku karata can,mikewa sukayi gaba daya Amana fuska ba rahama Alim ma haka,Asiya dariya ta cika mata ciki wannan soyayya haka.
Suna fita tsakar gida Alim ya taho da sauri Amana ta matsa gefe amma saida yazo ya bangajeta ya fara tafiya,da gudu Amana Ido cike da kwalla ta bishi tare da cafko hannunsa ta ganya masa cizo da karfi kamar kura tayi hanyar part din yan mata,
Alim sai da ya saki kara,a fili yace sai na balla yarinyarcan ina wasa da itane,ina ruwana da ita zanyi maganinta.
Amana kuwa daki ta fada tana ai wlh kana min zan rama kaji mutum ina ruwana dashi saboda yana neman na masa rashin kunya ya ci min mutunci shi yasa yake tsokanata to ni kuwa bazan kyaleshi ba sai na rama karma yace tsoron sa nakeyi.
Ana ta shirin dinner Amare sunsha kyau,yan mata da samari kowa walkiya yakeyi,ana ta iba ana tafiya can,Amana ma ta shirya cikin tsadajjen lace light blue da red,gogoronta red,jaka da takalmi red,jambaki red,sarka dan kunne agogo duk red,pose dinta ma red,tasha kyau na gaske,dinkin fitted gown fadin kyan da Amana tayi bata bakine,
Har wajen kaka tsohuwa taje har an shirya Aabid,kowa yaba irin kyan da Amana tayi akeyi da wanda ya Santa da wanda Bai Santa ba,Aabid na Jin muryarta ya dago kansa da sauri tare da rugowa da gudu ya daka tsalle ya dane ta,dagashi sama tayi suna ta dariya,Momy ina kika tafi bana ganinki? Amana tace unguwa naje nan suka dinga surutu tare,sai ji tayi gaba daya har an tafi tana nan,Aabid ta dauka tayiwa tsohuwa sallama,tana fita Alim ma ya fito cikin shiga ta alfarma kamar wani dan sarki,yasha kyau sai kallon juna sukeyi kowa na yaba shigar dan uwansa,Alim cikin shadda Fara kal yake komai fari yayi kyau na gaske,suma taci kudi,kamshi da kyalline kawai ke tashi,
Tunawa Alim yayi ai sunyi fada da Amana basa shiri da sauri ya dauke kai ya juya,Itama Amana a hankali tace au jaka ni kamar muna shiri na wani kalleshi,to wanne ma kyau yayi shi din me, me ya hadani dashi tsaki taja ta wuce motarta ta bude tare da sa Aabid a gaba,Aabid ya fito fit yace Momy ga Daddy can motarsa tafi kyau muje a tasa,Aabid ya kwalawa Alim kira Daddy ka jiramu muje a taka,Amana tace to bazan shiga motarsa ba dalla wuce muje,Alim ma yaji me Amana ta fada shima magana yayi da dan daga murya yanda zata jishi ko kinzo ba daukanki zanyi a motata ba,ko kinji nace zan daukeki dama,da masifa Amana tace oho ko kace ma ba shiga zanyi ba ehe,kuma a daina kallona za a cinye min kurwa to tawa daci gareta kurwata kurrrr ta karasa tana huci,.
Alim shi dariya ma ta bashi da birgeshi,kinga na kallekine?baki kyau ba dai,ga masu kyau can sun tafi party,Da masifa Amana ta hayayyako me zasuci da kai ragowar mata,woooo ragowar mata an gama da kai sai ragowa zasu samu,mata nawa ka aura me auri saki,ina fada ma watarana wata sai ta harbeka kowa ya huta,
Dariya ta kusa kwacewa Alim sai ya kara mazewa ya tamke fuska yace haka na gani shi yasa kike bin abokaina kina fada musu su bani hakuri na dawo dake,
Kugu Amana ta rike tace kalleni tsaf na wuce ajinka Malam ai kai na gama da shafinka na jefa a shara masu kwashe shara sunzo sun kwashe ka an zubaka a katon rami.sai yanzu ma nakejin haushi kaina na auri Kazami yan... yan... yan.....tana yatsina fuska ta kara da cewa ko kyau babu,yanzu ma da kasan munin da kayi da baka je dinner ba ta tsaya tare da murguda baki,
Alim dariya fa yake tayi a zuciya ya samu abinda yakeso,da sauri yace wannan kuma karya kikeyi yarinya,kuka ne ya tahowa Amana tayi sauri ta maida shi tare da jan kwafa ta shige mota,Aabid Bai San me sukeyi ba har ya gaji da jira,kowanne ya figi mota ya hau titi suna tafiya idan Alim ya figi mota ya wuce Amana sai Amana ta cisga ta wuceshi itama,
Idan masifa ta ciyosu sai kowa ya danna mugun horn,yanzu Alim zai wuce Amana ya sauke glass kasa ya zo saitinta da mota ya fara mata gwalo,itama kuwa ta tako da karfi ta masa gwalo wullo wai dan ta tura masa haushi da yawa ta dallaro harshenta ta barshi a haka,tana kaga kaga suna hada Ido ta glass tace nafi karfinka baza ka iya Dani ba,na Riga na maka nisa na wuce ajinka,ta ce woooo wulluuuuuu, ta zuge glass tana haki cike da masifa tace nayi maganinsa ai Bai isa na kyaleshi ba,bazai ja Dani ba,
Alim kuwa yana rufe glass ya dinga dariya kamar me har suka karasa wajen dinner.tare suka tsaya Amana da Bala'i ta fito wai irin kar Alim ya rainata.
Alim kuwa ya shirya me zai taokaneta dashi.
AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳
170-175
Official
By
AsmaBaffa
MARCYCOOL JINJINA GAREKI,
DUK MASU SHARHI WANNAN PAGE NAKUNE,SANNUNKU DA KOKARI INA MATUKAR JIN DADI,KUNA KARA MIN KARFIN GWIWA.
Amana rike da hannun Aabid sauri tayi ta shige wurin da ake event din,wow wuri ya hadu sosai Dinner Baban Ishaq angon Sakina ce yau nasa da ya hada musu aka fara yi,Amare zaune da angwaye sunsha kyau,wurin ya cika da mata da samari dangin Amare da Angwaye,ga kawaye da abokai,wanka iya wanka,mata iya mata maza iya maza a wajen nan ba a magana.
Aabid kuwa da gudu ya tafi wajen Nura da matarsa da yarsu,Amana ana tafiya kwas kwas sai kallonta ake ta faman yi musamman maza,
Ta wuce zata zauna Ashe Alim yana bayanta duk inda tasa kafa sai yasa,sabo da kida bata ji tafiyarsa ba,Amare harda dagowa Amana Hanu suna zaune,Badriyya ta dagawa Alim babban yatsa shima ya daga mata tare da murmushi,Sakina ta masa inkiya da Ido,nan take Alim ya bar kusa da Amana wajen Asiya yaje tana zaune ita da Ahmad yayan Huzaifa ,Alim fuska ba wani walwala ya furta Asiya tashi ki janye min wancen Ku zauna tare,
Dariya Asiya tayi tace yaya Da Alama Allah laifi kayi mata shi yasa kabi ka nacewa mata ka kyaleta ta huta pls,
Zan mareki kije kiyi abinda nace,Ahmad yace kai masifaffe mufa ka ishe mu da wannan matartaka tunda tazo yanzu duk gidan biki gulmarku akeyi iskancinka gaban kowa yi kakeyi Ayu kawai.
Kana surikin nawa? ai an kusa bikinka idan naga dama sai na hanaka kanwata ka rufawa kanka asiri cewar Alim, Asiya kuwa tuni ta cika Umarnin Alim zaune ita da Amana dan auta ma wajensu ya dawo yana fadawa Amana wai ga wata can dan Allah taje ta hadasu ko zata soshi,Amana tace dan yaro dakai to ba Dani ba,dariya sukayi,Alim yana kallonsu yana ta Jin dadi.
Amarya Badriyya da Huzaifa MC ya kira su fito fili ana bukatarsu,Amana ce ta fara mikewa ta shiga fili, Amana bata rawa bata taba yin rawa ba saboda kar a rainata wai hee baya ga haka ma bata iya ba.
Yan Dari Dari ta fara lika musu, cikin takun isa da birgewa sai ga Alim yazo ya fara likawa Amarya da Ango yan Dubu Dubu shima yana liki
Kallon Amana yake yi idonsa na kanta suna hada Ido sai ya maka mata harara itama kafin kace me ta rama harda murguda baki,
mutane ne suka zo yuuuu mata da maza suka lullube wajen kowa liki yakeyi,wani Namiji ya fara likawa Amana kudi sosai,Alim takaici ya kama shi,Amana juyawa tayi ta dinga likawa Saurayin nan kudinta,Alim kamar ya hadiyi zuciya ya sheka lahira,
Kafin kace me ransa yayi bakinkirin,har idonsa ya canja color tsabar bala'in da yakeji,
Yana ta likinsa Bai fasa ba cikin zafin nama ya samu ya shige tsakiyar Amana da saurayi ya musu kerere a tsakiya tare da ci gaba da yiwa Amare likin Naira.
Amana Jin kamshin turaren Alim yasata lumshe Ido nan take ta fada tunanin rayuwarsu sanda suna tare yana nannadeta cikin kirjinsa ta shaki kamshinsa da dumin jikinsa son ranta
Matsowa yayi yanda zata ji shi cikin bacin rai muryarsa har rawa takeyi nace ki fita bana so me kikeyi haka kinawa kato liki for God sake, ko kallonsa Amana batayi ba,cikin karajin da Amana ce kadai zata ji ya furta zan yi maganinki ki bar ganin Ina wasa dake akan wannan bazan miki da sauki ba.
Amana ba walwala ta furta sannu Ubana Sulemanu kai awa?mene hadina da kai ta fada tana Balla masa uwar harara,haka kikace?cewar Alim,Amana ta kalleshi up and down tana fari da Ido tace wacce grass ce kai ko nace wanne weed ne? Wanne ruwan kwatar ne?wacce shara ce?
Me likawa Amana kudi tuni kudinsa suka kare yayi waje kuma yana jin fadan da sukeyi da Alim a ransa yace saurayi kayi asarar budurwa sai dai ka koma wajen Bazawara Amma wannan Budurwar yar dagwas gwas ni zan kwaceta.
Alim da ya tuno me yayi sai ya tuna fada sukeyi ba kishinta yakeyi ba ina ruwansa,
Sai ya canja magana da cewa taimaka miki nakeyi saboda bakiyi kyau ba abin kunyane aga ana miki liki ke baki ga dariya ake miki ba,Amana taci gaba da masifa Alim kake ko wa?ka sakar min mara nayi fitsari pls nace bana yinka kaje ka nemi irinka yanzu nafi karfinka ehe yawwa asakar min mara nayi fitsari,, murmushi Alim ya saki wanda ke kara masa kyau, Amana a ranta tace mijina me kyau, Alim ne ya katse mata tunani da cewa idan naki fa?
Itama ta fara magana kasan ni ai kasan Halina ko na gwada ma? ni da kake gani na ba mutuncine dani ba,ni abin kunya idan ya ganni to guduwa yakeyi saboda uwar gidansa tazo Amana ta furta cikin fushi kamar bata taba dariya ba,Alim yace hmm wanda kikewa ne suke kyaleki yarinya,Amana ta maida martani gaka nan Babban yaro brolas kajin gidan gona girman dare daya.
Gadan gadan ya nufi wajenta da niyyar damkota amma Amana da sauri ta sauka kasa tace idan yau za a kwashi wani zuwa hospital yazo ya biyoni ya gani, masu rawa da liki suka ci gaba da yi,
Amana tsakaninta Da Allah fada akeyi gagarimi, yanda take jin haushin Alim sosai ba mutunci,shima Alim haushin Amana yakeji baiga ciki jikinta ba,sannan ta wani manta dashi ta kara kibarta da kyau,da aurensa a kanta tana ta yawo inda taga dama.
Alim yaga Amana da gaske takeyi karta kunya tashi a mutane sai ya fasa ya koma ya zauna Amana taci gaba da shagalin bikinta,har aka zo cin abinci inda kowa zai tashi yawa kansa serving abinda yakeso,ana ta karbowa,Amana ta ebowa Aabid,little Zaliha,da Ikkram din Nura,
Komawa tayi zatayi serving kanta fara Eba tayi Alim yazo ya wani faffake wajen,Amana bata kulashi ba ta samu ta matsa, kara faffakewa yayi, lekawa tayi tana dogon wuya zata ebo ta wani cokalo bakin masifa,duk inda ta nufa da niyyar ebowa sai Alim yaje yayi blocking wajen,
Alim haushinta yakeji yanda ake kallonta ana yaba surarta, cokali me yatsu tasa tare da yakuso hannun Alim ai kuwa fatar hanun ta kwarzabe kamar yakushin damusa, ta eba tayi gaba.
Dinner tayi kyau da dadi,bayan an tashi duk an watse gida,su Mama sun tafi da Aabid,Alim ya fito ya hango Amana zata shiga Mota shima zai shiga tasa ya murde mata kunne sosai ya,Amana haushi ya isheta ta sai kawai ta shareshi ta shiga Mota ta figa ta hau titi,Alim ma haka,
Gani tayi Alim zai wuce ta tayi masa Over taking tare da sauke glass tana masifeshi dan jagaliya baka iya tuki ba ka koma ka koyi mata,Alim ma ya leko ya kwalla da karfi idan na raina kasuwa ko sautun Cincin bazan yi ba,
Amana tace dan kauyeeeeee,Alim yace daga birni nazo nazo ai,wai yayiwa Amana gori,
Nafi karfinka dai ni na wayar da kai,
Alim yace ai kin iya daurin dankwali yanzu,Amana tace ance maka da can iyawa kayi? ,Alim yayi maganar yan daba yace kya nuna mana Zara,ai mune Zara yar nan,
Ni ba karamin tantirin dan iska bane,Amana ta kwallo itama da karfi tace ai kuwa nima ba karamar tantiriyar yar iska bace kai dukkan mu ba kananan tantirai bane,Maganar ta irin ta nigogi tayi Baaaaba kana yawa,Alim yace motar aroceee,Amana tace dan mafiya me kudin tsafiiiii motar da ka siya da kan dan jariri.
Suna karasowa cikin gidan kowa ya Parker tare da fitowa zata wuce part dinsu,Alim ya kama yatsanta ya lankwasosu baya ta kwalla kara ta kwala masa jakarta,tana haki tace azzalumin mutum ni ba wasa nake da kai ba
Tafiya Alim yayi ya kyaleta yace yarinyar nan da gaske take amma na kyaleta daga yau ya furta cikin fushi.
Amana kuwa ciki ta shiga tayi wanka ta canja kayan bacci ta kwanta gefen Sakina da Badriyya.
Badriyya ce ta Mike ta fara magana Anty Amana ina kika tsaya haka kin San har 2am yanzu fa,banza Amana ta mata,Badriyya tace dama tambayarki zanyi dan Allah first night da Zafi?Allah tsoro nakeji,
Amana tayi dariya tace sanda kika dinga zuga Alim kina hadamu daki ki kulle kin nemi shawarata?
Ki kyaleni naji da abinda ya dameni pls,
Juya baya Amana tayi ta fara tunanin Alim yanda zata daina kulashi ko yayi magana ta daina kulashi,ita zai rainawa hankali ya mata laifi ko yayi tunanin lallashinta saima wani hade mata fuska da yakeyi tare da gwada mata mungunta.
Washe gari bayan Anyi sallar Asuba rana ta fito kadan kowa ya koma baccin safe,12pm Amana ta tashi daga bacci wanka tayi ta shirya cikin doguwar Rigar material Golding color tayi kyau Sosai kamar a sace ta,Amare da kawaye duk sun dau wanka anci ansha,Amana bata ci komai ba ta wuce wajen Maman Huzaifa tare da gaisheta da sauran dangi,Aabid ne yazo tare da makaleta,cike da kunya Amana tace Mama abinci nazo nema,Mama tace ke duk kowa yaci yasha sai yanzu kika fito ana jira a kawo lunch duk an wanke komai tare da gyarawa,shiga kitchen ki hadawa kanki,
Kitchen ta shiga ta dafo indomie da kwanta ta dawo Palo kusa da Mama zata fara ci Alim ya fito cikin 3qtr da Riga T-shirt yana kamshi,Mama tace girman lagos aikinka kenan yawo cikin Mata kaine nan kaine can ga shigar arna, Amana sau daya ta kalleshi ta dauke kanta gefe,
Matsowa yayi tare da gaisar da Mama kana ya kurawa Amana Ido tana cin Indomie Aabid yana gaida Alim ya zura da gudu ya bar wajen ya hango yara na wasa,
Alim kuma ya tsuguna ya dauke plate din Amana yayi tafiyarsa da abincin,Mama ta saki baki tace Alim zan bata maka wlh dawo mata da abincinta,Alim yace Mama yunwa nakeji fa,to ita kuma fa?Sai ta dafa wata Mama tace sai dai ka dawo kuci tare sai ta kara dafa muku wata Ku kara,
Amana tace ni na koshi kyaleshi,a'a baki isa ba cewar Mama spoon biyu kikayi fa, Mama ni bazan ci dashi ba Kazami ne fa Amana ta fada da azababbiyar shagwaba wacce tayi sanadin zukewar numfashin Alim, ajiye Alim kuci cewar Mama, cikin yan uwa duk suna palon,Alim ya jawo sallaya ya zauna yana masifa yacewa Amana sai ki sakko kasa ai kamar wasu yara, Amana gudun kar tayiwa Mama musu ga dangi za a gane basa shiri kawai ta sakko kasa ta zauna Mama harda mika mata pillow ta zauna tana hade rai,
Mama tace Asiya ta je ta dafa musu wata kafin su cinye wannan,
Asiya taso a kyaleta itama taga fadan su Alim amma haka ta wuce kitchen,
Fork spoon dayane Alim ya fisge a hannun Amana ya dinga cin indomie da sauri da sauri wai dan yafi ci da yawa Amana ta rasa ,Amana ta finciko cokalin a bakinsa yasa hakuri ya rike spoon din gam, da kyar ta zaro cokalin itama tai ta ci da yawa ya kwace cokalin tare da tattaro indomie gabansa,yana ta ci,Amana tace Mama kinga zai cinye du,Mama tace wai kai wanne irin mugu ne?bata spoon dinta taci,Amana ta warce itama ta sharba,Alim yace Mama kalli kazantar da takeyi wlh zata lalata abincin,Mama tace to kema baki dai dai ba bashi cokali yaci,Alim ya kwace yaci da yawa Mama tace kaima kayi zari ka bar mata plate din sai an kawo wata Alim yace haba Mama ko romon ni fa ban sha ba,Wata a cikin dangi tace to kai kaci girma mana akan Indomie kamar mayunta ku bari a kawo wata mana wlh Mama ke kike kulasu,ji nake jiya suka gama iskancin ture ture da yakushe yakushe,
Amana tace Allah ni bana kulashi shine yake takalata,cokalin ya dan buga mata a goshi,Mama tace ah...kema da halinki duk halinku daya,ni ban san Alim da haka ba sai yanzu,
Asiya ce ta kawo musu lafiyyar Indomie tare da mikawa Alim cokalinsa daban,
Nan kowa ya fara ci sai gwaren cokali sukeyi a plate,ka daina cimin gabana,cikin rada Alim yace tab wannan maganar tafi karfina kin jin nace ina nema zan....Amana tayi shuru har ya fassara mata magana. Suna ci gaba da ci Sai ta ebo yasa cokali ya kwace,Amana ganin mutane yasa ta kyaleshi,da yaga taki kulashi kuma so yake ya sata bakin ciki sai,ji tayi kawai ya turo plate din jikinta Indomie ta zubo mata a gefenn cinya ta bata mata kaya Amana kwalla tab a idonta tace Mama kin ganshi ko wlh kar na rama aga banyi dai dai ba,na gaji da halinsa sai yana dukana yanzu ma kina kallon can ya mareni kaji Amana da karya, wata dattijuwa tace abin naku iskanci ne kawai ,Mama tace kai ku rabu dani na gaji da halinku,Amana tace Mama shine fa yake ta min abu,jiya ma haka ya dinga dukana,har marina yayi a wajen dinner da zamu dawo,Wata a cikin yan biki tace wai ba mata da miji bane? akace mata da miji ne,matar tace iya shegen banza da ya kuke zama a gidan auren? Wannan ai sai kusa mutum hawan jini,
Mama tace Alim ka kiyayeni na fada maka,Kanwar Abban su Alim ce tazo tace Mama yaranan ina kallon gangancin da sukeyi da Mota a titi zasu je dinner suna ta fada ta windon Mota,mutane suka saki Salati,kunya Amana taji ta mike ta bar palon,Alim ma haka,mutanen wajen suka ce wannan matar tasa yar nema ce naga a tsaye take itama,amma Alim da miskili ne ta koya masa sun zama daya,wasu sukace wannan Yara da kuruciya suke abin dariya,fadan nasu duk ba fada bane.
Amana suna waje a zaune da mata da Maza kawaye da angwaye ana ta hira,Alim shi da wani frnd dinsa suka zo wajen kusa da Amana Alim ya zauna cikin hira Alim yace ai shi yasa akace mata duk sunfi yawa a wuta,Amana tana ji tasan da ita yake zaraf cikin dagewa da masifa tace ai wlh wannan karan sai dai ayi kunnen doki Maza rabi mata rabi,Mazan gasu nan duk azzalumai,
Alim a fusace yace kinji nayi magana dake zancen mu mukeyi zaki sa min baki,Amana ta shareshi,Alim ya kara cewa ai idan mace ta isheka to ka karo aure,Amana tace wace zata zauna da kai da baka san komai yanda duniya take ciki ba,duk mutane wajen shuru sukayi ana jin fadan su Alim,Alim yace dadin abin dai Aljannarku na kasan kafafunmu,Amana tace idan mun zo shiga ku take,ke da ke nake wai? Alim ya mike tare da Barin wajen yana masifa
9pm aka fara shirye shiryen tafiya dinner,Hamza ma duk sunzo kuma sun karbi motar hannun Amana suna kai kawaye,Amana data shirya ta fito cikin shiga ta gaske,ba kowa a tsakar gida duk an gama tafiya sai kakar su Alim kawai ta fito zasu tafi da Alim tana ta tsokanar Amana,Alim ya fito fes cikin rantsatsiyar shiga,kaka taja Amana wai dole su tafi tare,Amana taki yarda Amma kaka ta matsa mata,dole ta bude gidan baya a motar Alim ta shi ga ba walwala,Alim ma fuska ba rahma,ya zauna gefen kaka,Asiya ta fito ta shige gaban Mota,
Bai ce komai ba driver yaja Mota kamar abin arziki sun danyi nisa da tafiya, Alim da Amana sunsa Kaka a gefe karshen mota Amana a tsakiya Alim a gefenta
Alim ya leko da kansa ya kurawa Amana ido,dagowa tayi suka hada ido aí kuwa ya mata gwalo itama ta rama,
Bayan minti daya yace Anjima idan mun dawo zamuyi magana ta fahimta yayi zancen ne ba wasa da gaske,Amana tabe baki tayi tana so tace bata da lokacinsa Amma kuma Kaka na wajen da Asiya,kawai sai tace ba time,
Pls kinji?tayi banza dashi kamar bata ji ba,yace am talking to u fa,tayi banza dashi,
Nan ya zuro hannu tare da latsa cikinta ina abina?
Amana ta kwadawa Alim duka a hannun,Kaka tace yau naga fitsararre,Dariya Alim yayi ya Mika hannu again Kaka ta bige hannun,Amana ya kara rukowa hannu pls ki bani time,Amana ta rike hannun Alim ta garza masa cizo sai suka fara kokawa da hannaye, Kaka na kallonsu suna ta yakushe ya kushe,Alim ya kara tafkawa Amana mintsini,tana haki da Hawaye tare da cewa ka mintsinen?
gyara zama tayi suka fara kokawa sosai,garin fada suka tugewa Kaka dankwali Kaka tana mene haka ku bari lfy?saboda taga Amana harda kuka,Alim kuwa yi yakeyi Amma dariya ta cika masa ciki yanda Amana ta zage,Kaka ta daura dankwalinta,Amana tace Kaka kiyi hakuri kinga dai laifinsa ne ko,Kaka kuwa manne kanta tayi a jikin kujera tana gefe suna ta faman yi,Amana tace kai kai kai kai dannamin kashin wuya uhmm....zaka gani Amana ta Yakushi Alim ta cijeshi yayi kara da karfi,Kaka ta matsa sosai gefe suna ta yi,ganin haka kaka ta rabasu a tsakiya ta zauna a tsakiyarsu wai ta shiga tsakani, sai gashi sun tsallake kaka Alim ta gaban kaka ya zuro hannunsa sai ya taba cikin Amana,Ita kuma taki yarda shine suke ta faman kokawa,
Amana ta rike hannun Alim kamar kunama sai fasa masa cizo takeyi yana ta kwalla kara,Kaka tace yawwa jikata yi maganinsa,
Alim ya karbe hannunsa da kyar yasa dayan ya cirewa Amana gogoron da tasha wahalar sakawa ya ja gashinta da karfi,tayi kara Kaka ta sa hannu biyu tare da Dukan Alim ka haba ka bar yarinya ta sake,Driver da Asiya dariya kawai sukeyi saboda kowa ya kalli abin yasan ba fada sukeyi ba,
Amana tace nafi karfinka ko banza na cijeka da yawa kaifa me ka iya yimin ta karasa tana hakki kamar tayi tsere.
Alim ganin Kaka ce shi yasa baya Jin kunyarsa
Alim yace sai na ballaki kika kara yi min magana,Amana tace na gaba yayi gaba na baya sai labari,gobe i yanzu na tafi gida ina zaka ganni kuma kafin na tafi sai na tabbatar dana yi maganinka.
Ina ma da ne yaro da kagane shayi ruwane,Alim yace kanki ake ji,
Har aka je cece kuce akeyi,amma Kaka tasan da wata a kasa idan sun koma gida zata hadasu taji me laifi acikinsu,
Amana da Alim ba wanda ya kula wani har akayi party suka dawo gida,Kaka tace kuzo muje dakina zanji dalilin wannan shirmen da kukeyi a matsayin fada.
Suna dakin Kaka zaune a kasa Kaka tana saman Bed tace ke fada min jikata mene matsalar ke da mijinki? Amana tace ki tambayeshi,Alim yace ke dai ki fada,k a fada dai kai da akayiwa laifi,Alim yace in zakiyi bayani kiyi,bazanyi ba nan suka fara cacar baki,ita Amana mamakin Alim takeyi har yaushe yake da baki haka yanzu,
Alim ne ya gyara zama tun farkon haduwarsu da Amana da halin Mum da abinda Sulemanu yayi musu da sanadin rabuwarsu duk Alim ya kwashe ya fadawa Kaka yace Amma kaka sirri pls kinji iya mu dake,Kaka tace kaine da laifi baka kyauta ba,kasan da halin Mum Dinka dana Saude amma ka zargi matarka ba tunani ba komai,kayi kuruciya Alim ga matarka ta gari,kuma yanzu gashi kasan kayi laifi ba bincike ba komai maimakon ka fara bata hakuri da lallashi sai ka dinga fada da tsokana da yakushi,
Ke kuma jikata nasan yayi laifi bai kyauta ba kiyi hakuri ki dauka kaddarace,nan Kaka tayi musu nasiha sosai tayi musu fada sannan tace kar na kara ji da gani ya wuce daga yau,Amana a ranta tace tab yaci banza ma kenan wlh Bai isa ba,a fili Amana tace ya wuce Kaka insha'allah bazai kara faduwa ba,
Alim wani sanyi yaji da dadi a ransa marar misaltuwa,Amana ma taji dadi da sanyi sosai zuciyarta wasai saboda Alim baya zarginta yayi tunani ya San ta gari ce ita,
Alim ne ya kalleta tare da cewa Kaka kice ta biyani cikina,Kunne kaka ta toshe tace kai ban son shashanci,to wlh ta fadi inda ta kaimin ciki cewar Alim,Amana tace ciki ya zube ka auri wata ta haifarma ta Mike tare da ficewa,Kaka tace sai kayi aiki da lallashi fa,
Kaka yarinyar nan taurin kai gareta,nasan baza ta taba kulani ba shi yasa kika ga ina tsokanarta da fada,nasan tana da saurin zuciya shi yasa nake mata abinda zatayi magana in ba haka ba nine zan Sha wahala,
Koma me ta maka kai ka jawo ba tunani ba komai ka yanke hukunci cikin fushi,Kaka kishine wlh da shedan amma nasan Amana ba yar iska bace a virgin na samu abata cikin kwali a like,kaka tace tashi ka tafi marar kunya,
Fita Alim yayi tare da tunanin ta yanda zai bullowa Amana ta hakura,washe gari da rana Mum Alim ta sauka tana gadara da takama,
Amana ce ta shigo palon Mama tana neman Aabid,
Mum Alim ta gani zaune tana latsa waya,har gabanta Amana taje tare da tsugunawa har kasa ta gaisheta cikin ladabi,lfy kawai tace ta dauke kanta cike da mamaki dama jarabar yarinyar nan tana makale da Alim lallai aiki Bai kare ba,dole ta aikata lahira kowa ya huta.
Amana dama tasan abinda Mum zata mata kenan kawai sai ta Mike,Alim ta gani a bayanta ya harde hannaye yana ta murmushin Jin dadi an girmama uwarsa.
Ta gefen sa Amana zata wuce ya rukota tare da hadata da jikinta,wani so da shauki hade da shock sukaji gaba dayansu,Amana Hawaye ya cika idonta Alim ya kai bakinsa a kunnenta tare da cewa am so sorry ki yafe min kinji,missed u kwace jikinta tayi tare da ficewa daga dakin,Mum ta kalleshi tace kayi asarar halinka jibi yanda take tureka kana manne mata,Alim ficewarsa yayi baice komai ba,
Amana kuwa room ta koma tana share hawaye sosai ga wani sabon son Alim da yake azalzalarta,
Alim ma kasa Zama yayi ya rasa inda zaisa kansa matarsa yake so,kuma taki hakura
A ranar duk yanda Alim yaso suyi magana da Amana abin yaci tura,sam Amana taki ma yasan inda take,
Last party ma da zata je babu yanda baiyi ba ta kulashi ko ta saurareshi suyi magana ta kirki amma taki yarda
Duk hanyar dayabi ta tosheta, kukane kawai Alim baiyi ba,
Haka aka gama biki sannan suka dawo garinsu har Amare washe gari aka daura Aure tare da kai Amare abinsu shar komai yayi a gidansu.
Amana ta dawo gida washe gari da safe wanka tayi ta shirya tare da komawa baccin gajiya,Alim yazo gidan gaba daya sai da yabi dangin Amana da iyayenta wai su bata hakuri ta saurareshi,su kuwa kaf Alim nasu ne musamman yanda yake kyautata musu ba musu suka kwantar masa da hankali harsu Umma.
Gaba daya manya da yara tare da iyaye suka dungumo dakin Amana tana bacci suka tasheta,Amana gabanta ya fadi da ta gansu gaba daya,nan fa suka zauna zasu fara magana.