_jinjina gareku_
✍Golden pen writers Association.
_ina Alfahari daku Mun Amsa sunan, ZAMANA AMANA Allah yakara mana kaunar juna_
1&2
_A kofar gidan na hango motoci Ajere kamar wani sarki ne ko ince gwamna Amma abin mamakin Samarine matasa reras Akofar gidan_
_Koda na matsa domin in dakko muku labarin Abinda ke faruwa sai naga Abin mamaki_
_matashin saurayi ne Azaune kyakkyawa Ajin farko wato (first class) duk inda kuke tunanin shi ya kai,_
_bawai fari bane a'a chocolate colour ne kala mai tsada, ga cikar zati da kuma haiba,_
_gadai samari masuji da jini Ajika Amma duk cikar wurin ba kamar shi,_
_mamaki na to wai waye wannan da samari suka za ga ye shi haka?_
*KAMAL*
_Lieutenant colonel kamal Ibrahim kenan (the youngest colonel)_
_gaba daya matasan suna zagaye dashi, shi kuwa ba abinda yakeyi sai faman danna tsadaddiyar wayar dake hannun,_
_ya wani kishin gida kamar wani sarki, kana ganinshi kaga miskilin soja ga wani irin kalai laita kamar wata mace,_
_hirarsu kawai sukeyi atsakanin su Amma shi hankali shi na kan wayar shi,
_can naga wani matashi Wanda bazasu wuce sa o 'I da kamal din ba ya karaso kusa da shi,_
_ya duka saitin kunnen shi " Don' yakamata kayi wani Abu gayun nan su watse kasan Alhaji na jiran isowarka ko_
_cikin ginshira kamar kuma bayaso yayi maganar, "do something'_
_gayen yayi murmushi tareda girgiza kai ya Ciro wasu bandir na y'an one one thousand ya mikawa daya daga cikin su,_
" Kuyi hakuri da wannan kafin ya gama ganawa da mahaifin shi zuwa gobe,
_cikin tsananin farin ciki samarin suka fara yimai godiya da kirari "Allah yayima General shugaban matasa kafin su watse,_
Yarage daga shi sai wannan gayen da naji wani ya kirashi da Samir,
_"Don yanzu zaka iya Ajiye wannan wayar mu shiga daga ciki ko kuwa ya fada cikin kuluwa_
_mikewa kawai yayi cikin kuzarin su na sojoji ya kama hanyar shiga cikin gidan,_
_Hmm Ajiyar zuciya na sauke domin yanzu ne na kare mai kallo da kyau dogone sosai Wanda ya Amsa sunan shi namiji_
_Allah yayi mai k'ira irinta jaruman sojoji Masha Allah,_
_Abin mamakin shine nasan sojoji basa mu amala da manyan kaya Amma shi gashi harda hula ga lafiyayyan Agogon Rolex takalminshi wow_
(He is damn handsome Fan's)
_Sun nufi cikin gidan kai tsaye, direct wani part naga sun shiga saboda na lura gidane mai dauke da parts da d'ama,_
_wani dattijo na hango kishin gide acikin wani ma dai daicin falo w'anda akalla zaiyi sittin ko fiye da hakan,_
_Yanada cikar zati irin na girma da kuma haiba, ganin irin littafan dake cikin falon ya tabbatar min da cewar malamine_
_sukayi saurin karasawa kusa dashi bayan sunyi sallama, kamal yayi saurin cire hularda ke kanshi cikin girma mawa ya duka Agaban dattijon_
_baba munsameku lafiya? Cikin tsananin farin ciki ya amsa " sannu kamalu' kun samu shigowa; ai tun dazu nakeso infita saboda kafadamin zaka iso na tsaya jiranka_
Samir ma ya gaishe shi,
_"Allah yayi muku Albarka ya kuma kareku daga dukkan nin sharri_
Suka Amsa da Ameen cikin girma mawa
" nasan mutanen Ku na jiranku don haka zaku iya tafiya idan kun huta sai muyi magana,
Cikin tsantsar lad'abi yace "Baba ai mun sallame su, a'a duk da haka Ku shiga daga ciki Ku gaida sauran mutanen gidan ko,
Suka mike cikin natsuwa tareda yima tsohon godiya yana binsu da kyawawan Addu'o'i,
*Alhaji Ibrahim Khalil* malamine Wanda yasan Abinda yaka mata,
_Suna zaune ne Acikin Garin Zaria Acikin unguwar ban zazzau, gidan da yake ba shi kadai bane, yana tareda kanninshi_
_Alhaji Ibrahim shine babba sai kuma mai binshi wato Alhaji Suleiman sai kuma Autansu Alhaji umar,_
_Kowannen su yana zaune da iyalinshi acikin wannan gidan dake cikin ban zazzau,_
_part hudune agidan part na farko shine na Alhaji Ibrahim sai kuma na Alhaji umar na Alhaji Suleiman ne na uku sai part din karshe na mahaifiyar su,_
_wato tsohuwa mai ran karfe, hajiya Rabi'a wadda suke kira da gwaggo,_
_bawai gidane irin na masu Arzikiba a'a sunada rufin Asirin su ba Abinda ya fi karfin su Arayuwa tun ma kafin yaransu su girma suzama wani Abu_
_gidane mai cike da had in kai da kuma zumunci sunada iyali ba laifi Amma bazaka taba gane waye ya haifi waniba saboda tsabar hadin kai da zumunci_
_Duk kaninsu sunada mata Amma Banda Alhaji Ibrahim tunda matarshi ta rasu shekaru biyu da suka wuce kuma duk tsawon zamansu Allah bai basu haihu wa ba harta koma ga Allah_
Y'an uwan shi sunyi ta fama dashi yayi Aure Amma yaki yace "ya'yan su sun isheshi Arayuwa,
_idan ba Anfada maka ba bazaka taba sanin bai haihuba Agidan saboda komai na yaran gidan shi ya dauke tun daga karatunsu har hidimomin su,
Musamman Dan gatanshi wato kamal ga badaya yaron yatashi Agabanshi ne, shikan shi kamal din saida ga baya yasan basune suka haifeshiba,
_Kamal D'ane ga Alhaji Suleiman wato mai bin Alhaji Ibrahim su hudune Adakin su shine babba duk agidan sai safwan bilal sai Autar su Zainab_
_Alhaji umar kuwa yaranshi uku duka mata duk biyun sunyi Aure sai Autar su wadda take sa ar Zainab ce wato Asma'u Wanda suke kira da *HUSNAH*_
Atakaice gidane bawai mai yawan cikar ya'ya ba
*KAMAL*
_Wato Don yanda Abokansu suke kiranshi yasamu shiga aikin soja ne saboda tsananin kaunar da yakewa aikin tun taso war shi_
Bayan kammala diploma dinshi yasamu shiga makarantar horodadda sojoji dake cikin Garin Kaduna wato N.D.A Wanda yafito da babban matsayi,
_gashi yanzu harya kai ga matsa yin lieutenant colonel Acikin shekara talatin da y'an kai_
_Akwai girman kai Wanda bawai kanninshi mata kawai ke shakkar shi ba har ma da kanninshi mazan y'an Jami'a_
_Zainab da Husna sun ma tsani ace yau ya shigo Garin baya duka baya zagin su Amma kallo kawai ya ishe su_
*Husnah*
Tafi kowa tsanar lamarin shi saboda tafi kowa sanin wanene shi tun taso warta, acewarta yanada Fuska biyu Annabi a fuska firauna A zuciya.................✍
*taba ka lashe yanzu nafara acigaba da gashi my fan's*💃💃💃💃💃💃💃
[3/8, 8:37 AM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*👨✈
_patients love & sacrifice_
Story writing by
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
3&4
_Samir shine Abokinshi tun suna kuruciya tare suka taso unguwar su daya har zuwa lokacin da suka fara aiki shima sojan ne Amma kowa yana serving awuri daban_
_Akwai zumunci mai karfi atsakanin iyayen su kasan cewar su a unguwa guda kuma dukansu malamai yasa Amintar su ta core_
_Alhaji Ibrahim baida wani Amini da ya wuce mahaifin Samir saboda kaunar dake tsakanin ya'ya n su,_
_Husnah da Zainab sun taso cikin kaunar junan su kamar ciki daya suka fito saboda suntaso sunga kan iyayen su ma duk Ahade ba wani mai nuna ma wani banbanci_
_gaba daya rayuwar su sunayinta ne A part din inna Habi wato mahaifiyar su Kamal dasu Zainab_
_lokacin da margayi ya na Raye wato uwar gidan Alhaji Ibrahim gaba daya ita take kula da yaran gidan tarikeso kamar ya'yan cikinta_
_bayan rasuwarta kamal ya koma gefen inna Amarya wato mahaifiyar su Husnah kasan cewar Sam baya samun kulawa daga mahaifiyar su irin kunyar nan ta y'an fari_
_sanin da sukayi baida wurin zaman da yawuce can yasa sukafi mu amala da dakin inna habi gefen gwaggo wato tsohuwa kakarsu ma sai idan baya garin_
_ita Zainab tana son Dan uwanta sosai saidai tana bin ra ayin kawarta kuma yar uwarta don komai nasu tare sukeyi gida da waje y'an biyu ake kiransu komai nasu iri daya ne_
_A halin yanzu suna matakin k'arshe a secondary, shekarun su baza su wuce shatakwas ba don kana ganin su kasan Akwai kuru ciya atare dasu_
_kuma sunyi saukar Alqur ani mai girma sun sami ilimi da tarbiya sosai Awurin iyayen su Amma dai Akwai rawar kai da kuma tsiwa_
_ban taba mantawa lokacin suna j.s.s sun zo kamal ya zo pass Aka sasu su gyara mai dakinshi dake cikin part din Baba Alhaji yanda suke kiran Alhaji Ibrahim_
_sun samu kayan shi a acikin Akwatin shi suda aka aikesu su gyara mai daki suka buge da bude mai kaya suna mai Searching_
_Wanda suna cikin yimai binciken ne ya shigo dakin, kuma yayi dai dai da lokacin Husnah nafito da wata zungure riyar kwalba_
_Da ya daka musu wata irin tsawa ai tuni tayi wurgi da kwalbar suka cure guri guda tsabar tsoro da kuma firgita, cikin husky voice dinshi_
_Dan ubanku Abinda aka aike Ku kenan Kuyi; wayace Ku taba min kaya ai jikinsu ba Abinda yakeyi sai rawa suka fara rokonshi "ya kamal don Allah kayi hakuri'_
_Yace su wuce su samo bulala kowacce dai dai da tsawon ta, ai suna samun tazare suka ruga da gudu dakin inna Habi don sun San zasu tsira_
_tana sauraron labaru agidan redio suka fado da gudu har saida ta tsorata tayi wurgi da redion tareda dafe kirjinta_
_"kai waya koroku haka? Cikin kidima Zainab tace " ya kamal ne zai doke mu" ta hade fuska me kuka yimai da zai tabamin ku?_
_Husnah cikin rashin gaskiya tace "wai kawai don mun gyara mai daki baiyi da kyau ba, ita kanta Zainab tasan karya ne ta kalli Husnah kafin tayi magana inna Habi ta hau fada_
_akan me zai firgita min Ku haka; ina zuwa ta mike tareda nufar sasan inna Amarya itama har ta mike zata nufa cikin sasan inna Habin don taji gudun su sai sukaci karo tace_
_" yaya lafiya naji hayaniya? Tace ba dole kiji haya niyaba d'an ki ya firgita min yara, tace Safwan? dan nasan shine me shiga sabgarsu ko bilal,_
_"wannan yaron dai na awurin ki, inna Amarya takwashe da dariya don taganota wato kamal don ita akwaita da bwarkwanci_
_"Yaya indai D'ana ne sunyi mai laifine kema kinsan halin ya'yanki mu samman me idon nan A tsaye, ba Abinda Yata takeyi, suna haka ya nufo sasan yasamesu atsaye_
_"Yawwa kar ka sake katabamin yara inba hakaba ranka zai baci ya dukar da kai cikin ladabi yace " kiyi hakuri innan mu_
_"Aida Sauri tabar wurin tareda cewa saika nemi uwarka, ba Abinda inna Amarya takeyi sai dariya don don lamarin na su Abin dariya ne,_
_"shima da gan gan yayi don yasan ta tsani ya nuna itace uwarshi saboda tsananin kunya da k'ara irin ta ta_
_inna Amarya ta tanbayeshi me sukayi yayi mata bayani tace" nasan halinsu ai musamman Husnah kabarni da su, ka je ka ba yaya hakuri,_
_Haka yasameta har dakinta yabata hakuri takuma jamai kunne"kar ka sake inji ka taba min yara idan ba haka ba ranka zai baci, shidai yana duke ba Abinda yakeyi sai Bata hakuri,_
_saboda haka Sam baruwanshi da lamarin su saboda gudun Bata ma mahaifiyar shi rai Safwan ne shi kam ba ruwan shi yanzu yakai duka bare kuma bilal da baya basu iska,_
_koda yashiga soja ma basuda wani wayo Amma saboda yawan zuwan da yakeyi gida yasa suka wa ye shi da kyau Kasan cewar tunda yafara aiki ya daukewa iyayen su nauyin komai_
_tundaga hidimar Abinci har zuwa kan su tura da kuma karatun kanninshi, shi ya dauki nauyin Auradda kanninshi, wato yayyin Husnah murjanatu da karima,_
_shiya hana Alhaji Ibrahim aiki yace yanzu ya huta shi zai rika yin komai tunda yanada karfin yi Baba Alhaji yaji dad'i sosai kuma yasan bazai taba kukan rashin haihu wa ba Arayuwa,_
_kamal yazama abin Alfaharin shi yasan bazai taba daya sanin rashin haihu wa ba saboda ga yaran y'an uwan shi kuma ba mai yanke wani hukunci agidan sai Abinda ya zartar,_
_duk da kasan cewar part dinsu arabe baisa sun raba tukunya ba komai nasu yana hade a babban kicin tare sukeyin komai agidan tun margayi ya na Raye,_
_har zuwa yanzu haka suke tafiyar da gidan su, Ata k'aice gidane mai cikeda hadin kai da kuma fahimtar juna,_
*Cigaban labari*
_dakin mahaifiyar shi yafara nufa Samir na dariya don yasan mezai iya faruwa yanzu, cikin zolaya yace yanzu za akoromu,_
_shi kanshi kamal din saida yayi wani irin murmushi mai tsada irin na miskilayen maza kafin suka shiga daga cikin falonta da yadanji gyara ba laifi_
_jin sallamar su abakin kofar yasa tayi saurin dago kanta ganin su yasa ta kawar da kai tareda Amsawa cikin basarwa,_
_dukawa sukayi cikin ladabi kamal yafara gaisheta inna ina wuni ta dankalli gefen Samir da yake cemata inna munsameku lafiya?_
_ta amsa shi da sannu ya aiki; yace Alhamdulillah inna yana tafiya cikin Amincin ubangiji tareda Addu'o'in Ku agaremu, tace Allah yasa Albarka kuje innarku naciki,_
_suka mike atare Samir yaciro kudi ya ajiye mata yace inna asamana Albarka, tace " kai dannan zoka dauki kudin Ku mezanyi da kudi har haka bayan kun dauke mana lalurorin komai_
_yace Kuyi mana Addu'a kawai inna, banga k'anni na ba yau ma basa gidan ne? Tace " basu dawoba suna zuwa wurin koyan girki Yama kuke kiranshi?_
_yayi dariya yace catering school Ashe sun girma yanzu don yafi shekara biyu rabon da mu hadu dasu fa,_
_kamal yayi gaba don shi Yama manta da wasu yara agidan iyakarshi duk karshen wata yaturo ma da Baba Alhaji kudi domin hidimomin su_
_,wucewa yayi abinshi yabar Samir don shi tsabar naci yasa inna take kula shi dole,_
_gefen inna Amarya suka nufa ta taresu cikin farin ciki "maraba da ya'ya na ta kakkabe musu kujerar dake cikin falon jikinta narawa Ku iso Ku zauna sannunku da zuwa,_
_cikin tsananin girma mawa suka tsuguna a gabanta " inna sannunku mun sameku lafiya? Ta amsa da fara arta Allah yayi muku Albarka yasa Ku gama da duniya lafiya_
_"Y'an da kuke mana Allah yabaku masu yimuKu kuma Allah ya kare Ku daga duk kanin makiya dakuma ma hassada,_
_kamal nason Addu'o'in da iyayensu keyimasu don yasan Addu a Bata faduwa kasa banza da izinin ubangiji,_
_kafin kace me ta cika musu gabansu da kayan abinci irin na gargajiya irin cimar da tasan sunfi kauna suka mimmike akasa suka fara dibar girki,_
_sunci sunyi nak kafin tafara yimusu magana "naji dad'in zuwanku lokaci daya wannan karon Saboda muyi magana,_
_gaba daya suka bada hankalin su gareta " Samir Sahura tayimin maganar ka akan ta nema maka mata kace bakaso sai Abokinka yatashi zaku nema tare,_
_har zuwa yaushe ne iyayen Ku zasu cigaba da yimuku k'ara; ni nasan yaya kallonku kawai yakeyi idan yatashi yanke muku hukunci bazaiyi muku dadi ba,_
_don haka tun wuri Kuyi kokarin fitoda matan Aure, cikin sunkuyar da kai kamal yace inna Kuyi hakuri dama ni Abinda yakawoni kenan, nasamu mata mungama dai dai tawa da ita Abokiyar aiki nace,_
_inna tayi shiru.......kafin tace "kana nufin soja ce itama? Yace" eh inna, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya Hmmm, "to ba komai yanzu kabari zanyima yaya bayani Anjima_
_to kai kuma fa Samir; shi yanzu ya shirya Saura kai kuma, ya Sosa kai " inna zankawo tawa insha Allah, tace Allah yanuna mana yakuma Baku mata na gari_
_inna har yanzu banga su Husnah ba, sai yaushe suke tasowa ne? Tace ai wa innan sai karfe shida suda gidannan yaran nan Sam basa hutawa ko ranar sati,_
_daga sun dawo boko sun fita wurin koyan girki daga can su nufi hadda kuma ai yanzu sun natsu angirma tafada tana metuna kuruciyar su,_
_shi kanshi Samir yakan tuno kuruciyar yaran musamman Husnah, sundade kafin sufita gidan su samir suka isa inna Saura tanata farin ciki "lale da mutanen ikko Kamal take nufi da yake shi Acan yake serving,_
_sun gaisheta cikin girma tasamu su Albarka tareda Addu'o'i masu ratsa zuciya hade da nasi hohi ta Dora da nata fadan rashin Auren duk suka yi shiru,_
_" nasan Hajara ta cika muku ciki ai , Samir yace eh mun koshi inna ina bana yake? "Ai tare suka fita da Alhaji babba wurin daurin Aure,_
_daga nan dakin kamal suka koma domin Sudan wata ruwa,
karfe shida da kusan rabi kofar gidan takuma cika dankam da matasa
_na hango wasu y'an mata guda uku kyawa wa ajin farko musamman ta tsakiyar su duk suna sanye da hijabai dogaye har kasa har ma da safa kowacce na dauke da jakar hannu,_
_Wanda kana gani kasan ta debo takaddu Aciki daka ga yanayinsu kasan sun gaji, taku suke cike da natsuwa suna kuma yar hira atsakanin su_
_kofar gidan naga sunnufo gaba daya hankalin samarin yakoma Kansu ba abinda suke sai tasbihi saboda hango tsantsar haduwar su duk da suna cikin hijab_
_ta tsakiyar tafi kowa tafiya da hankalin su Samir kanshi kallon su yakeyi don bai gane kosuwaye ba saida suukazo dab dasu,_
_sukam tundaga nesa sun San ko waye yau agarin don haka Husnah tace " yau Akwai kulle adaki,Zainab tace saboda me? Bakya ganin mala ika jibirilu ya sakko yau,_
_dayar dake gefe tace waye mala ika kuma sarkin yan sharri tace "ya kamal mana shine ya iso daga ganin gidan nan yau_
_abinka da dan uwa Zainab sai murna wayyo yau zabga ya kamal " sis kusan shekara biyu bamu ganshi bafa bakya missing dinshi_
_tace Allah ya kiyaye ta dan matse fuska meyayi miki haka sis tace haka kawai ni na tsani SOJA,_
_dayar danake tunanin kawar suce tace wow soja ne nikam ina son *AURAN SOJA*..............somin tabi me my fans muje zuwa_✍💃💃💃💃💃💃💃💃
_need comment_
07062906225
[3/8, 8:37 AM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*
_patients love & sacrifice_
Story writing by
*Fenerh*
✍
Golden pen writers Association.
❄we bearers of Sooo golden we write assiduously percieven no pain so magical, our creative golden pen be our words A product of our pen savour our words for it couse you no pain❄
5&6
_gaba daya idanun gayun nakansu amma banda kamal da kanshi ke kan wayar shi yana faman dannawa saida su ka iso gab dasu Zainab da dayar suka gaishe su_
ya Samir sannunku da zuwa, Zainab tafada cikin fara a da kuma murna
Ya washe baki shima "Husnah'ko? Tace" a'a Zainab, ga Husnah nan, ta nuna ta
_yakalli Husnah tareda tasbihi cikin zuciyarshi wow "kan wata ba gaisuwa ne? cikin basarwa tace " ina wuni ya Samir'_
_sai Alokacin kamal ya dago kanshi jin wata irin murya mai dad'in sauraro yakai idonshi cikin nata saida gabanta ya wani irin faduwa_
_saurin dauke kanshi yayi Samir kuwa duk ya rude ganin wa innan kyawawan yan matan don ko Zainab ba bayaba fagen kyau_
_suka shige cikin gidan yana biye dasu tareda tanbayar su ya karatu? Part din goggo suka fara wucewa saboda sunriga da sun saba sai sun gaisheta idan suka dawo kafin suwuce nasu part din_
_"cikin tsokana Zainab ta fada mata kan jiki "ta tureta tareda cewa " karasa jikin girman zakiyi Husnah tace "sannu gwaggo' tace kema sannu miskila kinfi ma haukaci ban haushi_
_sunan da take kiranta dashi kenan Samir dake biye da su yace " uwar gida sannu da hutawa, ta washe baki "a'a na karfen ina na roban yake?_
_" yana waje jama'ar shi na wurin, tasa dariya "wannan sarauta ta zama ta dole kenan, " wallahi sun manna mai dole_
_cikin ran Husnah ta ce sune yake wani burgesu da ma sarautar samir suka ba ma da yafi Amma wannan sai zurfin rai da uban Jan aji kamar tsohuwar karuwa,_
_dayar ta mike tace " muje ingaida su inna in wuce gida magrib na yi "Fatima zaki wuce ? Tace eh gwaggo dare nayi kar mama tamun fada,_
_suka mike duka suka shige ciki Samir na binsu da kallo, saida ta gaisheda su inna ta wuce gidan su dake kusa da nasu tayi tayi sutaka mata Husnah taki saboda samarin dake wajen_
*karfe takwas na dare*
_Duk sun gama taruwa adakin Baba Alhaji iyayen harma da Gwaggo tana gefe yace " Alhamdulillah naji dadin wannan taruwa ta mu a yau_
_Gwaggo bayan na dawo Amarya ta sameni da maganar danta cewar yasamu mata Acan wurin aikin shi to duk kan mu nan Abinda muke fata kenan ya Ajiye iyalin kanshi kuma dama naso inyi mai maganar to sai gashi tazomin da zancen,_
_don haka zansa ayimin bincike akanta Akwai wani abokina yana aiki tareda su zansa yamin binciken_
_Gwaggo tace " hakan yayi Allah yayi muku Albarka daku da ya'yan Ku duk suka Amsa tare Baba Alhaji yace Suleiman bakuce komai ba akai,_
_"a'a yaya wannan ai zancenku ne kaida d'an ka saikuma Umaru ko yanada tacewa, shima Alhaji umar din yace " yaya duk abinda kayi akanmu ko ya'ya n mu duk dai dai ne_
_yaji dadi sosai "yace Allah ya kara hada kanmu, Gwaggo harda kwalla tana tasa Albarka,_
_haka suke gudanarda rayuwar su akoda yaushe cikin girma ma juna da hadin kai,_
_kwanansu uku suka juya wurin aikinsu , kuma duk tsawon kwana kin nan Husnah Bata kuma y'ar da sun hadu da kamal ba har ya koma, ko Samir duk nacin shi saida ya hakura_
_ahankali kwanaki ke Dada shurawa har zuwa lokacinda su Husnah suka fara shirye shiryen fara rubuta Exam gaba daya Kansu ya dauki zafi kullum suna cikin karatu don ma sun gama da catering school_
_suna zaune adakin inna Habi dukansu har inna Amarya " nidai yaran nan Kuyi Ku gama wannan jarabawa ko kwayi jiki duk kunbi kun rame saboda karatu,_
_inna Amarya tace" yaya kenan Safwan dake jarabawa a Jami a bai rame ba sai su, to ni akansu nafara ganin salo kala kala agidan nan da ace bamuda yan bokon tun farko da munga salo_
_tace " ai suna kokari kedai kyalemin yara na Zainab "tace wallahi inna karatu Akwai wahala na matsu mu gama muhuta_
_bayan tafiyar su kamal Baba Alhaji yasa aka yimai bincike Yarinyar da kamal yace zai Aura Amma baice komai ba akai yana jiran dawo war kamal din_
_su Husnah sun gama exam lafiya yanzu sai zaman gida iyakarsu zuwa hadda burin Husnah bai wuce jarabawar su tafito ba yanzu ta ganta a jami'a_
_yauma duk suna zaune a gefen gwaggo harda su Safwan anata hira Husnah tace " zee nifa nafison inje kadpoly,_
Bilal yai carab yace _first in history kenan anan gidan yarinya, "waye kika taba gani mace da Baba yabari taje jami'a, ko Aunty murja Agidanta tayi hakama Aunty karima,_
_inna Amarya tace kyale ma haukaciya zamu gani inkunfi kowane anan gidan_
_inna Habi tace da izinin ubangiji zatayi tunda suna so kuma nida Kaina zanyima yaya magana, ai tabuga wani irin tsalle ta makale inna tareda cewa " I love you so much my inna_
_Gwaggo tayi dariya naji nagani ke kuma fa, Zainab tace "nikam baruwana wallahi bansa ma araina ba_
_aiko inna saida tasamu Baba Alhaji tace mai " yaya nazo da magana ne akan Yata tace tana bukatar taci gaba da karatun ta idan jarabawa tafito,_
_yanisa tareda gyaran murya "Habiba karki damu ina jiran yayan su yazo sai yaje ya nema musu don yafini hanya yanzu,_
_itakanta tayi mamakin saurin Amincewar shi tasamu su Husnah da labari mai dad'i aranar kamar tasa ruwa akasa tasha_
_Zainab ma tayi farin ciki da Amincewar Baba Alhajin_
_kwana ki nata tafiya wannan karon kamal yadauki kusan wata shida bai shigo Zaria ba saidai waya kullum da iyayen shi_
_yau Garin yatashi da ni ima irin Yanayin da Husnah ke bala in so wato lokacin damuna don tun tana karama tanason wasa da ruwa don haka ko yanzu suna zaune tace_
_Allah yakawo ruwa yau inyi wanka, inna Habi tace " kiwa Allah y'ar nan karkice zaki shiga cikin ruwan nan kinsan Bakida jumurin ciwo kizo ki hanamu rintsawa_
_ai saidai ke ta hanaki yaya badai niba tunda yarinyace kamar y'ar ruwa, "waini yaya haka take kwana da hijabi ta wuni kuma dashi?_
_saikace konanniya lallai Akwai aiki, inna Habi tace " indai wannan hijabin ne nayi fama har na gaji, ke Anyi lokacin zafi saina bari tafara bacci infara kokarin cirema Amma sai kiga tarike shi carab_
_Zainab ta tuntsire da dariya Wallahi inna koni Bata barina ina ganin jikinta ko Riga zata canja saita cikin hijabin_
_ta zabga mata harara "karki wani harareta yaya da bamusan yanda halittar take ba danace tanada nak'asu, " to ya isheku haka keda y'ar ki gwara tarika boye jikinta gudun mayu karsu kama min ita_
_"farar fatar da ta sata zasu lasa kome; " tunda mayu basu yi komai daniba mezasuyi da ita ko kafata takama ne Allah natuba yaya inbanda girma ai jiya ba yauba_
"Ke Amarya inake ina Yata kedai kiyi shiru kawai kinji,
_itadai tanajin su kuma bakomai ke hanata cire hijabi ba sai kunya takeji aga nonuwanta don ita gaskiya bazata iya sa bra ba kuma inata zauna Ahaka zasuna ganin kansu_
_Bata taba mantawa mutum daya ne yataba ganinta ba Riga tun shekaru biyu da suka wuce lokacin da tafara k'irgan dangi lokacin yazo Hutu tafito wanka a dakin Gwaggo tana cire zaninta yana shigowa_
_tayi wani uban k'ara ta dunkule wuri daya shi gaba daya Alokacin ya dauka wani Abu tagani yatsorata ta saida ya lura da yanda take ta dunkulewa wuri daya yaga no ta_
_aikuwa cikin hasala ya fisgo ta " ke uwar me kike boyewa anan yafara kokarin dagota tafara kuka " don Allah ya kamal Karka kalleni wallahi ba kaya ajikinta_
_dariyama taso Tabashi y'an da ta keta wani kare kirjinta bayan yana ganin dan k'urjin datake boyewa saida ya saketa yafita tayita jeramai Allah ya isa kuma tundaga ranar take boye jikinta_
_Bata fatan kowa yakuma kalle mata jiki da ko ita kanta yanzu idan takalla kunya takeji yanda komai nata yacika some time ma matsesu takeyi da best kafin tasa Riga_
_sanadin tsanar shi kenan take mai kallon dan iska tama tsani taji sunan shi Akwai lokacin da ya aiko kaya da Salla aka rarrabawa kowa da har ta dauki wani material dayamata kyau_
_Tanajin labarin kamal ne yakawo tawurgar Allah yasa inna Amaryace kawai da Gwaggo awurin tace "kayan dan iska Allah ya kiyaye ta sa Ajikinta_
_aiko inna takaimata gwabza abaki tace " Ashe kuwa har Abincin gidan nan zaki daina ci saboda ko tsintsiyar gidan da zufanshi ake siya_
_kukanta yajanyo hankalin Inna Habi tazo tana tanbayar lafiya " waye yataba min ya? Gwaggo tace y'ar ki ko shakiyiya wai batason wa innan kayan suka rufe zancen kara irinta Matar nan ita tasiya mata wasu kayan_
*cigaba*
_kafin dare ruwan sama ya sakko wanda ya sanya kowa yanatsu acikin dakinshi suma su Husnah suna kwance akan gadon Inna Habi tana faman naci_
_innan mu indan shiga ruwan nan kadan, tace " a'a bazaki shi gaba ki kwanta kiyi bacci kamar yadda y'ar Uwarki tayi tabude baki zatayi magana sukaji sallamar shi_
_"Inna ta bude kofar tareda cewa" lafiya da Daren nan kuma cikin ruwa? "Wallahi munzo wani couse ne a jaji nida abokaina ne naga inna tayi bacci shiyasa nazo nan muna bukatar Abinci_
_tace " to bari ingani suna cin tuwo ko? Donshi mukayi yau agidan yace zasuci ai hausawa ne duka bari inje Aba yaran nan su kawo mana...............✍
*Bear with me fan's I have just started*
[3/8, 8:38 AM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*👨✈
_patients love & sacrifice_
Story writing by
*Fenerh*
✍✍✍✍✍✍
Golden pen writers Association.
✍✍✍✍✍✍
❄We are bearers of Sooo golden a pen we write assiduously percieven no pain so magical our creative golden pen be hold our words A product of our pen savour our words for it will couse you no pain.❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7&8
_tun lokacin da Husnah taji muryar kamal ta lafe kamar mai yin bacci, jin yana maganar akai mai Abinci harda bada umarnin a aiki yara tasan idan ta motsa karshen ta ita zata kaishi_
_yana ko tafiya inna tace " Husnah " tayi shiru takuma tab'ata "ke" Husnah " tashi ki kaima yayanki Abinci yazo da baki,_
_taleko da kanta tace "wallahi tsoro nakeji innan mu darefa yayi" tace "nasani daure karya kuma dawon daki kinji"_
_tasan da nauyi ta kuma musu da mahaifiyar shi yasa batada zabi sai na dole ta mike tana tura baki tareda gunguni " mutum kamar maye zai wani biyo dare dama yan fashi sun tare mugayen a hanya kowa ya huta_
_inna kam tayi gaba wajen hada musu komai a tray na silver harda zobo da su kunun zak'i ta fito da zunbulelen hijab inna ta mika mata " muje inraka ki kimika musu mudawo_
_taji dad'i suka fito har kofar dakinshi tayi sallama cikin zazzakar muryarta kafin ta shigo yayi saurin tasowa ya tareta cikin zafin nama ya karbi trayn_
_duk da cikin duhu ne bai hana shi ganin fuskarta ba acikin hasken fitilar dake cikin dakinshi gashi har zuwa lokacin ana dan yayyafi_
_yadan kalleta cikin muryarta kamar anayimata dole tafurta " sannu da zuwa ya kamal " saida ya amshi tray din kafin ya amsa can kasan halshe "Yauwa_
_"kikoma ciki' wani kallo tayimai Azuciyarta tace " ai kobakace ba malam ta juya Abinta batareda ta kuma cemai komai ba tasamu inna suka wuce Abinsu_
_inna tace " yi hakuri Yata kinji zamu hadu da safe zanja mai kunne karya kuma damun mu da dare yaje ya damu uwar shi, itadai gado kawai ta haye sai bacci_
_da gari ya waye suna yin sallar Asuba inna ta aiki Zainab tace " jeki samu Amarya kifada mata d'an ta ya shigo da dare, Zainab tayi tsalle "yehhhh ya kamal? tace " shi wuce kitafi_
_ana fada mata ta mike cike da d'oki tace bataga ta zama ba " koma ki kira y'ar uwarki Ku zo mu yimai Abun k'ari, tasamu Husnah akan sallaya ta na lazimi " kizo muyiwa yaya Abin k'ari inji Inna Amarya"_
_tace "kuth jiya ya hanani bacci yanzu kuma bazankoma baccin ba, inna Habi dake shigowa tace " ke wuce kubarmin y'ah ta huta hakanan Zainab tace " innace tace tazo fa_
_muje muyi aikin barta ta huta Zainab ta kalle ta " y'ar gatan inna kwanta mu bari muje aikin" tayi mata gwalo ta haye gado Abinta_
_aiko inna Amarya naji tafara fada " eh lallai yaya wato daure mata kikayi karta moru to shi kenan saboda Allah ga yar uwarta anan ita ta yi kwanciyar ta adaki_
_"jiya ya hanata bacci yanzu kuma ya hanata" idan sun tashi ta gyara musu dakin kuwa zamu gani_
Kafin gari yayi haske har sun gama shirya musu Abun k'ari irin na gargajiya kunun tsamiya da kuma kosai gefe ga ruwan zafi Wanda yaji kayan kamshi
_ana gama hadawa inna Amarya ta tasota " fito ki kaimu su Abin cin kuma ki tabbata kin gyara musu daki' kafin kidawo ta turo baki gashi ba inna Adakin dole tamike_
_" haka zakije da wannan hijabin kamar Matar liman tace "inna don Allah kibarni inje haka " Allah ya kiyaye wuce kiban wuri haka ta wuce ba don ranta na soba_
_ta Dade atsaye tana tunanin yazata tayi ta shiga ciki ga tray dinda ta dakko da nauyi cikin dauriya ta yi sallama, jin shiru yasa tasan basa ciki tasa kanta kawai_
Saida ta karewa dakin kallo rabonta da shi tun lokacinda su kayi mai bincike ita da Zainab taga komai ya canja harda sababbin kujeru katifar shi katuwa
_gudun karsu dawo su sameta yasa tayi saurin Ajiye tray akan dan center table dinshi tafara Kaye Kaye ganin hijabin na hanata Sauri tayi saurin cireshi dama wani dogon wando ne kawai da wata yar shimi ajikinta wandon ya kamata tam_
_ga shimin ma tayi mata dab ajiki kana ganin komai nata cikin Sauri take aikin ta don tasan masallaci suka je tayi tana gab da gama wa tafara gyara katifar kamal ya sawo kai cikin dakin_
_da Sauri ya koma baya yace ma Abokan nashi suje dakin baba Alhaji kawai bari Agyara musu nan, daya daga cikin su yace " bari indauki system dina'_
_no "bari indakko maka " wai meye haka ne Don saikace mai boyon wani Abun aciki da batare muka kwana ba zance Akwai wata acikine kake boye mana_
_"eh naji kujirani anan kawai cikin matse fuska duk suka bishida kallon mamaki kamar wani mai juju, yana shiga tana janyo hijabin ta juyowarda zatayi sai ganin ganin mutum kawai tayi_
Kasa motsi tayi har hijabin ya fadi daga hannunta shi kuwa tunda yashigo ba abinda yakeyi sai Aukin kallonta tundaga kasa har zuwa samanta ya tsayarda idanun shi cikin nata da sukayi kwalkwal da ruwa
_ya tattaro dauriya cikin wata irin murya mai bala in taushi yace " me kikeyi anan? Saita fara inda inda ganin irin kallonda yake aika mata yasa ta kalli jikinta kamar ta kurma ihu tsabar jin haushi tayi saurin daukar hijab din ta zura shi ta baibai_
_kafin cikin rawar murya tace Abinci na kawo muku ga shinan tafara shirin fita still kallon ta kawai ya keyi harzata rabashi tafita yaji muryar Abokinshi yana cewa Don kabani mana ko inshigone?_
_ya wani irin fisgota " stay hare " karki fita" ya shige ciki ya dakko laptop din yasakai yace gashi maye saika wuce ko " idan tayi wari maji ai " a'a idan ta tafasa ne dan iska,_
_yasa dariya ya wuce saida yaga yashige part din Baba Alhaji yakoma ciki " ki wuce cikin gidan' dama a matse take tafita da saurin ta tana famar tsine mai " d'an iska kawai karo na biyu kenan Allah ya isana ya tsaya kamar wani maye yana kallon mutum_
_tana fita saida ya fada akan gadon ta baya ya runtse ida nunshi yana maida numfashi ya dauki lokaci ahakan kafin ya mike ya fita dakinsu bilal ya nufa suna ganinshi suka Mike "sannu da zuwa yaya" cikin dakewa yace Akwai Abinci a dakina Ku kaimun dakin Baba na_
_yajuya abinshi Safwan yace " yafazo gayen nan bari inyi inbar gidan nan kawai bilal yasa dariya yace " bari nidai inkaimai nasan inada na pocket anjima_
_duk suna zaune adakin baban harma dasu baba ummaru yace " ina fatan lafiya ko da kuka shigo da dare? Cikin girma mawarda yasaba "eh baba wani course zamuyi na sati biyu a jaji kuma jiya jumu'a yakamata mu isa jajin ruwa ya hanamu yanzu sai ranar Monday zamu fara_
_" Toto to Allah ya taimaka "wa innan duk tare kuke aikin Acan? " eh baba yanuna mai laptop baba wannan sunan shi Abubakar, sai wannan kuma Ibrahim sai kuma Nasir_
_Baba yamusu nasiha mai shiga jiki sukansu sun yaba da mutum cin iyayen na kamal bayan sunyi wanka suka shiga ciki domin su gaisa da iyayen su mata_
_sasan Inna Amarya kawai yakai su domin yasan yaran nan na dakin Inna Habi suka gaisa cikin mutunci suka ajiyemata bandir din kudade suka nufi sasan Gwaggo_
_saida gabanshi yafadi ganin su acikin dakin dukansu harsu Safwan tana tsaye da guntun hijabi iya gwiwarta tayi ado cikin Riga da zani na atanfa six piece's tayi wani irin kyau_
_sai tsiya Safwan keyimata "kanwata dama haka kikeda kyau kullum kina cikin katon hijabi, ta murguda mai baki " ai dama ya Safwan kasan nafi budurwarka kyau yadan matso kusa da ita cikeda tsokana " ke ni Nafasa ma dake za ayi Amma kidan cire hijabin nan kisaka gyale muje ma ni zanraka ki_
_Zainab ta kwashe da dariya " ya Safwan Ashe bazakujeba indai saita sa gyale ne kasan ma irin famar danayi ta yadda tasa wannan hijab din_
_Gwaggo tace "ai kedai mijinki Nada aiki wallahi Safwan yace " nine nan mijinta baruwanku muje ki sa gyalen kinji my fiancé_
_ta kwabe fuska cikin sonyin kuka " Allah duk saina hadaku da Inna ta juya cikin Sauri Safwan yariko hannunta daidai da Shigowar su cikin dakin ya wani daka mai tsawa " kai meye haka?_
_"yaya hadani zatayi da Inna ai jin muryar shi yasa duk suka natsu Abubakar tunda yadora idonshi akan Husnah yake furta masha Allah,_
_Babyn badai haduwaba kamar wata bala rabiya, dama abinda yake gudu kenan don yasan halin Abokanshi Akwai son matan tsiya kuma shibaima ba Masan dalili ba da Sam bayaso su ganta gashi ta wani sa karamin hijab_
_tajuyo ganinda tayi mai harda Abokanshi masu irin fuskarshi dole ta gaishesu suka amsa cikin Sakin fuska tace zee muje rana nayi please_
"Zainab ma ta gaishesu Gwaggo tace " Ku shigo mazaje na Ku daina kallon wa innan kyau ya wa nafisu wayewa, duk sukasa dariya banda kamal,
_suna fita su Safwan suka bisu abaya jiyayi gaba daya baida natsuwa kawai mikewa yayi yafita waje sai kaiwa da komawa yakeyi ga direbansu da sojojin dake kula dasu suka taso " do u need something sir? Yace "no Emanuel_
_yana wurin suka fito still suna tareda Safwan Amma Bata canja hijabin ba yayi saurin taresu " kai ina zakuje ne wai? Zainab ce tayi magana " yaya Auren wata kawar mu za ayi shine zamuje mufara shiri_
_Dama yawo kuke zuwa ko? tayi saurin cewa " aa yaya yaune kawai kuma best friend din Husnah ce" wani irin kallo ya aikamata yana mamakin meyasa Yarinyar takeda shariya ne_
_shine kuke yawo da kana nan hijab bakuda manya ne? Husnah tayi carab" ba a dinka mana ba' ya girgiza Kai " OK kubari idan andinka muku sai kufita yanzu Ku koma gida_
_tsabar girman kai kawai ta juya kuwa Zainab ma tabita Safwan kuwa aiya sulale tuni gefen inna Habi suka wuce cikin fushi " kinga bakar maganar ki ta janyo mana ko! Yanzu me zaki fadawa ihsan din idan Bata ganmu ba?_yafita _Inna tayi ta tanbayar su Husnah tayi shiru saida Zainab tayi magana aiko ta hau fada takira bilal " jeka kiramun shi" bilal da tsokana yace " Inna waye? Tace kanin ubanka umaru' duk sukasa dariya yafita Amma har sun fita abinsu cikin gari_
" Inna yaya yafita fa' tace kutashi kutafi abinku kunji Inna Amarya taleko " kai yaya salon kijamai raini yace karsuyi Kice sai sunyi nidai gaskiya aa kuma wallahi kufita kuga ikon Allah
_tace to shikenan zai dawo zamu hadu dashi ne ai, kamal kuwa tunda suka fita Abokanshi ke damunshi "Don irin wannan kyawawan yan mata haka"_
_" gaskiya nidai inason wannan farar sosai" yayi saurin kallon Abubakar din " tanada Wanda take so saika yi hakuri' gaskiya bazan iyaba"_
_cikin zafi yace " look Sadiq na fadama tanada Wanda takeso" so leave my sister Alone, "mamaki abin yabashi sosai saboda baiga Abinda zaisa yaji haushi ba kawai don ya ce kawai yanason sistern shi_
_haka suka dawo yanata faman cin magani yana shigowa suka ci karoda Inna Habi ta balbaleshi baice komai ba sai hakuri dayake Bata ya mika mata ledar da yashigo da ita " Inna kibama yaranki wannan "_
_" takarba tareda godiya ta wuce ta mika masu " gashi inji yayanku" Zainab takarba cikin doki tabude ledar hijabaine dogaye sunkai kala goma hade da nikab dasu sock's_
_inna tace yakarama kananzir fetur kenan itako Zainab sai murna takeyi itakuwa tana tsarama kanta daga yau zata fara saka gyale tunda ba abinda yadameshi da sa hijabin ta bayan yagama kalleta,_
_Samir yakira shi yana fadamai bikin wani Abokin su gobe ya dafe kai " I totally forget wallahi "OK zanshigo da wuri duk kuna tareda su Sadiq ne? Yace yeah saika iso_
_suntashi dawuri suka nufi wurin telansu kafin lokacin bikin yayi bayan sunkarbo tace " muje mu gyara kai yau a saloon,Zainab ta waro ido tareda taba kanta_
_"sis lafiya kalau kike kuwa? Tacire hannunta " lafiya na kalau, yau ina ra ayin hakan ne, haka sukaje aka gyara musu kai tareda yar yada musu design na sajen Abinka da farar fata sukayi wani irin kyau_
_tunbasuyi kwalliya ba yan matan sun fito kamar wasu many an yan matan jami'a koda suka koma gida sai tsiya bilal keyi musu " wannan ai saiku tashi taron don kuna shiga anga kauyawa " hala yau kyauye day zasuyi?_
Ai sai tsalle suna buga kafa yana ganin sun nufi sasan Inna ya ware don yasan sauran,
_karfe hudu suka shirya zuwa wurin partyn da aka hada a Faisal co, center dake cikin Zaria cikin wani irin pink material sunyi kyau kamar ka sacesu ka gudu,_
Zainab tace sis yau meke faruwa ne haka zakije ina hijabin yau cikin tsokana "haka zantafi ko mai bazan yafa ba ina gwaggwaro na yake?
_gaba daya takasa ganema yar uwarta saikace mai Aljanu haka suka gama shirya wa dinkin ya karbi jikinta komai yafito das Inna sai masha Allah kawai takeyi ganin yan matanta sun fito tace " yaudai Yata ba hijabi ko,_
_" eh Inna gyale zamu yafa itadai dadi kawai takeji ta Ciro kudi gashi Ku rike ahannunku kwayi liki, suka amsa suna godiya Allah yabar mana ke innan mu,_
_sunfito kenan suka haduda Samir zai wuce Zainab cikin murna tace " ya Salim ina wuni' shima ganinsu saida yakusa Sakin key din dake. Hannunshi " kanne na ne haka? Gaskiya kun hadu Amma ina zakuje haka?_
_Zainab tace Faisal co zamuje Auren kawar mu ne yace " wow nima can zanje Auren Abokin mu ne Husnah ta yi saurin cewa " SOJA ne shima?_
Ya kalleta sister " kebakyason SOJA ne tace um gaskiya banason AURAN SOJA.
_"why? Just like that. Yayi dariya yace Ku shiga mutafi driver yataso da gudu wani kurtun soja ne yace " no am going with my sisters stay hare_
Zainab ta shige gaba ita kuma Abaya " sis ke kinason AURAN SOJA? Tace nidai suna birgeni sosai wallahi, yace harda ni? Ta sunkuyarda kai kasa cikin jin kunya,
_"look Zainab let be serious, " will you Mary me? Tayi saurin dago idanunta tanaso ta gazgata zancen shi yace yeah Am serious,_
_Husnah na baya tayi kamar Bata jisuba saida yakuma cewa " bani numbern ki saimuyi magana inkin yi tunani" tace bamuda waya dama baba Alhaji yace zai siya mana idan munci jarabawa,_
_OK ni zansiya muku dakaina suna tafe yana janta da hira har suka isa wurin duk suna tsaye awurin ana jiran isowar ango da Amarya ganin motar da ta tsaya duk sai hankalin mutane yadawo Kansu harma dasu kamal dake tsaye da sauran Abokansu ,_
_ganin Motar Samir yasa kamal yasaki murmushi yafara takowa zuwa wurin su saiyaga Zainab na fitowa ta gaban mota saida gabanshi yabuga fatan shi daya Ace Husnah Bata zonan wurin da irin wannan dressing din ba_
_baigama tunaniba tabude kofar tasako kafarta waje tafito zata kulle muffin motar gyalenta ya makale ajikin kofar yafita daga jikinta gaba daya_
_numfashin shi saida ya tsaya kafin yakarasa cikin Sauri yasha gabanta kawai ganinshi tayi a gabanta cikin fushin da Bata taba gani yayiba " koma cikin motar yafurta cikin fushi_
_duk kallon shi sukeyi cike da mamaki samir ne kawai yayi murmushi tareda mikamai key_
Yafada tareda fisgar motar yabar wuri n da d'an ban zan gudu hanya r gida yanufa
_suna tsaya wa ya hango iyayen shi duka maza harma da baban su Samir.......✍_
*What is going to happened fan's? More patients please*
[3/8, 8:39 AM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*
_patients love &Sacrifice_
✍
Golden pen writers Association.
❄we are bearers of Sooo golden pen we write assiduously percieven no pain so magical our creative golden pen be hold our words A product of our pen savour our words for it will couse you no pain.❄
*godiya nake maman Aisha da tukwicin katin da kika turomin Allah yabar kauna Husnah da kamal suna yinki nima ina yinki dozen*
*tareda ke mom sayyed &noor Ina jin dadin comment dinku dake Ummu nawax Allah yakara dankon zumunci*
9&10
_Bude motar kawai yayi yanufi wurin iyayen na su ya durkusa tareda gaisuwa duk suka Amsa cikin farin ciki tareda sa Albarka, itama tabude motar ganin yafita ta gyara gelenta da kyau ta karasa wurin su ta gai shesu cikin girma da kuma ladabi_
_sai fara'a Baba Alhaji keyi ta wuce zuwa cikin gida shima ya mike tareda binta cikin Sauri yakarasa cikin zauren ya fisgota saida ta tsorata_
_bai kyaletaba saida yakaita cikin dakinshi ya kalleta cikin fushi " ubanwa yace kifita Ahaka? Ta marai raice idanunta suka kawo ruwa_
_"ya kamal Zainab ma fa tasa gyalen. Yadaka mata tsawa "just shut the hell off, sai jikinta yafara rawa don ta mugun tsorata da shi sai hawaye_
_har yabude baki zaiyi mata magana yaga tana zubarda hawaye yaja da baya ya zauna bai kuma ce mata komai ba ta tsaya hartagaji tanemi wuri ta zauna_
_yana kallonta ta wutsiyar ido har tafara gyngyadi awurin, ya juyo tareda saita wayar shi yafara daukarta_
_saida yaga zata buge da center table ya yi saurin tareta jin hannun mutum yasa tayi zunbur ta mike tareda zaro idanu cikin mamaki me yake shirin yimata?_
_ganin irin kallon da take mishi yasa yace mata " ki wuce ciki" ai dama kamar tana kan kaya ta wuce da Sauri tana me faman Tara Tara da gyalen tana rufe jikinta har tafita yana binta da kallo,_
_tana fita yayi baya akan katifar shi yana me rufe idanunshi wurin partyn da bai koma ba kenan yana faman tunani afili ya furta "Ya Allah help me,_
_ita kuwa da kuka takarasa cikin dakin Inna Habi tayi saurin tarota" lafiya kika shigo da kuka? Me ya faru dake? Ina y'ar uwarki take? Me yasa kika dawo yanzu Angama ne? Duk ta jero mata tanbayoyin Amma bawanda ta Amsa tana ta rusa kukanta,_
_saida Inna ta gaji tayi shiru dan kanta tace " ya kamal ne ya hana ni zuwa party ya dawo dani." Saboda me? tamike afusace sai gefen gwaggo tasamu harda Inna Amarya tana wurin_
_"Gwaggo k'ara nakawo, tace toh karar waye kuma? " dan gidan Amarya. "Ai nasani wai ke yaya don Allah me Dana yayi miki haka ne? Nasan bai wuce zancen wannan y'ar taki mai ido tsakar ka,_
_"yanzu Gwaggo saboda Allah yarinya ta fita wurin biki ya dawo da ita yabar yar uwarta inba tsana ba me...._
_" kishinta yakeyi ba tsanarta yake ba. Sukaji muryar Baba Alhaji dake shigowa tareda Aminin shi Alhaji Mahmud, wato mahaifin Samir,_
_tayi saurin matsawa daga ciki tareda gyara mayafin jikinta " sannunku da shigowa yaya" suka Amsa " Yauwa Habiba inna Amarya ma ta gaishe su,_
_Alhaji Mahmud yafara gaida Gwaggo kafin baba Alhaji suka samu wuri suka zauna, su Inna sunmike zasu fita yace "kudawo " maganar ya'yan Ku ne_
_Duk suka samu wuri suka zauna " Gwaggo tace " na am Allah yasa muji Alheri. "Alheri ne ma insha Allahu, " mungama yanke hukunci nida Amini na akan hada yaran mu Aure,_
_"nasa anyi min bincike akan wannan yarinya da ya kawo Amma hankali na bai kwanta da lamarin ba a gaskiya shiyasa mukayi shawara nida Alhaji zamu hada Samir da Zainab Husnah da kamal._
_Alhamdulillahi" nagode Allah da yanuna min wannan rana Allah yasa ayi a sa'a yakuma sa Albarka. Yakara hada kawunan ku, duk suka Amsa da Ameen_
_"Inna Habi duk jikinta yayi sanyi don tasan Husnah bazata so wannan hadin ba Amma tafi kowa farinciki zuciyar ta_
_Kamal Abokanshi sai faman kiranshi sukeyi yaki daga wayar har zuwa dare lokacin da su Zainab suka dawo gida tareda Fatima suna ta tanbayar ta me ya faru?_
_tayi musu shiru har Fatima tawuce gidan su Bata kula suba don tsabar haushin da take ji gaba daya takara tsanar shi a zuciyarta Bata ko son koda hanya ta hadasu dashi_
_Baba Alhaji ya tarasu su hudu tunda taji Baba na kiransu gabanta ya mugun faduwa "me ya faru aka tarasu harda Wannan mugun mutumin?_
_Baba ya gyara murya tareda cewa ina fatar Kunsan dalilin taraku anan "kamal da"Samir, mun gama yanke shawara akan zancen Auran naku zuwa karshen wannan watan insha Allah,_
_gabanta ya wani mugun bugawa " Aure? Ita da kamal Baba yake nufi kome? Tayi nisa tana yima kanta tanbayoyi Baba yakira ta "Husnah' tace " na'am Baba._
_"kinji Abinda nake fada Auren Ku keda ya'yan ki Zainab da Samir. Ina fatan zakuyi min biyayya kamar yadda kuka saba, tunda yafara magana yake kallon ta ta gefen ido,_
_yana so yaga reaction dinta Amma bai fahimci komai ba har Baba ya sallame su suka shige cikin gidan Zainab kam tana cikin farinciki, domin tasan Allah ne ya Bata miji na nuna ma sa'a,
_"Husnah kam gefen gwaggo ta wuce tana shiga ta rushe da kuka mai uban karfi Wanda duk ya firgitasu,"Allah ya rabamu da kuka mudai inji Gwaggo,_
_Inna Habi ta taso da saurin ta " me yafaru? tsabar haushi inna Amarya tace " wallahi kina cewa tak saina sabautaki_
_saboda tasan da lilin kukan nata kuma tasan idan Bata kwabeta ba fada zatayi kuma ai ana barin halas kodan kunya,_
_Inna sai faman lallashi n ta keyi Amma ina sai famar ajiyar zuciya ta ke tsabar bakin ciki yasa Inna Amarya barin wurin ta nufi nata gefen yar karamar wayarta ta dauka takira yaranta mata dake Aure,_
_tareda yimusu bayanin komai ta Dora da cewa " Ku kwabi y'ar uwarku tun Bata jamin abin kunya ba nasan yau idan mahaifin ta yaji sai ya kusan yi mata baki_
_sun tausa mahaifiyar tasu kafin suzo gidan ita kuwa Inna Habi mijinta tanema tayimai bayanin cewar za ashigar mata hakkin y'ah don Bata so, Yace "Habiba' " idan har kika ga ba ayi wannan Auren ba to bana Raye,_
_"banga dan da zamu Haifa ya kasa yimana biyayya ba kuma shima kamal din na fada mai wallahi ko bayan baraina ya sabawa zancen dan uwa na ban yafe mai ba,_
_dole tayi shiru don batada tacewa abinka da mace ta gari sai tafara lallashinta hadi da nasihohi"kiyi hakuri Husnah da yardar Allah bazaki tabe ba bazan taba yarda dan gidan Amarya ya cuceki ba kinji kiyi shiru Abunki,_
_gaba daya tasan Bata kyauta ba yanda take nuna ma Inna Habi Bata kaunar danta kuma gashi tana kan lallashi n ta_
_Amma ya zatayi har cikin ranta Bata kaunar kamal ta tsaneshi......✍
*Happy for the next level Fan's*💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃
*Congratulations Baba buhari tukwici gareku masoyan APC*
*muhadu a next level*💃
[3/8, 8:40 AM] Feenat Marubuciya: 🌸🌸🌸🌼🌸🌸🌸
*AURAN SOJA*👨✈
_patients love & sacrifice_
✍
Golden pen writers Association.
❄we are bearers of Sooo golden a pen we write assiduously percieven no pain so magical our creative golden pen be hold our words A product of our pen savour our words for it will couse you no pain❄
*Welcoming to the next level fans Zinariya wannan nakine Alherin Allah yakai miki a duk inda kike. Page din sai yanda kikayi dashi ina Alfahari dake*
11&12
_kamal sun shirya tafiya washe gari suna zaune da samir yace " Don' yakamata Ku gana da yarin yar nan tun kafin A daura Auren ko._
_Ajiyar zuciya ya sauke " Samir kana ganin zan iya yimata magana ne? Yana maganar kamar bayaso, kasan sunada raini ne yaran kar taga kamar wai nadamu da ita ne._
_"kadamu da ita mana, da baka damuba da baka dakko ta jiya Awurin biki ba kuma nasan saboda kishinta da kake yine yasa hakan,_
_kallonshi yayi irin kallon bakada hankali " Samir remember she is my sister I must protect her no matter what, ya kwashe da dariya " ita kadai ce sister dinka? Me yasa kabar Zainab ka dakko ta ita?_
_"look Don nasanka tun muna yara nasan Abinda kakeso I no your hidden secret kana tunanin bansan meke faruwa ba ne? Ya kalleshi yace "u don't no anything,_
_" haka kace OK ni bari infada maka Abinda yake raina,"I love Husnah" yawani irin juyo wa "what? Matar taw.... Saikuma yayi shiru Samir ya kwashe da dariya sannan yace_
_" to be sincere I love Husnah. ya wani hade girar sama data kasa " not any more, tun lokacin Dana fahimce ka nakuma ga secret dinka a diary na cireta A zuciyata_
_"kamal koda ace ni nafara son Husnah zan iya hakura da ita inbar maka saboda nasan saboda ita ka kasa yin Aure duk tsawon rayuwar nan,_
_"nikuma na tsaya biye maka but am still happy saboda nima nayi sa ar mata and I promise you zankula da ita kamar raina ko ba komai kunfito ciki daya don haka Dole inso jininka_
_yayi Ajiyar zuciya "tank you frnd, cikin sanyin jiki, Yacigaba da cewa " yanzu inkirata ne Kuyi magana? " no. " but why? " bcos she doesn't love me impact she hate me,_
_"cikin wata irin murya mai ban tausayi, shi kan shi Samir he feels bad yasan Abokinshi yana bukatar kulawar ta don yayi dakon so shekara da shekaru shi kadai batareda yafada ma kowaba'_
_"zankirata inji ra ayinta kafin mu tafi' suna cikin maganar suka fito tareda Zainab dama suna zaune ne a kofar gidan nasu yau ba fadawan kuma Abokanshi su sunwuce Kaduna,_
_har su odilin shi duk suntafi kafin yazo Samir na ganin su yamike don sun bala in burgeshi cikin wata blue atanfa Riga da sket hijab dinsu tree quarter sunfito sunyi bala in kyau kamar wasu taurari_
_shi kanshi ogan yakasa daurewa kallonta yakeyi, ita kuwa tunda tafito ta gansu ta daure fuska kamar Anyi mata mutuwa Samir ya matsa kusa da su " gimbiya ta ina zuwa da safen nan ne ?_
_"zamuje tudun wada gidan Aunty kareema' tafada cikin fara a tareda kuma kunya Husnah kuwa ko gaisuwar ma basu samu ba tawani dauke kai zata wuce"_
_"haba Amaryar mu irin wannan dauke kai? Da girman kujerar ki uwar gidan colonel kamal Ibrahim, ji tayi kamar ta tsala ihu batasan lokacin da tawani zabgawa Samir din harara ba"_
_daga nesa yana ganin ta saida yaji wani iri har cikin ranshi "bari inkai Ku ko, Samir yafada, sanin Husnah bazata yarda ba yasa tace mungode ya Samir zamu biya nan gidan su Fatima ne mutafi tare,_
_" OK karku hau mashin to yaciro rafar yan Dari biyu yamika mata Ku hau napep da wannan ta sunne kanta Aa ya samir inna ta bamu na mota ai"_
_ya karbi yar karamar Jakarta ya bude ya saka mata yace banson musu kuje kawai tayi godiya tawuce saboda Husnah harta shige gidan su Fatima_
_yana dawowa kusa da Kamal yace "kaga irin rainin ko? " Hmm zata daina Kaine zaka saukar da kanka komai zai daidaita'_
_" zata raina ni kawai idan taso ayi zaman lafiya za ayi idan kuma taki ita zataji jiki, kar ayi haka Don karamar yarinyace fa yanzu suke eighteen_
_" sai kuma ta raina ni? Karshen raini kuda zakuyi Aure har gadon baccin ka saita gani girman naka ma ai nata ne yace " Allah ya kiyaye ya zatayi dani?_
_" y'an da kowace mace keyi da mijinta kabar raina Allura karfe ce" yace " mubar zancen kawai"_
_sun isa gidan Aunty Kareema tace " aini nasan badon Inna ta aiko kuba bazuwa zakuyi ba bilal ma da yake namiji yafiku ziyarar y'an uwa suka fara dariya tace " kaga Amaren nan da sati hudu. Ai tuni Husnah ta Bata rai"_
_"waike dama da gaske kikeyi bakyason Auren? " "Husnah meye illar yayan mu Allah yabaki miji na kyace raini Amma kinason kiyima kanki bakin ciki ga yar uwarki ta karbi nata hannu bibbiyu Allah ya shirye ki_
_"dama naso inzo gobe don haka bazan zoba sai zuwa jibi idan na gama hado muku kayan gyaran jiki don gyaraku zanyi tsab zankira murja ma inyimata bayani itama ta shirya"_
_niba mai yimin gyaran komai " to Mara kunya zamu gani, haka suka wuni agidan har yamma kanin mijin Aunty kareema yashigo cikin falon nasu dauke da yaronta da yaje dashi gidan su_
_tunda ya shigo idonshi ke kan Husnah gaba daya ta tafi da imaninshi dama sun gama shirya wa suka mike Aunty zamu tafi tace tana zuwa, tabasu sabulai da su mayuka sukaiwa su Inna sukuma tabasu kayan make up sukayi ta godiya har da Fatima tace " Ismail don Allah ka saukemin su agidan mu'_
_yamike zunbur tareda cewa "bada muwa kumu je sai kallonta yakeyi itakuwa tawani daure fuska Koda suka fita Zainab da Fatima suka yi saurin shiga baya dole batada zabi ta shiga gaban motar_
_tunda suka dauki hanya su Zainab keta zabga zance ita da Fatima itakam tayi tsit har suka isa unguwar ta su Alokacin jama ar na nan dankam a wajen,_
_kamal dama tun da suka fita ya kasa zuwa ko ina sai kallon hanya yakeyi gaba daya ranshi ya gama baci sai kawai yaga mota na tsaya wa dan nesa dasu don Fatima tace A sauketa a kofar gidan su suma sukace anan zasu sauka,_
_" mungode cewar Husnah da har ta bude mota zata fita suma sun fita suna godiya yace " jimana y'an mata' Husnah dake kokarin fice warta ta runtse ido aranta tace nasan a Rina'_
_"don Allah kibani number wayar ki mana inaso muyi magana idan bada muwa " aa bawata damuwa kawai wayarce ban ma da ita harzata fita ta hango fuskar kamal kamar hadari tadan kara juyowa_
_"munfa gode Allah yabiya yace bakomai yiwa Kaine' sai mun kuma haduwa koda tafitan saida takara tsaya wa ta window ka gaida gida cikin fara'a,_
_shima mamaki yakeyi Meya canja ta yanzu yanzu bayan tun lokacinda ya ganta fuskarta a hade" why the sudden change?ya daga Kafada kobanza nasamu hadaddiyar baby"_
_Zainab harta fito daga cikin gidan su Fatima tace mu tafi ko "zaki hadu da ya kamal kinga fuskar shi kuwa,wama ya aikeki sauraren Ismail, " ra ayina ya aikeni ,"_
_taja bakinta ta tsuke don ita batada fitina suna kaiwa wurin su tayi saurin shigewa dama tunda yaga zuwansu ya shige zauren gidan, suna shiga yatare hanyar " ina kuka tsaya ?_
_ita kanta datake takama da tsiwa ta tsorata dashi bare kuma Zainab " kunake tanbaya? Ina kuka fito wane katono kuka shigo motarshi ?" Wallahi yaya kanin mijin Aunty kareema ne_
_"ki wuce ciki da Sauri Zainab ta wuce zata bita yace " bada keba ki tsaya "tasan da ita yake tayi burus zata shige ya fisgota tareda dawo da ita_
_what do you tink of your self? me wannan gayen yake fada miki ? Cikin rashin tsoro tace " sona yakeyi ' saida ya runtse idanunshi yadaga hannu kamar zai kaimata duka ya naushi iska_
_"what is your Answer to him? " that I love him too yawani irin juyowa saboda Tabashi amsa kai tsaye she don't even care how he is going to feel,_
_cikin minti biyu idanun shi sunkada sunyi wani irin ja cewa kawai yayi "go' yafada yana fitarda numfashi, ita kuwa taji dadin y'anda tabata mai rai kuma yanzu tafara baimaga komai ba"_
_dakyar ya saita natsuwa r shi yafito masallaci kawai ya nufa saboda ankira magrib koda aka idar shibai fitoba tsaya wa yayi cikin masallacin har zuwa isha shi kadai yasan me yakeji acikin zuciyar shi,_
_bayan isha Baba Alhaji yakuma tarasu shida Samir akan zancen inda za a ajiye musu matansu,_
_"nasan yanayin aikunku yanzu da wuya kudawo nan kusa kila sai bikin yazo gab, Samir yace baba ni inada gida Anan cikin barikin dake jaji kuma anan unit dina yake, ina ganin can din za akaita kawai,_
_"to shi kenan kai kuma kamalu ya za ayi kaida ke Lego's? ya gyara zama " Baba dama naso idan mungama course din da zamuyi sai mu tafi Lego's din nida ita"_
_"Alhamdulillah saiku fara shirye shirye zuwa nan da sati hudu. Suka dukar dakai "mungode Baba Allah yakara girma da lafiya"_
*washe gari*
_Samir yakira Zainab yabata wayoyi guda biyu itada Husnah Acikin kwalayen su aiko tana shiga cikin gidan tasa ihun murna sai dakin Inna ta mikawa Husnah dayar" waye ya bamu wannan wayar?_
_"ya Samir ne tace " OK tnks suka fito da wayoyin Samsung galaxy note 7 Husnah tasa ihu sister kintuna irin wayar nan ce nake nuna miki a pz ranar nan har kike cewa uban wa zai iya siyamin,_
_"kidai duba dakyau wannan fa anrubuta dubu hamsin ajikinta "eh wallahi itace sai ihu sukeyi maha kurci mawadaci gashi farkon wayar su sun samu mai tsada haka suka nunama iyayen su suka sa Albarka,_
_daba sunada numbobin kawayensu arubuce sai kiransu sukeyi suna fada musu sunyi waya suma,_
_kamal har ya wuce bai kuma y'arda sun haduba donta batamai rai fiyeda tunani, bayan kwana biyu Aunty kareema tazo hargida taroki Baba cewar tanaso ta tafi da kannen ta zatayi musu gyaran Amare_
_Yaji dadi kuma yabata damar tafiya dasu Inna Habi tace itadai ba a. Kyauta mata ba duk tsawon shekaru basu taba barinta ba sai yau, Inna Amarya tace suda zasubar gidan ma gaba daya yaya yake nan?_
_yanzu y'an matan ta tafiya zasuyi subarta duk jikinta yayi sanyi kareema tace " Inna kinfison su dani ko don nikoda nayi Aure baki wani damuba Amma su yanzu aronsuma dakyar kika bani,_
_"kareema lokacin Ku murja na nan Amma su gaba daya za adebemin su, Husnah ta rungumeta "Inna ta ba inda zanje inbarki muna nan atare Inna Amarya tace kudaije gidan Auren tare shi yafi_
_Zainab tace " nidama banbanci ake nunamin anan gidan don haka gwara ma intafi " to Mara kunya,_
_Agurguje dai komai na tafiya yadda yakamata sungama shirya komai har akwatunan su saiti biyu kowacce kayane masu balain kyau da tsada komai yaji masha Allah_
_Wata mata Samir yasamu tahadomusu komai gefen bra tace kawai yakira Amaren yatanbayesu aiko bayan kiran Zainab yace gimbiya size nawane kuke sawa? tace mene? Kai tsaye yace " bra'_
_ido waje Tacire wayar daga kunnenta ta kashe ta ajiye agefe dama duk suna tareda su Husnah anayimusu gyaran jiki tace "lafiya kike zaro ido? tace" ya Samir ne wai infadamai size nawane muke sawa "to shine me nidai kinsan 37 ne takalmina kema kuma haka tace ke banza breziya yake nufi,_
_itama ido waje tace y'an iskane sojojin nan wallahi ina ruwan su da wannan maiyimusu dilka me zatayi inba dariya ba takira Aunty kareema tace wallahi kinada aiki sosai agaban ki ta yimata bayani tace yara kamar yan kyauye bani wayar_
_Ita. Ta yimai bayanin komai yace mungode kareema ki dan gyara mana Amaren mu dakyau Bari ma inhada tukuici atake yamata transfer na dubu Dari yace saima sun hadu_
_gefen gida kamal yasaki kudi komai antanada tunda ga kan abinci har zuwa kayan dakin Zainab don yafada ma Baba komai Akwai agidan shi shima samir agidan su ne za a. Saka na Zainab'_
_don duk wani SOJA bayason A kwashi kaya daga gidan Ku akaimai saidai su suyi kayan su_
_su Husnah sunyi wani irin kyau saboda gyaran da suka sha gaji wani hadi datayi musu sukesha komai nasu yakara cikowa musamman Husnah da kirjin kamar yafaso Riga_
_Fatima kanta saida tayita sanyin hadu war su " gaskiya Aunty tayi kokari sojoji zasu dibi angara tafada cikin tsokana "Husnah kinga kirjinki kamar anyi pompin din su?_
_Zainab tace ya kamal zai more, cikin jin haushi tace " duk wani maye saidai yakalle su cikin hijabi duk matarshi kuwa.......✍
*wai hakane fan's? nidai baruwana zamu gani muje*
*nidince dai Taku har kullum maman Ammar marubuciyar HARAMTACCIYAR SOYAYYA*