Bismillahirahamani raheem..
Page1⃣〰5⃣
Nashiga uku yar nan zatajawomin abin fade acikin kauyen nan ya Allah kataimakeni karta fita ,dagudu tafito cikin dakin tana fadin ai wlh tunda zainabu ta ta6ani yau saitagane batada wayau ba babanta maigari ba ko mai kano ne wlh saitagane kurenta zata fita kenan matar tariko hannunta tanacewa safi bazakije koina ba kallon hannun matar takeyi tanacewa gogoji kirabudani wlh yausainayiwa zainabu illa kuma saitagane ta ta6i safi jikar gogoji tafisge hannunta cikin Sauri tafita daga gidan gogoji ko tsaye take kyam kamar andasata saifadi take Allah kasa karsu hadu,,,cikin azama itama gogoji tafigi mayafinta tasaka takama hanyar fita kome ta tuna kuma saita dawo ta zauna tazuba uban tagumi bayan kamar minti goma shabiyar saiga safi tashigo tanacewa hoh wlh saini safi jikar gogoji yar albarka albishirinki gogoji ai wlh na turmurmusa hegiya jina jina naimata tanacan kwance a dandali tana numfarfashi kamar jakar datai aikin wahala ai yau nacika burina dole naje dandali nahada babbar wasa ,,,gogoji ko rai a6ace tanufo ta tana isowa ta watsa mata mari takara watsa mata harsau uku aiko saiga safi tazube akasa tana birgima tana ihu saicewa take wlh gogoji ko kasheni zakiyi bazan dena cin uban wayanda sukeson rainani va kuma wlh yanzu nafara saidai ki kasheni domin bazan yarda wasu ya'ya surainani ba kosu nemi su wulakantani va wlh Allah yayimin daraja danhaka bawanda zairainani nakyale ehe,,gogoji tace aisaikiyi maras kunya tamike taje kusada gogoji tarike hannunta tanamurzawa tanacewa gogojina kiyi hkr kinsan banason 6acin ranki ,,,ture hannunta gogoji tayi daga nata tanacewa karya kike bakison 6acin raina amma kuma kullum saikinyi abinda zaisa raina yana 6aci ahakan ne kike kin 6acin raina,,,,,,,,,,, safi tace gogoji kiyi hkr bazan sakeva kinji gogojina tana yimata murmushi cikin jindadi gogoji tace shikenan na hakura amma kada ki kuma ,,,tsalle safi keyi tana cewa wayyo gogojina babu kamarki aduk fadin kauyen nan shiyasa nake kara sanki araina Allah kabarni da gogojina,,,
Da yammaci gogoji na hada murhu domin nadaura girkin dare taji sallama ta amsa batare data juyo ba ,jitayi ance barka dai gogoji megari ne ya aikoni cewa yanason ganinki yanzun nan batare da 6ata lokaci ba cikeda faduwar gaba gogoji tace toh gani nan zuwa mekawo sakon yajuya yafita itakuma gogoji tadau mayafinta tayafa tafito tana kwalawa safi kira tanafitowa tace toh lambarkice tafito agun megari gashinan ya aiko intafi damade nasan haka zaibiyo baya Dan haka ki kula da gd,,safi cewa tayi toh su gogoji agaida megari,,,daquwa gogoji tayi mata sannan ta tafi ,,,gogoji nafita safi tayi dariya tadaga hannu sama tanacewa ya Allah kasa megari yakoremu awannan gari ameen ya rabbi ,,,,,,tofah nidai hanci baki ido duk nabude donjin irin wannan addu'a da safi keyi meban mamaki,,,,,,,
Wacce safi,,,___safinatu shine asalin sunanta mahaifiyarta kubra ya'ce ga gogoji ita kadai Allah yabawa gogoji diya mace sai maza guda biyu habibu da Suleiman ,,habibu shine babba sai Suleiman kebi masa sai kubra itace karamarsu ,,,su haifaffun kano ne cikin karamar hukumar tofah anan iyayensu da kakaninsu suke malam ibrahim shine mahaifinsu Allah yayiwa malam ibrahim rasuwa tun kubra Nada shekara takwas aduniya dalilin haka yasa mahaifiyarta salamatu take bata kulawa kuma tadauki son duniya tadaura mata awannan lokacin babu wata diya mace dake karantun boko shiyasa basufin shekara goma shadaya agida ake aurar dasu haka yakasance akan kubra lokacin data cika shekara shadaya akace tafiddo miji aimata aure tace ita bawanda takeso sai Dan limamin garin hankalin mahaifiyarta salamatu yatashi sosai itada yayyen kubra saboda sanin dasukayi cewa Dan liman din bashida tarbiya cikakke amma saboda basuson 6acin ranta haka suka rinka lallashinta akancewa zaabadata gawanda takeso koda sagir yazo kubra tafada masa yadda sukayi da iyayenta kansun amince da aurenshi yayi farinciki sosai anan yake tabbatar mata dacewa yanakomawa gida zaisanar da mahaifinsa haka ko akayi yana isa gida bayan sallar isha yasami mahaifinsa yasanar dashi kwanan zancen liman yayi Jim kadan kafin tace shikenan kaje zanyi shawara da yan'uwana duk abinda suka yanke shikenan ,,,bayan fitarshi liman yasa aka kira mashi saidu da iro kannenshi yayi masu bayanin abinda sagir yazo dashi baffa saidu ahiyafara magana cewa yana ganin auren shi zaifi kyau da alkhairi kilama yazam sanadiyyar shiriyar sagir din baffa iro ma yadaura dacewa kwarai nima ina hangen haka liman yace toh shikenan tunda abun yakasance haka gobe saikuje atsaida magana kome kukagani sukace hakan yayi Allah yakaimu*******
[20/11 3:07 pm] FAIZA: 💁SAFINA💁.
Written by Aysha Wakili
(Mrs ahmed)
Page5⃣〰1⃣0⃣
Ba'adauki lokaci metsayiba akayi bikin kubra da sagir iyaye hankalinsu yakwanta masoyanma suna jindadin rayuwarsu ,,,bayan aurenne yayyen kubra habibu da Suleiman sukabar kauyen sukaje cirani a Lagos ,,,bayan shekara biyu da auren kubra da sagir lafiya lau suke zaune saidai abinda yafara basu damuwa baiwuce rashin haihuwa ba haka suka shiga Neman taimako kala kala Amman shiru kakeji harsaida kubra takai shekara tara sannan rana daya Allah yabata ciki aiko farinciki agun kowani hannun iyalan baa magana sukuwa saimurna sukeyi suna rainon cikinsu harya kai wata tara ranar haihuwa akejira__ranar wata juma'a da daddare kubra nacikin bacci ta tashi firgigit kamar antsunguleta tana tashi sagir ma yamike yana tambayarta lfy kuwa tace masa marartane keciwo yayi mata sannu sannan yaauko ruwan addu'an da liman yake mata yabata tasha aiko tana aje kofin cikin na hautsinewa nan tafara ihu tana cewa sagir yatemaketa zata mutu tanayi tana salati tariko hannun sagir tanacewa sagir kayafemin laifin danaimaka kayafemin tanayi tana salati yace kubra bakiyimin laifin komeba kuma ko kinyima nayafe maki bari naje nakira hajiya tazo tadubaki tariko rigarshi tabaya tanacewa basai ka kira kowava sagir tsaya ,,,wani kara datasake yasashi juyowa daidai nan jaririya tafado tana chanchara ihu nan yafita dagudu yana kiran hajiya matar liman ta biyu kodasuka iso suka iske kubra ta nan nade jaririyar cikin zani tanarike daita tana hawaye SAGIR yaiso kusa daita yakar6i jaririyar yabawa hajiya tafara gyarata daganan hajiya tace yabasu guri tagyara uwar bayan fitarsa ne hajiya tashiga gyara kubra bayan tagyarasu tsaf koena yayi fes kamar ba haihuwa akayi va,,,,tace baritaje tafawa liman bayan fitarta sagir yashigo yaiske kubra durkushe rikeda ciki tana salati dagudu yaisa gareta yana tambayar lafiya kubra kai tadaga masa sannan tanunamasa cikinta yanaki idonsa gun jini yagani yanata zuba kamar anbude famfo salati yafarayi yatashi da niyyar fita tarikoshi tace karka fita sagir katsaya nafiso namutu ahannunka kaji mijina tanayin maganar he dawani irin yanayi kanajin yanayin kasan tanacikin mawuyacin hali nan da nan idon sagir suka kawo ruwa yace kubra bazaki mutuba zaki tsaya muraini safina sunan dasuke burin sawa diyar dasuka Haifa kenan innamijine kuma sawban,,,,,,kai tagirgiza masa tacigaba dacewa nayi burin inraini abinda zanhaifa saidai hakan bamai yuwuwa bane sagir inarokonka daka yafe dukkan laifin danaimaka nima kuma nayafe maka sannan ko roka min gogoji tayafemin dasauran mutani bakidaya sannan inaso ka kulamin da safina sosai kariketa da daraja domin itace sanyin xuciyarmu zanyi farin ciki idan naga kariki safina dakyau Allah yabaka ikon kuladaita ma'asalam,,,,,,,,tana rikeda hannun sagir tana nanata kalman shahada harcan sagir yaji shiru yana jijjigata yaji shiru yanaduba idonta yaga babu bakin saifari ga hannunta yayi sanyi sosai salati yasake hade da ihu nan shima yafadi sumamme hajiya tana hanyar shigowa taji ihu dasauri takaraso tanazuwa taga mutani biyu kwance ba numfashi dagudu taruga tana ta6asu amma shiru kakeji nan tafita takira liman dasauran jama'a kodasuka iso aka watsa masu ruwa sagir yafarfado yana fadin kubra karkiyimin haka Dan Allah kitashi ,,,,,,,,,kitashi muraini safina cikin so dakulawa karki barni kubra yaje yarike liman yanakuka maiban tausayi liman shima kansa saida yazubda hawaye sbd tausayin danshi dakuma babban rashi da sukayi domin rashin kubra babban gi6ine ga rayuwarsu bama iyalan liman kadaiva harda mutan kauyen baki daya domin kubra mutumce saidai fatan Allah yaimata rahama ameen ,,,,,,koda aka aikawa gogoji batun rasuwar bata girgizava sbd tanada yakinin kubra zata dace da rahamar ubangiji SBD tasamu shaida na kwarai abakin mutanin kauyen saifatan dacewa,,,,,,ranar addu'an bakwai aka radawa diya suna SAFINA kamar yadda mahaifinta yabukata hajiyace tacigaba darainon SAFINA hartsawon wat takwas lokacin SAFINA tayi wayo hartana tafiya koina tanashiga yarinya kyakkyawa daita gwanin shaawa kowa yaganta soyake yadauketa gata bulbul daita sambarka ,,,,alokacinne SAGIR yace yanaso shima yafita Neman kudi dazai rinka kula SAFINA liman badan yasoba dole ya amince masa ,,,kodayajewa gogoji damaganar tace aiko dole yamaido SAFINA hannunta sbd itakadai taragemata dazata kalla tajidadi dama abindayasa bata kar6ota va ganin sagir din yana nan kuma tanaganinshi amaimakon kubra Amman yanzun tunda zaitafi yakawo mata SAFINA tarinka ganinta amaimakon shida kubra baijada itaba sbd yasan gsky tafadi yaje yafadawa liman yadda sukayi liman ma ya amince ana gobe zaitafi yadauki SAFINA yakaiwa gogoji yafada mata asubanci zaiyi danhaka ga SAFINA nan takula mai daita tace karyadamu tashimai albarka yatafi cikeda kewar diyar asuba nayi Yakama hanya tunfitar da SAGIR yayi baikara dawowa ba,,,,,,bayan tafiyarsa da satibiyu wani al'amari yafaru a gidan liman inda gobara takama gidan bakidaya ba abinda aka fitar a gidan komai yakone hatta mutanin gidan baaga kodaga gawar mutun dayava toka aka kwashe Allahu Akbar Allah yajikan wannan ahali anyi rashi,,,,,,,,
Bayan shekara goma shadaya SAFINA tayi wayau tazama matashiya gakyau ga ilimi yanzu haka tana aji shida a primary a arabi kuma tanada izu talatin tanada tsayi amma ba sosai ba farace ammn bacan can ba tanada tsayin fuska da dogon hanci gadaradaran idanu dasukayiwa fuskar kawanya ga bakinta Dan karami labenta masu kyau kamar tashafa jambaki intai dariya kumatunta duk biyu saisun lotsa komai yaji masha Allah SAFINA akwai ladabi da biyayya ga girmama nagaba daita duk inda taganka saita gaisheka kodako batasanka ba haka halinta yake matsalarta guda dayace batada hakuri in anta6ota amman inbakata6o taba bazakajita ba SAFINA kenan ta gogoji yar albarka kirarin da gogoji take mata kenan lokaci lokaci ,,,,,to bari muje muji meke wakana gidan megari da gogoji******
[20/11 3:07 pm] FAIZA: 💁SAFINA💁.
Written by Aysha Wakili
(Mrs ahmed)
Page1⃣0⃣〰1⃣5⃣
Da Isar gogoji gidan megari tai sallama aka amsa tanemi guri tazauna tace ranka shidade ance kana nemana maigari yayi gyaran murya yace gogoji dama magana ne akan jikarki safi dazun aka kawomin zainabu rai a hannun Allah wai safice taimata duka kuma harta fasa mata baki toh a gsky bazan dauki irin wannan wulakancin va a garin nan sbd tunbayau ba nake shari'ah akan safi amma yau abun kaina yadawo danhaka nabaki nan da sati daya kutattara kubarmin gari inbahaka ba zanhadaki da hukuma sufitar dake da jikarki,shiru gogoji tayi tana sairaron maigari can tanisa tace toh maigari naji kuma insha Allahu bazamuma kai lokacin daka diba mana amma inaso kasani badan Koran dakayi mana ne zaisa mubar garin nan ba saidon dama safi tadade tanason mubar kauyen nan nice dai naki yards sbd mahaifata ce amma yanzu dole zamu barmaku kauyenku amma bawai gabadaya ba kome Daren dadewa zamu dawo natamike tace nagode maigari tafice daga fadar ,,,,,tana isa gida takwalawa safi kira saiki zuba ruwa akasa kisha hakanki tacimma ruwa maigari yakoremu yabamu satidaya mubar masa gari amma bazamukai satinba yauma Dan yamma tayine damun fice musu daga gari aiko tuni safi tadaka tsalle tafara tika rawa tanacewa Allah yayi Allah abin godia gogoji Allah yakar6i addu'ata zamubar wannan kauyen muje wani guri muyi rayuwa mai inganci gogoji dai kallonta take tace wai wani rayuwa zamuyi datafi Wanda tafi wannan damuke ciki inganci safi tace haba gogoji u won't understand malamin makarantar mu yace inkana birni rayuwarka dabance sannan zaka zama wani Abu arayuwa shiyasa nakeson mubar kauyen nan sbd inaso nazama wani Abu arayuwa nataimakeki gogoji kobakiso cikeda al'ajabi da jindadi gogoji takalleta tace inaso safin gogoji Allah yacika maki burinki inatare dake Dari bisa dari ,,,,fariciki ne yakama safi taje tarungume gogoji tace Allah yabarmin ke gogoji ,,,nan suka hau hada kaya suna zubawa ajaka cikin darema basuyi bacci ba sunata hada kaya asuba nayi bayan sun idar da sallah suka fita suka kama hanya sai cikin kano kodasuka isa garejin naebawa mota suka sake hawa xuwa garin Kaduna karfe goma suka isa garin Kaduna kodasuka sauka a unguwar ma'azu suka sauka sukaje gurin wata maisaida abinci suka siya bayan sungama cine suka fara tinanin inazasu nufa yanzu ,,,,,babu Wanda suka danhaka suka yanke shawarar Neman aikatau haka suka dinga yawo agarin Kaduna har yamma likis basu samu aykin va bayan sunyi sallar magriba ne suka tashi aukacigaba da tafiya agefen titi suka zauna kamar wasu almajirai harkarfe takwas nadare agefen titin sukayi salla ,,,,,,
Suna zaune harkarfe goma saura safi tafara bacci a jikin gogoje suna nan ahaka har karfe shadaya da yan mintoci saiga wata dalleliyar mota tazo tawucesu cankuma saiga motar tadawo glass din motar yasauka nacikin motar yace mama mekukeyi anan da wannan dare gogoji tace Dan nan gurin kwana muke nema mu bakine daga kano mukazo yace kuma bakusan kowa agarin bane kodai baku gane gidan ba gogoji tace bamusa kowava Dan nan yayi shiru can yace toh zanbaku gurin kwana zuwa gobe sai musan abinyi aiko nan gogoji tahau zubamai kwandunan albarka ta ta6i safi tace ke tashi Allah yaturo mana mai taimako aiko cikin sauri safi tamike tana mutsike ido nan suka shiga motar yajasuka tafi cikin minti dabaifi ashirin ba suka iso cikin unguwar sarki Horn yayi aka bude masa tangamemen gate din gidan yasa hancin motar cikin gidan parking space yanufa ya faka motar sannan yafito yabude masu suma suka fito yadau jakar kayansu yayi gaba suna binshi abaya harsuka isa wani tangamemen falo dayasha kayan alatu namore rayuwa sudai sun tsaya kallon kauyencinsu harya shige dakin ya aje masu jakar kayansu yafito suna nan suna kalle kalle murmushi yayi yace haba kaka kuje kuyi wanka kuci abinci Ku kwanta kuyi bacci dasafe kwayi kalle kallen aiko gogoji tace toh Dan nan mungode Allah shimaka albarka safi tajuyo tace yaya mungode Allah yasaka da alkhairi juyowa yayi ya kalleta da mamaki sbd jiyayi muryarta sak iri daya Dana kanwarsa little kubra baikare shiga rudaniva saida suka hada ido sak little kubra bata enda basuyi kamaba ya ilahi wacece wannan mekama da sis dina ta6oshi tayi da hannu tanacewa yaya inane dakin cikin Sauri yadawo hankalinsa yanuna mata dakin da hannu taja gogoji suka shige,,,,,,,,,,sunci sunsha sunyi wanka sunyi shirin bacci kowannensu farinciki fal zuciyarsa sai fira sukeyi har 6arawon yai awon gaba dasu bacci kenan 😜,,,asuba tagari safi da gogoji,*******
[20/11 3:07 pm] FAIZA: 💁SAFINA💁
Written by Aysha Wakili
(Mrs ahmed)
Page1⃣5⃣〰2⃣0⃣
Koda suka falka abacci salla sukayi bayan sun idar suka sake kwantawa basu falka va saikusan karfe goma shima sbd cikinsu yana Neman agaji shiyasa,,,,sunatashi sukayi wanka suka shirya suna nan zaune Suna ta6a hira saigashi yashigo da fara'a afuskarsa yazauna kusada gogoji tare dacewa kaka inakwana lfy klw Dan nan katashi lfy yace lfy lau kaka yagajiyan hanya tace alhmdlillah safi ma tace inakwana yace lfy lau kintashi lfy ta amsa da lfy klw yace bara nakawo maku breakfast yamike yafita jim kadan saigashi yashigo da tray a hannunsa safi tamike takr6a ta aje gogoji tace mungode Dan nan badan kaiba damun kwana atiti yace bkomi kaka kuci abinci yanzu inkungama sai nakaiku gun umma hajja kugaisa domin nagayamata zuwanku danhaka bara nabaku guri bayan fitarsa ne safi tamike tahau bude plate din ihu tasaki dayasa gogoji tafirgita tana tambayarta ko lfy,safi tace hoh yau zamuci dadi gogoji kwai nefa da kaza gakuma biredin birni tauhi kamar auduga gogoji naleka taga dagaske safi keyi ay itama saita hau murna nan suka hau cin abincin bako kaukautawa kan kaceme harsun tada abincin gabadaya nan safi tafata kakarin amai gogoji tamatse bakinta tanacewa ai baki isa kiyi aman nan ba dole kihadiya safi tajuyo da idanunta tace gogoji kasheni zakiyi ne gogoji tace a'a yaza ay nakasehki kawai sonake karkiyi aman safi tai kwafa tace ayzan rama ne gogoji taimata dakuwa tace tohzoki rama Dan gidanku ,,,suna cikin hakane yashigo yace kutaso muje tunda kungama suka mike sukabi bayanshi wani tamfatsetse gini yakaisu ido suka bude suna kallon irin tsari dahaduwar gidan wani hanya sukabi suka Shiga tawani kofah na glass saigasu awani shahararren falo kamar aljannar duniya safi tace wow gsky birni tayi arayuwa Ashe muna rayuwa cikin dajine bkauyeva😬 basu kara tsinkewava saida suka saka kafansu a lallausar carpet din dake falon habawa ai nan gogoji tabirkice tanacewa nashiga uku safi munhau wa mutani katifah zomu koma tunkamin sufito 😆shiko jagoransu maizaiyi inba dariya ba saida yakoshi da dariyar sannan yace bafah katifa bace carpet akecewa gogoji takalleshi tace kana nufin wannan zamu taka har tsakiyar falon kai ya gyada mata tace toh bara nayi addu'a kar in nitse aciki 😝nan fan gogoji tarike safi tarintse ido sai addu'a takeyi shiko dariya kawai yakebinsu dashi harsuka isa tsakiyar falon yanuna masu kujera yace suzauna gogji tace itafah bazata zauna akan kushin ba said akasa bayadda ya iya dole yabarta yashige ciki yakirawo mahaifiyarsa tafito cikin shiga takamala kana ganinta kaga wayeyyi yar mace dafara'a takaraso tanacewa sannunku dazuwa lale maraba gogoji tace inawuni hajiya ta amsa da lfy lau kunzo lfy gogoji ta amsa sannan safi itama tagaisheta ta amsa cikeda walwala take tambayar safi ya'ta yasunanki SAFINA tace nice name ,tacigaba dacewa yarona yafadamin kome gamedaku danhaka na amince zamu zauna daku inafata zaku rike amana cikeda farinciki gogoji kecewa insha Allahu hajiya tace toh Allah yabada eko ,ni sunana hajiya zuwaira sunan mijina ALHAJI habibu dankasuwane baicika zamaba yana yawon tafiye tafiyen kasuwancinsa ya'yanmu uku Abu safiyan shine nafarko munakiransa da safiyan shine Wanda yakawoku sai ibrahim maibi masa munakiransa da daddy sai little kubra itace Auta munakiranta da little ,safiyan shekrunsa ashirin aduniya yana makaranta a gwags jami'ar abuja inda yake karatun likita sai ibrahim shekarunsa shatakwas shikuma yana ajin karshe a secondary sai little itakuma tana firamare ajinkarshe kunji tarihinmu atakaice,,gogoji tace masha Allah,,,,Allah yatemaka ,,,nan gogoji kefadawa umma hajja sunan danaji safiyan yakirata dashi dazun cewa nima ina makaranta a kauyenmu amma rigima danakeyi da yaran kauyen yasa aka koremu agarin amma beko dameniba saima farinciki Danayi hajja umma da mamaki tace sbd me kike farinciki dakorar da akayi maku nan safi tafadi mata kauyen bacigaba sannan makaranta daga firamare sai aiwa diya aure safi tacigaba dacewa nikam banason aimin auren shiyasa naketa murna da aka koremu gogoji baki tabude tanasauraron zancen da safi kezubawa dama ashe dabararki kenan yar qaniya toh gara kitashi mukoma kauyen nabawa maigari hakuri daganan aimaki aure safi tadubi gogoji tace aisaidai kikoma Dan wlh bazankoma ba inkinga nakoma kauyen nan toh nasamu cikar burina sainazama cikakkiyar yar jarida ehe gogoji taimata dakuwa tace kinci gdnku itadai umma hajja dariya takeyi tana kallon dramar da akeyi tsakanin kaka da jika gwanin bansha'awa,*******
[20/11 3:07 pm] FAIZA: 💁SAFINA💁
Written by Aysha Wakili
(Mrs ahmed)
Page2⃣0⃣〰2⃣5⃣
Gogoji tace ke safi tashi mutafi masaukinmu karmu dami hajiya dasurutu dasauri umma hajja ta tsaida dariyar datakeyi tace haba gogoji kuzauna mana mucigaba da hira nibaku cikani dawani surutu ba inbandama dariya dakuke sani keda safi ,,,,yanxu safi kinason kiyi karatu sosai koh cikeda kaudi safi tace eh umma inason inzama cikakkiyar yar jarida shiyasa nakeso nayi karatu maizurfi,,,,umma hajja tace meyasa kikeson zama yar jarida, safi tace sbd shine burina tunda nataso sbd inaso inga anayiwa mutum tambaya yanabada amsa yana birgeni sosai ,,,umma hajja tace gsky nayaba da hangenki danhaka karki damu insha Allahu zaki zama abinda kike mafarkin zama cikeda farinciki safi tace Allah umma hajja dagaske kike zanzama yar jarida kai tagyada mata tanacigaba dacewa inhar kika dage da karatunki zaki zama duk abinda kikeso arayuwa wayyo dadi kashe gogoji badai safi ba cewa safi kenan datamike tana murna umma hajja koh ba abinda take sai dariya gogoji tace yadai kasheki baniva shaqiyar yarinya kawai,,,tace haba gogoji kina tsoron mutuwa ne 😝duka gogoji tadaka mata tace kifice kibani guri year qaniya umma hajja tace gogoji bakisan wani abuba wlh safi tana yimin kamada little sosai har ina mamakin wannan kama haka bambancinsu kadan ne itadai little batada kiriniya kamar safi, ekon Allah kenan cewar gogoji ,,,salamu alaikum abinda yakatse masu zancensu kenan tàshigo dagudu tafada kan hajja umma tanacewa hajja am bck gud p.m ,umma hajja ta amsa tare dayi mata nuni da mutanin dake zaune tanajuyowa taganmu dasauri tace inawuni gogoji ta amsa tana murmushi hade dacewa kindawo tace eh sannunku dazuwa gogoji tace yauwa tajuya kallonta ga safi tace tare kuke gogoji tace mata eh nan ta matso tamikama safi hannu waisu gaisa nan safi ta kyalkyace da dariya tanacewa haba saikace maza aisuke shan hannu huh little tace haba mana sister aimata ma suna musabaha tsakaninsu assalamu alaiki nan safi tamika hannu suka gaisa tace u re wlcm sister safi tace tnx nan little take tabawa safi labarin skull nata sannan tadora dacewa hajja kisaka sister a skull dinmu kinga saimuna zuwa tare umma hajja takalleta tace to sarkin tsari naji,,,,,little taja hannun safi suka haura dakinta nan safi tadinga kauyencinta little nayimata dariya ,,,,,hakadai ranar suka kasance cikin walwala kuma suka saba dajuna saikace sunta6a haduwa ,,,,
Yaune Monday kuma ayaune safi zatafara zuwa makaranta danhaka da wuri suka tashi tashirya driver kadai sukejira tana nan zaune gogoji nayi mata nasiha cewa tarike karatunta dakyau kartayi wasa da damar datasamu hakadai taitai mata nasiha saiga little tashigo tace sutafi driver ya iso nan sukayiwa gogoji da hajja sallama suka tafi sai RAHAMA ACADEMY adaidai gate din makarantar driver yayi parking motar suka fito shikuma yajuya Yakoma gida sukuma suka shiga cikin makarantar direct assembly ground suka wuce bayan angama ne kowa Yakama hanyar aji suma suka kama hanya suka wuce aji koda shigarsu ajin yan akin saitambayar little sukeyi su yan biyu ne dama eh take cemasu sbd batason dogon turanci,*******
[20/11 3:07 pm] FAIZA: 💁SAFINA💁
Written by Aysha Wakili
(Mrs ahmed)
Page2⃣5⃣〰3⃣0⃣
Sabo tirkin wawa,little da safi sunsaba dajuna sosai Wanda dalilin Sabon yasa duk wanda yasan little yasan safi domin duk Inda little tasaka kafa safi ma zatasaka,kawancensu gwanin sha'awa gasu dai yarane amma Allah yabasu hankali da basira ga ladabi duk Inda suka ganka saisun gaisheka koda basu sanka va hakan yasa kowa kesonsu,,amakaranta kuma yan ajin gabadaya tsoron safi sukeyi sbd bata daukan nonsense kanayi mata Abu ynzu zata lakada ma najaki harta malaman skull din sunsan halin safi batason raini da wulakanci sbd akwai watarana da wata yarinya tacema safi kazama habawa safi natashi tadauketa da mari sannan takama bakin yarinyar tana gurzawa dakasa harsaida yai jini koda aka kaita staff rum gun discipline master dayatambayeta meya hadasu saita tashi tsaye tace uncle loot at me 4rm up to down did I resemble a dirty girl uncle yagirgiza kai hade dacewa no, tace yauwa uncle to itacemin tai ni dirty girl ne shiyasa nikuma nayimata duka ,,,,uncle yace amma meyasa bazaki kawo kararta ba safi,,,tace tsorontama nakeyi kenan dazan kawo kararta ko angayamata ni matsoraciyace wlh duk shegiyar data ta6ani bazankai kararta ba inada karfin dazan hukunta ta sbd ita tafara takalata tohm,uncle dai kallon safi yakeyi edo waje yarasa abincewa,can yafara yimasu shari'ah dayaga dai safi taki yarda ai defeating nata yace duk sutafi class anjima zainemesu,,,,,,,baikarabi takansu ba yarabuda su
Akwana atashi bawuya awurin Allah gashi harsu safi ankamallah primary skull za'ashiga secondary saikaudi aketayi,,,,,safi ce da gogoji zaune suna fira saiga little tashigo safi ai yau abba zaidawo kinga yanadawowa saimuyi list na abinda mukeso asiyo mana sbd inyakoma tafiyan baya dawowa dawuri safi edo tabita dashi sannan tace toke ni abba aibai sanniva little tace injiwa ai inabashi labarinki sosai kuma hajja ma tafadamasa komai kullum yakira awaya saiya tambayeki kuma lokacin kinyi bacci shiyasa Baku magana amma ynzu haka yana hanya safi tace Allah yakawoshi lfy ,,,nansuka cigaba dahira ,,,saiga daddy yashigo yana fadin gogoji yaran nan sundameki dasurutu koh naga kinyi shiru gogoji tajuyo tanacewa wlh bacci nakeji amma ya'yan nan sunhanani yi gashi narasa yadda zanyi dasu daddy yace ai zanesu zakiyi inkingama kidauresu saikiyi baccinki gogoji tace dayake akuyoyine koh dariya daddy yakeyi yanacewa daga bada shawara kuma sai akoma kaina Allah yahuci zuciyarki 😃,,tace ameen yace to ni nawuce tunda shawarata batayiva gogoji tace Allah raka taki gona ,______da magariba abba yaiso su safi sunje sunyi mashi sannu da zuwa ya amsa yana kallon safi hade da mamakin irin kama dasukeyi da little yace ekon Allah kenan ,,,,yace safi ina kaka safi tace tayi tana lazimi inta gama tace zatazo taimaka sannu dazuwa yace kice takwanta tayi bacci dasafe sai mugaisa ido naganin ido safi tace toh abba Allah yakaimu yadubeta cikeda so yace ameen safi,,,,,,
Abba da hajja ne kwance suna bacci kiran wayar da akeyi yafarkar dasu abba yamika hannu yadau wayar yakara akunnensa tare da sallama bayan nadaya 6agaren ya amsane yakecewa alhaji anrike mana kayafah danhaka dole zamubi sahu gobe danhaka kashirya da asuba zamubi hanya kasan mutanin nan ba imani ne dasu va inmukayi sanya zamu eya yin asarar dukiyarmu abba cikin damuwa yace bakomi Allah yakaimu suka aje wayar hajja ketambayarsa ko lfy nan yake fadamata kayansu custom suka rike danhaka dole yabar Kaduna da asuba hajja cikeda damuwa tace Alla yadoraku bisa Kansu abba yace ameen zuwaira nasan kina hakuri akan tafiye tafiyen nan danakeyi Dan Allah kikara hakuri insha Allahu komai zaidaidaita ajiyar zuciya hajja tasaki kana tace kokadan banasa damuwa cikin raina sbd nasan damu kake wannan tafiye tafiyen sbd ka inganta rayuwarmu kullum inayimaka addu'a kuma zancigaba dayimaka har lokacin dakomai zaidaidaita mijina cikin farinciki yarungumota yana shimata albarka tareda cewa shiyasa kullum nake kara kaunarki kifi mata dubu agareni nagode nan sukaita love dinsu ,,,,,,,,,bayan sallar asuba abba yatafi amma yabar komai da komai babu abinda za'anema arasa ,,koda gari yawaye safi da little sukaxo gaisuwa basuga abba ba suka tambayi hajja kiya koma baccine tace a'a yayi tafiyace ta gaggawa sbd anrike mashi kaya shiyasa da asuba yatafi littleTace to Allah yadorashi bisa Kansu baki daya mukace ameen gogoji tafito suka gaisa da hajja take tambayar hajja ya abba da gajiyar hanya nan hajja take fadimata aiyatafi addu'a gogoji tayi masa sannan tace taso tagansa taimasa godia abisa zama dayabarmu mukeyi a gidansa hajja tace gogoji aiyiwa Kaine karki damu,,,,
Su little da safi yan secondary anciga aji daya a secondary saidai kowacce da ajinta sbd sa6anin raayi da akasamu ita little tana jss1A science itakuma safi jss1B art,,,amman hakan baicanza komai na amintarsu ba sannan basuda kawaye subiyu dinne dai suke rayuwarsu kamar kullum karatu sukeyi basa wasa sbd shine abinda yakaisu hatta malaman makarantar suna mamakin kwazo da hazaka irin nasu sunzama abin burgewa gakowa little da safi kenan yan BRILLIANT ACADEMY kenan yara sonkowa kinwanda yarasa kowa soyake yai kawance dasu amma subasu da lokacin hakan ga senior nasu sunasonsu kowa nasansu da skull daughter amma sunki sunce ummansu tahanasuyin wani MOMY and daughter,,,,,,,,su dady kuwa ana IBB university Inda yake karantar low,,, su safiyan kuwa ana abuja shima anata karatu Allah yataimak,*********
[20/11 3:07 pm] FAIZA: 💁SAFINA💁
Written by Aysha Wakili
(Mrs ahmedPage3⃣0⃣〰3⃣5⃣
kwanshi tashi bawuya harsu safi anshiga SS1 sunzama matasan yammata kyawawa dasu kana ganinsu kaga yanhutu jindadi dakwanciyar hankali duk sunsamu,,abubuwa dayawa aunfaru awannan shekarun ciki harda kamalla karatun safiyan da tafiyarsa england karo wani karatun nashekara uku daddy kuma yana shekarar karshe shima akaratunsa ,,,,,gogoji ce zaune itada umma hajja sunata6a hira kiran wayar da akayi yadakatar dasu hajja taje tadau wayar tanacewa gogoji yan england ne tazauna tare dakara wayar akunnenta tanacewa assalamu alaikum adaya bangaren aka amsa sallaman suka gaisa yana tambayarta gogoji tace gata bara nabata wayar tamikama gogoji wayar cikin farinciki gogoji kecewa mutan turai saiyau aketunawa damu abangarensa yace kullum kuna raina gogoji lokacine dabana samu yasa bankiranku kinsan yanayin karatun namu babu sauki shiyasa gogoji tace hkne Allah yataimaka yabada sa'a ya amsa da ameen hade dacewa inasu safi da little gogoji tace suntafi makaranta basudawo koba yace insundawo kice inagaishesu and I really miss dem gogoji tace kai kasan wani missn nidai zance kana gaishesu shikenan dariya yayi yace toh hakanma yayi gogoji barina aje wayar zanshiga lecture tace toh shikenan sai anjima nan yakashe wayar sannan gogoji tamikawa hajja wayar tanacewa yaro magana kadan saiya jefa turanci saikace wani bature,,,,hajja tai dariya tace kinsan zamadasu shiyasa suke kwaso dabiansa gogoji tace Allah yakyauta,,,,,sannan sukacigaba da hira hajja kecewa ,gogoji wani Abu nabani mamaki tunda kukazo gdn nan bakita6a ganin alhaji ba shima haka saidai kugaisa tawaya Amman idan yazo bakwa haduwa lokacin dazaizo kina bacci ko kinfita yanawucewa kinadawowa Allah baisa zaku hadu ba gogoji tayi murmushi tace ekon Allah kenan lokacine baiyiva dazamu hadu ,,,,,hajja tace aiko inyadawo wannan karon saina San yadda zanyi kuhadu sbd ynzu baya kwana ne dayazo yake komawa shiyasa gogoji tace karki damu kanki in lokaci yayi zamu hadu ay,,,,,,,,,,
Ayaune su safi sukeyin sendfort party dinsu kuma ayaune big bros dinsu zaidawo daga england danhaka sunacikin farinciki kana ganin fuskokinsu zaka fassara yanayin dasuke ciki gakuma murnar cikarsu shekara goma shatakwas aduniya ,,sunhada gagarumin party anci ansha an rausaya saikarfe 2:30pm suka iso gida agajiye suka shigo gidan suka baje a falo suna duba kyautar da hukumar makarantarsu taimusu na dalibai masu hazaka da tsafta na wannan shekara,,,,hajja tace lallai yarana kunyi kokari Allah yasa result naku yayi kyau sosai inhar naga kwazonku I promise to buy u car,,,huh yehhh insha Allah hajja d result will be A no B n C😃 hajja tace Allah yasa suka amsa da ameen ,,,,kuje kushirya driver yatafi airport dauko bros dinku by 3:00 jirginsu zaisauka inaga ynzu sun iso kushirya dining inkunfito ,,,,Sauri Sauri sukayi wanka simple make up sukayi sukaje dining suka hada komai in a normal place sannan sukadawo falo suka zauna,,,,,,,,,,driver ne yai sallama rikeda jaka ahannunsa nan suka hau ihu suna oyoyo bro oyoyo driver dai yawuce yana dariya hade dacewa inaso inga ranarda yaran nan zasu girma ,,shigowa yayi yana wakar oh my home oh my home wen shall I see my home aidagudu little da safi suka ruga Inda sukaji muryar natashi littlece tafara isa aiko tadafe jikinsa tana oyoyo bro welcome home we really miss u dialy itako safi kasa karasowa tayi sbd yadda taganshi kamar bashiba wannan kamar balarabe yake sabanin wancan dayake fari kyakkyawa Amman wannan yafishi komai ,,dogone fari maicikar hallita fuskrasa round ce ga sajen dayavari yakarawa fuskar kyau yanada manyan idanu Amman bacan can ba gadogon hanci da bakinsa Dan daidai labbansa jah kamar yasa lipstick gasumarsa akwance kamar na jariri sabon haihuwa ya illahi gsky anyi namiji anan ingarman namiji ne Wanda kowacce mace ke burin samu Allah yayi halitta ,,,,,batagama dawowa daga tunaninta ba taji yanacewa ina safi takene cikin Sauri Sauri mehade dagudu taisa gurin yabude hannunsa itama tafada kirjinsa tanafadin welcome home our bro we really miss u ,*********
[20/11 3:08 pm] FAIZA: 💁SAFINA💁
Written by Aysha Wakili
(Mrs ahmed)Page3⃣5⃣〰4⃣0⃣
Wani irin faduwa gabanta yayi lokacinda tafada kirjinsa shikuma yahade hannuwansa biyu abayanta yanacewa I miss u more my luvly sister's '''nan tazame jikinta suka riko hannunshi suna cewa bro hope kayi mana tsaraba meyawa koh yace masu tunyanzu bazama kubari nahuta ba,sukace sorry bro muje kahuta tohm afalo suka zube dukkansu hajja ce tafara fitowa nan bro yatashi yaje yarungumeta yanacewa hajja am bck I really miss u my swt mother tadago fuskarsa tace I miss u more my child hw is trip ,so fyn mum were is gogoji I did nt see her here,,,yana rufe baki tana fitowa taredacewa lale da mutanin turai barka dazuwa turawa aidagudu yaisa yarungume gogoji yanacewa kaka nayi kewarku sosai tace muma haka bature nayi farinciki da dawowarka inafata komai daidai koh yace Alhmdlillah kaka tace toh madallah haka akeso Allah yayi maku albarka suka amsa da ameen,,bro yace gogoji naga saiwani kyau kike karawa meye sirrin dariya tayi tace tambayi hajja zata fadamaka koma menene yakai dubansa ga hajja girgiza mai kai hajja tayi tayi mai nuni dabata saniba yatambayi su little aiko yanajuyowa garesu suka hada baki sunacewa new catch gogoji tayi shiyasa take kara kyau gogoji salati tasaki tace amma ya'yan nan kunci gidanku nizakui wa tsiya zangamu daku ay,,,,,,,nan dai akacigaba dafiran yaushe gamo anan yakajin labarin daddy yatafi open university Ghana karo karatu ,,,bayan sunci abinci annatsa ne yakawo tsarabar kowa yabashi little da safi komai iri daya ba bambamci riguna ne dogaye masu kyau da takalma jaka sai yankunne masu kyau na gold sai iPhone iri daya yabasu aiko nan suka hau murna yace gobe zasu fita yawo daganan saisu sayo simcard aiko nan suka dinga tsalle suna murna shidai kallonsu yakeyi yadda suka zabga uban girma ga kyau hankalinshi yafi tafiya akan safi dakomai nata taf acike yake ba abinda yafi daukar hankalinsa kamar nutsuwarta da yadda take magana saikace tana busa gsky godia ta tabbata ga ubangijin dayakagi wannan halitta masha Allah ,,,,
Dagari yawaye duk sun hallara a dining anacin abinci bayan sungama ne hajja kecewa nan da wata hudu abba zaidawo gida gabadaya babu sauran tafiye tafiye dazai rinkayi kuma wow suka fadi atare hade dacewa gsky muna murna gara yadawo murinka ganinsa akai akai ,,gogoji ma tace konima nasamu nagansa naimasa godia da irin alkhairan dayake mana tacigaba dacewa bature kaine sanadin zuwanmu gidan nan harmuka zauna muka zama yan gida babu Wanda zaice muba yan gidan nan bane danhaka kaima ina godia agareka yace kidaina yimin godia gogoji komai mukaddari ne daga Allah ,,tacigaba dacewa ya'yana uku aduniya daya ta tafi tabarni Allah yaimata rahama gabadaya sukace ameen saitai shiru batace komai ba hajja tace toh sauran biyun fah inasuke gogoji tashare hawayen fuskarta tace bansan enda sukeba ko amace ko a raye Allah kadai yabarwa kansa sani ,,,,cikeda tausayawa hajja tace in Allah ya yarda suna Raye kuma insha Allahu zaku hadu wata rana mubar komai in alhaji yadawo saimutafi kauyen mudubo kosun dawo inbasu dawoba sai ay cigiyarsu akoina ,,gogoji tace nidai bansan dame zansakawa alkhairinki gareni va saidai inai maki fatan alkhairi hajja tace gogoji ay yiwa Kaine ,,,,bayan sungama ne bro yace masu suje su shirya sutafi kasuwan 'atake suka mike suka wuce daki bayi suka fada bayan kowacce tayi wanka ne sukayi kwalliya sannan suka dauko dogon Riga acikin Wanda bro yakawo masu tsaraba suka saka wow gsky yammatan sunhadu saikun gansu dukkansu pink ne suka saka tareda pink lipstick sai farin mayafi Mara girma suka rolling nashi sannan suka dauko farin takalmi hill suka saka gsky sunyi kyau sosai koni nayaba dashigar😝 sun sauko suka iske baya falo hajja tace yana waje gun mota yanajiranku sukace da hajja saisun dawo gogoji dama takoma bacci,,dafitarsu sukaganshi gaban mota Tunda suka doshi gurin motar gaban safi kefaduwa tarasa dalilin dayasa data ganshi gabanta saiya fadi ,,ido yazuba mata tajikin madubi yana kallon yadda take sarrafa jikinta intana tafiya ta tafi da imaninshlol😝,*******
[20/11 3:08 pm] FAIZA: 💁SAFINA💁
Written by Aysha Wakili
(Mrs Ahmed)Page4⃣0⃣〰4⃣5⃣
Harsuka iso kusa dashi baisaniba little ta kwankwansa glass din hade dacewa bro mekake kallo firgigit yajuyo yace sorry I was lost somewere,,,yace kushigo mutafi dukkansu gidan baya suka shiga cos kowacce tace bazata rabuda yar'uwarta ba shiko yace bazai tuka motar ba sbd shiba driver dinsu neba nan dai little tace bainda zata itama safi tace bainda zata yace toh kufita kukoma anfasa tafiyar inkunshirya saiku fadamin nan dai safi tace pls little ki koma gaba little tace saidaike ki koma shikuma addu'a yakeyi Allah yasa little tayarda tadawo gaban sbd yajidadin kallon safi ta glass aiko hakan ne yafaru domin little tahakura takoma gaba yayinda shikuma yasaita madubin gaban daidai Inda safi tazauna yatada motar suka tafi gamji park suka nufa Inda suka dinga shawaginsu sunata kalle kallensu komai suka gani sai sunce bro yadaukesu photo tare da abin little tacewa safi zataje kallon yan drama tace saikin dawo nizani gun swimming pool little tace to mayyar swimming ni natafi nan kowacce tanufi gurin abinda takeso inda sukabar bro kan wata kujera yana hutawa """koda Isar safi gurin pool din kafafuwanta duk biyu tasaka cikin ruwan tanasaka hannuwanta tana wasa daruwan kana ganin yanayinta kasan tana cikin farinciki sai murmushi takeyi tana enjoying moment din """hangota yayi tana ta smiling mikewa yayi daga kishingidewar dayayi yana kallonta yaga kallon baimasa ba yaciro wayarshi yafara daukarta hoto duk yadda tayi saiya dauketa hoto harya manta da gajiyar dake taredashi yanata murmushi shikadai,,,,,,,,,,,,,,
kallonta kawai yake yama manta cewar yana daukanta hoto gabadaya yamika hankalinsa akanta,juyowa tayi da niyar tashi karaf idonsu yahadu dasauri tasauke idonta shiko safiyan wayencewa yayi dacewa safi ina little take kanta akasa tace tanawajen kallon drama bara nakirata yace OK kuyi Sauri mutafi kar lokaci yakure sbd akwai Inda zantafi idan na maidaku gida toh kawai tace tamike taje kiran little ido yabita dashi shidai yarinyar tana birgeshi yarasa dalilli,,
Sunjero suna tafiya suna hira little kecewa kaii wlh sister drama din nan zaiyi kyau inyafito saina nemeshi safi ta ta6e baki tace keda shirin hausa kebirgeki ba nikinsan baya gabana nafison Indian series yafi bada ma'ana little tace haka kullum kikecewa harsuka iso suna hira Inda suka barshi nan suka taddashi yace masu shine zaku shanyani saikace maigadinku ko suka rike kunnensu sunacewa sorry bro ,,,,,,nan sukawuce Inda sukayi parking motarsu suka shiga sukawuce Inda zasu saya simcard nan suka saya akai masu register suka wuce koda suka dawo gida yakar6a wayar kowacce yasaka mata nata simcard sannan ya loda makowacce katin 1,500 yayi flashing numbernsa yashiga yamikawa kowa nata yace asha phone call lfy sukace tnx bro yamike yace shizaitafi wajen abokinsa yadawo sukacewa adawo lfy agaisheshi kasiyo mana ice cream inkana dawowa yace toh masu bakin kwadayi kukawo kudi nan suka zumburo baki sunacewa pls bro yace olryt sainadawo sukace adawo lfy yatafi,*******
[20/11 3:08 pm] FAIZA: 💁SAFINA💁
Written by Aysha Wakili
(Mrs Ahmed)Page4⃣5⃣〰5⃣0⃣
datafiyarsa suka shige cikin gida suka gaida hajja suka koma falo suka samu gogoji nan suka baje sunata bata labarin Inda sukaje itako sai cewa take aitunda bature yadawo shikenan kunsamu kafar yawo bazama kuma dariya suka sannan sukace tohke gogoji kullum mutum agida bazai fitava saikace Dan prison baki tabude tana kallonsu hade dacewa eh aidole kuce haka dah bakusan kuna prison ba saiyanzu ,,,,nan dai sukacigaba da hira har akai kiran la'asar sukaje sukayi salla bayan sun idar ne suka shiga kitchen neman abinda zasu dafa na dinner bayan sunzabi abincin dazasu dafa suka koma falo sunajiran lokaci yakara jah kamin sudaura,,,,,,,,,,,,,
Karfe yakwas komai yayi ready akan dining kowa ya hallara banda bro safiyan hajja tace waini yayanku baidawova haryanzu ne suka amsa da eh hajja tace ke little kiran minshi awayarki little tace wayar tana daki safi kirashi danaki nan safi tadauka tama manta batayi saving numbern shi ba bt dayake yayi flashing nasu dazun saitayi dialing numbern Harya kariki ringing baadauka ba zatakara dialing kenan kira yashigo tadauka tare da sallama abangarenshi kuma ya amsa mata tace bro inaktsaya ne harynzu baka dawoba munatajiranka dinner is ready bt u nt wit us kodai kaje gun aunt dinmu ne ""murmushi yayi yace haka nafada maki kodai ke kike tinanin hakan tace a'a bro sorry I was told,will u keep quite cikin Sauri takatse wayar ta aje agefe tareda cewa hajja yace yanazuwa batagama rufe baki va yashigo rikeda Leda ahannunsa agefe ya aje ledar yagaida gogoji da hajja sannan yaja kujera yazauna little tace wlcm bro ya amsa mata safi ma tace wlcm bt babu walwala afuskarta kallonta yayi takasa kasa fakauda kanta nan akafara cin abinci dama kaedan gidan ne in anacin abinci ba'ayin magana harsai angama haka yakasance saida suka kammala gogoji tace itafah barci takeji safi ma tamike tace itama yau barci takeji nan dai kowa Yakama kansa koda suka shiga daki safi kwanciya tayi yayinda little keta saving numbers awayarta ,barci haryafara daukarta taji message yashigo cikin wayarta taduba taga bro ne tanabudewa taga anrubuta am sorry 4shouting at u on d phone,koda takaranta batayi reply ba tacigaba da barcinta ...
Dasafe itama tayi saving numbers dinta awayarta nan sukayi downloading watsapp suka hau netwk nanfah suka fara ihun dadi nandai frnds and family masuyin watsapp suka appearing nan fah suka hau chat ba kakkautawa anan sukaga bro nasu shima yanayi suka rubuta mashi hy bro nan shima yayi reply nasu da mamaki yace dis girls no go kill person oo,,,blushing☺sukayi
Haka rayuwa taciga a inda suka fara karatunsu saidai kowacce da skull dinta nd kowacce da motarta bro kuma yanzu yazama cikakken doctor inda yake ayki a general hospital na Kaduna ,,,Inda safi tafara soyayya dawani guy mesuna suraj sunhadu a watsapp awani group Inda yanuna yana kaunarta itakam tadai amsa mai ne alokacin bawai tanason shiba saidan bataso tawulakanta shi ahankali kuma Allah yafara samata sonshi nanfah soyayya tayi karfi little ma tahadu dawani kamal kuma itama tana kaunarshi sosai suna gudanar da soyayyarsu maitsafta gwanin ban sha'awa hakan baihanasu yin karatunsu ba inda bro safiyan kuma yakasa Neman kowace mace sukuma matan sai tururuwa suke masa musamman nurses din dake asibitinsu amma bayada lokacin kowacce daga cikinsu kullum tunaninsa yanakan safi tunyana karyata sonda yake mata harya amince saidai bazai iya fadimata ba dankar tarainashi cos shibazai iya tunkararta damaganar soyayya ba haka yaketa nukunuku dashi azuciyarsa in abin yadameshi saiya dauko waya yabude gallery gurin pics yaita kallon hotunanta yanajin sanyi aransa ,,,,soyayya kenann,**********