👠SATAR FITA 💃🏽
Da gudunta ta fito daga gidan hannunta dauke da qatuwar jaka tayi bakin titi, keke nepep ta dauka da sauri ta shige ba tareda sunyi ciniki ba tace malam gandun Albasa zaka kaini.
Tafiyar mintina 5 ce ta kaisu gandu tana fitowa ta miqa masa 70 naira ta shiga gidan da sauri. A tsakar gida taci karo da mamansu Aisha tana shara. Har qasa ta tsugunna ta gaidata matar ta amsa da fara'arta tace mata Aisha tana ciki.
Da sauri ta shiga ciki a daki ta iske aysha a bakin mirror tana kwalliya, ihu aysha ta saka ta rungume HINDATU sannan suka fada kan gado. Saida suka gama ife2nsu sannan aysha ta kalleta da kyau tace keh shegiyas na zata bazaki zo ba.
Baki ta tabe tace kedai bari wlh saida na jira umma ta shiga toilet sannan na fito.
Dariya suka sa gaba1 aysha tace Hindu wato ke bazaki taba canza halinki ba koh?
Tabe baki tayi tace sae randa gyatumaina suka canza halinsu na kulle sannan nima zan canza.
To naji, dan Allah tashi ki shirya da wuri kinga 8:15 nima da qyar na tsara ummi ta barni saboda baffa bayanan.
Da sauri hindatu ta bude Jakarta ra dauko ankonta na material pinki n purple ta zura ta tsantsara kwalliyarta tayi masipar kyau.
Aysha dake amsa waya ta juyo ta kalli hindatu a fili tace Wow!!! Shegiyas kinyi kyau dole kisa abokan ango suji jigi jigi! Keh idan ta kama har angon ma.
Dariya suka kwashe da ita suna tafawa Hindu tace Aysha bakida kirki wlh idan banda tsabar iskanci ina ni ina ango koko so kike mairo tayi sammako gidanmu taci ubana.
Murmushi Aysha tayi tace wlh kuwa kinsan maryam akan wannan mijin nata, sae wani kurantashi takeyi tunfa muna secondary suke tare, yaseen ya hadu.
Tabe baki hindatu tayi tana jujjuyawa gaban mudubi tace haka kurum umma zataimin buqulun ganin hadaddu, kinsan wlh maqasudin zuwana bikin nan saboda n qure qaryar mairo amma daga yadda naga kamunta naga Alamu babu qarya.
Muje plz aysha ta fada tana qara balbalawa Hindu turare suka jero. A falo sukaci karo da
[21/04, 23:23] Hassan India: Miss collapse
(2)
👠 SATAR FITA💃🏽
da ummi ta kallesu da kyau ta tabe baki tace Ku kula da kanku d kyau dan Allah kunga dai duniya babu gskia sannan dan Allah kafin 10:30 ku tabbatar kuna gida.
Murmushi sukayi tareda cewa insha Allah ummi. 2k ta miqa musu tace kuyi kudin mota suka amsa suna godia.
A qofar gidansu Aysha saurayin nata yai parking motarsa aysha ce gaba Hindu na binta a baya suka bude motar suka shiga.
Sama 2 suka gaisa d hindatu dan ita sam bata sakarwa maza fuska a cewarta batason raini koda kuwa samarin qawayenta ne kokuma en uwa. A cewarta a shekarunta da basu wuce 19 ba soyayya bata lokacine tunda tsarin baffanta ne dole sae mutum ya gama first degree ko HND dinsa sannan zaiyi aure.
Data gaji da hirar da Aysha takeyi da saurayinta kamal wayarta ta zaro ta zura earpiece ta kunna waqa.
Cikin en mintuna qalilan suka qarasa babban hall din da ake taron dinner din qawarsu maryam amma tsabar ji da kai da nuna su manyan yarane a cewarsu saida suka kwashi kusan 1 hour a cikin motar, a cewarsu hadaddu basa zuwa gurin taro da wuri sae an kusa tashi.
Saida suka qarawa fuskokinsu powder sannan suka shiga gurin taron suna takunsu daidai mai Jan hankali.
Aysha farace Tass kamar zabiya amma batada wani kyau sae kwalliyar balaee, wannan farin nata kuwa jarine babba a gareta domin yawancin mazan kano babu abunda yafi birgesu kamar farar mace, batada tsayi sosae amma ba gajeriya bace jikinta daidae musali dass ta ita.
Hindatu kam baqace amma ba sosai ba saidae ALLAH ya zuba mata madarar kyau tako wani fanni matsalarta 1 ce tsantsan tsiwa da futsara saboda duk girman mutum idan ya tabota zata antaya masa rashin mutunci ne shiyasa wani lokacin friends dinta sukance mata miss no nonsense.
Hankalin kowa a gurin saida ya dawo Kansu ban dauke ango da amarya ba saboda en matan 2 badai iya tsara kwalliya ba abunka da en matan kano, wannan ya basu damar dage kawunansu suna shan qamshi musamman hindatu wadda dama halinta ne idan taga mutane
[21/04, 23:23] Hassan India: Miss collapse
(3)
👠SATAR FITA💃🏽
can gefe suka nemi gurin zama, duk table mutane 4 ne suke zama amma cikin sa'arsu nasu table din su 2 suka zauna.
Kusan yawancin yan matan dake gurin sun sansu dan yawanci tare sukai secondary wasu kuma har yanzu tare suke schooling amma tsabar iya shege sae suka nuna kamar basusan anyi ruwansu ba sukai fuska suna hirarsu qasa2, can dae suka miqe sukaje suka gaisa da amarya da ango suka dawo, ananma sun kwashi en kallo dan ba qaramin yaqar mutanen sukaiba daga mazan har matan.
Wasu daga cikin friends din nasu sunzo sun gaisa yayinda wadanda sukeji da nasu kalar girman kan sukai banza dasu.
Kida mai tashi akasa a wurin bikin MC ya kira amarya da ango suka cashe dakyau, hindatu ta dauko purse dinta ta miqe ta shiga filin rawar, ga mamakin kowa kudine en 502 sababbi gall 2 ta dinga liqawa aiko gurin ya dauki sowa sosae wasu daga cikin abokan angon suka rufeta da yayyafin kudi,Aiko M.C ya dinga kurantata en baqin ciki suna harare harare, ganin abun yaqi qarewa yasa Aysha tashi ta janyota suka koma suka zauna.
Qasa 2 Aysha take cewa wato dan iskanci kudin ankon habeeban kike liqewa koh? Wani qayataccen smile Hindu ta saki har saida dimples dinta suka fito sannan tace haba Aysha sae kace baki sanniba, wannan abun da nayi ba qaramin kankarowa kaina mutunci nayi ba, dubi yadda su zuby suke harare2 kamar idonsu zai fado.
Ta gefen ido Aysha ta kalli bangaren dasu zubaidan suke ta fara dariya qasa2 tana cewa mutum ba ido ba yace zaiyi dariya.
Suna cikin hirarne wasu abokan ango suka qaraso gurin da sallamarsu.
Aysha ce ta amsa dan Hindu gefe tai da kanta tana kallon yadda biki ke gudana.
Dan Allah en mata idan bazaki damuba kidan ara mana friend din taki mana akwai maganar d zamuyi da ita.
Nan danan Hindu ta tsuke fuskarta sosae dama Aysha ta tsammaci hakan sai tace mlm kayi haquri qawata kurma ce bata magana.
Cikeda rashin yadda suke kallon Aysha dayan yace amma kuma ya akae ta gane an saka kida har taje tayi
[21/04, 23:23] Hassan India: Miss collapse
(4)
👠SATAR FITA💃🏽
an saka kida har taje tayi liqi?
Murmushin yaqe Aysha tai tace mlm ae tanajin mgn mayarwa ne bata iyawa.
Murmushi guy din ya saki yace aeta kwana gidan sauqi wlh indae tana sona a shirye nk zan aureta a hakan.
Dariya ce ta matso Aysha Hindu tai saurin taketa da qafarta aeko ta hadiye dariyar zatai mgn guy din yace ba saikince komae ba numbern ta kawai zaki bani.
Sum2 Hindu ta miqe ta fice daga hall din suka bita da kallon mamaki zasuyi mgn wayar Aysha ta fara ringing, miqewa tae tace musu tana zuwa tabar gurin da sauri tana amsa kiran kamal da yake ce mata yazo.
A bakin gurin suka hadu da Hindu babu bata tym suka shige motar kamal Aysha tace Hindu zamu fara saukewa a gidansu.
Qarfe 8:15 baffa ya dawo daga masallaci hannunsa riqe da carbi yana lazimi ya zauna a falo yana kallon labarai umma ta shigo. Sannu da shigowa tayi masa ta samu guri ta zauna ta fara qwalawa hindatu kira. Hindu!! Hindu!! Fito ki daukomin kulolin abincin baffanki a kitchen. Shiru taji ta qara maimatawa dan haka ta tashi da kanta ta shiga dakin ta fara laluben Hindu amma taga wayam hakan ya bata tabbacin hindatun ta tafi gantalin data saba.
Fitowa tae da kanta ta kwaso kulolin ta dire gaban baffa ta fata serving dinshi yace ina hindatun take?
Ban ganta ba, babu mamaki ta tafi yawon gantalin data saba.
Cike da takaici baffa ke kallon ummi! Ke wata irin uwace da erta zata fita bata saniba! A garin gaba 2 muke? Haba da Allah! Masipa sosae baffa yakeyi ta inda yake shiga batanan yake fitaba saeda ya kwashi kusan minti goma yanayi sannan ya juyo ya kalli umma yace safiyyah dakefa nakeyin magana.
Wani malalacin murmushi umma ta saki ta kalli Baffa tace yallabai me kakeso nace mk? Sanin kanka ne idan hindatu tayi niyyar fita dole saeta fita ko kaine a gidan nan. Nagadai ba daureta zanyi a gefen zanina na dinga yawo da itaba, kuma hindatu bawai yau ta fara gantalinta ba kuma nida kakemin masipa bawai fa nice hindatu ba
[21/04, 23:24] Hassan India: Miss collapse
(5)
👠SATAR FITA💃🏽
ka bari muna zaune anan zata dawo saeka yimata abunda zaka mata amma da Allah yanxu ka sauko kaci abinci.
Qwafa mai qarfi baffa yayi ya sauko qasa yanacin daddadan abincin matar tasa tana yimasa hira sama, hakan ya kwantar masa da hankali sosae.
Suna zaune a falon har kusan goma babu labarin hindatu. Cikeda takaici baffa yace kina ganin hindatu zata dawo kuwa?
Hadiyar yawu umma tai tace mai zai hana ka qara haquri kawai.
Har goma da rabi babu labarin hindatu hakan yasa suka miqe suka kashe fitulun gidan sukai nasu wuri.
10:51 kamal ya sauke hindatu a bayan gidansu, godiya tayi masa sannan sukai sallama da Aysha dakeyi mata dariya qasa2 dan ta karanci tsoron da qawar tata take ciki.
A hankali ta tura gate din shiga gidan nasu, godiya ta yiwa Allah ganin gate din baeyi qaraba ta dauki takalmanta ta maqalesu a hammata, A hankali ta sababa ta bude qofar falon ganin pitulu a bude yasa ta qara yiwa Allah wata godiyar sannan ta bude qofar dakinta ta rufe a hankali harda murza key tana godewa Allah dayasa iyayen nata sukai bacci kafin ta dawo. Takalman ta dire a qasa tasa hannu ta kunna fitulun dakinta tana juyowa ta tadda baffa da umma zaune a gefen gadonta
A tsorace ta fara fadin wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir raheem
Ta fada tareda juyawa tana qoqarin bude qofar key din yana faduwa.
Dukda bacin ran da Abba yake ciki b qaramin dariya hindatu ta bashi ba, wato a niyyarta gamo tai da Aljanu. amma ya gimtse ya tashi tsaye ya tako zuwa Inda take, tana ganin hakan ta durqushe a gurin tareda daura hannayenta biyu ta zabga ihu tana fadin, baffa dan manzan Allah kayi haquri wlh bazan kuma ba wlh.
Kusan 30 secns yayi a kanta sannan yace daga ina kike?
Uhmm....bafff....
Daga ina kike nace? Ya fada adan tsawace
Wlh baffa dinner din maryam mukaje kuma tareda Aysha mukaje ma, Dan ALLAH kayi haquri karka dakeni.
Guntun tsaki baffa yaja tareda cewa karki fasa halinki, zan dau mataki
[21/04, 23:25] Hassan India: Miss collapse
(6)
👠 SATAR FITA💃🏽
Yana kaiwa nan yasa kai ya fice umma tabi bayansa tare da fadin hindatu kinji haushi wlh.
Ajiyar zuciya mai sauti ta sauke sannan ta miqe ta shiga toilet tai wanka ta zura kayan baccinta.
Aysha ta kirawo tana labarta mata abunda ya faru Aysha ta fashe da dariya tace wlh Hindu idan baki daina SATAR FITA ba wataran saikin gane kuranki.
Murmushi hindatun tayi tareda cewa lallai Aysha har yanxu da sauranki a sanina,
Hirarsu suka cigaba dayi Aysha ta fara tsokanarta akan abokin angon dayace yana sonta.
Kin bata mana hira wlh, ki dubeshi da kyau yana fama da baqi kamar an goga masa yazo yace yana sona! Mtswww saeda safe ma kawai gobe 8 nkd lectures. Ta katse wayar tareda kasheta gaba 1.
Qarfe 7:30 ta fito cikin shirinta na doguwar rigar abaya tayi rolling fuskarnan tasha kwalliya ta fito cas da ita kamar a sace.
A falo ta taradda baffa yana kallon labarai ta qarasa har qasa ta tsugunna ta gaidashi.
Qasa 2 ya amsa tareda zaro kudi cikin Aljihunsa ya miqa mata, karba tai tana godiya ta miqe zata tafi baffan ya tsaidata dawowa tai ta tsugunna baffa yace yau ba qarfe 8:00 kikeda lecture ba?
"Eh baffa" ta amsa tanacin farce baffan ya juyo yana kallonta sama da qasa sannan yace shine dan shashanci sae yanzu zaki fito salon a hanaki shiga kice an koreki koh? Kawai kiyi kuskure result dinki na wannan semester din ya gaza 4 point, dubeki kinci kwalliya kamar me shirin zuwa gidan biki, cuno baki tae tace "baffa kayi haquri"
Kece da haquri Hindu, duk cikin yayyenki babu wanda yake sakamin ciwon kai sai ke da kikazo a qarshe, tashi ki tafi Allah ya bada sa'a, kuma ki tabbata kinci abinci kafin ki fita.
Zumbure2 ta cigaba dayi harta isa kitchen ta iske ummi tana suyan dankali.
Bayan sun gaisa ne tadan tsakuri dankalin ta fito zuwa inda Audi yake, shine mae adaidaita sahun da baffa ya dauka kuma shiyake kaita skul duk kwanan duniya amma kwata2 basa shiri saboda baya yadda suyi yawo kaman yadda takeso shiyasa kullum
[21/04, 23:25] Hassan India: Miss collapse
(7)
👠SATAR FITA💃🏽
a cikin rigima suke.
Rai a bace ta shiga keke nepep din suka tafi. Har cikin skul ya sauketa dukda securities din skul din basa bari masu keke nepep suna shiga amma ita ana barinta.
A gaggauce ta shiga lecture hall din nasu ta tana neman gurin gurin zama lecturer din ya juyo ta dubansa gurinta yace "my sister excuse me"
Daure fuskarta tae ta juyo tana kallonsa yace "what's d tym"
Kallon agogon hannunta tae sannan ta dago tana kallonsa tace 8:06
Daure fuskarsa yae yace get out!!
Tsabar rainin wayo irin na students saena bata lokacina na fito da sassafe nabar iyalina nazo ina koyarda ku amma ku kunfi kowa iya late! More especially u, saboda na riga na ganeki kullum a makare kike zuwa!
Daure fuskarta tayi tace "Sir gidanmu da nisa pa"
Babu ruwana! Ki koma hostel, get out ure wasting my time.
Tana qunquni ta fice daga lecture din a zuciyarta tana qissima irin rashin mutunci da zataiwa lecturer din.
A waje ta samu guri ta zauna kusan 30 mins wasu suka sake fitowa da alama korosu yayi.
Joining dinta sukayi kowacce na complain akan wulakancin lecturer din sukaji yana cewa TEST!
A razane suka juya suna kallon ajin hindatu da gabanta yafi faduwa saboda warning din da baffa yae Mata tace dan Allah a cikinku wakeda niqaf?
Kallon rashin fahimta sukai mata dayar tace me zaki dashi?
Cikin qosawa tace plz idan kinada shi ki aramin.
Jakarta ta zage ta fito ta niqaf ta miqawa hintatu, a gaggauce ta daura niqaf din ta sallaba ta leqa clx din.
Ganin lecturer din nasu ya juya yana rubutu yasata yin wufff ta shige clx din ta zauna a kujerar gaba.
Sowa sosae clz din ya dauka malamin ya juyo ya tsaida dubansa kan hindatu. Wani irin bugawa zuciyarta tayi a tsorace take kallon lecturer din tana karanto adduoin neman tsari
[21/04, 23:26] Hassan India: Miss collapse
(8)
👠SATAR FITA💃🏽
Tsit clx din sukai suna jiran suji matakin dazai dauka amma ga mamakinsu saeya share yace u can start.
40 mins students din suka kwasa suna rubuta test din mai baqar wahala sannan suka fara qoqarin submitting, ba abunda yafi bawa hindatu tsoro kaman yadda lecturer din yace kowa idan ya gama ya bashi a hannunsa sannan yayi singing.
Ta cikin niqaf din zufa ta dinga keto mata saeda aka rage baifi saura mutane 5 a clx din ba sannan ta miqe gabanta na faduwa ta isa gabansa.
Hannunta na rawa ta rattaba sunanta jikin paper din dake gefensa HINDATU BASHIR JAURO sannan ta miqa masa paper din kanta a katsa.
Ganin baida niyyar karba ne yasata dagowa tana kallonsa shima y kafeta da manyan idanuwansa, idonta tai saurin saukewa qasa shikuma ya daura fuska sosae yace hindatu koh? Da alama kin qware da SATAR FITA a gidanku.
Dagowa tai ta kalleshi fuskarnan tasa a daure babu alamun wasa tae saurin maida kanta qasa gabanta na faduwa.
Hannunsa ya miqa ya karbi paper din murya qasa2 yace ki sameni a office dina sannan ya qarasa yana karbar ta ragowar students din.
Me yace miki? Ya kukai dashi? Shine tambayar da yawanci students din suke mata amma amsa daya take basu wato babu komae.
Qarfe 3 Audi yazo daukanta, ta shiga keke nepep din fuskarta dauke da damuwa suna cikin tafiya tace dan ALLAH Audi ka taimaka muje old side akwai maganar da nakeso muyi da Aysha.
Alhj ya hana, kinsan kuma idan ya sani zaimun fada. Roqonsa tai tayi harya yadda ya kaita old side din, waje ta kirawo Aysha tana fada mata matsalarta.
Ba qaramin dariya ta bawa Aysha ba abun har saida ya qular da ita. To meya hanaki zuwa?
Chab! Kinsan ni wlh na tsani wani abu ya hadani da malamai musamman wannan dan wulaqancin mutumin.
Aeko dole kije indae kinason zaman lafiyarki, kawai kije ki bashi haquri.
Badan ranta yaso ba ta yadda zataje sukai sallama da Aysha.
Zuciyarta a cushe ta shiga gidan. A tsakar gida ta tadda wata yarinya tana wasan ruwa a tap
[21/04, 23:26] Hassan India: Miss collapse
(9)
👠SATAR FITA💃🏽
A tsakar gida ta tadda wata yarinya tana wasan ruwa a tap, da qarfinta tace baby!!
Da sauri yarinyar ta juyo tana ciccila qafa da saurinta ta taho ta dane hindatu, cikin farin ciki tace yaushe kikazo gidan?
Yarinyar da bata gama iya mgn ba tace "Azuu"
Daxu kenan
Murmushi mae kyau tayi tana shafa kan yarinyar tayi ciki tana fadin ummi!!! Yaushe baby tazo?
A falo tayi kicibus da mutanen d Sam batason gani ya hamza da matarsa ya khadijah. Nan da nan ta daure fuskarta ta dire baby a qasa tace umma sannu ta hutawa, fuuu tai cikin dakinta bama ta lura da baffa ba.
Da kallo suka bita baffa yace lpy dae koh? Ya hamza ne ya kalli baffa yace rabu d ita baffa damu take, daga rannan tayi halin nata munyi mata fada shikenan take gaba damu nida khadija
Allah ya kyauta kawai umma tace.
Yau ta kama Monday kuma yaudin zasu fara exams, qarfe 10 tabar gidan da saurinta sabida 12 takeda paper, libry ta wuce ta cigaba da karatunta 12 suka shiga exams, dadi sosae exams din take mata ana cikinyi taji mutum a kanta, da sauri ta dago suka hada ido da lecturer din nan nasu IBRAHIM, sosae zuciyarta ta buga danko harga Allah ta mance da batunsa.
Aeko suna gama exams ba shiri taje office dinsa, a darare ta zauna a kujerar daya nuna mata.
Ki saki jikinki hindatu bawai wani abu zanyi miki ba. Kawai inaso na zama friend dinki ne nd nothing more.
A tsorace ta dago tana kallonsa tace friend? Eh mana koh bakiso?
Murmushin qarfin hali tae tace baffana bayaso ina kula maza.
Bayaso kina kula irresponsible maza dae koh? Yanxu da girmanki baffa zai hanaki kula maza kina kallon kanki kuwa?
A kunyace tace sir! Mah! Yace shima yana miqa mata wayar hannunsa yace ki sakamin number dinki.
Ba musu ta saka masa ta miqe dan Audi ya fara kiranta d alama anzo picking dinta.
Qarfe 2 da en mintuna suka qarasa gida.
Da en waqe2nta ta shiga gida ta tadda umma na tankade. Harara umma ta zabga mata tace waeke a islamiyyar da kukae ba'a koya miki
[21/04, 23:27] Hassan India: Miss collapse
(10)
👠SATAR FITA💃🏽
sallama ba?
Kaiii!! Haba da Allah umma waeni meyasa kuka tsaneni komae nayi sai anyi magana akae tana fada lokacin data tura qofar falon.
Innanillahi ta fada da dan qarfi har saida dan saurayin dake kwance saman doguwar kujera ya dago ya kalleta.
Shikenan wannan dan takuran ya dawo zai cika mana gida! Kai!
Harara handsome guy din ya wurga mata yace kinyi kin gama, dan yanxu na dawo 9ja kenan.
Kaika sani, taja tsaki tana wucewa dakinta tana qunquni.
Asalinsu-
Alh. Jibril haifaffen garin yola ne wanda iyayensa suka rasu suka barsa da qannenshi 2 bashir da rumaisa, lokacin suna qanana, sun girma cikin maraici lokacin jibril ya shiga kasuwa neman kudi, fataucine ya kawoshi kano Allah yayi anan zai sami arziqinsa, Allah kuwa ya buda masa daidae gwargwado a lokacin yayi aure ya auri matarsa fateema ita kuma haifaffiyar garin kano ce, lokacin kuma ya dauko qannensa bashir da rumaisa suka dawo hannunsa, ya tsaya tsayin daka saida bashir yayi karatu har ixuwa matakin masters ruma kuma a diploma kawai ta tsaya.
Ganin qwazon da bashir yakeda shi yasa jami'ar BUK suka daukeshi lecturing a fannin mass.com a lokacin kuma suka sake haduwa da abokinsa sadauki wanda sukai karatu tare, Aminci sosae suka qulla lokacin dayazo gidansu yaga ruma ya nuna yana sonta, ba'a dauki lokaci ba kuwa akai aurensu. Shekarar farko ta haifi danta kyakykyawan gaske, kamarsa daya da mamansa kamar an tsaga Kara bayan shekara 4 ta haifi ruqayya daga lokacin bata qara haihuwa ba sae bayan 11 yrs ta haifi Aysha.
A daya bangaren kuma Alh jibril ya haifi yaransa 3, hamza shine na fari, sai Adam sae kuma halima.
Lokacin halima na da shekara 4 Alh jibril da matarsa sukai tafiya saudiyya a hanyar dawowarsu sukai hatsarin jirgi suka mutu. Mutuwar ta doki jama'a sosae musamman bashir da lokacin aurensa baifi 2 yrs ba.
Shine ya rumgumi yaran dan uwansa har sukai karatu sosae. Lokacin daya haifi yarsa ta fari yasa mata khadija itace ta auri
[21/04, 23:28] Hassan India: Miss collapse
(12)
👠SATAR FITA💃🏽
Lokacin daya haifi yarsa ta fari yasa mata khadija itace ta auri hamza wanda yake kulawa da kasuwancin mahaifinsu, halima ma tayi aure Adams dama shi dan boko ne tare sukai karatu da sa'ad sadauki a OMAN, Aminu shine dan Alh bashir na 2 sae kuma hindatu itace autarsu.
Hindatu irin yaran nan ne marasa jin magana tun tana qarama takeda shegen qiriniya, gashi batason zaman gida ko kadan yawo a cikinta kamar taci qafar kare.
Lokacin su Adam suna Nigeria batafi 6 yrs ba, idan tayi yawon haka yake kamata ya nadeta amma gobe saita koma.
Bayan tafiyarsu tana gama primary baffa ya tattarata ita da Aysha tunda dama hali yaxo 1 ya miqasu FGC munjibir, duk irin security na skul din haka idan ta rayo musu suke haurowa saI dae k gansu a gida, a dole za'a dawo dasu susha punishment amma haka bashi zai hanasu maimaitawa ba.
Lokacin da suka gama secondary a sa'arsu suka samu admission.
Aysha ta samu biology hindatu kuma computer science yanzu haka suna level 2
Washegari basuda exams dan haka a gida tae zamanta taya taya umma aekin hada breakfast aminu ya shigo yana gaida ummah, daure fuska tayi bata kulashi ba yace keh hindatu bazaki gaidani ba?
A zuciye ta juyo ta fara masipa, mlm dallah ka rabu dani kaji koh, kaga dae tunda kazo gidan nan ban kulaka ba.
Murmushi yayi yace "toni saena kulaki"
Tsaki taja ta juya aminu ya kalli umma dake aekin fere dankali yace umma kinsan fa jiya munyi waya da ya Adam.
Ah haba! Umma ta fada cikeda zaquwa, eh wlh umma kinsan cemin yayi zuwa nan d 3 wks zasu dawo Nigeria gaba1 shida ya Sa'ad.
Kaii!! Masha Allah! Aiko dasun kyautamin,sun maqale a wata qasa can shekara da shekaru babu bayanin su, ae gara suxo suyi aure.
Sosae gaban hindatu ya fadi ta juyo tace umma shi ya Adam din gidan nan zai dawo?
Qwarai da gsk, ai bashida wani gidan bayan wannan.
To wlh umma nidae hostel zan koma bazan zauna da wannan dan marasa mutuncin ba Sabo.... bige mata baki umma tae ranta a bace tace
[21/04, 23:30] Hassan India: Miss collapse
(13)
👠SATAR FITA💃🏽
wannan dan marasa mutuncin ba Sabo.... bige mata baki umma tae ranta a bace tace hindatu yaushe zaki koyi iya magana! Ki kalli tsabar idonmu kina cewa Adam dan marasa mutunci? To dasuwa kike?
Hannunta ta dora akan lips dinta taji ya kumbura! Kuka ta fara ta fice daga kitchen din, tana zuwa dakinta ta zari hijab da purse dinta bata bi ta inda umma takeba ta fice a kufule.
Kan doguwar kujerar gidansu Aysha ta baje ta fara kuka ummi ta shigo d saurinta tace Hindu lpy? Waya mutu?
Ummi duk duniya ke kadai kike sona! Komae nayi sae umma ta dokeni jibi yadda ta bugemin baki daga nace ya Adam bazai zauna a gidanmu ba ta fada tana matsar hawaye.
Murmushi ummi tae tace hindatu ina kikeson ya zauna! Hade fuska tae tace yayi aure kokuma ni n koma hostel
Dariya sosae ta bawa ummi, saida ta gaji d dariyarta sannan ta kalli hindatu tace lallai Hindu kinada daru da baffanki! Kima cire maganar hostel a zuciyarki.
Tunda tae breakfast suke hira da ummi dan ita sam batada matsala, sosae suke shiri da Hindu.
Wayarta ce ta fara ringing ta dauka ta kara a kunnenta tana fadin waye?
Daga daya bangaren akace Ibrahim ne, bakiyi saving number na b kenan?
Ummi ta kalla taga itama kallonta takeyi, da sauri tabar gurin ta shige dakin Aysha.
Qarfe 1 Aysha ta shigo dakin a gajiye ta tadda hindatu tana amsa waya. Da mamaki aysha ke kallonta dan tasan hindatu taqi jinin maza,balle kuma soyayyah, sauke kayanta tae tayi wanka ta dauro Alwala,hindatu ma lokacin ta gama wayarta Alwala ta dauro sukae sallah.
Suna cikin cin abinci Aysha tace ke wae dawa kike waya dazu?
Uhmm da wannan lecturer din namu dana baki labari,sunansa Ibrahim.
Spoon aysha ta ajje tana kallon hindatu tace shine kuma har kun qulle haka?
Kullah me?hindatu ta fada tana taunar abincinta.
Hararar wasa Aysha ta wurga mata tace wannan soyyayyar danaga kinayi harda lumshe Ido mana
God forbid! Allah y kiyaye! Ke nipa n fada miki mijina bafa dan Nigeria bane,akanme zan
[21/04, 23:31] Hassan India: Miss collapse
(14)
👠SATAR FITA💃🏽
God forbid! Allah y kiyaye! Ke nipa n fada miki mijina bafa dan Nigeria bane,akanme zan auri dan uwana baqar fata.
Murmushi Aysha tae tace meyasa kike kula wannan mutumin toh?
Ajiyar zuciya ta saki tace yace yanaso ya zama friend dina, kuma dae nima Ina dan kulashi ne saboda Ko babu komae zai zamemin academic donkey ( yawanci sunan ta en mata suke kiran samarin su na jami'a Ko higher institutions ta suke taimaka musu wajen karatu). Kinsan baffa ga cewa yayi idan result dina yae qasa baxanji dadi b.
Kuma kinsan wani abu? Ibrahim fa yanada aure harda yayansa 2.
Qwarewa Aysha tayi ta fara tari b qaqqautawa har saida hindatu ta bata ruwa tasha sannan ta dago tana kallon hindatu tace mijin aure kike kulawa?
"Ehn,menene?ae b haramun bane"
Chabbb!! Sannunki d qoqari Hindu,nipa wlh n tsani mutum mae aure y kulani haka kuma Ko gigin aure nakeyi bazan kula mae aure ba. Kinsan Allah na tsani kishiya! Ke koh labari naji ana saka kishiya haushi yake bani,idan kuwa naga gida d kishiyoyi Wlh har banason shiga.
Dariya hindatu tayi harda dafe ciki t kalli Aysha tace sannunki d Aiki,kinsan dae Allah y halatta auren 4 koh? Wlh gwarama ki shirya gwagwarmaya idan kin auri saurayi ance miki bazai qara aure bane Kokuma kula mai auren ciwo ne? Wlh garama ki kwantar da hankalinki karki saka kanki a halaka.
To naji malama hindatu! Yanxu dae muyi closing chapter din nan! Yaushe kikazo?
Oh na manta ban fada miki dalilin zuwana ba,ta fada lokacin da take kimtsa gurin ta suka bata takae plate din kitchen ta dawo.
Issho kinsan wani ya Adam a gidanmu?
Eh mana,na sanshi,kinsan lokacin da suka tafi karatu banfi 8 yrs ba ke kuma kina 6-7,so na sanshi b sosae b. Ae abokin ya Sa'ad dinmu ne.
Yauwa! Kinsan dazu Ya aminu yake fadamin wae zasu dawo nigeria da zama,kinsan dama aeki sukeyi acan.
N sani mana, Ae jiya ma munyi waya d ya saad a wayar ummy.
Tsaki hindatu ta saki ta kalli Aysha tace to wallahi Azim bara kiji,kinsan ya Adam din
[21/04, 23:31] Hassan India: Miss collapse
(15)
👠SATAR FITA💃🏽
Kinsan ya Adam din gidanmu ba qaramin dan rainin wayo bane,lokacin Ina yarinya babu irin muguntar da baimun ba,Amma Yanxu Wlh idan yae gangancin tabani sae yasha mamaki.
Me zakiyi? Aysha ta tambaya tana kallon hindatu take ta faman balaee tace Wlh ramawa zanyi,kinsan nipa b qyalle bace.
Murmushi Aysha tayi tace to kinga duk masifar ya Adam baifa Kai ya Sa'ad ba, wlh ni ban taba ganin masipappe Kaman y Sa'ad ba,gashi d murdadden hali,ga wulaqanci d gwaliya, matarsa ta shiga 3! Kinsan fa sanda muna ss2 danae rashin lpy na dawo gida,to Shima yazo yayi 1 wk,
Wlh hindatu da rawar Kaina bawan Allahn nan yace n gyara masa daki,wae na gama gyarawa pa, na dauko kayansa Ina dan goge masa waeni mutuniyar Arxiqi,tsautsayi rigar nan ta qone.
Ya Sa'ad bai dubi aekin dana masa ba,ya kamani ya dinga jibgata kamar sakwara,bazan taba mantawa b ranar n masa Allah ya isa fiye d sau dubu, kalli pa yanda y jimin ciwo,har saida akaemin dinki ta fada tana nunawa hindatu qaurinta.
Numfashi hindatu ta sauke ta kalli Aysha tace ashe kuwa zamu dambace.
Dawa zaku dambace din?
Wlh da duk wanda y daken,ae jiya ba yau bace,dole a sakarmin mara nae fitsari.
"Lallai ma hindatu,kin dade baki gansu bane,amma idan kin gansu zaki Maida kalamanki"
Hk kike gani pa,kins.....ringing din wayarta ne ya katseta ta juya ta dauki wayar,ganin number din umma yasa gabanta ya fadi ta dauka a sabule tace hello!
Sannu gantalalliya! Ina kikaje? Umma Ina gidansu Aysha pa ba wani gurin naje b.
Cikin fada umma tace wa kika tambaya?gantali gardi?
Allah ya baki haquri, sorry for urself hindatu. Kuma wallahi ki maza2 ki dawo kafin baffanki ya shigo gidan nan.
"Umma plz ki bari ae la'asar". Ban bari ba ki dawo yanxu! Tana kaiwa tai karab ta kashe wayar.
Cikeda takaici tabi wayar da kallo tareda miqewa tace Aysha I'm going, umma ta kira.
Ba damuwa muje n rakaki ki hau mota. A falo taewa ummi sallama, ummi tace kije driver y maidaki gida, ki gaidamun da mamanki
[21/04, 23:33] Hassan India: Miss collapse
(16)
👠SATAR FITA💃🏽
Zataji ummy,n gode ta fada tareda ficewa.
Driver na sauketa motar baffa ta danno kai, a tsorace ta rufe motar ta cikin gida da gudi tana hakki.
Kallan motar baffa yayi sannan ya wuce gida fuskarsa a daure tamau
Tana shiga gida ta shige dakinta,ta sauke hijab din jikinta kenan baffa ya banko qofar fuskarsa a daure yake kallonta sama d qasa sannan yace wani dan iskan ne yae dropping dinki yanxu?
Baya tadan matsa ta jingina da toilet din dakin tace baffa driver gidansu Aysha ne Wlh.
Qarya kikeyi! Idan driver ne mesa baki shiga baya b sae gaba?
Wlh baffa da gsk nk,k kira ummyn ka tambayeta.
Hannu baffa yasa a Aljihu ya zaro wayarsa ya dannawa ummy kira.
Hindatu tazo nan gidanki? Shine tambayar da ya fara mata
Bayan en seconds kuma saeya sauke wayan yana kallon hindatun yace Allah y ceceki,ya fice daga dakin.
Da daddare duka suna zaune a falo bayan sun idda cin abinci hindatu ta kalli baffa tace baffana dama akwai abunda nakeson fada mk.
"Toooh,Ina jinki hindatu"
Baffa dama so nakeyi idan babu matsala zan koma hostel d zama nxt session.
A mamakance baffa yake kallonta yana nazarin maganarta.
Can ya nisa yace ko meyasa? Akwai wani abu d kika rasa ne d kike tunanin hostel din yafi miki?
Tsagwal aminu yace baffa babu wani abu da aka mata,tsabar tsugudidi ne wae dan nace ya Adam zae dawo shine take cewa baxata zauna dashi ba.
Akanme? Baffa y tambaya yana kallon hindatu tana cika famm da ruwan masipa
Baffa nifa b ruwana da wani ya Adam,inason komawa ne saboda karatu na zaefi acan,kuma Shi Aminun dayake cewa baxa'a barni ba aeshi naga wata uwa duniyar yaje yae karatu.
Ajiyar zuciya ya sauke me dan nauyi yace toh hindatu bazan Iya barinki ki zauna a hostel ba, banida sha'awar haka.
Amma baff...Hannu ya daga Alamun baeson ji. A zuciye ta miqe tana hararar Amin tae dakinta cike d baqin ciki.
Qarfe 3:00 suka fito daga exams,amma saeta gabzawa dady qarya tace sae 6 zasu fito. Tana fitowa kuwa ta qarasa
[21/04, 23:33] Hassan India: Miss collapse
(17)
👠SATAR FITA💃🏽
kuwa ta qarasa jikin motar Ibrahim dan dama yace mata yana jiranta.
Gaban motar ta zauna yaja motar suna tafe suna hira sama2, a hanya baffa na tuqi ya hangota cikin motar Ibrahim suna hira,ranshi ya baci sosae amma saeya share ya wuce gida tunda basu ganshi b.
Shoprite suka zarce zuwa cinema sukai kallonsu,sae 6: 00 suka fito, tafe suke suna hira sama2 har suka qaraso inda sukae parking ta shiga suka fara tafiya,hira sukeyi cikeda nishadi basu ankara b sukaga wata mota tasha gabansu
A zuciye matar dake cikin motar ta fito,kallon Ibrahim nayi dan naga tana yowa side dina a fusace, da sauri ya qarasa inda take yana cewa shafa'a dakata plz,banason shirme akan hanya
A kufule ta juyo tana nunashi da yatsa tace dakata Ibrahim,dama n dade inajin maganganu akan karuwan da kake dauka a motarka kuna yawon banza ban taba yadda b saeyau dana gani d idona.
Shafa wannan fa b karuwa bace,wannan wata irin magana ce?
Bata saurareshi ba sae gani nae ta qaraso inda hindatu take ta bude motar ta fincikota, fito munafika,aeba motar ubanki bne.
Kallon sama d qasa hindatu tae mata sannan tace keh da Allah cikani ta fada tareda fincike hannunta, dubeki dallah,tsabar rashin tarbiyya kizo kina yiwa mutun fitsara a tsakiyar titi! Wlh n raina clx dinki sannan kuma karki qara gangancin tabani.
Kallon Ibrahim tayi ta tabe baki sannan tace wlh indae wannan ce matarka kayi asarar aure,mace b tarbiyyah
Kan ubahh! Ibrahim kanaji abinda wannan qaramar er iskar take fadamin! Wannan tatsitsiyar yarinyar da a haihuwar tumaki na haifeta?
Takaeci kadae y hana Ibrahim magana.
Rashin Sa'a akayi Niba tinkiya bace,kedae d kike tinkiya saeki tayi,
A harzuqe Ibrahim yace ya isheni plxxx! Ku duba kuga yadda kuka taramin jama'a Kaman wani barawo! Hindatu koma mota lemme take u home! Komawa hindatu tayi shafa ta fara zage2 cewa wallahi vazata shiga mota b tunda bata ubanta bace,
Shafa dan Allah ki koma gida zamuyi mgn ta fahimtar juna dake.
[21/04, 23:33] Hassan India: Miss collapse
(18)
👠SATAR FITA💃🏽
Baibi takan taba yaja motarsa da qarfi hindatu na masa kwatance har gida.
A bayan gidansu ya sauketa tana qoqarin fitowa taga baffa riqe da carbi da Alama masallaci zaeje. A fili tace innalillahi wa inna ilaihi rajiuun
Dukda ran Ibrahim a bace yake bae hana yace Lpy ba
Na shiga 3 baffa na,shikenan yau na mutu!
Da mamaki Ibrahim yace Lpy kuwa,ki tsaidashi mana naje n gaidashi
Kallonsa hindatu tai tace mlm bazaka gane bane,kaje kawai tana fadan haka ta fito da saurinta ta shiga gida.
Gaba1 ranar sukuku tayi ta, jiran dukan baffa kawai takeyi amma ga mamakinta ko mgn bai mata b,dan hk sae itama ta saki jikinta.
Yau Hindatu na zaune a falo tana nazarin. Course din da za'ae gobe umma kuma tana kitchen taga Aminu ya shigo janye da qatuwar akwati.
Da mamaki take kallonsa Kaman zatayi mgn sae kuma ta fuske a cewarta karya rainata.
Wata daddadar murya ce tae sallama wanda y tilasta hindatu Maida kallonta ga qofa.
Suit ce dark blue a jikinsa,takalminsa baqin covered shoe ne qirar Gucci,hannunsa daure da agogon dolcee&gabbana
Dogone tsayayyan namiji,fatarshi kalar chocolate,yadan tara gashi kadan a kanshi amma bada yawaba,shine ya qarawa cikakkiyar fuskarsa kyau da kwarjini.
Sosae suke kama da hindatu kaman an tsaga kara,tsaf zakayi zaton ko namiji ne,marabar su kawai wannan yadan manyanta dan a qaiqaice zae doshi shekara 28.
Tsaf hindatu ta kalleshi,qoqari takeyi sosae ta tuno inda tasan fuskar,Shima idanuwansa nakan hindatu yana qare mata kallo tareda mamakin rashin kunya irin tata da zataga mutim bazata gaidashi ba balle tae masa iso.
Fitowar umma ce t katse tunaninsu,lalee marhabun da zuwan baqaqen larabawa,wato dama yau zaka dawo shine dan shaqiyanci baka fadamin ba kuma aminu ma ya kasa fadamin?
Murmushi mae kyau yayi har saeda dimples dinsa suka bayyano ya qarasa ya rungume umma yana fadin I miss u a lot ummanah.
Murmushi umma tae tace miss u too Adam, ta fada tana shafar sumar kansa
[21/04, 23:33] Hassan India: Miss collapse
(19)
👠SATAR FITA💃🏽
Tsaf hindatu ta kalleshi,qoqari takeyi sosae ta tuno inda tasan fuskar,Shima idanuwansa nakan hindatu yana qare mata kallo tareda mamakin rashin kunya irin tata da zataga mutum bazata gaidashi ba balle tae masa iso.
Fitowar umma ce t katse tunaninsu,lalee marhabun da zuwan baqaqen larabawa,wato dama yau zaka dawo shine dan shaqiyanci baka fadamin ba kuma aminu ma ya kasa fadamin?
Murmushi mae kyau yayi har saeda dimples dinsa suka bayyano ya qarasa ya rungume umma yana fadin I miss u a lot ummanah.
Murmushi umma tae tace miss u too Adam, ta fada tana shafar sumar kansa sannan ta zareshi daga jikinta ta zaunar dashi a kujerar gefen hindatu.
Kallon hindatu tae dake faman raba idanuwa tace keh baki Iya gaida mutane b koh?
"Daure fuskarta tae tace suma mutanen basu nuna sun sanni bane shiyasa"
Cikeda takaici umma tace hindatu kin kyauta,Amma wlh sae naci ubanki tunda bakida kunya
Adam dake zaune gefen ummah ya maimaita sunan hindatu a ransa tareda mamakin girman da tayi,y sake dagowa yana kallonta zaiyi mgn suka hada Ido.
Harara ta galla masa tareda jan Dogon tsaki ta kwashi papers dinta tae cikin tana fadin haka kurum za'azo ae disturbing peace din mutum tayi ciki da sauri tareda banko qofa.
Da kallo suka rakata gaba1,Adam ya kalli umma yace umma wae wannan ba hindatun gidan nan bace?
"Eh itace mana"
Amma umma yarinyar nan batada kunya,haka take miki fitsara qiri2?
Murmushin takaici umma tae tace toh Adam zansa hindatu a raina ne tasamin ciwon zuciya? Wlh dagani har baffanku mun rasa yadda zamuyi da ita.
Kallon umma yae zaiyi magana sukaji sallama. Aysha ce ta shigo har qasa ta zube tana gaida umma, da fara'a umma ta amsa sannan ta gaida Adam, shima amsawa yayi ta miqe tayi dakin Hindu dan umma tace mata tana ciki. Binta da kallo Adam yayi harta shige sannan y juyo yana kallon umma yace "wacece wannan kuma"?
Ka manta Aysha er gidan Aunty ruma?
Haba dae umma?wannan qanwar sa'ad ce? naga ta girma
[21/04, 23:34] Hassan India: Miss collapse
(20)
👠SATAR FITA💃🏽
Murmushi umma tae ta tashi ta shige kitchen tana cewa to kodae dan nawa yana cikine.
Aysha ce ta kalli hindatu data maida hankalinta tana naxarin littafin gabanta, hannu Aysha tasa ta fincike littafin hindatu tae saurin dagowa tana kallon Aysha tace wlh kin bani tsoro! Yaushe kika shigo?
Zama Aysha tae a gefen gadon hindatu tana murmushi.
Zama hindatu tayi tana kallon Aysha tace keh lpy kike smiling?
Keh wlh yayanki ya gama haduwa! Ya gaji da haduwa wow! Aysha ta fada tana zabga murmushi
Aminun ne ya hadu? Hindatu ta tambaya tana tabe bakinta.
Ke dallah bashi ba, ya Adam mana, ba shine nagani a falo ba.
Oho miki! Shine kuma zakice yayana? Ni malama Aminu ne kawai yayana.
Ke kika sani ae, kamarku 1 duk inda kikaje haka za'a fada.
Allah ya isa Aysha,wlh kin cuceni kin gama dani
Oh haka kike cewa? ya fiki kyau fa.
Hararar Aysha tae ra finciki littafinta ta cigaba da karantawa.
Sae kusan 8 Aysha ta fito zata tafi, gaisawa sukai da baffan dake zaune yana kallon labarai tayiwa umma da Adam sallama.
Umma ta kalli Adam daya raka Aysha da kallo tae murmushi tace Adam yah maganar aure kuwa?k samo mana suruka koh?
Tsalam ya miqe yace umma ae mata saidae ki zabomin.
Toh baga Aysha ba naga ka yaba.
Gaba yae da sauri yayi part dinsu yana shafa qeya dan bayaso umma ta kunyatashi a gaban baffa.
Amma a zahiri Aysha tayi masa 100% saidai yana gudun raini irin na yan matan yanxu musamman ita datake qawar hindatu, kuma a yan awannin dayayi a gidan y riga y fahimci hindatu Sam batada kunya.
Tsam Riga da skirt din data saka suka matseta, tayi kwalliyarta tsaf ta fito ta tadda baffa ya ajiye mata kudin makaranta a falo. Dauka tae ta zura a hadaddiyar purse dinta har tayi niyyar taje ta gaida umma wayarta ta fara ringing
Kallon screen din wayar tayi taga an rubuta Fauzy fashion. Wata er clz dinsu ce da suke good time da ita. Kara wayar tayi a kunnenta tana amsawa sannan ta tura qofar falon ta fita
[21/04, 23:34] Hassan India: Miss collapse
(21)
👠SATAR FITA💃🏽
Kallon screen din wayar tayi taga an rubuta Fauzy fashion. Wata er clz dinsu ce da suke good time da ita. Kara wayar tayi a kunnenta tana amsawa sannan ta tura qofar falon ta fita tana sauraran abinda fauzy take fada mata.
Kehh! Taji an fada a bayanta
Juyowa tayi fuskarta a daure tana kallon Adam. Katse wayar tayi tareda jefawa a cikin jaka ta maida dubanta kanshi saboda taga yana takowa inda take.
Kallon sama ta qasa yayi mata sannan yace ina zakije da sassafen nan?
"A gatsine tace skul zanje mana"
"School" ya maimata tareda sake dubanta yace a haka zakije school din?
Duban kanta tayi sama da qasa. Cikakkiyar shigar hausawa tayi.
Atamface a jikinta dinkin riga da skirt, rigar ta sauko mata ta baya, sabon salon dinkin da ake kira shoky, sai tayi rolling da siririn mayafi a kanta kaman yanda yan matan yanxu sukeyi.
Ganin babu laifin daya samu kayan jikintane ya sata kallonshi kamar zatae mgn sai kuma ta juya ta fara tafiya.
Finciko hannunta yayi rai a bace yace keh dan bakida kunya kinaji ina miki mgn zaki shareni wato kin maidani dan iska koh?
Itama daure fuskarta tayi tareda fincike hannunta a fusace tace malam karka sake gangancin tabani! Ina ruwanka da yadda nae dressing dina banda tsabar shishshigi da sshiga likkafanin kishiya meye matsalarka dani? tunda kazo gidan nan kaga nai maka magana ne? Wlh da ba yanxu bane babu wanda ya isa ya takuramin idan ba hakaba na gaggayawa mutum magana.
Tunda ta fara maganar Adam ya saki baki yana kallonta da mugun mamaki! wannan tatsitsiyar yarinyar ce zata tsaya a gabansa tana gaggaya masa magana yadda taso!
Qarar bude gate din datayi ne ya dawo dashi daga tunaninsa. Da sauri2 ya fice ya hangota tana tafiya zata qarasa inda Audi Yai parking. Yana qarasawa baiyi wata2 ba ya fincikota. Tana juyowa ya falla mata wani bahagon Mari.
Jinta da ganinta ne suka dauke na wucin gadi. Wasu jajayen taurari take gani a idanuwanta har a lokacin ta kasa tantance me
[21/04, 23:34] Hassan India: Miss collapse
(22)
👠SATAR FITA💃🏽
Jinta da ganinta ne suka dauke na wucin gadi. Wasu jajayen taurari take gani a idanuwanta har a lokacin ta kasa tantance me yake faruwa.
Fincikar da yai matane ya dawo da ita hayyacinta aeko ta fasa ihu ta zube. Bai damu da faduwar da tayiba ya finciketa a qasa har cikin falon ya yasar da ita.
Umma dake kitchen tae saurin fitowa tana baza idanuwa tana kallonsu.
Ko ba'a fada ba tasan hindatu ce ta aikata wata fitsarar dan haka saita juya ba tareda tace qala ba.
Baffa nema yace lpy dae adamu? Ranshi a bace ya fadawa bbaffa yadda sukayi da hindatu.
Ka kyautamin Adam Allah ya maka Albarka. Na baka go ahead duk sanda hindatu ta aikata ba daidai ba kaimin maganinta.
Ihuuu tasaka tareda miqewa tana fadin baffa dama nasan baka qaunata shiyasa kakemin duk Irin wadan nan abubuwan! Kai kuma ya adam sae Allah ya sakamim.
Da haka ta shige dakinta ta fada kan gado. Saida tayi kuka mai isarta sannan ta miqe.
A dole ta sake wanka dan tayi futu2. Doguwar rigar Atamfa ta saka ta fito. Daure fuskarta tayi sosae ta fice ba tareda tacewa wani kanzil ba.
A masallaci Aysha take bawa Aysha labarin abunda ya faru. Aiko Aysha ta dinga qyaqyata dariya harda hawaye
Iya wuya hindatu tazo ta miqe a fusace zata fita aysha ta riqota
"Sorry ma'am wlh kin bani dariya ne. Keda kika gama cika baki kuma sae naga anyi miki 1 blow har an toshe bakin fitsara.
Wani malalacin smile hindatu tae tace Aysha kenan ae shammata na yayi kuma wlh kinji Allah kenan! bai mari burus ba wlh saena masa kafirin wulaqancin da zaiyi dana sanin marina dayayi
Aysha a gaban jama'a ya aAdam zai dallamin mari! Chabbbb.
Toh hajja hindatu kibi a hankali karkije ki janyowa kanki jibga.
Yauwa bari kiga
Hannu aysha tasa a bag dinta ta zaro IV ta ajiyewa hindatu a cinyarta.
Cikin rashin fahimta hindatu ta dauki card din ta karanta. Kamal ne zaiyi birthday?
Langwabar dakae Aysha tae tace eh wlh! Dazun nan saida mukai rigima dashi sabida nace baza
[21/04, 23:34] Hassan India: Miss collapse
(23)
👠SATAR FITA💃
Langwabar dakae Aysha tae tace eh wlh! Dazun nan saida mukai rigima dashi sabida nace bazanyi attending ba.
Saboda me? Hindatu ta tambaya a mamakance.
Bakiga tym en b? 8:00pm za'a fara pa. To saeme wlh ki shirya muje.
Ta yaya?kinsan ummy bazata taba barina ba.
Zo kiji" matsowa Aysha tae hindatu ta rada mata wata magana.
Qwalo idanuwa Aysha tae tace kai hindatu ba ruwana,kar asamu problem.
Tsaki hindatu tayi tace ae sai kiyi,dama bakiyi niyyar zuwa ba.
To naji zanyi, a ina zamu hadu?
Dan sosae Kai hindatu tae tace kuzo daidae bayan gidanmu.
Toh Aysha tace suka miqe Aysha na sake jaddadawa hindatu nisan gurin.
A qule ta koma gida dan har yanxu bata huce abinda Adam yae mata ba.
Tana ganinshi a qofar gida suna hira da wasu friends dinshi,suna hada ido ta balla mai harara ta wuce ciki.
Amin ne zaune a falo yana buga game sae umma dake amsa waya. Tsakin dataja ne ya dago dasu abun ma yaso ya basu dariya yadda ta shige daki ta banko musu qofa. Throughout ranar bata kula kowa a gidan ba sae faman cika take tana batsewa.
Ranar birthday-
Yau Saturday,Aysha na kwance a dakinta misalin qarfe 7:48 tana kitsa ta yadda zata fita ba tareda kowa ya ganta ba.
Shawarar da hindatu ta bata ta dauka, tsalam ta miqe tsaye ta janyo pillows din dake kan gadonta ta jeresu guri 1 ta lullubesu kamar mutum sannan ta miqe ta dauki Jakarta.
Tsaf ta shirya kayan ta zata tafi dasu da kuma makeup kit dinta ta jefa ta window din dakin sannan ta haura ta window din.
Sadaf sadaf ta wuce zuwa gate din gidan ta tadda mai gadinsu yana sauraren radio.
Gabanta ne ya fadi dan kwata2 a plan dinsu basu saka dashi b.
Kallonta Bala yayi saboda hasken fitulin gidan sun hasketa sosae da mamaki yace indo ina zakije da tsohon daren nan?
Murmushin yaqe tayi tae bala kaga wlh magani zanje n siyo a chemist din bayan layin nan.
Ah kawo n siyo miki mana. Babu musu ta zaro 200 tace panadol zakace.
[21/04, 23:35] Hassan India: Miss collapse