Purse dinta ta bude ta zaro wayar Aysha tace g wayarki zamu dinga mgn dukda dae n ganki d wata.
" Alh Musa ne y siyo ya aiko dazu da safe da nace wa Abba wayata ta bata" Aysha ta bata amsa tana qoqarin bude toilet, margin da isha duk a gidan sukayi sannan suka daura da wata hirar, larai ce ta katse musu hira data shigo tace hindatu tazo inji ummy wae yayanta yaxo. Gyalenta ta yafa tace Aysha muje ki rakani.
A falon ummy suka taddashi sunata hira da ummy da Alama akan sa'ad suke magana,gefe Aysha ta duqa ta gaidashi, amsawa yayi yana dubanta yace ya jikin?
Ummy dake qoqarin miqewa tace A'ah tace mk batada lfy ne?
Gyada kai yayi yace naga ta rame ne ummy har ina tunanin zuwa da Alluraina. Guntuwar dariya ummy tae Aysha ta qara qasa da kanta ummy tace sannu bokan turai. Saeda sukayi gaba ummy tacewa hindatu kicewa mamanki next week tazo karbar lefe. A tsorace hindatu ta juyo zatae mgn ummy ta juya tana fadin a gaida gida Adam.
Zugum hindatu tae a mota ta kasa magana har suka qarasa gida, bata kula kowaba tae cikin daki ta kwanta tareda rumtse idonta,nisa sosae daren yayi mata sae faman juye2 takeyi tana neman mafita gamma sam mafitar bata samu b,sae bayan asbah bacci yayi nasarar yin awon gaba da ita, da safe kam da ciwon kai ta tashi saeda tasha magani,baffa m saida y tambayeta ko wani abu yana damunta tace aa.
Tuwon dare umma take kwashewa hindatu kuma na gefenta tana aikin yankan kubewa,tayi nisa sosae cikin tunani bataji maganar d umma ke mata b saeda t qwace wuqar hannunta sannan ta dago a zabure
Ke hindatu anya kuwa lafiyarki na lura fa tun jiya d kika dawo ba qalau kike ba wani abun ne ya faru?
Ciccikowa idanuwanta sukae da qwalla ta kalli umma tace ummy tace na fada miki next week karban lefen Aysha....
Aysha kuma! Umma ta maimaita tana xaro idanuwa! Eh umma kuma wlh auren dole xasu mata dan Aysha batason mutumin ta qarashe maganar ragowar hawayen data maqale suka kwararo.
[21/04, 22:04] Hassan India: Miss collapse
(44)
👠SATAR FITA💃🏽
Amma saboda me?umma ta tambayi hindatu tana gyara zaninta. Umma duk akan laifina ne danaja hindatu rannan shine abbansu yaganmu a newspaper.
Dafe qirji umma tae tace jarida kuma hindatu!n shiga 3! Yanxu abunda kukaja a kanku kenan?
Cikin sheshsheqa hindatu tace wlh umma ba ruwan Aysha laifina ne, taya abbanta zai aura mata mutum sa'ansa mai mata 3 da yaya har 28.
Laqwas umma tai tana kallon hindatu a zuciyarta tana nanata wannan bahagon lamary, saedai kuma ta kasa tankawa har zuwa wani lokaci kitchen din yayi tsit sae sautin kukan hindatu dake tashi. Dafa kafadarta umma tae tace share hawayenki hindatu insha Allah zan samawa Aysha mafita,baxan bari rayuwarta ta lalace saboda wannan dalilin ba,idan basu sonta aeni ina sonta.
Wani dadine ya ratsa hindatu har saeda wata dariya ta subuce mata ta rungume umma tana zuba godiya.
2 days later--
Keh hindatu maza ki fito mana sae shegen nawa kamar hawainiya. Da saurinta ta fito mayafinta a hannu tana fadin ganinan fa umma inata zuba sauri ko powder ban shafa ba.
Tabe baki umma tae tace wuce da'Allah ayi rabu dani mutum sae shegen son kwalliya kamar yar Aljanu. Baki ta turo tayi gaba, bayan mota ta shige umma ta zauna a gaba har suka qarasa
Da sallamarsu suka shiga gidan, larai ce ta taresu har falon ummy dan lokacin ummyn tana toilet,saida ta cikasu ta kayan ciye2 tabar gurin, itama hindatu dakin Aysha ta shige tana fada mata tareda umma sukazo,fitowa tae ta gaidata sannan suka koma, suna komawa ummy ta shigo falon tana washe bakinta cikeda farin cikin ganin umma, Aminiyarta kuma matar yayanta, duqawa Aminu yayi yana gaida umma tace aeni bazan amsa gaisuwarka ba Aminu,ace ka dawo kasarnan k kasa zuwa gidana koh gaba mukeyi ae sai haka.
Sosa qeyarsa yayi cikin jin kunya yace wlh ummy na dade inason zuwa amma tunda n dawo ban samu zamaba abubuwa sunyi yawa. Qorafi bai karbu ba mlm aminu, sae kaxo gidannan kayimun wuni sannan zan iya saurarenka
[21/04, 22:04] Hassan India: Miss collapse
(45)
👠 SATAR FITA💃🏽
Kiyi haquri ummy zanzo yanxuma akan hanya nake wlh!
Ahaf!kinji koh Amina shima Adam haka yamin kwanaki kamar wandanda ake mitsilinsu. Dariya yayi yace zan dawo anjima ummyna.
Hira ce ta barke sosae tsakanin ummy da umma abunka da aminae har yamma,can dae umma ta muskuta ta kalli ummy tace ruma dama wata magana hindatu tazomin da ita ban fahimta ba shine nace gwara kawae nazo da kaina naji.
Wani zance kenan?ummy ta tambaya tana murmushi
Hindatu ta cemin wae kince karban lefen Aysha next week?
Hakane Amina,Auren Aysha yazo min a bazata shiyasa banyi miki bayani d wuri ba,amma dae kiyi haquri.
Kallon takaici umman ke yiwa ummy sannan tace toh shi mijin a ina suka hadu?
Amina nifa babu abunda na sani wlh!Abbanta ne y kawo mutumin yace shi zae aura mata kinga kuwa ae yasan mutumin kirki ne koh?
Eh lallai pa mutumin kirki! Yanxu ruma tsakaninki da Allah Abunda kuke shirin qullawa Aysha yayi daidai kenan? Saboda kawae kuna zarginta akan abunda bakuda tabbas shine zaku aurar da ita ga mutumin da bataso haba rumah!!
Amma Amina kinsan cewa da idanuwana naga photon Aysha a jarida cikin gungun karuwan da aka kama,akanme zan qaryata abunda n gani?
Dakata ruma! Hindatu ta fadamin duk yanda abun ya faru.nan danan umma ta shaidawa ummy duk abunda hindatu ta fada mata, dukda jikin ummy yayi sanyi saeda tace yanxu Amina daga hindatu ta fada miki magana saiki yadda?
Banida dalilin qin yadda ruma! Nasan cewa hindatu da Aisha basujin magana kuma basuda kunya amma kuma sam basa shashanci da maza zan iya shaidarsu akan wannan, kema kuma kin san haka bai kamata ki wofantae da yarki sabida wannan tsautsayin ba. Taya zaki yadda aysha ta auri dattijon mutum sa'an Abbanta mai mata 3 harda tarin y'ay'aye, ta yaya kike zaton Aysha zatayi zaman kishi da gogaggun mata sa'annin iyayenta haba rumah!
A sanyaye ummy ta dago ta kalli umma daketa faman bambami tace toh Amina ya zanyi? kinsan yallabai idan ya yanke hukunci babu
[21/04, 22:16] Hassan India: Miss collapse
(46)
👠 SATAR FITA💃🏽
kinsan yallabai idan ya yanke hukunci babu wanda ya isa ya sauya dominshi sae mahaifiyarsa kinga kuma bazan iya tunkararta da wannan batun ba tunda ta tsufa ga kuma rashin lfy, kuma banaso nayiwa yaya bashir zancen nan dan gudun kada Allura ta tono garma.
Kema kinyi gaskiya ruma amma dae dukda haka dole a tsaida batun Auren. Ki kwantar da hankalinki ruma kuma dan Allah kija Aysha a jiki saboda tasaka abun dayawa a ranta naga harta rame.
Da irin wadannan maganganun umma ta tashi tana qwalawa hindatu kira sukae sallama sabida Already aminu yaxo amma ya maqale a waje yaqi shigowa.
Tun a mota hindatu ta cika umma da tambayar ya sukayi da ummy amma amsar dayace "Bamu gama shawara ba"
Baffa na zaune akan center carpet din falonsa yanata faman kai lomar alkubus din da umma tae masa yana santi,umma dake gefenta saeta jawo pillow ta saka a bayansa tana fadin to ranka shi dade kardai ka fadi, dariya kawae yayi yace ae kona fadi saeki dagoni dan saena cinye wannan Alkubus din.
Saeda yaci ya qoshi sannan umma tace Alh. Baka tambayeni ba me muka tattauna da ruma ba nace mk zanje gidanta.
To yanzu so kike na shiga mgnr aminai haka kurum su gwaleni. Murmushi kawae umma tae tace Alh.ba haka bane wannan wata magana ce mai matuqar muhimmanci wadda ake buqatar kaima k shigo cikinta.
Gyara zama baffa yae yana sauraren umma ganin hakan yasa ta samu qwarin gwiwar yiwa baffa bayani dalla2 akan auren Aysha amma bata yadda sunan hindatu ya fito ba kamar yadda sukae da ummy. Gyada kae baffa ya shigayi yana jujjuya maganar sannan yace Amma nayi mamaki dan jiyama saeda muka dade muna waya d sadauki baimun zancen ba,gaskiya bai kyauta ba idan lallai sae yayiwa Aysha Aure ya samu Miji daidae da ita mana amma ina ita ina Alh. Musa!
K sanshi ne? Umma ta tambayeshi, farin sani ma kuwa, abokin kasuwancin mune kuma mun saba sosae,yakan bani labarin irin tashin hankalin dayake ciki saboda iyalensu kullum ciki rigima suke.
[21/04, 22:17] Hassan India: Miss collapse
(47)
👠 SATAR FITA💃🏽
Amma karku damu insha Allah da kaina zanyiwa sadauki maganar nan.
Ranar Friday da yamma baffa da kanshi ya samu Abba har gida bayan sun gaisa ya sako masa zancen Aysha. Bata fuska Abba yayi yace tooo Ayshatu har qarata ta fara kaiwa? Babu zancen qara sadauki kaima babu wanda ya mk auran dole akanme zaka tura yarinya cikin bala'i qiri2.
Ran Abba a matuqar bace yashe Alh.bashir bakasan abunda yarinyar nan taimun ba. Na sani ae shiyasa nazo d kaina n baka haquri. Haba Alh sadauki! Nipa dan siyasa ne tayaya zan bari yarinyar nan ta batamin reputation dina kuma tae spoiling image dina a idon duniya sannan kuma kace n rabuda ita bazai yiwu ba sadauki wlh bazan qara zaman wata1 da Aysha a gidannan b saidae a dakin mijinta.
Shiru baffa yayi ganin bambamin da Abba yakeyi bazai qareba sae yace to idan hakane sadauki ka bata dama ta fito d wanda takeso kokuma k zaba mata wani.
Alh. Bashir so kakeyi n zama qaramin mutum me canza mgn?
Ko daya Alh sadauki ka kwantar da hankalinka da kaina zan samu Alh Musa na bashi haquri kuma baza'a fasa mgnr auren aysha ba ammafa da WANI MIJIN. Babu yadda Alh.sadauki ya iya dole ya yadda d mgnr Aminin nasa bwae dan yaso b.
Har ciki baffaa ya shiga suka gaisa da ummy taeta zuba masa godiya sannan yace a kira masa Aysha. Itama kamar ta rumgume baffa takejI dan murna baffa yace Aysha Abbanki fa bawae ya haquri bane gaba1 sharadi ya bani. Qululuu cikin Aysha ya bata baffa y cigaba d cewa yace ki fitoda wanda kikeso idan kinada shi idan yaso sae ayi musanye. Kamar Aysha tae kuka tace baffa nifa banida Kowa wlh! Shiru baffa yae nadan mintuna can yace to babu damuwa,a cikin yayan abokanmu zan samu wanda zan turo miki,idan kun sasanta kinga shikenan amma fa idan baku sasanta b kimin bayani.
Godiyar da Aysha ta dinga yiwa baffa har saeda ranshi y kusa baci yana tafiya ta shiga daki ta kira hindatu tae mata bayani,wani irin ihu hindatu ta saka kamar tana kusa d Aysha
[21/04, 22:17] Hassan India: Miss collapse
(48)
👠 SATAR FITA💃🏽
Ji take kamar ta kwaso shoky a gurin nan tsabar murna suna gamawa ta tafi d gudu ta fada kan umma tana gaya mata,itama ummah godiyar Allah kawae tayi sae kuma da hada da yiwa hindatu fada, hindatu kam jin umma kawae take amma babu zancen umma dake shiga kunnenta.
Sanda baffa ya dawo yayiwa umma bayani tayi murna sosae,Amma saeta tambayeshi wa yakeda shi dazae tura, shiru baffa yayi can yace da ace Aminu yadan manyanta dashi xan tura amma a ganina yanxu bazai iya riqe Mata dakyau ba. Da gaskiyarka Alh.nikuma a ganina me zae hana muyiwa Adam magana idan bashida wata yaje ya nemi Aysha tunda er uwarsa ce kuma naga kamar zasu daidaeta. Baffa yaji dadin bayanin umma dan haka yace tayiwa Adam maganar.
Nayi kwance daedai akan 3seater din dake falonmu inajin dadin fankar dake wulwulawa a gefena kunnena maqale da earpiece kuma ina chatting duk a lokacin umma ta shigo,bansan magana takemin ba saeda ta dakan duka sannan na miqe a gigice ina sosa cinyana.
Daura fuska umma tayi tana fadin wato hindatu duk fadan da nake miki akan saka earpiece bakyaji ko? Turo baki nae nace sorry,guntun tsaki kawae tae tace maxa jeki kirawomin yayanki a dakinsa. Umma yanxufa Aminun ya fita yacemin sunada match. Ba tareda ta kalleni ba tace Adam nake nufi kice ya sameni a dakinsa. Nan danan fara'ar fuskarta ta dauke dan a rayuwa n tsani abunda zae hadani da ya Adam, amma ya na iya. Dakinshi na nufa cike dajin haushi na fara knocking, jin bae Amsaba yasa na danna kai cikin dakin ina baxa idanuwa.
Kwance na riskeshi akan gado yana amsa waya hankalinshi kwace,da alama yanajin dadin wayarne.
Amma duk gulmana n rasa gane da wanda yakeyin wayan. Dagowa yayi y kalleni da fararen idanuwansa ya yafitoni d hannu alamun naxo, ba musu n qarasa kusa dashi n zauna shima zaman yayi amma har a lokacin amsa waya yakeyi, a hankali ya riqo hannuna da dayan hannunsa da bae riqe wayaba yana murzawa a hankali, sosae na tsani wannan halin nashi dan duk
[21/04, 22:17] Hassan India: Miss collapse
(49)
👠 SATAR FITA💃
a hankali ya riqo hannuna da dayan hannunsa da bae riqe wayaba yana murzawa a hankali, sosae na tsani wannan halin nashi dan duk sanda zamuyi zaman arziqi dashi dole saeya riqemin hannuna kokuma ya kafeni da idanuwansa,a ganina kam Sam haka bae daceba a addininmu da kuma Al'adarmu ta Fulani. Can dai naji yace ok dude, nidae kasan yadda zakayi duk balaee ace next week kana 9ja dan ba qaramin missing dinka nakeba, bansan me akace a dayan bangarenba sae naji yace take care ya katse wayar.
Kallon nan yayi yawa madam! Abunda ya fada kenan daya dawo dani daga dogon tunanin dana tafi.
Lafiya zaki shigomin daki babu sallama? Haushine ya cikani na kalleshi nace aeko masallaci zan sauke anan baxakaji ba tunda kana waya da budurwarka,na zare hannunsa daga nawa miqe nae gaba ina cewa, umma tana nemanka a dakinta yanxu,ina fadar haka n banko masa qofa
Da ido ya bita yana mamakin rashin kunya irin tata, Sam bakinta baya mutuwa,dole yae maganin hindatu ya fada a ransa tareda miqewa.
Dakin umma ya wuce a lokacin tana qarasa shirya kayanta a wardrobe, gefen gado ta samu ta zauna shikuma yaja kujerar mirror ya zauna yana fuskantarta.
Saida umma ta fahimci yanayinsa sannan tace Adam wae nikam har yanzu babu wata tsayayyiya da kakeda ita wadda zaka aura?a shekarunka ya kamata ace ka ajje iyali tunda kanada aekinka mai kyau da gidanka Alhamdulillah.
Guntun murmushi ya saki yana kallon umma harta gama sannan yace umma tun tuni fa nace ki naimamin mata,saboda a zahiri tunda na dawo Nigeria banga wata wadda taemin ba.
Zama umma ta gyara tana godewa Allah a zuciyarta tace nikuma naga wadda taimun Adam,kuma na yaba da tarbiyarta da halayenta,munyi maganar da baffanka harya samu mahaifinta da zancen amma bansan ko zaka sota ba.
Murmushi mai sauti yayi yace umma banida zabi,indai kinga tayi miki shikenan,ni gurina babu damuwa.
Sosae umma taji dadin zancensa sae ta sake murmusawa tace bazaka tambayeni wacece matar ba?
[21/04, 22:18] Hassan India: Miss collapse
(50)
👠 SATAR FITA💃
Kallon umma yae da alamun tambaya a idanuwansa umma tace Aysha ce ta gidan ummy rumah qanwar sa'ad mun gama maganar komae da iyayenta cikin 3 wks akeson komae ya kammala.
Dammm!gaban Adam ya fadi zuciyarsa ta fara bugawa da sauri d sauri, mesa sae Aysha umma zata gano masa, shidae yasan Aysha cikakkiyar mace ce batada wata damuwa amma a ganinsa tayi qanqanta ainun a matsayin matarsa shi yafiso ya auri macen d At least tae shekaru 25 sannan kum.... katse masa tunani umma tae ta hanyar cewa babu tilastawa Adam,shawara ce na baka a matsayina na mahaifiyarka inaso kaje kayi tunani mai kyau saboda karka cutu.
Murmushi kawae Adam yayi yace umma ni gurina babu matsala,n yadda na amince da zabinki koba komae Aysha er uwata ce
Ba qaramin farinciki umma tayi ba wanda harya kasa boyuwa ta shiga zubawa Adam albarka da kyawawan Addu'oi,basu rabu ba saeda suka tsaida maganar komae Akan shi d Aysha.
Baffanmu da kansa ya samu Alh.Musa yai basa bayanin komae ya bashi haquri,badan yaso ba ya haqura saboda shima matsala sosae yake samu a gurin iyalansa akan batun auren Aysha.
Umma da kanta tayiwa ummy bayanin zuwan Adam itama sosae taji dadin wannan hadin, ita kanta Aysha batasan wainar da ake toyawa ba saeda ummy tace ta shirya baqonta yana falo. Ba wata doguwar kwalliya Aysha tae ba sannan ta fito, ta kasa yardarwa kanta cewa Adam ne, sosae ta rude harya fahimci haka. Saeda ya sake introducing kansa a gurinta sannan ta nutsu, har qasa Aysha tae tana gaidashi farin ciki ya kasa boyuwa a fuskarta ga wata masifar kunyarsa datake ji, dama can Aysha tana qaunar Adam tun farkon ganinsa datai amma tasan ba mutuncintq bane taje tace tana sonsa.
Adam bai wani bata lokaci ba yae mata bayanin dukkanin qudirinsa tae gaggawar amincewa ta hanyar gyada kanta,bai wani jima ba ya miqe bayan sunyi exchanging phone number sannan yace tae list din duk abunda take buqata da wuri tunda bikin yazo da gaggawa, har bakin motarsa Aysha ta
[21/04, 22:18] Hassan India: Miss collapse
(51)
👠 SATAR FITA💃
rakashi ya tafi ransa fes sannan ta koma gida a guje da ihunta, kan ummy ta fada da qarfi tana ihu ummy dake kwance tae saurin miqewa tana cewa keh indoo kanki 1 kuwa? Qanqame ummyn tayi tana fadin Ashe ya Adam ne wlh ummy yayi 100% jinake ko yanxu a daura wlh!!
Harara ummy ta zuba mata tace sannu Aysha!wato ko yanzu a daura! Lallai rashin kunyarki t girmama.
Kai ummy bazaki gane bane,ya Adam dinne he's very cool,smart attractive and.....kawai dai daidai irin mijin danake so, duka ummy takae mata ta zame ta fice tana dariya, tana shiga daki ta kira hindatu, bugun farko hindatu ta dauka,tsalam ta miqe tayi dakinta dan dama kallo sukeyi, yadda taji muryar Aysha kawae tasan tana cikin farinciki ihu kawai Aysha takeyi har hindatu bata fahimtar abunda take cewa, qarshe dae katsewa tae bayan tace kawae kizo gobe akwai lbry mai dadi.
Har Allah2 hindatu take washegary tayi dan taji me Aysha zatace, washegary qarfe 10 tacewa umma zataje gidansu Aysha, umma data riga tasan kwanan zancen sae tace "keh babu inda zakije wuce ki bani guri"
Dafe qirji hindatu tae kamar wani abu ya faru ta fara zubawa umma magiya har saida baffa yasa baki yace mata taje amma kartai dare, Audi na waje tace ya kaita, godiya tayi masa taje ta shirya ta fito da saurinta tae gaba, a bakin gate suka hadu da Adam, bata kulashi ba ta fara qoqarin kaucewa ta gefensa ya janyota baya, cike da takaici ta juyo tana kallonsa.
Daure fuskarsa yayi yace keh bakya ganine zaki bangajeni?
Sakin baki tai cike da mamaki tace ni kuma yaushe na bangajeka?
Harara ya balla mata yace yanxu kenan bazaki bani haquri ba koh? Allah ya baka haquri tace a gajerce tana qoqarin wucewa ya qara rumtse hannunta yace keh meyasa kullum idan zaki fita saeki saka damammun kaya?
Kallon kanta tae sannan ta dubi Adam tace meye ya matse anan?
Harara ya balla Mata yace look@ ur boobs,kamar zasu fito waje kalli yadda hips dinki ya fito wannan ae saikisa mai raunin imani ya
[21/04, 22:18] Hassan India: Miss collapse
(52)
👠 SATAR FITA💃🏽
Harara ya balla Mata yace look@ ur boobs,kamar zasu fito waje kalli yadda hips dinki ya fito wannan ae saikisa mai raunin imani ya samu matsala. Da sauri ta dago tana kallonsa shikuma ya fuske kamar bashi ya fada ba. Lallai ya Adam kunya ta maka qaranci ta fada a zuciyarta amma a fili tsit tae, can dae yace waima ina zakije da sassafe haka?
Gidansu Aysha zanje,sauri nakeyi. Da sauri ya dago kalleta kamar zaeyi mgn sae kuma ya fuske yace OK,bye. Da Sauri tae gaba shikuma y shige ciki.
Washhh!!ta fada lokacin data zauna kusada ummy tana dan dafa bayanta
Aah y'ar gidana meya farune? Wlh ummy bigewa nayi dazan shigo a bayana kinji zafi kuwa?
To sannu,Allah ya kiyaye gaba, tashi kije Ayshan na ciki nasan ba gurina kikazo b. Kwabe fuska tae tace kayy ummy kinsan fa kema ina zuwa gurinki. Murmushi kawae ummyn tai bata tanka ba hindatu tae ciki.
Dade ta zabgawa Ayshan datae daedae tana bacci,a gigice Aysha ta miqe tana Sosa gurin tareda mitstsike idanuwa. Saida ta nutsu sannan ta ballawa hindatu harara tace baqar muguwa wlh saena rama. Hararar wasa hindatu tae mata sannan tace a haka zakiyi auren qarfe 11 kina bacci?
Haba dae! Aysha ta fada tana dirowa daga kan gado tareda kallon agogon dake manne a bangon dakin. Da sauri ta fada toilet hindatu kuma ta kwanta akan gadon.
Saida Aysha tai wanka taci abinci sannan ta waiwayi hindatu daketa faman buga game a wayarta tace keh kinaji?
Dagowa hindatu tae daga kwancen datake tace eh meye labari.
Fari Aysha tadanyi sannan tace jiya wanda baffa yace zai turo yaxo p. Da sauri hindatu ta gyara zama tana fadin haba da Allah yayi miki?
Tsalam Aysha ta miqe ta isa gaban mudubi ta tsaya tana qarewa kanta kallo sannan tace ba dole yaimun ba! Haduwarsa dabance da sauran maxa,isarsa ce ta qara jan hankalina gurinsa,iliminsa da ajinsa,kyansa da kyawun halayensa,namiji ne da duk wata mace zataso ya xama mijinta dan samun kamarsa sai an tona, Hindu haqiqa nayi dace kuma na
[21/04, 22:19] Hassan India: Miss collapse
(53)
👠 SATAR FITA💃🏽
Hindu haqiqa nayi dace kuma na tsinci dami a akala Wanda ban taba zatoba.
Hindatu datae zaman en islamiyya ta rafka uban tagumi tanabin Aysha da kallo kamar ta samu T.V ta muskuta tace kinga Ayshh na gaji da wannan wassafo suffar da kikeyi ki nunan pic ensa kawai
Dariya Aysha tai tace me kikeci na baka na falling down,kedai kawai ki jira, yanxu dai banda shi a pic amma karki damu zaki ganshi a reality, kinsan ma me kuwa? Girgiza kai hindatu tae Aysha tace yanxu da nake kallonki sai nake ganin kamar shine a gabana.
Kallon banza hindatu ta watsa mata tare da fadin kyaji dashi wae meye sunansa? Murmushi Aysha ta saki tareda lashe lips dinta tace sunansa Adam. Chab amma baiyi dacen sunaba kice sunansa daya da yayana, kinsan yanxuma saida mukai dashi wae kullum idan zan fita sai nasa matsatstsun kaya.
Ae da gskiyarsa,kullum kayanki a dame suke kamar zasu tsaga jikinki su fito.
Zanci ubanki wlh hindatu ta fada tana er dariya tace kinsan wlh ko nayi sakakku kafin wata 2 zakiga sun matseni shiyasa kayana basa haura shekara 2 nake canzaja dole.
Canza maganar sukae ta hanyar fara tsare2n yadda biki xai kasance,a ranar sukaje kasuwa suka fidda anko suka rabawa friends ensu n kusa n nesa kuwa suka musu sending ta whatsapp, sai dare hindatu ta koma gida a gajiye,abunka da amara qirjin biki.
Umma da kanta taje Dubai ta hado kayan lefen Aysha,lokacin hindatu taje katsina aka kai lefe,basai n fada muku irin tsaruwar lefen ba,duka duka yanxu biki saura 1 wk.
Kai masha Allah! Hindatu ta fada ta sake maimaitawa data gama ganin uban lefen,lallai angonki yayi qoqari shattu,dole mu gwangwaje a biki, harara wasa Aysha tae mata tace kita batamin suna banxa, anjima fa Adam zaixo,ki fito ku gaisa. Bazan fito ba din er rainin wayo harkin gama boyonsa. Kai hindatu Allah ya baki haquri,ni n isa na boye miki angonmu. Dariya suka kwashe da ita gaba1 hindatu tace na u sabi.
Qarfe 4:15 ce tayiwa Adam a gidansu Aysha,har falo
[21/04, 22:19] Hassan India: Miss collapse
(54&55)
👠 SATAR FITA💃🏽
Qarfe 4:15 ce tayiwa Adam a gidansu Aysha,har falo y shigo suka gaisa da ummy ta tashi ta kira Aysha data cancada ado kamar yau ne bikin hindatu na faman zugata harta fito.
Hira sosae sukeyi da Adam daya sake jikinsa a yanxu,Aysha taiwa hindatu text ta whatsapp tace ta leqo taga surprise en,saida ta bata kusan 15 mins sannan ta zumbulo hijab din Aysha ta fito tana zuba takun nan nata mai cike dajan hankali. Turus ta tsaya acan nesa dasu cikeda tsantsan mamaki,saida ta sake murza idanuwanta sannan ta tabbatar da cewa ya Adam din ne dae,da sauri ta koma ciki ba tareda sun gantaba,haka kurum taji zuciyarta ta cunkushe ta rasa me yake damunta,text din Aysha ne ya dawo da ita tunaninta "bazaki fito ku gaisa ba"?
A gajerce ta mata reply da "na ganshi"
saida Adam ya tafi sannan Aysha ta shigo dakin, kwance ta samu hindatu tayi rub ta ciki tana kallon sama.
A gefen gadon Aysha ta zauna tana kallon hindatu,kusan 2 mins hindatu bata motsaba dukda kuwa tasan da shigowar Ayshan saeda Aysha tadan dagota sannan ta juyo ta kalleta fuskarta a daure. Murmushi Aysha tai tace harney(honey) ya akayi ne. Banza hindatu tai mata ta miqe a fusace ta zari mayafinta zata fita Aysha tai saurin janyota suka dawo kan gadon.
Cwthrt me akai miki ne naga kinata zumbure2?
Tsaki hindatu taja tace Aysha plz sakemin hannuna banason rainin wayo.
Amma hindatu meya faru?wani laifi na miki da zaki fusata haka?
Ban saniba Aysha!ask yourself!hindatu ta fada a fusace tareda zarar purse dinta da takalminta ta fice daga dakin tareda bankowa Aysha qofa, ko ummi bataiwa sallama ba tabar gidan zuciyarta nayi mata mugun zugi....
*** *** ***
Waige2 Adam yake tayi a babban filin jirgin malam Aminu kano, babu abunda yakeson gani a wannan lokacin sama da amininsa kuma dan uwansa SA'AD SADAUKI!, can ya hangoshi yana saukowa daga matattakalar jirgin cikin takunsa na qasaita, dai2 yake takawa kamar maijin tausayin stairs din
[21/04, 22:20] Hassan India: Miss collapse
(54&55)
👠 SATAR FITA💃🏽
dai2 yake takawa kamar maijin tausayin stairs din harya sauko qasa. Dogon namijine sosae tsayayye babu gargada ko doro a tare dashi hakan yasa ya qere yawancin mutanen dake filin jirgin, babu gashi mai yawa a kansa sai dan kadan daya bari wanda ya sauko yayi masa saje ya kuma kewayo ta gefen bakinsa wato quarter million kenan, farine Tass kamar balarabe, wannan hasken a gurin mahaifinsu suka gajeshi,manyan idanuwan da sukaiwa fuskarsa qawanya tareda da kuma dogon hancinsa su suka qara fito da tsabar kyawunsa waje, T-shirt ce dark blue a jikinsa da dogon wando baqi,tsintsiyar hannunsa daure da tsadajjen agogon LV hakama qafarsa take sanye d covered shoe n lv,duk kushenka/ki baka isa k kushe sa'ad ba.
Da sauri na tabo mhiss maria dake gefena nace yah nayi ko saboda kinsan dole inje in kula wancan Arab din yayi 100% kalli 6packs ensa. Dogon tsaki taja tace keh da'Allah gafara bakiga tunda ya sauko yake kallona ba yaga beautiful oyinye. Harara na watsa mata nace a snatching kikafi kauri dama ae na fada tareda maida kaina inda na hangoshi dazu.
Wayam din dana gani ne ya tadamin d hankali nayi saurin juyawa ina wulla idanuwa can na hangoshi rumgume da wani black Arab,sosae Adam yake yanayi da sa'ad amma kallo1 zakasan sa'ad yafishi kyau bawai sabida farin ba. Murmushi kawae suke zabgawa juna Adam yace dude! Nayi bala'in missing dinka a en kwanakin nan ji nake kamar nayi shekara ban ganka b. Hannu sa'ad ya daura akan shoulder en Adam yace haba lil bro!kaida kake gida kenan ma,nida nake wata uwa duniya me zance?
Da sauri nasa hannu n Sosa kunnena, nidae na kasa fahimtar Hausa yake ko turanci koko aa'ah larabci yakeyi,wani irin sautin nakeji yana fitowa a bakinsa wanda ya sani fara gyangyadi a tsaye. Dukan Mhiss maria ta kaimin tace dallah haka kikeson muje mu kulasu saisun rainamu? Kafin nace wani abu sun shige mota sun barmu a tsaye....
Sorry fans! Wasn't online for few days shiyasa kuka jini shiru
[21/04, 22:20] Hassan India: Miss collapse
(56)
👠 SATAR FITA💃🏽
Cikin qwarewa Adam ke tuqa motar fuskarsa dauke da fara'a,sosae yakejin farincikin ganin sa'ad a wannan lokacin,basu tankawa juna ba,dama Adam yasan haka ne zai faru dan sa'ad kwata2 bayada magana sai idan kunyi mugun sabo kokuma ta zama dole.
Can Adam yace bro wae bazaka tambayeni wace matar ba? Tunda na fara maka zancen auren nan saidai k jini kawai.
Kallonshi kawae sa'ad yakeyi ba tareda ya tankaba, Adam ya cigaba da cewa kaifa matsalarka kenan ana maka magana kana sharewa. Murmushi sa'ad yayi ya lashi lips ensa sannan yace to me zance Adams.
As in kace, wace ita, a ina take, a ina kuka hadu a en kwanakin nan da zakuyi aure da dai sauransu amma kayimin shiru kana kallona.
Gyara zama sa'ad yayi yace koma wace ai indai kana sonta ba damuwa,kuma idan kanason n sota ai ko pic enta sai kamin sending ba saina tambayeka ba kaga banson nai maka shighghigi.
Hararar wasa Adam yayi masa daidai lokacin daya tura hancin motar a cikin gidan yace like seriously sa'ad kanada problem babba,yanxu nidin zakace kanawa shishshigi,ashema xakaiwa kanka ya fada tareda zare key en motor hakan ya bawa sa'ad damar bude motar ya fito ba tareda ya bashi amsa ba. Bala driver Adam ya Kira yace ya shigarda kayan cikin gida sannan suka rufa masa baya.
Ummy na zaune a babban falon nasu tana kallon wani Indian film bala ya shigo da kaya, da mamaki ta kalleshi tace bala lpy kuwa na ganka da akwati?
Hajiya,ae angon Aysha ne yaxo da wani balarabe,yanxu ma suna waje. BALARABE kuma ummy ta jinjina maganar tareda yiwa bala alamar ya tafi. Yana fita su sa'ad suka shigo, da tsananin mamaki ummy ta miqe tana kallonsu bakinta a sake. Shima sa'ad din tsayawa yayi yana kallon ummy fuskarsa dauke da fara'a harta bawa dimples dinsa damar bayyana a sarari. Da sauri ya qaraso yana fadin ummyyyhhh ya rumgumeta gamm a jikinta kamar za'a qwaceta,yanda suka rumgumi juna kadai ya isa ya tabbatar maka da yadda sukai missing junansu.
[21/04, 22:20] Hassan India: Miss collapse
(57)
👠 SATAR FITA💃🏽
Sun kwashe kusan 3 mins sannan suka rabu da junansu ummy tace sa'ad kasan yau zaka dawo amma ka kasa gayamin dan shaqiyanci! Cikin sanyin muryarsa yace ba haka bane ummyh kinsan naso fada miki amma Adam yace gara ai muku surprise.
Daquwa ummy taiwa Adam dake zaune a gefe tace ja'iri wato haka zakaimin koh,shaqiyyin yaro.
Dariya Adam yayi yace ba ruwana ummy nifa wasa nakeyi masa shikuma kawai ya dauka gsk. Zama sukayi gaba1 akan kujera ummy tace bari na kira ladidi ta kawo muku abu mai sanyi.
Da sauri sa'ad ya tareta ta hanyar cewa ummy plz banson abun masu aiki ina wannan yarinyar take, yama sunanta...yadan daura hannu aka kamar mai naxari can yace Aliya koh? Harararshi ummy da Adam sukai a tare ummy tace Adam kayiwa abokinka fada sunan qanwarsa yake mantawa. Miqewa Adam yae yana fadin rabu dashi ummyna tsabar rainin wayone kawai sai yace ya manta mutum. Bai jira mai ummyn zatace ba yace ummy sai gobe nizan tafi. Da sauri ummy tace au bazaka ci komai ba ko ruwa? Ummy I'm full dazu fa aka cikan ciki. Murmushi kawai ummyn tai shikuma yace sa'ad na tafi gobe zanzo ka rakani mu cigaba da raba I.V. OK ango sai anjima ya fada yana kwantar da kafadarsa jikin ummy.
Ran hindatu a bace ta qarasa gida,a fusace ta banka gate din ta shiga gidan zuciyarta na tuquqi kamar zata fashe, ta finciki handle din qofar falon, umma ce da aminu a zaune a falon suna hira, gaba tai bata kulasu ba tai cikin dakinta. Dariya aminu ya fashe da ita sannan yace ummah da Alama yau an tabo autar taki. Ranqwashi ummah takai masa tana fadin so kake ka janyota kuzo Ku cikan ciki ko,Ku kullum cikin rigima kamar masu ganin hanjin juna.
Akan gado tai watsi da mayafinta ta zauna a gefen gadon,ita kanta batasan maqasudin bacin ran nata ba,to meye ma abun damuwa saboda Adam zai auri aysha, a ganina abun farinciki ne, amma meyasa kowa ya rufeni,ana biki a gidanmu amma a kasa gayamin! Tsaki mai qarfi taja ta miqe tsaye a fili tace zakuga
[21/04, 22:20] Hassan India: Miss collapse
(58)
👠 SATAR FITA💃🏽
Tsaki mai qarfi taja ta miqe tsaye a fili tace zakuga rashin mutunci.
Washegari hindatu na sane taqi fitowa breakfast, baffa daya lura da hakan yace waeni ina Hindu ne? tun jiya ban ganta b. Ummy ce ta amsa masa da cewar tana dakinta mana, bansan uban abunda akai mata ba tun jiya take fushi!
Dan tana fushi kuma shine zataqi cin abinci kai aminu maza tashi ka kirata. Har yayi gaba ummah tace banda tsokana pa. A kwance ya sameta tana tilawar qur'ani yace keh dallah ance kizo kiyi breakfast.
Bata kulashi ba ta miqe tsalam ta fito, gaida umma da baffa tayi ta zauna a gefen baffa ta fara hada tea, hindatu bazaki gaida yayanki bane? Umma ta tambayeta. Na gaisheshi da asbah hindatu ta bata amsa fuskarta a daure. Adam ya dago suka hada ido ta balla masa harara, saida suka kammala sannan Adam ya zaro wasu hadaddun cards ya dire a gabanta yace hindatu ga cards enki koh ki gayyaci wadanda zaki gayyata. Bata kalli inda cards en sukeba tace na menene? Ah,na bikin yayanki mana kiyi inviting friends enki koh umma ta bata amsa. Miqewa tayi tana fadin dani da friends dina bama zuwa gayyar sodi,biki maI dalili ma ana gayyatana bana zuwa balle wannan, sai yau kukasan da Hindu a gidannan. Cikin fusata baffa yace uwaki hindatu,kaji shashashar yarinya wani bikine mara dalili anan? Amma baffa tsakani da Allah ace za'ai biki a gidannan a kasa gayamun sabod.... inaaa hindatu take...maza dauki cards en nan kibar gurin nan kafin raina ya baci. A zuciye ta dauki cards en tai gaba kaman zata tashi sama.
Ajiyar zuciya baffa ya sauke ya kalli umma yace Aminatu wae meyake faruwa ne, na rasa dalilin dayasa yarinyar nan batada kunya ko kadan. Tabe baki umma tae ba tareda ta tanka ba ta kwashi kayan tabar gurin.
Qarfe 11:00 tayiwa Adam a qofar gidansu aysha. Wayarsa ya dauka ya kira sa'ad, sa'ad din dake zaune gefen ummy yai mata sallama tunda dama yasan da fitar. Bude motar yayi ya shiga yana fadin wai bazaka barni na huta ba?
[21/04, 22:21] Hassan India: Miss collapse
(59)
👠 SATAR FITA💃🏽
Ba tareda Adam ya kalleshi ba yace idan kaga k huta sai next week. Sai isha suka gama abunda zasuyi Adam ya nufi gida dasu yana fadin muje ka gaida umma.
Ba qaramin farinciki ummah da baffa sukai ba da ganin sa'ad,sai can dare ya koma gida.
Hijab mai kauri Aysha ta zumbula ta fito tana fadin ummy gidansu Hindu zanje bazan Dade ba, gyada mata kai ummy tae itakuma tai gaba, a hankali ta tura qofar falon, tayi farinciki sosai ganin ba kowa dan yanxu kunyar umma takeji. Dakin hindatu ta wuce da sallamarta Hindu ta dago fuskarta a daure ta kalleta sannan ta mayar da kanta kan game en datakeyi. Ganin haka yasa aysha tai wuff ta fincike wayar tareda katsewa.
Bani wayata malama,hindatu ta fada fuskarta a daure aysha tace haba cwthrt nah! Wai laifin mena miki kiketa fushi dani,jibi fa za'a fara biki amm... bai shafeni ba hindatu ta fada cikin bacin rai ta cigaba da cewa ishsho banyi expecting haka daga gurinki ba,idan kowama zaimun aike mai hanawa ce, ace bikinku keda ya Adam amma babu wanda ya fadamin kamar wata mai nufinku da mugun Abu!
Cikin sanyin murya Aysha tace haba Hindu ya zakice haka,wlh ni niyyata nai surprising dinki shiyasa na roqi kowa akan kar a fada miki amma idan hakan ya bata miki rai kiyi haquri. Tabe baki hindatu tai tana kallon Aysha,cikin sanyin jiki aysha ta miqe zata fita hindatu tace ah! Ina kuma zakije? Tafiya zanyi tunda naga bakya maraba da zuwana. Guntun Tsaki hindatu tai tace malama dawo. Dawowa Aysha tai hindatu ta gyara zamanta tace yanxu Aysha duk mazan duniya ki rasa wanda zakiso sai ya Adam,haba da Allah ni wlh baimun ba. Ke kikace, nikam wlh yayimun 100%. Tsaki hindatu taja tace yana baqi dashi, wlh ni bazan auri baqi ba. Qyalqyalewa da dariya Aysha tai harda dafe cikinta, hakan ya qular da hindatu,saida ta tsagaita sannan tace wlh ni farin namiji baya birgeni,duk hasken nan nawa so kike na haifi zabiya! Amma karki damu ai ya sa'ad ya dawo kuma ya fini haske sosae idan
[21/04, 22:22] Hassan India: Miss collapse
(60)
👠 SATAR FITA💃🏽
Saida ta tsagaita sannan tace wlh ni farin namiji baya birgeni,duk hasken nan nawa so kike na haifi zabiya! Amma karki damu ai ya sa'ad ya dawo kuma ya fini haske sosae idan kina sonsa saiki mgn. Allah ya kiyaye nipa banson auren zumunci,kedai da kikaga zaki iya. Da hirarrakin nan suka fito dan saloon Aysha zataje. Dayake a waje driver yayi parking sai suka fito, hirarsu sukeyi qasa2 sukaji tsawa a bayansu,a tsorace suka juyo,Sam basu kula da Adam da sa'ad ba, sa'ad ya basu baya yana waya Adam ya dumfaro su, a tsorace Aysha tace hindatu me mukayi? Cikin dakiyi hindatu tace OHO masa!
Rai a bace yake kallon hindatu sannan yace keh dan ubanki a haka zaki fita? Kallon sa tayi sannan ta dubi matsatstsun kayan jikinta da dan yelolon mayafin data yafo a kanta tunda bata daura dan kwali ba tace ni kuma me nayi?
Tambayata kikeyi?ya fada yana qarasowa daff da ita, kadan ta matsa yace wuce kije ki dauko hijab! Wlh bazan saka hijab ba,ina ruwanka dani.
To koma gida babu inda zakije! Murmushin rainin wayo ta sakar masa sannan ta fara qoqarin bude motar yai saurin cafko hannunta, ya Adam wae meye haka ne a cikin mutane,banason irin haka ta fada a tsiwace. Da qarfi ya finciki hannun nata tana ihu tana komai har cikin gidan,a falo ya watsar da ita yace naga uban dazai fito dake yau, fitsararriya.
Ummah dake gyaran falon ko kulasu batai ba har Adam yai gaba hindatu ta tashi zata bishi ummah ta buga mata tsawa tare d cewa koma ki xauna, bajewa tayi a tsakiyar falon ta fara rusa kukah umma ta tashi ta bata guri. Adam na fitowa yaga Aysha a tsaye, tsuke fuskarsa yayi yace keh me kikeyi anan? Cikin sanyin murya tace Hindu nake jiraaa. Bazata fito ba,kina iya tafiya.jiki a sanyaye ta juya zata tafi yace aysha banson yawan gantali plz,ki kiyaye. Gyada kai tayi ta shiga mota sukai gaba shikuma Adam ya juya gun sa'ad daketa faman amsa waya ya basu baya tun dazu. Yana qarasawa sa'ad ya katse wayar ya juyo ya fuskanci Adam yace
[21/04, 22:22] Hassan India: Miss collapse
(61)
👠 SATAR FITA💃🏽
Yana qarasawa sa'ad ya katse wayar ya juyo ya fuskanci Adam yace har kun gama!
Me fa! Adam ya tambaya yana bude drivers seat shikuma sa'ad ya zagaya baya.
Naji kunata ihu kaida amaren ka. Uhm amaren nawa har nawa ne? Adam ya tambaya.
Zama sa'ad ya gyara ya fuskanci Adam yace gskiya nayi mamaki,kanata yimun zumudi zakae aure, i thought zanga wata classy hot beb Ashe wannan qwailar yarinyar ce Aysha tsabar siyan raini shiyasa gashi tun ba'aje ko ina ba ta fara maka rashin kunya.
A mamakance Adam ya kalli sa'ad sannan ya maida dubansa kan titi yace yau kuma sadauki ne yake maganar mata! Harda cewa classy and hot! Chab! Ya fada yana yar dariya!
Tsaki sa'ad yaja yace kaida zakae aure nake fadawa kasan ni mata basu isheni kallo ba!
Well!! We shall c dude! Kasan dai kaiba mala'ika bane, dole kanada desires dinka, @ 30 yrs kuma ya kamata ace ka fara tara iyali.
Tsaki sa'ad yaja yace kanada problem! Ni yanxu banda tym din mata,sanin kanka ne banason raini, kalli pa yanda waccan yarinyar take gaya maka magana babu manners!
Uhm!sa'ad ni nasan cewa Aysha bazata taba min rashin kunya ba,ba da ita nake magaba b da hindatu nake,yarinyar batada kunya babu wanda take qyalewa har su baffa! Na rasa inda ta koyo wannan halin!
The name sounds familiar! Hindatu....sa'ad ya fada yana dan buga goshinsa kamar maison tuno wani abu.
Ba lallai k tunata ba gskia,nasan tunda ka dawo baku hadu ba amma yanxu kalli fuskarka a mirror.
Kallon mirror sa'ad yayi sannan ya maida dubansa kan Adam yace meye a mirrorn. So nake ka gane kamanninka dakyau saboda hindatu duplicate dinka ce incase idan kun hadu just call her name. Murmushi sa'ad yayi har dimples dinsa suka bayyana.
*** *** ***
Tsararriya kwalliya aka tsantsarawa Aysha kasancewar yaune kamunta, haka hindatu mutane da dama sun halacci kamun abun sai son barka, washe gari kuma suka shirya bridal shower dinsu,qananun kaya ake sakawa banda amarya da
[21/04, 22:22] Hassan India: Miss collapse
(62)
👠 SATAR FITA💃🏽
Kaff matan dake gurin riga da wando suka saka kuma dama iya mata ne a event din, mursisi hindatu taqi saka wando dan dama ita ba gwanar saka wando bace saita dora tummy skirt, a zahiri ta manta rabon datasa wando a rayuwarta saboda umma ta hanata, hips dinta yayi girma sosae wanda ko macece ta ganta zata iyajin wani abu,ranar ma bikin yayi kyau mashaAllah washegari kuma aka daura auren Adam da Aysha,daurin auren yayi mutane,makada da maroqa sun samu kudi, Aysha kam ana daurawa ta fara kuka,hindatu sai tsiya take mata, da rana akai kamu da daddare kuma dinner ce.
Purple din material ne jikin Aysha,tasha roseel pink, kwalliya akai mata ta nunawa sa'a,babu wanda ya isa ya ganta ya kushe a wanga lokaci,saida aka kammala mata tsaf akazo kan hindatu,da sauri ta miqe tana fadin bari naje naci abinci plz,banaso nayi kwalliya kuma naci abinci ta zumbula farin hijab din Aysha ta fito
Jiqaqqiyar shadda ce royal blue jikin ango, yasha tsadajjiyar hula da takalmi dark blue,qamshi kawai yake zubawa a gurin sa'ad dake gefensa yadanyi dariya yace oh ango kayi kyau fa. Murmushi kawae Adam yayi yana qara fesa turaren royal man a jikinsa, sa'ad din ma yayi kyau abunsa,shadda yasa army green sae zuba qamshi yakeyi,sosai kayan suka amsheshi bama a magana. Miqewa yayi yace bari naje gida na dauko motar koh dan shamx yacemin an fara kai qawayen amarya. Da azamarshi ya fita zuwa gidansu,takawa yakeyi kamar bayason taka qasa ya shiga gidan, a parking space yayi parking motar gidan a cike yake damm da mutane gashi key din motar na gurin ummy dole saiya shiga ciki,ba yadda ya iya haka ya kutsa cikin taron matan har part ummy, ya godewa Allah falon ummyn b kowa hakan ya bashi yaqinin itama ummyn bata nan,da sauri ya qarasa bedroom dinta yasa hannu ya riqe handle din ya murda daidai lokacin da hindatu ke qoqarin fitowa daga dakin hannunta dauke da kwanon masa d miyar egusi,yana budewa sukaci wani mugun karo da ita, tini plate din
[21/04, 22:22] Hassan India: Miss collapse
(63)
SATAR FITA
tini plate din yayi sama ya fado,rabin miyar ya
bare jikin sa'ad,tayi masa chaba2 a jiki, a fusace
ya dago ya kalli hindatu dake kallonsa,musayar
mugun kallo suka shiga yiwa juna,ita baqin
cikinta bai wuce abincinta daya bare ba shikuma
kayansa data bata masa, cike da tsantsar tsiwa
hindatu tace malam hala baka ganin abunda
kayimin dahar zaka tsaya ka dInga kallona
instead of kaban haquri. Cike da mamaki yake
kallonta yace keh!bakida kunya bakiga abunda
kikaimin zakimun fitsara! Harara mai kyau
hindatu ta watsa masa tace kai bakaga asaran
daka yimin ba! Nonsense kawai! Wani bahagon
mari ya kifa mata saida bakinta yayi jini, ranshi a
matuqar bace ya nunata da yatsa yace keh!naga
alama baki gaji tarbiyya ba!to bari kiji in gaya
miki ni ba sa'anki bane idan kika kuskura kika
qara koda kalma 1 wallahi saenayi qasa2 dake a
gurin nan, shashasha,kasa motsi motsi hindatu
tai cikin tsananin kaduwa da mamaki ta bishi da
ido harya dauki keyn ya fice, wani tuquqin takaici
da baqinciki ne ya tokare mata qirji,wannan shine
karo na farko da wani ya mareta bayan en
gidansu,haushin kanta da tsanar guy din ya dirar
mata a zuciya,saeda tai wajen 5mins sannan ta
iya motsawa daga gurin.
Rai a bace ta wuce dakin Aysha ta cire hijab
din,dama ita kadae ake jira ta zauna aka dandasa
mata kwalliya, Ita da Aysha ne kawai a daki
ummy ta shigo da fara'arta tace ku fito angon
yazo,
A hankali suka tako tare,Aysha na gaba hindatu
na bayanta har gaban motar, baya aka budewa
Aysha ta shiga ita da angonta hindatu kam gaba
ta shiga sukai gaba. Gaba daya ran hindatu a
jagule yake, tunaninta bai wuce inda zataga guy
din nan ba dan tayi rantsuwa saeta yimasa rashin
mutunci na qarshe
Sam bata lura cewa shidin ne dai yake tuqasu ba
dan tunda ta shigo ta fuskanci gefen titi shikuma
hankalinsa yana kan driving baima San wace a
gaban ba.
Basu dauki wani lokaci ba suka qarasa hall din,
hindatu ce ta fara fitowa tayi cikin gungun friends
ensu da su
[21/04, 22:23] Hassan India: Miss collapse
(64)
👠 SATAR FITA💃🏽
hindatu ce ta fara fitowa tayi cikin gungun friends ensu da suka taru,lallai sunyi musu halacci tunda kaf sunyi anko kuma sun halacci bikin kamar yadda suma koda SATAR FITA ne sae sun halacci shagalin mutum indai ya gayyacesu.
Sune suka tsara wadanda zasu fara shiga wato na gaban amarya da ango dana bayansu, suna qoqarin shiga wayar sa'ad ta fara ringing, baya yai ya barsu suka shiga ciki inda aka fara gudanar da biki cikin dadadan sautuka, hasken flash tako ina masu zuba selfie. Hannu Aysha tasa ta yafito hindatu,da sauri ta qarasa gurin, A kunne ta rada mata su haseena sunzo basu gane gurin ba kije ki shigo dasu. Gyada kanta tayi ta fita, tana fita M.C ya buqaci babban Aminin ango kuma dan uwa a gurinshi SA'AD SADAUKI yazo ya bada taqaitaccen tarihin ango.
Daidae lokacin dayake shigowa hall din, kyau da kansa kenan, a hankali yake takowa gurin kamar mae tausayin qasa harya qarasa kan stage din inda M.C yake, wannan karon shigar maroon yayi daga sama har qasa,bai bata lokaci ba ya karbi mic din ya fara bada tarihin Adam cikin wannan muryar tasa mai bugarwa dasa nishadi a zuciya, tabbas duk wata mace datake gurin dole sae sa'ad ya tafi da imaninta kai harma mazan yana gamawa ilahirin mutanen gurin suka saka tafi ya musu godiya ya fita daga hall din da alama wani abun zaiyi, bai jima da fita ba su hindatu suka shigo, itama tazo tayi bayani akan tarihin amarya,koban fada muku ba nasan kunsan hindatu tayi kyau dan ita dama can yar wanka ce. Haqiqa wanga biki yabar tarihi dan kuwa naira tayi kuka anyi rawa an cashe anyi liqi anyi brush da naman kaji sae 12 aka tashi wannan karon hindatu da aminu ta tafi dan kayanta na budar kan gobe suna gida.
Washegari akai budar kai aka kai amarya Aysha gidan mijinta Adam,Aysha tayi kuka sosae harda ruqunqume Aysha da zasu tafi daqyar aka rabasu. To Amarya indo da Ango Adamu asubah ta gari fatan za'a rage mana kajin dan da duku2 zamuzo mu amshi rabonmu.
[21/04, 22:23] Hassan India: Miss collapse
(65)
👠 SATAR FITA💃🏽
Abu kamar wasa auren Aysha sati 1 kenan. Tsaf hindatu ta shirya ta nufi gidan Aysha,wannan shine karo na farko dataje gidan abun kuwa ya batawa Aysha rai saida hindatu taita bata haquri sannan ta haqura anan hindatu take gaya mata next week fa zasu koma skul, na sani Hindu wlh ji nake kamar karna koma skul en nan dama zasu taimaka su qara 2 weeks. Tabe baki hindatu tai ta cigaba da cewa sannan kuma bikin maryam white next week dan ta kawomin iv dinki jiya ta fada tana zaro iv din tare miqawa Aysha, hannu Aysha tasa ta karbi iv din tana jujjuyawa sannan ta kalli Hindu tace kinsan wani abu ne? Bazan iya zuwa bikin maryam ba,kwata2 1 week da aurena saina fara gantali a titi! Haba Hindu. Sakin baki hindatu tai tana kallon Aysha can dai tace Amma idan kikai hk baki kyauta ba,duk events din bikinki babu wanda batazo ba amma kiyi mata haka? Gaskiya bai daceba.
Shikenan hindatu zan tambayi honey idan ya yarda zan miki magana sai..... ba inda zakije! Adam ya katseta tareda qarasowa cikin falon, ke dama babu abunda kikasa a gaba sai gantali da yawon banza kekuma Aysha dan qarancin tunani irin naki shine daga auren naki zaki fara fita! To bazan lamunta ba.
A tsiwace hindatu tace naga dai kaima sunzo bikinka idan ba dansu ba bikin bazai taba kyau ba,yanxu da buqatarka ta biya aka gama qawata maka biki shine zakace wani baxata je b. Daure fuska Adam ya sakeyi yace keh wato bakida kunya koh! Tashi ki fita daga gidan nan karna sake ganin qafarki! Da sauri Aysha tace honey plz kayi haquri karka koreta wlh bazanj..... miqewa hindatu tai ta bude jakarta ta ciro chewing gum tasa a bakinta ta tauna ta sake taunawa sannan tai masa wani mugun kallon banza tace dadinta dai nima munada gida da bamuda shi saina saka hannu aka nai kuka! Kuma bari kaji indai na cika diyar Amina da bashir bazan qara takowa gidanka ba, tana qarasa fadar haka ta fice kamar zata tashi sama ba tareda ta saurari abunda Aysha take ce mata b
[21/04, 22:23] Hassan India: Miss collapse
(66)
💃🏽SATAR FITA👠
Haka rayuwa taci gaba d tafiya da dadi ba dadi,hindatu bata fasa satar fita ba haka Aysha bata daina biyayyar aure ba,Adam baida matsi sosae yakan barta fita lokaci zuwa lokaci Idan yayi niyya,zamansu lafiya qalau babu wata damuwa balle matsala.
18 months later---
Farinciki ya kasa boyuwa a fuskar hindatu har zuwa lokacin data fito daga hall din exams din,Sanye dake da top mai colour royal blue a bayan rigar an rubuta Hindu da manyan harrufa a gaban kuma an rubuta department of computer science,sae skirt dark blue data daura haka ma mayafin datae rolling,ba ita kadai bama ilahirin students din dake fitowa daga hall din rigar dake jikinsu kenan hakan ya tabbatar man da cewa yau ta kasance ranar graduation dinsu, ranar sunsha selfie kala2,watse watsen ruwa da suka dingayi kamar bazasu daina ba dan nuna tsantsan farincikin su,sae kusan magrib hindatu taje gida ranar, a gajiye hindatu a baje a falon umma tana sauke numfashi,umma yunwa nakeji Wlh yau ban samu zama ba,ta fada da qarfinta saboda tajiyo motsin umma a kitchen,daga kitchen din umma tace to kina iya zuwa kidau abinci dan bazan iya fitowa ba. A shagwabe da bude baki zatai magana taji sallama, da sauri ta dago dan jin muryar Aysha datayi, a hankali Ayshan ke takowa da tirtsetsen cikinta dan kimanin wata 6, gefenta kuma Adam ne hannunsa riqe da waya yana amsawa, miqewa hindatu tai tana qunshe dariyar data ciyota tace ah uwar biyu zoki zauna anan mana kya tsaya a tsaye? Hararar hindatu tai tayiwa kanta matsuguni a kasan carpet din falon ta miqe kafarta, duk yanda hindatu taso Aysha ta kulata taqi,itafa a lallai fushi takeyi akan Hindu bataje Mata ba ranar graduation dinsu.
A haka umma taxo ta samesu,sakin baki tai tace aa tare kukazo ne daman? Aa umma nima ganinsu nayi yanxu hindatu ta fada tana kallon Aysha dake kumbure2, zama umma tai gefen Adam bayan sun gaysa da Aysha tana fadin adamu da basai ka fadamin zakuzo ba aeda na dafawa Aysha wani abun kwadayin.
[21/04, 22:24] Hassan India: Miss collapse
(67)
💃🏽SATAR FITA👠
Umma Wlh nima bansan da zuwan ba,Ayshan ce ta matsa dole saina kawota gurin waccan fitsararriyar ya fada yana nuna hindatu da wayar hannunsa. Harara hindatu ta manna masa sannan taja wani siririn tsaki a zuciyarta tana fadin idan ba'a damu da kasuwa ba.sallamar baffa ce ta katsesu suka juya ganin shigowarsu shida Aminu. A falo shima baffan ya zazzauna suka gaggaisa da kowa sannan. Aysha ce tadan chabe fuska ta kalli umma dake gefenta tace umma wlh kuskus nake sha'awa amma idan na dafa bana iyaci..
Ashsha!2,kuma tun tuni kika kasa fadamin umma da fada tareda kallon gefen hindatu tace keh hindatu maza2 tashi kije ki dafawa Aysha kus-kus,yunwa takeji. Turo baki hindatu tai tace Haba ummah taya zasu baro gidansu su biyo hanyar har gidannan sannan tace tanajin yunwa!ni gaskiya a gajiye nake ummah! Mijinta yaje ya dafa mata! Keh hindatu bakida kunya koh ba er uwarki zakiwa ba ko bakiga lalurar datake dauke dashi ba! Baffa ya fada cikin fada.
A qule ta tashi tana hararar Aysha dake Mata dariya danta tabbata da gayya tai hakan ta doka qafarta da qasa tana fadin waeni meyasa ake matsamin a gidan nan,baa ganin gajiyar dana kwaso sai aita sani aiki ta fada a tsiwace sannan ta juya! Baffa wlh kawai ayiwa wannan fitsararriyar yarintar aure dan naga,alama ra raina kowa a gidan nan! Wani shegen burki hindatu taja tareda juyawa cike da masifa tana kallon aminu!
To zokamin auren mana ubana! Kaji ta fada tana watsawa aminu wani rikitaccen kallo! Ina ruwanka da zamana ko a kanka nake kabi ka takuramin rayuwa! To wallahi ka kiyayi kanka dani idan ba hakaba kasha mamaki munafiki kawai!.
Duk idanuwa suka zuba mata dan dama sun tsammaci hakan,ita dai hindatu ta tsani ai mata zancen aure,umma ce ta katseta da fadin keh hindatu daga yace ai miki aure shine zaki fara masa rashin kunya ko sa'anki ne?
A hasale tace toh umma ina ruwansa dani! Naga dai ba akansa nake zama ba koh?
Tsaki umma taja tace to saime idan ance za'ai miki aure
[21/04, 22:24] Hassan India: Miss collapse
(68)
💃🏽SATAR FITA👠
Tsaki umma taja tace to saime idan ance za'ai miki aure,ae kinsan ba zama zakiyi muna kallonki kamar talabijin ba,idan banda shashanci ma baa aure mukayi har muka sameki! A fusace hindatu ta juya tai cikin kitchen din.
5 days later--
Insha Allah zanzo nawal,ae bikinki kamar dole ne a gurina ki kwantar da hankalinki,hindatu ta fada tana raka qawar tata bakin gate bayan tayi musu kwatancen gidan Aysha.
Aysha bazan iya barinki kije dinner din nan ba, sae 9 za'a fara,wayasan sanda zaa tashi, saidai kije kamu kawai umma ta fada fuskarta ba yabo ba fallasa!
Haba da Allah umma ya zakice bazanje dinner nawal ba,tarefa mukai sec.skul sannan mukae buk tare,ae wannan ma bai daceba.
Kinga hindatu! Bance bazakije ba,nace miki xakije kamu dinner kuma kiyi haquri wataran kyaje gidanta.
A qufule hindatu ta dauki cards en tai gaba tana qunquni baffa ya bita da ido sannan yaja gajeren tsaki.
Saida ta tabbatar babu kowa a falon sannan ta salallaba ra fita kamar barauniya, a gidansu saheeba wata daga cikin friends ensu ta qarasa shiryawa sannan saurayin saheeba ya qarasa dasu gurin dinner wajen 10, acan ta tadda Aysha,bama tayi tsammanin ganin Ayshan ba amma kuma taji dadin ganinta,anan suka zauna sunata hira har wajen 10:40, da sauri hindatu ta dauke qafarta cikeda azaba tana yarfe hannu sannan ta dago ta kalli matar data take mata qafa da takalminta mai tsini,rai a bace hindatu ta saka hannu ta fuzgo matar tace keh bakya ganine kin take mutum bazaki bashi haquri ba!
Cikin izza matar ta juyo ta sauke idanuwanta akan hindatu! Ba hindatu ba har matar saida zuciyarta ta bada sautin RASSSS...
[21/04, 22:25] Hassan India: Miss collapse
(69)
👠SATAR FITA💃🏽
Musayar mugun kallo suka shiga yiwa juna dan sun shaida juna qwara. Cikin tsantsar bacin rai matar tacewa hindatu keh! Har kin isa ki finciko ni? Tsaki hindatu taja mai qarfin gaske sannan tace ki godewa Allah ma fincikoki nai, dan kamata yayi ace na kifa miki mari.
Mari? Matar ta maimaita tareda fito da idanuwanta waje. Qwarai kuwa mari hindatu ta fada tana yatsina.
Kan ubah! Ke naga alama tarbiyya bata isheki ba,ni zaki kalla kice zaki Mara saboda bakida kunya!
Ke ae naga ta isheki,hindatu ta fada tareda kawar da kanta dan taga hankulan mutane ya fara dawowa kansu.
Hannu matar tasa ta finciko hindatu cikin zafin nama tace keh wato naga alama ibraheem ne ya baki damar rainani har kike tunanin zaki fadamin mgnr banza! To wallahi zan iya miki dan banzan duka anan gurin inga uban wanda ya tsaya miki. Kuma wallahi kiji in gaya miki ibraheem yafi qarfinki!
Dariyar rainin wayo hindatu ta saki sannan ta miqe tsaye, ta juya ta qara juyawa sannan tace iro kikace ko ibraheem! Haba madam! Dubeni daga sama har qasa wallhy nafi qarfin mijinki har abada,na wuce ajinsa niba kalarsa bace, kije ki bincika hadaddun mazan da suka cika maza kuma suka isa a kirasu maza da suke bina amma ban kulasu ba balle mijinki,ae ibraheem sai ke, tinkiya irinki macen da batada clx kary.... tau hindatu taji saukar mari a fuskarta,aeko babu bata lokaci hindatu ta rama, sai dambe, mutanen dake gurin suka shiga qoqarin rabasu dan Aysha tayi nauyi bazata iya ba, daqyar aka banbaresu daga jikin juna kowa a fusace yana zage,Aysha ce taja hindatu sukai waje cikin bacin rai Aysha ta fara fadin haba hindatu wannan ai bararwa dakai clx ne, da hankalinki da mutuncinki zaki tsaya kina dambe da waccan matar haba Hindu! Yanzu haka kike tunanin wani zai ganki har yayi sha'awar aurenki! Meye amfanin haka?
Bazaki gane bane! Na dade ina ciki da waccan matar sannan yanzu zatazo ta cimin mutunci a baynar nasi! Wlh sai tayi danasanin abunda taimin.
[21/04, 22:25] Hassan India: Miss collapse
(70)
👠SATAR FITA💃🏽
Me zakiyi kuma! Dan Allah kiyi haquri.
Qwafa kawai hindatu tai ta zaro wayarta ta fara latse2, kara wayar hindatu tai a kunnenta ana dauka tace kana ina?
Banji abunda akace a daya bangaren ba sai tace its urgent, inada buqatar ganinka zamuyi mgn mai muhimmamci. OK ganinan ta fada tareda katsewa tanada huci daidai lokacin motar Adam ta danno. Kafin Aysha tai magana hindatu tai saurin cewa ga mijinki nan ni zan wuce.
Ki bari mu kaiki gida mana!
Karki damu dani Aysha ba gida nai ba,kawai kuje byee tai saurin bin qaramar qofar wucewa tabar Aysha baki bude.
A hankali Aysha ta qarasa jikin motar Adam ta shiga, ya kunna sannan ya kalleta yace wa nagani kamar hindatu?
Eh itace, gida ma zata wuce yanzu.
Dubansa ya mayar kan hanya yana fadin meyasa bakice tazo mu kaita ba,bakya ganin dare yayi! Eh,cewa tai da kanta zata tafi ta fada tana qoqarin bagarar da zancen.
Keke nepep ne ya kaita har harabar tafkeken hotel din, a gaggauce ta shiga ciki batare da tayi la'akari da mutanen dake kara kaina a gurin ba, wani daga cikin ma'aikatan gurin ta tamvaya ya nuna mata room number 207, a gaggauce ta qarasa tareda knocking, Ibrahim dake expecting zuwanta ya bude qofar ta shigo fuskarta a matuqar daure. Har yanxu mamaki yakeyi tareda tunanin dalilin dayasa hindatun tazo gurinsa a wannan tsohon daren.
Zama tayi kamar yadda yai mata nuni da matsuguni,batako kalli ruwa da lemun dayai mata tayi ba ta fara balbala masifa akan yai mata katangar qarfe da matarsa, saida ta gama tsaf sannan ya bude baki zai mata magana aka danna bell! Tashi yayi ya bude guy din dake turo basket din ya shigo, da uniform a jikinsa ko baa fada ba kasan room service ne, saida ya ajje komai sannan ya dago idanuwansa suka sauka akan hindatu, kallon kallo sukeyi wa juna, shi da Alama kallon mamaki yake mata ita kuma gani take kamar tasan fuskar amma ta kasa tuna inda ta santa, ibraheem ne ya katseshi ta hanyar cewa mlm lpy dae? Sorry yallabai yace
[21/04, 22:25] Hassan India: Miss collapse
(71)
👠SATAR FITA💃🏽
ibraheem ne ya katseshi ta hanyar cewa mlm lpy dae? Sorry yallabai yace tareda saurin ficewa.
Dawo da dubansa yayi kan hindatu cikin taushin murya ya fara bata haquri sannan yace ni banma san zataje bikin ba dan saida nace mata kar taje, dayake tana gidansu ne mu namu gidan gyara ake mana, amma hindatu kiyi haquri plz i apologise on her behalf. Nidae kawai kayiwa matarka mgn shine abunda ta sake fada tareda miqewa ibraheem yana fadin baza kici komae ba. Agogon hannunta ta kalla taga qarfe 12 ta kuma tuna cewa SATAR FITA fa tayi, da sauri ta daga qafa tareda fadin sae anjima. Biyota yayi da niyyar yimata rakiya saidai me. Wani qarqarfan ruwa akeyi mai muguwar iska ga garin yayi wani Irin duhu ko hannunka baka iya gani.
Cikin firgici hindatu tace ibraheem na shiga uku ya zanyi naje gida yanxu? Cikeda tausayawa yace ni kaina bansan ya za'ai ba,gashi na bayarda gyaran motana. Amma kira gida ki gaya musu ko a sami mai zuwa daukanki.
Da sauri ta janyo wayarta ta fara lalubar number Aysha amma a kashe haka ta ya Adam, batai qasa a gwiwa ba ta fara lalubar number ya khadija amma not reachable hakama number ya hamza! Hankalinta yakai qololuwar tashi ta rasa inda zata tsoma ranta tasan ko giyar wake tasha baxata kira iyayenta ba,to idan ta kira ma me zatace, ina hotel tareda Ibrahim azo a daukeni! Mutuwa kenan. Daki suka koma ita da Ibrahim din, duk sanyin da garin ya dauka da kuma ac dake dakin bai hana gumi wanke fuskar hindatu ba. Wannan wani irin masifa ne ya sameni ta fada a zuciyarta tareda yin zaman dirshan a tsakar dakin.
Kusan mintuna 30 aka kwasa ba tareda sun sami wani solution ba Ibrahim yace yanzu babu wani wanda zaki kira ya kaiki gida hindatu! Ni kaina ina guje miki zargi shiyasa SATAR FITA batada wani amfani.
Da sauri ta miqe tareda fadin akwai yayana Aminu bari na kirashi. Da sauri ta wawuri wayarta tareda latso sunan aminu ta fara bugawa. Cikin sa'arta wayar ra fara ringing diiin diiin....
[21/04, 22:26] Hassan India: Miss collapse
(72)
👠 SATAR FITA💃🏼
Diiin Diin haka wayar ta qaraci burarinta ba'a daga ba hankalin Hindu idan yayi dubu ya tashi, dole ta sauke wayar ta juya tana kallon Ibrahim fuskarsa dauke da tarin nadama,tayi danasanin zuwa wannan dinner din,ita gata a cikin wani hali na masifa ita kuma nawal babu mamaki suna can suna sharbar soyayyarsu a cikin wannan ni'imtaccen daren.
Cikin taushin murya Ibrahim yace hindatu kiyi haquri yau haka Allah ya qaddara,ki kwana anan idan yaso gobe da kaina zanje nai musu bayani! A rikice ta dago tana kallonsa,lallai mutumin nan bashida kai, wato so yake na dauki wuqa da kaina na dabawa kaina kenan!ta fada a zuciyarta.
Haka yayita lallabinta,dole ta haqura ta kwanta akan sofa dan yace ya bawa jamila ATM card dinshi balle ya karbar mata daki, daqyar bacci ya kwashi hindatu.
Fadan da baffa yakeyi a gidan da badan ruwan da akeyi ba babu abunda xai hana maqobta suji, umma kam a gefe ta rakube ta zauna dan batada abun fada amma zuciyarta zafi kawai take mata, lallai hindatu ta cika isheshshiya wato duk kashedin datai mata bataji ba saita kwashi qafa ta tafi gantalin ko, gashi har qarfe 1 tayi. Ganin Daren yayi nisa yasa hankalin baffa da umma ya tashi suka fara dokawa mutane kira amma duk wanda suka samu tashi ta shiga amsar dai hindatu batazo ba,wayar Adam da Aysha kuwa a rufe take ta hindatu kam taqi shiga. Ranar a zaune suka kwana kowa yana saqe2 a ransa.
Qarfe shida da rabi Adam ya tashi yanata zuba sauri zai fita dan sunada wani surgery da zasuyi 7:30, Aysha tanata aikin hada masa breakfast a kitchen taji wayarsa ta buga, hanjin cikinta ne yai qara jin yana fadin umma ina kwana,da sauri ta katse abunda takeyi ta qarasa kusa dashi, hindatu kuma!! Taji ya fada da alamun mamaki, da sauri tasa hannu ta karbe wayar ta kara a kunne shikuma ya bita da ido
Ehh! nace hindatu na nan gidanku ne dan tun jiya da daddare bamu ganta ba.
Eh umma tana nan bacci ma takeyi amma zuwa anjima zata dawo. Dif umma ta kashe wayar
[21/04, 22:26] Hassan India: Miss collapse
(73)
👠 SATAR FITA💃🏼
Dif umma ta kashe wayar Aysha kam tsayawa tai tana kallon wayar zuciyarta tana rugugin bugawa.
Ina hindatun take? Adam ya tambaya yana muzurai. Cikin salon wayancewa Aysha ta miqa masa wayar tana fadin ai hindatu a gidan Amarya suka kwana jiya take cemin zasuyi budar kai zuwa 10 zata dawo tace kar a fadawa umma saboda kar hankalinta ya tashi kokuma a hanata tafiya.
Ke kuma kece mai daurewa qarya gindi koh? Ya fada yana kallon corridor kitchen din. Daga murya tai tana fadin sorry BAE.
A razane hindatu ta bude idonta saboda ringing din wayarta data jiyo, tsigeta tae daga chargyn da takeda yaqinin Ibrahim ne ya saka ta kara a kunne ganin sunan Aysha ya bayyana a saman screen din.
Helloww! Aysha ta fada zuciyarta tana bugawa, da sauri hindatu tace Ayshahh... ajiyar zuciya Aysha ta sauke a hankali tana fadin kina ina? A ina kika kwana?
Qarar bude qofar ce ta katse hindatu ta mayarda hankalinta kan mai shigowa. Jamilah! Ta fada gabanta na faduwa! amma hakan bai hanata tsare gida ba, daidae lokacin kuma Ibrahim ya fito daga toilet sanye da jallabiya. Wayar hannun jamila ce ta fadi qasa ta tarwatse,tashin hankali mara musaltuwa ya bayyana a fuskarta, Ibrahim! Dama dalilin dayasa kace a hotel zaka zauna! Ashe zuwa kakeyi kuna tarewa da wannan la'ananniyar yarinyar kuna cin amana ta!!
Kinga jamilah dakata! Tsaya ki fahimceni plz ki daina yawan zargi!
Oh zargi ma kake cewa Ibrahim! Na ganku turmi da tabarya da wannan jakar yarinyar sannan ka rainamin hankali
Ke da'allah dakata! Ke koh kissar nan da akeyi da makircin ma baki iya ba,bakiji kunyar qalawa muminin mijinki sharri ba! Koh kunya bakyaji?
Heeee!!! Dakata! Ta fada tana nuna hindatu da yatsa,banzo kanyi bama zaki nemi ki zageni! Wlh sai kinyi nadama ta fada tana daura mayafinta a qugu! Wai dambe. Ko gezau hindatu bata motsa ba ta tsaya tana jiran qarasowar jamila, da sauri Ibrahim ya tareta yacewa hindatu ta tafi gida da'Allah, mayafinta ta zara da jakarta tai
[21/04, 22:26] Hassan India: Miss collapse