Naso yimusu bayanin haka amma basu fahimta ba, nikuma yanxu bana tunanin zan iya rabuwa da hindatu,wlh halin dana ganta ya tayarmin da hankali Aysha, bansan a ina mafitar take ba.
Hadiye maqoqon dake maqoshinta tayi sannan tace hanya daya ce ta rage mana, kaje ka samu abbana da zancen nasan zai amince kuma da kansa zaiyiwa baffa mgnar.
Amma bashir bai kyauta ba,cewar Abba dake kallon Adam, idan har ku 2 bakuda matsala da auren ae shi bai kamata ya samu ba,shida zaiji dadi yayansa sun hade kansu shine zaice a'ah, haba habaa....
Wlh Abba naso fahimtar dashi haka amma yaqi saurarona, kuma kaga shi da kansa ya matsa akai zae mata aure amma yanzu kuma..
Kada ka damu Adam,badai kanason hindatu ba,ae aurenta kamar kayi ka gama kaje ka cigaba da aikin gabanta. Godiya sosai Adam yai masa sannan ya fita.
Yallabai wannan wani irin zance ne haka kakeyi? Da hadin gwiwarka za'a yiwa ita Diyar taka kishiya?
Da mamaki Abba ya dubi ummy yace rumah wacece kishiyar? Er uwar tata ce kishiya?
Koma wacece, wannan wata irin magana ce? Yaya suna zaune zaman lafiya zaizo ya fara zancen qarin aure kuma da hindatu?
Kinga dakata rumah! Laifi ne idan ya qara auren, kuma naga dai a gabanki yace Aysha ce ta taso da maganar. To idan ya auri hindatun ba jin dadinku bane tunda sunsan halin juna bazasu dinga samun wani dogon sabani ba.
A gaskiya nikam ban goyi da bayan wannan zancen ba,wannan ai munafurci ne da salon bata zumunta, bazan kuma taba lamunta ba,Aysha bazata zauna da hindatu a matsayin kishiya ba saedai ya zabi daya!
To bazai zaba ba din,kuma ki sani aurenshi da hindatu babu abunda zai hanashi sai wata BABBAR QADDARA, kuma aurenshi da Aysha ba abunda zai rabashi saidai idan shi adamun ne yaga damar rabuwa da ita, ke bakiji kunya ba da girmanki zaki dinga shiga sabgar yara har kina qoqarin chusa musu qiyayyah! To wallahi rumah ki kiyayeni.
[21/04, 22:34] Hassan India: Miss collapse
(97)
SATAR FITA
Cikin fusata ummyn ta miqe tayi cikin dakin tare
da fadin ayi mugani idan tusa zata hura wuta.
Next day-
Ni uwarki ce Aysha,duk duniya babu wadda take
qaunarki kamar ni, ki fadamin shin Adam tirsasaki
yayi ki amince ya auri hindatu?
Yaqen dole aysha ta saki tace ummy kenan, wlh
ko kadan ya Adam bai tursasani ba,in fact nice
ma na matsa masa akan ya aureta din saboda
bazan iya jurar ganin hindatu cikin wahala ba.
Zancen banza kikeyi Aysha,idan so kike ki
taimaka mata ta samu mijin aure ae ba dole sae
mijinki ba,dangin ubanki suna nan a garin
nan,samari wadanda zasu aureta ba tareda wata
damuwa ba.
Amma ba kamar ya Adam ba,nasan shi zai riqeta
bisa amana da gskiya,bazai wulaqantata ba duk
yadda ya sameta saboda shima yana qaunarta,
ummy wlh ya Adam yana qaunar hindatu fiye da
zatonki dan tun kafin ya aureni yake sonta.
Ke kuma kin zama er oho koh? Zaki zauna kishi
ya kasheki sabida kinsan wlhy bora zaki zama a
gidan nan,Aysha ina jiye miki hali irin na
DAN'ADAM.
Ummy ba haka bane, na tabbata hindatu bazata
taba yin wani abu dazai baqanta min ba,kuma ni
baxanyi kishi da hindatu ba,a ganina duk wadda
Adam ya nunawa soyayya a cikinmu to lallai ya
nunawa dayar ne saboda ruhinmu a hade yake da
juna gangar jiki ne kowa da nata ta qarashe
maganar tana maida qwallar dake qoqarin zubo
mata.
Ya sunan wannan abun da nake gani a
idanuwanki,wannan kishin? Wannan damuwar da
rashin walwala! Aysha yaushe kikayi girman da
zaki yanke irin wannan danyen hukuncin ba
tareda kin sanar dani a matsayina na
mahaifiyarki ba? Kokuwa kin sake uwa ne? Ko a
tunaninki akwai wanda zai fada miki gaskiya
kuma ya soki da gaskiya kamar ni.
Ummy ba haka bane,ita kanta hindu batasan
abunda yake faruwa ba,batasan da zancen
aurenta da Adam ba kuma batasan da hannu na
aciki ba,amma ummy wlh hindu ta cancanci
auren ada.... a moqoshi maganar ta maqale
ganin hindatu tsaye a bakin qofa manyan
idanuwanta da suka rine a Kansu tana musu wani
irin kallo
[21/04, 22:35] Hassan India: Miss collapse
(98)
👠SATAR FITA💃🏽
Qarasowa tayi dakin cikeda tashin hankali ta tsige earpiece din dake kunnenta ta gaida ummy, ciki ciki ummyn ta amsa,hindatu da hankalinta yayi kan Aysha bama ta lura ba tae saurin dafa kafadar Aysha tace Aysh meya saki kuka ne?
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi ta kalli ummyn dake tattare jakarta tace wai ummy ce takeso naje gida haihuwa,kuma ta fadamin na fadawa ya Adam amma yace bai yadda ba.
Ajiyar zuciya Ayshan ta sauke tace seriously hankalina ya tashi na zatta ya Adam aure zai qara wlh dan naji kamar kina cewa aure.
Cewa nayi shi yake aurena, ummy tayi haquri tunda bayaso.
Kallon ummyn hindatu tai tace ummy kawai ki dauketa ku tafi,idan ya biyoki gida ki masa bayani da kanki.
Barshi kawai hindatu,ni zan tafi sae kuma haduwa ta biyu,dama xaman ita kadai ce banaso. Daga haka sukai sallama.
Hindatu wlh nayi muguwar gajiya,jin jikina kawai nake wani iri yau.
To ki kwanta ki huta mana, saena dan mammatsa miki qafar taki, dubi yadda ta kumbura kamar gobe zaki haihu.
Dan murmushi Ayshan tayi ta kwanta hindatu na dan mammatsa mata qafa suna hira jefi2, yawancin hirar ma akan matsalar hindatun ce dake fadin ita ta haqura baffa ya zaba mata wanda yaga dama,Aysha nata bata baki.
Hindatu dan Allah wainar fulawa nakeso ki soyamin. Harararta hindatu tai tace saboda nazo gidanki shine zaki fara sakani aiki?
Gidanmu dae, Aysha ta fada a zuciyarta amma a fili sae tayi murmushi tace ae Allah nace.
Qamshin wainar fulawa ne ya kaure gidan har Adam ya shigo, yayi mamakin ganin hindatu har yana cewa yaushe tazo, ban dade ba tace ta cigaba da aikin gabanta, dakin matara ya shige,zuwa wasu en mintuna ya fito yana cewa hindatun zai fita, bazai dade ba, a zuciyarsa harya fara hasko irin zaman da zaiyi da matan nasa 2.
Ayshan ashe tayi bacci, hindatu ta fada a ranta cikin tausayawa,kadan taci wainar sannan ta ajjewa Aysha tata ta gyare gidan,haka kawai hankalinta yayi gida dan haka ko Ayshan bata tasa ba ta fice.
[21/04, 22:35] Hassan India: Miss collapse
(99)
👠SATAR FITA💃🏽
Amma Alh.Bashir baka kyauta ba, yaya kakeyin abu kamar wani qaramin yaro,meyasa zaka dinga qoqarin hana yaro aure kana biyewa shirmen mata.
Bazaka fahimceni ba sadauki,Adam har yanzu yaro ne, bazai iya riqe mata 2 ba bayan wannan nidae bazan goyi bayan Adam ya auri hindatu ba,banaso duk wani abu dazai bata zumuncin yaran.
Kaga alh.Bashir,yaran nan da kansu suka amince da wannan zancen basu kawo wata matsala ba,su da kansu suka kawo mun zancen.
Tursasawa ce Alh. Sadauki, tursasawa Aysha yaron nan yayi dan babu ta yadda za'ae wata mace ta yadda ai mata kishiya.
Ko daya Alh.Bashir, wlh AYSHA da kanta ta bijiro da wannan zancen,saboda batason qanwar tata ta shiga tashin hankali,kuma kaida kanka zaka bada labarin soyayyar da sukewa junansu, ita Ayshan ae ta fahimci adamun yanason hindatu shiyasa ta kawo masa zancen shiyasa datai masa zancen bai qiya ba,ya yadda dan haka dan Alh. Bashir ka rabu da yaran nan,Albarkarka kawai suke buqata,ni da kaina zanyi komai.
To ya zanyi dakai sadauki,tunda ka yanke hukunci da kanka, Allah ya sanya Alkhairi.
Dariya mai sauti Alh. Sadauki yayi ya janyo wayarsa yana fadin bari kaga, ringing 2 wayar tayi akan dauka da sallama Abba yace kai dan liti to aiki zakai min, yanxu yanxu nakeso ka bugamun katin daurin aure guda 100 na yayana, ranar juma'a zaa daura,zan turo maka details din ta text.
Rugugi kawai hindatu takeji a cikin kanta,ta kasa yadda da abunda kunnuwanta suka jiyo mata har saeda ta runtse idanuwanta ta bude,lallai Aysha ta cuceni,taci amanar yadda da amincin dake tsakaninmu. Fasa shigowa tai ta juya a guje, keke nepep ta tsare ta kaita gidan Aysha, wannan karon a falo ta iske Ayshan tana kallo,ganin yanayin hindatu yasa gaban Aysha yai mugun faduwa tai saurin miqewa, falon ta qaraso tana yiwa Aysha wani mugun kallo mai cike da tuhuma da takaici, haushin Ayshan takeji kamar ta makureta ta huta.
[21/04, 22:36] Hassan India: Miss collapse
(100)
👠SATAR FITA💃🏽
Hindatu lafiyarku kuw..... Tauuuu hindatun tasa hannu ta dauketa da wani bahagon mari sannan ta fara magana cikin hawaye tana cewa Aysha kin cuceni kin cutar dani kuma kin yaudareni,Ashe zaki iya watsi da amintar dake tsakanina dake,ashe akwai lokacin da xaixo da zaki yimun kallon kishiyarki,har kina mafarkin muyi irin wannan baqar rayuwar dake! Ban taba tsammanin haka daga gareki ba Aysha kinci amana ta! Baxan iya yafe miki ba... ta fada qwallar da takeyi na qaruwa.
Dakata hindatu ki saurareni, wlh banyi haka dan na bata QAUNARMU BA! Bazan taba cutar dake ba hindatu,wlh kaina ya riga ya qulle bana ganin kowa sae ya Adam,a ganina shi zai riqeki bisa amana da yadda, nasan ya Adam yana sonki tun kafin ya aureni, kuma nasan har yanxu akwai soyayyarki a zuciyarsa shiyasa nayi iya qoqarina ganin na hadaku domin na Samar muku da farin ciki na har abada.
Kin yaudari kanki Aysha! Hindatu ta fada a tsawace sannan ta qarasa gaban Adam dake tsaye yana sauraronsu ta finciko hannunsa tace muje ya Adams ka fadawa Aysha bata fahimta daidai ba! Ka fada mata mata baka taba sona b! Ka sanar da ita babu soyayyar aure a tsakaninmu domin kaidin dan uwana ne kamar Aminu! Ka tabbatar mata da cewa kai nata ne ita kadai kuma itama taka ce kai kadai babu wanda zai canza haka! Ya Adam ka mata bayani yadda zata fahimta cewa aure ya haramta a tsakaninmu sabida baka sona ta qarashe tana fincikarsa da qarfi.
Wrong! U are very wrong hindatu! Ni Adam ina matukar qaunarki ya fada cikin wata irin murya mai sanyaya jiki. A sanyaye ta zare hannunta daga nasa tayi baya zata fadi yayi saurin tarota ta hanyar riqo qugunta da gefen kafadarta sannan yayi qoqarin zura qwayoyin idanuwansa a cikin nata.
Na soki tun sanda na fara dora idanuwana a kanki! Tun kina jaririyarki! Tun bakisan kanki ba nake sonki,koda yaushe burina na aureki hindatu amma Allah bai hakan ba saina auri Aysha,lokacin da Aysha taxomin da zancen aurenki da fari naqi amincewa
[21/04, 22:36] Hassan India: Miss collapse
(101)
👠SATAR FITA💃🏽
Na soki tun sanda na fara dora idanuwana a kanki! Tun kina jaririyarki! Tun bakisan kanki ba nake sonki,koda yaushe burina na aureki hindatu amma Allah bai hakan ba saina auri Aysha,lokacin da Aysha taxomin da zancen aurenki da fari naqi amincewa saboda ZUMUNTARMU amma daga baya na yadda da hakan saboda BA HARAMUN BANE,yanxu bakin Alqalami ya riga ya bushe magana ta riga takai gurin manya dan haka ki fara daukana a matsayin mijinki daga yanzz......Daukeshi da tafi hindatun tayi cikin tsananin bacin rai tace Har abada ya Adam!bazan taba zama matarka ba idan mafarki kukeyi ku farka!
Aysha data kasa magana saboda tsabar kishi da tashin hankali tace ba gudu baja da baya hindatu!aurenki da mijina ya zama dole ki daina tunananin za'a fasa!
OK fine then,a yanzu banaso a fasa! Amma kuma za'a rasa! wlh saidae a daura da gawata amma bazan auri Adam ba,yau zan kashe kaina ta fada tareda ficewa daga gidan a guje! Cikin sauri Adam da Aysha suka bita amma kafin su qarasa sae tsintota sukai a tsakiyar titi mota tayi ciki da ita.
A gigice suka hada baki wajen fadar hindatuuuu!!!, Amma inaa,da sauri suka qarasa gurin dan mutane harsun fara taruwa, mai motar ma har ya fito dashi da matarsa. Da saurin su suka dago hindatu,matar ta wara ido a tsorace tace ishaq hindatu ce. Shima din idanuwan nasa a ware yake ya fara shirin daukarta, Adam d aysha suka qaraso,sunyi mamaki qwarai ganin ashe ya ishaq ne a motar,Amma ganin xasu bata lokaci yasa sukai saurin kai hindatu asibiti.
Babu bata lokaci doctors din suka karbeta dan yawancinsu sunsan Adam, a bencin dake gefen gurin suka zazzauna kowa hankalinsa a tashe, ya ishaq kam sai bankowa Adam harara yake da kallon zamu gamu dakai.
Ba'a jima ba doctor mariyah ta fito cikin fararen kayanta da farin glass,duk sukai kanta da tambayar ya jiki.
Ku kwantar da hankalinku plz,ta fada cikin iyayin nan nata sannan ta cigaba da cewa,she's not badly injured( bataji ciwo Sosae b), kawai dai buguwa
[21/04, 22:36] Hassan India: Miss collapse
(102)
👠SATAR FITA💃🏽
Ku kwantar da hankalinku plz,ta fada cikin iyayin nan nata sannan ta cigaba da cewa,she's not badly injured( bataji ciwo Sosae b), kawai dai buguwa ce a qafarta da kuma kanta, nayi mata allura zata tashi nan da 2 hours,sae kuma maganin da za'a siya saboda gurin ya warke da wuri ta zaro wata farar takarda daga aljihunta tana miqawa ishaq,da sauri khadija ta karbe tareda balla mata harara a zuciyarta tana cewa dubi er duniyar mata zatai min snatching.
2 hours din bama ta qarasa ba hindatu ta farka, agggrrhh ta fada tareda cije lips dinta saboda azabar da kanta yake mata, hannu ta dora akan taji alamun bandage,sae a lokacin ta tuna abunda ya faru,da sauri ta fara qoqarin miqewa Aysha da shigowarta kenan tayi saurin qarasawa gurin ta riqeta. Da qarfi ta fizge hannunta tare da fadin don't touch me! I hate u!
Cikin halin ko in kula Aysha tai murmushi tace madam bakida lpy,at least ki bari kiji sauqi mana. Bata kulata ba ta fizge drip din hannunta ta sauko, aeko tana taka qasa ta saka wani shegen ihun azaba.
Da sauri khadija ta fado dakin tana fadin lafiya?
Aysha ce ta bata amsa cewa wae ta dage ne saita sauko. Hade rai khadija tayi ta maidata kan gadon daidai lokacin doctor din ta shigo, mammatsa qafar tayi ta shafa mata magani tare da cewa zuwa anjima ciwon zai ragu,amma karta taka qafar. Babu jimawa wayar hindatun dake hannun khadija ta fara tsuwwa,umma ce dan haka khadijan ta dauka zatai magana umma ta rufeta da fada, saida tai mata tasss tana fadin wato kin koma gantalin naki koh sannan khadija ta iya cewa umma ba ita bace khadija ce. Dan jimm umman tayi sannan tace ina ita hindatun take?
Fito da ido tai ta rasa me zatace har saida umman ta sake maimaita tambayar sannan tace eh...tana cikin toilet ne umma, idan ta fito zan fada mata.
Inace gidan Aysha tacemin zataje, me kuma ya faru? Qaqalo murmushin dole hindatun tai sannan tace ehh umma ai nima ina gidan Ayshan.
To shknan,kice mata tai maza ta dawo tun
[21/04, 22:36] Hassan India: Miss collapse
(103)
👠SATAR FITA💃🏽
To shknan,kice mata tai maza ta dawo tun kafin magriba ta rufa,banson sakarcin hofi,daga haka umman ta kashe
Wayar tabi da kallo cike da mamakin saurin sauyawar mahaifiyar tasu cikin qanqanin lokaci, koma meya faru ai zama xa'ai a samu mashala bawai aita fada ba, ta kalli Aysha da tirtsetsen cikinta,tausayinta ya kamata ganin yadda take neman yin kasada da rayuwarta sannan ta maida dubanta ga hindatu dake wani irin kuka mai tsuma rai,tausayinta da haushinta takeji duk a lokaci 1, sallamar en mazan ne ya karkato hankalinsu duka banda hindatun data rufe fuskarta da mayafinta,kujera ishaq yaja ya zauna sannan ya yaye lullubin da hindatu tayiwa fuskarta,idanuwanta duk sun kumbura ga kuma wani shegen bandage dake nannade da kanta, shi kansa tausaya mata yakeyi wani sashe na zuciyarsa kuma haushin dan uwansa yakeji saboda halinsa na son zuciya daya gwada,kafin yayi magana Adam ya fara cewa dan Allah hindatu ki fahimcemu nida Ayshhh hararar da ishaq ya balla masa ce ta nutsar dashi yayi shiru.
Ya kikejin jikin naki hindatu? Cikin sheshsheqa tace da sauqi yaya, yaya dan All.....shiiii yasa hannunsa a bakinsa sannan yace kowata magana zamuyi bai kamata muyita anan ba,ku bari zuwa anjima tunda sunce yau zasu sallameki, shiru tayi bata qara cewa komai ba,amma xuciyarta ba qaramin quna takeyi ba.
Qarfe 10:15 doctor mareeyah ta sallamesu,a lokacin kumburin qafar harya dan sace kuma zafin ya ragu.
A babban falon gidan ya ishaq suka yada Zango dukkansu khadija data baro asibitin tunda wuri ta fara serving dinsu dan ta tabbata da yunwa suka wuni,ba wanda ya iyacin abincin sabida rashin kwanciyar hankali,har ita kanta Ayshan dake fama da tsohon ciki,hindatu kam na rakube a gefe tana narkar kuka kamar wadda ta rasa mahaifanta.
Ganin hakan yasa ishaq ya bude baki zaiyi magana tsuwwar wayar hindatu ta katseshi, umma ce again,wannan karon ya ishaq din ne ya dauka kafin umma tai magana ya katseta da fadin umma hindatu tana nan gida
[21/04, 22:37] Hassan India: Miss collapse
(104)
Ganin hakan yasa ishaq ya bude baki zaiyi magana tsuwwar wayar hindatu ta katseshi, umma ce again,wannan karon ya ishaq din ne ya dauka kafin umma tai magana ya katseta da fadin umma hindatu tana nan gidana,dan Allah ki barta ta kwana anan zuwa gobe saina kawota,dan jimm umman tai na en sakanni sannan tace to shikenan ishaq babu damuwa,Allah ya kaimu goben ta sallame dagaji kasan ba haka taso ba.
Idanuwansa ya maida kan Adam daya sunne kai sannan yace kai Adam yanxu abunda kayi ka kyauta kenan? Idan ba shirme da rashin kunya ba,sai kaje ka dubi tsabar idon Abba kace zaka yiwa yarsa kishiya sannan kuma shi ya shige maka gaba,haba Adam ana barin halal dan kunya fa.
Yaya ni a ganina ba laifi bane, Aysha da kanta ta bani go ahead nayi hakan ta nuna babu laifi to me zaisa ita hindatu bazata fahimceni ba?
Zancen banza kakeyi Adam,kuma ba ruwana da ko kanason hindatu ko baka sonta, wlh idan hindatu tacemin bata saka sai kaje kace musu k fasa,kaji na fada maka!
Gun hindatu ya maida dubansa,dago ki kalleni hindatu, ba musu ta dago ta dubeshi,ki fadamin shin kinason Adam zaki iya xama dashi a matsayin mijinki da kuma Aysha a matsayin abokiyar zamanki!ki fadamin gaskiya,wallahi idan kika nuna bakyaso da kaina zanje na samu baffa nai masa bayani
Qasa tayi da kanta cikin jin nauyin abunda zata fada tace ya ishaq nifa bawai banason ya ADAM bane,amma aurensa ne bazan iya ba,wallahi ya ishaq idan na amince na auri ya Adam zai qarashe rayuwata cikin rashin walwala da tunanin na shiga tsakanin rayuwar ma'aurata na tarwatsa musu farincikinsu,nasan watan watarana dole mu samu sabani da ya Adam kuma a koda yaushe zai dinga tunanin alfarma yamin ya aureni balle kuma Aysha dake matsayin kishiyata,dole mu yawaita samun sabani saboda aure ba xancen wasa bane, bana fatan ta sanadiyyata zumuncin mu ya samu rauni.
Cikin cikakkiyar gamsuwa da kalamanta ishaq ke gyada kansa,naji dadi sosai hindatu da kika zurfafa tunani akan wannan lamarin,kuma na gamsu sosae
[21/04, 22:37] Hassan India: Miss collapse
(105)
gamsuwa da kalamanta ishaq ke gyada kansa,naji dadi sosai hindatu da kika zurfafa tunani akan wannan lamarin,kuma na gamsu sosae,dan haka ya zama dole gareka ka haqura Adam,ka gaggauta janye batun nemanka domin na tabbata babu wanda yake goyon bayan wannan gajeren tunanin naku kaida matarka,nafison mu kashe maganar nan cikin girma da mutunci.
Amma ya ishaq kasan rantsuwa baffa yayi idan bata fito da mijiba zai xaba mata wanda yaga dama,kuma nasan hindatu bat...
Zan amince da kowani zabi da baffa yamin Aysha,na tsarkake zuciyana kuma xan zauna xuciya 1 da koma waye na tabbata baffa bazai zabar mun mugun miji ba saboda shiya haifeni duk abunda ya sameni shima sai yaji ciwo. Da haka suka tashi daga taron nasu bayan ishaq yayi musu nasiha mai ratsa jiki sannan ya qara jaddadawa Adam ya tabbatar yaje ya fadawa Abba cewa ya janye.
Da qarfe 10 ya isa gidansu Ayshan, a falo ya tadda ummy tana kallo, ciki ciki ta amsa sallamarta harga Allah yanzu haushinsa takeji, shima ya lura da hakan amma bai damu ba ya gaidata,kamar bazata amsa ba amma ta daure ta amsa.
Ummy! Abba yana nan kuwa?
remote din dake gefenta ta dauka tana canza tasha tace bayanan yaje Holland, amma ga wannan yace na baka ta zura hannu cikin jakar dake gefenta ta zaro himilin I.V din biki,adan rude ya ya karbi iv din ya fara dubawa,ko kadan baiyi tsammanin haka da wuri komai zai faru ba,
Ummy haka da wuri!nayi tunan.... Adam bafa dani kayi maganar zaka qara aure ba,wannan kukai maganar dashi sae ana gobe aurenku zai dawo dan haka ka taimaka ka bani guri banason raina ya baci ta qarashe maganar cikin hasala, jiki a sanyaye ya miqe yace Allah ya huci zuciyarki ummy. Da muguwar harara ta rakashi sannan taja tsaka tana taya diyarta kishi.
Shiko Adam bai zame ko ina ba sai office din ishaq.
Ya salaam!shine abunda ishaq yace bayan ya gamajin abunda Adam yace, yanxu hanya 1 ce ta rage mana, muje muyiwa baffa bayani idan ba hakaba bana tunanin akwai abunda xai canxa wannan
[21/04, 22:37] Hassan India: Miss collapse
(106)
😍this page is for you my fans❤ words cannot express yanda nake jinku a zuciyana,kuma ina qara muku godiya da bibiyar littafina da kukeyi. Love you all❤
muje muyiwa baffa bayani idan ba hakaba bana tunanin akwai abunda xai canxa wannan lamarin.
Yaya kana ganin baffa zai sauraremu?
Sai munje zamu tabbatar,ishaq ya fada yana maida kansa kan abunda yakeyi.
Da daddare ishaq ya dauko hindatu suka wuce gida,a bakin gate ya tadda Adam ya kasa shiga gidan,dagani kasan a rude yake dan baisan fahimtar da baffan zai masa ba, ishaq ne yai gaba, Adam da hindatun suka bishi a baya a darare, kamar kullum baffa na zaune a falon yana kallon labarai shida umma suka shigo, dama umman tayi tsammanin ganinsu amma bata kawo ganin Adam ba,saidai kuma kallonsu yafi karkata gun hindatu har saida umma ta kasa jurewa tace ita kuma wannan meya sameta?
Faduwa tai ummah!zamewa tayi akan tiles jiya shiyasa ma bata dawo a jiyan ba,ishaq ya amsa mata bayan sun gaisa. Badan ta yadda ba tace Allah ya sawwaqe, nayi tunanin ai wani abun ne, naga tana dingishi ga kuma bandage akai.
Bamu guri hindatu,zamuyi magana da baffa,ba musu ta miqe tayi dakinta zuciyarta na bugun 3-3.
Baffa dama akan maganar auren hindatu ta Adam nazo.
Toooh! baffa yaja fasali yana zare tooth peak din dake bakinsa,me kuma ya faru ishaq,nayi tunanin mun gama komai ai,dan har an fara sanarwa a gidajen radio.
Shiru ne ya biyo baya,kafin ishaq ya fara magana. Baffa kasan Adam har yanzu akwai quruciya akansa,wallahi banida masaniya akan katobarar daya aikata sai yanxu,amma nayi masa magana kuma yanzuu.....shiru yadanyi sannan ya dubi baffa da shima dubansa yakeyi.
Ehn ina jinka ishaq!
Baffa dama yanzu munyi magana dashi kuma yace kayi haquri ya janye tunda ita kanta hindatun bataso.
Shiru ne ya ratsa falon, kowa da abunda ke masa yawo a ransa, ta gefen ido suka kalli baffa daidai lokacin yana zare glass din idanunsa ya kalli Adam yace,shin Adamu nayi maka dole da maganar auren hindatu!
[21/04, 22:38] Hassan India: Miss collapse
(107)
Shiru ne ya ratsa falon, kowa da abunda ke masa yawo a ransa, ta gefen ido suka kalli baffa daidai lokacin yana zare glass din idanunsa ya kalli Adam yace,shin Adamu nayi maka dole da maganar auren hindatu!kokuwa ban nuna maka rashin amincewata ba amma saboda kanason nuna mun ka girma bakaji kunya ba kaje k samu sadauki da zancen,yanxu me kakeso nayi maka?
Yadan ja fasali sannan ya cigaba da cewa, ba gurina kazo neman auren hindatu ba,gurin sadauki kaje dan haka yanzu maza maxa ku tashi kuje Ku sameshi, ni ba qaramin mutum bane.
Kayi haquri ka duba lamarin baffa! Abban bayanan kuma Adam ya fahimci kuskurensa dan All.... isyaku tashi ka bani guri! Baffa ya fada murya qasa qasa,amma dagaji kasan ransa a bace yake.
Baffa dan Allah kayi haquri ka karbi tubana, Adam ya fada a sanyaye.
Murmushi baffa yayi bayan ya dago yana kallonsu sannan yace Allah sarki mutuwa! Allah yajiqan yaya jibril.. a raxane suka dago suna kallon baffan shikuma ya cigaba da cewa na tabbata da mahaifinku yana nan da ransa bazaku iya kallon tsabar idanuwansa kuzo masa da wannan maganar ba!amma dayake baku maidani ubanku ba shine kuke fadamin irin wannan maganar harda kai ishaq!kaida nake ganinka da hankali! Kunzo kuna qoqarin dauramin hawan jini! So kuke na mutu nabar muku duniyar! To shikenan!
Cikin rawar murya suka fara bawa baffan haquri amma sam yaqi sauraron su, ransa ya riga ya baci, daga qarshe ma korarsu yayi daga gidan yace bashida buqatar sake ganinsu,hindatu kuma baa gurinsa suka nemi aurenta ba,su tafi can su bashi guri! A sanyaye suka bar gidan kowa ransa babu dadi.
Ba qaramin fada umma tayiwa hindatu ba,cewarta itace ta tursasa Adam yace ya fasa bayan tare suka hado gulmarsu kuma ta rantse mata cewa haddai aka samu wata matsala daga gareta wajen auren nan to saidai ta nemi wata uwar ba ita ba,ranar hindatu taga tashin hankali danko bacci kasawa tayi, washegari da yamma gidansu hindatu ya fara cika da yan uwansu na Adamawa,cika sosai gidan yayi
[21/04, 22:38] Hassan India: Miss collapse
(108)
hindatu ya fara cika da yan uwansu na Adamawa,cika sosai gidan yayi cikin kwanaki 4 daya rage kafin biki,ana gobe kuwa za'a fara bikin Abba ya dawo!
Kamun amarya aka farayi,ranar hindatu taci kuka ganin fa yanxu bikinta akeyi,nan da jibi tazama mallakin Adam,mijin yar uwarta kuma aminiyarta Aysha, jitake kamar tabar duniya ta huta saboda takaici da baqinciki,daqyar qannen umma suka lallabata tayi shiru aka tsara mata kwalliyarta, lace ne dan ubansu ocean blue da head Royal blue tasaka,sama da qasa kasan hindatu tayi kyau dan ba qaramin gyara akai mata ba,babu laifi gurin ya samu albarkar yan mata da wadanda aka gayyata da yan gayyar sodi,qawayensu da dama mamaki sukeyi irin auren gaggawar hindatu ita da kowa yasan bata zancen yin aure ko saurayi batada, gulma iri iri,a cewarsu sai a dinner zasuga angon. Anyi kamu lafiya an gama, ranar hindatu dakyar ta samu damar yin bacci,Adam dama ba kiranta yake ba duk wasu shirye shirye a bakin Aysha da amin takeji,washegari akai yinin iyaye da daddare kuma dinner, wannan karon adon pink material amarya tasha,kyau kam ba'a maganarshi dan dama hindatu ba daganan ba wajen kyau,saidai kuma kana ganinta kasan bata cikin walwala ga kuma ramar datayi, cikin lumtsumemiyar mota qirir Benz ango Adam yazo,babu laifi shima yayi kyau cikin shaddarsa blue tasha aiki,babu wanda ya kula kowa a cikinsu har suka qarasa hall din, mustapha,abokin Adam daya tuqosu shiya fito ya budesu,hannunsu cikin na juna suka taka cikin hall din, m.c nata faman yin kirari ga ango mijin amarya,nan fa gulma ta kacame tsakanin yan matan dake gurin, dandazon matan our ladies our pride dasukayi qungiya guda harda yin anko na hango,sun caba ado kamar a bikin zahra buhari indimi amma gulma kawai suke zubawa, billy dake gefe tace keh miss collapse wannan ba Adam bane mijin Aysha sadauki,dama shine angon lallai hindatu ta cika maci amana, tabe baki nai cikeda takaici nai nace yoh baga irinta nan ba,sau dubu nawa nake fadawa aysha tai
[21/04, 22:38] Hassan India: Miss collapse
(109)
And did page is for my fans in OUR LADIES OUR PRIDE GROUP, I ADORE U ALL❤❤.
irinta nan ba,sau dubu nawa nake fadawa aysha tai kaffa2 da waccan uwar iyayin amma tana gwaleni,maganinta kenan.
Ku kuma ina ruwanku!cewar maman alfha dake zaune a gefe tana jinmu, da ruwanmu mana kuma wallahi sae naje nayiwa Ayshar magana cewar mhizz maria, a dawo lafiya mukace tareda gyara zama. Tana tafiya kuwa waiters suka kawo mata fried rice tasha kaji, bamuyi wata2 ba muka fara bawa ciki haqqinsa saega mhizz maria ta dawo gefen fuskarta ya kumbura da alama mari tasha, bin plates din tayi da kallo kamar zatai kuka tace ina nawa?
Dariyar data maqale mun ce ta fito nakuwa kwashe da dariya ina kallonta har saida ta gama quluwa sannan nace kin tafi gantali anyi babu kyau, cikin shammata ta fincike cinyar kazar dake hannuna,da harara na bita tareda fadin an dade baa hadu ba sannan na miqe,filin rawa muka fada, ranar mun cashe iya cashewa kuma munsha liqi,dan matan Hausa novels 2 badai mutunci ba, ranar har yan jamila umar tanko books saida sukazo dan ina hango maitama yanata baza babbar Riga amma ko sisi bai liqa ba,yan khaleesat haydar novels ne dai ban ganiba,amma naji labarin cewa zasuzo budar kai.
Da haka dinner ta tashi, gobe kuma daurin aure,kai amarya da kuma budar kai.
Key ta sakawa dakinta ta ciki bayan ta fito sannan ta kwanta akan gadon, takalmi da head din kawai ta iya warwarewa sabida tarin gajiya data kwaso,ta dora manyan idanuwanta kan agogon bangon dake maqale a bangon dakin 11;57 yace, taja wani guntun numfashi a zuciyarta tana hasashen irin wannan lokacin gobe, shikenan ta zama matar aure, matar Adam yayanta,abunda koda wasa bata taba kawowa a ranta ba,ko yaya zamansu zai kasance! Ko zumuncinsu zai daure da aysha! Allah kadai ya sani ta fada a fili tareda rumtse idanuwanta,a haka wani wahalallen bacci yai awon gaba da ita.
Sae 11:30 na samu damar shigowa gida wlh,kaga yaushe na shirya balle na taho.
[21/04, 22:39] Hassan India: Miss collapse
(110)
Gajeren tsaki Adam yaja yana qara gyara zaman wayar a kunnensa yace sa'ad dama can bakayi niyyar zuwa ba,kuma ka kyauta,11 zaa daura aure gobe shima idan kaga dama kace aikine ya riqeka,shiyasa k gagara samun matar aure wlh,wace zata zauna da gantalalle irinka! Toh naji ango!mijin mace 2! Kaga nifa babu ruwana da wata mace wlh,tasha zamanta indai har pillow na yana tare dani, kai kuma ka sani, kadaifi kowa sanin matsalar dake tare dakai, gara kasan abunda zakayi tun kafin dare ya maka ya qarashe tareda tsinke wayar.
Da murmushi sa'ad yabi wayar! Gaskiyar Adam ya kamata nayi settling yanzu nai aure! Saidai kuma har yanzu bai samu matar data dace da tsarina ba,mace dayace tak na taba gani wacce ta sacemin zuciya a lokacin dana fara ganinta,ta juyamin duk wani tunani danake dashi ta sakamun burin aure cikin raina, saidai kuma kash! A ganina na 2 da ita nayi danasanin saninta danayi,tun daga lokacin na fara qoqarin cire soyayyarta a zuciyata amma kamar kullum qara huramin wutar sonta ake! Pillow yaja ya rungume tareda lumshe idanuwansa yana ganin zanen fuskarta a idanuwansa,a haka bacci ya kwasheshi.
Qarfe 30:40 ya farka daga baccinsa,wani mugun ciwon cikine ya tasheshi, a wahale ya farka kuwa hannunsa akan cikin yana qoqarin miqewa ya kasa,azaba sosae yakesha gashi dakinsa da dan nisa da cikin gidan yasan ko magana yayi baza'a jishi ba,daqyar ya iya lalubar wayarsa ya danna kira,number Adam itace number ta qarshe daya kira dan haka yanzun ma ita din yakira, saida Adam ya razana ganin wayar sa'ad a irin wannan lokacin,yanayin yadda yake magana kadai ya tsorata shi,I'm dying Adam plx help me! Zan mutu! A gigice Adam yace lpy saad meya faru! Kafin ya samu damar amsa masa yaji ya saka wani mugun ihu! Ae a firgice Adam ya miqe aysha na tambayar ko lfy yace gurin sa'ad zaije! A 180 a qarasa gidan yana buga wani mugun horn mai gadi ya bude, da mamaki ummi da Abba suka leqo harma da wasu daga cikin yan biki! Da sauri suka qarasa suna tambayar
[21/04, 22:39] Hassan India: Miss collapse
(111)
Da sauri suka qarasa suna tambayar ko lfy? Haihuwar ce? Ummy ta tambaya adan tsorace. Noo Abba sa'ad ne bashida lafiya yanzu ya kirani yake fadamin. Sa"ad kuma? Yaushe ya dawo suka hada baki suna tambaya.
Dazun ya dawo ummy, let's check his room,part dinsa sukai da sauri suka banka qofar, a qasa suka ganshi kwance baya ko numfashi.
A gigice sukayi kansa ummy ta birkito shi tana fadin sa'ad! Sa'ad ka miqe!! Abban ma durqusowa yayi yana girgizashi amma ko motsi bayayi,Adam ne yayi dauriyar cewa Abba ya suma fa,asibiti zamu kaishi, Adam babu abunda zaka iyayi akai?
Abba muje asibitin kawai, daukarsa sukai zuwa bayan motar, ummy na bayan motar Adam na tuqi Abba na gaba, suna zuwa doctors din suka karbeshi dan tun a hanya Adam ya musu waya, kusan 2 hours doctors din suka kwasa a kansa sannan suka fito, babban likitan ne yace su biyoshi office.
A kujerun dake office din suka zauna, doctor peter ya kallesu bayan ya gama yan rubuce2nshi yace tun yaushe yake fama da wannan matsalar?
8 years back(shekara 8 kenan), Adam dake tsaye ya bashi amsa, amma Adam a matsayinka na doctor, koda dai nasan wannan ba field dinka bane ai kasan matsalar.
Kun samu a duhu fa,Abba ya fada yana kallonsu duk su 2.
Wato Alh.matsalar dake faruwa shine.....................
Ya salaam! Yanzu doctor babu wani solution? Ummy ta tambaya cikin tashin hankali. Sorry ma'am,wannan itace kadai hanyar data rage,kuma ku zaku yanke hukunci da kanku and I'm pretty sure duk inda kukaje a fadin duniya haka zaa fada muku ya fada tareda miqewa. Kuka sosai ummy ta saki tana cewa yanzu yallabai yaya zamuyi,bazan iya bari rayuwar dana ta lalace ba,ka taimakamin. Babu abunda zai faru ummy indai ina nan,ISA gobe i iyanxu komai zai zama tarihii Adam ya fada yana share gumin dake goshinsa
Amma ta yaya? Abba ya tambaya cikin tashin hankali shima
[21/04, 22:39] Hassan India: Miss collapse
(112)
Abba mu bari sa'ad ya farfado tukun. Gaba1 suka kwana a asibitin, bayan sunje sun duba sa'ad dayayi rama lokaci 1 saboda azaba,yanzu ma drip ne a jikinsa yanata sharar bacci. Qarfe 6 na safe ya farka, gefenshi ya kalla ganin ummy na zaune kan sallaya tana lazumi, bai motsa ba saiya maida idanuwansa bakin qofa yana kallon masu shigowa,Abba ne da Adam suka shigo wayar Abba a kunne da alama waya yakeyi.
Ka farka kenan! Adam ya fada da fara'a a fuskarsa,ai da baka farka ba har nayi niyyar 7 tanayi naje na sami mike na tambayeshi irin allurar dayai maka ya qarashe tareda zama gefen gadon. Tabe baki sa'ad yayi yace kaga nifa zama nakeso nayi dan na gaji da kwanciya kuma zan cire wannan abun ya fada yana nuna drip din da dayan hannunsa. Gaskiya ne, kaji sauqi Adam ya fada yana dariya tareda gyara masa pillow din ya zauna. Gaida iyayen nasa yayi suna tambayarsa me yake masa ciwo yanzu? Ba komai pa,naji sauqi na warware yunwa kawai nakeji. Nacewa ruqayyah ta kawo abinci ai, nasan yanzu tana hanya yanzu ka tashi kayi sallah koh,ka kuma wanke bakinka. Ba musu ya tashi ya shige toilet bayan Adam ya cire masa drip din. Yana iddar da sallah ruqayyah ta shigo hannunta riqe da basket ga kuma basma a dayan hannunta tana dan tsalle. Gaisawa sukai da mutan dakin har tana tsokanar
adam,ango kasha qamshi yayi dariya kawai sannan tayiwa sa'ad ya jiki,da sauqi ruqayya ya gidan naki? Lpy lau tace tana qoqarin fara zuba abincin data dafa aysha ta shigo. Waro sukayi gaba1 suna kallonta ummy tace ke wai baxaki daina yawo ba?
Kwabe fuska tayi tace nidai ummy dan Allah a rabu dani,ana bikin hindatu sai naqi fitowa na zauna a gida,ai sai duniya ta zageni. Kinjita ko ummy,idan nace ta zauna a gida yanzu saita fara kwararomin wasu dogayen bayanai. A sai a barsu, Aysha da hindatu ikon Allah wanda yace zai shiga tsakaninsu kunya ma zaiji har kaidin kuwa, ruqayyah ta fada tana nuna Adam tana wata er dariya, shima dariyar yayi zaiyi magana Abba ya katsehi ta hanyar c
[21/04, 22:39] Hassan India: Miss collapse
(113)
Adam tana wata er dariya, shima dariyar yayi zaiyi magana Abba ya katsehi ta hanyar cewa Adam muje ko akwai maganar daza muyi. Ko na biyoku yallabai ummy ta fada tana dan daga murya dan har sunkai qofa Abba yace kome muka yanke zan miki bayani,doctor zaizo yanzu ya baku sallama,idan kun gama a cigaba d hidimar biki ni inada baqi bazan dawo ba.
Lfy dai ko Alh sadauki? Baffa ya tambaya fuskarsa da alamun tambayoyi yana kallon su. Lpy lau alh Bashir,shawara ce nake nema shiya kawoni gurinka.
Wlh kasa gabana ya fadi sadauki,na zatta wani abun ne ya faru baffa ya fada yana bude dakinsa dan mutane sun cika gidan sosai.
Bayan Abba ya gama musu bayani baffa ya kalli Adam yace amma Adam kasan da wannan matsalar kayi qus! Baka kyauta ba kuwa. Ai kar kaga laifinsa sadauki,bana raba 1-2 sa'ad ne ya hanashi fada,kasan dan naka d shegen lunkufurci da zurfin ciki. Ajiyar zuciya baffa yayi sannan ya kalli Abba yace to Alh.sadauki da kake wannan zancen shi sa'adun ya amince ne?
Kaji wani zance kuma,ai kasan bazaiqi amincewa ba,kana tunanin zaiqi jininsa ne shida za'a taimakawa?
To shikenan sadauki duk yanda ka yanke ayi kawai. Yauwa haka nakeson ji, Adam aje a cigaba da shirye shirye Allah ya maka albarka. Ameen yace ransa fes ya fice daga dakin.
Qarfe 11 tayiwa Adam a qofar gidansu sa'ad, a gaggauce yayi part din sa'ad din ya sameshi ya fito daga wanka. A'ah ango yadai na ganka anan? Harararshi adam yayi sannan ya samu guri ya zauna bayan ya jefa masa ledar hannunsa. Ikon Allah sa'ad yace bayan ya bude ledar ya fiddo da shaddar dake ciki, kayan wanene wannan? Nakane mlm,dan Allah kasaka sauri nakeyi ana jirana. Amma meye abin dinko babban riga, kasan dai baxan sakata ba koh? Kallonshi kawai Adam yayi sannan bai tanka masa ba. A dole kuwa sa'ad yasa babban rigar. Yayi masifar kyau cikin blue din shaddar sai qyalli yakeyi,ya dubi mudubi yayi murmushi tareda gyara gemun dake fuskarsa. Kayi kyau fa shegen cewar Adam yana miqewa tsaye. Kaganka
[21/04, 22:41] Hassan India: Miss collapse
(114)
Kaganka kamar kaine angon gaskiya zaka ruda yayan mutane Adam ya fada yana murmushin mugunta, to qwalelensu danni har yanzu banga mrs. OK dita ba,dan haka sai su qara gaba. Hakane kuwa Adam ya fada yana dariya qasa2 sannan ya fara daukan sa'ad picx.
Na fada mk banson shirmen picx din nan Adam kuma kasan dalili dan Allah ka daina daukana. Ai yau ko kai aljani ne saina daukeka saboda tarihi dan wannan babbar ranace a gurinka. Sa'ad dabai fahimci abunda Adam yake nufi ba fita kawai yayi Adam din yabi bayansa. Qofar gidan kuwa ya dinke da abokansu sosai shi kansa sa'ad mamaki yakeyi dan kuwa harda abokansa wanda yasan bawani shiri sosai sukeyi d Adam ba. Tare suka rankaya gidansu hindatu. Ba qaramin cika gurin yayi ba da mutane, masu daukan photo,en jarida da sauransu,gaba1 sa'ad a takure yake har saida suka shiga tsakiyar gurin hannunsa cikin na sa'ad, can lungun dasu baffa suke suka fara qoqarin qarasawa sukaji wani maroqi na fadin AN DAURA AUREN SA'AD SADAUKI DA HINDATU BASHIR AKAN SADAKI NAIRA DUBU 100 LAKADAN BA AJALAN BA.
What! Sa'ad ya fada cikin rashin fahimta ya juya yana kallon Adam yace kaji wancan maroqin bashida Kai, jibi abunda yake fada, y kamata muje muyi masa magana ya fada yana qoqarin jan hannun Adam, Adam din yayi zaiyi magana wasu abokansu suka qaraso gurin da sauri suna fadin ango yasha qamshi, a mamakance sa'ad yake dubansu zaiyi magana wasu dattawa suka qaraso suna masa Allah ya sanya Alkhairi,amsawa kawai yakeyi amma kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake, ganin uncles dinsa a gurin ne yasa hankalinsa ya qara tashi ya fara laluben Adam,can ya hangoshi gurin Abba suna magana qasa2 yayi saurin qarasawa gurin zaiyi magana Abba ya fadada murmushinsa tareda fadin ango kasha qamshi,Allah ya albarkaci aurenka sa'ad.
Abba what are u saying! Bafa nine angon ba,Adam ne nipa ban ganeba. Kuje dashi Adam inada baqi bari naje mu gaisa yabar gurin. Saqon mugun kallo ya shiga aikawa Adam mai cikeda tambayoyi,hannunsa Adam
[21/04, 22:41] Hassan India: Saqon mugun kallo ya shiga aikawa Adam mai cikeda tambayoyi,hannunsa Adam yaja sanin cewa zai iya masa ihu a cikin mutane yayi cikin gida dashi,saida ya sallami mutane ya koma ciki.
A tsaye a samu sa'ad din fuskarsa babu alamun fara'a yace Adam me kuke boyemun! Meya faru nakejin ana cemin ango! I need an explanation.
*** *** ***
A rikice khadija ta miqe tana kallon taron matan dake falon tace kunajin abunda maroqin, ya canza sunan angon! Bashi ya canza ba khadija,agon aka canza baki1, wata qanwar ummy ta fada fuskarta cikeda walwala,ta cigaba dacewa Allah ne ya sauya danni dama can ban goyi bayan wai hindatu ta auri Adam ba,kodan saboda matarsa. Qofa suka kalla ganin Aysha ta shigo da saurinta,kallon mamaki suka bita dashi masu tsegemi nayi, a gaugauce ta gaidasu bata jira amsarsu ba ta fada dakin hindatu, kewaye take da yan mata qawayenta sunata yimata shaqiyanci ita kuwa tana gefe lullube da mayafi bakinta yayi qus!shiru sukayi gaba1 ganin shigowar Aysha, a tsaitsaye suka gaisa taja hannun hindatu tareda fadin zomuje. Ba musu hindatu ta bita, a dakin aminu suka yada Zango,da sauri aysha ta kulle qofa sannan ta juyo ta kalleta cikin tashin hankali tace kinsan an daura miki aure ko hindatu? Nasani Aysha! An dauramin aure! akwai wani abu dazan iyayi akan hakan ne? Ta amsa muryarta na rawa.
Kinsan kuwa dawa aka daura miki aure hindatu! Da yayana aka daura miki aure! Yayana sa'ad! Shine mijinki hindatu!
Wani sanyi ne ya ratsa hindatu wanda har a fuskarta saida ya bayyana,a fili tace Alhmdlh!
Cikin mamaki Aysha tace kin sanshi ne?
A'ah Aysha bansan yayanki ba kuma ban taba ganinsa ba,amma na gwammace aurensa akan na auri mijinki!
Lallai hindatu! Wallahi na tausaya miki! Bakisan waye sa'ad ba,na tabbata dakin sani da tuni kin fara kuka! Mijinki mutum ne mai matuqar wuyar sha'ani,hindatu kina tunanin zaki iya zama da mutum irin ya sa'ad,halinku kusan iri 1 ne, mutum ne mai matuqar taurin kai kuma baya juyuwa,bayajin maganar kowa sai abunda yaso
[21/04, 22:41] Hassan India: Miss collapse
(115)
👠SATAR FITA💃🏽
bayajin maganar kowa sai abunda yaso yakeyi,a yanda na sanki da tsiwa hindatu banajin zamanku da sa'ad zaiyi dadi,wannan zabin iyaye ne babu zancen rabuwa hindatu amm..... Aysha plz! Hindatu ta fada adan tsawace inaso ki sani a zuciyata banida wani wanda nakeso dan haka ban damu da wanda aka daura mana aureba haddai ba mijinki bane!bana buqatar sa'ad yasoni dan nima ba sonsa zanyI ba,idan yaso a iyakar zaman mu karya tunkareni hakan zai fiyemun dadi dan bana qaunar takura,dadina bazai wuce sanin danai cewa sa'ad bazai soni ba kamar yadda mkma bazan soshi ba,wannan kadai ya kwantarmin da hankali koba komai bazan dauki alhakinsa ba,tana fadar haka ta nufi qofa da saurinta. Da kallo Aysha tabita sannan ra tabe bakinta,har yanzu akwai ragowar quruciya akan ki hindatu,bakisan abunda ake nufi da zaman aure ba,amma watarana zaki fahimta,fatana ku hade kanku da sa'ad na tabbata zakuji dadin hadin nan,ta fada a zuciyarta.
*** *** ***
Bawai nufinmu mu boye maka bane dan dole kasan da maganar,matakin ciwonka yayi nisan dayasa dole muka yanke wannan shawarar,na tabbata aurenka da hindatu Alkhairi zai zamo maka.
Akanme zakaimun haka Adams! Akan wani dalili! Nace maka ina buqatar taimakon wani ne? A wani dalili za'ka bari a daura mun aure! That too with macen da kakeso!
Bazan maka qarya ba sa'ad inason hindatu! She's my first love! Amma tunda na auri aysha nayi qoqarin cireta a raina Aysha ce tadawo min da ita rayuwana,sa'ad bazan iya barin hindatu tayi rayuwar wahala ba shiyasa na amince da aurenta,amma da matsalarka ta taso, gani nayi banida wata hanya dazan iya taimakonka sai wannan.
To hell with you and your help! Adam ka cuceni ka batamin budget! Nace maka inasonta ne!
You'll learn to love her sa'ad! Ka yadda dani Hindu batada makusa!
Kaimun shiru Adam!zan iya sakinta wallahi and I don't care zan iya bar muku ita nabar qasar! Don't even think for a while zanso wata yarinya dan banida buqatarta ya fada a
[21/04, 22:45] Hassan India: Miss collapse
(116)
👠SATAR FITA💃🏽
fada a fusace,tuni har fuskarsa ta canza colour zuwa red tsabar bacin rai.
Do as u wish dear(kayi yanda kakeso) Adam ya fada yana dafa kafadar sa'ad sannan yace but don't forget duk abunda kayi zakaje kayiwa Abba bayani dan bani na daura maka aure ba kum.....wani wawan naushi sa'ad yakai masa yayi saurin matsawa yana dariya yace bani nakar zoman ba malam ratayi aka bani.
Ummy duk yadda nayi dashi ya shirya muje budar kai yaqi wlh! Garama kije da kanki. Ikon Allah!ummy tace tareda miqewa sukai dakin sa'ad din ita da Adam, a kwance suka sameshi ya daura pillow akan fuskarsa ummy ta qarasa ta zameshi. Idonsa a runtse yace Adam wai wannan wani irin salon wulaqanci ne! Ka rabu dani bazanje ba. Bashi bane,nice nan ummy ta fada tana qoqarin zama a gefen gurin yayi saurin miqewa zaune. Sa'ad maza ka tashi ka shirya ku tafi abokanka suna jira kuma ga mutane tun dazu suna jiranka babu dadi. Ummy nifa gsk.... sa'ad ba shawara nake baka ba umarni ne ka tashi ka shirya yanxu yanzu. Bai iya yiwa ummy musu ba ya miqe ya fada toilet, wannan karon shigar fari yayi tun daga sama har qasa ya fito sai qamshi yakeyi, wannan taron ummy ne dan haka qawatuwarsa ba'a magana,abokansa ne suka take masa baya har cikin gurin, mins kadan amarya ta qaraso itama cikin farar shiga, wannan budar kan ya samu halattar jama'a kamar ba gobe gashi ya qawatu, kyautar gidaje har biyu da danqareriyar mota hindatu tasamu daga bangaren ango, sa'ad kuma kyautar qatuwar gona akai masa. Saida taro yayi nisa sosai sannan aka bude fuskar hindatu. Kamar ance dago suka hada ido da sa'ad. Wani mugun bugawa qirjinta yayi a lokaci 1 qwaqwalwarta ta harba.
He's the same guy da muka taba rigima dashi lokacin bikin Aysha! Kuma shine dai wanda na ganshi a hotel din nan yana kallona! Kenan ya ganeni! shiyasa ya kafeni da idanuwa! To amma ya za'ai naga dan gidan senator sadauki a hotel dat too as a waiter! Ya salaam tace tareda rumtse idanuwanta. Ashe shine mijin
[21/04, 22:46] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(117)
Idan hankalin hindatu yayi dubu to yatashi, daga nan gida aka zarce, sau 3 tana shiga toilet har saida Aysha ta gane tabita ciki,a tsaye ta sameta tayi sharqaf da gumi takuma dafe goshinta da hannu,qarasawa kusa da ita tayi tareda zame mata hannun tace lfy dai hindatu ko cikinki ne ya baci? Kai hindatun ta girgiza mata jiki a sabule. To meye kuma hindatu gashi fa baffa yana kiranki. Aysha shine fa! Wlh shine! Hindatu ta fada cikin rawar murya.
Shine wa? Aysha ta tambaya tana kallon gefen da gefen toilet din a tunaninta ko wani ne ya shigo,nifa banga kowa ba,ayshan ta fada tana dafa kafadar hindatu, Aysha dama shine yayan naki? Shine sa'ad din dakike fada? Ajiyar zuciya Aysha ta sauke tareda cewa wlh kin bani tsoro n zatta wani abun ne, kin sanshi ne? Na sanshi mana! Shine wanda mukai rigima dashi lokacin bikinki a dakin ummy kuma he's d same guy dana gani a hotel din nan amma Aysha a matsayin waiter na ganshi fa!
Kukai fada kuma? Aysha ta fada tana dan zaro ido tace meya hadaku ne? Na manta aysha kuma wannan bai dameni ba, ganina dayayi da Ibrahim yafi komai tayarmin da hankali.
Hindatu ya zakice kinga ya sa'ad a matsayin waiter,wanna zancen naki yayi kama da almara. I'm not kidding Aysha wlh shi nagani kuma nasan ya ganeni saboda yanda yake kallona a gurin budar kai din ban,Aysha na shiga 3 hindatu ta fada tana qoqarin tsugunnawa Aysha tai saurin riqota tareda cewa hindatu ki qwarara kanki plz,ni dake munsan kinada gskia meye abun tayar da hankali,ki kwantar da hankalinki karkisa ya fara zarginki.
Amma Aysha kinsan kallon er iska zai dinga yimin,wlh jikina yayi sanyi a tsorace nake.
Amma hind......bugun qofar da akeyi ne ya hanata qarasawa tayi hanyar qofar tana fadin wanene? Aunty Asiya ce, qanwar umma tace ku me kukeyi a toilet ne gashi baffanku yana kiran amaryar,tun tuni masu daukan amarya sunzo danma na gida ne, aunty 10 mins yanzu zata fito kuyi haquri. To da Allah kuyi sauri ana jiranku ta fada
[21/04, 22:46] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(118)
To da Allah kuyi sauri ana jiranku ta fada tareda juyawa. Kiyi sauri ki wanka mlm tun dazu ana jiranki Ayshan ta fada tareda juyawa ta fice, cikin 7 mins hindatu ta fito,jikinta sai rawa yakeyi,mai kawai ta iya shafawa sae turare da Aysha ta tayata fesawa, rigar buba ta zura na wani Swiss lace tana daura dan kwali aunty Asiya ta dawo, har dakin baffa aunty Asiya ta rakata sannan ta fito, fada da nasiha mai ratsa jiki Abba da umma suka ringa mata,sautin kukanta kawai kakeji da akazo fita da ita ta qanqame baffa tana kuka mai tsuma rai da zuciya daqyar aka fizgeta daga jikin baffa ummy tayi saurin barin gurin dan itama dauriyarta ta qare, a tsakiyar aunts dinta aka sakata suka tafi, cikin daya daga cikin tafka tafkan gidajen sokoto road suka kutsa motar, motoci ne fululu a harabar gidan,ciki da waje,gida ne nagani nafada,tsararre kamar a birnin Korea,babu yawan tarkace amma duk wanda yaga tsarin gidan sai ya yaba,addua kawai hindatu ke zubawa a zuciyarta har suka shigo dakinta, nanma nasiha tasha gurin aunts din nata suka kuma tula mata magunguna, sha kawai takeyi tana ajje sauran,qarfe 9 gidan ya watse aka rage daga hindatu sai Aysha.
**** **** ****
A rikice ya shiga dakinsa Adam na bayansa,qofa Adam ya kullo a hankali yana cewa lfy dai sa'ad!
Wannan ce yarinyar da aka auramin? Sa'ad ya tambaya fuskarsa a daure idanunsa har sunyi mici mici dan bacin rai. Eh itace sa'ad Meya faru? Batai mk bne?
Wannan gantalalliyar yarinyar? Wannan er iskar yarinyar ce matana, mara kunyar yarinya,yarinyar d qiri2 n ganta a hotel tareda wani qato? Mesa za'amun haka bayan na tsare kaina amma a da mazinaciya! Ya fada cikin bacin rai.
Hold your tongue nd mind your words saad she's my sister Adam ya fada Shima ranshi a bace.
Ur sister! Amma anyi asarar tarbiya,koda yake wani lokacin duk qoqarin iyaye wajen saita yaransu sai kaga yaran sun baude.
Sa'ad meye hakan kake fada! U're indirectly insulting my parent.
[21/04, 22:46] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(119)
A rikice ya shiga dakinsa Adam na bayansa,qofa Adam ya kullo a hankali yana cewa lfy dai sa'ad!
Wannan ce yarinyar da aka auramin? Sa'ad ya tambaya fuskarsa a daure idanunsa har sunyi mici mici dan bacin rai. Eh itace sa'ad Meya faru? Batai mk bne?
Wannan gantalalliyar yarinyar? Wannan er iskar yarinyar ce matana, mara kunyar yarinya,yarinyar d qiri2 n ganta a hotel tareda wani qato? Mesa za'amun haka bayan na tsare kaina amma a da mazinaciya! Ya fada cikin bacin rai.
Hold your tongue nd mind your words saad she's my sister Adam ya fada Shima ranshi a bace.
Ur sister! Amma anyi asarar tarbiya,koda yake wani lokacin duk qoqarin iyaye wajen saita yaransu sai kaga yaran sun baude.
Sa'ad meye hakan s kake fada! U're indirectly insulting my parent.
Kaine ka fahimceni a haka Adam, kuma nasan kafi kowa sanin cewa qanwarka lalatacciya ce amma ka bari aka hadani d ita! Wlh nayi nadamar dawowa nigeria ya fada tareda wulli da hular dake hannunsa.
Don't dare to say it again sa'ad! Hindatu bawai ta rasa miji bane yasa aka aura mk ita! Is for ur own good! Kasan kai aka taimaka! Idan bk sonta k saketa mn,Nikuma zan nuna mk cewa ni dan halak ne KA SAKETA NA AURA! zai qara magana wayarsa ta fara ringing,number abba yagani ya dauka ransa a bace, I'm coming kawai yace sannan ya ajje wayar. Harara ya watsawa Adam sannan ya fada toilet, 10 mins ya fito daure da towel, saida ya gama goge jikinsa sannan ya shafa mai da turaruka,wani baqin yadi ya zaro cikin kayansa ya zura,sannan ya gyara kanshi ya fesa da gemunsa,baiko kalli Adam ba ya fice a fusace,abun ma har dariya yaso bawa Adam.
A parlor ya tadda ummy da Abba zaune suna hirarsu jefi2, gefen Abba ya samu a zauna kansa a qasa yana gaidashi.
Dan gyaran murya Abba yayi yace sa'ad,bawai sai na tsaya na maimata maka abunda ya faru yau ba,kasani yau an daura aurenka da qanwarka hindatu, nasan bawai a son ranka bane,itama bawai son ranta bane,zabin iyaye ne
[21/04, 22:46] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(120)
Dan gyaran murya Abba yayi yace sa'ad,bawai sai na tsaya na maimata maka abunda ya faru yau ba,kasani yau an daura aurenka da qanwarka hindatu, nasan bawai a son ranka bane,itama bawai son ranta bane,zabin iyaye ne, kuma tayi biyayyah,haquri ya zamar maka dole yanzu,banaso kaje kana gwada mata wannan halin naka, hindatu yarinyar kirki ce mai tarbiyya da sanin ya kamata,da sauri ya dago ya kalli abban,kamar xaiyi mgn sai kuma ya fasa, dan fasali Abba yaja sannan ya cigaba da cewa dan Allah sa'ad ka riqe yarinyar nan amanarka ce, banda daukan mataki cikin fushi,banda saurin hannu sa'ad ko yaji banson ji a tsakaninku balle saki,idan dawata matsala ka fadamin kafin a rakaka can gidan nk.
Shiru yayi kaman bazaice komai ba,can yace Abba da nace abar zancen tarewar zuwa next week,ni gabadaya ban shiryaba.
Huh! Abar zancen tarewa kuma sa'ad ina ka tabaji anyi haka, amaryarka tana can tana jiranka,kome kake buqata kayishi daga baya yanzu ka shirya tafiya Adam xai rakaka,ummy ta fada tana gyara zamanta. Toh shikenan na gode ummy da Abba ya fada tareda miqewa,ummy tace Allah ya maka albarka sa'ad,Allah sa muga yayanka,k dage da addua kaji. A ciki2 yace ameen sannan ya fice.
Zuciyarsa na tafasa ya fita, a dakinsa ya tadda Adam yana harhada kaya a akwati, meye hakan kakeyi Adam? Sa'ad ya tambaya daga tsayen dayake. Inner wears d sleeping dresses dinka nake hade maka,acan akwai kaya. Tsaki yaja bai kulasa ba harya gama sannan suka jera. Wai sa'ad da baqin kayan nan zata tafi kamar wanda akaiwa mutuwa? Adam ya tambaya yana zura akwatin a bayan motar. Ai garama ace mutuwa akaimun da sauqi nasan kowa zai mutu. Allah ya kyauta kawai Adam yace tareda jan motar sukai gaba. Shiru ya dauki gurin can Adam yace waini banji kayi zancen inda za'a siyo kaxar ba,haka zamu tafi hannu na dukan cinya?
Tsaki kawai sa'ad yaja ya maida dubansa ga window, cikin en mintuna suka qarasa gidan, Adam ne ya fara fitowa sannan sa'ad
[21/04, 22:47] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(121)
Tsaki kawai sa'ad yaja ya maida dubansa ga window, cikin en mintuna suka qarasa gidan, Adam ne ya fara fitowa sannan sa'ad,jakar ya janyo daga bayan motar sannan sukai gaba. Daqyar Adam ya iya lallaba sa'ad suka shiga dakin,anan suka taddasu hindatun tayi pillow dakan aysha, da ita kuma ayshan tana dan buga bayanta,sallamarsu ce tasa tai wunzir ta miqe zaune tana gyara mayafinta, Adam zai fara magana sa'ad yayi saurin katseshi ta hanyar cewa ke Aysha tashi kibi mijinki,an gode. Da mamaki ta dago ta kalleshi,ganin fuskarsa a daure yasa tasha jinin jikinta ta fara qoqarin miqewa hindatu tayi saurin damqe hannunta.
Dan murmushi Adam ya saki yadan yiwa sa'ad alamar y fito,bai musa ba ya biyoshi falon. Sa'ad meye haka din? At least k tsaya suyi sallama mai kyau mana ko baza'ai siyan baki ba,why are u acting like a child?
Tsaki sa'ad yaja sannan yace Mr.man I'm sleepy idan bazaka tafi ba ni zanyi kwanciya na.
Kasan kan gidan kenan,Adam ya fada tareda yin gaba. Sama2 Adam ke nunawa sa'ad tsarin gidan,4 rooms ne a part din hindatu da toilet sai kitchen d parlor, kowanne yasha tsari mai kyau,sai kuma part din sa'ad din daki 1 aka gyara dayake ba enough tym. Not bad yace tareda fitowa.
Kuka sosai hindatu takeyi tana roqon Aysha karta tafi ita kuma tana lallaminta da bata qwarin gwiwa dan kuwa ta fahimci hindatun a rude take sosai,saida tayi mata wayo sannan ta barta ta fito,tanajin tashin motar su aysha saboda dare ya tsala,sautin rufe qofar falon dataji ne ya sake hautsina mata ciki,tuni gumi ya jiqata ta fara tunanin ta yadda zasu kwashe da angon nata.
Ta waje ya turo qofar yayi part din da Adam yace nasa ne, babu bata lokaci ya shiga dakin ya sauya kayansa zuwa qananun kayan bacci ya fada kan gadon,tunani kala2 suka shiga zarya a qwaqwalwarsa,kowanni juyi tsaki yake bugawa da hakan bacci yayi awon gaba dashi. Ita ko hindatu a lokacin tashiga Toilet yakai sau 5,ganin har qarfe 3 angon bai shigo ba yasa tadan
[21/04, 22:47] Hassan India: Miss collapse