Tsaye yake ,tsayuwa irin na jaruman sojoji ,ya hard’e hannayen shi ta bayanshi ,kai a k’asa yana sauraron mutumin. Wanda ya cigaba da cewa ” Ashe in bana nan bazaku iya kula da komai ba ? Am very disappointed in you !! Wannan ai zancen banza ne!!!! A lokaci guda yayi wurgi da jaridar da ke hannun shi a fuskar jarumin gami da cewa ” take a look at these!!! Jaridar ta bugi fuskar shi sannan ta fad’i k’asa amma abunka da namiji ko motsawa bai yi ba!!! Dattijon da ke maganar yace ” na baka nan da sati daya a san yadda akayi aka nemo min kayayyakin nan in kuma ba haka ba I will held you responsible!!! Kaji na gaya maka! Yana kai wannan ya kwashi wayoyin sa ya fice wasu sojoji suka bi bayan shi , aka bud’e masa k’ofar mota ya shiga suka bar gidan..
Mutumin da ke tsaye kuwa wanda da ka ganshi kaga mai yi masa fadan ya tab’e baki ya nemi kujera ya zauna zuciyan shi na tafarfasa gaba d’aya tunanin shi ya dagule ,ya maida duban shi ga jaridar da ke jefe a k’asa ya sake kauda kai. Wata mata ce sanye da bak’in leshi yasha silver stones idonta da farin gilashi ke sauk’owa daga bene ,har ta zauna kusa dashi bai ma sani ba ,ta d’aura hannun ta akan nashi ta rike ,ya juyo ya dubeta ,tare da k’arfin halin yin murmushi ,itama murmushin tayi sannan tace” My son! Kayi hakuri ,Abban ka fa ya rasa a kan waye zai yi quenching fushin shi ne ,nima saida yayi min saikace ni din ma soja ce ,balle kai kuma da jiya ma sai bayan abun ya faru ka iso garin ranshi ne kawai a 6ace. Dan nata ya dubeta yace ” but mom ai……,.” Kafin ya k’arasa tace ” shhhhh!!! ” don’t stress your self !!, breakfast is ready! Naji kace kana da meeting ko? Ka tashi Kaje ka ci abinci ka shirya ka fita, bana kuma so in sake gani kana had’e rai!! Babu musu ya tashi ya nufi dining section don yin breakfast yayin da ita kuwa Hajiyar ta koma stairs abunta…….
asalin labarin
Major General Abubakar Rasheed babba ne a Cikin Nigerian Military kuma wanda aka dama aka shanye dasu a Army!! Matarshi Fad’imatu bafulatana ce daga Gombe state fara kyakkyawa doguwa amma kasantuwar sunan kakarta aka sa mata kuma suna k’iran kakar da inna sai ita ma suke kiranta da INNA FETEL (INNA K’ARAMA), Dansu guda d’aya tilo mai suna RASHEED sunan baban mahaifin shi aka sa mishi , suna zaune a Abuja army barracks ,Rasheed har ya girma burinshi ya zama soja irin baban shi ,sun bashi ilimin addini da na boko ,karfi kuwa ba’a magana domin tare yake workout da mahaifin shi ,balle ma Yaron da ya tashi cikin sojoji sannan kuma ya kasance mai himma haka kuma suke tafiyar da rayuwar su cikin jin dadi ,family ne mai cike da soyayya, duk da kankancin familyn akwai abokanan Rasheed da suke tare da shi a gidan su biyu Muhammed wanda suke ce mishi Al’amin da kuma Abubakar Sadiq wanda zaman su a gidan ya maida familyn tamkar babba ne domin Inna da Abba sun d’auke su tamkar yayan cikin su ne , Al’amin air force ne while Sadiq ma captain ne a takaice dai familyn duk taron military ranks akayi
. Wannan kenan.
Rasheed na gama breakfast ya nufi side nashi don shiryawa ,already ya kusa yin latti ma haka ya shirya cikin gaggawa ya fito ,direct sai d’akin Inna. Tana zaune sai faman rubuce rubuce takeyi yayi sallama, ta amsa fuska cike da fara’a tace ” har ka shirya kenan!” Murmushi shima yayi yace ” yes mom” tayi masa adduoi da ta saba in zai fita, ya amsa da Ameen sannan ya fice ya nufi motarshi
Ya d’auki hanya bai zame ko ina ba sai No 7 Garki road ,inda military defence headquarters yake ,isarsa gate din aka bude mar ya shige ya yi parking, yana fitowa wayar sa tayi kara saida ya gama kwashe files din da ke motan sannan ya d’aga wayar ,daga d’ayan 6angaren wanda ya kirashi yace ” ina hanya fa dude !! Na jika shiru tun jiya baka min emailing wannan article d’in ba” Rasheed ya d’an shafa kanshi yace ” Oooh !! Am sorry I was totally carried away by circumstances around here wallahy ni na k’osa ma ka dawo ko zan huta ” daga d’aya ‘bangaren yace babu wani nan !! Wato so kake in dawo a had’a dani a fad’an ko?” Rasheed yace hmm kana jin dad’i fa lallai mom tana yi da kai!! Wato har ta fad’a maka abunda ya faru ? ” yana maganan ne a lokaci guda yana kallon agogon hannun shi ,ya zaro ido waje:oops: sannan yace ” look dude!! We’ll talk later am already late for the meeting !! Dad is going to finish me up today,” Sadiq ya bushe da dariya yace ” OK ltr :D:D”
Sauri yake ta zubawa a hallway din nan yana wuce offices na manyan soji har ya kai meeting room sannan ya tsaya ya gama kimtsawa ya bud’e k’ofar a hankali yana shiga sukayi ido hud’u da Abba ,ya kafse kamar bai ma san da shi ba ,ya nemi guri zama ,bai zauna ba saida yayi apologising for lattin da ya maka ,don ya lura wasu har sun k’osa ma. Ba tare da ya kalle she ba Abba yace ” you may start presenting how the operation is going to be ” ya kwashi files din aka kashe wuta sannan aka kunna projector wato majigi sannan ya fara presentation din nashi hankali Kwance ya kammala duk Kowa kuma ya yaba da hakan. Minti talatin ne kachal dama meeting d’in Kowa ya fice banda Rasheed da Abban shi ,shi Abba kawai bai ga daman tashi bane amma Rasheed files d’in yake tattare wa , har ya gama zai fita Abba yace ” a office d’ina akwai wasu files guda biyu red colour an rubuta operation red I want you to go through them ,Kaje ka d’auka yanzu!!” Rasheed yace “SIR!!! ya fice ya barshi cikin room d’in….,…….
K’arfe biyar na yamma Sadiq ya k’ira Rasheed ,yana dagawa yace ” dude na iso fa amma kuma I can’t drive anymore jikina ba k’arfi sosai wlhy ,Kazo ka d’auke ni plssss!! ” Rasheed yace OK kana ina yanzu?Suleja road ! OK ganinan zuwa” ya kashe wayar ya tashi ya saka wata Yar shirt nashi blue armless gashi button din a bud’e hakan yayi displaying twelve packs nashi ,bai saka buttons din ba har saida ya iso inda Sadiq yake ,shima yayi hakan ne saboda tarin y’an mata da ya gani a chan gefe ,saboda mutum ne mai kunya when it comes to issue na mata saboda haka ne ko a barrack bai cika shiga sabgarsu ba sai na mutum d’aya ,wato childhood friend nashi wanda ban ambace ta tun farko ba ,sunan ta Imtihaal ya fita da wajen shekara biyar amma sun shaqu sosai, saidai yanzu bata k’asar ,taje karatu a Malaysia… Sadiq ya d’an lallaba ya k’araso inda motar yake ,shi kuma Rasheed ya bud’e masa ya shiga sannan ya zagayo shima ya shigo gami da rufe k’ofar, har zai sa key ya kunna ya juya ya dubi Sadiq da sai yamutsa fuska yake yi yace ” ya dai dude! Me ke damunka ne? ” wlhy ina fada maka na tsaya ne na ci fast food a wani restaurant cikina ya birkice sau wajen bakwai ina tsayawa a hanya sai na nemi gurin juyewa lol. Rasheed ya bushe da wata irin dariya ta mugunta wanda har saida yasa Sadiq razana ” yanzu kai dan Allah meye abin dariya ni shiyasa bana son fad’a maka wallahy nasan dama abunda zaka min kenan ” Rasheed ya ci gaba da dariyarsa haka suka isa gida tun Sadiq na fushi har shima ya biye masa suka ci gaba da dariyar
.
Rasheed na parking motar kafin kace me har Sadiq yayi wuf ya fice daga motar a guje yayi cikin gida ,mom na parlour ya wuceta ko gaisuwa babu ,ya barta da sake baki , Rasheed na fitowa daga motan ,dariya ta ci shi sosai yace ” nifa bani naje na ciyo mama abinci ba don haka bazaka barni da d’aukan wannan k’aton jakar taka ba!!” Shima ya bi bayanshi yana wasa da makullin motar tasa.
Yana shiga Falo ya hangi mom zaune ,kafin ya ce komai ta riga shi da cewa ” yaya naga mai gidan nawa haka? Sunan da take k’iran Sadiq kenan dayake sunan su d’aya da Abba ,abunka da bafulatana ganin Rasheed bai amsa mata ba ,ta zare glashin idon ta ,ta sake maimaita abunda ta fad’a, Rasheed da ya kusa kecewa da dariya yace babu komai mom ,daman yana fama da intestinal disorder ne , yanzu ma motarshi na chan bakin hanya ya kasa driving, yana magana yana Sosa ‘keya ,mom tayi murmushi irin nasu na manya tace its alright bari zan duba shi ” kai kawai ya girgiza mata shima ya haye sama yana dariya ,shi ba komai ke bashi dariya ba sai ,juyewa da Sadiq ya ambata . Oh ni hauwa’u!!! da ganin Rasheed kasan rigimamme ne musamman in yana tare da friends .wannan kenan!!!
GOMBE STATE
Rana ake yi kamar me ta fito daga wata silver coloured mota kirar Nissan maxima takalmin k’afarta black stilettos masu uban tsayi ta fara sauk’ar wa ta jima a haka kafin daga bisani ta fito ,wata yellow jallabiya ne a jikinta mai adon duwatsu black and white tayi rolling kanta da multicoloured gyale wanda yayi matching da kayan nata ,sai simple beaded bracelet da ta saka bak’i shima ,ba fara sosai bace amma baza’a sakaya ta a jerin bak’ak’en mata ba ,siririyar fuska gareta daga ka ganta kasan ta tashi cikin gata ,sannan kuma siririya ce ba wata k’ibar a zo a gani gareta ba sai wani shan kamshi take tana yamutsa fuska. Abuja quarters ne inda ta tsaya d’in d’aya daga cikin unguwannin da ake ji dasu a garin Gombe kenan. Juye juye take tayi kamar me neman wani abu ,chan kuma ta d’auko wayarta daga purse din dake hannun ta ta kira wata number ” hello !! Ke nifa na rasa gidan gaba d’aya na kasa gane wanne ne a ciki kawai ki fito ki kai ni!! OK toh ina jira kiyi sauri pls its sunny out here!” Abunda ta fad’a kenan ta katse wayar. Bata dad’e ba kuwa wata y’ar budurwar chocolate brown amma kyakkyawa ta fito sai washe 32 take yi:D suka dunguma suka shiga gidan tare……
Sadiq na zaune saman mota a parking lot na gidan nasu ,Rasheed ya fito d’auke da traveling bag nashi ya kafa waya a kunne sai faman zuba yake, sai da ya iso gurin motar yace ” imtihaal zan k’ira ki anjima ,pls I’ll be on my way to Gombe state ,gobe bikin cousin d’ina ,I missed you soooo much ! take care !” Sai ya katse wayar ,Sadiq yayi dariya yace sarkin surutun naka Mukam ta yaye mu gaba d’aya ,by the way how is she doing there in Malaysia? ” Rasheed yayi murmushi yace ” lapyarta k’alau ” nan suka shiga mota don tun safe su Inna suka tafi ,su sun tsaya sabga, yanzu karfe biyu ga uban rana amma haka suka d’auki hanya suna tafe Rasheed na zolayan shi ” Kar fa kace mu tsaya ka juye don bazan iya ba:roll:”………
Basu suka sauk’a a garin Gombawa ba sai wajen to nine, a gajiye ko kayan su basu d’auka a mota ba suka wuce side d’in da suka saba zama in sun zo ,akayi sa’a kuwa tun isowar su Inna ta sa an share an gyara don tasan halinsu da iya tafiyan dare, daga sukayi wanka da sallar maghrib da esha ai nan suka zube sai bacci ,gwara ma Rasheed cikin dare ya koma saman gado ya kwanta amma sarkin barcin kam ko juyi bai yi ba sai da aka k’ira sallar asubah .
Sukayi alwala , da yake akwai wasu kayan nasu a dakin suka saka ,sai masallaci basu ma dawo cikin gidan ba sai wajen seven thirty (7:30)am, ko da suka shigo main house suka shiga don gaida y’an uwa, kakar shi Maryama wato maman Inna ita ta fara hango shi, tace toh sai kuyi ta yi nima ga jika na ta zo “:D da dariya ya karaso domin ita Inna ba k’arami aikin ta bane ta maida namiji zuwa mace and vice versa, ya zauna gefen ta yace ” me sukayi miki ne kakcy?” Abunda yake kiranta da shi kenan, ta had’e rai tace kagan su nan basa sona 6ingel am!! Tun jiya sun samu yan uwansu sun ya dani ,toh nima ga jika na ya zo ” Rasheed ya sake kwanta wa jikinta yace kwarai ma kuwa !!” Mommy Yayar Inna ne sunanta na asali zubainatu amma auna kiranta da Adda jube, akwai mutum biyu maza tsakanin ta da Inna wato maman Rasheed ,uncle Hasheem, da Hamman last born nasu kuma Goggo Aisatu. A takaice mata uku kenan maza biyu a gun mahaifiyar su. Mahaifin su ya rasu ba da dad’e wa ba. Mommy wato Adda jube ta mik’a mishi food flask dauke da p. Soup na cow tail tace ga breakfast naku sai kuje ku karya an kai muku sauran ya karb’a rai a dagule yace ” ni fa mommy madara kawai zan sha” nan mommy ta had’e rai tace ” yanzu da sassafen nan so kake inje in tatso madarar saniya ,in tafasa maka ko kuma a ina zan samu madara !! Kai dai wallahy fulatancin nan bazai kaika ko ina ba fa ,kai Sadiq tashi Kaje ka karya ka barshi in ya ji yunwa zai je ya ci ai!” Su kakcy an tab’o d’an jikalle nan tafara azalzalar mommy da masifa don kaf jikanun ta babu wanda take ji dashi kamar Rasheed. Tashi tayi da kanta ta ce ” muje ni ina da madara tun jiya yana furji yayi sanyi muje ko kindirmo kake buk’ata akwai sai wanda kayi niyya ” ya mike ya bita yana danna wayarshi ko kallon su Inna bai yi ba balle Sadiq da suka zo tare.
Karfe goma aka d’aura auren Mujaheed cousin din Rasheed da Nusaiba Daneji. Taro akayi ba kad’an ba amma Rasheed bai ma san wainar da ake toya wa ba don tun da ya shiga gurin kakarshi bai fitoba suna chan yana ta mata hira yadda ya saba ,don shi yafi sabawa da ita akan kowa. Sadiq se k’iran wayar Rasheed yake bai san cewa mutumin ya bar wayar a cikin d’aki ba wanda yake amfani da shi kuma ko sim card babu a ciki ,don game kawai yake tayi da wayar. Wajen 10:30 tukunna ya fito yaga gida cike mak’il da jama’a da ‘kyar ya wuce ,filin gidan ma duka an d’aura canopies ana reception da sauri ya wuce ya bud’e side nasu ,yayi wanka ya kimtsa cikin farar shadda tayi mugun yi masa kyau ,ya kafa hula bak’a abunka da d’an fari ya fitar da shi sosai ,ya fito sai dube dube yake ,karaf ya had’a ido da Abba:oops: wani kallo ya watsa mar ,ya nuna masa ranshi a 6ace yake, Rasheed ya sunkuyar da kai ya nemi gurin zama bai ma san inda ya zauna ba sai da ya yi adjusting ya ga ashe ,Sadiq ne da Al’amin. Al’amin ya 6alla masa harara yace fi sabillilah har na iso ace kana chan kana shirme kamar ba bikin Mujaheed d’in ka ba ,ina ka shiga ne haka? ” Sadiq de bai ma ko kalle shi ba ,shima bai ku lashi ba don baya so ya takalo wa kanshi rigima……..
Ana gama reception Rasheed ya mik’e don ya nemo ango ,Sadiq yace ” toh masu kaka!! Saura in Kaje hiran ka manta akwai dinner da dare kayi zamanka :roll:” Al’amin de dariya kawai yake yi don yasan hakan zata iya faruwa. Rasheed ya daka musu harara yace ” Baku ma tsaya kunga inda zani ba kun fara surutan naku ,toh Mujaheed zan nemo ,kuma I need a quite place nayi magana da Imtihaal naga missed calls nata har hud’u. Sadiq yace ” Hmmmm daga nan kuma sai gun kakcy ko?!” Bai tanka masa ba ya wuce ,su kuwa suka bushe da dariya…..
Bayan sallar isha aka fara programs ,amarya da ango ansha kyau , k’awayen amarya ma haka , amaryar sai juye juye take yi da alama wata take nema ,chan wata daga k’awayen nata ta gano hakan ta zo tambayar ta ko me take buk’ata? ” Babu komai Hanan kawai banga Ilham bane ,ko ba tare muka fito bane ?” Hanan tace ” Haba amarsu ! Saikace ba kisan halin mutumiyar taki ba? Ai tana chan waje tak’i shigowa ,wata’kila in ruwan saman ya sauk’o zata shigo” kafin ta gama rufe baki kuwa aka fara ruwa…
Daidai bakin k’ofar shiga ta d’auki glass na cherry drink tana shigowa tana taku tabbas tayi stealing show d’in kam ba kad’an ba ,ankon bikin ne a jikinta kamar yadda sauran k’awayen suka sanya fushia pink da silver goggoro yau kam dai simple makeup tayi amma tayi kyau ,tahowa kawai take yi tana danna wayarta ,hannu daya ta rik’e glass cup ,suka ci karo da Rasheed da ke neman hanyar fita yana waya, duk wannan drink din ya zube a kayan shi ,gashi shadda ce fara da ita ,duk kallo ya koma kan su.
” Kai Malam baka gani ne ko kuma makaho ne kai da zaka na tafiya ba tare da ka duba inda kake tafiya ba? How arrogant!! Mtsew!!!!” Abunda ya ziyarci kunnen Rasheed kenan ,Sadiq sarkin zuciya har ya mik’e Al’amin ya hana shi , shima Rasheed din murmushi kawai yayi yana rike da inda drink d’in ya zuba ,ya fice ya barta tsaye a gurin sai tauna takeyi ,ta sake yin wata tsakin da ta ga su Sadiq sun bi bayanshi, duk da Sadiq baya son raini haka ya hak’ura ya wuce bai kulata ba ……. Haka dai aka gama dinner kowa ya watse.
Karfe shida na safe suka yi sallama da family su kakcy har mota ta rako jikallen ta . Abunda yarinyar nan ta mishi yayi matuk’ar 6ata mishi rai ,shi kanshi ya rasa dalilin da yasa ya kasa tanka mata……
Two weeks later::
Tafe yake yana waya da mutumiyar tashi ,wato Imtihaal ,wani ‘kara da yaji wata mota tayi yasa ya katse wayar da sauri ya juya. Hayak’i duk ya karad’e gurin , saida ya washe tukunna ta fito sanye da kayan sojoji saman shi ta d’aura lab coat ta kama gashin kanta kamar doughnut ta kasa sannan ta d’aura hular soji ,Barrett a kan ,tana tafe tana waina key d’in motar da ke hannun ta. Kai tsaye ta nufi office na lieutenant….. Tabbas Rasheed ya gane fuskar ta duk da ma yau shigarta daban da na ranar dinner d’in……
Toh fa !! Masu karatu d saga begins here!! Ni kaina bansan iyakar tsanar da Rasheed ke mata ba amma muje zuwa …….
.
.
MU CI GABA KUWA?
[3/11, 11:39 AM] 🅰 " 🅰 " D🅱⭕Y: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[3/11, 7:27 PM] 🅰 " 🅰 " D🅱⭕Y: 👨✈ *CAPTAIN RASHED* 👨✈
Page 21 & 40
.
Wata muguwar dariya yayi ya wuce yana wayarsa ko gurin bai sake waiga wa ba. Ya shiga gida kenan bai jima ba ,wayarshi tayi ringing ya duba yaga Abba ne ,” ka shirya Kazo yanzu da sauri zamu shiga emergency meeting ,ina fatan Sadiq na tare da kai ,your presence is needed ” yes sir” !! Kawai shine amsar da ya bayar ,ya shige bathroom……
Suna shiga defence headquarters , ya ga motar Ilham ne a gaban nasu ,kawai ya kara gudun motar da gangan ,ya buga mata bayan mota har danger motan ya fashe ,yayi wata muguwar dariya ya kau da kan motar shi ya wuce parking lot yayi parking motar shi ya barta a gurin tana ta surutai kamar mahaukaciya ,da gudu tabi bayan shi ta sha gaban su gashi ta tsuke cikin khaki. ” suna had’a ido ta sunkuyar da kai ,ta gane shi sosai ,gashi kuma ko a matsayi ya fita (rank). ” lapiyar ki kuwa? Kika tare min hanya ,ko dai kin tab’u ne? Sadiq kuwa bashi da aiki sai hararar ta don tun farko ya tsani yarinya , ganin bata da abun cewa yasa ta matsa suka wuce ,cikin ranta kuwa tace ” Oooo I see !! Wato rama abun da na maka kayi ko,in dai wannan ne kuwa ka d’ebo ruwan dafa kanka zan hadu da kai ne ,gani na kake yi baka san hali na ba:roll:.
Fitowan su daga meeting ta ci karo da shi da General ma’ana Abba ,abunda ya ziyarci kunnenta shine Kalmar DAD da ya ce wa General d’in. Ta wani juya idanuwa tace ” lallai wannan yana da k’arfi ta ko wanne fanni ,wato don shi d’an General ne sai ya wulak’anta ni ko?zan yi maganin ka! ” suka wuceta suna discussion nasu ta bishi da kallo ,yayinda shima ya tsareta da ido, duk abunda ta fada kuwa Sadiq ya ji ta ,don bata san yana bayanta ba , tana juyawa ta ci karo dashi,gata da tsoro tuni ta rikice ta rasa yanda zata yi ta bud’e wata k’ofa ta shiga ta rufe k’ofa, daga waje Sadiq ya bushe da dariya yace ” tabdi yarinya kin yi gudun gara ne kuma kin tadda zago
Office din Rasheed ta shige bata sani ba ,yana zaune yana fama da computer yaji an bud’e k’ofa a zaton shi ma Sadiq ne kawai ,sukayi ido hud’u ,idanuwan shi kadai kan bata tsoro in ya zaro su ,ta d’an daure ta juya zata fita ,yace ” come here!!! Ta juyo gami da watsa masa harara yace ” excuse me!!! Wannan kallon fa? Ta kauda kai gefe ,yayi dariya irin na mugunta ya watsa mata wasu files yace ” ki kai wad’annan wa captain Sadiq and pls hurry baby !!” Baby da ya k’irata yayi mugun bata haushi ,ganin hakan shi kuwa ya samu abin yi:D. Ta juya ta fice rik’e da files d’in.
A kofar fita ta hango Sadiq yana faman bud’e k’ofar mota ga dukkan alamu fita zai yi ,da sauri ta nufi inda yake ,tana isa ya tada motarshi ,ya sauk’e glass d’in motar yace ” ya dai?” Ta mik’a masa files d’in ” gashi captain yace in kawo maka ” Sadiq yayi wata y’ar dariya yace ,sorry ki rik’e yanzu Ina sauri pls Kar ki 6ata min lokaci ,in na dawo sai ki bani in kuma ban dawo ba mu had’u a barracks ya daga glashin motar ya yi tafiyarsa ya barta anan baki a sake. Bak’in cikinta ,tun da take ba’a tab’a cin mutuncin ta haka ba. Ta juya jiki a sanyaye ,tace ,zan rama ne!!”
Saman motar ta take a kan hanya metres kad’an daga headquarters d’in tana hango motar captain Rasheed ya danno kai kawai sai ta watsa wasu k’ananan k’usoshi a kan kwaltan ,ta ci kunu tana danna wayarta ta toshe da bak’in gilashi saboda rana da ake yi, duk da Rasheed ya ga abun da ta aikata kafin ya iso hakan bai hana shi bin hanyar ba ,kamar yadda take tsammanin gani ,tayun motar duk sun sace ,yayi parking a gefe ya jingina da motar ya fiddo wayar shi daga aljihu ya kara a kunne ya k’ira daga chan wani ya taho mishi da mota ,ya karb’a makullin sukayi wasu yan maganganu mutumin ya koma da baya ,ita kuwa tana zaune cikin mota ta shagala sai shek’a dariya take yi bata san wainar da ake toya mata ba , duk tayun motar ta Rasheed yasa Wannan sergeant d’in ya sace ,sai ji tayi tana yin k’asa, ba shiri ta fito tana ta dube dube a rikice ta rasa yadda zatayi ,ga zafin rana , ta fito ta banke k’ofar motan tana hararan Rasheed shi kuwa murmushi kawai yayi ya ja motar sa yayi gaba:D.
Yana tafe yana cewa lallai ma yarinyar nan ain in tana cin k’asa kamata yayi ta kiyayi na shuri!! Ya sake AC yaci gaba da tuk’in shi, sai da ya isa gida ya yi wanka ,har yaci abinci ,suna hira da Inna a palour Sadiq ya kirashi yana d’agawa yaji sai dariya yake ta yi kamar mahaukaci ” kai meye haka ka k’ira mutum kuma sai dariya kake kamar sintacce? Sadiq yace yanzu naga mutumiyar taka ,tana ta faman tafiya ga rana ,kaga ni ba gida zan dawo ba da na taimaka mata” jin haka ta bawa Rasheed tausayi yace ” bari na koma na d’auko ta ,haushi take bani yarinyar ta maida ni kamar wawa ,sa’an ta.
Tafiya take tana ta faman share gumi , duk wuyanta ya bushe gashi ba kowa ta sani a garin ba ma balle ta k’ira, motar Rasheed ce ta bullo ta tsaya a gabanta ,tana k’arasawa gurin ya bud’e k’ofar motar ba tare da ya fito ba ,ta tsaya tana ta shan kamshi, ganin ya saka hannu zai rufe yasa ta shigo ba shiri ,abun ya bashi dariya matuk’a ya girgiza kai ya tada motar. Tafiya suke babu wanda ya yi ko tari ,yasan zata ji kishirwa ,ya d’auko ruwa chilled a cooler ya bata ,kamar bazata karb’a ba kuma naga ta mik’a hannu,ta kafa kai bata sauk’e ba saida ta gama shanye ruwan sannan tayi relax a jikin kujerar sanyin AC na ratsa ta ta koina.
K’ofar gidan su ya dire ta ,bud’e k’ofar motan tayi ta fice ba tare da yi masa godiya ba,shikam ya ma kasa sa key a motar balle yayi tunanin tafiya ya bita da kallo don yaga iya gudun ruwanta, har tayi nisa ta dawo kai a ‘kasa tace ” nnn… Aa gode !” Ta fad’a ne kamar wanda aka tilastawa sai ta fad’a. A fusace ya fito a motan ,ya shak’e ta ya manneta da motan yace ” ke wace irin jahilar mace ce? I have been doing you Favour’s amma bari kiji in fad’a miki ,yau kin kaini mak’ura , a girme na fiki, amma bakisan ki girmama na gaba da ke ba ,who the hell do you think you are!!! Since from d first day I saw you naji na tsane ki !! I will give you this as a warning!! ,ki fita daga harka ta ,kar ki sake wani abu ya had’a ki dani ko da wasa don sai na miki wulak’ancin da bazaki tab’a manta shi ba har ki gama rayuwar ki!! Mark my word!!!!” Yana kai wannan ya juya ya barta a gurin ido cike da hawaye wad’anda suka kasa gangarowa har saida ya ja motarshi ya bar gurin.
Daren ranar Ilham ko runtsawa bata yi ba ,gaba d’aya abin duniya ya dameta ,daga ta rufe ido shi take gani ,” lallai nasan ban kyauta ba , kuma gashi na kasa samun nutsuwa! tabbas dole in bashi hak’uri but how? Gaskiya bazan iya giving up so easily haka ba !!!! Ilham kenan !! Ni kaina Jeeddah ja’o na ce tana da ji da kai !!!
Karfe sha d’aya na safe Rasheed ya shigo office d’in lieutenant kawai sukayi ido hud’u da ita ,ya kauda kansa gamida mik’a wasu file’s ma lieutenant d’in yace ” ina buk’atar reports within the next five hours ,ni zanje d’auko Imtihaal daga airport, kuma pls in har akwai wani sudden abu ka sanar da ni lieutenant ya Sara mishi yace ” yes sir!!” Rasheed ya juya ya fice ,bai ko sake kallon inda take ba.
Tafe take tana dariya rigar jikinta mai dogon hannu ne fari sai ta d’aura jacket na khaki a saman tasa wani skirt flattered bak’i ,Kyakkyawar gaske amma babu gyara ,don ita Sam a birkice take ,gashin kanta bak’i ta saka wata hula hat itama bak’a shirin de na hauka tana goye da jaka k’atuwa ,ga kuma trolley tana ja,tana hango Rasheed tsaye yana jiranta ,ta fara d’aga masa hannu tun daga nesa ta rugo da gudu ta k’araso inda yake ,ya ja hancin ta yace ” welcome home my precious!! ” abunda yake kiranta da shi kenan ya kama mata kayan suka fice daga airport sai barracks!!
Imtihaal akwai kyau ba na wasa ba a haske kuwa ta fi Ilham sosai ,saidai babu tsari a mode of dressing, yadda taga dama haka take shirinta kuma ga zafin zuciya musamman in aka mata dariya akan shigarta , kaf barrack babu wanda ya yi mata farin sani sai Rasheed don duk kusan d’abiun su d’aya ne, duk da ya fita nesa ba kusa ba. Saidai mace ce mai son murmushi ,da kuma bada dariya ,in har kana cikin 6acin rai tazo gunka toh har mantawa zakayi ma, sojojin nan babu wanda kuma baya shakkar ta da kuma 6acin ranta don baza su ga da kyau ba in har hakan ta kasance, in kuma tana tare da Rasheed shi kanshi rigimamme yake zama don tun asali dama rigimammun ne cliq nasu su hud’u ita da Rasheed sai Sadiq sarkin zuciya sai kuma Air force officer wato Al’amin, shi da yake ba a nan yake ba zuwa yake yi in ya samu tym…….
Hirar su suke ta shek’a wa har suka iso gida ,ita y’ar gidan major ne kuma abokanai ne da Abba wato General, itama soja ce amma ta fannin bincike,Babu kuma wani wanda ya kaita k’warewa a Wannan fannin ,saboda haka ne ma ta fita Malaysia don karanta psychology and was successful! Babu abunda ya fi soyuwa a zuciyar ta irin Rasheed duk da shi kawai ya d’auke tane a matsayin best friend nashi wanda babu wanda ya kaita kusanci da shi ,ko su Sadiq ma basu san wani halin Rasheed yadda ta sani ba.
Bayan ta huta, karfe hud’u na yamma ta fito zata gurin Rasheed ,ta saka wani over size Jean’s trouser blue, da wata rigarta shirt light blue takalmin k’afarta sneekers ne blue da fari, ta kafa irin hular nan me kama da na sanyi , hannun ta rik’e da wayarta ta saka dayan kuma a aljihun ta babu abunda ya dameta tafiyarta kawai take yi, horn d’in motar da taji a bayanta yasa ta juya ,Rasheed ne cikin motar Army ,ya ja birki ya tsaya kusa da ita yana murmushi ,yace ” hop in!! ” ma’ana ta shigo motar , shiganta ke da wuya ,sai ga Ilham ta iso ,ta d’an Kwankwasa glass d’in motar ,bai wani damu ba ya sauk’ar don jin da wacce ta zo yau kuma. “Nazo ne in baka hakuri captain, I know I was wrong since from d very beginning, pls accept my apology” murmushi kawai Rasheed yayi ya d’aga glass d’in motar shi yayi gaba ya barta nan tsaye jiki a sanyaye. “Bro Wai waye wancan d’in” tambayar da Imtihaal ta fara jefan shi da shi kenan, yace ” don’t mind her precious! Bata da tarbiyya ne kwata kwata ,I want her to learn some morales suna tafiya yana bata labarin abunda ya faru tsakanin shi da Ilham. Ta d’an yi murmushi tace ” forget that nutty girl and let’s have some ice cream yayi parking suka tsaya shan ice cream har kusan magariba sannan suka dawo,ya ajiye Imtihaal a k’ofar su sannan ya koma gida ,yana zuwa bakin gate nasu abun da ya gani ya bashi mamaki da kuma haushi……