Bismillahi
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,Abbas alh mustapha hamza shine cikakken sunansa
Ma haifinsa alh mustapha da ne wjn Mlm hamza Mlm hamza haifafen garin bauchi ne
Yy karatun almajiranci sosae ta yadda yagaji wani malaminsu Mlm shehu
,,,,,,Mlm shehu sa nanne ne lkcn da aka kawo hamza karatu makarantarsa ya yaba sosae da hanklin hamza kasancewar mlm shehu baya da yaro namiji Wanda zai gajesa yar'sa daya tilo adunia wato ummu salma
Yarinya CE mai hkr ga tarbiyya ga sanin yakamata ko da ake cewa wani lkc Dan Mlm baya halin Mlm amma ita kam salma tayi halin Mlm
Akwai wata rana salma taje kaiwa mahaifinta Mlm shehu abinci hamza tunda yaganta yaji zcyr Sa ta buga
Itama kuma ta bangarenta hkan ce ta faru
Tun a ranar hnklin hamza ya tashi domin ya fahimci daga kallo daya ne ya afka ....lol..
Haka dai yai ta dakon soyayyar ta itama din hkne a wajanta
Wani lkcn ma sbd ta Ganshi ne take kawowa babanta abinci duk da bata son fita
Ahaka dai hamza yana ta tunanin yadda zaice yana son Ummu salma SBD yar gdn malaminsa CE
Ahaka dai ana cewa abinda babba ya hango yaro koya hau rimi baxai hango ba
Mlm shehu harya fara gano boye boyan da hamza da yar'sa salma tilo sukeyi
Amma tun kafin ya fadawa hamza saida ya zaunar da salma yace mata yanaso ya hadata aure da almajirinsa hamza tanason shi ai kuwa ta miqe da gudu tayi daki tana dariyan farin ciki mamarta tasa albarka kafin yasa aka kira masa hamza yace yanaso ya hadashi aure da yar'sa salma hamza yaji ddi sosai haka Mlm shehu ya zamo uwa da uba wa hamza ka sancewarsa yataso maraya
Haka akasa ranar auren salma da hamza
Masu baqin ciki sunayi masu farin ciki sunayi
Rana bata karya ranar asab@r aka daura auren
Ummu salma Mlm shehu
Tare da hamza nayaya Mlm shehu
Zaman lpy sosae sukeyi gami da qaunar juna
,,,,,,hka dai rayuwa take ta tafia a kwana atashi asaran mai rai
Wata rana Mlm shehu ya hada dukkan almajiransa yace musu ko bayan ransa hamza shine dansa kuma shine magajinsa
Sbd hankalinsa da baiwarsa na ilmi
Bayan Mlm shehu yy wnn jawabin ne baifi da sati 2 b wata ranar laraba yatashi da ciwon cikin gske kafin hamza suyi qqrin kaisa asibity yace ga garinku nn
,,,,,,,Allah sarki rayuwa kullu nafsin zaa,ikatil maut ,,,,,,,,,,,,,allah kasa muyi kyakkyawar kashe Allah yasa mucika da Kalmar shahada ,,,,,
Laah ilaha illallahu Muhammadu rasulillahi sallallahu alayhi wa sallam
,,,,,,,,,,salma tasha kuka sosai harda hamzan ma da mahaifiyar salma amma kuma dole sai hkr daga nn nauyi ya koma kan hamza
Ana hkne salm ta fara laulayin ciki hamza yy farin ciki sosae harda mamanta shi kuma masha Allah makaranta tana qara bunkasa kafin kace me hamza ya shahara shima kamar margayi Mlm shehu Dan yawancin ansanshi agarin Bauchi ayankin kasan gada
Haihuwa Ummu salma tasamu danta namiji karkuso kuga murna wjn hamza ba tare da bata lkc ba kuwa ranar suna hamza ya rada ma dansa sunan Mlm wato shehu anyi suna an watse lpy
Watan jariri mai sunan mlm 2 a dunia shima yace ga garinku hauka ne kawai salma batayi ba daga baya ta hkr ta barwa Allah bayan rasuwan shehu ne taqara samun wani cikin ta haifi namiji shi kam ma tun kafin suna Allah ya karbi abunsa
Hka dai rayuwa ta cigaba da tafia sai da tayi shekara 2 kafin taqara samun ciki amma a tsorace take
Allah cikin ikonsa kuwa ta haifi yan biyu maza murna akasa musu suna Abubakar da Usman
Shekaran su Abubakar 5 ta qara samun ciki ta haifi mace aka Samata sunan Mmn salma wato zainaba suna kiranta da ummi awannan lkcn ne kuma Mlm hamza lkcn da ummi tashiga shekara 3 aka sata a mkrnt nursery skll wata malamarsu dama tasan mahaifin su Abubakar kuma ta jima tana sonshi ahaka dai wata rana su ummi suna wasa kawai ta fado asaman bishiya ta karya kafa malama CE ta kaita aka mata dauri daga nn ta kaita gd kullum saitaje duba ummi da dan lemunta ahannu
Ahaka har suka saba da salma wadda ayanzu yaranta suke kiranta da uwa
Baqaramin tasiri hajara tayi ba acikin zcyr uwa
,,,,,wata rana taxo mata ziyara ranar bb mkrnt
Suna cikin hira sai uwa tace hajara ke baxakiyi aure bane sai tace saina samu miji malami kamar naki shuru nadan lkc uwa tayi kafin tace to Allah yabaki
,,,,rayuwa tana cigaba da tafia kwanansu abubakar 2 basuje mkrnt ba hkan ne yasa hajara tace bari taxi ta duba ko da tazo sai uwa tace mata mamarta CE bb lpy shiyasa hankalin hajara ba karamin tashi yyi b kullum tana gdn mamar salma wato uwa tanayi mata hidima
Bayan sati da hkan itama mama tace ga garinku nan
,,,,,,,,,allah sarki mama tabi Mlm
Allah ya jikan magabatanmu damu baki1
Hajara tayi kuka saika rantse ko mamartace ta rasun ko da uwa tayi mata mgn akan kukan ya iya hk sai tace mata itama batada iyayen tun tana qarama sukayi hadari suka rasu ko fuskansu bata saniba
Bakaramin tausayi tabawa uwa ba
Bayan anyi adduar uku wa mama mutane anwatse uwa taje tasami Mlm
Tace mishi tanaso ya auri malamarsu ummi ta mkrnt kallonta kawai Mlm hamza yakeyi
****************mu hadu a page nagaba ta yadda zamuji shin mlm.hamza xai yarda ya auri hajara ko kuwa
****ta Ku
(Zahra Abdul)
(Momyn ahlan)
Comments
And
Share
[10/25, 2:53 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: 🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
*HALITTA DAGA ALLAH NE*
Na
*Zahrah Abdul*
(Momyn ahlan)
*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
```Thix is ur page my bestie😘kulsum much Luv to u```😘
*Bismillahir rahmani Raheem*
Page0⃣5⃣_0⃣6⃣
,,,,,,,,,,,,,,,,,umma ce ke riqe da uwa wadda sai suma take hnkli umma yakai kololuwan tashi tama rasa me zatayi ga fadila matar abubakar sai kuka take umma tace fadila jeki duba yaya ina yatsaya ko bb Doctor din da xai dubamin itane kam daga shi har baba mlm dinma shuru fadila ta miqe tana kuka tayi hanyar waje
Tana fita wayar ta ya dauki ruri tana dubawa tana SIS RALIYA da kuka tadaga raliya tayi sallama da kyar fadila ta amsa hnklinta ne yaqara tashi tace sis Dan Allah fadamin menene ya jikin uwan dai cikin kuka fadila tace wlh uwa sai suma take kuna inane tace gamu nan munkusan shigo gari nanda awa 1 da rabi insha Allah tace tare da ummi kk tace aa xasu taho da mijinta munyi waya da ita amma xamu rigasu isowa SBD motarsu ce ta lalace a hanya amma angyara suna nn xuwa fadila tace to Allah yakawoku lpy ki gaishe da Yy usman tace to
Tana yanke wayar tasa kuka shi karan kansa usman din daurewa yake yace Dan Allah raliya kukan nn ya isa hka tun akano kk yi ya kikeso nayi da rainane kam dame xanji da tashin hnkln ciwon uwa ko kuma da kukanki uwa adduah take bukata ba kuka ba Dan Allah kibarni naji da Abu daya
Hakika ba qaramin tausayin mijinta tajiba Allah dai ya kaisu bauchi lpy kawai
Bayan fitar fadila haduwa sukayi da baba mlm yace ya jikintan dai cikin kuka tace baba wlh sai suma take umma cema tace naxo na dubaka kai da Yaya
Baba mlm yace ahh abubakar din baixo da likitan bane tace eh suna cikin hka saiga abubakar da sauri fadila tace Yaya INA doctor din yace nima bansan inda yashigaba tundaxu sai kwatance akemin ynx ma wani office xanje dubawa baba mlm yace to kayi sauri bari ninaje naga jikin nata fadila tace Yaya naxo muje kallonta yyi yaga duk ta hangitse yace eh xomuje tace to tabi bayansa baba mlm kuma yyi hanyar dakin da uwa ke kwance sai goge gumi yake kawai daurewa yake SBD bayaso yatashi hnkln yaransa da matansu danyaga duk sun fita hayyacinsu shiyasa shi yake danne nasa
Yasha kwanan da xata sadashi da dakin yace mustapha shida kubra suka hada baki tare sukace baba ya juyo yace ahh harka daukota a mkrnt yace eh to kuxo mukarasa ciki suka ce to
Bayan fitar fadila dakin uwa ta farfado taga ido ta kalli Umma tace umman yara wani ddi ne yakamata tace naam uwanmu baki1 uwa tasaki murmushi abinda umma takasa ganewa shine yadda uwa ta tashi garau kamar ba itabace ta birkice daxu2 nn sai kuma taga fuskanta fayau dashi Umma ta kamo hannunta tariqe gamm tace dama nasan xaki tashi baxaki mutu kibarni ba uwa ta kuma yin murmushi akaro na 2 Dan batace komai ba Umma CE keta sambatunta
Uwa ta nisa tace umman yara nasan harga Allah ko mutuwa nayi banida fargaba akanki
Abinda xan roqeki shine Dan Allah idan har axaman da mukayi dake nataba bata miki kiyi hkr kiyafemin kinsan Dan Adam ajizine sosae hnkl Umma yatashi Dan tama kasa mgn sai jikinta daketa rawa kamar mazari tace hba uwa ni Dan Allah kidaina min irin wnn mgn hb nafarajin ddi kintashi amma shine......shine...shine.......kawai ta kasa karasa mgn SBD kukan daya kufce mata uwa ta rungumeta tace banji amsar abinda nk so naji daga wajanki ba sai da Umma ta kai kusan minti5
Kafin tace nice yakamata ace nayi wnn mgnr
Ke tadabance uwa kk Sa mijinki ya aureni sannan ban haihu da wuri ba kk dauki yar'mace daya tilo kk bani aurenta yaxo nice kangaba wajan hidima bikinsu Yaya yaxo nice nayi musu hidima duk kin sakarmin ni kuwa mai xakimin uwa Dan Allah nima idan na miki wani laifi kiyafe min abisa rashin sani uwa tayi murmushi tace baki tabamin komai ba umman yara idan kinmin wlh na yace dunia wa lahira tace nifa tace uwa ke alkhairice arayuwata bakimin komaiba idan akwai nayafe ballema babu uwa tayi murmushi tace ngd kanwata INA su usman sunkaraso kuwa Umma tace aa amma waisu usman sunkusan isowa ummice ba motarsu ta lalace ahanya saida akayi musu gyara tace Allah sarki ummina da usman da raliya Allah yaso saduwarmu
Kallonta Umma tayi tace kamarya Allah yaso saduwarku bata CE komai ba tayi murmushi tace xansha tea Umma ta miqe da niyyar xuba mata tea din saisu bba mlm sukayi sallama suka shigo shidasu mustapha da kubra amsawa sukayi harda uwa cikin farin ciki kubra da mustapha suka qarasa wjn uwa suna mata sannu tace yww yarana Allah ya muku albarka sukace ameen kubra ta kwanta ajikin uwa Umma tana juyowa taganta ta rufeta da fada wai ita meyasa batada kan gado ne bataga batada lpy bane kubra tace yi hkr Umma
Uwa tace aaa fa bar yarinya taji dumin jikin uwanta anjima INA ma xataganni mustapha yace kamar ya uwa anjima baxata ganniki murmushi tayi tace bkm yaron kirki Allah ya muku albarka Umma tace to ai saiku tashi kufita waje ko kubra tasa kai tafice abunta mustapha ma yabi bayanta uwa ta juya kallonta kan mlm tace mlm Dan Allah kayafemin duk abinda namaka yace bakimin komaiba Ummu salma idanma kinyi wlh nayafe miki nima ki yafemin tace bkm mijina
Bayan tagama shan tea din nn tace mlm xo xan kwanta ajikinka batare dayace komaiba yaxo ya xauna ta kalli umma sai faman share hawaye takeyi tace umman yara xona kama hannunki kukan Umma ne yafito da karfi Umma tace Allah yabaki lpy uwa tayi murmushi tace Allah yaso saduwarmu da hka tayi shuru can anjima tayi miqa tayi salati ta koma ta kwanta talafe ajikin mlm tariqe hannun Umma sosae
Ana hka saiga abubakar da fadila sunshigo da doctor
Ya kallesu yace ya mai jikin Umma ce tace da sauki tasha tea tasamu bacci ma doctor yace bari na dubata nagani yaxo ya tantabata yaji shuru ya auna yaji bb numfashi ko kadan ajikinta yace saidai fa kuyi hkr amma bb ita Dan tacika wani qara fadila tasaki ta sulale kasa asume abubakar yana tsaye yarada mai xaiyi ihun da fadila tasaki ne yasa hnklnsu mustapha da kubra tashi da gudu suna xuwa dakin sukayi kacibis da fadila a shinfide abakin kofa. Ga abubakar yana tsaye jikinsa sai bari yakeyi ga baba mlm na share hawaye Umma CE keta sambatu tana cewa wlh karyanka karyanka nave lkt bata mutu ba ynx muke hira da ita bacci takeyi lkt yace kiyi hkr hajia Umma tasaki qara tayi kasa sumammiya hkan ne yasa su kubra suka fahimci abinda ke faruwa kubra tace....... wayyoooooooo........Allah ....u...u...uw...u..uwa...t...taa....tayi kasa itama. Mlm hamza kasa motsi yyi shida abubakar da mustapha Sunrasa gane awace dunia suke lkt ne yafita yaje kiransu nurse's yace suxo su dauki matan abasu taimakon gaggawa da kyar mlm hamza ya iya Jan kafarsa ta tayi masa nauyi yaxo ya dafa yaran nasa yana bubbugasu ahnkl tukunna abubakar yasamu damar hawaye amma banda mustapha da yakeji kamar shima baya duniyar ne
Mlm hamza yace ka matso da motarka asa gawarta aje gd ayi mata sutura da kuka yace to ya juya yafita lkt yaxo aka bada gawar uwa
Suka wuce gd da ita suna hanyar tafia baba mlm ya kira usman yace muhadu agd yana fadi ya tsinke wayar ya kira mansur Mijin ummi yace muhadu agd nanma yakashe kiran
Bayan sun iso ne mutane aka taro sosae kamar miye Dan bb wadda baisan uwaba yar gdan margayi mlm shehu sannan matar mlm hamza
Wasu makotansu Umma sukayiwa uwa wanka suka mata sutura kafin afito da ita. Saiga motar usman ta danno kai tundaga kan layi suka hango jamaa salati kawai yake nanatawa afili da kuma ransa kuka raliya tasa tana salati
Suna shigowa aka basu hanya ai ko parking bai karasa ba yafito amotan yaga abubakar ya sunkuyar da kai kasa yana hawaye usman yafara hawaye shima abubakar ya rungumesa
Ita kuma raliya gdn tashige tana kuka tana shiga taga gawar uwa kwance amakaran (gadon sarautan da kowa sai andaukesa aciki 😭allah yasa my wanye lpy)
Kan makaran tayi tana kallo. Tace ba uwa bace wnn ko dan Allah Ku fadamin tunowa tayi lkcn daxasu koma kano take mata nasiha da albarkan data samata Mayan wjn ne sukace kiyi hkr ai itama saita xube kasa assume anxo andauki gawar uwa anfito da ita saiga su ummi da mijinta sun iso ummi gani tayi anyi sama da gawar mahaifiyarta ta fito da gudu amotan tana kiran uwa usman ne yakamata yyi cikin gd da ita sannan suka fito suka kama hanyar maqabarta
,,,,,,,,,,,,,,a asibity
Bayan fitarsu mlm.da uw
Umma tafarka d sambatu
Kubra ma tana tashi da sunan uwa tafara ita da fadila
Haka fadila taje ta tara musu taxi suka dauki hanyar gd
Sun iso sunsamu har antafi da uwa suka shiga gd
Ummi tana xaune ta takure gefe 1 ga raliya agefe itama ko mgn bata iyayi sai shigowa gaisuwa ake musu amma ba baka sai kunne
Kubra CE tafara shigo parlor din tana hango ummi tasaki kuka race anty ummi
Ummi ta miqe da gudu taxo. Ta rungume kubra suna kuka lallashinsu ake amma ina tashin hnklisu ma ynx itace umma da bata iya gane kowa saidai sambatu wadda ita karan kanta batasan tanayinsu ba
Allah sarki uwa alherinki yabiki hka akayi xaman makoki aka gama
Amma har ynx umma bata cikin hayyacinta kwana biyu ma kam abun yyi tsanani Dan aman jini take
Su abubakar suka kaita asibity lkt yace ta kamu da ciwon zcy kuma ga hawan jini duk itama xasu iya rasata akowani lkc
Tashin hnkln da wannan family suka Shiga baxai fadu ba awannan rana
--------------------- tofa kubiyoni muji mai xai faru taku har kullum ,,,,,,,,,,
Zahra Abdul
(Momyn ahlan)
Comments
And
. share
Fan's Dan Allah INA barar adduarku serious bani da lpy wlhy😰😰
[10/25, 2:53 PM] Rasheedat❤❤❤❤❤❤❤: 🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
*HALITTA DAGA ALLAH NE*
Na
*Zahra Abdul*
(Momyn ahlan)
🌈KAINUWA WRITERS✍🏻ASSOCIATON🤝🏻
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
```Dedicated to my fadeelarh😘💋
And rasheedah ya"Allah help me🙏🏼```
*Bismillahi rahmani rahim*
Page0⃣7⃣_0⃣8⃣
,,,,,,,,,,,,,,,,wasa wasa saida umma ta kwashi wata2 hospital sosae su abubakar suke bata kulawa kamar ransu suna qaunar suga umma ta warke amma kuma lkt yace a ckn zcyr ta akwai inda ya bule da wuya ta rayu ba karamin tashin hnkl suka shigaba umma tanada wata 2 da sati 2 a asbt tace masu abubakar su mayar da ita gd bbu yadda suka iya domin tace ko ba abata sallama ba ita kam tfy xatai abunta hka suka dawo da ita gd ta tarasu a parlor xatai mgn amma takasa saita sa kuka ummi CE dake xaune agefe itama tasa kukan SBD anyi2 ta bi mijinta su koma gd tace ita bb inda xataje sai umma tasami lpy
Haba umma Dan Allah umma kicecemu kidawo nml plss kukan ne yaci karfinta ta miqe tabar parlorn kubra ma tabi bayanta tana kuka fadila itama raunin zcy ne da ita hka itama ta tashi tana kuka raliya CE tayi karfin halin fadin Allah yabaki lpy ummanmu tayi daki da gudu itama da hka2 suka watse dukkansu har mazan akabar baba da umma shiya kamata ya kaita daki ya zauna abakin gado yafara yi mata nasiha kamar hka
Haba hajara menene hka Dan Allah kiji tausayin yaran nn kiduba kiga yadda suka rame duk sunfita hayyacinsu kwata2 basa cin abinci sainayi da gske Ummu salma dai Allah yafimu sonta domin shiya halicceta kuma ai dama wnn duniyar kowa xai barta bbu Wanda yaxo zama na dindindin salma adduah take bukata ba komai ba ynx awjn mu dan Allah kisawa zcyrki salama sannan kiji tausayin yaran nn dabasu da kwanciyar hnlk kwata2 atare dasu
Nauyayyar ajiyar zcy umma ta sauke ta bude bakinta da kyar tanason yin mgn domin hawan jinin ya bugeta abaki bakinta yadan koma gefe tace Dan Allah Mlm ka yafemin yace bakimin komai ba hajara idan ma akwai na yafe miki da kyar tace ngd ka kiramin yarana. Yace to yadaga waya ya kira abubakar yace ka kira yan uwanka kuxo ummanku tana kiranku da to abubakar ya amsa ya kalli fadila dake gefensa tana sharban kwalla yace Dan Allah my fadila kukan ya Isa hka adduah xamu dinga yi kinji kuma lkt yace kidaina sa damuwa aranki Dan xai iya taba mn babynmu tace to my yaya insha Allah yace yww to tashi muje ummanmu tana kira tace to
Bayan tashin ummi daga parlor tana shiga daki ta kira mansur mijinta ckn kuka hnkln mansur ne yatashi danshi a zatonsa xata cemasa umma ta rasune ckn tashin hnkl ya jero mata tmbyoyi
Subhanallahi!!my luv lpy kuwa?menene?meya faru??meyasa kk kuka?meya samu umma?ya jikin Umman dai??
Ckn kuka tace my anya umma xata tashi kuw.....bata karasaba ya katseta haba my wnn wace irin mgn kk yi kam cuta ai ba mutuwa bace mu dinga mata adduah insha Allah xataji sauki kinji tace to nan yadinga kwantar mata da hnkl kafin ya katse wayar tagumi ya zabga yana tunanin abinda lkt ya fada musu ranan cewa zasu iya rasata kowani lkc inna lillahi wainna ilayhirrajiun abinda yaketa nanatawa kenn afili da kuma zcy
Bayan mijinta ya ajiye wayar ne saiga kubra tashigo dakin da kuka ummi ta miqa mata hannu taxo ta kwantar da ita kan cinyarta tana lallashinta a hnkl saiga kiran Yy usman ya shigo wayarta tana dauka yace ummace take kiranmu yana fadi ya kashe wayar
Ta kalli kubra dake kwance tace knwt tashi muje ba musu ta miqe sunfito kenn suka hadu da mustapha idonsa duk sun canza xuwa jaa ummi ta kallesa tace qanina da kyar ya amsa da antyna tashafi gefen fuskansa alaman rarrashi murmushin karfin hali yyi ta kama hannunsa Dana kubra sukayi hanyar dakin umma
Suka shiga sukaga duk su Yaya sunrigasu shigowa can gefen kujeran dake dakin mustapha yaje ya xauna ya rakube
Umma ce ta kallesu tace Allah ya muku albarka yarana Allah yasa wata rana duniya tayi alfahari daku Ku xama manya mutane kowa yasoku sukace ameen
Wani abun mmk suka kasa ganewa umma sai hira takeyi fadila CE tace umma mai xakici naje na girka miki raliya tace umma kodai nayi miki alkubus ne kubra tace umma zakici waina(masar bauchi kenn😋hahaha lol!naga su sis surry &sis khadija journalist & Ummu nasma ana hadiye miyau to kwalelenku)
Ummu shuru tayi tana kallonsu tausayinsu ne yakamata ganin yadda suke ta murna ummi tace umma ki fadi mgn murmushi tayi tace komai ma xanci idan yarana suka girka amma kubrata karkiyi masa ynx kinga yamma tayi hade rai kubra tayi tace umma baxakici bane tace ahh xanci mn mamana ta miqe rana murmushi ta kalli ummi tace. Anty ummi tashi muje tace to knwt muje fadila da raliya suma dai tashin sukayi atare suna masu farin ciki da jin ddin ganin umma yau ahaka baba yace inyee kaga Umman yara lallai kam yau xamuci girki sosae dry sukayi dukansu batare da sunce komai ba suka kama hanyar kitchen
Girke2 suka shigayi dukkansu basu suka gama ba saida akayi kiran sallan magriba
Sallah suka farayi kafin suka kwashi abinda suka girka abinci kala2 sukayi kamar xasu gdn biki sukayi dakin umma tana zaune abakin gado tana adduah da sallama suka shigo dakin suka xauna agefe suna jira tagama lazimi Dan mazan basu dawo daga masallaci ba
Bayan ta idarne ta kallesu tace sannunku yaran albarka suka amsa da sannu ummanmu sallama mazan sukayi suka shigo dakin Yy usman yace kkkkkkkkkk wnn kamshin girki hka dry sukayi su duka umma tace to akawo Babban plate Dan yau atare xamuci abincin nn kuma saimun cinyeshi duka xare ido raliya tayi tace umma duka dai tace ehmn ya'ta duka xamu cinyeshi dry baba Mlm yasa yace tab lallai kam
Umma ce ta kalli mustapha wanda tun farkon shigowarshi dakin bayyi mgn b kuma ya xauna ya takure gefe daya ummi CE ta lura da hkan ta tashi taje ta xauna kusa dashi ta riqo hannunsa kawai yatashi yafita adakin ba umma ba kowa na dakin saida yabi mustapha da kallo ummice tabi bayansa
Yana fita yasa kuka ummi ta rungumosa tana cewa hba qanina miye hka kuma Dan Allah kana gani yau hnklnmu ya kwanta muna dry amma kanaso katayar mn d hnkl sabon mu da murmushi agdn tun yaushe Dan Allah ya Isa hka kaji
Ckn sanyin murya da kuka yace Anty ummi wlh idan naga umma sai inji gabana yana faduwa ga mugun bugun da zcyta takemin
Tace insha Allah bbu bkm ka kwantar da hnkln ka kaji yyi murmushi yace to antyna kuma sirkata ta kallesa tace bangane sirkanka ba yace insha Allah xaki haifawa da'na mata riqe baki ummi tayi tace yau naji rashin kunya wajan wnn yaron yace nifa d gsk nk kwanan nn xanyi aure baxan kai shekarun dasu Yaya suka kai basuyi aureb wlh baki bude ummi ke kallon qanin nata tace Allah ya shiryamin kai musty muje takama hannunsa yana dry kasa2 yace ameen Anty surka
Sallama sukayi adaki duk aka juyo ana kallonsu kusa da umma yaje yaxauna tashefi kansa tayi murmushi batare da tace masa komai ba hka su xauna ckn jin ddi suka hadu haba dayansu sukaci abincin kowani kala saida sukaci wani abun umma daurewa kawai take yi tanaci amma badin taso ba kuma yadda taga sunacin abincin ne takarajin tausayinsu hka sukaci komai tare suna gamawa ana kiran sallan isha,i, dan hka suka tashi suka kama hanyar xuwa suyi sallah mazan ma masallaci sukaje
Bayan sun idarne suka dawo suka baje tabarman hira wnn yace Umma kaxa yyi kaxa waccen ma tace Umma kaxa tayi kaxa Umma tana sauraronsu tana murmushi da nisa tace gsky abncin yau din nnn yyi ddi ni kadaice kawai na iya fadi amma su baba Mlm da Yy abubakar da Yy Usman da mustph ksa mgn sukayi dry sosae matan suka Sa baba Mlm yace lallai ma Umman yara wato hka ne abinko nan dai sukadinga hira basubar dakin Umma ba sai kusan karfe 1 na dare nanma abubakar ne shida Usman yace yakamata subarta da huta suka yimata saida safe suka tafi ransu fesss
Da asuba bayan ta idar da sallah ne taji wani rin sanyi yakamata ahaka su Usman da matan sukaxo suka gaisheta cikin dauriya ta amsa tana murmushin karfin hali bayan sunfita ne ta kalli Mlm tace sanyi nakeji rufa mata bargo yashigayi amma saitace baiyiba akara sun dauki awa daya ahaka kafin daga baya wani irin xafi yarufeta wulli tashigayi da bargunan da aka rufa mata sai da ta yayesu duka xufa kawai takeyi hnkl maxa Mlm hamza ba qaramin tashi yyi ba yama rasa maixai mata kawai ya debo ruwa ya hau shafa mata can anjima ta sauke ajiyar azcy mai karfin gsk a hnkl ta fara salati Mlm hamza yana rungume da ita a qirjinsa jin tayi shuru ne kuma jikinta kamar ya sake bbu alamun motsi hkan ne yasa yadagota a hnkl kiran sunanta yakeyi hajar!hajara!hajara!
Innalillahi wainna ilayhirajiun !!!abinda ya iya fadi kenn kawai yafara hawaye ya zauna bai kira kowa ba sannan bai tashi ba
9 na safe fadila ta tashi da Sauri Yaya yace ke kuma wnn saurinfa tace xanje na dubo Umma ne naga ynx har 9 tayi nasamu nayi mata girki tasha magani yace to yar albarka ta xunbula babbar hijab dinta SBD kayan bacci ne ajikinta tayi hanyar dakin Umma tsayawa tayi tana kwankwasawa taji shuru tayi sallama nanma shuru taxo xata juyo tace may be bacci take saiga raliya ita dauke da kayan tea ahanunta tace ahh sis gud mrnng
Mrnng sis tace Umman bata tashi bane fadila tace ai nima tmbyar da xan miki kenn danna ganki dasu kayan tea tace aa kawai na hadone tafara shan mgni kwankwasa kofar raliya tayi amma shuru fadila tace sis wlh gabana faduwa yake shawara suka yanke kawai su bude kofar suna budewa turus suka tsaya ganin dakin awargaje daga ido suka sakeyi ganin baba Mlm sukayi rungume da Umma yana kuka ga Umma kwance ajikinsa bbu numfashi qara suka saka mai karfin gsk wadda ba yan gdn bama har makotansu xasu iyaji sulalewa kasa fadila tayi jini yafara kwarara ta kasanta hkan ne yaja hnkln kubra da ummi Wanda fitowarsu kenn daga daki sukaji ihu da mugun gudu suka karaso da fadila sukafarayin karo sannan suka shige dakin jikin ummi da bari itada kubra sunma rasa mai xasuyi kukan ma yaqi xuwa sai sumar tsaye kawai mustapha ne yashigo dakin yagansu kuka yasa yana salati yana kiran sunan Umma
Saiga Usman shida abubakar ganin fadila yyi kwance akasa ga mini yanata ambaliya akasanta yana daga ido ga Umma ajikin baba bbu rai atare da ita da kyar yafita yaje ya gayawa liman sannan liman yafadawa matarsa kafin kace mai saiga mutane anyi cincirundo a kofar gdn mlm hamza
Da kyar aka karbi gawan Umma ahannun mlm wasu mata ne suka kai fadila asibity sannan akajasu ummi da kubra raliya aka kaisu daki aka kullesu bayan angama shirya Umma ne maza sunshigo daukarta ummi tanajin hka itada kubra suka miqe suka fara dukan kofa suna kuka
Amma tausayi yahana jamaa su bude musu kofa saida akadawo daga maqbarta sannan ana budewa kubra ta kwasa da gudu tana fadin wayyo Allah Umma innalillahi wainna alayhirrajiun Umma dan Allah kidawo bamugama jimanin rashin uwa ba kema kk tafi dan Allah Umma kidawo Usman ne ya rungumeta sosae yaki sakinta dan hangar waje takesonbi kuma ga maza birjim awajan itama ummi kuka take tana kiran sunan Umma da uwa
.!!!Allah sarki rayuwa!!!
!!Allah sarki Umma anbi uwa Allah ya jikanmu !!!
Hka akayi xaman makoki kowa yana tofa albrkcin na Cin tuwonsa tsakanin xaman uwa da Umma
Fadila tana asbt ana bata taimakon gaggawa dan duk xaman makokin da akayi bbu ita ana ta qqr aga yaron cikinta baifita ba kuma alhamdulillah yana nn din amma saidai ta wahala ba kadan ba
Sa satin Umma da rasuwa kuma anti adduah 7 Mlm hamza ya tarasu yamusu nasiha sosae yace kuxama uwa da uban kanku abubakar kaida Usman kuba yara bane sannan kema ummi hka inaso yau ki hada kayanki kibi mjinki ya kalle mansur yace katafi da matarka tau cikin ladabi ya amsa da to
Badon ummi taso ba tace to baba ta miqe tana hawaye kubra da mustapha sukabi bayanta Mlm yakara kallon Usman yace kaima ka koma wajan kasuwancin ka to shima yace daga nan y kalli abubakar yace ya matarka da jikin da sauki ya amsa sannan za ama sallema anjima yace to Allah kaimu Allah kuma yaqara lpy suka amsa da ameee
Ummi tana shiga daki taqara sakin kuka gani take kamar uwa da Umma basu mutuba amma gashi ya tabbata
Gsky kwashe kayanta tayi taja akwatinta zatafita kenn saiga su kubra sunshigo suma suna hawaye rungumesu tayi duka sukayi kukansu mai isarsu kafin tasakesu ta kalesu tace qanina knwt Allah yaqara mn hkr taja akwatinta tafita tana cigaba da kuka taje gaban mahaifinta tace baba xamu wuce kamar xayyi kuka yace Allah ya miki albarka ummina sai hkr kinji Allah ya kaddara saduwarmu tace ameen baba dai2 abubakar yadawo da fadila sai kuka take sallama suka musu ta juyo tace Allah ya saukeki lpy matar Yaya dan Allah kidaina damuwa SBD lpyr Dana baby tace to Anty ummi insha Allah su Raliya suka fito. Musu sikayi sallama suka kama hanyar kano
Abubakar ne yakwantar da matarsa yabata mgni yadinga rarrashinta har bacci ya dauketa sannan yafita yaje yasamu kubra daketa faman rusan kuka kaman ranta xaifita dan sai ynx taji gdn yamata tsit kamar ba kowa mustap ya rarrasheta amma taqi tayi shuru harshima yafara kuka yafita yabarta
Da sauri abubakar yakaraso yace ya salam autarmu kukan ya Isa hka dan Allah karya sakaki ciwo kwantawa tayi ajikinsa tace big Yaya wlh baxan iya zama agidan nn ba
Ba uwa ba Umma
Inna lillah yaqara sautin kuka yacs to naji ynx kiyi shuru can tmbyeki wani Abu bamusu tayi shurun ya hade rai yace gayamin tsakaninki da Allah kinason uwa da Umma ta daga masa kai alamun eh qara daure fuska yyi yace amsa xaki bani tace inasonsu big Yaya yaceto daga rana mai kamar ta yau karki sake musu kuka
Kina fa da ilmi kinsan azaban da akeyiwa mamacin idan anamasa kuka kuma shima yafison adduah dan HK mudage da adduah kinji autarmu tace eh jikinta ne yyi sanyi sosae
Shuru tayi kafin tace yayanmu baxan sake kuka ba amma baxan iya zama agdn nn yace eh kwanan nn xakibar gdn dama abokina ya dameni akan batun kaninsa rude fuska tayi dantasan mgnr yyi murmushi yasakai yafice adakin
Dakin mustapha yaje shima yadinga lallashinsa gamida yimasa nasiha sosae kuma yashiga jikinsa yyi masa alkawari akan cewa ma gobe xai koma ya qarasa krtns murmushi yyi yace Allah yasa albrk mustapha yace ameen big Yaya
Abubakar yanafita dakin uwa yawuce yashiga yasaka key ya kwanta agadonta sai alkcn yasaki kukansa kuka yakeyi sosae da iya karfinsa bbu kuma wadda xaijisa SBD ya danne. Bakinsa pillow
Yanayi yana adduah
_________________________
Hka dae rayuwa ta cigaba da tafia sosae Mlm hamza yake kwantarwa da yaransa hnkl tare xai zauna suci abinci suyi wasa da dry fadila tana samun kulawa sosae wjn mijinta da kuka qannansa kubra da mustapha
Kullum sai sunyi waya da yan' kano
Amma abinda su abubakar basu Sani ba shine tun bayan rasuwar Umma baba mlm yake fama da ciwo yaki ya gayamusu SBD yanaso hnlknsu ya kwanta tukunna
Ynx kimanin watan Umma 6 da rasuwa uwa kuma watanta 9 tsakaninsu wata 3
Fadila tashiga watanta haihuwa yau ko gobe
Baba Mlm kuma shima yau yatashi sai Aman jini yake amma tana dakinsa bbu wanda yasani
Angara mgnr auran kubra amma baba yace komai abubakar yyi shine uba
Yau safiyar alhamis fadila tatashi da ciwon baya da Mara da sauri abubakar ya dauketa ya kaita asbt akace masa haihuwa ne
Kiran kubra yyi tana skll yace mata gasu a asbt fadila xata haihu kubra murna take tace wani asbtn ne yace mata RIMI HOSPITAL tace to gani nn xuwa bari naje gd na dauko kayan baby yace to ya katse wayar
Ta koma gdn kenn tashiga dakin baba domin ta fada masa kawai taci karo da..........
```Idan nakarajin saukin
jikina zan kuma yin wani typing din anjima```