Naseer da Noor na zaune na hira, "Noor" ya kira sunanta da sanyin murya, Ta amsa cikin lallausar muryata "Na'am", Ya d'an yi jim kad'an sannan Yace "Idan Alhaji ya sake ki, Ina zaki? Ko kina da wanda zaki aura?".
Ta d'ago ta kalleshi da mamaki me zai sa ya mata wannan tambayar?, Ya d'an yi murmushi Yace "kina mamakin tambayar koh, but ba abun mamaki bane dan hka daure ki bani amsa", Ita dai har yanxu mamakin tambyar take tace "Gidanmu zani, nafi son na koma gida duk wahalar da zan sha, akan na cigaba da zama a matsayin matar Alhaji", "Yanzu ke ba wanda kike so?, wanda kike ganin inda Alhaji ya sake ki zaki aura".
Noor ta girgiza kai tace "Babu"
Yayi ajiyar zuciya Yace "madallah"
"But me yasa kamun tambayoyin nan?, Alhaji yace zai sake ni ne?"
Yayi murmushi yace "nan ba da dad'ewa ba, zaki ji dalilina", Ya mik'e "ni zan tafi"
"Allah ya kai ka lafiya, ina gaida su Ummi"
"Ameen, Zasu ji".
Naseer ya samu Alhaji kan maganar Noor, Bayan sun gaisa, Naseer ya d'an sadda kai, Yana kame-kame ya rasa ta ina zai fara mishi magana,
Alhaji yace "Ya dai Naseer, akwai wani abu ne?"
Ya sosa k'eya ba tare da ya d'ago kai ba Yace Dan Allah Daddy( haka yake kiranshi kamar yadda naji Imran na cewa) ina so ka fahimceni, wlh ba da wata manufa nazo ba sai manufar alkhairi.
Alhaji yace "Ina jinka Naseer, kar kaji shakkun komai ka fad'a mun"
Ya d'an yi shiru sannan yace "Akan Noor ne, Dan Allah Daddy ka dubi girman ka tausaya ma Noor ka saketa"
Alhaji yace "Naseer kazo da magana mai nauyi, bazan iya sakin Noor ba"
"Saboda me Daddy? Aurenka da ita bashi da amfani, dashi da babu duk d'aya, me zai sa bazaka saketa ba, ka huta kowa ma ya huta" Kafin Alhaji yayi wata magana, Hajiya ta banko k'ofa ta shigo
Ta kalli Naseer tace "Ashe kana nan"
Ya duk'a ya gaisheta , Ta amsa, Ta juya kan Alhaji "Me kuke tattaunawa?".
Alhaji yayi ajiyar zuciya yace "hmm! Rok'ona yake na saki Noor", Hajiya ta kalleshi a yatsine tace "toh kai me ye naka a ciki? Kaji yaro da kilibibi, ba za'a saketa d'in ba"
Naseer ganin indai bai fad'i dalilinshi ba zai iya rasa Noor, Yasa yace
"Sonta nake,ina so na aureta, Plxx mum ku tausaya mun ina matuk'ar son Noor, tunda Alhaji ba sonta yake ba ya saketa"
Hajiya tayi shiru tana kallonshi da mamaki, Murmushi tayi tace "Alhaji mu shiga daga ciki"
"Wannan wata hanya ce Allah ya kawo mana ta rabuwa da Noor cikin sauk'i"
"Ban gane ba?" Alhaji ya tambaya
"Kaga tsoronka shine kada ka saki Noor ta koma gida, zamu cewa Naseer idan ya aureta yayi nisa da ita, mahaifinta ba damuwa yayi da ita ba, baya ma tambayarka ina take? So kaga ko ka saketa, Naseer ya aureta bazai tab'a sani ba", Alhaji ya girgixa kai yace "Kin kawo shawara mai kyau, Yanzu sakinta zanyi?"
"Eh sakinta zakayi yanxu kuwa, mu huta da jaraba,annoba tunda tazo gidan nan bamu huta ba, sai yau Allah ya kawo mana hanyar rabuwa da ita".
Biro da takarda ta d'auko ta mik'awa Alhaji, Ya rubuta *Ni Alhaji Mamman na saki Noor saki uku*, Yana gama rubutawa ya mik'a ma Hajiya, ta karb'a tayi dariya zuciyarta fal da farin ciki, shima Alhaji ji yake kamar an cire mishi k'aya, Hajiya ta fito Alhaji ya biyo bayanta.
Naseer na zaune cike da zullumi yayi tagumi,
Hajiya ta kira sunanshi "Naseer", Da sauri ya zabura "Na'am"
"Mun tattauna ni da Alhaji, munga sakinta shine mafi alkhairi, amma muna so idan ka aureta kayi nisa da ita, idan da hali ku bar garin nan"
Naseer Yace "dama ba garin nan zamu zauna ba", Hajiya tace "Yawwa, madallah Ga takardar ta", Ta mik'a mishi,
Yasa hannu biyu ya karb'a cike da farin ciki, Zuciyarshi kamar an zuba k'ank'ara dan farin ciki, Yace "Nagode sosai, Allah ya saka muku da alkhairi"
Hajiya tace "Ameen, mune da godiya Naseer".
D'akin Noor ya nufa kai tsaye tunda yake bai tab'a shiga ba sai yau, Mamaki sosai ya kamata ta mik'e zaune tace "Lafiya Yayanmu?", Bakinshi yak'i rufowa sai washe 32 teeths yake ,Ya mik'a mata takarda, Sujada tayi anan tana godewa Allah da ta karanta takardar, Murna ta kamata, Sai kuma ta fara hawaye da tuna wahalar da zata koma, duk sonta da makaranta dole ta barta
Naseer ya duk'a gabanta a rud'e Yace "Subhanallahi! Kukan me kike Auntynmu? Ko baki ji dad'i da ya sake ki ba?".
Ta girgiza kai tace "nafi kowa farin cikin sakina da yayi, ina tunanin rayuwar da zan koma ne"
"Share hawayenki Noor, kinyi bankwana da Wahala har abada, ba zaki koma gidanku ba"
"Idan ban koma gidanmu ba, Ina zani Yayanmu?"
"Kalli cikin idona Noor, Me kika gani?", Tayi shiru dan ita bata ga komai ba,
"Ba abunda ke ciki sai tsantar sonki Noor, ina sonki ina k'aunarki zan aureki Noor, zan baki duk wata kulawa da farin ciki, plx ki amince dani a matsayin miji gareki", Runtse idonta tayi tana hawaye, Kasa yarda tayi da abunda kunnuwanta ke jiye mata, Naseer ke cewa zai aureta tabbas idan ta aure shi ta more, ta gama sa'ar miji sai dai kash Naseer ba sa'an aurenta bane.
Tace "Yayanmu kafi k'arfina, Ni ba sa'ar aurenka bace"
"Kar in k'ara ji kince haka Noor, Ina sonki kuma zan aureki na rik'e ki amana, tashi ki had'a kayanki, zanje na dawo na d'auke ki, gidanmu zaki koma kafin bikinmu".
Noor ta had'a kayanta komai da komai, Tayi ma su Hajiya sallama, Hajiya da far'a ta amsata, Su Ihsan duk sunji dad'in barinta gidan tun ba Khairat ba, Yazeed bai san me ke faruwa ba?, Duk taji ba dad'i coz ta saba da gidan, Tunani take idan Imran ya dawo yaga bata nan ya zai yi, Wata zuciyar tace mata "ai bazai damu ba tunda ya tafi ya barki".
Noor ta koma gidansu Naseer da zama, Ummi dasu Meenal na nuna mata so da kula sosai, An yanke shawarar had'a aurensu da nasu Imran, nan da sati biyu, Alhaji yace shine matsayin ubanta zai mata waliyyi, Naseer na nuna mata so har na fitar hankali, ko da yaushe suna tare suna hira, yana bayyana mata irin son da yake mata, Noor na son Naseer saboda kulawa da son yake mata but bata jin shi a ranta kamar yadda take jin Imran, Imran kullum yana mak'ale a ranta, Tana k'ok'arin cusa ma kanta son Naseer dan tasan duniya bata da wani kamar shi (a tunaninta kenan), Imran kuma ta manta dashi.
Bai sanar da Imran abunda ke faruwa ba, Yace Suprising d'inshi yake son yi, Yasan Imran sai yafi kowa farin ciki, sannan zai ji dad'i idan yaji zai auri Noor, coz idan ya auri Noor ya taimaki Imran ne, Imran zaiyi alfahari dashi _Readers kuna ganin Imran zaiyi haka kuwa_.
Yazeed da yaga Noor bata nan, Ya tambayi Hajiya ina take?, Tace "itama bata sani ba"
Hankalinshi ya tashi sosai, hadda kukanshi, Ranar sai da ya zagaye garin Abuja neman Noor bai ganta ba, Ya kira Naseer ya sanar dashi, Naseer Yace "shima bai san inda take ba" _dan yasan halin Yazeed sarai zai iya kira ya gayawa Imran, Alhaji ya saki Noor_
Yazeed duk ya gama haukacewa, bashi da lafiya hadda su k'arin ruwa.
Imran ya kira Naseer yace mishi "A ranar zai dawo, yana so yazo d'aukarshi airport"
Naseer yaji dad'i sosaii da jin dawowar amininshi yayi missing d'inshi sosai
Yace "i have a suprise for you, but sai dai ka iso"
Imran yace "Shikenan Friend, Ina Noor?"
"Noor na nan lafiya, idan ka ganta bazaka ganeta ba", "Ai ni bana ma son ganinta"
"Saboda me Friend", "manta kawai, ka dai ka muna addu'a Allah ya kawo mu lafiya"
"Toh Allah ya tsare ya kawoku lafiya"
"Amin bye".
Ya kashe wayar, tare da lumshe ido yana tunanin dawowa 9ja, Ya d'aga hannu sama "Ya Allah! Kasa kamowar nan da zanyi ya zama mafi alkhairi a gareni, Ameen"
Yayi ajiyar zuciya, Yaja trolley'nsa, Driver'nshi na garin yajasu zuwa airport.
Noor bata san da dawowar Imran ba, but tunda ta tashi gabanta ke ta fad'i, ta rasa dalili, Meenal tace ta shirya suje dinner Cousin d'insu ( d'an Yayan Ummi), Tasha kwalliyarta cikin Swiss lace light blue, ya mata masifar kyau, tayi simple kyau, Tayi kyau sosaii, A wajen dinner kowa ya ganta sai ya kalleta ya yaba kyan da tayi, Samari nata zuwa wurinta ba wanda ta kula, Wuri ta samu ta zauna ita kad'ai ta zauna jigum, tana jin gabanta na fad'i....
*TEAM NOOROUL IMRAN/ NASEER*
*ZEE YABOUR*😘🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
8⃣2⃣
*_This page is for yhu Zee Zee(Ablerh) and Memxiey fulla my naughty friendz😆 baku jin magana I love yhu guys ❤💖_*
*_Mutuniyar kirki My abeeda ina mik'o gaisuwa_*
Jirginsu Imran na sauka, Naseer ya isa airport, Suna ganin juna suka rungume juna
Naseer ya kalli Imran yace "Ka k'ara fari, kayi kyau, sai dai ka rame"
Imran yayi murmushi yace "dole in rame frnd, kasan school is not easy", "Allah dai ya bada sa'a yasa ayi mai amfani".
A mota suna ta hira, Naseer yace "Friend wai kasan yau ne dinner Haydar kuma ya kamata kaje"
"Ohh really Yau ne, na d'auka ai sai gobe", "A'ah Yau ne yanzu haka ana can an fara, ko mu wuce can kawai", "Gaskiya ba zanje haka ba, muje gidanku na chanza kaya, idan naje gida Hajiya baxata barni na sake fita ba".
Ruwa ya watsa, Ya saka shaddarshi brown sabuwa dal, Ya kashe hula tsakiyar kanshi da ya tara gashi, Yasa agogonshi rolex, Imran k'arshe ne wajen kyau da had'uwa, Ya salam! Imran yayi😍, ba macen da bazata so ya zama mijinta ba, Ya fesa turaruka sun kai kala goma duk designers sai da Naseer Yace mishi "turaren ya isa haka",
"Friend ka sanni da turare", "A dai rik'a sassautawa kar ka tada hankalin matan wurin", Imran dariya kawai yayi.
Naseer yace "Kyan nan da kayi, Nasan yau mata sai sun biyomu wlh", "Ka fara shak'iyancinka koh?"
"Haba! Frnd ai ba yau aka saba ba, Ka tuna Amal yarinyar nan mutuwa ne kawai batayi a kanka ba", Imran yaja siririn tsaki Yace "Da yawa matan yanzu basu da class ko kad'an".
Sun isa wajen dinner, Imran gabanshi ya hau fad'i,tunda ya shiga wurin mata ke kallonshi, kai hadda wasu mazan, idan ka ganshi zaka rantse ko zo bai sani da hausa ba, Wajen abokanan ango suka zauna, Kusa da k'awayen amarya, da yawansu sai notice me suke mai, Ya basar dasu kamar bai san sunayi ba.
Minti goma yana zaune a wajen da yaga kallon yayi yawa, Yacewa "Naseer tashi muje kayi dropping d'ina gida, na gaji sosaii i want to rest", "Ok plx bani 3mins", "Bani key d'in mota, zan jiraka a mota".
Ya kutsa ta inda ba mutane sosai, kanshi a k'asa baya ma kallon gabanshi so kawai yake yaga ya fita cikin taron nan, Noor ta tashi rik'e da wayarta, zataje ta kira Meenal tazo su tafi gida, Ya taho ta taho, Suka bangaji juna, Wayarta ta fad'i k'asa, Yai saurin duk'awa k'asa ya d'auko mata, tana tsaye tana jiran taga fuskar mutumin, dan daga ganin shigarshi ya had'u, Ya d'ago kanshi yana mik'a mata wayar.
Gaba d'aya rud'ewa tayi da ta ganshi, gabanta yayi wani mummunan fad'uwa, tai saurin juya baya, Ajiye wayar yayi, jikinshi har rawa yake, k'irjinshi kamar zai fito waje dan fad'uwa, Ya bar wurin kwata-kwata bai so ganinta ba, Gashi ganinta ya haddasa mai wani sabon sonta dan ta masifar yin kyau, ta chanza gaba d'aya kamar ba ita ba, lallai Naseer ya rik'e amana, but me ya kawota wajen dinner da daren nan?,
Lumshe idonshi yayi cikin mota yana tuna ta, "Ya Allah! Ka cire mun soyayyar Yarinyar nan a raina, Ya Allah! Ka mantar mun da ita".
Noor kasa motsawa tayi ko'ina, jikinta sai rawa yake, Ta kasa yarda Imran ta gani ko bashi ba? "Yaushe ya dawo Nigeria da har yazo dinner?, Gashi ya k'ara kyau da haske, Anya ba aljani ta gani ba, Meenal ta katse mata tunani, ta dafata tace "me kike yi durk'ushe anan?", Noor tayi saurin zabura tace "ba komai, wayata ta fad'i, nake dubawa", Meenal ta mik'o mata wayar tace "Ai gata nan bayanki"
Ta karb'a tana murmushin k'arfin hali, dan kar Meenal ta ganota, "Tashi mu tafi gida koh, nasan kin gaji".
Su Hajiya sunyi murna sosai da ganin Imran, girke-girke kala kala Khairat ta mishi, sai rawar kai take ta ganshi, Shikuwa haushi take bashi, ji yake kamar ya tashi ya shak'eta, A daren daga shi har Noor ba wanda ya iya yin bacci, Tunanin junansu kawai suke, Duk suna ganin d'aya ya k'ara kyau, Ga son junansu dake ruruwa a ransu.
Tun da safe Khairat ta tashi ta had'awa Imran breakfast, Yana kwance kan gado ya lumshe ido kamar mai bacci amma ba baccin yake ba, tunanin Noor yake,
Khairat tayi sallama ta shigo, Ya amsata ba tare da ya bud'e idonshi ko ya d'ago ba, Tace "Yayana breakfast na kawo maka", "Ok sannu thanks"
Da taga bashi da niyyar tashi, ta juyo ta fita ranta bai so ba, Jin fitar ta yaja siririn tsaki yana tunanin yadda za'ayi ya auri wacce baya so har suyi rayuwar aure, Ya furta Ya Allah! Ka taimakeni, ka zab'a mun abunda yafi alkhairi a rayuwata.
Tea kad'ai yasha, ko foodflask d'in bai bud'e ba balle yaga me ye a ciki, Wanka yayi ya saka doguwar jallabiya, Ya kwanta ya lumshe ido, Yana karatun Qur'ani da kai (kunsan mahaddacin Al-Qur'ani ne),
Naseer yayi sallama ya shigo, Imran bai amsa shi ba sai da yakai k'arshen aya, Ya bud'e idonshi a hankali, Ya amsa shi cikin sanyin murya, "Friend ya gajiyar jiya?", "Alhamdulillah!", "Toh madallah ga suprise d'inka".
Ya mik'a mishi takarda, Imran ya karb'a yana karantawa bai san sanda ya saki wata irin dariyar farin ciki ba Ya furta "Alhamdulillah, Allah kaine abun godiya, Ya akayi ya saketa?", Naseer yayi murmushi Yace "Rok'onshi nayi", Imran ya rungumeshi Yace "Thank you so much Friend, bansan da wane baki zan maka godiya", "Ba komai frnd, yiwa kaina ne",
Yanayin fuskar Imran ta chanza cike da damuwa yace "Yanzu tunanina ina zata zauna? , bana so ta koma gidansu", Naseer yayi murmushi ya dafa kafad'arshi Yace "ka kwantar da hankalinka, yanzu haka tana gidanmu ni zan aureta", A firgice Imran ya kallo shi Yace "What!", "Yes Frnd akwai matsala ne?".
Imran kanshi yaji na juyawa Yace "U mean auren Noor zaka yi, Naseer me yasa zaka mun haka? Na bar maka ita amana, shine zaka fara sonta, am so disappointed in you Naseer, U break my trust, kace zaka auri wacce nake so why? Naseer?, shiyasa kasa Daddy ya saketa dan ka aureta".
Naseer gaba d'aya rasa ta cewa yayi murya na rawa yace "pl...xxxxx Im..ran ka tsaya ka saurareni na maka bayani", Imran ya d'aga mai hannu yace "Dakata bana son ji, out of my room bana son ganinka", "Ka tsaya ka saurareni Dan Allah", Ya daka mai tsawa "Ka fita nace, before i loose my temper", Naseer cike da tashin hankali ya fita bai tab'a tunanin Imran zaiyi reacting this way, shi bai ga abun cin amana ba tunda ba aure tsakaninta dashi, idan ya aureta rayuwarta ya taimaka, Imran ya kamata ace yafi kowa farin cik idan ya aureta tunda yana son ta samu hutu.
Imran kan gado ya fad'a, Cike da tashin hankali wai Naseer zai auri Noor, Ashe soyayya suke bayan tafiyarshi (Kishi ya rufe mishi ido ya hana shi ya gane Naseer ba cin amanarshi yayi ba), Ji yake kamar ya mutu ya huta da yaga ranar auren amininshi da matar da yake mutuwar so, Zuciyarshi na zafi kamar zata fito waje.
Noor wunin ranar gata nan ne kawai, Son Imran ke ratsa dukkan sassan jikinta, ba wanda take son gani sai shi, ta rasa dalilin da yasa take son ganin Imran, At the same kuma tana jin haushin shi, Ya dawo ko ya nemeta, itama ya kamata ta tambaya dashi a tarihin rayuwarta kamar yadda ya manta da ita, Meenal ta tambayeta "me ke damunta?", Tace "ba komai", D'aki ta koma tayi zamanta ita kad'ai.
Naseer cike da tashin hankali ya dawo gida, Ya sanar da Ummi duk yadda sukayi da Imran, Ummi ta girgiza sosai da jin zancen( dama tasan Imran na sonta), Tace "ka kwantar da hankalinka Naseer, dole Imran zai ji ba dad'i tunda yana sonta, Kishi dole ne but zai huce, ya fahimce komai kuma nima zan kira shi na fahimtae dashi" , "Toh Ummi, Nagode", "kaje kiran babanku kuwa?", "A'ah wlh na manta"
"Ok maza kaje yanzu yana nan falo".
Ummi ta kira Imran, ta lurar dashi, Naseer ba don komai ya fara son Noor ba sai dan yasan ba aure tsakaninsu da Imran, Tana buk'atar taimako wanda zai kula da rayuwarta idan Naseer ya aureta ya taimaketa ne, zata samu hutu, tayi ta fad'a mishi maganganu da zasu kwantar mai da hankali su lurar dashi, Imran ya fahimci komai, ya daina ganin laifin Naseer, yaga Naseer taimakonta ne yayi, but still yana jin ba dad'i a ranshi (kishi), Ya kira Naseer ya bashi hak'uri for blaming him, Naseer yace "ba komai, Ya wuce".
Noor da Imran basu k'ara had'uwa ba tun wajen dinner, Noor na son ganinshi ko zata ji sanyin a ranta, Imran kuwa ko kad'an baya so ya sata a ido, ganinta cuta ne a gareshi.
Shirye-shirye bikin suke, Naseer ke ta faman shirye-shiryen both bikinshi da na Imran, Imran k'ara sukurkucewa yayi, gashi nan ne kamar mara lafiya, ko maganar bikin baya so ayi, Da Naseer yazo mishi da maganar zai b'ata rai ya nuna baya so tun ba idan akan Noor bane _ji yake kamar zuciyarshi zata fashe_, Kullum yana d'aki, idan hajiya ta mishi magana ga wani abu da take so ayi a bikin, ce mata yake tama Naseer magana, Imran ya k'ara ramewa, duk wanda ya ganshi yasan yan cikin damuwa.
Yazeed da yaji Naseer zai auri Noor, Yayi hauka yasha kuka, bashi da yadda zaiyi dole ya hak'ura, but sonta na nan a ranshi, Duk abunda ya rik'a mata tun farkon zuwanta gidn sai yayi regretting, Yaje wajenta ya nemi gafararta, Tace "ya tafi bata son ganinshi", Ya dawo gida cike da bak'in ciki.
Noor kwata-kwata bata farin ciki da auren nan nata kawai zatayi ne dan ta taimaki rayuwarta kuma ta manta da Imran, Ummi ta kira mai gyaran jiki, An fara ma Noor gyaran jiki, da bata had'e-had'e, Ummi na bata shawarwarin zaman aure, da yadda zata rik'e miji ta mallakeshi, Idan tana fad'a mata wasu abubuwa har kunya take ji, ( ta d'auki Noor tamkar wacce ta haifa da cikinta).
Imran ya rok'i hajiya kar ayi wani shagalin biki, kawai a d'aura aure sai walima, Hajiya tace "Sai sunyi kamu", Imran yace "ba damuwa" _tunda dama na mata ne_.
Ana saura kwana uku a fara biki, Imran yaje sashen Alhaji ya gaishe shi, Ya zauna falo yana jiranshi ya fito, Yana d'aki yana waya, Kamar daga sama yaji Alhaji na cewa "Ya zancen buga cacara nan, dafatan za'a samu mak'udan kud'i masu yawa, kuma ba da Alhaji Ibrahim za'a buga ba, kasan duk ya buga sai yaci, Dan ina buk'atar kud'i bikin d'ana za'ayi bani da wata hanya da nake samun kud'i idan ba caca ba".
Imran jikinshi ne ya fara rawa, Ya kasa yarda da abunda kunnuwanshi suka jiye mishi, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Daddy d'an caca ne" abunda yake maimaitawa kenan jikinshi na rawa, kanshi na juyawa yana ganin jiri, Falon na jujjuya mishi.............
*TEAM NOOROUL IMRAN/NASEER*
*ZEE YABOUR*😘
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
8⃣3⃣
Da k'yar ya iya mik'ewa tsaye, jikinshi na rawa, Zuciyarshi na tafarsasa, Ya bud'e k'ofar d'akin Alhaji da k'arfi, Ganin Imran tsaye gabanshi yai saurin katse wayar, Kallon tuhuma yake mishi ga jikinshi dake rawa, Alhaji gabanshi ke fad'uwa a ranshi rok'on Allah yake Allah yasa Imran bai ji wayar da yake ba.
Imran murya na rawa yace "Dama sana'ar da kake yi kenan Daddy, sana'ar caca da ita ka ciyar damu, ka shayar damu, ka tufatar damu, ka cucemu Daddy ka ciyar damu daga haram, Duk shekarun nan haram muke ci, Why? Ka zab'i wannan mummunan sana'ar, nayi bak'in cikin kasancewata d'anka".
Alhaji zufa ta fara keto masa, yama rasa ta cewa
Imran ya cigaba da cewa "Sana'arku d'aya da Baban Noor kenan?, naji kana kiran sunanshi"
Alhaji girgiza kai yayi alamar eh, Imran ya fuzgar da iska cike da takaici, yana jin kanshi kamar zai rabe biyu, wannan wane irin bak'in ciki yake gani Ubanshi d'an caca, bai tab'a jin ya tsani kasancewarshi duniya ba sai yau, Tambayar kanshi yake "Mummy tasan Daddy d'an caca ne ko bata sani ba?".
Fita yayi bai tsaya ko'ina ba sai sashen Hajiya, Da k'arfi ya tura kallon falon, Dukkansu suka juya suna kallonshi a tsorace ganin yanayinshi, "Mummy kinsan Daddy d'an caca ne?", Kamar daga sama taji tambayarshi, wata irin zufa ta keto mata, murya na rawa tace "a ina kaji zancen nan Imran?", "Mum just answer me?"
Miyau ta had'iye k'utt tace "Eh na sani amma a ina kaji?", "Mum kin sani shine kika barmu muna cin haram, Mum me yasa kuka zab'i irin wannan rayuwa ke da Daddy, wlh ina bak'in cikin kasancewata d'anku, Ya dafe zuciyarshi dake mai zafi, yana ganin jiri kamar zai fad'a, Yazeed yai saurin rik'e shi ya zaunar dashi.
Falon yayi tsit kamar anyi mutuwa, su ihsan sun kasa yarda da abunda kunnen su ya jiye musu, babansu d'an caca?.
Alhaji ne ya shigo falon, duk suka bishi da kallo, sai zufa yake daga ganinshi yana cikin tashin hankali, Wuri ya samu ya zauna, Ba tare da yace komai ba, Hajiya ta kalleshi tace "Alhaji ranar wanka ba'a b'oye cibi, Ya kamata mu fasa k'wan nan, mu gayawa yaran nan abunda muka dad'e muna b'oye musu, cigaba da b'oye musu bashi da wani amfani gashi Imran yaji, haka suma sauran ko ba dad'e ko ba jima, zasu ji a wani wuri, dan haka zai fi kyau idan suka ji daga bakinmu".
Alhaji ya girgiza kanshi alamun gamsuwa da zancen Hajiya, Imran idonshi a rufe suke, shi kad'ai yasan zugin da yake ji a zuciyarshi
Alhaji ya d'an yi gyaran murya Yace "ina neman afuwarku, ku yafe min a bisa b'oye muku sana'ata da nayi, Sana'ata ba komai bace face Caca, tun ina matashi nake yinta, da ita na zama abunda na zama yau, duk wata dukiyata ta caca ce, duk ranar da na bar caca talaucina yazo", Imran har a lokacin bai bud'e idonshi ba Yace "Taya ka auri Noor?, Me yasa baka son sakinta?, Alhaji yaja numfashi Yace " Mahaifinta ya sata a caca yace duk wanda yaci shi zai aureta, luckily naci shine dalilin auren....".
Kafin ya k'arasa Imran yai saurin bud'e ido a firgice, Yace "Kana nufin a caca ka sameta?",
Hajiya ce tasa baki tace "k'warai da gaske anan ya ciyota"
Imran shiru yayi ya girgiza da jin lamarin tambayar kanshi yake "Noor tasan a caca aka ciyota ko bata sani ba?, i have to ask her but before that..." Ya juya kan Alhaji Yace "Daddy shawarar da zan baka itace ka bar caca, duk dukiyar nan daka tara, kayi sadaka da ita, ka tuba zuwa ga Allah, ka tara tsaftacciyar dukiya".
A fusace Hajiya tace "ba zai bar caca d'in ba, su kake mu talauce mu tsiyace"
Imran yai murmushin takaici Yace "Gwara mun talauci da mu cigaba daga ci daga haram, shin kunsan cewa ba'a karb'ar ibadarmu, duk wanda ke ci daga haram Allah baya karb'ar ibadarsa, Hadisi na goma arba'una hadith <wani mutum da yayi tafiya mai tsawon gaske,yayi gizo, kuma yayi busu-busu da kura, yana d'aga hannuwansa sama, yana cewa: Ya Ubangijina! Ya Ubangijina! Alhali kuwa abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, kuma tufarsa ma haramun nee, kuma an ciyar dashi daga haramun, to taya zamu amsa masa, Muslim ya ruwaito shi.
Hajiya tace "Allahu Abkar! Toh bari kaji duk abunda zaka ce, Alhaji ba zai bar caca ba, Dan da ya bar caca asirinmu ya tonu, watan talaucinmu ya kama"
Alhaji yace "gaya masa dai", Hajiya tace "ku su Yazeed kuma kuna goyan bayanshi ne, Alhaji ya bar caca?", A tare suka had'a baki suka ce "Mu dai muna bayanki mum, idan daddy ya bar caca ai k'ayarmu ta k'are tunda mu da ita ya dogara"
Hajiya ta gyad'a kai tace "Yawwa kunji masu hankali".
Imran a fusace ya mik'e, zuciyarshi na k'ona tana tafarsasa Yace "idan ku son duniya ya rufe muku ido, ni bai rufe mn ba, bazan zauna na cigaba da cin haram ba, duk wani abu da na mallaka ta dalilinka Daddy na barshi, bana buk'ata, Zan bar muku gidanku, ku zauna ku cigaba da cin haram" Yayi hanyar fita.
Alhaji da Hajiya suka bi bayanshi suna kiran "Imran ka tsaya, kada ka yanke hukuncin da zaka dawo kana dana sani", Banza yayi dasu, Yayi hanyar gate yana zuwa bakin gate, ya fiddo wayarshi da mukullin mota ya mik'a ma Mai gadi, Kafin su Hajiya su fito ya tari machine ya hau.
Hajiya nan ta fad'i tana kuka tana fad'in "Imran Dan Allah ka dawo garemu, kada ka tafi", Alhaji ya fiddo wayarshi Yace "bari na kirashi"
Mai gadi Yace "ai ga wayarshi da mukullin mota ya bani" , Wani kukan Hajiya ta sake fashewa dashi, Alhaji dafe kanshi yayi ya rasa ta cewa.....
*TEAM NOOROUL IMRAN/NASEER*
*ZEE YABOUR*😘
[7/28, 21:33] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
8⃣4⃣
```Ina baku hakuri sosai sosai a bisa dadewa da nayi banyi typing ba,Wlh abubuwa ne sunyi yawa,Buh In shaa Allah i will try my best naga na cigaba da muku typing before na fara exam```
*This page is dedicated to all readers of Itace k'addarata, I luv yhu all*💕💕💕💕
Imran bai zarce ko'ina ba sai gidansu Naseer, ko kud'in da zai ba d'an achaba bashi da, sai da ya karb'a a wajen mai gadi Yace "zai bashi".
"Frnd lafiya?, Ya na ganka haka duk ba'a hayyacinka ba?"
Imran bai iya cewa komai ba, wuri ya samu ya zauna kanshi na masifar sarawa, Zuciyarshi na tafarfasa kamar ana hura mai wuta.
Naseer ya koma kusa da Imran ya dafa kafad'arshi, cike da damuwa Yace "Please ka fad'a mun me ke faruwa? Wlh hankali duk ya tashi"
Tsawon minti d'aya bai ce komai ba, Yaja wani irin numfashi Yace "A yau ina bak'in cikin kasancewata duniya, ban tab'a jin na tsani rayuwar nan ba sai yau, Naseer banyi dace Iyaye da Siblings ba..." Wasu hawaye na bak'in ciki suka biyo kumatunshi.
Naseer Yace "ban gane me kake nufi ba? Wani abu ya faru ne?"
"Wai Daddy d'an caca ne hasalima Noor a caca ya ciyota"
Naseer baisan sanda ya mik'e tsaye ba Yace "What?, ban yarda baa Imran, a ina kaji zancen nan? gaskiya da sake".
Imran yayi murmushin takaici Yace "da kunne na naji" Ya bashi labarin duk yadda akayi
Naseer Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai yake fad'a, Zufa na keto masa, Tausayin Imran ya kamashi.
Tsawon mintuna suka d'auka shiru, Naseer ya nisa Yace "hukuncin daka yanke shine daidai, dan bai kamata ka cigaba da ci daga haram ba, but ina rok'on ka Dan Allah ka zauna nan gidanmu har zuwa lokacin da Allah zai sa su Daddy su gane gaskiya".
"Am sorry to say bazan iya zama nan ba, kayi hak'uri, zanje na nemi halilata(halal d'inshi) bana son zama gari d'aya dasu Daddy, zanyi nisa dasu inje can inda ba'a sanni ba".
Cike da tashin hankali Naseer Yace "Dan girman Allah friend kar kamun haka, bani da wani aboki da ya wuce ka, ina raye zaka shiga duniya, kana so ka nuna mun baka d'aukeni a matsayin d'an uwa ba kuma baka d'auki su Umma a matsayin iyayenka ba".
Ran Imran ya d'an fara b'aci, cikin fad'a Yace "ka fahimceni mana Naseer, ina so nayi nisa dasu Daddy bana so su rik'a jin labarina, zama kusa dasu ba abunda zai haddasa mun sai bak'in ciki, wanda zai iya ja na rasa raina"
Naseer ya d'an yi ajiyar zuciyarshi Yace "Na fahimceka frnd, Ina maka fatan alkhairi a rayuwarka, duk inda zakaje pls ka sanar dani, In shaa Allah zan rik'a kawo maka ziyara".
Kai kawai ya gyad'a mishi, Yace "Kira mun Noor, ina son magana da ita"
Ba musu Naseer ya tashi ya shiga kiranta.
Noor na kitchen tana taya Umma aiki suna hira cikin nishad'i, Meenal ta tafi gidan k'awarta, Naseer ya shigo kallo d'aya ya mata yaji gabanshi ya fad'i, ya maida kallonshi kan Umma "Sannunku da aiki" ya fad'a
"Yawwa" suka bashi amsa a tare, "Noor kizo"
"Toh", Yayi gaba ta biyo bayanshi.
Tana ganin Imran ta juya zata koma, Cikin sanyin murya ya kira sunanta "Noor"
Har cikin k'wak'walwarta taji sunan, yanayin yadda yake kiran sunanta daban ne (ji tayi muryarshi ta k'ara dad'i), Chak ta tsaya ba tare da ta juya ba, "Dan Allah ki dawo muyi magana, nasan ban kyauta miki ba dana tafi na barki, maganar da zamuyi dake mai muhimmanci ce" Yana maganar kamar zaiyi kuka, Ba zata iya mishi musu ba, ko dan yadda taji muryarshi, Gabanta nata fad'uwa ta dawo ta zauna a k'asa nesa dashi, kanta a sunkuye k'asa.
"Ki zauna kan kujera", Kai kawai ta girgiza mai alamar a'ah ba tare da ta d'ago kanta ba, bata son kallonshi, maganarshi kad'ai tana sata a wani yanayi ballatana ta kalleshi.
"Duk tambayar da zan miki ina so ki fad'a mun gaskiya"
Ba tace komai ba, Ya cigaba da cewa "Kinsan Daddy da Babanki Yan caca ne?, kinsan a caca aka saki?".
Noor ba k'aramin girgiza tayi ba, Zuciyarta nace mata ta fad'a mishi gaskiya ko tace bata sani ba, wata zuciyar tace ki fada mishi gaskiya
Murya a sanyaye tace "Na sani"
"Me yasa kika b'oye mun, me yasa kika mun k'arya a lokacin da na tambayeki?".
Murya na rawa tace "Dan in kare mutuncin mahaifina da naku, bana so kusan sana'ar mahaifinku caca ta dalilina bana son na zama silar rugujewar farin cikinku"
Yayi shiru a ranshi yana cewa "Tabbas Noor nada hali mai kyau, ba kowa ne zai jure duk wulak'anci da cin mutuncin da aka mata ba, alhali tana da hanyar kubuta amma saboda farin cikin wasu tak'i" Wani sonta yaji ya k'ara shigar shi.
A fili yace "Gaskiya Noor kina da hali mai kyau, samun irinki cikin mutane sai an tona", Murmushi tayi tace "Ni zan koma cikin gida na bar Umma na aiki ita kad'ai" ( har yanzu haushin Imran take ji akan tafiyar da yayi, ya dawo kuma bai nemeta ba).
Murya a marairaice yace "har yanzu fushi kike dani koh?", Tayi banza kamar bata ji shi ba, Ya d'an yi murmushin dole Yace "Kafin na fad'a miki dalilin da yasa na tafi, ki amsa mun tambayar nan, Da gaske kike baki tashi da mahaifiyarki ba?".
Hawaye ta fara, ta basu labarin da Baba mai gadi ya fad'a mata bata b'oye komai ba, Daga Naseer har Imran hawaye suke, ta masifar basu tausayi.
Falon yayi shiru na mintuna, Imran Yace "Naseer ka fad'a mata dalilin da yasa na tafi na barta", Naseer ya d'an yi ajiyar zuciya, ya bata labarin komai da komai, Tayi mamaki sosai, kuma ta tabbatar ma kanta babu mai sonta a duniya kamar Imran, itama tabbas duk abubuwan da take ji a kanshi son shi take ba komai ba, Hawaye kawai take ta rasa na menene tausayin Imran, Son shi, Murna ko na menene bata sani ba?.
Har cikin ranshi yake jin kukanta, Ya taso ya durk'usa gabanta, Ya fiddo hankercheif daga aljihunshi, "karb'a ki goge hawayenki bana son ganinsu", Ba musu ta karb'a tana gogewa, ta tsayar da hawayen, Wata sanyayyar ajiyar zuciya yayi, Ya tsura mata ido ko k'iftawa ba yayi, kanta a sunkuye k'asa ta kasa d'agowa ta kalleshi.
Naseer mik'ewa yayi, ya fita bazai iya jure ganinsu haka ba, zuciyarshi wani irin zafi take da d'aci( Kishi).
"Noor Zaki aureni?" Imran ya tambayeta da muryarshi kamar mai shirin kuka, "Taya zan aureka bayan na tab'a auren mahaifinka?"
"Baki san auren da akayi a bisa caca haramun bane bai halatta ba, dan haka akwai aure tsakanina dake", "Idan na amince da aurenka Naseer fah, yau saura kwana uku aurenmu idan na mishi haka ban mishi adalchi ba", "Nafi Naseer sonki Noor, Ina miki son da duk duniya ba me miki irinshi, Nasan Naseer zai bar mun ke, Kina sona?"
"Ban da amsar baka tukuna, sai da izinin Naseer".
Wani kishi yaji ya turnik'eshi "hakan ya nuna mun Naseer take so", Ya fuzgar da wani iska mai zafi, Ya mik'e ya fad'a kan kujera, Ya rufe idonshi zuciyarshi na mishi masifar zafi kamar zata fito waje, "idan tak'i amincewa da soyayyata mutuwa zanyi".
Kallonshi take tayi, tana jin masifar son shi na shigarta da tausayinshi, but ba zata amince da soyayyarshi ba, sai in Naseer yace ya hak'ura da ita, ba zata iya juya ma Naseer baya ba.
*Toh readers a ganinku Naseer zai hakura ya barma Imran kuwa🤔*
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘
[7/28, 21:33] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
8⃣5⃣
*This page is for you Hafsat Yaro lots of luv*❤❤
Allah ya bar so da kauna tsakaninki da My Abeeda🤝
Duk maganganun da suke Naseer na tsaye bakin k'ofa yana ji, Sallama yayi ya shiga falon, Noor kad'ai ta amsa mishi, ta bishi da kallo, Imran yayi nisa a tunani, Kujerar kusa da Imran ya zauna, Yayi shiru na yan mintuna sannan Yace "Friend!", Imran ya amsa da "Na'am" ba tare da ya bud'e idonshi ba.
Naseer ya cigaba da cewa "Na hak'ura na janye zancen aurena da No..." Kafin ya k'arasa Imran ya bud'e ido ya rungumeshi Yace "Thank you so much Friend".
"Ba godiya tsakaninmu, dama can Noor taka ce, dalili yasa ka tafi ka barta har ni na fara sonta, bazan shiga tsakaninku ba, nasan irin son da kake ma Noor da halin da ka shiga duk akan sonta, Kafi ni buk'atar Noor kuma kafi ni sonta, Nasan Noor kai take so, bazanyi son kai na rabaka da abunda kafi so a rayuwarka ba, Noor ga Imran baki da wani masoyi da ya wuce shi, ki rik'e shi hannu biyu Amana" Ya k'arasa maganar kamar zai yi kuka (yasan shikam yayi bankwana da farin ciki tunda ya rasa Noor, yafi so ya rasa nashi farin cikin da amininshi ya rasa).
Imran kamo hannun Naseer yayi ya rik'e gamm, Yace "tabbas Naseer kai abokine nagari, ina alfahari da kai, nagode sos....", Yai saurin katse shi "bana son godiyar nan, tafiya zaka yi da Noor ko sai kaje ka samu wurin zama".
"Da ita zan tafi, a yau nake so a d'aura mana aure", Naseer ya zaro ido Yace "Yau d'in nan?".
"Yes friend! The earlier the better, bana so mu dad'e cikin gidan nan dan Su Daddy zasu iya biyoni nan", "Toh ita ka barta nan mana, tunda baka san inda zaka yanzu ba, idan kaje ka samu wurin zama, sai ka dawo a d'aura aure ka tafi da ita", "kaga friend k'afata k'afar Noor, a yau d'in nan nake so a d'aura aure, mu bar garin nan".
Zai sake magana Imran ya dakatar dashi "See frnd Dan Allah ka yarda kawai yanzu muje masallaci a d'aura mana aure", Naseer ba don son ranshi ba Yace "toh muje".
Noor ita dai bata ce komai ba, Farin ciki ta tsinci kanta dashi zata zama mallakin Imran abun kaunarta, Murmushi kawai take ita kad'ai, Naseer ya kai dubanshi gareta Yace "ki shirya kafin muje mu dawo".
Kai ta d'aga mishi sama, Imran bai ko kalli inda take ba ya fice (haushinta yake ji, saboda cewa da tayi sai da izinin Naseer zata amince da aurenshi) Naseer yabi bayanshi.
Suna fita, Alhaji da Hajiya suka shigo gidan, Hajiya har lokacin bata bar kuka ba, Duk ta fita hayyacinta a d'an k'ank'anin lokaci, Sun tambayi mai gadi ko Imran yazo gidan?, Yace "bai zo ba"( dan sunyi warning d'inshi kar ya fad'a yazo), Wani irin ihu Hajiya ta saki "Shikenan D'ana ya shiga duniya, Wayyo Allah ga abunda son duniya yaja mana", "Haba Hajiya Dan Allah kiyi shiru, In shaa Allah za'a ganshi, Imran ba k'aramin yaro bane komai daren dad'ewa zai dawo garemu", Bata ce komai ba tana ta faman kuka, Yaja mota suka tafi, Mai gadi ya bisu da kallo yana girgiza kai.
Goro, sweets da chingum suka fara tsayawa suka siya, Masallacin can kusan fita gari suka je, inda ba'a sansu ba, kuma ba zasu ga wanda ya sansu ba, Suka sami limamin masallacin suka fad'a mishi buk'atarsu, Liman yace ba damuwa, Ya tara mutane dama an idar da sallar azahar kenan, An d'aura auren Imran da Noor akan sadaki 20k, Naseer ya biya kud'in.
Imran "Alhamdulillah" kawai yake furtawa, farin ciki ya lullub'e zuciyarshi duk wani bak'in ciki da yake ciki ya nemeshi ya rasa, Naseer kuwa ya rasa meke mishi dad'i, kwata kwata baya jin dad'in zuciyarshi.
Noor tayi bankwana dasu Ummi, Ummi ta mata nasiha sosaii tare da bata wasu had'e had'e,ta fad'a mata yadda zata yi amfani dasu, Sun sha kuka ita da meenal, Driver ya kaita airport, Naseer ya siyan musu ticket zuwa Kano ( dan can Imran yace zasu) Yaba Imran cheque na miliyan d'aya Yace "Gashi nan ya nemi gida da sana'a, suna isa ya kira shi Dan Allah ya sanar dashi", Imran zai mishi godiya ya hana shi tare da cewa "Ina muku fatan alkhairi a rayuwarku, i'll miss ur company friend" Ya k'arasa maganar da hawaye, Shima Imran hawayen yake, Yace "I'll miss you too Friend", Ya juya ya tafi zuciyarshi na k'ona yana hawaye.
Imran har suka shiga jirgi, jirginsu ya tashi bai kalli ko saitin Noor ba, Yana ta murtuke fuska duk da wutar sonta dake ruruwa a zuciyarshi da farin cikin ta zama mallakinshi, Tacewa kanta "Me yake nufi da haka? K'ila yana tunanin halin mahaifinshi ne, Tunani take birjik a ranta har bacci yayi awon gaba da ita.
Yana satar kallonta yaga tayi bacci, Ya tsura mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta, ga d'an karamin pink lips d'inta ji yake kamar yayi kissing d'insu, bai tab'a mata irin kallon da yake mata yau ba( tunda yanzu ta zama mallakinshi).
Wani irin wutar sonta yake ji na hurawa a zuciyarshi, ga wani irin sabon feelings da yake ji akanta, kamar ya rungumeta haka yake ji, Har ya kai hannu zai tab'a ta sai kuma ya fasa, Ya jinginar da kanshi kan kujera ya lumshe ido, Yana jin wani irin sonta na shigarshi...........
*Tohm finally Imran ya auri Noor ta zama mallakinshi*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Sai ku biyoni dan jin Love story dinsu😍, Ya rayuwarsu zata kasance a garin kano*
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘 (ZEELISH)
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
8⃣7⃣
*D PAGE IS 4 YHU FIDDAUSI( YAR FICIKA)❤ THANKS FOR EVERYTHING😘😘,I VALUE YOU,ALLAH YA JIKAN MAMA YA KARA MIKI HAK'URIN RASHINTA AMEEN*
Noor tana ta tunane-tunane har bacci b'arawo ya saceta, Imran kuwa ko kad'an bai runtsa ba, Kiran sallar asuba yasa shi mik'ewa ya shiga toilet, yayi brush yayi alwala, Ya kabbara sallah bayan ya idar ya zauna yana karatun Qur'ani cikin k'ira'arshi mai masifar d'adi.
Sautin k'ira'arshi yasa Noor farkawa, ta d'auko ma radio ne ya kunna dan karatun kamar na balarabe saboda dad'i, Ganin Imran ne keta rera karatun suratul Rahman, idonshi a rufe, Ido ta zuba tana kallonshi, a ranta tace "gaskiya Imran is damn handsome ga addini, am so lucky to have him as my husband duk da nasan ya wuce da aji na", Ta lumshe ido tare da jin son shi na ratsa dukkan sassan jikinta.
Da k'yar ta mik'e ta shiga toilet, Da ta idar da sallah, ta zauna tana karatun Qur'ani, har ta gama Imran bai tashi daga inda yake ba, sai dai ya daina karatun, idonshi a lumshe.
Gabanshi ta durk'usa murya a sanyaye tace "Ina kwana?" Yayi banza da ita, sau uku tana maimaitawa yayi kamar bai ji ta ba, Muryarta kamar mai shirin kuka tace "Dan Allah idan wani laifi na maka, ka taimaka ka gaya mun na baka hak'uri", Banza ya sake yi da ita, Kuka ta fashe dashi.
Da sauri ya bud'e ido( idan yana son mutuwarshi yana son kukanta), "Mene ne na kuka kuma?, kin nuna bakya sona Noor, kin nuna Naseer kike so bani ba, Kinsan yadda zuciyata ke k'aunarki? amma kika k'i ta, Ya kike so na miki? Zuciyata ba zata iya hak'ura dake ba shiyasa na aureki da wlh na barki kin auri wanda kike so" Ya k'arasa maganar yana hawaye.
Tana kuka tace "Wlh kai zuciyata ke so Imran, Kai nake so nake k'auna ba Naseer ba, tun kafin nasan me ye so nake sonka har daga baya na gane sonka nake, Ina sonka Imran son da bana ma kowa shi, nace sai da izinin Naseer ne saboda kar yaga ban mishi adalchi ba", Jawota yayi ya manna k'irjinshi, Yana shafa bayanta yace "Kukan ya isa haka, bana son ganin hawayenki, kinsan yadda nake jin kukanki a zuciyata?", Shiru tayi tai lamo kan k'irjinshi ta lumshe ido.
Ya sake matseta, Yana ajiyar zuciya a hankali, Wani irin farin ciki ya lullub'e zuciyarshi yau Noor ta furta tana son shi, gata manne a k'irjinshi abunda ya dad'e yana buri, tsawon minti uku suna haka, ta d'aga kanta daga k'irjinshi tare da sunkuyar da kanta k'asa, Binta yayi da kallo sannan ya mik'e jikinshi a mace, Telephone d'in d'akin ya danna ya kira, Yace "a kawo musu breakfast", Ya juya ya kalli Noor da ta zuba mishi ido, yayi murmushi itama ta mayar masa.
Toilet ya shiga yayi wanka, ko da ya fito har an kawo breakfast, Noor na zaune bata fara ci ba, Yace "Noor me yasa baki fara ci ba?", Murmushi tayi tace "kai nake jira muci tare", Yaji dad'in furucinta, ya sakar mata murmushi mai cike da nishad'i yace "ok my queen", Da sauri ya shirya, Ya sanya wando da riga yan kati cikin wa'inda ya siyo, Sun mishi kyau sosaii, Ya fesa turaruka, D'akin ya game da k'amshin turarenshi.
Zama yayi yana bata a baki, Da farko k'in karb'a tayi, sai da yace yayi fushi, Ta karb'a, Chips ne da egg sauce, idan ya sama mata a baki sai yace ta gutsira, shi kuma sauran sai yaci, Har suka ci rabin plate d'in tace ta k'oshi, Yace "are you sure kin koshi?", Ta d'aga mishi kai sama, Ruwa ya tsiyaya a kofi ya bata tasha, ta rage saura, Yasa bakinshi saitin da tasha shima yasha, Noor satar kallonshi take ta gefen ido bata so yaga tana kallonshi, sonshi na shiga cikin jinin jikinta, Tissue ya d'auko ya goge mata baki, ya goge nashi.
Ya mik'e ni zan tafi cikin gari nema mana gida, da sauran abunda zamu buk'ata, Take care of yourself plx, if you need anything ki kira waya ki sanar dasu", Allah ya dawo dakai lafiya", "Ameen my Queen", Har ya duk'a zai yi kissing d'inta sai kuma ya fasa, yasan kissing d'inta zai iya haifar mai matsala ko kallonta yayi ya yakeji ballantana yayi kissing d'inta.
Yana fita, ta shiga wanka, bayan ta fito ta tsara kwalliyarta cikin doguwar riga material da ta mata kyau, Ta kunna Tv tana kallo tana tunanin Imran.
Hausawa zoo road anan ya samar musu gida, Compound ne gida 6 ne a ciki, Kowa da apartment d'inshi, Two bedrooms da toilet, 1 parlour, 1 kitchen sai yar verandah, Gidan ba laifi yana da kyau, kujeru ya siyo saiti 4 yan 70k, sai manyan katifu guda biyu, kayan kitchen da na abinchi, komai madaidaici ya siyo kasancewar kud'in bazasu isa ba, ko kayan kallo bai siyo ba, an jera komai a gidan.
A bakin gidan yasa aka buga mishi shagon kwano, anan zai zuba provision yana siyarwa, sana'ar da ya yanke shawara kenan ya rik'a yi tunda bai zo da takardunshi ba balle ya nemi aiki, kuma ya d'aukarwa kanshi alk'awarin zai nemi halal d'inshi duk wuyar da zai sha zai jure da ya koma gidan mahaifinshi ya cigaba da cin haram.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞
*ZEE YABOUR*😘 ZEELISH
[11/8, 08:30] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
8⃣8⃣
*BANSAN TA INA ZAN FARA BAKU HAKURI BA FANS OF ITACE K'ADDARATA,KUYI HAKURI PLEASE DA DADE DA NAYI BANYI TYPING BA NASAN DA YAWA KUN FARA MANTA YADDA LABARI YAKE*
```THE PAGE IS FOR YOU JAMSY MG, MARIYA AND MIZZ PURPLE NAGODE DA TURO MIN NOVEL DIN NAN DA KUKA YI AM SO GLAD😍😍```💃🏻💃🏻💃🏻
Washegari wajen k'arfe 12 na rana suka had'a kayansu, Ya biya kud'in kwanakin da sukayi a hotel suka koma Hausawa.
"Noor sai kinyi hak'uri da sabuwar rayuwar da zamu fara anan, kinga bamu da kowa nan sai Allah bamu San kowa ba, sana'ar provisions ce zan fara har muga abunda Allah zai yi, amma na miki alk'awari zan rik'e ki amana, zanyi iyakacin k'ok'arina wajen ganin na faranta miki kuma na kula dake"
Murmushi tayi tace "Allah ya baka iko, Allah kuma ya bamu zaman lafiya"
"Ameen my angel"
Tashi yayi Yace "zan fita shago"
"Allah ya Bada Sa'a"
"Ameen", Ya fice
Ta bishi da kallo tana murmushi sonshi na k'ara shigarta.
Gidan ta share ta goge ko'ina, Ta Shiga kitchen ta d'aura abinchi, Jollof d'in Taliya da kifi, Gidan ya game gaba d'aya da k'amshin girkinta, Da ta dahu tasa a kula, ta ajiye, Wanka tayi tasa wata atamfa lemon green d'inkin doguwar Riga, Tayi kyau sosai tana ta rambad'a k'amshi, ta zauna shiru tana tunanin yadda rayuwarsu zata kasance da Imran har ta fara tausayinshi dan bai Saba wahala ba.
Sallamarshi ta katse mata tunani, Da murmushi d'auke a fuskarta ta amsa mai sallamar, Kusa da ita ya zauna, k'amshin turarenta nata dukan mai hanci, Ya shafi fuskarta Yace "kinyi kyau my angel", Kunya ta kamata ta sunkuyar da kanta k'asa tace "bari na kawo ma abinchi".
Har ta mik'e ya jawo hannunta ta fad'o kan cinyarshi, "Zauna ban gaji da kallonki ba, ko bani kika ma kwalliyar ba", Wata kunyar ta sake kamata bata bashi amsa ba sai k'ok'arin sauka daga cinyarshi da take, ya sake matseta Yace "anan nake so ki zauna, nifah mijinki ne dan haka ki cire wata kunya gefe".
Hannunta ya Kama yana murzawa a hankali, har lokacin bata ce komai ba, Kissing hannun yayi, Yace "I Luv ur fingers they are so cute", Noor wani shock taji ta kasa ko da k'wakk'waran motsi, "Jeki d'auko abinchin muci tare".
Mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta nufi kitchen, kular abinchi ta d'auko da plate,spoon da ruwa, Ta zuba abinchin ya sauka daga kan kujera, Yana ci yana bata a baki har sai da suka cinye wanda ta zuba a plate d'in tas.
"My angel kin iya girki sosai"
Tana murmushi tace "Thank you", "Sai yanzu aka ga damar yi min magana"
Bata ce komai ba tashi ta kwashe kwanukan, Yace "ni zan koma shago ki kular mun da kanki",
"Toh ina so zan Shiga mak'ota mu gaisa"
"Amma kar ki dade"
Ta gyada kanta sama alamar toh
Hijabinta tasa, ta Shiga gidajen dake compound d'in, Gidan dake kusa dasu itama Amarya ce sunanta Ameerah, satinta biyu da tarewa, da kad'an ta girmi Noor, sunyi hira sosai Noor taji dad'in haduwa da ita, itama taji dad'in had'uwa da Noor, Da zata tafi ta bata turare Mai bala'in k'amshi ta rakota tace sai tazo.
Imran bai shigo gida ba sai k'arfe tara, Noor har ta gama abincin dare tayi wanka tasa doguwar riga ta bacci ta fesa turaren da Ameerah ta bata, Tana d'aki kwancen kan katifa, Ya shigo k'amshin turarenta ya dakar mai hanci, sai jinshi tayi ya rungumota ta baya, a kunne ya rad'a mata "You scent nice I Luv you so much"
Ya Fara kissing d'in wuyanta, bata hana shi ba, runtse idonta kawai tayi, tana jin dad'in hakan, ba tare da ta juyo ba, Ya Kai minti biyu yana kissing d'inta har fuskarta, A kunne ya rad'a mata ki had'a mun ruwan wanka, jikinta duk ya mutu ya sakar mata kasala, ta mik'e ta nufi kitchen, Imran ma wata irin kasala yake ji yaso ace ya zarce but duk da haka ya rage wani abu da yake ji a kanta, lumshe ido yayi sonta na k'ara shigarshi.
Yayi wanka yasa kayan abinchi, ya kwanta kusa da ita dan har tayi bacci, Ya d'aura kanta kan k'irjinshi, a haka sukayi bacci.
Da asuba ta farka ta ganta kwance kan k'irjinshi, murmushi tayi tace "I Luv u soo much Imran", Ta mik'e kenan taji mararta ta masifar murd'awa, ta durk'ushe anan k'asa tana murk'uk'usa tana kuka da fad'in sunan Allah, Sautin kukanta yasa Imran farkawa a firgice, Yayi kanta ya rik'ota ya rungumeta yana tambayarta " Me ya sameki?" ,
Kasa magana tayi sai mararta da take rik'ewa, Cike da tashin hankali Ya kwantar da ita kan katifa, Ya fita kamar mahaukaci, Mijin Ameerah ne ya ganshi Yace "lafiya na ganka haka?", "Wallahi matata ce bata da lafiya, Dan Allah ka taimaka ka kaimu asibiti da motarka", Yana ta zufa
"Muje in dubata nima Doctor ne"
"Alhamdulillah, muje toh"
Noor nata mirgina a k'asa, Imran ya d'agota yana hawaye, Dr ya duddubata yaje ya d'auko allura ya mata, Yana mata bacci ya d'auketa, Ya kalli Imran Yace "Matarka na fama da matsalar ciwon mara, wanda wasu matan keyi idan zasuyi al'ada toh ita abun ya had'e mata hadda k'arfin sha'awa da take dashi, da za'a samu ko sau d'aya ne to zata samu sauki sosai, Amarya ce hala?"
"Eh Doctor"
"Ok Allah ya bata lafiya"
"Ameen Ameen"
Maganguna ya mik'o mishi Yace "Inda ta farka taci abinchi sai ka bata tasha, ta kiyaye shan maganin kan lokaci"
"In shaa Allah, nagode sosai Dr"
"Nawa ne kud'in maganin"
"A'ah kar ka damu da wannan"
Imran ya mishi godiya sosai, Ya rakashi ya dawo, Kanta ya d'aura kan cinyarshi yana shafa mata marar a hankali, tausayinta duk ya cikashi.
*TEAM NOORUL IMRAN*💞💞
*ZEE YABOUR*😘 ZEELISH
[11/8, 08:31] Umar Dalha: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵🏵🏵
🏵🏵🏵
🏵🏵
🏵
*ITACE 'KADDARA TA!!!* 🎗
🎗🎗
🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
*_WRITTEN_* *_BY_*
```ZEE YABOUR```
&
```QURRATUL~AYN```
*_IN DEDICATION TO_*
MISS_XOXO EN AUTAR HAJIYA
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
8⃣9⃣
*PAGE DIN NAN NAKI NE FERTYMERH ZARAH💞, AM SORRY FOR THE LATE WISHES👏🏻*
``` You are a good friend and an even better person.May God bless you with wonderful times ahead. Happy Birthday and thanks for the friendship we share```😍😍
*_Allah ya Kara shekaru masu albarka Ameen😘_*
Awarta biyu tana bacci kan cinyarshi, ko motsi baya son yi dan kar ta tashi, ido kawai ya zuba yana kallonta, A ranshi yana cewa ya d'auki alk'awarin zai kula da ita da k'arfinshi da lafiyarshi, He will always be by her side no matter the situation, Tana farkawa suka had'a ido da Imran, Murmushi ta mishi shima ya mayarta.
Tashi tayi zaune
"Ya jikin naki?"
"Da sauk'i" ta bashi amsa
"Bari na had'a miki ruwaan wanka"
Da ya had'a ruwan, d'aukarta yayi ya kaita har toilet, Yace
"Zaki iya cire kayan ko in cire miki"
Da sauri tace
"zan iya"
Tsayawa yayi yana jiran ta cire ya mata wankan.
"Ya dai?"
"Kai nake jira ka fita"
"Bakya so in miki wankan?"
"Zan iya da kaina"
Ba musu Yace
"okay", Ya fice.
Restaurant yaje ya siyo mata takeaway na chips da k'wai, ko da ya dawo har ta fito daga wankan ta shirya, Plate ya d'auko ya juye chips d'in, ya had'a mata tea kakkaura yaji madara da Milo, A baki ya rik'a bata, Spoon biyar yana bata bai ci ko sau d'aya, Na shidan da zai bata tace
"kai ba zaka ci bane?"
Yayi murmushi Yace "naci nawa kina bacci",
"Uhmm shine baka jirani mun ci tare ba"
"Am sorry my angel, yunwa nake ji sosai"
"Da ka tasheni ai"
"Bana so na tasheki kina bacci, kanki yayi ciwo"
"Uhmm nima sai na rama"
"My angel rigima"
Ya cigaba da bata har sai da tace ta k'oshi, Ya bata tea d'in ta sha tare da magungunanta, Sauran chips d'in da ta rage ya zauna a kitchen yaci dan muguwar yunwa yake ji, idan dai ita taci, ko da shi bai ci ba, bai damu ba, D'akin ya koma ya jawota jikinshi ya rungume yana shafa gashin kanta a hankali, sun dad'e a haka ba mai cewa kowa komai, Noor tace
" ba zaka shago bane?"
"idan na tafi shago wa zai kular mun dake?"
"Ai naji sauk'i"
"Uhmm.. Korata dai kike"
"A,ah fah na isa na koreka, bana so ne kana wasa da aikinka"
"ok kula da matata shine wasa da aikina"
Dariya tayi tace
"toh zauna"
"Bazan zauna ba nayi fushi sai na tafi, sai ki zauna ke kad'ai tunda haka kike so",
Noor dariya tayi a ranta tace "ba zan iya da rigimar Imran ba"
Fita yayi shi a dole yayi fushi, Pillow ta jawo ta rungume tana murmushi a ranta tana cewa "Ashe lokaci zai zo da Imran zai zama nawa, Allah nagode ma da ka bani Imran a matsayin mijina".
Naseer yana ta jiran kiran Imran shiru, da yaga sabuwar number an kirashi zai d'auka Imran ne, har ya fidda rai yana addu'ar Allah yasa lafiya, Kano babban gari balle yaje nemanshi, Imran bai kyauta mai ba amma yasan duk daren dad'ewa watarana dole ya dawo gida, Yayi missing Imran sosai bashi da aboki kamar shi.
Hajiya kullum bata da aiki sai kuka ita dai Imran, Alhaji na k'ok'arin kwantar mata da hankali yace mata Imran zai dawo, su Ihsan ma kullum cikin lallashinta suke amma inaa bata fasa ba, Khairat tayi kuka kamar ranta zai fita but duk da haka bata cire ran auran Imran ba, komai daren d'ad'ewa sai ta aure shi.
Yazeed ungulu ta koma gidanta na tsamiya ya koma halinshi na bin mata da zuwa club, yanzu har shaye-shaye yake, ba kullum yake kwana gida ba, Alhaji bai fasa sana'ar caca ba, kud'inshi sai k'ara habb'aka suke, Mahaifin Noor shima dukiyarshi sai k'aruwa take ta hanyar caca, Yama manta yana da wata 'Ya Noor, sai cin duniyarsu suke da tsinke shi da mummy da 'ya'yanta.
Ranar da tayi wankan tsarki, tana zaune kan sallaya, ta idar da sallar la'asar, Imran ya shigo ganinta kan sallaya yasa shi jin wani sanyi a zuciyarshi dama ya k'osa tayi wanka, Kan gado ya zauna yana jiranta, Ta gama addu'o'inta sannan ta juya gareshi tace "Sannu da zuwa"
"Yawwa my angel, ina zaune shago naji ke kad'ai nake son gani"
Dariya tayi
Yace
"Ganin kyakkyawar fuskarki yasa naji sanyi a raina"
Ya taso ya k'araso inda take, Kiss ya mata a goshi
"Ina sonki my angel kece farin cikina"
Ya kamo hannunta ya had'a da nashi
"kimun alk'awari ba zaki tab'a barina ba"
"Ina tare dakai duk wuya duk runtsi, I will never leave ur side, I will always Luv u "
Rungumeta yayi dan d'ad'in furucinta, Yana rad'a mata sweet words a kunne, Ya saketa yana shafa fuskarta
"Zan koma shago amma ki sani kina zuciyata har inje in dawo"
"Nima kana tawa"
Ya mata peck a kumatu, Ya juya fuskarshi Yace,
"Nima kimun"
Kunya taji ta kasa yi
"Kimun mana ko kina so nayi fushi"
Da sauri da girgiza kanta
"Oya am waiting"
Ta rufe idonta tai mishi peck
Ta ruga da gudu cikin toilet, Dariya yayi ya girgiza kai
"Yau d'in nan zan cire miki kunyar nan"
Wajen k'arfe tara ta gama abinchin dare, tayi wanka tasa kayan bacci, bayan ta feshi jikinta da turaruka masu bala'in k'amshi, Ta kwanta kenan taja bargo, Imran yai sallama ya shigo, amsa mishi sallamar tayi daga kwance,
"Har kin kwanta my angel"
"Na gaji ne na kwanta in d'an huta"
"Ok sannu ko inzo in miki tausa"
"A'ah na hutar da kai, kaima nasan ka gaji"
"Ba wata gajiya"
"Toh ni dai na hutar da kai"
"Toh ni sai na miki, bari nazo"
Ledar dake hannunshi ya ajiye, Ya Shiga toilet ya watsa ruwa ya fito, jallabiya yasa ya fesa turaruka masu k'amshi, Tashi tayi ta d'auko abinchi da zob'o mai sanyi.
Yana bata a baki tana bashi, sai zuba santi yake ita dai tana ta murmushi dan ta gane santi yake, Da suka gama ta kwashe kwanukan ta wanke.
Ledar ya bud'e, kaza ce k'atuwa guda d'aya sai k'amshi take,
"My angel ga kazar ki ta amare da baki ci ba"
Tana dariya tace "kazar amarya sai yau, na yafe"
"Baki isa ba kuwa"
"Toh shikenan zamu gani"
Ya marairaice murya
"Haba my sweet angel kar muyi haka dake, zo kici"
Ganin yadda ya marairace yasa tazo, Kan cinyarshi ya d'aurata yana bata kazar kamar wata Baby,
"Kai baka ji toh" ta fad'a a shagwab'e
"Kina so inci"
"Eh" ta bashi amsa tare da d'aga kanta sama
"Ta bakinki nake so"
Ta tsaya tana mai kallon ban gane ba,
D'aga mata gira yayi alamar Yes, Ya yago kazar wajen tsoka Yasa mata a baki
"Tsotsewa zakiyi kar ki tauna"
Tsotsewar tayi, ya bud'e baki Yace
"Samun, da bakinki Zaki Samun"
Naman ta turo daga bakinta ta sa Mai,
"Uhmmm....wow its taste delicious saboda ya fito daga bakin ki"
Noor mamakin salon soyayyar Imran take,
"What are you thinking of?"
Ya katse mata tunani
"A haka Zaki cigaba da bani har sai na k'oshi"
Noor ba musu idan ya sa mata nama, Ta tsotse ta sa mishi a baki, Suna ta haka tare da k'ara jin so da k'aunar junansu.