🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
0⃣4⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*Kinfi Alawiyya farin jini unex ta hannun damata ( Hussaina Nasir )* Allah yabar kauna. *Alawiyya*👉🏼😝
*Federal University dutsinma*
Tun lokacin da Bilkisu ta siya ma Anwar break abun ya mishi tsaye cikin Rai saboda karon farko daya taba karbar kyauta daga hannun wani ko wata bayan iyayen sa.
Wasu mutanen basa raina alheri ko kadan hakan yasa Anwar yaji Bilkisu ta shiga ransa farat daya ba don Yana sonta ba ko makamancin hakan sai dai lura da yanayin takun yarinyar, Bata da Jaye Jaye kuma baya tunanin zatayi yawan surutu.
Ita kuwa tuni ta fitar da abun a ranta saboda bata dauki hakan da tayi da wani girma ba, kawai she feel like making him happy kamar yanda ita ma ta kasance cikin Jin dadin bayar da lokacin sa gareta ya koya mata karatu .
Ya kasa sukuni ganin lokacin yakeyi baya gudu duk wadanda keson Karin bayani ya Basu hakuri sai zuwa dare, yanayi Yana duba agogo da Kuma wayar sa Koda zata Kira, me yasa ni ban karbi wayar tata ba? Mtsew yaja guntun tsaki, uku na bugawa ya kasa hakura kawai yayi wanka ya shirya cikin kananan Kaya gayu yayi sosai, uku da ashirin ya Isa makaranta, anata Kiran sallar la'asar hakan yasa Shi wucewa masallaci. Lokacin da aka fito sallah uku da hamsin, ya kura ma wayar sa ido kamar ya rotsata da kasa, shin Wai bazata kirani ba?
Bummmmm......ta fada daga bayansa alamar tana son bashi tsoro.
Ya tuntsure da dariya lokaci guda Kuma zuciyar sa ta mishi sanyi, Ni Zaki ba tsoro? Ko kin dauka kowa irin ki ne matsoraciya?
Tayi murmushi kawai, Yanzu na fito masallaci Ina Shirin kiranka na hango ka........ Ba wani baki da niyyar kirana tun yaushe Kika karbi wayar ba sai ki yi mun ko flashing bane don Nima nayi saving taki?
Suka jera suna tafiya,
No need....kawai na barta ne sai lokacin da Zan Kira.
Bana daukar wayar da bansan no. Ba so better call me to save yeye.
Ta kyalkyace da dariya yabi fararen hakoranta da kallo.......Ni ce yeye?
Ya mata banza kawai.
Karo sukayi da Dr Dan Musa akan hanya, ta gaida Shi Anwar kuwa ko kallo ya wuce abinsa, ya bishi da kallo cikin bacin Rai laifi biyu gashi suna tare da Bilkisu sannan Kuma gashi baya gaida Shi kusan sau hudu kenan suna haduwa Anwar din na watsin kasa kasa dashi, don akwai lokacin ma da suka hasu banki Anwar din ya kalleshi ya watsar ba tare da ya gaida Shi ba. Ya kuta cikin Rai zaka ci ubanka, ya kalli Bilkisu sai Ina Kuma haka kuna da evening lecture ne?
A'a zamuje karatu ne Anwar zai mun bayani. Wanene Anwar?
Ya bukata, Hamza Yusuf wancen ta nuna Shi da yatsa Yana tsaye gaba kadan Yana ta faman latsa waya da alama ita yake jira, Au wancen Dan iskan yaron Mai girman Kai Wanda ya Raina mutane?
Ta zaro ido......raini Kuma sir?
Ya harareta kawai ya wuce abinsa yabarta tsaye. Ta bishi da kallo tana mamakin me ya hada Shi da Anwar din domin tasan Shi mugu ne ana kuka dashi a department.
Me ya hada ka da Dr Dan Musa? Ta karasa inda yake tsaye da sauri.
Ya kalleta cike da mamaki. What the hell are you talking about. Meye zai hadani dashi kuwa inba Yanzu da ya ganmu tare ba.......kada ka mishi fassara, yace ka Raina mutane and this is the second time I hard about something like this a bakin lecturer.
Me yasa baka gaida Shi ba Yanzu Kuma kaji na gaida......saboda baya gaba na.
Malama stop interrogating me about those idiots...... idiot? Anwar kanka lafiya kuwa?
Bai tanka mata ba har suka zauna wani class.
Ki fiddo littafin da zamuyi.
Bazan fiddo ba ....me yasa malamai ke cewa ka Raina mutane Kai kowa ma daukar ka yakeyi ka Raina kowa......Amma ai ke kinsan ban Raina ki ba ko? Hasali ma tsoron ki nakeyi to meye zai dameki? Ya karasa maganar Yana Yar dariya .
Ba wani... ai su malaman ka.....
Bilkisu me yasa kike kirkiro unnecessary problem ki dorawa kanki?
Meye abin dagewa anan Wai? Sun Dade basu kirani da Dan rainin hankali ba so what?.......sai suyi maka mugunta a result,
Basa iyawa ki daina damuwa......
An Gaya ma na damu ne?
Kai ba a Isa a fada ma kana kuskure ba ka gyara.? Ta dunga balbala mishi masifa.
Hannunsa duka biyu ya goya a kirji tare da tsareta da ido Yana mamakin.
Meye abin hakikancewa anan? Ita meye nata aciki? Wai me yasa take kokarin shiga harkarsa ne ma?
Ya sha mur Yanzu kin kirani anan ne don ki nemi rigima ko kuwa karatu zamuyi? Cos I'm tired of it already.
Ya janyo littafin dake gabanta bari mu Fara ...........
Gab da magariba suka gama, tare suka taho yana ta binta, har suka karaso kwanar gidan ta, lokacin ne ta kalleshi zaka bini ne?
Ashe kin gane , ya fada Yana murmushi....
Tabbb da ka ci na jaki kuwa muyi maka ihu Kato.
Wannan karon dariya yakeyi sosai nine katon?
Eh Mana namiji a gidan mata.
Kin San ma'anar katoa hausa kuwa? Ta kalleshi eh Mana gashi na fada kato namiji kamar Kai......barawo ake ce ma Kato fa ni barawo ne?
Kai Ni dai bance ba kada kamun fassara.
Test din gobe ina bayanka please.
Da gaske kike?
Allah kuwa......
Okay ba damuwa.
Kiyi man flashing nayi saving no. Ki Mana.
Zan kiraka anjima kada ka damu ai na ce Zan karanta abinda mukayi inda na manta Zan maka waya ka tuna?
Ke ban yarda ba kirani Yanzu.
Allah Zan kiraka kaji na rantse.
Sai da safe gashi can an Fara Kiran sallah.
Kina korata ne? Me yasa like zaune a off campus bakya son hostel? Hakanan Ina da kyankyamin toilet maganar gaskiya Kuma Ina son privacy in ma life.
Kai me yasa kake son zaman hostel?
Kar na Zama Dan iska Shi yasa a off campus mata zasu dameni Yanzu ma Yana iya......harara ta balla mishi sannan ta buga tsoki kaji dasu can, sai da safe.............. Bilkisu.... Bilkisu... Bilkisu..... Amma inaaaa tayi shigewar ta gida ta kyalesa.
Yayi murmushi yarinyar rigimammiya ce wallahi. Kut!
Wai ni Anwar yau mace tayi wa tsoki banji haushi ba shin Wai wanna yarinyar wacece ita?
**************
*KADUNA RIGASA*
Tunda suka Fara raba kwana matsaloli suka Fara kunno Kai daga bangaren Ummi, duk ranar girkin ta sai ta Mila tasha iska take data abinci wani lokacin sai dai Amirar ta dafa ma Yara indomie ko su Sha oat ko wani simple food, tun abun baya damun Amira har ta Fara Jin Yan aikin gidan kansu sun Fara korafi.
Gashi baya nan yayi tafiya.
Ranar da ya dawo kuwa akayi sa'a dakin amaryar yake.
Bayan sallar isha'i Yara sunyi barci ta sameshi acan. Yana kishingide bisa kujera ita Kuma tana saman kafet tana chatting......dukkan su ta kalla sannan ta watsar.
Ya Dan zabura Amira yau kece anan? Lafiya dai ko?
Domin bai taba ganin ta sashen ba idan Yana nan wata kila ko tana zuwa sai idan baya nan ne.
Zuwa nayi in tambayeshi ka, Kaine ka Sanya matar ka ta ringa yin abinda taga dama gidan nan?
Ya zaro ido Ni? Me tayi?
Ta zaburo Au karata.....ya daka mata tsawa idan Kika Kara magana bakin auren ki wallahi kada ki dauki mutane Yan iska ke gidan ku ba manya ne?
Abinda kikeyin mun daga ni sai ke Ina shanyewa idan Kika ce zakiyi gaban jama'a kece Masha wuya.
Amira me ya faru? Zo ki zauna..... Ba Zama ya kawo ni ba.
Ina so in sani cewa Kaine ka ce matar ka ta ringa Mana horon yunwa a gidan nan? Daman ka sanya doka ne na Mai miji tayi girki don ka fifita daya?
Tun zuwan Ummi gidannan a duk lokacin da aka ce kasa kafa kayi tafiya to mu da abinci sai taga dama Yara har sai sun Fara kuka sai dai a nema masu wani abun.
Bata ganin kowa da mutunci ban Isa in nuna mata kuskure ko shawara ba shine na ke son gani a gabanta ka fada mun idan Kaine ka daure mata...... Wallahi bani da masaniya.
Kuma me yasa tun farko Baki fada min ba ......saboda Ina tunanin ko hada bakunta ne Shi yasa Amma na lura galari ne da daurin gindi....wurin wa? Na rantse da Allah ban sani ba.
Ke Ummi kinji abinda ta ce haka ne?
Ta yatsina fuska, eh saboda Ni ko a gidan mu ba saba dafa abincin gandu da......what?
Nan gidan ku ne?
Da sauri ta kalleshi.
Ya zaburo na ce Nan gidan ku ne?
To bari kiji in fada Miki Nan gidana ne matukar kina son Zama Dani wallahi sai kinbi abinda nake so da abinda na tsara.
Waye zakiyi ma gadara kice gidan ku? Idan gidan naku kike so sai a maida ki kije kiyi abinda kike so Amma anan matukar kina son Zama to ya Zama wajibi kibi abinda nake so. Bazan taba daukar raini da wulakanci ba ai nasan halinki na ga take taken ki na rashin tarbiyya da tsageranci idan nayi la'akari da yanda kike datsa mun magana many times.
Ya nuna ta da yatsa wallahi ki taka a sannu......Amira dai juyawa tayi abinta.
Ya kirata Amira tana juyowa tace abinda ya kawo ni kenan idan itama tana da nata korafin Ina jiranta.....tayi ficewarta.
Amma ke wallahi Baki da wayau Ummi. Da kin San Hali irin na Amira da kin lallabata Kun zauna lafiya. Kin Aure mata miji Kuma kin dawo kina wani hauka...... Gori zaka mun? Ai ba ni na kawo kaina ba....... An Miki gorin.
Wallahi matukar kina son Zama Dani cikin Jin dadi sai kinbi Amira Kun zauna lafiya.....fuuuuu ya tashi ya shige daki ji kake gammmmm.
Kwalla suka zubo mata, zuciyarta tayi mata kunci wanna masifa dame tayi Kama?
******************
*Federal University dutsinma*
Sun fito lecture 9-11 kenan aka aiko registration officer dinsu na kiranta.
Babban mutum ne ana yawan Kira mishi kirki da mutunci.
Tana ta faman tunani ko lafiya?
Bayan sun gaisa ya mata fatan alkhairi sannan yace yaji dadin gajin result dinta da Kuma yanda ta Sami shaida a department na tare mutunci amatsayin ta na budurwa Kuma ita kadai mace musulma a ajin.
Sannan idan har tana da wata matsala kada tayi kasa da guiwa ta je ta sanar dashi in shaa Allah zai taimaka.
Tayi godiya sosai, ta koma aji dayake suna da wata lecture ta 11-1 sannan suyi test 2-4.
Sadeeq babban abokin Anwar, Wanda kowa yasansu tare tun aji daya, ya hangota yace mutumen ga fa bilky can .
Yayi kamar baiji Shi ba miskilin........
*Zainab wowo*..💖✍🏼ayi hakuri da kadan pls
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
0⃣5⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*Kinfi Alawiyya farin jini unex ta hannun damata ( Hussaina Nasir )* Allah yaba kauna. *Alawiyya*👉🏼😝
*********************
*Federal University dutsinma*
Tana isowa ya tashi yabar gurin.
Haushi ya kamata ganin zai dizga ta bayan Kuma yasan cewa wurin Shi tazo.
Sai Shan kamshi yakeyi yau ta rasa dalili.
Ta kalli sadeeq yau me akayi wa abokin ka ko Yan wulakancin ne bisa Kai.?
Yayi murmushi to wa ya sani.?
Sadeeq Yana da kokari Shima sosai musamman bangaren calculation ya iya Math sosai da sosai.
Tayi murmushi kyaleshi don nace zamu zauna test tare ne yake faman hade rai.
Murmushi kawai sadeeq yayi.
Suleiman na zaune gefen ta, tace sadeeq kara nuna mun nan please ta bude littafi ( Bilkisu kenan ba girman Kai indai maganar karatu ne ), ya danyi Yar dariya bari in Kira Miki mutumen ki kada.......bana so kyaleshi kawai nunan.
Tare da Suleiman ya nuna musu sai ma ta ga cewa yafi Anwar iya koya lissafi Shi Kuma yafi iya theory ( labaran banza ).
Yana shigowa ajin ya gansu tare da sadeeq ya Kara hade rai, wani haushi ya turnukeshi ji yakeyi kamar ya rufesu da duka su biyun.
Zai gitta sadeeq ya rikoshi malam zo ka koya mata.....kyaleshi banso ta fada a hasale.
Baka ga sai wani Shan mur yakeyi ba simply don nace Zan zauna test kusa dashi? Mtsew ta balla mishi harara.
Duk kunya ta kamashi, saboda Shima fa bai San dalilin fushin nasa ba,
Gaban sa ya fadi kaddai fa kishin yarinyar nan yakeyi. Yayi saurin kawar da tunanin yadanyi tsaki a hankali.....
Ke bana son Sheri, yaushe ma na ganki da har Zaki mun wannan shaidar.
Eh Mana, Ina ma ka ganni ai baka so ko ido mu hada kana ta wani muzurai......mtseew ya finciko sadeeq tashi munafuki. Ya zauna kusa da ita kamar ya ingije Suleiman yakeji , kawai baya son raini ya shiga tsakanin su.
Zaka karya nine?
Ya mishi banza..., Ita ma bai Kara mata magana ba.
Suleiman dai na gefe ta juya tana mishi magana......idan na wanko ga Anwar ka wanka kada kayi kasa da guiywa....ya kyalkyace da dariya ita ma dariyar tayi.
Ya Kara hade Rai....yarinyar nan ma ta daukeni Dan iska Amma ba laifin ta bane Suleiman zanci ma uwa......akan me? Wata zuciyar ta bukata. Yayi saurin kawar da zancen ya maida Air piece dinsa a kunne. Ya ajiye littafin sa ya fita waje.
Kowa nata karatu Amma Shi ba yanda zaka ganshi da littafi.
Handsome and intelligence guy amma girman Kai da wulakanci sun bata Shi. Vivion dake zaune gaba na ta fada tare da kallon uchechi.
Ai ya Raina kowa don Yana da kokari.
Ga kyau Kuma ko?
Eh, Amma baya birgeni saboda gadarar sa, jiya munyi ta kiransa yaki daukar waya nida su faith.
Hmmm mu samun sa mukayi dazun after lecture muna son ya koya Mana Amma kowa ya kasa Masa magana........ Maganar ta makale ganin Yana dawowa.
Ashe malamin nee gani ya taho.
Ko Zama baiyi ba ta nuna su uchechi gasu Nan suna son ka koya musu amma sun kasa tambayar ka......sai ke Mai Baki Zaki tambayeni?
Idan abun ya damesu ki bari su fada Mana.
Zata Kuma magana ya nuna mata hannu alamar ta duba ga malamin nan ya shigo.
Sadeeq na bayansa.
Ta fiddo paper zata rubuta suna yayi saurin daukewa ya rattaba nasa sunan ya wani hade Rai.
Ta kura mishi ido Baki bude.....gashi Bata da wata.
Ko wa ya dauke jakar sa....malamin ya fada.
Ya dauko jakar ta ya saka littafinsa Suleiman ya Miko nasa a saka mishi da wayar sa kawai ya Mike ya saka tashi wayar yakai jakar can gaban malamin.
Ita Bata San me yayi ba, Amma Shi Suleiman din yaji haushi sai dai Yana uchechi ta saka mishi a tata jakar.
Sadeeq kuwa dukewa yayi Yana sumke dariya.
Bilkisu tayi zugum tana zare ido Anwar ya kwace takarda.
Tana tsoron tayi magana ya canza mata wurin Zama.
Ko ajikin Anwar tuni ya Fara rattaba number sa bayan ya rubuta suna da course code.
Suleiman ya Ankara Ashe biyu gareshi. Ya Miko mata.
Wani sanyi taji ta balla ma Anwar harara sosai sannan ta Fara rubuta suna.
Gaba daya ajin yayi tsit!
Tana rubuta suna taga Anwar ya fiddo wata takardar ashe daman Yana da ita.
Haushi ya Kara kamata shin me take nufi da akoreta sit din ko meye? Nan da nan ta Kara kulewa.
Har malamin ya gama raba question paper Bata gama duminiyar Jan layi da rubuta suna ba.
Lokacin da ya bada umarnin a Fara kowa ya bude takardar Amma sai wutar kowa ta dauke saboda yanda ya mako muguwar tambaya Mai sarkakkiya.
Sadeeq taji na magana a hankali, Anwar wannan 35 din zamuyi amfani da ita kuwa?
Ya kada Kai alamar a'a.
Yawwa na gode.
Bilkisu tayi zugum, Suleiman ya zungurota alamar ta iya?
Ta girgiza Kai ya ce to kawai tayi ta kwafo musu na Anwar.
Ganin ya Fara rubutun tayi saurin maida hankali don samun abinda zata tsira.
Kamar injin haka yake rubutun zu..zu..zuu kafin tayi layi hudu har ya juya , haushi ya turnuketa bai jira ta gama? Wannan wace irin mugunta ce?
Nan da Nan ta zuciya kawai sai ta ci gaba da rubuta shirme.
Gara naci zero da in yi naka ....ta fada cikin zuciya.
Kafin kace kwabo har ya gama ya janyo wata sabuwar takardar, ya canza biro black ya ci gaba da rubutu, sakamakon ta farkon da ya Fara da blue biro.
Tana kallon sa ta wutsiyar ido ko ya Turo mata wacce ya Gama da ita ta rubuta sai ma ya sanyata kasan tashi , idanun ta har ruwa ruwa sukeyi saboda fushi .
Wallahi Ni da Anwar har abada au Ni zai ma rashin mutunci?
Duk inda ka waiga kowa sai mazurai yakeyi an kasa rubuta abin kirki.
Tana kallon sa ya gama kawai yasa hannu biyu a kirji.
Kamar tayi ta tsunkulinsa takeji don takaici.
*stop writing*, ya Fara karbar wadanda ke gaba layi layi........ai kamar jira akeyi ajin yau dauki gungunai.
Jin haka kawai taga ya dauro mata takarda bisa tata.
Sunanta, number, course code.....da komai da komai.
Ta zaro ido Wai Daman biyu yayi tawa da tasa?
Tayi saurin kallon sa, ki soke wannan shirmen da kikayi kisa mistake. Ta kalli takardar ita ce ya Fara solving da blue biro.
Suleiman ya Fara kunno Kai zai Fara kwafa , malamin har ya zo wurin su, duk suka Mika.
Shiru Suleiman din yayi yama rasa meye zaiyi don takaici, Tabbas yasan don Shi Anwar yayi haka.
Ta kalli Suleiman din cike da damuwa ka gama kuwa?
Wallahi banyi komai ba ya fada Yana kakaro murmushi,
Innalillahi..... Ta juya zata ma Anwar magana Ashe har ya bar class din.
Ta waiga ta Kara waigawa Amma Ina tuni yabar shiyyar class din ma.
Kayi hakuri , ta juya tana ma Suleiman magana.
Nima wallahi har na sadakas, ashe rubuta mun yayi. Kai Anwar karshe ne wallahi.
Murmushi kawai yayi.
Ai kaga da ya barni na kwafa har kaima kayi.....kayi hakuri Suleiman.
Haba ba komai wallahi. Ya fada Yana Yar dariya.
Haka suka fito duk jikinta wani iri.
Kai Anwar case ne. Watan Shi dole inba wulakanci yayi ba baya taba Jin dadi.
A bakin kofa sadeeq ya karaso Bilkisu ya test din....yawwa sadeeq zo kaji Dan Allah. Ta yi gaba Yana binta.
Sun danyi nisa kadan inda ba mutane sosai ta tsaya.
Ka ringa yi ma Anwar fada Dan Allah Shi me ya dauki rayuwa?
Me yayi ba dai tashi yayi ba ya bada ba tare da ya baku ba?
Hmmm , kusan haka.
Kaga yasan tare nake da Suleiman na Kuma fada mishi Amma sai ya hana in copying Yana ta sauri sauri Ashe so yakeyi yaci lokaci yayi nawa yayi nashi Kuma don mugunta bai bani ba har sai da za'ayi submitting saboda Allah ya kyauta?
Tun tsirewa yayi da dariya, Dan iska, abinda yayi kenan?
Wallahi kuwa, kaga ai Babu dadi.
Gaskiya ba dadi.
Kiyi hakuri Dan Allah Yana Ina yanzu?
Kasan halinsa ai, har ya gudu ya tafi.
Kiyi hakuri Zan mishi magana.
Ka kyaleshi Daman idan ka lura bai niyyar Zama Dani ba yau tun safe yake ta wani Shan kunu..... Baki tunanin ko kin Masa laifi? ...Laifin meye?
Jiya ne mukayi Zan kirashi a waya na manta inaga kilan shine ......shine ma kawai.
Mtseww.....to kyaleshi .
Anwar na Bilkisu.... Bilkisu ta Anwar ai in ba keba Shi.
Kai ai kyaleshi zanyi don ban iya hakurin wannan mugun halin nasa.
Dariya sadeeq keyi sosai.
Ta wuce fuuuu.
Waya ta dauka, ta kirashi.
Yana tsaye zai siyi *Pepsi* yaga Kira.
True caller ta bayyana sunanta a screen din wayar sa *Balky gada*
Kawai sai yaji gabansa ya Fadi ras!
Ya danyi murmushi....... Hello
Kana Ina?, Ta fada?
Cikin dakewa kamar bai San wake magana ba yace Ina Ina?
Eh kana Ina?
Wake magana ne?
Bilkisu.....kana Ina Wai?
Wace Bilkisu ? Ya Kara bukata.... Dariya ta kusa kubuce mishi Jin har ta Fara hasala.
Bilkisu Gada ....... Oh ya fada tare da yin shiru.
Au shine kayi shiru mtseww.....ta katse waya.
Yabi fuskar wayar da kallo Yana kyalkyatar dariya ohh ni Hamza tawa ta sameni.
Wai yarinyar nan idan Sona takeyi haka zata shigar da kanta da tsiya ba da ARZIKI ba?
Ni wallahi na Fara tsarguwa da tambayoyin da nake faman amasawa kullum akanta .
Ya kirawo ta......kamar bazata dauka ba har ta fito cikin makarantar sun rabu da Suleiman tun a bakin gate.
Ai naji kana ta wani rainan wayo saboda nice na kiraka ba credit Dinka ba. .......Allah ya bada hakuri. Kina Ina ne?
Ni na Fara maka wannan tambayar baka bani amsa ba don haka........ohhhhh na ma hangoki. Kawai ya kashe wayar.
Ta Fara waige waige....
**************
*KADUNA RIGASA*
Kutumar bala'i .....Kai Wai me aka daukeni gidan nan?
To bafa Zan Dauka ba.
Daman some somen hauka zubda miyau, Ni fa ko lallashin da akeyi ma Amarya ban samu ba, bani da wata kima sai ta bisa gado ya iya lallaba da lallashi bisa gado....yau za ayi ta takare.
Ta tashi Yana kwance rubda ciki, ta banka kofar da karfi har ya Dan razana....kace nan ba gidan mu bane daman na ce Nan din gidan mu ne?
Ya dago Kai da sauri ....kada ki kawo man hauka....an kawo ma hauka kayi maganina Mana mijin tace?
Nine mijin tace?
Kaine......kana da wani sunan da yafi wannan shanyayye?
To Bari kaji in fada maka idan an shanye ka ni ba'a shanye Ni ba, ba malam ba boka amma dole ka maidani gidan ubana bani wannan wahalallen auren naka marar fa'ida..... Ke ba a Isa a Gaya miki gaskiya ba ko? Duk lokacin da kikayi kuskure aka nemi a Miki gyara......haka ake gyara a wulakance da cin fuska?
Ai Daman kallon ka nakeyi tun kafin in zo gidannan kake nuna mun bani da wani matsayi sai matarka..... Shut up.....ya daka mata tsawa......bazanyi Shurin ba......ita ma ta daka mishi tsawa....ka sake Ni a yau Mana idan kana ganin Kai ke iko da kanka ba wat ke juya ka ba. Idan Kuma baka iyawa .....ta bude kofa kazo ka wuce ka tambayo ta idan ta amince yau ka bani takarda ta ita wacce ke auren naka.
Kai Bari kaji in fada ma Bashir.....wallahi wallahi baka cikin tsarin mazan da nake so in aura saboda Ni duk Mai mata baya gabana musamman Wanda bai da gabata irinka sai abinda aka gindaya mishi.....Ummi Ashe Baki da kunya?.... Yau ne kasan haka?
Kai baka iya maganin rashin kunya ba?
Ka je ka tambayo ta ya ake maganin marar kunya sai kazo kayi hakan Dani mijin tace....fuuuuu ya tashi yabar dakin ta bishi tana balbala bala'i ta inda take shiga Bata Nan take fita ba....idan hankalinsa tayi dubu yau a tashi yake, yayi hanyar dakin Amirar....ta daga murya....Arrrrrr Ni nasan baka da idea din kanka sai wacce aka saka maka.......nesa nesa yake Jin maganar.
Da karfi yake buga mata kofa.....a rude tazo cikin tsoro take magana...wanene?
....ke bude nine....da sauri ta bude....lafiya baban Ahmed?
Waccen yarinyar Bata da tarbiyya Amira wallahi wallahi ban tunanin Zan iya Zama da ita.....Nan da Nan tamu ta mata ta motsa ( kishi )....to Yanzu me kake nufi?
Zan kwanta anan ne saboda........saboda ita tafi karfin ka?
To ba anan ba wallahi.
Ta barshi tsaye ta shige dakinta kawai tasa key........
Ya zaro ido😳😳😳😳
Nima na zaro nawa😳........✍🏼
Ayi hakuri da kadan.......✍🏼 *ZAINAB WOWO*
*Maman Abdallah*💖
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
0⃣6⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*Masoyana ku sani cewa Ina alfahari da ku 100% a ko'ina kuke. Na gode da kauna*👏🏼
****************
*Federal University dutsinma*
Duk dube dubenta bata hango ta inda zai bullo ba, juyawa tayi don tafiyar ta..... Saura kadan suyi karo.
Ta razana ainun, hazbunallah! Ta fada da sauri tare da yin baya kadan ........harara ta banka mishi kafin tace. Wallahi ka tsoratani.
Ya danyi murmushi matsoraciya kawai meye zai kamaki Yanzu da rana gatsal cikin wannan bainar jama'ar?
Mtseww...... Ta gittashi zata wuce.
Ina zakije Kuma Ina ce nemana kikeyi.
Barshi kawai , ta fada tana Kara yin gaba.
Ikon Allah, ya fada tare da rufa mata baya..... Wai ke me yasa kin cika nemana da rigima?
Ta Dan harareshi, ni nake nemanka da rigima ko kuwa Kaine ke nemana da rigima?
Me nayi?
Saboda me yau kayi wa Suleiman wulakanci ni kuma ka kunyata ni?
Kunya ta ki Kuma?
Eh, ai kasan tare muke dashi sannan ka tabbatar idan na copy naka zai Sami damar yi shine ka rufe kayi biyu Kuma don mugunta baka tashi bani ba sai da aka ce submit.
Shine laifin da nayi?
Ban sani ba.
Allah ya Baki hakuri what next?
Kaje kaba Suleiman din hakuri......you are not well wallahi nine Zan ba Shi hakuri? Da na mishi me?
Shi ko kunya baya ji zai zauna mace na goya Shi Kuma......ai baya ganewa.
Please Bilkisu come to your senses Mana. Me yasa kike kawo fada marar amfani tsakanin mu.
Ya ja ya tsaya Bari kiji na fada Miki, tunda Kika ajiye girman Kai Kika nuna kina son ki karu dani toba abinda bazan miki ba don naga kinyi passing no matter how, Amma duk masu zagi na suna mun shaidar banza a class kallonsa kawai nakeyi.
A gabanki ake cewa Ina da girman Kai, bani da kirki....this and that..Amma Ina so in tambayeki lokacin da Kika nuna Zan koya Miki karatu Kinga negative response a wurina?
Akwai Wanda Kika taba Jin yazo wurina da sunan Zan koya mishi karatu na koreshi ko Kuma nace bazanyi ba?
Ko kuwa saboda kawai Ina son a yaba mun sai nayi ta yake baki Ina shelar ku taho kutaho Zan muku karatu imagine for God sake.
Eh na fahimceka amma ai baka sakin fuskar ma da za a tambayeka.....ke me yasa Kika tambayeni?
Tayi murmushi ai ni kace.
Ke Bilkisu ko?
Ashe ka gane ....ta fada tana Yar dariya.
Mtseww......ya kamata ki daina mun wannan rigimar gaskiya bana so........ Sai kayi kokari ka canza Hali?
Nayi meye?
Na farko, Idan ka shigo class ka danyi wa mutane magana, na biyu, ka ringa yarda ana hada ido da Kai sai kayi Dan murmushi.......wata muguwar dariya ya saki har Yana buga kafa kasa.
Yarinyar nan wallahi kin rainani da yawa. Watan kaman wani karamin yaro ko?
Suka ci gaba da tafiya.
Nidai na fada maka.
To naji, sai Kuma me?
............. Shegen gora, wallahi daman sai da Anas yace tare da Bilkisu kake wannan ihun.
Dukkan su suka juya, sadeeq ne da Anas.
Yawwa sadeeq Allah ya kawoka zo ka taya ni yi mishi fada.......duk suka zaro ido fada Kuma? Ai wannan mugun dan daba ne wallahi yafi karfin mu.
Au baku fada mishi gaskiya kenan?
Kedai jaraba....suka ce tare da wucewa suna Yar dariya.
Shi kuwa sai hararar su yakeyi.
Ta rike baki....ohh, watan Kai kowa tsoron ka yakeyi......Banda ke,
Hmmm,ai wallahi koni ma ta Kara sauri sai anjima kaga tafiyata.
Shima ya Kara sauri Ina zakije Ina Jin yunwa muje ki siya mun abinci tunda kin Fara dandana mun.....eh lallai yi kokari ka cinye Yan pocket money din ta fada tana hararar sa.
Ba Shi kenan ba mun koma 1/1 kenan..... Amma muje Zan jira ki dafo mun indomie....ta zaro ido, Kai rufan asiri koma kada ma ka janyo mun surutai ace .......kin Fara yawo da Dan iska?
Ko kin Fara zuwa da Dan iska kofar gida......na tuba, ba haka nake nufi ba, inba haka kike nufi ba sai ki zabi daya, ko ki dafon indomie ko muje ki siya mun suya ko kaza ko chips......ta kyalkyace da dariya watan sai ma ka zaba,
Ka jira anan naje na fito da kudin nan Babu a jaka, muje na ranta miki gobe ki fito mun da kudi.
Ikon Allah kamar cin rabo?
Eh, ai nasan karamin aikin ki ne idan kin shiga inji shiru kinki fitowa.
Mtseww......au abinda kasa ma ranka kenan.....ke mufa juya wallahi bazaki shiga gida ba.
Haka ta juya badon ranta yaso ba suka je shagon Alhaji Hari, ta kalleshi zabi abinda kakeso toh.
Ya koma gefe zabo mun dai ni wace gareni tunda kawoni akayi?
Kamar ta nutse kasa don kunya shagon cike mutane an musu ratai da ido. Kowa yasan Anwar Kuma Mai shagon yasan wanene Shi mamaki kawai yakeyi yau shine tare da mace?
Ta Sha mur Alhaji bani meat pie hudu, Pepsi biyu, shortbread biscuit din can manya biyu.....gaban Anwar ya Fadi Jin kayan tsadar da take lafto mishi Amma da ya tuna Shi zai biya kudin sai ya kyaleta.
Leda bammm aka cika. Ya mata totalling dubu hudu da dari shidda....... Ta bude jaka ta fiddo ATM Daman Yana da *POS* tace fidda kudin pls.
Ba karamin faduwa gaban Anwar yayi ba.
Ya rasa yanda zaiyi duk yaji wani iri.
Ta fito niki niki da leda oya muje ta fada tana hararar sa.
Ya sunne Yana Yar dariya.
Dan mashin ta tsaida mishi sannan ta kalleshi Yanzu ka shafan lafiya ka tafi ko?
Ya kyalkyace da dariya korata kikeyi?
Eh, ka isheni...go!
Wannan karon dariya sosai yayi, shikenan ba damuwa.
Zaki Kuma nemane ai.
Ta Mika mishi ledar bayan ya zauna kaci yau kaci gobe acici.
Wannan lokacin tare sukayi dariya.
Ta wuce tabarsu anan.
Tana niyyar tsallakawa titi ne suka suka zo zasu wuce yace: *A ringa duba titi*
Ta mishi murmushi kawai tare da daga hannu.
Haka kawai ta tsinci kanta cikin wani irin matsanan cin farin ciki,
Shi kuwa Anwar gaba daya ya kasa fassara yanayin da yake ciki haka kawai fuskar sa ta kasa daina guntuwar dariyar da yakeyi lokacin da suka daga ma juna hannu.
Anas ya rabka salati......Wai da gaske Bilkisu ta maka shopping yau ma?
Murmushi kawai yayi,
Sadeeq ya Kai mishi duka, munafuki kwa gama sumke sunken ku bayyana kanku, Daman na lura ka Fara tsanar Suleiman simply don Yana tare da ita, Kiri kiri dazun ka hanashi amsa wallahi baka kyauta ba Anwar........suka dunga mishi surutai ya musu banza miskilin bai dai ce kunyi gaskiya ba bai Kuma karyata su ba.
Duk abinda Bilkisu Bata so Yanzu kafa biyu Anwar gudun sa yakeyi.
Ba Wai ajin nasu kadai ba har takai aji daya ma nemansa sukeyi don ya koya musu.
Maimakon hakan yayi wa Bilkisun dadi sai ya kasance kullum cikin fada da rigima sukeyi musamman idan ta ganshi tsundum cikin mata sun saka Shi tsakiya kamar tayi hauka sai su kwana biyu uku Bata mishi magana ba Shi Kuma ya rasa dalili.
Idan kuwa ya kuskure ya dauki hoto da wasu to sai sun kusa sati bai sanyata ido ba, ko lecture sai dai tasa a mata attendance.
Ya rasa inda zai saka kansa.
Taki yarda suyi magana daya nemeta sai ta zille,
Yan mata sunyo mishi chaaaaaa har Yan wasu department ashe daman ko wace ta ciki na ciki rashin bada fuska ne.
Hakan ya Kara harzuka Bilkisu Jin kowa Anwar .... Anwar.
Gashi ta riga ta Saba da bayanin sa, duk Wanda zai mata sai dai ya Gama babatunsa Amma Sam Bata fahimta.
Shi kansa yana bala'in son koya mata.
Ranar Alhamis ana fitowa lecture tana kokarin fita ya tare kofa ya maida ya kulle.......gaba daya ajin akayo masu chaaaaaa da ido.
Kamar ta bude kasa ta shige don kunya.....ke me na Miki kike fushi Dani?, Na gaji da fadan hakanan wallahi mu shirya.......Dan Allah bani wuri in wuce ji yanda kasa ake kallona.
Duk wannan mazuran naki yau bazasuyi tasiri ba sai kin fada mun Yanzu Kuma laifin me nayi naga abun naki Dada hauhawa yakeyi.
Ta kalleshi sama da kasa , sai naji zafin makara tukun ta ja kofar da karfi ta fice ya bita a fusace saboda yaji haushin abinda tayi...
Wai Bilkisu me na Miki haka? Ko kin gaji dani ne kina son in Baki wuri in kyaleki?
Yau kusan kwana uku Ina kokarin kizo muyi karatu kina zillewa.......ta dallo mishi manyan idanun ta, yaushe kake da wannan lokacin?
Ai Yanzu mutane sun Fara maka yawa batani kake ba......Nan da Nan ya sauko zuciyarsa tayi sanyi kalau sauran kadan dariya ma ta kubce mishi Wai yarinyar nan badai kishi ke damunta ba?
Ya tari gabanta.....jira muyi magana daina tafiya.
Wallahi tallahi Ina da lokacin ki, basune suke zuwa na koya musu ba?
Ke kuwa nemanki nakeyi ko ranar Monday nace ki jira Ina son ganin ki kawai Kika gudu Kuma kece kemun fadan Ina sharesu da farko Yanzu kulawar ce zata haddasa Mana matsala?
Gabanta ya Fadi kada fa ya mata fassara.
Ta Fara in..in..in.
Bude Baki kiyi magana. Idan har Baki son in koya ma kowa wallahi daga yau na daina.
Ni Yanzu Kika ce Babu ruwan ki Dani Bilkisu ai na shiga uku waye zai ringa siya mun kayan dadi?
Bata San lokacin da ta yi dariya ba.
Shima dariyar yayi...kiyi hakuri na tuba bazan Kara ba. Daga Yanzu matukar kina son time dina ko wane lokaci ne Zan baki Ina ce Daman shine damuwar ko?
Ta Dan zumburo Baki eh.
Yayi murmushi, Zan kiyaye. Yanzu Ina zakije?
Daki.
Karatun fa?
Tayi shiru,
Kinji?
Ko har Yanzu Baki huce ba?.....
Kai Dan Allah. Ta fada tana Yar dariya.
To muje muyi ko sai anjima?
Eh,
Da karfe nawa?
Hudu.
Yanzu meye zakiyi idan kinje dakin?
Girki.
To zanci. Kizo mun dashi 4 din.
Okay.
In rakaki ko in kyaleki?
Kyaleni kada ka janyo mun duka gun Yan......maganar ta makale.
Ya zaro ido gun wa? Karasa Mana.
Tayi Yar dariya kawai, ya kuwa bita da kallo har tayi nisa........ Kyaleta hakanan tunda tayi nisa maye. Sadeeq ya gani gabansa.
Ya dunkule hannu zai Kai mishi duka ya goje.
Zanci ubanka ne, na gaji da wannan sa idon naka Kuma da alama kaman Bilkisu kawai kake man wannan shisshigin.
Kai mugu ai na lura kwana biyu baka da sukuni saboda ta Fara daina kulaka.
Mtsew you are not well, ya fada tare da barinshi wurin tsaye .
**************
*KADUNA RIGASA*
Ya Fara dukan kofar kamar mahaukaci, Amira Ni Zaki rufewa kofa?
Naje na rufe, Daman baka shirya ma irin wannan ranar ba da mace zata hanaka barci ka karo auren?
Idan laifi kayi mata sai ka koma ka Bata hakuri ku sasanta da matar ka...idan kuma ita ce ke da laifi sai ka koyi yanda ake hukunta mace dai dai laifinta ba ka kaurace mata ba.
Kaine ka kawo dokar Banda raba kwana Koda za'ayi soke soken wuka...au fadan na maganganu ka kasa dauka har Kaine yau zaka karya dokar ka da kanka?.......Amira ki dubi girman Allah ki buden kofa zuciyata na iya bugawa......
Wallahi bazan bude ba saboda hakan haramun ne a wurin ka dani.
Ka koma can dakin matar ka.....watan idan ana dadi zanji shiru sai ta baci .......kada kishi ya janyo kiyi mun butulci.
Butulci ai Kai ne kayi mun tunda har ka iya hango wata bayan ni.......kasa daurewa yayi yabar gidan a fusace.........Ya duba agogo karfe Sha daya saura, ya kuwa Danna Kira......
Bugu biyu ya dauka.
Hello Abokina ya?
Kazo gidana Yanzu Ina nemanka, Ummi na bani matsala mukhtar.
Gabansa ya Fadi yasan a rina, ko a gida Ummi bata da kunya ta Raina kowa.
Cikin mintuna Sha shidda ya karaso.
A waje ya tareshi saboda tun fitar sa zuwa gidan Amira itama ta garkame side din nasa.
Tare da mukhtar din sukayi ta dukan kofa Amma taking budewa su duka suka hasala.
Cikin fushi ya kalleshi Abokina gobe kawai ka maido Yar iska gida idan ta dandana zaman gidan a matsayin zawarci ......bani sakinta wallahi. Ya katseshi.
To ka mayar da ita duk da haka ka Bata hutu kamar na wata guda taji taji. Kuma kada kaje ka Bari Ni Zan ma su hajiya bayani babu ruwanka.
Yayi shiruuuuuuuuu......ya ka sa magana Yana dai nazari.
Ayi ta hakuri kaman yarda na ce Ina da hidindimu Shi yasa
*Zainab wowo ce*...✍🏼💖