🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣0⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
************
*KADUNA RIGASA*
Tun daga bakin gate yake jiyo kamshi, mamaki ya cika Shi, shin ko yayi batan lissafi ne gidan Amira yake ba Ummi ba?
Tana tsaye cikin Riga da skirt na leshi tasha ado ya shigo.
Da gudu ta rungumeshi yaji wani tsammmmmmm...... Anya Ummi ce?
Nan danan ta Fara sabon salo. Shigowa yayi kawai ya ajiye jaka ya wuce wurin Amira sannan ya dawo Amma inaaaa tuni hankalin ya karkata........ Bayan yayi wanka, ta zauna tana bashi abinci kamar yaron goye tun a daki da ya motsa sai ta bashi hakuri yanzun ma tana bashi abincin tana Kara lallashi duk ya sukukunce ya rikice.
Ya kalleta wallahi Ummi Ina sonki, kawai halayenki ne suka Sanya mun ko kwanto a zuciya Shi.......ta rufe bakin da chokaci ta debo peppé soup, sorry my love zaka ga changi I promise...... Ai na ga changi wallahi please keep it up.......
Amira Bata Sanya Shi ido ba sai bayan isha'i ta gama kulewa ta Kai karshe.........
**************
*Federal University dutsinma*
Kowa yasan sadeeq baida fitina, murmushi kawai yayi yabarshi a wurin yana babatu.
Sai kawai ya Fara fushi dashi.
Cikin bacin rai sadeeq ya samu Anas, Yana fada mishi abinda Anwar din yayi mishi Kashi na biyu akan Bilkisu.
Yaja guntun tsaki, kayi hakuri sadeeq wallahi *So* ke wahalar dasu duka for now ka bashi time zai nemeka.
Tun daga ranar Bilkisu ta koma sadeeq ke nuna mata, sun kyale Anwar.
Hankalin Anwar yayi matukar tashi ga exams na karatowa, hanya ma idan ta hango shi canzawa takeyi.
Ya rasa inda zai saka ransa.
Ko kallo bai isheta ba. Idan ta zo school amma tana komawa daki zata ci kukan ta tayi ma'ishi.
Yanzu fa kowa ya fahimci an bata Bilkisu da Anwar. Tsalle da Murna mufeeda ta ringa yi.
Tana zaune class za'a yi lecture ya shigo.
Yana ganin ta yayi saurin shiga sit din zai zauna kusa da ita...... Sai da ya karaso gaf! Daman can karshe take sai kawai ta kwashi kayanta ta dora waya a kunne , helllooo....yes inajinki.
Tayi waje kamar me amsa wayar gaske.
Tana fita tayi jimmm sannan ta dawo tare da canza layi ma gaba daya.
Ransa ya baci, hankalin sa ya Kara tashi, kowa ya fahimci abinda tayi.
Sam ta rage fara'a in kaga tana dariya to tare take da Suleiman.
Ana gama lecture ya tsaya bakin kofa yasa hannu duk Wanda zai fita sai ya mishi magana, tana ganin haka ta yi zamanta, Shima ya ayyana a ransa wallahi yau Kam sai dai su kwana haka.
Masu shigowa da masu fita kowa sai ya mishi magana sannan.
Ta dawo gaban sit suna magana da chinyere, tayi sa'a ya juya suna magana da wani dan aji daya da alama bayani yakeyi mishi har ya manta ya saki hannu Yana magana cikin nuni da hannu....tayi wuf, ta wuce ko alama bai lura ba sai da tayi nisa ya waiga class din da sauri ya tabbatar lallai ita ce.........wani mugun tsoki yaja tare da dunkule hannu ya daki bango har yaron ya tsorata.
Cikin tsawa yace yaron ya bace mishi da gani.....
Daki ya tarar da sadeeq nacin abinci. Yasa chokali kawai Shima, ya kalleshi malam zaka Sanya mun Rani.....dama jira yakeyi yayi magana ko sa shirya.
Anje an Sanya.
Ya Galla mishi harara kawai.
Anwar din ya rike kunnuwa biyu am sorry my friend pls sorry.
Murmushi sadeeq din yayi kawai.
Ya Fara magiya, har Anas ya shigo yasa baki.
Nan da nan aka koma normal.
Ya kallesu kamar zaiyi kuka. Dan Allah ku shiryani da Bilkisu yarinyar nan tayi fushi dani sosai.
Wallahi nayi tunanin bayan kwana biyu zata bani hakuri shikenan komai ya wuce ashe ita zafin nata yafi nawa......
Anas ya harareshi, kunfi kusa, a da idan kunyi fadan ku waye ke shirya ki?
Wallahi tsoronta nake yanzu, bana iya tunkarar ta ku taimaka ku shirya mu....
Zamu jaraba gobe....inji sadeeq.
Duk an Fara covering ana shirye shiryen tafiya sallah break ( babbar sallah ), da andawo Kuma da sati za'a Fara exam.
Tana zaune can baya sadeeq ya sameta.
Bayan sun gama gaisawa ya kalleta.
Bilkisu ya kamata ku shirya keda Anwar fadan ya Isa hakanan Dan Allah Kinga....... Mikewa tayi tsaye, tace, sadeeq Ina ganin kimarka da mutunci wallahi duk ranar da ka Kara mun maganar Anwar kaima Zan daina magana dakai har nabar makarantar Nan.........ta kwashi books dinta lecture din da bata dauka ba kenan ranar.
Gaban Anwar sai faduwa yakeyi...... Tana fita ya koma inda ta tashi... Yaya?
Sadeeq din ya bata rai tare da fada mishi abinda tace, sai kawai ya dora Kai bisa table yayi shiruuuu!
Ya dan sunkuya da Kai Anwar idan kana son yarinyar nan ka sameta ku daidaita........mtseww Shima ya figi takardu yayi waje....ya bishi da ido yace ikon Allah!
Anas ya taso Yana dariya...... sadeeq ma ya kyalkyace da dariya suka tafa.
Ni naga karshen wannan girman Kan nasu, ko wane ta ciki na ciki sai wahalar da juna ake....
Laifin Anwar ne kasan Allah sadeeq maganinsa Bilkisu.
Bashi da aiki sai dai ya dauko waya yayi ma sunan ta zuruu Yana kallo. Text din da ta mishi na birthday ya Zama tamkar paracetamol ga Mai ciwon Kai.
Kwance yake ruf da ciki suka iso, Anas ya tabo Shi ...abokina barci kakeyi?
Ya tashi firgigi yace no, Ina jinku kawai na kwanta ne na huta Yaya?
Ya Mika mishi littafi exercise question din nan zaka solver Mana please...... Wallahi tallahi bazan kara koya ma kowa ba school din nan inbaku shiryani da Bilkisu ba.....hada rantsuwa sadeeq ya zaro ido.
Kana wasa ko?
Ya Kara Bata rai try me and see. Ya koma ya kife a katifa.
Nan da nan suka shiga damuwa, Anas ya kalli sadeeq lallai abun nan ya girmama.
Sadeeq ya nisaaa, kagane kamata yayi mu Sami Suleiman da Helen muje mu Kara bata hakuri kasan Dan iskan yaron nan fa zai Kira Mana ruwa mu shiga uku.
Yana zaune ya ajiye littafi alamar ita ya ajiyewa sit sakamakon ita ce lecture karshe kowa yayi covering shine yayi saura.
Suka Mika mishi hannuwa ya bisu da ido Yana mamaki saboda yasan clique din su basu daukeshi bakin komai ba har gara gara sadeeq suna gaisawa jefi jefi idan Yana tare da Bilkisu.
Suleiman wannan zuwan naka ne,
Toh, gani lafiya dai ko?
Da sauki gaskiya, akan Anwar ne da Bilkisu ya rantse cewa duk semester din Nan ba Wanda zai karu dashi matukar ba'a shirya su da ita ba Kuma wallahi ni dana Mata magana cewa tayi na Kara Nima zata daina mun magana.
Murmushi kawai yayi.
Anas yayi karaf! Yace, shine muka yanke shawara mu sameka Dan Allah kasa Baki muje mu Bata hakuri.
Ya Kara murmushi okay ba damuwa.
Har aka tashi class bata zo ba,kawai suka yanke shawarar zuwa gida su sameta .
Aisha ta Fara haduwa dasu ta fito da alama garin zata bari take shaida masu ai tun karfe bakwai Bilkisun ta tafi Kano zata hau jirgi ta tafi Abuja..........
Kofin dake hannun Anwar ya Fadi ji kake tartsatsatsa...... Lokacin da Anas ke Mata bayani.
Ya kallesu asanyaye... shikenan tunda ta tafi.
Washe gari Shima suka tafi.
Abinda yafi komai bata mishi rai shine bata chatting, ya Kira duk wadanda suke tare ko tana da wani layin na daban Amma sunce layinta daya ne kwal!
Ba abinda ta boye ma mommy hada kukanta.
Yar dariya kawai tayi tace zaku shirya karatu ya gaji haka.......zumburar baki tayi kawai ta wuce ciki.
Shima ya kasa sukuni, ya gama ayyana ma ransa dole ya kirata ranar sallah ya Mata Barka da sallah tunda ranar kowa na cikin farinciki yasan dole ta saurareshi Kuma ta sauko.
Hakan kuwa akayi, misalin Sha daya na safe taci kwalliya tana tsaye kitchen tana zuba gasassar hanta a plate Kiran ya shigo.....
*Anwar* shine abinda true caller ta nuna Mata, kamar zata ki dauka sai Kuma ta tuna gara ta dauka ya gane cewar ko number sa bata dashi ........
Assalamu alaikum. Ta fada a hankali.......luuuuu ya tafi tare da lumshe ido kafin yace wa'alaiki Salam *Barka da sallah*....... Wake magana?
Ta bukata a dake,
Ya zaro ido kamar tana kallonsa.... Bilkisu kin goge number ta?
Tayi shiru kwalla sun taru idonta....
Kinji? Na ce kin goge number ta awayarki?
Kwallah suka shatato Mata tayi tsoki kawai ta kashe wayar......yace what???
Ya Kara Kira.
Tana kallo taki dauka sai da yayi missed call biyar amma Bata dauka ba.
Ya dankara wayar a kasa ta tarwatse sannan ya dafe Kai saboda juya mishi da yakeyi.
Ita kuwa sadadawa tayi zuwa dakinta taci kuka Mai isar ta tukun sai bayan azahar ta fito Shima fa'iza ce ta kirawo ta su fito zasu tafi millennium Park duka gidan.
Tambayar duniya gida Anyi ma Anwar cewar meke damunsa amma yace ba komai fargabar jarabawa ce .
Sati daya ya koma school ita kuwa sai ana gobe jarabawa sannan.
Don haka basu hadu ba sai dakin jarabawa, ya hangota can gaba, tun kafin su shiga sadeeq ya fada ma Suleiman ya tsaidata ko ta gama don su ganta.
Sai gashi ma duk sun rigata fitowa har Anwar din.
Ya tafi can nesa bakin bedi ya tsaya su Kuma suna gaban class suna jiranta.
Suleiman man ya Fara tarar ta sannan sauran suka matso aka Mata zobe .
Ya kalli kowa, sannan ya kalleta wannan zuwan naki ne fa, Dan Allah kiyi hakuri ku shirya da Anwar haka nan kinji yace matukar ba'a shirya ku ba ya gama koya ma kowa karatu........and then?
Sai su dage su koya da kansu Shima ba da iyawa aka haifeshi ba, Suleiman ka fita maganar Nan ba huruminka bane.......ta juya tayi tafiyar ta.
Anas ya zaro ido.... Suleiman ya kallesu Yana murmushi ku Kyaleta Zan lallabeta zasu shirya...... please try your best Dan Allah sadeeq ya fada tana wucewa Anwar ya karaso. Yaya?
Anas ya dankara mishi harara yayi gaba kawai.
Hankalin sa ya Kara tashi jin ba wata nasara. Amma Suleiman din ya masu alkawarin zai shawo kanta.Hankalin kowa a tashe yake cikin department ganin da gaske Anwar yake bazai koya ma kowa ba matukar bai shirya da Bilkisu ba.
Ya daina ma kowa dariya tun su sadeeq na daukar abin wasa har suka ga lallai da gasken gaske yake fa.
Ba Wanda ke iya tunkarar sa, idanun sa cikin facing cap yake shigowa Yana rubuta jarabawar za a nemeshi a rasa.
Courses din ana Shan wahalar su, Bilkisu kuwa tuni ta sadakas, idan tana ta exam 3 tun 7 take shiga library sallah kawai ke fiddo ta. A cewar ta in kaji maraya raggo.
Bai taba tunanin Bilkisu zatayi wannan zuciyar ba Yana tunanin yanda ta Saba da tutorial din sa bazata taba karatu babu Shi ba.
Sun Sami interval na kwana daya, da marece tana class tana karatu Suleiman yazo.
Suka Fara karatun tare...... Wani wuri ya Dan kakare masu.
Yayi murmushi Kinga da kin huce da duk wannan wahalar bamu Sha ta gashi kinja ma kowa, Anwar...... Suleiman ka kasa ganewa na fada maka wallahi ko sunan Anwar bana son inji an fada.....
Saboda me?
Ni bakiyi mun adalci ba wallahi sai nake ganin kamar bani da kima ko mutunci a idon ki, tunda ya Baki hakuri Nima na Baki sai ki......yaushe ya bani hakuri? Wallahi bai bani hakuri ba.
Mutane nawa ya Aiko Miki?
To ai mutane kace Shi in person baizo ba ta Yaya Zan San cewar ya gane kuskuren sa?
...... Yanzu idan yazo da kansa ya Baki hakuri Zaki hakura ku koma normal?......
Tayi shiruuuuu.... Me yasa Suleiman zai Sanya ta kwana.
Kinji? Dan Allah Ina son Anwar yaci albarkaci na ki yi hakuri Kinga Yanzu idan ya dauke hannunsa ga kowa tabbas an Sami matsala Kuma kece sila...... Ni?
Yayi murmushi, kiyi hakuri Bilkisu Yanzu dai, Dan Allah kiyi hakuri.
Ya Gama daureta ta ko'ina, tafi mintuna hudu bata ce komai ba.
Ya Kara kallon ta, Ni zakiyi ma wannan alfarmar ba kowa ba kiyi hakuri.
Kwalla suka suka zuba Mata...... Ta mayar dasu da karfin tsiya sannan ta ce shikenan ya wuce...... Ya zaburo, kin hakura?
Eh, amma ka sani saboda Kai...... Na sani wallahi. Na sani Bilkisu na gode na gode words cannot express my gratitude.
Suka jero tare ya rakata har bakin gida sannan ya tafi.
Hostel yayi ma tsinke, kamar daga sama suka ganshi karon farko da ya taba zuwa dakinsu.
Anwar na kishingide Koda Suleiman man din ya shigo ya maida ido ya rufe kunnen sa like da ear piece, ba wani music da ya kunna duk Yana jinsu,
Sadeeq ya fadada murmushi wannan babban bako ne sannu da zuwa Suleiman. Ya ce yawwa tare da Mika ma kowa hannu Banda Anwar.
Ya kalli sadeeq muje in ganka...... Suka fita tare.
Anas ya kaima Anwar duka Amma Kai Dan iska ne wallahi. Yaron nannya shigo don wulakanci shine ka rufe ido Dan ubanka..... Mtsew yaja tsoki kawai.
Ya kalli sadeeq, na shawo Kan mutuniyar ku, ta hakura ta ce komai ya wuce sai ka fadawa Anwar din saboda kasan........ya riko hannunsa duka biyunKace wallahi......
Yayi murmushi wallahi kuwa. Amma Suleiman mun gode Allah yabar zumunci dama inata zullumi ranar juma'a za ayi econometrics gashi yayi burus da kowa.....Ya Mika mishi hannu suka Kara gaisawa sannan yace mun gode fa bari naje na mishi albishir .....ya koma daki da sauri.
Kallo yayi ma sadeeq ya watsar.
Ni kakeyi ma wannan Dan iskan kallon? To Suleiman zuwa yayi ya fada Mana ya shawo Kan Bilkisu tace ta hakura zaku koma normal.......zumbur ya Mike... Are you serious????
Ya galla mishi harara na ban sani ba kaga wulakancin da kayi mashi da yazo ko kallo......forger about that please ta hakura????
Anas yaja dogon tsoki sai kaje ka fada Mata ka kusa mutuwa..... Ya kyalkyace da dariya a'a ka manta mutuwar nayi.
Eh Mana, Kuna ta wahalar da kanku a banza....... We are just friends jor what are you talking about???
Ai maganin sa Bilkisun, nifa yarinyar ta bala'in birgeni wallahi ta nuna mishi ita din ta daban ce......Anas ya fada Yana Kara doka mishi harara.
Ya lumshe ido ya koma ta baya ya kwanta...ku yau kuka San Bilkisu ta dabance ko?
Duk suka dunkule hannu suka Kai mishi duka ... sadeeq yace asirinka dai ya tonu munafuki.....ya Kara bushewa da dariya.
Washegari suna da exam 3, karfe biyu ta fito library jikin wata bishiya bisa kujera ta Kira Suleiman...... Hello ka shigo?
Eh, kina Ina ne?
Ina ta wajen library wallahi na kasa game wannan last part din, zo kamun dalla dalla please..... Okay Ina zuwa.
Ashe tun karfe tara suna tare da Anwar Yana koya musu a class, ya kalleshi cikin kosawa.......Yaya?
Dariya yayi kafin yace, last part din nan ne bata gane ba take so na nuna......tashi muje ya Mike.....
Anas ya kalleshi Dan uwarka mu Kuma fa ?
Ya dalla mishi harara ku gane ...yayi waje.
Daga nesa ta hangosu , tayi saurin boyewa bayan bishiya sannan ta saka wayar ta Airplane mode.
Tana kallonsu sai safa da marwa sukeyi amma ta boye. Har kusan uku saura kwata sannan ta hangosu sunyi hanyar class din da zasuyi jarabawar......... Watan Suleiman kiranshi yayi ko? Ta buga tsoki.
Lokacin da ta Isa har sun zauna invigilators sunzo, ta shiga...idon sa na kanta, Koda wasa Bata yarda ta kalli inda yake ba, Suleiman na bayansa ya Dan gyara alamar ta zauna sai kawai ta wuce kamar bata lura ba.
Ana gama jarabawar, tayi saurin submitting tabar shiyyar.
Suleiman na fitowa ya kamo hannun sa, kaga ta tafi ko?
Murmushi kawai yayi.
Abu kamar wasa har saura exam uku su gama amma Bata yarda sun hadu ba.
Ya Sami Suleiman kamar zai mishi kuka yace shifa bai gane ba.
Dole ya sameta yace Dan Allah tayi hakuri ta saurareshi.
Tasha mur, au ni zan sameshi bashine zaizo yaban hakuri ba?...... Ohhh toooo kiyi hakuri zaizo, ta wuce abinta tabarshi wurin saboda yama bata haushi.
Suna rabuwa ya Kira Anwar din yace tace Shi baida bakin bata hakuri ne?
Gaban sa ya Fadi.....Anya zai iya tunkarar ta Yanzu Kam har ga Allah tsoron ta ma yakeyi.
Haka ya kwana dardarce, ko barci kirki ya kasayi da ya tuna sai ya yi firgigi ya tashi zumbur.
Jarabawar ta safe ce, farar shirt ya saka Mai kwala tana da ratsin ja, da farin jeans sai jar facing cap. Agogon hannun sa kirar *Rado* baka .
Ya rufe ido da makeken glass dinsa Baki. ( Anwar akwai kyau da iya wanka ).
Ba abinda gabansa keyi sai faduwa Anya zai iya mata magana?
Duk inda ya gitta sai an kalleshi ya wanku iyakar wanka sai kamshi ke tashi.
Yana tsaye jikin taga ya hangota sun taho tare dasu Aisha sai faman dariya sukeyi.
Ya bude littafi kamar Yana karatu amma ita kawai yake kallo.....tana matsowa kirjinshi na Kara bugawa.....kafin ta iso har invigilators sun iso, dole ya shiga hall din ya zauna.
Yana Zama tazo zata wuce yasa kafa tun daga nesa ta hango abinda yayi sai kawai tabi dayan layin.
Ya rigata fitowa, Banda faduwar gaba har Yar kyarma ya Fara lokacin da ya hango tana fitowa.
Ta zukunna gaban Helen tana fadin .....duba mun wannan shin sune characteristics din nan?.......
Kamar daga sama taking yace *Bilkisu*........
Gabanta ya bada rasss!!! Maganar ta makale Mata.......ya Kara kiranta a hankali Yana tsaye bayanta..... *Bilkisu*...........Zainab wowo ce✍🏼😄😄💖
Ayi hakuri da kadan
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣1⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
****************
*KADUNA RIGASA*
Ranta a bace amma Sam hankalinsa baya kanta sauri sauri yakeyi daman tun da ya iso an shigo Mata da tsarabun da yayo.
Gabanta ya fadi, wannan rawar kafar ta mecece?
Ta daure ta dan boye fushin ta, kafin tace : Wai lafiyar ka kuwa?
Yau ka dawo sai Yanzu ka shigo nan Kuma kana ta wani sauri sauri........ Nan da Nan guiltiness ya kamashi, ya Fara Yan kame kame..... Nan da nan ta gano bakin zaren tayi murmushi ko hada gajiya halan?..... Ya kakaro murmushi gajiyar ma ce gaskiya.
Gaskiya ne.
Ta Mike , mu kwana lafiya kaje ka huta......wuf Shima ya Mike Daman jira yakeyi yayi waje Yana fadin Allah ya tashe mu lafiya.
Ta bishi da ido kawai, lallai namiji akala ne, ta kuta zaka gane kirenka ka gama kwanakin ka dawo...amma zanje in ga kalar wainar da ake toyawa.
Ummi nada tsawo Kuma doguwa ce tafi Amira .
Ita kuwa Amira irin Dan jikin Nan gareta Mai kyau da tsari, kallo daya Kai kace ummi keda Yara biyu ba ita ba.
Tana gyara jikin ta don ko tsakanin Ahmad da almustapha shekara biyar ne.
Ta bashi kamar mintuna arba'in kafin ta saka bakar jallabiya matsattsa tabi jikinta da turaren da ya fi so ta nufi sashen sa don ta San Yanzu suna can.
Ta danna karaurawa, ummin ce ta zo ta Dan leka.....ta kalleshi tare da yin Yar dariya *Yaya Amira* ce.
Oya bude ya fada Yana kishingide Yana Shan kankana.
Ummi na sanye da dogon wando jeans ya matse ta da Yar matsattsar Riga kanta ba kallabi ta yi kitso shuku Wanda ta daure da katon ribom saboda karancin gashi .
Ta kalli ummin sama da kasa sannan ta danyi murmushi sorry for disturbance please.....laaa ba komi karaso ciki.
Ya tashi zaune Yana Yar dariya Amira Yaya?
Tayi Yar dariya.....zuwa nayi in ji ka siyo mun book din nan kuwa dazun na mance in tambayeka......ohhh yes, Yana mota Bari na dauko Miki........ya yunkura..
A'a barshi kawo key din na dauko Yana ta wajen Ina?
Wurin Mai tuki jikin kofa Yana Nan....Ummi dauko key din.
Ta Mike.
Ya Kura Mata ido, Yana son tayi shigar doguwar Riga, wannan kamshin zuwa akayi ayi mun kwalele?
Good and fine, ta ce cikin zuciya, sannan tayi murmushi ta ce hmm kawai.
Kinji?
Gobe zanje kasuwa Dan Allah da safe ba dadewa zanyi ba, Zan biya gidan Salma.....me akeyi gidan salmar?
Ta dan mishi warrrr da ido, zumunci......duk sai ya diririce, Ni Zan kaiki ko?
Ta Dan Kara farrr da ido tare da Yar dariya, lokacin da Zan fita bana tunanin ka tashi cos by 8 nake son zuwa kasuwa Kuma Kai ba ma'abocin son zuwa kasuwa bane.....Zan biki please.
Saura kadan ta tuntsure da dariya yanayin yanda yayi maganar. Ta danyi murmushi.....Ummi ce ta fito da key.
Ta mike Bari na dauko book na.
Ya bita da ido Ummi ta dankara mishi harara Amma Sam bai lura ba.
Bude tabar kofar tana dawowa Bata shigo ba ta tsaya bakin kofa....ga key din Ummi, ....wuf ya Mike Bari na karbo.
Tana daga waje ya hada da key din da hannun ya rike in fito goben muje?
Nooo, kaga Ummi zata ji haushi kayi hakuri ka bata full time dinta don nima turn Dina.....ya murza hannun da karfi.
Tayi Yar Kara, ya dawo Yana dariya...... Ummi kamar zata fashe amma ta daure ta cije duk da haka sai da ya danga chanji amma sai kawai ya share.
Butique ta tafi, ta siyo rantsattsun English wear sabbi hada three quarters wando da skirt da crazy jeans.
Har ta dawo wajen Sha daya bai fito ba.
Ta fada wanka Yara sun tafi islamiya tahfeez, ta kulle kofar ciki tabar Mai aikin ta kitchen tana fita ta kofar baya.
Amira nada gashi sosai, kanta kananan kalaba ne duk sun zuba bisa bayanta wani sky blue crazy ta saka da wata crazy riga Mai hannu daya nononta kawai rigar ta rufe kasan ta Kuma bazace, ta cikin Bazar kana hango cibinta.
Kamshi kawai ke tashi gidan.
Sha biyu saura ya fito, motar ta kawai ya gani yasan ta dawo.
Ya nufi bangaren nata don agaisa.
Tana Jin motsin sa ta ruga daki ta dawo rike da littafi kamar me karatu ita a dole bataji shigowar sa ba.
Mutuwar tsaye yayi ya kusa sarkewa da miyau sai kawai taji Yana tari.....ta dago Kai da sauri irin ta razana din nan.......
*****************
*Federal University dutsinma*
.....Ta kasa dagowa ta amsa, jikinta ya Fara Yar kyarma.
Helen ta kalleta, Anwar na Miki magana...
A hankali ta juya kamar Mai ciwon wuya , idanun sa cikin glass Yana Dan murmushi........ Minti biyu. Ya fada kafin ya juya ya Fara tafiya can nesa wurin parking motoci.
Ta Mike jikinta duk ya mutu tabi bayansa.
Jingina yayi da mota hannuwan sa duka cikin aljihu ya kura Mata ido.
Kanta a kasa ta karaso fuskar ta babu yabo ba fallasa. Ta kasa magana.... Ya Kara nutsar da idanun sa gareta yace: Ranki ya dade ya exam din?
Ta danyi murmushi kadan Alhamdulillah...Ina kwana.
Lafiya Lau, na Aiko a Baki hakuri kina ta ba mutane wahala kince dole sai nazo da kaina to gani nazo.
Ta Kara kasa da Kai tana murmushi...... ban taba tunanin zakiyi fushi haka dani ba ko kadan.
Tayi shiru dai,
Har kiranki nayi da sallah without knowing u deleted my number....... Shikenan dai ya wuce. Ta fada a hankali.
Kin tabbatar ya wuce?
Eh,
Mun shirya?
Sai kawai tayi Yar dariya saboda yanda yayi tambayar kamar wani karamin yaro.
Yabi fuskar da kallo...... Ji yakeyi kamar ya kamota ya rungume... Yayi murmushi kinji mun shirya Yanzu ko?
Eh,
To na gode, Zan kiyaye daga yau Allah ya Kara Baki hakuri shikenan ko?
Um, tace a takaice.
Ina zakije yanzu?
Gida Zan tafi.
To muje na rakaki ..... A'a barshi kawai na gode, ta katse shi tare da yin gaba abinta.
Ya bita da kallo baya so ta tafi ko kadan.
Ya hura iska.... nawaoooo yarinyar nan miskila ce ta karshe.
Wani sanyi zuciyar ta keyi mata, tana zuwa daki ta fada bisa katifa ta rungume filo ta maida idanu ta rufe a hankali.
Su Anas suka bushe da dariya, ya cire glass Yana hararar su , Helen na bayansu, tana so taji yanda akayi.
Munafuki sai kace yau neman shiri zakayi Shi yasa tun karfe biyar ka yo wanka kana faman shiri.
Mtsew yaja guntun tsaki, suka jera suna tafiya.
Ya kalli Helen din dake kokarin jerawa da su yace ke kuma lafiya kike faman binmu?
Kamar za ta nutse dan kunya, ta juya kawai ta koma...... Sadeeq ya harareshi wallahi ka daina dizga mutane haka Anwar.
Ya maida glass din a idon sa, inba gulma ba ubanwa zatayi cikin mu?
Kasan tun dazun ina tsaye da Bilkisu hankalin ta na nan?
Kayi mamaki ne? Inji Anas.
Waye bai San ta mutu kanka ba...... Ban san abinda kuka mayar dani school din nan ba. Ko wace jik and jak Sona takeyi? Mtseww kada kusanya inci ubanta da kyau fa. Mufeeda ma ta gama haukanta ta shafan lafiya bare wata arniya....... Kada ka taba yarinyar mutane arnan can sun fika hauka..... Ko in gwada? Muga cikin mu wa ya darar ma wani?
.......Anas ya zaburo Kar ka Soma wallahi. Babu ruwanka da ita baka San tana yi ba kawai ka ci gaba da nuna Mata baka ganeba.
Naji! Ya fada a takaice.
Yaushe zaka Mana bayanin Economic of production?
4, yace a takaice.
4, Kuma?
Eh, saboda zanje wani wuri da daddare.......duk suka kalleshi.
Yanzu barci zanyi, 4 Kuma sai muyi zuwa magrib ko bai muku ba?
Amma ai yau ba ball ina zakaje ne?.... Murmushi kawai yayi.
Suka Kara binsa da ido.
Wai lafiya? Ya bukata Yana Yar dariya.
Ina zaka je muka ce?
Wanda zai bini ya shirya ban hanaku ba.....
Duk sukayi shiru, suna kallon kallo.
Ya kyalkyace da dariya wallahi ku munafukai ne...... sadeeq ya Kai mishi duka wallahi baka da gaskiya.
Ya kyalkyace da dariya.
Mashin daya suka hau.
Dakin acike bai samu ya yi barcin ba daga wannan sai wannan, ya gaji matuka. Shi ba koyawa ko bayani ke baya son yi ba, cin lokacin sa da akeyi ke sanya Shi kosawa.
Sai da yayi wanka sannan ya Fara shiri cikin farin boyel ya dauko hudaddun takalma ya saka na fata *masarati*, yana cikin sharce gashi suka shigo.
Duk suka zaro ido..... Ya fiddo turaruka ya shiga fesawa kusurwa kusurwa, lungu lungu.
Sadeeq ya kalleshi *Anwar Ina zaka je?*
Bai ma kowa magana ba ya Mike, har ya Kai bakin kofa ya waigo ku bakwa ganin karuwa da danta baku tambayi ubansa ba.
*Zance Zan je*....... Ya fice da sauri suka Fara surma mishi zagi.
Yana tafe Yana tunanin Yanzu kuwa Yana zuwa ya tarar tana tare da wani to ya zai yi?
Ya tofar da miyau, Wai kada abin ya Zama gaskiya.
Mashin din Salim, roba roba ya karba.
A bakin gidan yayi farking ya kafe mashin din tare da Zama saman Shi kamar kujera sannan ya Kira wayar ta, tana kwance da Yar shimi ta barci rike da littafi tana karatu wayar tayi Kara........ Tunanin ta mommy ce.
Ta muskuta, Ba tare da ta kalli screen din ba tace.
Mommy.....
Mommy Kuma? Ya bukata.
Ta zaro ido tare da kallon fuskar wayar sai akwai ta mayar a kunne....still Baki mayar da no. Ta ba ko?
Ya hakuri Ina wuni?
Gani waje Ina jiranki....... Waje Ina?
Kofar gidan ku.
Na shiga uku.....Bata San a fili ta fada ba sai da taji yace.....zuwan nawa ke da shiga uku?
Ta zaro ido. Duk ta diriri ce.
Ko baki maraba dani na juya?
Ina zuwa... Ta fada a hankali.
Jikinta yana ta Yar kyarma. Ohh ni Bilkisu ko lafiya?
Sauri sauri ta shirya ta zumbula hijabi har kasa ta fita.
Kallo daya tayi mishi tsikar jikinta ta tashi Yarrrr....
Anwar a manyan Kaya????
Tayi murmushi kunyar duniya ta kamata gabanta ya dunga faduwa tana zullumin me ya kawo Shi?
Ya tsareta da ido, yaki magana.
Ta dago Kai sai ta zumbure baki ta maida Shi kasa.
Yayi murmushi, haushi kikeji nazo saboda ba Suleiman bane ko?
Kallon sa tayi da sauri , ya Sha mur!
Kin tsaya kina ja mun class kamar irin nazo zancen nan.
Dariya tayi.
Yanzu dai Ina wuni, me ya kawo ka cikin tsohon Daren nan?
Yayi murmushi, zance nazo can baya na biyo mu gaisa ko ban kyauta ba?
Gabanta ya fadi, ta dan tsuke fuska. Hmm.
Ko ban kyauta ba?
Kayi daidai.
Ke baki iya tarar bako? Ko haka kikeyi wa Suleiman idan yazo?
Suleiman again? Ta ce cikin zuciya. Wai meye kake ta fadin Suleiman...... Ba Kya so long sunan sa na fada kada gabansa yayi ta faduwa?.
Ikon Allah ta fada.
Eh Mana. Gashi kin kasa sauraron kowa sai shine ya shirya mu....... Baka ji dadin hakan ba?
Ya Dan harareta meye tsakaninki dashi? Ki fada mun sirrin..... Anwar rigima kazo muyi ko kuwa zuwa kayi mu gaisa da gaske?
Duka biyun nazo yi.
Karatu nakeyi. Nasan kayi covering gobe ka Fara ansar extra sheet ina page 2 ina zare ido...... Suleiman zai Baki amsa.... Na shiga uku. Ta fada tare da kallon sa. Yasha mur, ko ruwa bazaki bani ba da gaske......juyawa tayi kawai.
Ya bita da kallo. Kwalin fresh milk ta fito da Shi da cup a hannu, gashi amma ba sanyi.
Ya karbi kofin ya Mika Mata alamar ta zubo mishi.
Ya tsareta da ido sai Yar kyakkyarwa takeyi.
Nayi kyau da manyan Kaya?
Ta tuntsure da dariya...... Yau naga ta kaina.
Shima dariyar yayi, to naji kin ki yabawa ..... Ta dalla mishi harara ita wacce kaje gurinta Bata yaba bane?.
Ya Kai kofin bakinsa yasha kafin yace, ta yaba tayi comments kema kiyi naki.
Har zata ce ni budurwar ka ce sai Kuma tayi shiru kada yace *Eh* tafi so *YA FURTA* Da bakin sa.
Me yasa baki WhatsApp?
Hakanan.
Bai yiwuwa , saboda duk Mai hankali baya abu babu dalili. Me yasa bakya yi?
Allah kawai bana son abun da zai daukar mun hankali daga karatun nan.
Muga wayar.......ta kalleshi.
Ya nutsar da idon sa cikin nata tayi saurin kawar da Kai.
Kada Inga text din Suleiman? Bazan shiga can ba......ta Mika mishi da sauri, yayi murmushi. Zan dawo Miki da ita gobe ya saka aljihu. Meye password din?
Ta zaro ido, Daddy na kirana every asubah..... don't worry I'll talk to him meye password din?.
Dan Allah ka bani saboda....... Saboda Suleiman bazaiji dadi ba? Sau nawa nake ganin ta a hannun sa?
Wai lafiyar Anwar kuwa meye Yanzu magana daya sai ya ambaci Suleiman????
Na rantse da Allah sau biyu ne, Kuma duk chargy ya kaimu ya Kuma karbo.......
Yasha mur meye password dinki?.
Gabanta ya Fadi duk ta rikice saboda ANWAR ne password din. Ya kalleta wallahi wurina wayar Nan yau zata kwana Kuma sai kin fada mun password din..........✍🏼😄
Zainab wowo ce 💖
Ayi hakuri da kadan. An dameni da cigiya 😄
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣2⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼 *Godiya ta musamman ga :*
*Mowa ( maimuna Nasir )*
*Hauwa'u, ( mum khady nima Ina kaunarki matuka*
*Da masu mun waya, text da kirana direct ku sani cewa zainab wowo Bata Raina masoya wlhi Ina kaunar ku sosai*
👉🏼 *Unex*💖
***************
*KADUNA RIGASA*
Ta dan rike kugu tana Yar rangwada.... Mura kakeyi haka?
Wuffff.... Ya riko kugunta, kece Zaki Sanya mun ita Yanzu, Ina Kika Sami kananan Kaya haka?
Sai faman shinshinarta yakeyi ya nutsar da kansa cikin wuyanta.
Tayi wani juyi tare da mayar da fuskar ta gab da tasa saboda ya sunkuyo tayi warrrr...... Kawai taji ya hada bakin sa da nata...... Fittt... ta fizge. Ta danyi baya tare da buga wani makirin tsalle rigar tayi sama cikinta ya fito fili..... Kanka qalau kuwa?
Ya yunkura zai Kara chafko ta tayi baya tana Yar dariya idanunsa sun kada sunyi jawur.... Ya kalleta kamar Mai Shirin yin kuka *Dan Allah ki tsaya bani da karfin binki ko'ina*.......
Amma kasan ba anan kake ba ko?
Ya langwabar da Kai, please one kiss.... Tabbb wlhi Haram. Ta fada tana wata karairaya.
Ya kura Mata ido duk hankalin sa ya tashi.... Amira kada ki hadu da fushin Allah ki tsaya....
To Yanzu....... Charaf! Taji ya damke ta cikin taku daya. Yana riketa ana dukan kofa da karfi.
Kafin yayi wani motsi ya jiyo muryar hajia ( mahaifiyar sa ) tana fadin Amira ko Bata ciki ne?.
Ya buga wani uban tsoki ya ingijeta ya wuce bedroom dinta da sauri.........
***************
*Federal University dutsinma*
It seems like baki da gaskiya fa!. Ya fada tare da tsareta da ido.
Ta dake ta kalleshi Yanzu dai Wayata ce zaka tafi da ita ko?
In shaa Allah, ya fada Yana murmushi.
Wai meye zakayi da wayata ne Anwar?, Bincike......., Ya fada Kai tsaye Yana kallonta, tayi shiruuuuu.......
Naji Zan baka, kawo na goge abu daya shikenan....menene?
Wallahi dana goge Zan baka hoto ne.....hoton Suleiman?
Ta doka tsoki Wai Kai komai Suleiman??????
Eh, ai kema komai shine....mtsewww to ba nashi bane nawa ne.
Kiyi hakuri bazan Baki ba don Ina son ganin hoton.
Ta Sha mur bani da Riga ne, Shi yasa da best Aisha ta daukemu muna cin abinci akwai hotuna da yawa nawa sai ka gaji da gani amma wannan bana son ka ganshi.......Ni Kuma naji Shi kadai nake son gani ma .....ta zaro ido. What?
Cikin fushi ta juya gara ta nade tabarmar kunya da hauka... shikenan sai da safe ka cinye wayar ko kaje wurin Yan gyaran waya su bude.....dawo dawo....zo ...zo..zo please. Gashi zo ki goge ya fada da sauri Yana fiddo wayar daga aljihu.
Ta kusa sakin dariya Amma ta daure ta Mika hannu okay bani.
Ya rike wayar yaki saki.....ki rantse da Allah ba text ko hoton wani Zaki goge ba...... Wai me ka daukeni ne?
Ya langwabar da kai hoton nawa Zaki goge?.... Ikon Allah ta fada duk ta Fara kosawa, guda daya ne ko?
Ta sakar mishi wayar ganin baida niyyar Bata..... Ya Kara mikowa ungo amma kiji tsoron Allah kada ki gudu da ita Kinga na rantse.
Wallahi Zan baka Yanzu.
Ya sakar Mata ta Dan ja baya ta fidda key din sannan ta shiga setting ta chanza password din, tana dannawa zata Kara confirming yayi fit!!.... Da wayar, Wai meye kikeyi?.
Kawo na karasa please baka zanyi...... Password kike canzawa??????? Ya fada Yana Mata wani kallo.
Tayi murmushi, Yanzu dai Kara confirming ka Sanya *Balky02* shikenan.......
Dirowa yayi bisa mashin din saura kadan ya fada Mata tayi saurin ja da baya, kawai ya Fara binta Yana magana cikin daga murya.... password Kika chanza? Hankalin sa duk ya Fara tashi cikin bacin Rai....... Ai ...ai ....tanayi tana ja da baya Yana binta.
Gama korar awakin na rantse da Allah sai kin sanar Dani tsohon password dinki da dalilin da ya Sanya Kika canza....au ni Kika mayar photo?
Bayanta ya daki bango ta daga hannuwa sama Dan girman Allah ka ja baya Anwar......waye password dinki?
Ta runtse ido...... Dan Allah kaja baya Zan fada maka...... Kina fadawa Zan koma inda nake meye tsohon password dinki?
Dabara ta fado Mata, sunan da ake kirana gidan mu ne Kuma bana so ka ...... *Balky* shine abinda ake kiranki saboda har daddy da mommy suka tafi banji sun kiraki da wani suna ba bayan haka wane password ne Kika goge Wanda bakya so na sani?
Ka koma yanda kake kada wani ya ganmu a...... Suleiman kike gudu da samarinki ko? Ya Kai hannu daya a bango.
Ta runtse ido na shiga uku.....sai kwalla sharrrr....... Ya kura Mata ido jikinsa yayi sanyi sosai, ya sauke hannun a hankali ya Dan ja baya tare da saka hannuwan sa duka ga aljihu ya kura Mata ido.
A hankali ta bude ido, ita kanta Bata iya fadin ga dalilin kukan, saboda wani yanayi ne ta fada Mai rikitarwa.
Ke shagwababbiya ce?
Kamar ta shako wuyansa,
Tayi mishi banza.
Meye tsohon password dinki?......woohoho, Anwar idan maye ne ya Kama mutum tabbas sai mutuwa.
Kina so kiga irin tawa rigimar ko?....... *Yar Fara* ta fada a hankali, kakata ce kafin ta rassu take kirana da haka shine na saka........ta karasa maganar tana addu'a a zuciya ya Allah ya ceceta ya yarda da hakan.
Yayi jimmm, sannan yayi murmushi me yasa baki so nasan haka?
Ta galla mishi harara ban sani ba .....Nima meye zakayi da wayata?.
.......yayi Yar dariya, bincike....ai Ni ban boye Miki ba.
Karfe nawa?
Ina ruwanki da ko karfe nawa keda kike bakin kofar gida fadawa kawai zakiyi?.
Ina binki bashin abinci Wanda aka mun kwalele lokacin da mufeeda tasa nayi laifi......ta doka uban tsoki, kaje ta dafa maka mana.
Saboda me?
Saboda yarinyar ka ce.
A'a na kawata nake so my best friend Bilkisu.... Hmmm.
Ko ni ba babban abokin ki bane?
Shine, ta fada a gajarce.
Kika ce mun bakya fitar dare ya akayi yau Kika fito ??? Wannan karon Yar dariya tayi Wai haka kake da masifar tambaya?
Ya bi kumatunta da kallo, yau Kika San haka?
Tayi hamma ,
Barci yazo?
Da sauri ta daga Kai.
Yayi murmushi, to jeki kwanta...... Ta juya da sauri daman kafafunta duk sunyi dayi saboda tsayuwa.
Tace sai da safe.......ya bita da kallo Jin bai amsa ba ta Dan waigo....ya tsareta da ido ta dalla mishi harara.....wallahi ka fiye kallo da yawa. Ya matso da sauri me?
Ta kwasa da gudu ta fada gida tana fadin Wai yau meke damunka ni Bilkisu??????
Ya Kama dariya kawai ya juya ya haye mashin. Tana jinsa ya tada ya tafi sannan ta shige daki.
Ta cire kayan ta mayar Dana barcin da ta cire ta kwanta.......akwai tambayoyin da nake son yiwa Anwar amma inajin nauyi.
Ta lumshe ido.....yau dole ta kwana karatu kada gobe taci kaniyarta, abubuwan da suka faru suna dawo Mata a hankali.
Ya Allah kasa Anwar mijina ne....ta fada a hankali.
Tayi tagumi, nasan Yana Sona.....Amma Ina son ji daga bakin sa, ya Allah yasa da gaske abinda nake gani a idanun sa har cikin zuciya ne ya bashi ikon *FURTAWA*........ Ta lumshe ido........
Sha biyu saura ya shiga daki.
Dakin a cike ana jiransa.
Ganin hada Yan 100level yasa bai saki fuska ba kada su Anas su kawo mishi wasa( .....Kai Anwar case ne ).
Kowa jinin sa akan akaifa don karamin aikin sa ne ya fatattaki kowa yace barci zaiyi.
A hankali yake kallon kowa daman duk dudumar za'ayi dakin Babu Mai hawan gadon sa,
Ya zauna bakin gado yace to bisimillah....... Duk suka zaburo.
Bai Sami kansa ba sai uku saura.
Tuni su Anas sunyi barci.
Ya kwanta daga Shi da best Daman akwai wuta ya janyo laptop dinsa yayi connecting da wayar Bilkisu ta nuna mishi option ya shiga *transfer file*...
Gallery din ya shiga, a screen din system din yake kallon pictures din......ba karamin tashin hankali ya shiga ba ganin hotunan ta da yayi ba Wanda ta dauka babu hijab.
Duk duniya ba abinda yake son gani a kullum irin ya kalleta ba tare da hijabi ba.
Tsikar jikinsa sai tashi takeyi yayi ma wani hotonta kuri da ido Yana kallon kirjinta........hazbunallah ya fada.
Ya zaro ido ganin wani hoton Shi Kuma ba kallabi gashin ya zubo Mata a kafada ya zarce kirjin ta...... Attachment ne ko nata? Ya fada Yana rike Baki......
Wannan yarinyar anya Bata fi karfina ba?
Zumbur yayi ganin ta cikin kanan Kaya riga da wando tana rungume jikin daddyn ta, gefe mommy ce da kannen ta biyu maza. daganin pic din kasan ba Nigeria bane......yayi Mata kuri da ido Yana kallon kugunta..... Ya fadada murmushi *this is Dubai*....... Nawaoooo.
A hankali yake ingiza hotunan a system din sa. yarinyar nan gaskiya ta gama haduwa.......kutt!!! Ya Kara rike Baki.
Duk wani hotonta dake cikin wayar sai da yasa a system dinsa.
Ya shiga videos, mafi yawa Indian music ne.
Ya shiga text nan yayi karo da text din Suleiman Yana kyarma ya Buda.
```Aslm, Dan Allah lecture din yau karfe nawa ne ?```
Ansa: ```Four```
Na biyun
```Bilkisu ya murar? Allah ya Kara lafiya?```
Ansa:
```Amin thank```
Ya buga tsoki...... Dan iska uban chusu..... I hate this idiot.
Ya bincika ba wani sauran text daga na kawayenta Mata sai nasu Daddy da mommy.
Ya tafi dialing calls, mafi yawan Kiran Suleiman shine yake Kira kusan idanun sa Kira biyu ya gani tayi mishi.
Ya Kara doka tsoki.
Ya Kara komawa message baiga text din da ta mishi na birthday ba.
Ya doka tsoki watan ni ta goge ni ko?
Ya Fara dialing number sa Nan da nan sunansa ya bayyana ```ANWAR```
Ya saki ajiyar zuciya ya Danna sunan ya bi ta message sai kawai yaga text din ya fito, Nan da nan ya gane ta saka Shi secret conversation ne.
Yayi tsammmmm! To me take nufi da hakan?
Bana son Mata yawan tambayoyi ko don munyi fada tayi hiding?...
Ya kada Kai kawai.....hmm.
Ya hada xender ya tura Mata GB WhatsApp ya Mata installing.....
Ya rubuta Mata a wall status din ta *You can hide what is on your mind not eyes...*
Profile picture din Kuma ya saka Mata hoton Mommy da daddy Wanda suka dauka tare cikin jirgi......
Kiran sallah yaji an Fara ..... Ya zaro ido....yau akwai chakwakiya fa.....ya rufe da sauri, ya kashe wayar ta sannan ya dauko littafi saboda 8 suke da exam.
Rutsum , itama bata runtsa ba, Rabi karatu Rabi tunani.
Shi ya tayar dasu sadeeq sallah.
Daga masallaci Basu Kara ganin sa ba ashe school ya gudu ya boye Yana karatu.
Babu abinda idanun ta keyi sai zafi. Tana zaune can baya ana shirya su har an Fara raba question paper babu Anwar.
Hankalinta a tashe ga sadeeq ya Mata nisa bare ta tambayeshi.
Tana Shirin mikewa ta dauki excuse ta ari waya ta kirashi ya shigo, Yana ta mazurai Yana Bata rai...... Malamin ya bashi question dinsa da booklet ya ce biyoni..... Sukayi baya.
Yana zuwa dai dai inda take zaune ya sa biro ya zunguri hancin ta malama kalli paper karki sa in Fadi.....ta rasa inda zata sa kanta saboda kunya saboda hatta malaman kowa yaga abinda yayi Kuma Harga Allah ita ba Shi take kallo ba. Tayi sauri ta sunkuyar da Kai bisa table.
Kowa addu'a yakeyi Allah yasa akawo Shi kusa dashi amma malamin nan ya kaishi can karshe last.
Jarabawar tayi zafi, matuka.
Tunda yaga questions din Shima hankalin sa ya tashi yasan sunyi wahala though Shi ba wacce bazai amsa ba.
Bilkisu kawai yake tunani saboda jiya yayi obstructing karatunta.
Yana rubutu Yana dago Kai. Sai ya hango ta tayi zugummm.
Addu'a kawai yakeyi Mata Allah yasa ta Sami mafita...... Da kyar ta iya amsa tambaya daya *b* part din ma da kame kame ta karasa...... Na shiga uku ta fada.
Na kusa da ita kowa yayi zugummm.
Wadanda ke gaban Anwar suka Fara juyawa Nan ya Fara fada musu kwatsam..... invigilator ya hango su.....hey.....hey....yayo baya.
Come....come.....come....ya nuna Anwar taso daga Nan zonan....
Ya tashi a hasale Yana jiyawa na kusa da Bilkisu na Mata magana ko ta gane question 2? Ya hangoshi yace Shima ya taso.......saura kadan Anwar ya taka rawa yace Alhamdulillah a hankali.....suka hada ido da sadeeq ya daga mishi gira sadeeq din ya mishi dakuwa kasa kasa......ya danyi dariya. Ya fiddo wurin yace ma Bilkisu matsa ciki ya ce Kai Kuma zauna.
Yana juyawa Anwar din kafin ya zauna ya ajiye Mata booklet dinsa Shi Kuma ya dauki nata sannan ya zauna kawai ya Buda .
Ya Fara karanta shirmen da ta rubuta kawai ya soke ya bude sabon shafi.....
Tsoro gareta....jikinta ya Fara karkarwa, ta bude tana karantawa.... Ya cika booklet din tabbb...kaiii Anwar *guru* ne wallahi. Ta fada cikin zuciya.
Ya iya bada amsa ga turanci Shi yasa kullum cikin photocopy din C.A din sa akeyi Yan aji.
Tunani kawai takeyi ta Yaya zai karbi tashi ya Bata nata?. Tayi sukutiiiii........ Chinyere ta hango zata you submitting...... Ya daga kai, idan kin gaji go and submit..... Bata San ta mishi wata uwar harara ba......shin nashin zata bayar amatsayin tata?
Dukewa yayi Yana Yar dariya yaci gaba da rubutu.
Sit biyu ne tsakanin ta da Suleiman tana son daga mishi na Anwar Amma sunyi nisa.
A hankali aka Fara submitting...... invigilator din nan yazo yayi tsayi tagar kusa da su.
Anwar na gamawa kawai ya Mike yaje yayi submitting yayi signing out ya fice.....
Kaiii Anwar karshe ne.
Ta kasa tashi. Har sai da akace time out....stop writing, aka bi ana karba...... Ta saki ajiyar zuciya a hankali sannan ta mike taje tayi signing out.
Yana can zaune bisa taga..... Ya kura ma kofar fitowar ido. Tare suka jero da Suleiman.... Bilkisu yau Nasha wahala Allah dai ya kyauta..... Bilkisu kinyi duka ko? Naga Anwar aka maido miki.....Helen ta dafa kafadarta.
Tayi murmushi eh.
Suleiman yayi karaf, da kyar na amsa question one *b* da question three *a*.
Sai na tafi question 4 na buga mishi kame kame ya Allah kasa ko *e* mu Samu na gaji da carry over wallahi....ai Bata da dadi ta fada tana Mai jajanta mishi.
Wallahi Suleiman *Anwar* dan rigima ne Wai kasan Shi yamun jarabawa yayi submitting Ni kuwa yaban tashi na bayar?
Ya zaro ido ban gane ba.
Ta bashi labari...yayi dariya yace *Hmmm* kawai.
Yana ta kallonsu...ji yakeyi kamar ya je ya Shakure Shi.
Na Miki Barka wallahi Allah ne ya duba Miki.
Wallahi kuwa Alhamdulillah ai jiya na kwana du'a'i wallahi saboda daman na tabbatar Ina ruwa....... Karaf suka hada ido dashi.
Ya bata rai,....Ina zuwa Bari na karbo wayata wurin Anwar....... Okay sai gobe Nima zanje waje wani ke jirana.
Ya wuce, saboda yasan ba dawowa zatayi ba dan Yanzu.
Kun gama? Idan baku gama ba kije gashi can zai tafi.....Anya ba kishin Suleiman Anwar keyi ba?
Ta fada a zuciya. Shiru kawai tayi.
Baki da lokaci na?
Ta kalleshi, wallahi duk ka sauya Mani, Yanzu Abu kadan sai ka Fara fada kana sako Suleiman, Yana fada mun yanda yasha wahalar exam ne shine fa ka ganmu....... Bana sonji.
Kina son fada mun cewa kowa baisan Shi din saurayinki bane.?
Zatayi magana ya Mika Mata wayarta, ungo idan daddy ya tambayeki kice wayar ba chargy ta kwana saboda na kasheta b4 ya Kira don't know what to tell him.
Fishi kayi?, Ta ce ba tare da ta karbi wayar ba.
Akan meye zanyi fushi, Ina abinda ya dameni, na Isa in rabaki da Suleiman ne while Nima albarkacin sa nakeci na........ *Anwar*..... Ta Kira sunan sa.
Ya kalleta,
Wallahi ka canza, bana Jin dadin abubuwan nan har ga Allah.
Magana takeyi kamar me Shirin yin kuka.
Yayi shiru kawai,
Amma kayi hakuri idan na bata maka Rai shikenan ko?
Naji karbi wayar ......
Ta danyi murmushi ta Kai hannu.
Kina Sanya attachment?
Da sauri ta kalleshi, ya kura Mata ido....
Ta sunkuyar da Kai Allah ya sawake ban taba ba...... Gashin ki ne haka?
Haka me?.... Daman ka karbi wayar ne don ka man kwakkwafi kazo ka addabeni da tambaya?
Ya bushe da dariya...... Me yasa anan bakya sa ko gyale bare ki kwatanta saka wando mu gani........ Juyawa tayi ta Fara tafiya, ya dirko da sauri ya bita....Ina zakije?
Yasha gabanta.... Dan Allah kiyi hakuri na daina.
Hmmm, ta ce.
Na ce na daina ko?
Shikenan, bani wayar.
Tafiya zakiyi?
Eh, tace,
Suka jera suna tafiya,
gobe ne last paper kuma morning ana fitowa Zan gudu......... Nima gobe Zan tafi. Ta fada mishi.
Haba, Abuja ko sokoto.
Tayi Yar dariya Abuja..... Shikenan na Sami lift har gida ke zanbi ko? Ance Kano kike kawa jirgi Yar gayu ......... Tayi Yar dariya.....inji wane magulmacin.?
Ke fada mun Zaki tafi dani na shirya ko..... Shatar mota zanyi fa ba zuwa akeyi daukana ba....... Shatar mota?
Eh,
To kawai ki Bari mubi motar gidan su sadeeq idan anzo......Kai nifa bana son rabe rabe..... Ba damuwa nida sadeeq daya ne kada ki damu we are now family.
Shikenan Zan fadawa mommy yanda tace ....... Ya watsa hannu fine.
Ta harareshi Kai wallahi Anwar din Nan ka fiye yanga kamar mace......
Ya tuntsure da dariya a'a kin manta nine Bilkisu.
Barci kawai kowannen su keji. Koda suka suka rabu gado kowa yabi lafiya..........
Shako wuyansa yayi suka yi bayan daki.....Kai lafiya ....Wai Anwar kana da hankali kuwa?????
Warning Zan maka wallahi tallahi idan kayi kuskure *you are dead* ya mishi nuni da yanda a wuya.
Da Bilkisu zamu tafi gobe na fada Mata Kai zamubi idan ka saki ka nuna Mata inada alaka da tafiyar you are sorry Dan ubanka.
Zan ma Umar waya in mishi bayanin komai...... Kaji ko?
Naji banza....sakarni toh.
Yayi murmushi. Good and fine.
Wace karyar ka shirga Mata?
Ya tabe baki wallahi bance Mata komai ba Kuma nasan bazata tambayeni ba.....
To kaja ma Umar kunne wallahi......bai da matsala. Kuma wannan karon Shi kadai zaizo ba wani security saboda Kai zaka zauna gaba nida Bilkisu a baya ...... Dan ubanka ni oga Kuma a gaba? Eh, Kai zakayi arranging hakan.......mtsew naji.
Cikin kwanciyar hankali tayi wa mommy bayani. Tayi Mata nasiha da addu'a , ganin Bata boye Mata hakan ba, (munafunci ga yaro Shi keda ciwo).
Umar yasan dakin su, can ya biya aka Sanya musu kayansu kafin ya karaso cikin makarantar.
Suna fitowa ya tareta Yaya?
Ta ce ta shirya.
Haka suka biya ta dauki jakar ta suka wuce.
Sadeeq ne oga ya kame a gaba.
Shida ita baya..... Ya kalleta. Kinga WhatsApp???? Tayi murmushi eh,
Zamu ringa chatting kinji?
Toh,
Ko Baki da time?
Me zai hana......
Good, ya fada.
Kinyi break?
....tambayo. Ta fada a zuci. A zahiri tace Nasha tea.
Tea?
Umar akwai abinci motar nan?
Eh, yalla....... Yayi saurin datse maganar ya canza da cewa, Yana daga Nan baya.....
Sadeeq ya juyo Kai bana son hauka abincin nawa zaka cinye?
Bilkisu zata ci ko zaka Mata rowa ne......Ni na koshi ma ta fada tana Yar dariya....... Au Bilkisu waa nakeyi I tot koshine keson ci.
Ya yunkura ya dauko cooler sadeeq ya Miko mishi spoons biyu, yabude.....kamshi ya buge motar... Gasassun kaji ne da soyayyen dankali da kwai.
Ya kalleta kici ....
Tayi murmushi.....na gode.
Wani kallo yayi Mata....bakici?
Ta tabe baki Alhamdulillah.
Ya daga kafada, kufa wadannan an Saba haduwa ko? Wurin mu ne sabbin zuwa ya waxgi kaza ya Fara ci.
A hankali a hankali yaci ya koshi tana kallonsa ........Kai namiji baida kunya ita Ina zata iya Shan ko ruwa a nan?.
Ya Mika ma sadeeq ungo...... Miko mun maltina Mai sanyi gaban ban......Ashe Yar cooler ce ta ruwan sanyi dankare da lemuka .......
Ya kalleta me zai Miko Miki?
Ta girgiza Kai na koshi...... Ke kuwa Dan Allah hajiya Kisha ko Mai sanyin ne.......Kyaleta umar tana tsoron kada mu saka Mata baliyan....... Ta zaro ido....yasha mur...... sadeeq bani maltinar Nima...... Ungo wannan Kisha Ni ta isheni. .....ya Miko mata tasa.
Kurba biyu tayi da kyar, ya tsareta da ido.....ko kadan baijin kunya ko nauyin kallonta, taci gaba da rikon ta.........tana jujjuyawa.
......... Kina tunanin Suleiman ne?...
Wohohoho Kai kuwa a Rana sau nawa kake ambaton Suleiman a rayuwar ka Wai meye ya tsare maka?.
Inba tunanin sa kikeyi ba Kisha.....na koshi ne kaima ka kasa shanyewa bare Ni?
Kuna da Yan uwa a Kano?
Um, um.... Ni ban ma taba zuwa Kano ba sai ta dalilin karatun nan.
Da gaske?
Allah kuwa.....
Kai Dan asalain Kano ne?
Yayi murmushi ciki da bai kuwa.....ya bangan ka da tsagen kanawa ba?
Yayi Yar dariya, daga kaina aka daina gidan mu kinsan nine auta gidan mu muna da yawa..... Ya sunan anguwar ku?.
Keda Baki San Kano ba Ina ruwan ki da sunan anguwar mu kuma?.
Eh, Ina son sani.
Yayi Yar dariya ni ba cikin garin Kano nake ba kauyen Kano karkashin karamar hukumar *Rano* kin San wani gari *Dagama*?
Nope, ta fada.
Yayi Yar dariya.
Suna shiga Kano ya ce a tsaya ya sauka.
Ya Dan fita can gefen hanya.....ya Kira Alhaji Mubarak a airport.
Hello an Gama komai?
Ya rusuna, angama Allah Shi taimakeka.
Yawwah.
Ya shigo motar da sauri, Umar airport muje Airport da sauri please....... Ta kalleshi zakewa????? Shi Dan karo sai instruction yake badawa tun dazun.
Tun daga bakin gate ake Basu girma. Ko kadan Bata kawo wani Abu a ranta ba.
Ya tokare bakin kofa zan koma mota, sadeeq sune Yan gari zasu raka ki har ciki......
Toh, na gode sai munyi. Sai Yan waige waige kamar marar gaskiya......zamuyi chat kinji?
Tayi murmushi ba damuwa....... Manyan mutane biyu ta gani sun zube gabansa Allah Shi taimakeka Barka da sauka.........
Ya zaro ido ita Kuma tabi fuskar sa da kallo........✍🏼😄😄💖
Alawiyya ma na gefe...😝
*ZAINAB WOWO* 💖💖
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣3⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💖💖💖💖 *For Gaje Abu*
👉🏼 Alaweez😍😘🥰🥰😘😘 Ana mugun tare.
*Ya Allah ka Kara Mana katangar karfe da masu bakinciki damu* *Hassada ga Mai rabo taki ce duk Wanda Allah ya tarfa ma garinsa nono wallahi ko ana mazuru ana shaho sai yasha* masoyana ga taku👉🏼💕💞😘
***************
*KADUNA RIGASA*
Tayi zaune falon suna labari da hajiya bayan ta sako doguwar hijab.
Ta kawo Mata lemu da naman kaji......gidan Alhaji shamsu naje shine na biyo ni in ganku tunda Shi ya kwammace yayi ta kullenku da ya barku zumunci.
Murmushi tayi kawai.
Ya kuke ba wata damuwa dai ko?
Babu damuwa, ta mike tsaye bari na Kira ummin ku gaisa.
Da gasken gaske hankalinsa ya tashi sha"'awar Amira ta addabeshi.
Da farko yaji haushin kwalelen da ta mishi amma da ya tuna haramcin yin haka saboda ya shiga hakkin Ummi, sai ya bata uxuri.
Ya shiga toilet dinta yasa ruwan zafi ya warwatsa a jiki saboda ya Sami sauki, sannan ya fito.
Zaune suka tarar dashi suna labari da hajiar, ya kasa dauke idonsa daga Amirar duk inda tayi idanun sa na kanta har Ummi ta Shaka.
Koda suka raka hajiyar Sashen Amirar ya koma.
Ya riko kugunta wallahi gobe sai kin gane kurenki......
Wai Ina Kika saki Kaya haka bayan nasan ke ba ma'abociyar su ba ce?
Inji waye? Ina ra'ayi Kaine naga kamar basa birgeka.......wallahi Ina so. Da kin tsaya dazun tabbas da ba kiss kadai zanyi ba........... Maganar ta makale ganin Ummi ta banko kofa kamar an biyo ta....
**************
*Federal University dutsinma*
......Malam ba Wanda kake tunani bane get lost.... Ya bude baki zai Kara magana ya fiddo mishi idanu I said get lost ya fada cikin tsawa.......... Wai Kai baka girmama manya ne?
This is not your business mutane fa Yanzu kasar nan a firgice suke kamar.....kamar kowa ya haukace irin ka?
Da sauri mutumen ya kalleta, sai kawai ya tashi yabar wurin.
Ya kamata kasan darajar mutane fa......naji kiyi hakuri go....ya Mata nuni da baki.
Kana korata ne don na Fara fada maka gaskiya....... Bilkisu muje...... sadeeq ne ya karaso da sauri.
Sadeeq kayi ma Anwar fada abunsa ya Fara wuce gona da iri ta Yaya zai ringa yi wa magidanta tsawa babban mutum mai kima...... Dan Allah kiyi hakuri ban karawa...ohhh my God.
Ya akayi ne? Inji Sadeeq.
Ta juya suka jera suna tafiya tana magana cikin fada fada, Shi ya raina kowa, mutum da kimarsa yayi mishi magana mistakenly it might be ya mishi Kama da wani ne Wai kaga wulakancin da ya mishi? Haka kawai ya janyo ma kansa dauri a banza........ Kiyi hakuri Zan Kara mishi nasiha don Anwar Kam sai dai nasiha ba fada ba.
Suna wucewa ya saki ajiyar zuciya....... Ya ruga mota.
Yana Zama ya kirata a waya, kamar bazata dauka ba tana kokarin hawa jirgin bayan sun rabu da sadeeq.......
Hello...fly mode Zaki Sanya wayar ki Kuna landing in the next 40-50 minutes I'll call..okay?
Naji, thank bye....ta latse wayar.
Yayi dariya, Bilkisu rigima.
....... Yana bude mota ya shako wuyansa.....Dan ubanka me yasa kakeyi Mata boye boye?
Ya kyalkyace da dariya,
Wane babban mutum ne kayi ma wulakanci a gabanta...... Wallahi su Alhaji murtala ne kasan Shi ya cika shisshigi Ina Jin saukarsu kenan.
Ya zaro ido? Shi ka yankwana???
Kwarai kuwa......anjima idan yazo lissafi Kuma fa me zaka ce mishi?.
Inaaaa bazan bashi fuska ba yasan bana son haka gaban mutane.
Ya kalleshi, jirgin kayan nan fa ya iso tun last week, jibi zanje Lagos nayi clearance a Fara distribution.......
Masha Allah.
Amma me yasa baka son Bilkisu tasan Kai wanene?
Yayi murmushi saboda Suma suna da kudi Kuma...... Kuma ubanwa??..... Ko makaranta kaki nuna ko Kai wanene Wai me yasa kake haka?
Yayi Yar dariya, Kuma fa yarinyar ta gane Zan masifa amsa questions irin lokacin da tasan ni first class ne.
Kana son Bilkisu ko Anwar?.....
Ya kalleshi bana son irin wannan tambayar taka na Fara gajiya da ita, saboda ka kasa fahimtar baka da amsarta Yanzu......mtseww nonsense. Ya Kai mishi duka.
Tarihinka Zan Bata Dan ubanka, Zan fada Mata Kai din wanene..... Da kayi nadama irin Mai ban tausayin nan wlhi.
Sadeeq din suka Fara ajiyewa sannan so gida unguwar makil da jama'a Yan maula kofar gidan ba masaka tsinke .........
*TUSHEN LABARIN*
Babban gida ne a Kano, Alhaji Hamza hamshakin Dan kasuwa ne Wanda aka sani ko'ina a fadin duniyar.
Yaranshi shidda hudu Mata sai biyu maza.
Matansa uku, Allah bai azurtashi da yawan yaran ba,sai yawan dukiya.
Ta farkon hajiya maimuna keda Yara hudu, maza uku mace daya, ta biyun Allah bai Bata haihuwa ba hajiya Jamila, sai karamar keda Yara biyu mace daya namiji daya Kuma Wanda ya kasance Auta a gidan watau mahaifin Anwar (Alhaji Yusuf ).
Ya tashi cikin tsana da tsangwama ta Yan uwa, ganin hakan yasa mahaifiyar Shi ta maida hankali ga karatunsa fiye da harkar kasuwanci.
Babu Wanda mahaifinsu bai jaraba ba cikin yaransa maza 3 Amma dukkan su sai da suka ha'ince Shi.
Yusuf bai da lokaci ma bare a kwatanta kullum Yana makaranta.
Ya gama jarabawar aji shidda suna jiran sakamako mahaifin su Allah yayi mishi rasuwa daga ciwon ciki.
Nan da nan rikicin rabon gado ya taso.
Aka raba rabo na son zuciya.
Cikin gidajen da suka gada shida Yar uwarsa da mahaifiyar sa suka koma can wata unguwa.
Allah ne gatanta shine jigonta.
Ya ce zai ci gaba da kasuwanci kawai tunda ga jari sun samu.
Nan da nan ya Fara fita China Yana saro turaruka Yana rabawa manya manyan shaguna a garin Kano.
Tun Yana tsayawa Kano kadai har ya Fara kaiwa kaduna, zariya......wasa wasa sai ya bulla har Lagos, Abuja da sauran wurare.
Arziki Kashi........ Nan da nan ya Kara da cosmetics, takalmomi, jakunkuna.....Kai kayan masarufi........kafin kace kwabo Yusuf ya taso da zafi....hakan yasa mahaifiyar sa bata duba karancin shekarun sa ba tace lallai sai yayi aure.
Bai da ko budurwar ma saboda bashi da wannan lokacin.
Itace ta nemo mishi diyar kawarta Yan asalin Yola Fulani basa ko hausa cikin gidansu, lokacin duka bai wuce shekara ashirin da biyu ba.
Shekarar su daya cif da Aure aka haifi Anwar.....bayan ta haifeshi kuma tace ga garinku nan Shi bai San mahaifiyar sa ba.
Tunda ga lokacin ko maganar Aure baya so.
Anwar ya tashi hannun kakarsa, Yana Dan shekara 2 bayan an yaye shi yayar babansa Aunty murja tayi Aure.
Ya kasance gidan daga Shi sai kakarsa mahaifinsu ba mazauni bane sai Yan aiki dake kula dasu suna musu dawainiya.
Duk Yan uwansa arzikin ya tsiyace sun dawo karkashin sa.....
Cikin kankanin lokaci ya nunka mahaifinsu kudi linkin baninkin.
Yan uwan cutarsa sukeyi amma kullum kudin kamar ana Kara musu taki.
Ya mallaki kaddarori iyaka, kamfunna a Nigerian ba inda baya dashi komai Yana shigowa dashi Kuma ana yi na cikin gida.
Anwar na primary school ya Kara Aure, ba hausa Amma mazauna saudiyya yarinya Mai hankali da sanin ya kamata.......watansu uku da Aure hatsarin jirgi ya rutsa da Alhaji yusuf.
Anji mutuwar sa a kasa Baki daya, sanarwar rasuwar ya barar da tayin cikin Amarya.
Illahirin dukiyar Anwar da kakarsa suka gaje ta, Nan take ta ce ta yafe ma Anwar komai na mahaifinsa amma nata na mijinta a fiddo Mata, haka akayi kuwa aka Bata ta karawa yarta murja.
Kafin marigayin ya rassu Yana yawan fadawa mahaifiyar sa amintattun mutanen sa da wadanda ke cutarsa. Baya boye Mata komai.
Cikin amintattun hada Alhaji murtala ( wadanda suka hadu da Anwar airport ), shine kan gaba wajen Jan ragamar kasuwancin.
Tsaron shaguna aka ba wasu daga cikin macuta.
Allah da nashi iko, sai ya dubi maraitar Anwar ya Kara bunkasa dukiyar........
Yana j.s one wata Rana an dauko Shi school sun shawo layin gidan su kawai suka ga yaro gabansu da Keke......da karfi suka taka birki ji kake kuuuuuu.... Yaron ya Fadi da karfi lokacin da keken ya daki motar Kan ya karye tayar ta lauye....Shi Kuma ya karya musu madubi ya karci motar.
Anwar na kwance bayan sit, yaki ko motsi tunda yaga abinda ya faru ya kishingida bai Kara dagowa ba....... Drivern ya fita mutane suka taru sosai, ihu kawai yaron keyi Yana kururuwa wallahi sai an biyashi keken sa, kowa yasan laifin yaron ne amma sai aka goya mishi baya.
Shurun tayi yawa hakan yasa Anwar din fitowa, ya kalli Umar driver yace ya akayi?.......
Sai kawai yaron ya cakumo wuyan Anwar, na rantse da Allah ban sakin sa sai an biyani kekena........ A hasale Anwar din ya kalleshi cika ni ko Kuma wallahi in maka mugun duka anan...ya fizge tare da ingijeshi yayi taga taga.....Nan Yan unguwa kowa ya Fara darewa an San Hali.....
Ya Kara shako wuyansa..... Umar yayi wuf ya fizgeshi...... Sai abun ma yaba Anwar dariya.
Keken nawa yake?
Koma nawa yake wallahi sai kun biyani, don ba inda zakuje ya babbake hanya Yana ware kafafu.
Shigo muje .....Akan wannan shegen keken.....wani nushi ya Kai mishi a gefen fuska, Nan da Nan suka rukume fada...kichaaa...kachaaaa.
Mutane suka yo kansu da gudu.......kowane sai haki yake.
Yau naga bala'i Kai wane irin Dan iskan yaro ne?....... Mugun bugu Zan maka, wallahi na gane fuskar ka matukar ka Kuma zagin keken Nan sai nabarka kwance saboda zufar ubana ce....ita wannan motar zufar uwarka ce da ka fado Mana ko baka ga ka Mana barna muma......
Sunfi awa ana abu guda daya Anwar yace Basu biya Shi Kuma ya hanasu tafiya......har hajiya ta Kira waya taji shiru.
Hankalin ta a tashe ta fito...... Tasa aka iso da ita wurin da ake rigimar .
Yaron ta kalla lokacin da ta iso tace zo muje a siya ma wani keken....ta kalli Umar saka wannan mota......Yanzu naji magana...ya figi hannun Anwar zo muje tare kada a yaudareni.......suka fada motar hajiyar da tazo ciki.
Anwar na shakkar hajiya baya kaunar bacin ranta duk duniya.
A motar yaji tana waya..... hello Yanzu Yanzu Aiko da sabon Keke Mai inganci na Dan samrayi sa'an Anwar .
Suna shiga Anwar yayi saman bene da gudu cikin bacin Rai.
Suka zauna falo Shi da ita.....ta kalleshi ya sunan ka?
Yace *sadeeq* da sauri.
Babanka ya siya maka ne?
Eh, ya zumburo baki cewa yayi idan nayi na daya a makaranta zai siya mun, yau kwananshi biyu fa da saye!.
Tayi murmushi.....to ba sai ya Kara siya maka wani ba idan yaje kasuwa?......ai ba a kasuwa yake yin faskare ba nan kusa da gidan mu ne kullum.....dai dai Anwar na saukowa bene....ta ce innalillahi faskare yakeyi?
Eh, shine yayi ta tarawa ya siyo mun keken.
........hansa'u!!!!!!! Ta kwala ma cikin Yan aikin Kira. Da sauri ta karaso, kawo ma yaron nan abinci.
Ya washe baki Yana Murna,Nan da Nan Anwar yaji tausayin sa musamman da aka kawo abincin yanayin yanda yakeci.
Ya tashi kawai yabar gun.
Da gudu Anwar din yayo baya cikin firgici jin ihu ba kakkautawa........Ashe sabon keken ne aka shigo dashi..
Kawai ya dunga buga tsalle Yana ihu da rawa..... Da hajiya da Wanda ya kawo keken sukayi ta dariya...... Kai Wai baka da hankali ne ? Ya daka mishi tsawa ka bani tsoro a banza wajen hauka......Allah ya baka hakuri Yanzu ko duka na kayi bana ko kallon ka...mtsew ya yi hanyar daki.
Ya ruga ya kamoshi.....zo muje mu dana tare kafin na tafi a titin cikin gidan Nan...... serious ya kalleshi...are u mad?
Baya jin turanci ko kadan ya figi hannun sa kazo mu je ka tukani in tuka ka kowa ya Rama ma kowa sannan in tafi...... Sai kawai Anwar din ya bushe da dariya....Ni yau na hadu da matsala.
Hajiya ta Sanya musu ido kawai da tsiya ya fidda Anwar din.....
Ta kalli labaran da ya kawo keken.....yaron can dole ya Zama abokin Anwar saboda zasuyi dai dai........ Shi yasa na tsani karatun kasar waje Ina so yayi anan yasan duniya....... Arziki irin na yaron nan Yanzu Yana da hadari a gareshi....... Hayaniyarsu take jiyowa suna ta wasa.
Da abu yayi dadi a mota aka Kai sadeeq har gida da sabon keken sa da ma tsohon Basu da nisa sosai.
Mahaifansa sukayi ta godiya, tun daga ranar kullum sadeeq sai yaje gidan su Anwar wasa su hau Keke, shillo kamar kananan Yara.
Shakuwarsu yasa Anwar din kawai yace a maida su school daya suka dauki nauyin karatun sa.
Abin mamaki tun a lokacin sai Anwar din ya ringa mishi kandakun kada yaje Yana bada labarin gidan su.
Aka ba iyayen sadeeq jari Mai tsoka Banda taimako da zakka sannan hatta Kaya sutura Anwar ke ba sadeeq tun Yana bashi kwance har ta Kai Shima nashi ake siya mishi.
Suna girma Anwar na Kara miskilanci sadeeq Kuma na Kara lakantar sa ciki da bai.
Yana ss 2 ragamar dukiyar sa kaf! Ta dawo mishi mafi karfin kasuwancin yafi karfe a *Dubai* sai ya kasance da anyi hutu yake tafiya sadeeq Kuma ya tsaya Nan Yana wasu ayyukan.
Ko kadan Anwar baida fahari.
Ko a Dubai yasha Kira cikin yaransa yayi acting as shine Anwar din wajen wata Hulda idan tazo.
...... Babu kasar da baya zuwa da sunan kasuwanci.
Shi yasa da jarabawa ta fito ya cike Nigeria jihar katsina Kuma, don ya na son surveying area din ciki da bai, saboda suna da karancin kasuwa a katsina matuka......
Jiragen sa shidda sannan ya na da share a Abu Dhabi airlines suna bayar da hayar jiragen su. Anwar hamshakin Mai kudi ne Amma duk duniya ba abinda ke birgeshi irin ya boye Identity dinsa Yana acting as normal person hakan na saka Shi nishadi Shi yasa karatu kasar waje bai taba birgeshi ba yafi so yayi cikin normal mutane cewarsa masu kudi naturally suna da wani abnormality Wanda basu fiye sanin hakan ba........ Duk wani taimako da ake bayarwa makarantar fudma daga miliyan daya zuwa sama Anwar ne ba tare da an sani ba.
Yana da tausayin talaka, Abdul Mai shop yasan Anwar masu kudi ne saboda kyautar da yakeyi mishi na ya Kara jari Kuma ya mishi mugun kashedi Koda wasa kada ya fadawa kowa.
Yana da gadara haka ya tashi fil azal............
*wannan kenan*
Falon cike da mutane ya shigo duk suka Mike Allah Shi taimakeka.......
Wayarsa tayi Kara , *Bilkisu ce* da sauri ya daga Ranki ya Dade Kun sauka?
Um, gashi ma har na Kama hanyar gida....good nima shigata gida kenan mun biyata gidan su sadeeq....Ayyah, ka Kara mun godiya ga sadeeq Allah ya Kara arziki.....Baki da matsala.
Zamuyi waya Anjima please.
Okay bye....ta latse wayar.
Ya kalli Alhaji murtala....... Yallabai yau ka dawo ne?
Ya rusuna Allah ya Kara ma daraja eh wallahi.
Yayi Yar dariya Dan Allah idan Kun ganni da jama'a ku daina irin haka bana so Kun San haka, za a ringa kallona bani da tarbiyya matukar Ina tsawatawa Kuma tabbas bana Jin dadin hakan......kuskure ne ayi hakuri in shaa Allah...... Ina takardun jirgin da ake gyara Jidda??
Ya Mika mishi file gashi............. Sai karfe shidda da Rabi ya shiga ciki.
Tana zaune bisa abun sallah ya shigo........ Yaro da akidar manya....tsohuwar ta fada.
Yayi dariya hajiya tuwo zanci akwai ko?
Eh, ........ Ya Mike a hada mun kafin na watso ruwa na gaji yau Zaki Sha labari.....
Tana kwance bisa kafar mommy falo kiransa ya shigo......ta daga hello Anwar.
Ranki ya Dade......ya gajiya?
Ba gajiya yasu mamah?, Ya danyi jimmm, kafin yace Hajiya lafiyarta kalau,
Ohhh, hajiya yake Kiran mamansa?
Yasu mommy ya katseta. Ga mommy nan kusa dani...Ina gaisheta please.
Tana amsawa.
To meye labari?
Labari na wurinka ni na iya labari ne?.....mommy ta zameta tare da mikewa...
Ki koya Mana sai ki bani.
Me yasa gidanku babu hayaniya ko yaran sunyi barci?
Auwal da musbah ne suna can dakin su.
Ke Kuma kina makale da mommy ko?.... Tayi Yar dariya ai ta tashi ma ta shiga ciki.
Ya Kano din?
Kauyen Kano dai? gamu ciki ya fada Yana dariya.
Ta ce hmm.
Zan Fara fita kasuwa gobe kin San talaka baya Zama......kana kasuwanci ne?
Eh, Ina bin wani ubangidana Ina mishi tsaron shago cikin sabon gari a garin Kano......kin San kasuwar sabon gari?
Naji dai ana fada.
Okay toh can.
Tausayin sa ya kamata.......rashi bai hanashi gadara da izzah ba, Mai Hali baya barin halinsa....kinyi shiru.
To Allah ya bada sa'a ka samo kudi da yawa Wanda zamuci biscuits next semester....ya kyalkyace da dariya ni Zan siya Miki?
Kwarai kuwa a rama wa kura aniyarta nima sai na ci kudin ka next semester.....hahahaha ya Kama dariya.
Naji Zan dage na samo da yawa.
Ke me Zaki kawo mun tsaraba?
Abinda kake so,
A'a kawai ki dai kawo man ko menene.
Hmmm, tace.
Ko bazan samu ba?
Zaka samu in shaa Allah.
To me Zaki kawon?
Ka fada Mana me kake so?
A a bani da zabi.
To shikenan ka jira zaka gani.
Na gode.
In kyaleki haka ko?
Okay gudnight ta kashe kawai....... Ya doka tsoki jira takeyi ne?
Yarinyar nan tafini
gadara wallahi.
Washe gari bai Sami kansa ba ko kadan, abubuwa sun taso, ba shiri karfe shidda ya bar kasar......
Yanayin abubuwan sai da ya kwana biyu bai samu yayi magana da Bilkisu ba.
Ta nemeshi a waya har ta gaji.
Da ta Kira sai a Fara nata faransanci Ashe France ya tafi ya Kuma chanza layi.
A Rana ta biyu ana ta meeting a katon office din sa Kira ya shigo through WhatsApp ya kalli turawanya ce kowa yayi shiru,
Ya daga... Hello Bilkisu.... Duk kasuwar ce wayar ka Bata shiga? Ina Kira sai wani yare ko ka Sanya Ni voice mail ne?..... Voice mail Kuma ? Yayi dariya kiyi hakuri wasu kayukane muke shiga Saro tattasai Kuma ba service wurin kiyi hakuri muna lissafi da Mai gida anjima zamuyi chatting......
Hakan kuwa akayi tun Sha daya suke chatting har kusan biyun dare.
Amma ita dashi lokutan sun banbanta.....
Daga ranar kuma bai Kara samun lokaci sunyi magana ba.
Fushi tayi Bata nemeshi ba, Suleiman kuwa duk bayan kwana biyu sai ya nemeta sun gaisa.
Ranar da zai baro France aka mishi waya zasuyi meeting Abuja da managers din, *Next, ShopRite da Sahad*
Dole sukayi landing Abuja.
Motoci shidda kebin bayan tasa biyu na gaba. Saboda tafe yake da nashi mutanen.
Ko a cikin motar waya kawai akeyi.
Bayan an gama meeting din suka zagaya ta kofar shiga ShopRite wurin ice cream security sai kyarma sukeyi yau ga Anwar...... An cunkushe kofar an tsaida masu shiga.
Ya Kira Angelina suna magana.........Ai sai ku bamu wuri mu wuce ko?
Da sauri ya waigo *Bilkisu ce* rike da iyayen ledoji..........😄✍🏼
*Ayi hakuri a hankali za a ji yanda labarin ya ke da yanda zai Kare* Banda sauri please mubi komai a hankali.
Zainab wowo ce💖💖😄
👉🏼💖