🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣7⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
***************
*KADUNA RIGASA*
Duk ina son ganin ku falona da karfe takwas...
Ya tura ma kowace sako.
Duk sun you zugum suna mamakin wannan Kira , abinda bai taba ba.
Ya rage karar TV.
Agurguje ba lokaci maganar zata dauka ba, da farko Ina godiya da Jin dadin yanda ko wace ke kokarin faranta mun da Kuma dagewa wurin kyautatawa, hakika naga canji a gidan Nan. Allah ya saka ma ko wace da mafificin alkhairi.
Magana ta karshe doka ce Zan saka na neman shawara ko neman izini ba.
Daga yau na Hana ko wace ziyarar dakina matukar ba ita ce da girki ba. Sannan daga yau kada wacce ta Kara bina ko ta shiga sashen dayar ku matukar Ina ciki.
Wannan shine.
Ummi kina iya tashi ki tafi sai da safe...... Ya Mike yayi ciki.
***************
*Federal University dutsinma*
Gaban Bilkisu ya fadi ita Kam ta tsani fitina a rayuwar ta, tayi kasa da Kai tare da wucewa a hankali..... Ya chafko hannunta ya rike gammm, ba Bilkisu da mufeedar ba duk wadanda ke wurin sai da suka fiddo idanu waje.
Yasha mur ya Kara janyo facing cap dinsa ya rufe idanun sa Yana kallon kowa kasa kasa sannan ya maida kallon sa ga Bilkisu Yana janyota baya a hankali Yana fadin ```yaya Zaki tafi ki barni bayan kin San...``` Amma Anwar ka maida mayar dani Yar iska. Au daman saboda wannan sillan Karan kake Mana yawo da hankali....tabbas yau na gane ma ido na.....
Sake mun hannu Bilkisu ta fada tana doka mishi harara, yayi kamar baiji ta ba.
Ya kalli mufeeda kin gama mu tafi?...... Na gama ai daman ban tsayar da Kai ba ko?
Ta fada tana huci.... Ya ja hannun Bilkisu suka wuce..... Kwallah suka zubo Mata sharrrrrr ta fizge hannun ta da karfi yayi saurin kallonta cikin hula Yana Mai daga kansa sama..... Kuka again?
Ya fada Yana kallonta.
Ni zaka zubda wa mutunci a gaban bainar jama'a? Ana ganina da kima da mutunci.....ke! Wai me nayi?
Hannu na da ka rike ni muharramarka ce? Ta zaro mishi ido. Yayi murmushi Bilkisu rigima, na lura duk duniya ba abinda Kika fi so da kauna irin na taba ki saboda na fada Miki cewar matukar Ina tare dake ban sallameki ba Kika nemi Bari na ki tafi wallahi ko a gaban waye Zan Kama ki, me yasa ke baki ganewa kiyi mun biyayya?......
Bazanyi biyayyar ba, na ce bazanyi biyayyar ba.... Ta nuna Shi da yatsa jira kaji Anwar na lura da take taken ka kana son mayar dani irin su mufeeda da ke binka suna maka biyayya kana musu yanda kaga dama ko?
Saurara da kyau, bana tsoron ka , bana shakkar ka na gaji da wannan dokokina naka marassa Kan gado.
Ka tafi kaje mufeeda is ready for that not me.....ta hada hannuwa alamar tana rokonsa abeg leave me alone.... Ya rungume hannuwa duka a kirji ya tsareta da ido kawai Yana kallo.
Ta mishi kallon up and down ta wuce tabarshi a tsaye.
Yabita da ido har ya daina ganinta...
Yayi shiruuu, me yasa bazan kyale yarinyar can ba?
Anya Bilkisu ta damu dani kamar yanda nake jinta azuciya?
Me yasa ta fita daban cikin matan jami'ar nan take bani wahala ta kasa gane irin qimar da nake da ita.?
Wai ko wannan haukan da Yan Mata keyi a kaina me yasa ita bazata ringa mun yanda nake so ba don su fahimci tafisu?
Mtsewww yaja dogon tsoki, sannan ya fiddo waya ya kira sadeeq, *zo ka daukeni*
Yanayin muryar sa kawai yaji yasan an Kara kwafsawa .
Kicin kicin ya iskeshi bakin gate ya hau mashin din kawai suka tafi.
Yana zuwa daki ya fada bisa gado yayi ruf da ciki....
A bakin kofa ta hadu da Aisha ta bita da kallo kafin ta rufa Mata baya suka nufi dakin Aishar........ Yau ma kuka?
Kuka Zaki ringa mishi lallai kina da aiki...... Aisha bana son abinda Anwar kemun kawai a gaban su mufeeda ya rikon hannu Kuma ya rikeni yaki saki saboda Allah me zasu daukeni?
Ke yau ai na shiga uku Kinga kallon da kawayenta ke mun da ita kanta....... Ai dole. Kut! Wallahi dole su kalleki, Al'amarin Anwar ya Fara ta'azzara gaskiya Kuma Shi yaki fitowa ya Fadi ainahin abinda ke ransa ...... Yana jiran ni na bishi irin su mufeeda haka na lura amma wallahi ki barshi idan yasan wata bai San wata ba.
Ta wuce dakin ta don ta gabatar da alwalar magriba.
Ta kashe wayarta kada ma ya kirata,
Washe gari tara suke da lecture, akayi sa'a malamin ya zo. Ya bayar da first assignment cikin part of outline din da zasuyi semester din, Anwar na baya can karshe idanun sa na Kan Bilkisu dake tsakiya ita da su Joseph, lokacin da ya fita ne ta karbi littafin Joseph din tana rubuta inda aka wuce ta. Tana gamawa ta mike Anwar ya kwada Mata Kira.....
Bilkisu.... Ta waiga da sauri saboda yanayin yanda ya daga murya duk ya janyo hankalin wadanda Basu Kai ga fita ba.
Zo ki zauna anan ya nuna Mata kujerar dake gefensa ..... Kowa ya tsareta da ido Yana jiran response dinta,
Me Zan maka? Ta fada tare da tsuke fuska.
Kawo mun note dinki zanyi using ...... Bai rufe baki ba ta jefa mishi littafin har ya daki fuskar sa, gashi nan idan ka gama gobe Zan karba Ina sauri ta yi hanyar waje.....da gudu ya fito har ya ba wasu tsoro.
Ita kanta sai da gabanta ya Fadi lokacin da ta wurga mishi book din saboda tasan cewa ta debo ma kanta wutar dafa kanta.
Ta yi sauri ta tsaya tare da rike kugu....... Ni Kika jefa?
Ya fada Yana zaro ido.
Ta mishi kallon up and down kafin tace idan kaji haushi ka maido mun littafi na Mana.... Jeki dauka bana so ya fada Rai bace .
Fine , ta fada tare da wuce Shi ta koma class din.
Duk aka kawar da fuska ganin ya biyo bayanta, samm bata lura ba Bata Kuma ji takunsa ba.
Littafin ya fada can karkashin desk ta kutsa can ciki ta Kuma duka tana kokarin dauko Shi, ya shigo sit din ya zauna, ita kuma tana ciki.
Dagowar da zatayi taji ta fada bisa kafar mutum ta mike da sauri innalillahi.... Wai kanka daya Anwar??? Ta daka mishi tsawa.
Idan baki so na Miki abinda Kika tsana ki zauna silently muyi magana wallahi idan Kika kuskura anan zan Miki abinda...... Bazan zauna ba bani wuri in wuce.
Naki na bayar ko Zaki daukeni da tsiya ki fitar? Me yasa kike da gardama Bilkisu???
Kai Kuma me yasa baka da zuciya?.
Yayi murmushi nima Ina neman amsar nan wallahi..... Ta ja tsoki kanka akeji bani wuri.
Ya kalleta alamar ba wasa yayi baya da hular sa , kin san Allah idan Baki zauna ba Zan daura ki a bisa cinyata ki zauna in kuma rikeki har sai na gama maganar da zanyi ko bazan iya ba?
Tayi shiruuuuu, sai Kuma ta zauna saboda tasan karamin aikin sa ne sai dai idan ya aiwatar daga baya ya bada hakuri.
Ya bita da ido Yana murmushi..... Ta Kara tsuke fuska Ina sauraron ka ba ka tsareni da ido ba......
Me yasa Kika tafi Kika barni jiya?
Saboda ka gane baka gabana bana son wannan shisshigin, Kuma na Kara fahimtar fakai bana son kana taba ni na tsani hakan .
Kin tabbatar bana gabanki?
Ta kalleshi shekeke Zan ma karya ne don Ina tsoronka ko kana nufin...... Ina nufin mufeeda ce ta Kara Bata Miki Rai ko?
Mufeeda? Mtseww a'a ka manta.
Idan ba ita bace me yasa Kika hasala sosai Kika tafi Kika barni?
Saboda ka rike ni na kuma fada maka bana so..... Me yasa ke bazaki daina abinda nima bana so ba?
Ajiyeni kayi? Ko kana iko dani da zaka Sanya mun doka kace kuma dole sai na bi?
Kiyi hakuri, ya fada a hankali.
Tayi sokoko ta kasa ci gaba da masifar.
Ya tsareta da ido, Dan Allah kiyi hakuri naji nayi kuskure bazan Kara ba I'm sorry please.
Tayi shiru,
Bana son fadan nan wallahi, bana son kina wannan tada jijiyoyin kina fushi dani bana so ko kadan please kiyi hakuri shikenan ko?.... Ba shikenan ba, sai ka mun alkawarin bazaka Kuma taba ni ba sannan.
Yayi shiruuuu, gaskiya ban yi alkawari ba amma Zan kiyaye.
Ya wuce ko?
Eh, ta fada a hankali.
Mun shirya?
Ta dan harareshi.
Yayi Yar dariya. Mun shirya ko?
Um, ta ce tana murmushi.
Hmmm, Bilkisu kenan kina yarda Kika ga dama.
Karfe nawa Zaki kawon tuwo?
5, ta ce .
Lokacin na gama mutuwa da yunwa ko?
Ba abinci dare zakaci ba?
Waya fada Miki?
Shi zanci a matsayin lunch..... Tuwon???
Yayi Yar dariya yes!
Hmmm,
Zaki kawon irin two din nan?
I'll try. Ta fada a hankali.
Waye Zaki Aiko ko nine Zan turo?
Zan kiraka idan na gama dai.
Ya Mike tashi muje.
Ga book din ta Mika mishi .
Yayi Yar dariya daman ke nake bukata ba Shi ba...... Ta zaro ido what?
Ya Kara yin dariya ya ce Ina nufin ke nake so kizo inyi magana dake ba littafin ne a gaba na ba.
Tace hmmmm.
Suka jera suna tafiya..... Tana tsallaka titi sadeeq ya karaso suka wuce.
Ta zagaya can baya wurin Mai nama ta siyo tsoka Mai kyau ta Shani kilo daya.
Tana shiga ta cire hijab ta Fara hada Miya...( Duk kudi irin nasu Bilkisu baisa anyi sake da koya Mata girki ba ) har catering school tayi ga karance karance da tambaye tambaye saboda girki na daya daga cikin abinda take so a rayuwarta.
Ta shirya miyar kuka Mai Rai da lafiya, naman yayi ruguf a ciki wurin Aisha ta Samo kukar da daudawa saboda bata dasu Kuma Bata Kai ga ta siya ba, anan daman take siye.
Duk wacce taji kamshin sai ta leko. Tana gamawa ta daura tuwon bai wani dauki lokaci ba, karfe daya da kwata ta kullashi a leda, ta janyo sabbin coolers manya cikin kwali Wanda batayi amfani dasu ba daya kawai take amfani da ita karamar tana zuba Miya.
Ta jera tuwon guda Sha biyar aciki.
Ta zuba Miya ga Mai bi Mata duk naman ta kwashe musu kaf! Ta bi da manshanu saboda bata rabo dashi ita ma'abociyar taliyar hausa ce dahuwar daudawa Tasha manshanu.
Ta kwalala mishi ta rufe.
Ta jera a basket ta Sanya mishi gwangwanin biscuit biyu cikin wadanda ya siya Mata da lemuka kala kala, ta dauki basket din da 200 ta fita.
Napep ta tsaida tare da mishi kwatancen hostel..... Zan kirashi ya fito sai ya karba sunan sa Anwar..... Anwar? Ya zaro ido... Anwar din zai fito ya karba? Ta banka mishi harara ka San sa ne?
Ni kuwa na sanshi an bani abinci na Kai mishi kwanaki nafi awa banga kowa ba na Kira abokin sa da aka bani number sa Koda yaji zancen nawa ya kashe waya bai Kara..... Malam zaka Kai mun sakon Nan ko na nemi wani?
Zan Kai Hajiya Amma idan bai karba ba Ina Zan ganki saboda wadancan kayan har Yanzu suna gidan mu...... Kaga compound gashi can??? Ka ce Bilkisu kake nema ta ajiye mishi basket din ta bashi 200 ta juya kawai.... Ya kalleta a yamutse wahalallu.....
Ta kanga waya a kunne tana Kiran sa..... Barci yakeyi kasa rika Kuma yanajin dadin barcin.
A hankali wakar *Because you love me* ta Fara tashi ta cylindion.
Yayi firgigi saboda Bilkisu kadai keda ring tone din.....
Hello ya fada cikin muryar barci.
Ina hanya Zan kawo maka tuwon na kusa karasowa na sameka bakin gate din ku kada ka barni Ina jira......ta kashe wayar.
Idanun sa suka bude tangaran ya bi fuskar wayar da kallo..... Ya Mike zumbur ya zura jallabiya ya fice da silifas kafarsa.
Dai dai tsayuwar Mai napep din Yana hango napep yanufe ta da sauri Yana lekawa..... Kai ne Anwar?
Sai kawai yayi murmushi watau yarinyar nan dabara tayi mishi don ya fito?
Ya kalleshi eh, tare da Mika hannu ya karbi basket din.
Yasa hannu aljihun jallabiya ya fiddo 500 ya Mika mishi.... Ta biya yallabai.
Yayi Yar dariya to in mayar kenan baxaka Kara ba tunda na fiddo?..... Yayi charaf ya karbe Yana fadin wazai mayar da alheri?.
Na gode yaba napep wuta Shi Kuma ya nufi hostel Yana murmushi.
Ya bishi da kallo Yana jinjina Kai. Yanda suke fama da student wurin neman ragi da amsar chanji amma ga wani na kyautar 500, ita Kuma ta biya 200 zuwa kawai..... Wurin Nan akwai magana ya ce kafin ya chilla keken titi.
Sadeeq nata barci bai motsa ba. Yasa kafa ya Kai mishi harbi.... Tashi Dan ubanka Bilkisu ta Mana girki..... Zumbur ya Mike Yana kallon basket din.... Yayi dariya wallahi tuwon ne ta kawo .
Yunwa sukeji Daman, sadeeq ya Fara kwashe lemukan Yana ajiyewa kasa, sannan ya fiddo coolers din, kamshin manshanu ya buge dakin Anwar ya hadiye wani tsinkakken miyau ya gyara Zama .
Baiwar Allah hada biscuit ta debo da lemuka...... Tana so ta rage su ne sun Mata yasa Anwar ya katse Shi Yana murmushi.
Sun kwashi tuwon sosai musamman Anwar kulli hudu suka Bari.
Amma fa yarinyar ta iya girki in har itace tayi.... Ita tayi nasan bazata ba kowa yamun ba ya janyo waya .
Hello ta fada tana Yar dariya..... Ni Kika mayar gaki nan zuwa ko?
Ta kyalkyace da dariya.... Tuwon nan yayi dadi fa ga Sadeeq nan Yana lasar kwano.... Shi na Bari Yana lashewa karya yakeyi ya fada da karfi.
Ta tuntsure da dariya..... Na gode sai na maido kwanonin Allah ya biya thank you so much Bilkisu Mai gadon zinari...
Ya fada Yana dariya.
Ta ce hmmm.
You and this your hmmm. Bye wanna baf. Ya kashe wayar.
Haka kawai taji ranar ta Mata dadi tana nishadi. Wunin ranar wani nishadi takeji.
Akan hanyarsu ta dawowa daga masallaci isha'i take ba Aisha labarin wayar da sukayi cewar yaci tuwon.
Kamar daga sama suka ga mutane gewaye dasu hada maza..... Gabansu ya Fadi suka tsarata ainun Aisha tayi karfin hali tace lafiya?
Mufeeda suka gani ta fado gabansu tana taunar chingam.
Ta kalli Bilkisu ke karamar Yar iska ce wallahi.... Ni zakiyi ma karuwanci?
Akan Anwar har kisan Kai Ina iyayi na rantse da Allah ta daga hannu zata kwada Mata Mari akayi charaf da hannun aka rike Shi ta baya.... Kowa yabi hannun da kallo zuwa inda aka Kama don suga waye?
Anwar ne yasha boyel fari kansa da hula kube ya murzata irin sa hular kanawa sai kamshi ke tashi, hannunsa dayan rike da basket........✍🏼
*ZAINAB DAHIRU WOWO DUTSINMA*💖
*KAUNAR KI AZIMUN CE Ina yinki over RUKAYYA BAKO DANBATTA* *ZAINAB WOWO NA JIN JINA MIKI ALALH YA SHIRYA ZURI'A AMIN*
A ringa mun uzuri, Ina zuwa aiki, Ina da miji Ina da Yara kafin na Fara rubutun na fada I won't be able to post all the time na Fadi haka saboda Ina da hidindimu.
Alawiyya ciwon ciki🗣🗣🗣🗣🙄🙄
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣6⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.* ( Allah ya Kara tsareki daga sharrin munafukai Kuma azzalumai ).
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
************
*Federal University dutsinma*
......Ta rike kugu ta tsare shi da ido sannan ta ce *Who are you?*
Ya kyalkyace da dariya *Nine Anwar*..... Wallahi ka Fara bani tsoro ni ban yarda da Kai ba,kawai ta firgice mishi tana baya baya...... Tana neman Tara mishi jama'a ya Fara magana a hankali ```look calm down please I'll explain let's go```.......ba inda Zan bika sai kwallah sharrrr, duk jikinta ya tsinke da rawa.
Ya zaro ido yace ```this is serious```....... Yallabai an saka a mota.... Please zanyi magana bani minti biyu just go away...
Bilkisu please kizo muje Zan Miki bayani.... Wallahi bazan bika ba. Kai Bari na fada maka ni ban ma yarda da dakai ba......sai kuka.
Ya runtse ido yace ohh my God this girl nawaoooo.
Ya fiddo waya, ya Kira sadeeq.... Sadeeq please come to Abis super market now am there with Bilkisu... Ya latse wayar..... Kiyi shiru Dan Allah ke ba ki wuyar kuka what's wrong with you???
Ta mishi banza...
Ya sa hannu zai kamota tayi baya saura kadan ta fada cikin kwalayen lemuka.... Zaki Fadi fa ya daka Mata tsawa.
Ta makure wallahi kana tabani Zan maka ihu.
Ya kura mata ido kawai ya maida hannuwa ya rungume.
Yana hango sadeeq mashin ya ajiyeshi ya fita da sauri..... Please save me she's suspecting me...mtsew ya doka tsoki ya wuce Shi.
Tana tsaye ko motsi ta kasayi, sadeeq ya kalleta zo muje Bilkisu kinji.
Duk jikinta ya mutu ta biyo shi, ya bude Mata mota tana Zama shima ya shigo ya rufe kofa, Sadeeq ya shiga gaba suka tafi.
Bayan an sauke kayan kaf, sadeeq ya kalleta ya akayi ne Bilkisu me ya faru?
Kwallah suka zubo mata, Dan Allah kiyi hakuri kiyi shiru menene ya faru? Idan Kuma kina da tamabaya akan Anwar kiyi mun Zan baki amsa wallahi...... Wanene Anwar?, Wallahi ni ban yarda dashi ba, duba ka gani ta nuna mishi tulin kayan da hannu wannan siyayyar hankali ce? Kuma naga dollars sun fado aljihun sa yace ajiyar ka ce he's always hiding something from me why?.…..
Kiyi hakuri...... Wallahi bazanyi hakuri ba yace mun Shi a kauyen Kano yake Yana business da wani ubangidan sa Kuma...... Karya yakeyi. Sadeeq ya katseta.
Ya kalleshi da sauri, me kake nufi?
Ina nufin gidan ku akwai kudi Kuma cikin garin Kano kake ba kauye ba. Ya kalleta what else do you want to know?........ Ya ingijeshi shikenan ka tafi tunda taji daga bakin ka Zan Mata bayanin saura.
Ya yi dariya, wannan rawar kafar da kakeyi Shi ke tona maka ASIRI..... I said go ya Kara tura shi.
Allah ba inda zanje.
Bilkisu karya yakeyi babba gida ya fito.
Ni meye nawa a ciki da yake boye mun? Ta fada tana hararar sa, ya yi murmushi hankalin ki ya kwanta Yanzu?
Ban sani ba ta juya...... Ya kamota, me yasa baki ganewa ne ke? Nace idan Ina Miki magana ki daina tafiya bazaki daina ba ko? Sai ranar dana kamaki gaban wadanda kike ji ma kunya Zaki.....Amma Kai iyakar Dan iska ka Kai.
Saketa wallahi.
Ya saketa Yana Yar dariya.
Kinga Bilkisu je kirawo kawayenki su shigar Miki da kayan Nan.....bazata dawo ba Kuma wallahi binta zanyi ciki Kama fada Mata.
Don't mind him jeki abinki.
Ya bita da ido.......
Zaka rikita Yar mutane Anwar wallahi ta tsora fa da gaske...... Ya kwashe da dariya kawai.
Asirin ka ya Fara tonuwa sai ka yi kokari Kuma Yanzu ka *FURTA* Mata.... Uwarka.... Yakai mishi duka.
Yarinyar can sadeeq rigimammiya ce Kuma shagwababbiya...... Komai sai ta bude Baki tana kuka.
A gaskiya ka takura mata..... Fitowar su yasa ya tsayar da maganar.
Ko kallonsu baiyi ba ya ce Bilkisu minti biyu..... Ya danyi gefe can nesa.
Tayi tsaye, sadeeq ya kalleta kije kada ya Kara Mata Mana lokaci I'll talk to him please.
Ta wuce kanta kasa, ta rasa inda zata sa ranta.
Ta tsaya nesa dashi,
Ya kalleta ki matso koni nazo Nan.... Ina jinka daga na...... Taku daya ta ganshi gabanta wallahi kina motsawa Ina kamaki, ya fada.
Tayi kasa da Kai.... *tawa ta sameni ni Bilkisu* tace a zuciya.
Ya kamata kiyi mun godiya ko?
Ko nayi laifi ne?
Hmmm, na gode Allah ya biya.
Good, yace Yana murmushi.
Ya kalli hannun sa *I really like this watch honestly*
Ta ce hmm, kawai.
Yanzu hankalin ki ya kwanta kin Kuma yarda dani tunda kinji na fito daga babban gida?
Um, ta ce a takaice.
Gobe ba lecture ko?
Ta ce um.
Sai dare kenan zamu hadu?..... Anwar Dan Allah ka rage zuwa wurina bana son abinda zaiyi affecting karatu na gaskiya.
Ya kura Mata ido yayi shiru.....har sai da ta dago ido ta kalleshi.
Ta mayar da Kai kasa.
Kamar zaice wani Abu sai Kuma ya fasa yace okay I'll try.
Ta ce na gode, sai da safe.....
Ya matsa baya kawai ya bata wuri ta wuce.
Ta Dan kalleshi kadan fuskar sa ta canza alamar damuwa.... Kirjinta ya buga da karfi.
Kamar tayi magana Kuma ta fasa ta wuce.
Sadeeq na tsaye su Aisha Kuma sun shiga da kayan, ta mishi sai da safe ta wuce....
Har ta shige idon sa na kanta ya kalli sadeeq shi Kuma ya banka mishi harara, wannan rawar kafar ita zata......I don't know how to control my self. Abun ya Fara damuna.
Wata muguwar dariya sadeeq ya saki tare da fadin *Anzo wurin.*
Murmushi kawai yayi.
Kana hauka ne kayi Mata irin wannan shopping din?
Mtsew wallahi Bilkisu da kake gani ta banbanta da ko wace irin mace class din yarinyar yayi yawa could you imagine she refused to take abinda takeso sai da taga da gaske Zan kwashe kayan shagon?.
Da sai ka bita a haka for once gaba gaba idan kun Kara sabawa sai ta dauka...... I don't think so.
Kuma wadannan banzayen dollars din ne suka rikitata cos har muka Kare she was shocked but couldn't..... Gaskiya ta firgita.
Ya kamata fa ka Kama kanka gaskiya wallahi kada ta birkice maka kuma ko ta tsorata tsoron yasa ta gujeka.
Mtseew.... I said I'll try. Ya fada Yana yarfa hannu.
And ka rage kakkamata fa..... Ba laifina bane wannan fa, sadeeq yarinyar nan fa baza ka gane ba. Wallahi sai muna tsaka da magana sai ta nemi guduwa I told her this is what will happen idan tayi she refused to listen....and I have no choice than.... This is not an excuse idiot. Ya katse Shi.
Ya kamata fa ka duba kada kazo ka kasa shawo kanta bayan ta rikice maka..... Mtsew naji Zan jaraba.
Yanzu ai hankalin ka ya kwanta ka fada Mata Ina da kudi..... Kuna da kudi dai ba kana dashi ba.
Bari kaji na fada maka a yanda kayi Mata Yanzu wannan kadai ce hanya da zata fisshe ka.
Kana tunanin Koda kudi nane da gaske kana iya wannan gabatar? Kayi abinda hankali zai dauka Mana. Amma Yanzu na fada maka Kuna da kudi komeye ta dauka zata ajiye.
A yanda ta firgita some muka fada Mata bayan wannan wallahi Koda ta yarda a fili a zuciyarta zata ci gaba da wasi wasi Kuma hakan zai haifar Mata da bincike akanka... Kayi tunani Mana.
Kuma fa hakane.
Yawwa.
Amma Yanzu kaga tasan Kai Dan masu kudi ne zaka iya komai shikenan.
Yayi ajiyar zuciya *I too much like you sadeeq*
Suka kyalkyace da dariya tare da tafawa......
Aisha kadai ta tarar dakin a zaune ta tasa Kaya gaba tana kallo.
Ko takalmi bata cire ba ta fada bisa katifa....... Aisha na shiga uku.
Wai ya akayi ne? Fada kukayi da Anwar din bayan fitar ku? Naga alamun kinyi kuka Shi Kuma sai babbata Rai yakeyi...... Aisha Anwar yafi ciwon ciki.... Ta kwance Mata zance kaf!
Ko kadan Aisha bata razana ba. Sai tayi murmushi tace, ni wallahi nasan Anwar Dan manyan mutane ne. Haba kiyi tsam da Rai ki kalleshi da kyau ya Miki kama da mazauni kauye?
Ko fatar jikin Anwar Kika kalla kinsan ana rayuwa cikin A/C da Jin dadi.
Bari in Baki karamin takadiri ki kalli yanayin shigar da yakeyi duk kayan Anwar tsadaddu ne daga manyan kamfuna manya manya irin su *Gucci, M&S, C&K* ke gasu nan. Ji takalmomin da yake sawa..... Haba mutane, Ni wallahi nasan karya ne ace duk sadeeq ke musu sai dai na yarda shikeyi ma sadeeq saboda ko dressing yanayin dauka a jiki ma ba daya ba Koda kuwa iri daya suka saka .
Ji lokacin zuwan su daddy ke baki lura bane Amma wallahi wani taku da Anwar keyi nasan yaron yaji bariki wallahi.....
Ke ni al'amarin sa ya Fara bani tsoro Aisha...... Hakuri zakiyi sonki yakeyi Kuma ya kasa *FURTAWA* kawai idan ya Miki kina sonsa Ina Baki shawarar kada ki Bari wata tayi Miki shigar kutse sannan kada ki yarda ki nuna kin San inda ya dosa ki barshi har ya gaji ya *FURTA* idan da gaske yakeyi.
Koda yake wannan hauka haukan da ya Fara tabbas saura kiris ya *FURTA*....... Aisha bana iya wa Anwar har ga Allah..... Ba Kya son sa?
Ta tsare ta da ido...... Tayi shiru ta kasa magana.
Kinji?
Idan bai Miki ba ki fada mishi ya rabu da ke, naga dai yanda Yan Mata ke neman kashe kansu saboda Shi Amma ke ya zabe ki kamar tumun dare Zaki..... Understand me please.
I'll never understand you. Namiji kowa da kalar soyayyar sa, Anwar miskili, gadararre, Wanda ya Raina kowa kije kina bada labarin da kike bani Yanzu wani sai ya mare ki saboda cewa zasuyi karya kike yi amma Ni ganau ce ba jiyau ba.
Amma ji yanda yake Miki rawar kafa.
Wallahi Yanzu dan ana farkon dawowa ba mutane Amma tabbas ni nasan wannan semester din akwai daru za 'ayi kallo. Sai ki dage..... Abinda ke tayar mun da hankali kenan wallahi.
Tayi dariya zai tare Miki nasan dole ya..... Wani abun ba agaban sa zai faru ba Aisha.... Yanzu ni ya zanyi da wadannan Kaya ni Bilkisu.... Ci zamuyi. Yanzu fa aka dawo.
Ai wallahi mun gode......... Wayarta ta Fara Kara.
Ta kalli Aisha Anya Anwar zai barni nayi abin kirki wannan semester din?..
Tayi dariya ta kwashi biscuits da wasu tarkace tace keni sai da safe...... Taja Mata kofa.
Ta kanga wayar a kunne ba tare da tace komai ba...
Ko har wayar ma an Sanya Mata doka?.
Ya fada Yana Yar dariya.
Hmmm, kawai tace.
Ke na gaji da hmm, dinnan da kike neman ki ringa kawoshi bana son sa ki bude Baki kiyi mun magana kinji ko?.
Toh, tace a hankali tana murmushi.
Da gaske ba Kya so Ina zuwa wurinki?
Eh, tace da sauri.
Saboda me?
Ta runtse ido anya mutane sun San Anwar kuwa da ake mishi shaidar baya magana?... Kinyi shiru. Ya katseta.
Haka Nan,
Baiyiwuwa ki fada mun dalili ko Kuma gobe ki ganni...... Dokar daddy ce, sannan zuwan naka zai rinka haddasa mun fitina tsakanina da Yan matanka, idan Kuma aiki yayi nisa Zan Sami raunin karatu...... Zuwa gidan naku?
Eh,
Fine. Zan daina zuwa shikenan ko?
Eh, ta ce tana murmushi.
Idan Zan ganki muyi magana Kuma fa?
Sai na sameka class....fine, gobe mu hadu new lecture rooms by four. Yana fadin haka ya kashe wayar.
Ta bi wayar da kallo tace ikon Allah..... Allah ya kawoni ni Bilkisu.....
Tayi shiri daga sallar la'sar, a hankali take tafiya ga nisa daga masallaci zuwa classes din, kanta a kasa kadan kadan take gaisawa da mutane.
Kugin mashin taji a bayanta tayi saurin Kara matsawa gefen titi, gabanta suka tsaya, ya sauko sanye da kananan Kaya kamar kullum ya rufe ido da facing cap... Ajiye ni a nan.
Ta dago ido da saurin Jin maganar sa. Shida sadeeq ne bisa sabon mashin fari duk leda jikinsa.
Sadeeq Ina wuni ta fada tana murmushi.
Lafiya Lau Bilkisu.
Ta Dan kalli gefen sa Ina wuni.
Yayi kamar baiji ba, ta ce ai kaji tsiyar Shi dizgi wurinsa bai daukeshi bakin komai ba.
Ka kawo man upstairs Yanzu please ya fada Yana kallon sa ya juya da mashin din Shi Kuma ya jera da ita suka ci gaba da tafiya bai ce komai ba,
Ina gaishe ka amma kayi shiru.
Ya dago ido cikin facing cap kince sadeeq Ina wuni Ni Kuma kin wani ce Ina wuni sunan nawa Yana Miki wahalar fada ne?
Murmushi tayi kaii ikon Allah Wai haushi kaji?
Anwar Ina wuni?
Sunana Hamza.... A'a Nan Kuma daya fa. Sunan da kowa ke kiranka Zan ambata sai dai idan kana neman magana ne sai inji.
Shiru kawai yayi Mata.
Tayi Yar dariya yau gadara ake ji, ta fada cikin zuci tana satar kallon sa Yana ta faman Shan kamshi Yana Bata rai.
Maganar meye zamuyi kace mu hadu yau?
Kina sauri ne?
Tayi dariya ohh ni Bilkisu halan bani da ikon tambaya.
Murmushi kawai yayi ta gefen kunci.
Suka shiga class din ba kowa sai mutum daya shima da alama chargy yakeyi, kasancewa farkon semester ne.
Ta toge bakin sit....ya kalleta wuce ciki ko ni Zaki saka cikin kujera?
Ka zauna ni Bari....... Ya ingizata da karfi tayi ciki ya bita dole ta matsa da sauri kada ya Kara kamata...... Kina da gardama, na fada Miki idan Baki son Ina kamaki ko taba ki kada kiyi mun gardama amma da alama kina da kunnen Kashi...... Ya karasa maganar Yana Zama kujerar kusa da ita.
Da sai ka bada tazarar kujera daya tunda magana ce zamuyi ba karatu ba...... Bazanyi hakan ba.
Tayi shiru tare da sunkuyar da Kai tana wasa da yatsun hannunta.
Yasu daddy?
Lafiya lau, dazun munyi waya yace mun zasu tafi Paris da mommy.
Haba?
Allah.
Yayi murmushi *Yan gayu*.
Ta Dan harareshi.
Dafatan baki sanar da kawayenki abinda ya faru jiya ba, kin San bana son yawan surutu ne yasa bana nuna ni din wanine.....
Aisha ce Kuma ta rigani sani... Tasan meye?
Kuna da kudi?
Kice wallahi.... Tayi murmushi Allah kuwa, ta bashi labarin yanda sukayi.
Ya danyi tsoki, kawai don Ina sa Kaya masu kyau Shi zai nuna muna da kudi? She's not well.
Eh din. An dai gano ka.
Ya danyi dariya kawai.
Wace magana zamuyi kace nazo?
Ba gashi munayi ba?
Ko wata ta daban kike so muyi?...... Tsayuwar mashin din sadeeq yasa maganar da zatayi ta koma.
Ya dora Kai bisa table ta bi bayanshi da kallo.
Ko baka lafiya ne yau? Naga duk kayi sukuku Anwar..... Sadeeq ya shigo ya ajiye ledoji bisa table din gashi nan Zan je na karbo sako isah kaita idan ka gama ka kirani.
Bai dago Kai ba Yana duke ya rufe ido kawai.
Tayi shiruuuuu tana kallonsa...
Anwar..... Ta kirashi a hankali.
Ya dago Kai ya akayi?
Baka lafiya ne?
Ya yamutsa fuska yunwa nake ji ..... To ba gashi nan sadeeq ya kawo maka ba Kuma kana Jin sa Anwar kamar karamin yaro kayi shiru.
Fiddo ki ban ya fada tare da kokawa ya kife..... Bata San lokacin da tayi dariya ba ta Mike tare da saka hannu ta janyo ledar sai gogar jikinsa takeyi yaki Kuma gyarawa.
Ta fiddo hollandia biyu milk and strawberry, tashi gashi ta fada tare da fiddo wata leda, katuwar gasassar kaza ce taji cabbage da kayan miya nade a foil paper.
Ta bude ikon Allah dadi za'aci Alhaji Anwar..... Ya dago Yana Yar dariya keni wallahi tuwo nake son ci miyar kuka..... Ta kalleshi ka iya tukawa ko?.
Yayi murmushi Allah da gaske nake Ina son cin tuwo Bilkisu ya langabe Kai.
To ka je ka siyo Mana.
Ke zakiyi mun. Zan siyo semo kiyi mun anjima...... Kam wallahi kada kasa ma ranka abinda bazaka samu ba. Zan samu yau sai naci tuwo Kuma ke zakiyi mun.
Ya bude kazar ya cire wurin cinya ya Fara ci.
Tayi shiru kawai.
Wane kike so milk din ko strawberry?
Kai wane zaka sha?
Bani da choice as long as nidai cikina zai cika..... Ta yi dariya kawai ta dauko milk din ta Fara Sha a hankali.
Zakici kazar ko kunya kike ji?
Ta Kara Yar dariya, na ci abinci na koshi.
Me Kika ci?
Taliya muka dafa.
Zaki mun tuwon?
Zan maka Amma ka Bari sai gobe yau dai marece yayi sosai.
In siyo semo din?
Ina dashi Kar ka damu.
Good.
Ba za kici ba da gaske?
Allah na koshi....... Zan baking baki matukar Baki sa hannu kinci ba..... Rage mun idan naje daki zanci da dare.
Mtsew, Allah ya raba ki da gardama.
Yaci gaba da cin abinsa.
Mamaki kawai takeyi Wai me yasa maza Basu da kunya ?
Kamar ya karanci zuciyar ta ya kalleta...... Ni banjin kunyar ki.
Ta danyi dariya ....yabi kuncinta da kallo....
Kin San cewa kina da kyau kuwa?....... Ta kalleshi da kyau me kace?
Yayi murmushi kina son in maimaita abinda Kika Riga kinji?
Hmm, tace.
Samarin ki nawa?
Zaka Fara ko?
Ana zaman lafiya ka Fara tamabayoyi marassa amfani kuma azo ayi fada ko?
Ba Kya so na sani ne?
Ina ruwanka da samari na an fada maka irin ka ce da kowace jik and jak ...... Ya sa hannu ya buge Mata Baki...... Kai Kai Kai ta rike Baki.... Sai tayi kwal kwal zatayi kuka.
Ya harareta wallahi yau kikayi mun kuka Zan baki mamaki ke baki da aiki sai shagwaba.?
Gaskiya bana son abinda kakeyi mun Anwar..... Gaskiya bana son abinda kake yi mun Anwar ya maimaita Yana kwaikwayonta.
Karfe nawa Zan zo na karbi tuwo gobe.... Zan Aiko maka Dan Allah ba sai kazo ba ko ka turo sadeeq ya karba.... Wani kallo ya jefe ta dashi kafin yace *why are you pushing me away?*
Ba haka bane...... Haka ne.
Bazan zo ba, ki Aiko mun ya Miki ko?
Tayi murmushi eh,
Duk ya kware tsokokin kazar ya tura Mata kasusuwa ga naki..... Ta danyi dariya wallahi kana da ci Anwar...... Ya yunkura zai Kara buge bakin ta tayi baya tana dariya.
Tashi muje kada six tayi na gaji tunda ka gama.
Ki shanye tukun.
Tabbb bazan ya ba.
Shi yasa ba Kya kiba.
Hmm, kawai tace.
Wayarsa tayi Kara Yana dubawa ya Mike please Ina zuwa...... Ta mishi wani kallo ya nuna Mata fuskar wayar Alhaji Abbas ne kin gani?... Ya fice Yana dariya kunya ta Dan Kama ta ganin zai fassara ta.
Ya Dan dade kafin ya dawo tana ta latsa waya taji yayi fit da ita.......
Bani naga suwaye samarinki.......Aka Kara kiransa a waya.
Ya kalla sai kawai yayi tsoki, sai ka bar nan ka kirata ne?...... Sai bani kawai yayi picking yasa handsfree.....
Ya akayi?
Haka ma zaka ce?
Baki bani amsa ba nace ya akayi ne?
Jiya an Kai maka abinci ka dawo dashi, tun jiyan nake kiranka kaki dauka Wai me yasa..... Nace kiyi mun abinci?
Sai kace sannan zaka ci?
Ke idan Baki da abin fada Ina da abinyi ya kashe wayar.
Ya kalleta kin yarda Yanzu ita ce ke damuna bani nake binta ba?.
Kai ji Ni me nace toh?
Sai kince? Rigimar ki ai nasan ta.
Wannan semester din na ganki da wani Kato wallahi sai naci ...... Maganar ta makale ta zaro ido ya Mike da sauri tashi muje na rakaki.
Ka karasa abinda kake son fada?
Yayi murmushi kawai,
Ya daure fuska ta mike ka Isa ka hanani gaisawa da mutanen arziki na?
A matsayin a na wa to da zaka Sanya mun irin wannan dokar?
Ke ya Isa tunda nayi shiru kuma Dan Allah ki kyaleni.
Suka jera suna tafiya.
Suna karyo wata kwana su mufeeda na tahowa ta tsaya gaban sa kutumar uba Wai kana cikin school din Nan............???????✍🏼
*Zainab wowo* 💖💖
Zan kawo muku wani true life story anjima Dan Allah Ina bukatar comments din ku please. Na gode masoyana Ina kaunarku.💖
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣9⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
***************
*Federal University dutsinma*
........ Bani da wani feelings akan Anwar he always telling me we are just friends....just friends, so Ina tunanin all this is because he likes me as that shine kawai....... Kada ki yaudari zuciyar ki wallahi....... Kada ki rantse Anwar bashi da alkibla.
Idan Yana Sona let him say it idan Kuma bai *FURTA* ba I cannot waste my time and wait for unknown..... Anwar din ne unknown...yes to me he is.
Abinda na tabbatar wa kaina shine ko naji Ina sonsa bazan taba yarda ya gane ba bare har nace Zan fada mishi..nooo! Bana iya hakan.
Dai dai sunzo kofar gida, suka sauka Aisha ta biyota da sauri ganin ta yi saurin shigewa....... Amma saboda Allah bakya jin kin Fara son sa?
Tayi murmushi.
Um?
Aisha forget about this.... Dan Allah ki amsa ni. Ko kadan bakya jin kina sonsa?...
So!, So!.... Ta maimaita.
Suka bude daki ta fada bisa katifa..... To Wai ya zanji idan na Fara sonsa?
Yawan tunanin sa, son ganinsa ko Jin muryar sa, komeye zai yi zakiga baya Baki haushi.... Koda kin fusata zakiji azuciya Baki Jin haushinsa, kishin sa...... Tayi Yar dariya.... Please Aisha fita Kija mun daki barcin nan ya dameni.
Anya Bilkisu????
Anya meye?
To nidai Kisha oat din kada ki haddasa mun fitina anjima don Anwar sai ke wallahi.... Abeg go.!!
Zan fita but please Kisha.... Zan Sha Yanzu.
..........ya dafa kafadar sadeeq, kaji menstrual pain ke damun Bilkisu.... Ka dubi girman Allah kada ka nuna Mata kasan haka zaka Bata kunya Anwar.
Ya tuntsure da dariya, to me yasa Bata boyewa Dr ba sai .....
Sai ubanwa? Shi ba Dr bane? Idan bata fada mishi rashin lafiyar ta ba zai San wane magani zai bata ne?.... Ikon Allah, sadeeq akan Bilkisu wata Rana kilan ka dakan ko?
Tabbas, saboda ka takura Mata da yawa fa...... Meye abin takura anan.
Na dai fada ma, wallahi kada ka nuna kasan me ke damunta zata ji babu dadi... Kai nafi so ta Saba da Hali na tun Yanz.... Maganar ta makale da alama yayi *Subul da baka*.
Hahahahahahahaha, finally..... Ya galla mishi harara finally what?
Nothing forget...ya fada Yana dariya.
*Sixtus* ya shigo kunji anyi closing school till further notice?????
Sadeeq ya kalleshi saboda me?
Corona virus...... Anwar yace hazbunallah are you serious?
Of course. Ya fada.
Anwar yayi saurin daukar waya ya Kira academic secretary.... Ya tabbatar mishi....
Ya kalleshi sadeeq is true.
Ya zaro ido Nawaoooo..... ya zanyi da yarinyar nan sadeeq??
Kamar ya?
Sai yayi shiru..... Ya kura mishi ido huh?
Mtsew ya buga tsoki ya fita waje.... Ya bishi da ido Yana murmushi, saboda ya gano inda zancen sa ya dosa.
Abinda ya tayar mishi da hankali ganin student nata parking ana buga ma wadanda Basu dawo ba akan su yi zamansu.....
Ya Kira number Bilkisu gashi tana ringing Amma Bata dauka ba, saboda barci ta sanyata silent mode da alama ta sami yin barci.
Aisha ta Kyaleta har kusan karfe shidda ta wuni zungur tana barci... Ko da ta tashi wata azababbiyar yunwa ce ta tashe ta, ga mamakin ta taga Yar cooler kusa da katifar, tana budawa taga kuskus da miyar Dankalin turawa, tayi murmushi Allah sarki Aisha.
Sai da taci nayi nat! Sannan ta shiga wanka ..... Tana cikin saka riga Aisha ta shigo, kin tashi?
Ta fada tana murmushi, ta mayar mata da murmushin ta nuna Mata cooler da Baki tace Kinga alama can..... Sai duk sukayi dariya.
Yunwa ta tasheni, wallahi kin taimaka..... Ai kin shaa barci, Ni kuwa nasan haka na farka naga 23 missed calls..... Tabbb.
Kin kirasu ko?
Mommy kadai na Kira sauran sa nemeni idan ya damesuuu......wayar ta Fara kugi duk suka kalli juna.
Ta nufi wayar, ta Dan kalli Aisha *Anwar* ne.... Tayi Yar dariya Ina zuwa , ta juya tabar dakin....
Assalamu alaikum,
Kin tashi kenann....
Amsa sallama wajibi ne malam..... Wa'alaiki assalam. Sai me Kuma? Tayi Yar dariya, Ina wuni?
Ya kike ya jiki?
Alhamdulillah.
Cikin ya daina ciwo ko kina ji har Yanzu?
Bana ji da sauki sosai.
Zan kawo Miki maganin anjima kinji ko?
Ka bada akawo mun Mana ..... Saboda bakya son ganina?
Ba haka bane.
Haka ne Mana . Ba maganin kadai Zan kawo ba ai Ina son duba jikin ki ne...
Shikenan sai kazo.
Zaki iya dafan indomie din????
Innalillahi kaii Anwar fitina ne wallahi.... Nine fitina Bilkisu.????
Ta zaro ido kayi hakuri wallahi maganar zuci ce ta fito....... Da kyau Ashe a fili kike nunan ba wani abu kina can kina zagina cikin Rai ko?
A'a wallahi....eh Mana. Gashi kin kirani da fitina....Dan Allah kayi hakuri.
Bazanyi ba.... Ya Fara fada kamar da gaske Yana son yaga how much she care about him ... Kina da fuska biyu kenan Bilkisu? Watau a fuska kike nuna mun .....Anwar kayi hakuri.... Bazanyi ba nace.
Ba zakayi hakurin ba?
Gabansa ya Fadi ya tuna fadan su na baya..... Yayi saurin cewa zanyi amma ba Yanzu ba .
Sai yaushe?
Sai nazo anjima kin kalleni kin bani hakurin da gaske..... Tayi Yar dariya wannan na karya ne?
Da alama. Ya fada.
Shikenan sai kazo. Ya kake son indomie din?
Ki barshi kawai bana ci.
Dan Allah kayi hakuri..... Na ce ban hakura ba?
To ka fada mun yanda kake son indomie din kasan kowa da yanda yake son dahuwar indomie.....kiyi mun yarda ki ke dafawa idan zakici... Karfe nawa zaka zo?
Eight, ya fada Yana Yar dariya ko nayi latti?
Ta Dan harari wayar kamar Yana kallonta kawai tayi shiru..
Kinyi shiru kina ta Duran zagi a zuciya ko?..... Kaiii Anwar.
Eh Mana.
A'a wallahi.
To fadan da kikayi shiru me zuciyarki ta saka Miki?
Ta kyalkyace da dariya kaiii nikam na bani ..... Yayi murmushi.
Ke Kam kin bani zuciyar ta saka Miki?
Ta zaro ido... A'a.
To fadan me ta ayyano Miki.?
Cewa tayi eight din is okay..... Yayi Yar dariya are you sure???
Yes. Ta fada tana ci gaba da murmushi.
Shikenan sai nazo. Kin hada kayanki ko?
Sai anjima.
Ya zaro ido kinji labarin Coronan ne?
Eh, mommy ta fada mun da mukayi waya.
Yaushe Zaki tafi?
To gani dai.... Ban gane gaki dai ba.
Ka bari idan kazo anjima zamuyi magana.... Shikenan sai nazo.
Ashe yayi waya yace a kawo mishi mota da maganin. Ko da aka kawo sai driver ya juya gata haya yabar musu motar.
Katuwar mota kirar Jeep Amma Honda baka, Kai da kaga motar kasan lallai Mai ita *Don* ne.
Ta Sami Aisha daki, sai na jiki shiru.
Eh, wallahi Ina parking ne.
To Wai strike din ne ko Corona?
Duka fa, Anwar ya fada Miki?
Mommy, Ina tashi naga ta kira nabi Kiran,shine take fada mun, kema gobe Zaki wuce?
In shaa Allah, sai gida....Kare yasha taba. Duk suka bushe da dariya.
Ke sai jibi ko goben zaku wuce?...... Har na ma driver waya gobe in shaa Allah na fada mishi ana gama sallar asubah zamu bar garin nan six da izinin Allah..... Anwar din fa, ba dashi zaku tafi this Time ba????
Noooo, bama zai sani ba..... Gaskiya bazai ji dadi ba....kada Allah yasa yaji so what?
Ta kura Mata ido, wannan Jan ajin naki fa ya Fara yawa ki zauna idan zaren ya tsinke zakiyi wa kanki.
Tayi murmushi, sai dai ya tsinke Amma ko Zan rasa Anwar bazan taba binsa kamar rakumi da akala...... Yanzu me Zaki fada mishi? Ko kunyi maganar?
Bamuyi ba, sai anjima ya ce zaizo kawai Zan nuna mishi banyi deciding ba.... Bilkisu....
Aisha please mubar maganar Nan.
Dan Allah idan ya kawo Miki maganin ki dibar mun saboda Hafsa ( kanwarta ) ita ma the same problem with you.
In shaa Allah.....ohhh Wai carton, komai Shi sai yayi hauka..... Ba hauka bane kulawa ce.
Gasu mufeeda can time dinsa kawai suke so Amma sun kasa samu..... Haka ne .
Ai shu'umi ne wallahi. Nake ga kamar duk abun Nan Yana Axergurating ne don ya Sami sauki Yan mata.... Yanayi bil hakki da gaskiya.
Ko?
Allah kuwa.
Ta ce hmmm. Kawai.
Suleiman ya kirata, da sauri ta daga hello, Suleiman Ina wuni.
Bilkisu ya karfin jiki?
Na zo dazun har Kun fita da Anwar halan asibiti kuka je.
Eh wallahi. Jikin ma Alhamdulillah.
Mashaa Allah, sai Kika ji Kuma hutu ko?
Bari Kai dai.
Wallahi naji haushi da na Kara jinkirtawa Kinga da ban wahala a banza ba.
Ai kuwa. Ta fada.
Shikenan Allah ya say ya zamo alkhairi garemu duka ya kawo Mana karshen wannan fitina.
Amin ya Allah.
Sai nazo Allah ya Kara lafuya.....ta ce Ai.... Amma tuni ya latse Kiran Sam bai ji cewar zatayi wata magana ba.
Ta kalli Aisha naji Yana sai yazo kada yazo gobe na tafi ko in Kuma kiransa Kinga babu dadi.
Kyaleshi goben sai ki Kira. Yanzu kada ya zargi wani abu kin San maza..... Eh Kuma fa. Ta fada.
Ta dafa mishi indomie da kifin gwangwani, ta Sanya tarugu da albasa Mai lawashi sai kuwa spices dinta.
Tayi masifar dadi sai kamshi ke tashi..... Kafin ta sauke ya kirata.
Ta dauka hello...
Ina waje. Yana fadin haka ya kashe.
Gabanta ya Fadi,jikinta ya Dan dauki rawa, ( Wai me yasa Yanzu ko waya sukeyi takejin wannan yanayin? ).
Doguwar Riga ce jikinta blue, tana da duwatsu yayyabe jikinta.
Ta dauko hijab maroon har kasa ta saka, ko kwalliya batayi ba turaren da ya siyo Mata ne ta fesa kawai ta juye indomie a plate ta rufe ta dauki robar ruwa da maltina ta fita.
Yana hangota da Kaya ya fito daga motar..... Gabanta ya Fadi. Anwar a irin motar uncle? ( Wani kanin mommy ne Mai masifar kudi ) wurin Shi suka Fara ganin motar Shi bama Nigeria yake zaune ba Soja ne a America.
....... Ya karbi plate din Yana Yar dariya, kawo na taimaka Miki.
Ya shiga motar ya zauna wurin Mai tuki ita Kuma tana tsaye ta rike murfin kofar tana son ya karbi ruwan da maltina.
Ya Dan kalleta zagayo Mana ki zauna....um um Nan ma ya Isa.
Ya Kara kafa Mata ido , sai Kuma yaki cewa komai ya Mika hannu ya karbi ruwan.
Zaman kujera yayi ya sako kafafunsa waje duka biyun Yan facing dinta. Ta Dan ja baya ,yayi kamar bai lura ba .
Riga round neck navy blue ya saka da jeans dark blue. Kansa yau ba hula, ya kwantar da gashin sa inda ya bada kusurwa kusurwa ( waves ).
Yayi kyau matuka.
Ya bude plate din sama, kamshi ya daki hancin sa ya Dan lumshe ido waww.... Daga ji zatayi dadi fa.
Tayi murmushi kawai.
Ina folk din ko hannu Zan saka????
Ta Dan bude idanu innalillahi...Bari na dauko na manta..... Ta juya da sauri.
Kinga dawo ga wani Nan ...
Ya fada .
Ta dawo ya gyara fuska alamar seriousness yace duba aljihun kujera a baya akwai spoons dauko mun ciki.
Ba gardama ta ce toh.... Ta bude ta shiga lalube takeyi sosai tun kafar ta na waje har ta shiga motar ciki tana tura hannu kawai taji kofa ta rufe wani Abu yayi Kara Nan da Nan ta gane locking yayi.
Ta dago Kai da sauri sai taga Yana ta cin indomie din a hankali..... Au dama da spoon dinka a aljihu kana son na shigo motar ne...... Kina baya Ina gaba hakan ai ba matsala bane unless Zaki takura na dawo bayan..... Karka dawo ta fada da sauri.
Motar ta dau sanyi da wani da dadden kamshi..... Kamshin ya Mata dadi Amma hankalin ta duk ba a kwance yake ba.
........ Amma indomie din nan tamun dadi kin ci?
Eh, ta fada da sauri.
Kice wallahi na ci.... Ba sai na rantse ba.
To idan ma bakici ba nidai na cinye tas!
Ta ce hmm.
Ya bude maltinar ya kafa Kai.... Yana shanyewa ya kalleta kina da fridge ne?
A'a.
Yanaji da sanyi ko siyo mun kikayi?
Ina ruwanka Kai dai kasha maltina.
Ya kyalkyace da dariya. Wallahi ke Bilkisun nan kin iya gwasale mutum..... Ta harareshi kawai.
Ya dafa kujerar say ta baya ya juyo sosai Yana kallonta..... Dan Allah in dawo Nan....a'a wallahi ta fada da sauri. Yayi murmushi shikenan.
Yanzu yaushe Zamu tafi gida?
Kai da wa?
Da ke!
Tayi murmushi, tare muka zo?
A'a Amma tare zamu koma.
Shikenan mu jira gobe muga abinda Hali ya bada ko?
Ya rungumi kujera okay as you wish...
Ya Miko Mata ballin magani ungo Kisha ga ragowar can a boot ance kullum daya zakisha har kwana hudu.
Sannan every month da kin Fara expecting Zaki Sha sau biyu a Rana safe da yamma har ki ganshi ...... Ta mishi banza.
Kin fahimta. Eh. Ta ce a kagare.
Ya sumke dariya ganin tana ta faman kasa da Kai.
.....Wayarta tayi Kara, Suleiman ne. Ta Dan zaro ido a hankali ta daga tare da kangawa a kunne yayi fit! Ya fizge. *Suleiman eco* yaga an Sanya.
Nan da Nan annurin fuskarsa ya bace ya sa handsfree hello kana magana da Anwar..... Kawai sai Suleiman din ya latse wayar...... Ya kalleta kutumar uba ni zaima hanging phone???
Ta mishi banza.
Ya daka Mata tsawa meke tsakanin ki da Dan iskan yaron nan?
Akan me zaka Kira Shi Dan iska???
Ya zaro ido.
What?
Ai kaji abinda nace. Kai ya Kira? Akan meye zaka dauki wayar da ba taka...... Ya wurga Mata wayar ta daki kirjin ta yace get out of my car.....
Ta dago da sauri ta kalleshi ... Ke kurma ce? I said get out ya Kara daka Mata tsawa......✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Ayi hakuri da kadan yau ban zauna ba wlh
*Zainab wowo ce*💖
*ALAWIYYA NASIR MY FAVORITE THANK YOU SO MUCH TAWAJENA*🥰
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣0⃣
*Gargadi* Bana son ana rubuta mun komai a page din dana tura. Naga 1⃣9⃣ wat t rubuta *Anzo wurin* bana so. Duk wacce ta Kara taba mun page daga ranar *Wallahi wazai furta ya Kare*
Labarin Nan saboda soyayyar makarantar ne nake rubuta tashi na fada don ku nakeyi to a daure a karbi iya abinda aka gani.
Sannan masu cewa na Sanya sunan su a page ku sani cewa wallahi idan dambu yayi yawa bayajin Mai. Duk yanda kuke Sona wallahi nafiku. Akan KU nakan hana kaina abubuwa da yawa don kada na Bata muku. Dan Allah a bani uzuri. Ina kaunar duk Wanda ke Sona ko wanene wallahi bana Raina masoya.💖💞💕😘😍🥰💗
Tsoron Corona yasa har yau na kasa lekawa RIGASA KADUNA🤪
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.
****************
*Federal University dutsinma*
........Ta rude ta kidime Ni kake Kora..... Ya bude mota da karfi ya fita ya zagayo ya bude kofar bayan....get out I said are you dumb?
Kwalla suka zubo Mata sharrrr...... Ta sauko a hankali. Suleiman na gefe yaga ta fito.
Ya koma gefe ya tsaya, tana fita ya maida kofar da karfi gammmm. Ta kalleshi da sauri, ya banka mata harara am I safe now??? Idanun sa sunyi jawur duk sun kawo ruwan masifa.
Ta kawar da Kai ta nufi wurin driver ya finciko ta da karfi kada ki shigar mun mota...... Zan dauki plate ne ta fada kwallah naci gaba da shatatowa.....ya ingijeta ya kwaso plates din watso kasa....ya kalleta Yana zare ido you can go now!!!!!!........ Anwar duk akan Suleiman....... Ya doka tsoki ya juya zai fada mota, wata zuciya ta debeta Bata San lokacin da ta fizgo rigarsa ba ya dawo da karfi...... Kai har ka iya kamun irin wannan wulakancin in kyaleka??........ Ya zaro ido. Suleiman dake kallon su shima fiddo nashi....... Ya daskare ya sankame tare da tsareta da jajayen idanun sa.....Wai me yasa yarinyar nan bata tsoro na.????
......... Kwallah kwance cikin idanun ta, ta turashi da karfi bayanta ya daki murfin mota tayi kansa kamar zata matseshi duk ta fita hayyacinta......... Na rokeka kazo Nan????
Ya yunkura zai dawo ta mayar dashi da karfi wasu zasu wuce suka Dan tsaya kamar zasu fahimci wani Abu, hakan yasa Shi kasa biye Mata kada su Tara jama'a........ Na ce kiranka nayi kazo??????
Matsa Bilkisu in wuce..... Ta galla mishi harara sannan ta juya kadan ta kalli inda ya watsar plates din ta ce ```dauko su day hanmunka``` ...... Ya kalleta da sauri..... Wallahi tallahi ka dauko su ka Miko mun da hannunka ko Kuma nida Kai har abada mun rabu daga Nan...... Gabansa ya Fadi... Ya Kara kallonta.
Ta matsa nesa dashi ta tsaya tare da rungume hannuwa..... Kaka kara Kaka...ya yi shiruuuu..... Ban tilasta maka ba, kana iya shiga mota ka tafi, wacce ka koreni cikinta kana ikirarin *motar ka*........ Ya runtse ido, taci gaba da cewa Amma ka sani na fita motarka salin alin wallahi Alan plates din nan Zan rabu dakai rabuwa ta har abada........ Ya Kara runtse ido tamau.
In ba rainin wayo ba, Kai har yau baka ganin kowa da mutunci kana iya cin mutuncin kowa baka shakkar......kawai taga ya dauko plates din ya Miko mata. Fuskar sa murtuk....... Ta karba ta juya...... Kizo ki dauki maganin...... Bana so *jikan karuna*..... Ka hada da maganin da motar ka cinye nafi karfin dukiyarka da wulakancin ka Anwar...... Ya fizgota da karfi, Ni kike gayawa magana????........ Ta fincike an fada maka ta nuna Shi da yatsa wallahi Ka Kuma taba ni Zan sharara maka Mari....... Ya zaro ido what?????
Ta kalleshi shekeke....kafi karfin hakan ne? To idan kana musu ka jaraba... mtsewww ta buga tsoki ta juya.....ya tari gabanta da sauri....
Wai ke da me kike takama ne? Ya fada da karfi..... Lokacin ne Suleiman ya karaso.
...... Anwar meke faruwa ne...... Ji kakeyi tasssssssss ya ramtse Shi da Mari..... Ya kidime ya gigice..... Bilkisu ta ja baya da sauri tare da daura hannu aka...... Yana dagowa ya daga hannu zai Rama ya Kara wanka mishi biyu double one after another.....sai jini ta hanci......... Bilkisu ta kwada ihu zata ruga ya janyota da karfi ta dawo kanta ya daki kirjinta........ Gashi na taba ki , Kuma na Mari wannan Dan iskan sai ki Rama mishi Kuma ki hukuntani da wani Marin Wanda Kika mun...... Ta zukunna kasa ta fashe da kuka .... Ya kalli Suleiman ko bar nan ko na halaka ka....... Suleiman Dan Allah tafi..... Dan girman Allah Suleiman tafi..... Sai nanatawa takeyi tana kuka, yasa habar rigarsa ya toshe hancin ya wuce kawai Yana huci,... ya fizgi Wayarta ya Kira Aisha..... Anwar ne fito ina waje......
Cikin hanzari ta fito, ganin Bilkisu duke tana kuka yasa ta rikice wata kila ya Mata halin nasa..
Ya fiddo kwalin maganin ungo kije Mata dashi ciki, ko soke soken wuka mukayi hakan bazai shafi neman lafiyarta ba........ Bana so Ina ruwanka da lafiyata??? Aisha bar mishi tsiyarsa bana so, ta rushe da kuka........ Kin dai ga halin kawarki ko? Kiyi Mata fada........ Haihuwata tayi da zata mun fada?
Wai me ya faru Bilkisu??? Aisha ta bukata cikin damuwa....... Wai daga Suleiman ya kirani a waya fa, Ina abinda ya dameshi da wayata Ashe Yana son yace mun yazo ne ...... Uban me yazo yi?........ Kai me ya kawo ka? Ta daka mishi tsawa..... Ta kalli Aisha Kinga Marin da yayi mishi ya fasa mishi hanci........ Innalillahi yaushe? Aisha ta fada a rude. Yanzu Mana,
Ya buga tsoki, idan Baki ja mishi kunne yayi nesa da ke ba wallahi Zaki janyo mishi nasifa da bala'in....... Kai a wa? Ta Mike tare da rike kugu..... Ya kalli Aisha Kinga irin action dinta da mood ko? To a duk lokacin da wancen Dan iskan..... Ka daina zagin sa wallahi..... na ce mishi Dan iska ko Zaki Rama mishi?........ Don darajar Allah kuyi hakuri......... Bilkisu ta buga tsoki ta juya kawai ya fincikota da karfi........ Ta kuwa Kama hannunsa ta gantsara mishi cizo da karfi.....ya saketa da sauri Yana fadin Kai Kai Kai Kai, ta kwashi kasa ta watsa mishi a jiki sannan ta kwasa da gudu tayi ciki........ Tana shiga daki ta Sanya sakata ta ciki....... Ya biyota a guje, kafin ya karaso ta garkame........Aisha ta rude ta rikice gidan ya harmutse Jin irin hargagin da yakeyi akan ta bude..... Wallahi zan karya kofar nan ki bude kizo ki fada mun dalilin watsan kasa...... Ban budewa.......har daya yayi ma kofar ta fada ciki tayi tsalle ta Haye katifa ganin zata bigeta........ Aisha ta Fara rokonsa yayi hakuri ita Kuma ta makure ta Fara ihu tana kuka........ Ni Zaki watsa ma kasa saboda wancen Dan iskan........ Wallahi ba saboda Shi ba....... Ya sungumeta a kafada yayo waje Aisha da sauran mutane suka biyo su....... Ya juya duk shegiyar data fito sai na karya ta. Aisha zo muje........ Ko wace tayi dakinta tana surutai......... Kafin kace kwabo magana har kunnen mufeeda.
Ya direta jikin mota ya kalli Aisha tambaye mun ita dalilin watsan kasa.......Dan Allah kayi hakuri Anwar.
Kika kawai Bilkisu keyi......
Ya kalleta ke kina da gadara da taurin Kai ko? Kina tunanin duk wannan abun ba shine Kika janyo wa fitina ba?...... Dan Allah kayi hakuri Anwar. Aisha ta Kara fada.
Aisha na fadawa Yarinyar Nan bana son yaron can me yasa bazata kyaleshi ba?.......Akan wane dalili Zan kyaleshi Kai meye naka aciki da zaka hanani mu'a mala da wani?.....saboda..... Sai Kuma yayi shiru.
Saboda me?
To baka Isa ba, Yanzu na Fara kula Suleiman...... Kinji ko Aysha? Kinji abinda take fada ko?
Dan Allah kayi hakuri Anwar zata daina kulashi........ Yaudarar ka zatayi, ba Wanda ya Isa ya rabani da Suleiman Kuma ka sani daga yau bani bakai, bana son abotar kaje ka nemi wata idan na Kara ganin ka anan ko kamun waya Kai ko tunani na kayi a zuciya ban yafe.......... Ya buge Mata Baki.
Ke kin Isa ki yanka mun doka?
Ta rike bakin tare da runtse ido...... Ya kalli Aisha kina Jin halin kawarki ko? Duk garin nan akwai yarinyar dake mun haka?
Ta girgiza Kai da sauri Babu kayi hakuri.....
Idan kin lura ta na nemana da rigima sosai......
Kayi zuciya ka kyaleni daga yau a fita harkar Bilkisu..... It's alright take care, Kawai ya fada mota yaja ya tafi .... Gabanta yayi mummunan faduwa, ta yi shiruuuuu kafin Ta figi hannun Aisha zo muje.
Suna zuwa daki ta fada katifa ta saki kuka.... Ai kinyi kuskure me yasa zakiyi mishi irin wannan wulakancin Bilkisu...... Ta dago fuska jage jage da hawaye.... Aisha na rasa gane inda Anwar ya dosa, masifar nan tashi ta isheni gara ya kyaleni na huta.... Wallahi bazaki huta ba. Ta Kara kallon ta da sauri, yes bazaki taba hutawa ba saboda kina matukar kaunarsa.... Bilkisu nasanki nasan wacece ke, gwargwado nasan waye Anwar shima wallahi tallahi matukar baku fito Kun fadawa junanku surrin da ke zukatanku ba tabbas zaku kashe kanku a banza...... Ni na taba ganin jarababbiyar soyayya irin taku?
Ko wane idan kishin Dan uwansa ya motsa sai ya Kare kansa?...... Ta kife Kai a filo ...ta Kara sakin kuka a hankali.......
Idan kin gama ki tashi kiyi parking, ga maganin nan na dauki kwaki goma .... Ta fice jikinta duk ya mutu tana mamakin irin wannan soyayya wacce ko a littafi Bata taba karanta irin ta ba.
Gaban sadeeq ya Fadi....... Anwar lafiya na ganka a firgice haka ko jikin....... Tashi ka shirya mu tafi Kano.
What?
Ya mishi wani kallo gaban Sadeeq ya Fadi ya tsorata Anwar lafiya?
Zaka je ko na tafi?
Ya kamo Shi ......ya fizge sadeeq Dan Allah ka kyaleni *I hate this world*........ Ya ci gaba da harhada Kaya...... Dole sadeeq ya Mike shima ya Fara hada jaka..... Amma wallahi bazaka tuka mu cikin wannan mood din ba ... Bai rufe Baki ba ya wurga mishi keys din a kirji ya figi jakar sa yayi waje..... sadeeq ya bishi da gudu tare da rufe dakin....Sha biyu da Rabi na dare suka bar dutsinma yana kwance a sit ya Dora kafa daya a dash board ya kwantar da sit yayi filo da hannayen sa idanun sa rufe..... Kadan kadan sadeeq na lura dashi sai faman tsoki yakeyi.
Batayi tunanin abin zai dameta ba sai da ta koma gida, kwana daya , biyu...sati. Anwar bai nemeta ba.
Suleiman kuwa yayi Kiran duniya ta kasa dauka kamar tana son Jin haushin sa ganin shine jigon wannan fitina.
Gaba daya gidan an ga canjinta, bata walwala, kullum tana daki kwance.
Ranar da tayi sati biyu da dawowa mommy ta sameta daki, ta zauna bakin gado, Bilkisu mi ke damunki? Na lura tunda Kika dawo Baki da walwala, meke damunki? Saboda har dadyn ki ya Kai ga yin magana...... Ko maganin da Kika ce Anwar ya siya Miki ne kike ganin yayi yawa?....sai kawai taga kwallah na zubo Mata.... Hankalin momy ya tashi ko dai daukar magana Yar tata taje......subhanallah. tayi saurin kawar da tunanin. Ta janyota fada mun menene?
Ta goge hawayen mommy bana Jin dadin abinda Anwar keyi mun...... Ta Bata labarin duk abinda ya faru..... Sai kawai taga mommy na dariya.
To Bilkisu Anwar ai kishi ne ke damunsa tunda baya son ki kula Suleiman din sai ki kyaleshi....
Ina wayar ki?
Ta Mika Mata kawai..... A'a Anwar din Zaki Kira kice yayi hakuri tunda ke kin damu bai Kira ba..... Tabbb wallahi bazan kirashi ba mommy..... To ya Zama dole ki fitar dashi a Ranki domin Shi da alama ya manta da ke kamar yanda Kika mishi gargadi...... Kirjinta ya buga da karfi kwallah suka Kara cika idonta ...mommy ta mike wannan shine sai ki zabi daya cikin biyu, Amma bazan dauki wannan dararewar ba da kikeyi cikin gidan Nan... Tana Gama fada ta fice tare da Jan kofa gammmm.
Tayi zugummm, dabara ta fado Mata kawai Bari ta Kira Sadeeq......
Anwar kuwa yafi Bilkisu shiga tashin hankali, ya koma kurman karfi da yaji, hankalin Hajiya yayi mummunan tashi tana zargin ASIRI ne ke son kamashi.
Ita kadai ke shiga dakin sa sai kuwa sadeeq, kullum sai ta lallasheshi yake cin abinci....
Abun har ya Fara affecting kasuwar sa, kowa shakkar kiransa yakeyi a waya saboda masifa da bala'i.
Tana zaune ta tsareshi ya shanye tea din ta Sha mur alamar ba wasa kamar kullum, ya Sha mur, ya tsuke fuska rabonsa da dariya tun ranar da ya rabu da Bilkisu Yana cusa kwai a Baki jinsa yakeyi kamar madaci.
....... Sadeeq ne ya turo kofa Assalamu alaikum.
Hajiya yau kina ciki?
Eh sadeeq maraba, Wa'alaikumus Salam.
Kamar zatayi kuka ta kalli sadeeq na rasa ainahin meke damun Anwar, shin ko ta sanar dakai ......ya wurga mishi harara Yana horonsa da ido kamar kullum akan kada yace wani Abu...... Hajiya ina ga malaria ce, kin San fa dutsinma akwai sauro sosai Daman ya Saba duk hutu sai ya kwanta ..... Ba irin wannan kwanciyar ba. Yaro ya takure ya makure sammm Anwar ko murmushi ya daina yi...... Zai dawo normal hajia aci gaba da addu'a.
Ta Mike , kaima ai bakin ku daya, ko ma menene bazan yarda da wasa da abinci ba... Ta fita.
Ya kalleshi ...ya kamata ko don tsohuwar nan ka daina wannan abun, nasan wallahi duk wannan damuwar Bilkisu ce... Ta kirani dazun ta fada mun duk abinda ya faru hada kukanta, ta ce wallahi Babu abinda ke tsakanin ta da Suleiman, Anwar hakuri akeyi..... Please sadeeq ka kyaleni..... Bazan kyaleka ba tunda kaima baka kyale kanka ba .
Ta ce na baka hakuri....bazanyi ba tace na Kyaleta hakurin me zata bani?..... Har wannan maganar ta fada mun ta ce kuskure ne bacin Rai yasa ta Fadi hakan..... Karya takeyi. Tana son bani haushi ne don na Mari Suleiman...... Wannan zafin kishin naka bazai taba sany.... Kishin ubanwa zanyi? Ya Mike ....ya kamoshi da karfi ya mayar.... Dan Allah kayi hakuri Anwar tunda wallahi Koda mukayi ways kuka takeyi..... Kaine zata Kira taba hakuri ba ni ba? Tunda Kaine tayi wa laifi ko?
Ikon Allah.... Tana tsoron kada ku Kara wani fadan ko kaki dauka ....... Ni zaka zo ka tsara sadeeq???
Tsari??? Wallahi da gaske nake ita ce ta kirani....ya fiddo waya aljihu...duba ka gani ni na Kira ko ita? Minti nawa ka gani?
Sai kawai yayi murmushi ko kadan bai San yayi ba.....ya zaro ido are you smiling?????
Ya Kai mishi duka ya goce..... Munafuki ni na dade da sanin wannan cutar taka Bilkisu ce.... Dan Allah fada mun tayi maganar cikin damuwa?
Wallahi kuka takeyi lokacin da muna maganar alamar abun ya dameta...... Mtseww ita ce ke Sanya mu damuwa ai..... Iye? Sadeeq ya fada , ya banka mishi harara Yanzu dai kirata kace ta kirani da kanta ta bani hakuri..... Message ya shiga wayar Anwar din karammm..... Ya dauko da sauri jin alamar shigowar message din ta ne,
```I'm sorry very sorry please and I don't mean to hurt you```..... Sai kawai ya washe fuska.... Sadeeq Bilkisu ce....
Dan Allah Kira mun ita.... Suna Kira wayar a kashe. Abu kamar wasa kusan kwana uku duk lokacin da aka Kira a kashe..... Shi kansa ya nema Amma bai Samu ba.... Hajiya dai taga Anwar lokaci guda an warware har Yana fita tawon *Bike* da suke zuwa da marece Shi da yaran governor.
Ta warware amma duk ta Dan rame kadan..... Kullum tunanin Anwar.
Ta kasa bude wayar ta saboda tana Jin kunyar idan ya Kira me zata fada mishi bayan ita ce ta bayar da hakuri?
Ta Kama lahadi suna gida duka har daddy, tana sanye da Riga da skirt na atamfa super Holland Mai flower yellow dinkin ya bi jikinta, dogon hannu ne na *net* yellow duk atamfar yayyabe flowers din suke da stones masu sheki kamar diamond.
Kanta ba kallabi ta maida gashinta baya ta kulle jelar kwance bisa bayanta..... Motsin get suka jiyo. Daddy ya Mike da sauri ya daga labule....jibga jibgan motoci ne bakake suke shigowa.... Ya ce innalillahi.. waye zai bamu surprise visit Haka?.. aka Fara fitowa yaga securities ko wane da abin magana a kunnensa ya saki labule da sauri, ya kallesu inajin foreign affairs minister ne ..... Yayi ciki da sauri..
Suka tashi duk suka fada daki. Bilkisu ma ta shige nata.
Ya fito Yana gyara hula, falon kamshi kawai ke tashi na freshner ta ko Ina .... Ga A.C ta gauraye ko'ina.... Ring bell ya Fara kadawa a hankali... Da daddy da kansa ya bude..... Ya bude ido sosai cike da mamaki compound din gidan makil da securities suna tsaye ya Sha fararr gizna dinkin falmara ce yasha aiki kansa cikin kube murjin kanawa...... *Waye in ba Anwar ba*....... Anwar??? Daddy ya fada ....sukayi saurin zubewa shida Sadeeq daddy Barka da yammaci...... Ku tashi .... ku tashi.... Ya kamo Anwar.... Ya riko hannun sa suka shigo ya kwadawa mommy Kira ta fito da sauri.... Tayi turus ganin Anwar tare da washe Baki *Anwar a gidan mu*?
Sai sumke Kai yakeyi.... Daddy ya zauna suka gaisa sosai ya kasa hada ido dashi sai sadeeq ne ke faman amsawa .
Tuni mommy tayi ciki tasa Rahina Mai aiki ta fara kawo musu abin Sha....
Daddy ya Mike ya haye sama.
Mommy ta shigo suka Kara gaisawa ta koma ciki.... ya kalli sadeeq Dan ubanka ka tamabaya kace Ina Bilkisu?????...... Ya zaro ido ya Kai mishi duka......
Tana kwance ta kunna t.v din ta tana kallon wani Korea series *Innocent man*
Mommy ta shigo, ke kullum idan anyi Baki sai ance kizo ki gaishesu??? Tayi zumbur Ina da niyya mommy ayi hakuri..... Ta galla Mata harara.... Tabbas kowa yasan surprise visit ya Bata don me zata fada Mata.... Gara ta fita idanunta su gane Mata.
Ta dauki dan mitsilin gyale ta Yana a fuska bai ko rufe rufe rabin gashinta dake kwance a baya ba..... Ta raba momyn ta wuce ..
Assalamu alai........ Ya dago da sauri sukayi tozali.... Sai kawai ta dafe kirji tayi baya da sauri kamar wacce taji tsoro , mommy na tsaye bakin kofar dakinta Bata fita ba.... Ta ruga ta makalkaleta..... Mommy da gaske Anwar ne?.........✍🏼
*Zainab wowo*💖