Rufaida ce zaune adakin ummansu taji wayarta naringin murmushi tayi ganin sunan Besty dinta kafin tadaga wayar
"uwar gidan ghailan ya akayine kira haka da yamm....."
sauran zancen yamakale jin jawaheer tasaki wani kuka daga jin kukan kasan ba lpy ba
"jawaheer kiyi shiru mana gayamin meyake faruwa" rufaidah tafurta cikin damuwa
"rufaida momyce zata rabani da ghailan dina don Allah ki taimaka min wlhy idan ta hanani aurensa sedai na kashe kaina kona barmata gidan" rufaida ta jinjina wannan batun sannan tace cikin sigar rarrashi
" kinga jawaheer wannan maganar bata waya bace kiyi hakuri insha Allah gobe zanzo dama inada niyyar zuwa nakawomiki iv din bikin husna"
tadan sassauta kukan tace
"to rufaida sekin zo ina zuba ido" damurmushi a fuskar rufaida tace "ni kwantar da hankalinki kinji kinga kun kusa fara exam karkizo kiyi failing"
"insha Allahu zan maida hankalina kizomin da awarannan na unguwar Ku" dahaka sukai sallama,
Ghailan ne adakinsa abin duniya ya isheshi tunanin me jawaheer takeyi yayi ayanxu bari dai yakirata yaji dauko wayarshi yafara latsa lambobinta
"hello my prince"muryarta da alamun kuka ta furta hakan
"kuka ko my princess? Banason kukannan indai kinasona kiyi shiru ga exam dinki akusa kinzauna kinata faman kuka maza tashi kiyi salla kifara karatu banason shiririta inba hakaba yannxunan nazane ki"
sautin dariyarta yaji yadda yayi maganar ne yabata daria tatuna lokacin tana jss1 yadda yakemata inzatayi exam shima dariyar yayi yace
"Alhmdllh nasaki dariya naji dadi kinsan inason ki sosae wannan dalilin na momy ba komai bane kinsan yadda nakeson ki insama da kasa zata hade bazan yadda arabamuba I so much luv u my princess"
" I luv u too my prince Allah yabarmu tare"ya amsa da ameen "my prince bani labari mana"
"Babu labari princess aje aci handout kawai kinsan akwai bikin Khadijan Anty Sha'awa kina gama exam zamu tafi silami se munyi sati zamu dawo" tsalle tasaka tamkar wata yarinya
"wow Allah yakaimu my prince"
Turo kofar d'akin taga anyi tana juywawa taga momy,wanketa da mari kawai tayi tamika mata hannu tace
"Dan uwar ki bani wayar hannun ki, wato har kinyi girman dazaki kaini kara ko?"
Jiki na rawa ta mik'a wayar tahau magiya dama jawaheer akwai tsoron duka
"Momy dan Allah kiyi hakuri karki dakeni wlhy baran karaba" dukan akawo wuqa momy tamata sanda takasa koda motsi sannan ta rabu da ita.
Edited by Billy Galadanchi
Fiyyah
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: *ALMAJIRINA*
*©Exquisite online writers*
_written by sofiyyah galadanchi (lazy writer)_
_in dedication to Sha'awa Ibrahim_
19
Washe gari tun 8 yakai jawaheer skul yadawo ya leqa dakin adnan donsuyi hira yasameshi yana bacci dama shi haka yake idan yashige se azata baya gidan ghailan komawa dakinsa yayi ya kwanta yakasa bacci se juyi yake
10:32am yaji ringing din wayarsa 'my princess yagani' murmushi yayi kafin yakashe yakirata back
"My princess har kunfito daga lecture dinne"? "Mun fito Yaya saura 12 to 2 "tafada tana yatsina fuska "to shikenan
My princess a mayadda hankali bakyadai jin yunwa ko"?
"Inajin yunwa mana"
"To kije kici abinci mana"
"Ai yanzu nakoshi dama yunwar muryarka nakeji tunda najita nakoshi"
Seda yayi daria kadan kafin yace "kinyi kokari my princess nikuma jinake gidan ba dadi ainaga wani sati zamu fara zuwa aiki a company momy tace tagaji"
"Kunji dadi kunhuta da wahalar skul"
Muryarta da alamun gajiya
"Angayamiki zuwa aikin ma wasa ne?
Kema idan kinmaida hankalinki sekiga ba wahala Allah dai yabaku Sa'a"
"Ameen my prince"dahaka suka sha hirar su sunata soyayya kamar ba gobe daya ga 12 takusane yaimata sallama kamar karya kashe wayar haka taji dolenta dai ta hakura,
Zaune suke a dinning sunacin lunch se satar kallon juna suke suna sakarwa juna murmushi duk abinda suke a idon momy azuciyarta tace "duk kugama boye boyenku ke auta ki kama kanki Dan ghailan sedai yazama ubanki badai mijinki ba"(wannan abin kunyar dame yayi kama),
Ghailan ne kwance adakinsa yagama making mind dinsa akan suje sufadawa momy halinda suke ciki wayarsa ya janyo yayi kiran princess dinsa itakuma tagama wanke toilet dinta tafito saboda dasafe tamakara tanata sauri yasa bata tsaya wankewa ba karar wayarta taji da saurinta tadaga ganin me kiranta "my princess idan ba wani Abu kikeba kizo muje mufadawa momy abari ya huce shiyake kawo rabon wani"ajiyar zuciya tayi kafin tace 'shikenan my prince kafito mutafi ba abinda nake" batareda dayayi maganaba ya katse layin kusan atare suka fito,
Adakinta suka sameta zaune tana duba wasu takaddu agabanta tana dubawa gaisheta suka karayi ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa ghailan ne yafara magana "momy dama ihmm cewa mukai bari muzo mu sanar miki cewa...sai kuma yayi shiru,
Dagowa tayi ta kalleshi ta furta cikin daure fuska "ehn ci gaba ina jinka" kasa karasa wa yayi ganin yanayin fuskarta,sanda ta kuma cewa "ya akayi ne shalele?" Gyaran zamanshi yayi ya furta
"Momy dama zancen auren dakika mana ne shine nace dama tuni nida jawa munrigada mun shirya kanmu,bamu sanar miki bane mukaga yafi yanzu datake jami'a saimu sanar dake" tafi mintuna goma bata dago ba,sanda taga dama sanna ta ce
"Ghailan karna kumajin magana makamanciyar wannan tafito daga bakin d'aya daga cikinku, ina mai tabbatar muku cewar ba wani abu mai kamada aure a tsakaninka da jawa har abada ko bayan raina ban yadda da wannan maganar ba,kai yayanta ne kuma ubanta bazaka tab'a zamtowa miji agaretaba kaine zaka aurar da ita wa mijin daya dace amma ba kaine zaka auretaba" tana kaiwa nan tayi shiru taci gaba da kallon paper dake hannunta,jawa datafara kuka tunda momy tafara magana ta furta cikin muryar kuka
" Momy Dan Allah ki rufan asiri wlhy yaa ghailan shine farin cikina,idan kika mun haka....mari momy ta kai mata kanta karashe maganar ta furta "Maza ki rufamun baki,wlhy nakuma jin wannan maganar abakin ki saina illataki, maza ki tashi kibani waje" sum sum jawa tabar d'akin tana kuka, mikewa ghailan yayi shima da zummar barin d'akin tace dashi
"Zauna zanyi magana dakai"ba musu ya zauna yana share kwallah
"Shalele zuwa yanzu yakamata ace ka fahimci irin k'aunar danake maka,kaida kanka kasan bayan rasuwar marigayi nasamu manema da dama amma ban auri kowaba, babban dalilina kuwa shine kaunar danake maka, wlhy shalele naso nacireka araina amma nakasa ka taimaka ka aureni tunda ba haramci acikin yin hakan ko annabi ya auri zawara da kuruciyarshi, kafita batun cin jawa ka taimaki momynka" sororo yayi yana kallonta domin kuwa ya dad'e da zargin hakan saidai yakasa gasgata zuciyarshi ne,mamakine sosai ya bayyana a fuskarshi wannan ya sanya ya kasa furta komai,jawa kuwa datake lab'e tana jinsu rikicewa tayi kuka yaso cin karfinta ta to she bakinta tayi hanyar dakinta da gudu....
_Allah ka karemu da sharrin shaidan Allah kasa mufi karfin zuciyoyin mu ameen_
_edited by billy galadanchi_
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: *ALMAJIRINA*
*©Exquisite online writers*
_written by sofiyyah galadanchi_
_in dedication to Sha'awa Ibrahim_
20
Azuciyarsa yake fadan nashiga uku (wannan Kalmar ta matace amma ko maza idan suka shiga rudani sesu tsinci Kansu da furta hakan)na Dade ina hango wannan abin a idanun momy amma sena kawarda hangena saboda tamkar uwace a gurina kuma nasan ba jahila bace,jikinshine ke rawa danyama kasa furta banda kallon momy ba abinda yake mik'ewa yayi yabar d'akin da sauri tana tsayar dashi amma ina ya gagara tsaya wa da gudunshi yaje dakinshi...
Jawa d'akinta ta tafi ta had'a kai da gwiwa tana kuka,jin an turo kofar yasanya ta d'ago kanta ta kurawa momy ido
"Ke dalla dauke idonki akaina kika zubaminsu haka kamar an soya gyada"momy tafada tana Hararar jawa se asannan ta dawo hayyacinta kafin wasu zafafan hawaye suzubo daga idonta da batasan akan wane bakin ciki ne takeyinsu ba,
"Maza tashi ki Dora mana dinner tuwon semo da miyar kubewa zakiyi mana ki ciro zobon nan daga freezer nasan yayi kankara kila yayi melting kafin mutashi cin abinci kiyi sauri kigama kihuta kafin dare yayi kicigaba da karatunki naji kince kunada test gobe ga exam ta kunno kai"ta fada tana ci gaba da kallon jawaheer, jawa kam miqewa kawai tayi dan har jiri take gani batareda tace komai ba tafice kitchen ta nufa Dan Dora abincin azuciyarta tace ko ina en aikin gidan oho,
Adaki kuka ghailan yakeyi jijiyoyin kansa sun fito fuskarsa tayi ja bakinciki da takaici sun cukushe masa zuciya azaune yake kamar hoto momy ce tayi magana yasa yadawo da hankali sa gareta
"shalele kaida adnan zaku fara zuwa company bansanma mekuke jira ba kukace se wani satin banyadda da wannan ba gobe zaku fara zuwa karbi wannan papers din kaduba su tareda Ku zani na gabatar daku ga ma'aikatan gurin"kallonta yake yi kafin yasamu bakin magana
"momy magana ce me muhimmaci mukazo da ita bakima sauraremu ba" hararar shi tayi
"bazan taba saurarar kuba shalele kacire ranka da samun jawa a matsayin mata tuntuni nake maka hannunka mai sanda kaki ka gane tobari na fitoma baro baro kaji ninan nice matarka tunda aure kakeso base an ja lokaci me tsawo ba wani satin ma se a daura " jiyake kamar zuciyarsa ta faso kirjinsa ta fito miqewa kawai yayi yafice aransa yana fadin "lallai momy ta haukace zuwa zanyi nasamu kawu Ahmad na fada masa halin da ake ciki"
Dakin jawaheer ya shiga ya duba be ganta ba,fitowa yayi yanufi hanyar kitchen acan yasameta tana wanke nama sunanta yakira cikin wata dashashiyar murya
"jawaheer" d'agowa tayi tana kallonsa sekuma ta fashe mai da kuka,cikin damuwa yace
"meye Haka my princess?banson kuka kiyi shiru kinsan dai Matar mutum kabarinsa babu Wanda ya isa ya hana kizamo matata se Allah kuma idan yayi hakan jarabawace wadda yakamata ace mun karbeta hannu bibbiyu muba masu raunin imani bane kowane musulmi anaso ya yadda da kaddara mekyau ko sabanin haka saboda haka ki kwantar da hankalinki exam zaki fara banason ganin carry over ko d'aya kibada himma kinji"
kada kanta tayi kawai tana share hawayen fuskarta sekuma tabude baki tace" my prince bakaji abinda momy tace ba wai insa araina bazan tab'a aurarkaba,Allah ni baran iya rayuwa inba kaba"
zazzafan ajiyar zuciya yayi saboda shima dauriya kawai yake shikadai yasan me yake ji aransaka "jawa plss ki kwantar da hankalinki zanje na samu kawu Alhamd nasan zaizo yamata magana"
uhm"Allah yakaimu goben" ameen yace yana shirin fita Sega momy ta shigo "me kake anan sekace mace?zoka fita kafin na saba maka banason rashin kunya" fita kawai yayi batareda yace mata ko kala ba Dan bazai yarda yakara musa mata ba Dan yasan ba lpy.
_ikon Allah na kwance ya fadi_
_Allah kabamu hakuri ameen
_Domin hakuri shine ribar zaman duniya duk abinda hakuri be Baka ba to rashin sa bazetaba baka ba musa hakuri acikin zukatanmu zamuga daidai insha Allah,,_
_Allah kakara bamu hakuri kuma karkasa mugajiya da hakurin damuke Ameen thumma ameen_
_edited by billy galadanchi_
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: *ALMAJIRINA*
*©Exquisite online writer's*
_written by sofiyyah galadanchi_
_in dedication to Sha'awa Ibrahim_
21
Washe gari bayan sallar azahar kawu ya iso gidan dama momy tasan da zuwanshi amma batasan dalilin zuwanba yadai kirata awaya yafada mata yananan zuwa hakan yasa tashiryawa zuwansa dan tasa anyimasa girki wanda tasan yanaso da kunun aya yasha sanyi😋
Yasamu tarba mekyau momy se washe baki take kawunta yazo suka gaisa cikin mutunci kunun aya kawai yasha yace abincin dashi zaitafi dan yanzu bayajin yunwa,
Gyaran murya yayi hakan yasa momy tamaida hankalinta gareshi "wani zance naji daga wurin ghailan"gabanta ne yayi mummunan faduwa hartaso ta daburce sekuma tayi kokarin saita kanta kawu yacigaba da magana "yacemin zaku hada marwan da jawaheer aure bayan kuma kinsan ghailan da ita jawaheer suna son juna koba haka ba?" Murmushin yake tayi kafintace "hakane kawu zamu hada marwan da jawaheer aure amma bansan zancen ghailan da ita jawaheer ba dama muna so mukara dankon zumunci ne"kallonta yayi sosae "shi marwan din ko ita jawaheer dayansu yace muku yanason daya"idonta akasa tace "a a kawu kawai munyi la'akari da shirin dasuke ne" "toshikenan bari nakira ita Shafa din "janyo waya yayi yakira Shafa yacemata duk abinda take ta ajiyeshi tazo ita da marwan"tayi mamakin wannan kiran na gaggawa amma ahaka tafadawa marwan da dama yanagidan suka fita,
A palo suka samesu suma suka zauna bayan angaisa ne kawu yace akira mai jawaheer
Marwan yakala yakira sunansa "kanada labarin iyayenku zasu hadaku aure da jawaheer" Kansa akasa yace eh kawu kwanaki momy ta fadamin "kayi na'am da batunsu kokuma bakada ra'ayi da hakan ?" Kallon kawu yayi cikeda damuwa yace "kawu nibanason jawaheer da aure sedai so na en uwantaka amatsayinta na kanwata batada banbanci da muneera awurina kuma naso nanuna ma umma hakan taki saurarata kuma ni inada wacce nakeso iyayenta ma sunmatsamin akan naturo magabata na" maida kallonsa yayi gun jawaheer
"Ke fa jawaheer kinason marwan ?"kanta akasa tafara magana "kawu kusan ra'ayinmu daya nima inada wanda nakeso"
Kawu yacigaba da magana "to Ku kunji tunda basaso banga dalilin takurasu ba" anty Shafa tace "gsky nima nabi bayansu tunda sunce basuda ra'ayin auren juna kuma sunada wayanda suke so mubarsu su auri wayanda sukeso kar aje garin Neman gira arasa ido"
Kawu yace ke jawaheer wakikeso "yaa ghailan"cikeda kunya ta amsa kanta akasa "masha Allah inji kawu harkama ta gidace"
"To wallahi bari kiji jawaheer babu zancen aure tsakaninki da ghailan koda baki auri marwan ba to kicire ranki da auren ghailan"momy ce ke wannan rattaben fuskarta hartasoma yin red tsabar masifa datake cinta kawu yace "meye dalilinki?"
"Nidai kawai bana ra'ayin hakanne idan tanada hankali ai ghailan kamar adnan yake awurinta" jinjinakai kawu yayi "hakan ba haramun bane koda sun auri juna ina hankalinki yatafi? Er baba kisake tunani karkijefa yarannan cikin mawuyacin hali"
"Kawu ba wani hali da zasu shiga kawai shashancine yamusu yawa " adnan fake zaune yayi shiru ne yafara magana "nima momy nabi bayanki Yaya ghailan kuma ai tamkar uwa daya uba daya muka daukeshi Kaine baban yayanmu dakai za aje nemarmin aure kuma kaizaka bada auren jawaheer kayi hkri yaya da auren jawaheer "ghailan shiru yayi yana kallon adnan azuciyarsa yace bakasan manufar momyba dakake wannan halakon amma bazan fadamaba with time zaka ji kuma kagani" kuka kawai jawaheer ta saka dagudu ta wuce dakinta tana kuka me tsuma zuciya
Babu yadda anty Shafa da kawu basuyiba amma momy ta kafe hakan ya tunzura kawo yace tunda basu isa da itaba duk abinda taga dama tayi amma kar wani Abu yabiyo bayan tanemesu ta kuka da kanta yayi ficewarsa anty Shafa kam cewa tayi tabata lokaci tayi tunani dan taga ranta yabaci sosae ,
Jawaheer ko tana daki kuka kawai take batasan da wannan halin na momynta ba tana matukar bakincikin kasancewar hakan wayarta tajanyo tayi kiran rufaida...
_kushirya muje yaki dan gsky bazamu yaddaba nidai ina bayan anty Sha'awa saboda ni matsoraciya ce_😂😂
_edited by billy galadanchi_
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: *ALMAJIRINA*
*© Exquisite online writers*
_written by sofiyyah galadanchi (lazy writer)_
_in dedication to Sha'awa Ibrahim_
22/23
Rufaida ce zaune adakin ummansu taji wayarta naringin murmushi tayi ganin sunan Besty dinta kafin tadaga wayar
"uwar gidan ghailan ya akayine kira haka da yamm....."
sauran zancen yamakale jin jawaheer tasaki wani kuka daga jin kukan kasan ba lpy ba
"jawaheer kiyi shiru mana gayamin meyake faruwa" rufaidah tafurta cikin damuwa
"rufaida momyce zata rabani da ghailan dina don Allah ki taimaka min wlhy idan ta hanani aurensa sedai na kashe kaina kona barmata gidan" rufaida ta jinjina wannan batun sannan tace cikin sigar rarrashi
" kinga jawaheer wannan maganar bata waya bace kiyi hakuri insha Allah gobe zanzo dama inada niyyar zuwa nakawomiki iv din bikin husna"
tadan sassauta kukan tace
"to rufaida sekin zo ina zuba ido" damurmushi a fuskar rufaida tace "ni kwantar da hankalinki kinji kinga kun kusa fara exam karkizo kiyi failing"
"insha Allahu zan maida hankalina kizomin da awarannan na unguwar Ku" dahaka sukai sallama,
Ghailan ne adakinsa abin duniya ya isheshi tunanin me jawaheer takeyi yayi ayanxu bari dai yakirata yaji dauko wayarshi yafara latsa lambobinta
"hello my prince"muryarta da alamun kuka ta furta hakan
"kuka ko my princess? Banason kukannan indai kinasona kiyi shiru ga exam dinki akusa kinzauna kinata faman kuka maza tashi kiyi salla kifara karatu banason shiririta inba hakaba yannxunan nazane ki"
sautin dariyarta yaji yadda yayi maganar ne yabata daria tatuna lokacin tana jss1 yadda yakemata inzatayi exam shima dariyar yayi yace
"Alhmdllh nasaki dariya naji dadi kinsan inason ki sosae wannan dalilin na momy ba komai bane kinsan yadda nakeson ki insama da kasa zata hade bazan yadda arabamuba I so much luv u my princess"
" I luv u too my prince Allah yabarmu tare"ya amsa da ameen "my prince bani labari mana"
"Babu labari princess aje aci handout kawai kinsan akwai bikin Khadijan Anty Sha'awa kina gama exam zamu tafi silami se munyi sati zamu dawo" tsalle tasaka tamkar wata yarinya
"wow Allah yakaimu my prince"
Turo kofar d'akin taga anyi tana juywawa taga momy,wanketa da mari kawai tayi tamika mata hannu tace
"Dan uwar ki bani wayar hannun ki, wato har kinyi girman dazaki kaini kara ko?"
Jiki na rawa ta mik'a wayar tahau magiya dama jawaheer akwai tsoron duka
"Momy dan Allah kiyi hakuri karki dakeni wlhy baran karaba" dukan akawo wuqa momy tamata sanda takasa koda motsi sannan ta rabu da ita.
Edited by Billy Galadanchi
Fiyyah
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: *ALMAJIRINA*
*©Exquisite online writers*
_written by sofiyyah galadanchi_
_in dedication to Sha'awa Ibrahim_
24/25
"Aiba dukanki zanyiba amma bazaki koma riqe waya ba tunda nizaki nunawa soyayya ghailan yayanki ne ba mijiba"
Tana gama fadar haka tafice daga dakin itakuma jawaheer tasaki kuka me tsuma zuciya "nashiga uku ni jawaheer",
Momy ko tana fita tafigi key din mota tafita se gidan anty Shafa ghailan kuwa yana jikin window yaga fitar momy hakan yasa cikin sauri yafito yanufi dakin jawaheer dashiharsa yasameta tayi zaman dirshan akasan tile tana rizgar kuka dago kanta tayi tana kallonsa da idanunta da sukayi ja kafin tafara magana "my prince momy ta karbe min waya bansan meyasa batason ka aureniba"
"Haba my princess seki zauna kinata kuka haka aisekija kanki yayi ciwo kalli yadda idonki yayi ja Dan Allah ki kwantar da hankalinki idan kina haka aiseki saka nima na gigice ki daina kukannan haka ya isa" cikeda tausayinta yake magana yana tunanin yadda yakeji azuciyarshi itadake mace me rauni ce yatake ji? "My prince kukanne na kasa tsaidashi bansan lokacin danakeyinsa ba"
Murmushi yayi "haba my luv nidai kidaina kukannan I love u so much" murmushin itama tayi "I love u more my prince" dahaka dai har yashawo kanta ta Dan sake "my princess bari naje na kwanta nagaji kafin momy tadawo tasameni anan"
"A huta lpy" murmushin nan dai yasakeyi sannan yafita daga dakin,
A Palo ya hadu da adnan amma abin mamaki adnan ko kallon Yayan nasa beyiba ya shige dakinsa,haka kullum yake fama da adnan idan sun hadu baya ko kallonsa haka indai yanazaune daga ghailan yazo ze tashi yabar wurin koda shi ghailan yayi kokarin yimai magana baya samun fuska daga gareshi idan adnan yayiwa ghailan magana to akan aiki ne hakan kadai kesa yaimasa magana shima don ta kama dolene ,ghailan kuwa aransa ya quduri yiwa adnan uzuri saboda besan kan lamarin ba dayasani bazai taba goyon bayan momy ba,
Yana zaune adakinsa yaji wayarsa na ringing sunan momy yagani seda yaji kamar karya daga sekuma ya daure yadaga "shalele magana zamuyi Dan Allah kasaurareni" uhm kawai yace "ghailan inaso kacire jawaheer aranka don wallahi bazan iya rabuwa dakaiba inasonka sosai jawaheer yatace akwai soyayya tsakanin uwa da danta wannan soyayyar tadabance don Allah karka ja wannan abin ya haddasa tsana atsakanina da yata" nannauyar ajiyar zuciya yasauke "momy inaso kigane soyayyar jawaheer acikin jinina take kuma wallahi bazan taba iya aurenkiba koda ban auri jawa ba" yana gama fadar haka ya kashe wayar,momy kuwa tsayawa tayi tana nazarin kalamanshi ,
Cikindare yakasa bacci kanshi yadau zafi daga baya kuma seya yanke shawarar barin gidan gabadaya,
Washe gari tunda safe ya sulale yabar gidan batareda yafadawa kowa ba Dan ko jawaheer batasan yatafi ba.
Kowa ya hallara dinning za ayi breakfast amma banda ghalan "bari na dubo shalele yau ko gaisheni bezo yayiba yanxuma be fito cin abinciba" tafice daga wurin itadai jawa sebinta take da ido shikam adnan ko lokacin ghailan bashida se cin abincin sama dayafara,
"Adnan dubomin ko motar ghailatananan naduba dakinsa bayanan" fita yayi bejimaba yadawo "momy bataman inaga yafita ne" damamaki take kallonsa "fita kuma tunda sassafe kuma befadamin ba? Bari nakirashi naji" tayimai miss call yafi akirga amma bedaga ba "to ina yaronnan yatafi?" Sanin bazata samu amsa bane yasata tayi shiru tana tunani , bangaren jawaheer kuwa tunda taji ance motarsa batanan gabanta yafadi koya tafi silami ne? Kai a a aida Kobe fadawa kowa ba ze fadamin kila dai fita yayi wani wurin,
Wasa wasa har la'asar babu ghailan babu dalilin sa hankalin momy yatashi don betaba yin irin haka ba azuciyarta tace "nidai yau be kwana gidannan ba nasan fushi yayi yai tafiyarsa to ina zashi? Silami?amma idan Allah yakaimu gobe zanje silami Allah yasa yanacan ameen"
Jawaheer kuwa tayi kuka har bata koshiba shikenan momy ta tunzurashi yagudu yabarmana gidan tasake rushewa da kuka ranar kwana tayi kuka,
💗feeyah💗
[3/25, 12:40 PM] shaawaibraheem💝: *ALMAJIRINA*
*©Exquisite online writers*
_written by sofiyyah galadanchi (lazy writer)_
_in dedication to Sha'awa Ibrahim_
26/27
Momy ce zaune adakinta tanashirin zuwa silami sega kira daga adnan tazo za ayi baki a company kuma ghailan bayanan taji haushin abin amma Yakama dole taje danhaka tadaga zuwa silami se gobe,
"Momy zan biki silami gobe Dan Allah" inji jawaheer dasuke zaune itada momy a palo " bakida hankaline jibi zaki fara exam babu inda zani dake " shiru kawai jawaheer tayi Dan tasan inzata haihu babu ciki momy bazataje da itaba,
*silami*
Bayan An gaggaisa inna tanata murnan ganin momy "Hajiya bari na kawo miki er gidanki fura na kirawomiki dannaki naga ma kamar bashida lpy tunjiya yaki sakewa se aukin zama adaki" da murmushi a fuskar momy tace "ai da kinbarshi ma naje nasameshi dakaina nasameshi"
"A a Hajiya ayi haka?"
Suna cikin haka sega malam yashigo da sallama suka amsa inna taje takarbo kayan dake hannunsa tanamai sannu da zuwa,
Ghailan ne yafito daga daki daniyyar barin gidan yadan zaga gari ganin momy yasa yadan basar Dan kar su malam su fahimshi wani Abu yakarasa suka gaisa kamar ba komai "shalele tare zamu koma kyau Dan jiyama anata nemanka a company" da mamaki yake kallonta yadda ta ke magana kamar tasan yananan ba nemansa tazoyiba kenan inda bata sameshi anan ba da wani abin zatace yakawota sekuma yayi saurin kawarda zancen yace "to momy dama gobe zan koma amma tunda kinzo zamu koma tare" Dan murmushi tayi tafara magana tana kallon malam "malam abinda yakawoni dama shine zancen aure Khadija ne ghailan yafadamin wai andaga shi saboda matsalar kayan daku"?
"To Hajiya yazamuyi akwai wasu en abubuwa damuke jira ne kuma basu kammalu ba shiyasa muka ga yakamata adaga har komai ya daidaita"
"Haba malam meyasa baku fadamin ba banajin dadin yadda kukemin shikenan komai se Ku ringayin abinku kukadai bazaku sakoni aciki ba nifa bana daga cikin mutanen da abin duniya ke rudasu suna wulakanta en uwansu wlhy sam banji dadi ba" magana take fuskarta cike da bacin rai "munaganin zamu kara dora miki wani nauyin ne shiyasa mukaga wannan matsalar zamu shawo kanta"
"Babu wani doramin nauyi da zakuyi ghailan ai danane kawai dai bancancanci afadamin bane"
"Wlhy ba haka bane Hajiya amma tunda kindauka haka kiyi hakuri don Allah"inji malam inna ma dake zaune tasako bakinta "kiyi hakuri insha Allah hakan bazata sake faruwaba kuma mungode Allah yasaka miki da gidan Aljanna" ameen,
"To malam a aika gidansu mijin afadamusu babu wani daga bikin daza ayi zuwa wani satin insha Allah komai ze daidaita kaikuma ghailan tareda driver nake zamu wuce seka bimu abaya kuma kabawa malam lambata duk abinda ake ciki akirani afadamin da yardar Allah zan taimaka indai baifi karfina ba" tana gama fadar haka ta miqe tanayi musu sallama "maman ghailan bakima sha furar ba" inji inna "inna bani na tafi da ita ko faraufarau nayi" ghailan kuwa wucewa yayi dakinsa yadauko akwatinsa yasaka amota kasan atare suka tafi motarshi na bayan tasu momy,
Jawaheer murna fal ranta ganin momy tadawo tareda ghailan jitake kamar taje ta rungumeshi amma tasan hakan bame yiyuwa bane bazama ta nuna murnarta afiliba dankar momy tagani tahanasu sakewa Dan tanaso tafadamishi yadda tai missing dinsa kwana biyunnan,
Haka rayuwa tacigaba babu wayar dazeyi magana da jawaheer kuma agaban mutane yana nuna bakomai tsakaninsu,
Ahaka jawaheer tafara exam cikeda rashin walwala da takura wata rana idan taje exam din dakyar take amsa tambaya daya shima wata rana batada tabbacin abinda ta rubuta daidai ne danko karatu take ba abinda take ganewa sedai kawai taringa kallon littafi tana tunani kullum kwana take kuka idan taga kukan baze fiddataba seta fara sallar dare tanakaiwa Allah kukanta yauma kamar kullum suna cikin exam hall jitake kamar kanta ze rabe gida biyu ga cikinta naciwo saboda yunwa bata iya cin abinci dakyar ta amsa 2Q suma Dan tayi karatune dazasu yi test haka tamiqe tai submitting wuce gida har wanii jiri jiri ke dibarta.
_edited by billy galadanchi_