Yau kam basu fara karatun da wuri ba, hakan yasa har suka wuce goma na dare basu tashi ba. Amman shigowar Asim yasa ta yi addu'ah ta sallami ɗaliban nata da mafi yawansu matan aure ne.
Har gobe ba zata daina girmama Asim ba, tana bashi haƙƙinsa a matsayinsa na mijinta, dan ta karanta ta gani, ta san irin girman da miji yake da shi ga matarsa, ita dai kam ta kan yi ƙoƙarin ganin ta bashi dukanin haƙƙinsa dan tasan ko mutuwa tayi sai dai idan shine ya cuce acan Allah ya yi musu hisabi.
Ƙarfe shida suke tashi daga gurin da yake aikin, amman baya dawowa gida sai goma ta gota na dare, zaman majalisa yake irin zaman nan da baya amfanar da komai sai zunubi da hassada, zaman zagin wane da wace, zaman matar wane tafi matar wane, wacce aure ya mutu wacce biyar maza take. Kusan ma shine yaro a cikin masu zaman majalisar dan duk sun girme shi dukansu magidanta ne.
Kicin-kicin ya shigo gidan baya ƙaunar kallon Namra, idan akwai wata maƙiyiyarsa yanzu a duniya to Namra ce. Ita kam idan sabo ta saba dan yanzu ba kasafai take ganin rahamar fuskarsa ba.
Tufafin jikinsa ya kwaɓe ya jefar saman katifar ya ɗauki wata guntuwar jalabiya ya saka yazo ya zauna tsakar ɗakin yana kallon kyanɗir ɗin dake hasken ɗakin
“Ina abinci na?”
Ko rufe baki be yi ba ta dire masa abincin gabansa da ruwan sha, sannan ta ɗauko mafeci tana masa fita, sai murmushi take tana masa fira dan kawar mata da ɓacin ran dake tare da shi. Har ya gama cin tuwon ya sha ruwa be kula taba balle ya tanka ta a firar da take.
Tsabar ƙazanta da rainin wayo cikin kwanon daya gama cin abinci ya wanke mata hannu. Ita kuma ta ɗauka ta kai waje ta aje. Sai gata ta dawo ɗakin da gudu jin wayarta na ringing.
Da murna ta ɗauka ganin number Anty daman haka take kullum kamar ba jiya tayi magana da ita ba, zaka rantse kace ta shekara ba ta yi magana da ita ba.
Bayan sun gaisa Anty take faɗa mata za a kawo lefen Maryam cikin weekend ɗin nan mai ƙarewa, ta kuma nuna mata tana son ta shigo ko dan kwana biyu da suka yi ba su ganta ba, kwanki babu yadda Anty ba tayi akan ta zo amman Namra ta nuna mata karta zo yanzu ta bari har gaba.
Da fargaba ta aje wayar dan tasan ba lallai bane Asim ya bar ta taje, amman a haka ta sake fuska tana faɗa masa Anty ce ta kira.
“Okay”
Kawai ya faɗa irin ina ruwan ɗin nan. Ya hau saman katifa ya kwanta yana mata wani kallo da ita kaɗai ta san kiran da yake mata.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *50*
AMIRA POV.
Har suka isa katsina babu abinda take tunani sai Abdool saƙe-saƙe kawai take a zuciyarta na yadda zata sace zuciyarsa da kuma iyalansa.
Babu abinda take annawa a zuciyarta sai sabuwar rayuwar da za ta shimfiɗa na kanta.
Duk irin yadda take misalta arzikin gidan su Abdool sai ya ci gaban tunaninta, ya sha banban da abinda take tsamani. Haka ta zaka kamar ba wacce ta fito daga garin Abuja ba. Idonta ya biɗe sosai lokacin da motar da take ciki ta kunna kai cikin gida.
Ga matakan tsaron daya shimfiɗa ma gidan kamar masaukin shigaban ƙasa. Part biyu ta gani a gidan sai dai part ɗin da suka sauka ya fi girma da tsaruwa, hakan ya tabbatar mata da wacan ɗin part ɗin Abbansa ne ko kuma nasa.
Tana fitowa motar idonta ya sauka kan wani ƙaton Garden dake gefen part ɗin, babu abinda kake ji sai sautin kukan tsuntsaye, ga wani swimming pool da tafi ɗaukar hankalin a hangen nata, daga ruwan swimming pool ɗin har itacen da suke gurin komai kore ne. Peacocks sai kai da kawo suke a bakin Garden ɗin.
“Let's go Madam”
Ɗaya daga cikin sojan da suke tarar a gurin ya faɗa yana nuna mata ƙatuwar ƙofar shiga falon, wacce ta kasance abun kallo, idan ba wanda ya sani ba sai kan rantse kace da zinari aka ƙerata.
A hankali ta cira ƙafarta ta fara takawa, zuwa gurin ƙofar dake kashe mata ido saboda kyawonta. Hannu ta kai zata buɗe ƙofar lokacin data ƙarasa sai kawai ta ga sojan ya danna wasu numbers, sannan ya matsa gaban wata ƴar ƙaramar severity camera yayi magana. Bayan kamar minti biyu sai ƙofar ta buɗe da kanta.
Ƙofar kawai ya nuna mata ya juya ya wuce.
Tun kamin ta saka ƙafarta falon wani irin ƙamshi da sanye suka fara mata lale marhabun. Taku ɗaya ta yi a ɗan ƙaramin downstairs dake ƙarasar da mutun cikin falon, zuwa na biyu na uku ta tashi zamewa saboda sulɓi da kuma tsantsin da tiles ɗin yake da shi.
Haleema ta yi gaggawar riƙeta
“Be careful”
Amira na kallonta ta san ƙanwar Abdool ce dan ga kamanin Abdool nan shimfiɗe a fuskarta. Ita ta taimaka mata ta sauko saman stairs ɗin, tana riƙe da hannunta har suka ƙarasa tsakiyar falon gurin da sauran ƴan'uwanta suke zaune.
“Welcome Sister”
Fauza ta faɗa tana faɗaɗa murmushinta ga Amira, Meesha kan aikin dannar waya kawai take ko inda Amira take zaune bata kalla ba. Amal ce ta karkace fuska tana mata kallon ƙyama ɗin nan, daman ita ta fi uban kowa wulaƙanci a gidan, cikin ma tana tsoron Ummi da Abdool dan sam basa son wulaƙanta ɗan'adam.
Haleema da kanta ta zaunar Amira a ɗayar kujerun da suke gurin, dan falon ya kasance mai part biyu ko kuma a'ce uku, idan a ka haɗa da dinning area.
Bayan ta zauna Meesha ta ɗaga kai ta kalleta tare da miƙa mata hannunta.
“Hey Sis Welcome, my name is Aisha aka Meesha, ke ce Amira ko?”
Amira ta ɗan ɗaga kai tana murmushin mai nuna tsantsan ladabi da kunya, da kuma sanin kai, kana ta miƙa mata nata hannun ita ma.
“Eh ni ce nice to meet you Meesha”
“Nice to meet you too”
Ta ɗan sakar mata murmushi kaɗan, sannan ta tashi ta nufi ɗakinta, till idonta na kan waya.
Tsire baki Amal tayi ta tashi ta nufi ɗakin Ummi.
“Shukura....”
Fauza ta ƙwala mata kira tana kallon tv kamar ba ita ce tayi kiran ba. Da gudu wata baƙar mace ta fito da gudu daga wani ɓangare na falon ta zo haban Fauza ta tsaya.
“Hasiya ga ni”
“Ba ki ga mun yi baƙuwa ba? A kawo mata abin sha mana”
Wacce aka kira da Shukura ta kalli Amira tana washe baki.
“A'a baiko na mu ne ta zo, sennu sennu, sennu da zuwa, bari ya kawo miki abinse yanzu, ahh sennu baiko”
Ta juya da sauri ta nufi kitchen. Yanayin shigarta da kuma maganar ya tabbar ma da Amira bayarabiya ce. Ƙasa ƙasa Amira take kallon tsarin falon tun daga kujerun har labulayen da flowers da aka ƙawata falon da su komai maroon color ne har center carpet ɗin.
Ga wasu golden gulob da aka ƙawata falon da su, wanda Amira bata taɓa ganin irinsu ba iya tsawon rayuwarta.
Fitowar Ummi ne yasa Amira ta karkata tana kallon yadda Ummi ta doso gun da take tana murmushi. Babu shaka wannan Mahaifiyar Abdool ce dan ga kamaninsa nan sak a fuskarta, dakakkar shaddar dake jikinta ta haske ta sosai, kamar wata sarauniya, hauru makka guda biyu dake a bakinta sun haska fuskarta sosai.
Zubewa Amira ta yi ƙasa tana gaishe ta. Ummi ta dafata tana mai jindaɗin yadda Amira ta bata girma.
“Tashi tashi ƴata”
Wannan furucin da tayi ya faranta ran Amira sosai, cikin kuzari ta tashi amman bata zauna a kujerar ba sai ta zauna ƙasa ta nutsar da kai.
Ummi ta ture Amal da ke riƙe da hannunta tana zuba mata shagwaɓa ta shafa kan Amira.
“Sannu ƴa ta ya hanya?”
“Alhamdulillah”
Ummi ta kalli Haleema tana ɗan zare ido.
“Miyasa ba a kawo mata komai ba?”
Haleema ta juyar da babban yatsanta tana nunawa Ummi kitchen. Sai fmga Shukura ta fito ɗauke da ture da kayan ciye-ciye niƙe-niƙi a saman turen. Har zata dire turen gaban Amira sai Ummi ta girgiza mata kai.
“No kai mata ɗakin Amal”
“Tau Mama Ummie”
Shukura ta faɗa ta nufi ɗakin Amal ɗin.
“Tashi ki bita ki shiga ciki ki yi wanka sai ki ci abincin”
“To”
Amira ta unƙura ta tashi ta bi bayan Shukura tana ƙarema ɗayan ɓangaren na falon kallo.
Sai da ta shige ɗakin sannan Amal ta fashe da kuka kamar wata ƴar shekara uku ta narke a jikin Ummi har da kuka.
»“Ummi za ki ce ta je ɗakina ni warinta na ƙe ji”
“That's why na ce ta je ɗakin ki, ba kece mai jin warin mutane ba? Wannan wane irin iskanci ne zaki ce kina jin warin mutane, dan iskanci”
“Wallahi Ummi mutane wari suke”
“Tau yayi kyau, kullum ina rabaki da wannan halin kina ƙarawa ko? Wannan dai baƙuwar Yarima ce idan kika wulaƙanta ta Dude ɗin ki kuka wulaƙanta”
Ta ƙara ɓare baki tana kuka, sai duk ƴan'uwan suka sa mata dariya, especially Haleema data fi kowa raina ta. Ummi kan tashi ta yi ta bar mata falon ta nufi kitchen.
RASHIDA POV.
Duk yadda take misalta yadda zata rayu ba tare da Hilal ba sai ta farka daga mafarkin da take, bata san son da take ma Hilal yayi yawa a zuciyarta ba sai yanzu, ta take ƙoƙorin lallasar zuciyarta ta haƙuri da rashinsa.
Saka wayarta da ya yi a blacklist ya dame ta sosai, tun da ko text ɗinta ba ya iya karantawa a yanzu. Gashi yayi blocking ɗinta a facebook da whatsapp duk inda take iya ganinsa ta samu sanyin zuciya bata ganinsa a yanzu.
Yau weekend ne ba ta zuwa aiki, amman kwata-kwata ta kwacewa abinci da kuma zaman falon da take ɗan yi dan ragewa kanta damuwa.
Bata fito ba sai da ta ji motsin ƴaƴan ƴar'uwarta Ummul Faisak, da suka zo weekend, sannan ta fito dan bata son kowa ya gane damuwarta.
Tayi ƙoƙarin yin far'ah dan da ɓoye damuwarta, amman hakan be hana Momy yi mata magana ba.
“Yau yanzu aka fito”
Ta zauna kusa da ƙanwarta tana sotsar kanta.
“Bana jindaɗi ne”
“Ai kullum ba za ki taɓa jindaɗi ba matuƙar baki cire Hilal a zuciyarki ba, ai mutumen be mana hallaci ba kuma ya ci amana”
Ta yi ƙasa da kanta hawaye na mata zuba, sai ta shiga murza yatsun hannunta. Ummu ta dafa ta
“Ki kwantar da hankalin ki duk abinda take taƙamar ta miki wallahi sai ya karye, kowa ya san wannan ba halin Hilal ba ne, mutumen da ke son ki kamar ya mutu sai kuma.ace yau shine ya sake ki hmmm sherin mata yawa ne da shi”
Momy ta girgiza kai ta tashi ta nufi gurin da yaran suke wasa tana faɗin
“Addu'ah itace kawai mafita, idan ma wani abun ta yi miki sai kiga ya karye”
Sai da ta shige ɗakin tana gargaɗin yaran kar su mata ɓanna sannan Ummu ta Kalli Rashida tace
“Ke ma.fa sai kin tashi tsaye, ai tun farko kece kika yi sakkiyi har haka ta faru gashi nan kina nadama, ƴan matan nan na zamani, ai dole sai ka tashi musu tsaye balle ance yarinyar nan ta daɗe fa ba tayi aure ba, kin ga ko ai dole ta nemi ƙorar ki dan ta mallake miki miji”
“Ina ta ƙoƙarin yaƙar zuciyata ne wajen ganin ma fitar da son Hilal a rai na, ina tsoron kar son da na ke masa ya kai ni ga hallaka”
“Au shikenan kin yarda ki bar mijin ki? Uban ƴaƴanki? Saboda wata can ta mallake miki shi? Ashe ƙaryar so kike tun da ba ki iya yaƙi nemawa kan ki ƴan ci, ai yanzu ko wani auren kika yi baki san inda zaki faɗa ba ƙila ma ta fi wannan bala'i ƙara ma wannan ki ƙyaƙeta wallahi tun wuri”
Tayi shiru tana share hawayen ta, tare da nazarin kalaman Ummu Faisak babu shakka tana son mijinta kuma wannan juya bayan da Hilal yayi mata a take ya tabbatar mata da lallai ba a banza ba ne ya yi mata haka. Kuma idan bata zauna da Hilal ba waye zai aure ta? Tasan ta gama aure duniya dan yanzu da wahala ta samu wanda xai aure inda har wayayyen mutum ne sai ya nemi su yi gwaji idan ko har ya gano tana ɗauke da cutar ba zai aure ta ba. Kuma a halin yanzu babu wanda ya kamata ya zauna da ita sai shi tun da shine ya mori jikinta sai yanzu dan wannan matsalar ta same ta sai kuma ya guje wannan ma ai butulci ne, ko da yake baya cikin hayyacinsa.
“Ke....”
Ummu ta girgizata ganin tana ta mata magana tun ɗazu amman bata jinta.
“Ke kwantar da hankalin ki, akwai wani buzu da yake unguwar mu, kuma ance yana aiki sosai, zan masa magana yayi mana aiki akai a kare abunda ta yi masa ”
Rashida ta yi saurin dafata.
“A'a ki barsa kawai ina nan ina faɗawa Allah buƙata na kuma na san zai karɓa min, very soon za ki ga asirin ya karye”
“Toh Allah ya amsa, amman duk da haka ta kin shiga malamai kinjinta bakin su, kin san fa asiri ko Annabi ya kama balle wani Hilal”
“Haka ne, zan gwada amman ba yanzu ba, sai hankalina ya kwanta sosai”
“To amman ni bana son ki cika idda ba tare daya mai da ke gidansa ba”
“Karki da mu komai za yi dai-dai inshallah, bari na leƙa gidan su ƙawata Asmee”
“Ai ƙara kan kina fita ko damuwa zata rage miki. Bari na shiga na gaida Dady”
“Ai baya nan ya tafi ɗaurin aure”
“Okay”
Rashida na shiga ɗakinta ta ɗauki jakarta ta saka hijabinta ta ɗauki makullin mota ta fito a gaggauwacw tayi ma Momy sallama fitar ta fice daga gidan kamar zata tashi sama...
Ba gidan Asmee zata ce je ba, daman ta faɗa ne dan ta yi hujja da gidan kawai.
Garin da Malamin ya ke ta nufa, bata ko tsoron tuƙi ita kaɗai gata mace yadda take gudu kai ka ce wani ne ya biyota. Sai kuwa gashi ta isa garin cikin ƙanƙanen lokaci.
Yau bata tararda layi kamar ko yaushe ba. Bayan mutane dake gabanta sun gama abinda zasu yi sun fito sai ta shiga da kuzarinta.
Haka ta zauna gabanta tana zayyana masa irin son da take ma mijinta da kuma neman komawa gidansa ta ko wane hali.
Kuɗi mai tsoka ta ciro a jakarta ta miƙa masa da sunan somin taɓi, sannan tayi masa alƙawarin idam har aiki yayi zata kai shi makka ta siya masa mota kuma ta bashi gidan ta dake a cikin garin Zaria.
A take ya fara tsiface-tsifancesa sannan ya ɗauko wani kanko mai ruwa, ya aje gabansa ya karanta wasu dala'ilai sannan ya kira kwari da baka suka zo da kansu gabansa suka tsaya. Rashida taji tsoro sosai amman a haka ta dake ta tsaya a inda take tana ƙara girmama iya aikinsa.
Kwari da bakan ya haɗa ya saita ruwan yana karanta wasu abubuwan da shi kaɗai yasan yaren da yake sannan ya ɗora da
“Ajib ya dala'ilu, ajib ya sargirfir... Kalsoom Kalsoom Kalsoom...”
Haka ya kira sunanta har sau uku, sai ga hoton Kalsoom ya bayyana tana zaune a falo tare da Rafiq sai wasa take masa. Sai Malamin ya harba kwarin cikin ruwan. Sai ta yi tsaye tsakiyar ruwan, a take ruwan ya soma sauya kala zuwa launin ja kamin daga bisani ya zama jini gaba ɗaya.
Sannan ya kalleta
“An jima zamu yanka baƙar kaza, da kuma kaza mai wake-wake, ke kuma ki dafa tuwon dawa ki yi sadaka, idan ba zaki iyaba sai ki siye”
“Na gode Malam shikenan yanzu?”
“Eh yanzu kam shikenan ki koma gida kawai ki saurari sakamako”
Ta ji babu daɗi duk da tasan bata da wata mafita sai wannan, yanzu kam tasan tun da akayi ma Kalsoom harbin kanko shikenan haukacewa za ta yi, dole ne kO Hilal.ya rabu da ita ko kuma ya mayarda ita gidansu dan ya nemo wanda zata riƙa masa ɗansa.
Cike da farinciki ta dawo gida wani ɓangaren kuma tana ganin rashin dacewar abunda ta aikata, sai xuciyarta ta kan zuga wajen ganin abun ya gushem mata a zuciya, tana ayyana yadda ita ma Kalsoom tayi mata ta raba ta da mijinta........
Pray for my mother she's sick.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *51*
NAMRA POV.
Ashe wuya tana canja mutum, iɗan ka hango Namra a yanzu ba zaka taɓa cewa ita ce ba, ta canja sosai tun daga kan hallitarta zuwa suturar dake jikinta. Zane daban riga dabam sai faman hurin wuta take hayaƙi duk ya boɗe gurin, sai fama.take ta itacen kamar wata tsohuwa.
Sam bata damu ba da hanin zuwa tarbar lefen da Asim yayi mata, ta san ko ba komai ita tana shakar zuwa yanzu dan bata san yadda ƴan'uwanta za su kalleta ba, duk ta wani koɗe kamar ba ita ba.
Daker ta samu wutar ta kama har ta dumama tuwo sannan ta wanke kular da take sakawa Asim abinci ta zuba masa ta kai masa sai ta sake fita ta ɗebo masa ruwa ta aje masa.
Gefensa ta zo ta zauna ta lanƙwashe ƙafafunta irin ladabin nan, sannan ta soma magana gabanta sai faɗuwa yake
“Asim magana nake son mu yi ina son ka ba ni aron hankalin ka”
“Ai kunne ne yake ji ko?”
Ya faɗa yana auna ɗummen a bakinsa.
“Asim ba zai yiyu kullum na riƙa ci da kai na ba, Allah be ɗora min ciyar da kai na ba, fisabilillahi abinda kake min baka kyauta min, bana yin abinci ka yaba, baka bani abin dafawa balle ma kuɗin cefani yanzu tsakani da Allah ka kyauta kenan?”
Ya ɗaga kai ya kalleta yana suɗar hannu.
“Namra kenan, wallahi kina da matsala wani lokacin ƙwaƙwalwarki ƙarama ce, yanzu idan nace zan baki abinci kawai ko kuɗin cefane ina su ke? Ba sai da abu ake yinsa ba? Ko babu zan ba ki?”
“Amman naga kana fita aiki Asim ba za ace kullum baka samowa ba ki kaɗan ne dole wata rana sai ka samo”
“To ɗan abinda na ke samowa ai ba zai wuce na hau achaɓa ba, ba fa wani samu muke sosai ba, ni kaina na fiki son na ciyar da ke dan Aallah ya fi bawa mai yi iyalansa, sannan babu Namijin da zai so mace ta ciyar da shi ko dan gudun irin wannan gorin”
“Ba gori na ke maka ba, gaskiya nake faɗa, idan mu ka zauna muka ce wannan kuɗin na sana'ah kullum shi za'a ci, sai mu cinye sana'ar mu zauna a haka babu komai”
“To ya zan yi Namra? Sata zan yi na baki ko kuma kai na zan siyar na ciyar da ke? Kina gani ba wata sana'ah ce da ni ba daga yanzu ki lissafa duk abinda san kin kashe na ciyar da kan ki da ni idan na yi kuɗi zan biya ki, ni bana son gori akai na farau rashin arxiki? Ko kuma ni na kawo tauasaci duniya? Idan ma kin gaji da zama da ni ne sai ki faɗa min kawai ba wai ki riƙa min magana any how ba”
“Babu mace da zata zauna da kai a yadda na zauna da kai Asim, na watsar da jindaɗin gidan mu dan kawai na yi maka biyayah na zo na zauna a nan gidan ina rayuwar da ban taɓa mafrkin shiga, ka dubi jikina, duk wanda yasan ni ya gan ni a yanzu ba zai ce ni ba ce, amman kullum baka gani sai anbanta ni kake”
“Mtssswww kaji ba, sai jawabi da ƙaryar arziki, duk arzikin gidan ku me suka ƙulla miki? Babu wanda zai gan ki yace ke ƴar gidan ce, tun da kika yi aure har yau babu wanda ya taɓa tako ƙafarsa ya zo gidanki, haka ake rayuwa, ai ko bunsuru kike aure idan basu yi dan ni ba sayi dan ke, ko riƙon ki ake ya kamata ace wani naki yazo garin nan ganin amman ko ciwon da nayi har na warke babu wanda ya leƙo kamar na kashe musu wani”
“Me zai kawo ƴan uwana a gidan ka, bayan sun san dalilin aure na da ka yi? Me za su zo su yi? Ciwon da ka yi wane irin jawabi ne ba ka min akan jinyar da kayi sai ka ce sune suke da alhakin ɗaukar naunyin ɗawainiya da kai, Mama da take mahaifiyarka me tayi maka? Kuɗin data karɓo ai dashen da kuke ne, duk ni nayi ɗawainiya da kai”
Tasss ya watsa wanke mata fuska da mari, ya hau shurinta sai kaurar fuskarta yake yana faɗin.
“Duk iskancin ki ya tsaya a kan ki, karki kuskura saka uwata a cikin sheɗancin ki, dan ba warin ki ba ce”
Kuka take yi sosai tana rufe idonta da ta ke jin kamar ƙasa ta watsar mata a cikin. Be kula irin aika-aikar da yayi ba yasa ƙafa ya fice.
Haka ya wuni a ɗakin tana aikin kuka kamar ta cire idonta, sai da aka kira salla azahar sannan ta samu kukan ya tsaraita mata har ta unƙura ta tashi.
Wanka tayi tare da alwala sannan ta saka wasu tufafin tayi salla. Sai ta ɗauko qur'ane tana karatu.
Guraren uku da kwata wayarta tayi ringing ita har ta manta da sha'anin wayar sai yanzu. Bata kula wayar ba sai data ta kai ƙarshen suratul Yasin, sannan ta rufe qur'anen ta yi addu'ah daga bisani ta maida alƙur'anen mazauninsa, sannan ta nufi wayar ta duba.
Number Anty Yasmin ce. Ta yi mamakin ganin kiran Yasmin har four miss calls, ta manta when ma Yasmin ta kirata tun suna shiri. Bata da kuɗin da zasu isheta magana amman tasan ba zata rasa na flashing ba.
Kamin ta kira sai ga Yasmin ta ƙara kira. Namra tayi saurin picking ta kara a kunne.
“Assalamu alaikum Anty”
“Na'am My Sis ykk”
“Lafiya ƙalau, ya Gwaggo”
“Tana can gida, ni na zo katsina seminar ne, tun shekaran jiya yau zan koma, kuma bana son na wuce ban gan ki ba”
Gaban Namra ya faɗi bata ƙaunar wani yace zai kawo mata ziyara a yanzu, sai dai bata jin zata iya hana Yasmin zuwa gidanta tun da har ta nuna son zuwa.
“Ayyah Anty Yasmin yanzu za ki zo?”
“Eh anjima kaɗan zamu koma”
“Okay ki ce a kawo ki Nasarawa, idan an kawo ki sai ki shiga ta cikin unguwar zaki ga gidan daya ƙone sai ki shigo nan”
“Okay gani nan zuwa yanzu”
Ta kashe wayar. Namra ta juya tana kallon ɗakinta, to be frank bata son kowa ya san halin da take ciki, sai dai babu yadda ta iya.
Kimtsa ɗakin ta shiga yi dan yau duk batayi shara ba tun da wuni tayi kukan dukan da Asim yayi mata.
Wajen gidan ma ta gyara bakin inda zata iya dan baɗin gidan ba mutum ɗaya ne zai iya share shi duka ba, yaro ta aika da kuɗi aka siyo ma Yasmin gala da ruwan sanye ta aje mata. Sannan ya canja tufafin jikinta ta saka masu ɗan kyau ta zauna zaman jiran isowar Yasmin.
Tana jin an turo ƙofar gate ɗin gidan gabanta ya yi mugun faɗuwa. Cikin ƙarfin hali ta taso ta doso gate ɗin gun da Yasmin take tana doka sallama da kallon gidan tana mamaki.
Rumgume ta Namra ta yi tana nuna murnar ganinta. Ita ma baki har kunne, ta ke ɗokin ganinta.
“Namra ke ce? Duk kin canja”
“Ni ce Anty”
“Duk kin canja kin, kin yi baƙi Namra kin lalace”
“Bana jindaɗi ne kwana biyu, mu shiga ciki”
Cike da ƙyaƙyami Yasmin ta zauna dan ita duk gidan be mata ba, mamaki ma take yadda Namra take zaune gidan.
Namra ta dire mata gala da ta siyo mata ta aje mata tare da ruwan sanyi
“Ban yi girki ba yau shine na siyo miki gala”
“My Sis meya samu fuskarki?”
Ta tambaya ganin fuskar duk ya kumbura. Namra tayi shiru bata ce mata komai ba.
“Haka kike wannan rayuwa Namra? Dube ki dubi gidan da kika zaune, yaushe kuka yi gobara?”
“Tun Asim na asibiti an kwana biyu, abubuwan ne suka sauya amman yanzu ai ya samu aiki komai zai walwale”
“To Allah yasa”
Sama sama suka yi fira, bata wani daɗe ba tayi ma Namra sallama ta ciro 20k ta bata. Har bakin gate Namra ta rakata, sai da ta shiga motar da ta kawo suka kama hanya sannan Namra ta koma cikin gida.
ASIM POV.
Cike da ɓacin rai ya fito gida, ya doshi gurin sana'arsa. Ko da ya isa ya tararda abokan aikinsa har sun buɗe shagon suna fitar da kayan aikin.
Haka ya samu guri gefe ya zauna sai fuci yake kamar sune suka masa wani abu. Har suka gama fitar da kayan aikin suka rura wuta suka zauna suka fara zuga. Yana can gefe yana tunanin rayuwarsa yadda zai yi ya rama abinda Namra da iyayenta suka masa.
Wayarsa ya ciro ya dannan number Hajiyar nan dan yayi saving ɗinta tun jiya. Ringing tayi sai da tana daf da katsewa sannan ta yi picking.
“Hajiya Ina wuni”
“Lafiya ƙalau who's this?”
“Asim ne Hajiya, wanda kika ba number ki jiya, kika ce za a miki gyaran gate”
“Oh that Handsome Guy ko? ”
Yayi dariya cike da jindaɗin lafazinya
“Hajiya, ɗan talakan nan dai”
“Ai ajinka ya wuce talaka, kawai dai ka riƙe sana'ar da bata dace da kai ba ne”
“Hajiya abin ne sai a hankali kin san nigeria tayi zafi”
“Ta yi zafi ga wanda be san kanta ba, amman wannan sana'ar ai bata dace da kai ba sam. Anyway yaushe zaka zo ka duba min gate ɗin ne?”
“Wai da yanzu zan ɗauko abokanin aikina sai mu zo mu gani”
“Eh amman kai ya kamata ka fara zuwa ka ga yadda aikin yake, sai ka ce su zo daga ba ya, ko kuma ka koma ka ɗauko su”
“To aikin yana da yawa ne”
“Ba wani yawa gefe ne kawai ya ɗan ɓalle”
“Okay to bari na zo yanzu na duba yadda aikin yake”
“Sai ka iso, number ka ne wannan?”
“Eh Number na ne Hajiya”
“Okay”
Ta kashe wayar. Shi kuma sai faman murmushi yake
“She's so friendly, bata wulaƙanta mutane duk da tana da arziki, ta hutawa kan ta”
Ya faɗa a fili sannan ya tashi yana kaɗe rigar ya nufi gurin aikin nasa, sai da ya sanar musu da aikin ya faɗa zai je ya duba ne sai ya dawo sannan ya tari ɗan a chaɓa ya hau.
Kai tsaye gidan Hajiya Sadiya ya nufa, be sha wahalar ganewa ba, saboda ta karanta address ɗin na ta tun farko.
House number 7 ya shiga, kai tsaye ya shiga gidan kamar wani wanda ta saba zuwa, sai wara ido yake yana ƙara kallon gida da kyau da kyau. Mai gadin ne ya tare shi yana tambayar inda zaije.
Kamin yayi ma mai gadin magana ya ciro wayarsa ya kira number ta.
“Hajiya ga ni na iso, mai gadin ki na ƙoƙarin hana ni shiga”
Sai kawai ya miƙa masa wayar. Mai gadin na karɓar wayar ya kara a kunne sai kawai ya ce
“To Hajiya”
Ya miƙawa Asim wayarsa, yana nuna masa inda zai shiga. Ka ɗa kai kawai yayi ya doshi gurin daya nuna masa yana tsaki, dan ya tsani mai gadi ya wulaƙantasa, shiyasa baya son zuwa gidan da za a tambayeshi inda zai je.
Manyan motoci ya gani a harabar gurin jere, ciki har da wacce taje da ita gurinsa jiya. Tsayawa yayi ya ƙwanƙwasa ƙofar har sai da aka masa ixinin shiga sannan ya tura ya shiga yana sallama kamar ba shi ba.
Da murmushi a fuskarta ta tarbeshi tana nuna masa kujera.
“Maraba da samari”
“Hajiya ina wuni”
“Wuni ko kwana? Ko ɗazu fa wuni kace min ko matar ka ta caja maka kai ne? Kasan matan yanxu sai a hankali, ko da yake baka yi kama da mai aure ba”
“Bana da mata gaskiya, sai dai zafin ƙasar nan”
Tayi dariya tare da nufar gurin freezer ta ɗauko masa lemu da kofi ta zuba masa.
“Ga lemu ka sha, na san dai ka karya ko a kawo masa breakfast?”
“A'a na gode”
Ya ɗauki lemun ya sha, yana kallon ƙaton tv ta na bango dake can ƙarshen ɗakin.
Kallonsa take sosai tana murmushi, tare da gyara doguwar rigar atmafa dake jikinta.
“Na ce ka duba gate ɗin in ya zo gobe sai ku zo ayi aikin, dan yau zan yi baƙuwa gaskiya”
“Okay to ba matsala, gate ɗin na bakin ƙofa ne?”
“Wh ka tambayi mai gadi zai nuna maka”
Ya aje lemun bayan ya shaye shi kaf sannan ya tashi.
“Yo bari naje na duba gobe kamar gaushe zan zo?”
“Da la'asar idan rana ya yi san yi”
Wani irin rausayarda ido take lokacin da take magana da shi tana wani langaɓarda jiki. Shi kuma yayi murmushi yana sa hannayensa aljihu.
“Tau ina zuwa”
Ta juya ta soma tafiya cikin wani irin karairaiya, ta nufi ɗakin. Bata wani daɗe ba ta fito riƙe da sabbin yan ɗari biyu biyu ta mika masa.
“Ga 10k ka hau a chaɓa, sai na gan ka goben”
Ya faɗa tana murmushi tare da shafo hannunsa a lokacin da zai karɓa ɗin.
“Haba Hajiya ayi haka?”
“Ba komai ai irin ku abun tausayawa ne masara aikin yi”
“Na gode Allah ya saka da alheri ya ƙara aixiki”
Ya fito daga falon baki har kunne. Sai da ya tambaya mai gadin ya gwada masa gurin da gyaran yake sannan ya wuce.
KALSOOM POV.
Yau da wuri ta sallami yara da Hilal kasancewar yau Monday ce ranar aiki. Sannan ta shiga gyara gidan, baya ta share ko ina tayi mopping sannan ymta shiga kitchen ta haɗa kayan wanke-wanke ta somawa wankewa tana sauraren ƙira'ar dake wayarta.
Tsin-tsin'tsin ta riƙa jin kamar ana tsokararta, sai tsikar jikinta ya fara tashi.
“A'uzubillahi minal shaɗanin rajin”
Ta furta tana girgiza kanta da take jin yayi mata nauyi. Tunawa tayi da bata da ɗankwali a kanta, sai ta yi saurin komawa falo ta ɗauki ɗankwalin ta ɗaura, ta koma kitchen ɗin ta cigaba da wanke-wanken. Tana cikin wanke wanke ta ji kamar an kiran sunan, cikin muryar Hilal tsayawa tayi tana saurere ba tare data amsa ba, daman can bata da ɗabi'ar amsa kira idan har sau ɗaya ne, sai kuma ta ƙara jin kiran a karo an biyu, a maimakon ta amsa sai kawai ta aje wanke-wanke da take ta nufo falo dan taga idan har Hilal ɗin ne. Har waje ta fito tana dubawa amman vata ga motar Hilal ba balle alamunsa. Tana juyawa ta koma ta sake jin an kirata in Hilal voice.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Allaahumma munzilal-kitaabi, saree'al-hisaabi, ihzimil-'ahzaaba, Allaahumma ihzimhum wa zalzilhum. اللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ الأَحْزَابَ، اللَّهُمَّ اهْزِ مْهُمْ وَزَلْزِلْهُمْ ”
Gabanta ya faɗi da farko, kuma ta tsorata sai dai addu'aj ɗa tayi yasa taji tsoron ya guje mata a take. Daman addu'ah ce ta neman tsari daga makiya.
Sai kawai ta koma ciki ta cigaba da wanke-wankenta. Wani irin ƙwallowa tayi Rafiq dake bachi ya buga. Ba shiri tayi bar wanke wanke ta nufin ɗakin yaran. Ƙasa ta tararda shi yana fisge-fisge kamar wanda za a cirewa rai.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Ta ƙarasa da sauri inda yake ta ɗaukesa tana girgixawa. Amman ina ido da jiki duka a ƙafe sai wani ƙogi yake yana kallon silin, aje shi tayi ta nufi ɗakinta da gudu ta ɗauki wayarta ta kira Hilal.
AMIRA POV.
Tana shiga ɗakin ta tararda komai na ɗakin pink color ne, sai manyan hotunan Amal dake jikin ginin ɗaki har da waɗanda ta yi ƙasar waje, wani gurin tana tare da Abdool wani gurin kuma da Ummi wani da Meesha wani da Fauza sai kuma wanda suka yi da Haleema, ma bin su shine wanda tayi da duka familynsu Hilal yai ma Ummi side hug yai mata kiss irin na nuna tsatsar ƙaunar nan na ɗa da uwa.
Wanda Amal tayi da Hilal ta fi tsurawa ido tana kallon yadda Hilal yake feeding ɗin Amal ranar birthday ta. Hannu ta kai ta shafa hoton tana murmushi.
“Kai na daɗe ina mafarki Abdool, kai ne irin mijin da nake so, sai yanzu na gane dalilin daya sa na bar gida na, ashe rabo ne kirana, saboda kai akayi ni Abdool nima kuma saboda ni aka yi ka, haƙiƙa ban yi sadaukarwar banza ba”
Ta juya ta jingina da ginin gurin ta lumshe ido tana sauke wani sayyayen numfashi.
Babu wanda take gani sai Abdool, rayuwarta da tasa take hangowa irin jindaɗi da kuma rayuwar da za su yi idan ya aureta.
Bayan tayi wanka ta maida tufafin dake jikinta ta zauna ta ci abinci tana ƙara ƙarewa ɗakin kallo. Ta jinjina kai
“Lalai ba ƙaramin dukiya Abdool ya tara ba shi da mahaifiyarsa, amman ina mahaifinsa yake? Ina jin baya nan gidan dan gidan be nuna alamun gidan sarauta ba”
Ta sauke ajiyar zuciya tana auna kanta a matsayin matar Abdool. Irin kallon da yayi mata take tunowa yadda idonsa yake da fari har wani ruwa ya kwanta a ciki kamar balarabe. Tashi tayi ta ƙasara gurin madubi tana kallon kanta, bata da munin da namiji zai ganta yace baya son ta. Idan har baka yabe ta ba to ba zaka kusheta ba.
Shukura ce ta dawo da dare ta kawo mata abinci sai ta kunna mata tv ta ɗauki wasu ɗaga cikin kayan da Amal za tayi amfani da su, da dukan alama Amal ɗin ce tasa a ɗauko mata har da ƴar ƙaramar iphone ɗinta.
________________
Ni kam nace Kar Hajiya ta lalata mana Asim 😏😏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *52*
KALSOOM POV.
Ta yi masa kira biyar be ɗaga ba, ga dukan alamu suna tiyata ko meeting dan shi kaɗai ne yake hana sa ɗaukar wayarta.
“Wayyo Allah na na shiga uku Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Ta furta cikin muryar kuka hawayen na bin fuskarta, zubewa ta yi a gurin hannunta ɗaya saman kai, ɗayan kuma riƙe da waya tana ƙoƙarin kiran Hilal. Still be ɗaga ba, a nan ta jefar da wayar ta koma ɗakin da Rafiq yake tana kuka. Wannan karon abinda ta gani ya bata tsoro dan har kumfa yake fitarwa a bakinsa.
Da sauri ta ɗauke shi ta fito da gudu ta nufi harabar gidan tana ihu. Mai gadin ne yayi kanta yana tambayar ba'asi. Ganin halin da yaron yake ciki ya sashi sallalami tare da karɓarsa ya girgiza.
“Hajiya ki kira Alhaji ki faɗa masa”
“Na kirasa be ɗaga ba”
“Ki sake kiransa kar yaron nan ya mutu”
Jin an ambaci mutuwa yasa ta ƙara rikicewa ta falla da gudu ciki, ta koma ɗakin ta ɗauki wayarta a inda ta jefar da ita.
A rikice ta kira numbersa wannan karon tayi sa'ah kira ɗaya ya ɗaga cikin muryar daya saba mata a duk lokacin data kirasa
“Maman yara...”
Kukanta da yaji yasa gabansa tsinkewa ya faɗi.
“Kalsoom what happend?”
“Rafiq ne Hilal ka zo gida yanzu kar ya mutu...”
Tana jin haka ya katse wayar ya mike daga zaman tattaunar da suka gama yanzu-yanzu ya nufi gidan hankali a tashi. @360 ya hau titi duk hankalinsa sai ya tattara ya koma gida, zuciyarsa sai yayo masa take, wani abun Rafiq ya hau ya faɗo ko kuma wuta ta jashi, kwata-kwata be kawo ma ransa abinda ya tarar yaron na yi ba. A firgice ya fito motar ya nufo gurin da Kalsoom take riƙe da Rafiq tana kuka.
Ya sa hannu biyu ya karɓe sa ta juyo da sauri ya nufi mota, dan babu lokacin tsayawa tambayar abunda y same shi.
Komawa tayi ciki ta ɗauko Hijabinta ta saka, ta ɗauki jakarta ta fito da sauri kamar tana son haɗaw da gudu, sai kuka take irin mai nuna tsantsar tashin hankali. Ba tare data kulle gidan ta fito titi, tari adai-dai sahu ta hau, tana faɗa nasa inda zai kai ta. Be sauketa ko ina ba sai American hospital inda Hilal yake aiki, sai da ta sallami mai Napep ɗin sannan ta nufi emergency duk da bata da tabbacin can ɗin ne ya kai shi ko a'a. Wasu nurser ta tambaya, suka tabbatar mata da xuwansa da kuma ɗakin daya nufa da yaron. Da gudu ta ƙarasa gurin tana share hawayen da suka ƙi su tsaya mata.
Kai da kawo ta riƙa yi ita kaɗai tana jiran fitowar Hilal ko kuma wasu daga cikin, amman shiru har kusan mintuna arba'in da takwas.
Sannan wasu Nurser suk fito daga ɗakin, ita kuma ta zura kai sai leƙo take ko zata ga wani halin da Rafiq yake cikin.
Hilal ne ya fito, sai ya janyo ƙofar ya kulle. Fuska babu annuri ya nufi office ɗinsa, ba tare da kula ta ba, balle ma ya bata amsar tambayar da take masa.
Binsa tayi a baya tama tambayarsa amman be kula ta ba har sai da ya shiga office ɗin. Ita kuma duk hakalinta ya tashi a tunaninta ko Rafiq ya rasu ne.
“Me kika ma Rafiq ? Ya aka yi ya ci guba?”
Itace tambayar da Hilal ya fara mata suna shiga office ɗin. Ras ras ras gabanta ya faɗi har jakar dake hannunta ta faɗi idonta na kan Hilal tana kallonsa hawaye sai zuba suke mata ba tare data sani ba.
“Gu....Ba....Bah...”
Ta maimaita cikin rawar muryar tana mamakin furucin daya fito a bakin Hilal. Shi kuma sai kallonta yake fuska babu annuri.
“Eh guba, ya aka yi ya ci guba?”
“Wallahi ban sani ba, amman Rafiq ko abinci safe be ci ba, bachi ma yake, sai kawai na ji ƙyalowarsa ina shiga ɗakin na tararda shi a ƙasa yana fusge-fisge”
“Be ci komai ba guba zata zo ta shiga jikinsa ne? Ni dai a sanina indai ba batir ɗin remote ba mu da wani abu mai guba, da Rafiq zai yi saurin ɗauka ya saka a baki”
“Ban gane ba me kake nufi?”
“Ina baki damar da nake baki ne Kalsoom dan ki samu damar zama uwa a gurin ƴaƴana, kuma dukansu kamar marayu suke a gare ki tun da babu uwarsu a tare da su, babu abinda Ezzah bata faɗa min amman bana kulawa saboda na ɗaukeki a mtsayin uwar data haife su, a tunani ba zaki taɓa musu abinda be kamata ba but wannan yayi yawa, idan ba shi akayi ba taya kamar Rafiq zai ɗauki guba ya ci?”
Ta yi shiru ta kasa magana, sai idonta ne suke magana. Jikinta ya mutu lis har ji take kamar ta zube a gurin. Ba ita ce ta bashi gubar ba, bata da tabbacin gubar ce ma yaci tun da tasan be karya ba, sai dai kuma bata da abinda zata wanke kanta, dan tage gun da kalaman Hilal suka dosa.
“Idan na cutar da Izzah na kashe Rafiq me zan ji?”
“Nima ban sani ba Kalsoom, ban sani ba, wata ƙila ba ki son zama da su ne ko kuma kin gaji da su, amman ni ina son ƴaƴana fiye da yadda nake son rayuwata, kuma zan iya barin komai a kan ƴaƴana, dan sune zasu zauna da ni ko a wane hali nake ciki ina ta avoiding abinda kike ma yaran nan Kalsoom but you cross your limit”
Bata ce masa komai ba, tasa hannun hijabinta ta goge hawayenta, ta duƙa ta ɗauki jakarta ta juya jiki ba gwari ta fice. Binta yayi dan zuciyarsa na raya masa ɗakin da Rafiq yake zata je. Hanyar da zai kai mutum ward ɗin ta nufa ga dukan alamu can ta nufa, tun da ga hanyar fita harabar asibitin nan ta bari. Daga inda yake ya ɗaga muryarsa ta yadda zata iya jiyosa yace
“Kalsoom don't, we don't need you for now”
Tsayawa tayi cak! Kamin ta juyo ta soma takowa ta dawo inda yake. Sai da ta kawo daf da shi sannan ta ɗaga muryar cikin zafin rai ta ce.
“Thank you, thank you so much”
Ta faɗa in low voice sannan ta juya, hawaye na cigaba da zuba a fuskarta ta nufi hanyar data zai fitar da ita harabar asibitin.
NAMRA POV.
Tun faɗan da suka yi da Asim ya fita bata sake saka shi a ido ba sai washe gari, ita kaɗai ta kwana a gidan, tana aikin data saba na kuka, bayan ta faɗa ma Allah buƙatarta.
Sai da safen ta gurka sabon abinci dan kwata-kwata jiya bata yi girki ba, saboda bata cikin ɗaɗin rai. Bayan ta gama, ta gyara gidan, ta ɗora ruwa tayi wanka sannan ta zuba abincin ta zauna ta ci sai kawai ta fashe da kuka, haka ta riƙa rera kuka har tayi ya isheta sannan ta share hawayenta ta ɗauki abinci ta mayar. Dan bata iya ci. Har zata kwanta sai wasu yara suka shigo siyen magi da manja, sai da ta sallame su sannan ta shimfiɗa tabarma waje ta ɗauko matashin kai zata kwanta kenan sai ga Asimya shigo.
Sai da tayi kamar kar ta masa magana ganin be shigo da sallama ba, kuma be kalli inda take ba, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, ko ba komai mijinta ne dole ta yi haƙuri ta zauna da shi a haka.
Binsa ta yi cikin ɗakin, sai ta same shi yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa. Yana ganinta ya wani kawar da fuska, ya ƙara haɗe rai.
“Sannu da zuwa. Jiya baka kwana a gida ba lafiya?”
Ya tsaya daga cire wandon da yake ya kalleta
“Uwata ce da zan sanar miki dole? Ke kike iko da ni ko kuma ni nake iko da ke?”
“Ba ni bace amman ina da haƙƙi, Asim mi yasa kake min haka ne? Ina ta ƙoƙarin taushe zuciyata dan na zauna da kai lafiya amman baka so, look at me, haka nake a da duk na bi na canja saboda kai har kunya nake ji wani ya gani a halin da na ke, kana cin amanata Asim kana zalumtana”
Ya nuna kansa.
“Nine azzalumin?”
Baya baya tayi ta girgiza masa kai, dan ta san dukanta zai yi.
“Yi haƙuri dan Allah”
“Bakin ki ya saba da furta kalami mai daɗi a gare ni ko kuma jikinki ya faɗa miki”
Ɗaga kai tayi ta kalleshi da idonta dake zubar da hawaye, Asim ɗin baya take hangowa Asim ɗin da yake ce mata idan babu ita a duniya ba zai iya rayuwa ba, wanda yake ce mata zai iya sadaukarda komai na sa danta, zai iya bata dik abinda take so, Asim ɗin data watsar da kowa a kansa, wanda ta bijerewa Abbah saboda, wanda Maryam da Anty suka yi ta tunantar da ita akansa amman idonta ya rufe, yau shine yake gargaɗinta. Wani baƙin abu ne mai kamar ƙaho taji ya tsaya mata a zuciya har ƙafafunta suka kasa ɗaukarta ta zube ƙasa tana yaƙi da baƙincikin dake neman numfashimta.
“Kur wallahi kurwata kur sai dai ki ci kan ki”
Ya faɗa yana yatsine ganin kallon da take masa ɗazu. Lumshe ido tayi, ta rarafa ta ƙarasa saman katifar ta kwanta, tana sauraren ciwon zuciyar daya game ilahirin jikinta. Nan take jikinta ya ɗau rawar fever sai kuma zafin jiki. Bedsheet taja ta lulluɓa dan tsanyi take ji ya baibayeta.
Asim kan ko a jikinsa, fita ma yayi daga ɗakin yaje yayi wanka ya dawo ya saka wasu tufafin ya mata waɗanda ya cire a tsakar ɗaki yayi lafiyarsa.
Gurin aikinsa ya koma, daman yayi da abokan aikin nasa zasu je gurin Hajiya Sadiya gyaran gate. Dan haka yana isa suka wuce.
Shine yayi musu jagora a cikin gidan har suka yi aikin suka gama, sannan ya koma ciki ya sanar mata da sun kammala aikin sai ta ɗauko 30k ta bashi akan aikin da be wuce 8k ba. Hannu biyu yasa ya karɓa yana mata godiya.
“Allah ya saka da alheri Hajiya Allah ya ƙara arziki, wallahi halin ki na musaman ne”
Ta yi dariyar jindaɗi.
“Na ce ka iya mota kuwa?”
“Eh na iya mota Hajiya”
Ya amsa da sauri jikinsa har rawa yake.
“Idan ba damuwa, ina son ka riƙa jana a mota dan yanzu bana da direbe, kuma kaga gidan nan yayi min girma da yawa dole akwai buƙatar wanda za a aika a duk lokacin da aka tashi da kuma mai ban ruwan fulawowi da sauran ayuka”
“Wallahi Hajiya duka zan iya, wallahi komai kika sani zan iya”
“To idan ka shirya sai ka min magana, idan ban takurawa aikin ka ba”
“A'a ai aiki ina yi dan na samu na taɓawa, ai ko a yanzu ai na tashi”
“A'a kaje dai kayi shawara dan ni a gidana zaka dawo idan har ka fara aikin”
“Ba matsala Hajiya, zan iya zama a gidan ki”
“Yanzu dai idan ka kimtsa sai mu yi waya”
“Toh Hajiya na gode Allah ya saka miki da aljannah”
Da murmushi ta amsa nasa ba tare data ce amin ba. Sai ya juya ya fito baki har kunne zuciya kuma fal da farinciki.
A bakin ƙofar ya tsaya ya cire 20k ya saka a ɗayan aljihunsa, ya ƙarasa da 10k ya miƙa musu yace su ta bashi. Su kansu sun yaba da 10k ɗin sai kowa ya cire na abin hawan da ya hawo suka komawa Ƙanen Babansa da sauran kuɗin sai ya miƙawa kowa nasa. Duk da 20k dake aljihun Asim be hana shi sa hannu ya karɓi abinda Ƙanen mahaifin na sa ya bashi ba.
Basu tashi aikin ba sai 6 kamar yadda suka ba, sannan suka rufe kayan aikin na su. Sai dai ba su bar gurin ba sai da suka yi sallah magariba.
Sannan yayi sallama da su ya nufo gida, ba kuma gida kai tsaye ba, unguwarsu dai dan be shiga gida ba sai da 10pm. Babu abinda yake ransa sai saƙe-saƙen tunanin yadda zai sarrafa 20k tare da sauran kuɗin da yake ajiya su zame masa millions.
Yana ganin halin da take yasan vata da lafiya, dan tun fitarsa da zazzaɓin ya rufeta bata tashi daga inda take sai idan sallah zatayi, maganin ciwon kai ma sai da wata mai siyen magi ta shigo sannan ta aike ta ta siyo mata ta sha. Amman saboda ƙarfi hali yaƙi yace mata sannu balle tambayarta abinda yake damunta.
Haka ya kwaɓe tufafin jikinsa ya saka ɗan guntun wando data wanke masa jiya ta farar falmara, ya je ya ɗibi abinci ya ci sannan yaje ya rufe gidan, yazo bayanta ya kwanta yana lallubarta. Tabbas bata da lafiya dan yaji jikinta da zafi sosai. Cikin ƙarfin hali ta ɗaga kai ta kalleshi.
“Haba Asim bana jindaɗi”
“Ai na ji Allah ya sauwaƙe ya baki lafiya”
Sai dai hakan be sanya shi daina abinda yake da niyar yi ba....
AMIRA POV.
Tare suka yi breakfast da sukan ƴan matan Ummi, da kuma Ummi ita kanta. Yadda Ummi take ƴaƴanta ya burge Amira ainun hakan yasa ta kwaɗayin shiga cikim familyn dan ita ta zama ɗaya daga ciki. Suna gama cin abincin safe Abdool ya kira Ummi ya gaishe ta, bata iya jin abinda yake cewa duk da taso haka ganin fuskar Ummi da Murmushi alamun wata magana ce yake mata mai daɗi mai kuma muhimmanci.
Tsakaninta da Ummi akwai tazara sosai, dan tana ɓangaren falon ne ita da Haleema. Ummi kuma tana ɗayan ɓangaren ne. sai dai hakan be hanata kashe kunne ta jiyo abinda Ummi take faɗa masa ba.
“Good son haka na ke son ka zama”
“Allah ya kai mu me za a girka maka?”
“To yayi kyau ɗan Mai Martaba kuma Babansa”
Ƙyalƙyalewa Ummi tayi da dariya, ga dukan alama ita ma wani abin yace mata. Haka kawai Amira ta samu kan ta cikin farin ciki, ta san ko ba komai yanzu Abdool.yana can cikin walwalah da farinciki.
Farincikin dake zuciyarta ne yasa ta kai hannu ta riƙo hannun Amal dake shirin aje school bag ɗin a doguwar kujerar da Amira take zaune.
Wani irin ƙyalowa Amal tayi tana yarfarda hannu alamar ƙyaƙyami ta nufi bathroom ɗin falo dan wanke hannunta.
Haleema ta girgiza kai.
“Haka take, ƙyanƙyamin mutane take, Amal ƴar iskar yarinya ce, sai kin yi haƙuri da ita”
Amira tayi murmushi tana nuna abinda a Amal tayi be dame ta ba ko ɗan.
“Ba komai ai wata rana zata daina”
“Yeah amman Amal will never change, bari na koma ciki zan yi bachi”
“Ba ku da class ne?”
“Muna da amman sai da yamma”
“Okay sleep tight”
“I will thanks”
Ta wuce ɗakinta tana rangaji irin na ji da kai ɗin nan. Da Ido Amira ta bita har ta shige sannan ta ƙara mai da hankalinta gurin Ummi dake faɗawa Shukura abinda za a girka musu. Sai da Ummi ta tashi sannan Amira ta bi bayan shukura kitchen ta karɓi girkin ta girka musu white rice and pepper soup. Ummi bata san Amira tayi girkin ba har sai da taga tana jerawa a dinning. Ita kuma tana saukowa daga stairs.
“Shukura...”
Ummi ta ƙwala mata kira. Sai gaba da gudu tazo gaban Ummi ta tsaya.
“Ya kika barta tana jera kaya? Aiki aka ce miki ta zo yi ne?”
“A'a Wullahi Haseya sene yase zse girka ni in tafee”
Ummi tayi murmushin jindaɗi da kuma yabawa da halin Amira.
“To je ki taya ta jera kayan”
Da sauri shukura taje tana taya Amira har suka gama.
YASMIN POV.
Tun da ta dawo tunanin Namra take damunta, tana ganin idan har bata faɗawa Anty halin da Namra take ciki ba bata kyauta ba. Sai dai kuma tana tsoron faɗa musu kar ya zama tayi ma Namra kashin aure ko kuma ita Namra ɗin taga laifinta.
Dan Uzair ya gargaɗe ta akan karta faɗa tun lokacin data faɗa masa a irin halin data samu Namra.
Yau ma nanata mata yake kamar kullum.
“Babu ruwanki da matsalarta idan abin ya dame ta ai ita zata faɗa da kan ta, ba ita ta zaɓe shi ba, kin manta irin cin mutuncin da yarinyar nan tayi min?”
“Komai tayi maka Uzair be kamata mu ƙyaleta a halin da take ciki ba, wallahi baka gan ta abin tausayi, har dukanta yake duk ta canja kala”
“Ina ruwanki da canja kalar ta? Ba auren soyayyah tayi ba? To taje can su ci soyayarsu, wallahi Yasmin idan baki fitar da maganar nan daga ran ki ba, sai mun samu matsala da ke, kiji da cikin da yake jikinki dan Allah”
“Amman Uzair ni lauyace kuma..”
Ya taso ta haɗe bakinsa da nata......
DEDICATED THIS CHAPTER TO ZAGON K'ASA PAID GROUP MEMBERS. I LOVE YOU ALL 💖💖💖
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *53*
KALSOOM POV.
Haka ta fito asibitin hawaye na bin fuskarta amman bata damu ba, kamar ma bata san suna zuba ba. Bata iya gani sosai saboda hawayen daya cika idonta, sai dai hakan be hana ta tsayar da Mai a daidaita ba.
Tana shiga be sauke ta ko ina ba sai unguwar su Salma mai Napep ɗin ya sauketa, ɗari biyar ta miƙa masa bata tsaya karɓar canji ba ta smtura gate ɗin gidan ta shiga hawaye na bin fuskarta.
Ganin motar mijin salma yasa ta tsayawa a bakin ƙofar falon ta share hawayenta ta gyara tsayuwar hijabinta sannan ta tura ƙofar ta shiga tana sallama da muryar kuka.
Babu kowa a falon kasancewar yau monday ce yara basu dawo scul ba kuma ita da mijinta suna ɗaki. Saman kujera Kalsoom ta xauna ta dafe kanta tana sauraren hawayen da suke son zubo mata. Ta ɗauki mintuna talatin zuwa talatin da biyar a haka sannan Salma ta fito daga ɗakin mijinta tana dariya. Ganin Kalsoom ya razanata, dan da farko ta zata ko ba ita bace sai daga baya ta yarda Kalsoom ɗin ce jin sheshshekar kukanta. Ƙarasawa tayi ta dafata
“Ke miya same ki”
A maimakon ta yi magana sai kawai ta ƙara fashewa da kuka. Hakan yasa hankalin salma ya tashi sosai, har zauna kusa da ita tana girgiza ta
“Dan Allah ki yi magana ko wane ni ya mutu”
Daker ta samu natsuwar sai ta kanta sannan ta kalli salma ta soma mata bayani ba tare da hawayen sun daina mata zuba ba.
Salma ta girgiza da jin labarin har ta rasa yadda zata fassarashi tun da Kalsoom tace be ci guba ba.
“Kalsoom ko dai ya ci baki sani ba?”
“Wallahi be ci ba, bachi ma yake yi”
“Dole ne ya zarge ki Kalsoom ni kaina zan iya aikata kwatankwacin abinda Hilalya aikata, ba ze iya banbance ƙarya da gaskiya ba a yanzu, wata ƙila ya ci gubar ne ba tare da kin sani ba”
“Ba mu da abinda Rafiq zai yi saurin ɗauka ya ci a yanzu, he's just three years old, ni kuma ba zan dauka abu mai cuta na bashi ba, wallahi ban masa komai ba”
“Ba za ki masa ba Kalsoom ba halin ki ba ne, amman taya haka ta faru”
“Ban sani ba Salma wallahi ban sani ba”
Ta faɗa cikin wani irin kuka mai ban tausayi. Salma ta dafa ƙawarta tana hawaye ita tace
“Rashida bata zo gidan ba?”
“Bata zo ba, tun ranar daya sallameta bata sake zuwa gidan ba, kayanta ma sai daga baya ta turo ƙannenta suka ɗibi wasu”
“Allah kaɗai ya san ko mienen wannan abin. Amman abin akwai ban mamaki”
“Amman dai ɗazu na ji ana kirana a muryar Hilal lokacin dana leƙa ban ga kowa ba, har sau uku, a lokacin ne na ji ƙyalowar Rafiq”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah yasa ba lamarin iska ba ne, kar ace ke aka jefa ya faɗa kan yaron ko kuma tayi ma yaron jifa dan ya mutu ace ke ce”
Kalsoom ta kalleta da sauri
“Ɗan ta ne fa”
“Ko ɗan ta ne fa? Ai zata iya aikatawa, idan zuciyar mutum bata da imani komai zai iya aikatawa”
“Na ji ni zata iya yin amman ba zata iya yi ma ɗanta ba, mu riƙa kyuatata zato Salma”
“Hmmm Allah dai ya kyauta, yanzu ina zaki je?”
“Ni ban sani ba, idan naje gida ban san me zan faɗa musu ba, ba lalle bane suma su yarda da ni”
“Kar ma kije gida a yanzu ki koma ɗakin mijinki”
“Amman yace min basa buƙata a yanzu”
“Komai yace miki tun da be ce kije gida ba karki je, idan kin koma gidan ki sa masa ido shi da yaransa babu ruwanki da sha'aninsu, har sai idan ya saki, amman yanzu idan kika koma gida zai ƙara jin haushin ki ne, ki bashi lokaci ya huce ya fahimci komai shi da kansa zai dawo yayi miki magana”
“Idan kuma na koma gidan ya wulaƙanta ni fa?”
“Ki jira har ya wulaƙanta ki ɗin amman yanzu gaskiya ban baki shawarar zuwa gida ba, Kalsoom ki koma ɗakin mijinki”
“Da nasan haka aure yake da ban yi ba, tun da na shiga gidan kullum da matsalar da take buɗe min sabon shafi, idan kuma ka zauna ba kayi auren ba jama'ah su zage ka, idan kuma auren ya mutu ace ka kaso auro ka dawo ma zaman gida, ba su san matsalar ka ba”
“Haƙuri zaki yi, haka LAMARIN DUNIYA (my previou novel) yake, kowa da yadda Allah ya tsara masa tasa rayuwarwa, no matter what you do how you try you can't escape your destiny and you can't change your past, all what you can do is wait for your future with hope and smiled behind your tears, rayuwar aure kala kala ce kowa wace ta kalar nata jarrabawar idan kika ji wani ma sai kin riƙe ba ki marriage is like going to a restaurant and order your choice from the menu, and then look at neighbouring table n wish you”d ordered that dole ki yi haƙuri babu komai a cikin rayuwar aure sai ƙalubale shiyasa kika ji akan ce kayi haƙuri haƙuri dai, kuma idan kika yi haƙuri tun a duniya sai Allah ya saka miki”
Kuka kawai take, bata iya cewa komai ba har Salma ta gama nusar da ita akan hanyar da take ganin kamar ita ce mafita a gareta.
Sai da tayi sallah la'asar sannan salma ta raka ta ta shiga Napep ta koma gidan mijinta, ba dan ranta yazo ba.
Cikin fargaba da tunani ta koma gidan a zatonta ko Hilal ya dawo, kar ya tambaye ta ina ta fito bata san me zata ce masa ba, tun da ba gida yaje ba. Sai ta tarar be ma dawo ba sai su Izzah da suka lalata falon da shinkafa suka watsar da uniform ɗin su a tsakar falon da scul shoes da bags duk a falon. Saman kujera ta zauna tana sauke ajiyar zuciya. Sai ga yaran sun fito cikin shirin islamiya sun, Ulfah ce taje ta rumgume ta, Izzah kam ko gefenta bata kalla ba ta fice.
“Anty mun dawo baki gida”
“Eh naje wani gurin ne”
Ta faɗa tana murmushin ƙarfin hali idonta duk ya cika da ƙwalla.
“To mun tafi makaranta kina da biyar ki ba ni?”
Ta tambaya tana cizon hijabinta. Naira ashirin Kalsoom ta ciro daga jakarta ta miƙa mata.
“Ki raba ke da Izzah”
“To mun gode”
Ta daka tsalle ta nufi ƙofa. Tana daf da ficewa Kalsoom ta kira, sai ta juyo tana kallon Kalsoom dake hawaye.
“Ki min addu'ah kin ji?”
“To mi zan ce?”
“Kice Allah yayi min mafita”
Sheƙowa tayi da gudu ta dawo ta rumgume Kalsoom tana share mata hawayenta.
“Ki daina kukan zan miki addu'ah i love you”
“I love you too”
Ta sake ta, ta juya da gudu ta fice tana kiran sunan ƴar'uwarta.
“Ezzah jira ni......”
Sai da suka fice sannan Kalsoom taja dogon numfashi ta cire hijabinta ta shiga gyaran falon.
YASMIN POV.
Duk irin jan kunne da kuma gargaɗin da Uxair yayi mata akan karta faɗawa kowa halin da Namra take ciki bata ji ba. Dan ta kada samun sukuni tun lokacin data ga halin da namra take ciki. Abin ya tsaya mata a rai, da ace ba Namra bace da kotu kawai zata saka Asim ta nemawa Namra haƙƙinta, an suna da ƙungiyar data hana cin zafin mata musmman mata hausawa da basa iya magana akan komai.
Daga kotu bata zame ko'ina ba sai gidan Anty. Daga Aisha sai Anty Amarya kawai ta tarar a gidan. Daga Hajiyia Barau har su Maryam sun je walima.
Anty Amarya tayi mamakin ganinta, duk dai ta kan biyo wani lokacin idan Uzair ya kawo ta gaishe da Hajiya Barau, sai dai ba kamar yau ba, dan ta sake sosai kamar ba ita, ta koma Normal kamar yadda take da.
“Yau Yasmin gidan mu? Hajiya ko bata nan”
“Eh Na sani ai, dan nasan zata je walimar Fateema, gurim ki na zo ma”
“Mashallah yau tafiyar tawa ce kenan”
Anty Amarya ta faɗa tana murmushi. Aisha ta dire mata drinks sai ta bar musu falon, daman can tun lokacin data na shiri da Namra jininta be haɗu da Aisha ba balle yanzu da suka koma zaman doya da manja.
Sai da ta sha lemun sai ta fara tunanin ta inda zata fillowa Anty dan bata jin zata iya faɗa mata maganar kai tsaye.
“Na ce when last kika je gurin Namra”
“An daɗe gaskiya tun mijinta na jinya, na so na koma sai tace na yi zamana ai za ta zo, lafiya dai ko?”
“Ayyah nima samina mukaje katsina sai na biya gidan ta”
“Ai ko kin kyauta Yasmin ko ke fa? Amman ace ɗan abu kaɗan dan ya shiga sai taren ku ya ɓace? Yadda kuke da Namra kamar wacce kuka fito ciki ɗaya da ita”
“Ni kai na da nasan haka rayuwar auren Namra zata kasance da ban hana Uzair aurenta ba...”
Jindaɗi da Murmushin dake fuskar Anty Amarya ya ɓata, ba tare da ta ƙarasa fahimtar gun da kalaman Yasmin suka dosa ba.
“Wani abin ne ya faru?”
“Anty da dai kin shirya kin je da kan ki kin ga Namra, kar na zama sheɗan”
“Babu wani Sheɗan Yasmin faɗa min, dan Allah ki faɗa min”
“Anty Namra tana cikin wani hali tana rayuwa irin rayuwar da babu wanda ya taɓa mafarkin zata shige ta, gidan da take ciki na ƙone a bq sune zaune, kuma mijinta ba shi da sana'ar yi, manja da magi take saidawa, kuma ko da naje fuskanta duk ya kumbura da alama dukanta yayi, tayi baƙi ta lalace kamar ba ita....”
Jikin Anty Amarya yayi sanyi sosai, har ta kasa furta kalma daga bakinta, mamakin labarin da Yasmin ta bata take ta sakarwa Yasmin ido tana kallonta har Yasmin ta koma.tunanin wata ƙila Anty bata yarda da maganar ta bane.
“Kishirya kije ki gano ma idon ki dan Allah karki ce ni na faɗa miki”
Kai kawai Anty ta ɗaga mata ta kwanta a kujera ta lumshe ido tana yaƙi da hawan jinin dake son taso mata. Yasmin na ganin hakan gabanta ya faɗi sai duk tsoro ya rufe ta kar wani abu ya samu anty ace ita ce, da sauri ta ɗauki makullin motarta da wayarta ta fice.
RASHIDA POV.
Tana aiki wayarta tayi ringing, amman bata ɗaga ba sai da ta kammala dukan abinda take. Sannan ta duba Number mai kiran.
Cousin ɗinta ce Shafa wacce suke aiki a asibiti ɗaya da Hilal.
Sai da ta kiran numbers ɗin da suka kira bayan ita suka gaisa suka yi maganar da za su yi sannan ta kira Shafa.
“Matar likita, ina ta kira baki ɗaga waya ba”
“Wallahi ina office ne aiki yayi min yawa, ya kike?”
“Au har kin samu damar aikin ɗan ki na kwamce asibiti”
“Ɗa na? Ɗa na na cikina ko na ƴan'uwa”
“Wai tsaya karki ce min baki sani ba”
“Wallahi ban sani ba me ya faru?”
“Wallahi ɗa zu da safe aka kawo shi guraren goma wai ya ci guba daker aka ceto shi”
“Guba...?! Garin ya?”
“Wallahi ban sani ba, mu dai muka taimaka masa gurin coto rayuwar yaron. Ni kam nayi mamakin rashin ganin ki a gurin”
“Guba ta bama ɗana kuma?”
Rashida ta faɗa cikin kuka.
“Au wai baki sani ba? Zance duk ya karaɗe asibiti ɗan doc ya ci guba an kawo shi asibiti, amman dan Allah ki rufa min Asiri karki ce gare ni kika ji”
Kashe wayar Rashida tayi ta tashi yana kuka ta fice daga office ɗin. Tana fitowa kowa ya soma tambayar ba'asi ganin tana kuka.
“Kishiya ta ce ta sama ɗana guba, yana can asibiti”
Kowa Amsar data ke basa kenan. Su kuma sai tsinewa Kalsoom Albarka suke suna aybantata. Kamin ta ƙarasa gurin motarta har ta kira su Momy ta faɗa musu.
Wani irin kuka take tana tuƙin motar har cikin ranta take jin abinda Shafa ta faɗa mata. Kamin ta ƙasara asibitin ana ta kiranta numbers ɗin ƴan'uwa da alama suma sun ji ne.
AMIRA POV.
Wani kalar daɗi ne ya baibaye ta tun lokacin data ji Ummi na labarta ma ƴaƴanta Abdool na nan zuwa dan sun gama meeting ɗin da zasu yi, ya samu free days zai dawo gida yayi su, daman tun faruwar abin nan be zo gida ba.
A ranta take shirya irin nata tabarda zata masa, wanda take tunanin zai ɗauki hankalinsa izuwa gareta. Girki ne abinda ta fara kawowa a ranta dan tasan ta ƙware a wannan fannin. Sai dai matsalarta ɗaya Amal dan itace mai cewa ba zata ci abinda Amira ta girka ba, a kullum idan Amira tasa hannunta a abincin gidan sai ta ce ba zata ci ba.
Ta baro part ɗin falon inda take zaune ta nufo gurin da Ummi take zaune ta zauna ƙasa kusa da Ummi kamar ta shige jikinta.
“Eh haka nek son ayi idan ya dawo sai kuje a duba gidan nan a gyara a zuba sabbin ƴan haya, dan gidan marayu ba a barinsa haka”
Sai da Ummi ta ƙare zancen da take sannan ta kalli Amira dake ƙasa zauna tana murmushi.
“Amira akwai da son jiki kamar Abdool”
Amira tayi murmushi idonta na cika da hawaye.
“Haka nake jin ki kamar mamana kina tuna min da mamana sosai, yanayin rayuwarki”
Hawaye ya silalo daga idon Amira, wannan maganar har cikin zuciyar Amira take, tabbas tayi missing Ammy gashi kuma bata san ranar da zata sake haɗuwa da ita ba, bata san halin da take ciki ba.
Zubar hawayen Amira yasa Ummi ta ji babu daɗi, wannan karon da kanta tasa hannunta ta share mata hawaye.
“Ki daina kuka kin ji? Zan zame miki uwa inshallah, kuma nan gaba zaki koma gurin uwarki na miki alƙawari”
“Na gode”
Ta rumgume Ummi tana wani irin kuka mai taɓa zuciya........
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *54*
Hankali a tashe ta isa asibitin, hawaye na bin fuskarta. Duk wanda ya ganta a lokacin sai ya tausaya mata dan sun san abinda ya kawo ta asibitin. Daman tuni labarin ya karaɗe asibitin cewa Amarya Doc ta saka ma ƙaramin ɗansa guba. Sai ma a yanzu ne wasu ne suke jin cewar Doc ya rabu da Rashida.
Kowa tsinewa Kalsoom yake wasu na faɗin daman kishiyoyin yanzu haka suke su shigo su kore uwargida kuma su mallake ƴaƴan miji da miji.
Wani irin banka tayi ma ƙofar office ɗin Hilal ta shiga kamar zata tashi ɗakin.
“Ina ɗa na yake?”
Shine abinda ta tambaya hawayen na bin fuskarta. Ɗagowa yayi daga dafe da kan da yake ya kalleta. Be yi msmakin ganinta ba daman yasan zata zo tun da akwai ƴan'uwanta a asibitin da zasu kai mata labari.
“Ina ɗa na yake Hilal?”
Ya sake tambaya ganin yayi mata ƙuri da ido kamar ba dashi take magana ba.
“Ɗan ki ko ɗa na?”
“Ɗa na, si kai baka san zafin sa ba da baka bari wata ta kai ga ba shi guba ba”
Miƙewa yayi tsaye ya daki teburin dake gabansa.
“How dare you, idan kin san zafinsa ai bs zaki taɓa zuwa wani gurin ki aikata zina ba, ba zaki taɓa bada kan ki ga kowa ba sai ubansu, amman haka kika taka igiyar aure Rashida kika tsallae ƴaƴanki kika aikata zina da namijin da ba muharramin ki ba, na ƴi nadamar haɗa zuri'ah dake da ace wats na aura ba da rayuwar ƴaƴana bata kasance a halin data kasance a yanzu ba”
Tun da yake maganar take baya baya har ta jingiya da ginin ƙofar idonta na hawaye.
“I need to my son”
“You won't see him”
Ta muna kanta yana mamakin yadda duniyar Hilal ta birkice mata.
“Hilal ni ce!”
“And so what? Get the hell out of my office”
“Kotu zata raba mu da kai ba zan ƙyale kai da matarka ku kashe min ɗa ba”
Ta buɗe ƙofar da ƙarfi ta fice. Be damu ba dan yasan ya riga ya kulle ɗakin da Rafiq yake ciki tun bayan tafiyar Kalsoom.
Ba shida wani aiki amman haka ya zauna a office ɗin dan baya son zuwa gida kwata-kwata gidan ya fita aransa.
Haka ya riƙa karɓar masu shigowa suna masa jajen abinda ya faru tare da masa Allah ya tsare gaba, wasu kan tambaye shi ta ya lamarin ya faru wasu kuma su kuma basa tambaya ganin kamar cin fuska ne.
Bayan yayi salla magariba ya koma ɗakin da Rafiq yake ya zauna yana kallonsa. Ga dukan alamu ya samu sauƙi dan bachinsa yake hankali kwance, humfashinsa na tafiya dai-dai kamar yadda ake so. Ana daf da kiran salla isha'i Hajiya ta iso tare da wasu ƙanensa.
Hilal na ganinta ya tashi a kujerar da yake zauna ya miƙa mata ta zauna, sannan ya soma miƙa mata gaisuwa. Bata karɓa ba ta kalli Rafiq cikin tausayi tace
“Hilal ya aka yi haka ta faru? Wai Kalsoom tasa masa guba?”
Shiru yayi yana tunanin ta ta inda zai soma maganar da bata daɗin faɗi. Idan har ya amsa da ita ɗin ce bashi da tabbaci ita ɗin ce idan kuma ba ita ba ce to wanene bayan daga ita sai Rafiq ne abin ya faru?
“Wallahi ina meeting ta kirana ni ban ɗaga ba sai daga baya na kirata sai ta ce min na zo fida Rafiq babu lafiya, ina zuwa na tarar bakinsa na kumfa ko da na ɗauko na kawo sa asibiti kamar ba zai yi rai ba, bincike dai ya nuna guba ya ci. Tun ɗazu aka masa hoto amman ban karɓo ba”
Hajiya ta taɓa hannu tana salati.
“O o ita kuma haka take? Hilal baka dace da matan ƙwarai, yanzu ɗan wannan ƙaramin yaro ko kashe tayi me zata ji? Kai duniya”
Shi dai yayi shiru be ce komai ba, hannyensa zube a aljihu. Kamin su ƙara cewa wani abu sai ga Ummu Faisak ta turo ƙofa ta shigo fuska babu annuri irin yau tana cikin masifa ɗin nan.
Hajiya tayi mata kallon marar kunya da tarbiya ganin yadda take huci kamar baƙin maciji.
“Haba Maman Faisak ai ko ɗakin kafirai ne kya dokko ƙofa kamin ki shigo balle musulmai”
Uffan bata cewa Hajiya dan tana cikin zafin rai tasan kuma idan har tace zata tsaya maidawa Hajiya magana to dukansu rayuwarsu sai ta ɓace dan Hilal ba ƙyalewa zai yi ba.
“Ɗa zu Adda Rashida ta zo nan ka hana ta shiga ta ga ɗan ta, akan wanenen dalili ko ita ba uwarsa bace? Ba zamu ɗauki tsarin wulaƙancin da kake son mana ba akan shegiyar matar ka, ta fitar da Rashida cikin gidan yanzu kuma tana son ta bi ƴaƴanta ya kashe, idan ba zaka iya wani abu ba mu za mu iya dan ba zamu zuba ido ta kashe mana ƴaƴa ba”
Wani wulaƙantancen kallo Hilal ya watsa mata kana yaja tsaki, sannan ya kai hannu ya kwaɓe wayar wata ƙanwar Rashida dake ɗaukar Rafiq a waya.
“Ku fita ku bani guri ko nasa ayi muku wulaƙanci, idan ita Rashida bata iya ba ke taya zaki iya, banza a banza, ko dan kina ƴar jarida? Ku fitar min daga office yanzu nan”
“Za mu fita ai bamu zo dan zama ba, amman ka jira sakamakon ka, ba za mu ɗauki a wulaƙanta mana ƴar'uwa ba”
Cewar Khady sannan ta duƙa ta ɗauki wayarta, Suka fice. Hajiya ta dafe kai.
“O Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wannan masifa da me ta yi kama? Hilal ka rabu da matar nan ka huta daman masu tsantsar ladabi sun fi komai cuta”
Balki ta taɓe baki.
“Ni wallahi ban zata Kalsoom zata iya aikata haka ba, shiyasa ake cewa baka shedun mutum, mutum mugun ice”
“Hilal ka rabu da matar nan tun wuri kamar abin yayi maka yawa, ko ma shari'ah za su yi da ita suje can su yi amman ba tana gidan ka ba, sannan duk mace data fara da ƴaƴanka wata rana akan ka zata faɗa”
“Idan na rabu da ita kuma.. Da wa zan zauna”
“Sai ka nemi ƴar gidan malamai ka aura, kai ni ma zan nema maka ga mu da su a family masu hankali da natsuwa”
“Amman Hajiya zai zama ina ta aure aure”
“Ai kowa ya ji dalilin ka dole ya ɗaga maka ƙafa, amman ni gasjiya ban baka shawarar zama da matar nan ba”
Agogon hannunsa ya kalla.
“An kira Salla bari naje kar na rasa jan'in”
“Muma ai tashi za mu yi, amman wa xai kwana da shi?”
“Ni zan kwana da shi gida zan koma na canja tufafi sai na dawo”
“A'a ga Balki da Amina ai zasu iya kwana a nan”
“Akwai abubuwan da zan masa idan ya farka, so zai fi kyau na kwana da shi ɗin”
“Allah ya sauwaƙe ya bashi lafiya”
“Amin ya rabb”
Tare suka fito, sai da ya raka su gurin mota sannan ya nufi masallacin asibiti yayi salla isha'i.
Bayan ya fito daga masallaci ya koma office ɗinsa ya kulle office ɗinsa sannan ya nufi ɗakin Rafiq ya duba ya fito ya nufi gurin da aka tanadar likitocin asibitin su yi fakin ɗin motocin su.
Motarsa ya shiga, yayi mata key. Har ya fita harar asibitin be daina jin baya son zuwa gida ba. Be ƙara jin gidan ya fita ransa ba sai da yayi farkin harabar gidan. Ya ɗan daɗe cikin motar sannan ya fito.ya shiga cikin gidan.
Da gudu Ezzah da Ulfah suka zo suka rumgume ahi suna masa sannu da zuwa. Durƙusawa yayi a gurin yana shafa kansu.
“Dady Anty tana ta kuka tun ɗazu tace min Rafiq be da lafiya wai yana asibiti”
Ulfah ta faɗa tana wasa da rigarsa.
Be ce musu komai ba sai kawai ya nuna musu kujera alamar suje su zauna. Ezzah ce ta riga zuwa dan yau tana cikin nishaɗi, ganin Kalsoom na kuka duk yasata jindaɗi kamar wata kishiryarta.
Tashi yayi ya shiga ɗakinsa. Kwantawa yayi saman gadon ya lumshe ido yana sauraren kansa da ke tsarawa. Buɗe idonsa da zai yi ya ga Kalsoom tsaye a kansa hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta, ta canja kama sosai fuskarta ta ɗan zurma idonta kuma ya kumbura har bata gani sosai da shi.
“Ya aka yi?”
Ya tambaya yana tashi zaune.
“Ya jikinsa?”
Maimakon ya amsa mata sai kawai ya miƙe tsaye ya soma cire kayansa har ya ɗaura tawul be ce mata komai ba sai kawai ya shige bathroom. Ta so ta nuna masa takardar sammaci da ɓoye a bayanta wanda Rashida ta aiko mata, amman rashin samun damar haka yasa ta juya ta koma ɗakinta, cikin wani irin baƙiciki da take jin kamar ta mutu a yau ta huta.
Bayan ya fito wanka ya saka wasu tufafin ya ɗauki abinda yasan zai buƙata ya fice daga gidan. Har ya kai gurin mota sai kuma ya dawo yayi ma yaransa sallama tare da shafa kan su ya samu albarka sannan ya fice.
ANTY AMARYA POV.
Ta daɗe kwance a gurin tana jin zujin da zuciyarta take mata ga numfashinta dake ta sama. Daker ta unƙura ta tashi ta ɗauki ruwan da aka kawo ma Yasmin ta sha. Sannan ta samu ɗan saussauci.
Ko da Aisha ta fito har abun ya ɗan kwata mata. Ita ma sam bata jidaɗi labarin da Anty ta faɗa mata na Namra ba, duk da tana ƙarama amman sam be mata daɗi ba, kukan Anty Amarya yasa ita ta fara rera tana kukan tana bawa Anty haƙuri.
Sai kusan la'asar Maryam da sauran ƴan gidan suka dawo, suma duk ba su jidaɗin yadda suka samu Anty ba, dan abinda suka zo dashi na walima sai duk suka kasa a ci.
“Ni daman na yi mamakin hana mutane zuwa gidanta da take wallahi daman nasan ba ban xa ba”
Cewar Maryam tana riƙe da hannun Anty Amarya dan tausasa mata zuciyarta.
Anty ta share hawayen ta
“Zuwa zan yi na zo da ita, gobe goben nan, bana son na mutu na barta a cikin halin damuwa, ita ce yayarku idan bana da ita za zata riƙe ku. Ba ina ƙyalar talauci bane amman wannan rayuwar sam bata dace da Namra ba”
“Amman Abbah zai bari kuwa?”
Cewar Hindatu dan tasan halin Abbah idan yace A'a to a'a ne no matter what.
“Ba zan faɗa masa da ita zan zo ba, sai idan na dawo ya ganta, idan kuma ya ce ba zata zauna masa a gida ba, to zamu bar masa gidansa ni da ita, ban san minene yake bibiyar Namra ba, ina jin tsoron wannan rayuwa nata”
Maryam ta sauke ajiyar zuciya.
“Amman Anty kin san Abbah ba zai bari kije ba”
Anty tayi shiru tana sauraren sanyin ac dake tsara jikinta. Duk wata magana da suka yi a tsakanin su suka yi ta Anty bata sake cewa komai ba, dan jin take zuciyarta ta riƙe har cikin bayanta. Sai dare ta nufi part ɗin Abbah a lokacin ta tabbatar ya gama cin abinci duk da tasan yau ba girkin ta ba ne.
Yana ganinta yasan akwai damuwa a fuskarta, dan ya karanci matarsa sosai, yakan gane nishaɗinta da kuma akasin haka, a duk lokacin daya kalli fuskar sahibarsa.
“Lafiya dai ko? In ce ba ni nayi laifi ba?”
Tun kamin tayi magana yayi mata tambayar ƴana kallon yanayinta, gaba ɗaya hankalinsa ya tattara ya koma gurinta. Ita kuma ta kasa magana saboda Hajiya da ke badroom ɗinsa tana gyara zanen gwadon da bata samu canjawa ba ɗazu saboda fitar da suka yi. Sai da ta gama abinda za tayi ta fita sannan Anty ta zauna dai-dai gaban Abbah tana shirin masa kuka ta soma magana cikin muryar data san shiga ƙwaƙwalta, dan tasan Abbah baya son kukanta, duka kuwa da ita ɗin ba ƙaranar yarinya ba ce amman wani lokacin haka zata sashi gaba tayi ta masa kuka akan abubuwa.
“Gobe da safe ina son naje katsina, sai na dawo da yamma”
“Gurin me? Miya faru?”
“Namra bata da lafiya ina son ganin ta”
Yayi shiru kamar be ji ba. Babu abinda yake tunanin sai maganganun Hajiya Barau data faɗa masa shekaran jiya akan halin da Yasmin ta samu Namra.
“To ki shirya sai direba ya kai ki, amman dai ganin kawai zaki yi, karki ɗauko min ita, dan ba zata kashe aurenta tazo gidana ta zauna ba, ko bana da rai ban lamunta ba”
Anty bata musa masa ba, dan tasan idan ma tace xata tsaya jayayya dashi sai su kwana a nan suna yi abu ɗaya. Amman dai tasan idan har ta dawo da Namra, duk abinda zai faru sai dai ya faru idan ma ya tsaya haƙai akan Namra ba zata zauna masa a gida ba ita zata bar masa gidan wanda ta san ba zai so haka ba.
Tashi tayi ta karɗe jikinta ya fito daga part ɗin xuciyarta da ɗan sanyi barinta da Abbah yayi taje gurin Namra.
Tun cikin daren Anty ta soma shiri, ta kuma kira driver ta faɗa masa sai yaje gidan man Abbah ya cika motar dan ta faɗa masa tun 6 zasu kama hanya dan samun dawowa da wuri.
Duk yadda Maryam ta so binta Anty ƙiyawa tayi dan tasan zasu iya rigima da Asim can, Aisha da Hindatu kuma makaranta.
*WASHE GARI...*
Kamar yadda tace tun da tayi salla asuba ta shirya, sai dai bata ci komai ba dan bata jin cim abinci daman haka take idan zata yi tafiya balle kuma tana cikin rashin daɗin rai.
Har gurin mota suka rakota. Hajiya Barau kam ta window ta tsaya tana leƙenta tana tabe baki zuciyarta cike da gulma kala-kala, ganin Anty amarya bata faɗa mata inda zata ba tasan baya da buƙarta ta san inda zata je, ita kan ta bata tabbacin inda zata ɗin dan Abbah ba lallai ne ya faɗa mata ba, dan ba kasafai yake faɗa ma sirrin wata matar ga wata matar ba.
Tun da suka kama hanya babu abinda Anty taje sai salati da istigifari. Duk bayan awa ɗaya Maryam take kiranta ta tambaye ta ya hanya, Hindatu ma da take makaranta ba abarta a baya ba, ta kan kira ta tambayar.
Hakan suka share awa shida suna tafiya a hanya ba tare da sun tsaya ba. Ba laifi direban yana ɗan gudu dan Anty ce ta buƙaci hakan ta matso ta ganta gurin ƴarta. Ana saura awa ɗaya su isa Katsina motarsu ta fara basu matsala, Anty ta tsorota sosai ganin a hanya suke, sai direban ya riƙa ƙoƙarin kwantar mata da hankali akan cewar zasu isa lafiya kamin ta tsaya in yaso sai su samu wanda zai duba musu ita a can katsina ɗin.
Sun isa Katsina lafiya, sai a mararraba motar ta soma gaba tana baya, hakan yasa direban fakawa gefe ya fito yana duba motar.
Anty ma fitowa tayi tazo ta tsaya gaban motar gurin da direban yake tana duba abinda yake taɓawa tare da tambayar abinda ya samu motar.
Motocin dake kai da kawo babu wacce ta tsaya, sai wata kafirar mota mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ita har ta wuce sai ta dawo kusa da su ta faka.
Buɗe motar Abdool yayi ya fito ganin dattijowa kamar Anty a cikin zafin ranar nan ya hana shi wuce ce, dan daga gani yasan motar ce ta tsaya. Cikin wani irin taku ya ƙaraso gurin, shi ba na sauranta ba ba kuma na yana sanye da kakin soja ba.
“Lafiya me ya samu motar?”
“Wallahi muna tafiya ne ta fara bamu matsala ina jin ko ingin ne”
Matsawa yayi ya duba motar ya buɗe abubuwa ya gani, sai ya koma motarsa ya ɗauko ruwa da baƙin mai ya zuba mata sannan ya maida komai ya gyara shi kamar yadda yake.
“Shiga ka tashi motar mu ga”
Da sauri direban ya shiga ya tashi motar yayi baga yayi baya yaga ta dawo normal sai ya faka ya fito yana godiya.
“Mun gode Sosai”
“Ba komai amman a riƙa kula da irin waɗannan idan za'ayi tafiya mai nisa”
“Inshallah mun gode”
“Allah yayi maka albarka”
Anty Amarya ta faɗa tana ɗan murmushi, dan tasan ko waye Abdool tun da tana ganinsa a tv, sai dai bata tabbatar da shi ɗin ne ba tun da ya tsaya ya taimake su, sai dai kuma kakin dake jikinsa da stars sun nuna haka.
Ɗan rinawa yayi yana murmushi.
“Amin Mama na gode”
Juyawa yayi ya koma motarsa. Suma suka shiga tasu, da hau titi sai da ya ɗaga musu hannu sannan ya cigabansu da mugun gudu.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *55*
*NAMRA POV.*
Yau kan ta ɗan samu sauƙi ba kamar jiya ba. Dan yau har aiki ta samu tayi, ta gyara gidan tas sannan tayi wanke-wanke, sannan ta shiga tayi wanka. Ta shirya cikin baƙar abaya sannan ta fito harabar gidan ta ɗauko murhunta na gawai ta ɗora girkin rana.
Bayan ta ɗora ta tashi ta koma cikin ɗakin ta ɗauko tabarma da filo ta shimfiɗa, dan ta soma jin ciwon kan na taso mata.
Bachine ya soma ɗaukarta, sai gyangyaɗi take, bata son yin bachi ta bar girkinta ya ƙone. Hakan yasa ta tashi ta wanke shimkafa ta zuba ta gyara wutar sai ta koma ta xauna tana kallon gate dan horn ɗin ta take ji ta yi yawa.
Bata jin za ta iya zuwa ta ga mai horn ɗin, duk da tana jin a gidan ake horn amman bata zaton za tayi wani baƙo mai mota, da zai iya zuwa gurinta yanzu.
Kwantawarta tayi tasa ɗan tsinƙe tsintsiya tana gyara akaifarta. Bata ɗago ba har sai da aka turo ƙofar gate ɗin aka shigo. Sannan ta ɗan juyo taga ko waye ne. Ganin Anty yasa ta tashi tsaye da sauri tana mamakin ikon Allah. Mafarki take ko gaske? Anty ce ko aljanarta? Tsaye tayi a gurin kamar an dasata. Idan har da gaske Anty zata yi farinciki ganinta dan tayi marmarinta sai dai kuma bata fatar amAnty taga ganta a halin da take ciki.
Bata gasgata Anty bace har sai da ta ƙaraso inda take ta dafa tana mata kallon mamaki dan duk yadda Yasmin ta faɗa mata sai taga abun yafi haka muni.
“Namra...!”
Rumgume Anty tayi ta fashe da kuka. A maimakon Anty ta rarrashe ta sai kawai ta tureta daga kafaɗarta.
“Wane irin hali ne wannan Namra? Jibe ke, a haka kike zaune kamar baiwa? Namra me yake ƙwaƙwalwarki? Kina rayuwar da ko amafarki ban taɓa tunanin za kiyi ba?”
“Idaba nake Anty, bautar Allah na ke, talauci da arzki duka na Allah. Da ace talakawa Allah yayi mu da sai dai mu hange wasu masu kuɗi suna sha'aninsu, mu muna cikin talauci. Dan kawai ina ƴar mai kuɗi ba shi yake nuna zan dauwama a daular duniya ba, duk wanda yayi arziki dole ne arzikin ya barsa ko kuma shi ya mutu ya bar arzikin, amman ba'a dauwama da duka biyu”
A natse take maganar cikin hikima tana son Anty tayi ma maganarta karatun ta natsu, ƙoƙarin lurar da Anty take kwaɗayin dukiya ba zai sa ta ƙi zaman aure ba. Ajiyar zuciya Anty ta sauke, tabbas ba xata iya canja abinda Allah ya rubuta ga Namra ba, amman tana ganin rashin dacewa a zamantakewar auren ta, wanda abu ne mai wahala da iya ɗauke idonta akan haka, bayan kuma tasan Asim ɗin ba dan Allah yake zaune da ita.
“Namra wannan rayuwar bata kamace ki, ƴar gata ce dubi inda kike zaune, yaushe gidan ya ƙone? Baki faɗa ba? Kina tunanin zurfin ciki zai miki magani ne?”
Ta share hawayenta ta hannun rigarta.
“An daɗe da yin gobarar, ban faɗa ba ne saboda ba lalle bane ku yarda a wacan lokacin”
“Je ki haɗa kayan ki, gida zamu je yanzu, zaman ki a gidan nan ya ƙare, an faɗa min har dukan ki Asim ya ke Namra wai me ke toshe miki ƙwaƙwalwa ne?”
Gabanta ya faɗi, tana jin rashin kyautawa a abinda Anty take ƙoƙarin aikatawa, dan me zatayi tattaki dan kawai ta kashe mata aure?
“Abbah ne yace ki zo da ni?”
“Ki shiga ki ɗauko hijabin ki na ce...!”
Anty ta katsa mata tsawa... Ja da baya Namra ta yi tana hawayen
“Ba zan biki ba Anty, Abbah ya faɗa min kar na kuskura na tunkaro gidansa da sunan saki ko yaji, ya nanata min lokacin da naje gida, ya ce duk na zauna masa a gidan sai dai ya kore mu ni da ke. Ba zan kashe miki aure ba, ba zan ƙara jefa kai na a halaka ba, mutane ba zasu jefe ni da biyu ba, ace na kashe miki aure kuma na bijirewa mahaifina”
Har cikin zuciyarta take faɗin haka, dan ta haƙiƙance a ranta ba zata taɓa biyar Anty ba, ba zata ja mata wani zagin ba, sai ace taje ta kashe mata aure. Bayan kuma tasan Abbah ba zai taɓa yarda ta zauna a gidan sa ba, ta kuma san Anty zata iya rabuwa da Abbah akan ta.
Wani irin kallo Anty take mata na mamaki da rasa abinda zata ce mata.
“Namra ke ba cikakkiyar mutum ba ce, ke rabin mutum ce! Ban san wanda ta haife ki bayan ni ba, da sai nace ke ba ƴata ba ce, ina da sanyin hali amman be kai ka ki ba ke sakarya ce, marar hankali dabba wace bata san ciwon kan ta ba. Na yi tunanin kin yi hankali na ɗauka kin gane inda duniya take a yanzu, ashe ke wawuya ce....”
Cikin zafin rai da ɓacin rai Anty take maganar sautin muryarta na fita ko'ina da ace ba babban gida bane da tuni an yi musu taro. Hawayen takaici.
“Na yi hankali Anty kuma zan zo gareki idan har Allah ya ƙaddaro rabuwa da tda Asin ya bani takardar sallama”
“Tam Allah ya ba ku haƙuri zama”
Ta duƙa ta ɗauki carbinta daya faɗi sannan ta miƙe tsaye ta kalli Namra da kyau da kyau. Sannan ta juya ta soma tafiya jiki ba ƙwari.
Rugawa Namra tayi a guje ta sha gabanta ta rumgume ƙafatunta, tana kuka sosai.
“Dan Allah Anty karki yi fushi da ni, dan Allah ki fahimci ne”
“Ba zan taɓa fushi dake ba Namra, ba zan tdine miki ba, Allah yayi miki albarka, idan kin lalace dole za a ce ƴata ce, idan kin ɗaukaka dole kuma ace ƴata ce, amman ba zan sake wauwayar gidan auren ki da Asim ba ko da kuwa gawarki ce a ciki, kar kuma ki sake roƙo na komai, ba zan baki ba matuƙar ba ki yi hankali ba kisa wannan a zuciyarki...!”
Ta janye ƙafarta ta bar Namra nan tana aikin kuka, ta nufi gate hawaye ya gangaro a idon Anty. Wani irin kuka Namra take, kukan da ita kanta ta manta when last tayi irinsa, ko ba komai tasan ta ɓata ran Anty, tabbas Asim ba mijin aure ba ne, amman ta yi alƙawarin zama da shi har iya rayuwarta dan kawai ta cika umarnin Abbah. Idan har ta bi Anty a yanzu duniya zasu zage ta ita da Anty kuma zata ƙara ɓata ran Abbah.
Tashi tayi taje gurin gate ɗin ta tsaya tana kuka, tana kallon motar Anty har ta suka bar unguwar. Sai ta zube a gurin ta ƙara fashewa da kuka tan mai jin kamar ta falla da gudu ta bi Anty.
Iya hawayen da Anty tayi a gidan Namra ne hawayen tausayin Namra, har ta suka isa gida bata sake wasu hawayen ba, dan yanzu ta fahimci Namra ba abar tausayu bace tun da bata tausayin kanta. A hanya Namra nata kiranta amman ta ƙi ta ɗaga wayar.
Su Maryam tun kamin ta yi musu bayani suka fahimci komai tun daga yanayinta da kuma ganin ba a zo da Namra ba.
Bayan ta huta ta faɗa musu abinda ya faru, duk basu jidaɗi ba, musamman Maryam da tafi so zafin rai, kasa haƙuri tayi har sai da ta kira Namra ta yi mata faɗa kamar wata yayarta.
A ɓangaren nan kam
Haka ta wuni cikin kuka daman aikinta ne shine ya zame mata abokin fira. Sai goman dare Asim ya dawo kamar yadda ya daba yana ganin yanayin Namra ya san ba lafiya ba, amman saboda mugun hali yaƙi ya tambaye ta damuwarta.
Sai ƙoƙare kai mata buƙatarsa yake. Ture masa hannun tayi ta tashi zaune cikin ƙunar zuciya ta ce
“Aikin kenan, Asim ka rako maza duniya, kai wayayye amman wayewar ka bata maka amfani ba, babu ruwanka da damuwa kai dai na gurka kawai ka ci, dare yayi ka kawo min buƙata, shine kawai...!”
Nuna kansa yayi duk da ɗakin babu wani haske sosai.
“Ke ni kika faɗa ma wannan maganar? Wuyanki yayi kauri ko Namra? Kin rai nani saboda bana da naira saboda ni takala ne ko?”
“Idan har talaucin ya dame ka miyasa baka yi ihun arxikin ya zo maka ba? Miyasa idonka ya rufe akan neman abinda za ka mutu ka bari, kai ne baƙon arziki shiyasa kake yawantar faɗarsa”
Tashi yayi ya ƙara motsa kusa da ita da zimmar dukanta, jikinsa har bari yake.
“Ni kike faɗawa wannan maganar Namra? Ni sa'anki ne?”
Mari ya kai mata ta gauce, ta fita waje da sauri. Bata zame ko'ina ba sai inda take girki, wuƙa ta ɗauko ta shigo ɗakin da ita idonta a kafe irin yau ba imani ɗin nan ta nuna sa da ita.
“Karka kuskura kace zaka taɓa ni Asim, zan iya kashe ka Asim, baƙin cikin da yake rai na zan iya juye maka shi a yau, tun da ka shigo gidan nan baka tambaye damuwa na ba, baka tambaye waya mutu waya rayu ba kai dai kawai matsalarka ka sani, saboda kai na ɓata ran mahaifina, saboda kai yau mahaifiyata ta koma gida cikin ɓacin rai, na kira ta bata ɗaga ba Maryam.ta kira ki babu irin cin mutumcin da bata min ba duk a kan ka Asim. Tam ya ƙare yanzu wuta ba zata sake cin ƙara ba, sai dai quta ta ci wuta...!”
A baki take furucin zuciyarta cike da yaƙinin ita ɗin zata iya, shi kansa Asim yaga hka idonta sai dai babu abinda zuciyarsa ta ayyana masa sai aljanu, ganin yake aljanun Namra ne suka taso cikin daren nan. Nan da nan marar ta cika da fitsari, be nuna tsoro a fuska ba, amman a zuci tsoron har yayi masa yawa, ala-ala yake kar aljanun su caka masa wukar, dan shi dai yasan Namra da kanta ba zata iya masa haka ba.
Uffan be ƙara cewa ba, sai kawai ya ɗauki tabarma da filo da abin rufa ya koma waje ya kwanta, dan baya jin zai iya kwana ɗakin karya kasheshi cikin dare.
A wajen ma sai ya koma can nesa da ƙofar ɗakin sannan ya shinfiɗa ya kwanta. Duk bayan minti ɗaya biyu yake farkawa ya tofe kansa da addu'a sannan ya sake komawa. Kamin safiya ta qaye har ya matsu. Yana fita salla asuba, yai fitar gaba ɗaya.
*AMIRA POV*
Tana jin parking ɗin mota, ta ayyana a ranta cewar Abdool. Da sauri ta ƙarasa shafa hodar da take ta ɗauki ɗankwalinta ta yafa saman kai ta biyo sawun kannensa dake masa oyoyo.
Amal ce taje da gudu ta rumgume shi, Ummi da sauran ƙannensa kuma suka tsaya a jikin ƙofar falo suna jiran ya ƙaraso. Hannu Amal ya riƙa suka nufo falon hularsa a hannu yana murmushin data ƙayata kyausa.
Ɗan risinawa ya yi lokacin daya kawo bakin ƙofar falon, ya gasheta da Ummi kamar yadda ya saba. Sai ta amsa masa murmushi tana faɗin.
“Mu duk mun ɗauka jirgi zaka biyo fa”
“Wallahi haka kawai naji ina buƙatar driving da kai na”
“Amman ka biyo haka babu kp ƴan rakiya Abdallah abinda Mai Martaba yayi ta maka magana akai kenan, kana da maƙiya fa ya kamata kana bawa kan ka tsoro mana”
Murmushi yayi ya lanƙama Ummi suka shiga falon tana faɗin.
“Abinda Allah ya bututa babu mahani”
Amira bata jidaɗin yadda ya wuce ta ba, sai yayi kamar be ganta ba. Ba kuma dan be ganta ba ɗin sai dai rashin kular da yake nuna mata, dan shi sam bata burge shi.
Saman kujera ya zauna tare da Mahaifiyarsa yana dariyar yadda take masa faɗan ya take masa na zuwan da yayi ba tare da bodyguards ɗinsa ba.
“Haba ummi bodygrsd zasu tsare ni ko Allah?”
“Ni ba wani wa'azi na ce ka min ba”
Ya ɗaga hannayensa sama yana dariya. Kallonsa kawai Amira take cike da shauƙi, bata zaci yana dariya haka ba.
Ruwan sanyi Amal ta kawo masa tare da kofi, ya sha ruwan sosai ya jiƙa maƙoshinsa. Sannan ya tashi ya fice daga part ɗin ya nufi part ɗinsa. Tuɓewa yai ya ɗaura tawul ya shiga banɗaki yai wanka tare da alwala, sannan ya fito ya shirya cikin ƙananan tufafin daman sune tufafin daya fi so inda a gida yake. Sai da ya feshe jikinsa da turare sannan ya fito. Ya nufi masallacin gidansu yai salla azahar, bayan ya gama ya gaisa da wasu mutanen unguwar tare da sojojin da suke gadin gidan. Be fita da komai a aljihunsa ba shi kuma mutum ne mai alheri baya jindaɗin ya ganka be baka komai ba, sai dai kam akwai zuciya dan baya ɗaukar raini. Tsayar da mutanen yayi ya dawo cikin gida ya ɗauki kuɗi masu ɗan yawa ya miƙawa wani soja yace ya raba masu. Aiko har da waɗanda ba su yi salla a masallacin ba sai sheƙowa suke suna samun nasu rabo.
Sai da ya tabbatar kowa ya samu sannan ya juyo ya dawo cikin gida. Part ɗin Ummi ya nufa dan cin abincinsa na rana.
Duka ƙanensa suna dinning har Ummi suna cin abinci, Amira ma ta maida hankalinta sai cin abincin take kamar bata ga shigowarsa ba, Amal ce kawai ta kawarda kai tana yamutsa fuska kamar mai ƙyanƙyami.
Kujerarsa yaja ya zauna yana naɗe hannun T-shirt ɗinsa yana rabon ido, dan be san wane abinci zai fara ci ba.
“Dude don't..!”
Amal ta faɗa tana yarfar da hannu.
“Why?”
“All these things wannan yarinyar ce ta girka”
Ta faɗa tana nuna Amira. Daga Ummi har Abdool ɗin da kansa be jidaɗin abinda Amal tayi ba. Ɗan murmushi Amira ta yi, irin murmushin na rashin jidaɗi ta tashi daga cin abincin da take ta nufi ɗakin Amal ɗin wanda yanzu ya zame mata kamar ɗakinta a yanzu.
Sai ta ta shige sannan Ummi ta kalli Amal cikin xafin rai tace
“Dan ta girki abinci kike cewa karya ci ita ba mutum bace? Bata taimake ku ba? Bata fiye muku wannan inyamurar da take girka muku abinci ba? Miyasa kika ɗauki rayuwa da zafi ne Amal, ke dai baki rayu da babanki ba, balle na ce shine ya koya miki, wannan sam sam ba ɗabi'ar ƙwarai ba ce, ɗan 'adam ba abun wulaƙamtawa be ne”
Fashewa Amal.tayi da kuka ta tashi da gudu ta shiga ɗakin Meesha. Abdool ya zuba abinci ya soma ci yana faɗin
“Ummi you shouldn't talk to her that way marainiya ce”
“Ai daman kai kake buɗe mata ƙofar yin abinda duk take so, babu dama ayi ama Amal faɗa a gidan nan, duk abinda take yi hundred percent kai kake supporting ɗinta”
“Ummi ba haka bane, Amal itace ƙarama a cikin mu, kuma yarinyar nan ko da ta yashi bata san mahaifinta ba, ya kamata ace tana jin sanyi wani gurin”
Ummi tayi shiru tana cigaba da cin abinci. Tasna abinda Abdool yake faɗa gaskiya ne da acw mahaifin su an nan da ko hararsu Ummi bata isa tayi ba, dan game da yaransa ba shi da kyau babu mai taɓa masa komai kusancinsa da kai, musamman Amal da yake jin ta kamar ransa. Sai dan tana marainiya ba zai bata damar wulaƙanta kowa ba, Ummi bata da wannan halin daman can halin mahaifinsu baya burgeta, Amal ce ta kwashe halin gaba ɗaya, sai kuma Meesha dake ko-in-kula da mutane.
“Amman shi kenan, dan tana marainiya sai ta riƙa irin wannan halin? Dubi ka ga yarinyar nan wai har warin mutane take ji haba wannan iskanci ai har yayi yawa”
Abdool ya yi dariya
“Ƙurciya ne zata daina nan gaba kaɗan”
“Allah yasa”
“Amin”
Yaja tissue ya goge bakinsa, sannan yaja kujerar ta yi baya, ya miƙe tsaye ya nufi ɗakin da Amira take.
Kife ya tarar da ita saman gadon tana kuka. Sai ya zauna a kujerar dake ɗakin yana ƙarema ɗakin kallo kamar baƙonsa.
“Funny you indai akan Amal zaki riƙa kuka zaki ƙarar da hawayen ki ne kawai baki gama kukan ba, the more Amal knowing you are crying for her the more she will do something to insult you, haka rayuwarta take akwai ƙuruciya a cikin ta sosai”
Daga lokacin da kalaman Abdool suka fara shiga kunnenta sai ta ji duka kukanta ya yanke, sautin muryarsa da take ji sai tsigar jikinta ta tashi. Tashi tayi zaune ta share hawayenta, ɗaga kanta da zatayi caraf cikin idanuwansa. Eyeball to eyeball suke kallon juna ita da shi, kowa da irin abunda yake tsaƙawa a zuciyarsa. Ita ta riga kawar da nata idon saboda kwarjinin da yayi mata, sai ta kawarda fuskarta gefe. Tana murmushi a zuci.
“Sorri for what Amal did to you”
“Never mind”
Miƙewa yayi tsaye ya fice ɗaga ɗakin ya nufi ɗakin Meesha inda Amal take. Ita ma lallaɓata yayi har tayi shiru sannan ya fito ya koma part ɗinsa ya canja kaya ya nufi gurin Mai Martaba.
Ba shi ya dawo ba sai da dare ya raba, daman duk yaje gurin Mai Martaba ko da rana ne sai ya daɗe balle ya je late. A falo ya sami Ummi Amal na saman ƙafafunta tana bachi, murmushi yayi ya zauna kusa da su yana kallon Amal ɗin.
“Har kun shirya”
“Ta ya za'ayi uwa da ƴa, ita ta kawo kanta tace min ta daina”
“Hmmm Amal kenan wannan ɗabi'ace kawai ta ɗan adam, amman idan kin lura har ƴan'uwanta bata bari ba”
“Jiya ma haka suka yai ita da Haleema akan Amirar nan”
“Ai tana gama wannan makararar ƙasar waje zan kai ta tayi karatu a can a huta”
“Ta dai ƙara lalacewa”
Dariya yayi ya miƙe tsaye.
“Ummi good night”
“Aha night, Abdallah yaushe zaka koma?”
“Jibi, akwai aiki a gaban mu abuja”
“Ai kai Allah be raba ka da aiki ba, ni dai kamin ka koma ina son kaje gidan nan na Haleema ka duba mana shi, yadda gyaran zai kasance sai ka kira yaron nan Isma'il ka faɗa masa, dan kasan gidan marayune ƙara a gyara idan ma wasu ƴan hayar za a zuba sai”
“Okay zaje gobe inshallah dan gobe babu inda zan je, a ina ne gidan ya ke? Tun da akayi gobarar nan ma ban je na duba shi ba”
“Yana nan Nasarawa na can wajen gidan action kuɗi ƙasa, kasan irin abubuwan nan sai maza, ni mace wano abu sai dai na ɗaga ƙafa”
“Inshallah gobe zanje”
“Allah ya kai mu”
“Sai da safe”
Yana hamma ya fice daga part ɗin dan duk ya gaji sosai.
*HILAL POV*
Lokacin daya isa asibitin be wuce ɗakin da Rafiq yake ba sai da ya biya ya karɓo hoton da akayi ma Rafiq ɗazun. Sai dai ba iya ya buɗe hoton ba har ya koma office saboda fargaba, sai yanzu ya gane irin abunda majinya suke ji idan wani nasu aka ce yana da wani ciwon ko kuma za ayi masa aiki.
Zamansa kenan a office, sai ga Alhaji Bashir ya shigo cikin mayan tufafin na shadda, tun kamin Hilal yayi masa uwarnin zama ya zauna yana nuna alhininsa akan abinda ya faru.
“Ɗazu nake jin labari babu daɗi ban samu na shigo ba sai yanzu”
Ya faɗa yana miƙawa Hilal hannu su gaisa. Hilal ya maiyarda Hoton gefe ya aje yana sosa kansa yace
“Ƙaddarori ne”
“Wallahi shiyasa kaga bana son ƙara auren nan dan rigima ce kawai ko wacce da kalar matsalar da take zuwa da ita, yanzu miye abin na sawa yaro guba”
“Babu tabbacin ita tasa Bashir, amman dai ita kaɗai ce a gidan”
“To ai shi ya nuna ita ɗin ce, kuma kasan fa ita ta fitar da Rashida a gidan yanzu kuma tana son ganin bayan ƴaƴanta, gaskiya abun be yi daɗi ba, ai ota Rashida tace ba zata ƙyale ba, dan Asma'u ta ce har ta aika mata sammaci ko? Amman dai ban jidaɗi ba gaskiya”
Hilal ya jingina da kujerarsa yana lilo.
“Ni ne na saki Rashida da kaina san ganin damana, maganar kotu kuma taje duk inda zata je ta kai Kalsoom i will surely depend her”
Alh. Bashir ya masa kallon mamaki.
“Doc kasan abinda kake faɗa kuwa? Ɗan ka ne fa ɗan ka ta nemi kashewa”
“Kana da hujjar ita ɗin ce ta kashe shi? Amanarta na karɓo a gurin iyayenta yanzu haka tana ƙarƙashin kulawa ta ne, dole na yi abunda zan kare ta”
“Kana nufin za ka ci gaba da zama da ita kenan?”
“What do you expect?”
Ya ɗaga kafaɗunsa.
“Nothing, ya mai jiki”
“Da sauƙi bachi ya ke”
“Okay Allah ya ƙara lafiya, ni zam koma da safe zan zo na duba shi”
Hilal ya miƙa masa hannu suka sake gaisawa.
“Na gode sosai”
Wani kallon Alh Bashir yayi masa, yana mamakin yadda Hilal ya sauya masa kamar ba shi, duk irin tare da suke a can baya yana aure Kalsoom duk ya watsar ta ɗauke masa hankali. Lallai yanzu ya yarda da maganar da ake cewa magani tayi masa, tun da har Hilal ya furta zai tsaya mata, bayan kuma ɗansa ne tayi ma wannan karen aiki.
Bayan Alh Bashir ya wuce Hilal ya koma saman kujear ya zauna, yana tunanin maganar sammacin da Alh Bashir yace Rashida ta aika Kalsoom. Duk waɗancan maganganun yayi ne kawai dan ya nuna kamar ya san abinda yake faruwa bayan kuma besan komai, yayi hakan ne dan bayan son ayi Alh Bashir yai insulting ɗin matarsa. Saboda ya tsani haka.
Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin yadda zai ɓullowa lamarin. Sai kuma ya kai hannu ya ɗauki hoton ya buɗe yana dubawa. Abinda ya gani ya tayar masa da hankali, da sauri ya tashi yana ƙara dubawa dan tantance abinda yake ganin ɗin. Da sauri ya bar Office ɗin ya nufi inda zai laƙa hotunan su fito a majigi...
*RASHIDA POV.*
Tana sauke wayar ta ƙara ɓata fuska, zuciyarta ta sosu matuƙa, akan abinda Alh. Bashir ya gama faɗa mata, na cewar Hilal zai tsaya ma Kalsoom, a tunaninta shi da kansa zai saka ta kotu yadda tasan yana jin da ƴaƴansa.
Hawaye suka zubo mata sai tasa hannu ta share. Hankalin ƴan'uwa sai duk ya dawo kanta, daman tun ɗazu maganar da suke kenan har da wata ƙawarta wacce suka yi makaranta a tare.
“Ke mai ya faru?”
Khady ta tambaya tana dafa ta.
“Wani abokinsa ne ya kira ni yanzu yana faɗa min wai Hilal yace zai tsayawa Kalsoom”
Ummu Faisak ta daki ƙirji.
“Da gaske? Lallai wannan Kalsoom ɗin ta wanke ta bashi ya sanyen, kan uban nan ayi ma ɗanka abu amman kasa yin komai har kace zaka tsaya mata”
Dukansu jinjina lamarin suke. Zainab ta kada baki tace
“Wannan abun har ƴan Human Rights sai mun saka, ai idan ya san wata be san wata ba, ƙaramin yaro zaka bari a wulaƙanta yama baki ɗan kawai tun da bayan son zuri'arki”
Ummu ta jinjina kai.
“Hmmm Ai wallahi sai na masa rashin mutucin, dan har a tv sai na nuna su, ai daga ganin wannan abin kinsan Hilal ba cikin hankalinsa yake ba. Kuma wallahi tallahi matuƙar ina numfashi sai Kalsoom.ta bar gidan nan, ba ko mallaka ne aikinta wallahi ko a gabanta bokanci ya yake saƙa sai na nuna mata shayi ruwa ne, ai ko baba da babansa”
Rashida tayi saurin rufe mata baki 5ana kuka.
“Dan Allah ki ƙyaleta, ni dai bana iya, ita ta sani can ita da Allah”
“Ai ban ci ki iya ba bada kuɗin ki zan yi ba, amman wallahi tun da ta taɓa ki sai na taɓa ta”
Wani yatsine yake tana tsine ɗankwali irin ita ga ga tantsiriya ɗin nan. Maimunatu ta girgiza kai
“Daman kin yi sake tun farko Rashida Namiji kamar Hilal kinsan duk wace ta shiga gidansa kan ba fita, ni da nice ke Wallahi da wannan abokin nasa zan aura, in yaso ya mutu....”
Ta murguɗa baki. Fashewa Rashida tayi tda kuka tana narke musu kamar wata ta ƙwarai, su kuma sai tausayinsa suke suna bata haƙuri....
INA JINDAƊIN COMMENTS NA KU. THANKS........🙏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *56*
Idonsa ya cika da hawaye, jikinsa ya mutu sosai har yana ƙoƙarin zamewa ya faɗi kamar ba Namiji ba.
Hannunya kai ya taɓa hancinsa ya lumshe, tana girgiza kai. Abinda yake bashi mamakin results a yanzu ya nuna ba guba bace gas ya nuna kuma har yayi effecting ɗin ƙwaƙwalwar Rafiq, that's mean zai zama wani iri kenan. Wanda abu ne mai wahala ya koma dai-dai, ko da kuwa an ɗora shi akan ganine.
Ya daɗe idonsa a lumshe, _Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un_ Shine abinda yake ta maimatawa a zuciyarsa. Daker ya buɗe idon ya ƙarasa ya ciro hoton ya bar ɗakin yana mai jin kansa kamar marar lafiya.
Be shiga office ɗinsa ba sai kawai ya nufi ɗakin da Rafiq yake kansa na mugun sarawa. Tsaye yai a bakin ƙofa yana kallon Rafiq cike da tausayin Rafiq, ya daɗe jikin ƙofar kamar mai tsoron ƙarasawa. Juyawa yayi ya koma office ɗinsa, ya zauna kaman kujera ya dafe kansa still takardun na riƙe a hannunsa. Babu abunda ya faɗo masa a rai sai ya sake ɗaukar wani hoton ya gani, wata ƙila wannan ƙarya ya nuna masa...
Ɗaga kai yayi ya sake kallon hotunan, yana sauke ajiyar zuciya. Ya ɗauki mintuna talatin yana kallon hotunan sannan ya buɗe wani gurin ya saka su ya ɗauki abubuwan daya shigo dasu office ɗin ya fito, da kansa ya kulle office ɗin sannan ya nufi ɗakin da Rafiq yake. Har lokacin bachi yake abunsa, be farka ba.
Wani ɗan ƙaramin tebur Hilal ya nufa ya ɗora kayan a kai sannan ya ƙarasa gurin da Rafiq yake yaja kujera ya zauna, ya riƙe hannunsa yana hafawa, wani irin tausayin Rafiq ne ya ke shiga zuciyarsa.
Haka ya zauna ya tsare Rafiq da ido yana jin kamar yayi masa kuka, ko da kuskure bachi be doshi idonsa ba.lokaci lokaci yake sauke ajiyar zuciya kana ya haɗe yawu. Rafiq be farka ba sai kusan uku da rabi na dare. Murje-murje ya fara yana kiran ruwa kamin ya buɗe ido. Da sauri Hilal ya tashi ya buɗe jakar da ya shigo da ita ya haɗa masa tea ya ta sheshi zaune ya soma bashi tea ɗin, yana masa sannu kamar wani babba.
Yana gama shan tea ɗin ya langwaɓarda kansa jikin Hilal bakinsa yai gefe kamar zai talalarda yawu.
“Rafiq”
Hilal ya faɗa yana girgiza sa dan zuciyarsa ta katse gaba ɗaya. Ɗagowa Rafiq yayi kaɗan ya kalli Daddynsa sai ya maida kai gurin ƙofa yana kallo kamar mai jiran shigowar wani.
Can kuma ya ɗaga kai yana kallon ɗakin, kamin ya sake kallon Daddynsa.
Rumgumesa Hilal yayi yana hawaye. Daga bisani ya ɗauko wasu magunguna ya bashi, sannan ya maida shi a ƙirjinsa ya kwantar. Haka suka kwana, Rafiq na kwance a ƙirjinsa, Hilal kuma be rumtsa ba, a kan idonsa aka kira salla asuba. A hankali ya kwantar da Rafiq yai alwala a toilet ɗin ɗakin ya nufi masallacin asibitin.
Ya daɗe yana addu'a bayan yai salla, a nan masallacin ma sai da ya gaisa da wasu da suka sanshi har suna masa ya jikinsa ɗansa.
Sai da ya koma ɗakin ya ganshi sannan ya fito harabar Asibitin yana amsa wayar Hajiya dake tambayarsa ya jikinsa. Be faɗa mata a results ɗin da hoton ya bada ba, dan ba labari bane mai daɗin ji.
Ko da ya isa gida 6:30am, dan garin be ƙarasa wayewa ba a lokacin. A mota ya zauna har 30 ɗin ta ƙarasa sannan ya buɗe ya shigo nufi ƙofar shiga gidan. A kulle ya jita hakan yasa ya kai hannu ya ƙwanƙwasa, sai ya kawar da fuskarsa. Bayan kamar minti biyu zuwa uku Kalsoom ta buɗe ƙofar.
“Sannu da zuwa”
Ta faɗa cikin sanyayayyiyar murya. Be amsa ba be kuma kalleta ba sai kawai ya raɓa gefenta ta shiga cikin falon.
Kai tsaye ɗakin su Ulfah ya nufa, shiri ya tarar suna yi na makarantar boko.Dukansu ya shafa kansu yana masa good morning ɗin da suke masa, sannan yaja su jikinsa ya rumgume.
“Gobe za ku koma gurin Hajiya da zama, a can za ku zauna har na gama gyara wannan gidan”
Ezzah ta daka tsalle, tana murna, Ulfah ma Murna ta yi, dan suna son zuwan gidan Hajiya ko dan su yi wasa da ruwaz ga gidan akwai yara da yawa sa'aninsu.
“Daddy har da Anty?”
Ulfah ta tambaya cikin zumuɗi. Shiru Hilal yayi kamin ya amsa mata.
“A'a Anty a nan zata zauna”
Bata wani damu ba dan tana son gidan Hajiya, sai dai ta san zatayi missing Anty kan sosai, a ranta take auna a weekend zata zo ta ganta.Bayan kamar minti biyar ya miƙe tsaye ya nufi ɗakinsa. Yana tura ƙofar ɗakin yana Kalsoom zaune saman gadonsa tana hawaye.
Be kulata ba ya nufi wardrobe ya buɗe yana cire wasu tufafin. Da kallo ta bishi har ya gama cire kayan sannan ta soma magana cikin muryar tausayi.
“Baka buƙatar canjawa yaran ka gida Hilal, ni kake buƙatar canjaw! Ni kaina ban cancanci zama da ƴaƴan da mahaifinsu be yarda da ni ba, ko kaɗan ɓan ga laifin ka ba akan abinda ka aikata, ko ni kwatankwacin haka zan aikata”
Sauka tayi daga saman gadon ta durƙusa ƙasa ta haɗe hannayenta alamar roƙo.
“Ma gafarta min akan abunda na yi maka Hilal, ba zan sake hararar yaran ka ba balle na cutar da su”
Juyowa yai ya kalleta.
“Kin Aikata kenan?”
Kai ta ɗaga alamar eh.
“Na aikata kuma ina neman ka yafe min, dan dajarar iyayenka ka sake ni a yau, irin sakin da aure ba zai sake shiga tsakanin mu ba, irin sakin da ko na so na yi tunanin zuciya zata hanani, irin sakin da zan manta da wanzuwarka a doron ƙasa, irin sakin da zai sa na cire ka a zuciya.
Ina roƙon ka Hilal karka horar da ni da irin horon da zan cutu, karka saka zuciyata cikin ramen da ba zata iya fita ba”
Tun da take maganar hawaye take, irin hawayen nan dake hana sautin kuka fita. Miƙewa tayi tsaye ta ɗauko takarda da biro dake gefen gadon ta zo gabansa ta aje masa gabansa, ta miƙe tsaye ta bar ɗakin.
Notebook ɗin ya tsurawa ido yana nazarin kalamanta.
Wanka yai ya shirya cikin wasu tufafin ya feshe jikinsa da turare, sannan ya ƙaraso gurin gadon ya ɗauki takardar yayi mata rubutu, ya naɗe ya ɗauki kayansa ya fito.
Ɗakin Kalsoom ya shiga, sai ya same ta zaune ƙasan gado tana rusar kuka. Tsayawa yai cak yana sauraren kuka nata dake shiga har cikin zuciyarsa, be san dalili ba duk da abinda Kalsoom ta aikata masa still yana son a zuciyarsa, har yanzu natsuwarta da yadda take gudanar da al'amuranta burgeshi ya ke. Sai da ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ƙarasa cikin ɗakin ya miƙa mata takardar.Idonsa na shiga cikin nata gabansa yayi mugun faɗuwa, ta rame sosai kamar ba ita ba, ga wani ja da idonta yai, kamar ta saka garwashi a ciki, a take tausayinta ya rufe shi. Ita kuma ta sakarwar takardar ido sai kallo take tana tsoron karɓa, ta haɗe yawu ya fi a ƙirga kamin ta miƙa hannunta dake ɓari ta karɓi takardar.
“Na gode Allah ya haɗa ka da mata ta gari..”
Cikin sarƙewar murya ta faɗa bayan ta karɓi takardar. Har ya buɗe baki yai magana, sai kuma ya fasa ya juya ya fice.
A jikim mota ya tarar da yaransa suna jiransa. Yana shiga suma suka shiga, har suka isa scul ɗin Ulfah bata daina tambayarsa ina Rafiq ba, sai dai be amsa mata ba dan be san me zai ce mata ba, Hilal irin mutanen nan da idan matsala ta shiga tsakaninsa da iyalansa baya son kowa ya ji, har yaransa, dan aganinsa ba muhallinsu ba ne.
Ƴan canji ya zaro a aljihunsa ya miƙa musu, sannan ya kama hanyar asibiti yana neman number Rashida daya saka a blacklist ya kira ta. Ta daɗe tana ringing kamin ta ɗauka, dan sai da ta tabbatar ta tantance cewar number Hilal ɗin ce sannan tai picking.
“Ki janye maganar kotu nan”
Shine abinda ya fara faɗa mata, a tunaninta zai bata haƙuri ne ko kuma yai mata wata maganar ta daban.
“Ba zan janye ba, ba za a dake ni a hana ni kuka ba, ba zaka cutar da ɗana kuma ni ka hanani ɗaukar mataki ba”
“Ɗan ki ko ɗa na? Bakin ki yana kurkure gurin faɗar kalmar nan”
“Ai da ɗan ka ne da baka ce za ka goyi bayan ta ba, wai har ka kace zaka tsaya mata bayan ita ce take ƙoƙarin aika ɗan ka lahira, dan kawai ta mallake ka”
Ya taka burki.
“Kar ki soma faɗa min maganar banza, ni ba wawa ba ne irin ki, kuma na faɗa miki ki janye zancen kotunan ko kuma na faɗawa duniya dalilin sakin ki da na yi kuma try me ki gani”
Be tsaya jiran abinda zata ce ba, ya kashe wayar. Sai ya kira wayar Alh Bashir sai da yai masa two missing calls sannan ya ɗaga, Hilal be tsaya jiran komai ya ce
“Idan kana son shiga cikin maneman Rashida ka shiga kawai ba sai ka riƙa ɗaukar maganar da muka yi ba ka kai mata, wannan ba girman ka ba ne”
Ya katse wayar ya jefar a front seat yana wani huci da bugu sitarin motar.
*RASHIDA POV*
Mamaki ya isheta, yadda Hilal ya juye ya zama maƙiyinta, mutumen da ko a mafarki aka ce zai mata zata musa, balle kuma a fili.
“Lallai na yi sake da har na bar ka ka auri wata ban mallake ka a lokacin ba, Kalsoom ki biya bokan ki haƙiƙa ya iya aiki. Zan janye maganar kotu, amman kuma dukan ku sai kun ƙwamace kiɗa da karatu...! Wallahi wasan yanzu aka fara, Hilal sai ka zo da kan ka ka nemi yafiya ta, Wallahi zan aikata ko minene matuƙar buƙatana zata biya... Sai na banbance muku aya da tsakkuwa”
Tashi tai tsaye ta cigaba da shirin zuwa office da take zuciyarta a dake irin na masara imani ɗin nan, dan a yanzu babu imani a kusa da inda take ma balle ace kusa da ita.
Sai da ta shirya tsaf sannan ta ɗauki jakarta da keys ɗin mota ta fito falo, already tai breakfast tun 6:30. Ɓangaren Mahaifinta ta nufa dan har Momy tana can. Cikin ladabi ta shiga ta samu guri ta xauna ta gashe su sannan ta ɗora da..
“Daddy zan janye maganar kotu nan, mu barta kawai da Allah”
“Wallahi kin yi tunani Rashida, nima abunda naga yafi kenan, indai cin amana ne baya taɓa ɗaurewa, Allah zai nuna mata sakamakonta tun duniya”
Momy ta faɗa cike da jindaɗin hukumcin da Rashida ta yanke. Dady yaja dogon tsaki.
“Ku kan Allah ya waddaran zuciyarku komai sai a ace a bari ga Allah? Ai musulucin ya ce idan an yi maka cuta ka rama gwargwadon abunda aka yi maka idan ba zaka iya yafewa ba, sannan irin wannan abun bw kamata ace a ba ga Allah ba, sai fa anje lahira kenan fa? Haba ai ƙara ayi mata tun duniya ta kunyata dan Wallahi idan yai wasa har shi sai nasa an kulle”
“A'a Alhaji ya kake magana kamar ba mai tunani ba? Haka sam be dace ba, hukuncin data yanke shine dai-dai”
Ya kawarda fuskarsa daga ta Momy ya kalli Rashida dan a tunaninsa ko Momy ce tayi mata wannan shawarar.
“Ke kina son abi miki kadin yaron ki?”
Ta girgiza kai.
“A'a Abbah na janye, na barta da Allah”
“Akan me?”
“Kawai haka naga ya fi”
“To ni zan bi kadin jika na (grandson) idan ku baku san abunda ake kira da humanity ba, ni na sani... Tashi kije office Allah ya kiyaye hanya”
Ba zata iya musawa Dady ba kar ya zargi wani abu, sai dai zuciyarta bata so haka ba, dan babu banbanci mahaifinta ne yasa ba ita ba. Tasan Hilal zai iya cewa wani sabon salo ne ta mayardar shari'ar gurin Mahaifinta.
A hanyar ta zuwa office ta kira Mom Shuraim, bayan sun gaisa take faɗa mata idan ta tashi daga aiki zata biyo ta gidanta, akwai magana mai muhimmanci da zata yi da ita.har da narke murya tana faɗin wai tana cikin matsala, amman dai sai tazo zata ji komai.
*ABDOOL POV*
Sai ten ya tashi bachi, dan yana yin sallah azuba ya koma bachin gajiya, farkawar da yayi ma a yanzu ba dan ya gaji da bachi bane, sai dan son zuwa gurin da Ummi tayi masa magana ne jiya. Be fito part ɗinsa ba sai da yayi wanka bugaggar shadda mai tsana blue color, ta fito da shi sosai kasancewar fari sol, ga ɓaƙar hulal da ya ɗora akansa kamar wani sabon balarabe,baƙaƙen takalmi ya saka sannan ya feshe jikinsa da turare, ya fito daga part ɗinsa ya nufo part ɗin Ummi shaddar har amsawa take a jikinsa, ga wani maiƙo da take kamar an zuba mata mai.
Ita kanta Ummi sai da tayi murmushi ganin yadda ɗan nata ya fito mashallah kamar ta cinye abunta.
“Ina fatar ka yi addu'ah”
“Addu'ah me?”
“Idan mutum yayi kwaliya ya dubu kansa a madubi yana kyau yace Mashallahu laƙuwwati illa billah, to ko wani yayi maka baki (kanbun baka) Ba zai kama ka ba, idan ma zaka ita ka riƙa karantawa da safe kullum sau uku”
Dariya yayi yana kallon cucumber da Ummi take yankewa ya ɗauki ɗaya ya ci.
“To ni da ba mace ba miye na wani kanbu zai kama ni, amman dai zan riƙa yi”
“It better”
Ya faɗa tana cigaba da yanka cucumber take. Shi kuma ya zauna kusa da ita yana tambayarta yaje yanzu ko sai anjima.
Ƙamshim turarensa ne ya isarwa da Amira saƙon isowarsa a falon. Ras! ras!! ras!!! Ga banta ya faɗi kamar yadda ya basa mata a duk lokacin da ta ji ƙamshin turarensa. Da sauri ta walƙato ta sauko daga saman gadon da take ta nufo falon idonta cike da maitar ganin Abdool kamar bata taɓa ganinsa ba.
Cikin wata irin siga take tafiya, takalmin dake ƙafarta plate ne amman hakan be hana su amsa amon gurin ba saboda yadda take buga da tiles ɗin gurin. Ummi ce kawai ta ɗago ta kalleta wanda kuma ita bata so haka ba. Abdool kam ƙin ɗagowa yayi dan sarai zuciyarsa ta raya masa Amira ce, dan yasan by this time duka ƙanensa suna makaranta.
“Ina kwana”
Ta gaishe shi cikin ladabi har tana son risina masa.
“Lafiya”
A kaikaice ya amsa, yana mai miƙewa tsaye. Wanda hakan be ma Ummi dadi ba,sai kawai ta kada baki ta ce.
“Amira shiga ciki ki ɗauko mayafin ki ki rana yayanki unguwa”
Ta fasa zaman da zata yi ta miƙe ta nufi ɗakin data fito. Sai da ta shige sannan Abdool.ya kalli Ummi yana ware hannayensa ya ce
“Haba Sweet Mom ya za ki min haka? Kin san fa ni Allah be haɗa jinina da mata ba, kuma it so annoying naje da ita unguwa”
Wani Kallo Ummi ta masa.
“Abdool... Karka soma halin Amal, tun da yarinyar nan ta zo kullum tana ciki gida bata fita ita ma ai ƙara ta ga gari ko?”
Be ƙara cewa komai ba ganin Amira ta fito, sai kawai ya jiya ya nufi kowa yana wani shan ƙamshi.
Ko da ta isa har ya tashi motar ita kawao yake jira su wuce. Tana shiga ya fisgi motar kamar baya son ransa har sai da Amira ta tsorata.
Bata ce masa ba, shi ma be ce mata ba haka suka yi ta tafiya har suka isa nasarawa. A bakin gate ɗin gidan yayi parking ya fito yana ƙarewa gidan kallom ganin yadda ya kone.
Yana rufe gambun motar Amira ta buɗe ta fito, sai ya kalleta ya ce
“Ba daɗewa zan yi ba, kina iya zama a cikin kamin na dawo”
Ba musu ta koma cikin motar ta zauna, zuciyarta cike da tunani kala-kala.
Baya tunanin akwai mutane a gidan dan Ummi bata faɗa masa ba, hakan yasa be yi sallama ba ya tura kofar gate ɗin kawai ya shiga ciki. Gaban gidan ya fara dubawa kamin ya zagaya baya, tana nan ya hango mace tana girki a BQ. Hannayensa yasa aljihu ya nufi bq ɗin yana sallamar da kusan shi kaɗai ne zai iya jinta, sai kuma wanda yaga bakinsa ya motsa.
Namra na ganin mutum tayi saurin komawa ciki ta ɗauko hijabinta ta saka sannan ta fito. Ko da ta fito har ya ƙaraso bq ɗin yana ƙare ma bq ɗin kallo dan ita bata yi komai ba.
“Haba Malam waye kai zaka shigo babu sallama”
Dago da dubansa yayi gurin mai maganar. Ganin Namra yasa numfashinsa hijira daga jikinsa ma ɗan wasu daƙiƙu, sannan ya dawo. Be ɗauke idonsa daga gareta ba be kuma kyafta ba, haka ya ƙafe da ido kamar wani hoto. Nan da nan zuciyarsa ta soma rabawa jijiyoyin jikinsa jini da ƙarfi.
Rassss rassss rassss gabansa yake faɗuwa, sai dai kuma ba irin wacan faɗuwar ba, ta tsoro ko fargaba, faɗuwar gaba ne da shi kansa ba zai iya fassara na minene ba.
Ita sai yanzu ta gane ko wanene shi, daman tun ɗazu ta ga ganin kamar fuskar sani, mutume daya bita asibiti. Ƙamshin turaresan ya haddasa mata ciwon kan da bata yi zato ba, daman tun jiya bata cikin daɗin rai.
“Subhanallah malam wannan kallo ya haramta a musulumci”
Daɗin sautinsa yasa shi lumshe ido yana murmushi.
‘A'uzubillahi minal sheidanin rajin’
Ya furta a zuciyarsa yana ƙoƙarin da abunda sheiɗan yake son masa, sannan ya buɗe ido ya haɗe fuska kamar be taba dariya ba.
“Su waye ku?”
“Mu ne waɗanda suka kama hanyar wannan gidan”
Ta amsa masa a gautse.
“Bq kuka kama ko Main house”
“Main house muna ciki aka yi gobara sai muka dawo nan da zama”
“Ina mijin ki?”
“Baya nan ya tafi kasuwa”
“To idan ya zo ki ce an baku one week ku tashi za ayi gyaran gidan”
Gabanta yayi mummunan faɗuwa.
“Innalillahi wa'inna ilaihi dan Allah ku gyara babban gidan sai ku bar mana BQ ɗin wallahi ba mu da gurin zuwa idan muka bar nan, dan Allah ku taimaka mana”
Ta haɗe hannayenta idonta na son cika da ƙwalla.
“Da yaushe ake tarar da mijin ki?”
“Da safe ko kuma da dare guraren goma”
“Okay zan zo na yi magana da shi gobe”
“Allah ya kai mu na gode”
Be sake cewa wani abu ba, ya juyo hannayensa zube a aljihu ya fito gidan. Har lokacin Amira na cikin mota zaune tana jiransa, yana shiga motar yayi mata key suka juya. Wannan karon ita ce ta ke ɗan jansa da fira shi kuma jikinsa duk ya mutu baya ma iya amsa mata. yawancin tambayarta akan gidan ne da kuma unguwar, sai kuma yaba garin Katsina da take. Shi dai har suka isa gida sai dai ya ɗaga mata kai kawai.
Ta rigashi fita daga motar, dan yau ranta fes yake ta ta fita tare da sahibinta. Bata tsaya a falo ba sai kawai ya wuce ɗakinta tana ƙoƙarin ɓoye nishaɗinta. Shi kuma ya zauna a falo, kusa da Ummi da take zaune a inda ya barta ɗazu, sai dai wannan karon ita da Shukura ne kuma carrots take gyarawa.
“Har kun dawo?”
“Yeah ai ba wani nisa”
“Kaga gidan ko?”
“Eh duk ya lalace idan aka ce za a gyara shi sai anci kuɗi kam ”
“ Ai dole a gyara shi tun da gidan marainiya ce, a ciro kuɗinta ayi mata gyaran, daman kasan Amal bata da daɗi ta matsa min tuni kamar ni ce na ƙone gidan.Yanzu sai ci nawa idan za a gyara shi?”
“A lot, nawa kika siya mata shi?”
“Ba da kai aka yi cinikin ba, da Alhaji Ƙasimu da Mansur”
“Kai ai bana iya tunawa kin san abu da yawa”
“Nine million aka siye shi”
“Na siya 15 million”
Ummi tayi saurin dubansa.
“Joking abii?”
“I'm serious wallahi na siya”
“Ba zamu siyar ba”
“Saboda me?”
“Muka sani ko zinari aka gani a gidan zaka mana wayo”
Ta faɗa tana tashi ta nufi kitchen, dan ga dukan alamu yai da kanta zata yi girki. Dariya Abdool yayi ya cire hular kansa ya jingina da kujera yana faɗin
“Indai Amal ce ai abu mai sauƙi ne”
Lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya. Babu wacce yake gani sai Namra, da sauri ya buɗe ido ya tashi ta nufi Gardem.
FIVE READ MORE.....🙌🏻
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *57*
Bata taɓa sanin haka jikin da zuciya suke ba idan wani abu marar daɗi ya faru da mutum sai yau. Duk tashin hankalin da ta shiga lokacin da Rafiq ya kamu da ciwo be kai wanda take ciki ba yanzu.
Wannan karon kuka ma yayi ƙaura daga idonta duniyarta sai juya mata take. Gani take kamar mafarki take ba da gaske ba ne Hilal ya miƙa mata wannan takardar.
Miƙewa tayi tsaye sai gata ta dawo xaune saboda rashin ƙarfin jiki, ga wani sanyi da take jin ƙafafunta sun mata.
Wani abu taji yayi mata tsaye a zuciya, hango kanta take a bazarawa, irin rayuwar da tayi ta budurci kuma yanzu ace aurenta ya mutu bayan bata daɗe gidan mijin ba. Takardar ta ƙurawa ido tana auna yadda Mominta zata ji.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shi tai ta maimatawa sannan ta samu ƙarfin jiki, har ta unƙura ta tashi. Durowarta ta buɗe ta ɗauki canjin da yake ciki da Atm ta saka a jikarta tare da takardar ta saka hijabin ta fito falo. Saman kujera ta zauna tana maida numfashi kamar wanda tayi gudun fanfalaƙi. Hannu ta kai ta rufe bakinta saboda kukan daya zo mata gadan-gadan.
Sai dai hakan be hana hawayenta zuba ba, ashe da gaske hawaye suna da zafi, sai a yau ta tabbatar dan yau ta ji hawayenta kamar ruwan zafi.
“Me yasa zan yi kuka akan abunda ba zai sauyu ba? Miyasa zan kuka akan mutumen daya zaɓi rabuwa da ni? Anya Hilal ya cancanci hawaye na?”
Sune tambayoyin da tayi ma kanta a fili, sai dai har ta tashi ta kai bakin ƙofar falon bata samu amsarsu ba. Kamin ta ƙarasa gate ta gyara fuskarta, ta goge idonta da Hijabin gudun kar wani ya gani ya zargi wani abu.
Sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu Napep, sai da ta shiga sannan ta faɗa masa inda zai kai ta. Har suka isa estate ɗin su idanuwanta basu daina cika da ƙwallah ba.
Tana biyan Mai Napep ɗin ta shiga gida hawaye na bin fuskarta. Bata samu kowa a falon ba, daman by this time ba zata samu kowa a gidan b Sai Momynta. A saman kujera ta zauna ta haɗe kai da gwuiwa tana kuka. Sautin kukanta ne tashi daga bachi da take ta fito da sauri falo. Ganin Kalsoom ya tashi hankalinta, tasan da maganar kotu da Rashida ta sata amman bata zaton shine zai sa Kalsoom wannan kukan bayan ko kotun ba'a shiga ba. Kusa da ita ta zauna tana ƙoƙarin ɗago kanta.
“Ke miya same ki?”
Ɗagowa tayi cikin kukan ta rumgume Mominta. Girgiza Momi tayi
“Ke ki min magana mana, waya mutu? Ko Rafiq ɗin ne ya mutu?”
“Ni ce Momi Hilal ya sake ni...!”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, me kika masa?”
Kasa magana tayi sai kuka take kamar zata shuɗe, Momi ma hawaye take, ita kanta bata jidaɗin maganar da Kalsoom ta faɗa mata ba, babu mace da zata so auren ƴarta ya mutu sai dole, balle Kalsoom da aka samu aka yi auren daker.
“Ya isa bari kuka, aure rai ne da shi idan lokacin yin sa yayi sai an yi, idan kuma mutuwarsa yayi dole ya mutu, ki kwantar da hankalinki”
Ta faɗa tana share mata hawaye, sai dai kuma ita na ta hawayen ba su daina zuba ba. Daker Momi ta lalaɓa Kalsoom tayi shiru, har ta shiga ɗakin Momi ta kwanta, kanta sai sarawa yake, ga wani ɗan banzan nauyi da yayi mata kamar an ɗora mata dutse, idonta kuma har ji take kamar ƙasa ce a ciki.
Momi kan cikin rashin kuzari tayi girkin yau, sai dai har tayi ta gama bata lasa miyar ba balle ma ta ci abincin. Sai da ta zuba a plate sannan ta kaiwa Kalsoom, banɗaki ta tararda ita tana alwala, dan lokacin ɗaya da rabi tayi, ta daɗe a banɗakin tana aikin kuka sannan ta fito.
“Haba Kalsoom ina ce kin saba da irin wannan jarrabawar, komai fa idan an yi haƙuri za'a ga riba”
Momi ta faɗa tana kallon fuskarta data kumbura. Kusa da ita Kalsoom ta zauna, idonta cike da ƙwalla ta ce
“Momi yanzu duniya zata ɗauka da gaske na aikata, yanzu kowa zai zarge ni akan ni ce ma bawa Rafiq guba, tun da ga shi har Mahaifinsa ya zaɓi rabuwa da ni”
“Amman baki masa bayani ba ne? Ko da yake ba lallai ne ya gamsu ba, saboda gidan daga ke sai yaron ne, kuma abun mamaki ne ace ya sha guba, dole duk wanda ya ji ya zarge ki, ni ba ma abunda ya ɓata min rai kamar zuwa kotun nan da za'ayi”
“Ya ce min babu maganar kotu, ɗazu da zai ba ni takarda”
“Allah ya sauwaƙe, idan auren ku akwai alheri a ciki Allah ya maida shi, idan babu kuma Allah ya kawo miki na ƙwarai, shi kuma ya haɗa shi da matar ƙwarai”
“Ina jin saki uku ne, aure ba zai sake shiga tsakamin mu ba”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, miya kai shi aikata wannan babban kuskure? Har saki uku? Ai idan rai ya ɓace hankali baya gushewa, amman Hilal be yi ɗa ba, ai komai bincike yake so”
Ƙasa tayi da kanta tana kuka.
“Daddyn ki ba zai ji daɗin wannan lamarin ba, ana murna an yi abu sai gashi kuma ya zama na riƙici, ko da yake malamai sun ce idan saki uku aka yi shi a lokaci ɗaya za a iya ɗaukarsa a matsayin ɗaya”
“Ba furtawa yayi ba, a rubuce ya bani”
“Rubuta ya yi saki ɗaya, biyu, uku? Kalsoom bana son ki dawo xaman gidan nan ne, sannan duk wanda ya ji dalilin mutuwar auren ki ba zai aure ki ba, saboda wannan ɓacin suna ne. Nasan ba halin ki bane ko kin ji kin haɗu da mugayen ƙawaye ne masu kai mutum kai hallaka”
“Wallahi ban aikata ba, ke ma zargina kike ko?”
“Ba zargi bane Kalsoom kawai ina tsoron sherin zuciya ne, da kuma kishi, babu abunda basa sawa”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah kaɗai zai shede ni shi kaɗai zai shede ni da ban aikata ba”
“Ba zargin ki na ke ba Kalsoom, amman wannan lamarin abu ne mai sarƙaƙiya, ga abincinki ki ci”
Kai ta girgiza hawaye na mata zuba.
“Ki daure dai ki ci, Allah zai kawo mafita inshallah, wallahi wahala bata taɓa tabbata, kuma tun da har ya ci amanar ki sai Allah ya saka miki, Hilal butulu ne”
“Karki ga laifinsa Momi ni na nemi ya sake ni, a tunani na hakan shine mafita, ashe bala'i ne, ni ce na ce yayi min saki uku”
“Subhanallah Kalsoom ke kika jawa kan ki matsala, dam me zaki yi haka? Kin fi son ki dawo gida ki zauna tare da ni? Mutane da suka zage ki lokacin da aure yayi miki tsawaiko su sake buɗe miki sabon shafi? Kin tonawa kan ki asiri kowa zai ji dalilin fitar ki gidan miji, gashi ba saki ɗaya bane balle a gyara saki har uku wallahi baki da hankali Kalsoom kin yi wa kan ki, da wane ido zaki kalli baban ki? So kike ciwon zuciyarsa ya tashi ko?”
Ta ƙasara da kuka. Tana mai jin kamar ta kama Kalsoom ɗin tayi ta dukanta. Wani irin kuka Kalsoom take sai yanzu take nadamar abunda ta aikata.
“Ina takardar take?”
Momi ta katsa mata tsawo. Jikarta ta nunawa Momi tana cigaba da kuka. Tashi Momi tayi taje ta ɗauki jakar ta zazzage kayan ciki sai ga takardar ta faɗo, ita kanta ta ji wani ɗarrr kamar ka ta ɗauki takardar sai dai tana da buƙatar sanin ko saki nawa ne idan da gyara a gyara tun kowa be ji ba.
Warware takardar tayi tana karantawa. Wani dogon tsaki taja lokacin data gama karantawar ta jefa ma Kalsoom takardar ta fice tana faɗin.
“Yayi tunani da hankali wallahi...”
Sai da Kalsoom ta ci kukanta ta ƙoshi sannan ta ɗauki takardar tana dubawa cikin kuka.
_Idan na sake ki ina za ki? Wa kike tunanin zai aure ki a halin da kike ciki yanzu? Kowa yana zargin ki da kin kore Rashida kina son kashe ƴaƴata, saboda basu san dalilin sakinta da na yi ba._
_Zan miki uzuri Kalsoom akan abinda kika aikatawa ɗa na, saboda kin nuna musu so a can baya, xuciya bata da ƙashi, dukan abunda kika aikata dan kina so na ne, kina kishi na shiyasa kika aikata, kina ganin kamar ina son ƴaƴan da ba naki ba da yawa ko?_
_Ba zan sake ki ba, saboda naga so na a idonki, kina neman sakin ne saboda kina ganin kamar shine mafita a gareki ko? To ba zan sake ki ba, har abada haka zamu zauna da ke, amman ba zan sake barin ƴaƴana a tare da ke ba, ba zasu sake raɓar ki ba, saboda zuciyarki ta sauya a yanzu, kin tashi daga Kalsoom ɗin da nasan ki kin koma wata dabam, amman hakan ba zai hana na so ki ba, ba xai hana na xauna da ke ba, ina son ki sosai Kalsoom amman ban cancanci abinda kika min ba, nasan mace ce ke kina da rauni shiyasa kawai na ɗaga miki ƙafa_
_Idan kuma har sakin kike so da gaske sai ki kai ni kotu._
*Ur Faithful Husband*
Shine abinda ya rubuta daga ƙarshe cikin manyan harufa. Rumgume takardar tayi a ƙirjinta tana sauke ajiyar zuciyar da bata san lokacin data zo mata ba.
Wani sanyi ta ji ya saukar mata tun daga saman kai har ƙasan ƙafafunta, nan take ta nemi ciwon kanta da kuka da take ta rasa, wani irin ƙaunar Hilal ne ta ji ya ratsa zuciyarta.
Hijabinta da ta bari falo Momi ta jefa mata.
“Tashi ki koma ɗakin ki tun Mahaifin ki be dawo ba”
Buɗe ido tayi tana kallon Momi da murmushi a fuskarta babu ko kunya.
“Bari na yi sallah”
“Idan kin je can kya yi, amman wlh karki sake kuskure cewa ya sake ki, in ba dan Allah yasa yana da tunani ba ai da shikenan”
Bata musa ma Momi ba ta ɗauki hijabin Momi ta saka ta ɗauki takardar da jakarta ta fito falo ranta tasss kamar ba ita ce ta gama kuka ba. Har bakin gate Momi ta rakata tana mata gargadi, sai da ta hau Napep sannan Momi ta koma ciki tana yi Allah Hamdala tare da sawa Hilal albarka...
*NAMRA POV*
Sai da dare Asim ya dawo, kamar yadda ya saba, idan ka ganshi ba zaka ce shine ya fita da tsoro ba ɗazu, yau yayi ciniki shine sirrin farincikin na yau.
Ba laifi ya ɗan sake fuska ya shigo har da sallama, kamar ba shi ba. Ita kanta Namra da mamaki ta amsa masa sallamar tana ƙara kallon fuskarsa dan ta tantancesa. Ya zauna kusa da ita, yana shewa.(fito)
“Sannu da zuwa”
“Yauwa ya gidan?”
“Gida yana nan yadda ka bar shi, masu gidan ma sun zo guba abun su kuma sun ce mu tashi”
“What? To ina za mu koma? Ai kuɗin dana biya be ƙareba, ba zamu tashi ba wallahi”
“Su zaka faɗawa ba ni ba, ni dai na faɗa masa ya zo da safe ko da dare zai same ka”
“Bari ya zo ɗin amman wallahi ba zamu tashi ba, duk inda za a je sai dai aje, amman wannan iskancin ba zan ɗauke shi ba, haka kawai dan ina talaka sai a nemi wulakanta ni”
“Miye abun wulaƙanci dan masu guri sƴn nemi aba su abun su? Sai mu tashi mu basu gidan su, ni dai na roƙe su akan su bar mu mu zauna bq idan har basu yarda ba shikenan sai mu nemi wani gurin kuma”
“Ai kaji matsalar masu kuɗin nan, wallahi duk inda yake baya ƙaunar talaka”
“Ka cika mai da zazzaɓi ciwo Asim, yanzu sun san kai mai kuɗi ne ko talaka? Amman kasan babu talakan da zai iya kama gida kamar wannan ya zauna ko?”
“Sun san talaka nake mana tun da na zauna bq, nima lokaci na yana zuwa zan yi kuɗi har na mamaki”
“A haka za kayi kuɗi matarka tana cikin ƙunci? Ban taɓa ganin ragon namiji irin ka ba Asim, sai dai na girka na baka da ƙarfin ka da komai?”
“Dan Allah ki yi haƙuri Namra, kin ga ɗan aikin da nake be wuce na samu na shan ruwa ba, amman yanzu na samu wani aiki, sai dai aikin mai gidan ya faɗa min cikin gidan zan koma da zama saboda aike-aike idan sun taso, kuma a matsayin driver zai ɗauke ni kuma yaron gida, tun last week muka yi maganar amman nace ba zan kama aikin ba sai na ji ta bakin ki”
Ta jidaɗi dan tasan aikin ya fi wanda yake yi yanzu, sai dai maganar komawa can ne bata gane ba.
“Amman ka koma can har da ni? Ko ya”
“A'a ni kaɗai zan koma can saboda ya fi son ana kwana ta can”
“Amman kai ba aikin gadi ba ce kuma sai ka kwana ina ma laifin kaje da safe wuni”
“Ba kullum zan riƙa kwana can ba, ina jin wani lokaci ne kawai, kin ga ƙara mu samu mu riƙa wannan aikin kamin mu ga abinda Allah zai yi gaba kuma”
“Allah yasa haka shine mafi alheri”
“Amin ya rabb”
Ya rumgume ta yana murmushin jindaɗi, daman ya faɗa mata ne kawai dan ta karta daina ganinsa da dare, amman ko da tace bata aminta ba zai sa ya fasa aikin ba.
*ABDOOL POV*
Suna dinner yake nanatawa Ummi maganar siyen gidan da zai yi, but still bata yarda ba, duk da ta ga alamun da gaske yake.
“Wai mi za ka yi da gida daya ƙone har xaka siye shi 15m?”
“Just”
Ya faɗa yana ɗaga kafaɗu.
“Dude na bar maka, ko kyauta ma zan iya baka ma”
Amal ta faɗa jikin har rawa yake. Kallon Ummi Abdool yayi yadda take watsawa Amal harara yasa shi dariya, sai ya aje spoon ɗin hannunsa ya tashi ya ɗauki kofin tea ya wuce ɗakinsa. Haka kawai ya samu kansa da murmushi ba dalili.
Wata ƙaruwar durowa ya buɗe ya ɗauko wata ƴar ƙarmar jaka baƙa. Ya nufo part ɗin Ummi hannunsa ɗaya riƙe da tea ɗin.
Saman kujera ya jefar da jakar yana kallon Meesha dan ya yarda da natsuwarta.
“Aisha zo ki cire min 15m a nan, ko wanne 1m ne”
Dinning ɗin ta baro ta zo ta zauna saman kujera ta buɗe kuɗin ta fara ƙirgiwa har ta cire 15m, ta aje gefe.
“Ga su”
Sai ya kalli Ummi
“Ummi ga kuɗin”
“Abdallah ana ciniki dole ne? Na ce ba xa a siyar ba”
“Amman mai abu tace ta siƴar”
“Wai me za ka yi da gidan ne”
“Kawai ki sai da min”
“An siyar maka, shikenan?”
“Thank you”
Ya ɗauki ragowar kuɗin ya maida ɗakinsa. Saman madubi ya ɗora copin tea ɗin ya faɗa saman gaɗon zuciyarsa cike da nishaɗi.
Haka ya kwana da nishaɗin da be san ta ina yake xo masa ba balle dalilinsa ba. Shi dai baya iya faɗin abunda ɗaya ta san ya shi ne silar farincikinsa tun jiya har zuwa yau.
Yau zai koma abuja ko ba komai dole yayi sammakon tashi, balle kuma Namra tace masa da safe ake samun mijinta.
Be tsaya wani karin kirki ba, dan a tunaninsa kamar idan ya daɗe ba zai samu mijin nata ba
Ko da bakwai tayi yana ƙofar gidan, sai dai be shiga ba sai da ya buga gate ɗin, ganin babu wanda ya fito yasa ya tura gate ɗin ya shiga cikin, black suit ne jikinsa yayi mugun masa kyau kamar balarabe.
Nesa da bq ɗin ya tsaya yayi sallama cikin muryarsa mai sanyin da daɗin saurora, da ace ma'aikatan sa zasu ganshi a yanzu da sun rantse wannan muryar arota yayi.
Asim ne ya fara fitowa yana samawa, daman tun da yaji sallamar ya raya a ransa cewar masu gidan ne. Sai dai yayi mamakin ganin mutuen duk da be san sunansa amman yasan shi ne ya biyo Namra asibiti. Ƙarasowa Asim ya yi yana masa wani kallo da shi kaɗai ya san fassararsa.
Hannu Abdool ya miƙa masa.
“Sunana Abdallah Ahmad Mai-doki, na zo ne a kan maganar wannan gidan, matarka na ciki?”
Be masa hannun nasa ba sai kawai ya ce
“Eh miye haɗin ka da matata?”
Abdool ya ɗan wara ido tare da taɓe baki haɗi da ɗaga kafaɗu.
“Nothing, jiya na zo akan maganar gidan nan ne sai take roƙo na akan dan Allah na taimaka na bar su a bq su zauna dan basu da gurin zama, so shiyasa na yi ƙoƙarin mai da gidan mallakin ku gaba ɗaya”
Asim ya washe baki, tare da miƙa masa hannu
“Mashallah Allah ya saka maka da alheri”
Daga nan da yake ya ƙwalama Namra kira. Sai gata ta fito cikin hijabi, kamin ta ƙaraso gurin asim fuskar Abdool kawai yake kallo ya gani idan ya kalli Namra. Babu abinda yake rayawa a zuciyarsa sai munafurcin da Namra take masa, wai shi za a maida wawa ya kawo mata gida ya ce ya basu dan tasan idan ya bata ita kaɗai dole za a gane abunda yake tsakanin su. A fili kuma murmushi yake kamar gaske yana kallon Namra da take gaishe da Abdool. Kallo ɗaya Abdool yayi mata ya ɗauke kai ya ciro takardar dake aljihunsa ya miƙawa Asim
“Daga yau wannan gidan ya zama na ku, ba zaku sake biyan kuɗin haya ba balle ace ku tashi”
Hannu biyu Asim yasa ya riƙe hannunsa yana masa godiya kamar zai shige cikinsa. Namra kan mamaki ya hana ta tace komai balle har ta yi godiya.
Sai Asim ne yake ta zuba masa godiya yana murna baka da zuci dan yasan shi zai mori gidan ba Namra ba.
“Mun gode sosai Allah ƙara arziki ya ƙara wadata jazakallahu khairan”
“Amin”
Ya faɗa sannan ya juya ya nufi gate, yana ƙara kallon gidan. Har cikin ransa yaji addu'ar da Namra tayi masa. Sai da ya wuce sannan Asim ya juyo ya shigo gida zuciyarsa cike da zarge zarge. Sam be nunawa Namra ya gane shi ba, sai kawai ya nuna mata ya fi kowa farinciki abinda yayi musu duk da zucin ma farinciki ne dan yasam shine zai ci amfanin abun.
“Kin gani ko yanzu kan alheri ya fara shigo mu, yanzu duk wannan gidan na mu ne kai Alhamdulillah Allah”
Namra tayi murmushi dan ita tun ɗazu mamaki take da tunanin dalili kyautar gidan da Abdool yayi mata, bayan acan baya ya taɓa binta yace yana sonta, ko dai akwai biyu a kyautar ne? Bata bar Asim ya gane abunda yake ranta ba, gudun karya zargenta, ko kuma yayi wani tunanin na daban daman can ya taɓa zarginta.
Dumamen shimkafar da tayi ne ya zuba masa, ya ci sannan ta kai masa ruwan wanka yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin data wanke masa. Sannan ya fito waje ya ciro ɗari biyar ya miƙa mata.
“Gashi ayi cefane”
Hannu biyu tasa ta karɓa tana muryar yau mijinta yyi abun kai
“To Allah amfana”
“Amin sai na dawo”
“Allah ya tsare”
Ya nufi gate zuciyarsa cike da ƙunar cin amanar da Namra take masa, abun har ya fara wuce gurin har ana kai ga kyauta gida.
“Hmm Lallai ma wannan matar wai har ni za a rainawa hankali, bari na zama Asim ɗi na na ƙwarai ki ga yadda zan yi da ke, ku yi ta abun ku yanzu na ba ku dama”
Ya filin yake maganar ya miƙe hanyar data zata kai shii babban titi, sai dai hanyar gidan su Mardiya ce, da gangan ya bi dan ya ganta.
Ya ko yi nasarar angota da ɗaura gaba tana tsaye ƙofar gida tana ciniki a warwaro da mai tutu-rutu, ƙirjinta kawai yake kallo yana siffantawa kansa ita, har ta kawo kusa da inda take.
“Barka da safiya Asim”
“Yauwa barka Mardiya ya gida?”
“Lafiya ƙalau, ina Namra?”
Ya ɗan ƙara washe baki dan be yi tunanin zata kawo maganar Namra a yanzu ba.
“Tana nan ba kin guje mu ba”
“A ni na isa ku ne dai kuka guje ni”
Dariya yayi ya ƙarasa gaban mai ɗan kunnen yana kallon kayan
“Me aka siya?”
“A warwaro ne da ɗan kunne”
Babu ko kunya take masa magana kamar bata sam ɗaura gaba ne a jikinta ba. 1k ya ciro ya miƙa mata
“To a siya da yawa”
Hannu tasa ta karɓa.
“Na gode sosai Allah kawo wa su, ayi irin mu huɗu”
Dariya yyi kamar ba shi ba ya amsa da amin yana tsayardar mai okada. Sai da ya hau sannan ya faɗa masa inda zai kai sa.
Hajiya Sadiya tayi mamakin ganinsa sosai dan a ƴan kwanakin daya ɗauka ta zata ko ba zai dawo ba ne, ruwa ta kawo masa da abinci, sai wani ƴauƙi take kamar ta ga mijinta. Shi kuma ya sake jikin sosai kamar gidansa, baya kallonta idan tana kallonsa ko taɓa gabansa sai ta bada baya yake kallonta.
“Baka buƙatar kwaso kayan ka ko wani abu, akwai komai da zaka buƙata a ɗakin da za a sauke ka, ni na ɗauka ma ba zaka dawo ba”
“Me zai hana? Mutum ya bar samu?”
Dariya...
“Aiko dai, ina kallon lokacin da kake ta ciwon nan kamar ba zaka tashi ba”
Gabansa ya faɗi dan be yi tunanin ko ta san shi ba, se dai be gama saƙe saƙensa ba ta cigaba.
“Lokacin da muƙa ɗauko ka daga asibitin Funtua zuwa nan katsina, lokacin kana cikin ciwo ba zaka gane ba, amman na san kana da mata ka ɓoye min ne kawai”
Ido cikin ido yake kallonta dan tantance abinda take faɗa.
“Ban gane ba”
“Hmmm Asim ko? Ni ce na ɗauko ka da mota na na kawo ka Asibitin katsina na biya kuɗin gado da magani, amman nasan ba zaka iya tunawa kancewar lokacin kana cikin ciwo”
“Eh...eh..ha...k...a..ne.... Ashe kin san ni”
“Na san ka nima farko ban gane ka ba sai daga bayan lokacin da nasa ayi min bincike akan ka”
“Bincike kuma?”
“Eh mana ai duk wanda xaka xauna da shi kana da bikatar sanin ko waye shi, gudun abinda zai je ya dawo amman miyasa kace min baka da mata bayan kana da ita?”
Ya ɗan sosa kansa yana cire hannunsa daga abincin daya fita ransa.
“Wallahi Hajiya naga kamar ba ki son mai matar ne shiyasa, ni kuma bana son na rasa wannan aiki na ki”
Tayi murmushin ƙasaita.
“Ba mai mata ne bana so ba, yadda nake son a min spending time ne nasan mai mata ba zai iya ba”
“Zan iya wallahi dan ni na fi ƙarfin matana na, duk abinda kike so zan miki”
“Hakan yana da kyau, namijin duniya irin ka na ke so”
Ya jidaɗi sosai.
“Anything for you Hajiya”
“Gobe aikin ka xai fara, yanzu idan ka gama, sai kaje gurin mai gadi ya nuna maka wasu abubuwan”
“Hajiya ai ni na gama ma”
“Ka daina kirana da Hajiya ka kira ni Sadiya na”
“Ai da nauyi sai dai ko nace Anty Sadiya”
Wata harara ta watsa masa.
“Na yi maka kama da Antyn ka ne?”
Kallonta yayi a zahiri kam tayi yi, dan wannan yasan ba sa'arsa bace sai dai kuma bata isa haihuwarsa ba.
“A'a Sunan ne ba zan biya faɗi a fili ba”
“To ka riƙa ce min Sadiya Babe, amman idam cikin mutane ne ka riƙa kirana da Hajiya na”
“To am gama na gode”
Har ya juya tace
“Kuma bana son sa ido, kar ka damu da baƙina ko ƴaƴan 'uwan da suke zuwa gidan nan kai dai kawai ka yi aikin ka”
“Inshallah ba zaki same ni mai tsaɓa uwarnin ki ba”
“Albashin ka 100k per month”
Da sauri ya kalleta fuskarsa ƙarara da mamaki, sai gashi kurfane ƙasa yana mata godiya.
“Allah ya ƙara miki arziki Allah yayi miki yadda kika min”
“Amin kai dai ka cigaba da biyayya kawai zaka iya samun fiye da haka ma”
“Inshallah”
“You can go, sai ya nuna ma ɗakinka da kuma aikin ka”
Ya juya ya fice yana jin wani irin nishaɗi da be taɓa jin irinsa sai yau.
*ABDOOL POV*
Ko da ya isa gida duka ƙanensa sun wuce scul Ummi ce kawai a dinning sai Amira suna karƴawa. Tun daga nesa Ummi ta hango nishaɗin dake fuskar ɗanta. Har ya ƙaraso kusa da su ya zauna a kujera daya saba zama.
“Ina ka je da safen nan haka?”
Be son maganar gaban Amira, sai kawai yayi murmushi ya ɗauki kofi ya soma haɗa ma kansa tea.
“Good Morning Yaya”
“How are you dear..”
_Dear_ taji kalmar har cikin ranta, shi kuma ya amsa mata ne da murmushi kuma ba tare da wata manufa ba.
“Ummi yau zan koma fa”
“Yeah i know i just want to know the secret of your smile?”
Shi kansa be san yana murmushi sai yanzu da Ummi ta yi magana. Yayi saurin kawar da murmushin
“Nothing”
Ya miƙe tsaye yana kallon agogon hannunsa.
“Around 9: za mu tashi”
Amira ta ji babu daɗi. Sai ta tashi jiki a sanyeye ta nufi ɗakinta, sam bata son Abdool yayi nisa. Komawa Abdool yayi ya zauna ganin Amira ta shige ɗaki.
“Ummi ina wata da na taɓa baki labari nace miki na ganta a pharmacy da hospital har na ce ina son ta sai tace min ita matar aure ce?”
“Yeah yeah na tuna what happed?”
“Ita ce take haya a gidan Amal ita da mijinta, sune suka yi wuta yanzu sun koma bq da zama saboda mijin nata talaka ne sasai”
“So...?”
“Shi ne sai na siya musu gidan...”
“Saboda me?”
“Just”
“You still love her ko?”
Ya ɗan yi shiru yana tambayar kansa. Kamin ya ɗaga kai alamar eh
“Yeah and i d....”
Be ƙarasa ba Ummi ta mikr tsaye tana dakan dinning ɗin ta katsa masa tsawa
“That it, baka da lada baka yi da Allah ba, kai baka ji kunyar kanka ba ace matar wani kake so? Kai zaka so wani ya kashe maka aure ne?”
“Ummi ba auren ta zan kashe ba, i just help”
“Help? You want to use her dan kasan mijinta talaka ne, ka kashe mata aure huh? Duk ƴan matan garin na ka rasa wacce zaka so sai matar aure Abdallah mike damun ƙwaƙwalwarka, abunda kake be kamata ba, kallon ta a gareka haramun ne, kamata yayi ace kana yaƙi da sheɗen ba wai kana bari na kai zuciyarka ga halaka ba.
Dole zan yi magana da Mai Martaba dole ayi maka aure ko baka so, dan na fahimci baka da hankali”
Cikin fushi ta ƙarasa maganar tana mai ƙyamar abunda ɗan ta ya aikata. Shikam kasa cewa komai yayi dan be da bakin magana.
Duka abunda suke Amira na jikin ƙofar ɗakinta tana sauraensu duk da akwai ta zara, dan da farko bata ji abunda Abdool da Ummi suke tattaunawa ba sai da Ummi ta ɗaga murya tana masa faɗa.
‘Wace mai sa'ah ce wannan wanda Abdool yake so? Me take da shi?’
Tambayar da tayi ma kanta kenan tana mai ƙarasawa gaban modubi ta dubi kanta.
*HILAL POV*
Yana isa asibitin ya wuce ɗakin da Rafiq yake, zaune ya same shi yana kuka. Amina da wata nurse na kusa da shi tana lalaɓashi, bakinsa ya karkace sai dalalarda yawu yake kamar musaki, ko kuma irin yaran na dolaye. Yana ganin Hilal.ya riƙa ƙokarin sauka yaje inda yake, sai Hilal ya ƙaraso da sauri kusa da shi cike da tausayawa ya ɗauke shi.
“Shiiii Daddy ya zo”
“Good mornig Sir”
Nurse ɗin ta gaishe shi sannan ta fice, Amina ma ta ɗora da nata gaisuwar tana nuna masa abincin da Hajiya tace a kawo masa.
“Okay”
Ya faɗa yana ciro wayarsa dake ringing.
“Ya aka yi?”
“Wallahi nayi lallaɓa Dady yace shi sai ya saka ƙarar”
“To shikenan aje kotun ai sai Allaura ta tono garma, amman wannan abun da za ayi ba zai na ƙi tsayawa Kalsoom ba she's my wife”
Ya kashe wayar ya maida Aljihu. Amina sao kallonsa take tana mamakin furucin da yayi, a zuciyarya ta ƙumshe zance da sunan dai ta je gida ta faɗawa Hajiya.
*RASHIDA POV.*
Bayan Rashida ta ƙare waya da shi ta cigaba da aikinta, kamar yadda ta saba. Sai da lokacin tashinta yayi sannan ta shiga tayi ma Alh Bashir sallama ta fito. Kai tsaye gidan Mom Shuraim ta nufa. Ita kanta tayi mamakin ganin Kalsoom mace da zata shekara bata kira a waya ba ma balle kuma ziyara amman yau gata gidan ta.
Abinci ta kawo irin nasu na ƴan nijar ya ji albasa har ya gaji, da ruwan sanyi sannan ta zauna suka soma firar yaushe gamo. A cikin firar na Rashida take labarta mata mutuwar aurenta da kuma abinda Kalsoom tayi mata. Mom Shuraim ta cika da mamaki matuƙa. Sai Allah wadai take tana tsinewa Kalsoom.
“Ke dai bari wallahi ina cikin matsala shiyasa na zo gurin ki ko kin san wani malami inda zamu iya zuwa a kare wannan asirin dam ance min ƴan nijar kan suna da abubuwa da yawa”
Mom Shuraim tayi shiru dam ba kowa bane yake son buɗe sirrinsa.
“Ai ko nan akwai su”
“Ni dai ki taimaka min idan zaki kai ni.can nijar ɗin ko kuma ki haɗa da wanda zata kai ni amman fa idan kin san mai aiki na gwarai”
“Toh Yanzu dai sai na bincika can gida idan na yi waya da su, zan faɗa miki”
“To na gode zan kira ki inshallah”
“Amman xaki.iya xuwa har can?”
“Wallahi ko chana ne zan iya xuwa balle nijar”
Dariya Mom Shuraim tayi ta rakota har ƙofar gida tana ta tunanin maganar a zuciyarta, sai da Rashida ta miƙawa yaranta 500 kowanensu sannan ta shiga motar ta f ɗauki hanyar gida. Ba dan zuciyarta ta gamsu Mom Shuraim ɗin zata kai ta ba, ɗan bata ga alamun haka a tare da ita ba.
Tunaninta duk ya tattara ya koma gurin abokanta, har ta isa gida tunani take wacece cikin ƙawayenta take da wannan shige shigen malamai.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *58*
Cikin rashin daɗin rai ya bar katsina saboda faɗan da Ummi tayi masa, shi kansa sai yanzu ya ke jin rashin daɗi akan abinda ya aikata. Sai dai shi yasan be dan wata manufa ba, be kuma yi ba dan ya kashe mata aure, sai ya yarda da abu ɗaya, shine son ta abu ne kuma da ba zai iya cirewa kansa shi ba amman yana ta yaƙi da zuciyaraa wajen gani ya anta da Namra a duniya.
Damuwarsa bata hana shi aikinsa ba, amman duk wanda ya ganshi a ya san akwai damuwa sosai a tare da shi. Maganar Ummi ta tsaya masa a rai na auren da ta ce zata ma Mai Martaba magana ayi masa, wata ƙila shi ne fita a garesa, sai dai yana tsoron auren mace da baya so gudun kar ya cuci kansa ya cuce ta.
Har gobe babu wacce yake gani idan ya rufe idonsa sai Namra, dukan mafarkansa akan ta ne, miyasa baya da tunani sai matar wani? Dan me zai riƙa mafarkin da babu ranar farkawarsa.
“What's wrong with me? There's something inside me, this is not me it's another Abdool behind me”
A fili yayi furucin ya miƙe tsaye ya nufi window office ɗinsa ya tsaya, yana hango wasu sojoji dake farati a rabar wajen. Kallonsu yake amman hankalisa baya gurin, can kuma ya ɗauke kansa ya juyo ya jingina da gurin yana kallon office ɗinsa.
Wayarsa dakr kan dinning tayi ƙara, alamar saƙo, kallo ɗaya yayi ma wayar ya ɗauke kai, yana cigaba da tunanin abinda yake ganin kamar shine a gare shi.
Ɗan risinar da kansa yayi yana shafa dogon hancinsa, tare da jan dogon numfashi.
Ya samu minti talatin tsaye a gurin sannan ya nufi kujerar zamansa, ya koma ya zauna yana lilo. Hannu ya kai ya ɗauki wayarsa. Saƙon sama ya buɗe wanda aka aiko masa da baƙuwar number.
_If you love something, let it go. If it comes back, it was meant to be. If it does not, hunt it down and kill it. *Smile* good evening hope you had a nice day and a pleasant evening as well._
*AMIRA*
Ya ɗan taɓe baki yana maman inda Amira ta samu waya bayan yasan bata da waya a can baya.
“Maybe Ummi ta bata”
Ya faɗa a fili sannan ya kai hannu ya ɗauki telephone ɗin dake saman tebur ɗinsa tana ringing.
*AMIRA POV*
Murmushi tayi ta tana wanda yasa Haleema kallonta.
“Kin saka number?”
“Eh na saka sai ta wa kuma?”
“Sai ta Meesha”
Haka ta riƙa bata number kowa na gidan cikin har da Amal da Shukura. Ɗaya bayan ɗaya Amira ta riƙa sawa har ta gama, sannan ta kalli Haleema tana murmushin jindaɗi tace
“Na gode sosai Haleema Allah ya saka miki da alheri”
“Ba komai ai nasan zata rage miki kewa ko da game kawai”
“Sosai ma wallahi, Allah ya bar zumunci”
“Karki damu ai komai yi ma kai ne”
Ya faɗa tana murmushi sai ta tashi ta nufi ƙofar fita tana dannar wayarta. Amira kan wayar ta sakarwa ido tana kallo, farincikin saƙon data aikawa Abdool take, bata damu da rashin reply ɗin da be mata ba, daman bata sa ran zai mata ba. Rumgume wayar tayi a ƙirginta, wani kalar nishaɗi ne ya same ta, marar misaltuwa. Tunawa da faɗan da Ummi tayi masa akan wata yasa ta jin babu daɗi, that's means akwai wace take ransa kenan, bata gane dalilin faɗan na Ummi akansa ba, sai dai taji yana faɗin bashi da lada, sai kuma maganar da tace masa idan shi ne zai so wani ya kashe masa aure.
‘Wacce yake so matar aure ce ko kuma an mata engaged ne? Akwai buƙatar na san ko wacece wata ƙila tana da wasu halaye da Abdool yake da su. Sai dai taya? Taya zan nuna na san wata da yake so? Idan har na nuna hakan za su ce ina musu sa ido, bayan kuma sun yarda da ni’
A zuci take zancen a fili kuma sai ta ce
“What's the solution?”
Kanta ta ɗaga sama tana kallon pop.
‘An ya zan iya bari wannan damar ta wuce ni? Ace na shiga rayuwar Abdool kuma ba bari wata ta ƙwace min shi? Anya zan iya barin wannan daular ta wuce ni? Zuciyata a yanzu Abdool kawai take so mutumen dana saɗaukar da rayuwata akan sa’
Ajiyar zuciya ta sauki, tana ta zancen zuci, sai dai har aka kira salla bata samu wata gamsasshiyar mafita ba. Unƙurawa tayi ta tashi ta nufi ɗakinta tana auna irin abunda za tayi ma Abdool wannan karon.
“Amira...”
Daf da zata shiga ɗakinta Meesha tayi mata kiran tana nuna mata ɗakin Ummi da alama Ummi ce take kiranta. Juyowa kawai ta yi ta nufi ɗakin Ummi cikin ladabi. Kusa da Ummi ta zauna ƙasa ta matse Ummi sosai kamar zata shige cikinta.
Sai da Ummi ta gama abinda take sannan ta cire madubin idonta ta kalli Amira a natse ta ce
“Amira ina tunanin yanzu hankalin ki ya kwanta, natsuwarki kuma ta dawo jikin ki, zama haka ba shi yi, ya kamata ace izuwa yanzu kina gaban iyayenki, ba mu san halin da iyayen ki suke ciki ba, i'm mother too i know how it feel like idan ɗan ka baya kusa da kai, musamman mace”
Ɗagowa tayi ta kalli Ummi idonta cike da ƙwalla.
“Dan Allah Ummi ki min haƙuri ki bar har nan gaba, ni kaɗai nasan halin da nake shiga idan na tuna da iyaye, kuma nasan dole na koma garesu”
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke.
“Ba komai Allag yasa haka shi ya fi alheri, Haleema ta baki waya ko?”
“Eh ta ba ni”
“Yana da kyau ki kira wani daga cikin familyn ki ku gaisa”
“Zan yi ƙoƙarin yin haka Ummi na gode”
Ta miƙe tsaye cikin rashin kuzari ta bar ɗakin. Ɗakinta ta dawo ta xauna gefen gado tana kuka, ita kanta tasan abar tausayi ce idan ta tuna da rashin iyayenta.
“Na rasa iyaye saboda kai Uzair, ka cuce ni ka yaudare ni, kai ne ka saka rayuwarta ta koma a haka, na rasa iyayena da duka family amman ba zan rasa Abdool da familyn su ba, ba zan zama loser ba”
A fili tayi furucin zuciyarta cike da yaƙinin abinda bakinta yake faɗa.
“I have to make it work, i can't lose them both, i deserve happiness too”
Saman gadon ta faɗa ta rumgume filo tana wani kuka mai taɓa zuciya.
“Kin cuce ni Namra abotarmu bata amfana min komai ba sai nadama da baƙin ciki, nayi nadamar sanin ki a rayuwata, You and Uzair have to paid for what you both did to me”
Wani kuka take Sosai tana buga ƙafafunta kamar wata ƙaramar yarinya. Turowa ƙofar ɗakin da Haleema tayi ne yasa ta saurin tashi ta goge hawayenta, gabanta sai faɗuwa yake tana ala-ala idan bata ji zancen da ta yi ba.
Kusa da ita Haleema ta zauna cike da tausayawa, dan akan kunnenta Amira ta faɗi komai.
“Kin cancanci farinciki Amira, ba kiyi ƙarya ba kin cancanci komai daga wanda kika sadaukarda ranki gare shi, mu kuma kin cancanci soyayyarmu tun da kika ceto ɗan'uwan mu”
Hannayenta Haleema ta kama, ta riƙe
“Ba zaki rasa mu ba, ba zaki rasa familyn Abdool ba har a bada”
Da mamakin Amira take kallonta kamar wacce bata fahimci inda zantukanta suka dosa ba.
“Na daɗe da fahimtar kina son Ya Abdool, tun lokacin da kika shigo gidan nan, na lƴra da ke Amira kina rasa natsuwarki idan Abdool yana cikin gidan nan, a yanzu ma bayan Number Ummi Numbersa kika tambaya a na biyu, kina son Abdool Amira i can't hide it”
Rumgume ta Amira tayi a ƙirginta gamgam, tana kuka.
*ASIM POV.*
Bayanai gadi ya gama nuna masa ko ina na gidan, sai ya dawo falon dan faɗa ma Hajiya yadda suka yi da mai gaɗin. A inda ya barta a nan ya same ta tana zaune ta ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaƴa tana kallon ƙofa kamar ta san da shigowarsa.
Saman kujera ya zauna dan shi yanzu jin gidan yake kamar nasa, yayi sallama sai dai bata amsa masa sallamar ba har ya zauna tana murmushi.
“Hajiya an nuna min komai, gida mashallah”
Sai a lokacin ta buɗe baki tana masa magana kamar mai nauyin baki.
“Amman bana son ka faɗawa kowa abinda ka sani game da ni”
“Hajiya ai ban san komai ba, balle ma na faɗa, kuma ni bana daga cikin mutane nan masu yawan surutu”
“Zaka sani ne ai shiyasa nake gargaɗin ka tun yanzu, zaka san komai a kai na, tun da har ka furta zaka iya yin komai”
“Wallahi zan iya miki komai Hajiya”
“Yayi kyau, kaga ɗakin ka?”
“Eh yayi kyau sosai”
“Anjima zan baka kaje ka siyo abubuwan da babu, sai ka sawa ɗakin, saboda ina son ya zama ɗakin ka na ainahin, so nake ka manta da cewar kana da wata mata dabam”
“Ba komai Hajiya komai kika ce shi za'ayi inshallah”
“Thank you you're very loyal”
Ta tashi ta nufi ɗakinta tana murmushi, har a zuciyarta take jin Asim dan taga alamun zai iya komai na neman kuɗi, haka take so daman.
Shi kuma sai daɗi yake ji yadda take masa, ko kaɗan be kawo komai a ransa ba, abu ɗaya yake tunanin zata nema a gunsa, wata ƙila ba zai wuce sex ba, kuma he's ever ready indai wannan nan ne, sai dai kuma shi ɗin kansa yana buƙatar sanin ko wacece ita, dan be ga alamun tana da yaya ba.
Zuciyarsa cike da nishaɗi ya fiddo ƙaramar wayarsa ya shiga duniyar facebook. Notifications ya tarar mai yawa, ga massage da friend requests. Rabon da hau duniyar facebook tun Namra tana amarya tana ɗan cikin yanayin jindaɗin nan kamin komai ya canja.
Notifications ɗin ya fara dubawa yaga na gani sannan ya shiga massage, ya samu mata da yawa daga cikin masu masa massage kansancewar hoton dake profile ɗinsa yayi kyau, sosai idan ka ganshi sai ka ɗauka wani shege ne.
Sama-sama ya amsa massages ɗin sannan ya duba friend requests yayi accepting wasu ya bar wasu.
Be wani daɗe ba ya sauka daman be cika jindaɗin hawa da ƙaramar waya ba, rabon da yayi chat da babbar waya kuma tun yana farko farkon scul ana yayin karyar nan.
Saukowar Hajiya Sadiya ne yasa shi ɗaga kai yana kallonta. Sai kuma ya sauke irin wai shi ladabi tun da ita ce boss. Keys ɗin mota ta jefa mishi tare da Atm.
“4782 shine password ɗin, ka siye duk abunda ya kamata, ɗan bana son ƙazanta”
Ya ɗauka ya miƙe tsaye har wani zumuɗi yake, zuciyaraa fes.
“Toh Na gode sosai”
Bata amsa shi ba, shi kuma be damu da sai ta amsa ɗin ba sai kawai ya fice yana auna yadda Allah ya maida shi wani a dare ɗaya.
Be sa ko wace mota bace har sai da ya danna makulin tayi ƙara sannan ya nufi motar ya buɗe ya shiga.
‘Kamata yayi na siyar da gidan nan, idan ya zo sai na riƙa juyawa ina siyen zinari ina sai dawa, ga wannan albashi walh nan da nan za ka ga na yi kuɗi, sai dai kuma ban sani ba ko bata son na haɗa da wani aikin, wata ƙila ma zata iya min kyautar mota fa, ji yadda ta yarda da ni nan take har da ba ni atm ɗinta ta faɗa min password, daman mai haƙuri mawadaci’
Shine abinda yake ta saƙawa a zuciyarsa yana tukin motar da yake hango kansa a matsayin wani ƙaramin alhaji.
*RASHIDA POV*
Ajiyar xuciya ta sauke har da hawayen ƙirƙira dan kawai Teema ta tausaya mata, haƙiƙa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne Teema ta tausaya mata sosai har tana jin kamar tayi mata maganin matsalarta yanzu.
“Ki kwantar da hankalin ki Rashida, zan taimake ki akwai wani malami yana nan ɗan ƙauye sokoto ne, wlh malamin har ƙasa ƙasa ake ɗaukarsa yayi aiki, aikinsa kamar yankan wuƙa yake, a take komai kike so zai miki zan kai ki gurinsa idan kin shirya”
“To ai ni kullum a shirye na ke, ni ko yanzu kika ce muje zamu je wlh”
“A'a ban da yau dan ban shirya ba amman dai gobe ki zo da wuri sai mu tafi”
“To inshallah zan zo”
“Amman aikin ki fa nasan ba hutu kuke samu ba”
“Karki damu da aikina wannan ita ce muhimmiya”
Teema tayi dariyar mugunta. Tashi Rashida tayi, Teema ta raka ta har gurin motar ta ta shiga motar tana ɗagawa Teema Hannu.
Daga gidan Teema ta wuce Asibiti dan karɓar maganinta, a mota ta tsaya ta saka niƙabi da hijab sannan ta fita.
A wani gurin ta tsaya kusa da inda ake ba da maganin, tana kalle kalle mutane, daman haka take duk ta zo wai gudun kar taga wanda ta sani. Duk da wannan shine zuwanta na biyu.
Bayan ta gama dube dubaneta ta shiga ciki ta ga likita, ya ƙara mata shawarwari, sannan ta fito ta nufi gurin karɓar maganin kai tsaye. Security dake gadin ƙofar asibitin ce ta saka ta cire nikaɓ ɗinta dan haka dokar asibitin ta gada, Rashida bata damu ba ta cire niƙab ɗin daman ko wacan zuwan da tayi sai da tasa ta cire shi.
Da fargaba ta kunna kai a gurin tana ɗan kallon mutane ƙasa-ƙasa, gabanta sai faɗuwa yake kamar zai faɗo. Kamar daga sama taji an dafata ana ƙoƙarin juyowa da ita, juyowar da ta yi sai kawai suka yi ido huɗu da Safiya cikin Uniform ɗinta.
Wani irin kallo Safiya take mata kamar wacce ta rude cox she's can't believe Rashida ce ta gani a nan ƴar'uwarta jininta.
Ita kanta Rashida mamakin ganinta take, dan iya saninta wannan ba asibitun su bace, ya aka yi ta zo nan me ya kawo ta.? Yawu Safiya ta haɗe ta wuce da sauri ta fita daga gurin gudun kar wani daga cikin manyan su ya ganta, daman fitowarta kenan daga wani ɗakin ta hango mai kama da Rashida, ashe ba kama bace, ita ɗin ce amman mai zai kawo Rashida HIV/TB unit.? Shine abinda ya tsaya mata a rai.
Miƙewa Rashida tayi cikin dakewar zuciya ta cigaba da tafiya tana son ɓatarwa da Safiya da lissafi, sai dai kuma yanzu bata san liyin da zata bi, tb ko hiv?
*HILAL POV*
Asibitin ya wuni, da rana ma Hajiya ce ta kawo masa abinci. Duk wanda ya zo sai ya tauyasawa Rafiq ganin yadda ya koma musaki sai dalalar da yawu yake. Tuni Hilal ya ɗosa shi akan magani, yasa aka sake masa wasu hotunan dan ganr ainahin matsalarsa.
Ƴan'uwansa da dama sun yi ta xuwa ganin ɗan nasa, ƴan uwan Rashida ma sun zo, sai dai ba sosai ba, Dady Kalsoom ma ya zo shi da Momy, duk da suna jin nauyi ganin kamar ƴarsu ce ta aikata abun.
Sai da yayi ma Rafiq Alurra bachi sannan ya rufe ɗakin. Ya koma office ya cigaba da aikinsa, bayan ya gama, ya sake leƙa ɗakin yaga har yanzu bachi yake. Sai kawai ya nufi gurin motarsa dan yana buƙatar taje gida yayi wanka.
Yana hanyarsa ta tafiya Hajiya ta kira shi wai zata shigo da dare akwai magana mai muhimmanci da take son suyi, shi dai da to kawai amsa mata ba dan ransa yana cikin daɗi ba, ya faka a rabar gidan ya fito jiki ba ƙwari ya shiga ciki.
Tun a falo gabansa ya soma faɗuwa jin sautin kukan Kalsoom, da sauri ya karasa ɗakinta, sai dai kamin ya shiga ya ji ba acan kukan yake fitowa ba, a ɗakin su Ezzah ne. Ƙarasa yayi ɗakin ya tsaya daga jikin ƙofa yana kallonta. Juyowa tayi ta kalleshi da idonta da suka yi ja saboda kuka.
“Haƙiƙa ina son ka Hilal, dukan abunda ya dangance ka ina sonsa ko da kuwa abun nan mai cutar da ni ne, miyasa zuciyarka ta yarda na aikata bayan ban aikata ba? Ka raba ni da ƴaƴanka Hilal bayan yanzu sun zamo jinin jikina, ban aikata abinda kake zargina da shi ba Hilal Wallahi ban aikata ba”
Ya rumgume hannayensa yana mai jingina da jikin ƙofar.
“To waya aikata?”
“Ban sani ba, amman na rantse maka da Allah ban aikata ba, idan har na aikata Allah ya isar masa ya saka masa, kuma ya bayyana gaskiya”
Jikinsa yayi sanyi sosai, yasan ba zata yi ma kanta wannan mugun furucin ba. Kasa cewa kamai yayi sai kawai ya juya ya nufi ɗakinsa. Saman gado ya zauna, ya dafe kansa dake masa wani zafi.
Jin yayi ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ɗagowa da zai ya ga hannunta rike da ƙur'ane da dukan alamu rantse masa zata yi. Da sauri ya tashi ya ƙarasa inda take.
“No need Please ki aje ƙur'anen nan Kalsoom”
“Rantse maka zan yi Hilal ko zaka yarda da ni”
“Na yarda da ke aje please”
Bata son musa masa, sai kawai ta aje ƙur'ane saman durowarsa tana kuka. Rumgume ta yayi tsantsan a ƙirjinsa ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya.
*NAMRA POV.*
Tun lokacin da Asim ya bata 500 yace tayi cefane bata dake saka shi a idonta ba, kullum idan ta kira zai ce mata aiki ne ya sashi gaba, yau kusan kwana uku kenan.
Ita kam abun duk yabi ya dame ta, musmman yanzu da take ɗan samun sakewa da shi sai kuma aiki ya ɗauke masa hankali.
Sai dai kwana biyu bata jindaɗin jikinta, yawun bakinta ya kan canja ɗanɗano, ga kasala da take fama da shi, sai yawan amai akai akai, ga ciwon kai.
Sai dai bata kawo ma kanta komai ba, sai hawan jini, duk da bata san alamominsa ba, amman tana jin kamar wannan ba zai rasa nasaba da hawan jinin ba, a iya saninta ta saka roba balle tace ko ciki ne, dan tana jin irin alamomin da ake faɗi na masu ciki. Tun jiya ta ci alwashin zuwa asibiti dan bincika matsalarta gudun kar ciwo yayi mata zurfi a rasa gane kansa, amman Allah be yi ba sai yau. Dan haka da wuri ta shirya ta nemi ƴar fulani data raka ta suje tare, dan bata son xuwa ita kaɗai musamman inda bata saba zuwa ba.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *59*
*RASHIDA POV.*
Ganin Safiya ta fita yasa ta juyo bata tsayawa karɓar maganinba, ta fito gabanta dai faɗuwa yake, saƙe-saƙe take na abinda zata cewa Safiya yau kan ta san kashinta ya bushe, bata da wata mafita sai ta Allah.
Kalle-kalle ta fara lokacin data fito harabar gurin ko zata Safiya amman bata ganta ba, da sauri ta nufi harabar asibitin gurin da tadan tayi parking motarta.
Zagawa tayi ta ɗayan ɓangaren ta buɗe motar sai taga Safiya tsaye tana kallonta, idonta cike da hawaye. Yanzu kan babu kayan ɗazu a jikinta, daman suna saka su ne idan zasu shiga ciki.
Dakewa ta yi tana ƙoƙarin ɓoye tsoro da fargabar dake ranta ta kalli Safiya tana murmushin ƙarfin hali
“Ke baki wuce ba, tun ɗazu nake neman ki fa”
“Ke na zo nema daga asibitin ku nake aka ce kun zo nan ku yi wani aiki”
“Ni...?”
Ta nuna kanta cike da mamakin yadda ƴar'uwarta take ƙoƙarin canja abunda yake a zahiri.
“Amman bayan kin gan ni kin cigaba da tafiya ciki...!”
Ajiyar zuciya Rashida ta sauke a hankali yadda Safiya ba zata ji ba, sannan ta kalleta da fargaba ta ce
“Safiya kar dai kina zargina da wani abu ne? Don't you trust your sister?”
“I trust you but... Me kike nema gare ni?”
“Akwai inda na so ki raka ni, but seems you don't trust me ba sai na je da ke ba”
Bata tsaya jiran abunda Safiya zata sake cewa ba, ta buɗe motar tana mai nuna tsananin ɓacin ranta ita ala dole abunda Safiya ta gani ba shi bane, gaskiya take son canjawa ƙiri-ƙiri.
Da kallo Safiya ta bita har ta tuƙa motarta ya bar harabar asibitin, kallo na mamaki abinda Yayarta take son canjawa, da kuma tunanin abunda ya kawo ta asibiti a hiv unit. Tana ɗa buƙatar bincike dan gano gaskiyar lamarin, dole ne ta bincike ƴar'uwarta, wata ƙila ma tana da masaniya akan Asmee tana da shi.
‘What if ita ma tana da shi fa?’
A zuci tayi furucin tana tafiya, da sauri ta girgiza kai.
“No no A'uzubillahi min shaidanin rajin”
Ƙoƙarin kawar da abin take, dan tana ganin kamar hakan ba zai faru ba, idan kuma har ya faru to sai idan Mijinta ne ya laƙa mata shi, dan bata san yayarta da ɗabi'ar banza ba, sai dai kuma abinda ya tsaya mata a rai tunanin abinda zata faɗi a gida, idan ta faɗi ta tonawa ƴar'uwarta asiri idan kuma ta rufa na su asirin ya tonu.
Tun a cikin mota Rashida ta fara kuka, ganin take kamar asirinta ya tonu, tun da Safiya ta ganta, har kuma ta soma zarginta, idan kuma har ta faɗa a gidan to tasan kowa zai gujeta ne, sunanta zai ɓace haka zai dagula lamarin komawarta gidan Hilal, sannan kowa zai dan dalilin fitar ta gidan, za'asan alaƙar dake tsakaninta da mijin Asmee taren su da Asmee zai lalace, duniya zata san ko wacece ita...!
“Anya zan iya bari wannan abun ya faru? Ya zan yi na hana Safiya faɗa? I can't let her do this, zata saka rayuwata a matsala data tsaka ni a matsala ƙara komai zai faru ya faru”
A fili ta yi furucin, bayan ta faka motarta a harabar gidan, ta ɗan ɗauki lokaci kamin ta buɗe ta fito tana farucin
“Idan Asirina ya tonu ai zaman gidan nan ma sai ya gagare ni, duniya ba zata kawo ƙarshe yanzu ba, i can't let it happen”
Jakarta ta ɗauka ta rufe motar already ta cire hijabin tun a hanya. Sannan ta nufi ciki tana ra saƙe-saƙe a ranta, da tunanin mafita.
Bata bari kowa yaga dawowar ta a gidan ba, saboda bata son a takura da magana ko wani abun na daban, nata ya isheta, har aka yi salla magariba bata leƙa falo ba, sai ana daf da salla i'sha, shima kuma dan taji muryar Safiya ne, sai ta fita ta zauna falo tana ganin kamar idan tana gurin Safiya ba zata iya faɗar komai ba.
Kallonta kawai Safiya take tana saƙe-saƙen faɗar ko a'a, ita kuma taɓa mata kallo ɗaya ta ɗauke kanta tayi kamar bata san da ita ba a zaman falon. Da zaman ya isheta ne yasa ta tashi ta nufi kitchen ta ɗubi abinci ta zo falo ta zauna tana ci ba dan taɓa son cin ba sai dai ta nunawa Safiya kamar babu komai a ranta.
Ita dai Safiya bata ce mata komai ba, bata kuma nuna mata ba sai kallon mbc 2 take, sai dai a ranta ta ƙudiri aniyar sai ta binciki ɗakin Rashida gobe da safe tun da tana rigan kowa fita a gidan saboda aikinta.
Sai da ta gama ci tsab sannan ta tashi ta maida plate ɗin ta sha ruwa, ta wuce ɗakinta, babu komai a zuciyarta sai tashin hankali. Saman gado ta zauna tana mamakin yadda duniyarta ta canja mata lokaci ɗaya, lallai duniya idan ta so ka, kai wawa ne, idan kuma ta ƙi ka, ka shiga uku, kai ne ya kamata ka ƙi ta a lokacin da take so ka, take zaurencen ka, ka so ta a lokacin da take ƙin ka, tana nuna maka kai ba kowa bane, ta haka zaka gama rayuwarka ba tare da ta yaudare ka ba.
Hawaye take, irin hawayen da baƙin cikinsu kan hana kuka fita, makomarta kawai take tunani ta san ko yau ba, wata rana zata samu kanta a irin wannan rayuwar da take gudun shiga, dan tasan asirita ba zai cigaba da rufuwa ba har abada.
“Na yi dama wallahi, duk wannan Alh Bashir ɗin ne yaja min, laifin Asmee ne ita taje ta ɗibo a wani gurin ta saka mana, wallahi duk na shiga matsala ita sai ta shiga, sai na sata a matsala”
Kaɗan-kaɗan take rera kukanta dan bata bukatar kowa ya ji, yau ma ya zame mata kamar ranar da Hilal ya sake ta, har garin Allah ya waye babu abunda take tunanin sai rayuwar da ta yi a baya, yadda take farkawa a gidan, ta wuni da Hilal sahibin ruhinta, yau kuma duka babu wannan, wacan rayuwar ta zamar mata kamar mafarki.
Wani abu taji ya tsaya mata a ƙahon zuciya ya yana numfashinta tafiya dai-dai har tayi salla asuba. Haƙiƙa wanda Halal be wadata shi ba, to Haram ba zai wadatar da shi ba, ko da kuwa ya wadatar da to ya aure shi ne na ɗan wani lokaci ya sake shi, a lokacin ne zai gane illar abinda ya aikata. Zina ya zama ruwan dare yanzu babu matan aure babu budare, an maida abun ado, wasu har gobe suna cin ribar abun saboda Allah yayi musu istijira'i na ɗan wani lokaci, kamin su haɗu da shi, wasu kuma tun a duniya Allah zai bayyana su. Da yawa sun ɗauko ƴaƴan da bana miji ba an kawo ciki gida walau ta gurin bin bokaye ko kuma ta gurin aiki ko abokan banza, shiyasa zaka ga yara suna kashe iyayensu ko kuna musguna musu ko suna wani abu da bae dace ba, wanda abu ne mai wahala ɗan halak ya aikata haka. A social media ma yanzu zina ake macen aure ta kawo wanda ba muharraminta ba gidan mijin ta,, gidanta na sunna, har ta jashi su aikata alfasha. Wasu akan yi musu lamani kaɗan, wasu kuma da yawa, sai dai babban tashin hankali gurin haɗuwa da Ubangijin ka...!
Sai a yanzu ta soma nadamar abunda ta aikata, sai dai nadamar bata yi tasirin yanke kuɗirin dake zuciyarta ba, na komawa gidan Hilal, ta yarda asirinta ya tonu amman a gidan Hilal, ta yarda ta kauce dukan hanyar da zata kauce inda har zata koma a gidan Hilal.
Bayan ta yi wanka ta shirya cikin atamfa pink color ta ɗauki mayafinta ta yafa sannan ta ɗauki handbag ɗinta, bata tsaya karyawa ba ta fice, daman ko ta tsaya ba zata iya cin komai ba. Kai tsaye gidansu Teema ta nufa ita kanta tayi mamakin sammakon data dako mata tun da safe, sai ta shirya ta karya sannan Teema ta faɗawa Iyayenta wai zata raka Rashida gidan Rasuwa, sannan suka fita.
Rashida take driving Teema na nuna mata hanya har suka isa garin ɗan-ƙane, cikin dajin suka kai kutsawa har suka isa gidan mutumen. Wannan kan ba'a kira sa da malam ba sai dai boka, dan babu komai a jikinsa sai walki da fatu, irin arnanan ne na kaduna masara imani waɗanda zasu iya aikata komai ba tare da fargaba ba.
Sun tarar mutane da dama, cikin har da ƴan siyasar da Rashida ta sansu, da kuma wasu matan manya, inda Allah ya taimake ta ta saka niƙab ba kowa ne zai gane ta ba.
Sai da mutane da ke gabasu suka gama shiga, sannan suka shiga a lokacin sun cin ma layi.
Irin kayan tsafe-tsafen da ta gani yasa gabanta faɗuwa, har da wani ƙaton madubi baƙi an masa rubutun larabci da jan jini. Cikin fargaba da tsoro ta zauna gaban bokan tana kallon walkin dake jikinsa.
Zata fara bayani ya ɗaga nata hannu.
“Bana buƙatar ki faɗa min komai, ni zan baki labarin duniyarki, sai dai idan baki son kowa ya ji zamu iya sallamar ƙawarki”
Ta jidaɗin maganarsa dan har ga Allah bata son Teema ta ji sirrinta, dan daga ganin wannan mutumen ba zai ɓoye komai ba.
Ba tare da tace ba, Teema ta tashi ta bar mata ɗakin.
Shi wannan bokan da jini yake duba a maimaikon ƙasa da wasu suke yi da ita, sai da yayi rubuce-rubucensa sannan ya dubeta ya ce
“Auren ki ya mutu, saboda mijin ya gano kina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki, kin yi asiri wa kishiryar ki da take gidan mijinki ya faɗawa ɗan ki! Wata ƴar'uwarki na daf da shirya miki wani abu, akwai yiyuwar ki koma gidan mijinki amman idan har kin yarda ki daina salla azahar na tsawon sati ɗaya, tabbas buƙatar zata biya, idan har kika zake jefar abokiyar zaman ki to buƙatar ki zata biya zaki same ta, amman akwai yiyuwar jifar ta dawo kan ki, haƙiƙa baƙin duhu yana bibiyarki, wannan baƙin duhun baƙar rana ce...!”
Da sauri Rashida ta miƙe tsaye tayi baya-baya tana kallonsa tashin hankali ƙarara a fuskarta. Bata iya ce masa komai ba ta fice daga ɗakin kamar wacce ta ruɗe. Tana fitowa hannun Teema kawai ta kama ta jata tana hawaye suka fice daga gurin. Teema na tambayar lafiya amman Rashida bata tsaya faɗa mata komai ba, ta shiga motar tayi mata key ganin hakan yasa Teema ta shiga gidan gaba, kamar za su tashi sama haka Rashida ta riƙa tuƙin motar suna ratsa dajin, har sai da Teema ta riƙa ta tana girgizawa, sannan ta dawo hayyacinta har ta rage gudun ta faka gefen titi tana kuka.