A gidan Hajiyarsa ya zauna har dare, sai da kowa ya watse sannan ya shiga sallama da Hajiya zai mata sai da safe.
Wani kallo uku saura kwata ta yi masa iron kallon Namijin da be san ciwon kansa ba, ƙasan carpet ya zauna kansa a ƙasa yana mai nuna mata tsantsar ladabinsa.
“Ban yarda ku kwana daki ɗaya da matar nan ba, kai dai ba jahili ba ne tun da kasan babu aure a tsakanin ku a yanzu”
Ba tare da ya ɗago kai ba ya ce
“Amman musulumci ya yarda da zaman idda, Hajiya zan bi duk wani umarni na ki, amman dan Allah karki gina katanga tsakanina da matana wallahi ina son ta”
“Kai wawaye Hilal, baka iya son mata ba, kana zurfafawa har ya zama baka iya ganin laifinta, ba zan gina katanga tsakanin ka da matar ka ba, dan ni ba irin surukar nan ba ne, amman zan nisanta ka da ita har sai ta gane kuskurenta ta yadda gaba ko ance ta aikata ba zata aikata ba, kuma ya zama dole ka ƙara aure!”
Ajiyar zuciya ya sauke still be ɗago ya kalleta ba, sai dai ransa be masa daɗi ba akan kalamanta.
“Zan yi duk yadda kika ce Hajiya, ke na fara sani kamin na san kowa a duniyar nan, ba zan zaɓi wata akan ki ba”
“Allah ya yi maka albarka, zan nema maka matar da zaka aura da kaina inshallah mai mutunci”
“Consider it done Hajiya, mu kwana lafiya”
Miƙewa ya yi tsaye idonsa sun rine sun yi ja sosai, irin ran maza ya ba ce sosai.
KALSOOM POV.
Tun da kowa ya watsa aka barta ita kaɗai sai duk ta ji babu daɗi ga kuma danuwar data saka ta gaba, tana ji a jikinta Hajiya ba zata barta ta zauna da Hilal ba. Haka ta zauna ta ci kukanta tun tafiyarsu har dare bata aikin komai sai kuka.
Tana jin tsayawar motar Hilal gabanta yayi dakan uku-uku. Ji take kamar ya zo mata da wani sabon abu, jin take kamar wata maganar zai faɗa mata wacce kunnuwanta ba zasu iya ɗauka ba.
Bata ƙarasa tsorata ba, har sai da ta ga ya ɗauki tsawon lokaci be shigo cikin gidan ba, hakan yasa ta unƙura cikin rashin kuzari ta miƙe tsaye, ta fito falo. Zaune ta same shi saman kujera ya haɗa kan sa da gwuiwa.
Ta ji babu daɗi sosai, sam bata jin damuwarta, ta sa damuwar take ji, bata san me Hajiya tace masa ba, amman a yanayin yadda taga mijinta ta karanci damuwarsa, duk abunda Hajiya zata ce mata ba zai wuce akan zamanta gidan ba, ko kuma wani abun daya shafe ta.
Juyawa ta yi zata koma ciki, sai kawai ta ji muryarsa ta daki dodon kunnenta.
“Ɗauko mayafin ki zamu je gida mu yi na su Momi bayani”
Bata juyo ba, ba kuma amsa masa ba, sai kawai ta cigaba da tafiyarta, hawayen na bin fuskarta.
Hijabinta yana kusa da gadonta, amman tsabar hankalinta baya jikinta haka ta bi tufafinta ɗaya bayan ɗaya bata ga Hijabin ba, sai kawai ta bude wardrobe ta ɗauko wani, Sannan ta ɗauki wayarta, ta handbang ɗin ta ta fito hawaye na cigaba da bin fuskarta.
Kamar mai koyan tafiya haka ta fito daga ɗakinta zuwa falo, shi kuma har lokacin yana nan zaune a yadda ta bar shi. Zuwa tayi ta tsaya bayansa tana hawaye.
Be yarda ya haɗa ido da ita ba, sai kawai ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa ba tare da ya ce da ita komai ba.
Sai da ya yi ma motar key sannan ta fito daga falon ta shiga gidan baya, ja fisgi motar da ƙarfi, mai gadi na buɗe masa gate ya fara gudu kamar zai tashi sama. Shesshekar kukanta ne yasa ya rage gudun da yake ya faka gefen titi. Ya juyo ya kalleta.
“Try and cry so that i can tell you not to cry, Na fi ki shiga damuwa Kalsoom, ga damuwa na ga na ki ga na Hajiya ga na ƴaƴana ga na rashin yaro na duk ni kaɗai. Ba ki san waye Hilal ba shiyasa kike damuwar kan ki, yanzu haka za muje gida kina ciki damuwa da kuka? Kuka ba komai yake ƙara min sai karya min gwuiwa”
Be jira abunda zata ce ba, ya hau ttiti ya cigaba da tuƙa motar a hankali, har suka isa estate ɗin su. Gabanta ya faɗi sosai lokacin da ya danna horn a ƙofar gidansu.
An ɗan daɗe kamin a buɗe musu gate ɗin kasancewar a lokacin goma da ɗan gota, daman can a al'adar gidan da tara ta yi suke rufe gate.
Sai da mai gadin ya fara buɗe gate ɗin ya leƙo su ya ga su ne sannan ya koma ciki ya buɗe musu gate ɗin. Nesa da motocin gidan ya faka motarsa sannan ya jingina kansa jikin sitarin motar yana karanto irin bayanin da zai ma Daddy har ya fahimta.
“Ni ce zan faɗa musu komai?”
Dagowa ya yi ba tare da ya juyo ba ya ce
“Ta wace fuska?”
“Ta fuskar da za su fahimta, ka jira ni a nan”
Gefen hijabinta ta saka ta ƙara goge fuskarta sannan ta buɗe motar ta fita. Ita kanta tana fargaba yadda zata faɗa musu tun da ba magana ba ce mai daɗi, sai dai basa buƙatar a ɓoye musu komai. Ta daɗe tsaye jikin ƙofar falon tana tunani kamin ta tura ƙofar ta shiga.
Sallama tayi can ƙasan maƙoshinta, muryarta a dakishe alamar kuka ya kamata, babu kowa falon kuma kayan kallo a kashe, hakan ya tabbatar mata da sun shiga bachi ko kuma ƙannenta suna can suna karatu. Sai kawai ta juya ta fita daga falon ta nufi falon Dady.
Tun daga bakin ƙofar falon ta jiyo muryar tv, da alama yana kallon labarai ne.
“Assalamu alaikum”
Ta faɗa a daƙishe, haɗa baki suka yi gurin amsa mata. Duk da mamaki suka kalleta Momy ta aje plate ɗin abincin dake hannunta.
“Kalsoom shigo mana kika tsaya jikin ƙofa kamar baƙuwa”
Shigowa ta yi tana kuka, ta zauna kasa tana duƙunƙune fuskarka. Kallon natsuwa Dady yayi mata kana yayi gyaran murya ya ce
“Idan kin jin wani abu ne ya shiiga tsakanin ki da mijinki kuma ke ce mai laifi kar ma ki soma ba mu labari”
Cikin muryar kuka ta ɗago kai ta kalle shi
“Ba ni ce mai laifi ba, kuma Hilal ba shi da laifi, mahaifiyarsa ce ta saka ya sake ni”
Momi ta dafa ƙirjinta.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Dady kuma ya rumtse ido yana sauraren yadda maganar ta daki dodon kunnensa.
“Me kika mata?”
Momi ta sake tambaya.
“Wallahi ban mata komai ba, saboda mutuwar Rafiq ne”
A nan ta kwashe labarin duk abunda ya faru ta faɗa musu, sai da ta kai aya, sannan Dady ya kalleta ya ce
“Je ki shigo da shi”
Ba musu ta tashi tana kuka kamar ta shure ta fita. Hilal na tsaye jikin mota ta fito, yadda ya hango ta zuciyarsa ta nasalta masa bata faɗa musu gaskiyar abunda ya faru ba.
“Dady ya ce ka shigo”
Ta faɗa tun kamin ta ƙaraso kusa da shi, sai kawai ta juya, shi kuma ya rufa mata baya, zuciyarsa cike da zullumi.
Jimmm yayi lokacin da ya isa bakin ƙofar falon, sannan ya shiga da sallama yana mai sadda kansa ƙasa. Can jikin ƙofa ya zauna dan baya jin sakewar da zai ƙarasa kusa da su ya zauna.
“Kalsoom ta faɗa mana komai, kuma ba mu ga laifin ka ba, ko nine kwatankwacin abunda zan aikata kenan”
Cewar Dady. Hilal ya ɗan ɗago kaɗan ya ce
“Fushin Hajiya na ɗan wani lokaci ne, nan gaba kaɗan zata sake, shiyasa na ce za tayi zaman idda acen kamin Hajiya ta yarda na mai da ta”
Dady ya gyara zamansa, yana yi ma Hilal kallon hankali da kamala.
“Hilal ina son ka kasance mai haƙuri a duk halin rayuwar da ka tsinci kan ka. Kalsoom zata koma gidan ka amman ba yanzu ba, zata zauna a nan har sai lokacin da Hajiya ta ce ka zo ka tafi da ita, kuma ina mai baka shawara ka nemi matar da mahaifiyarka dake jin hankalinta ya kwanta da ita ka aura”
Da sauri Hilal ya kalli Dady
“Amman Dady bata hana....”
Dady ya ɗaga masa hannu.
“Ni a ɗana na ɗauke ka, kuma ba zan baka shawarar da zata cutar da kai ta cutar ƴata ba. Ka ɗauki shawarata kawai”
Maida kansa ya yi ƙasa.
“Amman Dady ita Kalsoom ta yarda?”
Dady ya kalli Kalsoom da ke kusa da Momi tana aikin kuka ya ce
“Zata yarda, ai tasan mahaifinta ba zai mata abunda zai cutar da ita, ka tashi ka je kar dare ya yi maka, ke kuma ki wuce ɗakin ƴar'uwarki”
Ita ce ta riga tashi ta nufi hanyar da zata sadata da ɗakunan tana kuka. Hilal kuma ya miƙe tsaye jikinsa a sanyaye ya bar falon, zuciyarsa na raya masa Dady yayi fushi ne shiyasa har ya yanke wannan shawarar.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *67*
Rasa ya yi inda zai sa kansa, gaba ɗaya ganin yake gabas da yamma sun haɗe masa, musamman ma daya dawo gida.
Sai tunani ya taru ya yi masa yawa, wanka daya saba yi kamin ya kwanta yau kam be yi ba, ko kayan jikinsa ma be damu ya canja ba haka ya hau gado ya kwanta, bachi ya ƙwauracewa idonsa gaba ɗaya, har safe be rumtsa ba, sai juyi yake kan gado.
Biyar da rabi na safe ya yi sallah asuba, bayan ya gama tasbihinsa ya ɗauko alƙu'ane ya buɗe ya fara karatu.
Ƴar ƙara wayarsa ta yi alamar saƙo ya shigo, sai dai be duba wayar ba, har sai ya gama karatun nasa yayi addu'ah sannan ya maida ƙur'ane mazauninsa ya aje. Kayan dake jikinsa ya cire ya ɗaura tawul ya shiga wanka, ya daɗe zaune a bathroom ɗin sai tunane yake kamin ya samu kuzarin watsa ruwa ya fito. Cikin rashin daɗin rai ya shirya, Farar shadda ya saka, be damu da duba kansa ba a madubi ba, ya saka agogon hannunsa tare da hulla, sannan ya ɗauki wayarsa yana duba ya nufi ƙofa,
Tunawa yayi da be saka turare ba hakan yasa shi ya dawo ya saka turaren sannan ya fice.
_Ka yi blocking ɗin number na, ka raba ni da ƴaƴana, Hilal ka ci amana ta, ina roƙon ka alfarma, dan Allah dan Manzon Allah ka bar ƴaƴa su dawo a gare ni su ne kawai gata na_
Yana karanta saƙon yasan daga inda ya fito duk da ba number ba ta bace. Wani godon tsaki yaja.
“Duk halin dana shiga ke ce sanadi Rashida”
Sai da ya yi deleted ɗin saƙon sannan ya buɗe motarsa ya shiga. Ya ɗauki hanyar da zata kai shi gidan Hajiyarsa.
Be iso mutane sosai a gidan ba, kasancesar Safiya ne, kuma mutum na ƙaramin yaro ɓe ba babba ba, ita kanta a lokacin da ya shiga cikin gidan tana can cikin ɗakinta tana shiryawa.
Guri ya samu a falonta ya zauna, yana kallon tv duk da hankalinsa baya gurin, ɗai da ɗai ƙannensa da mutanen gidan suka riƙa shigowa suna gaishe shi da yi masa ya haƙuri, shi kuma yana amsa musu kamar an cilasta masa.
Sai takwas saura Hajiyaraa ta fito daga ɗakinta. Ta yi mamakin ganinsa a falon kamar wani baƙo mutumen da ya saba shiga har ɗakinta idan ya shigo cikin gidan.
Ƙarara Hajiya ta ga damuwa da rashin bachi a idon ɗanta, ba ta yi mamaki ba, daman can ta tsammaci haka, sai dai ita aabunda yake duba mas ba shi yake hangowa ba.
“Hajiya ina kwana”
Ya gaishe ta ba tare da ya ɗaga ido ya kalleta ba.
“Lafiya ƙalau ya haƙurin mu?”
“Alhamdullah”
“Ka yi haƙuri Hilal haka rayuwa take zuwa wani lokacin, kai taka ƙaddarar ta rashin mata na gari ne, ta ɗayan ba daɗi wannan ma ba halin ƙwarai, amman inshallah zaka ji daɗi, zan nema maka mata mai hankali da ladabi, mun yi magana da mahaifin ka ma, da ba dan wannan gaisuwar ba da kaje ka ganta, dan bana son auren ku ya wuce wata biyu ko uku ba, yarinyar ƴar gidan mutunci ce”
“Duk yadda kika ce Hajiya haka za'ayi amman ina roƙon alfarmar zan je aiki idan da dama a yi addu'ah yau, tun da yaro ne kuma daman can sunna bata koyar da mu wannan zaman kwana ukun da ake ba....”
“Eh Mahaifinka ma yayi wannan maganar amman naga tun da kwana uku ne, kuma kaga yanzu kwana ɗaya ya rage ai ƙara ka yi haƙuri kawai,amman kai zaka iya juwa aikin ai”
Kamin yayi magana sai ga Ezzah da Ulfah sun fito cikin shirin makaranta, da gudu suka zo suka rumgume shi.
“Dady i miss you”
Ulfah ta faɗa. Ita Ezzah sai tasa kuka.
“Dady shikenan Rafiq ba zai dawo ba?”
Kansu ya shafa cike da ƙaunar ƴaƴan nasa, da kewarsu kamar ba jiya ya rabu da su ba.
“Kin taɓa ganin wanda ya rasu ya dawo? Sai dai ki yi masa addu'ah”
“Ni kam i hate Anty Kalsoom ita ta kashe mana Rafiq”
Ya buge mata baki kaɗan.
“Kar na sake ji, akwai mai kashe wani bayan Allah ne? Kar bakinki ya sake irin wannan furucin”
“Dady wallahi ita ce ta kashe shi”
Ulfah ma ta faɗa, ta fuskanta kamar za ta yi kuka.
“Kuje driver na jiran ku zaku je school”
Hannu yasa aljihu ya ciro dari biyu ya mika musu, suka karɓa da far'ah suna godiya.
Da kallo Hajiya ta bi su har suka fice sannan ta ce
“Ni wallahi tausayi suke ba ni, shiyasa nake son ka auri yarinyar nan dan ga alama tana da natsuwa zata kula da su”
miƙewa ya yi tsaye yana dai-daita hular kansa.
“Zan leƙa office, idan na gama abunda na ke zan dawo”
“Amman ka karya kuwa?”
“A a zan karya a can”
“Allah ya tsare amman da ka tsaya ka karya a nan dan na san a can ba komai za ka ci ba”
“Zan ci”
Daga haka yasa kai ya fice, ransa a jagule.
NAMRA POV.
A ɗakin ta wuni har yamma, tun tana kuka mai hawayen har hawayen suka daina zuba, sai dai tayi kukan kawai babu hawaye.
Gaba ɗaya yanzu hankalinta ya tattara ya koma gida, tana kewar ƴan'uwanta sosai, duk da tadan itace bata kyauta musu ba, sai dai tana jin son mahaifiyarta a ranta tana kewarta.
“Bana jin ina daga cikin masu daɗewa a duniya, ina ji kamar mutuwa ta tana kusa da ni, ina da bukatar ki Mama, Abbah ka yafe min na tuba”
Magana take da kanta kamar wata taɓɓabiya. Miƙewa ta yi tsaye ciki da ƙargin hali dan bata jin karfi sosai a jikinta, fitowa ta yi waje, tana sun sun da kai kamar mai jin kunyar kallon inda su Neina suke.
“Ba wuta ai ƙara ki fito nan kam ki sha iska”
Neina ta faɗa tana gyara mata gurin da zata zauna. Ita kuma har ga Allah kunyar haɗa ido takw da Lamido balle kuma ta zauna inuwa ɗaya da shi.
“Zo ki zauna mana, jiri zai iya ɗaukar ki idan kina tsaye”
Ya faɗa ganin yadda ta tsaya a bakin kofar kamar ba zata zo ɗin ba, sosai gabansa yake faɗuwa, har murƴarsa na ƙoƙarin gargadar a maganar da yake mata saboda faɗuwan gabansa da ya tsananta.
Tana fara takawa gabansa ya fara fisgarsa yana wani zillo, da zaka tsaida idonka a lokacin da kyau a ƙirjinsa zaka ga yadda zuciyarsa take bugawa. Saurin ɗauke kansa ya yi daga kallo tafiyarta da yake kamin ta ƙaraso kusa da su.
Tana ƙaraso gurin sai kawai ta ɗauki filon da Neina ta aje mata, ta kalli Uwani ta ce.
“Dan Allah dan duba cikin jaka na akwai waya sai ki ɗauko min”
Ba musu Uwani ta tashi nufi ɗakin. Bata ɗauki tsawon lokaci ba ta fito da wayar a hannu ta miƙa wa Namra.
“Na gode”
Ta faɗa sai ta juya da zimmar komawa.
“Ai da kin zauna a nan”
“A.a daman wayar kawai nake son ɗauko wa”
“Zauna a ɗakin kawai, make yourself comfortable”
Kai kawai ya iya ɗaga masa, ta juya ta koma cikin ɗakin. Zaunawa ta yi tana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta kafe wayar da ido kamar mai shakkun kunnawa.
Can dai ta kunna wayar zuciyarta cike da fargaba, da tunani kala-kala. Gabanta ya soma faɗuwa lokacin da saƙwanni suka riƙa shigo mata bayan ta kunna wayar. Sai dai mafi yawanci su duka na Mtn ne, sai saƙo ɗaya mai ɗauke da number Yasmeen. Saƙon ta fara buɗewa, tana tunanin wane irin saƙo ne Yasmin ta aiko nata.
_Salam Namra na haihu na samu baby girl, na kira wayarki ban samu ba_
Murmushi ta yi tare da hawaye a lokaci ɗaya.
“Allah ya raya miki babyn ki, ya baki lafiyar shayarwa”
Shine furucin da tayi a fili, ta rumgume wayar ta lumshe ido.
‘Ya kamata na koma gida, ko me me zai faru ya faru a can, na yi kuskure tun farko da ban sauka gidan mu’
Tunanin da take a ranta kenan, kamin ta buɗe ido, ta fara kallon ɗakin.
“Gobe... Gobe ya kamata na je gida, an cire duk wani fargaba da yake rai na, zan cire tsoro zan gwada ƙarɓar sunana ko Alƙah zai za na dace, ba zaka taɓa winning ko losing ba matuƙar baka taɓa gwadawa ba, i hate to try”
A fili ta yi furucin zuciyarta cike da yaƙinin lallai zata iya, kuma ta shirya fuskantar ko wane irin hukunci na Abbah.
“Taya zai yafe min idan ban je ba? Taya zan shirya da Anty idan ban je ba? I have to do this, Allah ka taimake ni”
Komawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.
ABDOOL POV.
“Lafiya ƙalau aka ɗaura aure”
“Mashallah Allah ya nuna mana na ka, ya maka albarka”
“Amin Mai Martaba”
“Ka yi kyau sosai, ka fito kamar wani babban sarki”
Kallon Mamaki Abdool yayi kamar ance masa Mai Martaba yana tsaye gabansa.
“Waya faɗa maka?”
“Babu ruwanka, ai har hoton ka an turo min alkyabar ta karɓe ka sosai”
Dariya yayi cike da mamaki, dan shi dai be san ya ɗora hoton daya saka alkyaba ba a media balle yace ko wani ne ya tura masa.
“Mai martaba kasan ance informer hukunsu ɗaya da da mai fashi da makami ko”
“To ayi haƙuri Major ayi haƙuri muma muna kan aikin mu ne”
Ƙyalƙyalewa yayi da dariya daga shi har Mai Martaba, daga bisani Mai martaba ya ɗora da.
“Ƙarfe nawa zaka ta so?”
Shiru yayi kamar mai tunani, haka kawai ya samu kansa da rashin jindaɗin tafiyar.
“Zan turo maka dogarawan ka sai a bar min Sadauki, zamu kwana biyu kamin mu dawo”
“Why?”
“Just kawai ina son ganin kaduna ne, kasan rabo na sa kaduna since... I can't even remember”
Ya ɗan sosa kansa yana kallon titi da mutake ta kai kawo suna sha'aninsu.
“Fine as you wish, amman aikin ka fa”
“Mun samu hutu ai ko ka manta?”
“Haka ne, to ba matsala amman dai karka ɗauki lokaci i have surprise for you”
“Thank you super Dad”
Daga haka ya kashe wayar ya kalli Sadauki dake front seat ya ce.
“Mai Martaba ya ce sauran za su iya kama hanya yanzu kai kawai zaka tsaya sai jibi za mu koma”
“An gama Yarima, Allah ya ƙara maka lafiya”
Be amsa ba sai kawai ya maida hankalinsa kan titi. Can kuma ya kalli agogo hannunsa.
“Yaushe zamu isa Kaduna?”
“Allah ya taimaki Yarima, nan da minti goma sha biyar zamu isa”
Daga nan be sake cewa komai ba har suka isa masaukinsa. Su suka buɗe masa mota ya fito suka rufa masa baya suna masa kirari, iya ƙofar falon suka tsaya. Sai ya juyo ya kalli Sadauki ya ce.
“A ba ko wannensu 30k kai kuma ka shirya anjima zamu je mu duba marar lafiyar nan”
“An gama Yarima, takawarka lafiya ɗan sarki jikan sarki, an gama ɗan adalin Sarki”
Sai da ya shige sannan suka janyo ƙofar suka rufe masa. Alkyabar jikinsa ya fara cirewa sannan ya buɗe maɓallan rigarsa, ya kishingida saman kujera, ya lumshe ido.
Tun da ya shiga ciki be fito ba sai da aka yi kiran sallah magariba daman basu baro zariya ba sai da aka yi la'asar.
Tare da Sadauki suka yi sallah a masallacin da ke kusa da gidan, sannan suka nufo gida. A hanyar su ta dawowa ne Abdool yake masa jan kunne.
“Bana son abunda kake min, karka sake ɗauko min takalmi ka aje min, kuma daga yau kar na sake jin wani kirari nawa a bakin ka, ka kira ni da Abdool kawai ko Yarima amman ba sai ka min kirare ba”
“Allah ya taimake ka za a daina”
Ya faɗa cikin girmamawa.
“Zaka iya tuna inda muka je gidan mai Napep ɗin nan da muka kaɗe?”
“Allah ya taimake ka, zan gane”
“To za mu koma mu duba shi, akwai canji a hannunka ko? Zamu siya musu fruits”
“An gama Yarima”
“Zan shiga na canja sai muje”
“A canja da kyau ɗan Sarki, Allah yaja zamanin ka”
Kallo ɗaya Abdool yayi masa ya kauda ido yana girgiza kai.
******************
Bayan salla magariba Uwani ta shigo ɗakin ta kunna mata kendir, ta aje mata maltina da Madara da kuma tea mai kauri, tare da biredi.
“Kuma ɗawainiya da ni na gode sosai”
Mirmushi Uwani ta yi
“Ba komai ai yi ma kai ne. Ki ci dai ki samu karfin jiki”
“Ni kaina ina son na samu ƙarfin jikin ko zan samu damar komawa gurin iyayena”
“Tafiya za ki yi?”
“Gobe na ke so idan Allah ya yarje min”
“Amman ina laifin ko nan da sati idan kin ƙara jin sauƙi?”
“Wata ƙila idan suka ga na samu sauƙi su ƙi karɓa na, amman ganina a hakan zai sa su tausaya min”
“Amman dai da kin yi haƙuri har ki ji sauƙi”
“Ina son tafiyar ne”
“To bari na faɗawa Neina”
Ta juya cikin rashin jidaɗi dan yanzu sun ɗan fara sabawa da Namra, zancen tafiyarta be mata daɗi ba.
“Neina wai kin ji Namra zata tafi”
Abunda ta fito tana faɗa kenan, ganin Yarima yasa ta yi saurin sadda kanta ƙasa jikinta ya shiga rawa.
“Barka da dare”
“Barka...”
Ya amsa kaɗan-kaɗan yana tsaye kan Lamido, dan ya kasa zama tun da ya shigo gidan yanzu ma ya samu kansa da ƙyamar gidan. Farar shadda dake jikinsa sai ƙara haska shi take. Uwani ta yi mamakin ganin sa ba dogorai, sai dai haka be hana ta gane shi ba.
Unƙurawa Lamido yayi ya tashi zaune daga kwance da yake, dan zuwan Abdool be sashi ya ɗago ba duk da cika masa ido da yayi, da kuma kwarjinin da ya yi masa, yana jin rashin sakewa da Abdool wata ƙila saboda ba matsayin ɗaya ba, ko kuma dan kaɗewar da yayi masa ne ya hana shi ganin farinsa sai haushinsa yake ji. A ƙoƙarinsa na avoiding ɗin Yarima ya kalli Uwani da Neina ya ce.
“Wani abu aka mata ne?”
“A'a wallahi sai dai ko ta gaji da zama ne, ko tana son ta koma Katsina ne”
Cewar Neina. Sai Uwani ta amsa da
“A'a wai ta ce tana son ta koma gida ne, ko zasu tausaya mata su karɓe ta, kuma wai gobe zata je, kamar wace ake kora”
“Amman Namra bata da tunani, taya zata koma gurin iyayenta cikin wannan hali?”
“Wlh kuwa, ni ma na ce ta yi haƙuri dai har gaba...”
Tsawa Sadauki ya katsawa Uwani, wanda shi kansa Lamido sai da ya zabura balle kuma Neina da daman jikinta rawa yake, ganin ɗan sarki tsaye a gidansu.
“Ke ƴar talakawa ba a wata magana a gaban Ɗan Sarki, kama kan ki ki iya bakin ki...”
Sosai Uwani ta shiga natsuwarta tsabar tsoro ma har ji tayi kamar ta amayar da hanjin cikinta. Abdool kuma wa watsa ma Sadauki Harara, dan sosai yake jin daɗin maganar da suke, sarau zuciyarsa ta raya masa da Namra ake, duk da bashi da tabbacin hakan.
Tsawar da Sadauki yayi ma Uwani ne yasa Namra ta san da akwai baƙo a gidan dan ta ji muryar da ba ta ɗan gidan ba. Hakan yasa ta aje maltinar dake hannunta, ta gyara tsawyuwar Hijabin dake jikinta ta leƙo ƙofar ɗakin.
Bata gane ko waye ba, bata kuma ta mu da ta sani ɗin ba, sai kawai ta juya ta koma ɗakin. Shi kam Abdool sarai ya gane ta, dan ya daɗe da haddace fuskarta, duk da duhun magariba ya fara saukowa hakan be hana shi gane ta ba.
Ya daidaita tsayuwar hannayensa da ke cikin aljihu, ya juya ba tare daya ce da su komai ba, sai sadauki ne yake musu Allah ya ƙara lafiya, duk suka amsa da Ameen ban da Lamido.
Be yarda yayi ma Abdool kallon banza ba, ko wata yassar magana sai da ya juya baya ya fice.
“Wani zai nunawa isa, girman kan tsiya”
“Aa Lamido karka jawa kanka, dan Allah ka iya bakin ka”
Neina ta faɗa zuciyarta cike da tsoro. Wani wawan tsaki Lamido yaja ya wuyar da fuskarsa zuwa ɗakin da Namra take ciki.
**************
Tafiya yake guda guda yana tsotsar bakinsa kamar mai shan minti. Jinginawa yayi da motar da suka zo, yana kallon Sadauki yana tsaya gefensa cike da ladabi.
“A bincika min baƙuwar fuskar da take gidan nan, wacce ta zo daga Katsina i can't recall her name amman ai ka ji yarinyar da suke magana akai ko?”
“Za a bincika, Allah yaja zamanin ka, ya ƙara maka lafiya”
Wannan karon Abdool da kansa yayi driver zuwa suka ɗauki hanyar masaukinsa, sai tariyar maganar su Uwani yake, yana analyzing.
ASIM POV.
Ledodin dake hannunsa ya dire mata yana sauke gajiya tare da miƙa mata ragowar canji.
“Yayi Kyau Asim kana ƙoƙari sosai. Ya kamata ka hutu kam nima zan je gida na da yake can cikin gari dan yata zata zo, kuma bata san ina wannan sana'ar ba, dole acan nake sauka idan zata zo, dan haka zaka yi hutun kwana biyu sai kaje gurin matar ka ku yi murnar mota ka ɗauke ta kuje gari ku shana”
Ya ɗan yi murmushi tare da sosa kansa, shi kansa ya jidaɗin wannan hutun da zata ba shi dan zai bashi dama ya je gurin baƙuwarsa, kuma daman can yana son ɗaukar Mardiya su fita gari.
“Ai bana da mata Hajiya bana da mata yanzu, ina dai kam nema”
Ta masa kallon rashin fahimta.
“ Kamar ya ba nasan kana da mata ba ada?”
“Eh mun ɗan samu matsala ne, har mun rabu ai”
“Subhanalillahi, kai kam Asim me ya kai ka?mata mai haƙuri da juriya haka? Me ta maka”
“Wlh Hajiya ta cika kwaɗayi ne, ga complain akan aiki nan, shiyasa kawai naga rabuwar ta fi, yanzu dai wata na ke so idan Allah ya yarda”
Idan ran Hajiya Sadiya yayi dubu ya ɓace a yanzu dam bata jidaɗin maganar nan ta Asim ba
“Amman Wallahi sam ba ka yi tunani ba, taya zaka sakin matar da ta rufa maka Asiri har haka, ka gaggauta mayarda matar ka matuƙar tana son mu shirya da kai, ni bana son ana ciwa mace mutuci”
“Wallahi Hajiya bana jin daɗin zama da ita ne, duk ita ce silar halin rayuwar dana shiga, sam arziki na da nata be haɗu ba, daman can ban yi istiƙara ba na aure ta, yanzu muna rabuwa komai nawa ya dawo daidai, arziki sai shigowa yake”
“Na dai faɗa maka, rufin asirin ka ka maida auren ka a yanzu duk inda matar ka take ka yi gaggawar mayar da ita shine kwanciyar hankalin ka, kaje ka yi tunani, ni sam bana son ana wulaƙanta mace akan aure, to kacewa iyayenta me? Sam dam baka da tunani Asim, idan ma akan aikin ka ai da ka yi sahawara da ni dole za mu samu mafita yadda za'ayi”
Miƙewa ta yi tsaye cike da ɓacin rai ta nƴfi ɗakinta. Shi kam Asim da kallo ya bi ta yana mamakin yadda ta haƙiƙan akan Namra kamar wata ƴar'uwata, tunani yake yi da ace ya fada nata gaskiyar rabuwarsu da Namra akan ciki ne wata ƙila ma ranta ya fi haka ɓaci.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *68 NOT EDITED*
Ta ina zai fara neman ta? Taya ma zai je neman yarinyar da yake ganin rabuwa da ita kamar ya huta da ƙaya ne?
“Zata dawo, na san bata je gidan su ai da yanxu an kira ni, amman na san zata dawo gare ni dole, amman neman ta yanzu a gare ni ai aiki ne sabo, kuma zata jidaɗi sosai idan har na neme ta”
Abunda yake faɗa kenan yana tuƙa motarsa a hankali. Wayarsa ce ta yi ringing, da sauri ya ɗauka ganin mai kiran har da murmushi a fuskarsa.
“Hello Babe”
“Hey how are you?”
“Fine i'm just thinking of you”
“Kar ka damu ai gobe za mu haɗu, zaka gan ni a fuska nima na gan ka a fuska”
“I can't wait, me kike so a shirya miki?”
“Na yi waya da Mom nawa zata shirya min komai”
“Ya yi kyau lallai Mom tana ji da ƴar nan ta ta”
“Ai dole ta ji da ni, ni kaɗai gare ta, ko ƙawaye na ma Mom son su take balle kuma ni”
“Wow kai lallai ko zata so miji ki ma sosai”
“Sosai ma”
“Gaskiya na yi sa'ah”
“Sa'ah?”
“Eh mana, ai kin san dole Mom ta so ni sosai, to da ni mijin Nably ne right?”
“Uhnn. Yeah”
“Ko dai ban kwanta miki ba ne?”
“Idan baka kwanta min ba, ai ba zan tsaya ina baka lokaci na ba, ni fa ban ma yarda da rayuwar social media ba amman kai lokaci ɗaya ka shiga rai na sosai wallahi”
“Haka nake so kin san ni da gaske na ke yi wallahi auren ki zan yi matuƙar kika amince min”
“Wannan maganar ya kamata sai idan mun haɗu tukuna mu yi ta”
“To na bari gimbiyata”
“Zan duba abu sai na kira ka”
“Okay i love you”
“Thank you”
Daga haka ta katse kiran. Shi kuma ya mannawa wayar kiss zuciyarsa cike da farinciki dan har ga Allah yana ƙaunar Nabila, kuma ita yake fata ta maza matarsa ta biyu.
Wani tsiririn tsaki ya ja lokacin daya isa bakin gate ɗin gidansa, cox he hate one thing buɗe gate, gani yake a yanzu ya kamata ace buɗe masa ake, shi gaba ɗaya gidan ma ya ishe shi, plan ɗinsa a yanzu na samun sabon gida ne mai rai da lafiya, gidan da duk wanda ya kallesa sai yayi magana ba wannan ƙonanne ba.
Sai da ya fito ya buɗewa kansa gate ya shiga da Motar sannan ya dawo ya rufe gate ɗin. Kusa da BQ ya faka motarsa, ya faka motarsa ya buɗe ya fito, daga shigarsa cikin ɗakunan da suke BQ ɗin sai ya fara ya ƙuna fuska, like yana ƙyama, gurin duk ya yi datti kamar be taɓa zama a gurin ba. Da shigarsa ɗakin first thing da ya fara yi ɗauko murhun gawaye da ragowar gawai ɗin da Namra ta bari, ya zuba masa kanazir ɗin da Namra take kunna wuta da shi ya saka kofinta na roba na ƙyasta ashana, nan ta ke wutar ta kama, kamar an saka mata hetur.
Ƙamin tukunyarta ya ɗauka ya ɗauraye ya zuba mata ruwa, ya ɗora saman wutar sannan ya shiga ciki ya ɗauki tsintsina ya share ɗakin tsab kamar mace, ya ruba zuwa yayi mopping, sannan ya cire tufafin jikinsa ya ɗaura tawul, ya zo ya zube ruwan a roba ya sirka da ruwan sanyi, ya kai ɗaki.
Sai da ya tura kofar ɗakin, sannan ya cire tawul ɗin jikinsa ya zauna cikin robar, kamar wani ƙaramin yaro. Ƙasansa yake gasawa, dan har yanzu zafi yake masa duk da ya sha magani, kuma yana kan sha, amman gurin na masa zafi musamman idan zai duƙa ko kuma zai yi bayan gida.
Sai dai Hajiya ta faɗa masa dan yana sabon shiga ne da ya saba komai ba zai ji ba.
Ya samu kusan minti talatin a cikin ruwa, sannan ya tashi ya ɗaura tawul ɗin ya ɗauki ruwan ya zubar a can waje. Be da mu da ƙorar da tufafinsa na ɗazu suka yi ba, ya ɗauke su a haka ya saka, ya kwanta saman katifa, yana danna wayarsa.
Number Mama ya saka, duk da yana da ita a contact ɗinsa be tsaya nema ba sai kawai ya saka ya danna mata kira.
Ta daɗe tana ringing kamin ta ɗauka tana masa complain
“Ai na ɗauka na manta da ni, ka sake wata uwar”
“Hahha Mama kenan ni na isa duk duniyar nan ai bana da uwa kamar ki”
“Amman Ibrahim ace ko ɗan kiran nan na waya babu, babu aike, babu komai, daga na yi jinyarka ka warke shikenan Namratu ta karɓe min kai?”
“Wallahi Mama kina nan cikin rai na, kawai dai akwai irin da na ke ne, akwai kuɗin da nake jira ina son da na zo zan siya miki gida na nema miki mai aiki, na saka miki komai ba za ki nema ba”
“Ibrahim da gaske?”
“Wallahi Mama”
“Wane irin kuɗi ne wannan? Karka ka jefa kan ka a halaka, garin neman gira a rasa ido, zamani ya lalace tsafi ya yi yawa”
Dariya ya yi dan yasan abunda Mama take tsoro, kamar kar ace tsafi ne a bada ita.
“Ba tsafi na ke ba, kuma ko tsafi na ke ai ba zan bada ke ba, wannan matar data ɗauke ni aiki ce take ba ni kuɗi kuma kullum idan na mata ciniki a shagonta riba uku ake kasawa ita da biyu ni da ɗaya”
“Wane irin sana'ah ne haka?”
“Wayoyi ne mu ke sidawa, da zinari”
“Hahaha Mashallah, ka ga abun Allah ko? Sannu-sannu sai ka fi haka ma, ai ina nan ina maka addu'ah indai kuɗi ne suna nan zuwa”
“A cigaba da yi mana addu'ar nan ai ita cw ke bin mu. Nan da wata ɗaya zan zo gurin ki”
“To Allah ya yarda, ya dafa maka, ɗan Albarka, irin alheri”
Dariya ya yi kana ya ɗora da.
“Zan aiko miki kuɗi ta hanyar Yusufa, zai kawo miki dubu dari da hansi ki riƙe kamin na zo”
“Kai Alhamdulillah Ibrahim Allah ya biya ka yau ɗa na ne yake ba ni wannan kuɗi Allahu akbar...”
Sai kawai ta sa kuka. Shi kuma ya kashe wayar yana dariya, da ganin kuɗin a gare shi yanzu ai ba wani abun ba ne, he past that level, manyan su ma yake hange, he's feeling so high.
KALSOOM POV.
Life goes on yadda take tsammanin rayuwa ba haka ta zo mata ba,tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta kwamtar da hankalinta, 5ana koyar yadda zata yi rayuwa babu abokin rayuwarta, but she can't duk abunda take tunanin sauƙi ne a gareta, sai ta ga ba haka ba.
Duk lokacin da tayi unƙurin danne abunda yake zuciyarta, ta manta da komai, sai ta kasa. Sai yanzu take gane aure rahama ne dan har ta manta da ɗan zaman da tayi na budurci a gidan, sai take ganin kamar yanzu ne ta ke koyon komai, ga maganganun mutane su na ta kai kawo a kunenta, wai ta kashe aurenta ta dawo gida, some people be like daman can irin wayayun ƴan bokon nan basa zaman aure, wasu kuma wai ta kashe ɗan kishiyarta mijin ya sake ta, maganganu dai kala-kala har da na fitar hankali.
Abincin da ta ɗibo ta saka a gaba tana kallo, ta san dai ba iya ci zata yi ba, dan ba ta jin cin komai ga kuma yunwa tana ji, kusan kullum haka take wuni, ta fi son abu mai ruwa sai kuma ɗan furau-furau, wannan abincin ma Momi ce ta cilasta mata ɗibowa wai ko zata iya ci, amman ta kasa.
Ɗaukar abincin ta yi ta nufi falo da shi, da zimmar kai wa kitchen.
“Ba ki ci abincin nan ba ko?”
Cewar Momi da ke zaune saman kujera.
“Wallahi Momi ba na zan iya ci ba”
“Sai yaushe za ki cirewa kan ki damuwar nan ne Ummu?”
“Momi dole na damu, ki duba ko abunda abunda mutanen unguwar nan suke cewa, wai na kore uwar gidana na kashe ɗan ta, ni wallahi da na san haka auren mai mata yake da ban aureshi ba, ni da ma na san haka rayuwar auren ta ke tun farko da ban yi ba”
Ta ƙarasa zancen da kuka. Ajiyar zuciyar Momi ta sauke.
“Na san ba abunda mutane suke cewa ba ne ya fi damun ki, hukuncin da mahaifin ki ya yanke ne ya hana ki sakewa, ina son ki san be yi hakan dan ya cutar da ke ba, sai dan nema miki yanci, ba wai dan ya shiga tsakanin ki da Hilal ba”
Hawayen idonta ta share, ta aje plate ta zauna.
“Ba wai rai na ya ɓace ba ne da hukuncin Dady ,kawai abun yana damu na ne, duk duk yaushe na yi auren nan yanzu ace har na dawo gida, a can gidan auren ma ba wani daɗi na ji ba, matar nan ta hana ni sakewa, ta bi ta fitine ni bayan fitar ta kuma kishi ya koma tsakanin ni da ƴarta, wallahi yaron nan ban san lokacin da ƴa ci guba ba, amman sun ce ni ce na kashe shi, da wanne zan ji? Ga shi mahaifiyarsa ta sa ya sake ni na dawo gida kuma mutanen unguwa sun ɗasa na su gulmar, dole na yi damuwa”
Da kuka ta ƙarasa maganar tana rufe fuskarta. Momy taja wani dogon numfashi ta sauke tana kallon ƴarta cike da damuwa.
“Allah zai saka miki ai zalumci baya ɗorewa, gaskiya zata bayyana sakamakin ki zai fito, kawai ki cigaba da addu'ah kina faɗawa Allah buƙatar ki, zai yaye miki komai”
Kuka ta yi sosai, sannan t tashi ta nufi kitchen ta aje plate ɗin ta fito.
“Ko za ki je gidansu gidan Salma ki ɗan yi fira ko zaki rage damuwa”
Da to kawai ta amsa ma Momi ta nufi bedroom ɗin ta, fuskarta ta fara wankewa sannan ta ɗauki hijabi ta saka ta ɗauki jakarta, ta fito.
“Na tafi”
Ta faɗa murya can ciki.
“Sai kin dawo ina a gaishe ta”
A hankali ta fito daga gidan, tana.fitowa gate ta yi sa'ar samun Napep kasanceqar an sauke wata ne gidan da ke kusa d na su, tara kawai ta yi ta shiga tana faɗa masa ind zai kai ta.
“Sauke ni a nan”
Ta faɗa tun kamin ya ƙaraso kusa da gidan Salma. Naira ɗari ta miƙa mas sannan ta fita daga napep ɗin ta ƙars da ƙafa.
Tun da ta hango gate ɗin buɗe ta fahimci Salma zata fita ne.
A hankali take tafiya har ta ƙarasa harabar gidan. Lokacin da ta isa ƙofar falon si t ki hannu zta buɗe sai ga Mijin Salma ta buɗe ya fito. Ja ta yi da baya tana ƙirƙiro murmushi, tare da gaishe shi, shi kuma ya amsa mata yana gyara hular kansa.
“Lafiya ƙalau Kalsoom ce a gidan na mu!”
“Eh wallahi yau na ce bari na leƙo Salma ne”
“Ayyah gashi bata gida Wallahi ta je suna”
Juyawa ta yi tana faɗin
“Okay idan ta zo a gaishe ta”
“Wuce wa za ki yi?”
“Eh”
“Bari na sauke ki mana, nima fita zan yi”
“A'a zan hau Napep”
“Haba di Kalsoom sai ka ce baƙuwa”
Yayi saurin ƙarasawa gurin motar ya buɗr ya shiga yayi mata key, sannan ya buɗe mata front seat.
“Bismillah”
Bata kawo komai a ranta ba, ta shigaotar tare da mai da ganbun ta rufe.
Tun da suka hau titi bw ce da ita komai ba, ita kuma t tattara duka hankalint tmaid gurin titin. Can ya kai hannu ya kunn fm, sai ya ɗan kalleta kaɗan.
“Kalsoom na ji abunda ya faru kuma sam ban jidaɗi ba, amman ki bar wa Allah komai xai fito miki da haƙƙin ki, ai duk wanda ya san wacece ke ba xai yarda kin aikata ba, wallahi tun da na ji labarin kika ban tausayi sosai, inshallah zaki samu wani na ƙwarai”
“Ai be yarda na aikata ba, laifin mahaifiyarsa ne ita ta saka sai ya sake ni”
Wani guntun tsaki yaja.
“Shi ma dai da laifinsa, ai ba a bin umarnin iyaye a saɓawa Mahalicci, dan wannan saɓawa Allah ne, ni da zaki bi shawara ta da kin bar shi kin fita harkarsa ko da ya dawo, duk da n san kina son sa sosai, amman fa kin san mu maza ba a nuna mana so”
Ya ƙarasa maganar tare da parking a bakin gate ɗin gidan su. Buɗe motar ta yi ta fita tana faɗin
“Na gode”
Ba ta jira ya amsa mata ba, bata kuma waigo ba, shi kuma be bar ƙofar gidan ba sai da ya ga ta shige sannan ya kaɗa motarsa yayi gaba.
ABDOOL POV.
Lemun d ke hannunsa ya aje yana murmushi
“Amman dai Ummi idan ban kira ba ai kamata ki kirana ni kiji ko lafiya”
“Ai na san lafiya, da ba zaka yi shiru haka nan ba, kasa muka shirya maka abinci amman baka zo ba”
“Amman ban ce amin komai ba, indi ba neman a ɗora min laifi ba”
“Yayi kyau, gobe kaga mai sake maka, faɗa min me ya hana ka dawowa jiya?”
“Kawai ina son ƙara ganin garin ne, kin san na daɗe rabona da Kaduna”
“Yanzu yaushe zaka dawo?”
Ya ɗan sosa kansa
“Uhhhh Maybe laraba”
“Allah ya kai mu”
“Amin thank you Ummi”
Ta katse kiran shi kuma ya sauke wayar cike da ƙaunar mhaifiyarsa.
Juyawa yayi ya kalli Sadauki.
“Je ka shigo d shi”
Da sauri Sadauki ya tashi ya fita, Abdool kuma ya ƙarasa gurin window falon yana kallon wani ɓangare na gidan.
Tare suka shigo da Sadauki, bakinsa ƙumshe da sallama. Juyowa Abdool yayi fuskarsa ɗauke d murmushi ya nunawa Mustafa gurin zama. Ba musu Mustaf ya zauna yana miƙa masa gaisuwar girmamawa.
“Lafiya Ƙalau sannu, ya Sunan ka ma?”
“Mustafa”
“Yeah, ka san ni ne?”
“A'a Sai dai na ga fuskar sani”
“Ina son zan baka wanki ne da guga ance kana yi da kyau”
“Ƙwarai ko ai sana'a ta ce”
“A ina kake da zama?”
“Nan unguwar malamai”
Abdool yayi wani abu da kai kamar da gaske he know him.
“Yeah na tuna kai na na kusa da gidan su Lamido ko?”
Mustafa ya washe ba ki jin an ambaci sunan abokinsa.
“Ashe kasan lamido”
“Sosai ɗan'uwan mu ne, ai kwana ki ma wata ƙanwata a gidan ta sauka, yanzu haka wata ma tana nan”
Abdool ya faɗa yana kallon Saɗauki.
“Je ka haɗo masa kayan wanki”
Sai kuma ya mai da hankalinsa gurin Mustafa.
“Ance min yaji ciwo ma ko?”
“Eh Wallahi, wani neya kaɗe shi, ni da yake bana nan sai da y kira ni na ke ji ma, Ai Allah ma ya tsare abun ya zo da sauƙi”
“Idan na samu dama zan je na duba shi”
“Aiko masu kuɗi fitar ku wuya ta ke muku”
Abdool ya ɗauki remote ya canja channel yana hamma kamar gaske.
“Mu ai har zama gidan mu na yi, baka ga baƙuwar fuska ba?”
Mustafa yayi shiru dan ya gano kamar yana bincikensa ne.
“Ina kayan su ke ne?”
Abdool yayi masa wani kallo.
“Za'a kawo”
Sai ga Sadauki ya fito da tufafin da basu fi kala huɗu ba, ya miƙawa Mustafa. Shi kuma yana karɓa y miƙe tsaye. Sai Abdool ya zaro sabin kuɗi a aljuhunsa ya miƙa masa.
“Gashi ko, a wanke da wuri”
Da mamaki Mustafa ya karɓa ganin kuɗi haka da yawa.
“Na gode Allah yasa albarka, gobe zan kawo maka su”
Murmushi kawai Abdool yayi masa as respond, ya bishi da kallo ya har ya fice.
‘Duk wannan ba zai yi ba, kawai naje na samu yarinyar nan na yi magana da ita kawai shi ya fi’
‘Idan kuma ta ƙi ta saurare ni fa?’
Ya ɗaga kafaɗunsa yana cigaba da zancen zuci.
‘Sai na ƙyale ta, ta yi ma kanta’
Miƙewa yayi tsaye ya nufi bedroom ɗinsa.
RASHIDA POV.
HILAL POV.
Yana tsaye jikin motarsa, yana kallon takunta har ta ƙarasa kusa da shi.
“Assalamu alaikum”
Ya faɗa cike da tsananin kunya da tsantsandar da kai.
“Wa'alaikissalam, Teema ko?”
Ta ƙara yin ƙasa da kanta
“Haka ne ina wuni?”
“Lafiya ƙalau ya gida?”
“Lafiya ƙalau”
“Mashallah, sunana Hilal kamar yadda aka faɗa miki Hajiyata ta ce min ta miki bayanin komai, zan zo mu gaisa da ke ne”
“Haka ne, ni kuma sunana Fatima Abdullahi, a nan nake zama ina ƙarƙashin iyayena”
“Mashallah haka yayi kyau”
Ya faɗa 6ana kallom yadda ta zuba hijabi har ƙasa gwanin sha'awa.
“Ba zan tsayar da ke ba, daman na zo ne kawai mu gaisa duk wani labari kamata yayi sai idan mun sake haɗuwa ko”
Murmushin jin kunya tayi ta ƙara ƙasa da kanta.
“A gaida min Hajiya”
“Zata ji”
Ya buɗe motar ya ɗauko ƴar siyayyar da yayi mata ya miƙa mata.
“Ga wannan”
Sai a lokacin ta ɗaga kai ta kalleshi, sai ta yi saurin girgiza masa kai.
“A'a na gode”
Bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta nufi cikin gidansu da sauri dan kar ta karɓi kayan. Shi dai da kallo ya bita fuskarsa ba yabo ba fallasa har ta shige sannan ya ƙarasa gaban ƙofar ya aje mata ya juya.
Cikin wani yanayi ya shiga motarsa ya bar gidan. Har ya isa gidan Hajiyarsa be wani sake jiki sosai ba, shi kansa be san dalili ba, yana jinsa dai kamar cikin wani sabon yanayi.
Da far'ah Hajiya ta tarbesa dan tasan inda ya fito tun da ita ta haɗa masa abunda zai kai mata ma. Bata bari sun yi maganar a falo ba, har sai da ta shiga ɗakinta shi kuma yana biye da ita, bayan ta zauna, ya zauna y soma labarta mata yadda suka yi, farinciki duk ya cika Hajiya.
“Ai yarinyar akwai kirki ga mutunci, ina fatar dai ta maka”
“Ba laifi, umarni nake bi ai”
“Hilal bana son kana abu kamar ina tirsasa ka, ni sam....”
Shigowar Dadyn Hilal ne yasa ta maƙale maganar bata fito ba.
“Amman bn taɓa sanin baki da hankali ba, sai yau, ki kashe mas aure ki sashi neman wani aure? Bayan kin san yana son matarsa? Dan me zaki shiga tsakaninsu? Idan ma aure kike so ai sai kice ya ƙara aure amman ba sai ya saki matarsa ba, ni duk abunda ake ban sani ba, ban ɗauka abun har ya kai ga saki ba sai ɗazu”
Miƙewa tayi tsaye tana kallon Alhaji da ransa ya gama.ɓaci.
“Haba Alhaji, baka ga abunda yarinyar nan ta aikata ba ne? Zata iya kashe yaran nan, shi kansa ma”
“Shi be fiki sanin zafin yaransa ba? Be fiki damuwa da kansa ba? Kar wannan maganar ta sake fitowa bakin ki, idan aure kike so ya ƙara wannan daban amman babu yadda zaki shiga tsakanin shi da matarsa”
Hilal dai be ce Uffan ba har sai da Alhaju ya kallesa ya ce
“Tashi muje gidan su”
Miƙewa yayi tsaye ya bi bayan Alhaji da ya kaɓa rigarsa ya wuce, Hajiya ta saki baki tana kallon ikon Allah.
“Wato maganin yanzu har da ubansa ta yi ma, tayi min ta ga ni be kama ni sai ta koma ga ubansa, to wallahi ni ba ki isa ba, kurwata kur kashede uku lahaula bakwai”
Cikin fushi ta yi furucin tana jin tsanar Kalsoom a ranta.
MARDIYA POV.
Fisgice ta farka tana faɗin
“Innalillahi”
Mafarkin wutar nan da ke zo mata jifa jifa yau ma ta sake yinsa, bama kamar yanzu da har bayanta zafin gaske yake mata kamar ta tsaya kusa da wuta. Sai da ta karewa ɗakin kallo sannan hankalinta ya kwanta ganin inda take.
“Allah ka min maganin wannan masifar, ko minene yake bi na Allah ka kawar mon da shi, idan ma wata jifar ce aka min Allah ka mayar da ita ga wanda yayi ta”
Har da kukanta take wannan maganar dan har ga Allah wannan mafarkin wutar da take ya isheta, kuma ya hanata sukuni.
Kasa komawa bachi ta yi daman duk ranar da ta yi irin wannan mafarkin bata iya komawa bachi, idonta biyu har aka kira sallah asuba, amaimakon ta bari sai ta yi sallah sannan ta kwanta sai kawai ta buge da bachinta, ba ita ta farka ba sai sha ɗaya na safe, ƙirƙiri ta yi sallah azuba babu ko kunya, ko da yake abun ya samo asali ne daga gurin mahaifiyarta da bata tsawata mata.
Tana sallame sallar wayar Asim ta shigo mata, da sauri ta ɗauka tana kwabar da tasbihin da take.
“Hello”
“Good morning Mardiya ya kika tashi?”
“Lafiya ƙalau na yi missing ɗin ka”
“Nima Haka har na so na ɗauke ke ki muje yawo dan akwai maganar da nake son mu yi mai muhimmanci”
“Wace magana ce?”
“A'a ba za tayi a waya ba, kamata yayi sai mun zauna”
“Okay yaushe zaka shigo?”
“Idan na samu time zan kira ki, sai na zo na ɗauke ki”
“Okay ina jiran ka”
Daga haka ya kashe wayarsa, ita kuma ta miƙe tsaye cike da jindaɗi ta nufi waje dan ɗibar neman mai siyo mata indomie.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *69*
Be ji zai iya kwana a yau ba,ba tare da yaje gurin Namra ba, daman yasan duk daɗin bakin da yake yi ma Ummi ba wani barinsa zata yi ya daɗe ba, kuma idan har ta bar shi Mai Martaba ba zai bar shi ba, and what's on his mind nowa ya ji labarin yarinyar duk da bashi da tabbacin ko zata yarda ta saurareshi ma.
Miƙewa yayi tsaye yana duba shaddar da ke jikinsa.
“I really need to do this, ko zan samu peace of mind”
Closet ɗinsa ya buɗe ya fiɗo wata kafirar shadda golden color, ya buɗe ɗayar wardrobe ya ɗauko hular ƙobe ya aje saman shaddar, sannan ya shiga Bathroom ya watsa ruwa.
Bayan ya tsane jikinsa da tawul ya shafa mai, sannan ya saka body spray, ya saka short da white singlet, sannan ya shafa wani turare, ya ɗauki shaddar ya saka.
Wani mai ya ɗauka ya shafa ma fuskarsa, sannan ɗora da turare. Ya ɗan soma jin babu daɗi lokacin daya tuna gidansu Lamido zai je, yasan he has zero reasons to hate Lamido, but he still hate him.
“Maybe he's bad person”
Ya faɗa yana murza wani turaren a wuyansa, kamin ya ɗauki hular ya saka a kansa. Agogon hannunsa ya kalla, yaga tara da kwata, hakan yasa shi ɗan hanzarin ɗaukar wayarsa ya fice.
Sadauki na ganinsa ya tashi, sai Abdool ya ɗaga masa hannu.
“Ni kaɗai zan je”
“Allah ya tsare ya kiyaye hanya, Allah ya kare ka daga dukan ni abun ƙi, Allah yaja kwanan ka”
Abdool be kula shi ba, balle ya amsa addu'ar da yake masa, sai da ya kawo gurin motocin da suke harabar gidan sannan ya ƙwalama Sadauki kira, sai ga shi ya fito da sauri.
“Key wacan motar na ke so”
Ya nuna masa wata baƙar mota mai baƙin gilashi, wanda ke aje can gefe. Da Sauri Sadauki ya koma ciki ya ɗauko masa key ɗin motar ya miƙa masa, sai da ya sake duba agogon hannunsa sannan ya nufi motar ya shiga, gabansa sai faɗuwa yake.
Sai da ya hau titi, sannan ya ciro wayarsa ya dannawa Ummi kira. Sai da yayi mata one missed call sannan a na biyu ta ɗauka.
“Assalamu alaikum”
“Wa'alaikissalam. Ummi ki min addu'ah zanje wani guri neman abu a yanzu, kuma babu tabbas zan yi nasara, idan kuma har na ƙyale abun hankali ba zai kwanta ba”
“Abdool mi zaka aikata? Thought baka aiki yanzu ka ce sun baka hutu?”
“Eh ba aikin office ba ne, wannan aikin nawa ne na sa kai”
“Abdallah karka aikata abunda zai sa rayuwarka cikin haɗari, ka dawo gida gobe”
“O my god”
Ya dafa kansa.
“Allah Ummi ba wani abun ba ne, kawai i need your prayers”
“Ka dawo gida gobe na faɗa maka, kasan dai kullum rayuwarka tana cikin haɗari ko? Karka kuskura ka wuce gobe, umarni na ke baka”
Ta kashe wayarta cike da fushi, dan ta san idan ba haka ta masa ba, ba zai ji ba, gashi duk ya tsorata ta, da wannan maganar na shi daman ita ba son take yana tafiya nesa da ita ba.
Iskar bakinsa ya busar yana cigaba da tuƙinsa a hankali.
“Daga neman sa'ah sai kuma abu ya zama ɗan zane, ban san salon da ya kai ni faɗa mata ba, Allah ka taimake ni”
Unguwar bata da kyau sosai, amman haka ya riƙa kunno kai cikinta yana kallon ƙananan gidajen da suke unguwar har ya isa bakin ƙofar gidan. Wani tunanin ne ya zo masa, sai kawai ya ƙara gaban da gida sannan ya faka motar, ya buɗe ya fito.
Ya samu minti salati tsaye a gurin sannan ya kira wani almajiri da ke bara ya nuna masa gidan su Lamido.
“Je can gidan ka ce ana sallama da baƙuwa”
Sai da almajirin ya kama hanya, sai kuma Abdool ya kira shi ya dawo.
“Ba haka zaka ce ba, ka ce Abdallahi daga Katsina ya na sallama da Namra, Namra ko? Yes Namra zaka ce”
“To”
Almajirin ya nufi gidan da sauri. Faɗuwan gabansa ya ƙaru lokacin daya fara tunanin irin amsar da almajirin zai dawo masa da ita.
NAMRA POV.
Ba laifi yau ta dan sake bisa da jiya, ko dan yau sun ɗan tausasa ta ne kuma ta wuni a tsakar gidan ansha fira da ita. Sai dai bata janye maganar tafiyarta ba, ta yarda ta bari har sai nan gaba, idan ta ƙara jin sauƙi abubuwa sun ɗan dai-dai.
Yau ba iya Maltina da madara kawai Lamido ya bada aka siyo mata ba, har da gasasshen nama, sai dai bata ci ba kasancewar komai bata jindaɗinsa a yanzu.
Sai da aka yi sallama magariba sannan ya bada aka siyo mata tea, yadda yake damuwa ta ci abinci shi kansa be damu da ya ci abincin ba, sam mantawa yake da nasa ciwon wata ƙila ko dan be jimu sosai ba, yake dauriya irin ta maza, ko kuma dan hankalinsa ya ɗauko gurin Namra ne. Shi kansa yana mamakin yadda yake damuwa da Namra, sai dai yana fi karkata hakan da tausayinta da yake, su kansu su Neina suna kula da halin kuwalar da Lamido yake bawa Namra, duk da sun san halinsa na karancin amman wannan kamar yana ƙoƙarin wuce guri, dan ko magana ake Namra ta saka baki zasu ga ya tattara hankalinta ya miƙa mata ya natsu sosai yana saurarenta.
Yau Neina taja Namra da fira sosai musamman bayan Sallah isha'in nan, abinci na fula take labarta masa da kuma al'adansu na fulani, a nan take taɓo labarin Baban su Lamido da kuma ƙuruciyar Lamido, dariya sosai Namra take idan ana faɗin labarin halin ƙiriniyar da Lamido ya yi. Shi kam iya karsa murmushi idan Neina ta faɗi wani abun.
“Salamu alaikum, wai Abdullahi daga Katsina ya ce yana kiran Namra”
Dam dam dam, gabanta ya tsinke ya faɗi, duk wani farinciki da yake zuciyarta sai ya ta neme shi ta rasa, a take murmushin fuskarta ya disashe. Da sauri ta kalli almajirin dake tsaye can jikin ƙofar gidan yana jiran amsa.
Bata san ko waye ba, amman jikinta ya bata wani yanayi na daban, ga shi kuma anxe daga Katsina, kuma an faɗi sunanta, lallai ko wanene ya santa. Sai dai ya akayi ya san inda take zaune? Miyasa be zo da rana ba sai da dare? Shin waye Abdallah ma? Ko dai Asim ne ya canja suna? Amman taya Asim zai san inda take?
“Ko mijin ki ne?”
Tambayar da Lamido yayi mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Kai ta girgiza.
“A'a ba haka ne sunansa ba”
“Ɗan'uwan ki ne?”
Shiru ta yi tana tunanin irin amsar da zata bashi, idan har ta ce ɗan'uwanta ne zata sanu damar fita ta ga ko waye ne, to idan kuma ya kasance Asim ne ya canja suna fa?
Idan ma shi ɗin ne ai babu yadda zai yi da ni, dan yanzu babu aurensa a kai na, idan kuma har aurensa ya zo maidawa to yayi satti, dan na cika idda tun da na yi ɓari!
“Eh ɗan uwana ne”
Sai a sannan hankalinsu ya ɗan kwanta, Neiɓa ta ce da almajirin.
“Je ka ce tana zuwa”
Sai da almajirin ya juya sannan ta kalli Namra ta ce.
“Ɗauki fitila ki je”
Miƙewa tayi tsaye sai Lamido ya ce.
“Ya aka yi ya san gidan nan?”
“Ni na kwatanta masa, a waya”
Kai tsaye ta bashi amsar ta nufi fitilar ta ɗauka ta nufi ƙofar fita gabanta sai faɗuwa yake. Sam Lamido be so ta fita ba, haka kawai ya samu kansa da rashin jindaɗin kiran da aka mata duk da be san me kiran ba. Neina kuma ta kawo wani zargi a ranta, dan tana ganin kamar Namra ta ɓoye musu wani abu ne.
Zuciyarta cike da tsoro ta fita daga gidan, da tunani biyu, Asim ne ko kuma wani nasa yake mata sallamar. Bata ga kowa a ƙofar gidan ba, hakan yasa ta ɗan ɗaga fitilar tana yade, hangota da ya yi yasa ya tako ya ƙaraso kusa da ita.
“Assalamu alaikum”
Ya furta nata cikin murya mai taushi, da sanyaya zuciyar mai sauraro.
“Amin wa'alaikassalam”
Ta amsa masa ba tare data wayence shi ba. Ya ɗan yi gyaran murya.
“Na san baki gane ni ba”
Ya fido wayarsa ya kunna fitar wayar ya haska fuskarsa. Wannan karon ba faɗuwar gaba kawai Namra ta ji ba, har da tsoro, ja tayi da baya yana nuna shi da yatsa, sai maganar ta naƙale ta ki fitowa.
“Nasan zaki yi mamakin gani na, amman ina son ki ba ni aron lokacin ki kuma ki saurari abunda zan faɗa miki”
“Ba kai ba ne ɗan sarki daya kaɗe Lamido?”
“Ni ne, kuma na san ba a nan kika san ni ba, a Katsina ko?”
Kai ta ɗaga masa duk da bata da tabbacin zai ga hakan kasancewar akwai duhu a gurin.
“Miyasa kake bibiyata?”
“Ba saboda ke na zo garin Kaduna ba, ke ma kuma ina da tabbacin ba dan ni kika zo ba, amman zuciyata ta kasa natsuwa da hakan, direba ne ya kaɗe yaron gidan sai kuma na gan ki a gidan shine abun yake bani mamaki, bayan nasan a Katsina na san ki”
“Ba wasu kalamai na ce ka min ba, amman bari na gargaɗe ka, karka sake zuwa ƙofar gidan nan da sunan gurina ka zo”
Ɗan murmushin takaici da mamaki yayi.
“Babu mace da ta taɓa ɗaga hannu ta mare ni sai ke, babu mace da nake gani na bibiya sai ke, babu mace da ta taɓa faɗa min irin wannan maganar sai ke. Zan bar ƙofar gidan nan amman ina son ki faɗa min tsakanin ki da Allah kina da aure? Kuma ina son ki faɗa min tsakanin ki da Allah waye Mahaifinki, kuma miye alaƙarki da mutanen gidan nan?”
Wani haushi ne ya cika mata zuciya, har take jin kamar ba zata iya amsa masa tambayoyinsa ba, amman Allah daya haɗa ta da shi ne take jin ba zata ɗaga daga gurin ba har sai ta ba amsa.
“Ba na da aure, kuma babu wata alaƙa tsakani na da mutanen gidan nan, sunan Mahaifina Manjo Usman Zamau”
Bata tsaya jiran Abunda zai ce ba ta juya ta shige ciki gidan. Shi har tsoro ta bashi cox the way da take bashi amsar kamar tana masa faɗa.
“Wow”
Ya faɗa yana shafa fuskarsa, kamin ya zuba hannayensa aljihu ya nufi motarsa.
Sorry for the short chapter 🙏🙏🙏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *70*
‘Manjo Usman Zamau, Manjo Usman Zamau’
Sunan yake ta maimaitawa, tana tunanin kamar ya san mai sunan amman ya kwanta masa, sai dai jin Manjo ma ya tattabatar masa da soja ne.
Murmushi ya samu kansa da yi lokacin daya tuna wasu kalamai da Namra ta yi masa.
“She's so Unique”
Rage gudun da yake, ya fido wayarsa ya nemo number Sadiq ya aika masa kira. Ringing ta yi sai da ta kusa katsewa sannan aka ɗaga.
“Shegen gari baka kira sai ta samu”
Ƙyalƙyalewa ya yi da dariya.
“Chief Sadiq Northwest”
“Au yau Chief na samu kuma? Kai dai faɗa min abunda yasa ka kira ni”
“Kiran ka kawai na yi na gaishe ka, ko kuskure ne kiran manya kuma?”
“Na ji, ya gida ya hutu, ku ai kun samu hutu”
“Gaskiya ba laifi, amman ba wani mai yawa ba ne, ina Madam”
“Madam na nan ƙalau go straight to the point miyasa ka kira ni?”
Dariya sosai Abdool ya yi kamar ba shi ba, sam ba zaka za ci akwai mutumen da Abdool yake sakewa da shi ba, bayan mutanen gidansu.
“Kasan waye Manjo Usman Zamau?”
“Aha ni nasan akwai wata a ƙasa, ai baka kiran mutum hakan nan kawai”
“Ni dai amsa min kawai, ban ce ka min surutu ba”
“Na san shi, kai ma ai kasan shi, amman yanzu ya yi ritaya ai”
“Nima ina jin kamar na san shi amman sunan ya kwanta min”
“Ai mun yi zama barrack da shi ai, a Yola, shine mahaifin su Salwee and Abdulraman na manta sauran ɗiyansa dai, yanzu ina jin yana sokoto zaune, ance ya zama babban ɗan siyasa ma”
Abdool ya bugu sitiyari motarsa da ƙarfi.
“Yes I knew it!”
“Easy Man what happened to him?”
“Ba komai, kawai wani ɗan bincike na ke ne”
“Okay abokin su ekwieu ne tare suka yi aiki, suna shiri sosai”
“Amman kana da addireshinsa?”
“Kai Malam, tun da ba shi na ke wa aiki ba, haka kawai zan aje addireshinsa”
“Okay okay bye”
Sai kawai ya katse kiran zuciyarsa cike da farinciki. Wata number ya sake lalubowa ya aika mata kira.
“Salim a bincika min addireshin Manjo Usman Zamau mai ritiya, kuma a bincika min a cikin ƴaƴansa akwai Namra, aɗan min bincike akan ta”
Be jira abunda Salim ɗin zai bashi amsa ba ya katse wayar, dai-dai loƙacin daya faka a harabar gidan. A yanayin yadda ya shigo cikin gidan ba zaka ce shine ɗazu ya fita a haka ba, yadda ka san wanda aka yi bushara da aljanna haka ya dawo fuskarsa a sake, zuciyarsa fari ƙal.
Yana shigowa falo ya zauna saman cushion yana kallo falon kamar wani baƙo. Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana ciki nishaɗi, dan hankalinsa ma baya gurin da yake kallo. Wayar hannunsa ya kallo kamar mai son magana da wayar, sai kuma ya watsa yatsunsa saman screen ɗin ya danna number Sadauki, bugu ɗa ya ya ɗauƙa.
“Sadauki ga ni a falo ina jiran ka”
Be jira abunda Sadauki zai ce ba, ya katse kiran fuskarsa shinfide da murmushi. Ba ayi minti biyu ba sai ga Sadauki cikin falon da rawar jikinsa.
“Allah ya taimaki Yarima, Allah yaja kwanan ka, Allah ya baka abunda kake so”
Abdool ya kallesa fuskarsa da Murmushi.
“Amin Sadauki, addu'ah tana tasiri sosai, kaga Allah ya fara ba ni nasara. Yariman ka ya kusa samun gimbiya”
Sadauki ya riƙe baki tare ta washe da dariya
“Mashallah, babban goro sai magogin ƙarfi, Allah ya taimaki Yarima, Mai Martaba zai fi kowa jin farincikin wannan labari”
Abdool ya ɗan risino daga zaunen da yake
“Ya kake auna farincikin Mai Martaba idan ya samu labarin na samu matar aure?”
“Allah ya taimake ka kamar mutum ne, da yake cikin tsamman nin ƴanci, yake cikin baƙin ciki da damuwa, ga yunwa da ƙishin ruwa ya dame sa, masaukinsa kuma babu daɗin zama, me kake tsammani idan aka aka basa sabon masauki mai cike da ƙuramon wanka, ga kuma abinci da abun sha, bayan kuma an ƴanta shi?”
Komawa Abdool ya yi dai-dai saman cushion ɗin ya ɗora hannayensa saman kushin ɗin yana kallon silin.
“Zai kasance mai tsananin farinciki, har zai ji kamar ya haɗe zuciya ya mutu saboda jindaɗi”
“Toh haka zuciyar Mai Martaba zata kasance matuƙar ya samu labarin Yarimansa ya samu Gimbiya”
Murmushi mai ƙayatarwa Abdool ya yi, ba tare da ya kalli Sadauki ba ya ce
“Bana Sadauki da kai za'aje Umara”
Faɗuwa Sadauki ya yi yima Abdool godiya, yana zuba masa kirari, da yabo. Hannu Abdool ya ɗaga masa alamar ya tashi ya bashi guri, haka ya tashi ya fice baki har kunne tsabar murna da farinciki.
Sai da Sadauki ya fice sannan Abdool ya maida dubansa gurin wayar yana lalubo number Mai Martaba. A handsfree ya saka wayar ya ɗorata saman center center tebur ya nufi freezer ya bude ya ɗauko power horse, ya kai bakinsa.
Daga inda yake tsaye yana jiyo muryar Mai Martaba da yayi picking wayar tare da sallama.
“Allah ya taimaki Mai Martaba, i have a good news for you”
“I have good news for you too Son”
“Amman nawa ya fi na ka daɗi, dan nawa idan ka ji ma sai ka bani goro”
“Nima ai sai ka bani goro ba kuma ɗan ƙarami ba ma”
“Me zaka ba ni idan nayi maka albishir da abunda ka daɗe kana jira”
“Zan baka yankin Bakori da kewaye, kuma za a naɗa ka motar Mai Martaba kai fa wace kyauta zaka min?”
Zauna Abdool yayi saman kujera yana dariya har da buga ƙafa, ko ba komai Sarautar da Mai Martaba ya ce zai bashi ta sashi dariya balle kuma yau yana cikin nishaɗi.
“Ni kuma bana da gumi na zaka je Ummara gaida Ubangiji”
“Lallai yau Ɗan Sarki yana ciki farinciki, ɗan tsakura min kaɗan daga cikin labarin ka mana”
“ Ina ai ba tsakure, sai ga ni ga ka, gobe zan sauka sokoto cikin rahamar ubangiji, kuma ba zan kwana ba, har sai na labarta maka abunda zan labartawa Ummi”
“Allah ya kai mu, ya dawo da kai lafiya”
“Amin ya Rabbi. Na gode Mai Martaba, mu kwana lafiya”
Daga haka suka yi sallama, sai Abdool ya ɗauki wayarsa ya nufi bedroom yana kalle kallen gidan kamar yau ya fara shigo shi.
Bayan ya rage tufafin jikinsa ya aika ma wani yaronsa saƙo. Akan ya nema masa jirgin da zaije Katsina gobe.
Bayan kamar minti goma sha biyar yaron yayi masa reply da akwai wanda zai tashi da safe zuwa Katsina.
Daga nan Abdool ya aikama Sadauki da text na maganar tafiyarsu gobe gida, akan yayi duk abunda ya kamata cikin lokaci, duk da be so hakan ba, sai dan Ummi da ranta ya ɓaci.
NAMRA POV.
Da tunanin abunda zata faɗa ma su Neina ta shiga gida, a ɗayan ɓangaren kuma tana tunanin bibiyar da Abdool yake mata. Babu abunda ya fi tsaya mata a rai kamar tambayoyin da ya yi mata.
“Har ya tafi?”
Tambayar da Neina ta yi mata ya firgita ta, har ta zabura, sam bata san ma ta kawo kusa da su ba.
“Eh ya wuce”
Karaf idonta cikin na Lamido da ke dannar waya, kasa kawar da idon ta yi, shi ma kuma ya kasa janye nasa, suka yi ta kallo kallo ita da shi, har sai da Uwani ta maimaita tambayar da take mata.
“Na ce shi ne wanda kika sani ɗin?”
Sannan ta lumshe ido, tana sauraren bugun zuciyarta. Kamin daga bisani ta buɗe idon dake cike da hawaye ta kaɗawa Uwani kai alamar ‘Eh’ ta wuce ɗaki.
Samun kanta ta yi da kuka marar dalili, wani abu take ji yana ratsa mata zuciya mai wuyar fassara, numfashi take da ƙarfi kamin ta samu saita kanta, ta numfasa a hankali tana gode Ubangijinta.
Abdool ya tsaya mata a rai, tambayar ina ya fito ina zaije ya hana ta sukuni, wace manufa yake da ita akanta, shi ya hana ta rumtsawa har dare ya raba.
RASHIDA POV.
Hawaye ne suke mata masu zafi sosai suke mata zuba, keys ɗin dake hannunta take ta juyawa, tana mamakin irin abunda iyayenta suka mata.
‘Ashe akwai ranar da iyaye suke tsanar ƴar cikin su? Ashe rana zata zo da Momi da Dady zasu buƙaci na bar gidan nan? Ban ga laifin Hilal ba dan ya zaɓi rabuwa da ni, ga shi yanzu iyayena ma sun zaɓi haka’
Matsa ƙwallar tayi ta kai hannu ta ɗauki wayarta ta nemi number Teema ta aika mata kira.
“Ƴar gari”
“Teema kin ce zaki shigo kuma har yau baki zo ba, wallahi ina cikin matsala”
“Me ya faru wace irin matsala kuma?”
“Daddy na roƙa ya ba ni keys ɗin gidansa da yake by pass”
“Me hakan yake nufi?”
“Zan fi jindaɗi idan ina ni kaɗai, shiyasa na roƙa ya bani gidansa can na zauna, kuma ya anince min, yanzu matsalar da nake ciki ta rashin makama ne, Teema ina son na koma gidan miji na ko ta halin yayana”
Daga can cikin wayar Teema ta sauke ajiyar zuciya.
“Rashida miyasa ba zaki haƙura da mijin nan ki ba? Ya nuna miki ƙiyayya tsantsarta, ki ƙyale shi mana, Allah zai kawo miki wani”
“Teema har yanzu baki san miye so ba, saboda ba ki taɓa yi ba, bakin irin zafin da mace take ji idan ta rabu da uban ɗiyanta ba, dan Allah ki taimaka min”
“Gaskiya Rashida taimako ɗaya zan iya miki, kawai ki haƙura da shi, Allah zai saka miki, amman idan kuma baki ji ba, zan zo gobe na kai ki gurin wani malamin wanda zai taimaka miki ko Allah zai sa a dace”
“Eh ki zo dan Allah, da ƙarfe nawa zaki zo?”
“Tara da rabi?”
“Sai kin zo, daga nan ma sai ki taya ni maida kayana wacan gidan”
“Okay Allah ya kai mu”
“Amin Sai na ji ki”
Ta katse kiran tana share hawaye.
“ I deserve happiness, Allah ka duba lamari na, Allah ka sassauata min wannan rayuwa, ka rufa min asiri, Allah ka juyo da hankalin mijina a gare ni, Allah na tuba ka yafe min”
Ta shafa addu'ar fuskarta shakaf da hawaye, tana jin tsantsar nadamar zinar data aikata da aure, tun da itace silar shigarta duk wannan halin da take ciki, ta rasa kowa nata saboda ciwon dake jikinta, idan ta tuna yadda Mahaifinta ya matsu ta bar gidan sai ta ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu.
KALSOOM POV.
“Anty Kalsoom, Daddy yana kiran ki, yana falon baƙi tare da Hilal da Abban Hilal”
Da sauri Kalsoom ta ɗago ta kalli Saleena dake tsaye riƙe da gambun ƙofarta tanaata magana. Gabanta ya faɗi sosai, a take ta aje jaridar dake hannunta ta ɗauki Hijabinta ta saka, ta ƙaraso kusa da ƙanwarta Saleena.
“Me kika ji suna tattaunawa?”
“Ban ji komai ba, amman dai har Momi tana can, kuma duka fuskokinsu ɗauke da farinciki”
Ajiƴar zuciya ta sauke sannan ta ratsa ta gefen Saleena ta nufi hanyar da zata sadata da falon Dady, zuciyarta cike da fargaba.
Cikin natsuwa ta shiga falon, bakinta ƙumshe da sallama, sai da ta fara gaishe da Abban su Hilal sannan ta zauna kusa da Momi kanta ƙasa.
“To ga mijin ki nan shi ba zaki gaishe shi ba?”
Cewar Dadyn Hilal yana murmushi, sai duk suka sa dariya har Hilal ɗin da zuciyarsa ke cike da farinciki. Dady ya kiran sunan Kalsoom a natse, ta yadda zata maida hankali ga abunda zai faɗa mata.
“Kalsoom. Hilal ya mayarda sauran igiyoyin aurensa da ke tsakaninku, kuma yace yana da buƙatar ki koma ɗakin ki”
Samun kanta ta yi da kasa furta ko da kalma ɗaya, wani abu ta ji yana ratsa zuciyarta shi ba farinciki ba, ba kuma ɗan 'uwansa ba, wato baƙinciki. Su kuma duk natsu suna son su ji abunda zata ce, ganin hakan yasa Abban Hilal magana.
“Ai ba zata iya cewa komai ba, kasan ita mace ce, kuma ko ba komai suna son junansu. Kawai shiga tsakani ne irin na mata, kai kuma ka biye musu ka zama macen”
Dadyn Kalsoom ya ƙyalƙyale da dariya.
“Matan ne ai sai a hankali, ni na so ta zauna har sai yayi auren ne, tukuna ta koma, zamanta a can a yanzu zai ƙara saka tsanarta a zuciyar Hajiya ne kawai”
“A a ƙara ta koma ɗakinta, aure kuma ban hana yayi ba, kin dai shirya zama da kishiya ko?”
Ya ƙarasa yana kallon Kalsoom wacce ta noƙe kai tana mai jin kunya.
“Tashi ki ɗauko kayan ki muje”
Sai a lokacin Momi ta saka baki
“Tun yanzu ai da an bari har gobe sai ƙanwarta da Ƙawarta ta raka ta”
“A'a nima ai na isa na rakata, tashi ki ɗauko kayan ki”
Kasa tashi Kalsoom ta yi har sai da Momi ta zo ta riƙa ta suka bar falon tare. Daddy Hilal ya kalli Daddyn Kalsoom yana faɗin
“Wato abun ne da ɗaure kai, kasan kuma zuciya wani lokacin bata da ƙashi, ni kai na abun ya ɗan ɗaure min kai da farko, amman ganin soyayyar dake tsakanin dole a ɗaga musu ƙafa, kuma koma minene shi uban ɗa be yarda ba, kai miye na ka a ciki har ka raba musu aure ƙaramar ƙwaƙwalce kawai ta mata”
Murmushi Dadyn Kalsoom ya yi ya girgiza kai
“Allah dai ya kyauta ya bayyana gaskiya”
Dukasu suka amsa da Amin har Hilal dake ƙoƙarin miƙewa tsaye.
YASMEEN POV.
A gajiye ta aje hakar hannunta ta karɓi Babynta daga hannun mai mata reno tana murmushi.
“Sorry Dear i'm back”
Uzair ya aika mata wani kallo mai cike da jin haushi.
“Ni fa wannan aikin na ki ya ishe ni, ace har kana jego ma sai kaje, yau kwana biyu da suna har kin fara fita”
Kallonsa ta yi fuskarta da annuri.
“Am sorry dear, daga yau ba zan sake fita ba sai next week”
Wani tsakin haushi yayi
“Ai kaji fa fitan ya fara kenan, ai ba aure lawyer ba, zamanta a gida ma aiki ne”
Dariya tayi tana gyara sunan da take ba ƴarta, tare da kallon Adnan dake wata tafiya a wahalce.
“Kai me ya same ka?”
Bude baki yayi zai yi magana sai Uzair ya karɓe.
“Da...”
“Ina jin Basir ne yake damunsa, ko kuma ya zauna wani abu ne, ɗazu ma na duba gurin ya masa ja sosai, i will take him to hospital”
Yana gama faɗar hakan ya miƙe tsaye ya riƙa hannu Adnan da sauri suka fice, ita kuma bata wani ɗauke abun serious ba, ta maida hankalinta gurin Mai mata reno.
“Me aka girka?”
“Wake aka yi, shi yace na girka ta daya ga Namra na ta kuka”
“Ayyah Namra na, i'm sorry ba zan sake fita ba dake ba, i love you”
Ta aikawa babyn kiss tana murmushi. Sannan ta tashi ta nufi ɗakinta tana cire ɗankwalin kanta, ɗayan hannunta kuma na ɗauke da new babynta Namra.
ASIM POV.
Be farka ba, sai bakwai da rabi, yana yin sallah asuba ya sake komawa baci,ba shi ya tashi ba sai sha ɗaya na safe, wayarsa dake kusa da shi ya ɗauka ya lalubo number Mardiya dan yau a bachinsa na safe ita yayi mafarki, be wani daɗe sosai yana waya da ita ba, ya miƙe ya shiga wanka.
Sha biyu saura ya shirya ya fita, kai tsaye gidan Hajiya Sadiya ya zuwa, tun kamin ya taso ya tanadi ƙarya da zai mata akan Namra, sai ya tarar bata gidan, mai gadi ya labarta masa tun jiya da dare ta bar gidan wai taje birnin kebi.
Ko kaɗan Asim be jidaɗin hakan da Hajiya tayi masa ba, sai ya zuciyarsa ta soma nuna masa ko dai Hajiya ta yi fushi da shi ne, shiyasa har taje Kebi bata faɗa masa ba, duk da ta faɗa masa zata bashi hutu saboda baƙi zata yi ai bata ce masa zata bar garin ba. Har ya ciro wayarsa ya kirata sai kuma wata zuciyarta ta hanasa, a ganinsa yanzu ba zata sauraresa ba tun da tana cikin fushi ƙara ya bari har sai an kwana biyu sannan ya kira ta, idan bata dawo ba.
Ƴar ƙara wayarsa ta yi, yana duba ya ga alert daga diamond bank saƙon miliyan biyar ya shiga asusun ajiyarsa.
“Wow”
Ya faɗa yana karanta sunan wanda ya aiko masa da kuɗin.
“Yayi Kyau Alhajina”
Ya faɗa cike da tsananin farinciki, kaminɓya ɗora da saƙon daya biyo baya.
“Na aiƙo maka da kuɗi, kazo gobe sokoto ina son ganinka, kuma ka zama mai riƙe sirri”
“Zan zo gobe tun da safe inshallah”
Haka ya mayar masa da amsa, sannan ya rumgume wayar a ƙirjinsa yana dariya har ta fitar hankali. Komawa yayi motarsa ya shiga, yana cigaba da dariya har da jijjiga jiki.
Yana yi ma motar ki kiran Nably ya shigo wayarsa, cikin sauri ya ɗauka yana dariya.
“Hello my second wife”
“Au ba ma nice ta farko ba kenan?”
“Yes karki sa ma ranki zaki zauna ke kaɗai a gidan Asim”
“Ashe kai ba Saurayi ba ne?”
“Saurayi ne kuwa sabo hul, amman bayan ke wata zan ƙara, ko kuma ma akai ku ku biyu a tare”
“Kai da bakinka kake faɗin haka, lallai na yi fushi, na bar mata”
Da sauri ya haɗe hannayensa kamar tana gabansa.
“Sorry my nurul khalbi, wasa nake miki just to get your angry, yanzu dai ya hanya?”
“Au kasan da tafiya na, amman baka kira ka tambaye ni ba”
“i'm sorry dear i'm just kind of busy, In fatar kin sauka Lafiya”
“Na sauka ƙalau idona sai ƙaiƙayin ganinka suke yi ”
“Gani na kan hanya nan da mintuna talati”
“I can't wai to see you”
“The same here”
Yana aje wayar ya ƙara ma motarsa jiya ya nufi wani boutique, dan siyen kaya mai kyau da tsana wanda zai sa yaje gurin gimbiya Nabila.
ABDOOL POV.
Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi jirginsa ya sauka Katsina, yana sauka ya kira Ummi ya faɗa mata ya sauka, amman ta ƙi ɗaukar wayarsa, har sai da ya aika mata da saƙo, Sannan ta aiko masa da direba.
Daga filin jirgi zuwa gida tafiyar minti goma sha biyar ce, amman sai yaga ta yi masa tsayi kamar na awa ɗaya saboda zumuɗin da yake na bawa Ummi labarin dake cikin ransa.
Suna shiga harabar gidan farincikin fuskarsa ya ɗaɗa ƙaruwa, ko fakin ɗin kirki direban be yi Abdool ya buɗe ya fito, sai duk sojojin da suke gidan suka maƙe guri ɗaya suna sara masa, hannu kawai ya ɗaga musu ya nufi Babbar ƙofar gidan.
Amira da Haleema na tsaye dinning suna jera abinci Abdool ya shigo da sallama.
Da gudu Amal taje ta rumgume shi.
“Dude i miss you”
“I miss you more”
Kaɗan kaɗan Amira take satar kallonsa tana murmushi, Haleema ma kallonta take tana murmushi dan tasan abunda yake zuciyarta. Fitowar Ummi ne ya ɗago da duka hankalinsu har Amira ta samu damar kallon Abdool da kyau tana auna irin missing ɗinsa da ta yi.
“Ka kuru da baka dawo yau ba ko”
Dariya yayi yana wasa da hannun Amal.
“Ummi ina da labari mai daɗi da zan ba ki, duk da kin katse min uzuri na”
Zaunawa tayi saman kujera tana murmushi.
Sai shi ma ya zauna yana tambayar Amal abunda ya hana ta zuwa makaranta. Lemu Amira ta ɗauko ta kawo masa a gabansa ta dire masa, tana masa sannu da zuwa.
“Yauwa Thank you so much”
Ta jidaɗin kalma nan da yayi mata, bama kamar murmushin da ta gani shimfiɗe a fuskarsa. Cikin natsuwa ta tashi ta nufi dinning dan zuba masa abinci.
Kallon Ummi yayi fuskarsa ɗauke da abunda ke zuciyarsa.
“Ummi kin yi suruka, matar da na taɓa baki labari ina so na samo ta, finally mafarki na zai zama gaskiya...”
Tartsatsa... Suka ji ƙarar fashewar plate mai ɗauke da abinci, wanda Amira ta sake saboda maganarsa da ta soki gadon bayanta, da sauri ta ɗuka tana kwashewa, kamar wacce ta ruɗe, a take hawaye ya fara bin fuskarta, sai dai su basu gani ba kasancewar ta basu bayana ne.
“Ba ki ji ciwo ba?”
Ummi ta faɗa tana ɗan leƙen ta. Sai Haleema ta yi saurin amsawa.
“A'a plate ɗin ne kawai ya fashe”
Ummi ta maida hankalinta gurin ɗan ta.
“Im happy for you Son, na daɗe ina jiran wannan ranar, you have no idea how happy you make me, sai dai ban gane wacce kake magana ba akai kam ba”
“Ye... ”
Ringing ɗin da wayarsa ta yi ne ya hana shi ƙarasa maganar sai yayi saurin tashi ya nufi wani ɓangare na falon yana amsa wayar.
“Salim”
“Sir mun bincika, Manjo Usman Zamau yana sokoto da zama a unguwar clapperto, yana da mata biyu da ƴaƴa goma sha uku Namra ita ce ta goma, kuma ainahin sunan ta shi ne Khadija, ta yi makaranta a dan fodio tana level 300 aka yi mata aure, kuma har yanzu tana gidan aurenta zaune, facebook username ɗin ta Khadija Usman Zamau instagram kuma Namra's, haka yake a twitter da snapchat”
“Amman ba ku bincika zaman auren ta ba? Har yanzu tana da aure?”
“Binciken mu ya nuna har yanzu tana da aure kuma tana a garin katsina da zama, sunan mijin da take aure Ibrahim amman anfi kiransa da Asim”
“Thank you”
“Your Welcome Sir”
Wayar ya ƙurawa ido yana mamakin yadda Namra zata masa ƙarya, bayan ya tambaye tsakaninta da Allah, taya aurenta zai mutu kowa bai sani ba, hakan yana mufin ƙarya ta masa kenan ko kuma akwai abunda take ɓoyewa.
Juyowa yayi yana ƙoƙarin ɓatar da mamakin dake fuskarsa ya kalli Ummi yana tahowa ya ce.
“Wani aiki ya tashi Ummi Ana nema na a Kaduna yanzu yanzu nan”
“What?”
Ummi ta faɗa da mugun mamaki. Shi kuma ya ɗan ɗaga gira yana kallon Amal.dake zumuɗin labarin daya fara badawa.
Hello habibaties nasan kuna haƙuri da ni dan Allah ku ƙara haƙurin. Wallahi abubuwa ne suke min yawa, ga kuma rashin wutar nepa a gusau, yau four days babu wuta, sai an tashi engine ne muke samu mu saka. Idan kuma ka matsa za'a ce sai ka biya na Mai 😂 you know how our grandma's are, sai haƙuri 😂
Love you all fisabilliah ♥️🌹🌺❤
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *71*
Ɗauke kansa yayi daga kallon da yake ma Amal ya kalli Ummi, irin babu zacen wasa a kalamansa.
“Nima sai da na ce miyasa ba su bar ni nayi aikin ba acan ba sai yanzu da na dawo”
“Abdallah ka ce min kun samu hutu fa? Aikin me zaka je yi yanzu?”
“Wai General ne zai zo daga Abuja zuwa Kaduna gobe, kuma dole ne muje. Bari naje ya canja kaya gobe da safe ai zan dawo”
Be jira abunda Ummi zata ce ba, ya nufi ƙofar fita yana lalabar number Salim dan ya sama masa jirgin da zai koma Kaduna yanzu ko da Yammar nan.
Ummi dai da kallo Mamaki ta bishi, ta fi kowa sanin ɗanta dan haka ta san ba aiki ne zai maida shi Kaduna ba, sai dai wani abun na daban, kai ta girgiza tana kallon Amal data wani turo baki.
“Be ma ƙarasa mana labarin ba”
Ummi ta miƙe tsaye ta nufi kitchen tana faɗin
“Uhnm kya ji da shi”
AMIRA POV.
Tana gama kwashe plate ɗin da ya fashe ta zuba a shara, sai ta nufi ɗakinta cikin wani irin kuka marar misaltuwa.
Saman gadon Amal ta faɗa ta kife tana rera kukanta a hankali yadda wani ba zai ji.
“Shikenan na rasa komai, wata yake so ba ni ba, shi ma na rasa shi”
Tausayin kanta take da kanta tana tunanin irin rayuwar da zata yi nan gaba. Bayan ta rasa duk wani abun da zai iya saka ta farinciki. A hankali Haleema ta turo ƙofar ta shigo fuskarta ɗauke da tausayin Amira,wanda har zuciyarta haka ne. Kusa da ita ta zauna ta kai hannu ta taɓa ta.
“Ki yi haƙuri Amira, ni kai na ban san haka zai faru ba...”
Da sauri Amira ta ɗago ta kalleta da idonta da suka gana canja kala saboda kuka.
“Ke ma kin yarda na rasa ɗan uwanki ko? Babu wani abun da za kiyi? Dan Allah ki taimaka min Haleema kema mecece zaki iya shiga a halin dana shiga, kin san irin abunda nake ji, Wallahi ina son Yaya kuma tsakani da Allah zan zauna da shi, idan har na ci amanarsa na yarda amanar Allah ta ci ni, na rantse da Allah ba zan cutar da shi ba”
Kuka take sosai zuciyarta a narke, ta kama hannayen Haleema ta riƙa tana mai jin kamar Haleema ta yi mata maganin damuwarta.
Cikin kuka Haleem ta ce.
“Babu wani taimako da zan iya yi miki Amira, Big Bro babu mai saka shi dole idan ba Ummi ba, kuma idan har ya nuna baya so ita ma bata so, babu abunda ya cutar da ke kamar zama ba a gurin iyayen ki ba”
“Ba zan iya komawa ba, ban san yadda zan yi na koma ba”
Ya zube ƙasa zaune tana rushewa da sabon kuka. Haleema ta riƙa ta tana bata haƙuri. Kamin ta tashi cikin ɓacin rai ta nufi hanyar fita, Amal ta samu tsaye jikin ƙofar ta yi wani wuƙi-wuƙi da ido.
“Ummi tan kiran ki”
Ta faɗa a sagarce, sannan ta falfala da gudu ta nufi ɗakin Ummi ɗin. Haleema ta rufa mata baya tana share hawayenta. Ƙusƙus ta tarar Amal na yi gurin Ummi, hakan ya tabbatar ma da Haleema Amal ta ji abunda suke cewa.
Meesha na gaban maduba Ummi tana ɗanɗasa kwaliya ita da Fauza, dan su basu ma san Abdool ya dawo ba.
“Ummi ga ni”
Ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zama kusa da ita.
“Gulma ta kuke yi?”
Da sauri Haleema ta sake kallon Ummi baki sake, kamin ta maida dubanta gurin Amal.
“Amman yarinyar nan munafuka ce Wallahi, gulamar ta kika ce na yi, aiko sai na miki ɗan banzan duka a gidan nan”
Ummi ta katsa mata tsawa.
“A'a akan me? Maganar me kuke ke da ita har kuke kuka?”
“Walahi akan big bro ne, dan ta ji ya samu mata shine take kuka ina bata haƙuri”
“Dan ya samu mata sai aka yi me?”
“Kin san son shi take sosai wallahi”
“Amman dai Haleema baki da hankali, ke ko a mafarki aka ce yayanki zai aureta idan kika farka ai kya nemi tsarin Allah, macen data zauna da yan fashi? Kika san ciki nawa ta zubar? Baki san zaman ta a nan ma it very risk ba”
“Haba Ummi ciwo ƴa mace na ƴa mace ne, yanzu idan nice a wannan hali zaki jidaɗi? Ba ita ta ƙaddaro ma kanta ba, kuma ta yi sadaukarwa ma Big Bro ita ta cancanci ya so ta wallahi”
Ummi kasa magana ta yi saboda mamakin furucin Haleema. Meesha ta taso daga gaban madubi da take zaune tana faɗin.
“Kin san me Ummi zata iya saka mana guba duka mu mutu idan har ta ji Big Bro ba zai aureta ba, ƙila ma turo ta aka yi, ta ina ma.taji Yaya ya samu mata? Kodai ta ga alamun ba zai so ta ba ne”
Fauza ta amsa.
“Kuma Wallahi irin waɗan nan ba tsoron kisan kai suke ba, tun da sun saba”
Ran Haleema ya ɓace sosai.
“Ku daina judge mutane ne, hakan be da kyau, Allah ma yana karɓar tubar bayinsa balle kuma mu....”
Shigowar Abdool ne yasa duk suka warsar da maganar, Fauza da Meesha suka fara ɗaukin shigowarsa tare da masa sannu da zuwa.
“Ai kune ba ku san ya dawo ba, mu tuni muka sani har ya ba mu labarin matarsa da zai aura”
Ya ɗaga gira ɗaya yana kallon Amal, ita kuna ta shigar da kai jikin Ummi dake dariya, ita ala dole ga auta.
“My girls ku fita za mu yi magana”
Ya faɗa yana ƙoƙarin zama a kujerar dake fuskantar gadon Ummi. Ba musu duk suka fita har Amal uwar son zancen dan bata ga alamun wasa a fuskarsa ba balle ta tsaya.
“Maganar gaskiya Ummi ba aiki zani ba, gurin yarinyar nan zan koma, kawai ki min addu'ah, gobe da safe zan dawo”
“Na gama karantar ka sarau Lamiɗo kallon ka kawai na ke yi. Allah ya kai ka lafiya, kuma a gaishe min ita sosai da sosai”
‘Ai ba gaisuwa ba, ni kaina ban san makomata ba’
Zance daa ya faɗo masa kenan a rai kamin ya ɗago ya saurari zancen da Ummi ta ɗora da shi.
“Dan Allah ka nemo iyayen yarinyar nan, idan ba zata iya zuwa ba, su suzo su tafi da ita”
“Ummi laifin wa? Idan na yi magana ai cewa kike na ɗaga mata ƙafa”
“Ai ba ƙafa ba komai ma.an ɗaga mata, yanzu kam ya kamata ace tana gaban iyayenta”
Miƙewa yayi tsaye yana faɗin
“Don't worry Ummi, if she planning something evil, za a sanar da ni, ai akwai mai kula da cctv camera. A min addu'ah jirgin mu zai tashi nan da ten minutes”
“Allah ya kiyaye ya kai ku lafiya”
Tasowa ta yi ta suka fito tare da shi yana labarta mata maganar da suka yi da Mai Martaba.
Ko da ya isa airport sauran minti uku jirgin ya tashi, abun ka da manya a take aka masa checking ya wuce.
Be da sukuni har sai da jirginsu ya sauka garin Kaduna, yana sauka airport yayi waya daga Abuja, suka kuma suka yi waya a kaduna, cikin minti ashiri sai ga direba in military uniform sun zo ɗaukarsa.
A cikin motar ya sha ruwa, kamin ya buɗe biscuit ya ɗan ci kaɗan yana faɗa musu inda zasu kai shi. A masallaci unguwar ya ce a aje shi, suna yin parking da sauri wani ya fito daga cikin motar yazo ya buɗe masa yana sare masa, umarni ya basu na suje sai ya nemesu. Ba musu suka sake tsara masa suka koma cikin motar suka juya. Yi yayi kamar be kula da mutanen da suke kallonsa ba, yayi alwalarsa ya bi jam'i, har aka gama sallar kowa da abunda yake faɗa, wasu wai ya zo bincike ne, wasu kuma wai akwai wanda zai kama, shi dai yana gama sallah la'asar ya kanyar kwanar da zata sadashi da gidansu Lamido,daman daga masalacin zuwa cikin gidan babu wani nisa sosai. Hango mustafa da yayi yasa shi sauri juyawo ya ciro wayarsa a aljihu ya neman number direban Mai Martaba da yake gidansa da suka sauka da ke Kaduna.
Cikin mintuna da basu bi goma sha ɗaya ba sai ga direba ya iso, be faka ko'ina ba sai gaban Abdool da sauri Abdool ya buɗe ya shiga, yana nuna masa inda zaije.
Mustafa na zaune gindin wani icce yana kallon motar har suka faka ta dai-dai ƙofar gidan su Lamido. Ya maida hankali sosai da son ganin wanda zai fito daga motar, sai kawai yaga baƙuwar fuska ta fito daga gidan gaba mazaunin direba yana buga ƙofar giɗansu Lamido.
“Waye...”
Suka amsa daga can ciki kamin ɗan uwani ya fito waje ganin mai buga ƙofar.
“Shiga ciki ka ce Abdallahi daga Katsina yana sallama da Namra”
“Toh ya juya da gudu ya koma”
Shi kuma direba ya juyo dan mayarma da Lamido saƙo.
“Wai Ance bata nan”
Yaron ya faɗa yana tsaye jikin ƙofar gidan. Abdool ya buɗe motar da kansa ya fito.
“Kije ka ce idan bata fito ba, ni zan shigo”
Yace da yaron babu alamar wasa a maganarsa, haka ma a yanayinsa. Da gudu yaron ya koma, ko minti biyu ba'ayi ba sai ga Namra ta fito cikin farin Hijabi ta doso inda yake. Yana kallonta dukan natsuwarsa taje gareta, kalaman daya tara zai watsa mata marar daɗi sai duk ya neme su ya rasa har ta ƙaraso kusa da shi ta tsaya.
“Ban ce kar ka sake zuwa nan ba? Jiya jiya ban maimaita maka wannan maganar ba? Ka ɓace ka bar ƙofar gidan nan”
Ta faɗa a tsawace, fuskarta babu annuri. lumshe ido Abdool yayi ya buɗe ya kalleta.
“Kina burge ni idan kina ba ni Umarni, da ma ace bakin ki be iya faɗar ƙarya ba, kin ce ba ki da aure bayan kina da shi”
“Idan na maka ƙarya nawa zaka ba ni? Miye ribata idan na maka ƙarya bayan ka tambaye tsakani da Allah?”
“Amman ƴan gidanku sun tabbatar mana da kina da aure, Asim be sake ki”
Wani irin kallon ta jefa mata mai cike da tashin hankali da mamaki.
“Ina ka san ƴan gidan mu? Waya faɗa naka sunan mijina? Waye kai? Me kake nema a gare ni”
“Naje har gidanku ne neman auren ki, kuma sun tabbatar min da kina da aure, auren ki be mutu ba”
Ta ɗora hannu saman kai.
“Na shiga uku na lalace, ka ɓata komai yanzu shikenan ba za su karɓe ni ba, miyasa baka bari na faɗa musu mutuwar aurena da kai na ba? Kaico na ni Namra, duk inda na dafa taɓen mi yake yi, ka cuce ni shiyasa ka tambaye ɗan ka ƙara jefani a halin baƙinciki da damuwa? Wayyo ni Allah na”
Ta juya da sauri ta koma ciki tana kuka. Shi dai kallonta kawai yake har ta gama faɗa masa abunda zata faɗa masa ta juya ta shige. Jikinsa yayi sanyi sosai, ko bata faɗa masa ba yasan there's something behind those words and tears da ya ga suna zuba a idonta. Juyawa yayi zai buɗe motar ya shiga sai ga Mustafa ya iso.
“Ranka ya daɗe naje kai maka kayan aka hanani shiga, kuma aka ƙi karɓa wai baka nan”
Ko kallonsa Abdool be yi ba ya ɗaga masa hannu.
“Na bar maka”
Ya shige motar, cikin rashin jindaɗin rai. Tun kamin su bar unguwar kalaman Namra suka riƙa dawo masa, idan ya tuna hawayen da ya ga suna zuba a idonta sai yaji wani abu ya tsaya masa a zuciya marar daɗi.
“Ranka ya daɗe ina za muje?”
Ya tambaya ganin har sun hau titi amman Abdool be ce da shi komai ba.
“Masaukin Mai Martaba”
Ya faɗa cikin sanyayiyar murya mai nuna mutun yana cikin damuwa.
-----------------------------------------------------------------
Ku yi haƙuri da wannan.
*72*
Da kuka Namra ta shiga gidan, bata kula su Neina da ke tsakar gidan suna gyaran giɗa ba ta wuce ɗakin Uwani, saman katifa ta faɗa tana cigaba da rera kuka.
Duk mamakine ya kama su, daman tun jiya ba su gane ma kanta ba.
“Uwani je ki gani mana”
Lamido ya faɗa yana kallon Uwani, duk ya ji babu daɗi ganin tana hawaye.
Da sauri Uwani ta tashi ta shiga ɗakin, hannu ta kai ta ɗago Namra tana tambayar
“Lafiya miya same ki?”
Sai kawai Namra ta faɗa jikinta ta cigaba da kukan. Jin kukan nata ya ƙaru yasa Neina shigowa ɗakin.
“Ke lafiya miya same ta?”
“Wallahi nima ta kasa min magana, sai kuka take”
“Toh Allah dai ya sa lafiya, ko wani ne ya mutu?”
Sai a lokacin Namra ta samu ta girgiza musu kai, tasa hannunta ta share hawayenta.
“Mutumen da ya zo yanzu, shi ne mutumen da ya zo jiya, kuma shine mutumen da ya kaɗe Lamido”
Ba shiri Neina ta zauna sake da baki dan shan labari, Uwani kuma ta yi ma Namra kallon Mamaki.
“To miyasa kawo shi? Miya ce miki”
A nan Namra ta kwashe labarin abunda ya faru, ta faɗa musu, sai dai bata yarda ta faɗa musu sanin da ta yi masa a Katsina ba.
Dukansun cika da tsananin mamaki, bama kamar Neina da take ganin kamar lokacin da ya zo gidan ba su yi ido biyu da Namra ba.
“Amman Namra in ban da abin ki miye abun kuka a ciki? Ke da Allah ya kawo miki ɗauki? Yanzu ko abunda tsohon mijin nan na ki ya yi miki ai wannan idan kika duba sakamako ne Allah zai miki”
Uwani na kai aya. Namra ta yi mata kallon baki fahimce ni ba.
“Ya ƙara ɓata min komai Uwani, yanzu iyaye na sun ji aure na ya mutu, kuma za su yi tunanin ko nice na tura sa neman aure na, idan yanzu na koma gida ban san mi zan ce musu ba”
Neina ta ɗaga kai ta kalleta
“A yadda na fahimta, idan har yana son ki da gaske ne, hakan ba zai sa ya ƙi ki ba”
“Ya so ni, ko ya ƙi i, ni duka ɗaya ne a guri na, ban shirya mutuwa sau biyu ba, ban shiryawa yaudara Namiji ba, wani na Namiji ba zai sake ɗiga min baƙinciki a rayuwata ba, na rufe shafin Namiji a rayuwata, dan haka ni ba shi nake ji ba, iyayena na ke ji da makomata”
Duk shiru suka yi, suna sauraren kukan da take rerawa. Kamin hankalinsu ya koma kan sallamar da Mustafa yake yi. Neina ce ta tashi ta fita Uwani kuma ta tsaya yana bawa Namra haƙuri.
“Maraba da Mustafa, yau an dawo shago da wuri?”
Ya zauna saman kujerar tsakar gida ta mata, yana faɗin
“Wallahi yau ban ma je ba, ya mai jiki?”
“Jiki yayi sauƙi Alhamdulillahi”
Lamido ya amsa da kansa yana miƙa masa hannu su gaisa.
“Allah ya ƙara sauƙi, naga kun yi wani babban baƙo ne a waje, amman kamar be shigo cikin gidan ba”
“Eh gurin Namra ya zo ɗan'uwanta ne”
Cewar Lamido, kamin Neina ta amsa da
“Wai Ɗan Sarki nan ne da ya kaɗe ka, shine ya zo wai yana son ta, kuma har yaje can gida ita bata ma sani ba”
Da sauri Lamido ya kalli Neina, wani irin abu ya daki ƙirjinsa, be ji daɗin maganar ba, kuma be ji rashin daɗinta ba, sai ya samu kansa cikin wani kalar yanayi na dabam.
“Me ta ce masa? Ai na ga ta dawo da kuka”
Ya tambaya kamar ba komai, sai a baɗini yana jin zuciyarsa kamar ta rabe biyu. A nan Neina ta kwashe labarin da Namra ta faɗa musu ta faɗa ma Lamido.
“Ba duka maza ne ƴan iska ba, ba duka maza ne mayaudara ba, ba a taru aka zama ɗaya ba, yadda wani yake da kwaɗayi ba haka wani yake da shi ba, ba a taru a zama ɗaya”
Ya faɗa a hankali yana kallon wani gurin kamar mai nazari. Har Neina ta buɗe baki zata yi magana, sai Mustafa ya jinjina kai ya ce.
“Amman abun da ya ba ni mamaki, wannan mutumen yayi min kama da wanda na sani, kuma shine mutumen da ya aiko yaronsa ya kira nia ka bani wanki, ya ɗauki dubu goma sha ɗaya ya ba ni wai na wanki ne, har yake labarta min wai shi ɗan'uwan ku ne, kuma yana zuwa gidan, da neje kai masa wankin sai aka ce baya nan, ina nan kuma zaune sai na gansa, ina masa magana wai ya ba ni tufafin”
Lamido ya riƙe baki.
“Wallahi ba mu da wani alaƙa da shi, ai baka nan lokacin daya kaɗe ne da ka gani, anya ba yana da wata muguwar manufa ba ce akan yarinyar nan da mu ma?”
Neina ta yi saurin rufe masa baki.
“Dan Allah ka rufa mana asiri, ɗan Sarki ne”
“Dan yana Ɗan Sarki fa? So what? Ba a da ikon faɗar gaskiya, ku kuke tsoron sa”
Mustafa ma ya saka baki.
“Kai da ka rufa ma kan ka asiri. Ko ma minene iya karka ka yi addu'ah ka zura na mujiya”
“Wallahi ba zan yi ba, ba zan zuba ido wani ya cutar da yarinyar nan ba, iya wahalar da tasha ta ishe ta haka”
Ya faɗa cike da ɓacin rai. Mustafa ya miƙe tsaye bakinsa cike da maganganun da be samu furtawa ba, yana musu Allah ya sauwaƙe.
“Amin an gode Mustafa”
Neina ce ta amsa da haka, Lamido kan hankalinsa na can wani gurin.
ABDOOL POV.
Samun kansa yayi da damuwar abunda be kamata ace ya dame shi ba, ya sara sukuninsa tun hawayen da ya gani suna zuba a idon Namra.
“Na ɓata komai? Na ƙara ruguza mata rayuwa? Mi take nufin da hakan?”
Magana yake yi da kansa yana kallon tv, babu abunda kunnuwansa suke da buƙata a yanzu kamar jin labarin Namra.
“Allah kai ka san ina son yarinyar nan, kuma Allah kai ka saka min son ta, ya Rabb help me, wallahi daga gani sai ta yi taurin kai”
Ya shafa fuskarsa yana busar da iskar bakinsa. Can kuma ya kai dubansa ga wayar dake gefensa ya ɗauka ya danna number Ummi. Bugu ɗaya Amal ta ɗauka.
“Dude zaka cigaba da ba ni labarin matar ka ko?”
Murmushi yayi marar sauti kamar tana gabansa.
“Ina Ummi?”
“Tana falo, ni ina game da wayarta”
“Tau ki ce mata na isa lafiya ƙalau kin ji”
Be jira abunda zata ce ba ya kashe wayar, yana sauke ajiyar zuciya. Sam be jin yau zan iya haƙura be ji labarin Namra ba, dare kawai yake jira yayi masa ya koma unguwar, sai dai me idan tace ba zata faɗa ba fa?
“Tau ya zan yi? Ni Wallahi tsoro ma yarinyar nan take ba ni”
Ya sake magana a fili kamar mai magana da wani. miƙewa yayi tsaye ya nufi bedroom ɗinsa yana ware hannayensa.
“Ina ta ƙoƙarin zama mahaukaci akan wannan yarinyar, Allah ka da ka jarrabe ni ta wannan hanyar”
RASHIDA POV.
Da taimakon Teema suka kwashe duk wani abu na amfaninta suka mayar a gidan da Mahaifinta ya bata. Ɗan madaidaicin gida ne mai ɗauke da ɗakuna biyar, da kuma madaidacin tsakar gida.
Gidan yayi datti sosai duk da kasancewar ba a taɓa zama a cikinsa, sai dai daɗewa da aka yi ba a buɗe shi ba yasa ya koma kamar anyi yaƙi a cikinsa. Tare da teema suka jera komai, sam bata yarda ta nunawa Teema damuwarta akan komawarta gidan ba, hasali ma tana yawan maimaita ita hakan ya fi mata daɗi kuma ita ce ta nemi Dady ta bata gidan alhalin ba haka ba ne, duk yadda hawaye suka yi ƙoƙarin zubar mata sai ta yi kamar abu ya faɗa mata a ido.
Sai dai abunda Teema ta saka samun natsuwa da shi, ganin babu ɗan'uwanta ko ɗaya daya zo rakata a gidan, ko kuma su tausasata akan karta bar wacan gidan ta dawo nan ita kaɗai. Bata nuna mata komai ba har suka gama tsara komai suka share iya inda za su iya, sauran ta ce almajiri zai gyara mata, daf da za su fita Momi ta iso gidan da kukanta kamar wance aka cirewa rai. Duk dauriyar da Rashida ta ke sai da ta fasa na ta kukan, sai ita da Momi aka rasa mai bawa wani haƙuri.
“Ni Wallahi sam ban ga amfanin wannan kukan ba, miye na barin gida Rashida in ban da abun ki? Ai ƙara ki zauna cikin danginki, ko danuwa ai kya rage”
Rashida ta share hawayenta, tana jan majina.
“Ni na zaɓi zama a nan, na fi son na zauna ni kaɗai”
Momi kan bata iya cewa komai ba, sai kawai ta miƙe tsaye tana faɗin.
“Dadyn ki ya ce zai aiko da furniture da abinci, da kuɗi kuma duk abunda kike so ki riƙa faɗa mana”
Daga haka ta fice hawaye na cigaba da mata zuba. Bayan fitarta da minti goma shabiyar Rashida ta tashi ta shiga bathroom ta yi wanke fuskarta ta fito suka ɗauki hanyar dutsen Malam.
Rashida ce take driving, Teema kuma na zaune front seat, sai kallon Rashida ta ke yi ƙasa-ƙasa. Ɗan ƙauye ne da yake can waje gari sai dai kuma ba sosai ba. Shi wannan malamin da alama aikinsa ba yayi ko kuma sabon farawa, dan babu ƙowa a ƙofar gidansa. Matan biyu masu far'ah da son mutane, suna shiga suka ɗauko musu tabarma suka shimfiɗa musu da zimmar za su aika a kira Malam wai yana gona.
Sai ga shi ya iso cikin ƙanƙanen lokaci, jikinsa har ɓari yake, bakin nan cike da goro. Bayan ya gaisa da su yayi musu iso zuwa ɗakin da yake aikin nasa.
“Bismillah”
Ya nuna musu gurin zama yana ɗauko farra ƙasarsa dake cikin ɗan ƙaramin windi. Sai da Teema ta fara gabatar masa da Rashida sannan ta fara faɗa masa matsalolinta da kuma abunda ke tafe da ita. Kai ya girgiza ya sake girgizawa sannan ya shiga duba ƙasar, can ya ɗago ya kalli Rashida ya ce.
“Wato ni bana ɓoye komai, magana ta gaskiya ƙasa ta bada bayanin ba zaki taɓa komawa gidan mijin ki ba”
Rashida ta daki ƙirji.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Sai hawaye ya fara bin fuskarta. Teema ta nuna damuwa sosai.
“Malam ko dai ƙasar bata ba da bayani dai-dai ba ne? Dan Allah a sake bincikawa”
“Ai babu wani bincike, ni ba zan cuce ku ba, kun ga idan wani ne sai ya nuna muku kamar aiki zai ci ya riƙa cin kuɗin ku”
Miƙewa Rashida ta yi tsaye tana hawaye
“Teema tashi mu je”
Kamin Teema ta tashi har Rashida ta kai ƙofar gida.
“Zan kira ka Malam”
Teema ta faɗa tana aje mishi kuɗi masu ɗan dama gabansa. A tsakar gidan ma Teema ce ta yi musu sallama da godiya, ko da ta fito waje har Rashida ta yi ma motar key ita kawai take jira.
Wani mahaukacin gudu Rashida ta fara, kamar marar hankali, har sai da Teema ta riƙa ta.
“Idan har kw baki son kan ki ni ai ina son ki, be kamata kina wannan gudun ba, yawancin bokayen nan ƙarya suke faɗa fa, ki bari zamu je wani gurin”
Uffan Rashida bata ce cewa Teema ba har suka isa ƙofar gidansu Teema.
“Idan Hankalin ki ya kwanta ki kira ni zan kai ki wani gurin”
Sai ta buɗe motar ta fita. Rashida ta fi ƙarfin minti goma a gurin tana kukan sannan ta kaɗa motarta ta yi gaba.
ASIM POV.
“Nice House”
Ya faɗa yana ƙarewa gidan kallo, hannu Nably tasa taja hancinsa.
“Gida zaka yaba ba ni ba?”
“Ke ai babu kalmomin da zan iya amfani da su na ya be ki da su, amman gida ko akwai kalmomi da zan yabe shi da shi”
Ɗan murmushi ta yi, tana ƙara kallon harabar gidan.
“Momi na ta so ta gaisa da kai, sai dai tafiyar gaggauwa ta kama ta yau, amman gobe dole ne ka dawo, dan momi ta ga wanda nake yawan bata labari”
Ya kai hannunsa ya riƙo nata.
“Wato gulma na kike?”
“Ba wani gulma, ba kai ba ne ka sace mata zuciyar ƴa ba”
“Ko kuma ƴarta ta sace zuciyar wani ba”
Cikin wasa ta kai masa duka, shi kuma ya goce yana mata wani kallo, tuni idonsa har sun soma canjawa. Yar yar daya fara jin jikinsa na yi ne yasa ya saki hannunta yana faɗin
“Bari ma zo ma tafi na wuni a gidan na ku ai”
“Wato har ka gaji da gani na kenan?”
“Kai ni har na isa, kawai dai naga magariba tana gabatowa ne, ai kin ga dole jibi naje na kai ki birthday ɗin friend ɗin ta ki, kuma mu zaga gari”
“Ai gobe ne”
Ya buɗe ido.
“Tab aiko dai gobe tafiya za mu yi da oga na, ban da haka kan wallahi babu abunda zai hana ni kai ki ko ina ne a faɗin duniyar nan”
Ta wara ido.
“Kar ka damu, nima ai ban cika son kaje ba gudun kar wata ƙwace min kai”
Sai da aka soma kiran sallah, sannan ya tashi, ta rakoshi har gurin motarsa, ta buɗe masa, har zai shiga sai kuma a juyo ya kalleta ya ce
“Haka zan je ba good bye?”
Murmushi ta yi ta juya ta juyo, kamar mai nuna masa mazaunanta, daman jikinta babu mayafi, sai kawai ta kai masa kiss a baki.
“Shikenan?”
Ya ɗaga mata kai yana wani shegen murmushi. Sannan ya shiga motarsa tana ɗaga masa hannu har ya bar gidan.
“Wow wayayiyace sosai, i'm so lucky”
Abunda ya furta kenan yana ƙarawa motarsa giya. Be tsaya ko ina ba sai da isa unguwarsu, a lokacin har an sauko daga sallar magariba, sai da ya shiga gida yayi wanka sannan ya fito a masallacin unguwar yaje ya yi alwala ya yi sallah, sannan ya koma cikin gidan ya ɗauki motarsa ya ƙarasa ƙofar gidansu Mardiya.
Ko da ya kirata yace yana kofar gidansu, bata cikin gidan, dan haka sai da ya jirata har na tsawon mintuna talati sannan ya ta iso gurin da saurinta. Ta kanta ta buɗe motar ta shiga tana masa sallama.
“Ya gida ya su Mama?”
“Wallahi lafiya ƙalau, ya naka gidan?”
“Gida na babu daɗi fa”
“Subhannalla miya same ka?”
“Kin san na zama gwauro yanzu, tun da kin kore min Namra”
Mardiya ta riƙe baki kamar gaske.
“Wai da gaske ne da ake cewa Namra ta fita?”
“Ba ki sani ba? Kuma saboda ke ta bar gidan?”
“Saboda ni kuma?”
“Eh dan ta gano ina son ki, shine ta so na sake ta ni kuma na ƙi na sake ta, shine sai ta tafiyarta”
“Kai amman ban jidaɗi ba, kaje ka dawo da ita dan Allah”
“Ni yanzu ba ta ita nake ba ta ki na ke”
“Ni kuma?”
“Eh mana, ni fa tsakani da Allah na ke son ki, kuma auren ki zan yi, shine abunda ya kawo ni yanzu, na baki kwana biyu ki je ki yi shawara”
“Amman Namra ba zata ce komai ba?”
“Ke kike ta kanta, ga wannan ni zan wuce, dan gobe zan yi tafiya yau nake son na fara shiri na”
Ya miƙa mata dubu goma, ƴan ɗari biyar-biyar. Ƙin karɓa ta yi har sai da ya matsa mata sannan ta karɓa tana masa godiya, ta buɗe mota ta fita.
KALSOOM POV.
Be barta ta yi aikin komai ba, shi ya haɗa musu abun kari, kuma ya haɗa musu ruwan wanka. Daman ita ta gaji sosai, tun da ta yi sallah asuba ta koma bachi, shi kuma ganin hakan yasa be tashe ba, ya barta ta yi bachinta, har ta gaji ta tashi dan kanta, sannan ya shigo ɗakin fuskarsa da Annuri.
“Tun ɗazu breakfast yake jiran ki”
Ya faɗa yana zama kusa da ita. Agogon ɗakin ta kalla ta ga sha ɗaya har da kwata.
“Kai ya aka yi nayi bachi haka?”
“Kin gaji ne, shiyasa ban tashe ki ba”
“Amman kai ka karya ko?”
A maimakon ya amsa mata sai kawai ya sakar mata ido yana kallonta, fuskarsa da mirmushi. Ɗan sunkuyar da kai ta yi itama tana maida masa da saƙon murmushin.
“Amarya ta”
Ya faɗa, tana mai cigaba da kallonta.
“Amaryar ka tana nan zuwa, ni kuma na zama uwargida a yanzu”
Murmushi yayi mai sauti, dan yaga kishinsa a cikin idonta.
“Ai ba gida ɗaya zaku zauna ba, kuma ita zata zauna da yara ne, that's means ke ce Amaryar”
Kai ta girgiza tana dariya, kamin ta mike tsaye.
“Bari na je na wanki bakina”
“Lemme help you”
Ya miƙe tsaye shi ma suka shiga banɗakin tare.
NAMRA POV.
Tun da ta shige ɗakin, bata fitowa sai idan fitsari zata yi ko shan ruwa, duk ta bi ta damu kanta, ta takura kanta. Duk yadda Neina ta so ta fito waje su yi fira sai ta ƙi, haka ta wuni da yunwarta daman can ba abinci take ci ba, sai Maltinar da Lamido yake badawa ana siyo mata, yau kuma ko maltinar ta ƙi ta sha.
Bayan sallame sallar isha'i yaro ya shigo, da sallama yana riƙe da kwanonsa ya bara yace
“Sallamu alaikum wai ance ana sallama da Namra, wai Abdullahi ne daga Katsina”
Tana cikin ɗaki ne, amman hakan be hanata jin abunda almajirin ya faɗa ba, sai kawai ta lumshe ido tana sauraren tsaran da kanta ke mata.
‘Wannan wane irin mutum ne?’
Ta tambaye kanta, tambayar da bata da amsa.
“Je ka ce bata nan”
Cewar Lamido zuciyarsa har wani kawowa take.
“A'a kai je ka ce gata nan zuwa”
Yaron na ficewa Neina ta kalli Lamido ta ɗora da
“Saboda girman Allah ka rufa mana asiri, muna neman abunda za mu ci ka jefa mu cikin wani halin kuma”
“Amman Neina tun da bata so ai ba ci aka ana cilasta ba”
Cikin yaren fulatancin ta mayar masa da amsa.
“Lamido babu ruwanka baka san yadda abun nan yake ba, kai dai ka cinto gefen tiri baka san tsakanin su ba, ka kama kan ka, ɗan Sarki ne fa”
Tana gama faɗar hakan ta nufi ɗakin da Namra take.
“Namra tashi kije yana kiran ki”
“Ni babu inda zan je”
Ɗukawa Neina tayi kamar zata zauna ta haɗe hannayenta.
“Ki yi ma girman Allah ki rufa mana asiri kije, haba Namra kar ki ba ni kunya mana na faɗa masa ga ki nan zuwa, dan Allah ki tashi ki je”
“Neina ko naje mi zan ce masa? Ni na riga na faɗa masa karya sake dawowa ƙofar gidan mu”
“Wallahi ban ce ki faɗa masa komai ba, saurarasa zaki yi, ki rufa mana asiri Namra”
Magiya Neina ta riƙa yi ma Namra kamar zata fasa mata kuka, sannan Namra ta tashi cikin ɓacin rai da zafin zuciyata ta fita.
Gurin da ya tsaya ɗazun a nan ya sake tsayuwa, duk da dare ne hakan be hana farin wata haskar fatar jikinsa ba, ga manyan idonsa da ya tsare ta da su har take ƙoƙarin faɗuwa kamin ta ƙaraso kusa da shi. Kasa furta masa komai ta yi, duk wasu kalamai da take da unƙurin faɗa masa sai ta kasa, suka tsaya mata iya cikin cikinta zuwa maƙogaronta, dan bakinta ƙin bata haɗin kai ya yi, ga ƙamshin turarensa da ke ta kaiwa hancinta hari.
Hannayensa dake rumgume aƙirjinsa ya cire ya maida cikin aljihu.
“Bude ba ki kiyi magana, faɗa min duk kalmar da kike tunanin ta cancanta a da ni, ki yi duk abunda kike ganin idan kin min saki samu salama.
Ayau na tsayu gabanki ne saboda kawai na ji tarihin rayuwarki, ban je neman auren ki, amman nasa a min bincike akan ki, tsakanin jiya zuwa yau labarin ki da hawayen ki sun nuna min akwai abunda kike boyewa”
Hawaye ta fara, tana ƙoƙarin ture kalamansa dake son su yi tasiri a zuciyarta.
“Ba lallai ne na cimma burina akan ki ba, mman lallai ne na faranta miki rai, kuma na taimaka miki ki cimma na ki burin, ina roƙon ki ki bani kaɗan daga tarihin rayuwarki ko zan samu sukunin rayuwa, Namra ni ba ƙaramin mutun ba ne, kuma ba wasa ya kawo ni nan ba, ki taimaka min wata ƙila ni ne silal farin cikin ki”
Ɗaga kai ta yi ta kalleshi.
“Ta ya farinciki zai dawo ga yarinyar da ta butulcewa iyayenta? Taya farinciki zai dawo ga macen data zaɓi saurayinta sama da iyayenta? Faɗa min ta ya?”
Yayi shiru yana karantar kalamanta. Yawun bakinta ta haɗiye.
“Ba kowa ba ce ni, fa ce wacce ta butulcewa iyayenta, da zabi saurayinta sama da su, wanda shi ne ya kai ni ga hakala.......”
Ƙoƙarin tsagaita kukanta take, dan ta samu damar labarta masa tarihin rayuwarta ko zai samu salamar rabuwa da ita. Zagayawa yayi ya buɗe bayan motarsa ya ɗauko carpet ya shimfiɗa mata. Sai da ta zauna sannan shi ma ya zauna nesa da ita zuciyarsa cike da tsumayin jin labarin nata.
Sai da ta share hawayenta, sannan ta soma bashi tarihin rayuwarta...
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *73*
Idonsa sun kaɗe sosai sun yi ja, duk ɗigar hawayenta ɗaya sai ya ji kamar an watsa masa ruwan zafi, ya kasa ɗauke kansa daga barin kallonta, har cikin ransa yake jin kukanta da kuma zubar hawayenta, samun kansa yayi da mugun tausayinta.
Ita kuma ta rumgume ƙafafunta sai kuka take, ba ƙaƙƙautawa.
Handkerchief ya riƙo daga aljihunsa ya aje mata, ba tare da ya ce da ita komai ba. Hannu ta kai ta ɗauka ta share hawayenta sannan ta fyace majina.
“Kin yi kuskuren zabar saurayinki sama da iyayen ki. Shiyasa Allah ya jarrabe ki, bayan Ubangiji babu wanda ya cancanci girmamawa sama da iyayenki”
Ɗagowa tayi ta kalleshi idonta taf da hawaye.
“Amman wanda mahaifina yake son na aura ba cancance ni ba...”
Ya tari numfashinta.
“Amman ai ya baki damar fitar da wanda kika so, sai kika nace sai shi saboda kar ya ce kin yaudareshi, ko ba haka kika faɗa min ba yanzu?”
Ta yi shiru tana sauraren hawayen dake bin fuskarta.
“Daga ƙarshe sai kuma ya yaudare ki, ya ci amanar ki, da ace kin aure wanda mahaifin ki yake so, babu yadda za a ayi ya guje ki, wata ƙila sanadiyar hakan sai ya shiryu, kuma duk abunda yayi miki dole su ne da laifi ba ke ba, baki san fushin Ubanguji yana tare da fushin iyaye ba? Idan iyayen ki sun yarda da ke, to haka shi ma Allah ya yarda da ke, kin yi aure mahaifinki yana fushi da ke taya za ki ga ribar auren?
Kin yi kuskuren rashin komawa gida Namra, ko yanka namanki za su yi su dafa su ci, bai kamata ki dawo nan ki tare ba”
“Idan kuma suka ƙi karɓa ta fa? Mahaifina ya ce karna kuskura na dawo gidansa da sunan saki ko yaji”
“Komai ya ce miki haka ne, saboda yana cikin fushi ne, da kin koma ai ba zai iya korar ki ba, idan kuma har idonsa ya rufe ya kore ki, to duniya zata miki masauki, su kuma ta juya musu baya, jama'ar gari kuma su zage su, har sai shi da kansa ya koma neman ki”
Ta bikita ɗaƴan ɓangaren na handkerchief ya share majiyar data cika mata hanci.
“Na yi nadama yanzu, na gane gaskiya”
“Kin yi nadama a lokacin da bata da amfani, kin sake tafka kuskure a cikin kuskure. Namra ba mutum kika aura ba, mutum mutume ne mai kama da mutum, siffarsa da kamarsa tasa kika ɗauka mutum ne, har kika masa inuwa, shi kuma ya saka ki a rana, mutumen da bai shirya haɗa zuri'ah da ke ba, amman Namra da yanzu a ace m cikin ki yana nan, a nan za ki zauna ki haihu kenan? Ba tare da kin koma gurin iyayen ko ba?”
Miƙewa ta yi tsaye ta yi tsaye ya saka takalminta, da zimmar komawa cikin gidan. Sai shi ma ya miƙe tsaye.
“Can i have my handkerchief!”
Juyowa ta yi ta kalli handkerchief ɗin, sannan ta kalleshi.
“Yayi ƙazanta”
Ya faɗa cikin muryarta mai gaf da yin kuka.
“Please...”
Ya ɗaga mata gira ɗaya, like he's serious. Ta ɗan ɗauki mintuna kamar mai shawarar miƙa masa abunda yake mallakinsa na ne.
“Please stop cry..”
Ya faɗa cikin muryarsa mai rawa kamar mai shirin yin kuka. Sai kawai ta miƙa masa handkerchief ɗin cike da ƙyama. Shi kuma ya miƙa hannu ya karɓa idonsa na kan fuskarta. Bata tsaya komai ba ta shigerwa tana ƙirƙirar wani sabon kuka.
Damƙe handkerchief ɗin yayi da dukan no ƙarfinsa, kamar abunda za a ƙwace masa, ya kai fuskarsa ya lumshe ido.
Har cikin zuciyarsa yake jin sanyin hawayenta, ya samu mintuna biyu zuwa uku a haka kamin ya buɗe motarsa ya shiga. Still da handkerchief ɗin a hannunsa yake driving.
“Da kin auri wanda Mahaifin ki yake so wata ƙila da ba mu haɗu ba, da ba zan iya kawowa rayuwarki ɗauki ba”
Ya faɗa yana mai sa ɗayan hannunsa ya fiddo wayarsa, sai da ya hau babban titi sannan ya rage gudun da yake ya danna ma Mai Martaba kira.
Ta ɗan jima tana ringing kamin a ɗauka.
“Assalamu alaikum”
“Wa'alaikassalam, Allah ya taimaki Mai Martaba”
“Babana kana lafiya?”
“Lafiya ƙalau Mai Martaba, Mai Mairtaba yanzu idan Madina (Sister sa wance suke uba ɗaya) ta zaɓi saurayinta sama da kai ya zaka ji? Bayan kuma kai ka yi mata zaɓi?”
“Ba zan ji daɗi ba, sai dai kuma ba zan hana ta aurensa ba, amman kuma ba zata ga da kyau ba, ba kuma dan ina mata fata ba, no saboda ba kasafai auren da iyaye basa so yake zama alheri ba”
“Idan kuma bayan ta yi auren mijin ya sake ta fa? Bayan ya gana mata azaba, sai ta dawo gare ka, ya za kayi?”
“Zan karɓe ta da hannu biyu na mata masauki ta yadda zan shimfiɗa mata sabuwar rayuwar, ita da kanta zata yi nadama ta gane lallai Uba, Uba ne, ta yadda wata rana idan ta ga wanda zai aikata hakan ita da kanta zata hane shi”
“Lallai Mai Martaba kai ne za ka taimaka min wajen dawo da martabar Namra”
“Wacece Namra?”
“Gobe da safe zan dira Katsina zan tabarta maka komai Mai Martaba”
“Allah ya kai mu”
“Amin mu kwana lafiya, Allah ya ƙara mana nisan kwana da lafiya”
Ya aje wayar yana murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa.
AMIRA POV.
Tana gama rubuta wasiƙar ta naɗe cikin wata paper, sannan ta ɗauki salati ta saka, ta ta saka ta cikin wani madaidaicin kwali ta yi rolling da wani jan gayenta sai ya fito kamar gift.
Sai da ta gama abunda ta ke sannan ta kwashe komai ta gyara gurin. Saman gado ta koma ta kwanta tana kallon sili kamar mai tunanin wani abu. Haleema ce ta turo kofar ɗakin ta shigo fuskarta ɗauke da damuwa dan ita har ga Allah tausayin Amira take.
Kusa da ita ta zauna tana kallon kwalin dake gefenta.
“Yau duk baki leƙo mu ba? Ko abinci ba ki ci ba”
Sai a lokacin Amira ta tuna rabonta da abincin tun jiya da rana. Sai dai kuma har yanzu bata jin yunwa. Duk ta wani zurma kamar marar lafiya.
Unƙurawa ta yi ta tashi.
“Bana jin yunwa, Dan Allah Haleema ki taimaka min ki kai ni tasha na bada wannan saƙon”
“Saƙon minene Amira?”
“Wasiƙa ce na rubutawa mutumen da ya fara cuta na, wata ƙila idan ya karanta zai gane ina raye har ya wanke, na koma gurin iyayena ko Allah zai sa Yayan ki ya so ni”
Bata damu da sanin abunda yake cikin wasiƙar ba, ta miƙe tsaye
“Okay, bari na ɗauko mayafi na”
Tana ficewa Amira ta tashi cikin rashin kuzari ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta da hawaye ya ɓata ta fito. Wannan karon Hijabi ta ɗauka ta saka, sai ta zauna gefen gado tana kallon kwalin zuciyarta sai bugawa take.
“Mu tafi”
Haleema ta baɗa yayinda ta turo ƙofar ɗakin makulin motarta na hannunta. Da sauri Amira ta ɗauki kwalin suka fice. Maganganu masu daɗi da tausasa zuciya Haleema ta riƙa mata har suka isa tashar. Suna shiga aka riƙa tambayar inda zasu sai Amira ta amsa da
“Motar Sokoto muke nema”
Aka nuna musu, almajira suna haɗawa da gudu ganin haɗaɗiyar mota a zatonsu ko da kayan dako ne. A gafen motoci Haleema ta faka motar suka fito tare, da ƙafa suka ƙarasa kusa da inda ake lodin motar sokoto suka samu direban yana daga gefe zaune yana jiran a gama haɗa masa passengers. Sallama suka fara masa sai ya amsa tare da mutanen da suke gurin.
“Dan Allah saƙo za a kai mu a sokoto”
Cewar Haleema.
“Ok na minene?”
Amira ta dire musu kwalin, kana ta ɗora da.
“Wannan abun za a kai ga addireshin”
Ta ƙarasa tana miƙa masa wata ƴar ƙaramar takardar. Hannu ya kai ya karɓa.
“Okay to zaki bada kuɗin mota, da kuma number wayarki da wanda za a kaiwa saƙon”
“Zan dai baka number na, amman ban da number wanda za'a kaiwa saƙon, shiyasa na rubuta maka addireshin sa, dan Allah ka taimaka min ka kai masa har gida”
“Okay ba matsala, amman gaskiya ko baki yo ba sai kin bada dubu uku, dan za a kai masa har gida ne, kuma kin ga yanayin da ake ciki ba mu cika son karɓar saƙo ba ma”
“Ina zuwa”
Haleema ta faɗa, sai ta juya ta nufi gurin motarta, bata ɗauki lokaci ba ta dawo ta miƙa masa dubu uku ƴan ɗari biyar biyar.
“Gashi amman dan Allah ka tabbatar saƙon ya isa, ki bashi number wayarki so that idan ya kai sai ya kira ya faɗa miki”
Ta ƙarasa tana kallon Amira. Ba musu Amira ta karɓi number wayarsa ta saka a wayarta, sai ta masa flashing number ta ta fito, sai da ta tabbatar yayi saving sannan ta juyo ita da Haleema suka nufi gurin da suka faka motar su.
Haleema ce ta fara shiga sannan Amira, har suka isa gida babu wanda yace da wani uffan, Haleema na wani tunanin na dabam, Amira ma haka har suka isa gida.
Tun kamin su faka motarsu Haleema ta gane yayanta ya dawo, ganin yadda sojojin suka koma cikin natsuwarsu sosai.
“Big bro ya dawo kenan!”
Ta faɗa tana zare key ɗin motar, Amira dai bata ce komai ba, har suka fita motar suka nufi ƙofar shiga falon.
Gabanta ya faɗi sosai lokacin data saka ƙafarta cikin falo, ta yi ido biyu da Abdool.
Abinci yake aunawa a cikinsa yana zubawa Ummi satti, yanayin fuskarsa kawai zaka kalla ka fahimci baya cikin damuwa, dan annuri ne shimfiɗe a fuskarsa.
Cikin sanyin jiki Haleema ta ƙarasa kusa da Ummi dana wasar haƙura, dan tasan laifinta na fita bata faɗawa Ummi ba.
“Daga ina kike?”
Ummi ta tambaya fuskarta babu alamun dariya. Ta ɗan sosa kai tana tunanin irin ƙaryar da zata yi ma Ummi dan bata jin zata iya faɗa mata gaskiya.
“Ya Abdool an sauka lafiya”
Amira da ke can gefe Haleema ta miƙawa Abdool gaisuwa. Ba tare daya ɗago ya kalleta ba ya amsa.
“Lafiya ƙalau”
Sai ya miƙe tsaye yana yi ma Haleema wani kallo.
“Daga Ina kuke?”
“Pizza na ce ta raka ni na siyo kuma ban samu ba”
Ta faɗa tana pretending like she's serious.
“Amman idan zaku je siyen Pizza sai kawai ki kama hanya ku fita without permission?”
“I'm sorry Ummi i promise ba zan sake ba”
“You're very stupid, haka kawai zaki saka kafa ki fita ba tare da kin faɗa ba? Baki san rayuwarku tana cikin haɗari ba? Ba ni kaɗai za a riƙa farauta ba har da ku”
Abdool ya faɗa yana kallonta har handkercheif ɗin dake hannunsa ya faɗi.
“Haba Big Bros Wallahi ba zan ƙara ba, dan Allah ku yi haƙuri”
Ta faɗa kamar mai shirin yin kuka. Amira kan idonta na kan Abdool, annurin fuskarsa kawai take kallo, a ɗayan ɓangaren kuma tana Allah-Allah ya manta da handkercheif ɗinsa ta ɗauke, ta yadda zata fi jin daɗin tuna sa idan tana tare da shi.
“Miya hana ki zuwa makaranta?”
Ya tambaya yayinda ya risina ɗaukar handkercheif ɗin.
“Yau ba mu da lacca sai four”
Be sake ce mata komai ba, ya kalli Ummi.
“Zan je gurin Mai Martaba”
“Mu zaka ku? Tun da ka sauka naga ka kira shi fa, akwai abunda kuke shiryawa ko?”
“Kedai Ummi kawai ki sa ido ki yi kallo, wannan tsakanin ɗa da uba ne”
“Idan tayi tsami ma ji, miye sunan in-law ɗin tawa?”
“Da saura Ummi, bata kama hanyar zama in-law ba tukuna, sai mun yi settling abubuwa. Her name is NAMRA...!”
Wani irin faɗuwa gaban Amira yayi har sai da kanta ya tsara.
‘Namra’
Ta maimaita sunan a ranta tana, tuna wacan Namra wacce take ganin ita ce silar shiga ta wannan halin rayuwar. Kamin ta kalli Abdool da ya kai hannu ya ɗauki apple ya fice yana wasa da shi. Ummi kuma ta tashi ta nufi Kitchen, sai ya rage daga Amira sai Haleema ne a falon. Amira ta matsa kusa da Haleema ta dafa kaɗatar.
“Haleema zan shiga ciki, idan Ummi fa faɗi abunda za a girka da ranar nan kya sanar da ni please”
“Okay Sleep well”
Cikin sanyin jiki ta juya ta nufi ɗakin Amal da ya zame mata kamar ɗakinta.
ABDOOL POV.
Cike da zumuɗi ya isa faɗar Mai Martaba, kai tsaye ya wuce part ɗinsa da yake zama. A babban falonsa ya same shi, Hajiya Shafa na haɗa masa abun karyawa, yana ganin ɗansa ya washe haƙura, wanda hakan sam be yi ma uwaegidan Mai Martaba daɗi ba.
Cikin girmamawa Abdool ya gaishe ta, ta amsa masa kamar babu komai sannan ya gaishe da Mai Martaba yana masa kirari.
“Ba wani daɗin baki da zaka min sai da ka fara gaishe ta sannan zaka miƙa min gaisuwa”
Dariya yayi shi da Hajiya Shafa, sannan ya ce
“Ayi haƙuri Mai Martaba, zafi zafina na zo dan labarta maka komai”
“Muma nan ai mun aje maka labari har da ɗuminsa”
Hajiya Shafa ta faɗa. Abdool ya ce
“Tau a fara bani na sha”
“Wannan albishir kuma Mahaifinka zai maka shi”
Ta tashi ta fice tana dariya. Mar Martaba ya miƙa ma Abdool tea da aka haɗa masa shi kuma Abdool ya aje tea a gefe ya shiga haɗa ma Mai Martaba wani yana labarta masa labarin Namra.
Sai kusan Sha ɗaya da rabi suka gama karyawa tare da Mai Martaba yadda Abdool ya zage yana cin abincin ba zaka ce ya ci abinci gurin Ummi ba.
Mai Martaba ya jinjina lamarin Namra sosai kuma ya tausaya mata duk da be ganta, bama abunda ya fi taɓa shi kamar yadda ya ji tana raɓe a gidan wasu bayan kuma uwarta da ubanta suna raye.
“Amman Ina ka haɗu da ita?”
Abdool ya yi shiru yana tunanin faɗawa Mai Martaba gaskiyas lamari.
“Ranka ya daɗe ina binka bashin albishir fa”
“Albishir ɗin ka, zan faɗa maka idan ka samu natsuwa kun kai ƙarshen wannan matsalar”
“Yanzu ya kake ganin za a ɓullowa lamarin?”
Mai Martaba ya gyara zamansa.
“Abunda za mu yi, zan sa a rubuta masa wasiƙa daga nan Masarautar zuwa can inda yake, ai kana da addireshinsa ko?”
“Eh ina da shi, dan nasa an min bincike akan sa”
“Okay zamu saka a aika ma Sarkin Musulmi na sokoto shi kuma zai aika wani ya kai masa wasiƙar”
“Amman Mai Martaba me zai hana ka aika masa kai tsaye?”
“Ai mu sarakuna bama haka, dole ne sai sarkin gari ya san da abunda wani sarkin yake so a garinsa. Musamman babban sarki kamar shi”
“Okay zuwa yaushe za a aika?”
“Yau zamu aika, ina tunanin gobe zata isa gare shi”
Abdool ya ji daɗin haɗin kan da Mai Martaba ya bashi sosai da sosai. Daman ya tsammaci haka, dan ƴasan yana samun goyon bayansa a dukan abunda zai yi.
KALSOOM POV.
*Bayan wata biyu*
Tun da aka soma shigo da kayan har aka aje,be ji motsinta a falon ba hakan ya tabbatar masa da tana kitchen, kai tsaye ya nufi kitchen ɗin, fuskarsa ɗauke da murmushi. Ta baya ya yi hugging ɗinta ya aika mata da kiss a gefen fuska.
“Me kike girkawa?”
Wuƙar dake hannunta ta aje ta juyo tana dariya.
“Hancin ka zan girka”
“An ya zaki iya cin hancin na?”
“Kwarai kuwa ta yadda Amaryar nan da taga baka da hanci zata ce ta fasa auren”
Ƙyalƙyalewa yayi da dariya, ya zageye kunkurunta da duka hannayensa.
“Shikenan sai ki kashe min kasuwa ko?”
“Eh mana ai ƙara ni kaɗai zan riƙa ganin kyan ka”
Ya riƙa hannunta yana dariya.
“Zo ki ga wani abu”
Gabanta yayi mugun faɗuwa, haka kawai ta annayana a ranta ba abun alheri ba ne, cire hannunta ta yi cikin na shi.
“Bari na juya miya sai na zo”
Be mata musu ba, ya juya ya fice. Ta ɗauki minti goma a kitchen ɗin tana ta fargabar fita, duk da bata san abunda zai nuna mata ba, tana ji a ranta kamar ba alheri ba ne. Ba ƙaramin dauriya ta yi ba kamin ta wanke hannayenta ya juya miyar sannan ta nufo ƙofar falo.
Tana ganin akwatuna jere a tsakiyar falonta, bugun gabanta ya ƙaru, idonta kuma ya cika da hawaye. Ga invitation card da kwalayin minti da cinka a saman akwatunan mai yawa ana ɗora. Jikinta yayi sanyi sosai, hawayen dake maƙalle a idonta ya gangaro zuwa kumatun ta.
“Ashe haka Rashida ta ji lokacin da za a auro ni ko?”
Ta faɗa muryarta na rawa. Ɗagowa Hilal yayi ya kalleta, sai ya miƙa mata hannu alamar ta zo, sannu ta fara takowa har ta kawo inda yake ta miƙa masa nata hannun. Sai ya zaunar da ita ƙasan kujerar ya ɗora mata hannayensa saman kafaɗunta, kasancewar shi yana saman cushion zaune ne.
“Ki duba ki ga idan akwai abunda babu zan ƙaro”
Kai ta girgiza ta miƙe tsaye.
“A'a ni nabar mata kayan duka ka kai mata, ina da kayana”
Shima.ya miƙe tsaye.
“Na sani ai, ba tsirara na auro ki ba”
Sai ta yi ƙasa da kanta tana hawaye. Hannunsa ya saka cikin nata yaja zuwa ƙirjinsa, sai kawai ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi.
“Sorry dear, zan canja miki komai idan kina buƙata, just be strong”
Kuka tayi sosai har sai da ta ɓata mishi gaban riga da majina, sannan ta sake shi ta nufi toilet ɗin falo saboda amai da taji ya cika mata baki.
ASIM POV.
Tun safe ya tashi ko da goma tayi yana cikin garin sokoto, A hotel ɗin Shukura ya kama ɗaki, sai da ya ɗan huta sannan ya kira Ubangidansa ya sanar masa da ya iso. Ya bashi tabbacin sai dare zasu gana, da alama can zai kwana inda yake, dan ya faɗa inda zai same shi a gidansa da ke Sama road.
Fitowa yayi ya biya kuɗin wuni ɗaya, sannan ya ɗauki hanyar gidansu, zuciyarsa cike da nishani, yana mai jin kansa lallai shi a yanzu wani ne.
Ko da ya isa unguwarsu ƙarfe ɗayan rana yayi, dan haka irin mazan nan masu zaman kashe wando duk basa nan sai da yamma suke zama, kasancewar unguwar minannata, haka suke da yamma ta yi, amman hakan be hana wasu ganinsa ba, dan tabbatar da shi ɗin ne yasa wasu gayu zuwa su bashi hannu shi hannu su gaisa suna masa yaushe gamu.
“Kai ke da wannan?”
Ɗaƴan ya faɗa yana nuna motar dake kusa da su.
“Eh Wallahi sai a taya mu addu'ah”
“Toh Allah ya taimaka ya tsare. Kace kai ma ka shigo gari, ko da yake kana sirikin Manjo Usman ai dole ka hau wannan motar”
Ɗan murmushi yayi.
“Babu ɗigon dukiyarsa nan”
Duk dariya suka yi, ba dan sun yarda ba, sai suka ƙara gaba suna nasu zancen.
Da farinciki ya shiga gida, yana doka sallama kamar wani baƙo. Da gudu Mama ta fito dan tabbatar da muryar ɗan na ta ne ko bashi ba, ganinsa yasa ta daki ƙirji tana ƙare masa kallo
“Ibrahim kai ne? Allahu akbar”
Ta shiga shafa kayan jikinsa tana kuka, shi kam sai dariya yake yana kallon ƙanensa dake sanye da uniforn ɗin makaranta suna kallonsa. Da alama suma basu gama tabbatar da shi ɗin ba ne.
“Ji yadda kuka tsaya kallo na”
Sannan suka yi dariya suka rugo a guje suka rumgume shi, suna murna. Sai da suka gama zumuɗinsu sannan Mama ta ɗauko tabarta ta shimfiɗa masa tsakar gida, ko zama be yi ba sai ga maƙota sun soma shigowa ƴan ganin gwan, kar ayi ba su, dan kace kwabo har labari ya fara zaga unguwar.
Ya sha gaisawa da mutane sosai, dan sai a lokacin wasu ke masa ya jiki. Sai kusan La'asar ya samu keɓewa da Mama suna tattauna lamuran duniaya.
“Amman wannan matar Allah yayi mata tausayi, irin wannan hidima haka? Ko dai auren ka zata yi? Allah dai yasa taimakon Allah ne take maka”
“A'a ai matar babbar macece, kuma ta san ina da mata, Allah yayi mata tausayi ne kawai”
“Ai har gobe na Allah basa ƙarewa, Allah saka mata da alheri, ba irin waɗannan lalataccin mutanen ba, ai na so ka zo da Namra ta yadda zaka je kaita su ga irin buɗin da Ubangiji ya yi maka”
Ya ɗan yi shiru kamin ya ɗora da.
“Ai na saki Namra...”
Mama ta daki ƙirji tana buɗe baki tare da gwalo ido.
“Kai ɗan nan? Yaushe?”
“Yanzu an kusa sati biyu gaskiya, bata zo nan ba?”
“A'a wallahi ai da tazo da sai mun samu labari”
“Daman na yi tunanin ba zata zo nan ba, amman nasan duk inda taje dole zata dawo”
“Hmmm ai ƙara ma daka sake ta, sai mutane gane ba dukiyar ubanta bace,dan nasan yanzu duk wasu haka zasu ɗauka, kai lokacin ma da baka da lafiya har da masu cewa wai ubanta ne ya ɗauki nauyin komai, ko zaka maida ita sai nan gaba”
“Wallahi Mama ina sakinta sai abubuwa suka buɗe min komai yanzu ba ni da matsalarsa, yanzu haka zuwan da na yi na zo ne na faɗa muku na samu matar aure kuma zan siya muku gida mai kyau na miliyan biyu haka sai ku zauna”
Tashi Mama ta yi tana rawa, kamar wata bayarabiya sannan ta ɗire tana ma Allah godiya tare da sujada.
“Kai ɗan nan Allah ya zuba maka albarka, da mahaifinka na nan da rai da ya gode maka”
Dariya yayi yana mai jin kansa sosai da sosai. Sun deɗe suna fira kamin ya cire kuɗi mai yawa ya bata wai ta siyo kayan abincin, gida kuma ta sa abincika mata idan an samu ayi masa magana. Sai da magariba ta yi. sannan ya yi wanka ya canja kayan daya zo da su, ya gyara jikinsa ya bar gidan sai ƙamshin turare ya ke.
RASHIDA POV.
Juyi kawai take saman katifar da saboda wani mugun ciwo da zuciyarta ke mata, tea ma daker ta iya tashi ta haɗa ta sha.
Bata yi mamakin ganin irin kiran da take ta samu daga ƙawayenta ba, ciki har da Asmee, sai dai bata damu da ɗauka ba dan a tunaninta ko zasu tambayeta dalilin barin gidan iyayenta ne, taji zafi sosai da taga har da ƙawayen da take nesa da su ne cikin masu kiranta, babu shakka labarin barin gidan iyayenta ya same su kenan.
Wannan tunanin yasa ta ƙara jin wani irin zafi ya rufe mata zuciya, yana ɗaya daga cikin dalilin daya sa ta ƙaurawace whatsapp saboda yawan tambayar gaskiyar mutuwar aurenta da ƙawayenta ke yi, wasu kuma suna jajanta mata akan mutuwar Rafiq.
Yanzu ma wayarta ce take ringing, wannan karon Momi ce dan haka ita kam ba zata ƙi ɗaukar wayarta ba, cikin hali na kamar marar lafiya ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta.
“Hello Momi”
“Ke Rashida kin san abunda ya ke faruwa kuwa?”
Ta tashi zaune da sauri cikin rashin gane zancen da Momi take mata.
“Miya faru?”
“Kina da labarin Hilal zai ƙara aure?”
“Eh na taɓa ji amman ban tabbatar ba”
“Kin san Teema ce matar da zai aura”
Haka maganar ta riƙa yi ma Rashida yawo cikin kai har tana jin kamar ɗakin ya juya mata.
“Wace Teemar? Ba dai ƙawata ba ko?”
“Ita fa”
“How true it's?”
“Ga Iv nan Ummu Faisak ta zo da shi, ko ba ita bace Fatima Jafar Mai Goro?”
“Ita ce, ta ya hakan zai faru?”
Tayi saurin kashe wayarta ta kira Asmee, bugu ɗaya ta ɗauka.
“Hello na kira baki ɗauka ba, kinji abunda yake faruwa kuwa?”
“Da gaske ne kenan?”
“Ashe kin ji”
Ta katse kiran ta jefar da wayar saman katifa cike da tashin hankali, rasa gane ta yi inda take sama ne ƙasa ne, duniya ne ko lahira, sai juya mata ɗakin ke yi, tana numfashi guda guda.
“It can't be Teema, idan har ta tabbata da gaske ne sai na ci Uwarki...!”
Ta faɗa cikin wani irin zafin rai, a take ta zari mayafinta ta fice.
YASMEEN POV.
Yana jefar da scul bang ɗinsa, yasa hannu yana ƙwaƙwala gurin kashinsa, yana tafiya ararrabe ya nufi kitchen.
“Momee na dawo”
Be same ta a gurin ba, sai Mai mata raino ya samu tana girka mata abinci.
“Ina Momee”
Ya faɗa yana jan rigarta.
“Tana ɗakinta”
Juyawa yayi da fuskar kuka ya nufi ɗakin nata, yana cigaba da ƙwaƙwala gurin kamar mai jim ƙaiƙayi. Da hannu ɗaya ya tura ƙpfar ɗakin ya shiga.
“Momee na dawo, kin ce zaki ba ni chocolate da safe”
Harara ta watsa masa dan ta tsani wannan soshe-soshen da yake yawan yi.
“Ba zaka cire hannunka a nan ba? Zan ci ubanka Adnan idan baka daina saka hannu a gurin ba, kai ƙazami ne ko?”
Ya yi saurin cirewa.
“A'a Momee ciwo ne yake min”
“Bari Dadee ya dawo ya saka maka magani, yana can ɗakinsa”
Ya faɗa, dan hana kowa ya saka masa ganin sai shi kaɗai, hakan yasa ya aje ganin gurinsa shi kaɗai zai riƙa saka masa ganin.
“Zo mu gani”
Ta aje Namra dake hannunta, ta riƙa wandon makarantarsa ta cire, sannan ta sake cire pant ɗinsa.
“Wannan ciwon yaƙi ya warke, ko dai maci ɗan wawa ne, amman kuma shi ai ba nan yake fitowa ba”
Ta ƙara buɗe gurin da kyau tana dubawa.
“Momee da zafi, Dadee yace na daina bari a na buɗewa, kuma ya ce karna faɗawa kowa zai dake ni idan na faɗa”
“Okay sorry ina duba maka ne, ai idan ya ji nice ba zai dake ka ba”
“Ya ce har da ke, kuma ya ce idan na faɗa abunda yake min sai ya yanke kamar yadda ake yanka rago, ya cinye nama na, ya soye”
Dariya ta yi dan bata ɗauki abun gaske ba.
“Wasa yake maka, ba zai maka komai ba”
“Wallahi yayi rantsuwa, kuma ...”
Ya faɗa cikin muryarsa mai kamar kuka. Yasmee ta juyo da shi, ta zaunar.
“Kuma me Adnan..?”
Sai kawai ya soma matsa ƙwallah.
“Talk to your Mom”
“Yace zai ba ni duka da yawa idan na faɗa”
“Minene”
Ganin kamar ya tsorata yasa ta ƙyalƙyale da dariya ta soma masa cakulkuli, sai ta jashi jikinta ta rumgume.
“Zo mu yi sirri da kai, ba zan faɗawa kowa ba”
Cikin dariyar cakulkulin da take masa ya ce.
“Allah zaki faɗa”
“Ba zan faɗa ba i promise”
“To kawo kunnenki”
Ta matso da kunenta bakinsa. Kaɗan-kaɗan ya raɗa mata.
“Dadee yake sa min abun shi nan, a baya”
Ta ɗago da mamaki tana kallonsa.
“Kai Adnan mu yi gaskiya da kai”
Kamin ya ƙara cewa wani abu mai aikinta ta ƙwalo mata kira.
“Anti Ana sallama”
Sakin sa ta yi ta tashi ta nufi falon, Zuciyarta da ɗayan biyu. Mai gadinta ta samu tsaye a falon riƙe da kwali yana shirin miƙa mata.
“Ga saƙo wani ya kawo yace a ba Alhaji wai hannuna hannunsa”
Karɓa ta yi tana faɗin.
“Okay, wanene?”
“Wallahi ban san shi ba. Ya wuce dai”
Tana karɓa, ya juya ya fice. Ita kuma ta kalli yar aikinta.
“Abincin be yi ba ne?”
“Saura kaɗan”
Juyawa ta yi ta nufi ɗakinta, cike da son jin maganar da Adnan ya soma tsaƙura mata.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *75*
Ko da sha ɗaya na safe ta yi Abbah da Anty Amarya suna katsina, amman basu samu ganin Mai Martaba sai da aka sauko daga sallar azahar, duk da haka kuma be ba da izinin a shigo da su ba sai da ya kira Abdool dan ya sanar da shi. Sai dai yasa an masu masauƙi a gefen sauƙar baƙi, duk abunda ya kamata a yi musu, an musu, abinci ma kusan kala biyar aka jera musu shi drinks, ba a maganarsa.
Mai Martaba be fito ba sai da Abdool ya iso. Sannan suka fito fada tare, ɗaya daga cikin dogarai aka aika ya yi musu iso.
Daga Anty Amarya har Abbah faɗuwa gabansu yake, dukansu zuciyarsu ɗauke take da fargabar kiran da Mai Martaba yake musu. Tun daga ƙofar faɗar Abbah ya tada kai yana kallon irin dukiyar da aka narka a gurin, daman tun farkon shigowarsa gudan ya koma baƙauye, dan duk kuɗin Abbah wasu abubuwan be taɓa ganinsu ba, sai a gidan Mai Martaba, wata ƙila saboda yana sarki ne, shine abunda ya fi ayyanawa a ransa, ga uban sojojin da aka zube a gidan sun matuƙar burgesa, ko ina na gidan cctv cameras ne.
Be ƙara raina kansa ba, sai da aka walgale masa ƙofar faɗa ya shiga. Komai na faɗar ruwan zinari ne, daga kan kujerun har center carpet, da fankar tsaye da ta sama hatta da maɓallin wutar faɗar golden color ne, ga bangon gurin an masa kwalli da wani abu mai kamar zinari, ga wani ƙaton agogon gmt na zinari a gefen faɗar. Alkyabar Mai Martaba ma yau golden ya saka, kamar takalminsa, sai farin rawani da ke kansa. Yarima Abdool na zaune gefensa, cikin shiga ta farar shadda, ya ɗora baƙar hula a kansa, fuskarsa sai wani sheƙi take kamar ango.
Kallo ɗaya Abbah yayi ma Mai Martaba ya yi saurin sadda kansa, saboda wani kwarjini da Mai Martaba ya yi masa, sai gashi ya zube ƙasa yana kwasar gaisuwa, kamar wani ƙaramin talaka.
Mai Martaba be amsa ba sai dai dogaransa ne suke amsa, kamin ya ɗaga musu hannu, ya muku musu izinin fita ba tare da yaƴi magana ba. Tsif ɗakin yai sai sanyi ac dake tsara jikinsu, Abbah dai be sake cewa komai ba, balle kuma Anty Amarya da ko ɗaga kai ba ta yi ba tun da suka shigo.
Tun daga shigowarsu, Abdool ya fahimci Anty Amarya ce mahaifiyar Namra, dan ga kamanin Namra nan shinfiɗe a fuskarta. Mai Martaba yai gyaran murya, wanda hakan ya tatttaro hankalin Abdool ya dawo gurinsa, dan jin shinfiɗar da Mai Martaba zai yi.
“Kai ne mahaifin Namra?”
Da sauri Abbah ya amsa gabansa na faɗuwa, tare da ɗaga hannunsa ɗaya yana bawa Mai Martaba girma.
“Allah ya taimake ka Ni ne”
Mai Martaba ya ɗauki daƙiƙu ashiri da uku kamin ya ɗora da...
“Amman kamaninka da yanayinka be nuna zaka iya aikata abunda ka aikata ba, sam ba kayi kama da mutumen da ya kori ƴarsa saboda ta zaɓi wanda take so ba”
Anty Amarya ta ɗan ɗago kaɗan ta kalli Mai Martaba da kuma Abdool, da take ganin kamar ta san shi.
“Ko kana da dalilin yanke wannan ɗanyin hukuncin?”
Abdool ya tambaya, cike da son jin labarin ta ɓangaren Abbah, wata ƙila ya sha banban da na Namra, idan kuma ya zo ɗaya, Namra ta faɗa masa gaskiya daman be zaci zata masa ƙarya ba, sai dai yana tunanin zata iya ɓoye mata wani abu daga labarinta, ko kuma laifin da ta yi ma Abbah ta.
“Ta zaɓi son ranta ne, bayan kuma na yi mata zaɓi, sannan ina ganin kamar wanda ta zaɓa be dace da ita ba, ta ɓata taraiyyata da mahaifiyar yaron, kuma ta watsa min ƙasa a ido cikin family mu shiyasa na sallama masa ita gaba ɗaya.”
Mai Martaba ya rausayar da kai, tare da kallon ɗansa kaɗan ya ɗauke kai ya mayar gurin Abbah.
“Idan ta kasance kai ne kake son mata fa? Sai kuma iyayenta suka hana ka aurenta har ya zama ka aure ta sai su yi fushi da kai, ya kake tunanin rayuwarka zata kasance?”
“Allah ya taimaki Mai Martaba, ba zan jidaɗi ba”
“Miyasa ka auna ƴarka a muhallinka ba? Kai fa uba ne, ban yi tunanin zaka iya aikata abu kamar wannan, ka kai matsayin da idan wani ya aikata ka kirashi ka yi masa faɗa. Ƴarka ba ƙarar ta kawo a nan ba, kaga yaro gashi nan shi ya ji abunda ya faru ya gurgiza da lamarin har yasa muka kira ka anan”
Mai Martaba na ajewa Abdool ya ɗora.
“Mijin da take aure ya sake ta, saboda ya ce a zubar da ciki ta ƙi, yanzu haka bata cikin garin katsina tana Kaduna, gidan wasu rakuɓe, ba abincin kirki babu abun sha na ƙwarai, kuma kullum kuka take, tana tunanin yadda za tayi ta koma gida har ka karɓe”
Tun da Abdool ya soma magana Anty Amarya ta ɗago tana kallonsa, hawaye sai bin fuskarta suke, daman kullum cikin kukan rashin sanin Halin da Namra take ciki take.
Sai dai zancen sakin da Abdool ya labarta mata ya sanyaya mata rai, hankalinta ya kwanta sosai lokacin data ji dalilin kiran da Mai Martaba yake musu, daman da daɗi tana addu'ah sai yanzu Allah zai amsa mata.
“Kasan abunda nake so da kai?”
Abbah ya girgiza kai tareda ɗaga hannu sama.
“A'a Allah ya taimake ka”
“Ina son ka yafe mata abunda ta yi maka, ko da ba zaka zauna da ita ba, ni zan zauna da ita a matsayin ƴata, daman ni gida na gidan ƴaƴa ne, amman idan ka yafe mata kuma ka saka mata albarka zata ga haske a rayuwarta”
Abbah ya sauke ajiyar zuciya.
“Allah ya taimake ka, ba wai bana son Namra ba ne, kawai ta aikata min abunda ban taɓa mafarkin zata aikata min ba ne, ta zaɓi wani sama da ni, ta bar karatun ta da danginta saboda shi...”
“Wallahi ta yi nadama yanzu, abunda kawai Mai Martaba yake so ka yafe mata mu zamu zauna da ita”
Abdool ya faɗa yana mai saukowa ƙasa ya zauna kusa da Abbah. Anty Amarya ta ɗago ta kalli Abdool.
“Idan har ya yafe mata, ni na fi kowa cancantar na zauna da ƴa ta”
Abbah ya data kai ya kalli Anty Amarya sannan ya kalli Mai Martaba.
“Mamana ta shiga rigarka ta samu alfarmarka, duk da yake ina jiran zuwan wannan ranar da Mamana zata gane kuskure da kuma gangancin abunda ta aikata, na sani wata zata dawo a gareni ko da kuwa mijinta be wulaƙanta ba, nasani wata rana zata gane muhimmancin iyaye, da kuma irin gudumawar da suke badawa a rayuwa, ko da babu saki na sani akwai ciwo, ba fata nake mata ba, amman nasan wata rana zai iya kamata ba duk miji bane yake zama da mace mai wani ciwo, sam bana son na mutu na bar Mamana a cikin halin da ta zaɓi kasancewa a ciki, na sani wata rana zata ratu ba ni, sai dai bana son ta rayu a cikin halin ina fushi da ita, dan nasan ba zata ga dai-dai, ina son Mamana sosai, kuma na yafe mata duniya da lahira”
Mai Martaba yayi murmushin ƙasaita irin nasu na manya.
“Lallai kana son ƙulla abota da ni”
Abdool ma yayi dariya mai cike da farinciki da har suka bayyana haƙoransa da kuma dimples ɗinsa ya ce
“Ni da Mai Martaba muna godiya”
Anty Amarya ta share hawayen idonta tana murmushi.
“Dan Allah idan tana cikin gidan nan ku faɗa mata Mahaifinta ya yafe mata, ta fito mu ganta”
“Bata tare da mu, tana can a Kaduna a wani gida rakuɓe, bata san Mai Martaba ya aika maka ba, ni ne kawai na ga tana cikin matsala kuma na san irin matsalar da rashin zama kusa da iyaye yake haifarwa”
“Allah ya maka albarka Allah ya raya maka iyalanka, ya cika maka burinka, ya taimake ka akan dukan lamurranka, na gode sosai yadda ki yi wannan jihadin Allah ya baka abunda kake so”
Ya amsa da “Amin” Yana wani sunsun da kai, shi ala dole ga surukin da ba san da shi ba 😂.
Mai Martaba ya miƙawa Abbah hannu yana murmushi.
“Yanzu kam zamu yi gaisuwar mutunci da kai, kaga har ƙoƙarin raba uwa da ƴa kake.”
Mai Martaba ya faɗa yana miƙewa tsaye. Da sauri Abbah ya miƙe tsaye, da hannunsa biyu ya riƙa hannun Mai Martaba yana dariya.
“Tuba na ke ranka ya daɗe, Allah yaja kwanan ka”
Juyawa Mai Martaba ya juya Abdool ya miƙe tsaye da sauri ya take masa baya. Har turakarsa Abdool ya rakashi farincike shinfiɗe a fuskarsa, Mai Martaba na shiga Babban falonsa Abdool ya riƙa alƙyabarsa ya cire masa ya jingine, sannan Mai Martaba ya cire rawaninsa da kansa ya aje a gefe, da sauri Abdool ya ɗauki rawanin ya aje a muhalinsa. Sannan ya zo ya zauna ƙasan carpet ya dafa ƙafafun Mai Martaba yana dariya.
“Na gode sosai da karamcin da Mai Martaba yayi min, ba zan taɓa manta wannan ba, Allah ya ja zamanin ka”
Murmushi yayi sai da aka ɗauki daƙiƙu sannan Mai Martaba ya amsa da
“Amin. Nan da minti talatin zamu je ɗan dime ƙaddamar da zakka, idan da hali sai ka shirya muje”
“...A...”
Sai kuma yayi shiru. Kallonsa kawai Mai Martaba yayi hakan ya cilastashi ƙarasa maganar.
“Da naso naje ne can Kaduna na kai su inda take”
Mai Martaba ya sake kallon ɗansa, irin kallon nan na akwai wani abu a ƙasa.
“Babana be kamata kana saka kanka a cikin irin wannan rayuwarba, karka manta kai ɗan sarki ne, kuma nan gaba kaɗan kai Sarki ne, sannan kai mutun ne mai babban muƙami a nigeria, be kamata ana ganin fuskarka a ko'ina ba, wani gurin kamata yayi ka aika, ko kasa ayi. Shi babban mutum ba ko ina ake son yana kasancewa ba, musamman ƴaƴan sarakuna, yana janyo raini, wani gurin ma yakan zubar da mutumcin mutum, amman kai sai naga kamar baka damu da hakan ba”
Yayi ƙasa da kansa, dan yasan Mai Martaba ya faɗi gaskiya, sai dai shi kan har ga Allah yana son ya zama na farko da zai fara yi ma Namra wannan albishir ɗin ko ba komai zai ƙara kwarjini a idonta.
“Amman Mai Martaba ina son na kasance nina zan yi ma yarinyar nan Albishir, idan mun kama hanyar Kaduna yanzu kasan kamin yamma mun isa”
Mai Martaba ya shafa fuskarsa.
“Idan har ganinta kake son yi, zaka iya aikawa a taho da ita”
“She's so stubborn ba lallai bane ta zo, kuma abun zai fi burgewa idan iyayenta da kan su sukaje suka ɗauko ta”
Kallon tsab Mai Martaba yayi ma Abdool sai ya ɗauke kansa, tare da ɗaga masa hannu, alamar go ahead.
*** **** ****
Fitar da Mai Martaba da Abdool suka yi ne, yaba Anty Amarya damar data kai ta ƙare ma Faɗar kallo. Manyan hotuna da ta gani na Abdool ɗaya a cikin kayan sarauta ɗaya kuma a cikin kakin soja, yanzu kan sarai ta tuna waye Abdool. Mutumen da ya taɓa taimaka mata lokacin da motarsu ta lalace ana ruwan sama.
“Gaskiya yana da kirki, matar ka da ƴaƴanka sun yi dacen uba na gari”
Ta faɗa idonta kan hoton Abdool. Abbah dai be ce komai ba, sai fama idonsa abinci yake yana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi faɗar.
Fitowar Abdool ne yasa duk suka maida dubansu gurinsa. Wata shigar ce a jikinsa bata ɗazun ba, wannan ma ta fitar da kyausa, da kuma annurin fuskarsa. Zuwa yayi ya risina gabansu, ya yi ƙasa da muryarsa sosai.
“Idan kun shirya zamu je Kaduna yanzu sai na nuna muku inda Namra take”
“Abunda muke jira kenan”
Anty Amarya ta yi saurin amsawa.
“Mai Martaba yana shiri ne, idan ya fita muma zamu kama hanya”
Ya faɗa yana kallon fuskar Abbah dan yaji me zai ce. Murmushi kawai Abbah yayi ya ɗaga masa kai, yana masa kallon mutum mai hankali da natsuwa.
NAMRA POV.
Murmushi kawai take, sai ɗaga kai tana maidawa, duk firar da ake, bata saka baki saboda itama nata ya isheta, su kansu suna firar ne ɗan kawai su rage mata kewa. Amman ta ƙi ta sake, sai dai a kan yi murmushi ko ɗaga kai, gudun kar suce ta ƙyale su, tun da Abdool ya takalo mata maganar gida sai ta koma wata irin, tunanin rayuwar jindaɗin da take ciki ta baya ta riƙa dawo mata, da kuma tunanin halin da Asim ya jefata, ga halin ko in kula da ya nuna mata, da kuma ƙin son haɗa jini da ita, ace duk tsawon wannan lokacin be neme ta, da gaske baya da buƙatar ta kenan? A ɗayan ɓangare kuma tana tunanin yadda zata shirya da iyayenta har ta koma ta zauna a tare da su wanda take ganin abu ne mai matuƙar wahala yin haka.
Duk dariya suka sa lokacin da Lamido yake bada wani labari na ban dariya, ita kam Namra sai ta saka kuka tana mai ɗaga murya dan damuwarta tasa ta manta da agaban jama'ah take, babu wanda hankalinsa ya fi tashi kamar Lamido, dan ya tsani ganin Namra cikin damuwa balle kuma zubar hawayenta. Sai da taga hankalin kowa ya dawo kanta sannan ta sassauta kukan da take ta tashi da gudu ta shige ɗaki. Ajiyar zuciya Lamido ya sauke cike da rashin daɗin rai ya ce
“Yarinyar tana cikin damuwa, ni ko bana son ganin ta cikin wannan halin, dan zai ƙara mata damuwar ne kawai, babu abunda yake raina a yanzu kamar na maza sanadiyar farincikinta, zan yi iya yadda zan iya na ganin na cire ta cikin wannan halin inshallah”
Neina ta miƙe ƙafafunta tana kallon ɗanta cike da son sa da kuma tausayinsa ta ce
“Cire yarinyar nan a damuwa abu ne mai wahala Lamido, ga dukan alamu ƴar babban mutunce, shiga irin lamarin gidan su sai yi wahala gareka tun da kai ba ɗan kowa ba ne”
Ɗauke kansa ya yi ya maida gurin ƙofar da Namra take. Sai da Neina ta tashi sannan ya miƙe tsaye yana ɗan ɗingishi ya nufi ɗakin. Zaune ya same ta kusa da ƙofa tana raira kukanta mai ban tausayi da taɓa zuciya.
“Namra kukan nan da zai miki magani da tuni yayi miki, kina ƙara saka kan ki ne cikin damuwa ne kawai”
Ɗago kai ta yi ta kalleshi.
“Idan ban yi kuka ba mi zanyi? Kana tsammanin mace data shiga cikin halin da nake ciki zata yi abota da dariya ko farinciki? Ba zaka gane abunda nake ji ba”
“Nasan kin shiga rayuwa kala-kala amman kuka ba zai miki magani ba, ki taimaka min ki tausaya min ki daina wannan kukan Namra, saboda gani nake kamar nine silar zubar hawayenki, ina damuwa sosai”
Hannayenta biyu tasa ta share hawayenta, sannan ta miƙe tsaye ta nufi gurin katifa ta zauna, ta yo ƙoƙarin tsayardar kukanta ne kawai dan ta lura da damuwar da Lamido yake idan tana kukan, balle kuma har ya kai ga yi mata magana, ita kanta tasan ba kowa ne zai juri zama da ita ta dinga masa kuka kamar ƙaramar yarinya.
Ajiyar zuciya Lamido ya sauke ya shafa fuskarsa sannan ya juya ya fice. Ba tayi minti talatin da zaman ba, taji yaro ya doko sallama wai Abdallah daga Katsina yana sallama da Namra. Wani baƙin haushi ta ji ya turniƙe ta, yau kuma da wacce ya zo? Me yake nema a gareta ne? Ba zai barta da damuwarta ba! Tana jin motsin shigowar Neina ta yi saurin kwantawa saman katifar ta lafe sosai kamar ta yi bachi.
“Na san ba bachi kike ba Namra, kuma kon ji lokacin da aka ce ana sallama da ke a waje, ki rufa mana asiri ki tashi kije”
Neina ta faɗa zuciyarta Fal da tsoro, dan ita tun da taji ance ɗan sarki ne, duk fargaba da tsoro suka kama ta, kullum zulluminta ɗaya kar yasa ayi musu wani abu.
Sosai Namra ta so tayi pretending like tayi bachi amman jin yadda muryar Neina take mata magana kamar mai magiya, yasa ta motsa har ta buɗe ido ta kalle
“Neina ban san me mutumen yake nufi da ni ba, me zai zo yayi min a yanzu?”
“Kije dai Allah, ko ma minene zaki ji, kin rufa mana asiri Namra, kin ga mu talakawa ne bayin Allah, karki ja mana abun ba zamu iya ɗauka ba”
“Bana nufin janyo muku komai Neina, amman kamar ba ki fahimci abunda nake nufi ba”
“Na fahimta, kawai ki tashi ki tafi, idan kuma har baki jin tafiyar, ni zan iya bashi izinin ya shigo nan yayi magana da ke, wata ƙila ma carpet ɗinsa da daya manta shekaranjiya ya zo karɓa”
Kamin ta Namra ƙara yin magana. Lamido ya ɗaga labulen ɗakin ya kunno kai yana faɗin.
“Neina kina tsoron masu milki da yawa”
“Dole na tsoraci masu milki Lamido, kafi kowa sanin sune sanadin shigar mu wannan halin”
Tana kaiwa nan ta juya ta fice. Shi ma Lamido juyawa yayi ya fice cikin rashin daɗin rai, yakan samu kansa a cikin rashin jindaɗi a duk lokacin da Yarima ya tsaya ƙofar gidansu da sunan kiran Namra.
Namra bata motsa daga inda take ba, sai ga Neina ta dawo ɗakin riƙe da carpet ɗin ta miƙa mata.
“Tashi kije ki kai masa, ko ba komai wulaƙanta ɗan Adam babu kyau, balle babban mutun kamarsa”
Wannan karon Namra bata yi mata musu, ta tashi ta karɓi carpet ɗin ta miƙe tsaye, already tana da hijab ɗinta sanye, sai kawai ta bi bayan Neina suka fice tare, takalminta ta zura, ta nufi ƙofar fita.
As usual gurin daya saba tsayuwa ya tsaya, tana tunkara inda yake tsaye gabanta ya soma faɗuwa, ta rasa dalilin daya saka yake mata kwarjini, tana isa kusa da shi ta miƙa masa carpet ɗin ta ce
“Ga carpet ɗin ka dan nasan ita ka dawo ƙarɓa”
Be ɗago ya kalleta ba, balle ta gane maganarta ta ratsa kunnensa, sai sha'aninsa yake da wayarsa, kamar be san da tsayuwarta a gurin ba.
Tayi tsayuwar minti ɗaya a gurin zuwa biyu, kamin ya ɗago ya kalleta ta cika sosai da taji kamar ta jefa masa wata baƙar magana amman bakinta be bata haɗin kai ba, gashi sai jin take kamar ta jefa masa carpet ɗin, sai dai kwajininsa ya hana hannunta kuzari, ballema ta yi ƙoƙarin yin hakan.
Babu enough hasken da zai iya haske fusakarta sosai, amman hakan be hana shi karantar tana ciki fushi ba, ko ba komai yasan ya ɓata mata lokaci, kuma ya shiga huruminta na ƙinjin gargaɗin da tayi masa akan kar ƙafarsa ta sake tako ƙofar gidansu.
“Ƙomai naki kyau yake min Namra, fushinki da faɗanki da tsawarki duka burgeni suke, abu ɗaƴa ya rage min yanzu na gani naki, shine dariyarki”
Ya faɗa yayinda ya ke cigaba da dannar wayarsa, amman hankalinsa da idonsa suna kan Namra. Wannan karon tayi nasarar yaudarar kanta, har ta samu haɗin kan idanuwanta, ta jefe Abdool da wani shegen kallo.
“Carpet ɗin ka kawai na fito kawo maka, ban fito dan ka yaba fushi ko faɗa na ba, kuma bana tunanin an halicceka dan ka ga dariyata kawai, saboda haka karka ɓatawa kanka lokaci, ka karɓi Carpet ɗin ka”
“Miya hana ki bar carpet ɗin a inda na barta tun ranar? Wane salo ne yasa kika ɗauke ta? Yanzun da nazo na aika nace a bani carpet ne? Wato ba zaki iya ganin abun Abdool ki ƙyale ba ko?”
Wannan karon da murmushi a fuskarsa, ya soka mata wannan maganar, ya gyara tsayuwarsa yana kallon taurarin da suka yi sama ado.
“Ai mu ƴaƴan Sarakuna bama shimfiɗa kuma bama ɗaukewa, wacan karon ma ba na shimfiɗawa kai na bane a karon kai na, nasan wata rana zan rubuta a diary, bayan Mai Martaba da Ummina, na taɓa shimfiɗawa Namra carpet har ma na zauna da ni da ita”
“Amman kai ka baka da aikin yi Wallahi, Allah yayi min tsare da mugun ƙudirinka, baka cikin hayyacinka ne? Miyasa zaka zo kana min wasu kalamai kamar wanda be san halin da nake ciki ba?”
“Ina ma ina da mugun ƙudiri a kanki! Da kin ga yanzu sace ci kawai zan yi na gudu naje nayi rayuwarda da nake so da ke, ni kaina ina mamakin halin dana shiga saboda ke, ban san miyasa ƙwaƙwalwata take ƙoƙarin zautuwa da lamarin ki ba”
Kai ta girgiza ta jefar da carpet ɗin a ƙasa.
“Wallahi baka da tausayi baka da tunani kwata-kwata a zuciyarka, taya zaka kalleni ka yi irin wannan maganar, you're fake Prince ba asalin Yariman ƙwarai bane kai, wata ƙila sarautar ta ku ta ƙauye ce, dan yariman ƙwarai ba zai tsaya mace kamar ni tana faɗa masa magana ba”
Lumshe ido yayi yana murmushi, tare da tsutsar baki kamar mai shan Sweet Candy. Ko da ya buɗe idonsa har ta ɓace daga gurin kamar walkiya.
Murmushin da ke fuskarsa ya faɗaɗa, kamin ya shiga muhalin massages ya aika saƙo. Cikin mintunan da basu fi goma ba, sai ga wata mota ta faka a gurin ɗauke da Anty Amarya da Abbah.
“Ga gidan can”
Ya faɗa yana nuna musu da kai, sannan ya buɗe motarsa ya shiga. Su kuma suka doshi ƙofar gidan, Abbah ne ya tsaya daga waje, Anty Amarya ta kunna kai ciki, zuciyarta sai bugawa take fat fat fat...
HILAL POV.
Ba a'ayi wasu events ban da walima, daman can shi baya ra'ayi sai kuma aka ci sa'ah amaryar tasa uztaziyace ita bata da son duniya. Ranar jumma'ah akayi walimar bayana an saka amarya lalle kamar yadda al'ada ta gada. Sai aka ɗaura aure ranar asabar, an yi taro sosai musamman ta ɓangaren Teema tun da ita aurenta ne na fari, kuma ita ta farko mace da mahaifinta zai fara yi ma aure. Yadda Hilal yaƙe yaƙar baki yana amsa gaisuwar mutane da ala sa albarka sai ka ɗauka auren so da ƙauna ne suka yi shi da Teema, tun da sha biyu aka ɗaura aure aka yi liyafar cin abinci bayan a sauko daga sallar azahar. Shi kam be samu dawowa gidansa ba sai da yamma ta yi lis.
Yadda ya tararda Kalsoom be yi zaton zai same ta haka ba, ta bala'in ruɗashi, kyau tayi har na fitar hankali, bakar shaddace jikinta an mata riga da saket, ɗinkin ya matse ta ya fitarda surar jikinta sosai, ta kashe ɗaure ɗankwalinta ya kalli kudu masu gabas, ga wata uwar kwalliyar kanti da aka mata a fuska, yadda take motsa bakinta ma abun kallo ne.
“Ango ka sha mai”
Ta faɗa tana wani fari da ido. Shi dai mutuwar tsaye yayi a ƙofar falon yana kallonta, sallama ma sai ta gagari bakinsa, ji yayi kamar ya je ya rumgumeta sai dai ƙanenta da kuma Amiyarta Salma dake falon sun han shi rawar gaban hantsi.
Yana amsa gaisuwar da suke masa ya nufi ɗakinsa, zuciyarsa cike da ƙaunar matarsa, dan yaji daɗin halin daya same ta ta bashi ƙwarin guiwa sosai, shi da ya zo da zimmar ya lallaɓata kar ta saka ranta a damuwa, sai gashi yaga kamar ma ta fi shi farinciki.
Babbar rigarsa ya fara cirewa sannan ya zauna saman gado, sai gata ta shigo hannunta riƙe da copin madara ta yanka masa ayaba ciki ta saka sugar kaɗan. Saman ƙafafunsa ta zauna ta riƙa aika masa madarar a baki, shi ko sai wani lumshe ido yake yana buɗewa kamar wani tsohon ɗan iska, kamin yasa hannayensa ya zagaye kunkurunta.
“Wannan ado haka ai sai ki haukata, so kike amaryar nan ta rasa gane kai na ko?”
Murmushi ta yi ta aje kofin a ƙasa tasa hannayenta ta riƙa kunnensa ta ɗora goshinta saman nasa.
“Ai niban yarda zata gane kan ka ba, dan wata mace bata isa ta shigo gidana ta fini gane mijina ba, da dai Rashida ce da ita ba zan musa mata ba, saboda ta rigani saninka, ni kuma a yanzu na fi Amaryar ka sanin waye kai”
Murmushi yayi yana shafa bayanta da suka hannayensa biyu. Dauke kanta tayi daga nassa but stilll hannayenta na rike da kunnensa guda biyu.
“Wai ance ƙawar Rashida ce da gaske?”
Ya ɗaga mata kai yana wani lumshe idonsa da suka kaɗe.
“Uhnn amman ai ba ni nace ina son ta ba, Hajiya ce ta haɗa auren saboda ta yaba da tarbiyarta”
Ta yi murmushi kamar ba komai, alhalin na ciki na ciki.
“To Allah ya baku zama lafiya”
Sai ta saki kunnensa ta riƙa hannayensa dan tana jin yana ƙoƙarin wuce gona da iri, ta miƙe tsaye.
“Ina zaki?”
“Aiki zanje na ƙarasa”
Yayi saurin miƙa hannu ya riƙota.
“Haba karki zalince ni baiwar Allah”
“Ba wani zalinci, nima fa mai tsada ce kamar amarya, dan haka ni jiki zaka siya ba baki ba”
“Ai har kin fi amarya tsada, ke da ga wannan ciki, amman dai amin farashi mai sauƙi ta yadda zan iya biya”
“Ba yanzu zamu yi cininki ba, kai fa ango ne karka manta, nan da ƙarfe goma na dare sai yadda ka ga dama zaka yi da amaryarka”
“Bari wanka da kashi indan ganin hadari, ayi jiran abunda ba tabbas bayan ga ki ina gani”
Ta fisge hannunta ta nufi ƙofa.
“Ni kan nan gani na bari wannan wunin da daren ba nawa ba ne”
Ganin zata fice da gaske yasa shi wara ido, jikinsa a mace yace
“Wai da gaske kike yi? Ki taimaki bawon Allah, karki jefa rayuwarsa cikin haɗari”
“Au naka wasa ne kenan!”
Ta fice tana dariya kamar ba komai, sai dai can cikin zuciyarta ji take kamar an aza mata garwashin wuta a ciki, saboda kishi da baƙinciki. Tana ta ƙoƙarin yaƙar zuciyarta ne, dan bata son ta saka kanta cikin matsala saboda cikin dake jikinta, daman can lafiyar cikin be isheshi ba, idan kuma tace zata saka damuwa a ranta, to zata cutar da kanta ne kawai, tun dai aure an ɗaura, kuma tasan mijinta yana sonta, sai dai ɗan kishi da ba'a rasa ba.
Bayan fitarta, ta shiga bathroom ɗinsa yayi wanka, ya fito ya shirya cikin wata shaddar gizna mai kyau da sheƙi. Yana cikin saka agogon hannunsa Kalsoom ta shigo ɗakin ɗauke da plate ɗin abinci. Fried rice ce and pepper chicken sai ƙamshi take, kallo ɗaya yyi ma abincin ya ɗauke idonsa wai shi ala dole yana fushi da ita.
“Waya ce miki abincin zan ci? Ai ba yunwa na ke ji ba”
“Shikenan kuma ango sai yayi fushi ranar aurensa?”
“Waya ja nayi fushin? Sai ka taɓa abu a hanaka lasawa, ai wannan cin zalin ne”
Gwalo ta mishi taja ƙofar ta fice. Sai ta fashe da dariya.
“I love you”
Ya furta tana shirin zama ya ci abincin. Shi kansa be san yaji yunwa kamar haka ba sai yanzu, tass ya cinye abinci da da lemun kankana data haɗa masa mai lemun tsami ciki da sugar kaɗan, har ƙashin sai da ya taune ya tsotse ruwan, dan yaji daɗin abincin sosai, ga lemun da sanyi sai rmratsa ƙwaƙwalwarsa yake, bayan ya gama ya tashi yana hamdala. Tana shigowa ta saka masa ɗariya, har da riƙe ciki.
“Ni dai nasan mijin Amarya yana jin yunwa”
Shima dariyar kansa yake dan yasan yayi aiki.
“Ai ba ni na ci ba, aljanuna ne suka ci”
Matsawa yayi ya maita kiss a goshi.
“Amarya tace ta yafe miki daren nan na ta”
“Uhmmmm”
Ta wara ido.
“Wace sakaryar amaryace zata yarda ta yafe wannan daren mai tsada a rayuwar ko wacw ya mace, balle kuma da gwarzon namiji kamar ka”
Ya kalli kansa yana wani kaɗe shaddarsa.
“Allah? Ina jin daɗin yadda kike yaba ni”
“Ai ka haɗu ne Malam, dole a faɗa”
Ya riƙa fuskarta ransa fari ƙal da farinciki.
“I love you so so so very much”
Murmushi ta masa as respond, ya fice yana dariya. Sai ta ji tashin motarsa cire ɗankwalinta ta jefar, ta faɗa saman gadonsa ta fashe da kuka.
ASIM POV.
“Yes...!”
Ya bugi ganbun motarsa yana dariyar da har zuciyarsa ita ce.
“Kin biyani Mardiya, zan baki mamaki, kuma auren mu nan kusa nake sonsa ba sai nesa ba, dan haka daga yanzu ki shirya a ko yaushe zan iya zuwa gaishe da iyayenki, sannan na turo magabatana”
Hannayenta biyu tasa ta rufe fuskarta 5ana dariya, sai tayi cikin gidansu da gudu kamar wata mai kunyar gaske.
Ya daɗe tsaye a gurin yana kallon ƙofar gidansu, sannan ya zaro wayarsa dake ringing ya kara a kunne.
“Na'am Hajiya kin dawo ne?”
Ban ji ma tace masa ba, sai kawai naga ya gyaɗa kai yana faɗin.
“Okay kina ina yanzu?”
Can kuma sai naga fuskarsa ta canja.
“Eh nasan gurin. Okay gani nan zuwa”
Ya sauke wayar kamar mai tunani. Can kuma ya ɗaga kafaɗunsa. Ya buɗe motarsa ya shiga.
Yana cikin driving ya kira ƙanen mahaifinsa dan jin yadda aka yi maganar gida.
“Eh yana da kyau sosai? Bedroom nawa ne a gidan? To ko dai mu bari sai an samu wani? Okay ba matsala”
Ya kashe wayar, sannan ya ƙara gudun motarsa, cikin ƴan mintuna ya isa unguwarsu Nably, a kusa da gidansu ya faka ya sake kiran Hajiya.
“Gani na ƙaraso unguwar, amman ban ganr gidan ba”
Daga ɗayan ɓangaren ta amsa masa.
“Baka ga wani green gate ba?”
“Na gani, Mai farin fenti”
“Eh to ka shigo ciki amman ka tsaya daga gate zan fito na kawo maka”
“Okay”
Ya tashi motarsa ya nufi gate ɗin gidan. Be ƙara gasgatarwa ba har sai da ya shiga harabar gidan, kusa da gate ya faka, yana ƙara kallon harabar gidan.
“Akwai bura'uba...”
Ya faɗa yana kallon Hajiya Sadiya wacce ta fito riƙe da ƙatuwar leda, sai faman sauri take kamar wacce ta yi sata.
“Ka saka min a wannan account ɗin”
Ya miƙa masa farar takarda tare da ledar dake hannunta. Cikin ladabi ya karɓa ya na faɗin
“Hajiya wannan ma gidanki ne?”
“Eh jeka dan Allah da sauri, bana son a tararda kai”
“Okay”
Ya koma cikin motar yana ta kallon gidan. He just can't believe gidan Hajiya ne, mi hakan yake nufi ita mahaifiyar Nably ce ko yar'uwarta.? Har ya bar gidan be samu amsar tambayarsa ba.
YASMEE POV.
Tana jin tsayawar motarsa ta tashi da sauri ta nufi kitchen, cox she dunno what to do, kuma tana jin kamar bata son ganinsa, duk da tana ƙoƙarin yaƙar zuciyarta dan sanin gaskiyar lamari. Hannayenta biyu tasa ta dafe fuskarta tana busar da iskar bakinta.
‘Ni fa lauya ce, ni nake fawa wasu magana, ni na saba bincike, dan me yau kuma zan rikice, i need to do this ko dan na cire kaina daga zargi’
A zuciyarta take wannan maganar, a fili kuma murmushi ne shimfiɗe a fuskarta ta juyo tana amsa kiran da yake mata.
“Yau wace rana baki je office ba ne?”
Yayi mata kiss.
“No naje yau cases biyu ne kawai da ni, ina gamawa na dawo, ya aikin naka?”
“Alhamdullah, ina da labari mai dadi, Abbah (Baban Namra) ya buɗa mana wani sabon kamfani a Abuja, kuma nasan niɓe zan kula da shi”
“Wow amman Abbah ya kyauta mana, Allah yasa hannu a ciki, ko shi yasa aka aiko maka da wasiƙa? Ɗazun an kawo wasiƙa a aje maka”
“Waya kawo”
“Wallahi ban sanshi ba, tana nan ɗakinka na aje maka”
Freezer ya buɗe ya ɗauki gorar ruwa ya nufi ƙofar fita yana tambayar abunda aka dafa. Da kallo Yasmin ta bishi bayan ta bashi amsa idonta cike da ƙwalla.
“Allah ka sani ina son mijina, Allah karka tabbatar da zargina akan sa”
Ta share hawayen da suka zubo mata. Tana ƙoƙarin fita sai gashi ya shigo riƙe da wasiƙar hankalinsa tashe.
“Kin karanta wasiƙar nan Yasmin?”
“A'ah miya faru?”
Ba komai, ya juya ya fita da sauri. Sai da ta tabbatar ya shige ɗakinsa sannan ta rufa masa baya. A bathroom ɗin falo ta tsaya ta sakama ƙafafunta ruwa gudun kar yaji sawun takun ƙafarta. A bakin ƙofar ɗakinta ta kara kunnenta, sai dai bata ji alamar motsinsa a cikin ɗakin ba. A hankali ta tura ƙofar ɗakin daman be mata rufin ƙwarai ba, nan ma babu alamunsa har toilet ɗinsa taje ya leƙa bata ga kowa ba. Mamaki ne ya kamata ina yaje,da sauri ta juyo ta fito. Har zata shiga ɗakinta, sai kuma ta nufi gurin engine ɗin wankinta. Daga inda take tsaye ta hangosa yana waya, daga gani ba wayar aiziki bace yake, dan yadda yake jinjiga jikinsa yake safa da marya na ya nuna haka. Yana gama wayar ya juyo yana faɗin.
“Namra bata zame min matsala ba ke zaki zame min, babu wanda ya isa ya datsa min rayuwar jindaɗi wallahi”
Karaf idonsa cikin na Yasmin, dake tsaye gafen ƙofa.
THE GAME IS ABOUT TO START...😿
_____________________________________
I feel much better Alhamdulillah. Na gode sosai da addu'ah da kulawa, Allah ya bar zumunci. Jazakallahu khairan all 😘
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *74*
Ko parking ɗin kirkir bata yi ba a gidansu Teema ta fita Motarta, zuciyarta na bugun bugawa, taron mutanen da tara a gidan ya ƙara tabbatar mata da maganar Asmee da kuma Momi.
Teema na hangota ta tashi daga cikin mutanen da take ta nufi wani ɗakin wanda babu kowa a cikinsa.
Kai tsaye Rashida ta bita daman ta ga shigowarta, wasu daga cikin ƙawayen Teema har sun fara magana, dan wasun su sun san mijin Rashida ne zata aura, wasu kuma a yanzu suke samun labari, ganin yadda ta shigo cikin gidan a birkice.
Da wani irin ƙarfi Rashida ta banki ƙofar ɗakin da Teema take ta shiga hasale.
“Marar mutumci wacce bata gaji arziki ba, ni zaki yiwa ha'inci? Ki zagaya ta bayan idona ki ci dunduniyata”
Hannayenta biyu Teema ta kama ta riƙe tana hawaye.
“Dan Allah ki saurare ni, karki yanke min hukumci ba tare da kin saurare izuri na ba...”
Rashida ta fisge hannunsa tana mata wani kallo na uku saura kwata, kamin ta katsa mata tsawa kamar wata ƴarta.
“Babu wani daɗin baki da zaka min, macuciya wai tsabar rashin kunya ni zaki ciwa amana..”
“Ban ci amanarki ba Rashida ko kowa ya zarge ni ke be kamata ki mun haka ba, ni kaina ban san da wannan haɗin ba, dan be taɓa zuwa fira gurina ba sai da zai kawo min iv, su Hajiya ne suka haɗa komai”
Ta ƙarasa da kuka tana wani ƙara narkewa kamar gaske. Rashida ta watsa mata wani kallo.
“Ke kar nake kallon ki, kamar naira a hannun yaro, yadda kika yi boka haka na yi karki nemi raina min hankali, wallahi mafitarki ɗaya ki fasa auren nan ko kuma na ci uwarki”
Teema ta yi wani Shu'umin murmushi tana kawardar hawayen ƙarya dake fuskarta.
“Idan kuma ba ki ci uwata ba, ni sai na ci ubanki, da aka halitto Hilal an ce miki ke kaɗai zaki aure shi ne? Ke in ban da haukarki ma miye na kishi bayan ya sake ki da ya kama ki da wani ƙato ko kin ɗauka ba'asan abunda ya fitar da ke gidan Hilal ba? Kina ganin kamar ba san komai a rayuwarki ba ko? To malamin dana kai ki gunsa, shi ya faɗa min komai a kan ki”
Jikin Rashida yayi sanyi har tana sassauta murƴarta duk da tana cikin zafin rai ne.
“Yayi dai-dai kuma ina fatar ya duba miki ya faɗa miki igiyar aure ba zata taɓa shiga tsakanin ki da Mijina ba, dan Wallahi sai na rusa wannan auren ko ta yaya, dan babu yadda za'ayi yar iska irin ki ta tarbiyantar min da yara, sai na faɗawa Hilal irin matar da zai aura”
“Yar iska kamar uwarsu ko? Ai abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne, kuma idan baki rusa auren nan ba, baki haihu ga uwarki da ubanki ba, ai Hilal ba mijin ki bane mijin Kalsoom ne da Angon Teema, ƴar baƙin asiri kinje kin yi ma kiahiya ya dawo kan ki kin kashe ɗan ki da hannunki, Ni ko nafi ƙarfin ki gaba ɗaya ke da danginki, kuma wallahi duk kika kuskura sake saka baki a maganar auren nan sai na faɗawa duniya dalilin mutuwar auren ki, da kuma dalilin mutiwar ɗan ki, ga kuma cutar da take tare da ke, dole har ƴaran ki su gujeki, ko kin ɗauka ba a san dalilin korarki da ubanki yayi ba?”
Gaba ɗaya jikin Rashida ya gama sanyi, zafafan kalaman da Teema tayi masa sun ƙatse mata duk wani hanzari da take da shi, har ta samu kanta da nauyin baki kasa furta mata komai, abun ka da mai sauri karaya nan da nan sai ta fara hawaye.
“Kin fi kowa sanin yadda na ke son mijina Teema, amman kika min zagon ƙasa har kika ja hankalinsa akan ki, waya sani ko asiri kika masa?”
Teema ta yi ƴar dariya.
“Wallahi ban masa magani ba, uwarsa cw da haɗa mu, kuma yaga yana so na, nima ina sonsa shikenan fa, amman ki kwantar da hankalinki zan ƙwatar miki ƴancin ki, kuma zan miki hanyar da zaki dawo gurin mijinki”
“Allah ya isa tsakanina da ke, kin ci amana ta kin min zagon ƙasa Teema wallahi ba zan taɓa yafe miki ba”
Tana kaiwa nan ta juya ta fice fuskarta da hawaye.
Wani banzan tsaki Teema taja.
“Aikin banza ai daman Allah ishenshe ne, kinji na roƙe ki ki yafe min ne, ni wallahi ko ubanki yayi min aurensa zan balle wani mijin ki ex-husband mtssssssss”
Rashida ya fito ɗakin idon kowa yana kanta, wasu na Teema rashin gaskiya wasu kuma suna ganin bata yi laifi ba, daman yanzu ko mijin ƙawarki ne aure shi za'ayi balle ita da har ta fita gidan miji. Bama kamar hawayen da suka gani a fuskarta. Ita kam ba ta nasu take ba, haka ta fito abunda yake ranta ya isheta, damuwarta tayi mata yawa.
Har ta shiga motarta ta fara driving bata da wani kuzari, hawayen da take kuma sun ƙi su tsaya mata. Wayarta da ke front seat ta yi ƙara alamar kira, kallo ɗaya ta yi ma wayar ta ɗauke kanta tana cigaba da rera kukan da bata san ranar tsayawar hawayenta ba, Alh Bashir ne, tasan shi ma ba zai wuce ya labarta mata Hilal zai auri ƙawarta ba, ita mamakinta ma ko Hilal ya manta Teema ƙawarta ce? Tsayawa tayi tunanin duk da tasan bata da ƙawaye barka tai hakan amman ba zai rasa sanin Teema ba, wata ƙila yayi mata haka ne dan ya rama abunda ta yi masa. Haka zuciyarta take nuna mata, cikin sauri ta ɗauki wayar ta faka gefen ti-ti, tana tunanin abunda zata faɗawa Hilal, da kiransa zata yi, sai kuma wata zuciyar ta bafa shawarar aika mata da saƙo. Sannan ta jefar da wayar ta cigaba da tuƙinta tana kuka har ta iso gida.
Ga wayar sai ringing take, friends har da waƴanda suka daɗe basu kira ta ba, yau kiranta suke dan su ji ƙwan. Bata samu gurin faka motarta ba, saboda Motar Ummu Faisak da ke waje ta tare nata hanyar gareji, daman can gidan ba wani yarwantaccen gida ne ba, gida ne na zaman mutun ɗaya.
Ba ta damu da share hawayen fuskarta ba ta shiga falon a haka. Ganin Momi da Ummu Faisak yasa ta ƙara narkewa ta fashe da kuka har da faɗuwa saman kujera. Nan take Ummu Faisak tasa kuka ganin yar'uwarta cikin damuwa. Momi kan tsawa ta katsa musu daga ita har Ummu Faisak ɗin.
“Miye abun kuka ga hukuncin Ubangiji? Ba ke kika jawa kan ki ba? Ai kin yi arziki da sai da kika fita gidan miji ita zata shiga, kuma ba ƴar'uwarki ce ta ci amanar ki ba! Ai ke kika fara yi ma kan ki zagon ƙasa da kan ki, kika taka mutumcin aurenki kika je kika bada kan ki ga wanda ba muharramin ki ba, ke wannan ma be isheki ishara ba? Cutar da take jikin ki bata isa ta nuna miki Allah ɗaya ne ba? Ai cin amanar miji Rashida ba ƙaramin haƙƙi ba ne, mijina yana can yana fafutar neman abunda zai kawo miki ke da ƴaƴansa, amman ke kina can kina cin amanarsa? Aiki hauka ne? Nasan 95% mahaifinki ne ya ja miki shi da ya tsaya kai da fata akan sai kin yi aiki, amman be ce kije can ki yi lalata ba, ai ba ke kaɗai ce mace ma'aikaciya ba, akwai da yawa waɗanda suke kare mutuncin mazan su da kuma na ƴaƴansu da na su da na iyayensu, ba ga ƴar'uwarki nan ba? Ummu Faisak aiki take, ita bata lalace ba saboda ta san mutuncin kanta, ki ba abun baƙin cikin ki ba ne ace wani namiji wanda ba mijin ki ba ya san surar jikin ki? Kin ɗauki rayuwar turawa kin sawa kan ki, baki da lokacin tarbiyantar da ƴaƴanki, tufafi ko sai waƴanda kika ga dama kike sakawa, nan aka auro miki Kalsoom na zo ina yaba shigar da take irin tarbiyar da ta samu a gidansu, kika ce min na fi son ta, da ke, kika ce ina miki abu kamar ba ni na haife ki ba, a lokacin ruɗin duniya na ke guje miki amman idon ki ya rufe.
Dan baki da hankali zaki wanke ƙafafu kije gidansu Teema to ki ce mata me? Ki zauna ki yi wa kan ki karantun ta natsu, ki nemi yafiyar ubangijinki, kuma ki nemi yafiyar mijinki tun haƙƙinsa be cigaba da binki ba, dan duk abunda kika aikata da aurensa haƙƙinsa yana saman kan ki, kin yi sa'ah da Allah ya rufa miki asiri tun wuri, dan duk mai cin amanar mijinta sai taga ishara wallahi ko ba daɗe ko ba jima, kiyi taka tsantsan da duniya Rashida dan ta fara barinki tun kamin ke ki barta, karki yarda ki ci amanar wani, ƙara ke a ci amanar ki, balle kuma miji. Tashi muje”
Momi ta ƙarasa tare da kallon Ummu dake gefenta, kana ta miƙe tsaye idonta cike da ƙwallah, ranta kuma a ɓace ta fice, Ummu Faisak ta rufa mata baya tana cigaba da hawaye.
Hannu Rashida ta ɗora saman kai, tana kallon ɗakin kamar sabuwar mahaukaciya.
“Innalillahi Allah kasa mafarki na ke yi, Allah ka farkar da ni daga wannan mummunan bachi, Allah ka farkar da ni Allah, Allah ka tashe ni...”
Ta rushe da wani irin kuka tana dafe da kanta da take jin yana jujjuya mata.
HILAL POV.
_Hilal ka san wacece Teema kuwa, wallahi wallahi bokaye ta ke bi, kuma ta fi karfin iyayenta, karka aure ta Hilal dan Allah, ban yardar ta tarbiyantar min da ƴaƴaba, ka auri ko cece amman ban da Teema_
Yana gama karanta saƙon ya saki tsaki, ya aje wayar saman teburinsa, ya miƙe tsaye ya fice daga office ɗin.
Duk inda ya wuce ango ake ce masa daman wasu tun jiya ya basu iv wasu kuma sun samu labari, yana isa gurin karɓar results ya buɗe ciki ya shiga. Daya bayan ɗaya ya gaisa da su, sai tsokanarsa suke, wai ango ka sha mai.
“A'a ban sha fa da saura”
Sai duk suka sa dariya har shi Hilal ɗin da yayi magana, ɗaya daga cikin likitocin dake tsaye ward ɗin ya ce
“Doc baka da kunya”
“To kunyar me zan ji kowa ai yasan komai, kai bani results ɗin Amarya ta na gani”
“Amarya ko uwargida?”
“Amarya dai, to duka yaushe na yi auren ?ba ƙaddarori bane dai idan Allah ya kawo babu yadda za'ayi”
“Aiko yanzu na ke shirin kai naka result ɗin, dan kana tafiya Doc Ahmad ya wanka hoton ya ce ina kake nace ya kawo wannan albishir ɗin ni zan yi ma madam shi da kaina”
“Ai ana ɗaukarta Hoton ta sha mun kai na maidata gida, ita dai ciwo take ji, shiyasa kaga na masu na ƙarɓi results ɗin so that na san abunda yake damunta kar mu yi cuta daban magani daban, tun jiya kuka take min wai tana jin abu a mararta kamar dutse sai amai take”
Kamin ya miƙa masa results ɗin sai da ya miƙa masa hannu.
“Congratulations ba dutse ba ne alheri ne, sai dai idan ka duba zaka gani”
Ya karɓa zuciyarsa fari ƙal.
“Wow ka ce na yi aiki Alhaji...”
Sai duk suka kwashe da dariya. Shi kam be ma kula su ba hankalinsa ya tafi gurin Hoton.
“Six months i'm surprise, kwata kwata ban kawo wa rayuwata ciki ba ne, dan tace ƙasan mararta kuma ita pain her, ko tsayin kirki bata iya yi, jiya gaba ɗaya a rikice muka kwana”
“Yeah yayi mata kwance ne, baka ganin yadda yake, sai kun kula da shi sosai gaskiya, Allah ya raba lafiya”
“Amin”
Ya fice da sauri, ɗaukar wayarsa ce ta zame masa dole, ba dan haka ba , ko office ɗin ba zai koma ba, a gaggauce ya ɗauki wayar ya fice. @360 ya bar asibitin tsabar zumuɗi ji yake kamar ma ya rumtse ido ya gansa gida. Cikin ƙanƙanen lokaci ya isa, daman be sa ran zai tarar da ita falo ba, dan haka ya wuce bedroom ɗinta kai tsaye, kwance ya same ta ƙasa ta duƙunƙune da bargo sai rawar sanyi take. Wani irin tausayinta ne ya kama shi, sai ya aje keys da takardar dake hannunsa saman mirror, ya kwanta bayanta ya yaye bargon dake jikinta ya ɗora fuskarta saman nata, jikinta yayi zafi aosai amman hakan be hana shi rumgumarta ba.
Ta buɗe ido da ker ta ɗan taɗo kai ta kalleshi.
“Gadon baya min daɗi”
Ta faɗa da muryar ta nan ta marar lafiya. Lumshe ido yayi yana murmushi.
“i'm sorry dear it's all my fault”
“Dan Allah ka min allura ko zan samu sauƙi”
“Ke da samun sauƙi sai nan da five months”
Ta yi dauriyar sake kallonsa cikin idonta na marar lafiya.
“Whats do you mean?”
“Sweetheart ƴou're pregnant”
Ƙarfin halin tashi ta yi, sai ya riƙa ta tashi zaune da kyau, ya kwantar da ita jikinsa.
“Da gaske?”
“Yes Dear six months”
Ta yi saurin kai hannu ta taɓa cikin, yo hwr surprise cikinta be yi girma ba, impact babu wani alama na ciki na jikinta idan ba wannan ciwon da ta yi ba.
“Amman ko dai one months...?”
“No wata shida dai, kin ga hoton da aka miki ɗazu can”
“Amman na yi menstruation last months fa”
“Nima abunda ya bani mamaki kenan, but kin tuna wacan lokacin da kika samu ciki ya ɓata? Ina tunanin shi ne ya kwanta miki, sai yanzu ya tashi, daman ana samun hakan nan wani lokacin, that's why we need to take good care of it, saboda mu samu ya dawo dai-dai”
Ɗagowa ta yi ta kalleshi, hawaye suka zubo mata.
“Congratulations”
Sai ya aika mata da kiss a goshi.
“Thank you Dear”
Ta ɗora kansa saman wuyanta, hannayensa zube saman cikinta.
ASIM POV.
A can ya kwana gurin Alhajinsa, da safe yasa aka kawo musu abun karyawa, sannan suka yi wanka, yadda Alhaji Nasir ya shirya cikin manyan tufafi ba zaka kalleshi kace yana aikata wani mugun abu ba.
Asim ma ya fito cikin ƙananan kayana kamar wani mutumen arziki, hankalinsa kwance zuciyarsa cike da natsuwar abunda ya aikata. Ba laifi yanzu be ji zafin da yaji da farko ba, sai dai har yanzu be fara jin daɗin da Alhaji Nasir da Hajiya Sadiya suke labarta masa zai ji ba, wata sai ya ƙara gwarewa akan harkar.
Alhaji Nasir ya saka turare ya kalli Asim ya ce.
“Har yanzu baka ƙarasa ƙwarewa ba a kan harkar nan, ya kama a sama maka kasuwan turawa nan ka kalla,dan ina son haɗa ka da manyan mutane ta yadda zaka ƙara gwarewa, ka ci moriyar ƙurciyarka”
Wani daɗi ne ya lumluɓe Asim, dan yasan kuɗi zai samu, daman burinsa kenan ya yi kuɗi.
“Zan ƙoƙarta Inshallah, ina godiya sosai”
“Idan kana da buƙatae wani abu ka riƙa min magana, dan yanzu nauyinka ya dawo kai na, shiyasa na tura maka wannan kuɗin dan ka samu na ƴi ma kan ka hidima, amman fa a riƙe sirri, kuma ni ina da kishi gaskiya ɓana son ka yi mu'amala da wani idan har ba ni na haɗa ku ba”
“Zaka same kamar yadda ka tsammace ni inshallah”
Daga haka Alhaji Nasir ya miƙe tsaye.
“Ni zanje Abuja ajima kaɗan, yanzu zan leƙa gida ne”
“Ba matsala Alhaji Allah ya kiyaye hanya”
Sai da ya fita da kusan mintuna latatin sannan Asim ya fito daga gidan ya nufo gida. Ko da ya shiga Mama har ta soya nasa dankali da ƙwai ymta haɗa masa tea mai kyau dan tasan shine favorite ɗinsa, shi kam ko kallon su be yi ba, dan yanzu ya wuce gurin kwaɗayin irin waɗannan, beside yama riga da ya ƙarya gurin Alhaji Nasir.
“Nayi tunanin zaka dawo jiya muka ta jira baka dawo ba, na kira wayarka kashe”
“Eh masallaci na kwana, bayan gama sallah isha'i daman na kan yi haka ko a gida yanzu saboda ina nafila dare”
Yayi mata ƙaryar ne saboda bashi da hujjar cewa ya kwana a wani guri bayan kuma ga gidansu. Ita kam daɗi ya mamaye ta.
“Ai haka na da kyau, ƙara a riƙa godiyar Ubangiji, sai kaga yana ƙara maka, kuma ya kamata ka samu lokaci muje gurin Malam na Allah ya baka ƙaiƙayi koma kan masheƙiya saboda maƙiya”
Miƙewa yayi tsaye.
“Kai Mama ni duk bana da lokacin wannan, yanzu dai ga kuɗi nan ki rabawa maƙota, idan na samu gidan sai a faɗa min”
“Toh ya yi Allah ya tsare min kai, amman har zaka koma yanzu? Jiya jiya fa ka zo garin nan ”
“Wallahi aikwai aiki a can, kuma ki ciri kuɗi ki buɗe account a bank zan turo miki kuɗi ki bawa su Baba sani, kuma ki faɗa musu anytime zasu iya jin kirana akan maganar auren nan”
Yadda yake mata magana kamar yana bada umarni ne. Wani jin kansa yake yanzu kamar minister. Ta so ya tsaya su yi fira amman bata samu dama ba dan ya nuna yafi son tafiya kamar wanda ake tsakala. Har bakin mota ta rako shi tana faɗar masa
“Yanzu sai iyayen Namra sun samu labari ka yi kuɗi, amman basu san ka sake ta ba, tun da bata zo gida ba”
“Dole ne ai su samu labari, ni nafi son haka ma”
Ya buɗe motarsa ya shiga. Tana ɗaga masa hannu har ya kama hanya.
Be tashi da wuri ba, dan ko da ya baro sokoto shabiyu har da kusan rabi. Ko da iya isa Katsina yamma ta yi sosai, sai dai Nably ta yi masa kira ya fi biyar dan jin lafiyarsa, Mardiya ma ta kira ta faɗa masa tana son ganinsa.
Yana isa katsina ya kira wayar Hajiya ya fara gaisheta, still ta faɗa masa tana birnin keebi, dan ya so ya fara zuwa ya gaishe da uwar ɗakin tasa ko zai goge laifinsa. Gidansu ya sauka yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin sannan ya wucce gurin ƙanen dad ɗinsa wanda ya manta rabonsa da yaje can sun suna aikin ƙira kamin su haɗu da Hajiya Sadiya.
Su kansu sun yi mamakin ganinsa, daman suna jin labarin yayi kuɗi sama-sama a gurin jama'ah, bama abunda yafi basu mamaki kamar yadda kuɗin suka taso masa lokaci ɗaya. Sun yaba da motarsa da kuma shigarsa har suka masa fatan Allah ya tsare, a nan ya ɗauki kuɗi mai yawa ya bashi, abkan da suka yi aiki tare ya raba musu wani abu. Sai da Ƙanen Baban nasa ya rakosa zuwa gurin motar yake labarta masa dalilin zuwan nasa.
“Gida nake so a sama min kamar na miliyan biyar, mai kyau sosai”
Shin kam riƙe baki yayi jin Asim ya ambaci miliyan har biyar, yana mamakin ace yana da wannan kuɗi haka da yawa, a take zuciyarsa ta raya masa ba kuɗin halal ba ne, sai dai babu damar faɗa masa gaskiya dan yana tsoro, daman idan kana da abun hannu ana tsoron faɗa maka gaskiya balle Asim da yasan zai iya yin cikinsa da masifa.
Da zimnar idan an samu za a kira shi a sanar da shi suka aje, sannan ya yi masa sallama ya kama hanyar gidansu Mardiya.
YASMEEN POV.
Tana shiga ta aje kwalin, ta koma kan Adnan daya sauka ƙasa yana zare zaren shoes ɗinsa, da hannu ɗaya but still hannunsa ɗaya yana gurin sai susa yake. Yana ganin Yasmee yayi saurin dainawa, yana wara idonsa na marasa gaskiya.
Hannu biyu tasa ta ɗauke shi sai ta zauna ta ɗora saman jikinta tana murmushi.
“Aya tell me mi Dadee yake ma ka?”
Rufe ido ya yi yana dariya, ita kuma ta maida kunnenta gurin bakinsa.
“Faɗa min mana ko mu ɓata”
“Ba zaki faɗa ba?”
“Ba zan faɗa ba”
“Wannan abun ƴake sa min a nan”
Ya nuna mata gurin fitsarinsa, sai ta sauke shi ƙasa.
“Nuna min mi yake sa maka”
“Wannan abu yake samin a baya, sai yacw na kwanta, kuma da zafi sosai yace idan na faɗa sai ya yanka ni da wuƙa ƙamar yadda ake yiwa rago”
Ya cire wandonsa ya nuna mata. Wani irin faɗuwa gabanta ya yi, a take ta samu kanta cikin wani irin tashin hankali, wanda bata taɓa sa masa rana ba, a take zuba ta fara karyo mata, numfashinta yayi mata mugun nauyi, sai tayi saurin rumgume Adnan dan kar ya ga hawayen dake ƙoƙarin zubo mata.
“Your Dadee did a great thing”
Ta soma shafa bayansa cike da tausayinsa kanta da kuma nata, sai dai ko kaɗan bata son ya ga hawayenta. Sai ta sauke shi ta mike tsaye.
“Bari na zuba maka abinci ka ji”
Ta yi saurin juya ta bar ɗakin. Kitchen ta shiga sai ta samu mai aikinta tana yanka salat da tumatur.
“Jeka kawai zan ƙarasa”
“Toh”
Aje ragowar da ke hannunta ta fice. Hannu biyu Yasmin tasa ta riƙe kitchen cabinets sai ta fashe da wani kuka marar sauti. Ƙafafunta kasa ɗaukarta suka yi, sai gata ƙasa jikinta har karkarwa yake.
“Innalillahi wa'inna ilaihi”
Shine abunda take ta maimaitawa, gudun kar kukan ya ci ƙarfinta. Kulolin ta buɗe ta ɗauki plate ta zuba masa white rice and pepper soup, ya saka nasa spoon, sannan ta ɗauki ruwa ta wanke fuskarta ta fito tare da abincin.
Ɗakinta ta nufa riƙe da abincin, hawaye sun ƙi tsaya mata. Aikin baban giwa ta samu yana yi, dan har ya buɗe kwalin data aje, azatonsa wani abun ci ne a ciki ko chocolate ganin. Ita bata ma bi ta kan kwalin da ya fasa ba, shi kawai take kallo har ta aje abinci, tausayinsa duk ya kama ta, sai ta riƙo hannunsa ta karɓi takardar dake hannunsa ta aje gefe. Taja shi jikinta, ta rumgume.
“Momee babu komai a ciki”
Cikin kuka ta amsa shi.
“Ba na ka ba ne, na Dadee ka ne”
Kuka take sosai tana ta ƙoƙarin ƙaryata abunda zuciyarta take son yarda da dashi, can kuma ta sake shi ta janyo abinci ta aje masa a gabansa. Ta zauna ta tsare shi da ido hawaye na cigaba da mata zuba.
Kamar kuma an tsikare ta share hawayen idonta, ta miƙe tsaye ta ɗauki wasiƙar da jimmar maidawa cikin kwalin, babu abunda ya bata mamaki kamar ganin da tayi babu komai a kwalin sai wasiƙa, babban kwali kamar wannan a'ce babu komai a ciki sai wasiƙa, to me wasiƙar ta ƙumsa ne haka?
Zaunawa ta yi a kusa da kwalin ta warware wasiƙar, gabanta sai faɗuwa yake ta soma karantawa.
_Zuwa ga Azzalumin mutun, macuci mayaudari, nasan kana nan raye kamar ƴadda nima na ke raye, ko kuma na ce ka so ka halaka ni Allah be baka dama ba, ka yaudare ni Uzair kace Namra zamu ma Asiri ashe ka haɗa kai da ita ne ni kuka yi ma wannan asirin na bar gida, ban taɓa gane haka ba, sai a yanzu da nake da buƙatar da dawo na kasa, Wallahi Wallahi kaje ka karya wannan asirin ko kuma na sa a kashe ka, dan kasan na san ka, kuma na san inda kake, ni ko baka san inda na ke ba a yanzu, kuma ina tabbacin baka san ko wacece ni ba_
Sai number wayarta daga ƙarshe. Abunda ya tsayawa Yasmin a rai, wacece wannan yarinyar? Sannan mi suka ƙulla da Namra? Mi mijinta ya aikata ne?
Ta miƙe tsaye cike da rashin kuzari, abubuwa biyu sun tsaya mata a lokaci ɗaya kuma akan mutun ɗaya. Wani tunanin ne ya zo mata, da sauri ta ɗauke kwalin ta fita da shi ta saka cikin shara, sai ta dawo ɗakin ta ɗauki wasiƙar ta mayar da ita a yadda take, sai ta je cikin littatafanta na aiki ta samu wata silver paper, ta yi wrapping ta naɗe wasiƙar ciki da kyau ta saka salatif, ta kai masa ɗakinsa ta aje masa.
Tana shigowa ɗakinta jiri ya kwasheta, ta faɗi dafe da kai.
ANTY AMARYA POV.
Cikin ƙarfin hali ta unƙura ta nufi part ɗin Abbah, dan yau bata jin daɗin jikinta sosai, wata ƙila fever ɗin ne zai sake dawo mata. Yadda ta tararda Hajiya Barau da Abbah a falon ya ɗan tashi hankalinta, dan a zatonta ya aika kiranta ne dan su tattauna maganar auren da ake na su Hindatu da Maryam. Zaunawa tayi tana kallon yanayin Hajiya Barau da ta riƙe baki tana kallon Abbah, sam bata lura da takardar dake hannun Abbah ba sai da ya mika mata takardar.
“Wai wasiƙa ce daga Faɗar Mai Martaba sarkin Katsina, wai ana bukatar gani na gobe”
“Subhanallahi miya faru?”
Anty Amarya ta tambaya zuciyarta na rawa fat fat fat.
“Wallahi ban sani ba, ni abun ya ban mamaki mi na aikata da Sarki Katsina zai aiko kirana? Ina ma na san shi?”
Hajiya Barau ta mere baki, har da wani ƙis take.
“Allah yasa ba Namra ta yi maka janye janye ba”
Kallo ɗaya Anty Amarya ta yi mata ta ɗauke kai, maganar na sukarka, ta miƙe tsaye ta bar musu falo.
“Zan sa ana ma min jirgin da zai je Katsina gobe da wuri zan sauka dan jin ko minene”
“To Allah yasa mu ji alheri, Amman da ka kira Abdulraman (Baban ɗansa) kun je tare, kar ka je kai kaɗai”
Ya ɗora ƙafarsa ɗaya saman ɗaya, Yana sosa gemunsa da hannunsa.
“A'a da Larai zan je (Anty Amarya)”
Uffan Hajiya Barau bata ce ba, dan maganar bata mata daɗi ba, sai kawai ta miƙe tsaye ta fice daga falon.
___________________________________________
There are no words to explain how sorry I am. Nasan duk abunda zan faɗa muku ba zaku yarda ba, wallahi i'm kind of busy those days, ku yi Hakuri dan Allah ku gafarta min Love you all Fisabilliah 🌹
I dedicate this chapter to Hajiya Ramatu, Mrs tijjani, My Asmee, Ahmad Ismael. I really did not know how will to write in words! But your gesture is such 😘 Thank you very much Allah ya ƙara arziki, ya bar zumunci.♥️
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *76*
“Me kike a nan?”
Ya tambaya yana haɗe fuska. Bayanta ta nuna ba tare data juya ba, sai dai bata san abunda zata faɗa masa ba. Ya nunata da phone ɗinsa.
“ I know kin karanta wasiƙar nan Yasmin”
Still wata kalma bata fito daga bakinta, wani kallo take masa kamar mai nazari. Raɓawa yayi gefenta zai wuce sai kuma tsaya yana kallonta ido cikin ido.
“Ba sai mun yi playing wannan game ɗin, nasan ke lauyer ce”
Da kallon mamaki ta bishi, ta kasa gasgata abunda kunnuwanta da idanunta suka ji mata. Me yake nufi da Namra bata zame masa matsala ba ita ba zata zame masa ba? Wacece ita? Da waya yake waya?
Da sauri ta rufa masa, sai ta same shi sitting room ya haɗa kansa da guiwa ya dafe. Tsaye tayi masa aka.
“Me waɗannan abubuwan suke nufi Uzair? Wacece wannan ? Mi kuka aikata kai da Namra? Da wa kake waya?”
Ɗagowa yayi ya kalleta, idonsa sun kaɗe alamar damuwa da ɓacin rai na tare da shi lokaci ɗaya.
“Miyasa kike son saka kanki ga abunda idan kika ji zai iya zame miki matsala? Miya kike son saka kanki ga abunda be kamata ya dame ki ba?”
Ya tambaya muryar ƙasa ƙasa kar ba komai. Zama tayi kusa da shi tana masa kallon mamaki.
“Ni matarka ce Uzair, damuwarka damuwata ce, Namra kuma ƴar'uwata ce, be kamata ka ɓoye min komai ba, please tell me maybe i can help”
ya shafa fuskarsa yana cikama bakinsa iska.
“Is about some business da zamu yi da yayanta, shine take min sheri, shine nace Namra bata zame min matsala ba ita zata zame min yarinyar da ta yi min ƙazafin Luwaɗi”
Wani ɗan murmushi tayi mai cike da rainin hankali, shi kansa ya fuskanci hakan.
“To be frank i read the message, Uzair you can't hide the truth jus...”
Yayi saurin riƙa hannayenta jikinsa a mace.
“Yasmin trust me please, kin san ina son ki”
“Ba maganar so ko ƙi muke a nan ba”
“Just promise me ba zaki bar ni ba”
Hawaye sun zubo mata.
“Idan har zargina ya tabbata a kan ka dole ne zan rabu da kai, ba zan iya zama da mutuemn daya zaɓi saɓon Allah sama da tsoronsa ba, mutumen daya zaɓi zubar da mutuncin iyalansa, zan iya yafe son da nake maka Uzair”
Ya girgiza mata yana ƙara damƙe hannunta cikin nasa.
“No Wallahi sherin sheɗan ne Yasmin, ba da son raina na aikata ba, kuma duk zugar su Najeeb ce, kuma nayi ne dan na kare kai na daga cin mutuncin da Namra ta yi min”
Maganarsa ta sha banban da tunaninta, ita gun data dosa daban shi kuma maganar da yake mata daban.
“Me ka aikata Uzair?”
Ya saki hannayenta.
“Ina ruwanki da abunda na aikata ne Yasmin?”
Ya faɗa a tsawace, sai kuma ya dafe kansa ya miƙe tsaye ya nufi windo.
“Ki tsaya a matsayin ki na matata Yasmin, zai fi miki”
Ta miƙe.tsaye itama cikin ɓacin rai.
“Yes zai fi min idan na rabu da Azzalumin mutun irinka, tirr da halin ka Uzair, ina kotu ina cases ashe akwai babban Case a gidana, nayi nadamar Auren ka a yau nayi nadamar daka kasance a cikin zuri'ar mu, nayi nadamar da ka zama uban ƴaƴana, ashe gaskiya Namra take faɗa, amman ka murje ido ka ƙaryatata...”
Ya juyo a fusace yana nuna saman kamta da ɗan tsayansa.
“Ke je ki faɗawa duniya nine na sace Namra, ni na haɗa kai da amiyarta aka mata asiri ya koma kan ƙawarta, amman karki manta ɗan'uwanki kika tonawa Asiri, kuma mahaifinta zai karɓe komai nasa daga hannuna, but i'm still your husband Yasmin the love of your life kuma uban ƴaƴanki biyu, asirina asirinki ne, kuma tona min asiri kamar tonawa kanki ne da ƴaƴanki”
“Ka buɗe shafin da ban san da shi ba Uzair, ashe kai ka sace ta? Sannan ka haɗa kai da amiyarta ka mata asiri? Wane irin zuciyane da kai Uzair? Wata ƙila ma ita ka aikata mata irin abunda ka aikatawa ɗan ka, you raped your very own son Uzair Allah yayi tirr da halinka”
Dariya ya soma yi ya doso inda take.
“Allah ya faɗa acikin matan ku akwai maƙiyanku, sai yanzu na gane kan ayar nan, amman ke babbar maƙiyiya tace Yasmin, ki rasa abunda zaki zarge ni da shi sai wannan? Kina da wata hujja ne? Ke daina ganin ke lawyer ce zan iya maka ki kotu, akan wannan mummunar kalma da kika jefe ni da ita, ai ko da gaske na aikata masa be kamata ki fito ki jefe ni da wannan maganar ba, idan ma na masa ina ruwanki ɗan ki ne?”
“Shiyasa bana burge ka ko? Baka da time ɗina, saboda ba mata bane a gabanka maza ne, mu kwana gado ɗaya mu tashi amman baka yarda ka bani haƙƙi na ba, da na maka magana, ka ce baka da lafiya, ko na cika desire, ashe kasan abunda kake aikatawa, kasan irin hukuncin da Allah ya tanadarwa masu irin wannan aikin kuwa? Cewa aka ƴi idan an kama su a jefosu daga saman bene su faɗo ƙasa, ko kuma a samu dutse a buga musu a kai, miye bana da shi ne Uzair? Wace hasara ce ta cin maka na neman maza ƴan'uwanka? Uzair me kake ji idan ka neme su?”
Hannayenta ya kama, ya faɗi ƙasan gwuiwoyinsa.
“Ki rufa min asiri Yasmin, ki taimaki rayuwata, kar kowa taji maganar nan, na miki alƙawarin ba zan ƙara ba, kuma zam je nasa a kare asirin dake kan Amira i promise, Yasmin ki dubi girman Allah ki yafe min, sherin zuciya ne, da zama da miyagun abokai”
Kuka da take ne ya ƙaru.
“Ka cutar da yarinyar nan Uzair, kasa mahaifinta da duniya suka zargi ta gudu taje gurin saurayinta ne, sanadinka kowa a familyn mu ya tsane ta, duk halin da ta shiga kai ne Uzair”
“Ki yi ta tunanin wasu har ki manta da ni, ki rufa asirin wasu ni ki tona nawa, idonki yayi ta rufewa akaina har maƙota suji abunda na aikata”
“Ba maƙota kaɗai zasu ji ba, duniya ce zata ji, sai duniya tasan wanene kai, sai kowa yasan abunda ka aikata”
Ya miƙe tsaye
“Wallahi duk kika bari wannan maganar ta fita, sai kin yi nadamar zuwanki duniya, sai kin gwammace kiɗa da karatu, kuma komai na zama ni mijin Yasmin ne, ai komai yana da buƙatar uzuri da bincike, kije duk abunda zaki aikata ki aikata ɗan shege ka fasa, indai kotu kike taƙama da ita sai na nuna miki baki san komai ba akan aikin ki”
“Haka ka ce?”
“Wanda duk yaƙi ji aiba zai ƙi gani ba”
“Baka bani mamaki ba, daman masu aikata irin aikinka ai basa da kunya, kuma basa tsoron Ubangijinsu balle jama'a tirr da halinka, wallahi sai na ƙwatowa Namra haƙƙinta, sai ka raina kan ka Uzair”
“Ni mijinki kike faɗawa haka?”
“Kai mijina ne zaka taka min bayan ɗa?”
“Sai ki fito fili ki faɗa mana, kice ɗana zaki min ƙazafi, ba wai ki raɓa da Namra ba, aikin banza kaiwai... Mtssssswww”
Yaja wani dogon tsaki ya wuce daga falon kamar walƙiya. Ita kamar jiran take ya fita, ta shiga ɗakinta ta zari mayafi ta, ta goyawa Mai mata reno little Namra, ta kama hannun Adnan suka fice.
NAMRA POV.
Da hawayw ta shiga cikin gidan, sai dai kasancewar dare ne, kuma babu wutar nefa a gidan shi ya hana su gane akwai hawaye a fuskar Namra, da wannan tayi nasarar shigewa ɗaki ta kife saman kafitar tana kukanta a hankalin ta yadda ita kaɗai zata iya jin sautin kukanta.
Da sallama Anty Amarya ta shiga cikin gidan, sai duk suka haɗa baki gurin amsa mata, gaisuwa ce ta biyo baya, sannan ta ɗora da tambayar Namra, duk kallon rashin sani suka mata, ko wanne abunda zuciyarsa ta bashi, wata ce ta tare da Yarima, wata ƙila taƙi ta saurareshi ne shiyasa ya turo wata.
“Eh tana nan ciki lafiya?”
Lamido ya tambaya. Cikon murya mai kamar ta kuka Anty Amarya ta ce
“Dan Allah ku yin magana da ita...”
Kamar an jefo Namra haka ta fito daga cikin ɗakin, tana ganin Anty Amarya ta rumtse idonta ta damƙe hannayenta gam, tana maimaita.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Saboda ta kasa yarda da abunda kunnuwanta da idonta suke nuna mata, ji take kamar mafarki take kuma ba mafarkin ba ne. Ta buɗe ido ta ƙarasa gaɓan Anty Amarya ta kama hannayenta, ta taɓa ta murja ta sake kallon fuskarta, sai kawai ta rumgume ta fashe da kuka.
Anty Amarya ma kuka take, ita da Namra aka rasa mai rarrashin wani, su kam su Neina sai kallon ikon Allah suke. Kuka sosai Anty Amarya da Namra ke yi kamar an muutuwa, sannan Namra ta zube ƙasan kafafunta ya kama kafafun Anty Amarya.
“Ki yafe min Anty, na tuba dan Allah ki yafe min, ki roƙi Abbah ya yafe min, haƙƙinku ma ta bina Anty, dan Allah ki roƙa min Abbah ya yafe min”
Ta ƙamƙame ƙafafun Anty amarya, tana wani irin kuka mai yaɓa zuciya. Yanzu kam Neina da Lamido sun fahimcin wacece Anty amarya. Anty ƙasa magana ta yi saboda majina data cika mata hanci. Can Namra ta ɗago kai ta kama hannayen Anty Kaamar wace ta ruɗe.
“Anty da gaske kece?”
Ta kalli Lamido da Uwani.
“Kuna ganin abinda nake gani, ko dai mafarki nake?”
Lamido ya ɗaga mai cike da ɗaurewar kai, Uwani kuma tace
“Muna gani Namra”
Anty Amarya tasa hannu biyu ta riƙo Namra ta tashe ta tsaye.
“Nice Namra, ba mafarki kike ba, Mahaifinki ma yana nan waje, tare muka zo da shi lokacin komawarki gida yayi”
“Anty waya faɗa muku nan? Na kasa yarda ba mafarki nake ba, kaina nake jin yana juyawa”
Ta miƙe tsaye ta nufi ƙofae waje. A gurin ta samu Abbah tsaye ya maida hannayensa baya kansa ƙasa kamar mai nazari.
“Abbah....”
Ta furta tana kallonsa da kyau da kyau. Ɗan murmurshi yayi kaɗan irin murmushin da be kai zuci ba. Sai kawai Namra ta faɗa jikinsa ta rumgumeshi numfashinta na rawa, kuka yazo mata a lokaci ɗaya.
Sai da tayi kukanta mai isarta taji ta samu natsuwa sannan ta sauko gurin ƙafafunsa ta riƙe.
“Dan Allah Abbah ka yafe min, ban kyauta maka ba, kwata-kwata abunda na aikata be dace ba, Abbah Asim ya sake ni, tsoron abunda zaka min ya hanani komawa gida, dan Allah ka yafe min Abbah”
Kanta ya shafa fuskarsa ba yabo ɓa fallasa.
“Idan ban yafe miki ba, ba zan zo nan ba Namra, nasan yanzu kin riga da kin gane kuskurenki, tashi tsaye kar ki tara mana mutane”
Fitar Namra yaba Anty Amarya gaisawa da ƴan gidan, wato su Neina har take faɗa musu ai tare da Abbah ta suke yana waje.
“Haba kije kice ya shigo mana ya zai tsaya daga waje”
Sannan Anty Amarya ta nufi ƙofa da jimmar faɗa masa sunce ya shigo. Sam sam sam Lamido be jidaɗin ganin iyayen Namra ba, duk wani farinciki da son da yake ta shirya da iyayenta sai yaji baya sonsa, musmaman yadda zuciyarsa take raya masa Yarima ne silar hakan,ko ba komai yasan Namra zata fi son Abdool sama da shi, shi ko yana da ƙudurora da yawa akanta, dan ya ɗaukarwa kansa alƙawarin sai ya nuna mata banbancin dake tsakaninsa da Asim na kyauwon hali, duk da suna ɗaya zasu amsa a fagen talauci,so yake Namra tasan ba duka talaka ne mai irin zuciyar Asim ba.
Wani abu yaji yazo ya tsaya masa a zuciya, tun ba aje ko ina ba, yana jin ya fara missig Namra, zata nisanta da shi yanzu, kuma ba lallai bane ya sake ganinta.
Sallama Abbah ce ta katse masa hanzari, ya dawo daga duniyar tunanin da yake ya miƙa idonsa i zuwa inda ƙofar gidan take yana kallon Namra dake riƙe da hannun Anty Amarya. Saman shimfiɗar da Neina tayi musu suka zauna, ita kuma ta zauna a saman ɗaƴar tana gaisawa da Abbah.
“Amman na jidaɗin da kuka zo gurin ƴarku, Namra bata da tunani sai naku, kullum cikin kuka take, nasan babu iyaye na gari da zasu ƙyale ƴarsu, matuƙar ƴar nan ta sunna aka haife ta, su iyaye dole sai kana kai xuciya nesa, sau da yawa ɗa zai aikata abu kai ka daurewa zuciyarka ka ƙyale gudun kar ɗan nan ya faɗawa halaka, kuma idan mutum ya gane kuskurensa babu a abunda ya cancanta da shi sai yafiya da kuma nuna masa illar abun nan da ya aikata, ƴaƴa da mata kamar kiwo ne, ko wanne za a tambaya ubngidansa akan irin kiwon da ya bawa iyalansa, yadda mu muke da haƙƙi akan ƴaƴanmu haka muma ƴaranmu suke da haƙƙi a kan mu. Wallahi kun faranta min zuciya dana ganku da ƙafafunku kun tako cikin gidan nan ku tafi da ƴarku, a halin da Namra take da ace bata haɗu da mu ba da zata iya faɗawa ko wane irin hali, saboda bata san kowa a Kaduna ba, kun ga ko a nan rayuwarta tana cikin haɗari”
“Gangar jikina ne kawai a gida, amman kullum zuciyata tunanin Namra take, ban san aurenta ya mutu ba, da wallahi ba zata zauna ko ina ba sai a gida, kowa kuwa mahaifinta zai zaɓi rabuwa da ni ne, kullum a tunani tana can yana azabbatar da ita, nasan Halin Namra idan abun duniya zai cita ya cinye ba zata faɗawa kowa ba, itace babba amman ita marar wayo da tunani a cikinsu, da wannan tunanin naƙe bachi naƙe tashi wannan tunanin ya kan hanani sukuni wani lokacin, shiyasa ƴan'uwanta suke ganin kamar itace silar ciwon nan nawa, kullum cewa suke, Namra ce ta kwantar da ni, duk da nasan gaskiya suke faɗa amman a haka zan musa musu, kudun kar suce nafi sonta sama da su, ni ko kullum tunanin kar na mutu na barta a cikin wannan halin”
Namra ta kama hannayen Anty Amarya ta riƙe.
“Ba zan sake aikata abu makamancin wannan ba Anty, ni ba zan sake aure ba balle har na tsallake wani sharaɗi na ku, hawayenki ba zai sake zuba a kan Namra ba”
Uffan Abbah be ce ba, idonsa na kan pure water da Maryam ta aje musu mai tsanyi, wadda ta siyo shago.
Maganar duk da suke tana cikin kunnensa, sai dai be jin zai iya furta wata kalma data ɗanganci labarin da suke. Ba laifi sun ɗan yi fira sosai da Neina, kamar waɗanda daman can san juna, sai duk firar da ake Namra na cikin jikin Anty hawaye sun ƙi su tsaya mata. Abbah ya kalli agogonsa tare da miƙewa tsaye yana faɗin.
“Ya kamata mu tafi yanzu, da safe Namra zata zo ta muku sallama kamin mu kama hanya”
Yana faɗar hakan ya saka takalminsa ya nufi ƙofar fita, Lamido da kallo ya bishi yana aunasa a matsayin lallai zai iya aikatawa Namra haka, da ga alamu yana ji da kansa, ko kuma be gama hucewa bane oho.
“Allah sarki Namra, ashe kuwa zamu yi marmarinki”
Uwani ta faɗa cikin rashin jidaɗi, dan har ga Allah ita tana tunanin rabuwa da Namra dan yanzu sun ɗan tsaba da juna.
“Nima ai sai na yi Marmarin ku, mutane masu karamci da sanin darajar ɗan'adam”
Namra ta furta tana mai jin kamar karta tafi ta barsu. Har bakin mota Neina da Uwani da Maryam suka rakosu, ko da suka fito har Abbah ya shiga mota, Anty Amarya ta fara shiga sannan Namra, su Neina na ɗaga musu hannu direban yaja mota.