Ta rame sosai ta koma kamar ba ita ba, tun ranar da taje gidansu su Teema bata sake leƙa ko ina ba, gurin aikinta sun yi kira sai ta tura musu saƙon bata da lafiya ta email, sannan ta kashe wayarta, saboda yawan kiran da ake mata akan auren Teema da tsohon mijinta. Bata iya cin komai banda tea, sai ɗan lemu wani lokacin, kullum a kwance take salla ce kawai take tashinta. Musamman jiya ta san itace ranar ɗaurin auren Teema da rabin ranta 😢. Babu wanda yasan inda take balle azo gurinta, Momi kuma ta juya mata baya da duk ƴan gidansu, lallai sai yanzu ta gane duniya ta juya mata baya, shiyasa ake cewa idan kana son duniya da yawa ka fara barinta kamin ta barka, idan har ita ta fara barinka to ba zaka ga da kyau ba. Yanzu kan ta fara gane baƙin duhun da yake bibiyarta sai dai bata san iya inda zai tsaya mata ba. knocked ɗin ƙofar falo da taji ana yi ne yasa ta unƙurin tashi taje ta buɗe. A zatonta Momi ce ko wata daga cikin ƴan gidansu, ga mamakinta sai ta ga Asmee.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Rashida haka kika koma?”
Rashida ta sakar mata ƙofar ta dawoɓsaman cushion ta zauna, Asmee ma zama tayi a kujerar dake fuskarta ta Rashida, tana yayw mayafinta.
“Haba Rashida, na san kina son Hilal kuma na san Teema bata kyauta miki ba, amman idan ta samu labarin halin da kika shiga ai daɗi zata ji, kin ware kanki ke kaɗai kina saka damuwa a aranki”
“Ya akayi kika gane gidan nan?”
“Gidanku naje aka kwatantamin nan, zulfa'u da Rafia duk sun je gida sai a ce musu kin yi tafiya, nima ban da na matsa da ba za a faɗa min inda kike ba, dan Allah Rashida ki cire damuwar Teema a ranki”
“Ba auren Teema abunda yake damuna a yanzu ba, irin rayuwar da zata shimfiɗa a cikin gidana yafi damuna, ita zata reni ƴaƴana, kuma wallahi azzalumace zata iya yi musu komai, gata ta iya neman magani zaya iya raba su da ubansu”
“Toh ya zakiyi Wallahi Teema ta ci amana”
“Teema ta ci amana kamar yadda nima na ci amana, ta auren min miji kamar yadda nima nayi taraiya da mijin aminiyata, Asmee duk halin dana shiga a yanzu mijin ki ne sila...”
Asmee ta gyara zama.
“Ban gane ba. Kamar ya mijina ne sila?”
“Kin ci amanar mijinki kin bada kanki ga wasu saboda neman mallakar miji, ahi kuma ya ci amanar ki ya bada kansa gare ni, mijinki shi ya saka min cutar hiv, saboda kin samo gurin wannan bokan kin saka masa, tun daga lokacin da naji kince ana zargin bokan da cuta, hankalina ya tashi saboda nasan bayan mijina, mijinki ne na biyu da nake mu'amala da shi, sanadin hakan naje nayi gwaji, aka tabbatar min da ina ɗauke da cutar, har Hilal ya gane gaskiya yaje yayi gwaji shi baya da shi da ƴaƴansa, da matarsa, sanadin hakan ya sake ni, shi kansa mijinki be san da hakan ba, amman ke nasan kin san kina ɗauke da cutar, saboda haka na ci amana, nima Teena ta ci amanata, sai dai ban san makomar yarana ba, ban san wane irin tarbiya zata basu ba”
Miƙewa Asmee ta yi tsaye gume na keto mata tashin hankali ya hana hawayen dake maƙale a idonta zuba.
“Duk yarda da Amincin dake tsanina da ke, ace kin rumtse ido ta auren ki kin yi zaman banza da mijina? Ina tunanin nayi abunda zan iya na hanasa aure, ashe na kashe macijina ban tsare kan ba, wallahi ko a mafarki ban za ci zaki min haka ba, ƴar iska macuciya, ai wallahi sai kin ga abun ki, dan Teema sai ta salwantar da rayuwar ƴaƴanki... Kuma Allah ya isa tsakanina da ke!”
Ta fisgi gyalenta ta fice a fusace. Rashida kan kuka kawai take, tana mai jin tsantsar damuwa da nadama a zuciyarta. Kuka tayi sosai, daman kullum cikin yinsa take, sannan ta koma ɗakinta ta ɗauki kkaton hijab ta saka ta saka niƙab ta ɗauki makullun motar ta ta fice.
ABDOOL POV.
Tun da ya baro ƙofar gidansu Lamido cikin farinciki yake, dan yasan sahibarsa ma tana can tana farinciki, kuma yasan zai samu ladar sulhunta uwa da ƴarta, horn ɗaya yayi aka buɗe masa gate, cikin nishaɗi yayi fakin motarsa ya fito da murmushi kamar wanda aka yi ma albishir.
What he saw a bakin ƙofar shiga part ɗinsa was surprise him, kurciyar daya gani a abuja itace a nan? Haske ne ta ko ina a gidan kamar rana, hakan ya bashi damar ganin layan dake wuyanta.
“Umar...”
Ya ƙwalawa Mai kula.da gidan kira, sai ga shi da gudu yana amsa kiran da yake masa. Keys ɗinsa ya miƙa masa.
“Zagaya ta baya ka buɗe ƙofar nan a hankali, kurciyarta nake son ta shiga ciki mu kamata”
“Ranka ya daɗe ai za'a iya halbeta da danƙo”
“Kana da danƙon ne? Kasan yadda zaka halbeta bata tashi ba?”
“Eh za a iya saitawa, amman ranka ya daɗe kurciya da dare baka san me take nufi ba, balle kuma ga laya a wuyanta”
“Idan mutum yana addu'ah babu abunda zai same shi, kawai ka halbe min ita idan zaka iya”
“Toh”
Ya nufi wani part ɗin na gidan, da ɓangarensu yake a can, be ɗauki dogon lokaci ba sai ga shi ya dawo da danƙon har da duwatsunsa guda biyar. Ayatul kursiyo ya karanta sannan ya saita inda take ya harba da bismilla. Firr tayi zata tashi sai ta faɗi saboda ya same ta a ƙafa. Da sauri Abdool ya ƙarasa zai kamata sai ta sake unƙurin tashi ta kasa har ya kama ta, sai da yayi bismillah sannan ya cire layar dake wuyanta. Umar ya miƙawa kuciyar ya shiga buɗe layar. Wasu surkulle ne aka yi aka kulle da fatar baƙar akuya, sai wata farar takardar a tsayarki takardar an rubuta sunan Namra da larabci.
“Namra”
Ya maimata sunan cike da mamaki da ɗaurewar kai.
“Miya kawo sunan Namra anan? Waya aikata mata haka?”
Yayi ma kansa tambayar da bashi da amsar ta.
“Umar kasan yadda ka yi da wannan kurciyar”
Ya faɗa sannan ya shiga cikin falon da abun a hannunsa.
KALSOOM POV.
Hannu ya kai ya shafa fuskarta.
“Haba dai baki kishi ranar ɗaura aure ba sai yanzu zaki yi? Ko dai wani ne ya zuga ki?”
Kai ta girgiza masa alamar a'a, ta janye hannunsa daga fuskarta ta miƙe tsaye.
“Zan shiga wanka”
Hannunta ya riƙe.
“Kalsoom ko na miki wani abu da ba daidai bane?”
Ta saka mashi kuka.
“Baka min komai ba, kawai dai...”
miƙewa yayi tsaye ya haɗe bakinsu, yana shafa bayanta alamar rarrashi. Sun ɗauki tsowon lokaci a haka sannan ya sake ta.
“I promise you ba zan miki wani abu da xai cutar da ke ba”
Ya kwantar da kanta ƙirjinsa. Ba shi take ji ba, Amaryar tasa take ji dan bata san da me tazo mata ba, bata son ta sake shiga irin rayuwar da tayi da Rashida a baya. Sai da ya tabbatar ta samu sukuni sannan ya sake ta yana tambayar me zai siyo mata.
“Ina son zogale”
“Okay”
Yayi mata kiss, ya shafi cikinta sannan ya juya ya fice. A gurin ta tsaya har sai da ta ji tashin motarsa sannan ta shiga wankan. Tana cikin wanka taji tsayawar mota sai kuma kamar ba ta Hilal ba, hankali kwance ta yi wankanta ta ɗaura tawul ta fito. Haka kawai ta ji bata da natsuwa idan bata leƙa taga wanda ya shigo ba, dan haka tana fitowa ta zira doguwar riga ta ɗora ɗankwalin a saman kanta ta nufi falon.
Abunda ta gani ya bala'in ɗaga mata hankali Rashida ce zaune saman kujera tana kallonta, fargaba da tsoro suka tunkarota lokaci ɗaya, idonta be gama tantance Rashida ɗin bace ko waninta, dan ta lalace sosai ta rame, idan har ita ɗince mi tazo yi gurinta, ga ta cikin hijabi niƙab a hannunta.
ASIM POV.
Yana saka kuɗin sai ga kiran Hajiya Sadiya, sai da ya shiga mota sannan ya yi picking.
“Hajiya na saka kuɗin”
“To yayi kyau, ina son muyi wata magana da kai Asim mai muhimmaci”
“Okay na zo kenan?”
“A'ah ba sai ka zo ba, saboda ƴata bata riga ta tafi ba”
“Toh ya za'ayi kenan”
“Ka same ni a wacan gidan, akwai zan maka wani tayi ne kuma ina fatar ka amsa”
“Okay what time zan zo?”
“An jima da yamma”
“Okay Allah ya kai mu”
Ta kashe kiran. Kai ya girgiza yana cizon bakinsa.
“Ta tabbata Nably ƴarki ce”
Ya kunna motarsa ya bar gurin. A unguwar su Hajiya sadiya yayi sallah la'asar, 6ana hango lokacin data shiga cikin gidan. Sannan shima yaja motarsa ya shiga cikin gidan.
Yana ta sallama bata amsa masa ba sai da ta fito bedroom sannan ta amsa masa. Cikin ladabi ya gaisheta yana kallon yanayin fuskarta mai ɗauke da damuwa.
Shi ya fara zama sannan itama ta zauna tana kallonsa.
“Asim ya maganar matar ka ta dawo kuwa?”
Ya ɗan sosa kansa.
“A'ah nayi nayi taƙi dawowa, kuma yanzu ta daina ɗaukar wayata ma, gashi ba gidansu ta je ba”
“Yanzu dai babu zancen dawowar ta kenan?”
“Gaskiya babu shi, daman ni dan kin matsa ne shiyasa nake son na dawo da ita”
Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta kalleshi a natse ta ce.
“Asim ina son ka auri yata, kuma auren shekara ɗaya, zan baka miliyan ashiri, zan baka gurin da zaku zauna, bana buƙatar ka yi komai, zan maka lefe zan baka kuɗin sadaki, zan mallaka maka shagona na siyar da zinari da sabuwar kasuwa, kuma duk wani event da za ayi ni zan ɗauki nauyi”
Da sauri Asim ya miƙe tsaye yana mamakin irin wannan narkakkiyar dukiyar da zata bashi, saboda kawai ya auri ƴarta ƴar da bata taɓa labarta masa tana da ita ba.
________________________________
BEST REGARDS 🌹
I LOVE YOU ALL♥️
*77*
Kalsoom ta yi baya-baya kamar zata koma ɗaki, sai Rashida ta yi saurin miƙewa tsaye ta ɗaga mata hannu.
“Dan Allah ki tsaya ki saurare ni, ba cutar da ke zan yi ba, zuwa na yi na roƙe ki kuma na nemi taimakon ki”
“Akan mi, mi zan miki?”
“Ki dubi girman Allah ki taimaka min ki riƙe min ƴaƴana...”
“Ban gane ba, kamar ya ƴaƴanki?”
“Bana son amaryar da Hilal yayi ta riƙe su, saboda bata da tarbiya kuma azzulamace zata iya cutar da su”
Kalsoom ta nuna ta da yatsa tana mai jin duk wani tsoro nata ya tafi.
“Ke Rashida yadda kika yi boko haka nima nayi, karki nemi raina min hankali wato na rikasu a sake cewa zan kashe su ko? Naga dai yanzu mu biyu ne, be kamata ace ni kaɗai kike kishi da ni ba”
Hawaye ya cika idon Rashida.
“Ba kishinki nake ba wallahi, gaskiya nake faɗa miki kuma nake roƙon ki, ki taimaki rayuwar ƴaƴana ki riƙe su”
“Teema ce tafi kowa dacewa data riƙa ƴaƴanki, saboda ita ce ta gari a idon Hajiya, kuma an yarda da tarbiyarta, sannan naga ƙawarki zata kula miki da su kamar ke, dan haka ki fita ki bar min gida ko na kira Hilal yanzu na faɗa masa”
Ta share hawayen da suka zubo mata.
“Ba sai kin kira shi ba, zan fita, na gode da kika saurare ni, ban cancanci ki saurareni ba amman kin saurare ni na gode sosai”
Ta saka niƙab ɗinsa, sannan ta juya cikin kuka ta fice. Rufa nata baya Kalsoom ta yi, ta tsaya bakin ƙofa tana kallonta, har sai da taga ta shiga motarta mai gadi ya buɗe mata gate ta fice sannan hankalinta ya kawanta.
“Allah ya min tsari da sherin ki ni wannan wane irin mugun kishi ne!”
Ta faɗa tana maida ƙofar falon ta rufe.
*** *** ***
Da wani irin kuka Rashida ta ƙarasa gida, tana mai jin zuciyarta kamar zata tsage biyu, saboda baƙinciki da damuwa, ta rasa inda zata sa ranta taji sanyi, ta rasa inda zata saka rayuwarta ta samu sassauci, lokaci ɗaya duniya ta juye mata ta zo mata baibai.
Bata samu gurin faka motarta ba saboda motar Alhaji Bashir da ke waje, hakan ya tabbatar mata da yana ciki kenan.
Tafiya take kamar wata tsohowa, daman bata da wani kuzari saboda rashin cin abincin kirki da kuma damuwar da ta gama karya mata gaɓoɓin jiki.
Safa da marwa ta hango yana yi a ƙofar shiga falonta, ko be faɗa mata ba, tasan Asmee ta kai masa labarin da ta faɗa mata ɗazun ne, dan tana iya hango tashin hankalin dake shimfiɗe saman fuskarsa. Tun kamin ta ƙaraso inda yake, ya soma nuna ta da hannu, cikin wata irin murya da shi kansa be san yana da ita ba.
“Macuciya azzaluma, dan taki rayuwar ta ƙare shine kike neman abokin kuka ko? To nafi ƙarfin ki Wallahi baki isa ki rushe min rayuwa ba”
“Kamin ka zo nan kana min hargagin banza ina fatar kaje asibiti sun tabbatar maka da kana ɗauke da cutar ko? To ni ba abokin kuka nake nema ba, kai ne kake neman abokin mutuwa, dan rayuwa sai ta fi taka tsawo, sannan na gama rushe maka rayuwa Alh Bashir matuƙar baka aure ni, dan ban dace da zama da kowa ba sai kai, kai ne ka sani a halin da nake ciki”
“Ko kuma kika sani ciki ba, daman ai na daɗe ina zarginki, duk mace da zata bada kanta ga wani namiji ba mutum ɗaya zata tsaya ba, waya sani ma ko mijinki ne ya ɗauko cutar ya saka miki ke kuma kika saka mana, ni ban san ƙaddararta kai ni mu'amala da ke ba”
“Ni bance ka zame min ƙaddara ba kai zaka ce na zame maka? Na rasa abubuwa da dama sanadin mu'alama da kai, ƴan'uwana sun guje ni, mijina ya sake ni, na rasa lafiya ta, da duk wani farinciki nawa sanadinka Bashir, duk kai ka jani ga wannan halaka”
“Ko kuma kika jani ba, da baki sake jikinki ba zan gani ne har na yi sha'awa? Idan baki yarda ba fyaɗe zan miki ne? Baki kiji na faɗa miki da zarar naje aka gwada jinina aka tabbatar ina ɗauke da wannan cutar kutu ce zata raba ni da ke...!”
Yana kaiwa nan ya doshi gurin motarsa. Ita kuwa ta raka shi da maganganu tana hawaye.
“Idan ka fasa kai ni kotu baka haifu ga uwarka da ubanka ba Bashir kai ba ɗan halak ba ne, azzalumi macuci wanda be ji kunya keta dokar Allah, sakarai mai neman Matar abokinsa Allah ya isa tsakanina da kai”
Sai ta ta kunna motarsa ya bar gidan sannan ta durƙushe a gurin tana kuka.
“Kaico na ni Rashida, ina ake siyar da farinciki ne na siya! Ina zan yi musanyar damuwa da kuka na samu sanyin zuciya! Mi na ma duniya haka ne? Miyasa suka ƙaddarori zasu taru a kai na ne? Allah na tuba ka yafe idan zunubi na ne yasa ni a wannan halin”
Kuka take sosai tana ji kamar ƙasa ta haɗiyeta ta mutu ta huta gaba ɗaya da wannan rayuwar. Ra rasa dalilin daya sa rayuwa take koya mata darussan da take ganin bata cancanci koyansu ba.
NAMRA POV.
Kai tsaye direban ya nufi gidan Mai Martaba kamar yadda Yarima ya umarce shi, horn ɗaya yayi aka buɗe musu gate, ɗayan part ɗin gidan ya nufa da su, sai ya faka daidai ƙofar part ɗin ya fito da sauri ya buɗe ma Abbah ƙofa.
“Ya ce akwai komai a ciki, idan akwai abunda kuke buƙata zaku min magana”
Kai kawai Abbah ya ɗaga masa ya nufi ƙofar. Anty Amarya ce ta amsa masa da to, Namra na riƙe da hannun Anty kanta kuma kwance saman kafaɗar Anty, har suka shiga falo, sanyin ac ne ya fara musu martabun, daga bisani ƙamshi ya biyo baya. Kai tsaye Abbah ya nufi wani ɗaki dake ɗayan ɓangare da wasu ɗakunan, yana shiga ya hango manya tufafi kala biyu saman gadon, sai kuma kayan bachi da ba a cire daga leda ba kala ɗaya, an ɗora takalmi da turare da hula mai kyau saman kayan, hakan ya tabbatar masa nan ne ɗakinsa, ɗan murmushi yayi kaɗan ya rage kayan jikinsa ya nufi bathroom.
Mamaki ya cika Namra da Anty Amarya lokacin kowa ya samu tufafin sajawa da kayan bachi saman gadonsa, bama kamar Namra da ta tarar har da pants da pad ya aje mata, ya akayi yasan bata sallah shine abunda ya fi tsaya mata a rai. Bathroom ta shiga, ta yi wanka, sannan ta shirya cikin kayan bachi masu kama da na maza, ta fito ta nufo falo. Anty Amarya da Abbah ta samu zaune a dinning suna cin abinci. Abbah ne ya fara ɗagowa ya kalleta, murmushin da ta gani a fuskarta yasa idonta cika da ƙwalla.
“Toh Sarkin kuka zaki fara ko?”
Cewar Anty Amarya fuskarta ɗauke da annuri, tana miƙawa Abbah tea da ta haɗa masa.
“Komai ya zo min kamar mafarki, gani nake kamar ba gaske bane, ban yi zaton Abbah zai saurare ni haka da wuri ba har ya yafe min, nasan nayi muku abubuwa marar kyau da yawa, amman duk da haka suka samu fili a zuciyarku kuka yafe min”
“Kin cancanci yafiya Mamana, saboda kin gane kuskurenki, sai dai kin shiga rigar mutane masu mutunci wanda hakan yasa kika samu yafiyata a kusa, sai dai ina fatar ba zaki ƙara aikata irin wannan kuskuren ba”
“Wallahi ba zan sake ba Abbah, na maka alƙawari har na koma ga mahallici na,ba zan sake aikata kwatankwacin wannan kuskuren ba”
“Allah yayi miki albarka”
“Amin Abbah na gode, i love you so much”
Ta zo da sauri ta rumgume shi tana kuka. Anty Amarya ta share hawayen idonta tana kallon Abbah.
“Allah ya saka maka da alheri, na gode”
“Yanzu ai ta kuka da ciwon zuciya ya ƙare ko?”
Cewar Abbah fuskarsa da murmushi yana kallon Anty Amarya cike da son Amaryarsa. Daga bisani ya kalli wayarsa da ke saman dinning tana ringing. Hajiya Barau ce rubuce a screem ɗin wayar. Miƙewa yayi tsaye, sannan ya kai hannu ya ɗauki wayar yana danna picking ya nufi bedroom.
A kujerar da ke kusa da Anty Namra ta zauna, tana share hawayen da suka ƙi tsaya mata.
“Na haɗa miki tea zaki sha?”
Ta gyaɗa kai.
“To ki zuba abincin ki ci idan kin gama zan haɗa miki”
“Bana jin yunwa Anty, tea kawai ya isa”
Ajiyar zuciya Anty ta sauke, ta shiga haɗa mata tea, tana faɗin.
“Namra duk kin rame kin koma wata iri, kin yi baƙi sosai, Yarima ya faɗa mana Asim ya sake ki ne saboda kina da ciki!”
Ta gyaɗa kai tana share hawaye.
“Kuma har yanzu be neme ni ba, ina gidansu Lamido cikin ya zube”
“Kin san ciki ba zai taɓa tsayawa a mahaifarki ba Namra saboda matsalar da kika samu, na yi mamaki ma da kika samu ciki bayan an saka miki roba”
“Shi yace sai na cire, kuma da ma samu cikin yace be shirya haihuwa yanzu ba, sai dai na zaɓa tsakanin cikin da shi, ni kuma na ƙi yarda na zubar shiyasa ya sake ni”
“Kin samu ƴancin kan ki yanzu, Allah zai bi miki haƙƙin ki. Amman ina kika haɗu da wannan yaron”
A nan Namra ta kwashe labarin komai na sanin da tayi ma Abdool ta faɗa ma Anty.
“Yana da mutunci sosai, kuma ina fatar zaki masa hallacci duk ranar da ya nemi ladan alherin da yayi miki”
“Kamar ya?”
Ta tambaya dan har ga Allah ita bata gane inda zancen Anty ya dosa ba. Anty ya miƙe tsaye tana murmushi.
“Kamar haka, ki je ki kwanta dare ya yi, zan kira Maryam na ce ta shirya zan vata mamaki, daman ta fi kowa damuwa da auren nan na ki”
“Na gode sosai Anty sai da safe”
Ta daɗe a gurin zaune sai ƙarewa falon kallo take sannan ta tashi ta nufi bedroom.
Har garin Allah ya waye, dan har yanzu ta kasa yarda da abunda ya faru, ganin komai take kamar mafarki. Idonta biyu aka yi kiran sallah asuba, unƙurawa ta yi ta tashi, sai ta nufi gurin maɓallin kutar ɗakin ta kunna. Ta shiga toilet ta tsabtace kanta sannan ta yi wanka ta fito.
Bata tsaya shafa mai ba, ta ɗauki abaya ta saka, sannan ta ɗora da hijab, gefen gado ta zauna sai ta ɗauki carbi tana lazimi, ba ita ta tashi ba sai bakwai da rabi saura, shi ma dan ta ji ana buga ƙofar falon ne.
Bata damu da tambayi ko waye ba kawai ta kai hannu ta buɗe ƙofar. Suna haɗa ido gabanta yayi mugun faɗuwa, da sauri ta sadda kanta ƙasa, shi kam ƙin sauke idonsa ƴayi har ta miƙa masa gaisuwa.
“Ina kwana?”
“Nan ba ina kwana suke cewa ba”
Ɗan murmushi ta yi wanda be kai zuci ba.
“An tashi lafiya?”
“Lafiya ƙalau, i hope you sleep well?”
“I did”
“Amman idonki ya nuna kamar ba ki yi bachi ba”
“Kana da buƙatar wani abun ne?”
Ta tambaya da nufin kawar da maganar. Wani dogon numfashi yaja ya sauke
“Ban sani ba ko kuna da bukata ne, yanzu zan kama hanya, Mai martaba ya kira ni yana da buƙatar gani na, ajima direba zai ɗauke ki zai kai ki a miki passport, da ƙarfe uku jirgi zai tashi, so za a muku duk wani abun da ya kamata, around nine za a kawo muku breakfast. I think Abbah suna bachi, ki faɗa musu na tafi”
Kai ra gyaɗa masa, sai ya zuba hannyensa aljihu ya juya zai wuce.
“Ab...da...llah”
Ta kira sunansa cikin wata irin siga da ba'a taɓa kiransa sunan yayi masa daɗi kamar yadda ita ɗin ta kira shi ba, har cikin zuciyarsa ya ji kiran nata da muryarta dake kamar zata fasa masa kuka. Juyowa yayi ya kalleta da manyan idanuwansa.
“Thank you”
Gira ɗaya ya ɗaga mata, alamar for?
“For helping me out”
Murmushi yayi mata mai fidda annurin fuskarsa.
“Safe flight”
“Wish you the same”
Murmushi yayi mata as respond ya juya ya cigaba da tafiya abunsa, kamar wanda baya son taka ƙasa. Haka kawai ta samu kanta da kasa ɗauke ido a kansa har sai da ya shige part ɗinsa.
ASIM POV.
Kallo Hajiya Sadiya ta bishi da shi, zuciyarta Allah-Allah ya amince.
“Miyasa zaki min tayi mai tsada akan kawai na auri ƴarki?”
“Saboda kai ne kaɗai na yarda da tarbiyarka, kuma nasan ƴata tana son ka, saboda ta nuna min hoton ka har tace zaka zo ka gaishe ni”
“Ko baki bani komai ba zan iya aurenta saboda aurenta na yi niyar yi, amman ki faɗa min gaskiyar abuda kike ɓoyewa wata ƙila zan iya taimakon ki”
“Ko da baka aureta ba, na yarda ka yi zina da ita, idan ta samu ciki sai ka rabu da ita”
“Miyasa sai ni?”
“Saboda ba zan iya facing yata na faɗa mata ta auri wanda bata so ba, kuma nasan ba zan saka ta aikata zina ba”
“Da baki yi gaggauwa ba, da aurin ƴarƙi zan yi, miyasa baki bar ni na aureta ba, iya ka kice min na turo iyayen Sai a ɗaura mana aure. Ki faɗa min gaskiya mana Hajiya”
“Zauna zan faɗa maka komai, saboda na yarda da kai kuma ina fatar zaka taimake ni”
Ya zauna yana fuskantar ta.
“Sunana Hajiya Sadiya kamar yadda ka sani, an haife ni a garin nan, amman ko da na tashi ban san iyayena ba, mahaifina da mahaifiyata duka Allah yayi musu rasuwar tun kamin na mallaki hankalin kai na, dan haka na tashi a gidan kakana Sarkin Katsina na wacan lokacin, na samu gata iya gata a gidan, duk da bani kaɗai bace wacce ake riƙo a gidan, amman saboda ni marainiyace, be yarda ya bar mu mun yi karatu a nan ba, a lokacin govnati na ɗaukar nauyin karatun saboda ana ƙyamar bokon ne, so duk wanda ke da ilmi za a ɗauki nauyinsa zuwa ƙasar waje karatu, Zuwaira da Murja da Sadiq su aka saka a ƙarƙashin govnati ni kuma shi ya biya min a cikin aljihunsa. Dukan mu mun yi karatu, duk da ba ƙasa ɗaya aka kai mu ba, dan ni na zaɓi London ne, su kuma Egypt aka kaisu suka yi karatun lafiya.
Na fi sawa shashanci gaba, saboda farar fatar da nake tare da su, na kan rakasu gurare daban-daban hakan yasa muka shaƙu da su sosai. Su san burina saboda ina yawan faɗa cewar nafi son nafi kowa ɗaukaka a makarantar nan, ranar sai wata take ce mun zata faɗa min wani sirri, zata kai ni inda za'a taimaka min na samu ilmin da ya fi na kowa, kuma na fi kowa ɗaukaka a makarantar. Ban yi musu ba, na biyeta ta sani a cikin wata ƙungiya, ashe ƙungiyar asirice, buƙatata ta biya tabbas, saboda a wannan shekarar ni nayi ta ɗaya a duk faɗin makarantar, daga haka sai abubuwa suka buɗe, duk abunda nake da bukata zan je ne kawai na faɗa kuma sai buƙata ta biya, a lokacin muna meet duk ƙarshen wata, amman lokacin dana ƙare karatun na dawo nan sai suka haɗi ni da manyan da suke abuja, a nan naga manyan mutane, maza da mata a cikin har da manyan ƙasar nan. Duk lokacin da za'ayi meeting ɗin, na kan bar Katsina na je abuja da sunan ganin wata Sister mu ƴar sarki, sai naje meeting idan an gama da kwana biyu na sai na dawo.
Na samu babban aiki a lokacin, nama fi kowa kuɗi a gidan mu, da haka na haɗu da baban su Nabila. Bayan mun yi aure yace baya son aiki, sai na haƙura, a nan su kuma suka soma saka min ƙa'idojin da ban san da su ba a wacan lokacin.
Sun ce min dole ne na riƙa neman mata ƴan'uwana, idan ba haka ba, ba su yarda na fitar da zakka ba. A dole na ɗauki ka'idar mu'amala da mata ƴan'uwana, tun ban saba ba har abun ya zame min jiki, ya koma bana jin daɗi mu'amala da mijina sai mata. Daga baya kuma suka ce suna son a riƙa kawo musu sabbin membobi saboda tsofin ciki suna mutuwa ne, kuma ina son a riƙa yaɗa abun.
A abuja nake zaune da mijina, ɗan haka duk lokacin da naso zuwa kawai nake gurin meeting ɗin ba tare da ya sani ba, wata rana da muka yi meeting sai suka ce suna da buƙatar na Sadaukar musu wani daga cikin iyalaina, ba ni da zaɓi dole na bada mijina, sai ya samu haɗarin mota ya mutu, daga nan kuma sai babban ɗa na, sai mai binsa, sannu-sannu suka cinye min duka ƴaƴana, Nabila ce kawai ta rage min. Shekaran jiya da nace maka zanje birnin keebi ba can naje ba, Abuja na je, gurin meeting ɗin. Yanzu kuma Nabila suke so, ko ɗanta. Ni ko da na bada ita ƙara na bayarda kai na, shiyasa nake son ka taimake ni, ka ceci rayuwata da ta ƴata saboda ita kaɗai ta rage min”
Asim ya sake miƙewa tsaye a karo na biyu.
“Wallahi Allah yana so na, wato da yanzu sai dai ki bada ni? Dan nasan zasu ma iya cewa ki kawo yaron gidanki, ko kuma idan mun yi aure ace ko bada surikin ƴar ki, ai ni duk sun kuɗi na be kai na iya rayuwata ba kuma ni daga yau na barki har a bada wallahi”
“Kar kayi saurin yanke hukuncin Asim kaje ka yi tunani”
“Ba wani tunani da zan yi, salon ki sani cikin mugun hali”
“Da ina da niyar saka ka da na saka tun farkon dana saka tun farko dana fahimci kana da son kuɗi, amman ba kai nake target ba matarka, saboda nasan idan na sata cikin ƙungiyar zasu biya kuɗi mai yawa wata ƙila ma ya iya zama fansar ƴata, amman sai gashi ka saki matarka, da yanzu ace zaka iya kawo min matarka zasu iya ɗaga min ƙafa”
Tsayawa yayi kallonta.
“Indai har Namra zata iya zana fansar ƴarki to zan iya kawo miki ita, bisa sharaɗin zaki bani naira billion uku”
“Wallahi zan baka, kuɗi ba matsala ta bace idan na faɗa maka abunda na tara sai ka haukace, kuma Namra ba kasheta zamu yi ba Wallahi, cikin ƙungiyar kawai za mu sakata”
“Amman taya zan kawo miki ita?”
“Zaka maida aurenka, sannan duk abunda zai biyo baya ya biyo, kuma idan kana so zaka iya auren Nabila”
“Ƴarki kam na yafe, amman Namra zaki sameta kamar yadda kike buƙata”
Ta miƙe tsaye ta shiga ɗakinta bata jima.ba ta fito riƙe da amt ta miƙa masa.
“Akwai milion talatin a ciki kayi amfani da su”
Ya miƙa hannu ya karɓa sannan ya juya ya fice.
TEEMA POV.
Tana kwance saman jikinsa, shi kuma sai faman dannar waya yake yana murmushi. Azatonta dan tana shafa jikinsa yake murmushi, shi kam hankalinsa gaba ɗaya ya tafi kan waya sai faman chating yake da Kalsoom.
Ƙyalƙyalewa yayi da dariya sannan ya kashe datarsa ya kalleta.
“Bari na leƙa office”
“Okay Allah ya tsare min kai”
“Amin dear. Amm anjima Hajiya tace zata aiko da su Ezzah”
Sam bata ji daɗi ba, duk da tasan dalilinsu aka auro ta, amman bata yarda ta nuna masa ba.
“Kai Amman ko na jidaɗi daman ina ta jiran su zo, Allah kawo su lafiya”
“Amin”
Ya faɗa yana ɗaukar hulal dake saman hannu kujera ya saka a kai.
“Okay I love you”
“Love you too”
Da kallo ta bishi sai da ya fice sannan ta miƙe tsaye.
“Sati uku da aure ace za a ɗauko yara a kawo maka, nifa ba bautarsu na zo yi ba, ko amarci ban gama ci ba za'a haɗa ni da ala ƙai ƙai, yara zaggan-zaggan da su, su riƙa sa maka ido idan ka yi ma miji wani abu, mtsssss”
Taja wani uban tsaki ta wuce bedroom ɗinta. Bata jima ba ta fito ta nufi kitchen, girki ta ɗora sai mita take ranta duk a ɓace, dan har ga Allah bata so a kawo su yanzu ba.
“Daman fa ance wasu uwayen miji ba son suruka suke ba, in banda sheri kin san ina Amarya ɗan Amarcin ma ba za'a bari na yi ba, kai kayi naka lokacin sai kace wani ba zai yi ba, nasan dan su aka auro ni amman ai a bari na ci lokacina, tun da can ba saman ƙaya suke ba, daga zuwanka da ƙurciya zaka fara aikin ƴaƴan kishiya”
Kamar mai faɗa da wani haka ta riƙa zuba surutanta har ta yi girkin ta gama mita take, sai da tasa komai a muhallinsa sannan ta shiga ciki ta yi wanka. Tana fitowa ta shirya cikin yellow atamfa, ta kashe ɗauri ta feshe jikinta da turare sannan ta fito falo ta zauna.
Tana jin tsayawar mota ta ƙara gyara ɗaurin ɗankwalinta, tana zaton ko Hilal sai kawai ta ji mota ta tashi, su Ezzah sun turo ƙofa sun shigo fuskarsu da far'ah bakinsu kuma ƙumshe da sallama.
Ciki-ciki ta amsa musu tana murmushin da be kai zuci ba.
“Maraba da ƴaƴana”
“Momi ina wuni? Momi ina wuni?”
“Lafiya ƙalau”
Sai suka zauna saman kujera. Daga nan bata sake bi ta kansu ba, sai da ta ji motar Hilal sannan ta tashi ta koma tsakiyarsu ta zauna ta jasu jikinta ta rumgume tana murmushi.
“Ku bani labarin Hajiya...”
ABDOOL POV.
Around ten ya sauka Katsina, sai da ya fara biyawa Mai Martaba ya ganshi sannan ya wuce gurin Ummi. Da murmushi ya shiga part ɗin Ummi, kamar yasan ita kaɗaice a falon, dan duk ƙannensa sun tafi makaranta.
“Ummi barka da safe”
Ya taɓe baki tana kallonsa.
“Ni ban ga amfanin wannan hutu naka ba, kullum kai ne yawo ba zama gida, yanzu da aure kake yi wace mace ce zata ɗauki wannan rayuwar”
Kusa da ita ya zauna yana dariya.
“To ai gurin matar na je, yau zan baki labarin komai saboda na samu mafitar matsala ta, amman fa nasha wuya but at the end yau tace min Thank you”
“Kana nan kana wahalar da ƴar mutane ai dole wata ta saka cin kwakwa, tun da ka tagi Amirar nan kuka take, na rasa gane kanta idan kuma na tambaye ta sai tace babu komai, yau ma ce min tayi gida zata je daker na hana ta”
“Ina take?”
“Tana ɗakinta”
Ya miƙe tsaye ya nufi ɗakin Amal. Yana tura ƙofar ɗakin ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta juya,
“Amira can we talk?”
“Maybe Later i need some space”
Ta faɗa da muryarta ta kuka.
“Okay but i just want you to know that i care for you, if you need someone to talk to, i'm downstairs”
Daga haka ya juya ya fice. Ita kuma. Ta fashe da kuka.
*78*
Kusa da Ummi ya sake zama yana kallon tv.
“Tana son ta saka kanta cikin matsala ne kawai Ummi amman tasan ba zan taɓa son ta ba”
“Nasan tana son ka har zuciyarta, amman sam ban yarda da yarinyar nan ba, mutanen da sukayi ƙoƙarin su kashe ka, waya sani ko plan ne aka yi ta yadda idan ta aure ka zata fin jindaɗin kashe ka”
Yayi murmushin gefen baki.
“Ko babu plan Ummi bana son ta, ko da kuwa tun can farko ita mai tarbiya ce, because if i love someone i mean it no matter what she did or whoever she is, and if i said i do i do, so i don't love Amira, i only fell in love once because i have never been in that kind of situation, but when it comes to Namra i take it so serious, and i love with all my heart and blood and mind and soul i love her more than you think Ummi”
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke, ta kalli ɗanta fuskarta da alamun damuwa.
“Tell me more about her”
Miƙewa ya yi tsaye ya nufi freezer.
“She's so simple and kind, but difficult to handle. You know when we first meet, she slap me and insult me in front of my boys, but i can't slap her back”
Ya ƙarasa yana bulbula ruwan da ya fiddo a cup. Ummi ta yi murmushi.
“I know how my son is ba ya faɗa da mata”
“Yap bana faɗa da mata because we are not in the same level, strength, brain, heart, soul and lot. Ban taɓa jin ina son wata mace ba, but lokacin da na ji ina son Namra, nasan our souls mean to be, duk da a lokacin na san tana da aure, amman zuciya ta kasa haƙura, and now what! Her husband divorce her ta je wani gida ta zauna, kuma ƙaddara ta sake haɗa mu kaduna na kaɗe yaron gidan ina zuwa sai gata a gidan, hmm' mmm funny, and now ni ne silar shiryawa da iyayenta, i hope you love her too?”
“Of course i love her ai dole naso matar da ɗa na yake so, but i'm just worried about Mai Martba, ba lalle ne shi ya so ta”
“Why”
“Saboda Bazawara ce! And i hear that Mai Martaba and Hajiya Shafa sun maka mata”
“What...!”
Ya aje cup ɗin ruwa dake hannunsa saman dinning yana kallonta fuskarsa cike da tashin hankali.
“How true it's?”
“Mai Martaba ya kira ni da kan shi, yana neman shawara akan zai ɗoraka a Sarautar Katsina, da na nuna masa be dace ba sai ya nuna ɓacin ransa, the following day ya sake kira a waya ya faɗa min Hajiya Shafa tace be kamata a ɗoraka a Saurata baka tare da iyalaiba, dan haka ta maka mata, zata aura maka Zaliha ƙanwarta, idan anyi auren da watanni sai a baka Sarautar, kuma Mai Martaba yayi na'am da hakan”
“Miyasa baki faɗa musu ina da wacce nake so ba?”
“Idan na faɗa zai ga kamar ina kare ka ne, amman ina son ka min wani abu Abdallah, duk yadda Mai Martaba zai yi karka yarda ka karɓi Sarautar nan, kai ne ɗa na uku a gurin shi, be kamata ya tsallake su ba, ya ɗauki Sarauta ya baka, nasan yana son ka, amman hakan ba zai jawo maka komai ba sai ƙiyayya da ganin laifi, kai kuma ka yi ƙanƙanta da irin rayuwar nan, kuma idan har ka yarda ka auri Zaliha, to ka jefa rayuwarka da ta mu cikin matsala, tun da ƙanwar Hajiya Shafa ce, kuma kasan wacece Hajiya Shafa a gareni da gare ka. Ka da ka amince da duka biyu idan har ya yi maka magana”
“Ai ba zan amince ba, ina son aiki na kuma ina alfahari da shi, ni ba Sarauta ba ce a gabana, kuma Namra ce kaɗai matar da nake so”
“And be careful with her love too, kar ya rufe maka ido ka saɓawa Mahaifin ka”
“My Dad is...”
Ummi ta miƙe tsaye tana tarar numfashinsa.
“I know who your Dad is, he's my ex-husband the Father of my own male son”
Ta nufi bedroom ɗinta. Shi kuma ya faɗa zaune saman kujerar dinning yana bugashi da ƙarfi.
“Damn it! miyasa abubuwa zasu zo min haka kuma yanzu? Shine surprise ɗin da Mai Martaba yake ta faɗi? Ya Salam...!”
Ya miƙe tsaye, sai ya nufi kitchen duk da ya san babu abunda zai ɗauka a gurin. He need some fresh air, sai ya buɗe ƙofar baya ya fita, jin ya gaba ɗaya gidan ya masa wani irin, kai tsaye ya nufi Garden, ko ba komai yana son kukan tsuntsaye maybe zai sashi relaxing ya sama ma kan shi mafita.
Gaban icen guava ya zo ya tsaya yana kallon pool, motsin mutum ya ji a bayansa, yasan cikin biyu ba za'a rasa ɗaya ba, Maybe Amira ce tun da ita kaɗai take gidan ko kuma barewa, dan tana masa haka a duk lokacin da ya shigo Garden ɗin. Juyowa yayi sai yayi ido huɗu da Amira fuskarta shakaf da hawaye.
“What do you want?”
“You told me if i need someone to talk to”
“It Abdool who told you that, and now i'm someone else, and my words could hurt you, i'm not in the mood”
Cikin muryar kuka ta ce.
“You already hurt me because i learn the truth, i know you upset because of what Ummi told you, we share the same pain, i'm in love with you while you're in love with someone else”
Ta share hawayenta da haɓar rigarta.
“Maybe i will have peace of mind if you tell me that you never love me, maybe i will back to my senses, think about my future and....”
Kuka ya ci ƙarfinta. Taku biyu yayi ya matso kusa da ita.
“Do you know what is best for you, ki koma gida cikin iyayenki, ki manta da ni a rayuwarki, and i promise you zan rufa miki asiri ba zan faɗawa kowa abunda kika aikata ba”
“Zan koma gurin iyayena, nima a yanzu babu abunda na ke so sai su, but forgetting you is the hardest thing ever, thank you so for letting me staying with your family and know you better, can you take me home now please, am eager to see my parents”
“Yeah... Zan ma direba magana, ki shirya kayan ki”
“Ban zo da komai ba a nan”
Har ta juya sai kuma ta juyo.
“Ina matar da kake so take?”
“Why?”
“Saboda ta fi kowa sa'ah a duniya, ina son na ganta ne kawai”
“I can't tell you Amira, i'm sorry to say this, i don't trust you”
“I know i shouldn't...”
Ta juya ta shiga ciki da kuka. Da kallo ya bita sai da ta fice sannan ya haka hannunsa aljihu ya ciro handkerchief yana shinshinawa.
“I loved you so much”
Ya ɗauki tsawo lokaci a gurin sannan ya nufi part ɗinsa. Be daɗe ba ya fito da takarda hannunsa ya kira ɗaya daga cikin direban gidan ya miƙa masa.
“Zaka kai Amira a wannan addireshin, karka yarda ka sauketa ko ina sai nan”
“Toh Ranka ya daɗe”
Ya nufi part ɗin Ummi. Su biyu ya samu a falon Amira ta yi kneel down tana riƙe da hannun Ummi tana kuka, Ummi kuma na hawaye.
“Ki min hallaci Ummi kin riƙe ni kamar ƴar cikin ki, baki taɓa nuna min banbanci da ƴaran ki ba, na yi fatar wata rana zata zo da zan saka miki abunda kika min, Na gode da karamcin ina fatar zaki yafe min duk abunda na miki”
“Ba ki min komai ba Amira sai alheri, Allah ya miki albarka”
Kuka ta yi sosai sannan ta saki Ummi ta nufi ƙofar fita kamar zata faɗi. Kai Ummi ta girgiza ta kalli Abdool ta ce
“Is not fair ya kamata ace mu muka kai ta gida”
Ya ɗago daga jikin ƙofar da yake jingine ya nufo Ummi
“No hakan zai fi mata, dole ta tanadi abunda zata faɗawa iyayenta, idan suka gan mu kawo ta za suyi zaton ko ina son ta ne, kuma dole zasu tambayi inda na haɗu da ita, ni ko kin san gaskiya zan faɗa musu, beside irin waɗannan mutane ba a yawo da su it risk baki san abunda suka tana da ba”
Kai ta kaɗa masa cike da gamsuwar bayanin da yayi mata. Sannan ya juya suka fita tare gurin mota suke je suka tsaya, ita kuma tana daga ciki sai faman kuka take. Hannu Abdool yasa a aljihu ya ciro takardar kuɗi ya miƙa mata.
“Maybe you will need this”
“No i don't”
Ta kawar da fuskarta tare da cewa direba su tafi. Daga Ummi har Abdool tsaye suka yi suna kallonta har aka buɗe musu gate ɗin farko, bayan sun fice aka rufe gate ɗin sannan suka daina hango motar ta.
“Ina jin kamar ba mu kyauta mata ba, kuma bata jidaɗi ba ta ƙi ya tsaya har su Fauza su dawo”
“Zamu iya mata alheri daga baya idan mun fahimci da gaske ta shiryu, ai ƙara haka idan suna nan ai zasu ta kuka suma”
“Allah yasa ta shiryun, but wata rana zamu yi visiting na ta”
Ya miƙa hannunsa yana miƙa.
“Bari na shirya na koma gurin Mai Martaba”
“Okay”
Ummi ta juya. Shi kuma ya nufi part ɗinsa. Cikin rashin jundaɗi ya nufi part ɗinsa, dan bana jin kamar be kyautawa Amira, but he has no choice but to let her go. Cikin mintuna shirin ya watsa ruwa ya shirya cikin manyan kaya dan cox he know how Mai Martaba hate ƙananan kaya, yana fitowa part ɗinsa sai ƙamshin turare ke tashi. In five minutes ya isa kan wuri. He got lucky Mai Martaba be je ko'ina ba, duk da yana da niyar fita yau, sai dai ya tararda fadar cike saboda baƙin da suka zo daga jibiya. Yana shiga suka fara miƙa masa gaisuwa da kirari, hannu kawai ya ɗaga musu ya juya ya fita.
Barori ya samu a babban falon Mai Martaba suna hidimar chanja carpet, da sauri suka zubar da abunda ke hannunsa suka zube ƙasa suna masa gaisuwa. Kamar wanda be gansu ba, haka yayi ya nufi ɗayan falon nasa, zama yayi saman kujera yana duba jaridu, can kuma ya ji gurin is so boring ya miƙe ya nufi can ɓangaren Mai Martaba inda babu wanda ya ke shiga sai iyalansa.
Saman wata kujera ya zauna mai lilo yana kallon pop ɗakin. Zuwa can ya fara jin bachi, daman a gajiye yake. Shigowar Mai Martaba ne yasa shi saurin sauke ƙafafunsa ya tashi zaune.
“Allah ya taimaki Mai Martaba ya ƙara maka lafiya”
Zaunawa yyi da murmushi a fuskarsa.
“Yarima Abdallah, kuma sarkin mu na gobe”
Yayi dariya.
“A dai bar ni a Yariman, har yanzu bana mafarkin zama Sarki”
“Aiko ƙara ja shirya, damin very soon zaka zama Sarki, kasan har yanzu ban faɗa maka albishir ɗin ka ba ko?”
“Shiyasa ma ka ga na zo yanzu”
Mai Martab ya ɗora ƙafa saman ɗaya yana kallon Abdool cike da natsuwa.
“Wato Albishir ɗin ka guda biyu ne, kuma dukaninsu suna da muhimmanci, kuma ina fatar zaka karɓa ka yi na'am da dukansu. Na farƙo dai ina maka albishir da cewar Hajiya Shafa ta baka Zalihatu kyauta, abu na biyu kuma mun yanke shawarar naɗa ka sabon Sarkin Katsina...”
Wani irin kallo yayi ma Mai Martaba kamar Ummi bata faɗa masa komai ba, sai ya sauka ƙasa yana nuna kansa.
“Mai Martaba ni?”
“Kai fa”
Ya faɗa da murmushi a fuskarsa.
“Ka fi kowa karantar waye ni Mai Martaba, ka fi kowa sanin abunda ya dace da ni, ba zaka taɓa zaɓa min sheri ba, kuma na san kafi kowa son farinciki da walwala. Sai dai akwai abun dubawa a maganganun ka Mai Martaba, kamin ni kana da ƴaƴa biyu, waɗanda ko baka raye su suka fi cancanta a ɗora a sarautar nan, bayan kuma Sarkin gari, da Baba Macido ƙanenka ne da ke tunanin idan a yau baka raye, za a iya basu sarautar Katsina, babu wanda zai jidaɗi a cikinsu, idan a ɗauki Sarautar nan aka bani ko da baka raye ballantana kana da ranka kuma kai da hannunka zaka ɗauki Sarautar nan ka ba ni, a iya sanin da na yi ma Sarautar nan, zaɓe ake idan za'ayi sabon sarki, nasan mutane da yawa za su ce ka shigo da sabon tsari ka nuna son kai. Na sani idan cancanta ake dubawa, na cancanta, amman ana barin Halak dan kunya, ni Wallahi ina son aikina kuma ina ƙaunar na mutu ina yinsa”
Mai Martaba yaja wani dogon numfashi ya sauke yana gyara zama. Tabbas Abdool yayi magana mai kyau da kama hankali, hakan kuma ba ƙaramin ƙara burge Mai Martaba ya yi ba, a ƙara karantar irin basira da fikrah da ɗansa yake da ita.
“Haƙiƙa kafi kowa dacewa da Sarautar Katsina, ana son Sarki mai fikra da Nagarta, kuma an fi son Sarki da baya son Sarautar kwata-kwata a ransa. Sai dai hakan be isa yasa na cilasta maka ba, wata ƙila gaba zaka iya neman Sarautar da kan ka”
Hannayensa biyu yasa ya riƙe ƙafar Mai Martaba ɗaya da ke ƙasa.
“Na gode sosai da ka fahimce kuma ka min Uzuri, Allah ya ƙara mana lafiya da nisan kwana. Abu na biyu kuma Mai Martaba na samu matar da na ke so...”
“Namra?”
Yayi ƙasa da kansa yana jin kunya.
“Zamu aura maka duk mace da kake so Babana, ba zamu maka cilas ba, abun da kawai yake da muhimmanci kana son ta”
“Ina fatar hakan ba zai ɓata maka rai ba, kuma ina son na ji ra'ayinka akan auren bazarawa”
“Baka san Annabi S.A.W ya auri Bazawara ba, Nana Khadija ta haifi ƴaƴa ma a wani gidan sannan ta auri Annabi yana yaronsa, balle wannan da ɓata ma haihu ba, indai yarinyar ƴar kirkici mun yarda ka aureta ɗari-ɗari”
Miƙewa yayi tsaye yayi wani tsalle ya dire kamar ƙaramin yaro
“I knew it, daman na faɗawa Ummi tace wai ba zaka yarda ba, har musu take min wai she know you better than i”
Mai martaba yayi murmushi.
“No my son know me better than her”
Rumgume Mai Martaba Abdool yai cike da jin daɗi yana jin kamar ya haɗe shi.
NAMRA POV.
Daga gurin passport tace direba ya wuce da ita gidan su Lamido. Idonta tab da hawaye ta shiga cikin gidan, muryarta kamar wacce zata fasa kuka ta yi sallama. Lamido ne mutumen da ta fara ido huɗu da shi a gidan, kuma ya ƙi ya amsa mata sallamarta balle kauda idonsa daga kallon tarayyar da idanuwansu suka yi.
“Kin zo ban kwanar ne? Ai dama baki dawo ba saboda zaki ƙara saka zuciyana cikin ƙuna ne kawai”
“Don't you happy na shirya da iyayena”
“I won't lie Namra, yes i'm not happy because you are going to leave,kuma ba nine silar wannan farinciki na ki ba bayan wannan shi ne mafarki na a kullum, ina kishin mutumen da ya shirya ki da iyayenki sosai, kamar mutumen da cire min duka tufafi ya bar ni tsirara, kin san ya tozarta ni ko? Ko ba komai idan kika tuna shi zaki yi murmushi ni fa?”
Ta share hawayen da suka zubo mata.
“Namra bata zo gidanku dan ka so ta ba, saboda Namra ta gama so a rayuwarta, na yi rilaya, ɗakin so kuma sai dai wata mai sunana ta shiga amman ba ni ba, ka daina yaudarar kan ka dan Allah”
“Daman na tsammaci haka, saboda ni ba Yarima ba ne, kuma ba wan....”
Hannu ta ɗaga mishi ta tsaka mishi tsawar da tasa su Neina fito daga cikin ɗaki da gudu.
“Shi haka yayi ya yaudare ni, wani namiji ba zai ƙara burgeni ba, put this in your mind i will never ever ever ever love someone again”
Murmushi yayi yasa kai ya fice. Neina ta nufo tana tambayar abunda ya faru.
“Babu komai kawai na zo na yi muku bankwana ne anjima kaɗan zamu wuce”
“Ƙaraso ki zauna mana”
“Ba sai na ƙaraso ba, direba yana jirana a waje”
Sai kawai ta rumgume Neina ta fashe da kuka.
“Zan dawo Neina, rabuwa ba mutuwa ba ce kun min halaccin da ba zan iya mantawa ba”
Nan Neina da Uwani suka saka kuka, dan Maryam bata nan a lokacin. Kamar ba zasu rabu ba haka suka riƙa riƙe juna suna kuka kamar an yi mutuwa, har maƙota suka leƙo suna kallon ikon Allah.
Namra na komawa aka aiko musu da abincin rana, lokaci na yi direba ya zo ɗaukarsu zuwa airport, kamar su ake jira suna isa jirgi ya kama hanyar sokoto. Suna sauka Abbah yayi ma direbansa waya ya zo ya ɗauke su, kuka sosai Namra ta riƙa yi cikin motar ta daman tun a jirgi ta fara abunta, sam bata ji daɗin kalaman da ta faɗawa Lamido ba, sai dai bata da wani zaɓi sai wannan, ga kuma kukan rabuwa da Neina, da kuma kuka dawowa sokoto birnin shehu birni mai albakar da karamci tare da iyayenta komai ya zame mata kamar sabo, bama kamar ta motarsa ta nutsa kai cikin gidan duk an fence shi an sabunta komai saboda bikin Maryam da za'ayi.
Suna jin mota duk suka fito waje har Hajiya Barau da Zinatu da zo jiya suna jiran Abbah da Anty su fito. Abbah ne ya fara fita daga cikin motar sannan Namra ta fito fuskarta da hawaye. Wani irin ihu Maryam ta saka taje a guje ta rumgume Namra suka fashe da kuka, sannan Hindatu da Aisha suka je suka rumgume ta, suma suka saka kuka, Hajiya Barau ce Mamaki ya hanata komai har Abbah da wuce da Anty Amarya sannan ta nufi Namra kunya kunya.
“Wai Namra ce nake gani nan ni mamaki ma ya hanani komai”
“Itace Hajiya, Abbah yaje ya taho da abar sa”
Cewar Maryam tana sharewa Namra hawaye. Sannan suka riƙa hannunta suka nufi cikin gida da ita.
YASMIN POV.
Lokacin da ta bar gidan mijita sai ta nufo gida, sai dai bata yarda ta nunawa mahaifiyarta damuwarta ba, gudun kar ta hana ta aikata abunda take da niyar yi, wuni ta yi a gidan suka sha fira kamar ba komai sai dare ta fito suka koma gida ita da yaranta da kuma mai aikinta. Bata tarar da Uzair cikin gidan ba hakan yasa ta ɗan ji sanyi dan bata ƙaunar ganinsa a yanzu. Abunda kawai take da buƙata ya za'ayi ta haɗu da Namta akwai buƙatar ta tattauna da ita kamin ta fallasa Uzair, ma'ana ta jawa Namra haƙƙinta ko zata samu sanyin zuciya akan abunda ya aikatawa ɗan sa. Haka ta kwana tana tunanin mafita washe gari ma kasa zuwa aiki ta yi duk da tana da cases a kotu, da an kira ta sai tace bata da lafiya ne. Uzair kuma be kwana a gidan ba, da alama akwai gun da ya kwana, sai dai hakan be dame ta ba ko kaɗan tun da tasan wanene shi a yanzu. Bayan ta gama waya da wani Barrister, sai ga kiran Mahaifiyarta ya shigo wayarta.
Bayan sun gaisa take labarta mata ance Namra ta dawo, kuma wai Abbah ne yaje ya taho ta ita, Yasmin ta nuna murnarta sosai daman abun nema ya samu. Dan haka tana kashe wayar ta aje little Namra ta shiga wanka, tana fitowa ta yi ma mata sannan suka shirya daman Adnan yana makaranta. Ƴar aikinta kawai ta bari a gidan ta nufi gidansu Namra.
Tana fita Uzair na shigowa, ciki wani irin yanayi ya buga ƙofar falon, sai mai aikinsa ta buɗe masa ƙofa.
“Sannu da zuwa”
Wani wawan kallo ya jefa mata, ya wuce ciki, ita kuma ta koma kitchen ta cigaba da abun da take.
TEEMA POV.
Yau da wuri ta gama girkinta saboda yau da fara amfani da abubuwan da ta karɓo gurin bokanta. Zoɓo ta haɗa masa ta zuba abun a ciki sannan ta saka wani a miyar giɗa, kana ta bi gidan ta turare ko'ina.
Sai da ta gama sannan ta shiga ta sake wanka, ta chaɓa ado, ta buɗe durowarta ta ɗauko wani rubutu ta zuba a hannunta ta yaye zanen gadonta ta watsa shi, sannan ta shafa wani a ɗayan hannunta, tana jiran ya dawo ta samu sa'ar shafa masa a jiki.
Tana jin tsayawar motarsa ta koma bayan ƙofa ta laɓe, a zatonta shine zai shigo ashe direba ya aiko ya kawo su Ezza da Ulfa. Sai duk suka watsar da jakunkunansu saman kujerarta. Ganin shiru-shiru ba a shigo ba yasa ta fito ta nufo falo.
“Kan Uban nan, uban wa zaku jefarwa da jaka nan? Ku kwashe su da sauri ku kai su ɗakin ku, kuma kar a sake zama min saman kujera, wannan ai rashin tarbiya ne manya su zauna a kujera ku ku zauna ni ba zan ɗauki wannan ba”
Ulfa ce uwar tsoro da sauri ta nufi jakarta ta ɗauka ta nufi ɗakinsu. Ezzah kan banza ta yi kuma ta ƙi sauka daga saman kujerar.
“Ke dan Ubanki ba da nake ba”
Sai a sannan ta ɗago kai ta kalleta.
“Mu a saman kujera muka saba zama”
Ta faɗa tana sauka ƙasa, badan hannun Teema da ke da rubutun ba da babu abunda zai hana ta dake ta.
“Wallahi kuka kuskura min rashin kunya zaki wahala a gidan nan”
Sai kawai ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinsu, Ulfah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin tana leƙo ta shige da sauri.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *78*
Kusa da Ummi ya sake zama yana kallon tv.
“Tana son ta saka kanta cikin matsala ne kawai Ummi amman tasan ba zan taɓa son ta ba”
“Nasan tana son ka har zuciyarta, amman sam ban yarda da yarinyar nan ba, mutanen da sukayi ƙoƙarin su kashe ka, waya sani ko plan ne aka yi ta yadda idan ta aure ka zata fin jindaɗin kashe ka”
Yayi murmushin gefen baki.
“Ko babu plan Ummi bana son ta, ko da kuwa tun can farko ita mai tarbiya ce, because if i love someone i mean it no matter what she did or whoever she is, and if i said i do i do, so i don't love Amira, i only fell in love once because i have never been in that kind of situation, but when it comes to Namra i take it so serious, and i love with all my heart and blood and mind and soul i love her more than you think Ummi”
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke, ta kalli ɗanta fuskarta da alamun damuwa.
“Tell me more about her”
Miƙewa ya yi tsaye ya nufi freezer.
“She's so simple and kind, but difficult to handle. You know when we first meet, she slap me and insult me in front of my boys, but i can't slap her back”
Ya ƙarasa yana bulbula ruwan da ya fiddo a cup. Ummi ta yi murmushi.
“I know how my son is ba ya faɗa da mata”
“Yap bana faɗa da mata because we are not in the same level, strength, brain, heart, soul and lot. Ban taɓa jin ina son wata mace ba, but lokacin da na ji ina son Namra, nasan our souls mean to be, duk da a lokacin na san tana da aure, amman zuciya ta kasa haƙura, and now what! Her husband divorce her ta je wani gida ta zauna, kuma ƙaddara ta sake haɗa mu kaduna na kaɗe yaron gidan ina zuwa sai gata a gidan, hmm' mmm funny, and now ni ne silar shiryawa da iyayenta, i hope you love her too?”
“Of course i love her ai dole naso matar da ɗa na yake so, but i'm just worried about Mai Martba, ba lalle ne shi ya so ta”
“Why”
“Saboda Bazawara ce! And i hear that Mai Martaba and Hajiya Shafa sun maka mata”
“What...!”
Ya aje cup ɗin ruwa dake hannunsa saman dinning yana kallonta fuskarsa cike da tashin hankali.
“How true it's?”
“Mai Martaba ya kira ni da kan shi, yana neman shawara akan zai ɗoraka a Sarautar Katsina, da na nuna masa be dace ba sai ya nuna ɓacin ransa, the following day ya sake kira a waya ya faɗa min Hajiya Shafa tace be kamata a ɗoraka a Saurata baka tare da iyalaiba, dan haka ta maka mata, zata aura maka Zaliha ƙanwarta, idan anyi auren da watanni sai a baka Sarautar, kuma Mai Martaba yayi na'am da hakan”
“Miyasa baki faɗa musu ina da wacce nake so ba?”
“Idan na faɗa zai ga kamar ina kare ka ne, amman ina son ka min wani abu Abdallah, duk yadda Mai Martaba zai yi karka yarda ka karɓi Sarautar nan, kai ne ɗa na uku a gurin shi, be kamata ya tsallake su ba, ya ɗauki Sarauta ya baka, nasan yana son ka, amman hakan ba zai jawo maka komai ba sai ƙiyayya da ganin laifi, kai kuma ka yi ƙanƙanta da irin rayuwar nan, kuma idan har ka yarda ka auri Zaliha, to ka jefa rayuwarka da ta mu cikin matsala, tun da ƙanwar Hajiya Shafa ce, kuma kasan wacece Hajiya Shafa a gareni da gare ka. Ka da ka amince da duka biyu idan har ya yi maka magana”
“Ai ba zan amince ba, ina son aiki na kuma ina alfahari da shi, ni ba Sarauta ba ce a gabana, kuma Namra ce kaɗai matar da nake so”
“And be careful with her love too, kar ya rufe maka ido ka saɓawa Mahaifin ka”
“My Dad is...”
Ummi ta miƙe tsaye tana tarar numfashinsa.
“I know who your Dad is, he's my ex-husband the Father of my own male son”
Ta nufi bedroom ɗinta. Shi kuma ya faɗa zaune saman kujerar dinning yana bugashi da ƙarfi.
“Damn it! miyasa abubuwa zasu zo min haka kuma yanzu? Shine surprise ɗin da Mai Martaba yake ta faɗi? Ya Salam...!”
Ya miƙe tsaye, sai ya nufi kitchen duk da ya san babu abunda zai ɗauka a gurin. He need some fresh air, sai ya buɗe ƙofar baya ya fita, jin ya gaba ɗaya gidan ya masa wani irin, kai tsaye ya nufi Garden, ko ba komai yana son kukan tsuntsaye maybe zai sashi relaxing ya sama ma kan shi mafita.
Gaban icen guava ya zo ya tsaya yana kallon pool, motsin mutum ya ji a bayansa, yasan cikin biyu ba za'a rasa ɗaya ba, Maybe Amira ce tun da ita kaɗai take gidan ko kuma barewa, dan tana masa haka a duk lokacin da ya shigo Garden ɗin. Juyowa yayi sai yayi ido huɗu da Amira fuskarta shakaf da hawaye.
“What do you want?”
“You told me if i need someone to talk to”
“It Abdool who told you that, and now i'm someone else, and my words could hurt you, i'm not in the mood”
Cikin muryar kuka ta ce.
“You already hurt me because i learn the truth, i know you upset because of what Ummi told you, we share the same pain, i'm in love with you while you're in love with someone else”
Ta share hawayenta da haɓar rigarta.
“Maybe i will have peace of mind if you tell me that you never love me, maybe i will back to my senses, think about my future and....”
Kuka ya ci ƙarfinta. Taku biyu yayi ya matso kusa da ita.
“Do you know what is best for you, ki koma gida cikin iyayenki, ki manta da ni a rayuwarki, and i promise you zan rufa miki asiri ba zan faɗawa kowa abunda kika aikata ba”
“Zan koma gurin iyayena, nima a yanzu babu abunda na ke so sai su, but forgetting you is the hardest thing ever, thank you so for letting me staying with your family and know you better, can you take me home now please, am eager to see my parents”
“Yeah... Zan ma direba magana, ki shirya kayan ki”
“Ban zo da komai ba a nan”
Har ta juya sai kuma ta juyo.
“Ina matar da kake so take?”
“Why?”
“Saboda ta fi kowa sa'ah a duniya, ina son na ganta ne kawai”
“I can't tell you Amira, i'm sorry to say this, i don't trust you”
“I know i shouldn't...”
Ta juya ta shiga ciki da kuka. Da kallo ya bita sai da ta fice sannan ya haka hannunsa aljihu ya ciro handkerchief yana shinshinawa.
“I loved you so much”
Ya ɗauki tsawo lokaci a gurin sannan ya nufi part ɗinsa. Be daɗe ba ya fito da takarda hannunsa ya kira ɗaya daga cikin direban gidan ya miƙa masa.
“Zaka kai Amira a wannan addireshin, karka yarda ka sauketa ko ina sai nan”
“Toh Ranka ya daɗe”
Ya nufi part ɗin Ummi. Su biyu ya samu a falon Amira ta yi kneel down tana riƙe da hannun Ummi tana kuka, Ummi kuma na hawaye.
“Ki min hallaci Ummi kin riƙe ni kamar ƴar cikin ki, baki taɓa nuna min banbanci da ƴaran ki ba, na yi fatar wata rana zata zo da zan saka miki abunda kika min, Na gode da karamcin ina fatar zaki yafe min duk abunda na miki”
“Ba ki min komai ba Amira sai alheri, Allah ya miki albarka”
Kuka ta yi sosai sannan ta saki Ummi ta nufi ƙofar fita kamar zata faɗi. Kai Ummi ta girgiza ta kalli Abdool ta ce
“Is not fair ya kamata ace mu muka kai ta gida”
Ya ɗago daga jikin ƙofar da yake jingine ya nufo Ummi
“No hakan zai fi mata, dole ta tanadi abunda zata faɗawa iyayenta, idan suka gan mu kawo ta za suyi zaton ko ina son ta ne, kuma dole zasu tambayi inda na haɗu da ita, ni ko kin san gaskiya zan faɗa musu, beside irin waɗannan mutane ba a yawo da su it risk baki san abunda suka tana da ba”
Kai ta kaɗa masa cike da gamsuwar bayanin da yayi mata. Sannan ya juya suka fita tare gurin mota suke je suka tsaya, ita kuma tana daga ciki sai faman kuka take. Hannu Abdool yasa a aljihu ya ciro takardar kuɗi ya miƙa mata.
“Maybe you will need this”
“No i don't”
Ta kawar da fuskarta tare da cewa direba su tafi. Daga Ummi har Abdool tsaye suka yi suna kallonta har aka buɗe musu gate ɗin farko, bayan sun fice aka rufe gate ɗin sannan suka daina hango motar ta.
“Ina jin kamar ba mu kyauta mata ba, kuma bata jidaɗi ba ta ƙi ya tsaya har su Fauza su dawo”
“Zamu iya mata alheri daga baya idan mun fahimci da gaske ta shiryu, ai ƙara haka idan suna nan ai zasu ta kuka suma”
“Allah yasa ta shiryun, but wata rana zamu yi visiting na ta”
Ya miƙa hannunsa yana miƙa.
“Bari na shirya na koma gurin Mai Martaba”
“Okay”
Ummi ta juya. Shi kuma ya nufi part ɗinsa. Cikin rashin jundaɗi ya nufi part ɗinsa, dan bana jin kamar be kyautawa Amira, but he has no choice but to let her go. Cikin mintuna shirin ya watsa ruwa ya shirya cikin manyan kaya dan cox he know how Mai Martaba hate ƙananan kaya, yana fitowa part ɗinsa sai ƙamshin turare ke tashi. In five minutes ya isa kan wuri. He got lucky Mai Martaba be je ko'ina ba, duk da yana da niyar fita yau, sai dai ya tararda fadar cike saboda baƙin da suka zo daga jibiya. Yana shiga suka fara miƙa masa gaisuwa da kirari, hannu kawai ya ɗaga musu ya juya ya fita.
Barori ya samu a babban falon Mai Martaba suna hidimar chanja carpet, da sauri suka zubar da abunda ke hannunsa suka zube ƙasa suna masa gaisuwa. Kamar wanda be gansu ba, haka yayi ya nufi ɗayan falon nasa, zama yayi saman kujera yana duba jaridu, can kuma ya ji gurin is so boring ya miƙe ya nufi can ɓangaren Mai Martaba inda babu wanda ya ke shiga sai iyalansa.
Saman wata kujera ya zauna mai lilo yana kallon pop ɗakin. Zuwa can ya fara jin bachi, daman a gajiye yake. Shigowar Mai Martaba ne yasa shi saurin sauke ƙafafunsa ya tashi zaune.
“Allah ya taimaki Mai Martaba ya ƙara maka lafiya”
Zaunawa yyi da murmushi a fuskarsa.
“Yarima Abdallah, kuma sarkin mu na gobe”
Yayi dariya.
“A dai bar ni a Yariman, har yanzu bana mafarkin zama Sarki”
“Aiko ƙara ja shirya, damin very soon zaka zama Sarki, kasan har yanzu ban faɗa maka albishir ɗin ka ba ko?”
“Shiyasa ma ka ga na zo yanzu”
Mai Martab ya ɗora ƙafa saman ɗaya yana kallon Abdool cike da natsuwa.
“Wato Albishir ɗin ka guda biyu ne, kuma dukaninsu suna da muhimmanci, kuma ina fatar zaka karɓa ka yi na'am da dukansu. Na farƙo dai ina maka albishir da cewar Hajiya Shafa ta baka Zalihatu kyauta, abu na biyu kuma mun yanke shawarar naɗa ka sabon Sarkin Katsina...”
Wani irin kallo yayi ma Mai Martaba kamar Ummi bata faɗa masa komai ba, sai ya sauka ƙasa yana nuna kansa.
“Mai Martaba ni?”
“Kai fa”
Ya faɗa da murmushi a fuskarsa.
“Ka fi kowa karantar waye ni Mai Martaba, ka fi kowa sanin abunda ya dace da ni, ba zaka taɓa zaɓa min sheri ba, kuma na san kafi kowa son farinciki da walwala. Sai dai akwai abun dubawa a maganganun ka Mai Martaba, kamin ni kana da ƴaƴa biyu, waɗanda ko baka raye su suka fi cancanta a ɗora a sarautar nan, bayan kuma Sarkin gari, da Baba Macido ƙanenka ne da ke tunanin idan a yau baka raye, za a iya basu sarautar Katsina, babu wanda zai jidaɗi a cikinsu, idan a ɗauki Sarautar nan aka bani ko da baka raye ballantana kana da ranka kuma kai da hannunka zaka ɗauki Sarautar nan ka ba ni, a iya sanin da na yi ma Sarautar nan, zaɓe ake idan za'ayi sabon sarki, nasan mutane da yawa za su ce ka shigo da sabon tsari ka nuna son kai. Na sani idan cancanta ake dubawa, na cancanta, amman ana barin Halak dan kunya, ni Wallahi ina son aikina kuma ina ƙaunar na mutu ina yinsa”
Mai Martaba yaja wani dogon numfashi ya sauke yana gyara zama. Tabbas Abdool yayi magana mai kyau da kama hankali, hakan kuma ba ƙaramin ƙara burge Mai Martaba ya yi ba, a ƙara karantar irin basira da fikrah da ɗansa yake da ita.
“Haƙiƙa kafi kowa dacewa da Sarautar Katsina, ana son Sarki mai fikra da Nagarta, kuma an fi son Sarki da baya son Sarautar kwata-kwata a ransa. Sai dai hakan be isa yasa na cilasta maka ba, wata ƙila gaba zaka iya neman Sarautar da kan ka”
Hannayensa biyu yasa ya riƙe ƙafar Mai Martaba ɗaya da ke ƙasa.
“Na gode sosai da ka fahimce kuma ka min Uzuri, Allah ya ƙara mana lafiya da nisan kwana. Abu na biyu kuma Mai Martaba na samu matar da na ke so...”
“Namra?”
Yayi ƙasa da kansa yana jin kunya.
“Zamu aura maka duk mace da kake so Babana, ba zamu maka cilas ba, abun da kawai yake da muhimmanci kana son ta”
“Ina fatar hakan ba zai ɓata maka rai ba, kuma ina son na ji ra'ayinka akan auren bazarawa”
“Baka san Annabi S.A.W ya auri Bazawara ba, Nana Khadija ta haifi ƴaƴa ma a wani gidan sannan ta auri Annabi yana yaronsa, balle wannan da ɓata ma haihu ba, indai yarinyar ƴar kirkici mun yarda ka aureta ɗari-ɗari”
Miƙewa yayi tsaye yayi wani tsalle ya dire kamar ƙaramin yaro
“I knew it, daman na faɗawa Ummi tace wai ba zaka yarda ba, har musu take min wai she know you better than i”
Mai martaba yayi murmushi.
“No my son know me better than her”
Rumgume Mai Martaba Abdool yai cike da jin daɗi yana jin kamar ya haɗe shi.
NAMRA POV.
Daga gurin passport tace direba ya wuce da ita gidan su Lamido. Idonta tab da hawaye ta shiga cikin gidan, muryarta kamar wacce zata fasa kuka ta yi sallama. Lamido ne mutumen da ta fara ido huɗu da shi a gidan, kuma ya ƙi ya amsa mata sallamarta balle kauda idonsa daga kallon tarayyar da idanuwansu suka yi.
“Kin zo ban kwanar ne? Ai dama baki dawo ba saboda zaki ƙara saka zuciyana cikin ƙuna ne kawai”
“Don't you happy na shirya da iyayena”
“I won't lie Namra, yes i'm not happy because you are going to leave,kuma ba nine silar wannan farinciki na ki ba bayan wannan shi ne mafarki na a kullum, ina kishin mutumen da ya shirya ki da iyayenki sosai, kamar mutumen da cire min duka tufafi ya bar ni tsirara, kin san ya tozarta ni ko? Ko ba komai idan kika tuna shi zaki yi murmushi ni fa?”
Ta share hawayen da suka zubo mata.
“Namra bata zo gidanku dan ka so ta ba, saboda Namra ta gama so a rayuwarta, na yi rilaya, ɗakin so kuma sai dai wata mai sunana ta shiga amman ba ni ba, ka daina yaudarar kan ka dan Allah”
“Daman na tsammaci haka, saboda ni ba Yarima ba ne, kuma ba wan....”
Hannu ta ɗaga mishi ta tsaka mishi tsawar da tasa su Neina fito daga cikin ɗaki da gudu.
“Shi haka yayi ya yaudare ni, wani namiji ba zai ƙara burgeni ba, put this in your mind i will never ever ever ever love someone again”
Murmushi yayi yasa kai ya fice. Neina ta nufo tana tambayar abunda ya faru.
“Babu komai kawai na zo na yi muku bankwana ne anjima kaɗan zamu wuce”
“Ƙaraso ki zauna mana”
“Ba sai na ƙaraso ba, direba yana jirana a waje”
Sai kawai ta rumgume Neina ta fashe da kuka.
“Zan dawo Neina, rabuwa ba mutuwa ba ce kun min halaccin da ba zan iya mantawa ba”
Nan Neina da Uwani suka saka kuka, dan Maryam bata nan a lokacin. Kamar ba zasu rabu ba haka suka riƙa riƙe juna suna kuka kamar an yi mutuwa, har maƙota suka leƙo suna kallon ikon Allah.
Namra na komawa aka aiko musu da abincin rana, lokaci na yi direba ya zo ɗaukarsu zuwa airport, kamar su ake jira suna isa jirgi ya kama hanyar sokoto. Suna sauka Abbah yayi ma direbansa waya ya zo ya ɗauke su, kuka sosai Namra ta riƙa yi cikin motar ta daman tun a jirgi ta fara abunta, sam bata ji daɗin kalaman da ta faɗawa Lamido ba, sai dai bata da wani zaɓi sai wannan, ga kuma kukan rabuwa da Neina, da kuma kuka dawowa sokoto birnin shehu birni mai albakar da karamci tare da iyayenta komai ya zame mata kamar sabo, bama kamar ta motarsa ta nutsa kai cikin gidan duk an fence shi an sabunta komai saboda bikin Maryam da za'ayi.
Suna jin mota duk suka fito waje har Hajiya Barau da Zinatu da zo jiya suna jiran Abbah da Anty su fito. Abbah ne ya fara fita daga cikin motar sannan Namra ta fito fuskarta da hawaye. Wani irin ihu Maryam ta saka taje a guje ta rumgume Namra suka fashe da kuka, sannan Hindatu da Aisha suka je suka rumgume ta, suma suka saka kuka, Hajiya Barau ce Mamaki ya hanata komai har Abbah da wuce da Anty Amarya sannan ta nufi Namra kunya kunya.
“Wai Namra ce nake gani nan ni mamaki ma ya hanani komai”
“Itace Hajiya, Abbah yaje ya taho da abar sa”
Cewar Maryam tana sharewa Namra hawaye. Sannan suka riƙa hannunta suka nufi cikin gida da ita.
YASMIN POV.
Lokacin da ta bar gidan mijita sai ta nufo gida, sai dai bata yarda ta nunawa mahaifiyarta damuwarta ba, gudun kar ta hana ta aikata abunda take da niyar yi, wuni ta yi a gidan suka sha fira kamar ba komai sai dare ta fito suka koma gida ita da yaranta da kuma mai aikinta. Bata tarar da Uzair cikin gidan ba hakan yasa ta ɗan ji sanyi dan bata ƙaunar ganinsa a yanzu. Abunda kawai take da buƙata ya za'ayi ta haɗu da Namta akwai buƙatar ta tattauna da ita kamin ta fallasa Uzair, ma'ana ta jawa Namra haƙƙinta ko zata samu sanyin zuciya akan abunda ya aikatawa ɗan sa. Haka ta kwana tana tunanin mafita washe gari ma kasa zuwa aiki ta yi duk da tana da cases a kotu, da an kira ta sai tace bata da lafiya ne. Uzair kuma be kwana a gidan ba, da alama akwai gun da ya kwana, sai dai hakan be dame ta ba ko kaɗan tun da tasan wanene shi a yanzu. Bayan ta gama waya da wani Barrister, sai ga kiran Mahaifiyarta ya shigo wayarta.
Bayan sun gaisa take labarta mata ance Namra ta dawo, kuma wai Abbah ne yaje ya taho ta ita, Yasmin ta nuna murnarta sosai daman abun nema ya samu. Dan haka tana kashe wayar ta aje little Namra ta shiga wanka, tana fitowa ta yi ma mata sannan suka shirya daman Adnan yana makaranta. Ƴar aikinta kawai ta bari a gidan ta nufi gidansu Namra.
Tana fita Uzair na shigowa, ciki wani irin yanayi ya buga ƙofar falon, sai mai aikinsa ta buɗe masa ƙofa.
“Sannu da zuwa”
Wani wawan kallo ya jefa mata, ya wuce ciki, ita kuma ta koma kitchen ta cigaba da abun da take.
TEEMA POV.
Yau da wuri ta gama girkinta saboda yau da fara amfani da abubuwan da ta karɓo gurin bokanta. Zoɓo ta haɗa masa ta zuba abun a ciki sannan ta saka wani a miyar giɗa, kana ta bi gidan ta turare ko'ina.
Sai da ta gama sannan ta shiga ta sake wanka, ta chaɓa ado, ta buɗe durowarta ta ɗauko wani rubutu ta zuba a hannunta ta yaye zanen gadonta ta watsa shi, sannan ta shafa wani a ɗayan hannunta, tana jiran ya dawo ta samu sa'ar shafa masa a jiki.
Tana jin tsayawar motarsa ta koma bayan ƙofa ta laɓe, a zatonta shine zai shigo ashe direba ya aiko ya kawo su Ezza da Ulfa. Sai duk suka watsar da jakunkunansu saman kujerarta. Ganin shiru-shiru ba a shigo ba yasa ta fito ta nufo falo.
“Kan Uban nan, uban wa zaku jefarwa da jaka nan? Ku kwashe su da sauri ku kai su ɗakin ku, kuma kar a sake zama min saman kujera, wannan ai rashin tarbiya ne manya su zauna a kujera ku ku zauna ni ba zan ɗauki wannan ba”
Ulfa ce uwar tsoro da sauri ta nufi jakarta ta ɗauka ta nufi ɗakinsu. Ezzah kan banza ta yi kuma ta ƙi sauka daga saman kujerar.
“Ke dan Ubanki ba da nake ba”
Sai a sannan ta ɗago kai ta kalleta.
“Mu a saman kujera muka saba zama”
Ta faɗa tana sauka ƙasa, badan hannun Teema da ke da rubutun ba da babu abunda zai hana ta dake ta.
“Wallahi kuka kuskura min rashin kunya zaki wahala a gidan nan”
Sai kawai ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinsu, Ulfah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin tana leƙo ta shige da sauri.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *79*
Su Maryam na wucewa Zinatu ta rufa musu baya ita ma tana murmushi. Hajiya Barau kuma ta koma part ɗinta, bedroom ɗinta ta shige ta ɗauki wayarta ta kira Uzair. Bugu biyu ya ɗauka, saman-sama ya gaisa da ita saboda shi ma be cikin daɗin rai, sannan ta labarta masa Namra ta dawo, he was shocked and surprise, sai ya ji maganar kamar daga sama.
“Da gaske kike yi?”
“Wallahi da ido na na gani, yanzun nan Alhaji ya dawo tare da ita, kasan na labarta maka ai Sarkin Katsina ya aiko ƴana nemansa ni na ɗauka ko wani abu ta yi, sai gashi kuma na ga sun dawo da ita”
“Aurenta ya mutu ne?”
“Bari naje gurin Alhaji na ji”
“Okay ki sanar da ni duk abunda kika ji”
“Tau”
Tana kashe wayar ta nufi part ɗin Abbah. Ko da ta shiga yana banɗaki, har ta zauna sai kuma ta yi saurin tashi ta koma part ɗinta, fruit ta yankawa Abbah ta saka madara, ta ɗauka ta nufi koma part ɗinsa. Wannan karon zaune ya same shi saman gado yana waya, sai ta zauna kusa da shi tana riƙe da fruits, sai da ya gama wayar sannan ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace.
“Hajiya fatar dai lafiya”
“Lafiya ƙalau bana da ikon da zan zo na ga miji na ne? Ga ɗan abunda na haɗa maka, abinci na kan wuta ban ƙarasa ba”
“Ai bama na ma jin yunwa kamin na taso sai da muka ci abinci”
“A can gidan Namra?”
“A'a a gidan Mai Martaba Ahmad Mai-doki Sarkin Katsina, dake Kaduna”
“Ban gane ba, baka labarta min zaka dawo da Namra ba, duk lokacin da na tambaye ka sai ka ce min wani babu wata matsala dai, ya akayi ka dawo da ita bayan kace ba zaka karɓe ta ba?”
Wani kallo Abbah yayi mata.
“Ya kike magana kamar wacece bata ji daɗin dawowar Namra ba? Komai ta yi min aduniyar nan she still my daughter, ko lalacewa ta yi dole za'ace ƴar gidan nan ce, ballantana ina son ta, kawai dai ta ɓata min rai ne kuma ta gane kuskurenta”
“Ta gane kuskurenta kamar ya? Alhaji yanzu baka tunanin mutane zasu zarge ka akan ka yi magana kuma ka zauna? Wannan ai talalace ka yi mata yarinya ta yi laifi kuma yanzu da miji ya wulaƙanta sai kace kayafe mata haka ake yi?”
Abbah yayi murmushi, yana gyara zamansa.
“Baki gane abun ba ne Hajiya wato da muka sauka Katsina...”
Ya kwashe labarin abunda ya faru ya faɗa mata, daman can Anty Amarya ce ta hana a faɗawa kowa wai tana son kawai su ganta ne. Mire baki Hajiya Barau ta yi ta miƙe tsaye.
“Yanzu Alhaji im ban da su mai da wani iri sai da Asim ya gama wulaƙanta ta ya sake ta sannan yanzu su haɗa baki da uwarta su nemo wani a kai ga Sarki, wannan ma ai rainin wayo ne, yarinyar ta yi wasa da hankalinka, yanzu kuma kai har ka yarda ta gane kuskurenta haba Alhaji wannan ai ka bata damar ƙara aikata abunda ta aikata ne kawai”
Wani wawan kallo Abbah ya watsa mata.
“Na bata damar, ko yanzu Namra ta kawo min wanda take so zan aura mata, daman na lura da ke ba son yarinyar nan kike ba, mi ko duk wanda be son Namra bana son shi, dan Namra jinina ce, ƴata ce, ina kula da yadda kika ɗauki matar nan ita ba haka ta ɗauke ki ba, baki son ta ita da yaran ta, ana gobe za mu bar garin nan nan cikin falon nan nawa kika saki wata magana wai Allah yasa Namra bata yi mana jaye-jaye ba, a gaban uwarta amman ta miki kawaici ta tashi ta bar miki falon bata ce komai ba, shiyasa na zaɓi zuwa da ita na ƙi na tafi da ke, iya haƙuri matar nan ta nayi yinsa da ke amman ke baki ga, ina kula da abun nan da Namra ta yi kamar daɗi yayi miki, ba zan ɗauka ba kar bakin ki ya sake furta mummun kalma akan ƴaƴana!”
Ta riƙe baki.
“Alhaji kai kake faɗa min wannan maganar akan Namra? Daga na faɗa maka gaskiya har kace wai bana son ta ita da uwarta? Kuma ka ce baka da so na saboda ƴarka? Anya banza matar nan ta barka Alhaji”
“Ba banza ta bar ni ba, ta kula da ni fiye da yadda kike tsammani, dan tana son ki ke da ƴaƴanki, ba kamar yadda kike nuna mata ba, kuma daga yau sai yau, kar wani munafurci da wata magana marar daɗi ta sake fitowa bakinki akan Ƴaƴa ko wannan matar tau a bakin auren ki! Kar wacce ta aake tadarmin fitina yadda na ga dama haka zan yi a gidana”
Mutuwar tsaye Hajiya Barau ta yi a gurin, tana mamakin Abbah ta ya juye kamar ba shi ba, wai yau shi yake faɗa mata wannan maganar, har yake cewa bakin aurenta. Uffan bata yarda ta sake cewa ba, ta nufi ƙofa cike da nauyin jiki fice sun-sun-sun, hannayenta a baya tana jin kamar an ɗora mata dutse saman kai.
NAMRA POV.
Cikin falo suka riƙa hugging ɗin juna ita da ƴan'uwanta, suna jin kamar su haɗe juna ita da su, sai faman kuka suke. Anty Amarya ta fito daga bedroom ɗinta fuskarta da dariya ta ce
“To ko haɗe ta zaku yi?”
“Anty Faɗa mana yadda aka yi ta yarda ta biyo ku kuma har Abbah ya amince”
Aisha ta faɗa tana laƙƙame da wuyan Namra.
“To ku sake ta taje ta yi wanka ta shirya zan baku labarin komai”
Aisha da Hindatu ne suka saketa yayinda Maryam ta laƙƙame hannunta suka nufi bedroom tare. Bayan sun tashi Zinatu ma ta tashi ta nufi part ɗin Mahaifiyarta. A sannan ne Anty take tambayarsu yaushe Zinatu ta zo.
“Tun ranar da kuka tafi, wai faɗa tayi da mijinta ya ce taje gida, shi ne wai ta baro masa yaransa”
“Subhallahi, miya haɗa su haka?”
“Wallahi bata faɗa ba, ai kin san Hajiya ba zata bari ta faɗi gaskiya ba, dan ita Hajiya ma ce mana ta yi bikin Maryam ta zo”
“Tau Allah ya sauwaƙe yayi mata mafita, ku tashi ku girka mana abinci dan ni dai ba zan ci taliya ba”
Hindatu ta mike tsaye tana dariya.
“Komai kuke so za a muku, sai ku ba mu labarin abunda ya faru”
A ɗaki da suka shiga Namra take labartawa Maryam irin abunda Asim yayi mata, da yadda ta yi rayuwa gidansu Lamido da kuma haɗuwarta da Abdool ya yadda ya haɗa ta da su Anty.
“Ke ni wallahi na jidaɗin da auren ya mutu kuma cikin ya zube, dan zai iya cewa ya maida ki ko dan ɗansa ko kuma ya ce zai maida ki kamin ki cika idda amman yanzu ba ciki ba goyo dole ya ƙyale ki dan ubansa, tsinan nen banza”
“Ba laifinsa ba ne Maryam, laifina ne a gareni ya ga wannan damar kuma ni na zaɓe shi sama da iyayena. Amman yanzu Alhamdulillahi tun da Abbah ya ƙarɓe ni”
“Gaskiya nima na jidadin hakan ciwon Anty zai warke, kuma za'ayi biki da ke, amman dai wannan yaron son ki yake ko?”
“A'a ba so a tsakanin mu, bikin wa za'ayi?”
“Bikina mana ni da Hindatu sati mai zuwa za'a ɗaura aure, Wednesday za'a fara biki”
“Amman shinw ba a faɗa min ba?”
“To ba kin zaɓi wasu family sama da mu ba”
“Haba Maryam, ai komai na zama ni ƴar'uwarku ce jininku, be kamata ku min haka ba”
Maryam ta laƙƙamo kafaɗarta tana dariya.
“Ai yanzu kin dawo ma hanya, komai da ke za'ayi Maman su Babanmu”
Ɗan Murmushi Namra ta yi ta miƙe ta shiga wanka. A wunin ranar haka suka riƙa treat ɗin Namra kamar wata sarauniya, sai faman dare-dare suke suna rumgume ta. Suna cikin haka sai kawai ta fashe musu da kuka da kuma dariya lokaci ɗaya.
“Ban taɓa tunanin rayuwa zata dawo haka ba, i miss my family a lot”
Hannu Aisha tasa ta share mata hawayenta, sannan ta miƙa mata wayarta da ke ringing.
Namra na karɓa ta zaro ido.
“Asim ne”
“Asim”
Maryam ta amsa da ƙarfi, kana ta ce.
“Ba ni shi”
Anty ta ɗaga mata hannu
“No barta ta yi picking mu ji me zai ce”
Sai da ta yi ajiyar zuciya sannan ta danna picking ta kara a kunne.
“Hajiya Namra kenan! Ina kika shiga na yi nemanki cikin garin Katsina da kewaye baki ciki”
“Ina kake tsammanin zan kasance bayan gidan Ubana”
“bakya giɗan ubanki kam dan na bincika aka ce min baki can, faɗa min inda kike je? Karki damu da tambayar da nake miki ina son naji lafiyar Baby na ne”
“Bka da wani Baby Asim saboda ka zaɓi rabuwa da ni ne saboda shi”
“Yanzu kuma ina son abuna sai yaya?”
“Amman babu kaskantacce wulaƙantacce wawa kamar ka Asim, yanzu da baka da kunya zaka kira ni ka ce min wai lafiyar cikin ka zaka ji?”
“Bana da damar hakan ne? Ai Allah ya ɗora min haƙƙin kula da ke har sai kin haihu, kuma dole ne na bincika ko da kina da buƙatar wani abun sai a kawo miki”
“Kai har kana ganin ka yi arzikin da zaka iya ɗaukar nauyin cikin ka, ka daina wahalar da kan ka dan ni yanzu babu ciki a jikina kuma karka sake kirana”
Tana kaiwa nan ta kashe wayarta tana huci. Anty bata muƙatar ta faɗa mata dalilin kiran nasa dan ta fahimci komai. Ko minti biyu ba tayi ba ya aiko mata sako.
_Wallahi duk kika zubar min da ciki sai mun shiga kotu da ke_
Namra na gama karanta ta nunawa Anty.
“Karki sake ɗaga wayarsa karki sake ce masa komai, har sai mun ji abunda Abbah ki zai ce”
Maryam ta yi ƙwafa.
“Wallahi samun family masu haƙuri irin wannan yana da wahala, wlh da wani guri ne da sai an wulaƙanshi kam uban nan...!”
Anty ta nuna ta yatsa.
“Maryam ki cire wannan zafin ran da kike da shi, aure zaki yi kuma mace kike, abunda duk haƙuri be baka ba rashinka be baka shi, duk wanda ya ci amana kin taɓa ganin ya ƙare da kyau, kar dai karka yarda ka ci amanar wani barshi shi ya ci amanar ka, ki zuba masa ido ki gani ba zai ga da kyau ba”
“Amman wani lokacin mutun yana buƙatar gargaɗi kai, da wannan haƙuri kike ta cutar da mu da kan ki, gashi nan a gida kullum mine ba mu da gata, komai na gidan nan Hajiya ce take da iko da shi, da an yi magana sai ki ce ayi hakuri, fisabilliah har na waje kuma sai a riƙa bari suna takamu”
Ta ƙarasa tare da miƙewa tsaye ta nufi bedroom ɗinta.
“Ke kan Maryam Allah ya shiryaki, da wannan rayuwar babu inda zata kai ki, ni ban san inda kika ɗauko wannan baƙin hali ba, ni dai ba haka na ke ba”
Bayan sun yi Sallah magariba, Anty ta shiga part ɗin Abbah da abinci a hannunta ta tsakura masa labarin abunda ya faru.
Washe gari Namra ta daɗe tana bachin safe saboda gajiya da kuma kwanciyar hankalin yau tana gida bata da wata matsala. Maryam ce ta shigo ita da Aisha suka tashe ta wai zasu je siyen wasu kayan kitchen, kuma ta fito da Yasmin a falo tana jiranta. Mulmula ta riƙa yi saman gadon sai da suka fice, sannan ta miƙe tsaye tana miƙa ta shiga bathroom, bakinta ta wanke, a nan take kallon kanta a madubi ita kanta ta san ta chanja kamar ba ita gaba ɗaya ta fita daga kamamninta, ta yi baƙi sosai idonta sun ƙara fitowa.
“Namra ko har yanzu baki tashi ba”
Jin muryar Yasmin yasa ta yi saurin barin gaban madubi ta nufo ƙofar fita tana zumuɗin haɗuwa da Yasmin.
“Anty”
Ta faɗa jikin Yasmin suka rumgume juna.
“Ashe kin ji na dawo”
“Eh Gwaggo ce ta faɗa min komai. Ban jidaɗin abunda ya faru ba Namra sai dai dawowarki ta min daɗi, saboda Uzair, ko da baki zo ni zan je har inda kike”
Gaban Namra ya faɗi ta mata wani kallo mai cike da mamaki.
“Uzair kuma, miya faru?”
Yasmin ta kama hannayen Namra ta riƙe.
“Ina son ki faɗa min tsakani da Allah, da gaske kin taɓa kama Uzair yana luwaɗi?”
“Dan Girman Allah Anty ki rufa in asiri na dawo yanzu cikin family na kuma saki sake tayar min da wannan maganar? Ko so kike Abbah ya sake kora ta ne?”
“Ko kaɗan, Namra kawai ina nema miki justice”
“Justice for what...?”
“For what Uzair did to you, shi ya ɗauke ki ranar da aka ce kin gudu kin je gurin Asim”
Idon Namra ya cika da ƙwalla.
“Waya faɗa miki?”
“Shi ya faɗa min da kansa, kuma yayi rape ɗinsa da kansa Namra, na rasa yadda zan yi abun yana ta ci na a rai, na kasa faɗawa kowa, amman na yi ma kai na alƙawari sai na shigar da ƙarar Uzair kotu da kai na, akan ki sai na nema miki haƙƙinki, saboda ɓacin suna da yayi miki kuma yasa duniya ta zargi kin gudu da saurayinki”
Kai Namra ta girgiza masa.
“Na yafe masa, dan Allah dan Annabi ki taimaka min ki bar wannan maganar”
“Kin tuna lokacin da Amira ta gudu? Shine sila saboda ke aka yi ma maganin sai ya koma kan Amira saboda ta ci amanar ki, Namra you deserve justice”
“Ke da kan ki zaki shiga kotu ki ƙalubalanci mijin ki?”
Cikin kuka Yasmin ta ce
“Yes Goyon bayan ki kawai na ke nema”
Namra ta yi saurin miƙewa tsaye fuskarta da hawaye.
“Zan yi tunani a kai, just go please”
Bata mata musu ba, ta share hawayenta ta mike tsaye ta fice. Tana fitowa falo ta karɓi Little Namra hannun Anty ta fice, ko sallama bata yi ma Anty ba. Anty na ganin hakan ta san ba lafiya dan haka ta tashi ta nufi ɗakinta inda Namra take.
ASIM POV.
Yana fita gidan Hajiya Sadiya, ya kira Matdiya ya faɗa mata ta faɗawa mamanta yau da dare zai zo ya gaishe ta. Haka kuwa aka yi, dare na yi yaje yayi wanka ya shirya cikin tufafi na alfarma, ya shiga motarsa da ya sa aka wanke masa, ya nufi wani boutique ya haɗu mata sabulai da mai da turaruka masu ɗan karen tsaɗa sai da ya kusa ciki bayan motarsa sannan ya shiga ɓangaren kayan ciye-ciye yayi leda uku, bayan ya biya ya kama hanyar gidansu.
Tass ya samu ƙofar gidan yau kam an share ba kamar kullum ba, zamansa yayi cikin mota ya kira ta a waya, ya shaida mata yana nan waje. Yau kan ta fi masa kyau fiye da kullum dan ta chaɓa ado da sari kamar wata amaryar india. Sama-sama suka gaisa yana mata wani kallo mai cike da alamar tambaya, ita kuma sai wani noƙe kai take ita ala dole tana jin kunya. Sannan ta yi masa iso, suka shiga cikin gidan tare. Ya raina gidansu sosai dan shi gani yake yanzu ya wuce irin wannan rayuwar. Bayan ya gama gaisawa da mahaifiyarta ya aje mata dubu hansi, sannan shiga ko wane ɗaki na gidan yana gaisawa da su sannan ya aje musu dubu goma. Su kan sai murna suke suna yabawa Mardiya kan ta yi miji, masu jin zafi suna ji, dan wasu har sun soma maganar ai yadda yayi ma Namra ita sakinta zai yi da ana kwana biyu.
Bayan sun fito yasa yara suka kashe kayan da ke bayan motarta suka shigar ma Mahaifiyar Mardiya da su cikin gida. Ita Mardiya ji tayi kamar ta ɗauke shi ta haɗe saboda ƙaunarsa dake ƙara mamaye mata zuciya, ko a mafarki bata zaci mutum mai kuɗi kamar Asim zai so ta ba, balle ma har ya ce zai aureta. Sun sha fira sosai sai kusan ƙarfe goma sha ɗayan dare sannan suka yi sallama.
A daren da farinciki suka kwana daga ita har Asim, har yana jin ba zai iya bari ta jima sosai ba. Sai dai abunda ya tsaya masa a rai miyasa bata nuna masa dangin ubanta ba? Ko lokacin da ya ce zai turo cewa ta yi bari ta faɗawa Uncle ɗinta.
“Idan ma bata da uba miye ruwana tun da ita nake so ba ubanta ba”
Ya faɗa yana fesa turare a jikinsa. Sannan ya ɗauki glass ya saka ya ɗauki makullin motarsa ya fice. Kai tsaye gidan ƙanen Babansa ya nufa, daman yasan a irin wannan lokacin yana gida kamin yaje gurin da yake aikin ƙira. Har ciki gidan ya shiga, sai qani ƙyaƙƙyami yake da ginin ƙasa, ya gaisa da matansa sannan suka fito waje suna tattauna maganar auren da Asim yake labarta masa na Mardiya akan maganar tura magaba, a nan suka kitse maganar sati mai zuwa sai nemi sauran ƴan'uwa suke je su nema masa aurenta, sannan kuma ya ɗora masa da maganar gidan da aka ce masa akwai amman milinya takwas ne.
Gidan ba shi da nisa sosai da unguwar hakan yasa suka ƙarasa da mota aka kira Mai gidan ya shiga da Asim ciki ya ga komai. Ya yaba da gidan sosai, komai na cikin gidan sabo ne ga sabo fenti ga fulawowi daman irin gidan nan ne da ake ginawa sababbin a saida. Ko tayawa Asim be yi ba, suka kutse magana akan idan ya dawo daga sokoto zai zo tare da shedu a bashi makulin gida takardu shi kuma ya bada kuɗi. Mutunen sai godiya yake ganin Asim be taya ba ya amince zai ba shi kuɗin. Bayan sun dawo ya aje Ƙanen Baban nasa ya miƙa masa dubu ashiri, sannan ya kama hanyar gidan Hajiya Sadiya yana aikawa Namra kira.....
Tsaki yaja bayan ya kashe wayar, lallai ma yarinyar nan ta raina masa hankali, shi zata yi ma ɓoyun ɗansa? Allah yasa ma da gaske ta zubar da cikin nan ta ga yadda zai yi da ita ƙut! ya yi ƙwafa.
Yayi mamakin ganin Hajiya Sadiya a gidan nata, bayan yasan a wacan take zama saboda ƴarta. Bayan sun gaisa ya zauna saman kujera yana kallonta.
“Mun yi waya da Alhaji yace na same shi sokoto, kuma na samu labarin Namra tana sokoto har ma na yi waya da ita, amman kin san ba lallai ba ne ta amince ta dawo gidana ba ko?”
“Nasan da hakan shiyasa ka ga na dawo nan gidan ai, nasan zaka zo nema na, abunda nake so da kai ka yi ta try har sai kaga ta aminci, idan kuma hakan be samu ba, to zan baka abunda zaka bata, kuma ka tabbatar ya kai ga bakinta, ma'ana ta ci”
“Mi zaki ba ni?”
“Ina zuwa”
Ta miƙw tsaye ta nufi wani bedroom. Shi kuma ya ƙurawa pop ido kamar yau ya fara ganinsa.
“Wallahi duk kika zubar min da ciki ko? Hmmm, Allah yasa ma Ubanki ne ya zubar da shi ta yadda zan fi jindaɗin shari'ah da shi...”
Fitowar Hajiya Sadiya ce tasa ya mai da dubansa gareta yana kallon farin ƙyalen da ke hannunta. Tana ƙarasowa ta warware ƙyalen ta miƙa masa apple ja.
“Ka tabbatar ta ci wannan apple ɗin ko da kaɗan ne, amman sai idan ta ƙi yarda ta koma ɗakinta”
Ya ƙurawa Apple ɗin ido
“Kar fa wani abu ya same ta, i mean kar ta mutu, akwai baby na a jikinta”
“Babu abunda zai same ta, ka yi yadda na ce kawai”
“Okay”
Ya miƙe tsaye tare da saka apple ɗin a aljihu, ya fice. Be yi nisa da barin gidan ba Nably ta kira shi, amman sai ya samu kansa da ƙin ɗauka shi kwata-kwata yanzu ta fita ransa, Mardiya ce on top.
KU YI HAƘURI DA WANNAN🙏
*Ku yi ta yaudarar kan ku da sunan wata ta siya ta ara muku ku karanta, idan mun je can inda baki be magana zamu tsaya gaban Allah ni da ku ya mana hukunci.*
HILAL POV.
SIX MONTHS LATER...
Suna jin ƙarar tsayawar Motar Dadynsu suka fita da gudu suna masa oyoyo. Zaune suka same shi cikin motar yana waya, hakan yasa Ezzah zagayawa a front seat ta zauna tana jiran ya gama wayar ta fara masa complain.
“Dady muna dawowa daga makaranta Mama Teema tasa mu wanki”
Yana sauke wayar daga kunnensa kenan, ta soma labarto masa abinda ya faru yau. Wani kallo yake mata, irin kallon nan na ɗa da ƴa, kamin ya kai hannunsa ya kama fuskarta ya riƙe.
“Ezzah kin yi ƙanƙanta da irin abubuwan nan, kullum sai kin ce Teema ta miki kaza bla bla bla, wannan sam be dace da ke ba, babu abunda Teema zata muku sai tarbiya, ƴar'uwarki bata taɓa faɗar an mata wani abu ba sai ke”
Ta turo baki zata masa magana da kuka a lokaci ɗaya.
“Dady ni bana son ta, a kawo mana Mummie mu”
“Ba za'a kawo ba, kuma kar bakin ki ya ƙara furta kalmar ƙi ga matata, ke kowa ai baki so, har Kalsoom ba haka kika mata ba? Saboda ku Hajiya tasa na auri Teema yanzu kuma ki bijiro min da wannan maganar! Kar na sake ji”
Ya fita daga motar ya kama hannun Ulfah, sannan Ezzah ta fito ita ma tana share hawaye ta rufe masa motarsa, ta rufa musu baya.
Teema na tsinkayarsu dan tana tsaye jikin window ne, sai dai ba zata iya jin me suke cewa ba. Tana ganin ya doso ƙofar falon sai ta bar gurin da sauri ta shige bedroom ɗinta ta zauna bakin gado ta soma ƙirƙiro kuka. Tun da ya saka kafarsa a falon ya ji be ji motsin Amaryarsa ba ya saki hannu Ulfah ya doshi bedroom.
Zaune ya same ta bakin gado tana rusar kuka, zama yayi kusa da ita cikin damuwa, dan yasan dalilin kukan nata baya buƙatar tambayarta.
“Sau nawa zan faɗa miki ki yi haƙuri Teema? Wasu ma sai da suka shekara ashiri a gidan miji sannan Allah ya ba su haihuwa, balle ke da baki yi shekara ɗaya ba ma?”
Ta ɗago kai ta dube shi.
“Hilal ina tsoron kar a'ce ba zan haihu ba ne gaba ɗaya, tun da na zo gidan nan ko ɓari ban taɓa yi ba”
“Idan Allah ya ga dama zai baki just be patient, wani lokacin abun mutum nesa yake, na shigo da farinciki kuma kin rusa min shi”
“Ka yi haƙuri rai na ne yake ɓaci”
Ta share hawayenta, har ga Allah wannan matsalar tana damunta, sai dai ta kan yawaita yi ma Hilal kukan hakan ne gudun kar ya zargi ta ci amanar ƴaƴansa, duk lokacin da ya tarar da ita cikin irin wannan halin ya kan kasa mata maganar yaran, ko da kuwa sun je masa sun kai masa ƙararta ne.
“Kuɗin da na faɗa miki muna jira jiya dai Allah yayi sun fito, dan haka yanzu ki shirya muje kasuwa da yara mu yi siyayya, gobe kuma zan je da Kalsoom Hajiya kuma kuɗi zan bata, sauran kuma sai mu ƙara a account, idan na samu hutu sai mu leƙa waje”
Hannayenta ta kama ta riƙe tana murzawa a hankali.
“Hilal ya kamata ka yi tunanin ma kan ka future, kai kake ta hidima da Hajiya duk da tana da waɗanda zasu iya mata beside Abbah ka yana da rai balle ace ko zata rasa wanda zai mata ne, ya kamata ace ka tanada abun ka har sai ranar da zaka nema ko kuma ita Hajiya zata nema sannan ka ɗauko ka yi amfani da shi, ƴaran ka babu abunda suka nema suka rasa, dan me za'ace a riƙa kashe musu kuɗi haka nan kawai a banza? Ka fara ginawa kan ka rayuwa Hilal, yanzu nan kuɗi ba ƙara ka gina gida da shi ba”
“Ina da gida Teema ba ɗaya ba ba biyu ba uku ba, kuma naga yanzu mi zan yi da gida?”
“Baka mafarki tara zuri'ah kamar ta Mahaifinka? Baka fatar haɗa ƴaƴan da matanka guri ɗaya yanzu? Ni abun da naga ya fi kawai ka kawo ko 150.000k ne asiya mata lace da atamfa, sauran kuɗin kuma ka ba ni nawa ita kuma Kalsoom ka bata ta siya abinda take so, Hajiya na san idan ka bata kuɗin kashewa zata yi amman idan aka siya mata kaya, ko sakawa ta yi ai ka ji daɗi, ni k8ma ina son na fara business”
Miƙewa yayi tsaye.
“Zan yi tunani akai, bari na je na duba Kalsoom ta ce min kan ta na ciwo”
“Ka gaishe min da ita, tun da ka ƙi yarda na ganta, amman ba zaka bari ka ci abinci ba”
“A'a sai na dawo kinsan matsalar mai ciki”
Ya faɗa da murmushi a fuskarsa sannan ya juya ya fice, zuciyarsa da kwankwato, ya lura duk lokacin da ya shigo da zimmar yi ma yaransa ko Hajiya abu sai Teema ta nuna masa ba haka ba, abunda Kalsoom da Rashida ba su taɓa masa ba kenan. Duk da yana tunanin wannan karon ta yi magana mai ma'ana kuma da bada dalili. Miƙewa ta yi ta rakoshi har gurin mota, ya shiga ta maida ganbun motar ta rufe tana ɗaga masa hannu har ya fice.
Ajiyar zuciya ta sauke, ta gaga mallakar mijinta har yanzu, iya shige-shigen da take tunanin zata yi ta yi amman kan Hilal ya gagara mallaka, bata da ƙudiri raba shi da mahaifiyarsa, sai dai tana ganin kamar hidimar da yake mata yayi yawa, tun da ba shi kaɗai ta haifa ba.
“Ulfah, Ezzah..!”
Sai ga su da gudun su, bama Kamar Ulfah da hanjin cikinta ke kaɗawa, dan jikinta har rawa yake kamar zata saki fitsari.
“Uban mi kuke faɗawa Baban ku ɗazu...?”
Ulfah ta yi sauri ɗaga hannunta sama.
“Wallahi ba ni ce ba, Ezzah ceta faɗawa Dady wai kin sata wanki”
Teema ta miƙa hannu ta kama kunnenta har sai da ta yi ƙara.
“Wato dan na saku wankin uniform shine abun magana? Ke komai sai kin kwashe kin faɗawa Dadynki? Sau nawa nake ja miki kunne akan faɗawa Dadynki magana idan na miki abu?”
Ta nuna mata wani ɓangare na gidan inda rana ta baje a gurin, kamar an hura wuta.
“Oya wuce can ki kama kunnenki, kuma karki taso sai na ce ki taso”
Da sauri ta ɗuka ƙasa ta riƙa kafafun Teema.
“Dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba”
“Wannan tsinin bakin na ki ba, ke me baƙi hali tun da kin yi mugun gado ko? Kije ki kashe min aure! Ke ce uwar rashin kunya uwar gulma ko? Zaki ci ubanki a gidan nan ba dai duk lamanin da na ke miki baki gani ba”
Ta faɗa tana matsar bakinta. Daman ta saba yi mata irin wannan horon a duk lokacin da ta yi mata ba daidai ba. Ta buge mata hannu.
“Ba zaki wuce ba sai na yi ƙwallo da ke?”
Ulfah ta sa kuka.
“Mama Teema Wallahi ba da ni ba”
“Ai ba da ke ba ita kaɗai, ki ki wuce ki gyara min kitchen”
“Tau”
Ta wuce da gudu idonta cike da ƙwalla. Ezzah kuma ta tashi tana kuka ta nufi gurin da ta saba tsayawa kama kunne ta kama kunnenta.
Juyawa Teema ta yi ta koma cikin falon, har ta zauna sai kuma ta miƙe tsaye ta nufi bedroom ɗinta tana ta saƙe-saƙe a ranta. Wani irin ihu ta ji da muryar Ulfah ba shiri ta zaɓura ta fito daga bedroom ɗin a firgice ta nufi kitchen.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Na shiga uku uban waya aike ki taɓa miya?”
A razane ta yi furucin kamin ta ƙarasa gaban Ulfah da ke kwance ƙasa lame-lame tana murje-murje da ihu kamar bata san inda take ba, jikinta har ya sale.
Har ta ɗaga ta tasheta sai kuma ta saketa ta fita a firgice tana kiran Ezzah.
Karo suka yi ita da Ezzah duk ta haɗa uban gumi.
“Mama Teema ga ni”
“Je ki Kitchen ki kama ƴar'uwarki yi sauri”
Ita kuma ta juya da sauri ta koma ɗakinta dan kiran Hilal.
KALSOOM POV.
tana zaune falo Hilal ya shigo bakinsa ƙunshe da murmushi da kuma sallama a lokaci ɗaya. Itama da murmushin ta amsa masa tana ƙara miƙarda ƙafafunta. Kusa da ita ya zauna daman tana zaune ne saman carpet ya kai hannu ya shafa ƙananan kitson da ke kanta yana murmushi.
“A bani canji na na kitso”
“Ba wani canji mai kitson ma ta ce sai an ƙaro”
Dariya yayi ya kai hannu ya shafa cikinta.
“Sai kice mata ai ke mijinki bawan Allah ne, ba mai kuɗi ba ne”
“Ba wani nan, ni sai ka ƙaramin”
“Baki da matsala yarinya ko nawa kike so za a ba ki, ƙuɗin da na ke faɗa miki ina jirajiya sun fito”
Ta zaro ido.
“Da gaske Alhamdulillahi”
Ya lanƙaci hancinta.
“Yes”
“Allah yasa musu albarka”
“Amin mi kike so a siya miki?”
“Ka fara cirewa Hajiya nata, sannan mu sai kuma ƴaƴanka, kai ai ko baka samu ba, ba matsala”
“Sai dai na ɗauki na ki”
“Ba matsala ai daman ni bana siyen komai yanzu”
“Ko da kin haihu?”
“Hilal anya zan haihu?”
“Haba ki daina wannan maganar mana, ke da Teema maganar haihuwar nan na ku ya ishe ni”
“Ƙara ita ai bata yi cikin ba, ni kuwa shekara har da wata huɗu ban haihuwa ba, cikin nan ya ishe ji nake kamar na cire shi na aje”
“Zaki haihu inshallah, tun da an bincika babu wata matsala”
“Allah yasa”
“Amin. Zaki haifa min Baby girl mai kama da ke”
“Baby Boy dai zan haifa mai kama da kai”
Bakinshi ya kai zai yi kissing ɗinta sai wayarsa ta yi ringing, kawar da fuskarta ta yi dan ta bashi damar picking ɗin wayarsa.
“Hello...”
Ya miƙe tsaye da sauri.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, gani nan zuwa”
“Miya faru? ”
Kalsoom ta tambaya a firgice.
“Wai Ezzah ne da Ulfah suka yi faɗa shine Ezzah ta watsa mata miya”
“Subhanallah miya haɗa su haka, ko na ɗauko hijab ɗina muje tare?”
“A'a zauna duk yadda aka yi zan kira ki”
Ya fice a firgice. Daker ta unƙura ta miƙe tsaye da tulelen cikinta.
Yana isa ya ɗauke ta suka yi asibiti tare da Teema, Emergency ya wuce da ita surgical Ward, wata Dr Khadija ce ta shiga bata taimakon gaggawa, dan Dr Hilal tsaye kawai yayi yana kallo saboda jikinsa duk ya mutu ko da suka kawo ta asibitin ma ta suma.
AMIRA POV.
Tun da suka kamo hanyar sokoto take ta aikinki kuka, har suka iso sokoto idonta ya kumbura sosai. Direban na yin horn a bakin gate ɗin gidansu, ta jita cikin wani irin yanayi marar misaltuwa, wani sabon kuka ne ya sake rufeta, musamman lokacin da ta ji muryar mai gadin su yana tambayar wa suke nema.
“Amira na kawo ka min magana da iyayenta zan danƙata hannun Mahaifinta ko mahaifiyarta”
“Amira...!”
Mai gadin ya daki ƙirji. Kamin Direban ya sauke gilashin motarsa ya hango Amirar ce da gaske. Jiki na rawa ya wangale musu gate sannan ya shiga cikin gida da gudu.
Sai ga Mahaifiyarta da duka ƙanenta sun fito har da Baban yayanta. Duk motar suka nufa. Ammy ce ta fara buɗe motar sai ga Amira ta fito daga ciki tana kuka, suka rumgume juna, ƙanenta kuma suka daka tsalle suka yi kanta, Big bro ɓata ne ya tsaya a gurin ya dake yana kallon ikon Allah.
“Ke ce Mahaifiyarta?”
Ammy bata iya amsawa ba sai kuka take, Babban yayansu ne ya amsa da.
“Eh ita ce, waye kai?”
Ya fiddo id cart ɗinsa ya nuna masa,sannan ya miƙa ma Ammy waya.
“Zaki yi magana da Ogan mu”
Cikin muryar kuka Ammy ta ce
“Hello”
“Ke ce Mahaifiyar Amira?”
“Eh nice”
“Kina magana da Major Abdallah Ahmad Mai-doki, da ga rumdunar bada tsoro ta Kasa wato Nigerian Army, da fatar ƴar ki ta shiga hannun ki”
“Ta shigo na goɗe muku”
Daga hakan ɗireban ya janye wayarsa ya buɗe motarsa.
“Wait...”
Big bro nata ya faɗa sannan ya ƙaraso kusa da shi.
“Ina kuka haɗu da ita?”
“Ba ni da wani abun da zan ce ita zata muku bayanin komai da bakinta”
Ya shige motarsa ba tare da ya tsaya jiran abunda zai ƙara tambayarsa ba ya juya a guje ya bar gidan. Sai da Ammy da Amira suka ci kukan su sosai a gurin sannan suka shiga cikin giɗan still suna kuka ita da ƴarta.
NAMRA POV.
“Miya haɗa ki da Yasmin?”
Anty Amarya ta tambaya.
“Ba komai saboda kawai na ƙi amincewa ta maka Uzair kotu ne”
“Kotu a wane dalili?”
A nan Namra ta labarta mata yadda suka yi da Yasmin.
“Karki yarda da ta sa sake jefa ki cikin halin da mahaifin ki zai tsane ki”
“Nima ba zan yarda ba Anty idan munje lahira Allah zai mana hukunci ai”
“Wannan shi ya fi, kin samu kin dawo gida kuma za su kawo miki wani ruɗani, qaya sani ko da mijinta aka haɗa kai ta aikata miki haka”
“Ƙoma ba da shi ba ne babu ta yadda zan yarda ta kai mijinta kotu saboda ni”
“Hakan ya yi ki karya kije ki gaishe da mahaifinki, breakfast ɗin ki na nan dinning”
“To na gode”
Tare suka fito da Anty, suka zauna dinning sai tattauna maganar suke, bayan ta gama karyawa ta koma ɗakin Anty ta ɗauki Hijab ta saka ta nufi part ɗin Abbah.
“Assalamu alaikum”
Ta faɗa yayinda ƙafafunta duka biyu suka tsunduma cikin falon Abbah. Abbah dake dinning area ya ɗago ya kalleta idonsa sanye da farin gilashi fuskarsa kuma ɗauke da murmushi.
“Mamana”
“Na'am Abbah ina kwana”
Ta duƙa har ƙasa ta gaishe shi tare da Hajiya Barau dake ƙoƙarin barin dinning ɗin, kamar zata fasa ihu tace wayyo haka ta bar falon. Sai Abbah ya nunawa Namra kujerar da ke kusa da shi.
“Zo nan ki zauna Mamana”
Ta zauna cikin wani irin jindaɗi marar misaltuwa.
“Kin tashi lafiya, kin karya ko?”
“Na karya”
“Mamana ina son na tunatar da ke akan rayuwa. Ki riƙa haƙuri da abunda ya same ki, kar hakan ya saka ki sakewa ko kuma wani tunani, ko wane bawa da irin ƙaddararsa, dukan abunda ya faru ga bawa zai zamo masa darasi ne ko kuma izna ko wata hanya ta samun cigaban rayuwa, ko da kuwa abun nan mai daɗi ne ko akasin haka, dan haka bana son ki saka damuwa a ranku ni dai na yafe miki, kuma ina son idan kin ɗan hutu kin samu sawaba sai kuma ayi maganar karatu, ina tunanin idan kika koma makaranta sake fi sakewa ki manta da komai”
“Na gode sosai Abbah Allah ya saka maka da alheri, kamin abunda ban taɓa mafarkin zaka min ba, ni kuma na maka alƙawarin va zan sake tsallake zaɓinka ba har a bada ko da kuwa a tufafi ne”
“Allah ya miƙe albarka, ni zanje na shirya akwai inda zan je kwana biyu nan ban samu na fita ba”
Ya miƙe tsaye yana faɗar hakan, ita ta miƙe tsaye.
“Tau Abbah Allah ya tsare”
“Amin”
Ya nufi hanyar da zata sadashi da bedroom ɗinsa, ita kuma ta juya ta fice zuciyarta cike da farinciki.
Ko da ta dawo part ɗin Anty ta tararda su Maryam sun dawo, ga manyan ledoji a gabansu amman sun riƙe baki sai mamaki suke, da alama akwai abunda ya faru.
“Lafiya?”
Maryam ta riƙo hannunta.
“Ke ƴar gidan Abbah wai Amira ta dawo”
“Amira kuma? Daman tun tafiyar da ta yi bata dawo ba sai yanzu?”
“Wallahi sai yanzu, kuma jiya ita ma ta dawo kamar ke”
“Amman kun ji wani abu game da ita?”
“A'a nima Iklima ce take faɗa min ta dawo”
Anty Amarya ta ce
“Allah ya kyauta”
Duk suka amsa da Amin.
UZAIR POV.
Yana shiga bedroom ɗinsa ya fito ya nufi na Yasmin dan yana son ya bincika ko da akwai sauran abunda ta boye, jikinsa na bashi ba saƙon wasiƙar ne kawai ba. Bincike ya fara mata cikin durowoyin ɗakinta kama ya koma gurin wasu takardu da suke gefen gadonta, be samu abunda yake so ba, sai kaiwa ya juya ya fita ya nufi wata ƴar ƙaramar durowarta da take aje takardun aikinta da littafanta duk ya bi ya watsar sai bincike yake mata. Wani abu ya ji ya tsoki tsararsa, kamar an soma masa mashi a kunkuru, tun yana juriya da riƙe kunkurun nasa har ya ji abun ya ƙara sukarsa da wani mugun zugi, wata zarananniyar ƙara ya saki yana jin abun masa ƙasa cikin ƙashin ƙafafunsa, ihu kawai yake yana mirgina, abun ba kyau maza a ƙasa😖
Da gudu mai aikinsu ta so kansa tana tambayar ba'asi. Ganin abun ba na banza ba ne ƴasa ta fita neman mai gadi ko zai iya taimakawa. Ko da Mai gadin ya shigo Uzair wani abu yake kamar mai ɗaukar rai. Da sauri Mai gadi ya kira Yasmin ya faɗa mata abinda yake gudana.
YASMIN POV.
“Zan turo maka number ka kira mahaifiyarsa ka faɗa mata”
Amsar da Yasmin ta mayar masa kenan ta katse kiran, ta aika masa number sannan ta cigaba da kuka tana zanawa mahaifiyarta abubuwan da Uzair yake mata wanda hakan kawai ya isa ya tabbatar da gaskiyar abunda ya yi ma ɗanta, bayan ta fito gidansu Namra ta nufo gidansu dan ta na jin bata buƙatar komawa gidan a yanzu.
“Ko ma minene shiru ya kamata ki yi ki rufawa mijinki asiri”
“Irin wannan rufa Asirin ne yasa mata da yawa maza suke cutar da su, idan aka muku fyaɗe ko aka yi ma ƴaƴansu, wannan abun yana cutar da mata da yawa, mu muke faɗar a daina ɓoye abu a riƙa fitowa a ana faɗa yau kuma sai a same ni da wannan aikin na ɓoyewa? Ɓoyewar nan da ake shi kw basu damar ƙara aikata abunda suke aikatawa, at least ko da ba a hukunta su ba, duniya zata kunyata su kuma asan ko su waye, ban ga dalilin rufawa Uzair asiri ba ko da kuwa ubana ne balle mijina, ina yawan faɗar cewa ni dai i would never in my life encourage anyone to live with an adulterer tun da har Allah ya ce a jifasu su mutu, they are as good as useless to be seen alive in this world, sai kuma na zama ni ce zan rufa masa asiri miye amfanin aikina?”
“Nidan indai zaki ɗauki shawarata ban ga abun burgewa ga mace ta kai mijinta kotu ba da sunan wai yayi ma ɗansa fyaɗe, kina da hujja ne?”
“Ko bana da ita dole zan samo ta”
“Ni kam ba da yawun baki na ba Yasmin wannan sam be dace ba, idan ma zama ne ba zaki iya da shi ba, sai ki nemi ya rabu da ke kawai ki hutu”
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
AMIRA POV.
“ji na yi gidan nan ya isheni ina ta jin kamar idan ban gudu ba wani abun zai iya faruwa da ni. Ban tsaya ɗaukar komai ba sai kuɗi, tun daga lokacin da na bar gidan nan nahau mota na kama hanya ban sake sanin inda nake ba, ban san inda direba ya sauke ni ba ban san ya nayi rayuwa ba, sai a ƴan kwanakin nan da wannan sojan ya tsince ni a bolar gidansu, shine yayi ta min addu'ah da komai har hankalina ya dawo, na faɗa masa inda nake ya saka direba ya kawo ni gida”
Duk kai suka girgiza cike da tausaya musamman Ammy da ke kuka kamar yadda Amira ta ke yi.
“Amman Namra ta ci amanar abota, ai gashi nan ta fara ganin abunta, ɗazu-ɗazu hajiya Haulat ta ƙira ta faɗa min ita ta dawo gida aure ya mutu, kuma ance can gidan auren ta ci kwakwarta”
Salman Big bro nasu ya kalli Ammy dake wannan maganar yana faɗin
“Ai ba laifinta ba ne, ita Amira ai cin amanar ta tashi yi, da yanzu da gaske ne idan an sakawa Namra wannan abun maganin zai kamata ai kim ga ita ta ci amana kenan, waya sani ma ko koma miki ne yayi, a haɗa baki da ke a sace ta har a ayi mata ƙazafi, wallahi kun ci amanar juna ke da ita”
Abban Amira ya ɗaga masa hannu cikin ɓacin rai.
“Idan kasan bakin ka ba alheri zai faɗa ba, ka tashi kawai ka bar falon nan. Allah zai saka miki Amira zura mata ido kawai daga ita har ɗan'uwan na ta”
“Wane irin a sa muku ido? Aja mata haƙƙinta dai, babu irin abunda ba'ayi ba amman yarinyar nan ita da mahaifiyarta suka tsaya kai da fata akan babu hannunsu a ɓatan Amira, aka kiɗa aka raya aka daka yarinyar ta ƙeƙashe ƙasa tace bata san gaibu ba akan ɓatan Amira sai yanzu kuma gaskiya ta bayyana za'ace a ƙyaleta”
Taɓe baki Salim yayi ya miƙe tsaye ya fice daga falon.
“Babu wani haƙƙi da za a ja mata ku zuba musu ido kawai, ko bayan rage kika zagaya kika ɗauki wani hukunci sai na ɓata miki rai Wallahi, tun da na ce a bar maganar nan barinta shine ya fi kawai”
Ya miƙe tsaye ya fice daga falon. Kuka sosai Amira take, sai dai ba kuka dawowa gida ba, kukan rabuwa da Abdool tana jin kamar zata mutu idan ta tuna baya kusa da ita a yanzu.
ABDOOL POV.
Ya ware hannayensa.
“You see Ummi na faɗa miki Mai Martaba bashi da matsala, na zauna na fahimtar da shi kuma ya fahimta”
“Hakan na da kyau ai, sauran yarinyar ko?”
“Wannan ba matsala ba ne, zan ji da shi, so na ke sai an kwana biyu sai naje na ganta ko?”
Ummi tasa dariya, the way da yake mata maganar kamar wani ƙaramin yaro.
“Allah ya baka sa'ah”
“Amin my happiness. This week zan koma aiki, hutun mu ya ƙare”
“Ai daman ai baka yi hutu ba, ina fatar da kana da number wayarta”
“Wallahi bana da ita saboda yarinyar akwai jan aji amman zan sa a nema min. Am ɗazu mun yi waya da mahaifiyar Amira ta isa gida lafiya ƙalau”
“Mashallah, yau za su kwana cikin farinciki, ita kanta zata fi sakewa”
Kafaɗunsa ya ɗaga irin ina ruwana ɗin nan. Ummi ta watsa masa harara.
“Bari yarinyar nan ta ƙi amincewa da kai, ta yi ta baka wahala”
Ya sa dariya.
“Haba Ummi karki min baki mana”
Ya miƙe tsaye ya fice yana dariya.
ASIM POV.
Da rana ya sauka sokoto, kai tsaye gidansu ya nufa, duk da be so sake dawowa garin ba tare da an canja musu gida ba, sai dai matsalar har yanzu ba a samu gidan da suke so ba. Mama ta yi mamakin ganinsa sosai tun da be kirata ya faɗa mata zai zo ba balle ta tanadar masa da wani abu.
“Wannan zuwa haka ba waya ga shi komai ba a tanadar maka ba”
“Ba komai nima zuwan ya kamani ne kawai”
“To Allah yasa dai lafiya”
“Lafiya ƙalau, na ji ance Namra tana garin nan ne, shiyasa na zo dan zan maida aurena ne”
Mama ta daki ƙirji.
“Auren ka Asim? Kai kam mi ya kai ka daga Allah ya raba da ƙaddara”
“Kin san tana da ciki fa na sake ta, ni gaskiya yanzu so na ke na maidata”
“Amman Asim kana ganin zaka iya tunkarar gidansu yanzu ka ce zaka maida aurenta, mahaifinta ai sai ya yanka namanka da wannan fitinanniyar ƙanwarta”
“Koma minene dai sai naje gidan, ai yanzu be isa ya wulaƙanta ni ba, dan na fi ƙarfinsa Wallahi”
Tattaunawa suka soma yi kan maganar aurensa da Mardiya da irin abubuwan da ya shirya, sannan ya bijiro mata da maganar samun gidan, a nan take labarta masa am samu wani a Abdullahi Fodio Road amman wai har miliyan uku, ita gani take kamar yayi tsada, waɗannan da ake samu kusa kuma duk bata son unguwar.
“Ƙar hakan ya dame ki, indai gida yayi miki za a biya kuɗi a saka komai sabo sai ku koma”
“Yanzu kana da har miliyan uku na gidanmu?”
“Akwai su, zinari fa na ke siyarwa, kin san kuɗin da mike samu kuwa?”
“Allah ya ƙara arziki ai haka nake so, sai ka samu kawon ka Na Malam ku yi magana shi ya san inda gidan ya ke”
Haka suka wuni suna fira sallah ce kawai ke tashinsa, sai da akayi magariba sannan ya shiga yayi wanka ya shirya cikin ƙananan tufafi ya saka turare ya shigo ɗakinta.
“Mama ni zanje wani guri da abokina sai gobe zamu dawo”
“To Allah ya tsare hanya”
Ya sa kai ya fice sai ƙamshin turare yake. Be daɗe da fita ba aka aiko ana yi ma Hajara sallama.
“Je kace tana nan zuwa”
Sai Hajara ta tashi ta ɗauki kayan kwaliyarta ta gyara fuskarta sannan ta saka Hijabinta ta fice. Bayan fitarta Mama ta ɗauki tabarma ta shinfiɗa a waje ta zauna tana sauraren Garkuwa Fm.
Tana haka sai ga Hajara ta dawo, ta doso inda take.
“Mama Yaya Asim ya bar makulli a ɗauko wayarsa a mota ya barta sai kiransa ake, kuma Mahmud (Saurayin da ya zo gurinta) Idan wasu suka ga wayar zasu iya fasa gilashin motar su ɗauka”
“Amman ya fita da wayarsa, sai dai idan ba ɗaya ba ce, lalaba aljihun wandon da ya cire ɗazu ko daki samu makullin ni dai be ba ni ba”
Ta faɗa tana tsakalen haƙori, da karen darbejiya bushesshe. Hajara ta nufi ɗakin Mama inda ya sarkafa wandonsa ta soma lalabawa ta ji kuɗi mai mugun yawa kamin ta yi arba da makulin.
“Ga makullin nan bari na ɗauko, amman Mama kin ji Aljihun yaya kuɗi cike”
“Ke da gaske?”
Mama ta yi sauri ta tashi ta nufi ɗakin. Hannu tasa cikin aljihunsa ta ciro rabonta saka inda take ajiyar kuɗi, sannan ta koma waje gurin tabarmarta zauna. Sai ga Hajara ta shigo da wayoyi biyu da makullin sannan kuma da Apple hannunta.
“Aje masa, wannan karki canye ki rage min”
Ta miƙa mata wayoyin da Apple ta juya, hankalinta yana gurin Mahmud kar ya ce ta bar shi.
“Ina kika samo tuffah”
“A motar Yaya”
Mama ta yi murmushin jidaɗi.
“Oh Yaro yayi kuɗi har tuffa ake ci a mota yanzu haka ya manta da ita da wayoyin nasa da ya bari, ko da yake abun ba ɗaya ba naga fa ya fita da wasu”
Ta faɗa tana gantsara apple ɗin, babu ko bismilah balle kuma ta damu da wankewa. Haka ta kama shi ta wanke tass tana cewa idan Hajara ta zo ta bata kuɗi ta siya wani wani tun da akwai shi a titi, har ta ƙaro mata ma dan wannan ma ta jidaɗinsa. Sau biyu ana kiran wayar Asim sai ta ɗauka ta ce baya kusa.
[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *Mama (Hajiya Zainab Kano) wannan shafin na ki ne, Allah kara miki lafiya*
*81*
Kaɗan-kaɗan ta fara tari alamar sarƙewa, tun tana yi a hankali har ya taso mata gadan-gadan ba sauƙi, sai faman bubbuga ƙirjinta take, daker ta unƙura ta sha ruwa, bata baro gaban firjin ɗin ba ta soma aman jini babu ƙaƙƙautawa, tun tana iya gane duniyar da take har ta daina ganin komai sai hudu, gashi yaran duk basa nan Hajara ya gurin fira, ba ita ta dawo ba sai goma har da dare, ganin Mama bata kan shinfiɗar tabarma dake waje yasa ta zargi ko ta shiga banɗaki ne, dan hankalinta be kawo ta kalli gefen da firjin ɗin yake ba, ledar turaren da ke hannunta kawai ta aje ta sake fita dan dawo da ƙannenta gida.
Moƙota ta shiga ta kira su, ta sako su a gaba tana biye har suka iso gida, sai a lokacin idonta ya kai gurin da Mama take kwance cikin jini, ihu tasa tana faɗin
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Ta nufe ta da sauri tana ihu, tana ƙarasa gurin da take nefa na yin tsiyarsu na ɗauke wuta, sai kawai ta ƙwala ma mai binta kira.
“Ɗauko Fitila Amina, ɗauko fitila yi sauri”
Da sauri Amina ta ɗauko fitila ta kunna ta nufo gurin da Hajara take. Suna yadawa duka suka saka kuka da ihu, Hajara ta shiga girgiza Mama tana kiran sunanta, amman ina idonta a ƙafe tana kallon sama. Da gudu Hajara ta fita ta shiga maƙota tana kuka, kan kace kwabo gidan ya cika da jama'a, kowa ya shiga sai ya fita yana girgiza kai wata maƙociyarsu ce da tafi kusa da su tasa hannunta tana kalmar shahada ta rufewa Mama idonta, da taimakon wasu mutane aka dawo da ita ɗaki, Maƙotan suka share gurin suka wanken jini, Amina da Hajara da ƙanensu kan sai kuka suke,ana ciki haka sai ga ƙanen Asim ya shigo nan take shi ma yasa kuka, sai kiran wayar Asim.ake baya ɗauka, unguwa har ta ɗauka wai Asim ya bada uwarsa, daman suna zargin ba kuɗin arziki ba ne.
Tun da direba ya ɗauke shi ya kai shi gurin Alhajinsa, suka ci amai kyau aka sha mai daɗi sannan suka koma sha'ani. Ba su bar juna ba sai da asuba shi ma dan zasu yi sallah ne bayan sun gama Asim ya nufi gurin da ya aje wayoyinsa ya duba dan yasan ya saka su silent ne. Missed calls ɗin da ya tarar ya ɗaga masa hankali sosai, daga ƙanensa da Number Mama a ɗayan ɓangare kuma ga na Hajiya Sadiya da na Mardiya ga kuma na Nably har sai ya rasa wanda zai fara kira. Maida wayar yayi ya aje dan yasan aduniya Alhajinsa ya tsani kiran waya ko kuma chat da wani a lokacin da suke tare da juna. Komawa ya yi suka kwanta wannan karon bachin gajiya suka yi saboda an kwana ana saɓa ma Allah. Ba su suka farka ba sai 11am, shi ma dan Alhajin nasa yana da meeting ne. Ada idan Asim ya aikata irin wannan saɓon yana jin ba daɗi, yanzu kan ba ya jin komai har daɗi abun yake masa, sai da suka yi sallama sannan Alhaji ya sa direba ya mai da shi gida, bayan ya faɗa masa zai sake aukowa a ɗauke sa za a kai shi gurin wani amininsa da yake minister of defence, Asim ya jidaɗi sosai da sallamar ƙwarai Alhajin yayi masa, ga kuma wanda ya ce zai haɗa shi da shi yasan shi ma zai samu kuɗi gareshi.
Taron da ya tarar a ƙofar gidansu na maza ya tashi hankalinsa sosai, daman tun da dreba ya sauke shi yake ji babu daɗi. Nuna shi jama'ar gurin suka riƙa yi a sannu-sannu suna tsikumin wai shi ne babban ɗanta, wasu na cewa ya bada uwarsa yayi kuɗi. Yana shiga cikin gidan ya tarar da taron mata gabansa yake sake faɗuwa, bama kamar yadda ya ga ƴan'uwan mahaifiyarsa da mahaifinsa mata duka a zaune tsakar gidan wasu har kuka suke, amman ko kaɗan be kawowa ransa mahaifiƴarsa ce ba ya fi alaƙanta abun da ɗaya daga cikin ƙanensa.
“Wai lafiya mi ya faru?”
Ya tambaya muryarsa har gargada take, dan yanzu kan ya fara tsarewa. Babu wanda ya amsa shi cikin mutanen da ke waje sai duk suka zuba masa ido kamar yau suka fara ganinsa. Hakan yasa ya nufi ɗakin Mama dan be ga ɗaya daga cikin ƙanensa waje ba.
“Hajara miya faru?”
Yana shiga cikin ɗakin ya aikawa Hajara da tambayar. Sai kawai ya ji an sauke masa mari har biyu a fuska. A gigice ya kalli wacce ta mare shi ɗin, Mama Inno ce, yayar mahaifiyarsa wato elder sister ɗin Mama.
“Baka da mutunci Ibrahim tir da kai tirr da halin ka, ace wai tun jiya ka bar gida baka san ka dawo ba, kuma ayi ta kira wayarka ka ƙi ka ɗaga, to burin ka ya cika daman ko gawarta baka son gani ko? To ba zaka ganta ba, an kaita gidanta na gaskiya sai kaje ka yi ta sharholiyarka daman ita ka sawa gaba”
Ta ƙarasa da kuka. Ji yayi kamar ana zooming ɗinsa, sam.ya manta da wayarsa na silent duk da yana da niyar idam ya fito zai kira duka wanɗanda suka kira shi dan ya ga har da new numbers, amman farincikin albishir ɗin da Alhaji yayi masa ya ɗauke masa hankali, zuciyarsa sai nuna masa take Mama ce yana kaicewa, a take idonsa ya cika da hawaye, mutumen da kukansa ma aiki ne.
“Kar dai ace min Mama ce...ce...ce
..”
Ya faɗa cikin kuka yana kallon gadon da ka agware.
“Ita ce, jiya da dare Allah ya karɓi abarsa..
”
Da sauri ya doshi gurin Hajira da ta amsa masa da kuka, ya ɗuka ya riƙa Hijabinta.
“Miya same ta Hajara miya faru faɗa min?”
Cikin kuka Hajara ta shiga masa bayani.
“Nima ban san abunda ya faru ba, ni dai kawai ina waje muna Fira da Mahmud bayan ya tafi na shigo cikin gida sai na samu babu kowa, naje maƙota ka kira su muka dawo gida sai kawai na hango ta can gefen firjin kwance idonta a ƙashe ta yi aman jini, ko da naje na kira maƙota kowa sai yace babu ta, maman Haruna ce ta rufe mata ido, na yita kiran wayarka baka ɗauka ba, kuma na ɗauki wayarta na kira ka baka ɗaga ba, na kira su Mama Inno da kawo Amadu na faɗa musu... Da suka zo aka kira wani likita (Maƙocinsu) ya duba ta yace ta rasu, da safe kuma aka yi ta kiranka baka ɗaga ba, har aka mata sutura aka kai ta”
Faɗuwa yayi zaune, ya dafe kansa wasu irin hawaye masu zafi suka soma masa zuba, ta ya za'ace mahaifiyarsa ta rasu daga ya bar ta kawai yaje ya dawo, sam be kawowa zuciyarsa zancen Apple ɗin nan ba.
Kuka ya dinga rerawa a gidan har sai da ya tashi kukan kowa a gidan, wani irin abu yake ji ana baƙinciki a zuciyarsa, be taɓa jin ɗacin da dafin mutuwa ba kamar wannan lokacin, daman ko da ya tashi be san mahaifinsa ba, dan haka be san zafin rabo ba sai a wannan lokacin, haka ya ɗinga rera kuka kamar mace, abun har babu kyau, tun wasu na tsine masa dan suna ganin kamar ya mafa mahaifiyarsa ne har suka fara tausayinsa.
NAMRA POV.
Duniya juyi-juyi a yayinda ake kuka mutuwar Mama, ta ɓangaren Namra murna ce ta cika gida ko ina sai guɗa kake ji ana yi, da kiɗin ƙwarya dan yau aka saka mare lalle, wato Maryam da Hindatu.
A cikin gidan aka yi sa salle ba kamar yadda wasu suke ba a ɗauka a kai wani guri inda ƴan'uwa. Yanzu ne wasu ƴan'uwan suke zuwa na garuruwa da kuma na cikin gati dan jiƙon lalle. Ƙarfe goma na safe aka saka jiƙon lalle wato ceremonial setting.
Amman ko da 9am ta yi gidan ya cika da jama'a abun da mai jama'ah, ba daga ɓangaren Abbah ba bana Anty Amarya ba, da kuma na Hajiya Barau, har mutane ƙauye sun iso. Goma dai-dai ƴan gidan angaye suka zo jiƙon lalle, yadda aka riƙa faka motoci a bakin gate ɗin gidan har aka rasa gurin aje wasu. Mutane sai mamakin ganin Namra suke da su a idonta suna mata kallon ta lalace ta yi baƙi, ita ko tana ganin har ta ɗan yi ƙuba a zaman nan na kwana biyu da ta yi a gida. Duka abubuwan da aka raba a gurin sa lallen daga ɓangaren Abbah ne aka kawo, wato gwaggwanin amare. Misalin huɗu na yamma aka yi wanki amare a gidan sama road gidan Alhaji Salisu Yayan Abbah amman wanda suke ƴan wa da ƴan ƙane (Cousin). An yi watsin kuɗi kamar ba gobe, bama kamar Hajiya Barau yadda ta zage tana watsin kuɗi sai ka rantse da Allah har a zuciyarta farincikin auren take, bayan kuwa ta ciki na ciki.
An raba abubuwa da dama a gurin bikin, bayan an raba abubuwan da al'ada ta tanada (Al'adar sokoto) wato raba kayan mata (Hakin maye) a gurin awankin amarya, sannan a ɗora ta su lalle da salatif da tsinke da ƙwarya da sauran kayanyakin aiki mata, daga bisani aka biyo da kayan ciye-ciye da na tanɗe-tanɗe.
Daman can tun kamin ka shigo gate sai an miƙa maka ledar takeaway, drinks kuwa sai wanda ranka yake so zaka ɗauka, bayan wanda zaka tarar a muhalin da zaka zauna tare da kayan tanɗe-tanɗe.
ASIM POV.
Haka ya koma kamar marar lafiya, sallah ma daker yake unƙurawa ya tashi ya yi, ya rufe wayoyinsa gaba ɗaya. Mutane sai gaisuwa suke masa. Bayan isha'i mutane sun fara laɓawa, ya koma cikin motarsa ya zauna sannan ya kunna wayarsa, yana haska cikin motar sai Apple ɗin yake nema, sai a lokacin ya tuna da wayoyinsa da suke cikin motar, da sauri ya fita motar wayarsa na ringing. Hajiya Sadiya ce take kiransa, sai ya koma can gefe inda babu mutane ya natsu ya amsa wayar.
“Asim ina ta kiran ka tun jiya baka ɗaga ba, ɗazu kuma na kira wayarka a kashe”
“Bana kusa ne”
Ya amsa mata cikin rashin daɗin rai dan zuciyarsa sak yanzu zarginta yake.
“Ina Apple ɗin da kace zaka bawa matarka? Wata ka bawa ne ko mi ya faru? Ni an kira ni sai faɗa suke min, wai an basu tsohuwa, ni kuma na san ba wannan maganar muka yi da kai ba, miya faru ne”
“Apple ɗin faɗuwa yayi a hanya ina da niyar kiranki na faɗa miki, maybe wata ta tsinceta ne”
“Amman Asim sai da na yi ta nanata maka kar a samu matsala yanzu gashi wata banzar tsohowa taje ta samu, garin yaya ma ka jefar da shi? Ko dai baka son kuɗin ne wai?”
“Ina so mana, ai yanzu akwai wani ko?”
“Eh amman sai naje na faɗa musu sai su ban wani, yaushe zaka zo?”
“Nan da kwana biyu”
“Zan je na ƙarɓo maka, amman dan Allah karka min sakakace irin wacan”
“Ba za a samu matsala ba wannan karon sai kin fi kowa farinciki”
“Haka nake so”
Ta katse kiran. Shi ko ya cige baki yana kallon wayar cike da baƙinciki. Yana son ya tambayi Ƙanwarsa yadda aka yi apple ɗin ya fito daga motarsa har Mama ta ci yana tsoron kar ta zargi wani abu.
“Kun samu sa'ar jinin Uwata... Wallahi kin yi nadamar sanina da kika yi a rayuwarki, sai na ɗanɗana miki wannan baƙincikin”
Yayi wulgi da wayar iya ƙarfinsa, yana huci.
UZAIR POV.
Tare da ƙannensa biyu suka iso gidan da kuma mahaifiyarsa, tana ganin irin halin da yake ciki suka ɗauki shi zuwa asibiti.
Emergency suka wuce da shi layin ƴan haɗari aka ware masa ɗaki daban likitoci suka hau duba shi, sai ihu yake kamar wanda be san inda yake ba, bayan sun yi ɗan bincike su aka tura shi gurin hoto, bayan an masa hoton suka sake dawowa da shi ɗakin suka masa allurar bachi, amman kamar an ƙara masa zafin ciwo yake ji gaba ɗaya ya fita hayyacinsa sai ihu yake. A take suka sake rubuta masa wani hoton, aka je aka ɗauka.
Lokacin da aka fito da hoton, sai Likita ya kira Hajiya suka nufi wani ɗakin da ita sai ya ƙala hotunan a jikin computer. Yana nuna mata.
“Ɗan ki ya taɓa yin haɗari?”
“Gaskiya be taɓa ba, amman ban sani ba ko be faɗa min ba”
“Gaskiya ƙashinsa na baya na karye, kuma na cinyarsa ma ya karye, sannan....”
Kamin ya ƙarasa ta miƙe tsaye ta sauri har kujerar da take zaune samanta ta faɗi.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Ganin hakan yasa likitan dakatar da bayaninta, dan ya ga alamun zata fara masa kuka, shi kansa yasan be kamata ya yi mata wannan bayanin ba, ganin tana mace amman babu yadda ya iya tun da babu wani namiji babban da yayi kusa da mahaifiyarsa. Da sauri ta juya ta fice daga office ɗin tana kiran wayar Abbah. Dan babu wanda ya san an kai Uzair Asibiti dan basu faɗa ba, tun bayan da Yasmin ta daqo gida ba ta damu da tasan dalili ba, tana ganin kamar yayi hakan ne saboda ta janye ƙudirinta.
HILAL POV.
“Miya same ƴar ka haka ne Doc?”
Doc Zara ta tambaya cike da mamakin irin ƙunar da Ulfah ta yi. Hannayensa ya zuba aljihu yana sauke ajiyar zuciya, ita kan Teema tuni ta kusa cikin ɗakin tana hawaye kamar gaske.
“Faɗa suka yi da ƴar'uwarta shi ne wai ta watsa mata ruwan miya dake kan wuta”
“Amman gaskiya ya kamata ka sa ido sosai akan yaranka Uzair, irin wannan abun yana sa kisan kai fa”
“Ƙaddarori ne kawai idan Allah ya kawo abu”
“Allah ya tsare gaba, Ina uwargida har yanzu bata haihu ba?”
“Har yanzu fa”
“To Allah ya raba lafiya”
“Amin”
Tun da suka jero suke maganar basu rabu ba sai da ta kawo kusa da pharmacy sannan ta ɗauki wata hanyar shi kuma ya ciro wayarsa ya kira Hajiya ya faɗa mata, ita Rashida text kawai ya aika mata, sai kuma ya kama hanyar gida dan yi ma Ezzah hukunci.
Sai da ya kama hanyar gida sannan ya kira Kalsoom ya faɗa mata halin da ake ciki, dan yasan zata tashi hankalinta sosai.
Bugu ɗaya ta ɗauka.
“Kana ina ne?”
“Ina hanyar gida, na kaita asibiti da sauƙi”
“Na je gida ban samu kowa ba sai Ezzah tana ta kuka, sai ta biyo ni gani cikin asibitin ma”
“Oooooo Kalsoom miyasa baki ragawa kan ki ne? Ba fa ke kaɗai kike ba a yanzu, da izinin wa kika fita, yanzu da wannan tulelen ciki yama zaki yi driving?”
“Napep na hau”
Ajiyar zuciya ya sauke.
“Tau gani nan juyowa”
Ya katse kiran ya juya ya koma hanyar asibitin. Yana isa aibitin su Hajiyarsa na isa yare da Mama ladi (kanwar mahaifiyarsa) da ƙanensa guda biyu. Jerowa suka yi suna tafiya yana yi ma Hajiya bayanin yadda abun ya faru.
Kalsoom na hango shi tafe tare da Hajiya ta ji babu daɗi musamman dan tana tare da Ezzah tasan dole Hajiya za tayi magana wata ƙila ma zata ce ita ce ta haddasa wannan husumar. Duk sai ta rasa yadda zata yi ga tulelen cikin nan ya mata tsaye kamar wacce zata haihu yanzu.
“Hajiya ina wuni”
“Lafiya ƙalau”
Tana amsa gaisuwar da Kalsoom ta yi mata ta wuce bata ko bi ta kanta ba. Hilal ne ya tsaya gurin matarsa.
“Miya hana ki shiga?”
“Ban san ɗakin da aka kai ta ba”
“Tau muje”
“A'a sai Hajiya ta fito, kar ta gan ni da Ezzah”
“Cemin ta yi wai tana tsoron karka dake ta”
“Ai ba duka kaɗai ba karye ta ma zanyi, ba dai ke har kin kai ki ɗauki ruwan zafi ki watsawa ƴar'uwarki ba...?”
Sai kawai Ezzah tasa kuka ta kama Hijabin Kalsoom ta riƙe gamgam tana kuka. Hilal be bi ta kanta ba ya nufi sashen da zai sadashi da ɗakin Ulfah, Kalsoom ta rufa masa baya tana faɗin Ezzah ta yi shiru ba zata bari ya daketa ba.
Ko da suka shiga Hajiya na kusa da Ulfah dake bachi, tana duba ƙonuwar cike da tausayi, can jikin ƙofa Kalsoom ta tsaya tana kallon Ulfah, Ezzah na riƙe da Hijabinta har lokacin tana kuka. Hajiya ta ɗago ta kalli Ezzah cikin tausayi da ɓacin rai ta ce
“Amman Ezzah baki da zuciyar ƙwarai, ko ɗauki ruwan zafi ki watsawa ƴar'uwarki haka?”
“Wallahi ba nice ba Wallahi Mama Teema ce...!”
Ta faɗa cikin kuka.
[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *82*
Teema ta katsa mata tsawa tana zare mata ido alamar dik kika faɗa sai na ci ubanki.
“Ke karki min ƙarya, munafukar yarinya fitsararriya”
“Wallahi ba ni bace, ke kika kira ni kika ce na zo naje kitchen na duba Ulfah ta ƙone...”
Hajiya ta kalli Teema ta kalli Ezzah, ƙoƙarin ɗaukar maganar ta ke, sai kawai ta jiyo kukan Teema wai Ezzah ta mata ƙazafi.
“Wallahi ba zan taɓa yafe miki ba, makira kawai munafuka”
“Ezzah kike cewa haka? Sai kace wata babbar mace? To wai kina aikin me haka ya faru”
Cewar Hajiya tana sake da baki. Ta soma bayani tana kuka da kallon Hilal ko zai kareta ɗin nan.
“Ina cikin kitchen ina girki, na ƙare tuwo sai na ce bari na ɗora miya, sai na ce ta daga kamin daddawa ita kuma Ulfah ta gyara min tabarnuwa, ni ban san gardamar mi suke ba sai kawai naji an taɓa tukuyan miyar da ƙarfi sai ihun Ulfah na ji ina juyowa na ga ta juye mata miyar”
Izzah ta tuma ta dire ta sake tuma ta dire tana kuka da jan Hijabin Kalsoom tana faɗin ba ita ba ce, amman babu wanda ya kula ta Hilal in banda harara babu abunda yake mata, yana cike da haushinta sosai Allah ka ɗai ya san irin hukunci da zai mata idan suka koma gida. Sai kawai ta saki Kalsoom ta ruga gurin Hajiya tana kuka.
“Wallahi ba ni bace Hajiya...”
“Hilal ka saurareta mana”
Kalsoom ta faɗa cike da tausayin kukan da Izzah take yi.
Hilal ya girgiza mata kai.
“Ba wani saurare da za'a mata, ai kin san halinta”
Izzah har da faɗuwa take a gurin taɓa tashi ta kama gyalen Hajiya ta riƙe ƙam.
“Ba zaki rufewa mutane ba ki ba, Wallahi zan dake ki yanzu nan, ba sai mun je gida ba”
Hilal ya faɗa ciki fushi yana mai jin kamar ya kamata ya ɓallata gida biyu. Ihunta ne ya tashi Ulfah daman can ba wani dogon bachi ta yi ba, saboda zafin wuta ko an maka allurar ba bari yake ka yi bachi ba.
“Wayyo Allah Momie, Hajiya, Dady ka kai ni inda Momie ko Anty Kalsoom ko inda Hajiya, bana son gurin Mama Teema ta watsa min wuta, wayyo zafi dady zafi Mama Teema ta ƙona ni, Anty Kalsoom, Momie, Hajiya”
Sune ƙawai sabbatun da take tana murza jikinta sai da Hilal ya riƙe mata hannu. Suna haka sai ga Rashida ta shigo hankalinta a tashe, tana kallon Teema hawaye suka fara mata zuba.
“Ɗaya bayan ɗaya za ki bisu ki kashe, na sani Teema kaɗan daga halinki ne amman ki sani kin ci amana kuma kema amana sai ta ci ki”
Sai kuma ta juyo gurin Kalsoom tana kuka, itana Kalsoom ɗin kuka take, Hajiya ma haka, balle Teema dake ƙoƙarin kare kanta, ƙanen Hilal ma babu wanda baya hawaye.
“Kin ci amanata, sai da na ce miki ki riƙe min yara na amman kika ƙi, yanzu ga shi abunda ya faru, bana da kowa a duniyar nan sai su, su ne farinciki na”
Jakar da ke hannunta ta saki ta nufi gurin ƴarta dake sabbatu, magangun ɗazu kawai take maimaitawa. Rashida ta gadon ta riƙe tana kuka.
“Laifina ne, nice ban riƙe mutuncin aurena ba, ni na kasa zama da ku ni na cuceku Ulfah laifi na, kuma na ci amanar matar da ke riƙon ku tsakani da Allah...”
Ezza ta yi gunta da kuka.
“Momie Wallahi ba ni bace, Dady ya ce sai ya raba ni gida biyu.. Wallahi ba ni ba ce”
“Ba zan ɗauka ba, wannan ba zata kwanta jinya ba, ka kama wannan ka karya min ba, ka saurareta Hilal Wallahi ba ita ba ce, karka ɗauki alhakin yarinyar nan Hilal”
Cikin kuka Rashida take maganar gwanin ban tausayi. Hajiya ta share hawayenta tana kallon Ezzah.
“Miya faru faɗa mana”
Ras Ezzah ta zana musu abunda ya faru, duk wani tsoro na teema yau baya tare da ita, tun da ta ji zancen Hilal yace zai raba ta biyu. Duk suka cika da mamaki sai kawai Teema ta ƙara rushewa da kuka, Hajiya ta girgiza kai tana faɗin.
“Amman Fatima kin ban mamaki, kw da ake yabo da salla?”
Hilal yayi saurin ɗaga mata hannu.
“Hajiya dan Allah kar ayi maganar nan a nan, asibiti muke, kullum sai ace nine family na cikin matsala”
“Kai dalla gafara can, kai har yanzu baka san ciwon kanka ba akan ƴaƴanka, ko wace mace ka aura da irin azabar da take gwadawa ƴaƴanka, Kalsoom ta kashe Rafiq wannan kuma tana ƙoƙarin kashe Ulfah wannan wane irin masifa ce”
Rashida ta kalli Hajiya tana hawaye.
“Wallahi ba Kalsoom ba ce ta kashe shi, Wallahi nice ni na kashe ɗana da kai na...”
Sai duk kallo ya koma kan Rashida har Kalsoom ɗin kallonta take. Hajiya tasa wani dogon numfashi ta sauke ta ce
“Muje gida mu yi wannan maganar, Hilal muje gidanka a yi wannan maganar, Ke ki tsaya nan ki kula da Ulfah”
Ta faɗa tana kallon ɗaya daga cikin ƙanensa, sai kawai ta nufi ƙofar fita tare da tawagarta. Rashida ma fita tayi ta rufa musu baya dan ta shirya fasa ƙwan yau kam, bata san gidan Teema ba dan haka ta nufi tsohon gidanta kuma gidan Hilal inda Kalsoom take zaune. Hilal kan sai ya bawa ƴarsa magani tare da allura ta koma bachi sannan ya sako matansa gaba suka kama hanyar gida. Ko da suka shiga falon Hajiya na zaune falon tana jiransu, Ezza kuma na riƙe da Hijabin Kalsoom kamin ta saketa ta nufi gurin uwarta da gudu.
“Maimata abunda kika faɗa ɗazu ko kina da wata shaida”
Cewar Hajiya tana kallonta. Rashida ta girgiza kai.
“Bana da wata shaida sai Allah da kuma Teema, amman Wallahi Kalsoom bata da hannu a mutuwar Rafiq, ni naja komai”
“Kamar ya ki fito ki yi bayani mana”
Hilal ya katsa mata tsawa, Teema ta yi saurin saka baki.
“Karki ci amanata Rashida ni ban san komai akan ɗan ki ba”
Rashida bata kulata ba, ta soma koro da bayani.
“Bayan da Hilal ya sake ni, sai na riƙa zagaya makarantar su Ezzaha ina zana mata irin makirci da rashin kunyar da zata yi ma Kalsoom, ina tunani kamar idan ta yi hakan zai tausaya musu ya dawo da ni, da naga hakan be samu ba, sai na koma bin bokaye, ina neman yadda za ayi Kalsoom ta bar gidan Hilal kuma ya dawo gareni, naje wanu gurin aka mata magani aka sako mata jini, cikin dake jikinta ya kwanta ya ɓace bat, na sake komawa na yi mata wani a wannan karon be faɗa kanta ba, ya faɗa kan ɗa na Rafiq, ni kai na ban san ya faɗa kansa ba, har sai da naje na kaiwa Teema kukana ta kaini gurin wani malami shi ya faɗa min cewar na yi magani ma kishiyata ya faɗa kan ɗa na, shiyasa a asibiti aka rasa gane kan wannan matsalar sai ya nuna guba ne sai kuma ya nuna gas ne, ba komai ba ne sai sihiri. Duk wani shige-shige da nake na magani tare da Teema nake yinsa, ta kai ni gurare da dama, saboda ta fini sanin bokaye, nayi mamakin da aka ce Hilal zai aureta saboda na san an gudu ba a tsira ba ne. Sai dai na ɗauki hakan a matsayin cin amanar aure da nayi na keta haddin Allah na tozarta aure, dole nima Allah ya tozarta ni, na ci amanarki Kalsoom na yi ta miki abubuwa ko a zaman da muka yi da ke a gidan nan, ashe ma ke ƴar'uwata ce ba kishiya ba...”
Kuka take sosai ita da Kalsoom da Teema, sai dai ko wannensu da abunda yake yi ma kuka. Kalsoom babu komai a zuciyarta sai farincikin yau Allah ya wanke ta da kuma tausayin Rashida da ƴaƴanta.
“Na yafe miki Rashida, Wallahi na yafe miki har a bada, kuma na miki alƙawarin zan kula miki da ƴaƴanki fiye da yadda ke zaki kula da su, amman idan Hajiya ta yarda”
Kalsoom ta faɗa tana kallon Hajiya data soke kai tana hawaye.
“Haƙiƙa na cutar da ke Kalsoom, na miki kurkuren fahimta, na ɗauki alhakinki, na cutar da ke matuƙa, Wallahi na ji kunyar kai na sosai”
“Haba Hajiya ai ko nice a matsayin da kike kwatankwacin abunda zan aikata kenan, saboda gaskiya ba ta bayyanaba a lokacin kuma ɗan adam da zahiri yake aiki sanin baɗini kuwa sai Allah, ni dai abunda kawai na ke so ki yarda da ni kawai”
“Wallahi na yarda da ke ɗari bisa ɗari kalsoom, kuma daga yau yaranki gurinki zasu zauna. Teema baki yi ƴa ba, kin bani mamaki, ina gani kamar na ɗauko ma ɗauka mutuniyar kirki ashe ɓara gurbi ce”
Kuka sosai Teema take ta sauka daga saman kujera ta zauna ƙasa kusa da Hajiya ta kama ƙafafunta.
“Wallahi Hajiya ƙarya take min, na miki alƙawarin zan canja daga yau, ba zan sake yin wani abu marar kyau ba”
“Nasa Hilal ya aure ki ne saboda ita tunanin ke ta ƙwaraice, Fatima ko da mun zauna da ke babu aminci a tsakanin ke da mijinki da ƴaƴansa da kuma ni, mace mai shige-shigen malamai iya mata sai Allah karki je ki yi mana irin na Rashida, kin ga ƙara a rabu tun abu be yi nisa ba, kije can Allah ya haɗa ki da rabon ki, ni kan Hilal ba dan kar na zama uwar banza ba da na baka shawarar rabuwa da yarinyar nan...”
Ta ƙarasa tana kallon Hilal. Shi kan uffan be ce ba sai kallon pop yake abun duniya ya taru ya tsaya masa, idan ya shiga wannan ya shiga wannan. Miƙewa ya yi tsaye ya fice cikin rashin daɗin rai.
Bayan fitarsa Hajiya ta miƙe ta fita, ta bar Teema na kuka, Rashida kuma na hawaye. Bata yi minti talatin da fita ba Rashida ta tashi ta fice, a lokacin ne Teema ta kalli Kalsoom ta ce.
“Zan taimaka miki ki haihu, nasan hanyoyin da zan bi ki haihu, wannan cikin na ki yanzu shekarar ɗaya da wata huɗu cikin na biyar, amman idan kika taimaka min kika hana Hilal ya sake ni, ina son ki saka baki a lamarin auren mu domin a yanzu na fuskanci kina da ƙima a gurinsa da kuma mahaifiyarsa fiye da ni”
Ido kawai Kalsoom ta sakar mata tana kallon ikon Allah, ta ya zata ce ta kaita wani gurin bayan yanzu aka gama rigimar tana bin bokaye, ita bata ma tsoron wani ya ji. Kamar daga sama suka ji muryar Hilal da ke tsaye bakin ƙofa rumgume da hannayesa a ƙirji yana kallonsu, dan sam basu san da shigowarsa ba.
“Kalsoom bata iya shige-shige irin na ku ba, kuma idan lokacin haihuwarta yayi zata haihu, ke ai naga haihuwar kike nema miya hanaki bin bokayen su baki haihuwa?”
Ta miƙe tsaye yana kallonshi.
“Haihuwar da na ke so Hilal saboda kai nake son ta, ina son na haihu da kai saboda ina ƙaunar ka ne, yanzun kuma abunda nake ƙoƙarin yi ma saboda ina ƙaunarka ne Hilal, miyasa ka kasa ganin haka? Tun kana mijin Rashida na ke mafarki miji irin ka saboda kana kula da ita yadda ya dace, ashe ma Allah yayi sai na kasance ɗaya daga cikin matan ka, ka tausaya min Hilal, zan iya yi maka alƙawarin ba zan sake bin ko wane malami ba indai wannan ce kawai matsalar...”
Ta ƙarasa tare da risinawa kamar mai neman gafara.
“Ba wannan ce kawai matsalar ba, ko na zauna da ke ba zan aminta da ke ba, kuma mai hali baya fasa halinsa, ai yanzu aka gama wannan rigimar amman kika ɗaga ido kika kalli Kalsoom har kina neman ki taimaketa, dan ta saka kar na sake ke, kin manta ita da ke duka a ƙarƙashin kulawata kuke? Hajiya ma dake gindaya min sharaɗi yin abu ko hani ta bani umarnin idan na ga dama na sake ki, tun dan me zaki dawo gurin Mamata kina neman ta taimake akan abunda zan iya yanke hukuncinsa yanzu?”
Kalsoom ta girgiza masa kai.
“Saboda ta san zan iya saka ka yi ne...”
“Kalsoom karki saka bakin ki cikin wannan maganar please”
Teema ta hasala ta miƙe tsaye cikin ɓacin rai da zafin zuciya.
“Ka daɗe baka sake ni ba Hilal, ni wannan wuƙancin da Rashida take ɗauka ni bana ɗaukarsa, sai kace kai ne kaɗai na miji ana magana kana ƙara butsewa, ka sake mana ai ni tafi nono fari, zaman gidanka ko zaman wahala haka kawai za ku ɗauko ni wani kula da yara wato ga ƴar aiki kenan ko saboda an maida ni shim mai ruwa uku sha-sha-sha, da ƙurciyata na lalata kaina gurin gina rayuwar ƴaƴan wata nawa ko zuwa duniya ba su yi ba”
“Shiyasa kike cutar da su? To Allah ya toni asirin ki, kuma ki je na sake ki saki ɗaya...!”
“Ai ni da uku ka yi da ka fi burgeni”
“Ɗayan dai zan miki ƙyaji da shi”
“Tafi nono fari, ai ba kai ne autan maza ba”
“Na sani shiyasa na sake ki saboda ki samu damar auren wani”
“Aiko zaka gani dan sai kasan kayi hasarar mace irina”
Ta kaɓe masa Hijab ɗinta ta fice kamar zata tashi sama.
“Hakan be dace ba Hilal kana wasa da saki, daga wannan maganar zaka ce ka saketa kuma kana ganin yadda take ta lallaɓaka akan ka barta ɗakinta...”
“Na faɗa miki babu ruwanki da irin maganganun nan, kin cika salo da saka kanki cikin irin lamurran nan shiyasa komai aka yi sai a kin saka bakin ki shiyasa komai ake ɗora miki laifi”
“Amman....”
“Na ce ki min shiru ko?”
Uffan bata sake cewa ba sai ta cigaba da wasa da kan Ezzah shi kuma ya juya ya fice.