Dad yana karasowa gun ya kalli Ammar wanda ya kauda kai, yace " me kakayi anan bayan a ciki ya kamata in ganku?"
Seemah ta matso kusa da Dad tace " Dad ni na fito dashi, kayi hakuri."
Ammar ya kalleta yace " Dad taya za'ayi ace Abba ya kore Seemah daga ciki? Ban fahimci me hakan yake nufi ba."
Da sauri Seemah tace " Dad ba wani abun bane, Ya Ammar kaya ya d'au abin da zafi ne."
Jikin Dad yai sanyi ya kalli Seemah cikin tausayinu sannan ya maida idansa kan Jalal harzai mai magana ya fasa ya juya tare da cewa Seemah muje ciki, itakam idanunta nakan Jalal shikansa kallanta yakeyi, kallan juna suke cikin wani yanayi, Ammar ya kalli yanda Seemah ke kallan Jalal jiyai ransa ya sosu, Dad ya juyo ganin Seemah batada alamar tahowa, Dad a harzuk'e yace " Seemah wuce nace ko?"
Dasauri tace " to dad." Tana juyawa Jalal yace " Dad inada magana."
Dad ya juyo ya bugamai wani kallo, ba shakka Jalal yananan kamar yanda yasanshi, sai dai yasan dabadan abinda ya faru ba yasan da amintarsu da Ammar bazata rabu ba.
Had'e rai yace " Jalaludeen sunan ka ko?"
Jalal ya d'aga kai yace " Eh, amma ban fahimci menene dalilin dayasa kaje har gidanmu kacima mahaifina mutunci ba."
Dad yace " me kace?"
Ammar ya matso yace " kai gyara bakinka wani shirman kake fad'a?"
Seemah ta kalli Jalal sannan ta kalli Dad tace "Dad kaje gidansu ne?"
Dad dake kallan Jalal yace " ka koma ka tambayi mahaifinka abinda ke faruwa bawai kazo nan kanamin shirme ba."
Jalal ya kalli Dad yace " Na d'auka maganar ni da Seemah a tsakanin mu zai tsaya amma yaza'ayi kamar kai kaje har ka shake mahaifina? Me yayi?"
Dad yai d'an wani murmushi a ransa yace " Jalal kenan bai mantashi ba halayensa nanan, tun yana karami baya shakkar tambaya."
A fili yace " bakaji amsata bane? Nace ka koma ka tambayi mahaifinka wanda a fili za'a d'auka mutumin arzik'i ne amma a zuciya" ya jijiga kai......
Ran Jalal yakai matuka gun tunzura, Seemah ta kalli Jalal ganin yanda idanunsa sukai yasa jikinta yai sanyi, Kallansa tai idanunta sun cika da kwalla, Jalal ya kalli Dad yace " ban fahimci kalamanka ba? Kasan mahaifi nane? Ko kuwa a ganinsa dakai yau shine yasa kake fad'ar haka?"
Dad ya kalleshi yace " indeed you are smart tunda har kai tunanin haka, sai ka koma ka tambayi Amadu ko ya sanni."
Amadu? Jalal ya maimaita, ba shakka wanda yasan Abba ne yake fad'a masa haka, to amma ta ya? Dad ya kalli Ammar dake jin kalamansu cike da mamaki yace " Ammar muje ko? Ina bukatar ganin Hajiyata."
Bai jira abinda Jalal zai fad'a ba yai gaba, Ammar ya bishi a baya, Seemah ta kalleshi tace " Deen meke faruwa?" Kallanta yai idanunsa a kad'e yace " Meemah I don't know, ni dai kawai ancemin Dad d'inki yaje gida har shakema Abbana wuya yayi, shiyasa nazo inji, to amma yanzu I am confused, ya akai Dad yasan Abba?"
Seemah ta kalleshi jiki a sanyaye, tace " Deen nasan Dad d'ina kwarai, duk da nasan bayasan alakarmu hakan bazai sa ya shakema Abba wuya ba, akwai dai wani abun."
Jalal ya d'ago ya kalleta jiki a sanyaye ya jinjina kai yace " karki damu kije gun mara lafiyar."
Yana kai nan ya juya, har yad'anyi nisa tace " Deen?" Tsayawa yai tare da juyowa ya kalleta ta matso kusa dashi kad'an tace " Can you promise me something? " kai yad'an langwab'ar tacigaba " can you promise me you will always love me?"
Wani sansanyar murmushi ya sakar mata ya lumshe ido sannan yace " u are my first love how can I stop loving you? "
Itama murmushi tai tace " yazanyi ind'ingajin muryarka bani da waya?"
Wayarshi ya mik'a mata tare da zare layinsa dayake amfani dashi yabar Etisalat d'in da ba wanda yasanshi dashi dama saboda browsing yake amfani dashi.
Ta kalleshi sannan ta kalli wayar tace ta meye? Yace kiyi using wannan ni nasai wata.
Murmushi tai harsai da fararan hak'oranta suka fito tace " karka damu nasan yanda zanyi inada idea."
Yad'an harareta kad'an yace a hakan? Tace zaka gani.
Tana kainan ta juya ta fara tafiya, tsayawa yai kawai yana kallanta zuciyarshi tayi wani sanyi.......
Dad kam yana shiga Abba yace " Isma'il tund'azu ina ka tsaya Hajiya na nemanka?"
Da sauri Dad ya matsa gunta, ya rik'e hannayenta, tana ganinshi ta rike hannunsa itama tace " Isma'il nasani ka ga rayuwa, kaga tashin hankali duk da dai muma mun gani a shekara 20 data wuce, sai dai abinda ka gani bai kai namu ba."
Dad ya kalleta sam yamanta da Habib da Ammar agun d'an hankalinshi nakan mahaifiyarsa, Hajiya ta cigaba" nasani haryanzu bakamanta azal d'in daya fad'a maka ba, 'yan gari sun tsaneka saboda abinda bakai kayi ba, matarka mahaifiyar 'ya'yanka wannan abin shine ajalinta, wannan dalilin yarabaka da kasarka muma dole ne yasa mukabar garin."
Tai ajiyar zuciya tare da share hawayen dake zubo mata, ba itaba hatta mamie da Dad hawaye suke, Ammar kam da Habib kallansu kawai suke mamakin kalaman nan suke.
Hajiya tasa hannu ta share mai hawayensa tace " kuma duk abinda ya faru dakai Isma'il ka rik'e yarinyar nan amana....."
Kawo ya kalleta yace " ya isa Karki kara tada ma kanki hankali ki kuma k'ara tadama d'anki."
Kallan Isma'il tai zatai magana numfashinta ya fara yankewa Dad ya rik'ece yace " a yi sauri ka k'ira Likita." Duk ya rikice Habib yai saurin fita, Yana bud'e kofa yana fita, yaga Seemah tsugunne a waje, bai kulata ba yai sauri yai gaba.
Ammar kam gaba d'aya kwakwalwarsa ta rufe, meke faruwa? Me kalaman Hajiya ke nufi? Wa aka rike? A iya saninsa 'yar Dad mace d'ayace Seemah to mekenan?
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
_This page is for you my Yar uwas, my cwty my chocolates, much luv to you😍 Maijiddah_
ayushermohd.blogspot.com
No. 4⃣2⃣
Seemah kam gaba d'aya kanta taji yana wainawa, bata fahimci inda maganar ta dosa ba saboda ta baro gun Jalal tazo zata shiga ta tuna d'azu ance ta fita, hakan yasa ta jingina da kofar sai dai adaidai lokacin taji Hajiya tace " Kuma duk abinda ya faru dakai Isma'il kuma ka rike yarinyar nan Amana."
A iya saninta mahaifinta ne Isma'il to wace yarinya ya rik'e amana?
Dawowar Habib da likita ne yasa itama ta mik'e ta wuceta sukai da sauri, tabishu da kallo tare da tsayawa a bakin kofar, Duk 'yan d'akin sun rikice ganin yanda jikin Hajiya ya tashi sosai, sai dai har yanzu hannunta kankame yake dana Dad, likita na zuwa suka shiga kok'arin daidaita numfashinta, sun wahala sosai ganin jikin ba dad'e yasa sukace kowa ya fita ya barsu, nan Dad suka fito kowa jikinshi a sanyaye, idanun kowa ka kalla kasan suna cikin tsananin tashin hankali, Dad na fitowa yaga Seemah a tsaya tana hawaye ganin yanda jikin hajiya yake, hannun ta ya kama sukai waje.
Nan aka rufe kofar, kowa yayi jugum yana addu'oi, sai da likitocin sukai minti 30 kafin su fito, suna share zufa, Abba da Dad da kawo suna ganinsu suka matsa kusa dasu, Abba yace " ya jikin nata?"
Likitan yace " kushiga sai dai kuyi a hankali karku kuskura kuyi abinda zai tada mata hankali ko taga abinda bataso, yin hakan babbar matsala ce, sannan kar ad'inga hayaniya a kusa da ita.
Suna kai nan sukai gaba, Habib ya matso kusa yace " Abba ya kamata ku koma gida, munyi yawa a asibitin gudun hayaniya ya kamata ka d'auki Mami da kawo ku koma gida, shima Ammar ya d'au Seemah su tafi inyaso ni zan zauna anan."
Abba yace " haka ne amma sai dai zuciyata bazata iya kwanciya ba in na tafi."
Kawo yace " nima kunsan bazan iya zuwa wani gun ba inbar matata anan ba."
Sunyi shiru kafin Dad yace " mu zauna anan ai mu ba maganar da zamuyi, kai Habib ku koma gida."
Habib ya kalli Dad yanasan yai musu anma yana tsoro, Dad ya kalli Kawo yace "kawo kaima kaje gidan yaya kai wanka kaci abinci inyaso da daddare sai ka dawo."
Haka suka yanke shawara Dad da Abba suka shiga ciki, Habib ya kalli Ammar yace " Ammar ka d'au mami da kawo gida."
Mami ta kalli Seemah itakam kasan ranta tana tausayin yarinyar tace " Mu wuce da Seemah ma kwana acan, sai ta kwana gun Zara."
Seemah ta kalleta jiki a sanyayi, Mami ta d'aga mata kai tare da mata murmushi, Ammar ya kalli Seemah sannan yace "muje kawo."
Sun fita Habib yabi bayansu da kallo, bayaji zai bar asibitin nan, juyawa yai ya shiga ciki, Dad da Abba na zaune jugum-jugum.
Ya koma gefe ya zauna.
Jalal kam yana fita daga asibitin ya shiga k'iran wayar Abba, sai dai bai d'aga ba, hankalinsa ya tashi ya rasa me ma zaiyi ga shi gobe monday yanada aiki bare ya tafi birnin/gwari yanzu, ga yamma tayi.
Haka ya cigaba da gwada number Abba sai can harya cire rai sannan yaji an d'aga, da sauri yace " Abba?" Jiyai ance " waye?" Da mamaki Jalal yace " ba number Abba bane?" Mutumin yace " wlh bamusan wayar waye ba d'azu muka ganta a shagon nan k'ila wani ne ya mantata."
Jalal yace " ina ne nan d'in?"
Mutumin yace " gurin buga kati ne."
Gaban Jalal ya fad'i wato da gaske Abba yake? Ya d'aure yace " ku ajiye wayar zan k'ira azo a amsa."
Nan sukai sallama, Jalal ya k'ira number Umma, sai data kusa katsewa ta d'aga tare da Sallama, Jalal ya amsa tare da cewa " Umma d'am Allah Abba fa?"
Tace " ya fita yanzun nan yamanta wayarshi a shagone shine yakesan yaje ya duba."
Jalal yai ajiyar zuciya sannan yace " Umma d'an Allah kinsan wani Alhaji Isma'il?" Yai tambayar cikin sanyin murya.
Umma kam gabanta ne yashiga dukan uku-uku, tace " Jalal anya kuwa?"
Yad'an jinjina kai sannan yace " maybe ke baki sanshi ba amma ba shakka Abba yasanshi, bakomai bari in kara neman Abba."
Dasauri Umma tace " Jalal ba ruwanka, karka kuskura ka tambayi mahaifinka Malam Isma'il."
Da mamakin kalamanta Jalal yace " Malam isma'il? Da alama kema kinsanshi kenan, d'an nidai a sanina Alhaji nace ba malam ba, kuma daga yanda kika fad'i sunan Umma ya nuna kinsanshi."
Umma ta had'iyi yawo tace " Jalal ka rufamana asiri d'an Allah kabar yarinyar nan, in a da ina tunanin zai iya yiwuwa ka aureta sai dai yanzu......"
Tana zuwa nan tai shiru idanunta suka zubo da kwalla, ganin tana alamar kuka yasa ta katse wayar tare da zana a gun, tace a filin Jalal yazamuyi? Ya Allah gani gareka!!
Abba ne ya shigo tare da kallanta yace " menene kuma?" Umma ta taso tazo kusa dashi tace " Malam ya zamuyi? Jalal fa yasan kasa Malam Isma'il."
Abba sai da jikinsa ya amsa, ya kalli Umma kawai ya shige d'akinsa, yawo ya farayi a tsakar d'akin "Yasan Halin Jalal sosai, idan yaji abinda na aikata ta dalilinsa bana tunanin zai tab'a yafe ma kansa."
Idanu ya runtse ya tuno laifin daya aikata saboda tsoron kar a tab'amai d'ansa, bai taba tunanin abinda ya aikata zaizo ya damesu a wannan lokacin ba, shi daga baya ma yafara tunanin ko rashin lafiya da zaheera ke fama dashi alhakin abinda ya faru ne, yasani sosai ya aikata lefi mai karfi anma ya zaiyi?
Jalal kam wayarsa yabi da kallo mamaki kalaman Umma ne suka dameshi, lalai akwai wani abun a kasa kuma dole ne yasan menene wannan abun, tunani yafara gun Dad yakamata ya koma ko gun Abba?
Ajiyar zuciya yai yace " Abba zaiyi wuya ya sanar dani, zan kara komawa gun Dad inji ko shi zai fad'amin." Da wannan shawarar ya shiga cikin d'akinsu.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 4⃣3⃣
Seemah kam tunda suka shiga mota ba wanda yai magana kowa da abinda ke damunsa, har suka isa gidan itadai Seemah kanta na kasa bayan sun isa mami da kawo suka fita Seemah ta kalli Ammar tace " yaya ni kad'ai zan kwana anan?"
Murmushi ya mata yace " ke kad'ai ce anan d'in? Ga Zahra ga mami nan?"
Tace " kasan bamu saba ba please ka shigo kaima saika kwana gun Ya Zaid inkananan sai hankalima yafi kwanciya."
Yai shiru shidai sam bayasan kwana a gun Zaid saboda Zaid hana shi bacci yakeyi ya d'inga mai surutu kenan sannan in 12 tayi kuma sai ya shiga waya da 'yan mata sam ya hanashi bacci, amma ya zaiyi? Bazai bari Seemah ta takura ba.
Seemah ta kalleshi jin shirun yayi yawa tace " Yaya na!!!!"
Ya kalleta yace " to kanwata muje ko?"
Wani dad'i ne ya kamata sannan ta bud'e motar ta fito.
Tare suka shiga Falon, Zara na tsaye a bakin window dama tunda mami tace da Ammar sukazo take lek'ensa, ganin ya fito yasa ta kara gyara fuskarta ta tsaya a bakin kofa.
Suna kwankwasa wa ta bud'e tare da wayancewa tace " Seemah na d'auka sai nazo na d'aukoki da kaina." Seemah tad'anyi yake tace " Zara ya kike?" Lafiya ta fad'a sannan ta kalli Ammar tace " laaaa Ya Ammar ai ban kula da kaiba."
Hararar wasa ya mata yace " anya kuwa kanwata? Bayan naga haske d'azu ta mota kamar da mutum a tsaye ta labule yana lek'e?"
Idanu ta rufe tace " kai yata bansan waye yake lek'e va."
Dariya Ammar yai yace gaskiya kam da alama ku 2 ne a falon.
Ta turo baki tace " yaya ai ko ka sani sai ka basar haka fa akeyi."
Seemah tai kasa dakai tana wasa da 'yan yatsunta, Ammar baiba Zahra amsa ba yace " kanwata kuje ciki kiyi sallah nima bari nai sai in dawo muyi hira ko?"
Kai Seemah ta d'aga alamar eh, Ammar ya kalli Zahra yace " Zara a kuma kularmin da kanwata."
Bai jira amsartaba yai waje, Zahra tabi bayanshi da kallo tana Murmushi sai daya fita sannan ta kalli Seemah tace " muje ciki." bata amsa ba kawai itama ta fara binta sun shiga d'aki Zahra ta nuna mata toilet, Seemah ta wuce ta shiga.
Tsaye tai a toilet tana kallan kanta a madubi, itakad'ai tasan me takeji a zuciyarta, Deen zai yi aure? Ta maimaita kalaman Zainab data mata a waya, hawayene ya ziraro mata ga mamakinta jitai kuka ya b'arke mata sosai, tsugunnawa tai kawai tana kuka.
Zahra dake d'aki ta na jiyuta matsowa tai jikin toilet d'in tace " Seemah menene?"
Kuka sosai takeyi Zahra mamaki ya kamata ta dad'e tana bugawa amma bata bud'e ba, Seemah kam ta dad'e tana kuka kafin ta daina, ita dana saninta d'aya dama batazo kasar ba kwata kwata da bata had'u da Jalal ba bare har sanshi ya kamata haka.
Alwala tai ta fito, Zahra ta kalleta tace "Seemah menene?" Jijiga mata kai kawai tai alamar a'a ta wuce ta d'au sallaya.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
A asibiti kuwa Hajiya ta samu bacci mai karfi saboda allurar da aka mata, da daddare Habib da saninshi ya kwanta yai lamo kamar bai bacci, Abba ganin kamar Habib yayi bacci ya kalli Dad yace " Isma'il inada magana da kai."
Dad ya kallleshi yace " inaji."
Abba yaja numfashi sannan yace " Isma'il tambayar dai dana maka shekara ashirin da suka wuce ita nakesan in sake maka, Isma'il tsakaninka da Allah bakasan mahaifin Seemah ba?"
Dad ya kalli Habib ganin da alama bacci yake yace " yaya wlh wlh bansan komai akai ba, sau nawa kakesan in rantsema." Ajiyar zuciya yai sannan yace "yaya kasan wa nagani yau?"
Abba ya girgiza kai, Dad yace " Amadu nagani."
Mik'ewa Abba yai yace " dafatan kasa an rufe mana shi?"
Dad yai tsaki yace " ai ni abinda nagani yasa ma nakasa mai abinda ya kamata, kasan mahaifin waye?" Abba ya girgiza kai, Dad yace " wai mahaifin Jalal d'in da Seemah keso ne."
Da mamaki Abba ya koma ya zauna yace " mene? JALAL? Taya hakan zata faru?"
Dad ya runtse ido yace " kabari kawai Yaya abin ya d'auremin kai, ko ya akai Jalal har yazo company d'in mu yana aiki har suka had'u da Seemah? Har hakan ta faru?"
Abba yace " Ikon Allah kenan, amma ai yanzu komai yazo gidan sauki, shi kansa Amadun ai ko kace ga Seemah ka bashi bazai aminta ba."
Dad ya kalli Hajiya bai kara magana ba.
Habib kam ya gama daskarewa agun da yake, meke faruwa? Ba Dad bane mahaifin Seemah kenan, sannan me? Bai masan mahaifin Seemah d'in ba? Meke faruwa kenan? Sannan mahaifin Jalal mene?"
Inaaaaa ai ko mai zai faru dole ne gobe a bashi amsoshin tambayoyinsa d'an kuwa shine babban d'a kuma dolene yasan sirrin gidan su, bazai kara bari a sashi a cikin tunani haka ba.
Jalal kam kwata kwata idanunsa basuga bacci ba zuciyarshi cike take da tunanuka kala kala, me ake nufi da Abba yasan Dad? Fitowa yai daga d'akinsu bai damu da daren dayai ba a waje ya zauna yai shiru yanaso zuciyarsa ta bashi amsar tambayoyinsa sai dai sam ya kasa lissafo komai abu d'aya dai daya tabbatar ma ransa shine, tabbas Dad yasan Abba kuma alak'ar dake tsakaninsu ba wai alak'ace ta mutunci ba, yazaiyi da auransa da ake shirin yi ranar asabar?
B'angaren Seemeh kuwa tana zaune a falo kusa da Ammar, Zahra nata jansa da hira, itakam Seemah a zaune kawai take ba ta sa musu baki ba, can Ammar shirun Seemah yafara damunsa ya kalleta yace " Kanwata menene?"
Kallansa tai batace komai ba, Zahra cikin zolaya tace " ba dai kuka zaki sake mana ba ko?"
Seemah ta kalleta kawai tai kasa da kanta, Ammar jin haka yasa ya kalli Seemah yace " kanwata kuka ki kai?" Shiru tai hakan yasa Ammar yagane matsalar, Zahra ya kalla yace " Zahra d'an bamu guri muyi magana please. "
Zahra ta kallesu sannan ta mik'e jiki a sanyaye ta fita, Ammar ya kara matsowa kusa da Seemah yace " Kanwata menene?"
Idanunta ne sukai rau rau tace "yaya kaima kasani ai."
Goshinsa ya rik'e yace "oh God Seemah akan Jalal ne?"
Kallansa tai cikin kalar tausayawa tace " yaya dama banzo kasar nan ba."
Murmushi yai yace " Seemah kenan."
Ta kalleshi tace " Yaya inasan intambayeka wani abu, d'azu naje shiga d'aki naji ana zancen Dad duk abinda suka mai wai kuma ya rik'e yarinyar amana."
Tai ajiyar zuciya tace " Yaya ban gane kalaman me suke nufi ba."
Ammar yai shiru can yace " Seemah ni kaina ban fahimci inda kalaman nan suka dosa ba, a farko na d'auka da ni suke to amma daga baya na gane ba ni bane, to amma me kalaman suke nufi?"
Ta jinjina kai tace " mu tambayi Dad gobe sai muji ko?"
Kai ya d'aga alamar eh
...
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 4⃣4⃣
A daren ranar Jalal da Habib idanunsu basuga bacci ba.
Washegari ya kama litinin, Habib zaune a d'akin da Hajiya take kallan Abba da Dad kawai yake yana tsananin mamakin yanda suka iya b'oye wannan sirrin batare da sun sanar ba, bayan ya gaidasu ya koma gun Hajiya ya zauna ya kalli Dad yace " Dad bari naje gida in dawo sai kuma kuje."
Abba yace to in kaje daga nan ka biya tagurin Mamie ka amso min sak'ona, Habib yace "to" sannan ya mik'e ya fita.
Agoggon Hannunsa ya duba karfe 7 na safe kenan, gida ya wuce yai wanka ya sa kaya sannan ya fito, gidan su Zaid ya wuce.
Bayan ya isa a bakin gate yaga Ammar, nan suka gaisa sannan Ammar ya tambayeshi jikin Hajiya, Habib yace " Da sauki, sai dai inasan magana da kai."
Ammar ya kalleshi da mamaki yace " akan me fa?"
Habib ya dafa kafad'ar sa yace " inaso ne kazo kuje gurin Mamie ina tunanin a wannan lokacin ita kad'ai ce zata warware mana abinda ke faruwa."
Ammar ya jinjina kai yace " ni kaina ban fahimci kalaman da Dad da Hajiya sukai jiya ba kuma da alama mu 2 ne kawai bamu san me suke nufi ba a d'akin."
Habib yai shiru can yace " Nagano maganar akan Seemah ne duk da bansan gaskiyar abinda ke faruwa ba."
Gaban Ammar ne ya fad'i ya kalli Habib yace " amma yaya........"
Habib ya katseshi yace karka damu mud'ai je ciki tukunna.
Nan suka shiga cikin gida, Zahra suka gani tana goge goge tana ganin Ammar ta mik'e tare da gaidasu, Habib yace " Zahra ina Mamie?"
Ta amsa da "tana d'aki."
Basu kara mata magana ba sukai hanyar d'akin mamie, sun isa suka kwankwasa, daga ciki Mamie tace su shigo, nan Habib ya murd'a kofar tare dayin sallama, Mamie ta amsa tare da mik'ewa ta rufe littafin Husnul Muslim d'in dake hannunta.
Ta kallesu tace " Habib kai ne?"
Habib ya shiga tare da zama a kasa kusa da inda take, Ammar ma ya zauna nan suka gaidata ta amsa fuska a sake tare da tambayar jikin Hajiya.
Sunyi shiru kafin can Habib yace " Mamie jiya da daddare sam idanuna sun kasa runtsawa tunani kala-kala sai daga karshe zuciyata tabani amsar tambayoyina."
Yai shiru bayan yazo daidai nan a kalamansa, Mamie ta kalleshi tace " ina jinka Habibu, mecece amsar?"
Habib yai ajiyar zuciya ya d'ago ya kalli Mami.
Daga d'aki kuwa Seemah ce ta fito daga toilet, tai saurin sa kaya ta fito a falo taga Zahra tace" Zahra ina ya Ammar? "
Zahra tace " yanzu sukai d'akin Mamie shida Ya Habib."
Murmushin farin ciki tayi tai hanyar d'akin da sauri fuskarta d'auke da murmushi tazo daidai zata kwankwasa kofar taji muryar Habib yace " Mamie da farko dai na gano abubuwa guda 2, na farko Seemah ba 'yar Dad bace, sannan abu na biyu babu alak'ar jini tsakanin Mu da Seemah wannan dalilin ne yasa Dad yake san had'ata aure da Ammar."
Tunda Habib yafara magana Ammar yake kallansa idanunsa cike da tsananin mamaki, kallan Habib yai yace " Ya Habib meye hakan kake fad'a? Kasan me bakinka ke furtawa kuwa?"
Habib ya d'ago ya kalli Ammar sannan ya maida dubansa ga Mamie data runtse ido ta sani tun jiya a asibiti dole ne zargin kalaman da Dad da Hajiya sukai ya bayyana.
Habib ya kalli Ammar yace " Mamie dan Allah ki sanar damu abinda ke faruwa, wannan ne kad'ai hanyar dazai sa mu taimaki kanwarmu sannan shirin auren da Dad yake sai munsan dalili tukunna abin zaiyiwu d'an ni tun sanda Dad yace Ammar ba d'ansa bane sam zuciyata bata aminta ba."
Seemah kam ta kame a tsaye silalewa tai ta zube akasa kamar abinda ba ya motsi haka ta koma.
Mamie tai ajiyar zuciya ta kalli Habib tace "Habibu?"
Habib ya kalleta yace " Mamie d'an Allah karku k'ara kokarin b'oye mana wani abu, d'an gaba d'aya na kasa fahimtar inda kuka dosa."
Mamie tai shiru can tace " Ni kaina banasan wannan b'oye-boyen, sai dai ina tsoron yanda zaku d'au al'amarin."
Ammar kam shi kansa ya kasa magana, kawai jinsu yake, Habib yace " Mamie babu wani yanda zamu d'auki al'amarin gaskiya kawai muke san ji."
Mamie ta runtse ido sannan tai gyaran murya.......
♢♢♢♢♢♢♢♢♢♢♢♢
Jalal kam har ya isa office ya zauna sai dai sam hankalinsa ya kasa nutauwa akan aikinsa mik'ewa yai da hanzari ya fito daga office d'in, asibitin da aka kwantar da Hajiya, inda suka had'u da Ammar ya tsaya jiya nan Jalal ya tsaya yana tunanin a ina zaiga Dad, cikin ikon Allah sai ga Dad da Abba sun fito daga wani d'aki da likita a kusa da su.
Da hanzari Jalal ya karasa gun, likita na tafiya Jalal yace " Dad ina kwana?"
Juyowa Dad da Abba sukai suka kalli Jalal, da mamaki Dad yace " Jalal kai kuma lafiya?"
Jalal ya karasa kusa dasu tare da kara gaidasu, Dad da Abba suka amsa Dad ya kara cewa " Jalal lafiya?"
Jalal ya d'ago ya kalli Dad yace " Dad kayi hakuri, sai dai hankalina ya kasa kwanciya, so nake naji mai mahaifina ya maka ka shak'e mai wuya? Naso in bar abin sai dai sam hankalina ya kasa kwanciya menene dalilin da zaisa kama mahaifina haka? Saboda inasan 'yarka ne ko me?"
Dad ya kalleshi da mamakin Kallamansa yace " Banace kaje ka tambayi mahaifinka ba?"
Jalal yace " haka ne haka kacemin sai dai a tunanina kai da ka mai hakan kai ya kamata in tambaya d'an zai iya yiwuwa shi baisan me ya maka ba."
Ran Abba ya fara b'aci yanzu ya gano wannan shine d'an gidan Amadun cikin b'acin rai yace " kai bakaji kunyar zuwa ka tsaremu ka fara mana tambayar banza ba? Ko rashin kunya ce?"
Jalal ya kalli Abba yad'anyi murmushi kad'an yace " ta ya za'ayi tambaya ta zama rashin kunya? Kamar yanda Mahaifina yake a guna haka Dad yake a gun Seemah, taya zan mai tambayar banza?"
Yai ajiyar zuciya sannan yace " sai dai duk inda d'a na gari yake dolene yaji haushi in har aka cima mahaifinsa mutunci ko da kuwa mahaifin nasa d'an fashi ne."
Dad ya kalleshi sam baya jin tsanar yaran zaiyi magana Abba yace " ka koma gun mahaifinka ga sako zan baka, kace masa yaci darajar Isma'il ne yaje gunsa ba ni bane da nine da wlh sai ya kwana a prison, ka kuma fad'ama mahaifinka sharrin dayama Kanina in ma laifin nasa ne ya rufe ko kuma akwai wani abu daya sashi yimai sharri, ko kuma so yake yaga kanina ya tozarta, to ka koma kasanar dashi matsayin Isma'il a wannan lokacin ka kuma sanar dashi a company d'in d'ansa kake aiki."
Abba na kainan ya ja hannun Dad suka shiga d'akin suka rufo sukabar Jalal a daskare a tsaye, sai da yai ta maimaita kalaman da Abba ya fad'a a ransa kafin cikin tsananin b'acin rai ya juya ya fita.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_For you Maman Shaheed, I sincerely dedicated this page to you😍thanks alot, Allah ya raya mana su Shaheed amin_
No. 4⃣5⃣
Mamie ta ja numfashi tace " Habib bazan iya baku labarin abinda ya faru ba saboda ni kaina ban san kanun labaren gaba d'aya ba sai dai zan iya sanar daku abu guda biyu zuwa uku.
Da farko dai kamar yanda ka fad'a tabbas Isma'il ba shine mahaifin Seemah ba.
Sannan Mahaifiyarta wato Fatima fyad'e aka mata sai dai mu kanmu bamusan waye ba sai dai bayan an mata fyad'en mai shagon da akai fyad'en yace Dad ne ya mata.
Wannan kalma d'aya daya furta yasa komai ya ruguje saboda alokacin saura kwana 2 a mata aure, alokacin wanda zai aureta ya fasa, Isma'il kuma 'yan gari suka tsaneshi har wuta aka sa a gidan Hajiya da kuma shagon da akai abin."
Habib yace " mene?"
Ammar kam hawaye ne kawai ke zuba daga idanunsa, me yake ji haka?
Mamie ta kallesu tace " abinda na sani kenan, bayan abin nan ya faru Fatima ta fiskanci wulakanci ta kowani b'angare har cikinta ya kawo haihuwa tana haihuwa tace ga garinku nan."
Habib ya mik'e tare da rik'e kansa, da sauri yai hanyar kofa ya bud'e yana bud'ewa yaji mutum ya biyo kofar, da sauri ya kalli kofar Seemah ya gani ta fad'i rim, jin karar fad'uwa yasa Ammar da mamie suka juya suma.
Habib da sauri ya tsugunna, Ammar ya taso da gudu yazo kusa da ita ya shiga jijigata yana k'iran sunanta sai dai inaaa Seemah kam ta suma.
Ammar ya kalli Habib idanunsa na hawaye yace " yaya kodai taji komai?" Kallan kallo sukai da Mamie, Mamie ta d'aure tace " akaita d'akin su Zahra."
Nan Ammar ya d'agata cak yai d'akinsu Zahra da ita, ya kwantar da ita, Ammar ya tsugunna a kusa da ita a rik'o hannunta idanunsa na zubar da kwalla, fita Habib yai daga d'akin d'an duk da yanajin tausayin Seemah a ransa amma yanajin haushin abinda akama mahaifinsa akan ta ta mahaifiyar.
Seemah kam ruwa Ammar ya shafa mata a fuska, hakan yasa ta bud'e idanunta tare da jan wani dogon numfashi, Ammar ya kalleta yace " Seemah!" a cikin wani irin yanayi mai ban tausayi ta kurawa Ammar ido, alokacin abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata.
Da sauri ta fizge hannunta tana girgiza kai cikin kuka mai ban tausayi kawai Dad take k'ira, Ammar ganin haka yasa tausayinta yak'ara kamashi ya mik'e tare da fita falo, Dad ya k'ira.
Daga can b'angaren Dad ya d'aga tare da cewa " Ammar ya akai?"
Ammar yace " Dad kazo da matsala fa."
" Matsalar me fa?"
"Dad kazo gidan Abba d'an Seemah na wani hali."
Cikin rud'ewa Dad yace " meya sami Seemar? Waya b'ata mata rai?"
Shiru Ammar yai kafin can yace " Dad bansan me zance ba."
Jin karar alamar sa makulli yasa ya juya da sauri ya kalli d'akin, da sauri yace " Dad kazo yanzu da matsala."
Yana kainan ya kashe wayar tare da saurin karasawa kofar d'akin ya shiga jijigawa, jiyai ansa sakata.
Hannu bibiyu yasa ya shiga bubuga kofar yana k'iran sunan Seemah.
Mamie, Zahra da Zaid da sauri suka zo jin ana bubuga kofa, nan suma suka shiga k'iranta.
Ganin ba alamar bud'ewa yasa suka tsaya jugum jugum Mamie tace " gashi babu wani makullin."
Ammar kam haryanzu bai gaji da bubuga kofar ba, yana k'iran sunanta cikin wani irin murya.
Sun dade agun kafin Dad ya iso da sauri yana zuwa ya kallesu yace " menene?" Shiru sukai Mamie tace "nice na fad'i abinda bai kamata ba kuma ina tunanin ta ji."
Gaban Dad ne ya fad'i ya sa hannu zai buga kenan yaji muryar Habib yace " Zaid d'an Allah kaida Zahra kud'an bamu guri."
Zaid ya kalli Habib cikin b'acin rai gani yake kamar rainin hankali ne hakan, a zuciye yai waje.
Habib ya maida dubansa kan Dad yace " Dad da alama Seemah tasan komai a kanta, menene dalilin dayasa zaku b'oye wannan babban sirri ga kowa? Sannan taya za'ayi a maka sharri saboda mahaifiyarta amma ka rik'e yarinyar da ba kaine mahaifinta ba."
Dad ya kalli Habib cikin takaicin kalamansa, kafin yai magana yaji Ammar yace " lalai ya Habib, wato kai abinda ya dameka kenan? Yarinya tana cikin d'aki Allah ne kad'ai yasan meke faruwa da ita a ciki anma kai abinda kake tunani kenan?"
Dad ya kalli Ammar kallon jin dad'i ga kalamansa, Dad yai baya sannan ya taho da gudu ya big'e kofar, sai dai bata bud'e ba, haka sukai tayi shida Ammar har sukai sa'a kofar ta bud'e, da sauri suka shiga ciki sai dai ba kowa a d'akin, ga mamakinsu kuma karar zubar ruwa sukeji daga b'an d'aki.
Ammar ya karasa da sauri tare da bubuga kofar toilet d'in.
Seemah kam tana cikin bathroom ta tsugunna a cikin ta saki shaya, ga bata cire kayan jikinta ba, ga ruwan sanyi ta sakar ma kanta, hakan yasa ruwa duk ya jikata jakaf, sai dai ko damuwa batai da jikinta ba kawai kuka takeyi, gani take wannan itace hanyar da ya dace da ita, ita kad'aice hanyar dazatasa takasa gane yawan hawayen datake zubarwa.
Kuka sosai takeyi sai dai ruwan dake zuba jikinta yasa baza'a gane ba.
Dad ya matsa jikin kofar ya shiga k'iran sunanta, tana jin muryarsa ta mik'e jikinta na rawar sanyi, sai dai bata bud'e ba, Dad ya shiga lalashinta, can cikin lallashi yace " fito Seemah inhar kika fito zan fad'a miki duk abinda ya faru a baya, na miki wannan alk'awarin."
Jin wannan kalaman yasa ta bud'e kofar a hankali, kofar tana bud'uwa Dad da Ammar sukai saurin shiga ciki, kallanta Ammar yai hawaye na zubo mai, kanta ya kalla sannan ya kalli yanda jikinta ke d'iga da ruwa, dukansu har Habib sai da sukaji tausayinta ya kamasu sosai.
A hankali sukaji tace " Dad kafad'amin abinda naji ba gaskiya bane, ka fad'amin kaine mahaifina, ka fad'amin gaskiya d'an Allah."
Dad ya share hawayensa ya matso ya rungumeta yana hawaye sosai, yace " Seemah ki kwantar da hankalinki."
Kai ta girgiza tace " Na fahimta dagaske ba kaine mahaifina ba kenan, mahaifiyata karuwa ce, tsintata akai?"
Kallanta Habib yai cikin tausayi da alama bataji komai ba kenan, Dad ya d'ago tare da share nata hawaye yace ki canza kaya Seemah zan fad'amiki komai, amma ko kusa Fatima ba karuwa bace, ba kuma tsintarki nai ba."
Kallansa tai ta kasa yin komai, sai hawaye da suke tsere a idanunta, Mamie ta kwallama Zahra ido, tana zuwa tace " taimaka mata ta canza kaya."
Dad ya kalleta yace " ki shirya ki fito fallo zan sanar dake komai."
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 4⃣6⃣
Zahra ta taimaka mata tasaka kaya, hannunta ta kama suka fito falo.
A falo kuwa Dad na zaune a saman kujera yayi shiru zuciyarshi na cikin damuwa, mami na zaune daga can b'angaren itama, Habib kuma da Ammar suna zaune a kasa, Zahra ce ta fito rik'e da hannun Seemah ta zaunar da ita a kasa kusa da Dad, hannu Dad yasa ya shafi kanta.
Kamar ba Seemah ba sam ta canza ga lab'anta duk sun bushi gwanin tausayi, Ammar ma ya kalleta tausayinta na k'ara ratsa gab'obin jikinsa.
Dad ne ya d'aure yai gyaran murya.
*TUNA BAYA*
Malam Isma'il wato Dad kenan, ya kasance malamin makarantar boko ne, a garin Birnin/gwari dake kaduna, yana zaune a jikin gidan mahaifinsa ne saboda rashin hali, gashi anyi sa'a dama gidan kawo gida ne babba, kawo matansa 3 ne, sai dai duk Allah bai basu haihuwa ba sai akan mahaifiyarsu Isma'il.
Hajiya 'yaranta biyu wato Dad da Abba (Abubakar) anyi sa'a Abba tun yana saurayi ya samu wani babban mutum d'an kasuwa a garinsu yake d'aukansa suna yawan kasuwancinsu tare, ganin kwazo dasan aiki irin na Abba yasa ya aura masa 'yar sa wato Mamie(Bilkisu) sannan ya d'aurashi akan harkokin business d'insa dake Abuja, tun daga nan ya koma can da zama.
Dad an masa auren zumunci da mahaifiyarsu Habib wato Samira, duk da baso yakeyi ba sai dai a lokacin bashida wacce yake so kuma zab'in iyayensa shine zab'insa, bayan auransu ne Kawo ya basu b'angare d'aya suka zauna a gidan.
A kwana a tashi har Samira ta haifi d'anta Habib, sannan ta sake haihuwar Junaid sai dai akwai ra ta a tsakaninsu, lokacin da Samira take da cikin Ammar ne ranar Isma'il ya dawo daga makaranta yaga wata bus tayi parking a mak'otansu, yarane 'yan mata su 4 suka fito daga motar, kana kallansu kasan fulanuwa ne aka kawo su irin aikin nan na aikatau.
Isma'il ya kauda kansa tare da wucewa gidansu, yaje daidai zai shiga yaji ance " Malam Isma'il?" Juyowa yai da fara'arsa saboda ya gane muryar, ya kalleshi yace " Amadu kaine yau a gidan namu?"
Wanda ya k'ira da Amadun yai murmushi tare da cewa" wucewa nazo yi shine naga kamar ana sauke 'yan aiki na d'auka kaine ka d'aukarma Samira." Yai maganar cikin zolaya.
Isma'il ya d'an kallesu caraf suka had'a ido da d'aya daga cikinsu, d'auke kai yai yace " lalai kai dai yakamata ka d'aukarma matarka."
Sun dad'e suna hirarsu har 'yan matan suka gama shiga da kayansu suma suka shiga, Isma'il ya kalli Amadu yace " ni dama shagon ka naje na amso ma Samira kayan shayi, naga kamar wannan cikin na wahalar da ita sosai bata iya cin abinci."
Amadu yace " Hmm nima haka nake fama da Hauwa'u inata so in tambayeka dama haka masu ciki suke shan wahala."
Isma'il ya maida jakarsa d'aya hannun yace " A'a wlh yanayi ne dai yake zuwa kaga Samira data haifi Habibu da Junaid ai duk batasha wahalar laulayin nan ba."
Amadu ya gyad'a kai yace " muje shagon in baka da har na kulli zance ganin Hauwa anma saboda kai zan koma."
Suna tafe suna hirarsu har suka isa Babban Shagon Amadu ya shiga ciki ya had'omai kayan shayi, Isma'il ya bashi rabin kud'in yace sauran sai karshen wata.
Haka Isma'il ya taho yan tafe ana gaidashi saboda ganin girmansa da mutane keyi, har ya isa gida.
Yanzun ma yazo shiga ya k'ara ganin 'yan matan sun fito sai dai ta d'azun nan tana matsar kwalla da alama kukan rabuwa sukeyi, wucewa yai ya shiga gida.
A kwance ya tadda Samira ta kasa komai, nan ya taimaka ya had'a mata shayi ta sha, da kanshi ya shiga gyara d'akin sannan ya taimaka mata ta kwanta a kan gado.
Ganin lokacin shiga makarantar su Habib da Junaid yayi ga kuma babban d'an Abba yasa Mamie ta ba Abba shawara akan akaisu England gun kanwarta, Abba yayi farincikin wannan shawarar ya k'ira kaninsa ya sanar dashi.
Ba Dad ba hatta matan gidan sun tayasu murna, su Habib sai murna sukeyi sukam, bayan sati biyu da maganar Dad dakanshi yakaisu Abuja suka wuce ta can.
Dad ya dawo daga Abuja a gajiye ya shiga gida anan ya tadda Samira ba lafiya su Hajiya da ragowar matan kawo na kanta, ya kallesu yace "Hajiya lafiya dai ko?" Hajiya tace " fita waje nak'uda ce."
Dad ya kalli Samira yaga yanda takeshan wahala yace " Kodai akaita asibiti?"
Hajiya tace " bakaji me nace ba?"
Jiki a sanyaye Dad ya fita ya zauna akan dakalin gidan, bai dad'e da zama ba sai gata ta dawo daga kai nik'a, a hankali cikin sanyin muryarta yaji tace " Ina wuni?"
D'agowa Dad yai ya kalleta ranar daya fara ganinta kaya daban daban ne a jikinta gashi tayi zanen baki duk a fuskarta yanzu kuwa ba wannan shirman a fuskarta sannan kayanta tsaf,ba shakka tanada kyau sosai.
Dad yace " ina gajiya."
Yana fad'ar haka ya kauda kai, matsowa tai kusa dashi tace " Malam menene? Naga kamar kana cikin damuwa."
Kalanta yai da mamaki, baisan sanda yai murmushi ba yace " Ta ya akai kika sani?"
Ta saki murmushi itama tace " kullum ina ganinka ai in na fito anma ba haka nake ganinka ba."
Dad yai murmushi yace "a ina kike ganina?"
Tai kasa dakai batace komai ba, yace " kije kikai aikenki kar a miki fad'a."
Ta d'ago ta kalleshi sannan tace to, wucewa tai ta shiga gida, ya bita da kallo haka kawai yaji damuwarsa ta ragu sosai, anma ya akai yarinya karama da bata wuce shekara 18 ba tagane yana cikin damuwa?
Yarinyar tana shiga gida ta kai markad'an sannan ta kalli matar gidan tace " Hajiya in d'an fita?"
Ta kalleta tace " Fatima ina zaki ke kuma? Naga yamma tayi."
Tace " yanzun nan zan dawo."
To sai kin dawo ta fad'a, da sauri Fatima ta juya ta fita, sai dai abin haushi tana zuwa taga ba kowa agun, waige waige ta fara yi sai dai bata ganshi ba, jitai anzo daidai kunenta ance " Fatima me kikeyi anan?"
Da sauri ta juya ta kalleshi, d'an gidan da take aiki ne ko ince d'an lele, da sauri ta matsa ya kalleta sannan ya kalli abokansa jitai sun kwashe da dariya, kifkif da ido tai tace " menene?"
D'an lelen wato Abdul yace " Abokaina kesan ganinki nace musu ankawo mana kyakyawar mai aiki shine nakeso su ganki ko zasu kyasa kamar yanda na kyasa."
Kallansa tai da mamakin kalamansa tace " mene?"
Dariya suka kara kwashe mata dashi, kana ganinsu kaga tantirai, Fatima kam ba abinda ta tsana irin Abdul ya shigo gida ya d'inga nanik'e mata kenan ita kuma batasan haka.
Cikin takaicin abin yasa tai saurin shigewa gidansu Isma'il.
© *THE SEEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 4⃣7⃣
Fatima na shiga gidan ta ga mutane a zazaune anata murna, idanu suka had'a da Isma'il, jitai ance " Baiwar Allah lafiya kika shigo ba sallama?"
D'auke idanta tai daga kansa tai saurin cewa Salamu Alikum, dariya suka sa mata Hajiya tace " daga ina kike?"
Fatima tad'an saci kalan Isma'il sannan ta nuna da d'an yatsarta tace daga nan gidan, Goggo(uwar gidan Kawu) tace shigo ki zauna nasan kukan yaro kikaji shiyasa kika shigo ko? Kallan yaran tai a hannun ta murmushi ta saki sannan ta karasa tare da gaishesu, suka amsa goggo ta mik'a mata d'an, Kuramai ido Fatima tai tana san yara itakam, a hankali ta d'ago tad'an kalli Isma'il ga mamakinta shima idanunsa na kanta da sauri tai kasa da ido tace " Allah ya raya." Sukace Amin.
Goggo tace " Isma'il ko zaka dubo mai kazar ko ya fito, naga tun d'azu mahaifinka bai dawo ba, ga shi ya kamata ama mai jego farfesu."
Isma'il yace " bari naje."
Ji sukai Fatima tace " bari ni naje nasan gurin."
Hajiya takalleta fuskarta da fara'a tace " keda kikazo barka, ya za'ai musaki aiki sannan ga magriba ta kawo kai."
Isma'il ya mik'e tare da cewa bari naje.
Yana fita, Fatima tace " bari naje gida zan dawo gobe." Nan suka mata sallama ta fito da sauri.
Can taganshi har yayi nisa, da sauri ta shiga binsa har da had'awa da gudu, tai sa'a ta kusa isa gunsa, a hankali tace " Malam." Ga mamakinta gani tai ya juyo d'an batai tunanin zai jita ba.
Tsaya tai tana hakki, Isma'il ya matso kusa da ita yace " yana ganki anan?"
Cikin hakki tace " biyoka nai."
Kallanta yai da mamaki yace " abu kikesan fad'amin?" Kai ta gyad'a sannan tace " Malam alfarma da taimako nakesan kamin."
Isma'il ya kalleta yace " namefa?"
Tai shiru tare dayin kasa dakai, ya kara kallanta yace " ke nake jira."
Tana wasa da 'yan yatsun hannunta tace " Karatu nakesan ka koyamin."
Dariya Isma'il yasa yace " in kinasan karatu sai kice a saki a makaranta."
Tai kasa dakai tace " ni na islamiya nakeso, kullum Hajiya sai tace in tashi inyi sallah nikuma a garinmu sai mutum yayi aure yakeyin sallah to in ina kula da yanda takeyi sai inga tana motsa baki amma bansan me take cewa ba, shine nakeso ka koyamin na islamiya insan yanda ake sallah."
Kallanta yai cikin tausayawa, gata dai 'yar kauye mara ilimi sai dai komai nata na birgeshi, da wani ne haka zai karashi rayuwarsa ba tare dayace a koyamai ba."
Yaja dogon numfashi yace " yanzu kije gida gobe kisame ni da yamma a kofar gida, sai insan yanda zamuyi karatun."
Murmushi ta saki tace " nagode Malam. "
Tanakainan ta juya ta fara tafiya, kallo ya bita dashi ya shagala yana kallanta yaji an dafa kafad'arsa, ya juyo a zabure Amadu ne ya kalli inda Isma'il yake kallo yace " kasanta ne?"
Isma'il yai saurin wayancewa yace " wa?"
" wacce kake kallo mana."
" ni kaga ina kallan wata? Kawo nake lek'awa munjishi shiru tun d'azu daya fita siyo kaza." Isma'il yai maganar yana waige-waige.
Amadu yace " Niba wannan ba gurinka fa zanje yanzu."
" haba? To gani Allah yasa lafiya."
Amadu yasa dariya yace " Habiba ta sauka d'azu da rana na k'ira wayarka bansamu ba shiyasa na yanke hukuncin zuwa gunka."
Fara'ar Isma'il ce ta k'aru yace " kai haba? Amma naji dad'i, nima yanzun nan Samira ta sauka, oh ikon Allah kaga sun haihu a rana d'aya."
Amadu ma fara'ar fuskarsa ya fad'ad'a yace " ikon Allah meta samu?"
"Namiji."
"Nima Namiji. "
A tare suka sa dariya tare da rike hannu Amadu yace " lalai wad'annan Aminai zasu zama da alama."
Nan Amadu ya raka Isma'il gun mai kaza anan suka tadda kawo, sun siya suka taho tare kawo na tayasu murna yace " Lalai naji dad'i Allah ya kare mana su." Amin suka fad'a a tare.
Har gida Amadu ya rakasu, nan matan kawu suma sukai ta tayashi murna, ya d'auki d'an cikin farinciki yace " Isma'il tunda mun haihu a tare sai muyi canje, ni zan rad'ama d'anka suna kaima sai ka rad'ama nawa."
Duk suka kwashe da dariya kowa ya shiga cewa lalai hakan yayi.
Amadu ne ya rad'ama Ammar suna na gaskiya sunan mahaifin Amadu wato Kabir sai yasamau sunan daza'adinga cemai Ammar.
Shima Isma'il da kansa yaje gidan ya rad'ama yaron Jalaludeen saboda sunan dayasu rad'ama Ammar kenan.
Murna agun mutane ba'a magana saboda kowa yasan amintar dake tsakanin Amadu da Isma'il.
Washegari da yamma yana zaune a dakalin kofar gidan Fatima ta fito, cikin tafiyarya mai nutsuwa, tana ganinshi tai kasa dakai tana murmushi, Isma'il ya shiga kallanta harta karaso gurin, ta gaidashi a hankali, shima ya amsa tare da cewa " na d'auka kin fasa koyar karatun ganin kin dad'e baki fito ba." Yai maganar cikin zolaya, abinka da rashin wayau sai tace " bayan yanzu kazo tun d'azu nake lekowa bana ganinka."
Dariya yai yace " ashe da gaske takesan koyan karatun."
Kasa tai dakai tana wasa da 'yan yatsun hannunta, Isma'il yace na yanke shawara, duk ranar asabar da lahadi shine bani da makaranta da safe, wajen karfe 11 sai ki d'inga zuwa islamiya ina koya miki zuwa karfe 1, kinga karfe 2 ne ake fara karatu."
Kai ta d'aga tace to "Malam na gode, amma wannan yaron d'anka ne?"
Isma'il ya kalleta da mamakin tambayarta, yace " meyasa kikesan sani."
D'agowa tai a hankali ta kalleshi batace komai ba ta maida kanta kasa tare da cewa " sai ranar asabar d'in."
Ya amsa da "Allah ya kaimu."
Ta juya tai ciki, kallanta yai tare da murmushi.
Itakam tana shiga ta d'au tsintsiya ta hau shara ba gaira ba dalili bayan gun a gyare yake tas, shara take Hajiyar Abdul na zaune taji karar tsintsiya ta mik'e tare da fitowa, Fatima tagani tanata zabga shara zatai magana taji muryar Abdul yace " Faty Shara kikeyi ne?"
Kallansa tai ta kaida kanra kan shara, itakam zuciyarta batasan ace d'an Isma'il ne d'an ita tanada mugun kishi shiyasa bazata iya auren mai mata ba, zuciyarta tace anya kuwa kamar malam zai rasa mata?"
Jitai Abdul ya dafata yace " meke damunki haka?"
Ta d'ago tace " d'an Allah ina rokonka kadaina tab'ani in zakamin magana."
Ga mamakinta jitai yace " Sorry na daina."
D'agowa tai tana mai kallan mamaki tace " ina abokan naka?"
Yai dariya yace " suna gidansu."
Tai kasa dakai tare dad'an tab'e baki a ranta tace " da walaki, d'an dama inshi kad'ai ne zakaga yanada saukin kai kuma bashi da rashin mutunci, anma da zarar sun had'u da abokansa shi kenan kuma sai rashin mutunci ta ko ina."
Kallanta ya tsaya yanayi tana shara, sai murmushi yakeyi, Hajiya dake tsaye tana kallansu tai murmushi itama, da alama Fatima ce zata sa d'anta ya shiryu d'an wannan shine addu'arta yaran maraya ne bashida uba, sai dai yabiyema kawayen banza sun canza mai halaye.
*THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 4⃣8⃣
Anyi suna lafita kowa na murna, Abba kam shima a lokacin Mamie nada tsohon ciki hakan yasa batazo ba, sai dai tunda akai suna jikin Samira yak'i dad'i kullum cikin cuta.
Fatima kam duk karshen sati suna zama da Isma'il a makaranta ya koya mata karatu, a sanu a sanu wata shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu batare da Isma'il ya farga ba, sai dai bai tab'a tunanin zai iya furta mata yana santa ba saboda sau dayawa yanaji tana zancen batasan kishiya.
Rayuwa kenan yanzu an wayi gari shekararsu Jalal 5, kusan kullum Jalal na gidansu Ammar inkuwa baizo ba to zakaga Ammar a nasu gidan.
Jalal ya taso yaro mai zuciya, shikuma Ammar hakuri gareshi, a duk lokacin da yara sukaso rainama Ammar hankali, Jalal ne ke zuwa ya musu shegen duka, hakan yasa suka daina tsokanar Ammar.
A b'angaren Fatima kam tana shiga gidansu Isma'il sosai sai dai a randa tasan yanada aure harda 'ya'ya ranar tasha kuka harda zazzab'inta, yanzu Fatima ta kile sosai d'an inba fad'ama akai ba bazaka tab'a cewa 'yar kauye bace.
Samari kuwa dake santa a k'aueyen nan yawa garesu, sai dai ita zuciyarta nakan Isma'il, ta kasa tsayawa da wani sam.
Kamar yanda ta saba yau asabar ta gama duk ayukanta, tace " Hajiya zan fita."
Hajiya tace " Fatima jiya da daddare sai nawa Abdul ya shigo?"
Fatima ta kalli Hajiya tace " Hajiya wlh bansani ba nidai harnai bacci banji motsin bud'e kofa ba, amma ai dama yace Campain yakeyi."
Hajiya tai shiru tace " wani campain me da daddaren Allah? Keda kin yarda? So yake yaja min zagi dama mutane nacemasa d'an mace tunda mahaifinsa ya rasu da daddewa."
Fatima ta matso kusa da Hajiya tace " Hajiya Allah ya gani kinayin daidai kokarinki ga matsalar kafar da kike fama da ita sannan ni fa hajiya? Kinsan iyayena sun rasu tun ina karama agun kanwar mahaifina na taso."
Hajiya tai murmushi tace " jeki ko ba gun karatu zaki ba?"
Mik'ewa tai tana murmushi ta mata sallama ta fita, Hajiyar Abdul ta bita da kallon k'auna.
Tazo fita taji an cafko hannunta, ko bata juyaba tasan waye hakan yasa ta dage ta fizge hannunta da karfi, Abdul haushi ya kamashi, yana takaicin yanda take nunamai kamar tana kyamarsa, sa hannu yau ya fizgota ya matseta jikin bango, ta d'ago tare da had'e rai, Abdul ya kalleta ya saki wani mugun murmushi yace "Fatima na yanke hukuncin muyi aure kawai."
Batasan sanda ta bugamai wata harara ba, batai auni ba taji ya kifa mata mari yace " ni kike harara? Ko kin manta ni waye?"
Kasa tai da kai tare da rik'e gun, ya saketa yace " ankusa nad'ani Chairman a garin nan, in har mai aikin gidanmu bata bani girma ba wa zai bani?"
Ta kalleshi a ranta tace " tir da wannan mik'amin da ake shirin ba ka." Ya saketa tare da shiga ciki, cikin takaici itama ta wuce waje.
Abdul na shiga ya gaida hajiya tare da cewa " Umma nikam aure nakeso."
Kallansa tai cikin mamaki da kuma murna tace " wa kakeso Abdul? Naji dad'i?"
Ya d'an sosa k'eya yace " ni Fatima zaki auramin."
Murmushin fuskarta ne ya fad'ad'a tace " Da gaske Abdul?"
Yai murmushi yace " sosai ma, amma d'an Allah Umma tunda yarinyar nan a gunki take kuma anan gidan zata zauna asa auren nan da sati 2."
Dariya ta saki tace " Abdul matsuwar ta menene haka?"
Yace " ni kawai so nake ayi nan kusa."
Shiru tai lalai dole ta yarda ai nan kusa, d'an tasan inka ga namiji ya matsu da aure sosai to gwara amai kafin abin kunya ya ratsu ciki.
Tace to naji jeka.
Nan ya mik'e tare da Murmushin mugunta, d'an shikam kullum da sha'awar ta yake kwana.
Fatima kam tana fitowa a waje kan dakali taga Jafar da Ammar, ta matsa tare da cewa " Me kukeyi a nan?"
Jafar ya kalleta yace " a zaune kawai muke."
Fatima tai murmushi tace " ku bakwa wasa irin na yara?"
Jafar ya kalli Ammar yace " yaran ne 'yan rainin hankali, munfisan muyi wasanmu mu biyu."
Tace " Ammar ina Babanka?"
Yace ya fita, tai murmushi tad'auko naira goma a jakarta tace " ungo kusai alawa."
Jafar ya kalleta yace " mun gode amma bazamu ansa ba."
Ta kalleshi sannan tace "Ammar kaifa?" Kallan Jalal yai yace "a'a mun gode. "
Ta d'an yi kasa dakai alamar rashin jin dad'i sukam sauka su kai suka shiga gidan da gudu.
A hankali take tafiya, samarin garin kowa na sha'awar yanda take da hankali ga kyau, harta isa makaranta, ta tadda Isma'il a zaune, ta gaidashi ya kalleta cikin kulawa yace " yau kin d'an dad'e Allah yasa lafiya."
Ido ta kuramai kamar batasan me yake cewa ba, ganin yanda take kallansa yasa yai murmushi yace "da alama kunyar fulani tabar jikinki."
Da sauri ta d'auke ido tace " Malam duk kunyata?"
"Hmm a da ba? Yanzu naga harkin fara kurama mutane ido."
Ta had'e rai tace " kaine mutane?"
Yai murmushi ya wayance da cewa " matso muyi sauri matata batajin dad'i."
Had'e rai sosai Fatima tai dama yasani, shikuma harga zuciyarsa yasan yanasanta sosai, sai dai yasani bazata iya auransa ba, ga 'ya'yan masu kud'i na santa samari, ina zai so abinda yake neman fin karfinsa?shiyasa yakesan itama ta daina sanshi.
Mik'ewa tai cikin tsananin kunar rai ba tace mai komai ba tai hanyar waje.
Isma'il ya kalleta yace " nayi zuwan banza kenan?"
Tsayawa tai cak batare da ta juyoba idanunta na zubar da kwalla, mai yasa zuciyarta bata iya b'oye so ba?
Haka ta juya sukai karatun ba dad'i.
Tana dawowa gida Hajiya tasanar da ita zancen aurensu da Abdul, cikin mamaki ta kalleta tace " ni kuka Hajiya? Mai zai yi dani 'yar kauye?"
Hajiya tace " Fatima kitaimakeni bad'an shi ba d'an ni ayi auren nan,wannan shine buri na d'aya da ya rage min a duniya, d'azu na k'ra kanwar Babanki bakiga murnar datai ba."
Fatima ta d'ago a ranta tace tayi murna mana tunda taji zan auri mai kudi.
Murmushin yake Fatima tai mata sannan ta mik'e ta shiga d'an d'akinta, tana isa ta fad'a gado kuka sosai ta shiga yi, meyasa ba wanda zai tambayeta ko akwai wanda takeso? Tasani da mahaifanta nada rai dasai sun tambayeta ko tanaso, ta dad'e tana kuka kafin ganin ba mai lalashi ta mik'e.
Isma'il kam ya dawo yana shiga d'aki, ya tadda Samira a zaune, ya shiga shima ya zauna, tamai sannu da zuwa tare da cewa" dagaske kaima kanacikin jerin masu san Fatima?"
Da mamaki ya kalleta yace " me kike fad'a haka?"
Ta juyarda kai tace " d'azu na fita gunsu Hajiya naji wani saurayi yazo kawo musu kara wai kana santa duk asabar da lahadi sai kun had'u a makaranta kunyi zance."
Ya mik'e tsaye yace " kuma sai kika yarda da zancen nakejan yarinya zuwa makaranta inayi?"
Juya kai ta sakeyi hakan yasa ya gane wato ta yardan kenan, a zuciye ya fito waje, Hajiya ya gani dasu Goggo suma suna maida zancen, kallansu yai cikin takaicin abinda kowake fad'a zaiyi magana sai ga Jafar ya shigo, ya kalli Isma'il yace " Dad wai ana magana dakai."
Yace " Jafar inji wa?"
Yace " Abba nane."
Tare suka juya sukai waje, bayan sun gaisa da Amadu ne yace " Amadu ya akai?"
Amadu yai shiru can yace " haryanzu kana koyama Fatima karatu ne?"
Kai ya gyad'a alamar eh, Amadu ya dafa kafad'arsa yace "kayi hakuri ka rabu da yarinyar nan, nasan ka sosai Isma'il nasan kuma kana santa, wani karatu kake koyamata har shekara 5?"
Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba " kaga d'azu a shago naji ana gulmarka, sannan naji ma yarinyar yaron gidan zata aura, Isma'il ka hakura kasan Abdul wanda za'aba Chairman ba mutunci garesu ba su da abokansa."
Isma'il zuciyarshi ta tab'u dajin wai anmata miji, ya d'aure yace " nagode Amadu, insha Allah kuma mungama karatun."
Tun daga wannan rana bata sake sa Isma'il a idanunta ba, zuciyarta takasa hakura da rashinshi, wani sa'in har gidan take zuwa sai dai kowa taga ya daina sakar mata fuska, ga abin takaici shirye-shiryen bikinsu kawai sukeyi ba wanda ya damu da halin da take ciki.
Isma'il kam shima komai nasa ya canza bai fiya magana ma sosai ba, duk 'yan gidan hatta Samira sun fahimci yanasan Fatima sosai, sai dai yaza'ayi?
Abdul kam abokansa sai dariya sukemai wai zai auri 'yar kauye, yace " nimafa bawai d'an inzauna da ita d'ind'ind'in nakesan auranta ba, d'an kawai in kauda kwad'ayi nane, dariya suka kwashe dashi sukace " in wannan ne ba kawai sai ka....."
Shidai kam zuciyarshi batasan wannan kawai....d'in.
Yau saura kwana 2 biki, d'anginsu Fatima sun cika gida, itakam kallan kowa take a baibai, sai dai ba yanda zatai, duk ta rame ta canza.
Dad nakawo nan yai shiru tare da kallan Seemah dake zubar da kwalla kamar an bud'e famfo, Ammar ma hawaye ke zubar mai, ya kalli Habib shima haka.
Yai shiru can yace " Ana saura kwana 2 auranta ne Ammar yazo ina zaune kusa da Samira da ba lafiya ya sanar dani wai matar nan ta gidan nan, tace d'an Allah tanasan ganina a shagon Abban Jafar. "
Samira dake kwance ba lafiya na kalla, na share maganar tare da kallan matata, Samira ta juyamin baya tana zubar da kwalla, tausayinta dana kaina ya kamani hakan yasa na watsar da maganar Fatima nasan ganina.
A b'angaren Fatima kam tun karfe 2 tazo gefen shagon take tsaye, har la'asar, Amadu tausayinta ya kamashi yace " Fatima anya zaizo kuwa?"
Ga mamakinsa murmushi yaga tayi tace " zaizo."
Anan shagon ta la'asar Amadu yabata biscuit da lemo, duk da yunwar datakeji taki amsa, duk k'iran da Amadu yake makama Isma'il a waya sai ace wayar a kashe, ga magrib ta duso, Jalal ne yazo gunsa, yace " yauwa Jalal zauna ka taya Aunty hira bari naje gidansu Ammar in dawo."
_Dad ya kallesu tare da matse kwallar sa_
Yace " Seemah bansan meya faru ba, nidai Amadu yazo mukai sallar magrib a massallaci tare muna fitowa yasanar dani komai, da sauri muka nufi shagon ni dashi.
Sai dai me? Shagon muka gani kamar ba kowa, hakan yasa na shiga ciki da sauri shi kuma ya zagaya, ina shiga na tadda Fatima tsirara ba kaya a kwance, kamar ma ta ruga ta suma, kana ganinta kasan ta karfi aka mata, na matsa da sauri na tallabota idanuna a rufe na riko zaninta na lil'iba mata, Amadu ya leko cikin tsoron abinda ya faru ya zube agun, nikam rungumeta nai na shiga wani irin kuka mai ban tausayi, ban farga ba naji mutane a waje ana hayaniya.
_Dad ya share kwallarsa_
_Seemah kam kukanta ya tsananta anan_
Amadu ne ya kallan yace " yi sauri ka fito da ita samarin garin nan ne bansan wa ya k'irasu ba."
Na d'agota tare da nad'a mata zani, ina fitowa aka fara jifansa da dutse, ganin zasu sameta yasa na juya sukai ta dukana, wani daga cikinsu ma bamusani ba ashe yasa kalanzir kawai sai ashana mukaga an kyasta, haka na d'aureta abayana dakyar mukasha zuwa gida.
Sai dai me? Bala'in dana tarar a gida a wuce nacan, Hajiya harta suma, Samira ma ciwonta ya tashi, sai numfashi kawai takeyi, tana ganina d'aure da Fatima kawai tayi baya luuuu, abinda ya firgitani agun tace ga garinku nan.
Kuka ma rahama ne, a wannan ranar hawaye ma kasa zubomin sukai, Kawo da jama'ar gurin suka had'u aka fara zancen yima Samira wanka, nan Kawu ya kalli Amadu a tsakiyar mutane yace " Amadu ka tabbatar da abinda ka fad'a cewar Isma'il shiya mata fyad'e?"
Da mamaki na kallesu ni kuma? Abinda ban tab'a zataba sai jinai Amadu yace wai eh, ya ganni da idanunsa.
Kuka sosai kawu yai, kowa ya shiga ala wadai dani, Abdul ya koma gida cikin taron jama'ar biki yace " bazai aure Fatima ba, d'an ankamata da wani a shago."
Tsinuwa kuka nashata, wani abin takaicin Fatima data farfado, sai kuma ba baki, ta kasa magana, duk yanda taso tai magana ta kasa, anan aka fara jifana akan lalai kafi namata da alama ma abu nasa na danne bakinta, yunk'urin ihun dataitayi yasa muryarta ta tafi.
Dad ya kallesu hawayensa sun tsanan ta yace ban tab'a ganin bala'i kiri kiri irinta wannan ranar ba, kowa ya gujeni, A lokacin na ba Fatima takarda akan ta rubuta min sunan wanda yamata fyad'e, tana kok'arin rubutamin, Tayi baya luuu, bakinciki harya gama cin jikinta, haka na kaita asibiti aka bata gado, sai dai kamar ba rayayyiya ba, tana kwance ne kawai sai numfashi, d'anginta suka sallamata aka watse da ala tir.
Fatima na asibiti har wata 2, Kawu da Hajiya sunyi sunyi inrabu da ita sai dai gani nake in na kyaleta mutuwa zatai d'an bakin ciki, alokacin ne kuma akace tanada ciki.
Ganin zaman garin na neman gagararmu yasa muka dawo Suleja, anan ne har Fatima ta kawo watan haihuwa, tana haihuwa tace ga garinku, Hajiya kam da Kawu sun ma dainamin magana sam, yaya ma duk yanda yaso da in rabu da Fatima sai dai na kasa, haka na zauna agun gawar naita kuka kafin aje amata sitira.
Dad na zuwa nan yakasa magana Seemah kam jitai kanta na juyawa Ammar ya matso kusa da ita yace " Seemah, in ihu ne kiyi amma karki had'iye komai a ranki."
Kallansa tai kawai tai baya luuuuuu, Habib ma kuka yake sosai, Dad ya mik'e dasauri ya d'auketa yai waje da ita.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
*_This Page is for you my dearest Friend Umma, and also my Swt kanwa Somaya😍 Miss Hot Purple luv u soo much_*
No. 4⃣9⃣
Jalal kam yana tsaye a gate d'in gidan su Habib, mai gadi ya kalleshi yace " Bawan Allah d'an Allah ka tafi na fad'ama Hajiya Seemah bata nan."
Jalal ya kalleshi sannan yace " naji ai baba kuma na yarda to so nake naji tana ina?"
Zaiyi magana sai ga Aisha ta fito da alama asibitu zata kai abinci ganin basket d'in kuloli a hannunta, kurama Jalal ido tai kamar tasan shi, can ta matso tare da mik'ama Bala basket d'in yasa a mota.
Ta kalli Jalal tace " Kamar na sanka ko?"
Jalal ya kalleta yace " anya kuwa? Amma da alama daga gidan kike, Seemah fa?"
Sai alokacin ta tuna shine yaja Seemah rannan da suka fita tare, ta sakarmai murmushi sannan tace " tana gidan Yayan Babanta amma yanzu ya Habib yai waya yace wai ankaita asibiti da alama batajin dad'i."
Jalal yace " mene? Meya sameta? Zazzab'i take?"
Dariya Aisha tai tace " wanne zan amsa daga ciki? Bayan nima bansan komai ba? Yanzu dai zanje asibitin sai ku tafi tare."
Jalal ya runtse ido sam hankalinsa ya gaza kwanciya, nan Bala ya fito da mota Jalal ya shiga gaba suka wuce asibiti.
Seemah kam bayan ta farfado sai ta hau rawar sanyi, nan likitan yasa mata drip sannan ya roki da abarta ita kad'ai da alama taji abinda ya firgita tane.
Abba, Dad, Kawo, Ammar, Habib, da Mamie suna zaune a d'akin da aka kwantar da hajiya, itama dai jikin ba dad'i a zaune kawai suke amma kowa da abinda ke ransa.
Sun isa asibiti, Aisha ta kalleshi tace " zamuje tare ne?"
Jalal ya tuna kalaman Dad na d'azu hakan yasa ya kakaro murmushi yace " Jeki kawai karma asan tare muka zo."
Ta kalleshi da mamaki amma bata tambaya ba ta ce to, sannan tai gaba.
Jalal kam zuciyarshi ta gama dakewa abu d'aya kawai yasa a ransa awannan lokacin shine bazai tafi ba tabbas sai yaga Seemah, saboda gobe yakesa ran zuwa Birnin/gwari d'an yaji menene tsakanin Dad da Abbansa.
Karasawa yai bakin d'akin da aka kwantar da Hajiya bai shiga ba kuma bai kwankwasa ba kawai a tsaye yake, sam baisan d'akin kusa da Hajiya nan aka kwantar da Seemah ba.
Bayan Aisha takai Abincin ta fito ne wajen bud'e kofa yasa Habib ya hango Jalal, ransa ya k'ara tunzura a zuciye ya fito waje yazo kusa da Jalal ko kofar bai rufe ba, a lokacin ne hankalinsu yakai kansa.
Habib na zuwa kusa da Jalal, kafin Jalal yai auni yaji an makamai naushi a kunci, dukan ya shigeshi d'an sai da gefen leb'ensa ya fitar da jini, Habib ya mik'e zai k'aramai wani Jalal ya rik'e hannun.
Daidai nan 'yan d'akin suka fito, Kallan kallo suka fara kafin Jalal yace " Ya Habib mena maka kuma?"
Fizge hannunsa yai da karfi sannan ya nunashi da 'yatsa yace " Jalal wallahi id'an har baka bar nan cikin minti 5 ba bansan me zan ma ba."
Kallansa yai da alamar tambaya yace " na maka wani abin ne? A iya sanina ban ma abinda zan cancanci duka ba."
Muryar Abba ce ta katsesu yace " Habib meye hakan kake?"
Habib ya bugama Jalal wani kallo sannan ya wuce d'akin, kowa ya koma d'akin aka rufe kofar, Jalal yabi kofar da kallo, jiyai ansake bud'ewa Ammar ne ya fito yazo kusa dashi tare da mik'amai handkerchief, Jalal ya kalleshi da jajayen idanunsa sannan ya amsa, a hankali ya furta thanks.
Ammar ya kalleshi yace " please Jalal ka tafi."
Jalal idanunsa suka kara kad'awa yace " Ammar menai? ni Seemah kawai nakesan gani naji ance bata da lafiya, banaji zan iya tafiya ba tare da na ganta ba."
Ammar ya runtse ido shima idanunsa suka ciciko, yace " Banaji itama Seemah zata so ganinka a wannan lokacin."
"Meyasa? Taya akai kasani? Banaji itama akwai abinda zaisa takisan ganina."
Ammar ya dafa kai sannan yace " ni kaina daurewa kawai nake amma basan magana dakai nakeba, ka koma ka tambayi mahaifinka waye ya rad'ama suna? Da wa aka haifeku rana d'aya? Sannan wani irin sakayya yama babban amininsa?" Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba" wad'annan amsoshin sune zasusa kagane meke faruwa."
Ammar nakainan ya bud'e d'akin da Seemah take yasa kai, daidainan Jalal ya hangota kwance akan gado ana mata k'arin ruwa, daga nesa ya hango fuskarta jiyai kamar zuciyarsa zata fito, kofar ce ta rufe sakamakon turata da Ammar yai, Jalal yabi kofar da kallo idanunsa sunyi jaa ga sun ciciko, kurama kofar ido yai, ga magrib tayi.
Wucewa yai yaje massalaci, suma sun firfito sallah, bayan sunyi sallah kafin su koma shi ya rigasu isa, harya sa hannunsa zai bud'e kofar, yaji bazai iya ba tabbas bazai shiga ba harsai ance ya shiga, kuma bazai tafi ba harsai ya ganta.
Komawa yai ya tsaya a gunsa na d'azu, ga mamakinsu duk sun d'auka ya tafi sai dai ganinsa yasa suka d'auke kai suka shiga, Dad da Ammar sukai d'akin Seemah, suna shiga daidai nan ta bud'e idanunta a hankali, haryanzu jikinta zafi tsau kamar garwashi, ta kurawa Dad ido, ita kad'ai tasan me take tunani, kallanta yai tare da cewa " Swthrt kin tashi?"
Ta k'ak'aro murmushin da kana gani kasan yak'ene ga leb'enta ya bushe, a hankali tace " Dad tambaya nakesan yi?"
"Inajinki 'yar Dad."
Had'iyar wani abu tai sannan tace " Jafar da aka haifa rana d'aya da Ya Ammar, wanda mahaifinsa yama sharri ya kuma cutar da mahaifiyata, shine........?" jitai ta kasa karasawa sai motsa baki take tanasan magana amma kuka ya hanata, Ammar ya share hawayensa tare da matsowa kusa da ita yace " Dad zan bata amsa jeka kawai."
Dad ya mik'e jiki a sanyeye, Ammar ya matso kusa da ita ya zauna, tare da kallanta yace " Seemah sai me? Inshine Jafar d'in da kikeso? Meye zaisa ki k'ara tada hankalinki?"
Kai ta shiga jijigawa tace " akwai komai kuwa yaya."
Hannu tasa a saitin zuciyarta tad'an buga kad'an tace " taya za'ayi zuciyata taso wanda d'ansa ya taimaka wajen ruguza rayuwar mahaifiyata? Meyasa nakejin zuciyata tana zafi?"
Kuka ne yaci karfinta hakan yasa ta kasa karasawa, Ammar ya share kwallarsa yace " Seemah please kidaina please Seemah."
Kuka take sosai ta kasa tsagaitawa, dakyar ta daina sai kuma ta shiga ajiyar zuciya akai akai.
Jalal kam har karfe 12 yana nan a tsaye, harsu Kawo da Abba da Habib suka koma gida sukabar Dad agun Hajiya, Ammar agun Seemah.
Kowa mamakin yanda yak'i tafiya yakeyi, gashi a tsaye yake ko gajiya baiyi ba ne ko me? Dad yana tsaye ta window yana kallansa, har bacci yafara d'aukan Dad, Ammar kam gun Seemah ya koma, ya kalleta yace " Seemah, Jalal fa na waje tun kafin magrib yake a tsaye a waje."
Kallansa tai cikin mamaki idanunta suka ciciko tace " Yaya?"
Jinjina mata kai yai yace " ko na karshe ne ki ganshi kuyi sallama."
Ta share hawayenta tare da cewa "Ya Ammar?"
Mik'ewa yai ya fito tare da kallan Jalal da kana ganinsa kasan dauriya ce kawai yakeyi ta jaruman maza amma tabbas ya gaji, ya kalleshi yace ka shiga.
Jalal ya d'ago ido tare da murmushi yace " tnz Ammar."
Sai dai me? Sam ya kasa d'aga kafarsa jiyai kafar tamai nauyi, sai Ammar ne ya taimaka mai ya shiga d'akin, a tunanin Ammar Dad yayi bacci, sai dai Dad jin magana yasa ya lek'o ta window yana kallansu har Jalal d'in ya shiga.
Kusa da Seemah ya zauna, sam ta d'auke kai daga kan Jalal, Ammar ya fita ya basu guri.
Jalal ya kalleta baisan sanda hawayen da yake b'oyewa suka zubo ba, a hankali yace " Meemah ya jikin?"
Jin sunan Meemah da yak'ira sai da zuciyarya ta amsa, batasan sanda ta kalleshi ba, idannunta na hawaye, yace " ya akai kika rame haka a kwana d'aya? Bakya cin abinci ko? Hala shiya haifar miki da zazzab'i."
Ta had'iyi wani abu sannan ta kalleshi tace " meyasa kazo nan? Bayan banasan ganinka?"
Jalal ya girgiza kai hawaye ya zubo mai yace " ta ina zakik'i san ganina bayan zuciyarmu na tare?"
Ta share hawayenta tace " a da kenan."
Jalal kalmar har ransa ta tab'a amma ya d'aure yace " bana tunanin a da ne, tunda haryanzu zuciyoyinmu basu rabu ba."
Mik'ewa tai ta zauna fuskarsu na kallan juna ta goge hawayenta tace " Deen I can't be with you ko da kuwa sanka shine zai zama ajalina, mahaifinka ya cuceni, ya cuci mahaifiyata, ya cuci Dad d'ina bama haka ba ya cuci duk zuri'ata data Dad banajin zan iya yafe mai."
Jalal ya kalleta cikin mamaki, idanunsa ya zaro yace " Meemah me kike nufi da kalamanki."
Hannu tasa ta fara dukan kafad'arsa tana kuka tace " Meyasa zuciyata bazata tsaneka ba why?"
Jalal ya rik'e hannunta yace " Meemah me mahaifina yai?ban gane ba?"
Ganiyai jikinta ya shiga rawa, duk ya rud'e tare da K'iran sunan ta, ai ganiyai tayi luuu gab'a d'aya jikinta.
Da karfi yake k'iran sunanta yana hawaye, Amnar ya shigo da sauri, ganin haka yasa ya fita k'iran likita.
Abinda yaban mamaki, Jalal nagani ya tsuguna yana kuka kamar mace, a raina nace baka fara bama d'an saurayi.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 5⃣0⃣
Jalal ganin Seemah a sume ya rasa inda zaisa kansa kuka kawai yake, yarasa meke faruwa shikem, addu'a kuwa duk wacce tazo mai yi yakeyi, kallanta yakeyi zuciyarshi sai kuna takeyi, Ammar ne yashigo da likita da sauri, nan likitan ya shiga duba Seemah, ya samu ta dawo daidai ya kalli Ammar da Jalal yace " ba nace kar a tada mata hankali ba? A barta ta samu nutsuwa ba? Ina tsorace muku abinda zai faru inbaku kiyaye dokukin nan ba."
Yana kai nan yai waje, Jalal ya kalli Ammar da idanunsa da suka sha zubar da kwalla, yace " Ammar am.........."
Ammar ya katseshi da cewa " Jalal please get out."
Jalal ya kalleshi cike da tausayi yace " amma......"
Ammar ya d'aga mai hannu tare idanunsa taf da kwalla yace " Jalal kake kawai please. "
A hankali Jalal ya karasa kusa da Seemah ya kalleta cikin tsananin tausayi da bege sannan ya juya harya kai kofa yaji muryar Ammar yace " idan kaje katambayi Mahaifinka waye mahaifin Seemah, shikad'ai ne abinda muke bukata yanzu daga gareka."
Juyowa Jalal yai cikin tsantsar mamaki bai fahimci inda kalaman suka dosa ba, me suke ba Dad bane mahaifin Seemah ko me?"
Dad ya gani a bakin kofa, wani irin kallo Dad yamai, Jalal yai kasa dakai tare da cewa " Yahkuri na sab'ama umarnink......"
Hanya Dad ya nuna mai alamar yai waje, hakan yasa Jalal ya taka a hankali yai waje, yana fita yazauna akan dakalin gun, tare da rik'e kansa dake wainawa, agogon hannunsa ya kalla karfe 2 na dare ya buga, mik'ewa yai a hankali bayaji zama ya kamaceshi dole gobe da sassafe ya dira a birnin/gwari d'an jin me mahaifinsa ya sani dangane da abinda ke faruwa, kofar d'akin Seemah ya kalla tausayinta ya kara ratsashi, da alama yau tasan ba Dad bane mahaifinta sannan me ake nufi da Abbansa ya sani?
Da alama Abba ne kad'ai yasan amsar tambayoyin nan.
Seemah kam sai karfe hudu ta bud'e ido a hankali, Ammar ta kalla dake zaune akan kujera yana bacci, ta mik'e a hankali tare da yaye bargon da aka rufa mata, tai bakin kofa, a hankali ta bud'e kofar gudun karta tasheshi.
D'akin Hajiya ta shiga, Dad na zaune shima yana bacci, ta karasa kusa da Hajiya tare da rik'e hannunta da hannuwanta biyu, Hajiya ta bud'e idanunta ta kalleta, Seemah hawaye suka zubo mata tai kasa da ido tace " Hajiya kiyi hakuri nasani dolene ki tsaneni, ko nice akama d'ana haka dolene in tsani duk masu hannu a harkar, sai dai nasani a kasan ranki baki tsaneni ba."
Kallanta Hajiya tai da alamar tambaya, Seemah ta matse kwalla tare da kakaro murmushi tace " da kin tsaneni nasan da kin tilastama Dad ya rabu dani, da bazaki bari har ya rainani izuwa yanzu ba."
Ta zare hannun hagunta ta share hawayen dake mata gudu tace " Nagode Hajiya da taimakonki, nagode sosai Allah ya saka da alkairi."
Hawaye ke zuba a idanun Hajiya a hankali tasa d'ayan hannunta akan Seemah sai dai abinda takeji a kirjinta mai nauyi yasa ta kasa magana, Seemah ta girgiza mata kai tace " A'a hajiya basai kince komai."
Tai ajiyar zuciya sannan tace " Hajiya na rok'eki ki yafema mahaifiyata da ni, d'an Allab ba dan mu ba."
Seemah na kawo nan taji kuka na neman kufce mata, Seemah tasa kanta a jikin gadon ta shiga kuka mai tab'a zuciyar mai sauraro.
Dad kam tunda ta shigo yanajinsu, kawai dai yayi shiru ne, Hajiya tasa hannu ta d'ago fuskar Seemah tare da share mata hawaye.
Sun dad'e a haka kafin Ammar ya shigo da sauri, a firgice yake da alama yad'auka ko Seemah ta gudu me ko wani abun, ganinta kusa da hajiya yasa ya saki nannauyan ajiyar zuciya, Seemah ta kalleshi tare da mik'ewa.
Bayan Sallah asuba su Dad sun tafi massalaci, suna dawowa suka ba kamar yanda suka barta ba, da sauri Dad ya karasa tare da tab'ata sai dai inaaaa.... Allah ya d'auki ran abarsa.
_Allah yasa mu gama da duniya lafiya Amin_
Ba karamin tab'asu tai ba wannan rasuwa, abu goma da ashirin.
Sun dawo dukansu gidan Abba anan aka mata wanka, Seemah ma ta matsa dole itama ta dawo gida.
Jalal kam yana sallar asuba ya wuce tasha, a mota a zaune kawai yake zuciyarsa taf take da tunani kala kala.
Sun isa birnin gwari ya hau mashin ya karasa gida, yana sauka ya tsaya a kofar gidan tare da kwankwasawa, ba'ai minti 2 ba akazo aka bud'e, ga mamakinsa kanwar mamansa ce, tana ganinsa ta saki guda ya shiga tare da cewa " Goggo yaushe kika zo?"
Ai ba gama rufe baki ba yaga 'yan uwan Abba da Umma suna ta fitowa ya kallesu da mamaki yace " toh! Taran me ake haka?"
Goggo ta harareshi tace " Lalai wannan Angon ba kunya, watoma da alama bakasan a taru ayi zumunci a bikinka."
Jalal ya maimaita kalmar Ango?
Umma ce ta fito fuska d'auke da fara'a tace " Jalal me kake a tsaye bazaka shigo ka kwashe gaisuwa ga 'yan uwa ba?"
Ya d'anyi murmushi kad'an sannan ya shiga ya zauna sannan ya fara gaishesu, kowa sai tsokanarsa suke, ya mik'e tare da tambayar Umma ina Abba?, tace " ya fita d'azu zaije siyo kayan abinci." sai alokacin ya kuka da har fenti anyi a gida, badai da gaske suke ba?
Yace "Zaheeda fa?"
Tace " tana d'aki." Nan ya wuce ransa duk a dagule, kusa da Zaheeda ya zauna, ta kalleshi tare damai murmushi yace " Kanwata da alama kina cikin farinciki, ko duk ganin 'yan uwa ne?"
Muryar Umma yaji tace " Dad'i takeji zaka auri 'yar uwarta Zainab."
Jalal ya juyo ya kalli Umma yace " Wai Umma meyasa kuke min haka? Nifa ban d'auka abinnan da gaske kuke yi ba."
Umma ta had'e rai tace " baka sani ba mai ya kawoka to? "
Jalal yad'an furzar da iskar bakinsa yace " Zuwa nai muyi magana da Abba, ni banajin ma zan iya jiranshi ya dawo, Umma kawai fad'amin inda yake."
Umma ta kalleshi tace " Ba dai cewa zakai ya janye auren ba?"
Jalal yad'an juya kai yace " ni auran nan ba'a gabana yakeba Umma, abun da ke damuna yafi karfin wannan auran."
Umma ta kalleshi da mamaki tace " Badai......"
Jalal yai saurin cewa " Umma d'an Allah ina Abba?"
Tace" Yana lambun Basiru."
Jalal ya mik' e tare da kallan Zaheeda sannan ya juya, Umma ta matso kusa dashi tace " Jalal yanaga kamar ka fad'a? Sannan da alama akwai abinda ke damunka naga gaba d'aya fuskarka ta canza."
Kallanta yai sannan ya runtse ido yace " Umma banaso 'yan uwa susan abinda ke damuna shiyasa nake kok'arin b'oyewa kibari inje gun Abba tukun."
Tai ajiyar zuciya tace " to sai ka dawo."
Jalal ya fito, sai tsokanarshi ake, shikam sai yake kawai yake musu, yana fita Goggo ta shigo gun Umma tace " Yaya Habiba nikam kamar Jalal baya farin ciki."
Umma ta kalleta tace " meyasa kikace haka?"
Goggo ta d'an rik'e hab'a tace " gaskiya bama haka Jalal yake ba sam, naga kamar ya canza, halayarsa ma kamar ta canza, Allah dai yasa ba wani abun bane."
Umma ta kalleta sai dai ta kasa bata amsa, Addu'arta d'aya Allah yasa ba zancen nan Jalal zaina Abbansa ba.
Jalal kam kai tsaye Lambun Basiru makocinsu ya isa, yanazuwa Basirun yace " yanzu kuwa yabar nan, ya koma gida."
Jalal ya juya yai hanyar gida, wayarsa ya rik'e wazai k'ira ya tambaya jikin Seemah?
Da sauri ya k'ira Sagir bayan sun gaisa yace "Sagir d'an Allah ka dubomin halinda Seemah ke ciki."
Sagir yace " to, nan sukai sallama."
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀