Seemah nata sauri dan ganin lokacin fita makarantarta yana neman kurewa yau ne suke taron kammala karatun degree da sukai, ta fito cikin riga da wando, rigar pink ce an rubuta sunanta a baya sai wando jeans baki, shigar da kowa zaiyi kenan, mayafi ta d'auka black tai rolling d'in kanta dashi tayi kyau sosai ta zura abaya baka ta d'au jaka ta fita.
A falo ta tadda Dad na karatun jarida ta gaidashi ya amsa yana cewa baby kin fito? Ta d'an turo baki tace " A'a Dad nifa nace banasan Baby nan shekarata fa 22 yanzu."
Yai dariya tare da cewa kiyi sauri ki fita sai mun iso, ta juya tana mai bye bye da hannunta, motarta ta fad'a ta kunna wakar data saba ji ta Kabhi Kush nan ta fara tuki cikin kwarewa, agoggon ta data ajiye a saman kan motar ta kalla tai murmushi tace " Good morning Deen." Ta fad'a tare da murmushi, tana isa makaranta tai parking sannan ta fito, ta shiga cikin kawayenta turawa da indiawa suka hau murna dan kuwa ba karya ranar murna ce.
An gama shirya komai nan mutane suka fara isowa, taro ya fara gudana, Seemah kam sai zirga zirga takeyi fuska a had'e waya ta d'aga ta kira Ammar abin haushi bai d'aga ba tai kwafa sannan ta kara kiransa, nan ma bai d'aga ba, haushi ya turnuko ta ta kira Ya Habib, ringing biyu ya d'auka ta shagwab'e murya tace " Yaya sun taho?"
Habib ya kalli Ammar yace " Wayyo kanwata kiyi hakuri bazasu samu damar zuwa ba."
Idanunta sukai rau rau tace " Harda Ya Ammar?"
Habib ya guntse dariyarsa yace " Ahh Ai Ammar ma bayanan ya tafi meeting. "
Cikin masifa tace " Meeting?"
" eh akwai wani babban Project da muke san yi ne to shine......"
Katse wayar tai a zuciye ta koma ciki.
Zama tai tare da hard'e hannayenta lalai ma Ya Ammar d'innan, ko a mafarki bata tab'a tunanin zai fifita aikinsa a kanta ba kwalla ta zubo mata, ta share tare da d'aukan wayarta kamar yanda ta saba, numberta datai saving ta bud'e ta tura ma kanta sako kamar haka " Deen yau an b'atamin rai, Ya Ammar da Ya Junaid bazasu hallaci taron kammala karatu na ba."
Tana gamawa ta turama kanta, tun bayan tahowarta duk abinda ya sameta sai ta tura ma kanta sako da zummar Jalal ta turama hakan na saukaka mata zuciyarta duk da kuwa tasan ba zai gani ba.
Tana nan a zaune wata kawarta yar Korea Yoo jung ta shigo, dafata tai tace mata " Someone is looking for you."
Seema ta kalleta tare da tab'e baki tace " Yoo Jung I am not in the mood to joke with you. "
Tai mata murmushi tace " 3 handsome men and one young girl."
Seemah ta kalleta da sauri sannan ta mik'e tsaye tace " are you sure? "
Ta d'aga mata kai tana murmushi da sauri Seemah ta waje.
A tsaye ta hangosu daga nesa, Ya Junaid, Ya Habib, da Ya Zaid, ta saki murmushi ganin Zahra a kusa dasu, juyawa ta d'anyi da kanta da alama wani take nema, ganin ba kowa yasa ta karaso kusa dasu, tare da kallan Ya Habib tace " Yaya shine d'azu baka fad'amin bako?"
Zahra ta matso kusa da ita tace " Seemah oh ni ashe zan ganki?"
Seemah ta d'an harareta tace " ni bansan wani dad'in baki yausge rabon da ki kirani?"
Junaid ya d'an matso kusa da Zahra yace " yanzu kuma metayi? Daga zuwa ganinki?"
Seemah ta juya kai tace " dama nasani ai yaya yanzu ka daina sona."
Zaid ya matso saitin kunnenta yace " kyalesu ni kaina bana shiga harkarsu sun zama super glue. "
Dariya tasa ta kalli Zaid tace " Ya Zaid at least kai nasan kana bayana."
Sun je shiga kawai taji jikinta ya bata kamar ana kallanta juyawa tai a hankali, da sauri ya lab'e a jikin bango, ta d'an kurawa gun ido kad'an Zaid ya kalleta yace " muje mana."
Ta d'an juya kai maybe mistake take, wanda ya lab'e ya fito tare da bin bayanta da kallo yai murmushi yace " Congratulation Meemah."
Ya juya yana murmushi, direct Airport ya nufa.
Seemah kam suna zazzaune a sama akan kujera ana kiransu d'aya bayan d'aya ana basu kwallin karatun diploma d'insu, kallan kofa take tayi d'an bataga Dad ba har a lokacin, kanta ta sukuyar fuskarta ba yabo ba fallasa, an kira sunanta kenan, ta mik'e a hankali tare da kara kallan kofa, wa zata gani? Ammar ta gani a tsaye ya hard'e hannayensa yana mata murmushi, itama murmushin tamai wani farin ciki ya kara kamata, a hankali ta karasa ta amsa sannan aka tafa mata ta koma ta zauna fuskarta d'auke da fara'a.
A hankali Ammar ya karasa ya zauna yana kallanta, ana gamawa ta mik'e da sauri ta karasa kusa dashi, Ammar ya kalleta cikin tsananin bege yasa hannu a hab'arda yace " Ahhh anya kuwa Seemah tace? Ba sai na shiga bincike ba?"
Ta ballamai harara tace " Yaya nifa nayi fishi dakai."
Yad'an saukar da kai kasa yace " Shikenan tunda bakiso ganina ba bari na juya na koma."
Ya fad'a tard da fara tafiya, da sauri ta karasa kusa dashi ta rike rigarsa ta baya tare da cewa " Wasa fa nakeyi yaya."
Ya juyo tare da sakin sansanyan murmushi yace " nima wasa nake, ya za'ayi in tafi in bar amarya ta?"
Ta d'an sadda kai kasa itakam ta kasa sabawa in yai irin wannan zancen bata iya mayar mai.
Zaid ne ya karaso kusa dasu yace " hmmm yau fa ba kanta Ammar yaga Seemah."
Seemah ta kalleshi tace " Yaya Zaid?"
Zaid ya girgiza kai yana nuna Ammar yace " wannan mutumin? in kinsan abinda yakemin kullum da dadd......"
Da sauri Ammar ya matso ya toshemai baki yace " To shigaban san magana banaji an tambayeka ko?"
Seemah ta kallesu tai dariya nan su Ya Habib suka matso aka cigaba da hira.
Jalal kam yana isa da kusan hour 1 sannan suka tashi zuwa kasar mu, a kasar Abuja suka sauka, ganin dare yayi yafara tunanin ko zuwa hotel.
Mota yahau ya wuce hotel yana shiga d'aki ya cire coat d'in jikinsa ya fad'a toilet, bayan ya fito ne ya kunna wayarsa sannan ya kira wata number, ringing biyu aka d'aga, Jalal yai sallama, da sauri mutumin ya amsa tare da cewa " Haba Malam Jalal tun wancan satin nake jiran kiranka amma shiru banji ka kira ba."
Jalal ya mik'e tare da zuge labulan window ya kalli waje tare da cewa " Director na amince da aiki a gidan tv d'inku sai dai inada sharad'i guda d'aya."
Ya saki wata dariya sannan yace " nagode sosai journalists Jalal tun kana Germany yanda naga kanada kwazo da kuma kwarewa yasa nake fatan yin aiki dakai, naji dadi."
Jalal ya kalli waje yace " bakaji conditions d'in nawa ba ai."
Ya kara sa dariya yace " Ai duk abinda zaka fad'a nasan bazai wuce kanasan adinga biyanka dayawa ba ko kuma akwai program dakake san yi."
Jalal yai wani murmusho yace " Indeed you are smart sai dai ba haka bane burina abu guda d'aya nakesan in fara gabatarwa kafin muxo kan wannan maganar."
Tattara hankalinsa yai gun Jalal yace " ina jinka."
Jalal yace " inaso ka gayyato mana Senate Abdullahi wanda yake kokari takarar zama shigaban kasa muyi hira dashi a program d'in dakasan yafi komai bunkasa ta tashe a gun mutane."
Shiru yai yace " Menene dalili......"
Jalal ya katseshi da cewa " karka damu ba abinda zai faru, kawai dai nasanshi ne ina kuma san inga na fara aiki dashi kafin in fara komai."
Ya jinjina kai yace " ba damuwa zan aika da takarda gayyata, inasa ran kuma zai hallarta dan mutum me shi mai san a sanshi."
Jalal ya daga gira yace " nasan da haka shiyasa banaji ta gunsa."
Suna gama waya Jalal ya kurama waje ido sannan yai murmushi yace " Malam Abdul sai mun had'u."
Sagir ya kira yace ya kawo masa abinda yace ta tattaromai yana hotel.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 6⃣2⃣
Yana gama waya da Zaid ya kira Abbansa, bayan sun gaisa ne yace " Abba kun isa lafiya?"
Abba ya kalli Zahida dake kwance, yace " gamunan tun azahar muka iso, gaskiya asibitin nada kyau ga kulawa."
Jalal yai murmushi yace " Mai suka ce gama da ciwon ta?"
Abba yai shiru can yace " Sunce ba wani abu bane serious kawai dai tun tana karama ya dace mukaita asibiti sai dai barin kashinta da mukai har yai kwari haka shine zai sa a sha wahala kafin ta mik'e."
Jalal ya jinjina kai sannan yace " Dad ya dawo yau."
Gaban Abba ne ya fad'i yai shiru baice komai ba, Jalal ya cigaba " Bai tsaya taron kammala karatu Seemah ba naga yataho." yai ajiyar zuciya sannan yace " tunda ka duba komai na asibitin sannan Umma nacan ka dawo muje ka roki gafarar Dad hakan zaisa Allah ya dubi zuciyarmu ya ba Zaheeda lafiya."
Abba ya runtse ido sannan yace " gaskiya ne Jalal na auna naga gudin nan danakeyi ya isa haka, abinda yafi dacewa dani shine in nemi gafarar Isma'il ita kad'ai ce zatasa hankalina ya kwanta."
Jalal ya d'an murmusa kad'an yace " yaushe zaka taho nan d'in?"
Abba yace " gobe ma, mai zan jira?"
Jalal ya jinjina kai yace " inkazo gobe sai muje jibi."
" Allah yakaimu, amma ka kira Zainab?"
Jalal yad'an tsuke fuska kad'an yace " Zan kirata."
Abba yace " Jalal ba dan ni ba saboda darajar aure agun ma'aiki zaka duba, nasani sarai Zainab bata gabanka ba kuma santa kake ba, sai dai kada ka manta d'aura muku aure akai, hakkinta dake kanka yazama dole ka saukesu in dai kana neman rahamar Allah. "
Jalal yai shiru, can yace " Zan kirata Abba."
Nan sukai sallama.
A bakin gado ya zauna ya kurama sunan ta ido dake kan wayarsa, Zainab yasa ya dade yana kallan sunan kafin ya daure ya kira.
Zainab kam ita kad'ai aka bari a gidan hakan yasa ta d'auko kanwarta, suna zaune suna 'yar hira sama sama ita wani sa'in mantawa ma take tanada wani aure, ganin kiran Jalal yasa taji gabanta ya fad'i rabonta dashi har ta manta, mik'ewa tai ta shiga d'aki da sauri, ta zauna a bakin gado sannan ta d'aga wayar.
A hankali tai sallama, Jalal ya amsa tare da cewa ya gidan? Tace lafiya kalau, shiru sukai dan basusan me zasu cema juna ba, can Zainab ta daure tace " Umma tace yau zaka dawo kasar nan ko?"
Jalal yace "nama dawo ina Abuja ne."
Zuciyarta taji ba dad'i amma ta daure tace " Yaushe zaka dawo nan kenan?"
" Ina da aiyukan yi anan zan d'au lokaci kafin in dawo."
Ta jinjina kai a ranta tace " Lokaci? Shekara 2 tayi kad'an kenan?"
Jalal ya katseta da cewa "ba abinda kike bukata ko?"
A zuciyarta tace " me nake bukata kuwa banda inganka?"
Amma a fili tace " babu."
Yace " okay" batai auni ba taji ya katse wayar, tabi wayar da kallo idannunta suka ciciko da kwalla ya zatayi?
Jalal kam agoggon hannunsa ya kalla wanda yakai aka canza mai glass d'in kullum yanzu shi ne a hannunsa ko da wasa bazakaga yasa wani agoggonba bayan shi, murmushi yai yace " Yau nasan kina cikin farin ciki mai yawa."
Kan kujera ya zauna ya d'auko laptop d'insa ya bud'e yafara aikinsa.
Jalal kenan in ka ganshi yanzu bazaka ce shi bane da, kwarewa da kwazo sun canzashi, kaifin tunaninsa ya karo sosai fiye dana da, tunda yabar kasar nan ya fara karatu ya samu wani company na gidan radio yana musu aiki, in zasu dauko rahoto ko wani bincike dashi ake zuwa, hakan yasa ya samu experience dayawa akan harkar karatunsa, haka kuma kud'in da suke biyanshi mai d'an kauri ne, ga kud'in da aka basu na scholarship.
Sunso rikeshi acan amma inaaa ai ko da wasa bai tab'a sawa a ransa zai iya zama a wata kasar ba.
Seemah kam sun gama taro an d'au hotuna kala kala, sun koma gida abin haushi wai Dad har ya tafi Nigeria shida matarsa, haka suka baje a falo akai ta hira, Seemah kam ganin hirar taki karewa yasa ta sulale ta gudu d'akinta, tana shiga tana kokarin Zama a bakin gado tace an murd'a kofar, ta kalli kofar da sauri, Ammar ne ya shigo da sallama ta kalleshi tad'an had'a rai kad'an tace " Yaya baka kwankwasa bafa?"
Ya had'a hannunsa biyu yace " au amin afuwa." Ya fad'a tare da komawa ya rufe sannan yai knocking, tad'anyi dariya sannan tace shigo, nan ya shigo yana cewa " yanzu dai banyi laifi ba ko?"
Ta d'aga kai tare da zama, ya matso ya zauna kusa da ita sannan yace " ya kamata ki kwanta da wuri d'an nasan kin gaji gashi gobe zamu tafi."
Ta kalleshi sannan tace " Yaya?"
Yace " Ummm"
Ta girgiza kai tace " Shikenan ma."
Yad'an d'aure fuska yace " So kike muyi fad'a?"
Ta girgiza kai tare da cewa " ba fa wani abu important bane."
Ya harareta tare da kafeta da ido, tai kasa dakai tana wasa da 'yan yatsun hannunta tace " Yaya dama so nake ka tambayar min Dad a wani gari mahaifiyata take sunan kawai nake san ji."
Ya kalleta cikin tausayawa yace " Karki damu insha Allah kafin aurenmu zan kaiki har garin."
Kai ta girgiza mai tace " basan zuwa nakeyi ba nima kawai sunan nake san ji."
Ya kalleta kawai baice komai ba, cam ya wayence yace "Saura wata d'aya bikin mu ba wani abu da kikeso ko kike tunanin yi?"
Kallansa kawai tai sannan ta girgiza kai, alamar a'a, jikinsa yai sanyi amma ya daure ya shiga bata labari har sai da ta saki ranta, sun dad'e suna hira kafin Ammar yai shiru, kallansa tai tace " Yaya lafiya?"
Ya mik' e jiki a sanyaye ya tsugunna a gaban Seemah tare da rik'o hannayenta, a hankali ta d'ago ta kalleshi ta kasa furta komai, Ammar idanunsa na kanta, ganin bazata iya jure kallan dayake mata ba yasa tai saurin yin kasa da idanta, Ammar cikin wata irin murya mai ban tausayi taji yace " Seemah wani abu na damuna."
D'ago wa tai ta kalleshi idannunta sukayi raurau tace " Name fa?"
Ya kalleta a hankali yace " Tunda aka fara zancen auren mu ba wanda naji ya tambayeki ko kin amince da hakan, na sani sarai haryanzu son da kike ma Jalal bai bar zuciyarki ba haka kuma bana kaunar wani abu dazai sa in zama nine sillar tauye miki rayuwar farin cikin ki, Seemah ina tsoro......."
Hannu tasa ta rufe mai baki hawaye suka zubo mata a hankali ta shiga girgiza mai kai, tace " Ya Ammar na san sarai meke ranka haka kuma nice na zab'a ma kaina auranka bawai d'an ance ba, a'a sai dan nima na amince, kasani sarai bazan iya auran Deen ba bayan abinda ke tsakanin iyayenmu bazan tab'a bin san zuciyata ba akan farin cikin ka dana Dad, nasani kuma ko ince jikina ya bani da ace mahaifiyata nada rai itama wannan zab'in zata min."
Ta share hawayenta sannan ta zare hannunta daga bakin Ammar tad'an yi murmushi tace " Karka damu Yaya nasani a hankali zuciyata zata manta da Deen sannan ka manta shima yayi aure? Maybe ma ya manta dani."
Ammar ya goge kwallar data zubo mai yace " Seemah?"
Mik'ewa tai da sauri tad'an juyamai baya tace "Yaya nafi kowa sanin babban farin cikinka a duniya bai wuce ka ganni ina cikin farin ciki ba na sani sarai da hakan sai dai nima bazan iya jurar ganinka cikin bakin ciki ba."
Ammar ya matso kusa da ita baice komai ba sai dai kalamanta sun mai dad'i sosai, juyowa tai ta kalleshi sannan tamai murmushi.
Kasa magana yai hakan yasa ta rangwab'ar dakai tace " Yaya baza'a barni in kwanta da wuri ba?"
Da sauri yai hanyar waje yana cewa " Inafa zanso hakan."
Ta kalleshi har ya fita, yana fita ta sulale ta tsugunna a katsa tare da rufe fuskarta da hannu biyu, hawaye ne suka gangaro mata ta d'aga hannu sannan tace a fili " Allah na rok'eka ka yayemin san Deen daga Zuciyata kakuma taimaken soyayyar danake ma Ammar ta 'yan uwanta ka ta juye ta koma soyayyar aure."
Nan ta shafa sannan ta zauna a gun.......
Washe gari da safe suka hau jirgi suka baro kasar England....
Nima nace Allah ya tsare...
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 6⃣3⃣
Jalal kam da safe ya shirya ya fita, gidan Tv d'in *KARAMCI* ya nufa yana isa ya kira director Abbas, nan ya turo aka shiga dashi ciki, sai da aka gama yawo dashi ya gama kallan ko ina kafin ya karasa cikin office d'insa, yana shiga yaga mutane guda uku, nan ya mik'a musu hannu suka gaisa, bayan sun nutsune Director ya kalli Jalal sannan ya kallesu yace " Shine wanda nake baku labari, wanda da kyar ya amince da aiki damu."
Suka kalli Jalal sukai dariya d'aya daga cikinsu yace " lalai munsha labarinka tunda ya dawo daga Germany bashida hira sai ta ka."
Jalal ya d'an yi murmushi kad'an sannan yace " naga ko ina ba komai yayi sai dai na duba programs d'inku kamar akansu ne zamuyi gyara sannan bakwa zuwa neman rahotanni da kanku, in har munaso gidan Tv d'innan ya zama ba kamarshi to sai mun dinga yawon d'auko rahotannin dazai sa hankalin mutane ya raja'a a kanmu."
Director ya kwashe da dariya yace " hakane kam, ya kuka ga Journalists d'in namu?"
Nan suka shiga tafamai sukace lalai munyi dace.
Jalal ya juya kai shi mamaki yake gani yai abin baikai abin dariya ba ko tafamai ba amma ya kasa gane meyasa sukeyi.
Nan ya fara tambayarsa akan program d'in dayace yanaso yai, Abbas yai murmushi yace " Jalal anyi dace shi da jiya dana kirashi ma cewa yai ko yau ne ayi saboda dama zab'e ya kusa yanasan ya nunama talakawa yanda yake kaunarsu."
Jalal yai wani mugun murmushi yace " gaskiya ne yanzu ka d'an kirashi muje ko gobe yanada lokaci."
Ba musu Abbas ya kirashi, PA d'insa ne ya d'auka nan Abbas ya mai bayanin dalilin kiran, PA d'in yace "ok ba damuwa in ya fito daga meeting zan kiraka."
Bayan sunyi sallama ya kalli Jalal tare da fad'amai abinda ya faru, Jalal yace " ba wani abu nizan koma yanda kukai naji, sai dai ina so ka fad'amai shirin da zamuyi dashi LIVE zamuyi, munayin shirin alokacin kuma mutane suna kallo ba wai sai mun gama anyi editing ba ko wani abun."
Abbas ya jinjina kai yace " zam sanar mai."
Jalal ya musu sallama ya fita, gun Sagir ya wuce ya tattara takardun dayasa Sagir ya had'amai sannan yace " Sagir gida nake nema ina tunanin zan fara aiki anan gwara in nemi gida."
Sagir ya kalli Jalal yace " Karka damu zansa a dubama amma wani iri kake so?"
Jalal yai shiru can yace " gida dai dabazai wuce daidai karfina ba, kamar falo d'aya da d'akuna uku, saboda ina tunanin in nace zan dawo nan sai an tilastani d'auko Zainab."
Sagir ya girgiza kai yace " Yanzu Jalal matar taka ce sai ma an tilastaka zaka d'auko ta?"
Harararsa Jalal yai yace " mubar maganar nan kar raina ma ya b'aci."
Sagir ya girgiza kai yace lalai Jalal, wayarsa ya d'auko ya kira Abba, bayan sun gaisa ne Abba yace yanzu zamu taho inaji wajen magrib dai zamu iso, nan sukai sallama.
Su Seemah an dawo gidan Abba, kowa murna yakeyi,nan Dad ya sanar musu cewa ya shirya 'yar karamar walima gobe na taya Seemah murnar gama karatunta.
Dadaddare Abbas ya kira Jalal ya sanar dashi Abdul ya amince gobe da karfe 2 zai zo su gabatar da wannan shirin, Jalal ya saki wani murmushin farin ciki, Abba dake zaune yanacin abinci ya kalleshi yace " Jalal kai da waye naga kana farinciki haka?"
Jalal ya girgiza kai yace " ba komai, gobe in Allah yakaimu sai dai kai ka fara zuwa gidan su dad d'in ni sai zuwa la'asar zan karaso."
Abba ya jinjina kai yace " gwara hakan ma dama banasan muje tare insaka bada hakuri akan abinda bakama sani ba."
Jalal yai shiru baice komai ba, komawa yai kan kujerar da aka ware a d'akin hotel d'in dan masu aiki ya kunna laptop d'insa ya fito da takardunsa ya shiga dudubawa, har Abba yai bacci sai wajen karfe 1 sannan shima ya kwanta a kasan carpet d'in d'akin.
Jalal tun karfe bakwai da rabi ya fita sai dai ya samu wani driver da taxi ya sanar dashi karfe 1 yaxo ya d'auki Abba yakuma mai kwatancen inda za'akaishi, gidan Tvn Karamci ya wuce nan suka shiga shirye shiryen gun da zasuyi program d'in haka kuma tun jiya aka d'inga tallan shirin a gidan tv har yau da safe, komai ya shiryu yanda ya kamata.
Karfe 1 Abba ya fito duk da jikinsa a sanyaye yake sai dai inya tuno Zahida sai yaji bayajin shakkar ko ma menene.
Sukam gidan su Abba kowa yana cikin farin ciki, sani ne ba'ai ba amma Abba da Dad sun sa Mami da matar dad sun gama shirya komai na lefe yau ne kuma suke sa ran a nunama yaram tunda dai komai a gida ne, gida sai farin ciki akeyi, Abba ya karaso gidan ya tsaya a bakin kofa, mai gadi ya kalleshi yace " Malam gun wa kazo?"
Abba jiki a sanyaye yace " Isma'il nake nema."
Mai gadin yace " yana ciki zaka shiga ko a kirashi?"
Abba ya d'aga mai hannu yace " bakomai bari na shiga."
Nan Abba ya shiga harabar gidan ya tsaya yai shiru,; Ammar dake zaune a harabar gidan ne ya kalleshi da mamaki ya taso yazo kusa dashi, hannu ya mik'amai suka gaisa, Ammar yace " wa kake ne....."
Kamar Jalal dake d'auke a fuskar Abba ne yasa Ammar kasa karasawa, A ba yai d'an murmushin yak'e yace " Isma'il nanan kuwa bawan Allah?"
Ammar ya kara kallansa yace " yana ciki anma....."
Abba ya katseshi da cewa " Amadu sunana mahaifin Jalal."
Da sauri Ammar yai baya cikin mamaki yake kallansa, Abba yai murmushi yace " Ka ganeni kenan d'an saurayi, da gani kai sa'an Jalal ne nasan bazai wuce Ammar ba ko?"
Ammar ya kalleshi idanunsa sunyu jaa, Abba yai jinjina kai cikin kalar tausayi yace " ga kamanan ai nagani."
Ammar ya daure dakyar yace " muje yana ciki."
Abba ya gyad'a kai sannan yabi bayanshi.
Sun isa kofar falon, Ammar ya kwankwasa, Abba, kawu, Dad, da Habib suna zaune suna hirar yanda suke tunanin auren zai kasance, jin kwankwasa kofa yasa suka maida hankalinsu kan kofar.
A hankali Ammar ya murd'a kofar ya shigo, kallanshi sukai sai dai gani sukai shima yana kallan kofa, hakan yasa suka maida hankalinsu kan kofar d'an da alama wanine zai shigo.
Abba ne ya matso a hankali kansa a kasa, Dad ya kura masa ido, gani sukai Dad ya mik'e cikin b'acin rai ya nuna Abba yace " Amadu me kakeyi anan?"
Abba ya d'ago idanunsa da suka ciciko, Abban Zaid ma ya mik'e a zuciye yace " kai ko kunya bakaji ba ka zo gidan nan?"
Abba cikin wata murya yace " Ku bani izinin shigowa dan Allah."
Dad zaiyi magana kawu ya katseshi da cewa "ya isa haka, bakon mu ne bako kuwa ku menene ba'a wulakantashi."
Kawu ya kalli Abba yace shigo ko?
Jiki a sanyaye Abba ya shiga gwiwowinsa ya sa a kasa ya sadda kansa kasa, duk yanda yaso ya b'oye hawayensa sai da suka zubo ya share tare da d'agowa ya kalli Dad yace " Isma'il na fi kowa sanin yanda ka tsaneni haka kuma nafi kowa sanin dalilin tsanar dakamin, naci amanarka na kuma yaudareka, nasakaka a kuncin rayuwar da duk farin cikin da kake ciki bazai d'aikema wancan bakin cikin ba."
Ya goge hawayen dake zubo mai yacigaba " Na rok'eka ka yafemin ba wai dan ni ba sai d'an darajar ma'akinmu, Isma'il naga ishara kala kala akan cin amanar abotar danai, yarinyata tana kwance ko mek'ewa batayi haka magana tun tana karama take a kwance."
Ya kara goge hawayensa yacigaba " ga yaron da nakeso Jalal san da yakema Seemah ya wuce duk yanda kuke tunani saboda ita ya canza karatunsa sannan mun mai aure amma inaa babu alamar shakuwa ko wani abun tsakaninsu, wannan abun danai yasa d'ana haka cikin yanayin daban tab'a tunani ba sam yadaina farin ciki......."
Kuka ne yaci karfinsa, kowa yai shiru Ammar ya share kwallarsa, Dad kam kansa yai kasa dashi Abba ya d'ago cikin tsananin kalar tausayi yace " Isma'ila ka yafemin ni nasan abinda na gaji tun bayan faruwar abin nan muke cikin rashi mai karfi, Jalal shi yai wahalar karatunsa haka kuma ya taimakemu, sai yanzu da Allah yataimakeshi ya zama wani abun, ka yafemin ko d'ana zai fara aiki cikin sa'a sannan yarinyata ta samu lafiya."
Sunyi shiru kowa ya kasa magana sai dai tausayin Abba ya ratsa kowa, agoggo Abba ya kalla, ganin karfe 2 daidai yasa ya kalli Abban Zaid yace " D'an Allah a kunna tashar Karamci Jalal yace yanada sako mai amfani dazai isar, sannan Seemah ta taimaka itama ta kalla."
Kallan mamaki sukai mai, Habib ya mik'e da kanshi ya kunna sannan ya kalli Ammar yace " ka kira Seemah muga sakon."
Ammar ya juya ya fita.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 6⃣4⃣
Seemah ta shigo falon itada Ammar da Zaid, kowq ya tattara hankalinsa akan Tv d'an ganin me Jalal ke kokarin isarwa.
A b'angaren Jalal kuwa bayan sun gama shirya komai, Senate Abdul ya shigo cikin isa directors da producers d'in kowa ya fito yana gaidashi, Jalal kam na zaune akan kujerar da zai gabatar da shirin, bayan sun gama gaisawa ne Senate ya kallesu yace " da wa zamu gabatar da shirin ne? Ban samu na ganshi ba."
Abbas ya juya yana neman Jalal can ya hangoshi gaba d'aya ma hankalinsa baya kansu, da karfi yace " Jalal?"
Juyowa yai ya kalleshi, Senate ma ya kalli inda director d'in yake kallo, Jalal ya musu murmushi sannan ya d'aga musu hannu, Senate ya kara kallan Jalal yace " waye shi dabazai zo gaidani ba?"
Abbas yai gyaran murya yace " hmm dashi zaku gabatar da shirin takardun da zakuyi amfani yake dubawa, ai shi haka yake bashi da magana." Abbas kam yai kokari gurin kare Jalal.
Abdul yai murmushin jin dad'i a ransa yace indai bashida magana ai hakan sai yafi dad'in yin shirin.
Kara kallan gun da Jalal yake yai kamar yasan fuskar amma a ina? Watsar da tunanin yai nan ya karasa ya zauna a kujerar dake kallan ta Jalal.
Jalal ya sakar mai murmushi tare da gaidashi, Abdul ya aksa tare da cewa lokaci yayi mu fara? Ina d'an sauri ne.
Jalal ya d'aga kai sannan ya mik'e ya duba komai, sai daya tabbatar komai yayi sannan karfe 2 dot da buga, suka fara gabatar da shirin kamar haka.
Jalal ya gaida mutane sannan ya sanar musu da sabon shirin su na yau da kuma babban bakon da suka gayyata wato *Senate Abdullahi* wanda yake tunanin neman kujerar shigaban kasa.
Bayan Senate ya gaishesu ne shima Jalal ya kalleshi yace " Honourable Senate kayi mukamai da dama tun daga kan Chairman har zuwa matakin da kake yanzu, shin ka tab"a fuskantar wani matsala a harkar siyasarka?"
Senate yai murmushi yace " hmm gaskiya ban tab'a samun matsala ba sai ma kaunar da talakawa ke nunamin inajin dad'i kwarai da yanda suke bani had'in kai."
Jalal yai murmushi yace " Gaskiya ne mutane na sanka, Allah ya kara d'aukaka."
Senate ya amsa da Ameen.
Jalal yace " Yanda mutane kesanka baka tunanin ka tab'a bata ma wani rai ko musgunawa talakawa da saninka ko cikin rashin sani?"
Senate ya had'a hannayensa biyu tare da kara sakin fuska yace " a iya sanina ina kokari gurin kyautatawa talakawa da mutane ina kuma kaunar talakawa kamar yanda nakesan nawa 'yan uwan to menene zaisa ni na wulakantasu? Bayan sun zama jinin jikina."
Jalal ya saki wani mugun murmushi ba shakka wannan mutumin ya iya siyasa Jalal ya cigaba " Gaskiya ne kam kana kokari gurin kyautatawa mutane, sai dai ina fatan Allah yasa yanda kakesan talakawa 'ya'yanka ma su so ka haka."
Gaban Senate ya fad'i me mutumin nan yake nufi? Bai amsa mai ba Jalal yai saurin cewa " yanzu 'ya'yanka nawa?"
Abdul ya kalleshi me ya kawo zancen 'ya'ya nan?
Amma ya daure yace " 'ya'yana uku mata 2 sai namiji yanzu yake primary 6."
Jalal ya jinjina kai yace " Allah sarki, Allah yaraya manasu."
Abdul ya amsa da Ameen.
Jalal ya kalli Camera yace " Kada ku manta kuna tare da babban d'an siyasan nan wanda talakawa ke kaunarsa wato Senate Abdul. "
Nan aka sake nuno Senate yana murmushi.
Jalal ya kalleshi yace " Sanda ka fara siyasa kayi aure ne?"
Abdul ya girgiza kai yace " A'a lokacin dai an kusa yin auren."
Jalal ya jinjina kai yace " munji labarin matar da zaka fara aura Allah baiyi auren tsakaninku da ita ba ko?"
Abdul ya bugama Jalal wani kallo tunawa dayai live ake d'aukansu yasa ya saki murmushi yace " gaskiya ne, matsala aka samu aka fasa auren."
Jalal ya d'an gyad'a kai alamar tausayi yace "Ayya!!! Na tabbata matsalar badaga kai bane."
Abdul ya d'anyi kasa dakai kamar me shirin kuka yace " amanata taci."
A ran Jalal yace " thank God."
Jalal ya kalleshi da mamaki yace " Amana kamar tame fa? Na tabbata masu kallo suna san ji."
Abdul ya had'iyi yawo yace " Amanata taci da wani banasan tuna asiri irin wannan a bainar jama'a."
Jalal yace " gaskiya ne ai tona asiri ma bashi da dad'i sai dai muce Allah ya rufa asiri."
Abdul yace " Ameen."
Jalal ya kalleshi yai murmuaji yace " Yanzu amma nasan ka yafe mata ko?"
Abdul ya kalli Jalal yace " na yafe mata d'an ni mutum ne mai saukin kai banasan kulatar mutum."
Jalal yace " I see, amma shi wanda yaci Amanar taka fa? Kana da wani sako zuwa gareshi ne ko kuwa shima ka yafemai?"
Abdul ransa ya fara b'aci ya kalli Jalal sannan ya daure yace " ba wani sako danake dashi, Amanata ya riga yaci nikuma na yafemai ."
Jalal ya d'an rangwab'ar dakai sanar ya murza ido, yana bud'e idanunsa Abdul yaga idanunsa sun kad'a sunyi Jaa kana ganinsa kasan b'acin rai ne karara a bayyane a idanunsa tsoro ya fara kama Abdul.
Jalal ya kalleshi da jajjayen idanunsa yace " Amma a binciken da mukai sai mukaji kamar fyad'e akama matar da zaka aura?"
Ba Abdul ba hatta ragowar masu recording sai da suka kalli Jalal cikin tsananin mamaki, a falo kuwa gaba d'aya sun kame kallan tv kawai sukeyi.
Abbas ya rasa yanda zaiyi yama Jalal magana tunda dai abin live ne.
Abdul ya kasa magana, Jalal ya d'an murmusa ta gefe yace " Ina mamakin namijin dazai iya yafema wada yama matarsa fyad'e ana saura kwana biyu auransu."
Abdul idanunsa shima suka fara canza kala, tsoro ya fara kamashi, Jalal ya kara wani murmushin yace " gaskiya na jinjina maka ba kowani namiji bane zai iya yafemasa."
Abdul hannunsa ya fara rawa cikin rawar murya yace " haka ne ni amma daga baya nai tunanin rashin d'aukan abin da zafi hakan ne yasa na yafemai."
Jalal ya d'aga kai tare da had'e fuska yace " amma sai naji kamar wanda akace yayi fyad'en shi kuma yace sharri aka mai"
Abdul ya zazzaro idanuwa cikin tsananin tsoro yace " me kake nufi da kalamanka?"
Jalal yai murmushi yace " ni d'an jarida ne ba lawyer ba bincike ba nawa bane sai dai a labarin da mukaji Kamar fyad'an ba shine yai ba sharri akamai, zai iya yiwuwa wanda ya mata sharrin ko bayasan auranka da ita yarinyar ne ko kuma santa yake, ko kuma......"
Jalal yai d'an karamin hucci yace " nayi mamaii a binciken ku da bakuyi bincike ba cikin wannan al'amarin."
Abdul ya mik'e a zuciye yace " me kake nufi? Wani nakusa dani ne dan bayasan na aureta ya mata fyad'e ko kuwa so kake ma kace ni na mata gaba d'aya , gayyatata kukai d'an ku wulakantani ko me? a iya sanina Fatima ta rasu, to waye zai ce nine na......."
Murmushin da Jalal ya sakar masa ne yasa yai saurin rufe bakinsa sam yamanga abin live ne, Jalal ya rike baki irin abin mamakin nan yace " badai kaine ka.....ahhh nasan haka bazai faru ba da kaije da tuni ka nemi 'yarka tunda ance har haihuwa tayi sannan da ka sanar damu 'ya'yanka 4 nasan ba kaibane to amma ban fah........"
Abdul ya fusata a zuciye ya d'aga hannu zai wankama Jalal mari, murmushi Jalal ya masa sannan yace " karka bari mutane su fahimci b'oyayen halinka da kake kokarin b'oyewa."
Cikin tsananin takaici da bakin ciki Abdul ya fita.
Jalal ya kalli Camera yace " muna sa ran kuto zatai kokari wajen gano mana gaskiyar wannan al'amarin kar muzu mu zab'i shugaban da ake kokwanto a kansa Bissalam."
Abdul ya fita a zuciye sai dai me? Yana fita zai shiga mota yaga mutane dayawa da ragowar 'yan gidan wasu tv d'in da gidan radio suna juranshi.
Jikinsa ne ya shiga rawa ya kasa tunanin komai...
Seemah kam da gudu ta mik'e tabar falon.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 6⃣5⃣
Abdul ya kara kallan mutanen a zuciye ya koma ciki, Jalal kam yana ma mutane sallama da kuma sai sun jisu a sabon shiri na gaba kawai yaji an shakumo mai riga, kallan Abdul yai cikin mamaki sam idanun Abdul ya rufe ya manta shiri akeyi kuma live, cikin masifa da bakin ciki yace " kai waye kai? Me na maka ko ince menene tsakanina dakai da zaka aikama ragowar 'yan jaridu dasuzo? Dama can ka shirya ci min mutunci ne bawai shirin mutunci kaso yi ba ko?"
Jalal ya kalleshi yace " Senate me kake yi haka bakaga shiri akeyi ba? Mutane fa suna kallanka."
Cikin masifa yace " da a kalleni da kar a kalleni ai ka riga ka gama cimin mutunci ya fad'a tare da nunamai Jaridar da P.A d'insa ya kawo masa yanzu."
Jalal ya kalli head line d'in inda ya bud'e " *SHIN DA GASKENE SENATE ABDULLAHI BASHI DA HANNU AKAN FYAD'EN DA AKAI?*
Jalal yai murmushi tare da ba masu aikin umarnin su daina d'aukan rahotannin, bayan sun daina Jalal ya kalleshi ya sakar mai wani mugun murmushi yace " Bana tsoronka, ba kuma na tsoron abunda zakamin, ka manta kalamaina lokacin dana je gidanka?"
Abdul ya kalleshi da mamaki "kai ne kaje gidana?"
Jalal ya d'aga mai gira yace " Kayi tunani dakyau, sanda nazoma da zancan 'yarka wani cin mutunci kamin ko ince kama yarinyar da ba ruwanta?"
Nan fa Abdul ya tuno jikinshi ne ya shiga rawa ya sake Jalal yana girgiza kai, kamar zararre.
Jalal yad'an zumburo baki yace " ayya I pity you, gashi yanzu na kai kararka kuto kana zuwa gida zakaga sammaci."
Kai Abdul ya cigaba da girgiza wa yace " karya kake d'an talakawa, ko Amadu bai isa yaja dani ba bare kai, inada arziki da karfin da ba wanda ya isa ya ja dani."
Jalal ya jinjina kai tace " hmm gaskiya ne wannan ni kaina na shaida, sai dai wannan karan dukiyarka da matsayinka bazasuma amfani ba, d'an kuwa al'uma sunga halin da ake ciki kana tunanin wani zai taimaka maka bayan shima yana tsoron kar mutane su tsaneshi irinka?"
Abdul cikin tsananin takaici ya d'aga hannu zai mari Jalal, hannu Jalal yasa ya rik'e hannunsa sannan yamai murmushin rainin hankali yace " wlh wlh kaci darajar jininka ne ke ya wo a jikin Seemah da wlh sai na maka abinda yafi wannan, sai naci ma zarafin da har karshen rayuwarka bazaka manta da abinda kama Fatima, Dad wato Malam Isma'il, Mahaifiyarsu Ammar da kuma Mahaifina Amadu ba da sai na sa ka fisu wulakanta a doron kasar nan."
Abdul ya kalli idanun Jalal yanda sukai jaa, tsoron kalaman Jalal ne ya fara kamashi ya kalli Jalal a tsorace sannan ya fizge hannunsa, Jalal ya had'iye wani abu sannan yace " ka b'atama mutane dayawa rayuwarsu tayaya ma zakayi rayuwa cikin farin ciki? 'Yar ka da batama sanka ba baka tab'a tunanin nemanta ba saboda giyar mulki na d'ibanka."
Harya bud'e baki zai sake magana sai kuma ya fasa ya juya ya fara tafiya, har yad'anyi nisa ya tsaya tare da cewa " sai na ganka a kuto."
Jalal ya wuce su Abbas da duk sukai tsuru tsuru suna kallansu cikin tsoro.
Jalal fita yai direct yahau sabuwar motar daya sa Sagir ya siyomai, kirar Mercedes benz fara tas, gidan su Abba ya wuce.
Sukuwa a b'angarensu Abba jikin kowa yagama yin sanyi, Dad ya share hawayen daya rasa na dadi ne ko name, ya kalli Amadu yace " Amadu a wani dalilin zaka bar Jalal yai wannan abu mai hatsarin gaske? Me kakeyi da bazaka hanashi ba?"
Amadu ya share kwallarsa yace " Isma'il wlh sam bansan me yaron nan yake shirya wa ba nidai kawai cemin yai ince a kunna tv a kuma kira Seemah."
Abban Zaid ya kalli Amadu yace " Abdul bazai bar jalal haka ba, amma dama Abdul shine yama Fatima fyad'e?"
Nan Amadu ya warware musu komai na abinda ya faru.
Sunyi shiru kowa na tunanin mafita, samari 'yan gari kuwa sun fito da sanduna suna zanga zanga a kofar gidan Abdul akan dolene ayi bincike dan suma basu yarda ba.
Jalal kam bayan ya isa gidan yai parking motarsa ya fito, a harabar gidan yaga Zahra da Zaid a tsaye, jiyai Zahra tana cewa " Yaya Zaid kazo ka duba Seemah inajinfa ba lafiya take ba wani abu takeyi kamar ba'a hayacinta take ba."
JALAL ya matso da sauri yace " ina Seeman?"
Zahra ta kalleshi da mamaki, Zaid yace " Jalal zo muje."
Nan sukai d'akin da Seemah ta rufe kanta a ciki, Ammar suka gani a tsaye a kofar yana kwankwasawa tare da kiran sunanta.
Jalal yasha jinin jikinsa, tsayawa yai cak batare da ya karasa ba.
Ammar ya kara buga kofar yace " Seemah meyasa kike min haka? So kike kiga hankalina yayi matukar b'aci ko kuwa?"
A hankali Seemah ta mik'e tazo ta bud'e mai kofa tana bud'ewa ta fad'a jikinsa ta rungumeshi tana wani irin kuka, Ammar ma kwalla ce ta taro mai a ido, yace " Seemah menene? Mahaifin naki ne bakyaso ko kuma nakiso akacimai mutunci ba?"
Kai ta girgiza tace" ni ba mahaifina bane, Dad ne kawai mahaifina, sai dai Ya Ammar nasan mutumin nan, na tab'a ganinshi a hotel d'in daka zauna, yaya bashida mutunci na tsorata da gani mutum irin haka. "
Jalal ya share hawayen daya zubo mai sannan ya kakaro murmushi tare da juyawa zai fita, Seemah zata sake magana kawai ta hango kamar Jalal, da sauri ta saki Ammar sannan cikin kakusar murya tace " *DEEN WAIT*
Tsayawa Jalal yai cak ba tare daya juyo ba, Seemah ta kalli Ammar tace " Yaya in mai magana?"
Gaban Jalal ne ya fad'i jin kalaman Seemah, amai magana? Au in zata mai magana sai ta nemi izini? Idanunsa ya runste.
Ammar ya d'agama Seemah kai sannan ya juya ya bar falon, ba shakka yaji dad'in yanda Seemah tabashi matsayi.
Zaid ma ya juya yai waje, Jalal baisan Seemah ta karaso ba jin kanshin turarenta yasa ya fahimta, a hankali ya bud'e idanunsa ya zubasu akanta.
Seemah ta kuramai ido gyambon data d'auka ya warke ne ya motsa, hawaye ne ya zubo mata, shima hawayen ne ya zubo, bakinta ya fara rawa ta kasa mai magana.
Jalal ya goge hawayensa sannan ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace " how have you been?"
Kallansa kawai take ta kasa magana, Jalal ya d'aga kai ya d'an ja hanci yace " I see, ya za'ai ma in tambayeki haka bayan nagani you are fine."
Ya had'iye wani abu yace " kinga abinda akai?"
Kai ta d'aga mai tana hawaye, Jalal ya share nashi hawayen tareda cewa " meyasa ruwan nan yaki daina zubowa daga idona, inaji wani abu ya fad'amin ne."
Kallan tausayi tamai tace " Deen me ya kaika shiga harkar mutumin can? Kasanshi kuwa? Kasan wani irin mutum ne?"
Jalal ya kalleta ya d'anyi dariya tare da cewa " Koma wani irin mutum ne ai baifi karfin Allah ba, sannan ni ba tsoronshi nake ba kin manta nine?"
Tasa hannu ta dakeshi da karfi a kirji tace " Deen meyasa kake abu domin ni? Meyasa bazaka manta dani ba? Why? Why are you making me miserable. "
Ta sa wani irin kuja tare da tsugunawa akasa.
Jalal ya kalleta zaiyi magana Ammar ya karaso gun ya d'agata sannan ya kalli Jalal, Seemah ta kara sa kuka tace " Ya Ammar?"
Ammar ya mata alama datai shiru yace " wuce d'aki." Ya fad'a tare da goge hawayensa.
Seemah ta juya tai d'aki tana tafe tana waiwayen Jalal.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 6⃣6⃣
Ammar ya dawo da hankalinsa kan Jalal hannu ya mikamai suka gaisa, Ammar ya kalleshi yace " Jalal mutumin da kai magana dashi wannan mara mutuncin shine kakeso kacemana mahaifin Seemah ko me?"
Jalal ya kalli Ammar yace " ni kaina dana fara ganinshi ban amince ma idanuna ba."
Ammar yace " inaaa... da sake taya za'ayi Seemah wacce ba ruwanta me mutunci ace ta fito daga tsatson wannan mutumin? I just can't believe it."
Jalal yad'an dafashi yace " Ammar kamar ka manta fyad'e yana mahaifiyarta? Duk mutumin da zai ma wacce saura kwana biyu ya aura fyad'e ai kasan sai a hankali sai dai koni banyi zatan rashin imani da mutuncin sa yakai haka ba."
Ammar yai shiru, Jalal yai murmushi yacigaba da cewa " kamanta Allah ne ke fitar da rayyaye acikin mattace kuma mattace acikin rayayye? Please Ammar ka daure zuciyarka idan zuciyarka ta karaya tun yanzu ya kakeso Seemah tayi?"
Ammar yad'an ture hannunsa daga kafad'ar sa ya kifta ido yace " waya fad'ama zuciyata takaraya? Sannan ce maka nai mun zama abokai da har zaka wani dafani?"
Yanda yai maganar ne yasa Jalal yasa dariya yace " Ammar bansa kanada wannan cute site d'in ba, duk sanda muke had'uwa cikin d'aurewar fuska muke."
Ammar ya d'an harareshi yace " yanzun ma acikin b'acin ran nake ai."
Jalal ya kalleshi yace " tuba nake Ammar nasan akan me kake cikin b'acin rai sai dai nasani tuni Seemah ta cireni a ranta kaima kasani dazatamin magana fa sai data nemi izininka."
Ammar yai shiru kawai yana kallan Jalal aransa yace Jalal kenan.
A fili ya wayancewa da cewa " kaje falo nasan Dad nasan ganinka."
Jalal ya d'aga kai alamar to sannan ya kalli kofar d'akin da Seemah take ya wuce.
Ammar bayan yaga Jalal ya wucene shikuma ya wuce d'akin Seemah, knocking yai dama tana tsaye jikin kofar tanasan jin me suke cewa sai dai ta kasa jiyosu, bud'ewa tai Ammar ya shigo.
Kallanta yai ta kalleshi tanasan tambayarsa meya cema Jalal sai dai inaa bazata iya ba, ta daure tace " Yaya amma ai ba mutumin nan bane mahaifina bako?"
Ammar ya kalleta kai ta girgiza tace " haba dai yaya it can't be, mahaifi fa akace, da mahaifinane ina ganshi ai ina tunanin jikina zai bani munada alaka dashi amma ni farkon ganina da tsanarsa na wuce ta ya zakuzo kucemin mahaifinane?"
Ammar yad'an harareta yace " na d'auka Seemah ta tace ba ruwanta koma waye mahaifinta itadai Dad ne nahaifinta."
Da sauri tace " eh haka ne amma...amma...amma.."
Ammar yasa dariya yace " amma me? Yau kece kike in ina?ko rasa abin cewa kikai?"
Ta juya yai tare da rangwab'ar dakai, Ammar yai murmushi yace " karki damu kinji kinmanta nabarmiki Dad nina koma d'an gidan Abba?"
Juyowa ai tana dariya tace " kai yaya."
Yace "ahhbhh aikina ya biya tunda kinyi dariya."
Kallansa kawai tai batace komai ba, ya matso kusa da ita tare da turo fuskarshi kusa da ita yace " kallam fa?"
Tasa hannu tad'an ture fuskarshi kad'an sannan tace " kai Yaya."
Tai maganar kamar zatai kuka, yai murmushi sannan ya fita, har yaje kusa da kofa ya tsaya, jitai yace " Jalal nagunsu Dad."
Da sauri tace cema akai inasan insan inda yake?"
Yanakai nan yai waje yana murmushi, Seemah kam yana fita ta furzar da wata iska tace " Deen me kakeyi acan?"
Jalal kam bayan ya shiga azazzaune ya taddasu suna maganar Abdul, Dad yace " nasan Abdul fa, bansan ya akai ya canza haka ba, duk ba bayaji amma iskancinsa baikai haryai fyad'e ko shan giya ba, nadaisan yana shan taba, ina mamakin yaushe ya koma haka."
Abban Jalal yace " Abokan fa? D'an alokacin bazan manta ba shima kamar bayasan shawarar fyad'en da kuma kama Jalal kawai dai sun sugashi ne sannan yana kwad'ayin hakan dama a kasan ransa."
Abban Zaid ya kalli Jalal yace " matsonan Jalal."
Nan Jalal yazauna kusa da Junaid tare da gaidasu, Dad yai ajiyar zuciya yace " Jalal kasan mutumin nan mai karfi ne tunda Senate ne da mutane ke sanshi meya kaika yimai haka? Sai ka sanar damu."
Jalal zaiyi magana wayar Sagir ta buga Abban Zaid yace " d'aga mana."
Jalal ya d'aga tare da cewa " Sagir ya akai?"
Sagir cikin tashin hankali yace " Jalal duk an tsayar da saida Jaridun nan sannan duk 'yan jaridan nan sun watse daga gidansa."
Jalal yace " What?"
Sagir yai ajiyar zuciya yace " Jalal yazamuyi? Nasan yanzu kanka abin zai dawo."
Jalal yad'an mike daga gunsu Abba zai d'an fita, Dad ne ya rikosa yace " yi wayar anan."
Kallansa Jalal yai sannan ya daure yace " Sagir karka damu ai dama nasan hakan zata faru, in ba'ai hakan ba kenan ba mutum bane mai matsayi."
Sagir yace " to sai kazo."
Nan suka kashe wayar, Jalal ya kalli Dad yad'anyi murmushi yace " Dad is not a big deal."
Junaid ha kalleshi yace taya zakace haka bayan da alama Abdul is out to get you."
Jalal ya kalli Abbansa sannan ya kalli Dad yace " Dad zan koma Birnin gwari yanzu nasan nan zai nufa dan cimin zarafi."
Dad kallan Jalal kawai yake, Abban Zaid ne ya daure yace " Jalal ka cire hannunka daga abun mutumin nan, mu zamu karasa abinda ka fara."
Jalal ya girgiza kai yace " me kenan akai Abba? Na fara abu sannan inbarku ku karasa? Idan Abun yazo da downfall d'ina sai in jawoku mu fad'i gaba d'aya kenan?"
Ammar ne ya katseshi da cewa " Ni zan rakashi muje Birnin gwarin tare, Abba dukanki please karkusa hannu a wannan harkar."
Jalal ya kalli Ammar yai murmushi, Ammar yai saurin juya kai tare da cewa " malam daina min murmushi bancema munzama abokai ba tukun."
Dariya dukansu sukasa a falon, Abban Jalal yace " nufinka kenan kunzama abokai, dama can abokan ne ku."
Ammar yai saurin juyawa ya fita, Jalal yai kasa dakai yana murmushi, Junaid ya matso kusa dashi yace " Ammar tsoro yake karka tafi kai kad'ai wani abun ya sameka."
Jalal ya jinjina kai yace " nagane nima, bayaso ya fad'i abinda ke ransa ne."
Nan suka sakeyin murmushi.
Ammar d'akin Seemah ya koma, a bud'e kofar take, Seemah tana zaune Zahra na tsaye tana 'yar mita yanzu shikenan baza ai partyn ba? Nafa fad'ama kawaye na, wai meke faruwa agidan ne?"
Seemah ta girgiza mata kai tace " kedai fad'i gaskiya bawai partyn kikeso ba so kike kiga an kawo miki lefen ki."
Zahra ta turo baki tace " eh d'in nibama lefe ba na kosa ma ai auran."
Seemah tace " dama ai na sani basai kin fad'a ba da alama kekam kin gaji da gida."
Zahra ta murguda mata baki tace " kefa? Baki kosa a d'aura muku aure da Ya Ammar ba?"
Seemah tai shiru zatai magana Ammar yai saurin katseta da shigowa yace " Ahh Zahra na kula kina neman takurama Seemah ta."
Seemah ta kalleshi, Zahra tace " haka kace yaya? Shikenan nima zan rama ai." Tana fad'a tai waje.
Ammar ya kalli Seemah yace " baki mamaki ba daga fitata harna dawo?"
Tai murmushi tace " nasani Yaya damuwa kai da halin da nake ciki."
Yatsarsa ya nunata dashi yace "hmm wannan kanwartawa ta gama sanina."
Ta juyar da kai tace " wa zai sanka bayan ni? Tare fa muka taso yaya?"
Yai ajiyar zuciya yace " Haka ne kinci gari, amma naji dad'i naga kin ware."
Tace " ba dole ba duk yanda kai kokari gurin sani dariya?"
Ammar har kasan ransa yaji dad'in kalaman nan yace " ina neman izini."
Tace " name fa?"
Yai shiru can yace " Zan d'anyi tafiya ne, amma yau zan dawo."
Ta kalleshi tace " Yaya inzakai tafiya sai ka nemi izini ai kawai sanar dani zakai."
Yace " haka ne amma ni nafisan in nemi izinin."
Tai murmushi sannan tace " an baka Allah ya kiyaye hanya."
Yace Amin, sai naji kamar......."
Harararsa tai tace " zaka fara ko yaya?"
Ammar yace " sorry na daina, sannan ya d'aga mata hannu yai waje."
Tabi bayansa da kalli tare da cewa " Deen ko ya tafi shima? Ahhh yazanyi?"
Kai ta girgiza tace " me ya dameni ma da koma ina yake? Meye tsakanina dashi dazan damu?"
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_'Yan Uwa rabin jiki godiya! Jinjina! Ga 'yan uwana._
_Na sadaukar da wannan shafin ne zuwa gareku My Sweet babbar Yaya Aunty Faty, Yaya Faen and my dearest kanwa Meema ('yar fara) love you sooo much_😍😘
No. 6⃣7⃣
Ammar ya koma falon inda Jalal yake, nan suka mik'e tare da yima su Dad sallama, Zaid ne ya shigo falon ko sallama baiyi ba ya kalli Jalal sannan ya kalli Ammar yace " shine zaku zame ku barni?"
Ammar ya kalleshi yace " Zaid mu zame kamar ya?"
Zaid ya burtso baki yace " ko ma miye I am in, dan kuwa dani za'ayi tafiyarnan."
Abbansa ya kalleshi yace " kai kuma me zakaje kayi? So kake kaje kawai ka hargitsa komai kome?"
Zaid ya shagwab'e fuska yace " ni wai meyasa akemin haka ne? Ni ba namiji bane? Koma menene nidai dani za'aje."
Jalal ya kalleshi yace " baka tsoro?"
Hararar Jalal yai yace " tsoro? Farauta zaku ko me? "
Junaid yai murmushin mugunta yace " Abba ina ganin ya kamata abar Zaid yaje, waya sani ko shima akwai tasa mahimmiyar gudun mawar dazai ba da?"
Abbansa yace " waye zai bada mahimmiyar gudub mawa? Wannan?"yafad'a yana nuna zaid da hannu.
Zaid cikin shagwab'a ya matsa gun Dad yace " Dad kaga Abba ko? San na kula bai yadda dani ba kallan soko kawai yake min."
Dad yace " to ya isa haka, yanzu dai kaje ka shirya kai ma ka je."
Zaid yace YES!!!!
Sun fito su uku, Seemah na tsaye a jikin kofar falo tana d'an lekowa kad'an,, ganin Ammar, Zaid da Jalal sun nufi mota a tare yasa tai saurin bud'e kofar ta fito, kallansu tai cikin mamaki.
Daurewa tai tace " Ya Ammar!"
Ammar ya juyo ya kalleta, murmushi ya mata sannan ya kallesu yace ina zuwa.
Zaid ya tab'e baki tare da girgiza kai yace " kuma wlh kar a shanyamu a tafi soy........"kallan Jalal dayai ne yasa ya kasa karasa abinda yake shirin fad'a.
Jalal dayakejin wani abu na kishi na tasomai ya daure tare da yin yake yace " karasa Zaid karka damu dani."
Yana fada ya kalli inda Seemah take, idanunta na kansa, ga Ammar na tafe kusa da ita, Jalal ya kurama Seemah ido, itama kallansa kawai takeyi har Ammar yazo kusa da ita bata kula ba.
Da mamaki Ammar ya kalli inda take kallo, ganin tana kallan Jalal yai shiru batare da ya katsesu ba, sai dai kasan zuciyarsa wani irin kuna ne ke ratsashi, haka zai zauna yana kallan Seemah daga gefe tana kaunar wani ba shi ba?
Jalal ne yai saurin dauke kansa daga kallan Seemah tare da saurin karasawa jikin mota ya bude ya shiga.
Seemah ta bishi da kallo harya shiga mota sannan ta juyo ta kalli Ammar da mamaki tace " yaya!"
Ammar ya kalleta sai dai duk yanda yakeso ya danne zuciyarsa karta gane ransa ya baci ya kasa.
Kallanta yai yace " naam"
Baki ta motsa dan ta fahimci ya dade agun, kasa tai da kanta da sauri tace " yaya I......."
Kai ya girgiza mata yace " Zamu wuce kar dare ya mana."
Ta kalleshi da mamaki tace " yaya wai da deen zaku tafi?"
Yamaimaita sunan Deen? Hmm haka ne da deen zamu tafi.
Ta kalleshi da mamaki yanda ya bata amsar, tace " yaya amma...."
Ammar ya kalleta tare da yi mata murmushi yace " karki damu Seemah kin manta kin bani izini?"
Ta d'an hade rai tace " amma ai bansan ba kai kadai bane."
Ammar yace " me? Bakyasan ki ganmu tare?"
Kai ta girgiza da sauri tace " a'a bafa haka nake nufi ba."
Yai sake yin murmushi yace " inje? Kar suyi ta jirana."
Ta daga kai tare da cewa " Amma me zakuje yi?"
Ammar yai shiru kawai yana kallanta.
Tai murmushi tare da cewa " shikenan Allah yakaiku lafiya."
Ya amsa da Ameen sannan ya juya.
Mota ya bud'e gaban mota gefen Jalal ya zaune.
Zaid ne a zaune ya hakimce.
Ammar a kalleshi yace " malam Zaid dan koma baya ko?"
Zaid ya kalleshi yace " kamar ya?"
Ammar ya furzar da wata iska yace " ahhh da ina tunanin baka number wata hadaddiyar yarinya dana gani amma da alama zan fasa."
Da sauri Zaid ya kalleshi yace " da gaske?"
Jalal ya guntse dariyarshi yace " gaskiya kam da alama zakai rashin yarinya.
Ai kan Jalal yagama magana Zaid ya haura baya da sauri.
Ammar yazauna tare da yin dariya Jalal ma dariya yasa basu san sanda suka tafa ba.
Sai da suka tafa kuma kowa ya kalli window irin waskewar nan.
Zaid ya matso da kansa yace " dariyar fa ta meye?"
Jalal ne ya tada mota yaja batare da ya bashi amsa ba.
Haka suka tafi Zaid na tasasu dariya har ya gaji yai shiru, motar tayi shiru kamar ba kowa, can cikin wata murya Jalal yace " nayi mamaki danaji zaka biyoni."
Ammar ya kalli window yace " sai ka daina mamakin tinda dai gamu a hanya."
Jalal ya jinjina kai baice komai ba.
Muryar Ammar yaji yace " Meyasa ka zama dan jarida?"
Jalal ya dan kalli Ammar kadan yace " Long wish dinane."
Ammar ya kalleshi ba tare da ya gamsu ba.
Jalal yai murmushi yace " why?bakai tunanin haka ba? Ko ka dauka saboda Seemah na zama?"
Ammar ya kalleshi da mamaki yace " me? Ba hakan bane?"
Jalal ya kalli Zaid dake bacci ta mirrow sannan yace " nidai nacema ba haka bane."
Ammar ya furzar da wata iska baice komai ba.
Shiru sukai har suka isa ba wanda ya sake magana.
Suna isa suka fito dukansu suka nufi lungun, Zaid kam ya kasa jurewa yace " wannan lungun fa...."
Ammar ne ya harareshi hakan yasa ya hadiya maganarsa.
Sai dai me? Suna isa suka tada sai watsi ake musu da kaya daga ciki ake cilo kaya zuwa waje, abubuwa sai farfashewa suke.
Idanun Jalal ne suka kada sukai jaaa, wani mugun bakin ciki ne da takaici suka ziyarceshi, a zuciye ya shiga cikin gidan daidai nan wanda ke watsi da kayan ya daga tabirma zai cillo.
Jalal ya kalleshi, bai taba ganin shiba, ga Zainab a tsugunne a kusa dashi tana kuka tana kuma bashi hakuri, Mutumin sai ihu yake yana cewa a kira mai Jalal.
A zuciye Jalal ya karasa ya rike tabirmar, mutumin ya kalleshi yace " kai kuma waye?"
Jalal ya dage ya wankamai mari tare da cewa " bakama san wanda kake nema ba?"wani irin ihu mutumin yai yace " ha ha ha! Yau ni aka mara? Ni Kumurci sarkin yaki, ba wanda ya isa yaja dani wanda kuwa yai gaggawar tabani to kuwa kabarinsa ne yake bukatar ziyararsa, ihuuuu sai ni Gatari bai sare namomin daji ihu ihuhu...."
Jalal ya kalli Zainab da ganinsa yasa ta mike da sauri tana hawayen tausayi, Jalal ya maida kansabkan mutumin yace " ba kumurci ba ko zaki ne kai baka isa kazo gidan iyayena ka dinga mana watsi da kaya ba."
Ya matso tare da nunashi da hannu yace " tun kafin in fasa ma baki ka koma ka sanarda wanda ya turo ka, in har yana san yamin wani abu to sai dai yazo da kansa bawai ya turo wasu tsolayen mutane kamar ka ba."
Yana kai nan ya fizgo hannunsa, yafara kokarin Jansa, Ammar ne ya matso ya kama dayan hannun nasa suka turashi waje suka rufe gidan.
Jalal ya kalli Ammar sukama juna murmushi, Zaid kam tafi ya fara yace " wow kaii Jalal ka burgeni dayawa."
Jalal ya girgiza kai sannan ya juya ya kalli Zainab, kusa dashi ta matso tace " yaya mai yasa ka fadi haka? In kuma ya turo wasu mutanen dayawa fa?"
Jalal ya kalleta duk ta canza ta rame, tausayinta ya kamashi, yace " ke kadai ce a gidan?"
Tace " nida kanwata ne to ta tafi islamiya ne."
Jalal yai ajiyar zuciya yace " shiga ciki zan gyara gun."
Kallansa tai tare da cewa " zan tayaka."
Jalal ya dago ya kalleta da sauri ta juya ta shiga ciki, da mamaki Zaid ya matso ya kalli Ammar yace " wacece?"
Ammar ya kalleshi yace " Zaid please keep quiet. "
©
*THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
😍😘
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 6⃣8⃣
Kallan kayan yai gaba daya ma kayan sun tsufa kamar irin kayan bulan nan, yabi kwanukan Umma da kallo idanunsa ne suka ciciko, yanaji tun kayan auranta ne a gidan, sai yan kwanukan da aka dinga siya a hankali daga baya in an dan samu wani abun, Ammar ne ya matso ya dafa kafadar sa, jiki a sanyaye Jalal ya juya ya kalleshi, Ammar yace " Jalal me kake tunani?"
Jalal ya kalleshi sannan ya kalli kayan, yace " Ammar duba kagani, me nakeyi har kayan mahaifiyata suka kona haka? Kalli kwanukan da kayan sawarta?"
Hawaye ne suka gangaro ta ta gefen idansa yasa hannu ya goge, Ammar ya kalli kayan shima jiki a sanyaye, sannan yace " me kakeyi kamar ya? Jalal in baka da halin canza musu satowa zakayi ko me? Kayi iya naka kokarin suma sun sani Allah ma ya shaida, kudi kake dashi a lokacin ko me?"
Jalal ya runtse ido ganin kayan Abba ma duk sun kod'e yace " Amma Ammar ban nemi kudi bane a da sosai, ai da zan iya....."
Ammar ya jijiga mai kai, yace " Jalal don't make ur life hard, na sani duk dabansan yakai rayuwa ba da nasan da kanada hali bazakabar iyayenka haka ba, sai dai yanzu da ka samu aikin dayafi waccan nesa ba kusa ba sai kayi kokarin cika burin dake ranka."
Jalal yai shiru yana kallan Ammar, Ammar ya sakeshi tare da cewa " me kakeyi a tsaye? Munfara gyara gun ko?"
Murmushi ne ya bayyana a fuskar Jalal, nan ya sukunya suka fara kwashewa, Zaid dake waje yana waya ne yashigo da sauri yace " Jalal wasu mutane ne sunzo wai hakimi ya aiko ana kiranka."
Jalal yace " ni kuma? Dama akwai wani hakimi a nan garin?"
Zaid yace " to nidai gasu can a waje."
Ammar ya kalleshi yace " muje mu duba mana."
Zainab dake tsaye ta window tana kallansu, ta sulale ta zauna a jikin bango, hawaye suka zubo mata a fili tace " Allah na rokeka Allah kasa ba wani abun Ya Jalal yai ba."
Jalal na fita ya kallesu kayan fadawa ne a jikinsu, ya mika musu hannu suka gaisa, sukace " a cikin ku wanene Jalaludeen?an isar mana da sakon ya iso garin nan yanzu."
Jalal ya kallesu yace " nine, menene?"
Suka kalleshi dayan yace " Hakimi ne ke nemanka zakuje gurin sarkin birnin gwari tare."
Jalal yace " ban gane zamuje gun sarki tare ba a wani dalilin kenan?"
Suka hade rai dayan yace " kai dan gidan talakawa in an baka umarnin abinda zakace kawai shine to bawai ka dinga tambayar wanu abu daban ba."
Jalal zai yi magana Ammar ya katseshi yace " bakomai muje."
Jalal ya kalli Ammar fuska a hade, Ammar ya ja hannunsa gefe, bayan sun dan matsa ne ya kalli Jalal yace " Jalal calm down, muje sai muji me zasuce ai basu isadai su hukuntaka ba akan abinda bana gaskiya ba."
Jalal yai tsaki yace " ni rainin hankali ne banaso, me ya damen da wani sarki dazasuzo su sani a gaba?"
Yai shiru can yace " muje."
Ammar ya danyi murmushi.
Sunje gun hakkimi aka wuce dasu gidan sarki, Zaid ya kalli Ammar yace " amma dai ba hukuntamu za'ai bako?"
Ammar ya fizge hannunsa yace " kayi wani abun hukunci ne ko kuwa?"
Sunje shiga fadar hakkimi ya kalli Jalal yace " wadannan su tsaya a waje."
Ammar yace " ban gane ba?"
Jalal yamai murmushi yace " nima banasan mu shiga tare, at least in laifi nai I won't drag you down. "
Ammar zai sake magana, Jalal ya kalli Hakimin yace " muje."
Nan aka musu iso suka shiga, Sarki na zagaye da fadawa, sai dai bayan sun zauna yamusu umarni su fita,nan suka fita dukansu akabar Jalal da Sarki sai hakkimi.
Sarki ya kalli Jalal yace " kaine Jalal?"
"Nine Jalal." Yafada tare da kallansa.
Sarkin ya dan gyara nadin rawanin daya kusa rufemai baki ya kalli Jalal yace " an turo sunan ka daga sama ance kayi babban laifi na wulakanta Senate dakai shine aka bani umarnin hukuntaka ba tare da hukuma ta sani ba."
Jalal ya kalleshi yace " in kace Sama kana nufin....."
Kai sarki ya daga mai, Jalal yai wata dariya yace " lalai mutanen nan basa tsoron Allah." Ya kalli Sarkin yace " I don't think kanada shirin hukuntani."
Sarki ya kalleshi yace " meyasa kace haka?"
Jalal yai murmushi yace " in har hukuntani kakesan yi bana tunanin zaka aiko a kirani kuma har ka sanar dani ai aiko a hukuntani."
Hakimi ya kalleshi yace " kai gyara yanayin kalamanka ko ka manta a gaban Sarki kake?"
Sarki ya kalli Jalal yace " indeed u are smart, ba hukuntaka zan farayiba harsai naji abinda ya faru a kasata shekara Ashirin din daka fada a jarida ko gaskiya ne."
Jalal ya kalleshi cikin rashin tsoro da sadaukarwa yace " zan iya fadama amma sai in har na tabbatar zaka taimakeni gurin bada hukunci ga wanda yai lefi duk matsayinsa kuwa."
Sarki yai shiru can yace " idan kuma na kasa yin hukuncin fa? Ko kuma sai ka gama sanar dani incanza shawarata?"
Jalal ya kalleshi tare dayin ajiyar zuciya yace " Ka sa a kulleni kamar yanda aka fadama."
Sarki ya kalli Jalal da mamaki yace " kamar ya?"
Jalal yai murmushi yace " haka nake nufu kasa a kulleni sannan ka sanar da wanda ya ya bugoma wayar ina da evidence akan laifin da Senate Abdul ya aikata, sannan in har baizo gobe ba na ba Abokina zai aika kuto."
Sarki ya kalli Jalal cikin tsananin mamakin kalamansa yace " Jalal ban fahimceka ba."
Jalal yai murmushi yace " kai ma mutum ne mai matsayi sannan akwai mutane dayawa da suke samanka kamar Senate Abdul, bazan iya sanar dakai komai ba tukunna, in ka amince da olan dina to in kuma ba haka ba shikenan sai in tashi in tafi."
Shiru sarki yai na wasu 'yan dakiku yace " Don't trust me, dan bansan me kake shirin yi ba, kar inje daga baya inga bazan iya ba inyi betraying dinka, daga baya kazo kace ban fadama ba."
Jalal yai murmushi yace " I don't trust you, sai dai daga sanda kace fadawanka su fita nasan at least kai ba kamar su bane hakan na nuna bakasan aji maganar da zamuyi."
Sarki ya jinjina kai yace " okay na aminta da shawarar ka sai dai baka tsoron Abdul?"
Jalal yace " inada 'yan uwa a waje tare mukazo dasu ba kuma na tunanin zasu bari wani abu ya sameni."
Sarki yace " shikenan zan kulleka kamar yanda ka bukata, zan kuma yi abinda kace in har baifi karfina ba sai dai inaso ka fadamin kalma daya, da gaske Abdul ne yai fyaden dayaja matsaloli da dama a shekarun baya?"
Jalal ya dago yace " Zan iya rantsuwa akan shine yai wannan fyaden."
Sarki yace " Na aminta dakai, ka birgeni sosai na dade banga wanda ya zauna dani yai magana kanshi tsaye ba haka kamar kai, ba ka tsoron in an gama in ma hukunci?"
Jalal yai kasa dakai yace " In har na gama abinda nakeson yi ba wani abu bane in ka hukuntani."
Hakimi kam ya zama kurma dan ya kasa sa baki a wannan al'amarin shikam sam bai fahimci me suke nufi ba shiyasa ma yai shiru kawai.
© *THE SEEMA[truncated by WhatsApp]
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No.6⃣9⃣
Jalal ya fito daga fadar mai martaba gunsu Ammar ya nufa, Ammar na ganinsa ya taho da sauri, hannunsa ya rik'e yace " Jalal menene?"
Jalal yai murmushi yace " ba wani abun, kawai dai I am gambling with my life ne, I don't trust him sannan banida solution a wannan lokacin daya wuce in yarda dashi."
Ammar yace " Jalal akan Abdul ne?"
Jalal ya jinjina kai sannan yace " turowa sukai amin hukuncin da bazan iya sake magana ba, sai dai bazan iya ba."
Ammar yai shiru, Jalal ya dafashi yace " karka damu Ammar dolene musa mutumin nan ya biya laifin daya aikata tun a duniya, inba haka ba banaji Seemah zatayi rayuwar farinciki har abada."
Ammar kallanshi kawai yake, Jalal yai murmushi kamanta alkawarin dana maka ne? Na cewar kafin bikinka sai na sa Abdul ya tsugunna agaban Seemah ya nemi yafiyar abinda yai."
Ammar yace " amma Jalal......."
Jalal ya katseshi da cewa " ba abinda zasu iyamin nasan bazaka bari wani abu ya sameni ba."
Ammar ya makamai hararra yace " in wani abun ya sameka banaji zan iya yafema kaina."
Jalal yai murmushi tare da cewa "bama abinda zai faru."
Waya Jalal ya fito a ita ya kira Umma, ringing 2 ta daga cikin farinciki tace " Jalal kai nake nema ai tun dazu ai, albishirinka."
Jalal yace " goro."
Tace " Jalal jiya da daddare anma Zahida aiki yanzu ta fara magana a hankali."
Jalal cikin tsananin farin ciki yace " Da gaske? Yanzu Zahii tana magana?"
Umma tai dariya tace " dazun nan likita yasata ta fara gwadawa."
Jalal ya shiga cewa " Alhamdulila."
Umma tai murmushi tace " Sai dai muna bukatar abubuwa na amfani ga mahaifinka bayannan."
Jalal yace " bakomai zan turo a kawo muku ."
" toh Jalal Allah yamaka albarka."
Yace Amin.
Yana kashe wayar ya kalli Ammar cikin tsananin farinciki yace " Ammar Zahii tafara magana."
Murmushi sosai Ammar yai yace " Naji dadi sosai, Allah ya kara mata lafiya."
Jalal yace Ameen sannan ya furzar da wata iska yace "Yarinyar nan tun tana karama akace za'a mata aiki mai tsananin cin kudi, duk yanda Abba yaso ya tara kudin amma inaaa, ko kwatan kwata bamu isa hadawa ba, haka muna ji muna gani take a kwance ga kudi suka cigaba da karuwa."
Yai ajiyar zuciya, Ammar yai murmushi yace " Allah ya riga ya kaddara sai a wannan lokacin zata samu lafiya, amma naji kana maganar sako ya za'ayi?"
Jalal yace " shine ai, tana wani babban asibiti ne a kaduna na Dr Bilal to yanzu ga abinda ya faru."
Ammar yace " bakomai ni sai inje da kaina."
Jalal ya kalleshi yace " anya kuwa? Da so nakeyi ka nemo mana manyan 'yan jarida wadanda kasan masu amana ne ko ta hanyar su Dad ne, akwai abinda nakesan a dauka bayan Abdul yazo, sannan inasan a inda za'a kulleni a sa camera yanda zata dinga daukan komai dazai faru tsakanina dashi inyazo."
Ammar ya jinjina kai yace " Amma Jalal daukan evidence ba tare da mutum ya sani ba, ba illegal bane?"
Jalal yai dariya yace " a'a a law ai in har wanda ya dauki rahotan, dashi a cikin video din yazama legal, ai abinda ba'aso shine daukan shaida a boye ba tare da sun sani ba su dukansu "
Ammar ya jinjina kai yace " hmmm na gane yanzu."
Jalal yai murmushi yace " Zaid fa?"
Ammar yai tsaki yace " ya fita daga ganin wata yarinya ta fito daga gidan ya bita."
Jalal ya girgiza kai yace " Kaiii Zaid sai a hankali."
Jalal yacigaba" Ammar dan Allah ka taimaka kahe gida ka fadama Zainab nace ta koma gidansu, in komai ya kammala zanzo in daukota."
Ammar yace " gwara kam, zamanta ita kadai shima matsala ne bamusan me wannam mutumin zai yi ba."
Nan suka zauna Jalal a dinga fadama Ammar plan din yanda abin zai kasance, Kwarai Ammar ya gamsu, fatansu dai daya kar Sarki yaci amanarsu.
Nan Jalal ya koma ciki, shiru Ammar yai yana tunani baima san Zaid yazo kusa dashi ba, Zaid ya tabashi yace " Ammar me kake tunani?"
Ammar ya kalli Zaid yace " Zaid me kake tunani akan sadaukar da komai da Jalal yai dan ganin yaba Seemah farinciki?"
Zaid yai dariya sosai yace " Tsananin san da yake mata ne."
Ammar yai shiru can yace " tare muka taso da Seemah shekararmu Ashirin tare, shiyasa nake jinta a kowace gaba ta jikina amma ina mamakin ya za'ayi Jalal daya hadu da Seemah kwata kwata na wata daya yake neman sadaukar da rayuwarsa saboda ita?"
Zaid ma yazauna tare da cewa " nikaina ina mamakin wannan soyayyar, sai dai ita soyayya nasan a ganin farko ma take shiga zuciya, sai dai irin wannan soyayya ce ban sani ba."
Ammar yai shiru, a ransa yanata maimaita Shekara 20, da wata 1.
Can ya daure yace " Zaid me kake gani a naka tunanin? Dani da Jalal waye yafisan Seemah?"
Zaid ya kwashe da dariya yace " ina zan sani? Inba zuciyarku aka tsaga na duba ba?sai dai nasan dukanku kuna santa kuma dole dayane zai aureta."
Yanakainan ya mike yai hanyar waje, Ammar yai shiru yana tunanin da ni kaina ban sani ba.
Jalal kam agabanshi Sarki ya kira Abdul bayan sun gaisa ne yace " Senate na kama yaran kamar yanda kuka ce amma me za'amai?"
Senate yace " ni kawai ayi yanda za'ayi yabar kasarnan ko a turashi niger."
Sarki ya kalli Jalal wanda wayar a handsfree take kuma suna recording sarki yace " Amma yaran nada taurin kai fa, dan da alama akwai shaidu daya tara akanka ina tsoron kar ya yad'asu a kafafen yad'a labarai ba tare da mun sani ba."
Gaban Abdul me ya fadi yace " Wannan wani irin jarababben yaro ne? Me yake so danine?"
Sarki ya kalli Jalal sannam yace " nidai bansani ba amma yace tabbas in gobe bakazo ba yasa abokinsa ya kai shaidun kuto da kuma gidan tv."
Abdul ya mike yace " what? Nashiga uku wannan wani irjn jarababe ne? Ko kudi zan bashi mai uban yawa?"
Sarki yace " nidai bansani ba sakonshi dai daya ne tabbas gobe kazo ko kuma kaga takarda."
Abdul yai shiru can ya kalli PA jikinsa sai rawa yake yace " naji zanzo gobe dan Allah karka barshi yai abinda bai kamata ba."
Sarki yace " to shikenan."
Nan sukai sallama Sarki ya kalli Jalal yace " yaro wai baka tsoro?"
Jalal yai shiru can yace " ko inajin tsoro ai tunda na fara ban isa ingudu ba ballema banaji, ni yanzu taimakon da zakamin shine kataimaka kasa 'yan sanda suzo gobe dan nasan inhar ba mutum mai matsayi irinku bame bazasu zo ba."
Sarki yace " insunzo kana tunanin akwai abinda zasu iya yima Senate guda?"
Jalal yai murmushi yace " nima babban burina shine karsuyi komai din kamar yanda suka saba."
Sarki yace " Jalal u are really smart ko ni bana fahimtar komai da kake nufi sai dai kar ka bari smartness dinka ya lalata ma rayuwa."
Jalal ya kurawa wani gun ido baice komai ba.
Shidai abu guda daya yasani kuma yasa a ransa, dolene Abdul yaba Seemah hakuri sannan yaba mahaifinsa da Dad hakurin abinda ya musu, sannan in anzo bikin Seemah ace mahaifinta ya hallarta, ya sani ko bata fadaba dole ne kasan zuciyarta zaiyi radadin wannan al'amarin, ko bata nuna ba zataso ko da mahaifinta mutumin banza ne ace a tarihin rayuwarta ace mahaifinta dai ya hallarci bikinta.
Hawaye ne yaji yana neman zubomai, da sauri ya mike tsaye, Sarki ya bishi da kallo, ba shakka irin wadannan mutanen kasarmu take nema, sai dai a wannan lokacin bayaji akwai namijin da zai sadaukar da rayuwarsa saboda hukunta wanda yafi karfin hukuma.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 7⃣0⃣
Duk wani tsare tsare na plan din Jalal ya kammala, sai da komai yai daidai sannan Ammar ya kalleshi jiki a sanyaye yace " Zainab nakaita har tasha ta hau mota, sai dai Jalal are you sure ba abinda zai faru in mutumin nan yazo?"
Jalal ya dafa Ammar yace " Ammar karka damu koda wani abun zai faru insha Allah sai alkairi."
Ammar ya kalleshi sannan yace " ni ina....."
Jalal ya danyi dariya yace " Ammar are you worried about me?"
Da sauri Ammar ya fizge kafadarsa yasa hannu yadan bigi cikin Jalal yace " ana cikin wannan yanayin shine ko kunya kake tsokana?"
Jalal ya dan hade fuska irinta tsokanar nan yace " Ahhh namanta na daina."
Atare sukai dariya, Ammar ya kalli Jalal yace " magrib tayi mu bari mu nemi hotel mu kwana tinda kai yanzu ka zama prisoner. "
Jalal ya dan harareshi tare da sa hannu a kuncinsa yace " ka tabbatar dai zaka iya bacci ko? Karfa ka kwanta tunanin halin danake ciki yasa ka kasa yin baccin."
Ammar ya girgiza kai yace " Jalal na kula sam baka tunanin komai."
Jalal yai murmushi baice komai ba.
Ammar yace " nidai gobe da sassafe zanje kaduna in kaima Umma sakon sai in juyo amma me suke so?"
Jalal ya kalli Ammar cikin jin dadin kalamansa yace " Ammar!"
Ja baya kadan Ammar yai yace " menenen?"
Jalal ya saki murmushi yace " nagode sosai."
Ammar yace " nifa da a yanda na daukeka na dauka mutum ne kai mai zafi mara kuma san magana amma na kula bayan ka dawo karatun nan kamar ka canza daga yanda nake ganinka."
Jalal yai murmushi yace " ni kaina ina mamakin in ina tare da kai bakina bayasan yin shiru."
Murmushi sukama junansu, Jalal yace " ga Atm dina dan ba kudi a hanuna."
Ammar yace " eh dole ka bani Atm dinka tunda ni banda abinda zan iya basu ai dole kace haka."
Jalal zaiyi magana Zaid ya karaso da sauri yace" nikam yunwa nakeji wai meyasa ku bakwa maganar Abinci? Su haka gidan sarautar suke bazasu bamu abinci ba?"
Jalal ya harareshi yace " ai a matsayin baki mukazo ba dole a bamu abinci ba."
Zaid ya turo baki cikin shagwaba yace " Mami kitaimaki danki yunwa zata kasheshi."
Dariya suka kwashemai dashi.
Ammar yace " Bari mu siyo abinci take away sai muzo nan muci dakai."
Jalal ya girgiza kai yace " a'a kamanta ni prisoner ne dolene in jure yunwa kodan Abdul inya ganni gobe ya fahimci an wahalar dani."
Ammar da mamaki yace " Jalal ban gabe ba?"
Da sauri Jalal ya fara turasu, yace " kuje sai da safe."
Yana kaisu bakin gate ya koma ciki da sauri, Ammar yabi bayansa da kallo zuciyarshi ba dadi.
Sun gama cin abinci wanda Ammar kadan ya iyaci sunyi isha'i sannan suka kwanta, Ammar yayi shiru zuciyarshi ta cika da tunani kala kala, abinda yake tambayar kansa a zuciyarsa shine, Shi yafi cancanta da Seemah ko kuwa?
Wayarsa da ya kashe ya kalla so yake yaji muryar Seemah sai dai inaa bayasan ta tambayeshi me sukeyi anan bayan bazai iya mata karya ba.
A wannan dare mutane 4 idanunsu baiga baccin kirki ba.
Jalal wanda yake tunanin ya gobe zata kasance musu, Abdul wanda bakincikin abinda Jalal yamai yasa mutane duk sun fara juyamai baya ciki kuwa harda shugaban kasa, dan da sukai meeting duk yanda Abdul yaso yabama shugaban kasa nashi ra'ayin a lokacin suna meeting ya hanashi, inzaiyi magana sai ai saurin katseshi, shi yasa ya kosa gobe tai danya dau babban hukunci akan wannan Jalal din.
Sarki wanda tunani ya hanashi barci, yana tsoron abinda zai faru gobe cigaba zai kawoma kasarshi ko kuwa matsala?
Sai Ammar wanda tunanin abubuwa suka hadu sukamai yawa.
Washegari da sassafe Abdul ya kamo hanya, Ammar ma ya wuce cikin garin Kaduna, baisha wahala ba wajen samun asibitin saboda kwarewa da suna da asibitin yai.
Number dakin da Jalal ya turomai ya nufa, tsaye yai a waje yana kwankwasawa, wani likitane yazo wucewa ya kalli Ammar yace " ba shiga zakai ba?"
Ammar yace " shiga zanyu amma naji shiru."
" Ka shiga patient din maganarta bata fitowa ita kuma mahaifiyar tata tana gu likita."
Ammar yamai godiya sannan ya tura kofar ya shiga.
Zahida na kwance sai motsa jikinta takeyi tana kiran Umma cikin muryarta da bata fitowa sosai, da sauri Ammar ya karasa gunta ya tsaya ta baya, Zahi najin motsi tace " Umma sosa min bayana kaikayi nakeji, jinake kamar wani abun na yawo."
Ammar yai tsaye yana kallan yanda takeyi rasa yanda zaiyi yai, Zahida takara cewa " Umma dan Allah ki sosamin zan mutu."
Ammar yasa hannu daya ya rufe fuskarsa sannan ya sa hannu a aljihu ya dauko biro yafara sosa mata a baya fuskarsa na gefe.
Zahi jin kaikayin yayi yawa ga umma ba gun take sosa mata ba tace " Umma dan Allah ki sosa min sosai ba nan bane."
Idanu Ammar ya zaro tunaninsa daya ina umman take to? In taganshi yace mata shine wa?
Gashi kuma bazai iya sa mata hannu a baya ya sosa mata ba, Zahida ta rasa ya zatai, zatai magana Umma ta shigo dakin, Ammar ta kalla da mamaki tace " Bawan Allah me kake a ciki?"
Da sauri Zahida tace " Umma? Waye?"
Umma ta matso ta gabanta tace " wani namiji ne."
Idanu zahida ta zaro bakinta na rawa tace " Umma ina yake?"
Ammar ne jiki a sanyaye ya dawo ta gabanta, ai tana ganin namiji ta saki ihu da karfinta na gaske, tare da runtse idanunta.
Umma tai mamakin yanda muryar ta tafito, ta kalli Zahida tace " menene? Wani abin ya miki?"
Ta fada tare da kallan Ammar da sauri Ammar ya girgiza kai alamar bai mata komai ba.
Zahida ta bude ido a hankali tare da sa kuka cikin kuka tace " Umma hannu fa yasamin a bayana."
Da sauri Umma ta kalli Ammar cikin mamaki tace " Hannu?"
Ammar ya kalli Zahida yace " yaushe na sa miki hannu? Kingani ne sanda nasa hannun ko kuwa?"
Zahi ha harareshi tace " to me kamin?"
Umma a zuciye take kallan Ammar tace " bawan Allah kai ko kunya bakaji ba? Baiwar Allah bata da lafiya shine zakazo ka sa mata hannu a baya?"
Ammar ya nuna mata biro yace" kinga abinda nasa mata nan, Umma tunda na shigo take kiranki akan ataimaka mata kaikayi ya isheta shine fa nasa biro nadan sosa mata, batasan banbancin hannu da biro bane?"
Umma ta kalli Zahida datai kasa dakai, Ammar yadan harareta yace " memakon ki godemin shine zakimin ihu?"
Zahida ta dago ta kalleshi, kaikayin ne ya cigaba da damunta tace " Umma bayana."
Umma ta kalli Ammar tace " dan Allah kadan kira mana likita."
Ammar ya fita, yana fita yai dariya a fili yace " lalai wannan kanwar Jalal din."
Jalal kam an kulleshi a can bayan gidan sarki a wani dakin da ko window babu sai daga can sama akadanyi hudi kadan kadan haske yana shigowa, yunwa yakeji sosai dan tana neman galabaitashi, duk yanda sarki yai dashi akan yaci abinci jiya amma yaki yarda.
Jin ana bude kwad'an dakin da aka rufeshi yasa yai saurin komawa lungu ya rakub'e, ana gama budewa Abdul ya shigo wasu maza kosassu suna biye dashi, Jalal ya kalli Camerar da suka saka yanda ba wanda zai gane, kasa yai da kansa.
Abdul ya shigo cikin isa, ya kalli Jalal tare da kwashewa da wata muguwar dariya, Jalal ya dago a hankali ya kalleshi, Abdul ya kalli dakin tare da jinjina kai yace "good dama haka nakeso ni wannan ma ya maka dadi dayawa."
Jalal ya kafeshi da ido, Abdul ya kalli mutanen yace ku fara.
Ai kafin Jalal ya fahimci mai zasu fara yaga sun matso sun kama dukanshi, sai da sukamai duka sosai, sannan Abdul yace " ya isa haka."
Sannan ya basu umarni su fita, kusa da Jalal yaje wanda duk jikinsa an jimasa ciwuka ya dago yana layi, Abdul ya sakeshi yamike tare da cewa " Jalal kai yaro ne, bakasan komai na rayuwa ba, taya zaka hada kanka dani? Nine fa Senate Abdul, akan can wata yarinya da kake kira da sunan 'yata daban santa ba har zaka nemi halakamin rayuwa? Kai din banza, me kake dashi? Me kuma zaka iya?"
Jalal cikin layi yace " Anya kuwa kanada imani a rayuwarka? 'Yarka ce fa? Baka tausayin abinda kama mahaifiyarta?"
Abdul ya kalleshi tare da nunashi da hannu yace " karka sake cewa 'yata wato so kake rayuwata ta hallaka ko? Meyasa tunda sanda ina karamin dan siyasa bakuzomin da zancenta ba sai yanzu da kukaga na girma ina neman wuce matsayina?"
Yai ajiyar zuciya yace " Fatima ta rasu, sannan banaji kunada wata shaidar da zata tabbatar da ninai fyaden nan, in kuma kanada ita ka tabbatar ka bani tun kafin nasa a kama iyayenka."
Jalal ya mike tare da yin wata dariya yace " me? Bamu kawo maka zancen ta ba tunda? Ita kanta yarinyar banaji zataso ganinka a rayuwarta, saboda tafi karfin ace mutum mai irin wannan zuciyar shine zata kira a matsayin uba, kuma tazauna dashi."
Abdul ya matso tare da wankama Jalal mari yace " Nima baso nake ta kirani da hakan ba, sannan daga kai har Amadun sai na nuna muku banbancin da dakuma yanzu."
Jalal yai murmushin karfin hali yace " Ko tambayar Malam Isma'il ma bakayi? Mutumin da kama sharri ka wulakantamai rayuwa."
Abdul yai murmushin mugunta yace " Isma'il? Ha ha ha au hardashi kuka hadu zaku wulakantani?"
Jalal yai shiru, Abdul ya matso tare da cewa " Ka koma ka sanar dasu abinda na maka sannan ka fadamusu nine na mata fyaden me zasu iya min? Yarinyace nace ta fadi kudin datake so nizan bata amma bawai a matsayin 'yata ba."
Alhamdulila Jalal ya fada burinshi ya cika Abdul ya aminta da bakinsa shiya ma Fatima fyade.
Wani abu ya danna, kan kace me sai ga 'yan sanda sun taho sun zagaye dakin gaba daya....
*Gaisuwa My Samra Thanks alot Sis......*❤❤❤
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No.7⃣1⃣
Abdul jin loudspeaker yai ana kiran sunansa, jikinsa ne ya shiga rawa ya matso kusa da Jalal tare da shakemai wuya da karfinsa, Jalal ya fara kakari, ko meya tuna kuma sai yai saurin sakinsa yana yin baya baya yana cewa " nafi karfin wannan, nine Senate Abdul wanda mutane ke so."
Jalal yarasa dalili kawai ganin yanda yake rawa da jikinsa yasa tausayinshi ya fara ziyartar zuciyarsa, kallansa yai idanunsa sun ciciko da kwalla matsowa yai kusa dashi ya rike hannunsa yace " wacce irin rayuwa kai? Bayan rashin adalcin dakama Fatima baka jin tausayinta da dana sanin abinda ka aikata a kasan zuciyarka?"
Hawaye suka zubo ma Abdul ya kalli Jalal yace " Fatima ta rasu dolene ni danake darai inyi rayuwar danakeso."
Jalal cikin wata sanyin murya ta ban tausayi yace " zaka iya rantsuwa tun bayan abinda yafaru baka taba dana sani ba? Sannan baka taba tunanin 'yar ka ba?"
Bakin Abdul ya fara rawa, kai ya shiga girgizawa hawaye na zubomai, Jalal ya kara matsowa kusa dashi yace " Zaka iya rantsuwa?"
Abdul ya dago jajjayen idanunsa yace " in ma nayi dana sanin ko tunaninsu menene amfaninsu yanzu? Fatima ta rasu ba tare da na nemi yafiyarta ba, sannan yarinyar data haifa ban taba ganinta ba bare inma san sunanta kana tunanin akwai amfanin da tunanin zaimin ko dana sanin?"
Jalal yai ajiyar zuciya yace " You are not a cruel person, da ace kai mugune da randa nazo gidanka dazancen nan bazaka barni na fita ba sannan da bazaka ce sarki ya kamani ba sawa zakai a kasheni ba tare da kowa ya sani ba, sai dai na kasa gane kai wani irin mutum ne da kake kokarin canza abinda ke zuciyarka."
Abdul ya kalli Jalal tare da share hawayensa yace " da farko I am not greedy but zama da abokai da cusa min ra'ayuyuka da kuma matsayi na power danake samu ba, hmmm bansan sanda nima na riked'e gaba daya na zama haka ba, bana tausayin kowa burina daya ne insamu abinda nakeso......"
Kasa karasa maganar yai, jiki a sanyaye ya dago tare da yima Jalal murmushi yace " hmm inaji Allah ne ke nemana da rahama shiyasa ya baka damar tsayar dani daga cigaba da abubuwan danakeyi."
Hanyar kofa ya nufa, da sauri Jalal ya riko hannunsa yace " 'Yar ka fa?"
Abdul ya runtse ido yace " a'a karka sanarda ita komai, in har bata gan ni cikin mutuncina ba bazan bari ta ganni cikin wannan yanayin ba."
Yana kainan ya bude kofar 'yan sanda suka matso tare da samai ankwai.
Shiru Jalal yai zuciyarshi kuma ta shiga radad'i abinda yake fata ne ya tabbata but meyasa yakejin shi haka?.
Ammar ne suka dawo shida likita, suna shiga dakin Zaid ya kirashi a waya, yace na siyo kayayyakin kana ina? Ammar ya fadamai number dakin nan Zaid ya taho, likita bayan ya duba Zahida yace bari yasa a kawo mata magunguna, yana fita Zaid ya shigo, Umma ta kallesu tace " ban gane ku bafa?"
Ammar yai kasa dakai tare da gaisheta yace " Ammar ne dan gidan Malam Isma'il."
Cikin tsananin mamaki Umma ta kalleshi tace " Ammar?"
Zaid ya matso tare da cewa ni kuma Zaid, ta kalli Zaid da mamaki tace " tare kuke?"
Ammar ya daga kai, Zaid ne ya karasa kusa da Zahida dake jingine da gado, fuskarta ya tsaya kallo, inya kalli nan sai ya juya kansa ta daya barin, Zahi ta gaji da wannan abin nasa ta kalleshi tace " malam lafiya?"
Zaid yace " wow! Ahh dan sake fada kinji?"
Zahi tace " me zan sake?"
Zaid ya rike kirjinsa bangaren zuciyarsa yace " Ammar wannan muryar tamin dayawa."
Kai Ammar ya girgiza ya kalli umma yace " karki damu Umma haka yake."
Umma tai murmushi tace " da alama yanada san wasa."
Zaid ya dago cikin shagwaba ya kalli Zahida yace " Yanzu bazaki sake fada ba."
Zahi ta makamai harara tare da cizan leb'enta tace " Naki d'in, kuma ka matsamin daga sai tin fuska."
Zaid ya sa dariya tare da toshe baki yace " in naki fa? Me zakiyi?"
Ya fada tare dasa hannu a haba, Zahi ta juya kanta gefe tace " Umma kice ya matsa min."
Tai maganar kamar zatai kuka, Ammar ya kalli Zaid yace " Zaid ka matsa mata mana tace bataso."
Zaid ya kalli Ammar yace " meya dameka? Hira muje tsakanin masoya ko patient. ...ahhh dama karatun likita na karanta."
Zahi tai wani irin dariya ta kularwa tace " masoya? Ha ha lalai mutumin nan da alama kai player ne, harda wani dama karatun likita ka karanta? Ahhh Allah yasa duk da akwance nake inajin labarai, dan yayata tana karantamin har littafin hausa, nasani sarai in naga mutun na neman yaudara."
Ta hade rai tare da juya kai.
Zaid ya matso kusa da Umma yace " Umma kun tabbatar yarinyar nan mara lafiya ce da gaske? Bakinta abude fa yake?"
Umma tai murmushi tace " to ko zata mik'e ta rakaka unguwa?"
Da sauri Zaid yace " Eh Umma in....."
Kafa Ammar yasa ya takamai kafa da karfi Zaid yai kara tare da cewa " me kuma nai?
Ammar yace " bata fa tafiya akwance take tun tana karama, Zaid meke damunka ne?"
Jikin Zaid ne yai sanyi ya kalli Zahi sannan ya kalli Umma yace " Bansani ba Umma nadaiji jiya ana cewa ta fara magana nadauka matsalar ta magana ce kawai. "
Umma tai murmushi tace " ba komai zuwanku ma ya isheni farinciki tun balle ganin Ammar danai wanda ban taba zata ba."
Ta fada tare da kallan Ammar.
...©
*THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No.7⃣2⃣
Seemah na xaune a daki tana cin Abinci Dad ya shigo, kallansa tai cikin sakin fuska tace " Dad shigo mana."
Dad ya karaso tare da zama kusa da ita ya anshi cokalin da take cin abincin ya deba tare da kaiwa kusa da bakinta yace Ahh....
Murmushi tai sannan ta bude bakin ya zuba mata, tanaci tana murmushi, Dad ya kalleta cikin tsananin kulawa yace " babban farinciki na bai wuce inganki kina cikin farin ciki ba."
Murmushi Seemah tai tace " Dad daga yanzu ko banasan dariya inna ganka zan dinga washe baki."
Dariya yasa mata yace " ni bance kuma a dingamin haka ba."
Kallansa tai cikin kulawa tace " Dad su ya Ammar fa? Sam na kasa samunshi a waya."
Dad yai shiru batare daya bata amsa ba cikin wata murya yace " Seemah?"
Kallansa tai cikin mamaki da tattara nutsuwarta saboda yanda ya kirata.
Dad ya kalleta cikin kulawa yace " Seemah bakyajin ba dadi ko bacin rai? "
Cikin mamaki ta kalleshi tace " saboda me kenan Dad?"
Yai murmushin karfin hali yace " Seemah nasani sarai Jalal kike so amma na hadaki aure da Ammar bakyajin haushin hakan a kasan ranki?"
Iska tadan furzar sannan ta rangwabar da kanta ta kalli Dad tace " Dad a kaf duniyan nan bani da kamarka, ko dan garuwa wanda bashida kwabo ka ce in aura to tabbas shi din nan zan aura babu musu balle tambayar dalili bare Ya Ammar?."
Tai ajiyar zuciya sannan tai murmushi tace " Dad bazan boyema komai ba saboda a haka muka taso banaiya boye ma komai da gaske inasan Deen sai dai duk sanda nake masa bazan iya ture Ya Ammar in zabeshi ba koda kuwa bansan abinda ya faru da ba, balle kuma yanzu na sani."
Hannun Dad ta kama tace " karka damu Dad bazan bari hallacin daka mana nida mahaifiyata ba ya kare akan san zuciya ta ba."
Dad idanunsa suka dan ciciko, yace " Seemah na sani naso kaina dayawa dana hada auranki da Ammar, sai dai babban burina daya ne a duniyan nan, bai wuce inga zuri'ar Fatima da tawa sunyi aure sun hayayyafa ba."
Seemah tai murmushi tace " Karka damu Dad insha Allah wannan burin naka zan cikama shi, tunda na taso agunka ni nake neman abu agurinka baka taba neman wani abu aguna ba sai wannan, ka sha wahala sosai akanmu nida Mahaifiyata insha Allahu wannan burinaka nizan cikama shi."
Tai magana tana kokarin boye hawayenta, Dad cikin tsananin sanda yake mata yace " Seemah inhar auren Ammar bazai......"
Da sauri tasa hannu ta rufemai baki, tace " karka karasa Dad kafi kowa sanin yanda Ya Ammar ke sona, tun ina karama har kawo yanzu, hawaye wannan bayaso yaga nayi, nima kasan yanda na damu dashi, insha Allah zanyi kokarin juya soyayyar danake masa ta 'yan uwantaka ta koma ta......."
Kasa tai dakai bata karasa ba, Dad ya kalleta shima baice komai ba tunani yakeyi, anya ya kyauta ma Seemah kuwa? Jalal ma a yanda ya gani yana tsananin santa.
Katse mai tunani tai da cewa " karka damu Dad zanyi kokarin ganin na cire san Deen a raina sannan na maka alkawari zan kula da Ya Ammar sosai, inaji a jikina wannan shine abinda zanyi wanda zaisa dukda mahaifiyata batada rai zatai alfahari dani."
Idanunsa ne yaji suna neman zubar ruwa da sauri ya mike yai waje, binsa tai da kallo tare da yin murmushi hawaye suka fara zubo mata, tafara cewa " Is Okay Seemah, cool down."
Jalal kwance akan gago yayi shiru tare da kankame memory din daya cire na cikin camera din daya daukesu shida Abdul, nurse ne ya shigo ya kara dubashi tare da bashi magunguna, Jalal ya sha tare da mikewa ya zauna yace " wayata please. "
Nan nurse din ya mikamai, Jalal ya amsa tare da kiran Zaid, dan yasan wayar Ammar a kashe take.
Ringing uku Zaid ya daga yace " Jalal ya akai? Ina cikin shaukin kauna zaka kirani?"
Jalal ya girgiza kai yace " Zaid matarka zatai fama, ni ba Ammar please. "
Zaid yasa dariya tare da cewa " ai matar tawa kanwarka ce kaga sai kushirya yin faman dakyai."
Jalal yace " me kake nufi?"
Dariya Zaid yai tare da mikama Ammar wayar, Ammar dake tuki suna hanyar dawowa ya amsa tare da cewa " Jalal ya? Allah dai yasa ba wata matsalar bace?"
Jalal yace " Ba wata matsalar Senate din sun wuce dashi police station sai dai....."sai kuma yai shiru.
Ammar cikin damuwa yace " menene? "
Jalal yace " tunani nakeyi anya ya kamata mu bada evidence din nan? Naga kamar zuciyarshi ta karaya shi yasa nake tunani."
Ammar yai shiru nadan sakwanni sannan yace " Haka ne mu barshi kawai kodan Seemah ma ina tsoron kar tagani dan ko bata fadaba nasan abin zai zamar mata gyambo a zuciyarta."
Jalal ya jinjina kai yace " kuna ina yanzu?"
Ammar yace " muna hanya munkusa shigowa birnin gwarin ma, Jalal yace " nagode Ammar sosai...."
Ammar ya katseshi " Zaka fara ko?"
Jalal yai murmushi yace " Sorry amma me dazu Zaid yake nufi?"
Ammar ya girgiza kai yace " kasanshi ai, daga gani Zahida wai ita yakeso kuma yanzu."
Jalal yai dan dariya kaan yace " kaii Zaid sai a slow...."
Nan sukai sallama suka kashe.
Jalal na zama wani bafade yazo yace " mai martaba na nemanka."
Jalal ya mike suka fita tare, zaune yake a kasa, mai martaba yace " ya jikin naka?
Jalal yace " da sauki."
Sarki yace " ya ya ina abinda aka dauka nima na gani?"
Jalal yai shiru, Sarki yace " ya akai kuma?"
Jalal ya kalleshi yace " matsala aka samu ai, ashe bamu kunna recording ba a lokacin."
"OHHHH abin dai baiyi dadi ba amma ba komai naji ance ya aminta da lefin yimata fyaden a station din 'yan sandan."
Jalal ya kalli shi jiki a sanyaye, yace " mun gode sosai da taimakon da ka mana, zan wuce nima yanxu 'yan uwana suna hanya."
Sarki ya jinjina kai tare da cewa " Kuma Abujan zakuyi?naji shima can za'a wuce dashi "
Jalal yace " eh."
Nan yamai Sallama zai mike Sarki yace " Jalal?"
Juyowa Jalal yai ya kalleshi, Sarki yai murmushi yace " ka birgeni sosai, I wish ina da yarinya da na hadaka da ita, sai dai inaso kaje ka duba ko wani gun aiki ne indai har ya maka kanaso to ka sanar dani ni kuma zan nemar maka aiki a ko inane a doron kasar nan."
Jalal yai murmushi yace " na gode."
Nan yamai sallama ya fita, Sarki yai murmushi cikin gaskiya Jalal ya kwantamai a ransa.
Jalal gidansu ya koma ya dan shishigar da kaya, yana gamawa su Ammar na isowa nan suka shiga mota suka kama hanyar Abuja.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 7⃣3⃣
Sunyi nisa a hanya Zaid duk ya ishe Jalal da zancen Zahida, hakan yasa Jalal ya kwantar da kansa a jikin kujera tare da rufe ido kamar mai bacci, Ammar ma yasa earphone a kunnensa tare da maida hankalinsa kan titi, shikam Zaid sai zuba yakeyi, ganin shariyar tayi yawa yasa shima haushi ya isheshi yai shiru, sunyi nisa jin Zaid yayi shiru yasa Ammar ya lekashi ta glass din mota, ganin Zaid yayi bacci yasa ya zare earphone din tare da kallan Jalal kadan yace " Bacci?"
" Nope kawai idona na rufe."
Ammar yai ajiyar zuciya yace " Me ka tsara yanzu zakai?"
Jalal idanunsa a rufe yace " Ina tunanin neman aiki a kaduna ne so nake mu koma can gaba daya, banajin zaman Abujan nan yanzu."
Shiru Ammar yai hakan yasa Jalal ma yai shiru, sunyi shiru kawai Jalal jiyai Ammar yace " Saboda Seemah?"
Cikin mamaki Jalal ya bude ido ya kalli Ammar sai dai ya kasa magana, Ammar ya maida kansa titi tare dacewa " Hakane kenan?"
Jalal ya mike zaune ya kalli Ammar yace " Ammar."
Ammar ya dan kalleshi tare da yin murmushin karfin hali yace " Jalal menene matsayin Seemah a gunka?"
Jalal ya kalli Ammar cikin tsananin mamaki yace " Ammar meyasa kake wannan maganar?"
Ammar yace " Jalal tambaya kawai na maka amma in kana ganin bani amsar zatai wuya mubar maganar kawai."
Komawa Jalal yai ya kwanta tare da kallan window yace " Ammar karka manta ankusa aurenku da Seemah saboda haka karka fara sa wani abu a ranka."
Gefen titi Ammar ya koma da motar yai parking tare da tattara hankalinsa kan Jalal yace " Jalal bazaka gane me nakeji bane a wannan lokacin, kawai dai ina daurewa ne nai murmushi na kuma ci abinci amma kasan zuciya ta jinake kamar I am useless, na ka sa yima Seemah komai kai kuma ka sadaukar da komai naka akanta, bazaka fahimci me nakeji bane."
Jalal ya kalleshi cikin wani yanayi yace " Ammar kenan, haka kake tunani a ranka? Ni a zuciyata nine nake useless mahaifina shine dalilin lalatama mahaifinka rayuwa, sai dai duk da haka baiyi tunanin komai ba ya rike Seemah kamar 'yarsa, kana tunanin wannan dan abinda nai yakai kwatan abinda mahaifinka yai?"
Ammar ya juya kai yace " Jalal ka manta ne? Mahaifina fa kace bani ba, na sani Dad yayi komai domin Seemah amma ni fa?."
Ya juyo ya kalli Jalal idanunsa suka kada yace " Jalal what about me?"
Jalal yai wani murmushi yace " Ammar taya zaka fadi haka? Kaine kuwa ka mata komai kasan tun da muka hadu da Seemah zancenta daya Ya Ammar, na tabbata da tun farko tasan kai ba Yayanta na jini bane da ko kallona Seemah bazatai ba."
Ammar kallan Jalal yake kawai, Jalal ya dafashi yace " nayi tunani mai yawa bayan naji abinda ya faru tsakanin iyayenmu, zance daya ne ya tsayamin na kuma tabbatar dashi, Ammar shine mutum na farko a duniyarnan da nakeji zai iya rike Seemah fiya dani, zai kuma bata kulawar da ya kamata, zai kuma sa ta manta abinda ya faru da mahaifiyarta."
Ammar ya runtse ido tare da kallan window, a hankali yace " Jalal I I I......"
Sai kuma ya kasa karasawa, Jalal ya kalleshi da mamaki yace " Ammar na san ya kakeji aranka saboda abinda naji kenan a lokacin da naji abinda mahaifina yai, sai dai abu daya na sa a raina, zanyi kokarin ganin na rage gaba da tsanar dake tsakanin mahaifanmu, inaji kamar in nai hakan ne zaisa mahaifanmu su koma kamar da."
Ammar yamai murmushi tare da cewa " Jalal na gode sosai."
Jalal yamai murmushi yace " Ammar ba wanda Seemah ta dace dashi kamarka, zaka kula da ita sama dani na shaida hakan."
Murmushi sukama juna, Ammar ya tada motar tare da hawa kan titi yace " Jalal nagode sosai, sai dai Seemah fa? Inaji ajikina kamar...."
Jalal ya katseshi da cewa " Ammar trust in ur self, Seemah yarinyace bata gama sanin menene so ba sannam karka manta macece ita, nina fadama ka sa a ranka ko shekara bazaku rufa da aure ba zakaga Seemah ta manta dani."
Ammar yadan harareshi yace " ce maka akai inasan ta manta dakai?"
Jalal yai dariya yace " to me kakeso?"
" taya zata manta dakai bayan amintarmu nanan?"
Jalal ya sakeyin dariya kadan tare da nuna Ammar cikin zolaya yace " yanzu ka aminta da amintarmu kenan?"
Ammar yai murmushi tare da cewa " Jalal bansan meyasa ba abinda bazan iya fadama Junaid ko Habib ba inaji a jikina zan iya fadama, banaji zan iya boyema komai."
Jalal ya dan furzar da iska yace " nima haka Ammar jinake kamar munyi shekaru dayawa tare."
Dariya sukai nan suka shiga hirar rayuwa.
Sun isa Abuja Jalal yace " Ammar saukeni anan."
" ina zaka haka?"
Jalal yace " inasan ganin Sagir ne akan gidan danace ya samomin, yanzu banajin zan zauna anan."
Ammar ya mai wani kallo yace " Jalal please kazauna a inda ka samu aiki taya zakaki zama anan bayan ka riga kasamu aiki, kai zamanka kawai kenan kana so kacemin in mukai aure zumuncinmu ya tafi kenan?"
Jalal yace " Ahhh to bari inji me Abba zaice tukunna, amma yanzu saukeni tukun."
Nam Ammar yasamu guri yai parking Jalal ya fita tare da cewa " oh ni wannan Zaid din taya namiji zai zake yai ta bacci haka?"
Jiyai Zaid yace " Idona biyu nadai barku kuyi magana ne."
Da sauri Jalal ya kalli Ammar shima Ammar ya kalleshi, Jalal ya hadiye yawu yace Ammar sai munyi waya ko?"
Ammar ya daga mai kai, nan Jalal yai waje, Zaid ya kwashe da dariya yace " au wai kunya kukaji?"
Ammar ya tada mota ya wuce baice komai ba.
Sunkusa isa gida Jalal yakirashi, nan Ammar ya daga, Jalal yace " Ammar yanzu aka kirani daga police station sun iso dashi nan Abuja, amma kana ganin ya kamata Seemah taje?"
Ammar yace " mu bari tukunna ya nemeta da kanshi."
Jalal ya jinjina kai nam sukai sallama.
Suna isa gida Ammar ya shiga ciki da sauri, falo ya duba baiga Seemah ba Zahra ya gani ta fito daga daki yace " Zahra tana ina?"
Zahra tace " tana kitchen, abinci takema."
Wani sansanyar murmushi yai sannan ya wuce kitchen fin da sauri, tana tsaye tana gurza karas a greater, Ammar ya lalaba ta bayanta ya rufe mata fuska, murmushi tai tace " Ya Ammar ka iso?"
Saketa yai ya dawo ta gabanta yace " ohh na dauka bazaki ganeni ba."
Tai murmushi tace " Yaya na fadama taya za'ai in kasa gane ka?"
Turamai kujera tai tace zauna yaya ka gani.
Ammar ya kalleta yace " taya zanyi inzauna ke kuma kina aiki?"
Tace " me? Zaka tayani ne?"
Kai Ammar ya daga mata alamar eh, tai murmushi sannan ta dauko albasa da wuka da kwano ta mikamai tace " To gashi."
Hararar wasa ya mata yace " hmmm wato wayau ko? Kin dauka bansan albasa yaji gareta ba?"
Tadan hade rai kadan tace " shikenan tunda ba tayani zakai ba kawo na karasa kayana." Tafada tare da kokarin dauke kwanon.
Ansar kwannan yai a sauri yace " cewa nai bazan yi ba?"
Tai murmushi tare da ajiyemai, can ta daure tace " ina kuka je?"
Ya kalleta yace " mun danje birnin gwari ne."
Ta kalleshi kadan tace " da Deen?"
Kai ya daga mata tare da kura mata ido, murmushi tai tare da saurin wayancewa tace " ahh Yaya albasar dai ba yaji ko?"
Daurewa yai shima yace " akwai amma kadan."
Suka kalli juna sukai murmushi.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_Ina bawa masoyana hakuri najina shiru da kukai, kuyi hakuri amma insha Allahu zanyi kokarin ganin na kammala littafinan acikin satinnan, nagode kwarai da san da kukema littafin nan....Luv U Ol ❤_
No.7⃣4⃣
Abdul zaune yana kallan uwargidansa kallan tsananin mamaki yace " Rabi kinsan me kike fada kuwa? Ban gani in sakeki ba ina cikin wannan yanayin ba?"
Wata dariyar rainin hankali tamai tace " me? Kana tunanin soyayya ce tasa na aureka?"
Tai wata dariyar rainin hankali tace " are you naive or fool? Kai kana tunanin duk mutanen dake kusa dakai saboda suna sanka ne ko suna san kudinka? "
Abdul cikin mamaki ta kalleta yace " Rabi da kikazo na dauka abu na farko da zaki fara tambaya shine meya faru a shekara 20 din? Da gaskene? Sannan ki tambayeni halin da nake ciki a gidan yarin nan amma......"
Katseshi tai cikin fada tace " so kake inzauna ka fadamin wani shirme dakai a baya? Ko ce maka akai na damu da halin da kake ciki? Takardata nake bukata dumin inasan barin kasar nan cikin gaggawa kafin laifinka ya fara kokarin shafata."
Abdul ya kalleta cikin tsananin mamaki yace " me ne? 'Ya'yan mu fa? Ko kin manta da 'ya'ya a tsakanin mu?"
Rabi ta saki wata dariya taban haushin mai sauraro tace " 'ya'ya? Ahh haka ne ashefa kai baka sani ba ko? Amma ina mamakin ina hankalinka yake, sai dai kayi hakuri 'ya 'ya nawa ne ba ka da hadi dasu."
Abdul cikin mamaki yace " me kike nufi nufi da kalamanki? "
Tai tsaki tace " malam inka ga dama ka saken in bakaga dama ba kai ta ajiye da sakinka zan koma dubai da abokinka Marfuz wato uban 'ya'yana inka ga dama ka aiko mana da takardar saki can." Tana kainan ta mike, cikin zafin rai ya riko hannunta yace " marfuz? Abokina? Me kike nufi?"
Hannu tasa ta fizge hannunta da karfin gaske tace " matsalarkace, tana kaiwa nan tai waje."
Kai ya shiga girgizawa ya tuna shine sanadiyar arzikin marfuz kuma shine abokinsa da ya dinga zigashi akan abubuwa marasa kyau ciki kuwa harda fyad'en dayama fatima.
Ihu yasa cikin tsananin takaici ya rike zuciyarsa dake kuna tare da tsugunnawa a kasa, lalai kuka ma rahama ne, jiyai sam ya kasa kuka, sai wani irin zafi da zuciyarsa keyi.
Guard din dake bakin kofa ya kalla yace " dan Allah......."
Ai bai karasa ba yaji numfashinsa ya rike, nan guard din ya matso da sauri ya shiga danna mai baya, dakyar numfashinsa ya dawo.
Abdul sam ya kasa cin komai, a zaune kawai yake shikadai yasan me yakeji.
Jalal kam ya zama celebrity a gari ko ina ka duba kaga hutunshi a magazine ko a jarida ansa Jarumin da baya tsoron hukuma sai gaskiya, duk shirin dayace zaiyi kuwa a gidan tv to lalai zakaga mutane sun zako akan ganin me jarumi kuma matashi zak gabatar.
Biki ya matso, sai dai Zahra ce kadai take shirin bikin amma sam Seemah batasa baki a harkar in Zahra tazo mata da xancen ya zasuyi kaza, kya kacinta kawai tace to, dama ba fita take ba inba gidan Ya Habib taje ba, yau saura sati daya biki, gida ya fara cika, hakan yasa yau Seemah ta tattara kayanta kamar yanda Dad yace akan ta koma gidansa saboda matarsa tazo itama, ta gana cikin gada kayantane ta ci karo da agoggon ta kurama agoggon ido tai nan fa ta fara tunano rayuwarsu ita da Jalal, kallan agoggon take ta kuma zarfafa cikin tunani, Ammar dake tsaye a jikin kofa ya taho da saurinsa zai nuna mata katin biki na dinner daya amso, ganinta a zaune tasa a goggo tana kallo yasa ya tsaya, hannu a harde tare da jingina da jikin kofar, basai Seemah ta fadamai ba yasan agoggon da take kallo me yake nufi dan kuwa agoggon dake hannun Jalal kenan kullum, ya kuma gansu iri daya sak, jiki a sanyaye ya juya harzai fita sai kuma ya fasa ya koma ya tsaya tare da cewa " Kanwata ko in juya ne?"
Kallansa tai da sauri tare da juyawa ta goge hawayenta ta mike tace " yaya yaushe kazo?"
Ammar yadan hade rai kadan yace " nafi awa biyu fa anan."
Cikin tsananin mamaki ta kalleshi tace " da gaske? "
Dariya yai yace " lalai taya za'ai ki yarda?"
Harararsa tai tace " Yaya wato dai kai na kula inba tsokanata kaiba sam bakajin dadi ko? "
Shiga ciki yai kusa da ita ya tsugunna kasa ya dauko agoggon data yar tana saurin mikewa, kallan agoggon yai sannan ya mike tare da mika mata, kallansa tai batare da ta amsa ba, kallanta ya sakeyi yace " amsa mana nasan abune mai mahimmanci a gunki."
Kallansa tai tareda shan jinin jikinta tace " Yaya ba......"
Murmushi ya mata yace " ansa mana."
Hannu tasa cikin sanyin jiki ta amsa, yace " me? Kinaso ki mai sallama ne kafin biki?"
Kallansa tai cikin tsananin mamaki, da sauri ta juyamai baya tace " bafa haka bane yaya, kawai ganin agoggon nai."
Ya dawo gabanta tare da daga kai yace " nasani Seemah nasan komai hakan ne yasa banaso kidinga boyemin komai, nine na tambaye ki bawai ke kika tambayeni ba."
Idannunta ne suka ciciko ta girgiza kai tare da cewa " how can I......?"
" I am okay!" Ya fad'a yana kallanta, tai kasa dakai, yace " banaso ki dinga tunanin bakimai sallama ba..."
Ganin tayi kasa dakai ya juya tare da cewa " in bakyaso shikenan."
Yana fada ya juya kamar zai wuce, jiyai ta riko hannunsa ta baya, ya tsaya batare da ya juya ba, duk da kishin dake damunsa amma bayaso yaganta cikin wannan halin saboda shi.
A hankali Seemah tace " Yaya zan iya?"
Bai juyo ba ya daga mata kai tare da daurewa yace " banine na ce ba?"
Ta goge hawayen ta da d'aya hannun tace " yaya zan mai sallama tare da ajiye duk wani ragowar abu dake zuciyata, bazan sake tunaninsa ba bare insa ka kaji ba dadi ba."
Ammar ya daure ya juyo ya kalleta tare da mata Murmushi yace " karki damu Kanwata farincikina bai wuce naganki kina farinciki karki damu dani farincikina na tattare dake."
Yai ajiyar zuciya tare da cewa " in har kinaso ki ganni ina farinciki to ke zan jira kiyi farinciki kafin ni."
Seemah ta share kwallarta jikinta yai mugun sanyin, tausayin Ammar ya kara shigar mata zuciya, zare hannunsa yai yace " kishirya in ajiyeki, in yaso sai ya dawo dake."
Yana kainan ya fita, kallon tsananin tausayi ta bishi dashi, zama tai a gun tare da runtse ido tace " Seemah meke damunki? Taya zakice zakije bayan kinsan koyace kije dolene yaji haushi?"
Ta dade a zaune kafin Ammar ya kirata yace tafito yana jiranta.
Jalal kam zauje yake a dan karamin gidan daya kama, saboda ya sai gida babba yanzu a kaduna inda Umma da kuma matarsa Zainab suke zaune acan, Zahida kam itama jiki ya fara sauki sosai Zaid kam kusan duk karshen sati sai yaje, tun Zaheeda na wase wa harta fara saki gashi ba laifi yanzu tana iya takawa kadan kadan inta rike sanda.
Takardu ya gama dubawa sannan ya mike danjin yunwa ta fara kamashi, kallan calendar dakinsa yai ya zagaye wata number da jan biro, karasawa yai jikin calender yace " saura 7 days?"
Ajiyar zuciya yai sannan ya kalli wayarsa dayaji tayi kara alamar text, dagata yai yaga sako ne ga mamakinsa daga police station ne, wai Abdul na nemansa, yataimaka ya ziyarceshi."
Wata iska ya furzar yace a fili " Allah yasa ya daidaita tunaninsa akan 'yarsa."
Window ya zuge ya kurama titi ido, yaushe rabansa da Seemah?
Kai ya girgiza tare da cewa " Ahhhh...."
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀.
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_Ina kara godiya da jinjina gareku 'yan group d'ina na *Queen Bee* da kuma *Ayusher Fan Club* na gode kwarai da kaunar ku.......Allah yabarmu tare Ameen_
No. 7⃣5⃣
Jalal na tsaye jikin window yaji kiran Ammar daga wa yai yana tsokanarsa Ango da kanka?
Ammar ya kalli Seemah dake zaune a gefensa tayi shiru yace " ka fito ina wajen gidanka."
Jalal yace " ok ganinan dama ina so muce wani guri dakai."
Ammar yana kashe wayar ya kalli Seemah datai shiru, yace " zaki kai minti nawa?"
Kallansa tai idanunta suka dan canza kala tace " ni kati kawai zan bashi sai sallama da godiya daxan mai sannan in bashi hakur....."
Ammar jiyai zuciyarshi takasa jure wa ya kalleta hakan yasa tadan juya fuska tace " kajirani anan yana fitowa zan fita minti 10 ma ya isa."
Ammar baice komai ba ya juya ya kalli hanyar kofar da Jalal zai b'ulo, itama shiru tai tana tunanin anya ta kyautama Ya Ammar?
Kallan inda Ammar yake kallo tai daga nesa ta hango Jalal ya fito, Jallabiya ce a jikinsa fara sai dai tamai kyau, ido ta kuramai gani tai kamar yanzu yafi da kyau jitai zuciyarta ta shiga bugawa ta kasa dauke idonta daga kanshi, Ammar daya juyo dan yi mata magana yaga yanda take kallan jalal jiyai wani kishi ya taso mai, haushin kanshi ya fara ji menene dalilinsa na barinta taga Jalal? Anya yasan me yakeyi kuwa?
Har Jalal ya kusa isowa motar, Ammar ya kalleta tare da daurewa yace " Ki sauka kije kinga cema Dad nai xamu anso dinkinki, kallan Ammar tayi tace " yaya mu tafi kawai."
Da mamaki ya kalleta yace " kin fasa sallamar daban hakurin?"
Kallansa tai idanunta sun ciciko tace " Yaya banaji zan iya......"
Ammar zai yi magana kawai Jalal shikuma zuciya daya ya bud'e kofar inda Seemah take da tunanin zama a gun dan suje inda yace, glass d'in motar irin wace na ciki yana ganin na waje ne amma na waje baya ganin na ciki, ga mamakinsa Seemah ya gani zaune da sauri ya maida kofar ya rufe jikinshi a sanyaye, zuciyarshi ce ta fara bugawa da sauri.
Juyawa yai kawai maimakon ya koma gida kawai ya kama tafiya, Ammar ne yabishi da kallon tausayi sannan yace " Seemah bazakije ba?"
Jiki a sanyaye ta bud'e kofar, dan tunda suka hada ido da Jalal taji gaba daya jikinsa ya kama rawa ta fita tare da kallan Jalal daya tsallaka titi kamar ta kula kawai tafiya yake hakan yasa ko Ammar bata sakema magana ba balle ta rufe kofar tai gunsa da sauri.
Sam hankalinta nakan Jalal, So take ta tsayar dashi gashi batasan ya zatai ba, Ammar na jingine a mota yana kallanta, tazo tsallaka titi wani mai babur ya taho a guje, karar da Ammar yai na kiran sunanta yasa Jalal juyowa, da gudu ya taho gunta, itakam sam hankalinta nakan Jalal ganin ya nufota da gudu yasa ta tsaya cak, ta manta sam a titi take.
Saura kiris mai babur yai gaba da ita Jalal ya fuzgota, yai baka tim, Tsoro ne ya kamata, ta dago cikin firgice, tare da fara jijiga Jalal, hawaye sai malala suke tana kuja tana kiran Deen! Deen.
Ammar ma daya taho da gudu yai turus ganin Jalal a kasa, ganin yanda Seemah take kuka yasa hankalinsa ya dawo, matsowa yai tare da cewa " Jalal!"
Ido Jalal ya bud'e tare da kallan Ammar yace " Ammar dan taimaka ka tayani na mik'e."
Seemah ce ta kalleshi cikin mamaki au dama yana jinta? Mik'ewa tai tare da fara goge hawayenta, tace " Ya Ammar kacemai mu tafi asibiti a dubashi."
Mamaki ne ya kama Jalal, bai kalleta ba shima ya kalli Ammar daya mikamai hannu ya kama sannan yace " Ammar kacema matarka basai naje asibiti ba."
Ammar ya karasa dagashi tare da kallan Seema sannan ya kalli jalal yace " ni ba sakon wanda zan isar, Amma Jalal ka tabbata zaka iya tafiya?"
Jalal ya dan cizi leb'ensa kadan yace " karka damu z......"
Seemah ce ta katseshi da kallan Ammar tace " Yaya a'a mu kaishi asibiti please kaga saboda nine."
Jalal bai kalleta ba yace " nace bazani ba, gida zan koma."
Seemah kam daurewa tai ta matso daf da Jalal sun kusa isa mota, tace "kalleni."
Jalal yaki kallanta, ta kalli Ammar sannan ta kara cema Jalal " Deen please. ..."
Jin yanda tai maganar yasa Jalal ya kalleta a sanyaye tace " Deen muje asibiti please. "
Ammar kam da tundaga faduwar Jalal yasa duk jikinsa yai sanyi, ya kalli Jalal yace " Jalal muje asibiti a dubaka inba sokake hankalinmu yaki kwanciya ba."
Jalal bai magana ba har suka karasa motar, Seemah da sauri ta bud'emai gaba, ya kalli Ammar yace " A baya zan zauna."
Jiki a sanyaye Seemah ta maida kofar ta rufe tare da bud'ema Jalal baya, Ammar ne yataimaka mai ya shiga, gyambon dayake fatan ya warke shine ya mik'e shikadai yasan meyakeji ganin Seemah a kusa dashi kuma wai ankusa bikinta, jiyai kamar ya dauketa su gudu, hakan yasa bayasan kallanta bare yimata magana saboda shikadai yasan meke ranshi.
Sun fara tafiya Seemah dai a zaune kawaj take sai dai akai akai tana goge hawayenta, Ammar yai shiru a mota kawai tuki yake, sai taimakon Seemah da Jalal yai shi kuma ya buge, ga Seemah tun dataga Jalal ya buge take kukan nan , wani irin so Jalal kema Seemah?
Tambayar dayake nanatawa a zuciyar sa kenan har suka isa asibitin, bayan yaga likita nan akasa a mai X ray.
Seemah tai shiru a wajen dakin daya shiga tana tuno yanda Jalal ya buge, Ammar kam yana gurin likita, Jalal na fitowa ya dan tsaya a jikin kofa yana kallan Seemah batare data sani ba, jin kamar ana kallanta yasa ta juya, da sauri Jalal ya dauke idansa tare da cewa " Ammar fa?"
Seemah ta mik'e tsaye tace " ba dai wani abun ko? Ba dai wani abun ko?"
Kallanta Jalal yai zuciyarshi ta kara karyewa, a hankali yace " kar ki damu ba wani abun."
Ta matso kusa dashi tace " Deen meyasa d'azu zaka taimakamin? Kana tunanin zanfi farin ciki ne in ni banji ciwo ba kaikuma ka ji?"
Kallanta Jalal kawai yake cikin wani yanayi, ta share hawayenta tace " me yasa baka barni ba? Kasan yanda nakeji kuwa ganinka cikin wannan yanayi a maimakona?"
Jalal ya d'auke idansa tare da daurewa yace " ko waye ma naganshi cikin wannan yanayi zan taimaka mai, ya wuceta zai wuce, sai dai tsayawa yai cak ganin Ammar ya juya baya, da alama ya gansu tarene yasa ya juya baya, Jalal na kallansa ya gangara yai wata hanyar.
Tausayin kansu ne ya kamashi, me yasa zuciyarsu zataso mutum daya? Why?
Muryar Seemah yaji kamar tasan me yake cewa tace " Deen ka taba tunanin ya nakeji a cikin raina? How can u walk away from me bayan kana ganin waye ya kawoni dan inma sallama? Meyasa zuciyarka bata tunanin halin danake ciki?"
A hankali Jalal ya juyo idanunsa sunyi jaa sosai kamar masu shirin kawo ruwa cikin raunanniyar murya yace " Meemah I am okay! Kije gun Ammar I think shine yake bukatarki."
Kallansa tai jiki a sanyaye tace " bam gane ba."
Ya kalleta da raunannan idanunsa yace " ta ya ma zakisa Ammar ya kawoki nan? Me yasa bakya duba halin dazai shiga? "
Jiki a sanyaye ta kalleshi, Jalal ya juya kamar zai tafi da sauri tace " I am Scared."
Cak ya tsaya batare da ya juyaba, ta cigaba " zuciyata na tsoron kar inyi aure ba tare da na ganka ba."
Jalal ya juyo ya kasa kuma danne abinda ke ransa, cikin wata irin murya yace " what about me?"
Cikin tsananin mamaki ta kalleshi, yace " kinsan halin da nake ciki me zai sa kizo gurina ki nemi tada min hankali dayawa? Meemah kin dauka ni basan ganinki nake ba?"
Yai ajiyar zuciya tare da girgiza kai yace " noo."
Kawai banaso ran mutane dayawa ya b'acine ta sana diyyar mu."
Ya danyi hucci kadan sannan ya juya ya fara tafiya, kuka Seenah ta cigaba dayi, tun tana kallansa har ya bace mata.
Jalal kam gate kawai ya wuce ya tari babur yahau.
Sai text yama Ammar akan yaje ya dauki Seemah shi ya wuce gida, karya damu buguwar batai karfi ba.
Ammar na ganin sakon ya taho gun da sauri, a tsugunne yaga Seemah tana kuka wiwi, tsayawa yai daga nesa kawai yana kallanta zuciyarsa sai kuna take, ba abinda ya tsana irin hawayen Seemah.
Sai data gama sannan yaje ya mikar da ita suka wuce gida.
Jalal kam da yamma yaje gun Abdul, rokansa Abdul yai akan yana san ganin Seemah.
Jalal ya fadamai zai sa Ammar ya kawota duk da yasan ba lalai tazo ba.
Jalal duk ya canza da ya dade bai ga Seemah ba amma yanzu tunda ya ganta yaji hankalinsa yaki kwanciya jiyake kamar yafi santa yanzu ma.
Haka Seemah tun bayan sun rabu da Jalal ta zama maman shiru, tsakaninta da kowa a gidan bai wuce gaisuwa sai eh da a'a.
Ammar kam shima ya shiga wani yanayi balle tunda yaga Seemah ta canza gaba daya, Jalal ya sanar dashi Abdul na nemanta amma daya sanar da Dad yace " ya bari sai andaura aure sai suje tare."
Duk abinda akasama rana tofa lalai zaizo da sauri, yau gashi ta kama ranar alhamis ranar kamu kenan, hidima kam sai yinta akeyi, kowa ka kalla yana cikin farin ciki yake.
Jalal kam yau da zazzabi ma yatashi a jikinsa, a kwance yake tun dare gashi ba kowa a gidan shikuma baisan kiran ko Sagir ne, Seemah ma kawai yake takeyi dan batasan Dad da Ammar su gane.
Sai dai Ammar tun da suka bargun Jalal yasan halin datake ciki.
Anyi kamu na gani na fada a gidan Abba, Amarya Zahra da Seemah ansha kyau, haka aka gama taru lafiya sai kuma washe gari daurin aure.
Ammar na kwance a d'aki yana kallan number Jalal ya dade kafin ya daure da kirashi, sai dai duk yanda ya kira Jalal bai daga ba ya kalli agoggon bango na dakin karfe takwas na dare, yasan tabbas baiyi bacci yanzu ba.
Ya dade yana kiran Jalal sai dai duk da haka bai daga ba, kallan Zaid yai dake faman waya da Zaheeda yai dan bugemai kafada yace " tashi muje gun Jalal."
Zaid ya cema Zahi yana zuwa sannan ya kalli Ammar yace " ban gane ba."
Ammar yace Jalal yaki daukan waya inaji ba lafiya ba.
Nan yai waje tare da cewa " Zaid ka biyoni muje."
Sunje gida sukaita kwankwasawa, Jalal dakyar ya mik'e dan tun dafe ba abinda yaci ga zazzabi mai zafi dake damunsa......
Yana bude kofar ya fadi kasa.......
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🏌♀
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 7⃣6⃣
Ammar na tura kofar yaga Jalal a kwance a kasa cikin kid'ima shida Zaid sukai mota dashi, asibiti suka wuce dashi hankalin Ammar yayi dubu gun tashi gani yake kamar shine sanadiyar wannan ciwon, suna zuwa asibiti akai emergency dashi, Ammar ya tsaya a wajen dakin jiyake kamar yai ihu, Zaid ya kalleshi yace " kazo likita nasan ganinka."
Ammar jiki a sanyaye ya karasa ciki, likitan yace " kaine Guardian dinsa?"
" eh, wani abun ne?"
Likitan yace " me kukeyi har jikinsa yakai haka? Ga bigewar dayai abayansa baizo anyi treating dinsa ba sannan ga rashin cin abinci dan da alama rabonsa da abinci tun jiya da rana, ga damuwa mai karfi dake ransa, so kuke ku kasheshi ko me?."
Yai ajiyar zuciya sannan ya kalli Ammar wanda gaba daya abinduniya ya dameshi likitan ya daure ya dafashi, yace " ba komai zamu dubashi dakyai."
Ammar ya kurama Jalal ido, nan likitan yasa akaja gadon Jalal akai wani dakin dashi, Ammar ya kalli Zaid yace " ka fito da wayarka?"
Mikamai Ammar yai yana cewa ya kamata asanar da su Zahee ko?
Ammar bai amsa mai ba ya danna number Dad.
" Ammar kana ina ne kawu na nemanka?"
Ammar cikin sanyin murya yace " Dad ina asibiti."
A zabure Dad ya mike yace " kana asibiti kamar ya? Me a sameka? Ciwo kaji?"
Ammar ya girgiza kai kamar yana ganinshi yace " Dad kazo please, Jalal na kwace ba lafiya sosai."
Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar Dad yace " inalilihi wa ina ilaihi raji'un, Ammar meya sami Jalal din?"
Ammar dake kallan Jalal yace " Dad nidai kazo please. "
Dad yai ajiyar zuciya yace bari na zo.
Jiyai Ammar yace " kazo kai kadai please Dad."
Dad ya amsa tare da fitowa.
Sunyi shiru, a inda Jalal ke kwance, Dad ya kalli Zaid yace " tsaya anan Ammar ina da magana dakai."
Sun fita waje can gun da ba mutane sosai, Dad ya kalli Ammar yace " meya sameshi haka? Duk ya canza?"
Hawaye ne suka dan gangaroma Ammar yasa hannu ya cire yace " Dad ya zanyi? It's all my fault. "
Dad yai shiru yace " Ammar!"
" Dad."
Yai maganar cikin wata murya, Dad yasan halin Ammar da tausayi dafashi kawai yai yace " kaje gida nizan tsaya anan."
Kai Ammar ya girgiza yace " bazan iya tafiya ba Dad sai naga Jalal ya ware."
Kai Dad ya jinjina yace " to Ammar amma kaga dare yayi ga gobe karfe 10 za'a daura auren nan baka tunanin ya kamata kaje gida?"
Ammar yai shiru, can yqce " Dad in Seemah tasan Jalal bashi da lafiya ya zatai? Balle intasan ciwon a dalilinta ne?"
Dad ya kalleshi batare da yace komai ba, Ammar ya cigaba " Dad ya zatai?"
Kai dad ya juya yace " Ai ba fada mata za'ai ba."
Ammar ya runtse ido sannan ya bud'esu idanunsa sun cika taf yace " Dad baka gani muna shiga hakkin ta?"
Da mamaki Dad yace " Ammar me kake nufi haka?"
Ammar ya had'iyi wannan abun yace " Dad babban bakin cikina aduniyar nan bai wuce inga Seemah cikin damuwar da harzai kaita gayin kuka, amma Dad kasan kukan da nasa Seemah ta dalilin yaron nan? Sau nawa ina ganinta tana kuka akan abinda baifi karfina ba ko ince akan abinda nine xan iya daidaitashi, amma haka nake ganinta tana kukanta bana iya tab'uka komai saboda wani buri na zuciyata."
Hawaye ne suka gangaro kumatunsa, ya kalli Dad yace " Dad nan!!!!"
Dukan inda zuciyarsa yake yai, da karfi yace " nan gun Dad ni kadai nasan ya nakeji inaga Seemah na hawaye, sannan ina tuna Sadaukar da rayuwarsa da Jalal yai saboda Seemah, kanwarsa batada lafiya amma baije gunta ba......"
Dad ya dafashi yace " Amma ai ita Seemah itama ta zab'eka."
Ammar ya girgiza kai yace " tadai zabi farin cikin ka ne Dad, yarinyar nan bataso ko kadan taji tama abinda bazai faranta maka rai ba ciki kuwa harda sadaukarwa da farincikin rayuwarta, na sani zan kula da ita, ina santa kamar raina sai dai nasan inda zuciyarta take , Seemah na bala'in sona amma son 'yan uwantaka takemin."
Dad yai shiru sai dai jikinsa yayi mugun sanyi yakasa furta komai.
Ammar yacigaba tare da share hawayensa yace " Dad duk farincikin da Seemah takeso nima inasan shi sai dai ina bakin cikin zuciyata tana neman canza min tunani na."
Dad ya kalleshi, Ammar ya tsaida hawayensa yace " Dad na tsaida solution gobe auren nan da Jalal za'a daura bazan iya ganin abokina da kanwata danafiso a duniya cikin damuwa ba nikuma ina farin ciki ba."
Kallan tsananin mamaki dad yamai yace " Ammar kasan me kake fada kuwa?"
Murmushi Ammar yai wanda kana ganinsa kasan na bakin ciki ne yace " Dad ka taimaketa ne saboda son da kake ma mahaifiyarta da kaunar da kake ma yarinyar ko?"
Dad ya daga kai tare da cewa " hakane amma...."
Ammar yace " ka taimakesu ne saboda Allah na sani Dad."
Dad yai shiru, Ammar ya cigaba " in har munaso ladanmu ya karfafa agun Allah mu bawa Jalal Seemah sai kaga Allah yakara daukaka mu ya kuma biya mana da mafificin gidan Aljanna."
Dad ya kalli Ammar cikin tsananin kulawa yace " Ammar kaifa? Ni gani nake kamar sai kafi Jalal shiga wani hali in aka rabaku da Seemah."
Kai ua girgiza yace " a'a dacan a matsayin kanwata take yanzu ma a haka zata zauna, na sani sanda nake mata ya wuce duk yanda kowa ke tunani amma tunda ni kadai nake santa haka banaji wani abun zai sameni."
Dad kam kalaman Ammar sun ratsa jinin jikinsa, yace " shikenan Ammar."
Murmushi Ammar yai yace " Dad dan Allah karmu fadawa kowa sai Abba kowa yaji a gidan bayan an daura in ba haka ba wani sai ya nemi canzama ra'ayinka."
Dad ya dafa Ammar yace " Ammar ka tabbata ba komai?"
Kai Ammar yadaga yace " marainiyar Allah itace first ni daga baya, sannan sai kamin addu'a Allah yabani wata."
Rungumeshi Dad yai yace " Ina Alfahari dakai d'ana ka fahimtar dani abinda ban yi tunani ba, Jalal yaron kirki ne tun yana karami, naji dadi sosai da kaunar da kukema juna kuna yara ta dawo muku yanzu."
Sun dade agun suna hira kafin su koma ciki, dad da Zaid suka koma gida.
Washegari kowa ya tashi anata hidima, Seemah ta rasa dalilin dayasa gabanta keta faduwa, Ammar ta kira sai dai taji Junaid ya d'aga, tace " yaya Ammar fa?".
Junaid ya kalli Zaid wanda yace Ammar yace kar afad'a mata inda yake, yace " yad'an fitane."
Ta kashe wayar tare da d'an had'e rai.
Zaune suke a massallaci an fara add'uoi za'a daura aure.
Abba zaune yayi shiru yana tunanin kalaman Dad, na jiya daddare, ajiyar zuciya yai alokacin da akace waliyin Jalal yaji dad yace " ganinan."
Dad ya riga ya sanarda mahaifin Jalal wato Amadu nan yai farin cikin da hakan har kuka sai dayai.
An dauren auren Junaid da Zahra, Jalal da Seemah akan sadaki dubu d'ari wanda da kudin da za'a bada na Ammar ne.
Mamakine ya kama 'yan uwan mahaifin Dad dana mahaifiyarsa, Habib ya kalli Dad cikin mamaki sai dai aikin gama ya gama.
Zaid ne ya kira Ammar dake asibiti gun Jalal yace " Ammar an d'aura."
Runtse idanunsa yai jiyake kamar yasa ihu, dakyar ya daure yace " ka fad'awa Seemah mijinta na asibiti ba lafiya."
Zaid yace " Ammar inzo in daukeka?"
Ammar ya d'aga kai, Zaid ya daga kai tare da cewa " Jalal din ya farka?"
Ammar ya girgiza kai yace " a'a ko ido ya bud'e sai dai inga ya maidasu, sai dai likita yace abarshi ya huta stress sunmai yawa ga damuwa."
Zaid ya d'aga kai.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
*Luv u oll my fans.......*
No.7⃣7⃣
Seemah na zaune tayi wanka tana jira agama ma Zahra kwalliya sannan a mata, rigace doguwa ta atamfa a jikinta aiki ne a jikin rigar har wajen ciki d'inkin yayi masifar kyau, a zaune kawai take amma gaba daya batajin jikinta daidai, jitai an fara kud'a hakan yasa gabanta ya sake fad'uwa, suka shigo d'akin sukace an d'aura, Seemah kasa tai da kanta ganin wayarta tai kara yasa ta daga, Zaid ne da sauri tace " Ya Zaid ina ya Ammar? Jinake kamar wani abu ya sameshi."
Zaid yace " Seemah ki fito ina waje mijinki ba lafiya."
" Naam? Me kake nufi?"
Kashe wayar yai dan jiyai baisan me zai ce mata ba, A zabure Seemah ta mik'e ko hijab bata dauka ba d'ankwalin data yafa akanta kawai ta sura tai waje ko takalmi batasaba.
A waje taga mutane sun taro anacewa " waye kuma Jalal?"
Tsayawa tai turus, can kuma sai tai tunanin ko ba Jalal d'in ta suke nufi ba, waje tai da sauri ta fada mota Zaid ya kalleta sannan ya ja motar, duk ta rikice tace " Ya Ammar meya samu Ya Ammar d'in?"
Kallanta yai jiki a sanyaye yace " Kunyi magana da dad?"
Ta girgiza kai tace " a'a yadai kirani da safe yacemin, ko mai na rayuwa mukaddarine, haka kawai yacemin."
Suna isa asibitin suka fito, duk Seemah ta rikice, harsunje shiga d'akin wayar Zaid tai kara, ya kalleta yace " nan ne ki shiga."
Ko kula shi batai ba ta fada dakin, daga nesa tafara ganin kamar ba Ammar ba, jiki a sanyaye ta karasa kusa da gadon, turus tai ganin Jalal a kwance duk ya rame sai bacci kawai yake.
Hawayene suka fara zubo mata a hankali takai hannu gefen fuskarsa hawayenta ne suka shiga d'iga kan kuncinsa, sai zubowa sukeyi ta kasa magana sai hawaye kawai take.
A hankali Jalal yad'an bud'e ido jin ruwa na d'igarmai, kallan Seemah yadauka mafarkine yasa ya kara lumshe ido, hawaye kawai takeyi, can ya sake bud'e ido daidainan ta kalleshi, idanu suka had'a yad'an motsa bakinshi kad'an yace " Meemah?"
Hawayene ya cigaba da zubo mata tace " Deen? Me ya sameka haka?"
Sai a lokacin ya tabbatar ba mafarki yake ba kallanta yai tare da cewa " me kike anan?"
" Naam?"
Tafad'a tare da kallan d'akin sai a lokacin ta tuna kamarfa Ammar ne yakamata ta gani ba shi ba, ta d'an juya tace " Ni cemin akai inzo in duba mijina na d'auka ya Ammar ne bashida lafiya."
Jalal ya d'an juya ido yace " meya sami Ammar d'in?"
Ta d'aga wayarta ta kira Zaid ga mamakinta Ammar ne ya d'aga.
Cikin tsanin damuwa tace " Ya Ammar kana ina?"
Yace " Seemah?"
Yanda ya kira sunanta yasa jikinta yai sanyi ta kasa amsawa.
Cikin wata murya yace " ki kula da mijinki, ke yake bukata a wannan lokacin."
Da mamaki tace " ban gane ba? Kana ina?"
Yai shiru can ya daure yace " An daura muku aure da Jalal karki damu dani ko kiyi tunanin wani abun, kawai ki kulada lafiyar mijinki."
Jitai kalaman sun shigar mata kunne banbarakwai sai dai kafin ta sake magana Ammar ya kashe wayar.
Kallan Jalal tai sai dai ganin yanasan tashi ya kasa saboda cikin dake bayansa, yasa ta daure matsowa tai zata taimaka mai, kallanta Jalal yai yace " bashi kawai, ki nemomin likita."
Bata kulashi ba kawai ta shiga taimaka mai, tana gamawa ta duba ga kayan shayinan da abinci hakan yasa ta hadamai shayi ta mikamai tace " ina zuwa."
Kallanta yai yace " kina zuwa ina? Me zaki dawo yi anan? So kike ran Ammar ya sake b'aci?"
Kallan yanda ya rame tai ta kauda kai tare da cewa ni kaina ban fahimci abinda ya Ammar d'in yake nufu da an d'aura mana aure dakai bane shiyasa nakesan ganinsa.
Bata jira mai zaice ba tai waje, Jalal ya kara maimaita kalamanta.
Seemah na fita taga Dad yana tahowa shida Abba, da sauri takarasa gunsa yace " Seemah muje ciki."
Kallan mamaki tamai sai dai ba zata iya musu ba.
D'akin Jalal suka koma bayan sun zauna shiru, nan Dad ya warware musu duk abinda ya faru jiya zuwa yau.
Seemah kuka take sosai, yana gama maganar yace " dan haka ki zauna anan ki kula da mijinki ki bar sha'anin biki su Zahra sayi."
Ta kasa magana haka ma Jalal wanda yakejin maganar kamar ta tsuniya, ganin halin da suka shiga yasa Dad ya mik'e shida Abba sukai waje.
Seemah ganin sun fita yasa ta mike da gudu ta bi bayan Dad ta baya ta rungumeshi tana wani irin kuka, Dad ya daure ya juyo da ita setinsa yace " Seemah?"
Cikin tsananin kuka tace " Dad meyasa ka bar Ya Ammar yai haka? Kamanta nace na hakura? Sannan babban burinka ne fa?"
Dad yad'an shafa kanta sannan ya kalli kafarta da ko takalmi babu yace " a haka kika fito ba ko takalmi?"
Hawayenta ne ya karo tace " Dad ina Ya Ammar d'in? I have to meet him. "
Dad yai murmushi yace " karki damu yayanki yace ki kulada Jalal."
Yad'an zareta daga jikinsa yace " karkiyi tunanin komai sai mijinki."
Yana kainan ya juya ya fara tafiya.
Tsugunnawa tai a gun ta shiga kuka, ta dade agun sosai mutane sai wucewa suke suna kallanta dakyar ta daure ta mike tai cikin d'akin ga mamakinta Jalal ta gani ya mik'e yana sa rigarsa, da sauri ta karasa inda yake? Idanunta duk sun canza tace " Ina kuma zaka?"
Kallanta yai yace " me Ammar yake tunani? Ni zanje in mai magana."
Cikin kuka tace " ni ina zansan me yake tunani, amma kaidai bazan barka ka fitaba bayan ba lafiya gareka ba."
Kallanta yai cikin wani yanayi yace " Meemah tunanin halin da Ammar yake ciki nake."
Ta goge hawayenta tace " naji wannan amma ka koma ka kwanta sai inkira Ya Ammar d'in."
Jiki a sanyaye Jalal ya zauna, ta mikamaj wayarta tareda dialling d'in number Zaid.
Ammar ya d'auka, Jalal yace " Ammar meke faruwa?"
Ammar yad'anyi murmushi kad'an yace " meke faruwa dame? D'an na bar maka Seemah ko dan kana tare da ita?"
A zuciye Jalal yace " Ammar meke damunka ne? How can u joke now."
Ammar yai ajiyar zuciya yace " kai dai dakake lovesick yanzu sai ka ware."
Jalal yace " Ammar ban aminta da...."
Katseshi yai da cewa " ka saketa to."
Yanakai nan ya kashe wayar, shiru Jalal yai yana maimaita kalmar saki.
Seemah ta zauna kusa dashi kadan tace " me Ya Ammar d'in yace? Wasa yake ko?"
Jalal ya kalleta cikin mamaki yace " da alama dagaske yake tunda haryake cemin wai in sakeki ."
Ta kalleshi da mamaki, mik'ewa tai da sauri tace " Me Ya Ammar yake tunani?" Tafad'a tare da hura iska.
Jalal ya daure yace " taimaka min in kwanta please. "
Harararsa tad'anyi tace " akan me?"
Kallanta yai sannan ya daure yace " hmm kiramin ko nurse ne."
Ta d'an tab'e baki tace " nurse d'in ai kala biyu ne, maza da mata wacce kakeso a kira ma?"
Jalal ya kalleta tunowa yai da masifarta ta da yace " auu kiramin koma waye ai ni patient ne."
Ta makamai harara tare da turashi gado da d'an karfi, zafi yasa sai daya saki kara yace " me kuma nai kinsan dai ba lafiya ce dani ba, irin wannan tureni?"
Ta harareshi tare da komawa gefe ta zauna, Jalal ya juya kai kamar mai bacci dan jin abin yake banbarakwai.
Text tama Ammar kamar haka.
_Ya Ammar na sani sarai kayi haka ne dan farin ciki na sai dai Ya Ammar aikin gama ya gama bani da abincewa a wannan lokacin, kalma daya zan iya fadama shine Allah ya sakama da mafificin gidan aljanna ya kuma baka matar data fini._
Tana turawa ta
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
*LAST PAGE*
No. 7⃣8⃣
Can gida kuwa wasu abin nan ya basu haushin gani suke Dad bai kyauta ba, wasu kuwa harda habaici na dama yarinyar da batada mahaifi me zaisa ya had'ata da d'ansa?"
Zahra kam taji ba dadi dasu Junaid sai dai ya za'ai tunda dai an riga da angama, Ammar ko gidan baije ba, sun riga sun shirya yin dinner sai dai Zahra ce da Junaid kawai zasu.
Jalal kam suna kwance, sai can Seemah ta farka, tana ganin Jalal idanunsa biyu da sauri ta mik'e tsaye tare da wayancewa da hmm ina toilet din ne? Tafad'a tana dubawa da gudu tai nufi kofa ta bud'e ta shige.
Jalal ya bita da dariya ganin yanda ta rikice.
Tunanin wayarsa ce tazomai yasa ya jawo wayar Seemah ya kira Abbansa.
Abba ya daga, Jalal ya gaidashi.
Cikin zumud'i Abba yace " Jalal kaji abin alheri ko? Bansan mezancema Ammar da Isma'il ba."
Jalal yadanyi murmushi yace " Zainab fa?"
Abba yai shiru, Jalal ya danyi murmushi kad'an nasan bazatai farinciki ba.
Abba yace " Jalal kayi tunanin inda Seemah zata zauna?"
" hmm ina tunanin tambayarta ko nan kaduna ko kuma nan, ni abin ne banbarakwai nake jinsa."
Abba yai dariya yace " ba wani banbarakwai Allah ya riga ya tsara Seemah matarka ce."
Jalal ya kalli kofa inda yaji motsin Seemah, yace " Abba sai anjima wayar Seemah ce."
Nan sukai sallama tare da kashewa, Seemah ta harareshi kad'an tare da cewa " wa yace a d'aumin waya?"
Jalal ya dan yi murmushi yace " yayarki na kira."
A zabure ta karaso kusa dashi tace " wacce yayata?"
Kallanta yai yace " haka ake jinyar baza'a bani abinci ba? Yunwa nakeji."
Ranta a b'ace ta bud'e kular da ta gani a d'akin fatan dankali ne yaji kifi sosai, ta zubamai a plate sannan ta mikamai, tace " wacce yayata?"
Jalal yadan rik'e ciki kadan yace " haka ake kula da miji ko abincin baza'abarshi yaci ba?"
Juya kai tai aranta tace " su miji manya."
Yana gama ci ta kalleshi tace " wacce yayata? "
Hannu yasa ya riko ta tare da zaunar da ita kusa dashi yace " Meemah bamuyi tunanin inda zaki zauna ba?"
Ta turo baki tace " inafa zan zauna?"
Ya kalleta yace " inda zamu zauna nida ke a kaduna ko anan."
Ta mik'e tare da cewa " ni yazanyi iyi sallah ko mayafi ban fito dashi ba, kallanta yai yace " ai kuwa sai dai kiyi waya a kawo miki dan bazaki fita a haka ba......"
Kusa dashi ta matso tace" to ya kakeso inyi?"
Yace " bana fadamiki ki sa a kawo miki ba nidai matata bazata fita a haka ba mutane su kalleta."
Ta sa dariya sai data tsagaita ta kalleshi tace " lalai mai mata."
Lumshe ido yai yace " sosai ma, Ammar ne ya bani matar da nakeso wacce ji nake duk numfashina tana tattare dani."
Dariya ta sakeyi tace " Kai Deen yaushe ka zama haka?"
Jawota yai jikinsa yace " ke kika maidani haka, mu zauna a abuja ko? Kinga kusa da Dad d'inki."
Ta turo baki tace " bayan bani kad'ai bace matar ka?"
Yai ajiyar zuciya yace " Meemah amma kinsan ai...."
Saurin cusa kanta tai a kirjinsa alamar kunya tace " na sani amma a da dan rannan tafiya kai ka barni."
Ajiyar zuciya yai yace " Meemah banasan zama a asibitin nan mu roke likitan ya sallamemu please kinji?"
Tace " naki wayan baka warke ba ta ina zamu tafi? Kuma ni banshirya tarewa yanzu ba."
Hararta yai yace " a ina? Ai kafata kafar matata Amnar yamin abinda ban taba zatoba ta ina nikuwa zan barki kije wani gida? Mu tafi gidana inyaso sai insa a nemarmana gida."
Baki ta turo tace " an fa kai min kayana can gidan Ya Ammar kuma kwasowa za'ai ko me?"
Jalal ya rungumeta yace " bakomai sai musai wani."
Ta mik'e tace naki wayan.
Washe gari kuwa sai da Jalal ya matsa aka sallameshi duk lokacin abinci ana aikowa daga gidan su Dad.
Ammar kam hotel ya koma kawai ya tare, su Dad basu sani ba ashe yayi booking d'in jirgi, washe gari da safe yazo ya sanar da Dad zai koma England amma ba dadewa zaiyi ba, ba musu Dad ya amince saboda yasan halin da Ammar din ke ciki.
Bayan Jalal ya warke da kanshi ya kaita gun Abdul, nan ya nemi yafiyarta tare da alkawarin canza halayensa, sunyi ziyara har garin iyayenta nan sukaje taga 'yan uwanta.
Jalal ya kama gida a Abuja inda suka zauna shida Seemah, kulawa kaunar dake tsakaninsu ta wuce duk yanda zan kwatanta muku, Yau yakama wata tara kenan da auren su, duk karshen mako yake tafiya kaduna Seemah ita ta tsara mai hakan saboda tana ganin yanda yake rashin damuwa da Zainab hakan bazai mata dadi ba, shikanshi yanzu yana daidai kokarin kwatanta adalci a tsakaninsu, sam Zainab bata jin haushin Seemah ita gani take ma auren da Jalal d'in yai shine sanadiyyar kulata da Jalal yake, Seema na d'auke da tsohon ciki, itakuma Zainab laulayi takeyi.
Jalal ya shigo gidan ganin yanata sallama ba'a amsa ba, a rude ya shigo gidan ya fara neman inda Seemah take, har daki ya shiga batanan, d'akinshi ya nufa, yana budewa yaga ta fesheshi da wani farin abu, baya yai yana mamaki, nan ta matsamai ya kalli d'akin, candle ne kanana an jera shi a kasa anyi kwalliyar I♡U dashi kwaliyar tayi kyau, ya kalleta cikin mamaki, kayan bacci ne a jikinta shara shara ya sakar mata wani sansanyar murmushi tareda karasowa ya rungumeta, murmushi itama tai tace " My Deen kardai a manta da babynmu."
Sassauta rikon yai sannan ya d'ago a hankali ya kai bakinshi cikin nata, wani irin salon kauna sukema junansu, jitai kafarta naneman kasa d'aukanta, Jalal ya riko kugunta nan suka cigaba da aikama juna sakwanni, a hankali Jalal ya jata kan gado sannan ya tare neck tie d'insa ya cigaba da sumbatarta, cikin salo a kuma hankali ya bakinshi na nata ya zare mata 'yar rigar dake jikinta, itama mab'allin rigarsa ta dinga cirewa har ta cire su duka, sumbatar kirjinsa ta fara nan fa suka shiga cikin wani yanayi wanda su kadai sukasan halin da suka shiga.
Sai da suka gama sannan ta kwanta akan kirjinsa, shikuma yana shafa kanta, yace " Meemah wannan gyaran fa? Decoration d'in yayi kyau, kara kwanciya tai a kirjinsa tace " a internet na dubo yanda akeyi."
Yai ajiyar zuciya yace " Meemah in miki wani alkawari?" Ta d'aga kai, tare da juya fuskarta saitinshi, yace " indai mace kika haifa sunan Mahaifiyarki zamusa mata Fatima, in kuma namiji ne to sunan Ammar ko Dad sai kizab'a a ciki."
Murmushi tai tace" nagode sosai Deen, amma ya maganar Ya Ammar?"
Yace " yace next week zai dawo."
Tai ajiyar zuciya tace " kaii nayi missing d'in yaya."
Mikewa yai ya sunkuceta sukai toilet, kafin suyi wanka sai daya wanke mata kai da kanshi, dan tace bata iya sunkuyawa, nan sukai wanka suka fito a tare, shi ya shafa mata mai sannan itama ta shafa mai tana shafamai tana tambayar yasu Ya Zainab?" Yace suna lafiya.......
Ammar ya zaune a cikin jirgi yana karanta jarida watace a zaune a kusa dashi ta zake sai bacci take, haushi ya kama Ammar ya juya kansa jikin window, tana gama baccin ta mik'e tare da yin mika, ta kalli Ammar tace " dan Allah awa nawa mukai?"
Kallanta yai yace " ke agoggonki tsayawa yai?"
Agoggon hannunta ta kalla ashe da agoggo a hannunta da sauri ta juya fuskarta, yai murmushi sannan ya juya, mai service ce ta karaso ta kallesu tace " mai kukeso a kawo muku? Tea ko coffee? "
A tare sukace " Coffee."
Kallan juna sukai sai sukai dariya, matar tai dariya itama tace " da alama ku couples ne kunyi matching sosai."
A tare suka kara cewa " a'a."
Tai sake dariya sannan ta tafi, tana tafiya Ammar ya kalleta kadan kyakyawa ce sosai, juyawa yai jiyai tace " A Abuja kake?"
Yace " eh kefa?"
Tace nima...........
Murmushi sukama juna a tare.
Zahra ma ankusa haihuwa, Dad da Abban Jalal aminta ta dawo sosai, yanzu Abban Jalal yananan yana kasuwancinsa a babban shagon da Jalal ya bud'e mai.
Zaid ma saura wata d'aya ya auri Zaheeda wacce ta warke sumul, har malami Jalal ya d'aukar mata yana koya mata karatu.
Abdul kuma an sakeshi yana zaune a dan karamin gidansa shida matar sa 'yar uwar Sagir, Ya canza kamar bashi ba.
Jalal da Seemah masha Allah kauna kam suna san junansu sosai........nace To Allah yasauketa lafiya
Nima nace mu had'u a wani littafin nawa in Allah ya yarda.......
*GODIYA TA MUSAMMAN GAREKU*
*Yan Group d'ina*
*THE QUEEN BEE*
*AYUSHER FAN CLUB*
Sannan ina godiya gareku 'yan
*NAGARTA*
BEELY BADARU GROUP
'YAN SAUYI NA KCK
EXCELLENT HAUSA WRITERS
MU SAN JUNA
TALENTED HAUSA WRITERS
MARYAM MAI DALA
HAUSA NOVEL
MY BLOG FANS
HAUSA NOVELLA
BE A LADY WITH FASHION
Da kuma ragowar group d'in da duk nake ciki ina godiya gareku.
Ina alfahari daku
*MY BEELY BADARU*
*SIS PHARTY*
ASY KHALEEL
MAMAN SHAHEEDA
MUNAY
SADNAS
AUNTY KYADY
FATTY
Ahh gaisuwa gareki babbar Aminiya *AISHA M.UMAR....*
*NI AYUSHER MUHD ke muku fatan alkairi*😘😘😘😘