Salma haka ta zauna har saida salman yagama cin abinci tana kalansa, daya ce taci sai tai murmushi tace ni ba yanzu ba, nafisan in kalleka har ka gama, yace in na kware fa? Tace bazaka kware bama in kuma hakan tafaru sai in baka ruwa😊 tai maganar tare da nuna mai jug d'in ruwa, dariya yai yacigaba da cin abincinsa, bayan ya gama ya mike, salma tace ina zuwa, ya kalleta da mamaki, d'aki tai da sauri, ta d'auko jotting book d'inta sabo ta duba rubutun ciki baifi 3pages ba dasaurI tasa hannu ta yage, sannan ta d'au biro ta makala a littafin ta fito da sauri.
Salman na tsaye yana jiranta ta karaso tare da mikamai, yakalleta yace na menene? Tace na karatunka mana😉, salman yace what? Tad'an turo baki tace a class in anyi wani abun ai zakai jotting, salman yace wa? Ni? Salma tace kai my prince☹ irin wannan dizgi😢? Salman ya kalleta yai murmushi yace hakan ne dizgi? Ta juya baya cikin shagwaba tace eh mana gashinan☹, ajiyar zuciya yai ya juyo da ita sannan ya anshi littafin yace happy? Ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace alot😊, ya sunkuyo yamata kiss a goshi ya fita, ta dade a tsaye tare da shafa gun kafin ta shiga ciki.
Salman shikanshi a mota ya dade kafin yaja mota, yana isa gidan najib a waje ya tadda shi, bai fita ba najib ne yashigo, salman ya ja mota sukai skul, sai da sukai parking najib ya kalli salman yace yarima gaskita na yarda aure nacanza mutane😁 salman yace bangane ba? Najib yace da ace da ne da gudu zamu shigo muna tada kura amma yanzu baka gudu da mota nakula, ko dan......salman ya kalleshi yace kodan me? Yace ohh ka manta? First had'uwarku da salma ta hanyarne? Salman ya tureshi yace najib na kula kwanan nan gulma ke cinka dayawa, najib yai dariya yace Ango Ango, salma ya bud'e motar tare da ya fita, najib ya kalli kusa da inda salman ya mike ganin littafi da biro yasa shi wani tsananin mamaki, da sauri ya fito, sai dai baiga salman ba, can ya hangoshi yana tafiya, da sauri ya bishi.
Salman sai dayaje kusa da theater d'in dazasuyi lectures ya tsaya, najib ne ya karaso yace kai wasa wasa kana da sauri, salman yace ina zan tsaya ka bayan kana ganin rana ake, najib ya kalleshi yace muje, salman ya kalli hannunshi yace wannan? Da sauri yasa hannu ya fizge, najib yasa dariya yace najib dagaske ne abinda nake zargi? Naka ne littafin? Lalai in nakane da alama za'ai ruwa da kankara, salman yace to parrot sai kai tayi, na matatane menene? Najib ya bud'e baki yace da alama naka ne da gaske😳 u? Littafi? Ha ha ha .
Salman ya makamai littafin akai ya wuce ciki, to ba najib ba salman gani yai kowa na kallansa da sauri ya d'aga rigarsa yasa littafin a ransa yace yazanyi da beauty🤔?.
Fulani zaune tayi shiru, ta kalli farha tace farha ki bani yau zuwa gobe zan samo mana wani plan d'in farha tai kasa dakai, itadai tafara tsoro sai dai salman ne batajin zata iya hakura dashi, farha ta mike tace to fulani Allah yakaimu goben, fulani ce tace farha kirami hindu( baiwar fulani ce) farha tace to, hindu ta iso tare da tsugunnawa, tace gani ranki ya dade, fulani ta kalleta tace kinsanar da ishaq d'in inasan ganinsa? Hindu tai shiru, fulani tace dake nake, hindu tace nafad'a mai amma yace kiyi hakuri bazai samu zuwa ba, kuma bayasa ran har zuwa gobe zai samu dama, fulani ranta ya kara baci,takalli hindu tace fita, hindu tace to dasauri tai waje, fulani ta rike kanta tace ni? Ishaq? Hannunta ta dunkule, aranta tace da alama sai na lalaboshi.
Salman zaune a aji ana lectures, sai dai wayace a hannunsa yana dane_dane, najib yad'an zunguroshi yace yarima bazakai rubutu a littafin love d'in ba? Ga malan nata bayanai? Salman ya ture hannunsa yace kai rubutun kake? Najib yace yanzu nake tunani da alama gobe zan shigo da littafi tunda matar ka ta sa mu😊 salman ya makamai harara, najib yace kawo naku na love ni sai in muki rubutun, salman yace ka manta kana nufin littafin beauty d'in zan baka kamin jagwalgwalon rubutunka? Najib yace ahhh hmmm ayi hakuri, salman ya juya tare da kallan wayarsa jin karar text, dasauri ya bud'e ganin daga salma ne.
" My prince please concentrate".
Ya kalli text d'in , yace ya akai ta sani? Wani text ne yakara shigowa.
" please "
Salman ya karanta tare da murmushi, sai kuma ya ajiye wayar yad'an d'ago ya kalli malamin amma dayake bai sababa haushi ya kamashi yaga ina... kifa kai yai akan desk d'in.
Salma dake zaune tana breakfask ta kalli wayar tare da murmushi, tun daren jiya tasan yazama dole su kwaci kansu a gidan nan, kuma duk tunanin datai abu na farko daya kamata shine salman ya gama skul........
By *AYUSHER MOHD*📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣7⃣
Salma zaune take akan sallayar datai sallar la'asar suna waya da Abba, jitai ana mata knocking da karfi, tanaji tasan basu hanne bane, cikin mamaki tace Abba sai anjima tare da mikewa, ta bude kofar ta fita, farha ce, mamaki ya kamata ta kalleta cikin mamaki tace malama lafiya? Farha ta kalleta cikin gadara tace bake nake nema ba😏 salma tace wa kike nema kenan? Farha tace kinfi kowa sani ai, salma tai murmushi tace kinfi kowa sanin baya gidan ai da alamun yanda kika bugamin kofa, farha tace matsalarki, dama abinda yasa na miki knocking so nake kiban d'ayar number yaya na kira mtn d'inshi ya ki dauka.
Salma takalleta baki bud'e tace ke da wa kike magana tukunna? Farha tace au mu 10 ne agun? Salma tace nakula marin jiya bai isheki ba, farha tai wata shewa tace toko zaki kara? Salma tai tsaki tace sai kuma aka samu matsala banda tym d'inki, ta juya ta koma d'aki tare da datsowa.
Farha tai zauna akan kujera ta tuna magajarsu da fulani, datace ki nunamata bakya tsoronta, sannan bakya kara akan san salman, kishi zaisa ta mareki ko ta miki wani abun, ke kuma duk randa ta miki abu ki tabbatar ab'angarentane dan bayinta su gani, in ta mike sai ki kawo kara guna, nikuma sai insamu sarki infad'amai, dan salman na kulaki ta miki duka, wai soyayya kuke, ni dakaina zanba sarki shawara.
Farha bayan tagama tunani tai tsaki tace yau plan d'in beye ba da alama sai na sake wani shirin, ta mike tai waje.
Salma kam a d'aki tsakiwa tai ta rike kafad'a tace what? Number yaya? Lalai farha tagama rainata, ba shakka sai ta d'au babban mataki akanta.
Salman sai bayan isha'I ya dawo, wasu bayi na biye dashi da ledoji manya guda biyu, a falo suka ajiye suka juya, salman ya d'au ledojin tare dayima salma knocking, da sauri takara shafa hoda tasa turare kad'an ta bude kofar tare da sakin murmushi, salman ya kalleta yai ajiyar zuciya, ta kalli hannunsa sannan ta anshi leda d'aya, yana shiha ciki ya ajiye kayan akasa ya jawota jikinsa ya rungume, ta shafa bayansa tace da alama prince d'ina ya gaji, salman yace kai I miss u beauty, jinai kamar na dade ban ganki ba, tai murmushi tace eh mama ka dad'e mana tunda tun safe ka fita☹ salman ya kara rungumeta yace gaskiya kam, ajiyar zuciya sukai a tare sai kuma suka saki juna sukai dariya duk hakoransu suka fito, salman ya zauna akan gadon yace ahh beauty da alama shiga zuciyata kike kima ganin abinda zanyi, tai murmushi tace au shiga ma nake? Nad'auka da a ciki nake🙄? Salman yasa hannu ya jawota ta zauna akan cinyarsa ya mata kiss a baki yace mantawa nai ashe a ciki kike? Salma tad'an mintsineshi a ciki sai dayai 'yar kara tace ashe? Dariya yai shima yasa hannu a cikinta ta d'auka ramawa zai sai taji ya sa hannunsa a cikinta yana wasa dashi, motsi tafara tana ture hannunshi tace please ka bari, wanna fa wayon chakulkuli ne, dariya sukai so sai suka kwanta akan gadon a rigingine, salman ya mike yace beauty taso yafad'a tare da d'agota, ta mike tana kallanshi yace kaya ma siyo miki, tace haba? Yace jawo ki gani, nan ta jawo ledojin, English wears ne kala kala, riga da wando, riga da siket, riga iya gwiwa ta d'ago d'ayan ledar, duk mii siket ne da kanannan riguna wanda ko ciki basu rufeba, da sauri takalleshi tace naji wancan nawa ne amma wannan fa? Salman yace shima nakine 😉
Ta kalleshi tace wannan? Tafad'a tare da d'aga kayan, salman yace eh kuma yanzu zaki kwada d'aya nagani ba🤔 salma tace naam? Salman yace ina jira, salma ta kalleshi ya had'e rai yaci wani magani, tace prince ai.....katseta yai yace in bazakisaba ki barshi, tace ba haka bane, tafad' a tare da d'aukan d'aya harzatai toilet ta tuna da sauri ta dawo jikin kujera tafara kokarin cirewa, tanayi tana kallan salman, sai dai shi ta kula hankalinsa nakam wayar hannunsa.
A hankali ta zura rigar ta kamata sosai, ga rigar bata gama rufe ciki ba, ta kalli siket din tasan ko cinya bazai gama rufe mata ba, takalli salman sai dai fuskarnan a had'e nan ta shiga sa siket, ya maseta d'am hips d'inta sun fito sosai ta kalleta tace kamar kiristiyana? Abinda batasani ba tunda tafara sa kayan salman ke satar kallanta ta gefe, ta tsaya tunanin kayan, batasan sanda salman ya karaso gunba, kanshin turarensa ne yasa ta d'ago, fizge zanin datad'an rufe yai tare da kallanta, yace Woooooo kai beauty kin ganki kuwa? Salma tad'an harareshi tace inafa zan ganni tunda an maidani kiristiyana😞? Salman yasa hannu sai jitai ya d'agata sama, tace prince? Juyi yai da ita sannan ya direta akan gado salma tai murmushi tace my prince? Salman yace umm, tace I am afraid😞 yace for what? Tai shiru can tace ganinake kamar I am too happy ya rungumeta yace bana fad'a miki ki daina wannan tunanin ba? Tace Allah in ina tare dakai mantawa nake da komai, ina tsoron kar farincikin danake ciki ya yanke, kallanta salman yai sannan ya sa hannu a gefen fuskarya ya shafo bakinta,ahankali yakai bakinshi nata, wani salo yake mata itama nan ta shiga maidamai, kan kace me? Duk sun fita hayacinsu, cikin wata murya salma tace i luv u dear, salman cusa kansa a rigarta a hankalI ya zagu mata siket.......nidai kam daga nan nai waje da d'an littafina, kafin salman ya bugo ni da sanda🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻
Ishaq ne zaune a kam kujera ya had'e rai, fulani ta kalleshi tace haba ishaq nice fa? Ya kalleta cikin ko in kula yace nasani ai, tace to naji kayi hakuri, yace nahakura amma in an kiyaue abu biyu, na d'aya kidaina nuna salman ya fini komai, sannan na biyi duk cikin plan d'inmu kar akuskura a tab'amin salmata dan bazan yarda ba ehe, fulani ta tabe baki a ranta tace Allah ya raba bawa da wahala in banda rashin tunani me zakai da matar kaninka? Kanin ma makiyinka? Ishaq ya kalleta yace ke nake jira umma, tace nayarda zan kiyaye duka, mun shirya ai ko? Yai dariya yace yanzu a ina zamu tashi?
................
Nace a inda kuka tsaya🙄😏aikin kawai
By _*AYUSHER MOHD*_📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣8⃣
Bayan sunyi wanka, suka sa kayan bacci suka kwanta, salma ta kwanto jikin salman sannan tace dear ya makarantar? Ya shafa kanta yace lafiya, tace kasanfa ba haka nake nufi ba, tafad'a tare da d'agowa ta kalleshi, salman yaja kumatunta kad'an yace beauty kenan, salma ta kalleshi batai magana ba, salman yai ajiyar zuciya, salma takalleshi tace badai bakai rubutu ko d'aya ba? Inbakai rubutu ba nasan kaji amma ko? yace badai haka za'a dinga min kullum ba ana sani a gaba ana tambaya, salma tai matso da fuskarta tace ah to, tun kafin in gano mijina bashi da kokari gwara ya nunamin, ko in dinga ma lesson? Salman yai wata dariya tare da mikewa ya zauna yace what? Baida kokari? Yimin lesson? Beauty nakula baki sani ba amma sanda nai karatu a paris bana wuce position 1 to 5, har nagama secondary na, zakice me? Salma tasa dariya tare da rufe baki, ganin salman na mata wani kallo, yace meke nan?baki yarda ba? In d'auko miki ki ganine😎?
Salma takara dariya tare da toshe baki tace bafa haka nake nufi ba, ya had'e rai yace me kike nufi to? Ta daure tace nayarda dakai wallahi, kaima kasani ai duk abinda kafad'a ina yarda, na kuma sani basai an fad'amin ba, salman ya kalleta yace dariyar to tameye? Tace yanda kakeyi ne yasani dariya, yace kefa kika faro maganar, harda wani zancen lesson, salma ta gyara zama ta juya baya tare da rungume hannayenta a akirji, salman yace mekuma akai? Salma tace please kamaida hankali akan karatunka, salman ya kwanta tare da jawota, yace nidai abar maganarnan a d'auko wata, salma tace shikenan zan d'aura gobe, yai murmumushi tare da kara rungumeta, haka sukai tad'an fira kasa kasa,bacci me dadi ne yad'aukesu.
Yau watan su salman d'aya da dawowa, salma kullum sai ta tunama salman zancen karatu, duk da yana sharewa amma azahiri yanajin dadin yanda ta damu dashi, basa zuwa ko ina, tana gida, tayi sa'a kwana biyu farha ma bata shigo ba, salma najin dadi sosai rayuwarta da salman, wani irin so takema salman da ita kanta batasan yawanshi ba.
Yauma tana zaune ya gama gyara d'akinsu dan ta hana kowa shigar musu turaka, ta gyara tsaf tai wanka ta d'auko riga da wando ta saka tayi kyau sosai, tai kama gashinta ta gefe, kallan gashinta tai a fili tace ya kamata in wanke kaina, waya ta d'auka tama salman text tanaso taje wanke kai, salman na gama karantawa ya kirata, ta d'aga tare da sakin murmushi, salman yace beauty ni zan kaiki amma ko? Tai murmushi dama haka take so, tace naga kai kana makaranta, yace mun gama ai, yafad'a tare da kallan malamin dake koyarwa, salma da mamaki tace da wuri haka? Yace hakan ne wuri? Tace shikenan in ka gama sai muje ko? Yace ganinan, salman na kashe wayar ya d'an bugama najib littafin dake gabanshi, yace shugaban sa ido, kai karatu da kyau ni zani gun matata, najib yace zan fad'a mata malam na aji kake fita😛, salman yace in ka samu dama kenan, yafad'a tare da fita ta kofar baya ko ajikinsa.
Salma a baya ta d'ora akan kayanta ta nad'a mayafin kayan ta d'auko flat shoe tasa, agoggo ta duba tace ah why am I so excited? Waya ta d'auka tafara game, bata dade ba salman ya mata waya, da kyar tajira tai ringing biyu ta d'auka, salman yace matar salman ki fito, mijinki na jiranki, salma tai murmushi tace mijin salma ya jira matarshi kad'an gatannan fitowa, tafada'a tare da kashe wayar.
Mikewa tai ta rataya karamar jakarta ta saka wayarta da wallet d'inta ta fito, a hankali ta karasa mota tare da bud'e gaba, ta zauna, salman ya kalleta yai murmushi, yace ahhh naji kanshi matata, salma tace kai prince😟 mota ya tada yace amma dai ba direct gun wanke kan zamu bako? Tace can zamu mana, yace ban yarda ba sai na d'an zaga da matata, tace to ina zamu? Yace ba ruwanki.
Sun fita daga gidan daidai nan ishaq yazo shiga, da mamaki ya kalli motar, salma da salman ya kalla suna ma juna murmushi, wani mugun kishi ne ya turnukoshi, har ya shiga ya fito ya bisu.
Salman kam a 212 yai parking ya kalli salma yace muje? Tace me zamuyi? Yace yunwa nakeji, tace ok, fitowa tai suka shiga salman yasa aka sa musu snacks a takeaway sannan yace asa icecream, nan aka had'a musu suka biya.
Ishaq ya kalli shagon haushi ya kamashi, ganinsu yai sun fito da leda suna tafe kana ganinsu kasan sunyi matching da karshe ga wani farin ciki dake zaune a fuskokinsu, ishaq ya cika yai fam.
Mota suka koma sukai can hanyar aminu kano, sai da sukaje gun fly_over sannan salman ya d'an gangara yai parking, bud'e kofa sukai, salman ya kalleta tare da cewa abani abu inci, nan salma ta mikamai chicken pie da lemo, daga d'an nesa kad'an taga wasu masu saida gurji, jitai yawunta ya tsinke ta kalli salman tace prince bari inje can, salman yace ina? Ta nuna mai gun mutanen data gani, yace inkaiki mana? Tace a'a da kafa zani, yace to nan ta fita, ishaq kam ya baya kad'an yana kallansu, ganin salma ta fito yasa yace da alama sunyi fad'a naji dadi.
Salma kam takarasa gun masu gurji, ta siya, taga gyad'a dafafiya nan ma ta siya, har zata taho taga mai gwaza, tace abani gwaza, nan ta sisiya dadi ya kamata ta juyo tana murmushi, salman ganin yanda take murmushi daga nesa yasa ya fito ya tsaya yana kallanta,ishaq ya kallesu wato ba b'atawa sukai ba? Wani kishi ne ya d'ibeshi ya fizgo mota da gudu yai inda salman yake gadan gadan, salma dake tafiya ta kula da yanda motar ta taso, hannu take nuna ma salman ya matsa, shikam ya d'auka ko wani abun take nufi, tace kamatsa, salman yace naki, sai kin karaso, salma kam ganin yanda motar takusa zuwa inda salman yake yasa ta taho da gudu tare da jefar da ledojin salman ya kalleta ganin yanda take gudu a titi ya kalleta yace beauty? Ishaq yakarajin wani kishi lalai yau zai karasa salman, Kafin salman ya kara wani magana salma ta karaso haka motar ma, salma ta rukeshi sukai gefe, sai dai duk da haka sai da motar ta bige salma.
Ishaq baisan abinda salma take kokarinyi kenan ba, ganin ya bige salma yasa yai parking ya fito da sauri,salman kam suman tsaye yai jiyake kanshi na wainawa, salma ya kalla dake kwance a sume, ga goshinta ya fashe yana zubar da jini, masu gurji ne suka karaso gun ishaq ma haka, salman sai kallan kowa yake amma baisan meke faruwa ba jiyake kamar bashiba, ishaq ya karaso tare da kallan salma idansa ya ciciko, salman ya jijiga sai dai yakula salman baya hayacinsa, yace kai bakaga yanda salma take bane? Dalla malam.....gani yai salman ya rike kirjinsa da kansa wani irin kurkusus yakeyi, mai gurji tace ka kaisu asibiti mana, kar a samu matsala, ai kai kaja, kuna tafiya bakwa kula dana gefen titi? Ishaq ya kalli salma da sauri yasata a mota, masu gurji sukace saura shi, salman sai murkususu yake, nan wani mai rake ya karaso ya taimakamai aka saau amota, asibitin aminu kano yai dasu, shikanshi hawaye yake baiyi zatan abin zaikai haka ba yanzu ga salmarsa itace ba lafiya.
Suna zuwa Aminu kano, akai emergency dasu, salman kam ya fita hanyacinsa dan ba maganinsa, likitocin sun dukufa akansu, ishaq kam kuka yake ya daure ya kira waziri ya fad'amai, sarki kam yanaji jiyai kamar yasa kuka,yana tsananin san salman in wani abun ya same shi yazaiyi?
By *Ayusher Mohd* 📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.4⃣9⃣
Waziri ya kalli sarki yace "bari inje asibitin".
Sarki yace "kana nufin barina zakai anan? Bayan salman da matarsa na asibiti? Wayasan awani hali suke? Waziri yace amma kaga kai bai kamata.....
Sarki yakatseshi da cewa "yanzu kaje ka gunsu, nikuma sai ka sanar dani halin da ake ciki da daddare sai inje dakaina".
Waziri ya amsa sannan ya fita.
Likitoci sun dukufa akan salman da shine ke jin jiki, salma bayan an mata dressing, sai jini da suke tunanin za'a kara mata.
Salman kam sunyi mamakin yanda ya hari ciwo ya kamashi haka, da akamu abin ya dade, da kyar suka shawo kan lamarin kafin su turosu sukaisu d'aki d'aya, dukansu bacci sukeyi sakamakon allurar da aka musu.
Ishaq kam duk ya rikece yana ganin waziri yai gunsa da sauri.
Waziri ya kalleshi yace " ishaq ina salman da matarsa?, ya jikin nasu? Abindai ba babba bane ba ko?"
Ishaq ya rike hannun Waziri yace "Waziri wad'annan tambayoyin sun min yawa, wane kakeso in amsa?"yai maganar tare da zubo da kwalla.
Waziri ya ja hannunshi ya zaunar dashi sannan yace "bari inga likita, dama ba kai yakamata intambaya ba, yahkuri yarima mai jiran gado."
Waziri ya sakeshi yai gun likita,knocking yai daga cikin aka amsa shigo, Waziri ya murd'a kofar tare da shiga da sallama.
Likitan na ganinshi ya mike tare da gaisuwa, waziri ya amsa tare da zama, likitan ya kalleshi tare da zama shima.
Waziri yace " nazo ne inji halin da d'an mu da matarsa suke ciki",
Likita ya mike yace "badai wanda aka kawo da matarsa kake nufi ba? ".
Waziri yace "eh salman da matarsa salma", likita yai shiru can yace " wanda yakawosu bai fad'amana ba hannu kawai yasa akan aiki, sannan a zahiri nayi mamakin yanda akai kuka bari yarima salman d'in ya kamu da heart attack,"
Waziri cikin kid'ima yace "what? Heart attack? Likita ban gane ba?".
Likita yai ajiyar zuciya yace " ka kwantar da hankalinka, ai salman yaro ne dama shi wannan ciwon yana wahalar warkewa ne ga wad'anda suka girma, to Alhamdulila salman yaro ne, saboda haka karku damu, akwai treatment daza'amai sai dai ba'anan ba."
Waziri yace " bangane ba anan ba?"
Likita yace " akwai wani babban likitanmu *DR BILAL*( mijin ilham tsohon littafina), yana zaune a kasar england to ya sanar mana zai dawo nan da wata d'aya, likitane kwararre dan kwarewarshi ce tasa suka rikeshi, inhar yadawo sai aka salman ya dubashi sai yasan meya kamata amai."
Waziri yai ajiyar zuciya yace "to Alhamdulila, salma fa?"
Likita yai murmushi yace wannan ba matsala kanta ne yabugu sai jini data zubar, munason kara mata jini."
Waziri yace " Alhamdulila"
Likita ya sake murmushi yace "amma tana d'auke da juna biyu na wata 1."
Waziri ya saki fara'a shima yace "kai masha Allah, ta farfado ne?"
Likitan yace "eh to yaci ace sun farfado yanzu, muje indubasu a canza musu d'aki,"
Waziri yace to yafad'a tare da mikewa sukai hanyar d'akin da aka kwamtar dasu Salman, Ishaq ma na ganinsu ya biyosu.
Sun shiga sun tadda Salman a zaune rike da hannun salman, idanunsa taf kwalla, Waziri na ganinshi yakarasa da sauri ya dafa Salman.
Salman ya juyo ya kalleshi ya kuma kasa magana, hawayen dake kwance a idanunsa ne suka zubo, mamaki ya kama Waziri tunda yake yau ce rana ta farko dayaga hawayen Salman bashiba hatta Ishaq.
Likitan ya kalli Salman yace ranka ya dade kwanta in dubaka, Salman ya kalleshi yace " ni lafiyata kalau ga wacce nake so inji me kuka mata da ya hanata farkawa?"
Likitan ya karaso kusa da Salma ya shiga dubata, ya d'ago yace "lafiyarta kalau komai nata normal, bansan me ya hanata farkawa ba,"
Salman ya mike yamai wani kallo yace "baka sani ba?"
Likitan yace "zata farfado nan acikin nan da 24hrs in bata farfado ba kafin nan zamu sake running d'in test."
Salman ya zuciya yayo kan likitan Waziri ya tareshi da sauri yace "Salman ka nutsu mana, Salma juna biyu gareta bai kamata a d'inga hayaniya haka ba."
Salman yace "me? Juna biyu? Likita da gaskene?" Salman duk ya rikice, Ishaq wani kishi ya kamashi juyawa yai ya fita da sauri.
Salman yabi Ishaq da kallo, sai dai yau farinciki yasa bashi da lokacinsa amma alkawarine dole ya koyamai hankali.
Salman komawa yai kusa da Salma ya kamo hannunta bakinshi yaki rufuwa yace " Beauty ki tashi please, ki tashi mu kula da Babyn mu, Beauty ki tashi please.....
By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO. 5⃣0⃣
Waziri da likita ganin yanda Salman yake kallan Salma yasa suka fita daga d'akin tare da jawo kofa.
Salman ya kurama Salma ido a hankali yakai hannunsa kan inda aka sa mata plaster ya shafa gun, jiyai jiri nad'an kamashi daga zaune, sauri yai ya kwantar da kansa akan pillow d'in datake, kansa kusa da nata, hannunta ya rike kam.
Tunani yafara yi, wato ishaq shi yaso bigewa?Baiwar Allah azal yafad'a mata, sashi akai? Abinda yafad'omai kenan aransa, yanzu da sun mai asarar cikinsa fa? idansa ne ya kad'a yai ja, a mike zaune ya kalli Salma yace
" I won't forgive them,duk wanda keda hannu a cikin wallahi I won't let them be."
Ishaq kam gida ya wuce cikin b'acin rai yai b'angaren fulani.
Tana zaune acikin kilisa, hankalinta akwance, sai ma farin ciki da take wai ance salman na asibiti da matarsa, itakam jitake ina ma su mutu ko ta huta da ganinsu.
Ishaq ne yai sallama ya shigo da sauri, fulani ta kalleshi tace " yanzu nake nemanka ka tayani murna, Allah ya saukaka mana komai."
Ishaq ya zauna rai a b'ace yace " wani sauki koma? Banda tashin hankalin danake ciki?"
Fulani tace " wani bakin ciki bayan Salma da Salman na asibiti."
Ishaq yai tsaki yace "Umma nikam kibar wannan zancen, ni fa kishi ya ciwoni naso makeshi, amma Salma ta kare shi."
Fulani ta mike tsaye cikin kid'ima tace "mene? Ishaq kasan me kake fad'a kuwa? Ishaq bangane kai kaje make Salman ba."
Ishaq ya share zufa data ketomai yace " bama wannan ba Umma, Salman ya ganni yasan ninai."
Fulani tashiga tafa hannu tace "shikenan na shiga uku, Ishaq yanzu yazamuyi? Me yakaika? Nafad'amaka kad'inga tunani da hankalinka."
Ishaq yace "ni dan Allah Umma kidaina min wannan zancen abinda ke damuna ma ya isheni."
Fulani ta zabura yace "meke damunka? Akwai abinda zai dameka daya wuce wannan?."
Ishaq ma ya mike rai a b'ace yace "haba umma ya kikeso inyi da raina? Ina kallo yanzu Salma zata haifi d'an Salman?"
Cikin mamaki fulani ta kalleshi sai kuma ta had'e rai tace "da kanaso ne Salman d'in yasata agaba yai ta kallo ko me?"
Ishaq yace "ba ciki ne da Salma ba ko 'ya'ya d'ari gareta nidai ina santa bakuma abinda yadameni da wani Salman ko wani da zai kawomin matsala."
Fulani data rikece jin kalamansa tace "me kace? Ciki? Ishaq me kake nufi?"
Ishaq yace "ciki ne da salma yanzu aka fad'a a asibiti, menene?, kema kina tayani kishi ko?"
Fulani ta harzuka tace dalla gafara banza, shashasha, Salma nada ciki inta haifi namiji fa? Kai matanka biyi 'ya'yanka hudu amma duk mata, shine maimakon kai tunanin abin da zai faru gaba shine kakemin zancan wata banzar soyayyarka?"
Sai a lokacin ishaq yai shiru, yanzu in bai haifi namiji ba fa? Kenan za'a iya bashi mulki daga baya aba d'an salman, yazaiyi? Yanda ya tsani Salman d'in nan."
Fulani tazauna tare da dafe kai tace "yau nikam da wani hannu na tashi? Wannan bakin ciki kala_kala?"
Farha ce ta fito da sauri ta kalli Fulani tace " zanje asibiti ance Yayana bashida lafiya," Ishaq yai tsaki yace to salman ya ware, sai dai in Salma zakije ki dubo daganan sai ki tayashi murna tunda sun samu karuwa."
Farha takaraso tace "bangane ba? Karuwa kamar me?"
Ishaq yace "ciki gareta."
Farha tace "mene? Ciki? Bangane ciki ba?."
Fulani dake rike dakai tace " Farha yaz'amuyi Salma dai ciki gareta."
Farha ta zube agun ta d'aura hannu akai ta sa ihu tace " ciki? Shikenan nasan yaya Salman bazai kulani ba, Amma wannan Salmar akwai yar iska."
Nace ko kuma ku ba.....
Salmah kam tana kwance itakam rayuwa mai dadi take acikin baccinta, yau taga fuskar saurayin nan Salman ne suna zaune a bakin ruwa, ta kwanta akan cinyarsa shikuma yana rike da littafin story book yana karanta mata, sosai takejin dadin labarin sai lumshe ido take, Salman ya kalleta yai murmushi sannan ya rufo gefen fuskarta da littafin hannunsa, yakai bakinshi kan lebenta ya sumbata, ido ta rufe cikin murya kasa_kasa tace "in aka ganmu fa?"
Salman yace "menene aciki? Keba matata bace?"
Murmushi sukai ta kalleshi tace "ka cigaba," tai maganar cikin shagwaba nan ya cigaba da karatun.
Sarki yau farin ciki ba'a magana zuciyarshi kamar ta faso, sai dai yana tsakiyar murnar yin jika dazaiyi ta tsatson Salman waziri ya nisa yace "amma akwai wata 'yar matsala, Salman nafama da wani ciwo."
Cikin tsoro Sarki yace "ciwo? Wani iri kenan?"
Waziri yace "yarima Salman na fama da ciwon heart attack."
Cikin rud'ewa Sarki yace "heart attack? Kasan mai kake cewa kuwa waziri?"
Waziri ya tsugunna yace " tuba nake ranka ya dade."
Sarki ya rike kansa, yama kasa magana.
Waziri yace "amma akwai likita, ance inyazo insha Allahu da yardar Allah Salman zai warke."
Sarki yai shiru can yace " waziri kasani yaron nan kaf cikin 'ya'yana ba wanda nakejinshi har cikin jikina irinsa, in wani abun ya sameshi bansan yazanyi ba, da alama ciwonsa ma nine sila."
Waziri yace "ya kake fad'an haka ranka ya dade? Kaine sila?ciwo ne dai daga Allah."
Sarki yace "nasani ciwo me daga Allah amma nasan bakin cikin daya kunsa yana yaro shiya jamai wannan ciwo."
Waziri nan ya shiga bashi baki, sai dai Sarki jinsa kawai yake, can yace "naji waziri yanzu ana isha'I kazo ka kaini inga halin dasuke ciki, waye agunsu?"
Waziri yace "na kira zeenatu tace tana hanya."
Salman ne ya kallin likitan dayazo duba Salma yace "yanaga bata farka ba?"
Likitan yace "karka damu kila itama tanajin dadin rayuwar da takeyi ne acikin baccin, amma zata farka nan bada dadewa ba."
Salman ya kalli Salma cikin tsananin tausayi.
Likita yace "amma ina tunanin za'a kara mata jini kad'an." Salman ya kalleshi yace "akara mata nawa ko leda nawa ne dan kuwa O+ gareni bana tunanin akwai matsala."
Likita yai shiru can yace "amma ina ga kai da bakada lafiya bai kamata aragema jini ba."
Salman yace "jikinka ne ko nawa? Ko kuwa inwani abun yasameta zakai d'au responsibility?"
Likita ya had'iyi yawo yace "a'a ayi hakuri yarima, bansan kalmar zata b'atama raiba."
Salman yamaida idansa kan Salma tare da riko hannunta cikin zuciyarsa yace " Beauty please"
Tunowa yai yakamata ya kira Abban ta, to karkuma ya tada musu hankali, ajiyar zuciya yai yace "Beauty yazanyi?
By *AYUSHER MOHD*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.5⃣1⃣
Zeena tazo sai dai duk yanda ta roki Salman akan yaci abinci amma yaki, tai fad'an har ta gaji, shikam yama dags akan ta rakashi agwada jininsa su tabbatar zai iya bata, a d'eba asa mata.
Zeena ta kalleshi tace " haba Salman mai yasa kake haka? Kabari gobe in an kira 'yan uwanta sunzo sai a gwadaso asamu wanda yai a kara mata, amma kai baka da lafiya ina kai ina bada jini? Sannan gashi sam kakicin abinci."
Salman ya kalleta yace " Aunty zeena har dake? Nad'auka ke ba halinku d'aya dasu ba, taya zakice gobe in 'yan uwanta sunzo, Salma matatace kuma saboda wani abun dabai gagareni ba bazan nuna mata nafisan kaina akanta ba, abinci kuma inkinga naci abinci to tabbas naga matata taci." Yanakai nan ya fita, Zeena tausayinsa ya kamata, wani irin so Salman kema Salma haka? A da taga ko kallo bata isheshi ba, yaushe abu ya juya haka?.
Salman da kanshi yaje lab d'in suka gwadashi sun tabbatar O+ gareshi kuma zai iya bata, wucewa yai gun likita yace "tashi muje ko?"
Likitan yace "Yarima dan Allah....."
Cikin fad'a Salman ya katseshi yace "Karka bata min rai, inace inason abu to kamin kafin ranka ya b'aci, nagaji da ganin matata a kwance."
Likitan yace "kayi hakuri ranka ya dade amma matarka badan jini bane taki tashi."
Salman yace " Naji, amma wuce muje inka kara mata jinin sai nu jira in ta wuce hours d'in daka fad'a hmm bansan kuma mai zan ma ba."
Salman ya juya, da sauri likitan ya fito sukai shigo da kayan aiki d'akin, an saita komai sai da ba'a fara ba mai martaba ya iso shida waziri.
Salman na ganinshi ya had'iyi wani abu tare da kara d'aure fuska, Sarki ya karaso kusa dashi, waziri ya kalli Zeena dake gaida Sarki yace inkin gama kowa ya fito yabasu guri, tace to.
Kowa ya fita yabarsu su biyu sai Salma dake kwance, Sarki ya kamo hannun Salman ya rike yace "Salman na tsorata danaji ance bakada lafiya na d'auka kaima rasaka zanyi."
Salman ya kalleshi idanshi yai jaa, dasauri ya maida kanshi gefen da Salma take, Sarki yace " Salman meyasa baka sanar dani larurarka ba? Ina zaune bansan halin da d'ana yake ciki ba."
Salman ya kalleshi yace " Ina zaka sani Abba? Tunda mukamin ka yafini daraja? Tunda kake dani ka taba tambaya ta yana tashi? Meke damuna? Naci abinci? Bani da wata matsala dake damuna?"hawaye ya zuboma Salman a ido yacigaba" Kun rufe mutuwar Ummana saboda san mulki, kun turani wata kasar dan bazaku iya kula dani ba, sannan yanzu Abba katambayeni wai zancen ciwo na? Ban fad'ama ba?"
Ya share hawayen dake zubo masa yace " kasan wace irin rayuwa nayi? Kai dai kullum kana zaune akan kujerar mulki sai abinda aka fad'ama."
Salman na zuwa nan ya runtse ido, hawaye suka kara zubomai ya share tare da kallan Salma, yace "zan iya jure komai amma banda a tab'a matata."
Sarki da tunda Salman yafara magana kwalla ta cika taf a idanunsa yasani sarai abinda Salman ya fad'a duk gaskiya ne, amma ya zaiyi? Tunda haka mulki ya gada.
Kafad'ar Salman ya dafa, ya d'ago ya kalleshi cikin tsananin tausayin d'an yace Salman na sani duk wani abu dake damunka laifinane na sani amma dan Allah Salman ka cirema zuciyarka komai ko ka samu nutsuwa, kaduba matarka, ciki gareta ka taimakeni Salman ka cire komai aranka kafin d'anka ya taso da kiyayyata, Salman kayi hakuri akan duk abubuwan dana maka, nasani sarai abin na damunka amma zuciyata inta ganka sai inji tausayinka bazai bari in tada maganar ba."
Salman ya kalleshi yace " So nake ka bani izini ind'au matata in bar gidan, dan banasan zama a cikin gidan, nafisan inda zamuyi rayuwa kamar kowa nida abinda za'a haifarmin."
Sarki ya kalleshi tare da jijiga kai, yace Salman banda wannan, zan iyama komai Salman amma bazan iya barinka nesa dani ba, bayan kaine magaji na."
Salman yace "magaji? Magajin me fa?"
Sarki yace "mubar maganan nan Salman dan Allah."
Salman yace " Abba?"
Sarki ta rike hannun Salman yace "Salman kayi hakuri ka yafema wannan mahaifin naka, yasani yamaka laifufuka da dama, amma ka sani kullum kana ranshi dai dai da minti 1 bai tab'a mantawa dakai ba."
Salman hawate suka kara zubomai, yana tsananin san mahaifinsa yazaiyi? Idansa ya runtse baice komai ba, Sarki yai shiru can yace "ance hatsarine, bakasan waye mai wannan d'anyen aikin ba?"
Salma ya tuno sanda yaga Ishaq amma sai ya daure yace "ban ganshi ba sai dai koma waye I won't forgive them."
Sarki yace "ko ni, sai dai in a rashin sani ne amma in har wanda yai da saninsa ne to bazan yafemai ba ko waye kuwa, I promise you this."
Salman yace "Abba karkai Alkawarin dabazaka cika ba."
Sarki ya dafashi yace "Salman kenan, ai sarki na gari baya magana biyu, amma nikam Salma taji jikine? Naga bata farfado ba?"
Salman yace" nima bansani ba wlh, yanzu dai jini za'a kara mata sai mu jira nan da wasu awanni kad'an mugani."
Sarki yace "da alama d'ana ne zai bada jini?"
Salman yai kasa dakai tare da sosa keya.
Sarki yai murmushi yace "naji dadi Salman da yawancin halayenka irin nawa ne, kasan me?"
Salman ya girgiza kai Sarki yai kasa da murya yace" Sanda inasan ummanka banajin komai, ganinake komai zan iyayi saboda san da nake mata."
Atare suka kwashe da dariya, waziri da zeena da sauran fadawan dake waje suka kalli juna cikin tsananin mamaki, duk cikinsu ba wanda yataba jin dariyar sarki haka, ko salman d'in ma.
Bayan sun tsagaita, sarki ya rungumo Salman yace karka damu d'ana Salma zata warke sumul kamar ba ita ta bige ba, Salman yai murmushi, wani irin farinciki ke ratsatsu, daga Salman har Sarkin.
A gaban Sarkin aka kira likitan ya juna kayan aiki nan aka fara karin jini, Sarki ya shafa kan Salman ya fita.
Hmmmm tsakanin 'Da da mahaifi sai Allah
......
By *[truncated by WhatsApp]
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
NO.5⃣2⃣
An gama karama Salma jini Salman ya mike da kyar dan jiri yakeji, kusa da ita ya zauna tare da riko hannunta, zeena kam jikinta yai sanyi, tana mamakin tsananin san da Salman kema Salma.
Salman na zaune har barci yafara d'aukansa hakan yasa ya kwantar dakansa kusa da ita, ahankali bacci yai gaba dashi, Salma sai datakai wajen karfe 3, alokacinma mafarki take, wai Salman sunyi fad'a ya juya zai tafi tabishi da gudu tana kira, sai dai kafin ta karaso ya b'ace mata, a firgice ta mike tace *PRINCE*cikin wata murya, dukansu sai da suka tashi zeena, Salman ya kankame hannunta yace" Naam beauty ganinan."
Bata kula da kowa ba kawai rungumeshi tau kam tana hawaye, shima hawayen ne ya zubomai, a hankali ya nemi ya d'agota amma ina....kara k'ankameshi tai, Salman yai ajiyar zuciya yashiga shafa bayanta.
Zeena kam tayi mutuwar zaune tana mamaki itakam bata tab'a ganin masu san juna irin haka ba.
Salma ta dade ajikin Salman kafin ta d'ago, ahankalita tab'a fuskarshi,sai alokacin abinda yafaru ya dawo mata, a hankali tace "ba abinda ya sameka? Salman ya shafa kanta yace "ba abinda yasameni sai tsoron abinda yasami matata."
Salma ta share kwalla, tare da tab'a kanta datajishi a d'aure, jin plaster yasa ta d'aure tace "na d'auka zan rasaka."
Salman yai shiru, ishaq ne ya fad'o mai arai, sai kuma ya share, tare da kamo hannunta yace abinci fa? Tace zanci, mikewa yai sai alokacin yaga zeena, ya sosa keya, itama Salma sai alokacin ta ganta, dasauri ta koma ta kwanta, ta rufe fuska, zeena tace " a'a love birds bansan wani salo, angama fitsara agabana sai kuma ashiga rufe ido?"
Salman yace "kema yaya zeena da kika ga haka sai ki koma ki kwanta."
Tace "au to ayi hakuri na koma bacci."
Tafad'a tare da kwanciya.
Dakanshi ya zubo mata abinci ya sa spoon ya matso kusa da ita, Salma ta mike a hankali tare da kallan agoggo, ta kalli Salman tace "wai ukun darene tai?"
Salman yace "eh mana duk kin gama tsoratani, ganin baki farka ba."
Tace " Yahkuri."
Yace "ci abinci dai tukunna."
Da kanshi ya shiga bata, tayi spoon biyu ta kalleshi tace" kaima nasan bakaci komai ba, sai dai muci tare."
Zaiyi magana tace "please"
Yai murmushi yace ok.
Tare sukaci, sai da suka koshi sannan ya bata ruwa tasha, ta kalleshi tace "prince mud'anfita?" Kai ya d'aga mata tare da taimaka mata ta mike.
Suna bude kofa yaga fadawa da sauri ta koma tace mun fasa, Salman ya kalleta yace "meyasa"
Komawa ciki tai tare da zama a kan carpet d'in dakin, Salman ya d'auko bargon dake kan gadon ya karaso kusa da ita ya zauna tare da rufa musu bargon, Salma ta kwanto da kanta kafad'arsa tare da zura hannunta jikin hannunsa.
Salman ya sa d'ayan hannunsa kan cikinta yace "babyna dafatan kana cikin koshin lafiya."
Salma ta kalleshi da mamaki tace " baby?, wa kenan, badai suna aka canzamin ba?"
Salman yai murmushi yace "babyna mana dake jikinki, wai ya akai baki sani ba?"
Salma ta d'aga kanta daga kansa tace" naam?" Salman ya d'aga mata gira, tace "muga wayarka?"
Nan Salman ya mika mata ta amsa tare da duba date, Dagaske ta wuce kwanankin period d'inta da 9 days, amma ya akai bata sani ba? Kallan Salman tai cikin farin ciki tare da shafa cikinta, ko shiyasa kwananan sai tai tajin kwad'ayi?.
Salman ya maido da kanta inda yake tare da cewa Beauty kiyi Sauri ki warke mu kula da babynmu, Salma ta d'ago da d'an karfi, jin kanta yad'an amsa tace ahhh.
Salman da sauri ya kalleta yace "beauty?menene? Zafi?"
Salma tai murmushi tace kan nawa ne sai injishi a d'ad'aure bansaba ba yace " haka ne ai, sannu, amma beauty da kika ture ni aka bige ki kinsan me kikai kuwa? Kina tunanin zanso wani abu ya sameki akaina?"
Salma ta maida kanta tace " ni alokacin gaba d'aya kaina ya kulle tsoro na d'aya kar wani abu ya sameka." Kwalla ta cika idanta tace " namanta da jikina, ni kawai kai nake gani."
Salman yai shiru, tare da lumshe ido, Salma jin haka tace "kasan mafarkin danai? "
Salman yad'ago ya kalleta, tace bazan fad'ama ba siri ne.
Yai murmushi yace in ansan siri ne ai ba sai an min zancen ba dan a samin san jin labarin.
Salma ta kara gyara kanta tare da rufe idanta, Salman shima ya rufe nasa idan, bacci ne ya d'aukeshi, a hankali Salma ta mike tare da wucewa toilet tai alwala, Sallah tazo ta tada ta rama salolin da ake binta.
Da safe zeena dakanta taje gun likita tace ya kamata a sallamesu dan da akama bazasu iya zaman asibiti ba, likitan yace to amma sai zuwa yanma tace to, sannan ta koma ta sanar musu.
Salman kam ba kunya dadi yaji.
Wajen karfe 9, Farha ta taho damai kawo abinci, tsoron shiga takeyi hakan yasa tace masu kaiwar su shiga dashi, ita kuma ta tsaya ajikin window tana kallan Salman dake zaune kusa da Salma, wani abu ta had'iya idanunta suka kad'a, kamar wasa Salman ya kalli window, Farha ya gani tayi tsuru, murmushi ya mata sannan ya mata alama da hannu akan tazo, Salma ta kalleshi tare da had'e rai, Salman yai kamar bai ganta ba.
Farha na shigowa jiki a sanyaye ta d'an tsaya daga nesa yace "kanwata matso mana."
Farha ta d'ago ta kalleshi cikin mamaki, Salma ma kallan mamaki take mai, Farha ta matso kusa tare da gaidashi ya amsa fuska a sake yace" meye na tsayawa acan." Tace "uhm yaya dama ai..."
Ya katseta yace " inkinzo neman lada ki nema da kyau" ahankali tace to.
Sannan ta kalli Salma dake kallanta rai a b'ace tace "in_law sannu da jiki"
Salma tace "yauwa"fuska a d'aure, farha tad'an dade kad'an kafin tace "bari in tafi yayana." Salman ya kalleta yace "to Farha nagode" murmushi tai tace "nice da godiya yayana."
Nan ta juya tai waje, Salma ta bita da harara tace "daka bita ai" Salman yace "ko?to in na batta ke kuma fa?."
Haushi ya kamata tace "ai bakaikad'ai bane a guna."
Ga mamakinta gani tai Salman ya mike, yai waje, ta kalleshi cikin tsananin mamaki, menene hakan?
Salman kam yana fita ya had'e rai tare da bin inda Farha tai, tana tsaye a jikin wata bishiya, tana waya, a hankali ya karasa inda take, jiyai a wayar tace "wlh yaya bai nunamin komai ba" bai ji me akaceba yadaiji tace " yama za'ayi ace Salma keda ciki bayan ni ya kamata infara haifar mai d'a? Fulani Nifa na tsani Salmar nan, kyau kamar aljanna."
Salman ya kalleta cikin tsananin b'acin rai, ga mamakina sai gani nai ya dawo ta gabanta da murmushi yace na fito miki rakiya ashe kina nan? Tsoro ya kamata ta kalleshi tare da yarda wayarta, Salman yace "ahhh Clumsy girl, yazaki yarda wayarki?"
Dasauri tad'auka tare da kashe wayar.
Salman yace "da alama rakiyar bazata yiwuba bari na koma gun beauty."
Farha da sauri tace "a'a inaso yayana"
Salman yai wani murmushi yace "muje to, ina kikai parking?"
A hankali ta nuna mai inda motarta take, dakanshi ya rakata sai daya tsaya ta ja tai gaba, sannan yabi motar da kallo yace " one by one ni zan koya muku hankali."
Farha kam farin ciki tad'inga jin jitake kamar tai ihu dan dadi.
Salma kam ta cika tai fam........
Nace to fa!!! Kowa da abinda ke ransa....lol
By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
*This Page Is Dedicated To My Besty DizzyHrt😍😘*
No. 5⃣3⃣
Salman ya koma d'akin inda ya tadda Salma a kwance, Zeena ya kalla yace bacci tai? Yafad'a tare da kallan Salma, Zeena "tace Na fito daga wanka naganta akwance maybe baccine ya d'auketa."
Salman ya zauna a kusa da ita tare da kallanta, idanunta a rufe suke tanaji zeena tace bari taje waje zatai waya.
Salman na gani ta fita ya matso daf da ita tare da sako fuskarshi daf da tata, yakai bakinshi gefen kunnenta yace "beauty nasan fa ba bacci kike ba"
Salma ta shareshi, bakinsa yakai inda akasa mata plaster ya sumbata, salma a hankali ta bud'e idanunta, ta kalleshi.
Salman ya d'ago idanunsa suka had'a ido, tace "har ka dawo?" Yace "Beauty ba inda ke miki ciwo dai ko?" Salma ta kalleshi har zatai magana ta fasa, can tace " ka fad'ama su Abba ne?" Salman yace " tun jiya nakesan sanar musu amma ina tsoron kar hankalinsu ya tashi." Tace "gwara da baka fad'aba dama banaso susani, hankali Abba tashi zaiyi."
Da yamma hajiya karama da kanta tazo ta taho dasu Salman, ba shiri suke ba hakan yasa daga gaisuwa da dubasu ba abinda yakara had'asu har suka isa.
Salman suna shiga ya kalli Salma yace "ina zuwa dear," Salma tace to.
Bangaren Fulani ya nufa, yana shiga ya wuce kilisarta, tana zaune itada Ishaq abin duniya ya damesu, jin sallamar Salman yasa suka kara shan jinin jikinsu, Salman ya shiga tare da neman guri ya zauna.
Cikin murmushinsa dabazaka tab'a gane me yake nufi ba yace" Umma tunda ke kin kasa zuwa dubo d'anki shi gashi yazo da kansa."
Fulani ta shiga in in na tace " Salman ba haka bane yanzu nake shirin fita, amma nikam ya akai hakan tafaru?" Tafad'a dan tabbatar da Salman yaga Ishaq
Salman ya kalleta yace " Hmmm to Nikaina bazance ga abinda yafaru ba, amma nikam kamar kana gun ko?" Yafad'a tare da nuna Ishaq, kan kace me? Ishaq ya rikice, jikinshi yafara rawa.
Salman yai wani murmushi yace " to ko ba kaina gani ba? Sai naga kamar kai ka taimakemu ka kaimu asibiti?"
Fulani jin haka yasa tai saurin cewa " shine mana, kasan halin Ishaq da rud'ewa, ya firgita ne ganin halin da kuka shiga."
Salman yace " ohhhh naga alama, nikam ina Farha?"
Fulani tace "tana d'akinta, hankalinta ya tashi dataji halin da kake ciki"
Salman yace "nasani ai." Yafad'a tare da mikewa, har yakai kofa yaji Fulani tace "Amma naji kamar ance kanada wani ciwo? Mai wuyar warkewa?"
Salman ya tsaya cak, tare da cizen leb'e, ya juyo inda suke ya saki murmushi yace " ba wani ciwo, kawai ganin matata tashiga wani yanayi ne yasa nima na shiga, ya akai? Kin shiga wani haline jin banida lafiya?"
Fulani tad'an tab'e baki tace "sosai ma, Alhamdulila da abun ba serious bane."
Salman ya juya batare daya mata magana ba.
D'akin farha ya isa tare da knocking, ta budemai, sai dai ganin Salman ya sa ta saki baki, Salman ya karasa d'akin yana cewa "to ko ba'ayi farin cikin ganina bane?"
Farha ta juya ciki da sauri tace "yayana, kaine?"
Yace "me? Bakiyi farin cikin ganina bane?"
Tace "inafa!!! Farin ciki yaimun yawa dai."
Salman ya karasa jikin madubi inda take yaga takardu, ya d'aga tare da cewa "badai anan kike ajiye passport d'inki ba?"
Farha tace a'a takarasa cikin jakarta tare da cirowa tace "ka ganshi nan"
Salman ya karasa ya ansa yace " banyarda adinga ajiyeshi a jaka ba, dan haka nizan ajiye miki daga yau."
Farha ta rufe ido tace " jinake kamar ka zama mijina yayana"
Salman ya buga mata wani kallo sannan ya karaso daf da ita, yace "lokacine ai."
Farha kam kamewa tai a tsaye har Salman ya fita bata sani ba, Salman na fita ya d'aga wayarsa ya kira wani friend d'insa, yace " zan kawo maka passport d'in gobe, please as soon as possible nakeso."
Ya kashe wayar tare da sakin wani murmushi, yace bazan bari ki kara canza hali ba anan garin.
Salma kam d'akinsu ta shiga gyarawa, Salman ya bud'e kofar, tana tsaye jikin gado ta juyo ta kalleshi, Salman ya karaso tare da bud'e mata hannu, murmushi tai, takaraso ta shige jikinsa, riketa yai tsam yace beauty kamar munyi wata bama d'akin ko? Tad'aga kai, yace "ahhh naji dad'in ganin mu, mu biyu, Salman ta kara shigewa jikinsa, rikota yai ya zaunar da ita kan gado, tare da mikarmata da kafarta, yace "ki d'inga zama kina hutawa sosai, karki d'inga wahalarmin da babyna."
Salma ta rangwad'ar da kai tace "Prince gyaran d'akin ma wahala ne?" Yace "eh mana."
Tace " to ai sai jikina yai tsami in haka ne."
Mikewa yai ya zauna a bayanta sannan ya kwanto ta jikinsa, yace "Beauty?" Tace "naam."
Yace " nikad'ai nasan farin cikin danake ciki."
Tace "ummm to in haka ne abani gift"
Yace "toh!! me Beauty na takeso?"
Ta juya kanta tace " exams dazakuyi this year, karka m'ika farar takarda."
Salman ya sakar mata murmushi yace "daga sanda naji kina da ciki, na d'au wannan alkwarin, bazan bari d'ana yataso yaganni coward ba."
Salma ta kai bakinta zata sumbaci kuncinsa, matsowa yai hakan yasa bakinta ya shiga nashi, tad'an d'ago ta kalleshi, hannu yasa a gefen fuskarta yakara jawota kad'an, shima ya matso, tare dakai bakinshi cikin nata, sun shagala sosai, salo suke ma juna, dukansu idanunsu a rufe, sun dade kafin su saki juna, a hankali Suka bud'e idanunsu, Salman ya had'a gushinsa danata, suka saki murmushi, tace thanks dear.........murmushi ya sake mata.
A ranta tace Allah nagode maka daka had'ani da wannan bawa naka.
Farha kam tsalle ta daka, jitake kamar ranar auransu ta zo, waya ta d'aga takira mumynta, tace "mumy bana tunanin zan dawo yanzu, maybe ma kune zaku taho, bani ba."
Mumyn tace " bangane ba"
Farha tace " kedai bari mumy, burina ya kusa cika."tafad'a tare da kashe wayar, tace "hmm wayaga idanun Salma?"
Lol.....nace har na hango....
By *Ayusher Mohd*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No.5⃣4⃣
Salman yashirya tsaf, Salma dakanta ta d'aukomai kaya ya saka, suka fito dinning Salma ta zauna ta zubamai abinci, Salman ya kalleta yace "yauma nikad'ai zanci?" Tace "a'a tarw zamuci" yai murmushi tare da kallan su hanne, ya musu alama da hannu su fita, nan sukai baya suka fita.
Salma ta sa spoon suka faracin abincin, Salman sai kallanta yake yana murmushi, suna gamawa ta d'auko mai littafinshi da mik'amai, yace "thanks dear" tace "Allah ya bada sa'a."
Salman ya mata kiss a kumatu sannan yai waje.
Direct school ya wuce, a hanya yama Najib waya yace "nashigo, ka karaso?" Najib yace " yanzu na shigo kana ina? Naji kace akwai magana."
Salman yace mu had'u a inda muka saba zama, ya kashe wayae tare da karasawa.
Sun had'u su uku da Amir, Salman ya kallesu sannan ya kalli agoggo yace "saura 5mins a shiga lectures, let me go straight to the point, daga yanzu no more play."
Najib da Amir suka kalleshi da mamaki, sukace yarima me kake nufi? Salman ya d'aga littafin hannunsa yace " Nadaina submitting d'in blank sheet, na kusa zama uba, ba zan bari d'ana ya taso yaganni a haka ba." Yana kainan yai cikin theater, suka bishi da kallo cikin tsananin mamaki, anya Salman ne kuwa? Sai dai Najib ya kalli Amir yace " kamar cewa yai ya kusa zama uba ko?"
Amir yace "haka naji."
Najib yai murmushi yace "wow da alama Salma ciki gareta."
Shima yai sauri ya shiga yana murna.
Amir ya bisu da kallo, shikam sam baisan karatu, haka dai ya shiga ranshi a b'ace.
Yan class gaba d'ayansu suka zuboma Salman ido, harda malamin, mamaki suke yau Salman ne ya shigo akan lokaci? Sannan kuma rike da littafi? Salman ko kulasu baiyi ba ya wuce ya zauna.
Malamin ya saki baki, sai da Salman ya kulu yad'an daki desk kad'an, sannan kowa ya juya, malamin ya d'auko biro a aljihunsa a rikice ya d'auka maker ce, sai dayaje rubutu ya gani, yan class suka kwashe da dariya, sannan yai saurin d'auko maker ya fara rubutu.
Salman rashin sabo yasa duk yaji ajin ya isheshi, yadaure sai gyara zama yake, yakai hannu kamar zai d'auko waya, Najib yace "ka manta ne baban baby?" Salman najin haka ya fito da hannunshi, har aka gama lectures kafin su fito.
Yana fitowa yad'au wayarsa ya kunna, text ne ya shigo daga Beauty "My prince ya karatun?"
Murmushi Salman yai sai dai maimakon ya kirata kawai sai ya kira wata number, yace "Asim ina zamu had'u? Na taho da passport d'in."
Sai kuma yace "alright" tare da kashe wayar.
Najib ya kalleshi yace "badai honeymoon zaku kara guduwa ba?" Salman yace to baban sa ido, mun kusa fara exam inafa zani wani gun?" Najib yace "kai abin nan na bani mamaki."
Salman ya d'an bige kafad'arsa yace " gwara ya daina ma baka, muje ka rakani."
Nan suka shiga mota suka fita.
Farha zaune kusa da fulani da ishaq, Fulani tace "yanzu wace shawarar zamu b'ulo?" Farha ta kallesu tace "ni ba wani plan da za'ayi dani, dan yanzu yayana yana sona banason nasake wani abu dazaisa ya kara jin haushina."
Fulani tace " ke yanzu kina tunanin Salman dagaske sanki yake."
Farha ta mike tace" ni ba abinda yadamen, abinda yayana Yafad'a dashi kad'ai zan d'inga amfani." Takarashe maganarta tare da mikewa tai d'akinta.
Ishaq yace "good haka akesan soyayya da confidence, da alama nima zan tari Salma in fad'a mata abinda ke raina, wayasani ko itama tana sona? Ganin na basar ne yasa ta share?"
Fulani ta kalleshi shekeke, tace "lalai Ishaq baka da hankali, matar kanin taka zakace kana so? "
Ishaq ya mike yace "nidai nagaji da biye miki abubuwa na basa tafiya daidai."shima ya juya yai waje.
Tai tsaki tace "ace duk cikinsu bada wanda zakai shawara? Ga ragowar 'yayanta maza bata saba irin wannan had'in dasu ba.
Salman sai bayan magrib ya dawo, yana parking yaga wayar farha, tsaki yad'anyi kafin ya d'aga, cikin salo da kisisina take maganar, tace "yayana baka dawo ba?" Salman yace "ya akai? Kanwata ta damu ta ganni ne?" Farha tace "sosai ma." Yace na shigo yanzu, anma zan tsaya gun mai martaba"
Tace " to sai ka gama." Ya kashe wayar batare da ya amsa ba.
Tsaki yakari yi, sannan ya kira Beauty, Salma ta d'aga tare dayin sallama, wani sanyine ya ratsashi, yace Beauty kinjini shiru ko? Tai murmushi tace " eh mana duk ba dadi." Salman yace "uhmmm lalai an damu dani dayawa, Me aka tanadarmin to?" Salma tace "komai ma, nidai ka dawo please"
Salman yace " amma dai ba inda ke miki ciwo ko?" Tace "nurse tazo d'azu ta dubani tamin dressing." Yace "good, na iso ma, zan d'an shiga gun mai martaba ne" tace "tam a mikamin gaisuwata." Yace "uhmm."
Ya kashe wayar tare da fitowa yai b'angaren mai martaba, yana isa, bafadan ya shiga yamai iso, Ishaq na zaune gun sarki, Sarki ya bada izini.
Salman na shigowa yaga Ishaq, shima Ishaq din kallanshi yake, Salman ya d'auke kai, tare da shiga, yai kasa dakai sannan ya kwashi gaisuwa, ga mamakin Ishaq bayan Sarki ya amsa harda tambayar jikin Salma, cike da mamaki Ishaq ya kalli Sarki, bai kara shan jinin jikinsa ba sai dayaji Sarki yace Ishaq bamu guri zamuyi magana, cikin tsananin mamaki ya amsa sannan yafita, sai kuma yai tunani ko dai fad'a za'amai? to amma in fad'ane ai sarki bazai amsa gaisuwarsa ba, meke faruwa?.
Nace kaika sani............
Salman ya dade sosai, da Sarki sai daya tirkeshi suka ci abinci tare, sannan yamai saida safe ya fito.
Kana ganin fuskarsa zaka gane yana cikin farin ciki, yau ce rana ta farko daya tab'a cin abinci da mahaifinsa, bazai iya tunawa ba ko kila yana yaro, amma shidai a saninsa yau ce ranar farko.
Bangarensa ya shiga da sauri, shi sam bai kula da Farha dake zaune a falo ba, zuciyarshi nakan yasanar ma Beauty abin farin cikin daya same shi, Salma kam, tayi kwalliya da riga iya gwiwa, da d'an wando pencil, ya d'ameta, ta fito daga toilet kenan, jin kamar zatai amai, sai dai taje ta kuma kasa aman, jitai an murd'a kofa ta juya dan tasan Salman ne, ganinshi tai ya shigo da sauri, yana shigowa ya sa hannu ya d'agata yafara juyi da ita, Salma tace "Prince? Wani abun ne yafaru?"
Sauketa yai sannan ya rungumeta yace "Beauty kinsan me?" Ta girgiza kai alamar a'a, yace "yau tare mukaci abinci da Abbana."
Wani sanyayen farinciki ne ya bayyana a fuskarta tace" Prince? Naji dadi sosai"
Shima yace "nima haka beauty."
Farha da kishi ya turnuketa ganin Salman ya wuceta yasa tabuga kofar da karfinta, Salma da Salman suka kalli juna, Salma ta karasa tare da bud'e kofar ta fita.
Farha ta gani hakimce akan kujera, tace " Yayana nake nema" Salma tace "haka b'atan kai kikai ko? Kin manta na hanaki shigomin guri?"
Farha ta d'aga waya ta iira Salman, ya d'aga tace "yayana ina falo fa?" Tai maganar cikin shagwab'a, Salma tai wani murmushi tace wahalace bata isheki.........maganarce ta tsaya a wuya ganin Salman ya fito, cikin mamaki tace "Prince?" Salman ya kalleta sannan ya kalli Farha yace "kinzo?" Ta makama Salma harara sannan tace "tun d'azu nazo fa, ina nan ka wuceni."
Salman ya kalli Salma data cika tai fam, ya kalli Farha yace "muje waje." Tace " to" sannan ta kalli Salma tace "inlaw Sai da safe."
Salma ai kasa magana ma tayi tana kallansu suka fita, bin kofar tai da kallo.......
Mekenan? Abinda ke yawo akanta kenan.
By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No.5⃣5⃣
Salman suna fita ya kalli Farha yace " gani neman me akemin?" Ta saki wani murmushin kissa cikin shagwaba tace " nemanka kawai nake in ganka, jinake kamar na dade bam ganka ba."
Wani kallo ya mata da ita kanta batasan nameye ba yace " idan bakya garin yazakiyi kenan?" Cikin rashin fahimta tace " bangane ba yayana." Salman yai murmushi shima tare da matsowa kad'an yace "just joking. "
Dariya tasa tace " kai yaya har ka tsoratani." Yace " yanzu dai nagaji, muje in rakaki in dawo inkwanta, bacci nakeji."
Cikin salon shagwaba tace " ba wani yaya so kake dai ka koma gun matarka." Gani tai ya murtuke fuska ya had'e rai sosai yace" in muna magana karki kuskura ki kara sako matata, banasan haka." Farha kam jitai jikinta yai sanyi, a hankali tace "kayi hakuri yayana."
Murmushi taga kuma ya mata, yace "ba haushi naji ba kawai banaso ne."
Tace "to yaya, zan kiyaye."
Nan suka fita ya rakata sai dai bai shiga b'angaren fulani ba yace mata " nizan wuce, sai na ganki gobe." Tace " to yayana. "
Salman ya juya ya taho, itakam tana tsaye tana kallanshi har ya kule, kafin ta shiga gida, waya ta d'aga ta kira mumynta, yanda taji muryar mumyn da alama bacci take ma.
Farha tace "Mumy natasheki ko?" Mumyn tace "ya akaine Farha?" Farha tace cikin rawar murya " Mumy ina tsoro fa?" Tace "tsoron kuma me? Kamar ba 'yata ba? Bansanki da haka ba."
Farha tace " ina tsoron in na auri yaya Salman da kyar insamu soyayyarsa ko wata kulawarsa." Mumyn tace " baya sanki ne?"
Farha ta share kwalla tace" Na kasa gane wa Mumy"
Mumyn tace " indai kinasan abu na dade ina fad'a miki ki tabbatar abin nan yazama naki, rayuwa d'aya ce ba biyu ba, kar kizo kiyi dana sanin abun."
Farha tace " ai abun nan danakeso Mumy dole ne ya zama nawa, ko me mutane zasuce." Mumyn tace "good, ke dama har kina wani tunanin soyayya? Bayan nasan kinsan komai, a yanda nasanki, ina tunanin ba namijin da bazaki iya karkato dakansa ba, amma kike shirin bani kunya?"
Farha ta zauna akan gado tace " mantawa nai mumy, gashi Salman d'in kwarjini gareshi, ina shirya a d'aki zanyi abu, ina fita sai in kasa."
Mumyn tace "to ko kinaso in ma yaya magana? Nasan dai zai duba maganata duk da ba uwa d'aya muke ba, inya duba hallarcin rike mai Salman danai, bazai ki ba" Farha tace " haba mumy ni banaso inje gidan wannan 'yar iskar matar tasa tad'ingamin wani kallo, nafisan in aureshi ta soyayya." Mumyn tace shikenan sai naji good news tafad'a tare da kashe wayar.
Farha tabi wayar da kallo tace " shiyasa nakesanki Mumyna."
Salman kam yana shiga gida Salma ya gani tsaye a inda ya barta, baice mata komai ba kawai hannunta ya kama yai cikin d'aki da ita, suna shiga ya jawota jikinsa yace "Beauty me yasa zaki tsaya a falo bayan kinsan ba lafiya gareki ba."
Salma ta daure tace " ina kaje?" Salman yace " Beauty do you trust me? " tai shiru can d'aga kanta, Salman yace " in har kin yarda dani then please just trust me." Salma ta d'ago ta kalleshi idanunta taf kwalla, tace " I trust you Prince but I don't trust that girl." Salman ya shafo gefen fuskarta sannan ya tsaida hannunsa akan gefen fuskarta, ahankali ta d'ago ta kalleshi idanunta sun cika da kwalla, yace " just trust me, kinji?" D'aga kai tayi alamar eh, nan ya kai bakinshi cikin nata, salon dasuke ma juna yasa suka gangara kan gado, sun shagala sosai da farantama juna rai, hakan yasa nikuma nai waje.
Da safe wajen 10 Salman bayan ya shirya yace itama ta shirya ya ajiyeta a gida, murna agun Salma kamar me, itakanta tanasan zuwa, tana tsakiyar murnarta sai kuna tai kasa da kai, Salman yace ya akai kuma? Ta nunamai inda aka mata d'inki tace " a haka zani?" Salman yace "zasu gani ko?"
Salma tace " banaso su zargi komai, inciwon ya warke na kirasu a waya."
Salman zaiyi magana wayarsa tai k'ara ya d'aga da sauri ganin Asim ne, yad'aga yace "abokina ya?"
Asim ya sanar masa yayi ciko ciko dan haka karfe 5 akwai flight dazai tashi, yai murmushi tare dayin godiya ya kashe wayar.
Salma ta kalleshi tace "wani abu ne?" Yace "is a secret bari inje gun mai martaba in dawo" tace to.
Dasauri ya fita, yai fadar mai martaba, akamai iso ya shiga, sun gaisa cikin sakin fuska kafin Salman yace yanada magana, jin haka yasa Sarki ya bada umarnin abasu guri.
Salman ya d'an matso kusa da Sarki, yace " Abba akan Farha ne." Sarki yace "nikaina inasan inma magana akanta."Salman yace " name?"
Sarki yai shiru can yace " d'azu da safe mahaifinta ya kirani akan wai Farha na sanka, kuma wai saboda kai tazo nan kasar."
Salman ya had'e rai yace" wannan zancensu ne, ni yanzu tunani nake yau zansa a maida ita kasarsu, dan nakula zamanta anan nema yake ya canza mata hali daga good zuwa bad."
Sarki yai shiru can yace " bangane canza hali ba? " Salman yace " wasu suna amfani da ita akaina, nikuma nasan ta duk da she is not kind amma she is not bad." Sarki yace " su waye wad'anan mutanen?" Salman yai kasa dakai yace " Abba abar maganar kawai." Sarki yace " shikenan amma da alama kenan baka san auran?" Salman yace " Abba yarinyarnan kanwata ce, kuma koba haka bama ni bani da tsarin auren nace biyu. "
Sarki yai murmushi yace " da alama d'ana yanzu yana fad'amin abinda ke ransa, naji dadi sosai, amma yanzu yazamuyi da iyayenta?" Salman yai wani murmushi yace " ba wani abun bane ni zan fad'a musu" Sarki yace "good inasan confidence d'innan naka."
Salman yai kasa dakai tare da sosa keya.
Kafin sallar la'asar Salman ya dawo gida, bangaren Fulani yai, tana zaune a kilisarta itada Ishaq, kallansu kawai yai yace Umma ina gaisuwa, Fulani haushi ya kamata, gashi agaban bayinta wannan ai cin fuska ne, Salman d'akin Farha ya wuce tare da knocking, ta bude da sauri dan yasanar da ita zuwanza, a kofa ya tsaya yace " Farha hado kayanki mu fita." Tace " kayana kuma yaya?" Salman yace "eh wani gida zan kaiki." Cikin rashin fahimta tace ina? Salman ya had'e rai yace " in bakyaso mu barshi kawai, nad'auka zakifijin d'ad'in can da nan."
Farha ta riko hannunshi tace "ya hakuri yayana, bari na had'o"
Salman ya jingina da kofa yana jiranta, Ishaq ne ya taho a zuciye, yace " kai Salman wato dan rashin mutunci, umma kama haka?"
Salman ya juya fuska sannan ya kara juyowa da murmushi yace "ahhhhh, dan nace ina gaisuwa?" Yafad'a tare da takawo zuwa gun umma, ya zauna sannan yai murmushi yace " Umma ashe wai haushi kika ji?" Itama ta kakaro yake tace "haba Salman wani haushi kuma?"
Salman ya mike tare da kallan Ishaq yace "kaji ko? Dama yama za'ai taji haushi akan wannan? Intaji haushi ai da matsala." Ishaq ya kulo yace " kaifa d'an rainin wayau ne."
Salman ya dafa kafad'arsa ya matso daf da kunnensa yace "rainin wayau ya wuce wanda kamin? Ka d'auka ban sani ba?" Yasaki wani murmushi ya wuce d'akin Farha.
Jikim Ishaq ne ya shiga rawa, badai ya sani ba? Me ya ke nufi da kalamansa? Bai fito yace yaganshi ba? To me yake nufi?
wad'annan tambayoyin su suka sa jikinsa ya shiga rawa.