Washe gari kuwa tin da safe kowa ya shirya a gidan, wannan umarnin Alhaji Mustapha ne domin yana so su isa da wuri domin ticket ɗin safe aka samu, aika Afnan yayi tayi kiran Ya Ameen ɗin da shi kaɗai ake jira bai fito ba, sai gashi kuma cikin takun shi na ƙasaita da sanyin shi da kan ƙara mashi kwarjini a fuskar jama'a
Sanye yake cikin wani lallausan yadi kalar sky blue, an mashi ɗinki Abuja style, da gani dai yana son ɗinkin, rigar iya rabin cinya ta tsaya bata kai guiwa ba, hakan ya ƙara fiddo da asalin kyawon halittar da Allah yayi mashi, kan shi babu hula sai dai gyaran fuskan da kan ƙara ƙawata fuskar tashi. Takalmin shi da hankachip ɗin da ke hannun sau ciki, shi duk kalar kayan ne sai zuba ƙamshi yake yi. Cikin ɗan sassarfa ya isa ga Lahajin dake tsaye da alama jiran shi yake yi ya fito.
Gaida dad ɗin nashi ya shiga yi cikin girmamawa, yayin da Alhajin ya miƙa mashi hannu don suyi musabaha, na daga cikin halin Alhajin ne sauƙin hali da sauƙin kai, hakan kan ƙara mashi shaƙuwa da ƴaƴan nashi fiye ma da mom ɗin tasu.
Matsawa yayi ga Hajiya Kubran da fitowar ta kenan cikin shigar wani ɗanyen boyel mai taushi da walƙiya, ɗan rungumo ta yayi cikin murmushi mai ƙara ƙayata kyakkyawar fuskar tashi, amsa gaisuwar tashi ta shiga yi cikin jin daɗi da ƙauna ga ɗanɗan nata, duk da bata manta ƙin yarda da maganar tata da yayi da a daren jiya, Amman ta bar ma zuciyar ta, ta kuma sha Alwashin ganin zargin ta da hasashen nata bai zama gaskiya ba.
Sauran ƙannen nashi suka shiga gaida shi yayin da ya duka yana ma Nasreem wasa da miƙa ma Ayan hannu sukayi musabaha yana mai gaida yayar tashi cikin sakin fuskan da sai yana cikin family ɗinshi ne kawai zaka ganta.
Shafo kanshi tayi tana faɗin "Brother fatan ka tashi lafiya" ta faɗa cikin murmushi da kan ƙara nuna tsantsar ƙaunar ta ga ƙanen nata.
Alhaji Mustapha ne ya kauda masu gaisuwar da suke yi cikin cewa "Al ameen ina ganin ya kamata mu zo mu wuce ko kasan da ƙarfe 08:00am ne lokacin tashin flight ɗin. ɗan sosa kan shi ya shiga yi da ɗan makullin motar shi da ke hannun shi sannan ya shiga faɗin" Dad ina ganin ni ba zan biku ba sai dai ko zuwa gobe ko jibi ne zan iske ku cen ɗin, saboda aikin construction ɗin nan naga yana neman tsayawa, Eng ɗin ne naga yana san sanya shiririta dan yaga na cika mashi cikon kuɗin shi, and Bilal ma yace man yau zai iso ina jin ma sun taso yanzu, Ga kaya da kamfani zai fitar yau ina so inje ayi komai gabana, kasan yanzu rashin gaskiya ta yawaita" ɗan murmusawa Alhajin nashi yayi, sarai ya fahimci Ya Ameen ɗin baya son bin nasu ne, May be dan yana gudun maganar da Hajiyar tasu ta taso ita ne jiya, tana iya zuwa ta zuga Granny Zuwaira akan zancen; ɗan ƙara murmusawa yayi yana faɗin " is ok Al ameen Amman wanne kamfani ne zai fidda kaya yau?" (Domin Al'ameen ɗin shine manager ɗin duka kamfanonin Alhajin duk da shima yana da nashi) "Eh sabon na costimetics ɗin nan ne" Ya shiga faɗi da ɗan guntun murmushi akan fuskar shi yana mai son Alhajin nasu ya yarda da uziri nashi, "Tau ba matsala for now, Amman dai ina fatan zaka je cen ɗin cikin lokaci, Kaga ka kwana biyu ba kaje ba, duk da kuna waya, ya kamata kaje kaima Kaga lafiyar kakannin naka"
"to Dad" ya bashi amsa yana mai buɗe mashi gidan baya ya shiga ya zagaya ya buɗe ma Mom ɗin tasu, da bata ƙara tankawa ba don duk ya tushe mata plan ɗin nata, amman ba komai, ai bata ma jin sai tayi kamun ƙafa da wani akan al'amari yaron nata, duk isar ta da dukiya ta, ita ta haife shi in ya san wata ai bai san wata ba;
Mota biyu sukayi ɗaya Alhaji Mustapha da Hajiya kubra sai driver kawai, sai kuma ɗayar da ta ɗauke Aunty feena da yaran nata sai Saudat, Nihal da kuma Abie da ya hakimce a gaba.
Kai tsaye motar shi ya nufa, bayan yaga ficewa mitocin daga cikin harabar gidan nasu, restaurant ya fara tsayawa ya siya abun break fast sannan ya wuce Asibiti da ya kwana tinanin su duk da son kauda tinanin nasu da yake yi daga cikin ran shi, sai dai baya iyawa, sau da dama shi karan kanshi kan shiga tinanin kan shi da kanshi, tabbas ya san yana tausayin na ƙasa dashi, da marasa galihu, da ƴan aikin nasu, tau sai dai yana mamakin kan nashi, su salon yanda yake tausaya masu ma daban ne, amman ya kan alaƙanta hakan ne da rashin lafiya da take damun Maman Suhan ɗin.
Sallama yayi daga bakin ƙofa, tsam na tashi daga kan kujerar da nake duƙunƙune tin bayan da na gama sallar asubahin na kuma komawa na kwanta domin in ɗan rutsa, don cikin dare umman tawa ta farka, cikin ƙarfin hali irin nata har fira muka ɗan taɓa tana kara jaddada man maganar karatun nawa, da kuma roƙo na akan in bama dukkan Abunda zan gani a rayuwa ta ta gaba baya.
Daga ciki na buɗe mashi, ina mai janyewa na bashi hanya domin ya wuce. Kai tsaye ya shiga har bakin gadon umman tawa, yana mai ajiye manyan ledojin take away da yayo mana; ɗan rankwafawa yayi daidai saitin gadon umman tawa, yana mai kallon bugawar lumfashin ta.
"ta samu bacci ne?" ya jefo man tambaya yana mai janyo kujerar gefen gadon ya zauna idon shi cikin nawa, "Eh ta samu bacci, Amman ta farka cikin dare jikin da sauƙi, don har ma fira mun yi" na faɗa ina mai ƙoƙarin janye nawa idanu, tinani na ke yi, shi wanne irin mutum ne? Mutum mai daraja irin ta Ya Ameen da ba ko domin arziƙi shi ba da na iyayen shi, shi mutum ne daban ko cikin matasan garin na Abuja akeji dashi, shine yake bamu kulawa haka? Gaskiya ya cencenci a yaɓa mashi, ya cencenci a girmama shi, da dukkan iyawa.
"Hop dai bata wahalar da kanta ba wajen magana? Kin dai san dokar likita, ki dinga kula" ya faɗa yana mai kauda idanu shi daga gare ni da har yanzu nake rakuɓe daga bakin ƙofa, kwarjini shi baya bari in sake a duk lokacin da nake gaban shi.
"To zan kula insha Allah" na faɗa a hankali iya fatar baki, miƙewa yayi cikin halin ko in kula da tsayuwar da nake tayi, sannan ya shiga faɗin "Dictor ya shigo?" Lokacin da ya shiga ta kowa a hankali zuwa ga bakin ƙofar domin ficewa, amsar da na shiga bashi ce ta sanya shi ja ya tsaya ga barin ficewa, hakan ce ta sanya muke tsaye gaf da gaf, duƙar da kaina na shiga yi, bazan iya jurar haɗa idanu nashi ba, idan ma zan kula da jikina wata ƴar kyarma nake yi a hankali, me ke damuna ne ni Suhana? "Bai shigo ba yaya, Amman Nurse ta shigo sannan tace idan ta farka a bata abinci mai sauƙin nauyi, sannan mu kira ta, in kuma likita shigo shikenan" "Is OK Let Me Check On Him" Ya faɗa cikin salon turanci shi da yake kama da na turawan amurka da nake kallo a Tb ɗin babban falon gidan, ficewa yayi cikin salon tafiyar shi ta jarumin namiji, idan yaso komai cikin zafi zafi yake yin shi, idan kuma yaso kai kace wahainiya ce ke tafiya masalan ma idan yana jin ƴan miskilancin.
Office ɗin likatan ya shiga yayi daidai da isowar shi kenan Dr Ashafa ne yayi azamar miƙa mashi hannu yana faɗin "Yallaɓai ba dai har ka shigo ba? Gaskiya waɗannan patient ana ji dasu, Fatan dai jikin na maman tamu da sauƙi? Ya faɗa cikin murmushi da san ɓoye wani abu acikin ran shi;" Zamu iya zuwa ka duba Dr saboda ina so idan jikin nata ya samu sauƙi kayi discharge nasu, zanyi tafiya ne kuma bana son barin su anan babu mai kula dasu, gara su koma gida" ya maida ma da likita amsa cikin ɗan ɗaure fuska, bai san me Dr ɗin ke nufi ba, Amman ya kula tin jiya da yanda yake kallon Yarinya da take ta fama da jinya mahaifiya tata, ko menene ma nashi na damuwa? "OK to shikenan muje rana ya daɗe" likita ya faɗa yana mai ɗan sanya shakku a ranshi, Amman dai koma minene ai zai fahimta, gaba Al'ameen ɗin yayi Dr Ashafa ɗin yana biyo shi a baya tare da kayan aikin su na likitoci
Sake shigowa naga sunyi shi da likitan, watau sai da ya kira likitan kenan? Haka na cigaba da rayawa a rai ina mai janye idanu a ga barin kallon su, bakin gadon suka ja suka tsaya, hakan yayi daidai da farfaɗowar umman tawa.
"Ƴan mata zo ki taimaka ma umman ki ta tashi zaune kinji, zamu auna ta ne" likitan ya faɗa yana mai waiwayowa ya kalle ni da nake zaune ina aikin binsu da idanu da nayi nayi ga barin kallon su Amman na kasa, Ya Ameen ɗin yayi kyau, wani abu ke taso man cen ƙasa rai duk lokacin da ya bayyana inda nake, tasowa nayi a hankali na kama umman tawa ta zauna sosai, shi kau gogan ko kallo na ma bai yi ba, kaman ma bai san ina ta wurin ba, ya koma mani Yaya Al'ameen ɗin da na sani tin cen baya, da baya ɗaukar wargi, fuskar shi Sam babu walwala saɓanin yanda ya fita ba daɗewa.
Aune aunen su na likitoci ya shiga yi, sannan ya ɗago yana mai faɗa ma Ya Ameen ɗin komai normal, za ta iya cin komai, kuma ta kula da shan maganin ta akan lokaci, zamu iya tafiya gida, Amman nan da sati ɗaya mu dawo a sake gwada ta a gani, dokoki sosai aka shinfiɗa ma umman tawa, sannan aka hana ta cin wasu abubuwa da dama; wayyo likita, bai san ma abincin sai wanda aka ga dama aka bamu ba, in kace ba zaka ci ba sai yunwa ta kashe ka babu mai sani.
A haka na kama umman tawa muka fito, bayan motar na saka ta, ta ɗan kwanta na koma na kwaso sauran kayan da suke mallakin mu, har da take away ɗin da yayo mana da ko kallon shi banyi ba, balle in buɗa inga Abunda ke ciki.
Har zan shiga bayan ya tsattsare ni da idanun nan nashi masu rikita dani, sannan ya mani alama da in shiga gaba, haka kuwa aka yi shiga nayi na takure, masalan ma ga umma ta acikin motar kuma idanun ta biyu ba bacci take yi ba.
Kai tsaye naga mun nufi hanyar kasuwa, ban da hurumin tanka wa balle in tambaya me zamu yo a kasuwa, ƙila uzirin shi ne zai kai shi; parking yayi bakin tanƙamemen suoer market ɗin da yake bakin kasuwar, fita yayi ya shiga ba dadewa sai gashi ya fito yaron shagon na biye dashi a baya, hannun shi niƙi niƙi da kaya, but ya buɗe mashi tare da Sanyawa ya rufe, ya zagayo ya tada motar muka shiga cikin kasuwar, nan ma soyayya yayi sosai, cikin ni da umma ta babu mai tankawa, kowa da abunda yake saƙawa cikin rai.
Gida muka nufa kai tsaye, yayin da yake parking ya yafito mai gadi da hannu, cikin hanzari ya iso inda muke ƙoƙarin fitowa daga cikin motar; umarni yayi mashi da ya kira mama talatin a sashe namu na masu aiki, aiko ya ruga cikin hanzari, sai gashi da mama talatun ta taho cikin sauri, umarni yayi mata da ta kama man umman tawa mu kai ta ɗaki mu kwantar, yayin da ya kirayi mai gadin da isa da yake tsaye yana gyaran flowers da suka taimaka wajen ƙayata gidan, kayan yace su kwashe su shigar mana dashi cikin ɗakin mu, yayin da ya ja motar shi yana mai barin gidan.
Kai tsaye ɗakin namu muka nufa da umman tawa da take ɗan iya taka wa a hankali a hankali, kwantar da ita muka yi, yayin da su isa suka shisshigo mana da kayan namu suka fice suna ma umman tawa sannu da Allah ya kyauta, ina kallon mama talatun tana jinjina kai tana mai ƙare ma niƙi niƙinbkayan da ta gani tare da mu, ta dai san wannan aikin Alhaji ƙarami ne, wato dama ya ƙi bin su Hajiya Babba ne domin ya tsaya bauta mana kenan ko? Wai menene haɗin shi da mu ne? Su dai basu ga wata alama da ke alamta masu akwai wani abu tsakanin Suhana ba da Alhaji ƙarami ɗin balle ace dan ita yake yi? Koma minene zata yi ƙoƙarin sanar da hajiya ɗin, me hakan ke nufi ne? Ya kamata hajiyar tayi wani yunƙuri akai wallahi, ita ta ma ga sanyar Hajiyar wannan karon akan yanda ta santa da in ta ƙi abu duk yanda zata yi akan taga bai faru ba ta sani, tana cike da tsantsar mulki da kuɗi, naira shegiya ce, mai maida tsoho yaro ta maida yaro babba.
(Humm🤔🤔 Ya Allah kayi mana tsari da Hassada, ƙyashi, ganin gari da munafunci ameen ya Rab🤲🏻)
Bayan duk sun fita ne, na gyara komai a ɗakin na adama komai inda ya kamata, kayan ciye ciye ne da basu da illa ga masu ciwon zuciya irin wanda likita ya bada umarnin aci, su ne ya kwaso mana su sosai da sauran kayan buƙatu har da kayan marmari ma da zasu yi ma mai rashin lafiya daɗin ci, gyaran ɗakin nayi nayo wanka na shirya kaina cikin baƙar doguwar riga mara nauyi na tattara gashi na na ƙulle cikin ribom sannan na ɗaura ɗan kwalin rigar a bisa kai na, nayi kyau daidai misali, sannan na ɗauko ledar take away ɗin da yayo mana tin asibiti na buɗe da niyyar zuba mana muci ni da umma ta, lafiyayyen chips ne da plantain, sai soyayyen ƙwai da miyar kayan ciki, sai ƙamshi take har yanzu da sauran zafin shi, saboda mazubin na glass ne, da gani dai abincin zai yi tsada, sai dai baya cuwuwa ga umma ta saboda farin mai da aka yi using wurin suyar, kaina kaɗai na zuba mawa na fidda sauran ga ƴan uwa na ma'aikata da har yanzu sun gagara shigowa yi mana koda sannu saboda tsabar hassada, Abunda na san zata iya ci wanda likita bai hana ta ci ba na zuba mata, saida na tabbatas taci na ɓalli maganin ta na bata tasha sannan na gyara mata kwanciyar ta, na koma gefen katifa na zauna ina ya ƙunar abincin ahankali
Fira mukeyi jefi jefi da umman tawa da take bina da kallon tsantsar ƙauna ga ɗiyar tata, addu'a dai kam Al'ameen ya sha ta daga bakin umman tawa, godiya take jerawa wanda hakan ne ta sanya ni ɗan murmusawa a hankali dai ina ci gaba da cin abinci na; Sallama yayi daga bakin ƙofar ɗakin yayin da umma ta ta bashi izinin da ya shiga daga ciki, lokaci ɗaya tana mai umartata da shinfiɗa mashi darduma.
Kasa tashi nayi, domin jikina babu hijabi babu gyale, gashi rigar mai bin jiki ce ta fidda duk surar jikin dake Sanye da ita, kuma a zahiri bai kamata ya ganni haka ba, saboda shi ɗin ba muharrami na bane, hakan ce ta sanya na shiga bin ko ina na jikina da kallo kaman mai son gano wani abu.
"Hauwa'u dake fa nake magana fa, nace ki shinfiɗa mashi darduma ya zauna kin bar shi tsaye" umman tawa ta faɗa tana mai yunƙuri tashi, a haka ta samu ta zauna daidai domin Nidai na gagara koda motsi balle in taimaka mata har ma nayi mashi shimfiɗar
Hankalin shi ya maida kanta da take ajiye plate ɗin abincin kaman mai tausayin ƙasar, ta shiga miƙewa a hankali, lura da yayi da Abunda take ɓoyo ko ji ma kunya ne ya sanya shi kauda kanshi gefe, ya maida hankalin shi kan umman tawa yana mai ɗan sakin guntun murmushi iya laɓɓa, ko me take ɓoyo? Wannan mitsitsiyar yarinyar ma, da yake kyautata zaton garin jiki ne ya kwashe ta, ita har tana ganin ma ta cika ta kai mace, ƙara murmusawa yayi daidai lokacin da take shinfiɗa dardumar ɗan nesa kaɗan da katifa tasu.
"Nagode" ya faɗa iya maƙoshi maganar tana mashi wahala, yana mai zama ya tanƙwashe ƙafafun shi irin zaman salla, lokaci guda yana mai gaida umman tawa, cikin sakin fuska ta amsa mashi, sannan ya ƙara mata ya jiki da Allah ya sauwaƙe.
Godiya ta shiga jera mashi da kuma fatan nasara da cigaba a rayuwa, harma da iyayen shi, hakan ce ta sanya shi jin daɗi, yana mai ƙara ƙaunar matar da son taimaka mata da duk ahalinta.
Ikon Allah, abikan aikin mu da tin ɗazu suka kasa leƙowa su ga jikin umman tawa su gaida ta, sai gashi ɗaya bayan ɗaya yanzu da suka ga shigar Ya Ameen ɗin ɗakinmu suna shigowa gaida ta da ganin ƙwam, kowa ya fita kuma sai ya ƙara da abin da ya gani gaba.
Sake natsuwa yayi yana mai ɗan yin gyaran murya a hankali, sai da ya maido kallon shi inda nake rakuɓe bisa katifa gefen umman tawa, sannan ya saki wani ƙayataccen murmushi ganin ta sanya hijabi da shi bai ma kula da lokacin da ta ɗauko shi ba, haƙuri ya shiga ba umman tawa, da mata Alƙawarin hakan ba zata sake faruwa ba, ya faɗa mata afnan ce ta sanar dashi komai; ɗan faɗa umman tawa ta shiga yi tana faɗin hajiyar ta isa ne ya sanya tayi masu faɗa, ai ba wani abu bane, gyara ne take so ayi, kuma mun ɗauka insha Allah.
Haƙuri ya ƙara bata sannan ya shigo mata da maganar makarantar tawa, ta bacin yardar ta ta ƙara bashi, sai dai tana mai shawartar shi da yayi komai a hankali kada ran hajiyar ya ɓaci, ya alƙawarta mata komai ya wuce kuma babu abin da zia faru insha Allah.
Maida kallon shi yayi yana mai cewa "Ki ɗauko man takaddun naki in gani ko, don mu san ta yanda zamu ɓullo ma al'amarin" ya faɗa yana mai kauda idanun shi daga kaina kaman ma ba dani yake magana ba.
Miƙewa nayi cikin ɗan sanyi gami da nufar wardroop ɗin tawa, gami da janyo ƴar ƙaramar folder da takaddun tawa suke na miƙa mashi.
Amsa yayi yana dubawa, mamaki fal a ranshi na yanda yarinyar take da ƙoƙari, gashi dai makarantar masu hannu da shuni tayi, saboda Alhaji Mustapha ne ya sanya ta a makarantar har ta gama, kafin abubuwa sukayi mashi yawa ya tafi wani aiki ƙasar Indiya daidai lokacin da Jarabawa tasu ta fito wannan shine ya sanya ya shafa'a da karatun yarinyar koda ya dawo kunsan mnyan mutane, ita kuma Hajiya Kubran bata tina mashi ba, a cewar ta hakan ma ya isa, wa yace ƴaƴan masu aiki na makarantar jami'a (🤔🤨😏 ke kika hana ko Hajiya Kubra)
Takaddu sunyi kyau ya shiga faɗi da ɗan murmushi shi irin na miskilai, kai kace ma bai yi ba, sannan ya miƙe dasu a hannun shi yana mai cewa za'a siya jamb sai in cike tare da course ɗin da nake so, in naga ban iya ba sai in same shi ya koya man (kun ji ba Bigboo, ko ya manta da halin gidan nasu ne?) da to muka bishi da umman tawa, kuɗi ya ajiye kusa da umman tawa masu ɗan dama yana faɗin ko zata buƙaci wani abu, sannan ya ƙara jaddada mata kar taci Abunda likita ya hana, idan muna nuƙatar wani abu muyi mashi magana.
Umman tawa ce ta shiga faɗin lallai ba zata amshi waɗannan kuɗi ba, cikin girmamawa ya shiga bata haƙuri da faɗin duk abin da yayi mana haƙƙinshi ne da yayi mana, wannan ba wani abun damuwa bane, duk ma in muna buƙatar wani abu mu tuntuɓe shi a shirye yake da ya taimaka mana.
Godiya ta shiga ƙara jera mashi da yabanma dukkan in hidima da yayi damu ɗin "ba komai umma, Allah ya ƙara sauƙi" ya faɗa yana mai taka wa ya bar ɗakin riƙe da Takaddu na a hannun shi.
Oh Allah🙏🏻 Ashe zanyi karatu a rayuwa ta? Ashe Ya Ameen na magana haka? Yanda naga ya zage suna ta fira da umma ta, kuma duk wata kalma da zai faɗa cikin taka tsantsan da girmamawa yake yin ta kaman yana magana da Hajiya kubra, murmushi na shiga saki akai akai, ina mai sauke ajiyar zuciya, mafarki a ya kusa tabbata, jikina na bani mun kusa fita daga cikin halin ƙuncin da muke ciki ni da umma ta, daga na gama karatu na samu aiki zan gina mana gida, na ɗauke umman tawa muje cen muyi Rayuwar mu, muma muci gashin kanku, mu rabu da takura da jaraba Hajiya kubra, Allah na gode maka, Allah ka saka ma wannan bawa da
Alkhairi a rayuwar shi, ka haɗa ci da mata ta gari, da zata kula dashi, kuma tayi haƙuri da halin hajiya Kubran.
"Tashi ki naɗe dadduman in kin gama murnar" u mata ta faɗa cikin murmusawa da ke nuna sallar jin daɗin ta, da farin cikin ta.
Yunƙurawa nayi ina mai da rawa a fili na shiga faɗin "umma ai dole inyi murna kin gama man komai, Allah ya cika mana burin mu, ashe da rabon zan yi karatu nima in samu ilimi kaman yanda kowa ke samu?"
Murmusawa tayi tana mai kishingiɗawa tare da faɗin "Ai wannan yaro ɗan albarka ne, Allah dai ya bamu ikon saka mashi da alkhairi kaman yanda yake mana shi da mahaifin shi, ki kauda kuɗin nan ki maida hankali ki ci abinci" da to na bita ina faɗin "ni wallahi ummana tsabar murna ma yasa naji na ƙoshi"
"ki dai maida hankali" umman tawa ta bani amsa tana mai lumshe idanun ta murmushi fal a fuskar ta.
Ta ɓangare guda kuwa Al'ameen ɗin na fita wayar Mom ɗin nashi na na shigowa, tare da umartar shi da cewa ko me yake ya tabbatas ya biyo jirgin yamma ya isa Katsina tana son ganin shi, shi kin mamaki ya shiga tambayar ta ko lafiya? "Lafiya lau" ta bashi amsa tana mai datse kiran, Layin Afnan ya nema gami da tambayar ta, ta faɗa mashi kawai dai taga an kira ta ne daga gidan Amman bata san ko wanene ba, kuma daga gani gulma aka kawo mata, "is OK" ya faɗa yana mai katse kiran ganin kiran babban Abokin nashi da zai kawo mashi ziyara yau ta shigo wayar shi.
Amsawa yayi cikin son kauda zargin komai daga ranshi, bayan sun gaisa ne yake faɗa mashi ya iso gashi a airport, cewa yayi ya jira shi yana zuwa ɗaukar shi.
Ko da ya isa ya tadda abokin nashi yana jiran shi, cikin son juna da tsantsar farin ciki suka rungume juna suna mai mararin juna da tsantsar ƙauna ga aminan guda biyu, basu bar airport ɗin ba sai da ya yanka masu ticket guda biyu tare da kallon Bilal ɗin ya shiga faɗin "yaro yau ƙauye zaka kwana, ka taddani tafiya ta gaugawa ta taso mani" cikin murmushi Bilal ɗin ya kai mashi ɗan ƙarami duka a damtsen hannu yana mai cewa "To ya zanyi Friend" ai ko ruga ka kai ni dole in kwanta, ya zanyi tinda na riga nazo?"
Cikin walwala da jin daɗi suka bari airport ɗin direct gida ya wuce dashi domin yaje yayi wanka ya huta kafin lokacin sallar azahar ta ƙarasa.
~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
_*Page ~13~*_
_To Readers_ --- *Abun da kuka ji da zai amfane ku ku ɗauka, wanda kuka ji akwai kuskure ciki, kuyi watsi dashi, mu ba muji wahalar zaunawa muyi amfani da idear ɗinmu ba mu rubuta maku labarin da zai amfane mu ba baki ɗaya ba, sai ku da zakuyi comment ƙarƙarinta layi biyu zuwa uku, shine zai ke maku wahala, Anya kuwa readers kuna kyautawa🤔? Muna maraba da gyara ko ƙorafi, Amman ba ta hanyar zagi, ko cin zarafi ba, kuskure kowa nayi indai kai ɗan adam ne, kuma ajizi, so saboda haka muna shawartar ku da ku dinga ƙarfafa mana guiwa, wadda kuma taga labarin baiyi mata ba, toh ta bar mana abunmu ba sai ta karanta ba, bamu sanya kowa dole ba, imfact ma babu dole sai rai yaso a rayuwa. fans muna godiya da irin supporting ɗin da kuke bamu 💓muna yinku over, Allah ya bar ƙauna, wannan saƙo ne daga ƴan ƙungiyar ~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Fira sosai suka shiga yi da aminin nashi da bashi da kamar shi, kaman ba Ya Ameen ɗin da kuka sani ba, har yana zaulayar abokin nashi, akan zancen bikin nashi da za'ayi watanni ƙalilan masu zuwa inda anan Abuja zai auri yarinyar ya tafi da ita cen.
Sai da sukayi wanka suka shirya tsaf sannan suka wuce wani eatery mai bala'i kyau da tsada suka ci abinci sannan suka koma gida domin ƙara hutawa.
Al'ameen ɗin ba mai yawan yawo bane indai yana ƙasa, yafi ganewa ya zauna a gida a part ɗin nashi yayi aiki.
Yanzu ma hakan ce ta faru, yayin da ya jawo laptop ɗinshi ya shiga aiki, wannan ce ta sanya Bilal ɗin fahimtar cewa ƴan maganar sun bar kan aminin nashi, to ko wacce magana zai yi mashi fa zai yi mashi shiru ne, har sai lokacin da yaso tankawar kuma baya maido da zancen da ya riga ya wuce, wannan ɗabi'ar shi ce tin yana ƙarami, balle yanzu da ya girma.
Kwanciya Bilal ɗin yayi domin yana jin baccin gajiya gashi ya ƙoshi har wani lumshe ido yake yi.
Bilal ɗan gayu ne na ƙarshe, yana da hankali da tunani sosai duk da kasancewar shi cikin jajayen fata, hakan bai canza halin shi da mu'amala shi ba, wannan ce ta sanya abotar su da Al'ameen ɗin da take tin ta yarinta take daɗa ƙarko har kwanan zancen.
Aikin shi yake yi cikin salo da kwarewa yake sarrafa kwamfuta, kaman dama cen shi ne ya ƙera ta, to ai dama karatun shi kenan kada ku manta.
Kiran salla ne ya farkar da Bilal ɗin yayin da Al'ameen ɗin har ya ɗauro tashi alwalar, bayan Bilal yayo ne suka nufi masallacin da yake gefe ta jikin ɓari ɗaya na gidan nasu.
Ƙarfe biyar daidai sukayi shirin barin garin, yayin da Al'ameen ɗin ya tara dukkanin ma'aikatan gidan domin bar masu jan kunne tinda za'a bar gidan ba kowa sai mu kaɗai.
Ni da umma ta ce kawai bama wurin, ja masu kunne yayi sosai akan su kula da komai, Bilal ɗin na tsaye gefen shi yana ta murmusawa domin ya san abokin nashi kwarai da rashin son wargi, gashi dai ya iya mu'amala da ma'aikata dama cen, sai dai shi mutum ne mai son taka tsantsan da kula.
Bayan ya gama dasu ne, ya nemi Bilal ɗin da ya raka shi ɗakin namu domin ƙara duba jikin umman tawa.
Kwarai Bilal ɗin yayi mamakin ina yake nufa haka da yake ta ratsa sashen ma'aikata haka, sai dai bai ce mashi komai ba ya cigaba da bin shi a baya har zuwa bakin ƙofar ɗakin namu da yake tsaf a share tas,
Sallama sukayi, yayin da umman tawa ta basu izinin shiga, kai tsaye suka cusa kansu cikin ɗakin namu da babu wadatar abubuwa.
Miƙewa nayi ga barin karanta littafin *Jinnul Ashique* (na Harira ƴar fillo) domin littafin ya tafi da hankali na akwai tsantsar soyayya da abun al'ajabi da ban mamaki cikin shi, ina ma nima zan samu wanda zai gwada man irin wannan soyayya haka? (zaku iya neman shi ku karanta, zaku same shi online)
Darduma mai ɗan girma na shimfiɗa masu lokacin da nake ficewa a ɗakin, Sam bazan lamunci zama na wuri ɗaya dashi ba, ƙamshin shi, idanun shi, ba ƙarami makami bane da kan taimaka wajen ruɗewa ta ba.
Jikin umman tawa ya duba, Alhamdulillahi sauƙi ya samu sosai, faɗa mata yayi tafiya ta gaugawa ta taso mashi, da fatan dai babu abin da muke buƙata? Babu umman tawa ta bashi amsa sannan ta ɗora da godiya ta haɗa har da Bilal ɗin da tana ganin shi jefi jefi a gidan Amman sai ayi shekaru ma, in ba Al'ameen ɗin na gari ba.
Harda Bilal ɗin a cewa babu komai Allah ya ƙaro sauƙi, kusan ma zamu iya cewa Bilal ɗin yafi gogan naku magana har ma da murmusawa, domin yau ƴan miskilancin na akai.
Miƙewa sukayi suka baro ɗakin, tarin tambayi yi fal acikin ran Bilal ɗin, Amman ba lokacin yi su bane, matar ta burge shi, to wacece yarinyar da ta shimfiɗa masu darduma ta fita bayan ta gaishe su?
Tsafta da ƙamshin ɗakin sun burge shi, abun ya ƙawatar dashi, matar kaman ya santa cikin ma'aikatan gidan fa, amman fuskar tata kaman ta ɓace mashi, any way🤷🏻♀ zai tambayi aminin nashi in sun natsu.
Ta inda nake zaune jikin ɗan dandamalin flours suka zo suka gitta ni, tin daga nesa Naji tahowar su ta dalilin ƙamshin Ya Ameen ɗin da ya fara isowa hancina kafin ƙarasowar tasu, sadda kaina kawai nayi ƙasa har suka wuce, bansan barin garin zasu yi ba, wannan ce ta sanya ban masu adawo lafiya ba, kuma koda cen ma ba halina bane yawan tanka ma maza aduk al'amurran da basu shafe ni ba, sai dai ina ƙara ganin girman mutumin da ya kasance mana kaman uban gida ne a gare mu bama mu kaɗai ba, duk wani da ya kwana ya tashi ya amsa sunan ma'aikaci a gidan.
Bilal ɗinne ma naga kaman zai tsaya sai kuma yaga abokin nashi bai tsaya ba, ya wuce kai tsaye zuwa ga motar tashi yana mai kwala ma Idi driver dake cen bisa kujeru dake wajen gate suna fira da mai gadi.
Dagudu ya taso ya wuce ta inda nake zaune, hankalin shi ma bai kai kaina ba, ga motar ya isa yana mai russunawa tare da faɗin "gani yallaɓai" makullin motar ya miƙa mashi yana faɗin "airport zaka kai mu sai ka dawo da motar"
"To" yace yayin da ya amshi makullin ya shiga mazauni driver ɗin, Bilal ɗinne ya shiga gidan gaba, yayin da Al'ameen ɗin ya shiga gidan baya, shiru ya ratsa motar in ka ɗauke ac dake yin aikin ta a hankali a hankali.
Ban jira tashin motar tasu ba, na miƙe a hankali cikin salon tafiyar tawa na nufi sashen namu; ta gefen idanu ya bita da kallo yayin da suke ficewa daga cikin katafaren gidan nasu, shi kau Bilal juyawa yayi ya bita da kallo har suka fice yana ƙissima abubuwa da yawa a ranshi.
Ƙarfe biyar da rabi jirgin nasu ya ɗaga zuwa Kaduna daga cen za'azo ɗaukar su domin ya ma mom ɗin tashi waya tin ƙarfe huɗu da ta turo driver ya ɗauke su.
Shidda da wani abu suka isa, sun tadda driver na jiran su, basu wata wata ba suka nufo gidan nasu kai tsaye, da yake lafiyayyar mota ce sai gashi bayan isha'i da kaɗan sun isa state ɗin tasu ta hauhuwa, (Katsina ta Dikko kenan, garin tudu ɗan marna, ɗakin kara kunya gare mu ba dai tsoro ba)
Mama zuwaira tayi murna da zuwan jikokin nata, masalan Al'ameen ɗin da Bilal dama ta kwana biyu bata ga Bilal ɗin ba, saboda ba yawan zuwa yake yi ba, family ɗinshi duka suna cen ƙasar, har ma da kakar tashi mace tinda namijin ya rasu.
Aiko babu wata wata ta ta sanya masu aikin ta suka shirya masu teburin cin abinci, kala kala, duk da cewa da suke yi sai sunyi wanka sun huta hakan baisa ta kyale su ba, jikin tsufa ya kama ta dole su lallaɓa ta, haka suka ɗan yayyabiɗa sama sama, suka tashi, shi Al'ameen ɗin ma yafi shan coffe da salak ɗin da yaji ƙuli-ƙuli, 🤣kunsan gidan tsofaffi ko da me ƴaƴan su zasu zama, sun fi son abincin su na gargajiya da muhalli su na gado🤣
Da yake shi Al'ameen a nan gidan Alhaji Isuhun yake da part, wannan ce ta sanya basu haɗu da sauran ƴan uwan nashi da iyayen ba daidai zuwa safe.
Bayan sun gama komai ne na al'adar kwanciya a ɗakin da yake mallaki Al'ameen ɗin suka kwanta domin gajiya ta baibayesu na zaman mota ga doguwar tafiya (a cewar su)
Bilal ɗinne yayi gyaran murya yana daga kwance gefen gadon, hakan ce ta sanya Al'ameen ɗin miƙewa zaune yana mai fuskantar abokin nashi, da ya daɗe da Miƙewa zaune shima.
Natsuwar da yaga yayi ce ta sanya shi gane cewa maganar mai muhimmanci ce, hakan ce ta sanya shi tattara dukkan Natsuwar shi shima a kan abokin nashi.
"Bros ina so ne muyi wata magana da tin ɗazu nake so inyi maka ita, Amman na zaɓi nan ne saboda naga yafi da cewa muyi ta a natse"
"Ehen ina jinka friend faɗa man minene kake son ji da baka san shi tattare dani ba"
Al'ameen ɗin ya faɗa yana mai gyara zaman shi gami da jingina bayan shi da makarin gadon.
Bilal ɗinne ya gyara zaman shi daga kan gadon sannan ya cigaba da faɗin "Ina so ne in san wacece matar nan da muka shiga ɗazu sashen ma'aikatan gidan ku muka dubo? Kuma wacece yarinyar da muka tada ɗakin? Menene alaƙarsu?"
Da kallo Al'ameen ɗin ya bishi na tsawon mintina biyu, ganin abokin nashi na so ya ɗauko mashi dogon labari gashi shi kuma bacci yake ji.
Ganin da yayi abokin nashi ya shiga koma ta tinani ne ya sanya shi sake faɗin" kayi haƙuri fa idan na shiga hurumin da ba nawa ba, Amman matar ta burge ni iya matuƙa, sannan bansan dalilin barin yarinyar ɗakin ba lokacin da muka shiga"
"Huh" Al'ameen ɗinne ya gumtsi fuska ya fesar lokacin da yake zamewa ya kwanta akan bayan shi yana rigingine yana kallon pop ɗin dake liƙe sama ɗakin da aka ƙawata da fitili masu matuƙa kyau, sai dai a kashe suke saboda dare yayi bacci suke so suyi, hannun shi duka biyu yasa ya tallafo kanshi dasu yayi matashi, lokaci ɗaya yana mai lumshe ido cikin sanyi halin shi na miskilai, a hankali ya buɗe bakin shi ya shiga furta "Frnd bacci nake ji mu bar maganar nan zuwa safe, ni yanzu tinani na yafi karkata akan dalilin da ya sanya umma ta kiraye ni cikin gaugawa"
Bilal ɗinne ya sauke dukkan ƙafafu nashi ƙasa daga kan gadon yana mai cewa "OK as you wish Bros, Amman ka sani na san halinka, baka komawa kan magana muddin aka yi ta ta wuce kenan, na lura baka son faɗa man ne, ina mai baka haƙuri akan shiga al'amurran ka da nayi, duk da na lura kana taka tsantsan" daga haka ya miƙe gami da shige wa toilet ɗin da yake ta cikin ɗakin.
Tinani da tarabbabi ya sanya Al'ameen ɗin ciki, tabbas bai kyauta ma aminin nashi ba, ya so kanshi da yawa, babu abin da suke ɓoye ma juna, abokan shawarar juna ne, ko wanne hali ɗaya ya shiga suna taruwa ne su warware natsalar su a tare, me Bilal ɗin ke son sani?shima bai san ita ɗin ko wacece ba, bai san umman Suhan ɗin ba kaman yanda ita ma kanta ɗiyar bata san kanta da ko ita wacece ba.
Bilal ɗinne ya fito yana tsane fuskar shi da ɗan ƙaramin towel, yayin da ya isa ga ƴar ƙaramar hangar kusa da mirror ɗin da ya mamaye kusan rabin bango ya maƙale shi cen, ya taka a hankali ya isa ga gadon gami da kwanciya yaja blanket ɗinshi mai taushi ya lulluɓe kusan rabin jikin shi
"Suhan, Umma Maryama"
Abunda Al'ameen ɗin ya faɗa kenan sound so husky, hakan ce ta sanya Bilal ɗin lamo yana sauraren shi, yayin da ya yi tsammani ma bacci ya kwashe shi, domin a yanda ya tafi ya bar shi a haka ya dawo ya iske shi, da alama ma ko matsin kirki baiyi ba, juyowa yayi yana mai fuskantar Al'ameen ɗin daga kwance.
"Nima ban san su ɗin ko su wanene ba," Al'ameen ɗin ya cigaba da magana ba tare da ya jira cewar Bilal ɗin komai ba, to shi ɗin ma baiyi niyyar tankawar ba, saboda ya san halin aminin nashi sarai.
"Shekarar su kusan sha bakwai a gidan namu, wannan baisa a san ko daga ina take ba tare da yarinyar dake hannun ta da take iƙirarin ita ce ta haife ta, sai dai sanin wanene mahaifi yarinyar, daga ina suke? Shine wannan sai ita umman, ciwon da Kaga mahaifiyar yarinya nayi Mom ɗita ce sanadi, wannan ce tasa Kaga ina basu kulawa daidai gwargwado" daga nan ya kwashe komai da ya sani ya faɗa ma Bilal ɗin na dangane da Rayuwar su Suhan ɗin, sannan ya ɗora da faɗin, "Bataso a taimaka masu ne ko alama, bansan minene matsala tata da hakan ba, na sha yunƙurin taimakon ta tana dakatar dani, Abunda na lura dashi ma, dukkan ma'aikatan gidan masalan matan, suna nuna masu wariya da ƙyarar su, Amman hali irin na Umman da take da haƙuri da tawakkali hakan bai nuna wata damuwa ko gazawa koda a fuskar ta ne kuwa, yanzun ma da ta amince da maganar karatun yarinya saida aka kai ruwa rana sannan, kuma ta gargaɗe ni da ɓoye duk wani taimako da zan masu dangane da karatun yarinya, ga dukkan alamu Mahaifiya ta ita ce babbar matsalar matar a gidan"
Dakatar dashi Bilal ɗin yayi gami da tambayar shi "yarinyar fa? Naga kaman bata son mu'amalan tar kowa a gidan ayadda na lura ko mutane ma kaman bata shiga, ka duba tin daga gaisuwar da tayi mana bata ƙara tankwa ba duk da a gaban idon ta muka gitta ta inda take zaune, ƙarshe ma Miƙewa tayi ta koma cikin sashen nasu"
Wannan karin, Al'ameen ɗin ne ya kalli Bilal ɗin ido cikin ido sannan ya shiga faɗin "Oho mata, ita wannan haka take, ban cika kula da al'amurran ta ba, Amman zan iya ce maka irin tarbiyyar da mahaifiyar tata ta bata kenan, bata saki jiki da kowa in ba mahaifiyar tata ba, hakan ya samo asali ne daga wariya da ƙyara daga sauran ƴan uwan nasu ma'aikata" ya faɗa yana mai ɗan taɓe bakin shi, sannan ya juya ya gyara kwanciyar shi gami da karanta addu'ar barci.
Ganin haka da Bilal ɗin yayi, ya san ba zai ƙara tankawa ba kenan ya kuma wuce da maganar kenan.
Shiru yayi shima yana mai hangen bayan kan Al'ameen ɗin da suma ta kwanta mashi luf abinshi, abun ka da farar fata sai yayi kaman wani ba'indiye, ta cikin haske dumlight ɗin da suka sanya mai ɗan duhu sosai kalar shuɗiya.
Shiru ɗakin yayi in banda ac dake aikin ta a hankali a hankali, sai kuma Bilal ɗin dake ta saƙa da warwara, idanun shi ƙyam akan murɗaɗɗen abokin nashi, da tini bacci yayi awon gaba dashi, yana ta sauke numfashi a hankali, a hankali.
Shima dai a haka baccin ya kwashe shi, washe gari duk suka haɗu a nan cikin gidan Alhaji Isuhun da duka nan suke karyawa da iyalan ƴaƴan nasu guda biyu watau Yaya Auwalu da Alhaji Mustapha Dambulan
Sai da kowa ya gama karyawa, har da Bilal ɗin kuwa sannan aka koma babban falon domin sake sabuwar gaisuwa ga iyayen nasu guda biyu da kuma sanya lokacin da za'a zauna meeting da ƙarfe biyu rana, wannan karo harda ƴan uwan nasu mata,watau Gwaggo Aisha da kuma Gwaggo Fatima dake aure nan cikin kankiya da kuma kannen su mata watau Hassana da Hussaina suma duk an masu waya, saboda irin wannan taron babban taro ne da yake ƙara haɗin zumunci da ɗabbaƙa shi, hatta da yaran su matan an kikkira su a waya, tinda ƴan uwan nasu duk sun zo har da waɗanda ke ma'aura ya kamata kowa yazo a gana a kuma ƙara sanin juna.
To sai mu ce Allah yasa ayi taro lafiya a kuma tashi lafiya Alhaji Isuhu family
~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~14~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Zama ne da akan yi duk lokacin da ɗaukacin family ɗin suke nan, wannan ma karon kowa ya hallara, Alhaji Isuhu ne tare da ƴaƴan shi maza suka fara zama, sun tattauna abubuwa masu mihimmanci wanda mafi akasari Yaya Auwalun ne ke zartar da hukuncin, kasancewar shi babba namiji, sai da suka kammala tattauna war su sannan aka umurci kowa da ya hallara a babban falon sashen Alhaji Isuhun, kowa ya zazzauna Amman banda gogan naku, hakan ce ta sanya Alhaji mustapha ɗaukar wayar shi ya kirawo shi tare da umurtar shi da yazo sashen iyayen nasu.
Taro ne da aka buɗe da addu'a bayan zuwan Yaya Ameen ɗin, inda aka gabatar da gaishe gaishe da kuma ƙara sani ga juna duk da dai kowa ya riga ya san kowa.
Alhaji Auwalu ne ya fara da godiya ga Allah subhanahu wa ta'ala, sannan ya ɗora da faɗin, "Ba dan komai muka tara ku anan ba sai dan kuji maƙasudin tara ku anan da hukumci da tsarin da muka zartar, kasancewar kowa ya san ba shawara muke tambayar ku ba, amman dai hakan ba zai hana mu jin naku ra'ayin ba, idan mun gama sanar daku Abunda muka tattauna da shi Alhaji gashi nan" ya faɗa yana mai nuna farin tsohon da yake zaune bisa kujera irin ta alfarma yana ta faman murmusawa da kallon jikokin nashi har ma da surukkan nashi guda biyu watau Hajiya Kubra da Mama Zainab dake zaune ɓangare guda, duk da kasancewar Mama Zainab ɗin babba ga hajiya Kubran, Amman kai kace ita ce babba, saboda jin daɗin da gogewar kai harma da suturar ba ɗaya ba.
"kai Aliyu, munsan buƙatar ka na anema maka auren Khadeeja, wanda mun yanke hukuncin nan ba da jimawa ba zamu je a nema maka auren" ya faɗa yana mai kallon babban ɗanɗan nashi namiji da ya sunkuyar da kai yana ɗan murmusawa, Yaya Auwalun ne ya cigaba da faɗin "sannan ku kuma Saudatu, da Nihal sai Hafsat (Ɗiya ga yaya Auwalun ta uku domin ta biyun mai suna Amina itama tayi aure har ma da ƴaƴan ta guda biyu, kuma itama tana zaune ne a wurin) kuma muna da buƙatar ku turo mana da manema aurenku zuwa gobe ko jibi domin mu tattauna dasu kuma mu basu izini" gabaki ɗaya sunkuyar da kai sukayi yayin da saudat ta zumɓuro baki ita fa bata shirya yin aure yanzu ba, dama Nihal ɗince mai saurayi, sannan ita hafsat dama tana da maneman ta masha Allah kasancewar ta nutsattsiyar yarinya ga kunya da girmama na gaba da ita, kyakkyawa ce masha Allah, domin su Nihal ɗin babu abin da zasu nuna mata.
Dakatawa yayi yana murmusawa tare da cewa idan Alhaji mustapha yana da magana yayi yana sauraren shi, to shi ɗinma cewa yayi babu sauran wani abu sai dai ko a cikin yayyen nasu mata idan da mai magana.
Goggo Aisha ce ta shigo da buƙatar tallafin karatun ƴaƴan nata maza da suka gama makarantar secondry yayin da Goggo Fatima tace ita kam babu abin da take buƙata, duk buƙatocin nata ƙannen nata sun gama mata komai sai Sam barka, tau suma ɗin dai haka Aunty Hassan a da hussainar babu abin da suka buƙata, sai godiya da suka shiga yi.
Yayin da aka tambayi su Hajiya Kubran dake Zaune gefe, Hajiya Zainab dai cewa tayi babu komai, yayin da Hajiya Kubra ta buɗe baki cikin isa, ta shiga faɗin "Maganar Al'ameen fa? Banji kunce komai ba dangane dashi, shima ya kamata ya fiddo mata cikin wannan lokacin, in ba haka ba zan zaɓo mashi da kaina cikin family ɗin ƴan uwa na ko kuma cikin ƴaƴan ƙawaye na" Alhaji mustapha ne ya shiga kallon ta cikin ɗaure fuska yayin da Yaya Auwalun ya shiga girgiza kai a hankali yana ɗan murmushi, kasancewar duk sun san halin ta ne ya sanya abun bai basu mamaki ba.
Shi kau Ya Ameen bazan iya fasalta yana yin da ya shiga ba, "wai me yasanya Mahaifiyar tashi take haka ne? Me yasanya idan zata yi abu bata tinani akai? Me yasanya, me ya sanya?" haka ya shiga furta wa cikin zuciyar shi da take ta kai komo, bugun zuciyar shi ya ƙaru, idan ko haka ne zai rufe bakin ta, zai bata mamaki, yana so ya cenza mata tinani, yana so ya cenza mata kallon da take yi ma kowa na bai isa ba sai ita kawai, yana son Mahaifiyar shi, ba zai so yana kallon ta tana tafiya bisa turbar da ba ita bace kuma ya sanya mata idanu ba.
Hajiya zuwaira ce ta sanya baki a karo na farko, tin zaman da aka fara kusan awa guda kenan da suka shuɗe, ita ɗin ma murmusawa tayi, yayin da ta kalli Hajiya Kubran ta shiga faɗin "Ke kau Kubura me yasanya kika sanya ma wannan mijin nawa ido ne wai? Mai mata kaman ni har a ce ya fiddo da aboki yar rayuwa, ko ba haka ba ma ai shi Ameenun baki ga yanda yake ba, wannan ma mai tsoron matan? Ina ce ma ni ban taɓa ganin ya tsaya kula ƴan mata ba ko jin labari" kowa sai da ya murmusa banda Hajiya Kubran da take zaune hakim ce gefe guda yayin da Hajiya Zainab mata ga yaya Auwalun ta ɗora da faɗin " wannan gaskiya ne Mama, kamata yayi a bashi lokaci ya fiddo a tsanake, kaman yanda Aleeyu yayi, gashinan abokanan shi har da masu mata biyu Amman shi sai yanzu ya samu ya lalubo, zaɓen aboki yar rayuwa ai abune mai wahala sai an bincika sosai.
Kowa yayi na'am da wannan maganar yayin da Hajiya Kubran ta Sake ɗaure fuska tana faɗin "Akwai ɗiyar Abokin wasa na Sen. Abubakar ɗan Malam, yarinya ce mai natsuwa, duk abin da ake buƙata mace da shi itama tana dashi, ta fito daga babban gida babban Family na yardar mashi yaje ya neme ta ni zan shige mashi gaba wajen aiwatar da komai" toh fa, Hajiya Kubra kenan, ita a ganin ta dukiyar ta arziƙin ta ya kai ta aiwatar da duk abin da take so, ta manta itama a ƙarƙashin wani take.
Wannan karon cikin ɗan zafin rai Alhaji Mustapha ya shiga faɗin "Babu wanda zai sanya in ma yaro na auren haɗi, bamu taso munga ana yi mana shi ba anan gidan, kuma duk mu muka zaɓo ku, haka su Yaya Aisha duk su suka kawo mazajen aure, in ma haɗin ne ai muna da yaran da suka taso gaban mu a cikin family ɗin gasu nan duk sun isa aure, Meyasa bamu ce ya zaɓa a ciki ba?"
Yaya Auwalu ne ya kamo hannun shi ganin abun na neman kwaɓewa, bai kamata a samu irin wannan saɓanin ba gaban yara, shi kau gogan naku, zaune yake kaman mutum mutumi, me yasa Mahaifiyar tashi take haka ne, mahaifan shi ke saɓani akan shi? Lallai babu wadda tayi mashi, baya kuma jin zai iya auren yarinyar da take nufi, kai shi Sam ma tarbiyyar ta bata yi mashi ba, dama ya kula da yanda take shisshige mashi idan yaje gidan, ashe da biyu ma Mahaifiyar tashi ke aikenshi gidan, itama yarinyar dalilin da yasa take mashi wasu abubuwan kenan? Sai yanzu ma zuciyar shi ta shiga hararo mashi wasu abubuwan, yayi nisa a cikin tunanin yayin da idanu wan shi suke rufe ya tsinkayo maganar wan Mahaifin nashi yana cewa "ya isa Mustapha, Ya isa su ai mata ne, tinanin su ragagge ne, kuma duk wannan abun dake faruwa shi yaron ai gashi gaban ku zaune, har yanzu bai tanka ba, bama mu sani ba shin ko akwai wadda tayi mashi cikin rai? Ko akwai wadda suke tare? A bari aji ta bakinshi tukunna" yayin da ya maida kallon shi ga Al'ameen ɗin sannan ya cigaba da faɗin
"Shin Kai Al'ameen a cikin ranka akwai wadda kake so kuka yi maganar aure da ita? Ko akwai wadda ka yima Alƙawarin aure ne?
Falon yayi tsit, baka jin komai sai ƙarar ac da take ta aikin ta ahankali ahankali, kowa ya maida hankalin shi da natsuwar tashi akan Yaya Al'ameen ɗin, yayin da kanshi yake ƙasa, da yawa daga cikin ƴan matan da suke falon suna so ace sune ya zaɓa a matsayin aboki yar Rayuwar shi, Al'ameen ɗin ɗaya ne tamkar da dubu, komai ya haɗa, kyau, natsuwa, ilimi, gayu, ga uwa uba naira, runtse idanu shi ya sake yi gam, yayin da yake jinjina girman maganar da zata fito daga bakin shi, ahankali ya buɗe idanun nashi ya fara ɗora wa akan kakan nashi, Alhaji Isuhu da shima kaf natsuwar shi na akan jikan nashi, kaka zuwaira ya kalla ta sakar mashi murmushi irin nasu na dattawan da suke cike da natsuwa da kuma dace da ƴaƴa nagari, sannan ya ɗauke kallon shi kacokam ya ɗora shi akan Mahaifiyar tashi da ta cika fam, uwa zata fashe, dan dai wayewa da kuma halin tarin rai irin nata, Sam bata kawo ma ranta cewa yaron nata zai bijire ma buƙata tata ba, na amsar tayin ƴar ɗan uwanta da tayi mashi ba gaban kowa, bata yi tinanin zai watsa mata ƙasa a ido ba.
Kallon shi ya maida kan iyayen nashi maza biyu da suke zaman jiran cewa shi, sake ajiyar zuciya yayi ahankali, yayin da ya gyara zaman shi kan lallausan carpet ɗin da ya malale ilahirin falon, sannan ya nisa ya cigaba da faɗin " Eh ABBA, Akwai wadda muka yi Alƙawarin Aure, sai dai kuyi haƙuri jin ko wacece, Nidai ita nake so, kuma itama tana so na, kuma ina mai roƙon alfarmar da aura man ita, ita na zaɓa a matsayin abokiyar rayuwa ta, uwar ƴaƴa na, tarbiyyar ta tayi mun, komai nata yayi mun, kuma, kuma ina mai roƙon ta yi maku kaman yanda tayi mun"
Ya faɗa cikin salon maganar shi mai kama da ta saraki, sannan ya ƙara she yana duƙar da kai alamar roƙo da girmamawa ga iyayen nashi har dama kakannin nashi da suke zaune a wajen.
Murmushi Alhaji Isuhun ya sake cikin halin dattako ya shiga faɗin " Alhamdulillahi Faɗi kanka tsaye Ameenullah, nan kowa jiran yaji taka zaɓen yake yi, in da hali sai a haɗa da na shi Aleeyu baki ɗaya ma a wuce wurin.
Toh fa! kan kowa da yake zaune a falon ya ƙulle, har da mahaifan shi Al'ameen ɗin watau Hajiya Kubran da Alhaji Mustaphan, Aunty Feena ce ta kalli ƙanen nata cikin wasiwasi da tarabbabi, kada ya janyo masu wani abun kuma, ita ta san bayada wata budurwa da yake so, kuma ta san babu wacce yayi ma Alƙawarin aure, toh fa! Kaman zata ce wani abu sai kuma tayi shiru, ganin Al'ameen ɗin ya fara magana
"Abba Hauwa'u ce ta gidan mu watau Suhaann.. ɗiyar Ma.. Ma Maryama ta ɓangare masu aiki"
Salati Hajiya Kubra ta sake tana mai miƙewa tsaye tana taɓa hannuwa kaman wata sakarai, jin maganar tayi kaman saukar aradu, sakin baki tayi, yayin da su kuma su Nihal suka ƙwalalo idanu, ba su ba har Aunty feenar ma ta shiga komar mamaki, Afnan kuwa murna da farin ciki ne suka mamaye ranta, Aunty Suhan fa! Ko dai kunnen ta ne ke gaya mata ba daidai ba? Nihal ce ta shiga zumɓuro baki tana faɗin wallahi yaya a'a mai aikin mu ce fa?
Murmushi Alhaji Mustaphan yayi, ko babu komai ya san dalilin yaron nashi na yin hakan, tabbas ya jinjina ma yaron nashi, yayi na'am kuma da buƙatar tashi, sannan kuma ya bashi goyon baya ɗari bisa ɗari, jinjina kai ya shiga yi yana faɗin "Masha Allah, haka ake so Al'ameen yarinya tayi, kuma ina tare da kai, insha Allah zan shige maka gaba wajen ganin komai ya daidaita" yayin da Hajiya Kubran ta koma ta zauna bisa kujera inda ta tashi tana faɗin "kai shashasha ne Ameenu? Ashe baka da hankali? Me zaka ci da wannan yarinyar? To bari kaji ban yadda ba ka auri yarinyar da bata da asali koda kuwa ace mata sun ƙare ne a duniya, Ban yadda ba Sam, idan ba haka ba kuwa zaka gamu da fushi na, au ashe dama munafintata kake yi? Kana cen kana soyayya da wannan ƴar jariri yar abun? Sam ban lamunta ba, Alhaji har kana faɗin ka yarda, tau bari kuji ni Sam ban yarda Bako sama da ƙasa zasu haɗe bazan lamunci wannan auren ba"
Alhaji Auwalu ne ya shiga kwantar mata da hankali yana faɗin "Kai Mustaphan bamu gane yarinyar da yake faɗi ba, kar dai ace yarinyar da aka zo da ita a goye gidan ka, ɗiyar wannan mai aikin?"
Jinjina mashi kai Alhaji Mustaphan yayi cikin son bashi tabbaci, yaya Auwalun ne ya shiga faɗin ai ko hajiya ta yadda mu ba zamu yadda da wannan abun ba har sai an nemo asalin ita yarinyar, kai Ameenu ka bamu lokaci zamuyi ƙwaƙƙwaran bincike akai, kuma bamu ce ka cigaba da neman yarinyar ba har sai mun samu cikakke bayani akan ta,
Alhaji Mustaphan ne ya shiga faɗin hakan yayi daidai, zamu bincika bayan wannan yarinyar bata da wani abun da za'a ce an kasa auren ta, kasancewar ta ɗiyar mai aiki, wannan ba hujja bace, ni na yarda da yarinyar da kuma tarbiyyar ta, Allah yayi maka albarka Al'ameen kayi Abunda ake so, ina alfahari da kai da wannan tausayi da jin ƙai da kake tare dashi, Allah ya ƙara ma Rayuwar ka Albarka duniya da lahira"
Da ameen kowa ya amsa, yayin da Hajiya Kubra ta miƙe ta fice daga falon kaman zata fashe, da kallo kowa ya bita yayin da wasu suka shiga jinjina kai, shi kau Al'ameen ɗin duƙar da kanshi ya sake yi ya maida idanu shi ya kulle, me ya sanya shi yin hakan? Me ya janyo mashi? Yana so ne Mahaifiyar tashi ta canza halin ta akan masu aiki, yana so ne ta gane mecece duniya da Abunda ke cikin ta, Suhan ɗin alkhairi ce duk da kasancewar irin taƙaddamar dake cikin auren, ba soyayya tsakanin shi da yarinya Sam, bata ma san wainar da ake toyawa ba, kuma da wanne ido ma zai kalle ta yace mata ita ce ya zaɓa a matsayin wadda zai aura? Ta yaya zata kalli abun? Ta yaya ummanta zata fassara abun? Baya tinanin idan har umman bata yadda ba ko ta bada goyon baya ba abun idan zai yuwu.
*Wacece Suhan ɗin???*
Tambayar da ya shiga yi ma kanshi kenan
Nisawa yayi yana mai sakin ajiyar zuciya ahankali ahankali, yayin da ya kai kallon shi kan sauran ƴan uwa nashi, tashin hankali da ƙyara ƙarara ya hango cikin idanu saudat da Nihal ɗin tau sai dai shi ba tasu yaje yi ba, yana hango Abunda zai faru ne nan gaba, da irin ƙalubalen da zai fuskanta nan gaba wajen Mahaifiyar tashi, gashi har ta fusata ma tabar falon, dama ya san hakan ce zata kasance, kuma shi baya jin idan zai iya janye maganar shi, hakan ma wata dama ce da yarinyar zata iya tantance wacece ita.
Alhaji Auwalun ne ya shiga kwantar mashi da hankali, yana faɗin ba zamu ƙi amince maka ba, muddin muka ga babu abun ƙi tattare da asalin yarinyar, sannan muna mai baka shawara ka koma ku sasanta da Mahaifiyar ka, saboda abun yayi maka albarka, idan babu mai magana zamu rufe taro da addu'a da kuma sanya ran cewa manema auren saudat da Nihal ɗin zasu zo gobe idan Allah ya kai mu.
Babu wanda yace komai, kowa da Abunda yake saƙawa acikin ran ta, abie ma ba zamu iya tantance halin da yake ciki ba, mutum ne mai zurfi ciki, kusan ma yaso yafi Al'ameen ɗin, tau sai dai shi ɗan ɓangare Hajiya Kubran ne, sai abin da tace, ko ta zartar, saɓanin Al'ameen ɗin da komin yake biyayya yaga za'a kauce ma gaskiya baya bin wannan ayarin.
A haka aka kulle taro da addu'a yayin da iyayen nasu maza suka cigaba da zama wannan karon har da mama zuwaira ɗin domin su ƙara tattaunawa
Kowa ɓangare shi ya wuce, wannan ce ta sanya suma su Nihal ɗin komawa cikin nasu sashen inda suka tarar da hajiya Kubran zaune tana ta faman cika, zaman jiran Alhaji ya shigo domin ita ba da Al'ameen ɗin zata yi ba da wanda ya ɗaure mashi gindin yin abun zata yi, zata ji dalili, kuma tabbas zaman munafukar matar cen ya ƙare a gidana tinda so ake a mallake man ɗanɗa na. Abunda take ta faɗa kenan yayin da ta miƙe ta shiga safa da marwa, su dai aunty Feena da afnan ɗaki suka shige yayin da su saudat suka zauna suna ta ƙara yi mata famfo da ingiza mai kantu akan al'amari, muddin aka ce yarinyar cen ta auri yayan nasu ai sun kaɗe, yarinyar da babu irin wulaƙanci da tozarcin da basu yi mata ba, Amman ace wai zata zama aunty su, tabɗijam "lallai Mom baki ga ta zama ba" cewar Saudat ɗin
°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Kai tsaye ɗaki shi ya wuce, kayan shi kawai ya cire ya faɗa toilet ɗin ya sakar ma kanshi shower, ko sauraren Bilal ɗin baiyi ba, da yake ta mashi magana, shi ɗin ma ya san halin ƴan kayanshi, ba zai samu amsa ba, balle ma ya lura da condition ɗin abokin nashi, anya kuwa wani abu bai faru ba a zaman taron na family ɗin? Yana cikin tinani Al'ameen ɗin ya fito daga toilet, ƙugunshi ɗaure da fari ƙar ɗin towel, yana ɗauke da ɗan ƙarami yana tsane kanshi, jikin shi ko ina gargasa ce kwance luf, baƙa siɗik, abun ka da farar fata, sai tayi mashii gwanin kyau, ko kaya bai tsay Sanyawa ba, balle ya cire towel ɗin ya faɗa kan gadon yayi rigingine fuskar shi na kallon cilling.
Kafaɗarshi Bilal ɗin ya dafa yana daga kwance "Man me ya faru ne? Ka gaya man na lura baka cikin natsuwa" kaman yana jiran cewar Bilal ɗin ya shiga faɗin "Friend na yanke ɗanye hukunci, ba tare da nayi tinani ba, Friend why? Me yasa nayi haka? Anya kuwa ban sha wani abu ba? Friend gaya man" ya faɗa yana mai tashi zaune ya juyo sosai busa gadon yana fuskantar abokin nashi, idanu shi sun kaɗa sunyi jajur dasu
"Yarinyar tausayin su kawai nake yi, babu soyayyar ta ko ɗigo cikin raina game da ita, me yasa haka? Na jawo ma kaina raini, duk dan in faɗa kar da mahaifiya ta akan illar tsanar mutum haka kawai, yaya Mahaifiyar ta zata kalli abun, miƙewa yayi yana mai gyara zaman to wel ɗin a jikin shi, ya shiga taka wa a hankali cikin ɗakin, kai komo ya shiga yi cikin ɗakin kaman yana neman wani abu.
Miƙewa Bilal ɗin shima yayi yana mai kamo hannun abokin nashi, tabbas ya san duk lokacin da yaga abokin nashi cikin irin wannan halin yana buƙata neman taimako ne.
Zaunar dashi yayi bisa sofar dake ɗakin mai zaman mutum biyu, "Cool down Friend, ka natsu ka gaya man meke faruwa ne?" kaman yana jiran shi ya ɗan zabura ya zamo daga bisa kujerar kaman zai zauna ƙasa, yayin da ya kama hannun Bilal ɗin ya runtse shi sosai, kaman zai tsinke hannun "Friend ni na zaɓe ta da kaina, ni na amince ma auren ta da kaina, yarinyar da ka gani jiya a gidanmu, na amince zan aure ta, Friend ka bani shawara, how am i going to do? Wannan ƴar yarinyar Friend, ko aure zanyi Ai tayi man kaɗan, Amman nine da bakina nace su Abba su nema man auren ta Friend ya zanyi? Bata san meke faruwa ba, bata san zan iya yanke wannan ɗanyen hukunci a kanmu ba, zata so ni? Zata yarda dani? Mahaifiyarta zata amince mani? Ya faɗa yana miƙewa tsaye, shima ɗin dai Bilal ɗin a kiɗime ya miƙe jin abin da abokin nashi yake faɗa mai kama da almara, mai kama da tatsuniya.
*"WHAT"*
*Al'ameen Are U In Your Sense?*
Bilal ɗin ya shiga faɗi a kiɗime cikin ɗaga murya, yana fatan kunnen shi basu ji mashi daidai ba, yana fatan ace mafarki yake yi, ina Al'ameen ɗin ina ƴar aiki, marar galihu, jiya jiya nan fa da daddare Al'ameen ɗin ke ce mashi ba'a san asalin yarinyar ba, inko haka ne me ya ja ma abokin nashi? Me ya shiga kanshi, saɓanin abin da yake son yaji ne ya shiga faruwa, lallai Al'ameen ɗinne ya shiga gƴaɗa mashi kai cikin tabbatas wa, da kuma neman mafita.
~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:25 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*
*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)
*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)
*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.
*Page ~15~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
"Hajiya Laila kina jina ko? Ki bani way out please ƙawata, ɗan cikina ne zai auri ƴar talaka? Talakan na ma'aikaciyar gida na? Wadda bata da komai, bata da asalin kirki ma? Kai ina ba zai taɓa yiwuwa ba sam wallahi"
Hajiya kubra ce riƙe da waya a hannun ta da alama waya take yi tin bayan shigar ta sashen nasu, ko zama t akasa yi sai kai kawo take yi a tsakanin tanƙamemen falon nasu da yaji kayan alatu kaman ba za'a mutu ba
"ina jin ki Hajiya Kubra" daga ɗaya ɓangaren aka bata amsa cikin isa da izza ga dukkan alamu dai ƙawarta ce.
"Ba kina jina zaki ce ba Hajiya Laila, mafita nake nema, kin dai sanni, kinsan buri na, kin kuma san yanda nake ƙaunar Al'ameen a duk cikin ƴaƴa na"
Ta tari numfashin Hajiya Laila cikin sauri
"Gaskiya ne Hajiya ta, ai wannan maganar ba ta waya bace, anya ma kuwa ba asiri sukayi mashi ba? Kin san fa tin lokacin da kika kula da shisshige masun da yake yi ya kamata ace kin taka ma abun burki, Amman son da kike mashi ya hana"
"Hajiya Laila wallahi nayi ƙoƙarin hakan tin lokacin, Amman ɗan banzan yaron nan yaƙi bani haɗin kai, kin dai sanshi da shegen zurfi ciki, da kuma miskilanci, ni kaina rasa gane kanshi nake yi"
Hajiya Laila ce ta tari numfashin hajiya kubran da cewa, "ba kince su keyi maku girki ba?". "Eh kwarai kuwa hajiya, in ba girkin su ba baya cin na kowa wlh" humm, Hajiya laila ta numfasa gami da sakin wani ɗan guntun murmushi ta cen ɓangaren, sannan ta ɗora da faɗin
"To wallahi ina mai tabbatar maki a nan suka samu, suka samu abin da suka barbaɗa mashi yaci, yanzu abin da nake so dake ki kwantar da hankalin ki, abun zai zo mana da sauƙi, kedai kiyi ƙoƙarin dawowa akan lokaci"
Nisawa Hajiya Kubra tayi cikin ƙunar zuciya da tsanani ɓacin rai, kaman zata haɗiyi zuciya ta mutu, sannan ta cigaba da cewa
"Shikenan Hajiya Laila, ina so please kiyi tinanin neman mafita, saboda ni duka ma kaina ya ƙulle wallahi, gabaki ɗaya yaron nan so yake ya birki ta mani lissafi, na yarda dake ne, insha Allahu kuma zanyi ƙoƙarin ganin na dawo akan lokaci, yanzu ma zuwan maneman su suhan ne kawai zai tsaida ni"
"Is OK Hajiya Kubra, baki da damuwa ki kwantas da hankalin ki, ina mai tabbatar maki da maganar nan zata sha ruwa, ko shi Alhajin da ya goya mashi baya, ba zai ma ƙara tada maganar ba, balle wani Alhaji Auwalu cen, da zaki ɗaga hankalin ki aka shi;To ko Isuhun ma bai isa ba balle ƴaƴanshi"😒
Hajiya Kubran ce ta murmusa mai cike da yaƙe, "Humm Hajiya Laila kenan, baki da dama, haka nake so, Shiyasa nake son ki nafi yadda dake akan kowa cikin ƙawaye na, na mayar dake aminiyata ta hannun dama ta, wuƙa da nama na hannun ki, a fara komai kafin in dawo, zan tura maki duk abin da za'a buƙata"
"Ba damuwa Hajiya Laila, ke dai sai kin dawo dai, ƙibar komai a hannuna, sai mun yi magana"
"OK shikenan a huta lafiya Hajiya Laila, sai Naji daga gare ki" ta faɗa tana mai datse kiran gami da zama cikin ɗan samun sassauci, saboda sanin halin hatsabibancin ƙawar tata, komai take so mai sauƙi samu ne, indai tabi ta hannun amini yar tata.
**************
"Look Friend kayi gaggawar yanke hukunci, aure ba abu bane da akeyi mashi hawan ƙawara, yarinya r zaka iya taimako ta, ba sai ka aure ta ba, ina so ka sani aure babu soyayya ba abu ne da ke ɗorewa ba, masalan yanda zaka yi manage na zama da ita, a yanda na san ka yarinyar bata yi daidai da ra'ayin ka ba, beside ma mahaifiyar ka...... "
Dakatar dashi Al'ameen ɗin yayi, ta hanyar ɗaga mashi hannu," Bilal! Please mubar maganar haka, kayi man addu'a kawai" abin da ya faɗa kenan, ya miƙe a hankali ya zura kayanshi, gami da zarar keys ɗinshi na mota ya fice daga gidan ma baki ɗaya.
Da kallo abokin nashi ya bishi dashi, "Hooo Al'ameen kenan, ko sai yaushe zai cenza? Kaman bashi bane yanzu yake neman way out, yaro kaman mai bira'izai? Wannan ko auren yayi wahalar da yarinyar kawai zai yi, bai iya wata soyayya ba, balle ya tsaya bata kulawar da ta dace, kullum kai kenan a murɗe? A baibai? Humm" ya faɗa a fili yana mai miƙewa shima ya fice daga ɗakin zuwa cikin lambu.
***********
Da sallama ya shiga sashen nasu, fuskar shi a matuƙar ɗaure, ko babu komai ya san bata kyauta mashi ba, a gaban kowa ciki har da iyayen shi ma, Amman taso tayi jayayya dashi, har tana ɗaga murya akan kowa da ficewa ma baki ɗaya daga perlour ɗin, dole ya nuna mata ɓacin ran shi, alwashi ne ya sha shi aure sai anyi, zai ga wanda yake gaba, cikin shi da ita; ko ɓangaren da take bai kalla ba, ya wuce kai tsaye zuwa bedroom ɗinshi domin wanka da shirya ma zuwa sallar magariba da ta gabato.
Haka yazo ya sake wuce ta, tana zaune tana kumburin ta da kaɗa ƙafa ɗaya dake kan ɗayar, Hajiya Kubra kenan, ai shi duk abin da Allah ya tsara baki da kuɗin da zaki cenza ikon shi akan komai
Itama tana kallon shi, Amman yanzu kam duk son da take ma Alhajin, zata danne shi ne, ba zata taɓa bari da girman ta, da ajinta ba, ta tozarta, to ai ajinta ma ya zube in har ta bari ƙawayenta suka ga wadda ɗanɗan nata yake son auro mata a matsayin suruka, yarinyar ƴar ƙauye da babu abin da ta iya sai bauta, sam Suhan ɗin ba ajin *Moh'd Al'ameen Al-Mustapha Dambulan* ɗin nata bace.
Wannan ce tasa har ya kuma fitowa ya fice baki ɗaya daga gidan bata kula shi ba, tasha Alwashin yi ma abun tufkar hanci, ba Alhajin ne yake taƙama dashi ba? To wannan karon har shi ba zata ƙyale shi ba.
-----------
Haka kuwa aka yi, washe gari da wuri maneman auren su Nihal ɗin suka iso, masha Allah yara ne ƴan gayu, ƴaƴan masu faɗa aji, kaman yanda hafsat ɗin take kamila da sanyin hali haka shima saurayi nata yake, kowa yayi mamakin shi duk da, da alama naira ta jiƙa shi sosai, Amman baya da jin kai irin na sauran masalan saurayi Nihal ɗin, ahaf, ai kowa yana samun daidai dashi ne, basu jima ba sosai bayan sun gabatar da kansu, iyayen na su saudat suka ga, ai iyayen nasu ba baƙi ma bane a wajen su, umurtar su sukayi da su turo su domin tsaida lokacin aure,
Abun Alkhairi sosai suka ba yaran su Goggo Aisha, sukayi ta Sam barka da sanya alkhairi, basu tafi ba sai da Kaka zuwaira ta zo ta zazzaulaye su, cikin wasa irin na kaka da jika, hakan ya ƙara faranta ran su, domin su ɗin dama sangartattun ƴan gata ne, sun saba zaulayar granny ɗinsu at any moment.
Atare suka koma zuwa Abuja gabaki ɗaya, bayan kammala zumuncin irin na wannan lokacin, da yazo da saɓani da abubuwan farin ciki da dama.
Ta ɓangaren Hajiya Kubran kuwa, har yanzu sama sama suke da Alhajin, domin ya sha Alwashin gargaɗar ta da kuma yi mashi katsalandan acikin Al'amari auren yaron nashi.
Kowa da Abunda yake saƙawa cikin zuciyar shi har ƙarasowar su zuwa cikin gidan, wannan ce ta sanya bamu san da labarin dawowar tasu ba, kowa part ɗinshi ya wuce kai tsaye, duk da suna farin cikin gabatar da masoya nasu ga iyayen su, Amman ta ɓangaren guda, ƙudirin yayan nasu ya kasa barin zuciyar su, haƙiƙa wannan labari ne mai muni, labari ne mafi ƙona zuciya da suka taɓa ji tin bayan mallakar hankalin kansu.
Al'ameen kuwa, Daurewa kawai yake yi wajen amsa ma abokin nashi duk maganar da yayi mashi, ziyara ya kawo mashi, baya so yaga kaman yana wulaƙanta shi ne, ta ɓangaren Bilal ɗin kuwa yayi mashi uziri, ya san damuwar abokin nashi, ya sani sarai, ya yanke hukunci ne cikin fushi, gashi abun yazo daga baya yana damun shi, kuma shi ba irin mutanen da suke amai su lashe bane, ya sani, koda za'a dinga yankar naman jikin shi, ba zai koma yace ya fasa ba, ba zai warware nuƙatar tashi ta auren Suhan ɗin wajen iyayen shi ba,koda kuwa hakan na nufin faruwar mummuna abu ne a gareshi.
*****
Tura ƙofar aka yi, gami da shiga cikin ɗaki kai tsaye, wucewa tayi i zuwa ga bakin gadon ta samu ta zauna, sanye take cikin kayan bacci irin masu mugun tashin nan, sai walƙiya take, Hajiya kubra kenan, ikon Allah,
"Alhaji nazo ne muyi magana da kai"
Shiru yayi mata kaman ma baya cikin ɗakin
Bata saurare shi ba, ta cigaba da faɗar Abunda ke cikin zuciyar ta.
"Alhaji ina so ne fa ka sani, ina nan kan baka na, lamarin auren Al'ameen da yarinyar cen ta sashen masu aiki, ban yarda dashi ba har yanzu, bana kuma tinanin zan yarda har abada, ni ce na haife shi, baya da ikon yin abun da ban yarda mashi yayi ba, mu ne gaba dashi, ba shine gaba damu ba, mune muka haife shi, ba shine ya haife mu ba, ina so ka sani muddin ya sake ya auri yarinyar nan, zan mugun saɓa mashi, bana so ka bashi goyon bayan auren baiwar mu..... "
" Ya isa Kubra, ya isa hakanan nace"
ya katse ta cikin tsanani ɓacin rai, da tsawar da ta gigita ta, har ta miƙe tsaye bata sani ba, to ita ai bata ma san lokacin da ya miƙe zaune ba.
"Idan baki son in saɓa maki ƙibar maganar nan, ina so ki sani muddin baki bashi damar auren yarinyar ba, to fa lallai ne ki bashi dama ya zaɓi wadda tayi mashi, namiji ne, mata ma bamuyi masu dole ba balle maza, namijin ma kaman Moh'd Al'ameen, Kubra me yasa baki tinani ne wai in zakiyi abu?kin gama tozarta ni gaban ƴan uwan nawa da ƴaƴan nawa, shine kika biyo ni nan ki sake ƙarawa? Yaushe har abun naki ya kai haka ban sani ba? Toh ina so ki sani, duk hukunci da na yanke nan gidan akan ƴa] a na ya yanku, ni ne sama dake acikin gidan nan, kuma dole kema kibi abin da nake so, ina so ki sani, maganar sake yin aikin Maryama da yarinyar ta acikin gidan nan na haramta shi, kaman yanda na faɗa maki acen baya, ban barsu sunyi aiki ba, ada cen saboda lafiya su, balle yanzu da suka zama *Surukkai na"*
A razane ta kalle shi, "Alhaji Surukkai fa kace? Yaushe har suka zama surukkan ka?"
"Ah to nadau faɗa maki, kuma abin da nace kenan, na gama magana, zaki iya cigaba da faɗar dukkan Abunda ke ran ki, ruwan ki ne ki ƙyale yaro yayi Abunda yaga ya fiye mashi, ko kuma ki sanya ya fara bijire ma umarnin ki, da biyayyar da yake maki" yana gama faɗar haka ya koma ya kwanta, gami da jan bargo ya lulluɓe jikin shi, sannan ya sanya hannu ya kashe dumlight ɗin ma gaba ɗaya, ɗakin ya gauraye da duhu.
Ƙutawa tayi, gami da tashi ta fice daga ɗakin zuwa nata, tana mai ƙudurce abubuwa da dama acikin ranta.
*********
"Son" Alhajin ya kira sunan yaron nashi da yake zaune bisa kujera mai cin mutum ɗaya, hakan ce ta sanya shi ɗago kyawawan udanun nashi ya ɗora su akan dad ɗin nashi, shigowa shi kenan part ɗin mahaifi nashi domin har yanzu ya kasa tun ƙarar mahaifiyar tashi,
"Ina so ka ƙara tabbatar mani da maganar da ka faɗa a cen kankiya kan yarinyar nan, shin da gaske kana so ta?" Alhajin ya jefa mashi da tambayar bazata da ta ƙara ruɗa shi, ƙasa yayi da kanshi yana mai murza yatsun hannun shi, ya ma rasa me zai faɗa ma dad ɗin nashi.
" Eh Abba, da gaske nake, ina so ta, kuma a shirye nake da in taimaka mata. "
Ya faɗa ciki-ciki, sai dai duk da haka Alhajin ya ji shi,
"OK Son, Abunda nake so da kai, kabar maganar nan for now, saboda hajiya ta huro wuta, hakan zai sanya ta matsa ma zaman su acikin gidan nan, akwai abubuwa da dama gabanmu, na san mahaifiyar ka ko wacece, hakan zai sa tayi tinanin mun bar maganar ne, to sai dai zamu shirya dukkan Abunda zai yuwu ne bayan mun gano asalin ita yarinyar, talauci ko rashin mahaifi ba zai sanya in kasa barin ka ka aure ta ba, ina so ka sani, ni ba kaman mahaifiyarka nake ba, kuma itama ina mata addu'ar Allah ubangiji ya shirya ta, ta gane gaskiya" da ameen ya amsa iya maƙoshi, sannan Alhajin ya ɗora da faɗin
"Maganar karatun yarinyar, ina so kayi dukkan mai yuwuwa ta tafi makaranta, hakan zai bamu damar bincike na haƙiƙa, dole kuma sai da haɗin kan mahaifiyar yarinyar, sannan kaje ku daidaita da mahaifiyar ka, ga nemi gafarar ɓata mata da kayi, hakan ba yana nufin ka janye maganar auren naka ba, ina so kuma ka cire dukkan wata damuwa da ke cikin ranka, komai Kaga ya yuwu yi ne na Allah, na san dalilin ka na son auren yarinyar, nima na bada goyon baya ɗari bisa ɗari, Allah ya tabbatar mana da Alkahirinsa.
Nan ma da ameen ya amsa cikin zuciya, Alhajin ne ya wayance ya shiga janshi da firar kasuwanci, da shirin buɗe sabon estate ɗin su mai suna *Dambulan estate* da za'ayi zuwa ƙarshen shekara, wadda take mallaki Al'ameen ɗin.
Da haka ne ya samu ya saki jiki dashi, nan suka karya su uku, har da Bilal ɗin da ya shigo daga baya gaishe da Alhajin, bayan sun gama ne suka fice atare da Alhajin kaman wasu abokan shi.
Jikin Ummantawa yayi sauƙi sai Sam barka, hankalinmu a kwance, saboda ƴannkuɗaɗen da ya Ameen ɗin ya bamu, su ne muke riritawa da siyan abubuwan da likita ya gindaya ma umman tawa cinsu, tin bayan tafiyar su hajiya da kwana ɗaya bamu sake jin ɗuriyar shi ya Ameen ɗin ba, sai bayan dawowa su ne, saƙo ya iske mu, na dakatar damu daga aikin gidan gabaki ɗaya da aka yi daga bakin mama talatin, a cewar ta wai saboda jikin umman tawa, to mu dai duk da haka jikinmu yayi sanyi kwarai matuƙa, sai dai gudun sanya zargi wani abu, ko damuwa ya sanya muka kauda dukkan wani shakku a cikin ranmu game da hakan.
Hankalinmu bai ƙara tashi ba saida aka dena bamu abinci gabaki ɗaya, mun gane hakan ne ta yau da safe da na kai cooler ɗinmu kitchen a zuba mana abinci, sai mama sauden (mai girkin ma'aikata) tace man ya ƙare, abun ya bani mamaki sosai, sai na share na koma ɗaki na haɗa tea cikin kayan da ya ameen ɗin ya siyo mana kafin ya tafi na sha.
Da rana ma hakan ce ta kasance, wannan karon free ta fito ta faɗi man cewa an dakatar da bamu abinci a cikin gidan, saboda yanzu mu ba ma'aikata bane, abun ya bamu matuƙar mamaki, me hakan ke nufi ne? Ko dai wani ne ya ja mana wani sharri kuma? Umma ta ce ta bani haƙuri, da unurtata kada in sake komawa amso abinci, har saida suka mula, suka sha iska dan kansu suka bamu.
Ɗan Abunda ke gare mu a ɗaki, shi muka dinga ci ni da ni da umma ta, sai gashi nima na koma cin abunda masu ciwon zuciya suke ci; amman ya zamuyi? Dole mu haƙura, babu, ce da zama ƙarƙashin wani ya ja mana. Amman ace a gida irin wannan ya wuce ace ana irin haka ga masu aiki, sai dai in da wani abu a ƙasa.
****************
Da sallama ya shiga cikin ƙayataccen sashen nata, tana zaune bisa kujera tana waya da ƙawarta Hajiya Laila, cewa tayi ta bata minti biyu zata sake kiran ta, kashe wayar tayi tana mai amsa mashi gaisuwar da yake mata ciki ciki tayi, sannan ta ɗora da faɗin "ya aka yi ne Al'ameen?"
"Mom kiyi haƙuri please, babu kyau iyaye na fushi da ƴaƴansu nazo ne in baki haƙuri" ya faɗa a taƙaice idanun shi na bisa fuskar ta don ganin yanda zatayi
Ɗan guntun murmushi ta saki, cikin duniya ci tace "haba son menene haka? Ai ya riga da ya wuce, na san ba zaka yi Abunda zai ɓata man rai ba, Allah yayi maka Albarka" ina so kaje ka yankar ma su Afnan ticket saboda zuwa anjima zasu wuce, hutun nasu ya ƙare kada su rasa flight"
"OK ya faɗa yana mai miƙewa cikin salon tafiyar shi ya taka ya fice daga part ɗin na mahaifiyar shi, da tin dawowar su bai shige shi ba sai yau, saboda bai san abin da zai je ya tada ba, zuciyar shi cike da wasu wasu, me mahaifiyar tashi take ƙullawa ne? Shi fa yayi mamakin sauri saukowa ta, Amman koma minene zai bita ta ƙarƙashin ƙasa in ta san wata ai bata san wata ba.
Ita kuwa a ɓangaren ta, da murmushi ta bishi tana faɗin "yaro yaro ne, koda kuw ɗan giwa ne, kaman yanda ka bari cikin cikina, Al'ameen ka bar maryam da ɗiyar ta har Abadan abada, hhhhh" ta kyalƙyale da dariya shu'umanci, domin kuwa hajiya Lailan ta bata tabbacin hakan, ita kuma ta yarda da hajiya Lailan ɗari bisa ɗari, in tace zata yi, to fa zata yin ne, koda kuwa sama ce zata haɗe da ƙasan.
~Toh fa! Anya kuwa Hajiya Kubra Alkhairi take ƙullawa kuwa 🤔~
~Ya makoma Suhan da Umman ta a Rayuwar da ake ciki na hana su abincin da zasu ci ma?~
~Al'ameen kuwa ya bar maganar auren suhan ɗin? Ko dai irin abun nan yayi mata na yaro bari murna...~
~Oum-Deedat cee~
[9/15, 7:36 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*_Page ~16~_*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Komawar Bilal ɗinne ya sanya abubuwa suka ƙara yi mashi yawa, ginin shi da kuma kayayyakin su da suka iso, wannan ce ta sanya hankalin shi ɗauke wa daga kan su suhan ɗin, to dama dai taimako ne kawai tsakanin shi dasu acikin ranshi, ba kaman yanda yayi iƙirarin soyayyar ba gaban mahaifan nashi.
Ta ɓangaren mu kuwa, komai yayi tsanani, rashin abinci ai ba ƙaramar barazana bace ga ɗan adam.
Idan hankalina yaso ya tashi umman tawa ce ke taɓo ni, da nasiha da wa'azoji da dama, dole ne in daure in maida komai ba komai ba, gudun ɓacin ran nata.
Bamu da wani aiki a yanzu sai sallah, wanka da kuma bacci, mu kan share tsawon yini biyu bamu ci komai ba, saidai ruwa da kuma ɗan farau farau ɗin da muke kaɗawa mu sha, saboda rashin kuɗi a hannun mu, sai umma ta ce ta bani ƴan abunda suka rage a hannun ta na siyo mana fura cen cikin gari, muka dama muka ajiye in munji yunwa mu ɗiba mu tsiyaya ruwa mu kwankwaɗe, da haka har muka kwashe tsawon yini biyu
Idan ma fita muka yi tsakar gida haka zamu dinga fuskantar ƙananan maganganu da habaice habaice daga sauran ƴan uwan namu ma'aikata, hakan ce ta sanya umma ta hanani fita, idan ba aike ba to fa mun gwammace muyi zaman mu a ɗaki umma tayi ta ƙara man karatu in mun gaji mu kwanta
Ko wanki a banɗakin ɗakin namu nake yi mana, iyaka shanya ce zanyi a tsakar gida, sai sharar ɗakin namu da ƙofar ɗakin.
Mun zama bare na ƙarfi da yaji a cikin gidan, gashi shi wanda ke ɗan tausaya mana ɗin ma ya ɗauke ƙafar shi ɗaf daga gare mu, afnan kuma sun riga sun koma tini, saidai kafin tafiyar tata, tayi dabara zuwa sashen mu, duk da ba kuɗi ta kawo mana ba, abubuwa ne masu yawa nata ta tattara ta bani, irin su kaya da kayan kwalliya.
Ta ɓangaren su hajiya Kubra kuwa, komai ya mata yanda take so, magana ta mutu murus, su ɗin da ta tsana ko jin ɗuriyar su yanzu bata yi, lallai Hajiya Laila ƙawar tata hatsabibiya ce, gashi ko Alhajin ma ta dena jin zancen auren Al'Ameen ɗin a bakin shi, gashi ya sake mata sun koma kaman da cen yanda suke
To dama dai ita ɗin wannan ne kawai burin ta, tini Al'Ameen ɗin ya samo masu kuku har biyu suna masu aikin abinci,
Wannan ce ta sanya ta ci gaba da harkokinta cikin kwanciyar hankali, ta ci gaba da zuba mulki da isa da ikon ta kaman yanda take so
Likafa ta ci gaba, yanzu bata ko zama sosai a gidan, tanƙamemen shagon kayan ƙyale-ƙyale da make-up ta buɗe, irin na manyan mata da riƙaƙƙun yara masu tashe da watayawa a faɗin Nigeria.
Yara ta ɗiba kyawawa ta zuba suke aikin, wannan ce ta sanya wurin haɓaka, duk wata mace da ta amsa sunan ta a faɗin garin na Abuja shagon take zuwa ayi mata gyaran jiki, da kuma siyan kayan ƙyale-ƙyale da take yo order ɗinsu daga ƙasashe mabanbanta
To shima Alhajin baiyi yunƙurin hana ta ba, asali ma, shi ma ɗin ba mazauni bane, gara ma Al'Ameen ɗin, yafi zama a gida Nigeria, yana kula da sauran ma'aikatan nasu da suke ma'aikata da kamfanoni daban daban.
Duk da cewa ya fara jan Abie yana koya mashi abubuwan da suka danganci kasuwancin, shi kaɗai ba zai iya ba, ina zai kasu? Gashi yanzu amana tayi ƙaranci a wajen jama'a.
*********
Duk wannan abubuwan dake faruwa, Al'Ameen ɗin bai san dasu ba, tsarin da aka ɓullo dashi a gidan na hana mu abinci,
Yana iyakar ƙoƙarin shi ganin cewa babu wani ma'aikaci acikin gidan dake fuskantar matsala,
Wannan ce ta sanya ya shafa'a Sam damu da al'amarin namu, gashi yanzu ko a hanya bama haɗuwa dashi, saboda babu inda nake zuwa, haka umman tawa, kullum tana ɗaki tana karatun ta, kuma tana iya bakin ƙoƙarin ta, wajen kauda tinanin komai, gudun sake tashin ciwon ta.
Tafe yake cikin takunshi mai ɗaukar hankali, sanye yake cikin fari ƙal ɗin wandon jeans da riga ƙirar polo mai ruwan makuba.
Cikin sauri ya kwala ma mudi driver kira, da ɗan gudun shi ya iso wurin, yana mai russunawa cikin girmamawa ga uban ɗakin nasu yake faɗin "Gani Alhaji"
"Mudi gashi" ya miƙa mashi ƴan makullayen motar, "yau bana jin daɗi sosai, so bazan iya driving ba, ina so ne ka kai ni office, aikin gaggawa ya taso mani, da bazan ma iya fita ba" mudin ne yayi saurin amsar makullin, yana mai ƙara russunawa yake faɗin "Angama ranka ya daɗe"
Buɗe mashi ƙofa yayi, ta mai zaman banza ya zauna sannan ya sake zagaya wa ya shiga yayi ma mota key, tare da danna horn ga mai gadi, cikin daƙiƙa da basu Gaza biyu ba ya wangale masu gate, yayin da mudi ya harba motar bisa titi, yana mai sake danne ma mai gadi horn alamar sai sun dawo, shi kuma ya shiga ɗaga masu hannu yana mai washe haƙora.
Mudi ne ya shiga kallon ubangidan nashi ta gefen ido, dafe yake da kanshi dake sara mashi, kaman zai faɗo, gyaran murya yayi sannan ya shiga faɗin "ranka ya daɗe ko dai asibiti zamu fara zuwa ne?"
Girgiza mashi kai Al'Ameen ɗin ya shiga yi cikin rashin son Magana irin tashi, sannan ya buɗe baki daƙyar yana faɗin "Naje jiya mudi, na sha magani ma ai" ɗan guntun murmushi mudin yayi kasancewar ya san ubangidan nashi yanda yake tsoron asibiti da Allura tin ba yanzu ba, idan akwai Abunda ya tsana baifi ace za'ayi mashi Allura ba
Sake nisawa yayi cikin san gulma, "ummmmm yallaɓai nace, dama...... Uhm" ya faɗa yana mai ɗan haɗiye miyau cikin in-ina, "Ina jinka" ya tsinkayi muryar Al'Ameen ɗin yana faɗa a hankali.
"Yallaɓai ka gafarce ni, na san in bani ba, babu mai zarafin gaya maka wannan maganar, dama ina ta son samun dama, ayyuka ne da naga sun yi maka yawa ne yasa ban tinkare ka ba"
Ya isa mudi, kawai ka gaya man meke faruwa ne? " ya faɗa har yanzu idanun shi na a lumshe, hannun shi har yanzu yana a bisa kanshi, ya to kare shi da murfin motar
" Maganar su Suhana ce Yallaɓai, yarinyar nan da suke zaune ita da mahaifiyar ta, da aka dakatar dasu daga aikin gidan..... "
Cikin hanzari ya buɗe idanun shi, da suka kaɗa sukayi ɗan ja, hakan ce ta sanya suka ƙara shanye wa.
Kallon muɗi ɗin yake yi cikin alama ta son jin meke faruwa dasu ne kuma?
Baice ƙala ba, hakan ce taba mudi tabbacin yana sauraren shi kenan
"Yanzu fa ba'a basu abinci a gidan nan, bama asan halin da suke ciki ba, gashi har yanzu lokacin albashi baiyi ba, nima a bakin saude mai dafa abincin naji, kasan su da ƙananan maganganu, kuma wai........
" Ya salam" ya furta cikin tsananin firgita, sauke hannun shi yayi bisa cinyoyin shi, hakan yayi daidai da ƙarasawar tasu bakin gate ɗin tanƙamemen company ɗin, mudi na shirin danna kan motar cikin gate ɗin da tini an riga an buɗe masu
"Mudi"
"Na'am Yallaɓai"
"Mu koma gida, muyi gaggawar komawa gida, me ya sanya baka faɗa man ba tini? Wanene ya bada wannan damar ta hana a basu abinci?"
Ya jefa ma mudi tambaya cikin ɓacin rai, "Magana nake yi maka mudi"
Cikin sanyin jiki, da nadamar gaya mashi zancen da yayi muɗi ya duƙar da kanshi ƙasa yana faɗin "Allah ya huci zuciyar ka yallaɓai, Amman Hajiya Babba ce ta hana tin waccen tafiyar da kuka yi, mu kuma muna tsoron gaya maka a samu matsala, hajiya ta gane daga bakin mu maganar ta fito"
Ya faɗa a sanyaye yana mai juya akalar motar zuwa inda suka fito.
"Haƙiƙanin gaskiya raina ya ɓaci mudi, menene laifin yarinyar da mahaifiyar ta? Aikin ai basu ne suka ce basa yi ba, wannan ɗaukar alhakin yayi yawa mudi, ya kamata ka dinga sanar dani abubuwan dake faruwa a gidan, saboda na kula munafunci yayi yawa a tsakanin mata ma'aikatan gidan nan"
Mudi ne ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya, yana faɗin "haka ne yallaɓai, Allah ya kyauta gaba, kayi haƙuri idan irin hakan ta ƙara faruwa, za'ayi gaggawar sanar da kai"
Shiru ne ya biyo baya cikin motar har zuwa lokacin da suka isa zuwa ga gidan, ko daidaita tsayuwar motar mudin baiyi ba, Al'Ameen ɗin ya ɓalle murfin motar, cikin sauri da azama ya isa zuwa ga sashen na masu aiki.
Cikin sallama yake ratsa sashen namu har zuwa bakin ƙofar ɗakin namu
Kwance nake nayi matashi da cinyar ummata da take zaune gefen katifa tana ƙara man karatun umdatul ahkam,
Nikam har ga Allah bana gane karatun Sam, yunwa ce kawai ke cina, ko motsin kirki na kasa yi, sauraren ta kawai nake ba tare da gane abunda take faɗi nake ba
Ita ɗin ma ƙarfin hali take, rabon da mu sanya abinci acikin cikin mu anfi sati, kullum saidai farau farau wanda tin jiya ma furar tamu ta ƙare
Sallamar shi ce ta dakatar damu daga karatun da mukeyi, banyi yunƙurin tashi ba, haka ma umman tawa bata matsa man ba, saboda ta san halin da nake ciki, ita ce ta yunƙura dakyal ta miƙe, bayan ta zame kaina daga saman tata cinyar.
Ɗakin da yake sakaye ta buɗe, da ɗan murmushi a kan fuskar ta, sannan ta shiga faɗin " a'ah Muhammad ne? Shigo mana, ka tsaya daga bakin ƙofa?"
Jiki a sanyaye ya sanya kai cikin ɗakin yayin da ummata ke shimfiɗa mashi yalwata ciyar dadduma a gefen ta katifar daga ƙasan tiles ɗin
Zama yayi yana mai gaida umman tawa, cikin natsuwa da girmamawa, haka itama umman tawa ta shiga amsawa da ɗan murmushi a kan fuskanta, kai daga gani ka san na yaƙe ne.
Nikau dakyal na ɗaga na zauna gami da ja na jingina jikin bangon ɗakin
"Ina kwana?" na faɗa a hankali, murya ta har bata fita sosai, kallona yayi cikin ido sosai yana mai amsawa, ya ɗauke kanshi zuwa ga umman tawa.
"umma nazo ne in baki haƙuri, a bisa Abunda yake faruwa acikin gidan nan" ya nisa sannan ya ɗora da faɗin
"Sam bansan me ke wakana ba, sai yanzu ne mudi driver ke faɗa mani, umma menene ya sanya in irin haka ta faru ba kwa sanar dani da gaggawa? Idan an dakatar daku aiki, ai ba hakan yana nufin ba kwa cikin gidan bane, kuna nan kaman yanda kuke a da"
Ya tsagaita yana kallon umman tawa da kanta yake ɗan duƙe tana murmushi, dame zata saka ma Al'Ameen ɗin? Lallai yaro ne ɗan albarka da bai biyo halin mahaifiyar tashi ba Sam, murmusawa tayi ta shiga faɗin
"kai haba babu komai ai Al'Ameen, Hajiya bata yi komai ba, ni ban ma so muɗi ya faɗa maka maganar ba, bana so hakan ya kawo saɓani tsakanin ka da mahaifiyar ka Muhammad, don Allah ina so ka bar zancen nan, Mungode da alkhairi ka gare mu, Allah yasa ka gama da iyayen ka Lafiya, ka cigaba da yi masu biyayya, insha Allah zaka ga haske a rayuwarka"
Cikin jin daɗin addu'ar da umman tawa tayi mashi ya murmusa yana faɗin "Ameen Umma, nagode kwarai da addu'ar ki, ina mai ƙara baku haƙuri insha Allah komai yazo ƙarshe, ina so komai ya tsaya iya mu ne dake nan, ku siyo abubuwan buƙata da Abunda zakuyi girki iyakar naku, ku dinga cin abinci, duk abinda kuke buƙata kuma insha Allah ku tuntuɓeni kai tsaye ina tare daku. Kuyi haƙuri da halin mahaifiya ta, ina mata Addu'a Allah yasa ta gane gaskiya"
Miƙewa yayi tsaye gami da ajiye mana kuɗi masu yawa sosai, gami da complement card ɗinshi da yake ɗauke d suna da number tashi ta waya, sai kuma matsayi shi na MD Dambulan And CEO Dambulan Estate and More, sai Address ɗin Office ɗin nashi.
Murmushi umman tawa tayi tana mai Cewa "a'a Muhammad ba zamu karɓa ba gaskiya, abun yayi yawa, ai ana hidima damu, kwarai da gaske, Allah ya ƙara buɗi"
Ameen ya amsa yana daga tsaye, yake faɗin "Umma ki amsa Alkhairin da nayi maku, ba kowa ya sanya ni ba, ni na sanya kaina, ba roƙona kuma kuka yi ba, ni ne naga dacewar hakan, indai kin ɗauke ni ɗanɗan ki da kika haifa, ki amsa ki sanya man Albarka umma" yana gama faɗar haka ya juya ya fice cikin azama, har yanzu kan nashi na sara mashi matuƙa gaya
Da kallo nabi bayan shi har ya idasa ficewa gaba ɗaya daga ɗakin namu, ajiyar zuciya na sauke a hankali ina mai zamewa na kwanta lamo abubuwa da dama na man kai kawo cikin ƙwaƙwalwa game da wannan cukurkuɗaɗɗiyar rayuwa da muke yi.
Watau ni na ma rasa gane kan wannan mutum wallahi, Ya Ameen daban yake cikin mutane, kallona na maida kan uban damin kuɗin da ya ajiye, in ba gizo idanuna keyi man ba, raper ce ta ƴan dubu ɗaya har guda biyu, sai katinshi da ke bisa kuɗin ajiye,
Ba ɓala lokaci na mirgina ina mai wawurar kuɗin, na sanya hannu na zaro masu ɗan yawa ina Miƙewa kaman zan faɗi
Mun daɗe bamu da ko sisi a daƙin, me zamu tsaya jira tinda ga dama tazo ta iske mu har inda muke? Ban bi ta kan ummata ba, na zari hijab ɗina ina mai ɗaura wa bisa kayan dake jikina na atamfa ɗinkin doguwa riga bubu dake jikina
"Umma me zan fara siyo mana muci kafin mu nemi mafita?" na furta daga tsaye ga dukkan alamu ma ba sauraren cewa da take yi "ke suhan menene haka?" nake yi ba
Ɗan murmushi tayi cikin tausaya war mahaifiya ga yaron ta ta shiga faɗin "Ko me kika nemo mana suhan zanci"
"To umma"
Na faɗa ina mai ficewa a daƙin, da zallan kallon tausayi ta bini dashi hawaye na biyo kuncin ta suna silalowa, "Allah yayi maki Albarka Hauwa'u ya ƙara shirya man ke, ya baki miji nagari, mai tausaya ma maraici ki, Allah ya ƙwato maki haƙƙin ki, ya kuma saka ma zalumcin da aka yi maki Ameen.
Ta daɗe zaune tana kuka tana share wa, gami da jera ma gudar tilon ɗiyar tata adduo'i na alkhairi da take fatan su bita ko bayan babu Rayuwar ta, sannan ta miƙe gami da kauda sauran ragowar kuɗin da kantin kada ƴan bani na iya su leƙo su gani, ɓalli ya tashi,
Abundant bata sani ba, tin bayan shigar Al'Ameen ɗin sashen ma'aikatan, mama uwani, da mama Talatu sun gashi, suna laɓe bayan ƙofar ɗakin su suna hangensu, saidai basa iya jiyo me yake faɗa ko kuma me yake wakana acikin ɗakin, fitowarshi, da kuma fitowar suhan ɗin ba jimawa da fitar Al'Ameen ɗin duk sun gani,
Cikin sauri mama uwani ta fito ta bi bayan Suhan ɗin, saidai cikin rashin sa'a ta tadda Al'Ameen ɗin ya fice cikin motar shi, da matsananci gudu yayin da ita kuma suhan ɗin tabi ta gefen titi tna tafiya alamar ma tafiyar tasu bata zo ɗaya ba, tinda su a tinanin su ko Al'Ameen ɗinne zai ɗauki suhan ɗin su tafi tare da ita.
Abinda duk basu sani ba shine, Al'Ameen ɗin dukan su tara su yake yi, lokaci yake jira yazo da dukkan su zai shayar dasu Madarar mamaki.
_Masu karatu kada fa ku manta har yanzu fa a cikin ma'aikatan gidan, babu wanda ya san da maganar auren Suhan ɗin da Al'Ameen ya bijiro da ita, har ita kanta suhan ɗin da umman ta_
~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:36 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~17~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Tini rahoto ya isa kunnen Hajiya kubra, wannan ne ya sanya ta wakilta mama talatun da ta kai mata tsogumin zuwa ɗakin namu ta duba mata me ke wakana, domin dai ita dakanta ba zata iya taka sashen masu aikin ba.
Cikin sa'a kuwa, ko da ta isa ta tadda umman tawa zaune bakin katifa tana jan carbinta a hankali yayin da idon ta yake kulle haka ta jingina bayan ta da jikin bangon ɗakin, bata yi sallama ba har saida ta isa tsakiyar ɗakin tana mai ƙare ma dukkanin lungu da saƙo dake cikin ɗakin kallo, cikin matuƙar mamaki umman tawa ta buɗe idanun ta tana mai bin mama talatun da kallo wadda har ta samu gefen katifa ta zauna, Amman duk da haka bata bar bin loko loko na ɗakin da kallo ba, ko zata hango wata leda ko wani abu.
"A'a Talatu ce yau a ɗakin namu? Sannu da zuwa" umman tawa ta faɗa cikin ɗan murmushi haka kaɗan a fuskar ta, domin dai ta san me ya kawo mama talatun ɗakin namu
"Eh wallahi kuwa Maryama, nazo duba jikin naki ne, ya ƙarfin jiki?" ta faɗa cikin ɗan ruɗewa kaɗan kama ta da umman tawa tayi tana mata kalle kalle a ɗaki.
"Aikuwa Naji sauƙi sosai Alhamdulillah wallahi Talatu, kinga kaman ba ni ba Naji ƙarfin jiki na, Allah dai ya saka da Alkhairin sa"
Umman tawa ta faɗa tana mai komawa ta jingina da bangon, daga haka ta ja bakin ta ta tsuke, hakan da mama talatun ta fahimta ne ya sanya ta cewa "Madalla Madalla, Allah ya ƙaro afuwa" ta miƙe cikin hanzari zata fice yayin da umman tawa ta bita da ameen tana mai kallon bayan ta, gami da girgiza kai a hankali a hankali
Daidai bakin ƙofa muka haɗu da ita, gaida ta nake yi ma, Amman Sam hankalin ta na ga ƙatuwar ledar da na ciko mana ita taf da siyayyar abinci da zamu ci kafin muyi tinanin mafita.
Har na gitta ta na shige ɗakin tana tsaye tana bin ledar da kallo, domin sanin menene ciki, niko ba ta ita nake yi ba, sanin halin ta da nayi, sai ma na tsinci kaina da baƙin cikin shiga ɗakin namu da tayi, koda yake ba zuwan kanta bane turo ta aka yi.
Jiki a matuƙar sanyaye ta wuce direct zuwa sashen hajiya Kubran ta zauna zaman jiran ta fito, domin taji ba'asin aiken da tayi mata.
Ta ɓangaren mu kuwa ba ma ta ita mukeyi ba, abincin mu muka ci cikin jin daɗi, da sanya ma Ya Ameen albarka, ko babu komai ya zo mana a lokacin da muke buƙatar shi, mu bamu damu da halin mahaifiyar shi ba, ko ma me zata yi ai yunwa bata da hankali.
Ƙarya da gaskiya ta shiga zayyane ma Hajiya Kubran, yayin da ita kuma take zaune hakimce tana sauraren ta, take gyaɗa kai a hankali, lokaci guda ta sallami talatun da take faɗa mata ƙarya da gaskiya gami da kiran hajiya Laila aminiyar ta, kuma maganin kukan ta.
****************
Washegari tin da sassafe sai ga mudi driver ya mana sallama, gami da miƙo man fararen takaddu ƙal dasu, yake shaida man Alhaji ƙarami yace in cike zai aiko shi ya amsa anjima
Amsa nayi gami da mashi godiya, na koma cikin ɗaki fuska ta fal da annashuwa, farin ciki nake yi sosai matuƙa, domin dai ko ba komai na fahimci ya danganci karatu na ne, umma ta na shiga nuna mawa, itama tayi murna sosai, gami da ƙara gode ma Al'ameen ɗin da ya tsaya ma Al'amarin mu kai da fata.
Bamu kaɗai yake ma haka ba, kowa a cikin gidan yana taimaka mashi, muddin abun ya sha kai, domin kwanaki ma sai da ya biya maƙudan kuɗi aka yi ma yarinyar mama saude mai girki aiki, muma cikin gida ne muke ta jin raɗe raɗi, da irin taimakon da yake ma ma'aikatan baya ga albashin su.
Cikewa na shiga yi, da gani dai kaman Jarabawa ce zan rubuta watau Jamb, inda naga ban gane ba sai in tsallake, a haka har na gama na maida cikin folder ɗin na ajiye jiran mudi yazo ya amsa.
Wannan ce ta bani damar yin aikace aikace na cikin jin daɗi, lallai ina dab da cika buri na, abun ya matuƙar ƙarfafa man guiwa, saidai na nazo wajen zaɓen choice na Abunda zan karanta tsallakewa nayi, na bar mashi ya zaɓa man, duk abinda ya zaɓa man daidai ne.
Zuwa azahar na gama komai, har list ɗin abinda zanje in sissiyo mana na buƙata nayi, wanka nayi cikin shiri na simple ba mai ɗaukar lokaci ba, doguwa riga ta material ce jiki na, Afnan ce ta bani ita cikin kayan da ta kawo mani kafin ta koma, da gani ma bata taɓa sanya ta ba, ta amshe ni matuƙa, gyale na ɗauko zan yafa, umma tayi man wani irin kallo, ba arziƙi na ajiye ina ƙumshe dariya a ciki na, oh umma bata so taga nayi gayu, ita har kullum gani take yi ba'a matsayin kowa muke ba, in ana ganin ka ƙwas-ƙwas ma sai ayi ta gulmar ka acikin gidan, dama ga shi ga irin zaman da mukeyi acikin gidan.
Sallamar mudi ce ta katse man dariya da nake yi a zuciya, ɗauko takaddun nayi na miƙa mashi ina ƙara mashi godiya, amsa yayi yana dariya tare da ƙara ma umma ta ya jiki, saboda ɗazu da yazo basu gaisa ba.
Sai da na gama kitsawa sosai, sannan na ɗauki ƴar jikka ta gami da takadda ta list ɗin abubuwan buƙatar, sallama nayi ma umma gami da ficewa daga ɗakin namu kai tsaye zuwa ga barin gidan cikin salon tafiyata da lokutta da dama umma ta kace Allah yayi mani nawar tafiya, su kuma sauran ma'aikatan kance ya ga ce, kai ba kowa kowa ba Galadima kashi🤣
Tin daga nesa na hango shi tsaye jingine jikin motar shi, mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, baƙa ce wuluk sosai, saidai gilassan ta masu sauƙi duhu ne, ni ban ma taɓa ganin shi a cikin wannan motar ba, da gani dai sabuwar siye ce, to abu da masu abunsu
Sanye yake cikin riga ƴar shara, da wando dogo har ƙasa, kanshi babu hula saidai baƙin gashin shi da akoda yaushe yake kwance luf bisa fatar kanshi, hannun shi na riƙe da makullan mota da takaddun nawa a hannun shi yana dubawa,
Baƙin sun glass ɗin da ya sanya ma idanun shi, su ke katange ka daga kallon cikin ƙwayar idanun shi, kaman kullum dai yana tsaye cikin kwarjini shi, da kamalar shi, Al'ameen mutum ne da idan ka kalle shi sai ka ƙara kallon shi
Duk da ba ni yake kallo ba hakan saida ya jaza mani harharɗewa, cikin son gyara tafiyar tawa na isa daidai saitin inda suke tsaye shi da mudi driver "Ahaf, yallaɓai ai gama ta nan tafe" mudi ya shiga faɗa mashi, ga dukkan alamu magana suke yi ko kuma aika mudin yayi ya kirawo ni.
"OK ce mata tazo ina kiran ta" Abunda ya faɗa kenan, har yanzu idanun shi na kan takaddun ko sau ɗaya bai ɗago ya kalle ni ba,
Kwala man kira mudin yayi "Ke Suhana, kizo yallaɓai na kiran ki" chak naja na tsaya, da ɗan ɓacin rai a fuskanta, in ma kiran ne ai sai ya isa inda nake ba ya kwala man kira ba haka gatsau kowa na saurare.
A hankali na juya akalar tafiyar tawa daga nhfar gate ɗin zuwa wurin su inda suke tsaye, da sallama a bakina na isa lokaci guda ina mai gaida shi "Yaya ina wuni?" bai ɗago ba har yanzu idanun shi na kan takaddun yana nazari su ya amsa mani da "Lafiya" a gajarce
Gyara tsayuwa ta nayi duk a takure nake wallahi, kwarjini shi kan ƙara ruɗani, ɗan guntun murmushi naga ya saki, yana mai juyawa kai tsaye zuwa ga bakin motar tashi ya sanya makullan da suke hannun shi ya buɗe tare da ɗauko wasu biruka guda biyu ya dawo inda nake tsaye
Still bai kalle ni ba, ya shiga man tambayoyi wasu ina bashi amsa, wasu ina yin shiru dan ban sani ba.
Choice ɗina ya tambaya na Abunda zan karanta, nan ma shiru nayi mashi, murya ta har rawa take idan zan bashi amsa da ya kula, inda Allah ya taimake ni mudi da yake tsaye ta gefen mu yana sauraren mu.
Maimaita man tambayar yayi, cikin san kauda shirun da nayi na duƙar da kaina sannan na shiga faɗin "Yaya na bar maka zaɓi, duk abinda ka zaɓa man, ni bani da wani zaɓi, ko wane course ne dai insha Allah zan iya kuma zanyi"
Ɗan shiru yayi jin ta kai aya, ɗagowa yayi a hankali ya zare glashin dake manne a idanun nashi yayi, kafe ni yyai da idanun shi, aikau na ƙara sadda kaina ƙasa, ko alama bana iya ɗago fuskata balle in kalli cikin ƙwayar idanun nashi da har wani zaiba zaiba suke yi
"OK zaki iya tafiya" Abunda yace kenan ya maida idanun shi kan paper ɗin, alamar ya sallame ni kenan
Cikin ƴar sassarfa na bar wurin ina mai hamdala da tambayoyi ba suyi tsawo ba, ba zai iya fahimtar yanda nake ji da aduk lokacin da magana ko tsayuwa ta haɗa mu wuri ɗaya dashi ba.
Cikin san kauda tinanin na tare abun hawa na hau, ina mai faɗa mashi inda zai kai ni, saidai duk yanda naso inbar tinanin ya kasa bari na, ko wanne course ne zai zaɓa man ni suhan? Koma dai minene kuma koma dai wanene zanyi insha Allah, da haka har na isa inda zani,na gama abinda nake yi na juyo gida da tarin siyayya ta
***************
Abubuwa sunyi mana matuƙar sauƙi, yanzu kam Alhamdulillahi, kwana biyar kenan ban kuma jin ɗuriyar hajiya ba, balle ƴan baran dan ta, hidimar bikin su aunty Saudat aka shiga yi ga dan gadan, abun ka da masu dashi, bikin dududu sati huɗu aka sanya shi, bayan iyaye sun shiga al'amarin, matuƙa Hajiya Kubra taso Al'ameen ɗin ya fidda matar aure, Amman fir ya nace shi fa indai bata kyale shi ba, tau ya riga ya zaɓi mata, kuma a shirye yake a ɗaura auren shi ko ma yaushe ne, in ma dasu Nihal ɗin za'a haɗa duk ɗaya ne
Hakan ya tada hankalin hajiya, ta ƙara kafa mana karan zuƙa, gashi yanzu ta fiye ta fiye suke ta yi, yin oder ɗin kayan ɗakin su Nihal ɗin, nima na samu ɗan sauƙi, domin yanzu na rabu da wahalhalun su, bama kullum muke haɗuwa ba, duk da duk lokacin da zamu haɗu ɗin saƙon harara ne kawai za'ayi ta aike mun har sai na wuce sannan a bini da daigon tsaki wani lokacin harda tofar da miyau, sannan ace Allah shi kyauta mu haɗa iri da waɗannan mugayen talakawan ƙasƙantattu.
Duk da bana jin me suke faɗa, hakan na mani ciwo, na dai san magana ce marar ɗaɗi suke faɗa a kaina da umman tawa, wannan ce ta sanya bana ma rawar ƙafa ko ɗokin zuwan bikin nasu, duk da wani lokaci ina jin sanyi na zasu bar gidan zan ɗan samu sauƙi, saidai nima ɗin ai ba zamana kenan ba a gidan
Ƴar ƙaramar waya ta ce ta ɗauki ringin, ajiye gugar da nake yi nayi, cikin mamaki na ɗauki wayar ina duba number ɗin da ta kira ni, na kasa ɗagawa har ta katse, ɗan taɓe baki nayi na ajiye, cikin zuciya ta ina mai faɗin koma waye in ya masu ya kira, Nidai bana da kati a waya, kuma bana da wannan number ɗin a waya ta, dama in Naji kira, ko dai Afnan, ko Aunty Saudat, ko Aunty Nihal, sai kuma ita uwar gayyar Hajiya Kubra, ko cikin ma'aikatan banda number kowa sai ta Mama Talatu, itama dan ita ce shugabar mu.
Cikin ko in kula na cigaba da Abunda nake yi, ina kallon umma ta na bina da ido har wayar tawa ta sake ɗaukar tsuwwa, cikin natsuwa na danna madannin amsawa da sallama a baki na
"Assalamu Alaikum wa Rahmatullah" Abunda nace kenan naja baki na na kulle, shiru ne ya biyo baya na tsawon daƙiƙa biyar, cikin mamaki na ɗaga na kalli fuskar wayar, Still dai wayar na tafiya alamar ba'a datse kiran ba, har zan danna da niyyar kashewa ganin nayi sallama ba'a amsa ba, kuma ga dukkan alama koma wanene yana jinya yayi man shiru
Muryar shi ce ta karaɗe illahirin kunne na, cikin salon maganar shi dake tafiya da hankalin mai sauraren shi ya amsa man sallama cikakkiya kaman yanda addini ya koyar.
A ɗan zabure na ɗaga wayar ina mai ƙara kallon number, kaman mai son gano ainahin kamannun shi a fuskar wayar, natsuwa na nema na sanya ma kaina, gudun kada ya gane mamakin da nake yi, ko ba'a faɗa ba shine, ina ya samu number na? Zuciya ta ta shiga saƙa man, "Afnan" wani ɓangare na zuciyar ya bani amsa, ganin ba zai ce komai ba, na kauda shirun ta hanyar gaida shi
"Yaya ina kwana?" "Lafiya" ya bani amsa a gajarce, ga dukkan alamun shi ne yin magana a gajarce, ya kauda man tinanin da nake yi ta hanyar faɗin "Ki shirya Gobe kuke rubuta Jarabawa, zan aiko mudi ya kawo maki abun buƙata, ƙarfe takwas na safe, in kin shirya ki kira ni da wannan Layin" yana gama faɗar haka ya datse kiran.
Da kallo nabi wayar, kaman mai son gano wani abu, a sanyaye na ajiye wayar daga kunne na, ina mai kallon umma ta d take bina da kallon tana buƙatar ƙarin bayani, "Eh umma, yaya ne, yace gobe zan rubuta jarawaba, muɗi zai kawo man abubuwan da zan buƙata" na ɓata amsa, ina mai sanya hannu na kashe Iron ɗin da nake gugar gami da silalewa na kwanta bisa tantagaryar tiles ɗin dake manne da ƙasan ɗakin, nayi matashi da hannuwa na.
Umman bata ce man komai ba, ta miƙe tsam gami da shige wa toilet ɗin dake cikin ɗakin tana mai mani addu'ar nasara acikin zuciyar ta.
Na daɗe ina muɗiɗɗika a tsakiyar ɗakin, nama rasa tinanin da zanyi, mudi yayi sallama a bakin ƙofar ɗakin, tsam na miƙe gami da buɗe ƙofar ina mai gaida shi, ya miƙo mani leda irin ta botique gami da cewa "gashi inji Oga"
Amsa nayi gami da gaida shi, ya man sallama ya wuce, yana mai cewa in gaida umma ta, da kallo na ishi, ko babu komai mudin yana daga cikin mutanen da nake ganin girma da daraja shi a idanu na, ganin cewa ban taɓa samun shi da koda alamun munafirci ba, irin na sauran drebobin gidan da zaka ga suna ƴan ƙusƙus da su mama mama Talatu da mama uwani.
Zaune nake ina ta juya ledar na gagara buɗewa, har u mata ta fito daga cikin banɗakin ga dukkan alamu dai wanka ta gama, "Menene haka? Kin Gaza buɗewa ki duba, ko kin fasa karatun ne?" umma ta jefo man tambaya tana mai zama gami da janyo kwandon kayan shafan ta tana mutsittsika mai a jikin ta.
Ban amsa mata ba, na shiga buɗe ledar bina fiddo kayan dake ciki, uniform ne ma su masifar kyau, da sandal da socks farare ƙal, sai ƴar ƙaramar jikka ta goyo Amman irin ta zamani an yi mata ado da flowers masu ƙyau da ƙyalƙyali, sai litattafai tili guda na karatu, da suka danganci physics, chemistry, biology, english mathematics ds.
A hankali na shiga warware kayan da suke a goge tas, da gani sababbi ne, skirt ne iyakar guiwa, sai riga longslip da belt da gani tok-in akeyi sai ƴar ƙaramar hijab, da zamu iya kiran ta kai tsaye da himar, cikin kwalalo idanu na kai duba na kan ummata da ta dakata da shafa man tana mai bina da idanu, baki na a buɗe na shiga girgiza kai, "bazan iya sanya waɗannan kayan ba, da gani ma wannan makarantar ba ta musulmai bace"
Umma ce ta wurga man wani irin kallo sannan ta shiga faɗin "kar ki sanya ɗin, sai ki canza wasu ai, tinda tsarin ki zasu bi, ko ba ta musulmai bace, ai rana ɗaya ne sai ki sanya dogon hijab, in kinje can kya cire, kada kiyi wasa da damar ki suhan"
Linke kayan na shiga yi ina mai jinjina yanda zan sanya kayan nan in rasa mutane, kaman wata ƙaura, Amman ba zance ba zan sanya ba, ko don gudun wasa da dama guda da Allah ya bani.
Haka na kwana karatu, lallai na yarda in ka bar karatu da yini guda zai barka da shekara ne, haka na dage nayi ta cusawa ina criming da joting har na samu na samu iya abinda zan iya ɗauka, san nan na duƙufa salla da addu'ar neman nasara, da da cewa duniya da lahira
~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:37 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~18~*
*Kyautar Page gare ki _Fatima Batula_ marubuciyar BUGUN ZUCIYA TA Nagode da ƙauna da kuna sadaukar da Page da kika yi mani, ina sonki tsakani da Allah kaman yanda kike so na, haka nagode da Alkhairin ki gare ni, Page ɗinnan naki ne, in kinga dama ki hana kowa karantawa* 🤣
~Masu karantawa Bakwa comment, kuna yi ma kanku, in mu marubuta mun yi maku yajin rubutu, naga me zaku karanta kuma har ku share?, in kunyi mana comment kun ƙara ƙarfafa mana guiwa dame kuka ragu? Ai ka nuna kaji daɗin Abunda akeyi maka ma wani ɓangare ne na godiya, haba jama'a, ai ko Allah da ya halicce mu yana son godiya balle mu da ya halitta ya sanya mani hali irin na ɗan adam, da kuma son a gode mana, da nuna Abunda mukeyi kuna amfanuwa dashi, please ku gyara ba don mu ba~
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Shawarar umma na bi, bayan na gama shiryawa, ni kaina kunyar kaina sai ta kama ni, ina kallon umma tana satar kallo na tana girgiza kai.
Riƙe nake da wayar tawa sai jujjuya ta nake yi ina daga tsaye, na kasa kiran shi, gashi lokaci yana daɗa ƙurewa, har takwas saura, shahada nayi na danna ma Layin nashi kira, wannan ne karon farko da hannu na zai soma kiran wani ɗa namiji a rayuwa ta, shi ɗin daban ne, abubuwa da dama shine mai buɗe man ƙofofin yin su.
Na zurfafa a tinani har wayar ta katse ban sani ba, sai dubawa nayi naga ashe ma bai ɗaga ba, ban ƙasa a guiwa ba na sake gwada kira, still dai bai ɗauka ba, haƙura nayi na koma gefen katifa na zauna, ina mai gyara safar dake ƙafa ta da take fara ƙar, sai ɗaukar idanu take yi.
Ci gaba nayi da craming ina mai gyara zaman jikkata a saman kafaɗa ta, idan ka kalle ni kai zaka rantse da Allah ba ɗiyar Hausawa bace, kayan sun matuƙar fidda man shape, skirt ɗin da yabi lafiya ƙuguna ya zauna ɗas kaman a wajen aka ɗinka shi, nayi matuƙar mamakin yanda aka yi har ya gane size ɗin kayan da zasu iya yi mani
Miƙewa nayi ina gyara zaman belt ɗin a saman ƙhgu na da yabi shafaffen cikina, kai kace bana cin abinci, duk da ni ba siririya bace hakan ce ta sanya kayan suka cika ni nayi ɗas ɗas dani.
Waya ta ce ta ɗauki tsuwwa alamar ana kira na, cikin hanzari na ɗaga kasancewar naga har takwas saura minti sha biyar tayi, gashi yace ƙarfe takwas ne ake shiga Jarabawar, sallama kawai nayi ko amsa mani baiyi ba, cikin hanzari yace "Fito" Abunda ya faɗa kenan ya datse kiran
Sallama nayi ma umma, ta shiga bina da addu'a kuwa, gami da gargaɗa ta da in kama kaina, in tsare mutumci na, kasancewar makarantar wadda take haɗe maza da mata, da murmushi na bita, ina jaddada irin ƙaunar da umman tawa take mani, da son kasancewa ta ta gari a duk inda na shiga. Hannu na sanya na ɗauki gogaggiyar zumbuleliyar hijab ɗita da take ajiye gefen katifa nayi, na warware ta na sanya, ba ɓata lokaci na fice daga ɗakin namu addu'a ɗauke a bakina.
Kasancewar safiya ce, babu kowa a harabar gidan, balle ƴan tsurku su samu na rahoto, ko ba haka ba ma kuma ɗaukacin mutanen gidan basa nan, wai sun tafi turkey siyayya, cikin hanzari na isa ga motar da take fake tsakiyar harabar gidan, da gani a cikin ta ne za'a kai ni makarantar.
Baya na buɗe zan shiga, har ga Allah na ɗauka muɗi driver ne zai kai ni, "dawo gaba" muryar shi ta doki dodon kunne na, ba gardama na maida murfin na rufe gami da buɗe gidan gaba na shiga. Ko zama ban daidaita ba ya fizgi motar gami da ficewa daga harabar gidan da tuni mai gadi ya wangale mashi gate.
"Kina cen kina shiririta har kin so ki makara" Abunda ya faɗa kenan ya maida bakin shi ya rufe kaman ba shine ya mani magana ba, ɗan ɗagowa nayi gami da ɗan waiwayawa ta gefen da yake zaune yana tuƙi na ɗan kalle shi haka, tuƙin shi yake cikin kwanciyar hankali da kwarewa, sharara gudu yake yi kaman waɗanda zasu bar gari, yayi kyau abun shi, cikin manyan kaya, da dukkan alamu yana son manyan kaya kaman ya san suna matuƙar da cewa dashi, ɗinkin dakakkiyar shadda ce mai masifar kyau da ɗaukar idanu, zamu iya kiran ta da royal blue, hakan ce ta sanya fatar shi haskawa sosai, fatar nan tashi kaman bata shan rana, lumui ga gashi da yake kwance saman ta, hannun shi na ɗauke da zoben azurfa mai kyau da ɗaukar idanu, yayin da agogon shi ƙirar iphone take ta walƙiya cikin hasken ranar da ya riga ya gama hudowa.
Maimakon in bashi ansa, sai na kauda zancen da cewa "Yaya Ina kwana?"
Bai bani amsa ba, sai ma ɗagawa da yake yi yana kallon agogon dake maƙale a hannun nashi, yana sarkin ɗan siririn tsaki.
Daidai bakin gaye ɗin makarantar yayi parking, yana mai waiwayo wa ta inda nake zaune yake faɗin "Ki tabbatar kin cire wannan hijabin kafin ki shiga makarantar nan, doka ne gashi nan rutuce a jikin gate"da" to" na bashi amsa ina mai ficewa
Tsayawa nayi tinanin ta ina ma zan fara cire wannan hijab ɗin ni na ma rasa ta yanda zan ratsa tsakiyar mazan dake ta wucewa zuwa cikin makarantar ga dukkan alamu dai mun soma makara.
Ban aune ba Naji muryar shi ta baya na yana cewa "ba zaki hanzarta ba sai sun rufe shiga? Bani hijab ɗin nan, ba zasu bari ki wuce da ita haka ba, zasu ga kaman exam malpractics zakiyi da ita, bana son ƙauyanci" ya faɗa yana mai ƙara sowa ta inda nake tsaye
Ɗan waiwaya wa nayi ina mai kallon shi cikin ɗan marairaice fuskar da babu komai samanta, daga hoda sai kwallo da lip balm,
Miƙoman hannu yayi alamar in cire na bashi.
Soma kiciniyar cire wa nake yi Naji yana faɗin "ai bake kaɗai bace a haka, haka dokar makarantar take, su a kamarantar su ake rubuta jamb ɗin, student ɗinsu basa zuwa ko ina, kiyi maza ki shiga bana so a samu wata matsala"
Miƙa mashi na yi, gami da juyawa na fara taka wa a hankali zuwa ga shiga makarantar da duk na tsargu, gani nake kaman kowa ni yake kallo, Amman a zahiri ba haka bane, wasu ɗaliban ma harda ɗan gudun su, zuwa cikin makarantar hankalin su duk baya jikin su, tafiya nake yi ina ɗan ƙara jan skirt ɗina ƙasa har ga Allah a takure nake.
Daf da zan shiga makarantar ne na ɗan juyo haka, yana nan dai tsaye inda na bar shi, ni yake bi da kallo duk wani taku na ɗaya akan idanun shi suke, wuf na faɗa cikin gate ɗin gami da ƙara ɗaga ƙafa cikin sauri na doshi babban hal ɗin makarantar da naga kowa na nufa.
Ɗan jingina bayan shi yayi da jikin motar yana mai sauke ajiyar zuciya, tabbas sai yanzu ne yake na damar menene ya zaɓa mata wannan makarantar da uniform ɗinta suke haka? Kayan sun matse ta da yawa, yanzu a haka kowa zai ta kallon ta? Amman baya da yanda zai yi, makarantar ita ce makaranta mafi girma da kyau da ƙayatuwa a duk faɗin garin na Abuja, makaranta ce da aka yi recomending akan irin ƙoƙarin ta da hazaƙarta, ɗaliban makarantar basa faɗuwa exam duk wahalar ta, saboda suna follow-up da kuma jajircewa wajen ganin ɗaliban nasu sun kai ga gaci.
A hankali ya shiga taka wa har zuwa ga motar murfin motar ya buɗe gami da zama, tada motar yayi yana mai ajiye hijab ɗin kujerar da shan ɗin ta tashi.
Ya rasa dalilin shi na damuwa da halin da yaga suhan ɗin ta shiga na tsarguwa da kanta, ya san tarbiyyar ta ce haka, shi in ba yau ba ma zai iya cewa bai taɓa ganin ta da ko gyale ba ma balle kayan da suka matse ta haka ba, ɗan runtse idanun shi yayi yana buɗewa gami da ɗan bugun sitiyarin motar, ji yake kaman yaje ya maida mata hijabin ta ta ɗora saman waccen da ita da babu duk ɗaya ne.
A haka har ya isa office ɗin nashi tinanin bai bar shi ba, yaji duk ya rasa sukuni, bai san menene haka ya tsaya ya to kare mashi zuciya da maƙoshi haka ba.
To ko bayan ya shiga office ɗin kasa taɓuka komai yayi, sai jujjuya kujera yake yi idanun shi a rufe ya ɗaga kanshi sama, duk da ya rasa tinanin da zai yi, ƴar ƙaramar ajiyar zuciya yayi yana mai jawo wayar shi ya latsa kiran lambar Bilal domin yaji ya shirye shirye nashi bikin ke tafiya.
***************
Cikin ikon Allah, ba zance banji wahalar exam ɗin ba, saidai zan iya cewa ta zo man Da sauƙi ba kaman yanda na zata ba, karatun da nayi ya matuƙar taimaka mani, inda na ɗan samu matsala kaɗai cumputer ɗin da ban san yanda ake amfani da ita ba, inda Allah ya taimake ni an nunnuna mana yanda duk zamuyi, sai gashi kafin lokaci ya cika ma na gama duka, ina dai ta addu'a cikin zuciya, saboda Jarabawa dace ce, ba ƙoƙarin ka ko hazaƙarka ke baka ba, iko ne kawai na Allah.
Bayan mun futo ne, ina jingine jikin bangon hall ɗin tsaye rataye da ƴar jikka ta, wayata tayi tsuwwa. Ina ɗauko wa naga Afnan ce, cikin hanzari na amsa, gaisa wa muka yi cikin mutu ta juna da ƙaunar juna ta shiga zaulaya ta, tana ceman ya exam ta kira yayan ta yace mata ina cikin exam, kuma ga lokacin da zan fito shine tace bari ta kira taji ya wasa kwalwa, cikin dariya nace mata "haba ai wlh ba wani wasa kwalwa, komai masha Allah, sai fatan fitowar ta lafiya" itama dariya tayi ta ɗaya ɓangaren tana mai cewa "kai aunty na, ko dai yayan nawa ya samo maki satar amsa ne? Baya so ki wahalar mashi da kanki?
Ɗan sororo nayi ina mai sauraren ta, to me hakan ke nufi? Me maganar tata take nufi ne? Ɗan murmushi nayi ina cewa" Haba afnan wace irin magana kike haka? Kaman ya in wahalar mashi da kaina? Wai tsaya ma yaushe ne na zama auntyn taki?
Cikin kwalalo idanu afnan ɗin tace "wai sorry" ɗif ta datse kiran tana mai maida numfashi da ajiyar zuciya ta maida kallon ta ga aunty feena dake zaune tana tsefe ma Nasreem kai, murmushi aunty feenar tayi nata cewa "Ah to uwar surutu, ina tinanin fa yarinyar da mahaifiyar ta basu san menene ke faruwa ba a gidan nan, gashi ke kin kira zaki gwangwaɗa mata, ke da Al'ameen ai, indai yaji katoɓarar da kika aikata mashi" cikin ƴar shagwaba irin wacce suka saba ta shiga diddire ƙafafu, Allah kuwa aunty ba zai ji ba, saidai in kece kika faɗa mashi, kinga ita suhan ba surutu ke gareta ba, hasali ma ban taɓa ganin suna magana da yaya ba, wallahi shaf na manta ance a bar maganar na ɗauka Mom ta amince ne"
"Ah to kedai kika sani da shegen surutun ki" Aunty Feenar ta faɗa tana mai sake murmusawa alamar zolaya.
Ta ɓangaren na kuwa sototo nayi da waya a hannuna, bayan na fahimci Afnan ɗin ta riga ta datse kiran daga ɓangaren ta, ɗan taɓe baki nayi ina mai sauke kafaɗa ƙasa, afnan da shegiyar shiririta take, bari Ya Ameen yaji mai take faɗa zata gane kuren ta ne, ni ce zata ding haɗawa da yayan? Abunda ta san wutsiyar raƙumi tayi wa ƙasa nisa, haka kuma sama tayi wa yaro nisa har a badan abada, ci gaba nayi da taka wa har zuwa bakin gate ɗin, naja na tsaya ina shawarar tarar abun hawa da zan koma gida.
Ta bayana Naji sallama, ɗan juyawa nayi, su uku ne tsaye sai faman murmushi suke irin nasu na ƴan gayu sakatattu alamar son suke suyi magana dani.
Kayan uniform da na gani jikin su irin nawa ne ya sanya ni amsa masu sallama tawa ina mai kauda kai gefe, ganin bani da Case dasu ne ya sanya ni fara taka wa da niyyar basu waje, ga dukkan alamu irin ƴan makarantar nan ne marasa kunya da duk yarinyar da suka gani sai sunyi mata magana.
Gaba na suka sha, suna mai faɗin "Haba beb, ya zamuyi maki magana kiyi banza damu ki kyale mu, har kina shirin gudu wa?" ɗaya daga cikin su ya faɗa yana mai ɗan girgiza kai da jiki haka, alamar ya daɗe cikin iskanci irin nasu na ƴaƴan masu kuɗi.
Bance mashi ƙala ba, na kuma zagaye su da niyyar wucewa, ɗaya daga cikin su ne ya sanya hannu gami da janyo hijab ɗina, dole naja na tsaya ina mai wulla masu manyan idanun a, alamar su kyale ni, basu ma kula da Abunda nake nufi ba, su a tinanin su ma fari nayi masu da idanu, Abunda ya ƙara burge su kenan.
"Haba beby, tin shigowa ki hall muka ji kinyi mana, kin kwanta mana, duk faɗin makarantar babu yarinyar da ta kaiki kyau da sura, ki kalle ki fa sama har ƙasa" ya faɗa yana nuna ni da hannu sama zuwa ƙasa
Gudan ya amshe da cewa "Ni sunana Adnan, wannan kuma Mujaheed, sai wannan Umar ana kiran shi U-Boy, in kinji ana cewa triples to mune, makarantar nan babu wata mace d zamu kalla muce muna so ta ƙi amsa mana balle ke da kike sabuwa zuwa makarantar"
Tsoki naja ba tare da na ce masu komai ba, na kuma zagaye su na wuce ina mai Allah wadarai da irin tarbiyyar su, ga kansu duk askin banza, hatta da wandon su duk sun saɓulo shi ƙasa ass down, to ni ko maza sun ƙare zan tsaya sauraren waɗannan ƴan tautsin yaran ne? Ƙila ma duk in ka bincika na girme su..
Basu haƙura ba suka sake biyo ni suna janyo mani jikka, cikin rashin sa'a kuwa har hannun jikkar ya katse, dama ɗan sirri ne, littattafan da waya ta ne suka watse ƙasa, cikin hasala na zuƙunna na shiga tattara wa, bana so in masu magana ne abun ya yi ƙamari, ina so mu rabu lafiya ne, tinda na san da wuya idan zan kuma komawa makarantar a rayuwa ta, dariya Naji sun kece da ita suna mai cewa "kanburauba, baba Kaga wata iphone waya nan? Ɗaya daga cikin su da bazan iya tina sunan da aka faɗa mashi ba ya shiga faɗa yana mai nuna waya ta da hannu yana tin tsira dariya harda buga ƙafa ƙasa.
Hannu ne kawai naga ya shiga tattara mani sauran takaddun da littattafan ya niƙo mani, cikin ɗan firgici na ɗago ina mai kallon shi, kwalla da nake ɓoyewa ta wulaƙanci da suke mani ce ta shiga silalowa, wata na bin wata, hannu ya sanya yana ɗauke mani hawayen cikin isa da kwarjini irin nashi ya miƙe yana mai zaro sabon hanky daga aljihun shi yana mai miƙo mani, amsa nayi ina Miƙewa gami da share kwalla tawa da ta fara yawa a fuska ta.
Sake zuƙunnawa yayi ya ɗauki wayar tawa da take gefe, ga dukkan alamu dukkan abubuwan da suke faɗa akan kunnen shi ne, da bansan yaushe ya iso wajen ba, saboda ban kawo ma raina zai dawo ɗauka ta ba.
Hannuwa na kawai Naji an shiga ja a hankali har zuwa bakin mota, ya buɗe man gidan gaba na shiga na zauna, ya zagaya ya buɗe ya shiga gami da yima motar key, saida muka hau saman babban titi sana ya sanya hannu ya jawo hijab ɗina da ya maida gidan baya, ya ɗora mani bisa cinya, alamar in sanya kenan.
Su ko yaran da kallo suka bishi, su kansu basu san lokacin da ya iso wajen ba, daidai suka gan shi zuƙunne, hankalin su na gare ni da suke ta yi man shaƙiyyanci.
Ɗaya ne daga cikin su ne yace shi kuma wannan waye? Ko dai ƙanwar sa ce? Ko kuma budurwar shi? Wanda aka kira da U-Boy ne yace "kai baba yanzu baka gane wannan gayen ba? Dambulan ne fa, shine babban ɗanɗan Alhaji mustapha, ai ni ta bayan layinsu muke, bansan wannan acikin ƙanen shi ba, ai su basa karatu Nija ma, ba dai san menene haɗin shi da ita ba, Mujaheed ɗin ne ya riƙe baki," kai haba U-Boy, ashe da mun ci ubanmu, yanda na san gayen cen baya da wasa ko alama, yana iya Sanyawa a kulle mu fa wallahi, baya son rashin kunya" "Muje Baba, Allah ya so mu ba gaban sauran guys ɗin aka yi ba, ai da mun sha kunya" Adnan ɗin ya faɗa yana mai jan hannun su suka cigaba da tafiya domin barin makarantar
***************
Muna isa gidan ya sauke ni baƙin gate, bai ceman ƙala ba, haka nima ban tanka mashi ba, na Miƙa mashi hanky ɗinshi, ɗaga man hannu kawai yayi alamar in bar shi, fita nayi na kulle motar, gami da ɗan ja baya, ina jiran ya miƙo mani wayar, motar shi ya ja ya wuce ba tare da ya ko kalle ni ba, jiki a saɓuke na shige gidan zuciya ta a cunkushe, har saida umma ta fahimta
Aiko ta shiga tambaya ta lafiya? Ko Jarabawar ce tayi wahala? Girgiza mata kai nayi, ina mai ƙaƙalo murmushi dole nace "a'a umma, Jarabawa Alhamdulillah, kawai gajiya nayi, gashi kaina yana ɗan ciwo, kinsan na kwana karatu jiya ban samu isasshen barci ba" cikin tausaya wa ta shiga ɗan ɗaga man kai alamar eh, sannan ta shiga cewa "to maza kiyi wanka da sallah, kici abinci ki kwanta ki huta, ai an daɗe ba'a gamu da karatun ba, dama sai a hankali" da to na bita ina mai kwaɓe kayan na shiga ban ɗaki domin yin wanka.
Sai da na kammala komai, sannan na shiga cin kafiyayyen abincin da umma ta girka mana, duk da zuciya ta babu daɗi akwai tinanin da nake son yi nafi so sai na natsu, gashi waya ta dake hannun Ya Ameen ɗin, naso in kira Afnan domin jin me take nifi da kalama ta na ɗazu? Saidai wata zuciyar tana mai ƙwaɓa ta, gami da tunatas da dani shirme da shiriritar afnan ɗin lokutta da dama.
Da haka bacci ya kwashe ni, bayan gama yabiɗar abincin, dama da tarin gajiya fal acikin a jikina.
~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:37 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~19~*
*Gaisuwa da ɗaukacin marubutan Golden Pen Writer s Association, Ina matuƙar yinku a ko ina kuke, kuci gaba da rubuta mana litattafai masu ma'ana, mu kuma muna suburbuɗa karatu Insha Allah, Allah ya ƙara maku ɗaukaka da zaƙin hannu. _Love u All_*
*kyautar Page gareki _Khadeeja s. Dogarai (Lipton Girl)_ shafinki ne wannan kiyi kaca-kaca da ɗan Albarka, abu naka maganin a kwaɓe ka* 🤷🏻♀
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Bacci yayi daɗi, nice ban tashi ba sai da kiran sallar la'asar ya tada ni. A gurguje na sake watsa ruwa domin in ƙara jin daɗin jiki na, na maida komai na adana daya danganci karatu na.
Mamaki nake yanda umma tayi mana girki a cikin ɗaki nake, kasancewar umma ta mace mai tsafta da kula, ya sanya bama a gane anyi girki a wajen har ta kauda ɗan ƙaramin gas cylinder ɗin da na siyo mana, aka ciko ta da gas, saboda stove akwai ɓata wuri, ga warin kerosine.
Wuraren ƙarfe biyar na yamma ne, abun duniya ya isheni, ina son waya ta a kusa dani, gashi abinda yaran nan suka mani ɗazu a makaranta ya tsaya mani a rai, ai duk shi ya ja mani da ya bar mani hijab ɗita a mutumce ba ɗan iskan yaron da yaso ma tunkara ta.
Naji mutum da ƙarfin hali, wai har cewa yake ina cen ina shiririta na kusa makara, ko sau nawa ma na kira shi bai ɗaga ba? 😡😏
Shashantar da zancen nayi, gami da miƙewa na janyo kayan guga ta da ban ƙarasa ba jiya na hau idasa wa.
*******************
Ya daɗe office zaune yana jujjuya wayar a hannu, ƙare mata kallo yake tsaf, shi dariya ma abun yake bashi, lallai mace sai dai a barta, bai ga abun kuka ba anan, ita bata san ma kukan da take masu zai ƙara masu ƙaimi wajen Abunda suke shirin aikata mata ba? Tin farkon biyo ta da sukayi yake kallon su ta cikin mota, har kawo inda ɗaya ya janyo mata ƴar hijab ɗin dake saman kanta, baiyi niyyar fita ba, Amman kasancewar hangowa da yayi abun nasu na neman wuce makaɗi har ta kai ga sun janyo mata jikka ta katse, shi ya tunzura shi ya fito a sukwane zuwa gare su, yayi niyyar hukunta su, sai kuma ya fasa ganin cewa zai iya ja mata, wata rana ko a hanya suka haɗu da ita su so su rama abinda ta sanya aka yi masu, hakan ce ta sanya bai ko tanka masu ba lokacin da ya isa wurin.
Hannun shi ya ɗaga gami da kallo, cen ƙasa zuciyar shi na raya mashi, me yasa ya kama mata hannu? Har da goge mata kwallar dake zirara saman fuskar ta? Me hakan ke nufi? Shi dai ya san in afnan ce ba zai iya bari yana kallo a so aci mata mutumci ba, ba zai iya jura ba, ita kuwa suhan ɗin yana mata kallon kamar afnan ne, ko don saboda tsananin ƙaunar afnan ɗin ga suhan ɗin.
"Sai dai kada ka manta, ita ɗin ba afnan bace, ba muharrama ka bace"
Abunda wani sashe na zuciyar shi yake tinano mashi kenan, ɗan murmushi ya saki yana mai girgiza kanshi irin na gamsuwa.
Murmushi ya sake saki har saida kuma tun shi gabaɗaya suka loɓa, tinowa da yayi da hajiyar shi ƴar drammer, da yanda ya rufe mata baki d damun shi da zancen aure da take yi, nisa wa yayi gami da jawo wayar shi, ya kamata ma ace sun dawo hakanan, gidan baya mashi daɗi ya kasance babu kowa daga shi, sai masu aiki, Alhaji nasu ma baya ƙasar duk da shima gaf yake da dawowa ko don hidimar bikin su Nihal ɗin.
Kira biyu yayi Alhajin ya ɗauka yana dariya "Yaya dai Son? Kwana biyu kajini shiru ko?"
Murmushi ya saki yana mai cewa "Nothing Dad, good afternoon, Ya aiki?"
"Aiki Alhamdulillahi Ameenullah, ya fama da jama'a? Fatan dai komai yana tafiya normal?" Amsa mashi yayi suka ɗan taɓa fira haka mafi yawanci da ya danganci aiki ne, yana kuma sanar dashi shirye shiryen kammala ginin gidajen nashi, da yanda za'a shirya ƙaddamar dashi, Alhajin ne yace su bari tukunna su gama da hidimar bikin su Saudat ɗin, saboda kada ayyuka su rincaɓe masu, ba haka yaso ba, yaso ya cigaba da shirye shiryen shi, hidimar biki ai ba tashi bace shi da yake namiji, kuma ba bikin shi ba ko na abokin shi Bilal, da to ya amsa ma Dad ɗin nashi, sannan ya sa yo buƙatar shi ta son Alhajin yayi ma Hajiyar tashi magana su dawo gida hakanan, duk abinda basu gama siya ba, akwai a gida nigeria, shi bai ga dalilin da za'a ce siyayyar kayan gida ba, sai an kwasa zuwa wata uwa duniya, murmushi Alhaji Mustaphan yayi, ko ba komai ya san yaron nashi wajen kishin ƙasar tashi ta nigeria, amsa mashi yayi da zai kira su ya sanar dasu, sallama sukayi suna mai marmari da begen juna, ƙauna ce mura ran mai tsafta Alhajin yake ma yaron nashi, ko dan kafin hankali da zurfi tinani irin na ɗanɗan nashi, duk ayyukan dake gaban shi, baya taɓa gajiyawa, ko ya nuna ya sare, balle ya gaza, addu'a yaci gaba da bin yaron nashi, Allah ya cigaba da taimaka mashi da haskaka mashi a dukkan al'amurran da ya sanya a gaba.
***********************
Ko da Alhajin ya kira su akan su koma gidan, a cen ƙasa ran Hajiya Kubran ba haka taso ba, saidai isa da izza ba zasu bari ta bari ta nuna ba har ma waɗanda suke tare su gane, watau su Hajiya Laila, da kuma wata ƙawar ta makusanciya watau Hajiya sa'a, dama su shidda ne sukayi tafiyar sai sabuwa ƴar aikin da suka samu itama yarinya ce duk da zata ɗara ma Saudat kanta a shekaru, idanun ta a buɗe yake, dama bata aiki sai gidan masu hali, ga iya tuggu da munafunci, wannan ce ta sanya ta ƙara shisshigi ma hajiyar, duk da tana jin haushin mulki irin na hajiyar, su bakwai kenan, Hajiya Kubra, Hajiya Laila, Hajiya sa'a sai Nihal da Saudat sai hafsat ɗiyar Alhaji Awwalu da za'a haɗa bikin nata da su Nihal ɗin sai kuma sabuwar ƴar aikin tasu mai suna Maria, ana ce mata Maree.
Ko da Hajiyar ta faɗa masu batun komawa tasu, basu ji daɗi ba matuƙa, kumburi suka shiga yi, harda cewa zasu kira Dad ɗin nasu su roƙeshi ya ƙara masu sati, Hajiya Kubran ce ta hana su, saboda mulki da taƙama na kai kawo acikin jinin jikin ta, kuma bata isa saɓa ma Alhajin ba, saboda shi ɗin namiji ne tsayayye a gidan shi, baya ɗaukar wargi ko saɓa dokar da ya gindaya akan kowa dake zaune a gidan.
Ta ɓangaren Hafsat kuwa abun yafi kowa faranta mata rai, cikin zuciyar ta dama ta ƙagara su koma ƙasar tata ta haihuwa, ta samu ta koma gidan su cen Katsina, dama abban ta ne ya tilasta mata zuwa, ko mahaifiya ta ba don taso ba, saboda ta san yanda family ɗin na ƙanen mijin nata suke da bala'i jin kai da sangarta, uwa uba kuma mahaifiya su da dama ba wani shirin arziƙi suke ba, domin ita ba zata iya binta ba, a matsayi ta na wadda take gaba da ita, ko ba komai daga ita har mijin nata basa jiran komai daga garesu, don dai ma kawai ƴan uwantaka, da kuma shi Alhaji Mustaphan da ba halin shi ɗaya ba Sam da matar tashi.
Ware ta suke yi, komai za'a siya ko za'a zaɓa ra'ayin su ake ɗauka, ba kuma komai bane in an siya masu ake siya mata ba, to don dai itama mahaifiya tata tayi ƙoƙari wajen ganin ta haɗo ta da ƴan kuɗaɗe daidai ƙarfin ta, gudun faruwa hakan, Hafsat yarinya ce mai natsuwa da kawaici, hakan ce ta sanya ko sunyi waya da mahaifiyar tata bata faɗa mata komai da halin da take ciki, ta riga da ta san Allah ya bata miji da gari, mai natsuwa na nuna ma sa'a, ita ba wannan abun duniyar ne yake gabanta ba, fatan ta dai kawai ɗaya ta koma ƙasar tata ta haihuwa, ko zata ga mahaifiyar ta mai share mata ku kanta, tana kewarta sosai, dan wanda zata aura bata jin shi, saboda kullum suna tare a waya ko kuma we-chat.
Saboda haka yanda suke ware ta ko kuma suke nuna mata halin ko in kula bai dameta ba, duk da abun na mata ciwo, wai ace waɗannan ƴan uwanka ne, Amman babu wata alaƙar arziƙi da zata haɗa ka dasu, kai su dai waɗannan ba suyi da cen hali ba, nazajen su sun kwasar ma kansu, yara babu abinda suka sani daga sangarta sai jin kai? Ta lura ita kanta ƴar aikin tasu Maree munafuka ce, bata cen bata cen, wannan ce tasa ta ja jikin ta bata sake masu sosai su kansu, balle su wulaƙanta ta, duk da ta san maƙudan kuɗi Alhajin ya haɗo su dasu, kuma Yayansu Al'ameen na sake turo masu wasu akai akai, hakan bai sanya mata kwaɗayin abun su ba Sam, kuma shi Alhajin da sunan siyayyar yara uku yake bada komai, har shi Al'ameen ɗin yana sake haddada masu duk da Abunda suka siya su siyawa Hafsat itama, Amman basa ji daga su har mahaifiyar tasu, da ta kwaso ƴan barandanta saboda kankan a suka wani taho siyayyar aure.
************
Cikin kwana na biyun da basu umarni sai gasu sun tarkato sun dawo dukan su da tarin siyayya raga raga, tare suka taho da kayansu, hayaniya ƴan taron su ne ya alamta mana da dawowar tasu, ba zance bamuji daɗi ba, saidai lallai gabanmu ya faɗi, daga ni har umman tawa.
Jiki ba kwari muka fito taron su muma, gefe mukaja muka tsaya gami da gaishe su, cikin su ba wadda ta amsa mana, sai a tsaki da Saudat tayi ta shige war ta cikin gida, Hajiya Laila ce naga tana mani wani irin kallo da na Gaza gane ma'anar shi, ita kau Hajiya Kubran ko kallo bamu isheta ba, Hafsat ce kawai ta matso inda muke tsaye cikin girmamawa ta gaida umma ta, cikin fara'a ta amsa tana mai tambayar ta Mamanta, Lafiyarsu lau ta tabbatar mata, sannan ta janyo hannuna da nake tsaye gefe guda cikin zaulaya tace "Ƴan mata ya ake ciki?" murmushi nayi ina jan hannun ta zuwa gefe, na shiga cewa "ke Hafsat zakiyi laifi fa, ki bari zamuyi magana anjima" da to ta bini, tana mai matsawa gefe, hakan ce ta sanya ta ƙara basu haushi, bata ko kula su ba ta shige cikin gidan.
Bamu bar wajen ba muna tsaye har saida suka shige cikin gidan, sauran ma'aikatan duk suka watse suka barnu nan tsaye, umma ta ce ta matso inda nake tsaye ta shiga kallo na cikin gargaɗi, "Ki kula suhan, kar ki ja mana wani abu daban, kinga dai yadda suka dawo, tin anan ya alamta maki yanda abun yake, ki kiyaye" gyaɗa mata kai na shiga yi cikin gamsuwa da maganar ta, wucewa tayi gaba Ina binta laƙwai-laƙwai har zuwa sashe namu.
***************
Al'ameen da yake tsaye ta jikin window ɗinshi, yana kallon duk abubuwan dake faruwa, tin daga shigowar shi gidan har watsewar su, ya sauke ajiyar zuciya, lallai Abunda yake gudun afkuwar shi ne yake faruwa, tsanar mutanen guda biyu ce yake hange cikin kayar idanun mahaifiyar da ƴan uwa nashi.
Tabbas ya san shine ya jaza masu, ba tare da sanin su ba, ta yaya zai bi ya warware wannan tsanar da suke fuskanta? Laifin shi ne, ina ma ace da wata yayi wannan trap ɗin ba suhana ɗin ba, "Huh" ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyin jiki ya ja ƙafafu shi daƙyal ya isa ga bakin gadon ya zauna yana mai dafe kanshi cikin matsananci yar damuwa, menene ya sanya yanzu yake yawan kula da al'amarin yarinya ne? Menene ya sanya yanzu tinanin ta baya fita a ranshi? Hannu ya sanya gami da jawo wata farar leda, fiddo Abunda yake ciki yayi ya shiga juyawa a hannun shi, waya ce mai masifar kyau, sabuwa dal a kwalin ta, ƙirar Samsung galaxy.
Tunani yake ta yanda wayar zata isar mata ba tare da kowa ya fahimta ba yanzu, tinda ƴan gidan sun dawo, su kansu munafuka masu aikin yanzu zasu dinga kai komo acikin gidan, wani tinani ne ya faɗo mashi arai, maida wayar yayi cikin ledar ya miƙe gami da aza ta bisa mirror ɗin da yake ɗakin ya fice domin zuwa yi ma Mom ɗin tashi barka da zuw.
A babban falo dukan su ya tada su, sun baje gajiya tayi masu ligif, Hajiya Kubra ce kawai bata wajen ita da aminan nata, suna cen sun ƙule a sashe na Hajiyar suna tattauna wa, gaida shi suka shiga yi, ya amsa masu babu yabo babu fallasa, sannan ya maida hankalin shi akan Hafsat ɗin da take jingine da kujera saman carpet, cikin ɗan dakin fuska yace "Hafsat ya gajiyar tafiya, fatan kun dawo lafiya?" ɗan murmushi tayi tana mai cewa "lafiya ƙalau yaya, ya muka same ku?" Lafiya lau ya bata amsa, yana mai nufar upstair domin zuwa ga Mom ɗin tashi.
Ƙwanƙwasa ƙofar ya shiga yi, daga cen ciki aka bashi umarni ya shiga, cikin takun shi na ingarma namiji ya taka ya shiga bakin shi ɗauke da siririya sallama, da kallon ƙauna mahaifiyar tashi ta bishi, ɗan nesa dasu ne ya samu kujera gami da zama, ya shiga gaida su harda ƙawayen mahaifiyar tashi, cikin fara'a suka gaida shi suna tambayar shi wajen aiki, ya amsa masu da lafiya, yana mai tambayar su hanya, duka lafiya suka shaida mashi, miƙewa yayi gami da cewa "Mom zan ɗan fita kafin ki gama dasu, ina dawowa anjima"
Bai jira cewar ta ba, ya fice daga falon, cen ƙasan ranshi, haushi fal na abokan mahaifiyar tashi, domin shi fa in ba zuga ta ba, da ƙara kambama mata kai baiga abinda suke yi ba, baiga dalilin ta ba ma na kwasar su su wani tafi siyayyar aure ba, Abunda ko daga nan gida nigeria zaka iya Kyi order ɗin duk abinda kake so, ya iso maka kuma har gida, salon ɓarnatar da kuɗi kawai, da son neman suna😒
Da kallo suka bishi dukan shi, har ya idasa ficewa a falon, ajiyar zuciya suka shiga sauke wa, sa'ilinbda Hajiya sa'a ta kalli Hajiya Kubra, "Lallai Hajiya ta, Al'ameen ne ya ƙara girma haka? Kina me da har yake neman jawo maki magana da raini, ta hanyar auren waccen koɗaɗɗar? Kiyo iya yin ki duk yanda zakiyi kiga kin daƙile wannan maganar wallahi, yaro mai jini a jiƙa kaman wannan ga naira ga kyau ga gayu? Tabɗi gaskiya kinyi sake, ni ba ma ga amfanin zaman da suke yi a cikin gidan ba, har ma zai dinga iya ganin ta kullum, kiyi amfani da damar ki, tin kafin kina kallon ruwa kwaɗo yazo yayi maki ƙafa, kina dai gani irin waɗannan yaran su ne yaran masu kuɗi da faɗa aji a faɗin duniya suke so su samu, ba ma nigeria ba, yo wannan ko a India yaga wata yace yana so ai wallahi ba zata yi mashi musu ba, balle waɗancen talakawan"
Hajiya Kubra ce ta nisa gami da cewa " Humm bari dai Sa'a, wallahi kina ganin shi haka shegen tarin kai ne dashi kaman mahaifin shi, ba yanda banyi ba Amman abun yafi ƙarfi na, dama da dukiya nake taƙama, tau duk kansu daga shi har mahaifin nashi babu wanda bai fini ba a halin yanzu, nayi ƙoƙarin nuna ƙarfin uwa akan shi, Alhaji yana man ba razana da aure na, ni kau kjnga ba zanyi sake in rasa alhaji ba, samun kaman Alhaji a yanzu zai yi mani wahala... " Hajiya Laila ce ta katse ta da cewa ki bar mana komai a hannun mu Kubra, ba zai gagara ba, me aka yi a kayi Maryama balle wata ɗiyar ta cen, bari a gama hidimar nan zamu san abun yi, in ance ya ƙara kallon su ma ba zai kalla ba ko da kuɗi, kuma beside ma ni bana tinanin son ta yake yi, kinsan fa waɗannan miskilan yanda suke, nafi tinanin dai yana so ya kulle maki baki ne akan zancen aure da kike mashi" duk kansu sun gamsh Sa da hakan sun kuma sha alwashi ɗaukar mataki bayan kammala bikin Saudat da Nihal ɗin da yake saura sati biyu ayi.
Kai tsaye sashen shi ya koma, baya jin ma mararin fitar, idan ma ya fita ba inda za shi, shi ba mutum bane mai yawo, Shiyasa ma ko abokan kirki baya dasu, sau tari yafi buƙatar ya zauna gida yana aiwatar da dukkan muhimman abubuwa a cumputer ɗinshi akan ya fita ya ɓata lokacin shi ga banza wajen abokai, duk kuwa da yanda samari da dama ke fatan ace shi ɗin abokin su ne, koda kuwa na wucin gadi ne.
Bilal ya kira suka sha firar su, yake sanar dashi shigowar shi satin sama, domin su fara tsara yanda tashi hidimar zata kasance, "Abokina kayi ƙoƙari kaima ka fidda matar aure, duk da na san kai mata basa ga anka, Amman ai ba zaka ci gaba da zama haka ba, ko so kake yi ne sai mun haɗa ka da abie ne sannan zaka yi auren, ka kuwa san lokacin ka tsufa babu wadda zata gani ta ƙyasa"
Murmushi yayi irin wanda ke ƙara ƙawata mashi kyakkyawa fuskar shi, sannan ya shiga maida mashi da amsa "Ai sai kazo kayi mani malan, na lura kaima team ɗin Mom kake, Kaga mubar maganar nan sai kazo zamu tattauna, bari in tashi in fita wajen mata san cen da na sanya a tattara mani zamuyi meeting dasu da ƙarfe biyar na yammaci kasan yanda abubuwan suke yanzu wallahi, ina tinanin zan basu hutu ne har agama hidimar nan ta bikin yaran nan, kada kwalwa ta ta buga hakanan" "Is ok Friend sai kunyi magana" Bilal ɗin ya amsa mashi ta ɗaya ɓangaren, sallama sukayi yayin da ya tashi ya fice hannun shi ɗauke da ledar wayar nan.
Muɗi driver ya ba, ya umarce shi da ya kawo mani, shi zai fita ne sai ya dawo mmanka kula.
Cikin hanzari kuwa ya russuna ya amsa yana mai cewa "To yallaɓai" kai tsaye motar shi ya nufa, yayin da mudinya nufi sashen namu ba tare da ya damu da ya san menene acikin ledar ba.
Sallamar mudin ce ta katse ni daga shirya mana kaya da nake ta faman yi a wardrop, amsawa nayi gami da zura hijabina na leƙa ina mai gaida shi, amsawa yayi yana mai miƙo manledar dake hannun shi, "Gashi inji Alhaji ƙarami yace in kawo maki" amsa nayi ina mai cewa tou Mudi an gode, juyawa yayi ya bar wajen tin kafin wani ya gashi, yayin da na koma cikin ɗaki ina mai nuna ma umma ta dake zaune bisa darduma tana karatu.
"Wai Ya Ameen ne yace ya kawo mani" na faɗa ina dire ledar gabanta, ba tare da na damu da sanin menene ciki ba, duk a zato na Abunda ya danganci karatu na ne.
"Ki buɗe mana kiga menene a ciki" cewar umman tawa, tana mai ɗan ɗaure fuska haka kaɗan bansan menene dalili ba.
Kwalin dake cikin ledar na fiddo, gaba na ne ya faɗi, na ɗan ɗago na saci kallon umma ta da ta tura mani idanu taga yanda zanyi, hannu na kuma Sanyawa na zaro ƴar mitsitsiya waya ta da Naji tana vibrating a cikin ledar.
Saƙo ne ya shigo, number ce ban damu da in buɗe ba balle inga Abunda aka rubuta, durkushe nake gaban umman tawa kawai ina so inji hukuncin da zata yanke a kaina game da amsar kyautar waya daga hannun yaya Al'ameen ɗin.
~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~20~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Sai faman zare idanu nake yi, kaman wadda tayi ma sarki ƙarya, hukuncin umman tawa kawai nake jira inji me zata yanke akai.
Shiru tayi na tsawon minti biyar, nazari ɗiyar tata take yi, fatan take ace ba ita ce ta roƙeshi ba.
Nisawa tayi kaɗan a hankali ta muskuta, tana mai ajiye littafin dake hannun ta, har yanzu bata ɗauke idanun ta akai na ba.
" Suhan! Ina fatan dai ace ba kece kika roƙeshi waya ba, ba zaki iya haƙuri da wadda Allah ya baki ba" na tsinkayo muryar ta kwatsam cikin kunne na.
Girgiza mata kai na cigaba da yi, ina cewa "a'a umma wallahi ban roƙeshi ba" kwashe yanda muka yi da yaran nan nayi a makaranta kwana biyu da suka wuce, har zuwa kan inda ya ɗauki wayar bai bani ba, Amman ban gaya mata ya goge man ƙwalla ba, balle ince ya kama man hannu, don na san tashin hankalin da zan fuskanta.
Shiru ta sake yi sannan tace "Allah shi kyauta, an gode, Amman ina so ki riƙe talaucin ki, ki dinga juya ma abun duniya baya, wannan ƴar ƙaramar ta isheki, sai dai bazan hana ki amfani da wannan ba, saboda zamani ne yazo da ita"
Cikin ɗan murmushi nace "to umma nagode" sake kallo na tayi da wani irin yanayi, sannan ta shiga cewa "sai ki kira shi kiyi mashi godiya ko? Sannan ki kula ba zan gaji da cewa ki kula ba, kindai san zaman da mukeyi a gidan nan"
"Eh umma haka ne, to zanyi mashi godiya insha Allah" na faɗa murya ta fal farin ciki, sai dai cen ƙasa zuciya ta, wani irin tsoro ne da fargaba, me zai faru idan aka ce maganan Afnan ce ta fara tabbata?, me ne ya sanya shi share man hawaye Wancen lokacin? Me hakan ke nufi?"
Jikina ne yayi sanyi ƙalau, komawa nayi na zauna, ina mai zaro wayar daga cikin kwalin ta, waya ce mai matuƙar kyau da tsada, ko a cikin ƴaƴan masu dashi ɗin ba kowa ne ke riƙe irin ta ba.
Gashi tana da girma, har ina jin tayi ma hannuna mugun girma wajen riƙewa, saidai ko babu komai nayi farin ciki, ɗan chatting ɗin nan da kowa keyi nima zan fara, zan ga me duniya ke ciki, lokaci ne nima da zan fita daga cikin wannan duhun kan zama waje ɗayan.
Ban mantawa, lokacin da nake secondry school, dukka kusan ƴan ajinmu na da waya, kasancewar ta makaranta da ƴaƴan manya, wasu ma biyu ne suke da ita.
Ɗan murmusawa nayi, tinowa da nayi yanzu fa har afnan zamu dinga magana da ita kullum, ga wata ƙawata tin ta makaranta mai suna khairat, ta soni sosai, tana tausaya mani, ita gidan su masu hali ne, har wayar taso bani, nice dai na ƙiya don na san halin umma ta, yanzu gashi da nayi haƙuri na samu irin wadda ban zata ba ban tsammani ba.
Kunna ta nayi, aiko ta ɗauka kaman jira take yi, nayi mamakin da layi ciki guda ɗaya, saidai babu komai a kanta sai Numbers guda biyu an masu saving da AMD bansan me hakan ke nufi ba.
Niyyar goge su nayi, sai kuma wani tinani ya ɗarsu a zuciya ta, in shi ya ajiye su da? In suna da muhimmanci fa? Share wa nayi ban ko taɓa mashi abun shi ba, na jawo waya ta ina maida numbobi na ciki, har da ta khairat ƙawa ta da na janye mawa kusan shekara nawa? Itama ganin hakan sai ta haƙura ta ƙyale ni, kada ta jaza man matsala, fahimta da tayi umman tawa bata son tarayya ta da ita. Ko tana ina ma yanzu haka?
Dukkan motsi na umma ta na kula dashi, tausayi na ne fal acikin ranta, tana addu'a Allah ya kawo lokacin da nima zan zama wata abu, lokacin da zamu fita a halin ƙuncin da muke ciki, lokacin da muma zamu zama mutane masu cikakken ƴanci kaman kowa.
Sallamar Hafsat ɗince ta katse mana zaman shirun da muke, niko ina ta faman jujjuya waya a hannu, mamaki ya cika ni, ta yadda naga kuɗi tsababa cikin wayar, yanzu ko na tabbata wayar tashi ce, ƙila siyan ta yayi yana amfani da ita ya bani, bata san shine ya siya domin ita ba, ya zuba kuɗi domin ita, saboda harga Allah cin mutumcin da aka yi mata yayi mashi ciwo, ace kaman wanda yake gidan su ace ana ci mashi mutumci saboda wani abu wai waya, menene amfanin arziƙi nasu in har ba zai kare mutumcin mutanen dake rayuwa cikin shi ba?
Da murmushi na bita ina mai cewa "A'a Hafsy ce? Shigo mana" na faɗa ina nuna mata gefen katifa inda nake zaune, alamar ta zauna, murmushi tayi ta ƙara so ta zauna tana gaida umman tawa, itama cikin dakin fuska ta amsa tana mai sake tambayar ta maman su, duk suna lafiya tace, a hankali suka shiga fira da umman tawa, yayin da ni kuma hankali na na kan waya, har umman tawa ta miƙe ta shiga ban ɗaki, sai a sannan ne ta maido hankalin ta kaina.
Hannu ta sanya ta amshi wayar, tana murmushi take faɗin "Ya Suhan, wannan mai zafin fa? Yaushe kika shiga yayi ban sani ba? Domin dai ina da number ɗinki, Amman naga ko WhatsApp bakyayi kuma kina da irin wannan babbar waya haka, ko ni fa bana iya riƙe irin ta" ta faɗa fuska cike da murmushi, ta ƙara she da zaulaya.
Hafsat ɗin dai kaman yanda kuka sani ɗiya ce ta yayan Alhaji mustapha Dambulan, watau Alhaji Auwalu da yaje zaune cen Katsina, tana zuwa gidan akai akai, in suna ƙasar, saboda iyayen su masu zumunci ne akai akai, suna yawan tura ƴaƴan su gidajen nasu, hatta su saudat ɗin ana tura su Katsina, duk da dai basa so, suna cewa takura suke yi wai basa walawa a gidan yayi masu ƙarami, duk da kuwa irin girman gidan nan da kayan more rayuwa dake cikin shi shima, domin yanzu Alhaji Auwalun ya kai matsayi director a ma'aikata tasu,ya samu rufin asiri daidai gwargwado, duk da kuwa bai ko kama ƙafar Alhaji Mustaphan ba. Bana hafsat kaɗai ba, dukkan in ƴaƴan Alhaji Auwalun da hajiya zainab, yara ne masu sanyin hali, girmama naga a dasu, da kuma kawaici, basa da girman kai Sam, wannan ce ta sanya tamu tazo ɗaya da Hafsat ɗin da ko zata girme mani tau fa da kaɗan ne. Ita dai ba'a isa a hana ta zuwa sashe namu ba, hasali a In tazo ba wani damuwa da al'amarin ta suke ba, ba ta ita suke yi ba, lokutta d adama ma haushin ta suke ji, suna cewa duhun kai yayi mata yawa, itama ta gama karatun ta tsaf a makarantar ummaru Musa ƴar adu'a dake jihar Katsina dabon.
Sai gashi kuma Allah ya bata miji nagari, na nuna ma sa'a, hasali ma dukka mazajen daga na Saudat, har Nihal ɗin babu Abunda zasu nuna ma nata, sai ma shi ya nuna masu tarbiyya da kuma dattako.
Murmushi na ɗanyi ina cewa "Uhm Hafsy kenan, nima yanzu wayar ta iso mani wlh" kasancewar ta mutum da ta san halin da muke ciki, da irin zaman da mukeyi, ya sanya na kwashe labarin yanda aka yi na samu wayar na faɗa mata.
Aiko murna ta fara yi, tana ce an "kinga kada ki damu, rabon ki ne ya rantse, ai Ya Ameen ɗin mutumin kirki ne, Sam shi ba halin su ɗaya dashi ba, yana taimakon na ƙasa dashi, ko bayan dawowar mu Naji ana cewa ya raba ma dukkan in ma'aikatan kamfanoninshi kayan abinci da tufa fi masu kyau da tsada, a bakin su Hajiya Naji da tana waya da wasu ɗazu.
Amsar wayar tayi ta shiga buɗe man abubuwa irin su WhatsApp, Facebook, da wani chat wai shi duo, nice nace ta bar shi hakanan, har sai na iya waɗannan tukunna.
Fira muka shiga yi sosai, har take cewa zata dawo ɗakinmu da zama kafin lokacin tafiyar tata yayi, nake ce mata tayi haƙuri ta rufa mana asiri, kwanciyar ta tayi tana cewa "uhmm, kanki kuma akeji Suhan, KEDAI Allah yayi maki tsoro kaman farar kura"
Koda ta sanar da umman tawa da ta fito daga banɗaki, murmushi kawai tayi, ai kaso mai sonka ka kuma girmama duk wanda yace yana sonka.
"Umma wata Alfarma nake so in roƙe ki don Allah, ki ara man suhana ta taya ni zuwa wajen gyaran jikin, da ƙarashe siyayya har zuwa lokacin da zan koma gida, kinga dai su Saudat ware ni suke yi, bana da aboki ko ɗan uwan da zan tun kara, Suhan ɗin dai ita ce"
Hafsat ɗin ta faɗa tana marairaicewa, kaman wadda zata yi kuka, lokaci guda tana kallon umman tawa.
Ba matsala umma ta tabbatar mata, saidai taja hankalin u akan mu kula da me mukeyi, idan mun fita mu san ina zamu, kuma kada mu sake mukai magariba a waje waɗannan sune sharuɗɗan ta.
Da to muka bita, hafsat ɗin kuwa taji daɗi, dama ko ba komai bata kawo ma ranta umman tawa zata hana, saidai ta san halin umman tawa, wani lokaci kaman mai aljannu take, zata iya hanawa a lokacin da ba'a tsammata ba.
Faɗa mata nayi ina son in kira yayan in mashi godiya Amman ina jin kunya, harara ta tayi cikin wasa tana cewa "menene na kunya Suhan? Ai ya yanki ne yanzu an riga an zama ɗaya, ki kira shi kawai wlh, ko kuma ki tura mashi text ai zai gani godiya daɗi gareta, balle yayan namu da yake miskili yana iya dakin fara godiya ya katse wayar"
Amincewa nayi da gara in mashi text, in mun haɗu a zahiri na ƙara gode mashi, sai dai fa inda gizo ke saƙar, bansan me zan rubuta ba, sai jujjuya wayar nake a hannu.
Hakan da ta fahimta ne ta fizge wayar a hannu na tana cewa "Dallah kawo nan, kai a tukunya, ai gara ma kizo kije makarantar ko kin ƙara wayewa, godiya ma kin gagara yanda zakiyi ta, wannan duk lokacin da kika yi saurayi naga yanda zakiyi dashi" ta faɗa cikin zaulaya da dariya, Nidai bance mata komai ba, sai a kishingiɗawa da nayi ina mai ɗan murmusawa a hankali.
Ban san me ta rubuta ba, na dai ga kawai ta jawo wayar ta ta ɗauki number ɗinshi ta tura, sannan ta miƙa man wayar tana faɗin "Done, saƙo ya isa"
Firar mu muka cigaba da yi, tana faɗ man yanda tsare tsaren bikin nata zai gudana, duk da ba wani pherty zata yi ba illa iyaka traditional day da za'a gudanar lambun gidan, wanda su kau su saudat sun haɗa pherty ya kai kala biyar wata rana ma sau biyu za'ayi.
Ita dai tace ba zata shiga ba, cikin hidimar su, bata da ra'ayi, duk da mijin nata yaso ayi ko kala biyu ne saboda abokan shi, Amman ta kafe kawai tace kowa ya sanyo kayan gargajiya, yazo yaci goruba ya sha rake🤣🤣
Nan ne na ƙara fahimtar sauƙi hali irin na hafsat ɗin, lallai duniya da Abunda ke ciki ta basa gabanta, tana tausaya ma mijin nata, tace wannan kuɗin da zai kashe sun isa yayi hidima da baƙin shi har su tafi.
********************
Shigar shi kenan part ɗin nashi, a matuƙar gajiye yake, waya kawai yayi ma Nihal ta kawo mashi snacs yunwa yake ji, kai tsaye ɗakin shi ya faɗa ya shiga kwaɓe kayanshi, wanka yake son yi ko zaiji sauƙi gajiyar dake nuƙurƙusar shi, gashi part ɗin nashi yayi matuƙar dauɗa, rabon da ya samu kyakkyawa n gyara tin wanda Suhan ɗin tayi mashi.
Bayan ya gama wankan ne, ya shirya cikin pajmas na maza, saboda sauƙin nauyin su, gashi yana so ya kwanta ya ɗan huta, sallama yaji ta baƙuwa murya daga cen falin nashi, a hankali ya miƙe gami da fita domin ganin wake sallama, kaman muryar mace yake iya jiyowa.
Maree ce tsaye, hannun ta ɗauke da farar roba mai garai garai, kana iya hango Abunda ke ciki, a tsakiyar falin ya iske ta tsaye tana ƙare ma sashe nashi kallo, ita asali ma bata taɓa shigowa cikin shi ba, saidai kawai ta hango shi daga nesa, duk da a zahiri kasan zubin nashi dama zai yi kyau, saidai ya zarta yanda take tunani.
Ƙamshin turare ne, ya alamta mata lallai akwai wani tsaye kusa da ita, ɗan zabura tayi kaɗan tana cewa "Yallaɓai barka da hutawa, gashi inji Aunty Nihal tace in kawo maka" ta faɗa tana miƙa mashi robar cikin ƴar rissinawa tana wani far-far da idanu, ko kallon ta baiyi ba, ya nuna mata stool dake gefen kujera ajiye, alamar ta ajiye bisa, gami da juyawa da niyyar komawa cikin ɗakin yana cewa "Ki turo mun Nihal ɗin"
Da kallo ta bishi ta baya har ya shige ɗakin nashi, ajiyar zuciya ta sauke, dama haka Al'ameen ɗin yake? Lallai dole ne ta sake taku, wannan ai kalar nasu ne, ko ba zai aure ta ba, lallai dole ne ta ɗanɗana zumar shi, zata san yanda tayi ta jawo hankalin shi gareta, saidai ita kanta ta san da wuya, da wahala, domin a yanda ta ganshi ba zai yi wasa ba ko ya ɗauki wargi, ƙafafunta ta ja gami da barin sashe tana ta saƙa mugun nufi da mugu nƙuduri akan bawan Allah Al'ameen.
Har ɗaki Nihal ɗin ta tadda shi, kwance yake ba bacci yake ba Amman idanun shi a kulle suke, ƙare mata kallo yayi daga sama har ƙasa, sannan ya shiga balbake ta da faɗan, ya sanya tayi mashi abu, ta sanya wata ƙazama cen ta kawo mashi Abunda zai ci, mamakin shi take yi, ai ita a sanin ta yana cin abun hannun ƴan aiki, tinda yana cin na Suhan da mama Maryamar.
Katseta yayi daga tinanin da take yi, "dole ki amshi hukuncin, gobe in Allah ya kai mu ki tabbatas kin gyara mani sashe na tsab, kaman yanda kika ga Suhan nayi mashi, bana son ƙazanta, baƙi zanyi cikin satin nan zaki iya tafiya"
Juyawa tayi tana kumbura baki, har ga Allah in har Yayan nasu na ƙasa yana takura masu, ya sanya sun dawo ƙasar kuma yana neman ya sanya su wahala?
Aikin gyaran wannan sashen ai ba ƙaramar wahala bane, ita da ko toiket ɗinta bata iya wankewa, yanzu saidai ta sanya Maree tayi mata, duk da bawai ta gansu da tsaftar mareen ba kaman suhana, zuciyar ta na raya mata ta sanya Maree ta gyara mashi, wani sashe na zuciyar nan kwabar ta, tabbas zai iya ganewa ba ita tayi ba, inko hakan ta faru ta kaɗe har buzunta, ba zasu rabu ta daɗi ba, ɗan guntun murmushi tayi, mafita da ta samo, ai yace irin yanda Suhan keyi ko? To ba matsala, ai Suhan ɗin ce ma zata yi maka yaya sha kuruminka, tinda aikin nata kake so. Da haka har ta isa sashen nasu, tana labarta ma Saudat ɗin yanda sukayi da yayan nasu, murmushi kawai saudat ɗin tayi gami da cewa "gara ki sanya ta tayi shegiyar, kinga yanzu daga dawowar mu har ta janye Hafsy, ai wannan yarinya wallahi akwai mayya". (😝😝 kunji fa readers ashe sun damu hda hafsat ɗin🤔)
********************
Bacci yake son yi, saidai yunwa ta ishe shi, gashi bai jin zai iya cin abinda yarinya ta kawo mashi, miƙewa yayi a hankali ya isa kitchen ɗin da yake mallakin shi, kaman wata macen, fridge ya buɗe ya ɗauko lemo kwali da ceramic cups ya fito, kai tsaye bedroom ɗin ya koma gefen gado ya zauna, gami da tsiyaya lemon ya sha, kaman wanda aka yi ma dole.
Wayar shi ce tayi tsuwwa, alamar saƙo ya shigo, share ta yayi ya cigaba da shan lemon shi har ya gama, gami da miƙewa ya maida kitchen, ya dawo daƙin gami da saisaita ƙarfin Ac ɗin dake aiki cikin ɗakin.
Gadon nashi ya haye, tare da jan lallausan bargon nashi ya rufe ƙafafun nashi ruf, wayar shi ya jawo gami da maida ta sylent, har zai ajiye sai kuma ya lura da ɗan akwatin saƙo da yake cen sama wayar a maƙale.
Cikin kasala ya buɗe, yayi mamakin ganin sunan ta ɓaro ɓaro a wayar, bai ƙara shan mamaki ba har saida ya karanta Abunda saƙon ya ƙunsa, karantawa yayi ya sake maimaitawa, ita ɗin ce kuwa? Zaune ya miƙe bisa gadon, gami da jan bayan shi ya jingina shi jikin lallausan tissue foam ɗin dake jikin wood ɗin gadon. Sake dai maimaitawa yayi, lallai ita ce ta turo idanun shi ba gizo suke yi mashi ba.
Hannu ya sanya gami da ɗan yin typing a hankali ya maida mata reply, unlight ɗin wayar yayi, gami da tura ta ƙarƙashin fillow.
Zamewa yayi ya kwanta idanun shi a lumshe, zuciyar shi na ta kai komon karanta saƙon nata, su kansu idanun nashi sun gaza dena nuno mashi hoton Rubutun, tiryan tiryan yake karanta shi cikin idanun shi, kaman yana kallon scream ɗin wayar ne, a hankali bacci mai nauyi ya kwashe shi.
Niko da muke cen ɗakin mu mun bararraje muna ta fira da Hafsy, ko ba komai dai Naji sauƙin kaɗai ci yau, na samu aboki yar fira, tana ta bani labarin tafiyar su, ina ji daman nice ace yau na ganni a ƙasashe ƙetare, mu biyu ne cikin ɗaki, domin umma ta ta fice ƙofar ɗaki gami da shimfiɗa tabarma ta zauna tana yanke farce.
Sabuwar waya ta ce ta ɗauki tsuwwa, alamar shigowar saƙo, hannu na sanya gmi da jawo wayar, na buɗa. Cikin ƙwalalo idanu nake kallon wayar, hakan ce ta jawo hankalin hafsat ta tashi zaune tana tambaya ta ko lafiya?
"ina fa lafiya Hafsy?" na faɗa bayan na gama karanta Abunda ta ta tura da shi kuma wanda ya turo.
"To menene a ciki Suhan? Naga ai godiya kawai nayi ba wani abu ba, menene na damuwa, shima ko kinji yace wani abu ne?" ta faɗa bayan ta amshi wayar ta karanta reply ɗin da yayo.
"A'a Amman ni kin sa har na fara jin kunya, waɗannan kalama ai irin naku ne na masoya hafsat, kada fa ki sanya yayi tsammnin wani abu" na faɗa hankali na aɗan tashe, har ga Allah kunya duk tabi ta baibaye ni, kaman ina gaban shi, sai yanzu nayi na damar barin ta ta tura Abunda ta rubuta ba tare da na amsa na karanta ba.
"kinga karki wani damu kanki Suhanan umma, ki kwantar da hankalin ki Yayan namu wayayye ne ba zai kawo ma ranshi komai ba akasin Abunda aka rubuta"
Ta faɗa cikin son ƙarfafa man guiwa, Nidai lafewa nayi jikin bango ina sauke ƴar ƙaramar ajiyar zuciya, gami da ce mata "To Hafsat Allah ya sanya"