Da daddare sultana bilkisu takira zarah bayan sun gaisa nan take fad'amata zuwan da yarima zaiyi gobe,
zarah saida gabanta yafad'i ammah tadake tace ummi Allah yakaimu.
A ranar kasa baccin kirki tayi, tunani da fargaba duk suka cikata.
wanshe kare shaheed shiryawa yayi yanufi gidan yarima, lokacin da yaje part d'in yarima nan guards d'insa suka gaishesa sannan d'aya yashiga yasanar da yarima zuwan shahid nan yarima yabada izini abarsa yashigo.
ko da shahid yashiga parlourn tsaye yayi bakin k'ofa yana kallon yarima da yake kwance saman 3 seater cike da mamaki yace haba yarima kaifa kacemin after la'asar zamuje ammah jibeka baka shiryaba.
yarima batare da ya d'ago kai ya kallesaba cike da rashin damuwa yace ina kenan?
cike da jin haushi shshid yace au kana nufin ka mance inda zamuje? yanzu saboda Allah amaryartaka ce kamance da ita ko me?
ta6e baki yarima yayi saboda shi shaf ya ma mance da maganar zuwan da zasuyi wajen zarah.
shahid jinjina kai yayi yace lallai yarima ka cika d'an wulak'anci.
harara yarima yawurga masa yace toh ina ruwanka ai sai kazauna kajirani inshirya,
dariya shahid yayi yace ba fa ruwana ranka yadad'e yanzu dai kaje kashirya kafito muje dan Allah kar kadad'e.
ko kallonsa yarima baiyiba yashige bedroom d'insa.
tashi shahid yayi yakunna kallo sannan yabud'e freezer yad'auko maltina yazauna yana sha yace kafin wannan d'an rainin hankalin yafito.
bayan minti ashirin yarima suhail ne yafito sanye cikin dakakkiyar shaddarsa blue wadda tasha aiki, kansa sanye da hula kalar shaddar, kamshin turarensane ya ankarar da shahid daga kallon da yake dasauri yajuya yazuba masa ido yana kallonsa yace kai yarima wannan kyau haka saikace yau zaka angwance? gaskiya kayi kyau sosai natabbata ita kanta amaryar bazata ganekaba kar fa karikita d'iyar mutane,
yarima suhail wayoyinsa yad'auka batare da yace ma shahid komai ba yawuce zai fita,
dasauri shahid yamik'e yabi bayansa, ko da suka fita nan guards d'insa suka take masu baya, wajen da aka tanadar musu motocin da zasu fita da su suka nufa tun kan su ida isa naga anbud'e musu bayan wata dank'areriyar mota bak'a da take tsakiyan sauran motocin, saida suka shiga aka maida aka rufe sannan cikin sauri guards d'in sukaje suka shiga sauran motocin.
A chan 6angaren zarah Aunty kubra sata tayi tashirya, sosai tayi kwalliya had'ewa tayi cikin material Black colour mai ratsin marron nan tamurza d"aurin kallabinta tare da yafa veil marron, takalmanta da jakkarta ma duk maroon colour ne.
ba ita kantaba hatta su Aunty kubra sun yaba ma kyaun da zarah tayi, 6arin turaruka akayi mata sosai a jikinta.
ko da su yarima suka iso mai gadi hangame musu gate yayi motocinsu a jere suka shigo; dasauri guards d'insa suka fito daga cikin motocin da suke sukazo suka bud'ema su yarima murfin mota, ahankali yasafko k'afarsa sannan daga baya ya ida fitowa daga cikin motar, cike da tafiyarsa ta k'asaita yake takonsa shaheed yana gefensa nan wasu daga cikin guards d'insa suka take masu baya har part d'in mummy sa'adatu, daga wajen parlour guards d'in suka tsaya inda yarima suhail da shaheed suka shiga ciki da sallamarsu lokacin mummy sa'adatu tana shirin tafito taje ta tarosu,
ganinsu yasa tayi murmushi tare da cewa marabanku da zuwa, yarima murmushi kawai yayi shaheed ne yace yauwa mummy sa'adatu shidai shaheed kansa a d'aure yake har suka zauna domin yayi tunanin d'iyar mummy sa'adatu ce yarima zai aura, shidai yarima daman ummi ta fad'amasa zarah tana nan gidan hajiya sa'adatu kuma ta ce yabiya gidansu zarah yagaishe da iyayenta saisa baikawo komai a ransaba.
bayan sun zauna nan suka gaisheta cike da girmamawa, ta amsa cike da kulawa tare da tambayarsu mutanen gida sukace kowa yana lafiya, nan da nan aka cika musu gabansu da kayan tand'e-tand'e da shaye-shaye, mik'ewa hajiya sa'adatu tayi tare da cewa son kugama cin abinci sai inkira muku ita.
shaheed ne yatsiya musu ruwan inibi yamik'a ma yarima sannan yace mummy wlh a k'oshe muke abincin bazai shigaba.
murmushi mummy sa'adatu tayi tace ku daman ina rik'e da ku bakwacin abincin ginnan, kokuma ma ai bazuwa kukeba duka wannan zuwanku na ukkune shima duk ta dalilin umminku, bakwason zumunci ko?
yarima suhail murmushi yayi yace insha Allahu zamu gyara, tace kullum wak'ar kenan bari inje inkira muku ita toh tunda kunk'i cin abinci.
ko da hajiya sa'adatu tafita shaheed apple yad'auka yana ci tare da kallon yarima da yake rik'e da cup d'in ruwan inibi yace kasha mana,
yarima batare da yayi maganaba ya aje cup d'in tare da jawo wayarsa yana operated d'inta, shaheed murmushi yayi tare da ci gaba da cin Apple d'insa.
Hajiya sa'adatu lokacin da tashiga part d'in da su zarah suke tun daga bakin k'ofa tafara washe baki tana kai daughter wannan irin kyau haka?
zarah dai murmushi kawai tayi tare da sunkuyar da kanta domin gabanta fad'uwa kawai yake,
Hajiya sa'adatu tace yauwa toh yanzu kitashi kije parlour na suna chan suna jiranki.
kallon Hajiya kubra zarah tayi, Hajiya kubra tace kitashi mana.
idanuwanta nan suka ciko da k'wallah, Hajiya kubra tace a'a zarah dan Allah kar kiyi kuka ki6ata kwalliyarki.
zarah murmushi tayi tace Toh Aunty kubra, nan kuyangin da ummi ta aiko mata da su suka take mata baya tafiya take cikin takunta mai aji hango motocin su yarima da tayi da sauran guards d'insa saida gabanta yasake fad'uwa duk tsoro da fargaba suka cikata har ta isa parlour nan guards d'in da suke tsaye wajen k'ofar suka gaisheta ahankali tabud'e labulen dakin tashiga inda tabar kuyangin tsaye waje.
cikin 'yar siririyar muryatarta tayi sallama, shaheed ne ya amsa mata tare da d'ago kai yakalleta zaro ido yayi yace wow masha Allah matarmu bismillah mana.
ahankali zarah tatako tazauna saman kujerar da take opposite d'insu cike da nutsuwa tagaishesu, shahid ne kawai ya amsa mata domin yarima har lokacin bai d'ago ya kalli inda takeba barema asa ran zaiyi magana.
Shaheed kallonta yayi yace amaryarmu gaskiya kin had'u, dafatan mun sameki lfy? , murmushi zarah tayi tace lafiya lou ya gida?
shahid yace kowa yana lafiya, sannan yamaida kallonsa ga yarima da yake zaune kamar baisan abinda akeyiba, murmushi shahid yayi yace ranka yadad'e kayi shuru bakace komai ba,
Zarah ahankali tad'ago kai takalli mutumin da tunda tashigo baiyi maganaba dannar wayarsa kawai yakeyi saida gabanta yafad'i, batare da yad'ago kai ya kalletaba yace akawai event d'in da zakiyi ne?
shuru zarah tayi tana kallonsa, ahankali yarima yad'ago kai yakalleta nan suka had'a ido, dasauri yajanye idonsa daga kallonta yace kamar nawa kike buk'ata inbaki?
zarah dakyar tabud'e baki tace bana buk'atar ko naira, ta6e baki yarima yayi, ganin haka yasa shahid yace a'a amarya kar kice haka kifad'i yadda kike buk'ata nagama kamar kunyata kukeji kowa yakasa magana bari inbaku waje kuyi magana.
Yarima yace no nima ai tafiya zanyi yanzu, harararsa shaheed yayi yace toh ai sai kugaisa dan naga ko gaisawa bakuyi ba kar ace ni nahana nabarku lafiya, yana gama fad'in haka yaficce yabar musu d'akin,
nan d'akin yad'auki shuru ba'ajin motsin komai zarah wasa kawai take da yatsun hannunta, jin baida niyar yin magana yasa tad'ago kai takalli yarima dayake ta dannar wayarsa kamar baisan da zaman mutum ba a wajen, zarah wani k'ululune taji ya tsaya mata a mak'oshi, janye idonta tayi ga kallonsa mamakinsane yacikata cikin ranta tace mutumin nan ko dai kurma ne? chan wata xuciyantace toh kuma ai yanzu taji ya yi ma d'an uwan nasa magana, chan da tagaji da shurun ahankali tace ina wuni?
shuru yarima yayi bai amsaba jin shurun da yayi yasa tad'auka baijitaba nan tak'ara d'ago kai takallesa har lokacin dannar wayarsa yake, sai a lokacin ya amsa mata cikin muryarsa mai dad'i, zarah mamakine yakamata domin bata d'auka miskilancin nasa yakai hakaba, ahankali tace lallai wannan mutumin d'an wulak'ancine, jiyo muryasa tayi yace magana kikayi?
cike da k'ulewa tace ni bance komaiba,
d'ago kai yarima yayi yakalleta kallo d'aya yayi mata yad'auke kai tare da mik'ewa tsaye, takawa yayi yaje inda take ya aje mata cheque a gefenta sannan yace gashinan idan basu ishekiba sai kiyi magana.
zarah ida k'ulewa tayi ganin baima jin zai iya bata saima ajemata yayi, cike da jin haushi tace kabarsu kawai ba abinda zanyi da su.
yarima kallonta yayi cikin rashin damuwa yace indai nafitar da kud'i bana maidasu idan basu ishekiba zaki iya yin magana, yana gama fad'in haka yawuce yafita yabar d'akin,
tsaki zarah taja tare da mik'ewa tabi bayansa domin suyi sallama da shaheed, ganinta yasa shaheed yatafo wajenta yana murmushi yace amaryarmu yanzu nake shirin zuwa muyi sallama.
Murmushi itama tayi tace nima cewa nayi bari nazo muyi sallama, yarima gaba yayi aka bud'e masa mota yashiga saida suka iso wajen motar sannan zarah tayi musu sallama takoma ciki tana mamakin halin yarima, cikin ranta tace ashe akwai babban aiki a gabana.
ko da su yarima suka kama hanya shahid kallon yarima yayi yana murmushi yace gaskiya yarima ka iya za6en mata kaga yadda kukahad'e kukai matching? yarima batare da ya kallesaba yace bawani dacewa ai wlh kai yakamata ma ace anma dole ka yi aure, dariya shahid yayi yace nima fa abin yana damuna ganin har kana shirin yin na biyu ammah ni ko d'aya banda ita, yamitsa fuska yarima yayi yace nima ba ason raina nayi aure yanzuba dan banma shirya yinsaba by my age, kaduba kaga duka yanzu fa 28yrs ammah mata har biyu tsaki yarima yaja cike da takaici yace ina ma amfanin hakan.
dariya shaheed yayi yace ai abun jin dad'ine hakan kuma matsayinka ya kai hakam, nima insha Allahu kwanannan zan faso zan baku mamaki,
ta6e baki yarima yayi yace wajen surutunka kayo yarinya ko?
shahid gyara zamansa yayi tare da cewa haba dai kabari zakasan ko wacece nan gaba jira nake agama wannan hidimar auren naka nima in6ullo kai dan bama zanso asa sama da wata d'ayaba,
yarima suhail jingine kansa yayi da sit din da yake zaune tare da lumshe idonsa,
ganin haka yasa shahid yaja bakinsa yayi shuru dan yasan maganarce ta ishi yarima.
tunda suka kama hanya basu zarce ko inaba sai gidansu zarah saboda tun dare sultana bilkisu ta kira iyayen zarah ta shaida musu yarima yana nan zuwa zai gaishesu, dan haka tun da safe suka dinga hidindimu kaji shidda baba yasiyo akayi pepper da ukku aka soya ukku, had'add'ar wainar shinkafa su mama sukayi da miyar ganye sannan suka had'a kunun aya wanda yasha madara, bayan sun gama duk suka shirya suna jiran zuwan yarima dan su Aysha sun k'osa sosai suga mijin zarah.
A gaban gidansu zarah sukayi parking d'in motocin dasauri guards d'in sukafito daga motocin da suke ciki sukazo suka bud'ema su yarima k'ofa tare da cewa ranka yadad'e nan ne,
yarima batare da yafitoba yadinga k'arema gidan kallo cike da mamaki, shima shahid mamakine yacikasa ganin gidan da yarima yanemi aure.
malam musa da yake zaune cikin gida jin k'arar mota yasa yakalli su mama yace ina tunanin sun iso bari inje induba,
cike da jin dad'i Aysha tace yauwa Allah yasa sune.
malam musa ko da yafito yaga jerun motoci cike da fara'a yanufo wajen, ganinsa yasa yarima yafito daga motar, nan guards d'insa suka shiga gaishe da malam musa.
malam musa hannu ya mik'a ma su yarima suka gaisa yace maimakon kushigo sai kukayi tsaye? shaheed ne yace daman yaro muke nema mu aikasa yayi mana sallama da kai,
malam musa yace ayyah Allah sarki toh bismillanku.
batare da sunyi musu ba sukabi malam musa suka shiga har cikin soron gidan, saman tabarma suka zauna.
cike da girmamawa suka gaishe da malam musa ya amsa musu tare da tambayarsu mutanen gida, shaheed ne yace suna lafiya lou, sunce agaisheku
malam musa yace muna amsawa sannan yakalli yarima da tunda yagansa yagane shine mijin da zarah zata aura, malam musa yace ya su mahaifiyartaka?
murmushi yarima yayi kansa yana sadde a k'asa yace lafiya lau suke.
malam musa yace toh masha Allah, mik'ewa yayi yace ina zuwa nan yashiga gida.
bai dad'e da shigaba yafito tare da su Rauda da suke d'auke da kuloli da sallamarsu suka shigo, su yarima suka amsa musu gabansu suka aje kulolin, tare da gaishesu cike da sakin fuska su yarima suka amsa, malam musane da yake tsaye yanuna rauda yace wannan itace yayar amarya, kallonta yarima yayi yana murmushi yace sannu yayarmu.
itama rauda murmushin tayi tace yauwa k'anena.
Aysha ce tayi karaf tace nikuma nice k'anwar Aunty zarah kuma autarsu.
gaba d'ayansu dariya sukasa mata banda yarima da yayi murmushi kawai, shahid yace tun ba'a tambayekiba?
yarima suhail yace ina ruwanka ai ni tafad'a mawa ko k'anwata?
'yar dariya Aysha tayi tace eh yayana, ammah ai kaine angon namu ba wannan ba (tanuna shaheed)
shaheed yace nine mana.
Aysha tace chab gaskiya wannan nafiso yakasance mijin yayata.
murmushi yarima yayi yace saboda me?
Aysha tace saboda kunfi dacewa da ita,
yaya rauda tace zanci gidanku Aysha banason rashin kunya.
shaheed yace a'a babbar yaya kibarta kawai tunda tace bamu daceba sai inhak'ura inbar masa.
Aysha tace A'a ni ba haka nake nufiba kaima ka dace da yayata sosai.
shaheed kallon yarima yayi yana murmushi yace toh ka dai ji abinda tace kaje nabarmaka ita.
shima yarima murmushi yayi yace k'yalesa my sis ai nine angon ba Shiba tsokanarki kawai yakeyi.
cike da jin dad'i Aysha tace yeahhh wlh naji dad'i, murmushi kawai suhail yayi batare da yace komai ba.
daidai lokacin abbah yafito daga cikin gida d'auke da swan water yace kutashi kubasu waje suci abinci mana.
atare suka mik'e suka shige gida, abbah ajiye ruwan yayi yace dan Allah kuci abinci.
shaheed ne yace Alhmdllh abbah wlh a k'oshe muke.
abbah yace gaskiya ba zanji dad'in hakan ba nasan kunfi k'arfin abincinmu ammah ko yayane kusanya albarka.
yarima ne yakalli abbah yana murmushi yace kar kadamu abbah zamu ci.
abbah yace yauwa gaskiya naji dad'i bari inshiga ciki kafin kugama.
Bayan abbah yashiga gida shaheed ne yabud'e kulolin cike da jin dad'i yace yarima ur best food ne fa,
yarima batare da yakalli abincinba yayi murmisho, shaheed ne yayi serving d'insu ya aje ma yarima nasa a gabansa.
yarima waina biyu yaci tayi masa dad'i sosai saida ya jinjina ma k'ok'arin da iyayen zarah sukayi wajen tarbarsu, kunun ayan dai saida yashanye 1 cup kasancewar yana sonsa sosai, shidai shaheed loda ma cikinsa kawai yake yana santi har yaso yaba yarima haushi.
bayan sun gama abbah yadawo nan yazauna suna d'an ta6a hira kad'an-kad'an sannan yashirga da su cikin gida suka gaishe da mama cike da girmamawa, da zasu fito yarima dubu d'ari yamik'a ma Aysha yace sunyi hidimar bikki, da fari k'in kar6a tayi dan baba yahana saida yarima yace shifa ba dan wani abu yabataba kawai saboda tayi kwalliyar bikkin yayarta da za'ayi a matsayinta na auta, dariya sukayi sannan sukayi masu rakiya har wajen mota suna godia, cike da jin dad'i domin suna ganin zarah tayi sa'ar miji mutumin kirki.
A cikin mota shaheed kallon yarima yayi yace gaskiya mutanen nan suna da mutunci sosai daman daga ganin zarah kaga mutuniyar kirki ashe wajen iyayenta tagada.
yarima a tak'aice yace danginta suna da kirki sosai.
shahid Jin maganar da yarima yayi yasa yayi murmushi yace Allah yabarmin kai yarimana.
kud'in da yarima yaba zarah nan tabarsu inda ya aje mata saida hajiya sa'adatu tashiga tagani sannan takaima zarah,
zarah ganin cheque din 300,000 saida ta tsorata tace nashiga ukku ina zan kai wad'annan mak'udan kud'in, daga k'arshe yanke shawara tayi tace kawai iyayenta zataba idan takoma gida.
Agurguje ana sauran kwana ukku bikki sultana bilkisu ta aika da mota aka d'auki zarah aka maidata gida, kasancewar tun ana saura kwana hud'u hajiya kubra takoma gidanta.
mummy sa'adatu taso abarmata zarah har sai ranar bikki ammah sultana bilkisu tace a'a abarta takoma wajen iyayenta tunda suma suna buk'atarta a kusa.
ko da aka maida zarah gida 'yan gidansu basu ganetaba mama ce kawai taganeta itama dariyar zarah tagane.
murna sukayi sosai da ganinta mamaki yacikasu ganin yadda takoma kamar ba itaba dan komai nata ya canza dan Aysha ma cewa tayi an canza mata yaya anbata 'yar gayu.
zarah kud'in da yarima yabatane taba abbah tace ayi gyaran gida, da fari k'in kar6a abbah yayi yace taje tayi hidimar bikki sauran kud'in neman aurantama suna nan zai d'auko mata, zarah tace a'a ta bar musu
abbah yace ai hak'intane, zarah saida tasa ma su abbah kuka sannan suka kar6i 300,000 d'in yace sauran kuma natane,
Aysha da ta zauna labarin yarima kawai takeba zarah irin kirkinsa da rashin girman kansa, ita dai zarah saidai tayi murmushi cikin ranta tace ku dai kukaga haka ammah inba ji da kai ba me ya aje...
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔
*PAGE* 2⃣2⃣
Abbah gyara gidansa yayi sosai akayi masa fenti yacanza ma mama kujerun d'akinta, d'inkuna kala ukku-ukku yayi ma su mama.
khairy ko da tazo taga zarah rikicewa tayi cike da murna tace sis anya kuwa kece ba canza mana wata akayiba mai kama da ke?
murmushi zarah tayi tace toh indai ana canza mutum toh nima an canzani,
khairy tace wlh kuwa dan ma bakiga yadda kika koma wata 'yar gayuba, ke ni ya maganar rabon invitation card gashi saura kwana biyu bikki ammah ba Wanda muka gayyata.
ta6e baki zarah tayi tace ba wanda zan gayyata domin ba abinda zanyi ayi bikkin kawai a haka.
khairy rik'e baki tayi tace kai zarah ammah dai bakida mutunci yanzu saboda Allah bazaki gayyaci kowaba? gaskiya bai daceba ace kamarki zaki auri yarima guda ammah ba ayi wani shagaliba,
zarah cikin rashin damuwa tace ba fa zanyiba kema kinsan auren nan zanyisane kawai ba dan ina soba.
zaro ido khairy tayi tace zarah kar dai kice min har yanzu baki daina son malam bello ba? yarima fa yafisa komai.
murmushin takaici zarah tayi tace har yau har gobe ina son malam bello, saidai idan nayi aurene zan daure inga na nisantar da zuciyata daga tunaninsa gudun kar injefa kaina ga halaka.
dariya khairy tayi tace kin dai karanta a islamiyya kuma kinsan babu kyau ehe.
ke wlh yaci ace kin cire son malam bello a ranki kifad'a sabuwar soyayya.
murmushin takaici zarah tayi tace kar fa kimance da tsohuwar zuma ake magani.
dariya khairy tayi tace injiwa? ai itama sabuwar zuman tana magani wani lokacin ma tafi wata tsohuwar, zamu dai zuba ido mugani.
su Hajiya sa'adatu sune ummi tasa sukaje sukayi jeran zarah, part d'aya aka fitar mata dashi daga cikin gidan yarima suhail,
d'akine mai d'aukeda parlour nd 2 bedrooms sai kitchen, kaya aka zuba mata na gani na fad'a a duka bedrooms d'inta sannan aka tsara mata parlourn ta yayi gwanin kyau, kitchen d'inta cika mata shi akayi da kaya, antsara ma zarah part d'inta sosai kamar na wata d'iyar wani attajirin mutum.
Abban sumayya ma canza ma d'iyar tasa kayan d'aki yayi masu kyau da tsada, sumayya taji dad'i sosai sai a lokacin ta safko daga fushin da take da mahaifinta akan auren da yaje yanemo ma yarima.
ana gobe bikki sultana bilkisu ta aiko da mota akazo aka d'auki zarah aka kaita wani hadad'en shagon gyaran jiki wanda sai amaren da suka amsa sunansu suke zuwa.
saloon akayi mata sannan aka zizira mata k'unshinta tayi kyau sosai.
gidan sarautar hidima ake ta gani ta fad'a ko da kowa 6oye murnarsa yake a ciki, ammah sumayya da mahaifiyarta a fili suke nuna basason auren.
gimbiya rahma ita take zuwa tana kwantar ma da sumayya hankali tun da bikkin ya matso kasancewar itama ba'a son ranta yayan nata zai k'ara aureba saboda tana ji da sumayya sosai tun k'uriciyarsu suke abota, taso ace ummi ta hanasa yak'ara auren ammah ummi tace babu ruwanta ita taje ta samesa tayi masa magana, jin haka yasa taja bakinta tayi shuru dan tasan bama zata iya tunkarar yarima da maganar ba.
________________
zarah bayan angama mata gyara around 3:30pm aka maidota gida, mamakine yacikata ganin mutane da suke shiga gidansu, kanta bai ida d'aurewaba saida tashiga cikin gida taga kowa ya shirya, Yaya rauda ce tafara hango zarah tace yauwa ga ma tanan ta dawo.
dasauri khairy da Aysha suka zo wajenta sukace tun d'azun muna ta jiranki please kizo kishirya lokaci yana k'urewa, zarah cike da mamaki tace ban fahimcekuba me zanyi?
jawota sukayi suka nufi d'aki da ita suna cewa koma dai minene kizo dai kishirya.
zarah fizge hannunta tayi tace wai mi za'ayi? ya naga kowa ya shirya?
dariya aysha tayi tace kai yaya zarah wa'azi fa za'ayi?
zarah da kanta ya ida d'aurewa tace wa'azi kuma? wa yashiryasa? muryar yaya rauda sukaji tace mune nan muka shiryasa mun gayyaci mutane, munga idan muka biye ta naki toh babu abinda zakiyi dan haka kiyi sauri ki shirya.
zarah turo baki tayi tace kai dan Allah yaya rauda meyasa zakuyi min haka?
yaya rauda d'aure fuska tayi tace isarmu ce tasa mukayi miki haka dan haka kiyi sauri kije kiyi wanka ko inje inhad'aki da mama.
zarah jin za'a had'ata da mama yasa cikin sauri tawuce taje ta shiga wanka tana fushi.
bayan ta fito kwalliya akayi mata sosai sannan aka d'auko mata material ash nd black colour tasaka sai aka d'aura mata alkyabba black colour mai ratsin ash daga saman kayan, tayi kyau sosai ya yaba da kyaun da tayi.
su yaya rauda ne suka fito da ita, a tsakar gidansu ya cika da jama'a a nan aka zauna akayi wa'azi, manyan malamai mata guda biyu sukayi wa'azin, wa'azin aure mai ratsa jiki inda aka jawo musu ayoyi da hadissai, ba zarah ba hatta sauran mutanen da suke wajen saida suka koka.
bayan angama su yaya rauda suka raba kayayyakin da suka tanada zasuba mutane, zarah dai mamakine yacikata cikin ranta tace nasan zaku aika tunda dai khairy tamatsa sai anyi wa'azi, chan kuma sai tayi murmushi cikin ranta ta ji dad'in hakan.
nan mutane suka watse kowa yana fad'in albarkacin bakinsa.
_*RANA BATA K'ARYA SAIDAI UWAR 'DIYA TAJI KUNYA*_
A yau juma'a masallacin juma'a da yake anguwarsu zarah cike yake da jama'a dan saida aka rasa masaka tsinke saboda yawan mutane anguwar cika tayi sosai dan har memartaba saida yahallara wajen.
Bayan anfito masallacine aka d'aura auren *Yarima Suhail Ahmad Umar* da *amaryarsa Fatima Zarah Musa* akan sadaki naira dubu d'ari,
a chan tsakiyar taron nahango ango da shaheed, ango yasha kyau har ya gaji sanye yake cikin shaddarsa fara wadda tasha aiki da bak'in zare, hularsa da takalmansa duka jajayene nan mutane sukaita zuwa suna gaisawa tare da yi masa Allah yasa alkhairi shidai yarima yana murmushi ne kawai dan saboda memartaba kawai ya amince yazo d'aurin auren.
takeaway aka shiga rabama mutane kowa yaci yasha aka watse cike da farin cikin auren nan masu tsegumi sunayi masu murna nayi.
gidan su zarah cike yake da 'yan uwa da abokan arzik'i abbah yayi k'ok'ari sosai wajen ganin anyi abinci na azo gani wanda kowa zaici yasan yaci hatta naman kaji sunyi kuka sosai a ranar.
A chan tsakiyar gadon mama nahango zarah zaune ta ci kwalliya ta had'e cikin less d'inta pink colour mai ratsin blue head ne blue a saman kanta tayi kyau sosai sai sharar k'wallah take gefenta su yaya rauda ne da Khairy suna lallashinta dan ita gani take duk wasane auren saida tajiyo hayaniyar mutane suna gud'a ana and'aura aure sannan ta tabbatar dagaskene.
mama ce tashigo d'akin taganta cikin wannan halin tace haba zarah miye abun kuka hak'uri zakayi domin shi aure haka yake.
zarah cigaba tayi da sharar k'wallarta ganin haka yasa mama taficce tana fad'a,
zarah da take kuka jin sallamar mutane da tayi yasa tashare fuskarta cike da mamaki take kallon jama'a buya guda da sukazo, nima kaina natsorata saida najawo My Hafnan muka koma gefe nace kin gane mutanen nan da sukazo?
hafnan harararsu tashiga yi tace hmm nagane wasu man wacchan tawagar masu pink d'in atamfa 'yan group d'in *yarima suhail fan's* ne, sai tamurga baki tare dagwada masu anko d'in blue tace wannan kuma na *Hibbatullah* fan's ne, sannan sai masu red d'in anko *Intelligent writer's fan's* ne, sai kuma tanuna wasu tace masu green *Nazir* fan's ne, masu coffee kuma *Aufana true fan's* da *sainah true fan's*, Masu navy blue kuma *Zaynav mtz fan's* sannan *Mummyn khalil fan's*, *Surbajo fan's*, *Sadnaf true fan's* ke da dai sauransu.
rik'e baki nayi nace chab nashiga ukku my hafnan yanzu saboda Allah duk wa yagayyaci wad'annan uwayen mutanen? murya muka jiyo daga bayanmu ance yoh wa fa yagayyacesu k'wak'wace takawosu kawai, juyawar da zanyi sai ganin My blood sis aufana da mummy sainah ummun meenal nayi, dafe kai nayi nace nashiga ukku kukuma wace k'wak'war takawoku? My blood hararata tayi tace yoh mu da tun d'azun muna nan damu akaci aka sha, su Mummyn afrah, meenah abbah, k'anwarki janaf, haleemah H.A.S, sis Aysha ke dama sauran intelligent writer's duk suna nan yanzu haka sunje kar6o mana nama kinsan mummy zill da 'yar mutan zariya basa barin nama,
had'e fuska nayi nace toh wlh wannan abun kunyar ba da sis nerja'art ba dole kowa yazo yakama gabansa babu wanda zai zauna, nan nakorasu nace muje inda muka fito nima nafasa zaman, kallon zarah sukayi sukace toh gimbiyarmu sai mun dawo wani taron,
murmushi kawai zarah tayi bayan sun fita takalli yaya rauda tace wad'annan masoyanmune fa nasan basu ganekuba saisa, yaya rauda dariya tayi tace haba saisa naga rawar kansu yayi yawa saikace Maman sadiq da mrs dawud😜 ke wani abun ma sai ummie adnan da mugirat ammah basukai mummyn khadija ba, aini naji dad'i da aka korasu.
Bayan sallar magrib wanka akasa zarah tayo bayan ta fito hafnan nd Aufana makeover ne suka zauna suna shirya amarya, kwalliya sukayi mata sosai wadda ita kanta zarah da takalli madubi saida tayaba kanta, atamfa tasa riga da skirt sun mata cif sannan aka murza mata d'aurin kallabi inda kyaun nata yak'ara bayyana.
bayan sallar isha'i aka aika da motoci biyu d'aya wadda amarya zata shiga, d'aya kuma na kuyangin da sukaje sutafo da itane saboda cewa akayi babu wanda za'aje da shi kai amarya, amarya kawai za'a tafi da ita.
wajen su mama aka kai zarah sukayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki duk dauriyar mama kasa daurewa tayi saida tayi kwallah, zarah tana kuka aka rik'ota aka fito da ita.
'yan unguwa sunji haushi sosai domin kowa yaci burin yaje yagane ma idonsa, wasu kuma burinsu suje suga sarki, wasu kuma suje suga yarima, wasu kuma burinsu suje sugano kwakwaf, Aysha kuka tayi sosai dan taso tabiyo 'yar auwartata, dole suka hak'ura suna gani aka fito da amarya an nad'eta da lifaya, jakadiya ce rik'e da zarah sai kuyangi biyu da suka take musu baya ahaka aka shigar da ita mota tana kuka.
nan 'yan unguwa wasu sukaita tsogumi ai iyayen zarah saboda son abun duniya suka siyar da d'iyarsu babu wanda yasan inda za'a kaita
haka akaita tafiya ita dai zarah ji take kamar ba a mota takeba saboda wani irin k'amshi mai dad'i da yake ratsata da d'in motar, bata d'ago kantaba har alokacin hawaye take tana tausayin kanta da takaicin iyayenta da suka amince suka aura mata wanda bata so.
ko da aka isa da zarah gidan sarautar tana ji bushe-bushe suna ta tashi batasan lokacin da aka tsayaba saidai gani tayi anbud'e mata k'ofa
nan jakkadiya tace ranki yadad'e kifito anzo, zarah ahankali tasafko k'afarta daga motar har a lokacin fuskarta na a rufe dasauri bayi da kuyangi suka zube k'asa suna k'awar gaisuwa angaishe da gimbiya angaishe da tauraruwar mata takawarki lafiya gimbiya, zarah duk jin abun tayi wani iri saboda bata saba jin hakaba sai a film tunda ita ba zuwa gidan sarauta takeyi ba ammah yau itace ake gaishewa ta bangirma.
muryar jakadiya tajiyo tana cewa ranki yadad'e muje mana, jakkadiya da wata kuyanga suka rik'eta inda sauran kuyangi da bayi suka zagayesu aka sa su tsaka ahaka ake tafiyar har aka isa turakar dada, duk mutanen da ke wajen taga sun duk'a suna kwasar gaisuwa a wajen dada, zarah har zata duk'a dada tace a'a akawota nan tazauna.
jakkadiya takamota takaita har kusa da kujerar da dada take zaune, zarah dasauri tazauna k'asa har a lokacin fuskarta a kulle take kyarma kawai take domin gani take kamar a mafarki.
nan duk sauran kuyangi da bayi suka bar d'akin, d'akin yad'auki shuru daga dada sai zarah, dada ce tayi gyaran murya tace barkanki da zuwa wannan gida namu mai albarka fatanmu kizauna da kowa lafiya, domin kinsan gidan sarauta sai anji ank'i ji, agani ak'i gani, kizauna da kishiyarki lafiya indai kikabi sumayya sau da k'afa toh zaku zauna lafiya domin ita batada matsala ko da kema da alama daga ganinki ba zakiyi matsalaba.
itadai zarah sauraren dada take batace ufanba har a lokacin kanta na sunkuye a k'asa ahaka har dada tagama nasiharta sannan takira jakadiya domin tazo tatafi da zarah 6angarenta, zarah duk'awatayi cikin muryarta da tadashe tace nagode sosai insha Allahu ba zan kawo muku matsalaba zan zauna da kowa lafiya,
dada taji dad'in lafazin zarah a karo na farko da taji ta d'an burgeta domin taga da alamu zatayi hankali.
dada tace zaku iya tafiya, jakadiya tace to ranki yadad'e muje,
zarah mik'ewa tayi suka fito nan duk sauran kuyangi suka take musu baya suka nufi part d'inta,
bedroom d'inta aka wuce da ita aka zaunar da ita bakin gado sannan jakkadiya tace ma kuyangi sutafi nan kuyangi suka zube suka kwashi gaisuwa wajen zarah itadai zarah tana jinsu batace komaiba daganan suka mik'e tare da cewa afito lafiya gimbiya, daganan suka fita daga d'akin.
nan jakkadiya tashiga toilet tahad'a mata ruwan wanka wanda yasha turaruka sannan jakkadiya tafito tad'auko towel tarussuna ta aje sannan tace ranki yadad'e ruwan wankanki sun had'u zaki iya shiga,
zarah tace a'a ba ma sai nayi wankaba,
jakadiya tace kigafarceni ya shugabata umurnin sultana ne nake cikawa kuma wannan tsarin gidan nan ne,
zarah tana jin haka tamik'e tare da janye lullu6inta, gabantane yashiga fad'uwa tana bin d'akin da kallo cike da mamakin tsaruwarsa cikin ranta tafara kokwanto anya wannan nawane?
muryar jakkadiya taji tanacewa ranki yadad'e akwai abinda zan iya taimaka miki da shi?
zarah d'aukar towel d'in tayi tare da cewa bana buk'atar komai daga nan jakkadiya tanufi 6angaren wardrobe d'in zarah,
nan zarah tacire kayanta taje tashiga toilet ko da tashiga tsayawa tayi tana k'arema tsarin toilet d'in kallo cikin ranta tace lallai idan kana duniya zakayi kallo, tsoron Allah ne taji ya k'ara ratsamata zuciya nan tashiga cikin ruwan da yayi mata dad'i dan saida tadad'e tana wanka sannan tafito.
ko da tafito jakkadiyace da wata kuyanga tsugunne a k'asa ganinta yasa suka mike cikin sauri tare da cewa takawarki lafiya gimbiya.
zarah wajen dressing mirror tanufa nan suka bi bayanta suka mik'a mata mai hadad'e mai k'amshi tashafa waccan kuyangar ce tayi mata 'yar simple makeup sannan kayan baccine masu kyau da tsada jakadiya tafito mata dasu,
doguwar rigace silk har k'asa mai hannun vest nan zarah tasaka, su jakkadiya suka dinga yi mata 6arin turaruka a jiki masu sanyin k'amshi, suka tufke mata gashinta da rubon Sannan aka sakamata had'ad'ar alkyabbar da aka tanada.
ko ni kaina da naga zarah saida nace wow masha Allah kamar ba zaran da nasani bace saboda kyaun da tayi
su kansu su jakkadiya saida sukayita santinta suna yaba kyaun da tayi itadai murmushi kawai take nan ma suka k'ara fesheta da turaruka, sannan sukace ranki yadad'e idan ba wani abu da za'ayi zamu iya tafiya.
zarah fuskarta d'auke da mamaki tace ina zamuje?
jakkadiya kanta a sunkuye yake cike da girmamawa tace d'akin yarima zamu rakaki.
zarah saida gabanta yafad'i jin an ambaci yarima dakewa tayi tace da munyi zamanmu a nan.
jakkadiya tace a'a ranki yadad'e ai tsarin sarautar gidan nan ne yau d'akin mijinki zaki kwana.
zarah batace komaiba tawuce gaba suna biye da ita a cikin ranta mamaki kawai take ganin komai na gidan sarauta a tsare yake, ko da suka zo parlournta nan sauran ma'aikata suka zube suka kwashi gaisuwa sannan suka take mata baya, jakadiya tana gaba ta rik'e zarah inda sauran suka bi bayansu,
zarah gabanta fad'uwa kawai yake domin batasan irin wulak'ancin da zata fuskantaba wajen mutumin da yake a matsayin mijinta.
yarima bai dawo gidanba sai wajen k'arfe takwas da rabi na dare fuskarsa babu annuri atattare da ita duk wanda yaduk'a yakwashi gaisuwa saidai yatashi hakanan domin yau ko d'awar hannun da yake musu basuda arzik'in samu.
ko da yashiga part d'insa komai yadda aka gyara masa ya burgesa direct bedroom yawuce nan ma Komai very need, mamakine yakamasa ganin farin bedsheet mai kyau da aka shimfid'a masa saman gado,
cikin ransa yace toh ba za a daina wannan al'adar ba yanzu aure nabiyu ammah shima ba za'a barni inhutaba, tsaki yaja cike da jin haushi yawuce yashiga bathroom,
bayan ya fito saida yatsane jikinsa yashafa mai sannan yad'auko kayan baccinsa yasaka yazauna bakin gadonsa yajawo laptop d'insa yacigaba da wani aiki nasa akan drugs d'in da yake buk'ata ayo masa order d'insu.
knocking d'in k'ofar da akayine duk atunaninsa gimbiya sumayya ce dan haka yace yes.
jakadiya ce tana rik'e da zarah suka shigo da sallamar jakadiya, yarima kallo d'aya yayi musu yad'auke kai jakadiya takowa tayi tazo gaban yarima sannan tasaki zarah ita taduk'a cikin girmamawa tace ranka yadad'e daman sultana ce tace akawo maka amaryarka, yarima cigaba yayi da aikinsa bai tankaba bare yace wani abu, zarah ma k'asa tazauna jikinta sai 6ari yake,
jakadiya ganin yarima baida niyar yin magana yasa tace Allah yaja da ranka akwai abinda ake buk'ata, yarima batare da ya kalletaba yayi mata nuni da k'ofa jakadiya cike da girmamawa tace ranka yadad'e nabarku lafiya, Sannan takalli zarah tace ranki yadad'e atashi lafiya sannan jakadiya tatashi tafita tare da jawo musu k'ofa
daga nan d'akin yad'auki shuru tsoro da fargaba duk suka d'arsu a zuciyan zarah, yarima ko kamar wanda aka ajema kayan wanki ko inda zarah take bai kallaba,
zarah dai har lokacin tana zaune a k'asa fuskarta a rufe cikin ranta tana cewa wannan wane irin mutum ne ko dai bebe ne aka auramin, ahaka tayita sak'e-sak'e a zuciyanta har tsawon awa d'aya tana zaune daga k'arshe bacci yafara d'ibanta,
nan k'asan ta ida kwanciya bata dad'eba bacci yayi awon gaba da ita, yarima sai wajen k'arfe sha biyu sannan yagama abinda yake kallo d'aya yayi ma zarah da take takure waje guda tana bacci, sannan yahaye saman gadonsa yakwanta cike da takaici wai ace kamarsa yakeda mata biyu duk friends d'insa daga mai d'aya sai wad'anda ma basuyi auren ba, gloves yakashe kad'an-kad'an ya yi tsaki ahaka bacci yad'aukesa........

_*Alhmdllh nasamu sauk'i, nagode, nagode da addu'o'inku agareni my fan's hak'ik'a kun nunamin so da k'auna zallah dan ni kaina saida nayi mamakin yawan callings da messages d'in da nasamu daga gareku, bansan irin godiyar da zanyi mukuba, bazan iya lissafokuba saboda yawanku, wad'anda ban samu naduba messages d'insuba kuyi min hak'uri ammah inaso kusani ana mugun tare, Sis Nerja'art tana sonku over Allah yabar k'auna😍*_
_~Wannan page d'in mallakinkune my fan's kuyi yadda kukeso da shi akodayaushe ana tare~_
*PAGE* 2⃣3⃣
Sumayya a ranar kasa bacci tayi kuka kawai takeyi musamman ma idan tatuno da yarima yana chan kwance da wata ba itaba, nan takeji tsanar zarah ta k'aru a ranta duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi motsi kad'an sai ta duba lokaci daga k'arshe zinat takira a waya
zinat da take bacci dakyar tajawo wayarta tana tsaki ganin sumayya ce yasa tad'aga cikin muryar bacci tace ya dai baby?
sumayya cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace dear ke bacci kike hankalinki kwance nikau nan nakasa
zinat cikin ranta tace kujimin mace sai ink'i bacci saikace ni akayi ma kishiya... chan kuma sai tace toh dear kema ke kika sa kanki rashin baccin miye na damuwa tunda dai kinsan dole yakasance da matarsa yau k'ilama ya mance da batunki.
sumayya cikin sheshek'ar kuka tace dolene indamu zinat kiduba fa kiga irin son da nakema yarima ammah yau ace shine tare da wata ba niba wlh natsani ko ma wacece,
zinat tace kikwantar da hankalinki ai wlh ba zamu kyaletaba nima ai dan bana k'asar ammah bari indawo sai munsan yadda mukayi muka fitar da ita daga gidan kinsani ai
sumayya cike da jin dad'i tace saisa nake sonki k'awata yanzu dai yaushe zakizo domin nima kaina ina kewarki
zinat 'yar dariya tayi tace kar kidamu dear very soon zan zo miki domin nima kaina ina kewarki sosai yanzu dai kikwanta kisamu kiyi bacci
sumayya tace hmm dear bana tunanin zan iya bacci a daren nan ni kid'an turomin d'an abinda zai sani nishad'i
zinat tace toh dear muhad'e a online.
sumayya tace ohk, sannan suka kashe wayar a tare,
sumayya ta dad'e batayi bacciba tana kallon abinda zinat taturo mata har daga k'arshe dai bacci yayi awon gaba da ita.
Kiran sallar asubane yatashi yarima daga baccin da yakeyi kallon zarah yayi da take takure k'asa ta6e baki yayi yawuce yashige toilet, jin motsinsane yasa zarah tafarka daga baccin da takeyi dasauri tamik'e tare da gyara alkyabbarta tafito daga d'akin, da karambani tamaida kanta part d'inta lokacin masu tsaron part d'intane kawai a wajen, cike da girmamawa suka gaisheta ta amsa sannan suka bud'e mata tashiga.
zarah alwallah tad'auro tazo tagabatar da sallar asuba bayan ta gama hayewa tayi saman gadonta saboda wani irin bacci da takeji nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.
yarima ko da yafito daga toilet baiwani damuba ganin zarah bata d'akin yaficce yafita masallaci.
bayan ya dawo bai koma bacciba yad'auko laptop d'insa a parlour yazauna yacigaba da aikinsa.
wajen k'arfe 8 guard d'insa yashigo duk'awa yayi yagaishe da yarima, yarima batare da ya kallesaba ya amsa, cike da girmamawa guard d'in yace ranka yadad'e daman jakkadiyace tazo shine nace bari infara dubawa inga in kana parlour,
yarima yace me zanyi mata?
guard yace ranka yadad'e bari inje intambayeta.
yarima kallonsa yayi nad'an lokaci sannan yace kubarta tashigo.
Duk'awa guard yayi yak'ara kwasar gaisuwa sannan yamik'e yafita yabar d'akin.
bayan kamar minti biyu sai ga jakkadiya ta shigo da sallamarta, ciki-ciki ya amsa batare da ya kalletaba.
zubewa jakkadiya tayi tace ranka yadad'e Allah yaja da ran yarima mai jiran gado, Allah yabaka tsawon rai, Allah yad'aukaka mana kai, Allah ya kunyata mak'iyanka dafatan katashi lafiya.
me ke tafe da ke? cewar yarima.
jakkadiya kyarma tafara tace am daman.
yarima batare da ya kalletaba yace ina jinki.
k'ara duk'ar da kanta tayi tace ranka yadad'e kagafarceni daman dada ce ta aikoni tace inzo induba lafiyarku sannan ind'auko bedsheet awanke.
ta6e baki yarima yayi yacigaba da abinda yakeyi saida yayi kusan minti goma sannan yace zaki iya shiga kid'auka.
shiga jakkadiya tayi tad'auko tafito nan tak'ara duk'awa tace atashi lafiya yarima sannan taficce daga d'akin.
wajen k'arfe goma zarah tafarka daga baccin da take daidai lokacin d'aya daga cikin kuyanginta tashigo dasauri taduk'a tagaishe da zarah cike da girmamawa, zarah amsawa tayi cikin sakin fuska, sannan kuyangar tatashi tashiga toilet d'in zarah tawankesa fes sannan tahad'a mata ruwan wanka, sannan tad'auko mata towel.
bayan ta fito duk'awa tayi gaban zarah tace ranki yadad'e ruwan wankanki ya had'u.
zarah murmushi tayi tare da kar6ar towel d'in tace nagode zaki iya tafiya.
kuyangar k'ara duk'ar da kanta tayi tace ranki yadad'e nice wadda zan dinga gyara miki d'aki mu biyune d'ayan tana parlour tana jiran fitowarki,
murmushi zarah tayi tace kubarsa kawai ni zan dinga gyarawa.
A tsorace kuyangar tace a'a ranki yadad'e kigafarceni aikinmune idan har akaga mun bari kinyi da kanki za'a iya korarmu.
zarah girgiza kai tayi tace baza'a koreku ba, mik'ewa tayi tare da wucewa tanufi toilet.
lokacin da zarah tafito angama gyara mata ko'ina k'amshi kawai yake tashi, ita kanta zarah yanayin gyaran da akayi ya burgeta,
gaban dressing mirror tazauna ta tsantsara kwalliyarta sannan taje tabud'e wardrobe saida ta tsorata ganin lodin kayan da suke ciki, Holland atamfa tasaka Red nd white colour, d'ankunnenta ma red colour tasaka, murza d'aurin kallabi tayi nan kyaunta yak'ara bayyana, k'ara kallon kanta tayi a mirror sannan tafeshe jikinta da turaruka masu sanyin k'amshi, plat shoes tasaka tatako ahankali tafito parlour, ganinta yasa duk kuyangi da bayin dasuke parlourn suka zube k'asa suna ranki yadad'e gimbiya, Allah yaja da ranki takawarki lafiya dafatan kin tashi lafiya?
zarah tana murmushi tataka cikin takunta taje saman cushin tazauna, saida sukaga ta zauna sannan suka d'ago kansu,
zarah har a lokacin fuskarta tana d'auke da murmushi tace wacece shugabarku?
d'aya daga cikinsu ce tace ranki yadad'e ganinan nice shugaba, sannan kowa anraba masa aikin da zaiyi.
jinjina kai zarah tayi tace dat's gud, dafatan dai zaku bani had'in kai muzauna lafiya, indai kukayi haka toh zakuji dad'in zama da ni sosai.
gaba d'ayansu sukace Allah yaja da ran gimbiya insha Allahu zaki samemu masu amana.
murmushin jin dad'i zarah tayi tace nagode zaku iya tafiya, nan suka k'ara duk'awa sukace atashi lafiya,
gyad'a musu kai zarah tayi nan suka mik'e, biyu daga cikinsu ne sukatsaya sukace ranki yadad'e mune masu kula da abincinki ga breakfast d'inki chan a dining idan kin bamu izini sai muje muhad'a miki.
zarah mik'ewa tayi tanufi dining nan suka take mata baya, dasauri suka jawo mata kujera nan tazauna, ganin zasuyi serving d'inta yasa tadakatar da su dakanta tazuba tad'anci kad'an sannan tamik'e,
nan suka gyara wajen, zarah saman kushin takoma tazauna tare da d'aukar wayanta takira mama suka gaisa,
tana cikin waya yarima suhail yashigo cikin takunsa nak'asaita sanye da alk'yabba yasha kyau, zarah kashe wayar tayi dasauri tamik'e tsaye tare da d'an russunawa tace barka da safiya.
yarima kallo d'aya yayi mata yad'auke kai yace kije kishirya kizo muje mugaishe da su memartaba.
zarah ahankali tace toh sannan tawuce tashige bedroom.
gyalenta tad'auko white tayafa tafito lokacin yarima yana zaune saman cushin, kallonta yayi yace babu alkyabbane cikin kayanki?
zarah tace akwai.
shuru yarima yayi baik'ara cewa komai ba, ganin haka yasa zarah takoma bedroom, red d'in alkyabba tad'auko tasaka sannan tafito tasamu yarima a zaune,
kallonta yarima yayi har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, mik'ewa yayi yace muje.
zarah bayansa tabi suka fito a jere nan guards d'insa da kuyanginta suka take musu baya yanayin yadda suke tafiyar kawai zaka kallah sai sun burgeka ko da ad'ankwai 'yar tazara a tsakaninsu anutse suke tafiya har suka isa fada itadai zarah duk fargaba da tsoro duk sun cikata kanta sadde yake k'asa har suka shiga fada da take cike mak'il da jama'a nan mutane suka fara gaishesu, yarima ne kawai yake amsawa ahaka suka isa gaban memartaba,
lallausan carpet ne aka shimfid'a musu nan dogarawa sukayi musu zobe har saida suka zauna bisa sannan suka janye manyan rigunansu gaba d'ayansu suka duk'a suka gaishe da su yarima, yarima gyad'amusu kai yayi nan suka mik'e sannan yamaida kallonsa ga memartaba da yake kallonsu yana murmushi.
Zarah ce tafara gaishesa sannan yarima suhail, gyad'a musu kai sarki yayi alamun amsawa, nan fadawa suka d'auka sarki ya amsa gaisuwarku yarima da gimbiya ku ma angaisheku, Allah yaja da ranku,
memartaba kallon zarah yayi yace Alhmdllh ina tayaki murnar shigowa wannan masarauta tamu muna fatan Allah yasa alkhairi a cikin aurennan naku.
nan fada tad'auka da Ameen.
wata 'yar jakka sarki yasa aka mik'o masa yaba zarah yace ga kyautata gareki.
zarah hannu biyu tasa takar6a tare da duk'ar da kai tace nagode ranka yadad'e Allah yak'ara girma da d'aukaka, nan kuyanga takar6a
nan fadawa suka d'auka sarki ya amsa godiarki gimbiya angaisheku.
memartaba kallon yarima yayi yace Allah yatayaka safke wannan nauyin da yahau kanka fatana Allah yasa ka kwatanta adalci atsakaninsu.
yarima kansa na sadde k'asa yace Ameen ranka yadad'e.
memartaba murmushi yayi yace zaku iya tafiya.
godia sukayi, dasauri dogarawa sukazo suka baje rigunansu suna ranka yadad'e atashi lafiya, takawarka lafiya jarumin jarumai saida suka tabbatar da sun mik'e sannan su kuma suka duk'e k'asa nan zarah da yarima suka fito sukabar fadar, kan zarah ya d'aure sosai ahaka suka shiga cikin gida turakar dada.
duk inda suka gifta duk'awa ake ana gaishesu, yarima d'aga musu hannu kawai yake itakuma zarah saidai tabisu da ido,
masu tsaron k'ofar dada ganinsu yasa sukayi saurin bud'e k'ofa tare da duk'awa sukace ranku yadad'e Allah yaja da ran yarima me jiran gado.
yarima bai tankasuba yana gaba zarah na biye da shi ahaka suka shiga nan kuyangin dada suka zube suka Kwashi gaisuwa sannan cikin sauri suka tashi sukabar d'akin.
yarima takawa yayi yaje saman cushin yazauna, zarah ko k'asa tazauna cike da ladabi tagaishe da dada.
dada nan ta amsa mata, fuskar yarima d'auke da murmushi yace 'yar tsohuwa ina kwana?
dada tace au yau kuma da tsokana kazo? toh bazan amsaba, yarima yace ayya yi hak'uri, murmushi dada tayi tace dafatan kun tashi lafiya?
yarima yace lafiya lou, dada kallon zarah tayi da har lokacin bata d'ago kai ba tace amarya ya bak'unta? zarah murmushi tayi tace Alhmdllh.
dada kallonta tamaida ga yarima tace akwai matsala fa
yarima yace tame fa?
dada gyara zamanta tayi tace babu wata sheda da kuka nuna mana, mutane suna nan sun kasa kunne suna saurare ammah shuru wai meyake faruwa ne naga bedsheet d'in babu komai a jikinsa, ta k'arashe maganarta tare da kallon zarah.
murmushi yarima yayi yace ranki yadad'e saboda Allah komai ace sai mutane sun shaida, wannan ai tonon asirine.
dada tace a'a yarima wannan kasan shine zai d'aga darajar mace a idon kowa dake masarautarnan sannan kuma gada mukayi tun kaka da kakanni, rashin ganin jini zai iya sa ad'auka mace tazubar da mutuncinta a waje.
zarah da take saurarensu saida gabanta yafad'i dan ta fahimci akan abinda dada take magana.
yarima cike da rashin damuwa yace haba dada inbanda abinki yanzu ai anbar wannan.
dada tace injiwa? abinda muka gada tun kaka da kakanni? kai ni banyarda da kaiba anya kakwanta da yarinyarnan? inkuma ka kwanta da ita toh ya akayi babu wani alama da yanuna budurwace?
murmushi yarima yayi tare da kallon zarah da duk tabi tatsure cikin ranta mamakin maganganun dada take tace gidan sarauta akwai tonon asiri,
ahankali yarima yace dada period takene saisa hakan takasance, zarah dasauri tad'ago kai takalli yarima da yake dannar wayarsa saikace bashine yayi maganar ba, yarima ya fad'i hakane gudun kar su ummi suji labari dan yasan sai dada ta fad'a musu kuma sai sun fahimci wani abu.
dada ce tace ayyah Allah sarki 'yar nan ai bamu saniba, kinsan haka abun yake, kinsan daren farko munaso muga alamar da zata nuna mana mace cikakkar budurwace dan hakan ne yake d'aga daraja da k'imarta.
zarah cike da kunya tak'ara sadda kanta k'asa, dada tace kikwantar da hankalinki zanyi ma kowa bayani yadda zasu fahimta.
yarima ne yace haba dada wannan ai tonon asirine.
.
dada tace gidanku, kaima ai kasan dokokinmu na wannan masarautar, yanzu dai yaushe ne zakiyi tsarki?
zarah kallon yarima tayi da shima yazuba mata ido, muryar dada taji tace ina saurarenki.
zarah batasan lokacin da tayi su6ul da baka tace jibi ba.
murmushi dada tayi tace Allah yakaimu, nan dada tamik'o mata alkyabba maikyau da turare tace ga tukuici na,
kar6a zarah tayi tare da godia ammah har lokacin jikinta rawa yakeyi.
nan yarima yayi ma dada sallama suka mik'e suka fito, daganan suka nufi part d'in sultana sadiya,
lokacin da suka shiga tana tsakiyan kuyanginta, da sallama suka shiga nan kuyanginta suka gaishesu sannan sukabar d'akin, ganinsu yasa gimbiya sadiya tad'aure fuska tare da wurgamasu harara, yarima baidamu da yanayin kallon da take musuba yaje saman kujera yazauna, inda zarah kuma tazauna k'asa tare da gaisheta, .
sultana sadiya shuru tayi bata amsaba, yarima suhail ne yace ranki yadad'e ana gaisheki fa, yamutsa fuska sultana tayi tace oh banjiba amarya kin tashi lafiya?
zarah k'ara duk'ar da kanta tayi tace lafiya lou, yarima suhail yace ranki yadad'e barka da safiya dafatan kin tashi lafiya.
lafiya, cewar sultana.
murmushi yarima yayi tare da kallon zarah yace wannan itace ummah sadiya mahaifiyar matata sumayya,
gyad'a kai kawai zarah tayi, ummah tace hmm mu ai muna nan muna jira muji anyi gud'a ammah har yanzu shuru babu abinda mukaji hakan yana nufin ba budurwa bace kenan kayayo mana cikin masarauta.
murmushi yarima yayi yace ranki yadad'e ai gud'a bashine ba kar kimance sumayya ma ba'ayi gud'aba lokacin da na aureta,
cike da 6acin rai sultana sadiya tace kar fa kayi min rashin kunya,
yarima cikin kwantar da murya yace haba ummah ni na isa inyi miki rashin kunya? kawai dai tuna miki nayi saboda laifi tudune katake naka kahango na wani.
zarah abun ya d'aure mata kai ganin yadda yarima yakeyi ma surukarsa,
sultana sadiya har ta bud'e baki zatayi magana sai ga sultan Abbas ya fito daga d'aki fuskarsa d'auke da fara'a yace a'a wai amarene?
murmushi kawai suhail yayi tare da d'an zamowa daga kujerar da yake yace abbah ina kwana?
sultan Abbas zama yayi yace lafiya lou yarima dafatan kuna lafiya?
murmushi suhail yayi yace lafiya lou Abbah, zarah k'ara sadda kanta tayi cike da ladabi tagaishesa.
cikin sakin fuska sultan abbas ya amsa mata tare da cewa amaryarmu ya kike ya bak'unta?
zarah tace Alhmdllh Abbah.
sultan Abbas yace masha Allah, dafatan zakiyi hak'urin zama da mu kinsan yanayin gidan sarauta sai andinga hak'urin zama da juna fatanmu kizauna da kowa lafiya, ko da yanayin ya nuna bazakiyi fitinaba.
Zarah cike da ladabi tace insha Allahu Abbah, mik'ewa sultan Abbas yayi yashiga bedroom bai dad'eba sai gashi yafito da wata leda nan yamik'a ma zarah yace ga kyautata,
zarah hannu biyu tasa takar6a tare da yin godia.
yarima suhail ne yamik'e yace abbah bari muwuce, sultan abbas yace to yarima mungode sosai a dai cigaba da hak'uri da juna.
yarima yace insha Allahu abbah mungode, nan zarah tak'ara yin godia sannan tataso suka fito.
ko da suka shiga turakar ummi duk inda suka gifta nan ma zubewa ake ana gaishesu, a parlour suka sameta kishingid'e ita kad'ai, ganinsu yasa tatashi zaune fuskarta d'auke da fara'a hannu tamik'a ma zarah tace zo nan kusa da ni d'iyata.
zarah cike da jin kunya tataka taje kusa da ummi tazauna, inda yarima yazauna saman cushin.
zarah cike da girmamawa tace ummi ina kwana? ummi tace lafiya lou daughter ya bak'unta?
zarah murmushi tayi tace Alhmdllh.
yarima ma cikin girmama yagaishe da ummi, itama ta amsa masa fuska a sake tace ya sumayya?
murmushi suhail yayi yace tana lafiya ummi, daddy fa yafita?
ummi mik'ewa tayi tace yana ciki bari inkirasa kugaisa nan tawuce tashiga bedroom d'insa bata dad'eba saigata sun fito tare da daddy,
bayan dady ya zauna nan suka gaishesa, daddy ya amsa musu daganan yad'anyi musu nasiha sannan yad'auko cheque yamik'a mata yace ga kyautata gareki.
zarah hannu biyu tasa takar6a tare da yin godia, daddy yace bakomai adaiyi hak'uri da zaman aure, sannan yatashi yafita.
ummi kallon yarima tayi tace inason magana da kai, saida tamik'e sannan tamaida kallonta ga zarah tace daughter yi hak'uri bari inzo,
zarah murmushi tayi tace toh ummi bakomai.
yarima tashi yayi yabi bayan ummi, bayan sun shiga bedroom ummi kallonsa tayi tace suhail menene haka kayi ban fahimcekaba daman nasan bakason auren nan yanzu saboda Allah kakyauta gashinan anata surutu akan baiwar Allahn nan?
yarima shuru yayi saida sultana bilkisu takai aya sannan yace ummi please kifad'amin menayi?
harararsa ummi tayi tace au kana nufin bakasan abinda kayiba kenan, yanzu saboda Allah an aura maka yarinya ammah babu abinda yashiga tsakaninku.
yarima sosa k'eyarsa yayi cikin jin kunya yace ummi am ba daman,
ummi tace daman me?
murmushi suhail yayi yace daman tana period ne.
dogon numfashi ummi taja tace toh ai shikenan na d'auka wulak'ancin nakane yamotsa nidai fatana karik'e min ita tsakani ga Allah kar kabani kunya.
murmushi suhail yayi yace ummi kenan saikace baki yarda da niba, kina tsoron inzalunceta ko?
murmushi itama ummi tayi tace ai nayarda da d'ana 100% Allah yayi maka albarka, murmushi yayi yace ameen ummina,
atare suka fito inda suka tarar da zarah inda suka barta, ummi murmushi tayi tace daughter munbarki kekad'ai ko?
itama zarah murmushin tayi tace bakomai ummi, wata leda ummi tamik'a mata tace ga wannan, sannan ummi tace rahama batanan da kun gaisa ammah insha Allahu idan tadawo zan turota kugaisa.
zarah tace toh ummi tare da yi mata godia, nan sukayi mata bankwana suka fito suka koma 6angarensu.
ahanyarsu ta komawa yarima suhail yakira sumayya
lokacin sumayya tana breakfast fuskarta babu walwala jin haushinta taje part d'in yarima ammah bata samesaba, dasauri wata baiwarta tamik'o mata wayar tace ranki yadad'e ana kiranki, kar6a gimbiya tayi a wulak'ance ganin mai kiranta yasa taja tsaki kamar bazata d'aukaba saida takusan tsinkewa sannan tad'auka babu ko sallama tace haba yarima yanzu saboda Allah ka.... yarima baijira tak'arashe maganarba yakatseya yace kisameni a part d'ina yanzu, bai jira jin abinda zataceba yakashe wayarsa.

*PAGE* 2⃣4⃣
Yarima ganin zarah tana shirin wucewa part d'inta yasa yace suje part d'insa yanason ganinta, zarah bata musaba tabi bayansa dan bata iya musama yarima saboda girmansa da take gani.
ko da suka shiga saman cushin yarima yazauna, zarah har zata zauna k'asa yace tazauna saman cushin tunda suka zauna d'akin yad'au shuru.
yarima kiran sumayya yayi tana d'auka cike da jin haushi yace kinsan dai bana jira kuma baki isa inzauna ina jirankiba.
tsaki sumayya taja tace ai ganinan a hanya.
bayan minti biyu saiga sumayya tashigo fuskarta babu alamun fara'a ganin zarah yasa taja bakin k'ofa tatsaya, dasauri zarah tamik'e tad'an russuna tace Aunty barka,
wata uwar harara gimbiya sumayya tawurga mata tare da jan tsoki, tace Auntyn munafunci? kece kika auran min miji ko? lallai natayaki murna tak'arashe maganar tare da yin k'wafa
jikin zarah duk sai yayi sanyi.
yarima da yake dannar waya yana saurarensu batare da yakallesuba yace ma gimbiya sumayya ai saikizo kizauna kin wani yi ma mutane tsaye,
sumayya tana hararar zarah tatako cike da isa tazauna saman kujerar da yarima yake zaune, zarah ma jiki ba k'wari tazauna inda take tare da saddar da kanta k'asa.
yarima shuru yayi yana dannar wayarsa baice komaiba saida akayi kusan minti ukku,
sumayya ta k'ule kallonsa tayi tace haba yarima ya zakayi shuru kabarni a zaune.
banza yarima yayi da ita saida yagama abinda yake sannan yad'ago kai yakallesu d'aya bayan d'aya tare da gyaran murya kamar bayason yin magana yace toh Alhmdllh ba akan komai natarakuba sai dan infad'a muku dokokina domin duk wadda takeson zama da ni dole tabisu, kallon sumayya yayi da taci face yace ke sumayya kece babba dan haka kija girmanki banason fitina ko tashin hankali, sumayya cike da masifa tabud'e baki zatayi magana, yarima hannu yad'aga mata yace kar kikuskura, kin san wanene ni idan ina magana ba'a tsinkemin.
sannan yamaida kallonsa ga zarah da take wasa da yatsun hannunta yace ke kuma kece k'arama dan haka dole kibata girmanta sannan kizauna da ita lafiya kar kikuskura inji kinyi mata rashin kunya, zarah shuru tayi batace komai ba.
yarima yacigaba da cewa kar wanda yasaki yakawomin tashin hankali a gidana, sannan maganar kwana bayan sati guda zaku koma kowace kwana bibbiyu, jinjina kai yayi yace na fad'amuku kar inji kar ingani banason tashin hankali wlh duk wadda tanemi takawo min raini zan d'au k'wak'waran mataki a kanta, yana kaiwa nan yayi shuru na d'an lokaci sai chan yace idan akwai mai magana zata iya yi.
ba sumayya hatta ita kanta zarah taji haushin maganganunsa, sumayya ce tace yanzu dai wad'annan maganganun naka ban ganeba kafito fili kace da ni kake wannan shine adoki mutum sannan ahanasa kuka, ka gama yimin kishiya sannan ka...... hararar da yarima yawurga matane yasa tayi shuru, d'an guntun murmushi yayi yace ban miki alk'awalin bazan k'ara aureba kai koda ace a nan gaba naga wadda tayimin nakeso toh sai na aureta saidai duk wadda taji bata iya zama toh k'ofa a bud'e take dan haka kutashi kuban waje.
zarah ce tafara tashi dasauri tafita sannan sumayya.
zarah tana cikin tafiya taji muryar sumayya tace ke!
zarah batare da ta juyoba tatsaya nan sumayya tatako cike da isa tazo inda zarah take, kallonta sumayya tayi daga sama har k'asa sannan tace gimbiya zarah ko? l
dariya sumayya tayi tace gaskiya natayaki murna gaki d'iyar talakkawa ammah zaki had'a miji da gimbiya kamata, chan kuma sai gimbiya sumayya tad'aure fuska tace wlh baki isa inyi kishi da keba dan haka yazama dole kirabu da mijina, inkuma ba hakaba bakeba hatta talakkawan iyayenki sai sunsan kwad'ayi yakaisu ya baro, dan suma sai sun gane kurensu dan haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya.
tana gama fad'in haka tazagaye zarah tawuce tabarta nan tsaye.
zarah dai binta take da kallo cike da mamaki kasa cewa komai tayi tawuce tanufi part d'inta zuciyanta cike da k'unci
zarah ko da takoma part d'inta sama-sama tatsaya suka gaisa da kuyanginta sannan tashige bedroom d'inta, saman gado takwanta tana tunanin maganganun da sumayya ta yada mata, sai tatuno da yarima suhail, tsaki taja tace wlh darajar alk'awalin da nad'aukar ma malam bello da kuma darajar aure wlh da bazan yadda a wulak'antaniba.
hawayene suka fara zarra daga idanunta chan tafashe da kuka cike da tausayin kanta.
wajen azuhur kuyangarta tashigo tahad'a mata ruwan wanka.
bayan zarah ta fito wanka tad'and'ara kwalliyarta gown d'in atamfa tasaka, bayan tayi Sallah tafito parlour, ganinta yasa kuyanginta suka zube suna kwasar gaisuwa, zarah bata ce komai ba saida taje saman cushin tazauna sannan tace banason irin wannan gaisuwar da kukeyimin kudaina duk'amin.
zabba'u shugaban kuyangince cike da girmamawa tace ranki yadad'e kigafarceni matsayinkine da k'imarki da cancantarki sukaja haka, murmushi zarah tayi tace nagode ammah kudaina, yanzu dai inason asani nishad'i wazai ban labari mai dad'i?
nan zabba'u takalli d'aya daga cikinsu tace daso aikinkine, wadda aka kira da daso nan tafara ba zarah labari suna dariya, cike da nishad'i suke hirarrakinsu.
chan wajen k'arfe ukku zarah tace yanzu lokacin cin abincinane, nan suka duk'a sukace toh ranki yadad'e atashi lafiya sannan suka mik'e suka fita.
masu kula da abincinta har sun tsaya nan zarah tace sutafi kawai.
zarah dakanta taje tayi serving d'in kanta taci abinci, bayan ta gama nan takira tace suzo sukwashe abincin suje suci.
bayan sallar la'asar zarah kallo takunna tana yi duk kad'aicin 'yan gidansu ya dameta, saida aka kira magrib sannan taje tayi sallah dakanta tashiga kitchen tadafa 'yar indomie, duk yadda kuyanginta sukaso tabari suyimata ammah tak"i tace musu zaman ne ya isheta saisa takeso tad'an motsa jikinta, kan dole suka hak'ura suka barta.
bayan sallar isha'i zarah 'yan gidansu takira sukasha hira tare da tambayarsu yaushe zasuzo, Aysha tace saidai kin ganmu kawai abbah ne yahanani dan naso inzo yau yace a'a sai kinkwana biyu.
zarah cikin rashin jin dad'i tace toh Allah yasa ya amince kuzo kuyi min kwanah ni wlh kad'aici yana damuna.
dariya Aysha tayi tace haba yaya zarah wane kad'aici bayan gidan akwai mutane kuma ga kallo, ni wlh ji nake daman nice.
tsaki zarah taja tare da kashe wayanta tace Aysha kenan, shirin bacci tayi ta sallami kuyanginta tayi kwanciyarta.
*wanshe kare* bayan zarah ta yi sallar asuba bacci takoma sai wajen k'arfe goma tafarka, nan aka had'a mata ruwan wanka tayi tashirya cikin material coffee colour kayan sun kar6eta sosai, nan tafito suka gaisa da kuyanginta tayi breakfast, bayan ta gama breakfast kallo takunna tanayi kasancewarta mai son kallo, kuyanginta suna zaune k'asa, sallamar da taji anyine yasa tad'ago kai, Rahma ce tashigo cikin shigarta ta alfarma sanye da alkyabba, ganinta yasa kuyangi suka duk'e k'asa suna kwasar gaisuwa, zarah tunda taganta tasan jinin yarima ce saboda taga kamansu dasauri tamik'e tare da d'an rissinawa cike da girmamawa tace sannu da zuwa, kuyangi bayan ta amsa musu tashi sukayi suka fita daga d'akin, nan Rahma tatako taje tazauna saman d'aya daga cikin kujerun d'akin saida tazauna sannan zarah ma tazauna tare da gaisheta.
Rahma da take k'arema d'akin kallo amsawa tayi ciki-ciki, zarah fuskarta d'auke da fara'a tamik'e tace bari inkawo miki ruwa,
sumayya yamutsa fuska tayi tace no kibarsa kawai am ohk, daman nazone mugaisa ina fatan kinji labarina wajen mijin naki, nice k'anwarsa.
murmushi zarah tayi tace eh ummi ta fad'amin jiya tace bakyanan ne saisa bamu had'uba, Rahma mik'ewa tayi tsaye tace zan wuce Allah yabada zaman lafiya, zarah ma mik'ewa tayi tare da rissinawa tace mungode Allah yakiyaye, Gimbiya Rahma batace komai ba tawuce tafita.
zarah komawa tayi tazauna tare da dafe kanta cikin ranta tace wannan indai halin yarima ne takwaso daga gani zatayi wulak'anci _(Ni kuma nace haba zarah gani d'aya kawai ammah har kin fassarata)_
bayan sallar azuhur wanka tashiga tayi.
zarah bayan ta fito daga wanka kwalliya tazauna tayi sosai sannan tashirya cikin boyel less d'inta blue nd orange colour d'inkin riga da skirt ne kayan sun kar6eta sosai sannan tad'aura alkyabba orange colour daga saman kayan tayi kyau sosai saida tafeshe jikinta da performs sannan tafito parlour lokacin kuyanginta na zaune k'asa suna jiran fitowarta ganinta yasa gaba d'ayansu suka rissina sukace barka da fitowa sarauniya tsarki ya tabbata ga ubangiji da yahalicci wannan kyakkyawar kuma mata ga sarki mai jiran gado angaisheki gimbiya.
gimbiya zarah takowa tayi tana murmushi kamar ba zatayi maganaba ammah ganin basuda niyar d'agowa yasa tace nafad'a muku banason hakan da kukemin ammah kunk'i dainawa ko?
kuyanga d'aya batare da ta d'ago kaiba tace ranki yadad'e kigafarcemu ke shugabace agaremu kuma mai mutunci dan haka girmamawa yazama dole muyi maki,
murmushi zarah tayi a karo nabiyu sannan tace wasu sutaso surakani 6angaren gimbiya sadiya.
kuyangi hud'u suka mik'e nan zarah tashiga gaba suna biye da ita a baya, tako take irin na masu ji da kansu,
duk inda tazo wucewa sai anduk'a angaisheta itakuma tana tsayawa tana amsa musu fuska a sake sannan tacigaba da tafiyarta ahaka har tazo 6angaren gimbiya sumayya.
bayin gimbiya sumayya biyu da suke tsaye k'ofar d'akinta ganin gimbiya zarah yasa suka duk'a suka gaisheta nan ta amsa musu fuska a sake dasauri suka tashi suka bud'e mata d'aki tashiga.
gimbiya sumayya da take zaune saman kujera inda bayinta da kuyangi suke zagaye da ita tana ta dannar wayarta.
gimbiya zarah ce tashigo da sallamarta fuskarta d'auke da fara'a kuyanginta suna biye da ita, ganinta yasa gimbiya sumayya tahad'e fuska,
nan ma'aikatan sumayya suka zube suna kwasar gaisuwa, tsawa sumayya tabuga musu dasauri duk suka mik'e tsaye, gimbiya zarah bata damuba tad'an rissina tace barka da rana.
wata irin harara gimbiya sumayya tawurga mata cikin tsawa tace meyakawoki d'akina?
zarah murmushi tayi tace nazo ingaishekine
gimbiya sumayya tace ashema kinzo kigaisheni to kirik'e gaisuwarki bana so ke ga kicifaffa watakau kinzo kimin iyayi
toh bari kiji kibar ganin kin auri yarima yadda kika shigomin gida dole kifita kibarsa sannan daga yanzu kar kik'ara shugo min d'aki duk ranar da kika k'ara gigin shigowa sai nanuna miki matsayinki a gidannan ke bakomai bace face talaka makwad'aita.
damamaki zarah takebin gimbiya sumayya da kallon yadda tadage tana ta zuba mata ruwan rashin mutunci.
sumayyw k'walama bayinta da suke tsaye bakin k'ofan d'akinta kira tayi dasauri suka gurfana gabanta kamar zasuyi mata sujjada dan tsoro sukace gamu mun amsa kiranki ya shugabarmu,
sultana sumayya a wulak'ance tace meyasa kuka bari wannan d'iyar talakawan tashigo min d'aki?
shuru sukayi suka fara 'yan kame kame
gimbiya sumayya kishingid'awa tayi a saman kujerar tare da cewa kufitarmin da ita na baku kinti biyu idanko ba hakaba a bakin aikinku.
zarah murmushin takaici tayi tare da cewa bama sai kinsa an fitar da ni ba, ni zan fita da kaina saidai inaso kisan wani abu d'aya, talauci da dukiya duk na Allah ne dan haka na barki lafiya.
tana gama fad'in hakan tajuya tafito cike da 6acin rai duk Wanda yake wajen baiji dad'in abinda gimbiya tayima zarah ba saidai kowa yabar abun a ransa domin gudun 6acin ran gimbiya
suna fita daga d'akin kuyanginta suka zube k'asa sukace Allah yahuci zuciyar gimbiyanmu,
murmurshi zarah tayi sannan tawuce gaba suka tashi sukabi bayanta ahaka har suka shiga part d'inta bata kula kowaba tawuce tashige bedroom tare da maida k'ofar tarufe tacire alkyabtarta cike da takaici tafad'a saman gado tace wannan wace kalar rayuwace duk inda nayi babu sauk'i, takaicinta maganganun da Gimbiya sumayya tafad'a a kanta, hawayene suka cika mata ido tace Allah gani gareka.
wanshe kare zarah tara kuyanginta tayi taraba musu kud'i tace kowa yaje yasiya abinda yake buk'ata, sunji dad'i sosai nan suka duk'a sukayi mata godia sannan suka fita kowa yana murna
haule ce da zabba'u zaune bayan part d'in zarah suna cin abinci, haule takalli zabba'u tace gaskiya natayaku murna dan kunyi dacen uwargijiya ba kamar tamuba.
murmushi zabba'u tayi tace mukam ai saidai muce Alhmdllh dan wlh tana da kirki sosai batada girman kai.
haule tace hmm muko kinga tamu girman kai da wulak'anci gareta ke ni har tsoro nakeji inga na6ata mata rai dan sai kagane kurenka, duk abinda zakayi mata toh bazaka ta6a burgetaba, daman nima amaidoni wajen gimbiya zarah ko bakomai zan samu sauk'in wani abun, zabba'u har ta bud'e baki zatayi magana ganin rabi tanufo inda suke yasa tafasa.
bayan sallar magrib dada wani farin bedsheet d'in taba jakkadiya tace aje a shimfid'a part d'in yarima, jakkadiya kar6a tayi tare da rissinawa sannan tafito.
ko da taje part d'in yarima baya nan guards har sun hanata shiga saida tace dada ce ta aikota tagyara masa d'aki sannan suka barta.
ko da tashiga saida tak'ara gyara d'akin fess sannan tafito tanufi part d'in zarah, lokacin tana kishingid'e tana chart,
jakkadiya duk'awa tayi tagaishe da zarah cike da girmamawa, cikin sakin fuska zarah ta amsa mata, nan jakkadiya tak'ara saddar da kanta k'asa tace ranki yadad'e daman dada ce tace inzo intayaki kishirya sai inrakaki d'akin yarima.
zarah saida gabanta yafad'i jin an ambaci mutumin da kusan kwana biyu rabon da tasakasa a idanunta.
kuma ta fahimci abinda ake nufi, cikin ranta tace nashiga ukku.
muryar jakkadiya taji tace kigafarceni ranki yadad'e, idan kin ban izini sai inje inhad'a miki ruwan wanka.
zarah gyad'a mata kai kawai tayi nan jakkadiya tamik'e taje tahad'a ma zarah ruwan wanka.
zarah dakyar taje tayi wankan gabanta fad'uwa kawai yake duk tsoro da fargaba sun cikata,
bayan ta fito lotion mai k'amshi aka bata tashafa, sai humra da kulacca, powder kawai tashafa ma fuskarta sai lipstick, had'ad'ar night gown ce fara har k'asa aka bata tasaka, zarah ganin rigar shara-shara yasa tazaro ido tare da cewa a'a jakkadiya ba zan sa wannan ba canzamin wata.
murmushi jakkadiya tayi tace ranki yadad'e kar kidamu ai alk'yabba zaki d'aura a sama.
Zarah dai badan tasoba tahak'ura tabar rigar,
saida aka k'ara fesheta da performs sannan aka d'aura mata alk'yabba daga saman kayan nan tayi gwanin kyau.
duk'ar da kai jakkadiya tayi tace ranki yadad'e kinyi kyau, d'an guntun murmushi zarah tayi.
jakkadiya tace ranki yadad'e idan kin bamu izini zamu iya tafiya,
zarah gaba tawuce suna biye da ita a baya fuskarta kawai zaka kallah kagane tana cikin tashin hankali marar misaltuwa.
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_
?👑👑

_*Ina kuke team d'in zarah da kuma team d'in yarima suhail kuzo yau ranar takuce, lallai kunyi k'ok'ari sosai, saidai kash ni bana tare da ku, duk wanda yake tare da ni a team d'in Gimbiya sumayya toh yafito😍*_
*PAGE* 2⃣5⃣
ko da suka shiga part d'in yarima lokacin bai dad'e da dawowa aikiba kasancewar busy yake idan yafita baya samun dawowa sai dare, tsaki yaja ganin bedsheet an shimfid'a masa yace kai dada ba zata ta6a kyaleni inhutaba.
bayan ya fito wanka ya shirya zaune yake bakin gadonsa yana waya jin ana knocking d'in k'ofa yasa yabada izinin ashigo.
zarah ce gaba sai jakkadiya a baya ido hud'u sukayi da yarima sai da gabanta yafad'i tsaye tayi takasa k'arasawa, jakkadiya ce tazube tana kwasar gaisuwa, d'aga mata hannu yarima yayi nan tafara kame-kame am daman... yarima katseta yayi yace zaki iya tafiya.
jakadiya k'ara duk'ar da kanta tayi tace atashi lafiya ranka yadad'e, sannan takalli zarah tace saidasafe gimbiya, zarah gyad'a mata kai kawai tayi.
bayan jakadiya ta fita yarima bai waiwayi inda zarah takeba, zarah tsayuwa tayi na kusan minti biyar ga tsoro da yabaibayeta ga gajiyar tsayuwa har tafara tunanin tazauna k'asa chan sai taji muryar yarima yace zaki iya zuwa kid'auro alwallah.
zarah muryarta tana rawa tace ina da alwallah, d'ago kai yarima yayi yakalleta sannan yatashi yashiga toilet yad'auro alwallah.
bayan ya fito wajen da aka tanada dan sallah yanufa babban dardumane a shimfid'e sai 'yar k'aramar drawer mai d'auke da alqur'anai da sauran littafan addini.
yarima batare da ya kalletaba yace kizo muyi sallah.
zarah ahankali tace nayi sallah, ganin yarima yajuyo ya kalleta yasa dasauri tazo bayansa ta tsaya, sannan tace banzo da hijab ba.
yarima batare da ya kalletaba yawuce yaje yabud'e wardrobe sai gashi da hijab nan yamik'a ma zarah takar6a tasaka.
yarima yana gaba zarah tana bayansa yaja musu sallah, raka'a biyu yayi musu bayan sun sallame addu'a sosai yayi musu sannan yajuyo yakama kan zarah yayi mata addu'a.
zarah ko da tana a tsorace saida ta jinjina ma ilimin yarima dan bata d'auka yana da addini hakaba.
yarima kallonta yayi nan yayi mata tambayoyi akan addininta zarah a nutse take basa amsa, shi kansa yarima saida taburgesa ammah bainuna mataba, wayarsace da tafara ringing yad'auka yana ta wayarsa akan wata kwangila da zai bada saida yayi kusan minti talatin yana waya har ya mance da zarah da take zaune bayansa a nan tafara gyangyad'i.
mik'ewar da yarima yayi ne yalura da ita, janye wayar yayi daga kunnensa yace kije kikwanta in bacci zakiyi.
zarah batace komai ba tana kallonsa yasa k'afa yafita daga d'akin.
parlour yakoma yasha ruwa sannan yazauna saman cushin yacigaba da wayar.
zarah jin shuru bai dawoba cikin ranta tace ko dai yabar min nan inkwanta shi parlour zai kwana, murmushi zarah tayi nan hankalinta yad'an kwanta tatashi taje saman bed d'insa saida tacire alkyabba da hijab d'in sannan takwanta tare da jawo blanket tarufe jikinta takashe gloves nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.
yarima ko da yagama wayar d'aga kai yayi yakalli agogon bango ganin 11:55pm yasa yamik'e yanufi bedroom dan yakwanta, kunna gloves yayi nan haske yagauraye d'akin hango zarah yayi tayi daid'aya saman gado sai baccinta takeyi, shi shaf ma ya mance da akwai mutumin a d'akin.
tsaki yaja har ya juya zai fita sai yayi wani tunanin, ahankali yataka yaje saman gadon yahau, kwanciya yayi gefen zarah tare da juya mata baya yana sak'e-sak'e cikin ransa.
saida yayi kusan minti goma sannan yajuyo yana mai k'arema zarah kallo ya dad'e yana kallonta sannan daga baya yakai hannu yajanyota jikinsa tare da rungumeta saida gabansa yafad'i, nan yakai hannu yafara shafar jikinta, wani irin yarr yaji saida yadad'e yana shafarta sannan yafara k'ok'arin rabata da rigar da take jikinta
zarah har k'ara gyara kwanciyarta take a jikinsa alamun taji dad'in kwanciyar jin ta6awar da akeyi mata tayi yawa yasa cikin bacci tayi firgit tafarka ganinta jikin yarima yasa wani tsoro yad'arsu a zuciyanta cike da tashin hankali tashiga turesa tace nashiga ukku menene haka please kakyaleni.
yarima k'ara matseta yayi a jikinsa muryarsa tana rawa yace kinsan dai dole ko bama so sai mun amince ma juna saboda ansa mana ido yin hakan kawai zaisa kar a zargemu.
zarah cigaba tayi da turesa tace nidai kakyaleni wlh bana so, bata ankaraba sai jitayi yarima ya rabata da rigar da take jikinta, fashewa tayi da kuka tare da turesa da dukkan k'arfin.
yarima ganin zata 6ata masa lokaci yasa yakwantar da ita tare da danneta, zarah cikin kuka tace dan Allah kayi hak'uri kar kayimin komai, yarima bakinsa yakai cikin nata yafara kissing d'inta, inda hannuwansa suka kasa tsayawa waje d'aya a jikinta, ba yarima ba hatta ita kanta zarah saida salon yarima yarikitata batasan lokacin da tafara mayar masa da martaniba, sun dad'e a haka sannan daga bisani yarima yanemi hanya..........
kuka, yakushi, cizo babu wanda batayi masaba ammah bai kyaletaba dan yarima tuni ya fita hayyacinsa baisan inda kansa yakeba saida yasamu nutsuwa sannan yamirgina gefe yakwanta yana maida numfashi.
wani irin nishad'i ne da sanyi yaji yana ratsasa ji yake kamar bai ta6a sanin wata maceba sai akan zarah, ahankali yabud'e idonsa yasafkesu kan zarah da hawaye suke zuba idonta, blanket yajanyo yalullu6e mata jikinta sannan yamik'e yashiga toilet dan yatsarke jikinsa.
bayan ya fito d'aure yake da towel saida yashirya sannan yazo inda zarah take har lokacin kwance take tana cize le6e idanuwanta a rufe, hannu yakai yafara yaye blanket d'in da take rufe da shi, dasauri zarah tabud'e idanuwanta da sukayi jawur tare da rik'o blanket d'in.
yarima kallonta yayi cike da tausayi yace ba abinda zanyi miki, taimaka miki kawai zanyi kiyi wanka.
zarah cikin muryarta da tadishe saboda kuka tace ni kakyaleni dakaina zanyi.
yarima yace ai baki iya takawa.
zarah cikin muryar kuka tace zan iya, tashi tayi zaune dakyar tare da k'ara gyara rufin blanket d'in.
ganin haka yasa yarima yatashi yad'auko mata towel yabata, nan zarah tafara kicin-kicin d'aura towel tana kare jikinta, yanayin yadda takeyi taso taba yarima dariya, ganin haka yasa yajuya har saida tad'aura sannan yajuyo, hannu yakai zai ruk'ota nan tafizge tace kabarni zan iya tafiya.
tana cize Le6e tasamu tamik'e, dakyar tasamu tayi taku d'aya nan tatsaya tare da lumshe ido, tana k'ara taku na biyu wani irin k'ara tasaki.
ganin haka yasa yarima yace ai daman nasan bazaki iyaba, d'aukarta yayi bai zameta a ko'inaba sai cikin ruwan d'umin da yahad'a mata, wata irin k'ara zarah tasaki tare da ruk'unk'umesa, yarima maidata cikin ruwan yayi tare da fizge towel d'in da yake jikinta, zarah dasauri takai hannu tarufe k'irjinta cikin kuka tace katafi zanyi da kaina,
jin haka yasa yarima yafito yabarta a toilet d'in, saida tadad'e cikin ruwan sannan tacanza wasu.
saida tagasa jikinta sosai sannan tayi wankan tsarki tajawo towel tad'aura, ahankali take takawa tana cize le6e har tafito, lokacin yarima har yacanza bedsheet
ganinta yasa yanufi wajenta, zarah muryarta tana rawa tace kabarni zan iya.
jin haka yasa yarima yatsaya yana binta da kallo har taje wajen gadonsa tazauna.
Zuwa yayi cikin lallashi yace kikwanta mana, girgiza masa kai tayi cike da tsoro tace a'a nan ma yayi,
yarima haushi yaji ganin yadda yake lalla6ata ammah sai botsarewa take dan haka yawuce yaje yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya.
zarah ganin haka yasa tajingine kanta da gadon a nan bacci yafara fizgarta, daga k'arshe da taga ba dama ta ida hayewa saman gadon ta kwanta chan k'arshen gado tare da takure jikinta har a lokacin tsoron yarima takeyi.
bayan kamar minti goma yarima yajuyo yanayin yadda take baccin yasa yayi murmushi nan yamik'e ahankali yagyara mata kwanciyarta tare da rufeta da blanket.
gefenta yakwanta tare da zuba ma kyakkyawar fuskarta ido yana kallon yadda take baccin cikin nutsuwa, daga k'arshe yajuya tare da maida idanuwansa yarufe, tunanin darensu na farko da sumayya yafad'o masa a rai, dasauri yajanye tunanin daga zuciyansa gudun kar zargi yashiga,
ya dad'e kwance sannan daga baya bacci yayi awon gaba da shi
saida aka fara sallar asuba sannann yafarka, kallon zarah yayi da taketa baccinta sannan yamik'e yaje yad'auro alwallah bayan yafito, tadata yashiga ammah tak'i tashi,
ganin haka yasa yarima yafara k'ok'arin zareh mata blanket d'in da take rufe da shi, dasauri zarah tabud'e idanuwanta cikin muryar bacci tace na farka.
yarima yucewa yayi yakabbara sallarsa, har yagama sallah zarah tana nan zaune saman gado, saida taga ya juyo ya kalleta sannan tamik'e dakyar tana bin bango tare da cize le6e ahankali take takawa har tashiga toilet.
bayan tayo alwallah rigarta tad'auko tamaida sannan tasaka hijab, nan tasamu tayi sallah.
bayan ta gama a nan k'asa tayi kwanciyarta tare da k'udindine jikinta nan da nan bacci yad'auketa.
yarima bayan ya gama addu'o'insa ganin zarah tayi bacci yasa yawuce yahaye gadonsa yayi kwanciyarsa.
zarah juyi takeyi baccin duk batajin dad'insa saboda k'asan da take kwance, juyawa tayi tare da farkawa jin wuyanta zaiyi ciwo yasa tamik'e dakyar tataka taje takwanta chan k'arshen gado nan tacigaba da baccinta.
wajen k'arfe tara yarima yafarka, mamakine yakamasa ganin zarah saman gadon baisan lokacin da tadawoba.
tashi yayi yaje yashiga wanka bayan ya fito shiryawa yayi cikin boyel d'insa fari yayi gwanin kyau, jin ana knocking d'in k'ofa yasa yakalli zarah da taketa bacci ahankali yabud'e k'ofar yafita gudun kar tafarka, a tsakiyar parlour yatarar da jakadiya tsugunne k'asa ganinsa yasa duk ta dabarbarce tare da duk'ewa k'asa tace ranka yadad'e kagafarceni daman dadace ta aikoni.
haushine yakama yarima cikin ransa yace wannan tsohuwar ba zata ta6a barina inhutaba, fuskarsa ba alamun fara'a yace me tace?
jakadiya tace Allah yaja da ranka daman bedsheet ne tace ind'auko a wanke.
yarima zama yayi saman cushin sannan yace zaki iya shiga kid'auka.
jakadiya tun kan ya ida rufe baki ta mik'e ta nufi bedroom d'insa bayan ta d'auko duk'awatayi tace ranka tadad'e... hannu yarima yad'aga mata tare da nuna mata k'ofa.
dasauri jakadiya tamik'e tafita.
yarima tashi yayi yashiga bedroom, kallon zarah yayi da har lokacin take bacci sannan yaje saman bedside yad'auko yawarya, yana d'auka zarah tabud'e idonta nan sukayi ido hud'u da yarima, ahankali yajanye idonsa daga kallonta, saida yafara tafiya zai fita batare da ya juyoba yace zan sa akawo miki kayanki nan sai kiyi wanka ga magani nan saman bedside idan kinci abinci sai kisha, wayarsace da tafara ringing yayi picking tare da fita daga d'akin.
zarah binsa tayi da kallo har yaffice yamaida mata k'ofar yarufe, runtse idanunta tayi hawayen da take dannewane suka shiga kwaranya daga idanunta tana jin wani k'unci a ranta.
yarima bayan ya fita part d'in zarah yaje bayan kuyanginta sun gaishesa nan yake basu umurni sukaima zarah kaya a part d'insa sannan yatafi.
A chan 6angarensu dada jakadiya da gud'arta tashiga part d'in dada, dada jin jakadiya tayi gud'a yasa tafahimci dalilin haka.
jakadiya gaban dada taduk'a cike da girmamawa tace ranki yadad'e, gimbiya ta kawo mana mutuncinta a masarauta, nan jakadiya tabud'e ma dada bedsheet tagani.
murmushi dada tayi tace Alhmdllh daman daga ganin yarinyarnan nasan zatayi hankali, gaskiya naji dad'i yanzu aje ayi sanarwa kowa yasani sannan kuje kugwada ma su memartaba da iyayen yarima.
duk'awa jakadiya tayi tace an gama ya shugabata sannan tamik'e tafita tana gud'a.
A fada memartaba shanuwa guda yaba zarah, sannan yabada babban sa guda yace ayanka kowa yaci, abban yarima rago biyu yabayar, sultan abbas ma rago yabayar, ko da akaje wajen sultana sadiya bak'in cikine yacikata haka tadaure taje tad'auko turmin Holland tabada, sultana bilkisu kuma sark'ar zinari tabayar,
nan gida yakauraye da murna, sumayya ko da taji dalilin murnar shigewa tayi bedroom d'inta tafad'a saman gado tacigaba da risgar kuka kamar wadda aka aikoma da sak'on mutuwa tsanar zarah taji ta k'aru a cikin ranta, dakyar tajawo wayarta takira sultana sadiya, sultana tunda taga Kiran tasan dalilin kiran da sumayya tayi mata.
tanayin picking tajiyo kukan sumayya cike da tashin hankali tace sumayya menene abin kuka? meyasa kikeson 6ata hawayenki akan wata banza 'yar talakkawa kiduba darajata da ta mahaifinki a gidannan kema kinsan kin zarce kowace mace.
sumayya cikin sheshek'ar kuka tace ummah wlh na tsani yarinyarnan zan iya kasheta saidai nima akasheni.
sultana sadiya cike da tashin hankali tace kisa kuma? haba sumayya nace kidaina ik'irarin kisa kibari mubi komai ahankali,
sumayya cikin kuka tace haba ummah kiduba kigani yanzu anyimin adalci saboda Allah? ni lokacin da na auri yarima duk bansamu wad'annan abubuwan na al'adaba ammah wata bare daga zuwanta ta samu.
sultana sadiya cike da lallashi tace haba sumayya kiyi hak'uri man, nima hakan yayi min ciwo kibarmin komai a hannuna wannan yarinyar dole tabarmiki kidinki kiwala ke kad'ai, ina gargad'inki kar kikuskura kija ta rigima, dan kinsan abun fad'a baya wahala a masarautarnan, kibarta daga ita har wannan miskilin mijin naku duk zanyi maganinsu.
sumayya share hawayen fuskarta tayi cike da jin dad'i tace yauwa ummana saisa nake k'ara sonki.
sultana sadiya saida taga ta kwantar ma d'iyartata da hankali sannan sukayi sallama takashe wayan.
A chan 6angaren zarah bayan yarima yafita dakyar tasamu tasafko daga saman gadon saida tagyarasa sannan tashiga toilet, tak'ara gasa jikinta tayi sannan tayi wanka.
mai tashafa, fuskarta powder da lipstick kawai tasamu, knocking d'in k'ofar da akeyine yasa tamik'e tajanyo hijab tasaka sannan tabada izini ashigo.
d'aya daga cikin kuyangarta ce tashigo cike da girmamawa taduk'a tagaishe da zarah, fuskar zarah d'auke da murmushi ta amsa, kuyangarta tace ranki yadad'e daman maigirma yarima ne yace akawo miki kaya.
zarah kar6ar kayan tayi nan kuyangar tamik'e tabar d'akin, zarah gown d'in atamfarta tasaka, tana gaban dressing mirror tana d'aurin kallabi taji ana Knockin dakyar tafito parlour sannan tabada izini ashigo jakadiya ce fuskarta d'auke da fara'a tashigo, duk'awatayi k'asa tace Allah yataimaki gimbiya da fatan kin tashi lafiya?
zarah tace lafiya lou.
zarah ganin bakin jakadiya yana motsi yasa tace jakadiya ya dai?
jakadiya washe baki tayi tace ranki yadad'e ai mu abun murna ya samemu shiyasa nazo inmiki albishir kyauta kika samu mai tsoka a gidannan.
zarah cike da mamaki tace kyauta kuma? ta me?
jakadiya gyara zamanta tayi tace mrmartaba yabaki sa, mahaifin yarima da mahaifin gimbiya sumayya sun baki raguna, mahaifiyar sumayya ta baki atamfa, mahaifiyar yarima tabaki zinari duk suna wajen dada sai yarima yadawo za'a damk'a masa yabaki.
zarah da mamaki ya ida kasheta tace jakadiya duk na minene?
murmushi jakadiya tayi cike da jin dad'in labarin da take badawa tace ranki yadad'e ai nakawo butulcinki da kikayine gidan miji.
zarah saida gabanta yafad'i cikin ranta tace nashiga ukku yanzu saida kowa yasan abinda nayi?
jin tayi shuru yasa jakadiya tace kinsan gidan sarauta mutuncin mace shine taje a cikakkiyar budurwarta.
zarah kwallah tacika mata ido ahankali tace yanzu saboda Allah saida kowa yasan wannan abun?
jakadiya gyad'a kai tayi tace eh ranki yadad'e ai dole kowa yasani dan abun murna da farin cikine, nan jakadiya tak'ara duk'awa tace nabarki lafiya ranki yadad'e.
zarah kasa cewa komai tayi har jakadiya tafita daga d'akin, ahankali tace wannan wane irin tonon asirine, yanzu saboda Allah sai kowa yasan abinda nayi?
kife kanta tayi tadinga rusa kuka saida tayi mai isarta sannan tatashi taje dining tad'anci abinci kad'an sannan tajanyo alkyabbarta tasaka tafito takoma part d'inta.
sama-sama ta amsa ma kuyanginta gaisuwarsu tashige bedroom d'inta, kwanciya tayi kanta yana kallon ceiling ahankali tunanin abinda yarima yayi mata daren jiya yadinga dawo mata a rai, hawayene suka dinga zuba daga gefen idonta, cikin ranta tace nasan ba'a son ransa yakusanceniba tsaki taja tace ina amfanin wannan masarautar da ake tursasa mutum dole, tunowa tayi da malam bello wani abu yatsaya mata a mak'ogwaro tace Allah sarki malam bello ina ma ace kaine kakasance mijina ba wannan ba, dasauri tajanye tunanin a ranta tare da cewa Astagfirrullah, sannan tajawo wayarta takira su mama dan sugaisa.
A chan 6angaren sumayya kuka taci sosai a ranar kasa cin abincin kirki tayi, kad'an-kad'an ummah ta kirata tabata hak'uri.
yarima ko da yadawo daga wajen aiki ko 6angarensa ba'a barsa yashigaba wani dogari yazo ya isar da kiran da dada takeyi masa,
ko da yaje turakarsu dada bayan yagaisheta dada fara'ar fuskarta takasa 6oyuwa kallonsa tayi tace d'an albarka hak'ik'a naji dad'in za6en da kayi dan ko bakomai takawo mana mutuncinta a gida kuma munasa ran bazata bamu matsalaba fatanmu nan da watanni tahaifo mana magaji.
shidai yarima tun da yazauna dannar wayarsa kawai yakeyi baice ufan ba, dada tana kallonsa tace yarima ina maka magana kayi shuru ka kyaleni, murmushi yarima yayi batare da yad'ago kansaba cike da k'osawa da maganar dada yace ina jinki dada.
dada tace au wulak'ancin nakane yamotsa? shuru yarima yayi baice komai ba, ganin haka yasa dada tace toh nidai nasihar da zan maka itace kazauna da matanka tsakani ga Allah, banda nuna banbanci, kahad'a kan matanka suzauna lafiya.
yarima yace toh dada,
mik'ewa dada tayi taje tad'auko masa kyautukan da zarah tasamu tabashi tace ga kyautukan da matarka tasamu sannan sanuwarta da raguna suna garke.
cike da mamaki yarima yace dada duk naminene? dada tace na mutuncinta ne da takawo mana a masarauta,
yarima murmushi yayi yace kai dada har yanzu dai kuna nan da wannan abun.
dada tace kuma bazamu ta6a dainawaba,
yarima mik'ewa yayi tsaye cike da tsokana yace ranki yadad'e indai kuna raye ba
dada ganin tsokanarta yake yasa tayi shuru takyalesa har yafita daga d'akin.

_~Alhmdllh laifin dad'i k'arewa, my blood zaynav ina tayaki murnar kammala novel d'inki mai suna *BASSAM* Allah yabaki ladar abinda kika fad'a daidai, kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, muje zuwa sai munjiki a sabon novel~_
_*Yau page d'in nakine Sis Harirah nagode sosai da kulawa da soyayyar dakike nunamin Allah yabar k'auna😍*_
*PAGE* 2⃣6⃣
yarima ko da yafito daga turakarsu dada tasu yakoma direct part d'in zarah yawuce, lokacin zarah tana kwance saman bed d'inta kanta yana kallon ceiling,
a parlour kuyangintane zaune ganinsa yasa suka zube suna kwasar gaisuwa yarima baice musu komai ba yawuce yashiga bedroom d'in zarah,
zarah da take kwance jin anbud'e k'ofa yasa tad'ago kai ganin yarimane yasa cikin sauri tamik'e tare da d'an rissinawa cikin girmamawa tace sannu da zuwa,
yarima takawa yayi yaje yazauna bakin bed d'in nata tare da yi mata nuni itama tazauna jikinta sai 6ari yakeyi, ahankali cikin tsadaddar muryarsa yace ya jikin naki?
zarah murya tana rawa tace nawarke, yarima kallonta yayi nad'an lokaci sannan yakai hannu yata6a wuyanta, yace kinsha drugs d'in da na'aje miki? zarah gyad'a masa kai tayi.
yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, saida yad'auki kusan 2 minutes sannan yamik'a mata ledar da take hannunsa tare da mik'ewa.
zarah ganin yana shirin fita batare da yayi mata bayaniba yasa tace aje maka zanyi?
yarima tsayawa yayi da tafiyar da yake batare da ya juyoba yace kyautar da su dada suka bakine sannan a garke akwai shanuwa daga memartaba sai raguna daga abbah da daddy, yana gama fad'in haka yafita yabar d'akin.
zarah binsa tayi da kallo har yafita sannan tabud'e ledar tana kallo dan daman jakadiya tayi mata bayanin komai, 'yar k'aramar sak'ar da tad'auke mata hankaline tad'auko tana dubawa tare da yin murmushi dan ko ba'a fad'aba tasan babbace, bayan ta gama duba kayan tashi tayi taje tasaka cikin wardrobe d'inta sannan tad'ibi kud'i taba wata kuyangarta tace takaima jakadiya.
tun daga ranar zarah bata k'ara taka d'akin yarima ba, shima kansa bai waiwayetaba ahaka har suka cinye sati d'aya.
A ranar da zata cika saki d'aya zaune take parlourn ta tana cin apple ammah hankalinta yana wajen kallo, bata ankaraba sai ganin gimbiya sumayya tayi ta shigo ba ko sallama,
fuskar zarah d'auke da murmushi tamik'e tsaye tare da d'an rissinawa tace sannu da zuwa,
gimbiya sumayya tsaki taja tana bin d'akin da kallo chan sai ta ta6e baki tace eh balaifi talakkawan iyayen naki sunyi d'an k'ok'ari wajen ganin sun fitar da ke kunya Allah dai yasa ba bashi sukaciba dan indai ma suna tunanin zaki samu kibasune toh bazaki ta6a samuba.
zarah da tunda tafara maganar tazuba mata ido cike da takaici tace sumayya duk wulak'ancin da zakiyi kitsaya a kaina kidaina saka iyayena a ciki.
dariyar rainin wayau sumayya tayi tace aikam dole ne iyayenki sushiga tunda kwad'ayi yasa suka bada aurenki, sannan inaso kisani yarima na gimbiya sumayya ne ita kad'ai babu macen da ta isa tara6i mijina tazauna lafiya, kinci sa'a da har kika iya had'a shimfid'a da mijina batare da nad'au matakiba, wama yasani ko kwad'ayayyun iyayenki suka cinna masa ke dan bana tunanin yarima zai iya son d'iyar talakkawa kamar ki.
zarah cikin 6acin rai tace haka dai kikace ammah ai shi yariman ba jahili bane yasan... katseta sumayya tayi cikin tsawa tace kar kisaki kid'aga min murya yakamata kisan da wadda kike magana
girgiza kai sumayya tayi tace hmm idan bakiyi gaggawar fita harkar mijinaba toh wlh zan iya yin komai, dan haka shawara tarage naki
tana kaiwa nan tajuya tafita tabar d'akin
zarah haushi ya ida cikata komawa tayi tazauna tare da dafe kanta tace wannan wace irin rayuwata? dole in samar ma kaina mafita dan wannan matar nalura bazata ta6a barina inhuta ba, chan sai zarah tayi murmushin da ita kad'ai tasan ma'anarsa.
_*After 1 week later*_
gimbiya sumayya ce nagani cikin shirin bacci ta fito sai karairaya take tanufi part d'in yarima,
ko da tashiga yarima kansa saida yayi mamakin ganinta shareta yayi yacigaba da kallonsa, sumayya ganin bai kulataba yasa ta isa wajen da yake zaune tazauna gefensa tare da kwantar da murya tace haba my sweetheart daga shigowata sai kad'auke min kai? yarima shareta yayi yacigaba da kallonsa,
sumayya kwantar da kanta tayi jikinsa tace kana fa jina, sai alokacin yace toh sumayya me kikeso ince miki? ko kina buk'atar wani abune wajena?
sumayya haushi yacikata cikin ranta tace wannan mutumin fa baida mutunci, chan sai tayi murmushi tace bana buk'atar kowa sai mijina rabin rayuwata.
yarima kallonta yayi alamun rashin yadda sannan yamaida kallonsa ga T.V
Sumayya kallon agogo tayi sannan tace sweetheart bacci nakeji please muje mukwanta.
yarima batare da ya kalletaba yace zaki iya tafiya kikwanta ni ba yanzuba,
gimbiya sumayya gyara kwanciyarta tayi a jikinsa cikin shagwa6a tace toh ni nan zan kwanta sai katashi kwanciya.
yarima baice mata komai ba yacigaba da kallonsa sai wajen 11pm sannan yatasheta suka shige master bedroom.
ahaka sumayya tayi kwananta biyu a d'akin yarima ko da sau d'aya bata yadda ta6ata masa rai ba.
zarah dai a kullum tana k'unshe a d'akinta bata yadda talek'o ko da wajen part d'inta ne.
yau dakanta tashiga kitchen tahad'a breakfast kasancewar ta tashi da wuri kuma tana da burin yarima yafara cin abincinta, dan tana ganin kamar hak'intane ita yafi cancanta tagirka masa ba masu aikiba.
had'add'en yam ball tayi sannan tahad'a kunun gyad'a wanda yaji madara peak.
bayan tagama, wanka taje tayi tare da shiryawa cikin gown white nd black colour har k'asa rigar take tana ja da k'asa sannan tayi rolling d'in kanta da bakin veil tare da feshe jikinta da turaruka,
kitchen takoma tajera kular da flask d'in saman tray sannan taba kuyangarta d'aya tad'aukar mata nan tafito tanufi part d'in yarima, duk inda ta gifta gaisheta akeyi tana amsawa cikin sakin fuska, tun kan ta ida isa guards suka hangame mata k'ofa tare da rissinawa suka gaisheta, cikin sakin fuska ta amsa sannan tashiga,
a saman dining taba kuyanga umurni tad'aura tray d'in sannan tasa tasafke breakfast d'in da taga anje masa, bayan ta gama zarah tace zata iya tafiya.
bayan ta fita fargaba da tsoro duk suka kama zarah dan tana tunanin wulak'ancin da zata fuskanta a wajen yarima, ta dad'e tsaye sannan daga baya tabud'e bedroom d'insa tashiga.
tsaye zarah tayi bakin k'ofa tana kallon baiwa da take sharema yarima d'aki.
ganin zarah yasa baiwar taduk'a tagaisheta cike da girmamawa, zarah hankalinta ya tashi sosai tace mekikeyi nan?
baiwar kanta a k'asa tace ranki yadad'e daman nice wadda gimbiya sumayya ta wakilta ina gyarama yarima d'aki.
daidai lokacin yarima yafito wanka, baiwar saida ta tsorata domin bata d'auka yarima yana nan ba tad'auka ya fita.
zarah batare da ta kallesaba tace mata daga yau kar kikuma shigowa d'akin nan nadakatar da ke daga gyaransa.
duk'awa kuyangar tayi tace ranki yadad'e Allah yahuci zuciyanki yadda kikeso haka za"ayi.
zarah hanya tanuna mata, dasauri kuyangar tafita, zarah ma a tsorace tafito tadawo parlour, nan tahau gyarawa mamakin gimbiya sumayya yacikata cikin ranta tace duk ajin nata ammah bata ji zata iya gyaran d'akin mijinta.
bud'e k'ofar da akayine yasa tad'ago takalli gimbiya sumayya da tashigo ranta a 6ace.
zarah d'an rissinawa tayi tace barka da safiya, wata uwar harara sumayya tawurga mata tare da cewa ke har kin isa insa ayimin abu kihana?
zarah kallonta tayi tare da kallon kuyangar da take tsugunne k'asa sannan tayi murmushi tace ban fa isaba saidai nima ina da right inyi abinda nagadama tunda d'akin mijinane,
sumayya a harzuk'e tace ke kar kisaki kiyi min rashin kunya,
bawani maganar rashin kunya idan ke kikaso kigyara to zaki iyayi ammah wlh ban amince 'yar aiki tadinga shigomin d'akin mijiba yadda kike da iko da shi nima haka ina da iko, dan haka indai ke bazakiyiba toh ni zaniyi.
sumayya tayi mamakin zarah domin bata kawo ma ranta zata iya magana hakaba, 'yar dariya sumayya tayi tace lallai talakka bai iya samun wajeba idan yasamu sai yanuna yafi masu gida zak'ewa.
murmushi zarah tayi ko da taji ciwon maganar da sumayya tayada mata ammah bata nunaba, tace Indai shi maigidan ya kasa gyarawa ai ba laifi bane dan an zak'e, tana gama fad'in haka tawuce tacigaba da gyaran d'akin tabar sumayya tsaye tana ta balbala bala'i saida tagaji dan kanta sannan tawuce a zuciye tashiga bedroom d'in yarima suhail.
duk abinda suke akan kunnuwansa dan yana saurarensu, ko da sumayya tashigo ko kallonta baiyiba yacigaba da abinda yakeyi, sumayya a k'ule tace yarima yanzu saboda Allah.... d'aga mata hannu yarima yayi tare da nuna mata k'ofa, tsaye tayi tak'i tafiya,
d'ago kai yarima yayi yaimata wani irin kallon da yaja ba shiri tafita tabar d'akin.
zarah ko da tagama gyara masa parlour ganin har lokacin bai fitoba yasa taje tayi knocking tare da bud'e k'ofan tashiga.
yarima da yake zaune ahankali yad'ago kai yakalleta.
zarah d'an rissinawa tayi tace ga breakfast d'inka chan a dining.
yarima shuru yayi baice komai ba, sai chan yamik'e yafito.
dining yaje yazauna zarah dakanta tayi serving d'insa sannan taje bedroom d'insa tagyara masa tass, bayan tagama tafito takoma part d'inta.
yarima ya d'anci ba laifi dan rayuwarsa yana son abincin gargajiya shi da memartaba halinsu ya zo d'aya.
bayan ya gama bedroom d'insa yakoma yad'auki wayoyinsa yafito yanufi wajen aiki.
zarah saida tatabbatar da ya fita sannan tafito tanufi part d'insa ko da taduba abincin taga yaci balaifi, har cikin ranta taji dad'in hakan, kuyangarta tasa takwashi kulolin tace suje suci, ko da tadawo part d'inta tunani tashiga yi me zata girka masa a k'arshe dai tayanke hukuncin tayi masa tuwon shinkafa miyar ganye dan daman ummi ta fad'a mata yarima yanason abincin gargajiya sosai,
kitchen tashiga bata yadda kuyanginta suyi mataba cewa tayi subarsa saidai gyaran kayan miya da blending kawai sukayi mata.
haka tazage tad'and'ara girkinta tasaka masa acikin had'add'un culars d'inta, nan kuyangi suka gyara mata kitchen tas.
Gimbiya Zarah saida ta tabbatar da dawowar yarima sannan tasa aka jera abincin asaman tray kuyanginta suka d'auka tana gaba suna biye da ita a baya har sukaje 6angaren yarima nan guards d'insa suka gaisheta cike da girmamawa sannan suka bud'e mata k'ofa tashiga, kuyangi a saman dining suka jera abincin sannan suka zube tare da cewa mun cika umurninki ya shugabanmu, gimbiya zarah gyad'a musu kai tayi sannan tace zaku iya tafiya.
suna fita cikin takunta tanufi bedroom d'in yarima suhail tayi knocking yarima da yake tsaye gaban mirror yana shiryawa jin ana knocking yasa yace yes saboda a tunaninsa gimbiya sumayya ce.
gimbiya zarah bud'e k'ofar tayi a hankali tashigo daga d'an nesa da shi kad'an tatsaya tad'an rissina kad'an tare da cewa ur lunch ix ready.
yarima suhail d'auke kansa yayi daga kallonta yacigaba da abinda yakeyi kamar ba zaiyi magana ba sai da suka share kusan minti biyu a haka sannan yace ohk am coming.
gimbiya zarah d'an rissinawa tayi sannan tafito tadawo parlour tazauna saman d'aya daga cikin kujerun d'akin, saida tayi kusan Minti goma a zaune sai ga yarima ya fito sanye da kayansa na alfarma yana takun nan nasa na k'asaita, zarah tana ganin ya fito tamik'e tsaye yana gaba tana biye da shi har sukaje dining ganin ya yi tsaye yasa tagane abinda yake nufi dan haka tajanyo masa kujera yazauna,
sannan tayi serving d'insa itama tajawo kujera tazauna tana dannar wayarta, ta gefen idonta tana kallon yarima suhail yana cin abincinsa ahankali yana yatsina fuska kamar Wanda akayi ma dole, yana cikin ci aka kira wayarsa, baici wani abun kirkiba yamik'e.
itama mik"ewa tayi tabi bayansa suka nufo k'ofa zasu fita, zarah tayi knocking dasauri guards suka bud'e k'ofar nan suka duk'a suna kwasar gaisuwa wajen yarima da gimbiya zarah,
yarima hannu kawai yad'aga musu sannan yawuce gimbiya gefensa tatsaya nan guards suka take musu baya.
gimbiya sumayya da tadawo daga 6angaren iyayenta kuyangi suna take mata baya tsayawa tayi cak tana kallon yarima da yake jere da zarah suna tafiya, dasauri tanufi inda suke tana zuwa tasha gabansu tatsaya, yarima suhail kallonta yayi batare da yace komaiba, gimbiya zarah d'an rissina ma sumayya tayi tace barka.
gimbiya sumayya harara tawurga mata sannan tamaida kallonta ga yarima tace yarima inason ganinka.
yarima suhail cikin rashin damuwa yace toh ai gani kin ganni, gimbiya ta6e baki tayi tace ai ba irin wannan ganinba magana nakeso muyi.
yarima suhail shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace ina saurarenki,
gimbiya cikin fushi tace haba yarima dan zanyi magana da kai ba zaka zo muke6eba kaduba kaga wannan 'yar talakkar tana nan kuma ga bayi da kuyangi gabansu kakeso inyi?
zarah murmushin talaici tayi tare da d'an rissinawa tace ranki yadad'e nabarku lafiya, har tajuya zata tafi da mamakinta kawai sai taji yarima ya rik'o hannunta dasauri tajuyo takallesa fuskarta d'auke da mamaki ammah shi kuma yarima ba ita yake kalloba fuskarsa tana akan ta gimbiya sumayya.
gimbiya sumayya cike da mamaki take kallonsa ganin baida niyar yin magana yasa tace yarima ya haka magana fa nakeso muyi miye nawani rik'o wannan gajar?
yarima suhail fuskarsa babu alamun wasa yace itama matatace kamarki kuma indai kinsan ba zaki iya maganar a gabantaba toh kibari kinzo room d'ina kisameni yana gama fad'in haka yaja hannun gimbiya zarah suka bar wajen nan guards suka take musu baya.
gimbiya sumayya takaici ya cikata ga kunyar dizgin da yarima yayi mata gaban ma'aikatansu jinjina kai tayi tace lallai yarima ni kawulak'anta kafifita bare akaina toh wlh ba zan yardaba, juyowa tayi takalli kuyanginta da suka sunne kansu k'asa domin sunsan yadda ran gimbiyarsu ya6aci toh suma sai ta6anasu, tsawa tadakamusu tace uban mi kuka tsaya kuyi min a nan watau saurare kukeko? jikinsu yana kyarma sukace a'a ranki yadad'e kigafarcemu, hanya tanuna musu cikin fushi tace kubar nan, dasauri har suna rige-rige sukabar wajen.
gimbiya sumayya cike da takaici tashiga zagaye wajen tana jin tsanar zarah tana dad'a k'aruwa a ranta.
zarah har wajen motarsa tarakasa saida taga ya shiga sannan tasunya jikin window tace adawo lafiya,
yarima hannu kawai yad'aga batare da yayi maganaba yabada izini akaja motar.
zarah ko da takoma part d'inta saman gadonta tafad'a murna shar takeyi dan tana ganin ko bakomai yarima yanuna itama tana da d'an matsayinta a wajensa ko da ace ba haka bane a cikin zuciyansa.
murmushi tayi tace yanzu zan nuna miki talakka ma daidai yake da kowa.

*PAGE* 2⃣7⃣
da dare zarah tunani take abinda zata girka ma yarima dan tana tsoron kar tagirka wani abu yak'i ci dan dama ummi ta fad'a mata ba kasafai yacika cin dinner ba, wayarta tajawo tanaso takirasa ammah ta rasa yadda zatayi takirasa, chan dai tadaure tayi dialing d'in numbers a karo na farko, wayar ringing take har tatsinke ammah baiyi picking ba, tsaki taja tace wannan mutumin ya cika wulak'anci wlh, a karo na biyu tak'ara dialing d'in number d'insa saida takusan tsinkewa sannan yayi picking, zarah gabantane yashiga fad'uwa kasa yin magana tayi, a chan 6angaren yarima ma shuru yayi yana jiran ayi magana dan Number d'insa da aka kirasa da ita wadda yake waya da family d'insa ne,
zarah jin baida niyar yin magana yasa tayi sallama, yarima da kamar ba zai amsaba sai chan daga baya ya amsa, zarah gabantane yashiga dukan ukku ukku muryarta tana kyarma tace am za zarah ce, yarima agadarance yace ohk, ya dai?
zarah shuru tayi tarasa abinda zatace sai chan tace daman tambayarka zanyi ko akwai abinda kakeso agirka maka,
yarima cikin rashin damuwa yace no bana cin abinci da dare, bai bari zarah tayi magana ba yakashe wayarsa.
zarah komawa tayi takwanta tare da jan dogon numfashi tace lallai mutumin nan halinsa sai shi.
around 9pm dot zarah wanka taje tayi tashirya cikin kayan baccinta, sannan tad'aura alkyabba daga saman kayan k'amshi kawai yake fita a jikinta, fitowa tayi tanufi part d'in yarima gabanta yana ta fad'uwa gudun kar ya wulak'antata sama-sama ta amsa ma guards d'insa gaisuwar da sukeyi mata, ko da tashiga parlour ganin baya nan yasa taji sanyi a ranta, kallon k'ofan bedroom d'insa tayi tarasa yadda zatayi taje tabud'e tashiga cikin ranta tace toh in na shiga mi zan ce masa? kawai ji tayi Zuciyarta ta karaya har ta juya zata bar d'akin sai kuma tayi wani tunanin, juyowa tayi takoma ahankali tabud'e bedroom d'in ahankali take bud'e k'ofar tashiga, yarima da yake zaune bakin gadonsa yana dannar wayarsa d'ago kai yayi yakalleta cike da mamaki ganinta tazo a lokacin,
zarah murmushi tayi tare da d'an rissinawa tace barka da dare, yarima da yake kallonta gyad'a mata kai kawai yayi, zarah takawa tayi cikin takunta mai jan hankali tanufi wajen bed d'insa, cire alkyabbar tayi ta aje gefe sannan tazauna gefen yarima da yazuba mata ido.
itama kallonsa tayi tana murmushi tace ranka yadad'e ko dai inhad'o maka coffee ko shine kasha nasan bakaci komai ba, yarima suhail d'auke kansa yayi daga kallonta yacigaba da dannar wayarsa.
zarah cikin ranta tace anya mutumin nan zai bada kai? murmushi zarah tayi tare da mik'ewa tanufi wajen freezer tabud'e nan tatsiyayo hollandia cikin cup sannan tadawo tazauna inda take, mik'a masa cup d'in tayi tace ranka yadad'e gashi,
yarima cike da mamaki yad'ago kai yakalleta dan bai ta6a tunanin haka takeba yad'auka wayewarta batakai hakaba, zarah cikin siririyar muryarta tace kakar6a ranka yadad'e.
yarima kamar bazai amsaba sai kuma yatuno wulak'anci baida dad'i dan haka yamik'a hannu yakar6a ahankali yakai cup d'in bakinsa yayi kur6a d'aya sannan ya aje saman bedside, zarah mik'ewa tayi tace akwai abinda kake buk'ata ne?.
yarima suhail cike da rashin damuwa yace no zaki iya tafiya.
zarah murmushi tayi tace ranka yadad'e abun kuma har da korata ake? komawa tayi tazauna tace toh bayanzu zan tafiba.
yarima batare da yakalletaba yace duk yadda kikayi daidai ne, ida kwanciya yayi saman bed d'insa tare da yin pillow da hannuwansa yamaida idanuwansa yarufe chan sai yace idan kin tashi fita kiyi switching d'in light d'in,
zarah jinjina lamarinsa tayi cikin ranta tace lallai mutumin nan yakai inda ban tunani baisan nima daurewa kawai nayi na aje kunya da tsoron da yake cikin rainaba, batace komai ba tayi switching d'in light d'in sannan takwanta gefensa cike da tsoro da fargaba babu wanda yak'ara yin magana ahaka bacci yayi awon gaba da su.
da asuba yarima ne yafara farkawa ta hasken da yake d'akin yakalli zarah da take ta baccinta yanayin yadda take baccin kawai zaka kallah kagane ta takure kanta, janye idanunsa yayi daga kallonta tare da mik'ewa yanufi toilet.
bayan yayi alwallah tsaye yayi bakin gadon yarasa yadda zaiyi yatasheta, dabara ce tafad'o masa nan yakunna gloves haske yagauraye d'akin.
ganin zarah ta motsa yasa yace kitashi kiyi sallah,
ahankali tabud'e idonta tasafkesu akan yarima da yake shirin fita,
saida yafita sannan tamik'e tashiga toilet.
bayan ta gama sallah alk'ur'ani tad'auko tana karantawa har yarima yadawo daga masallaci yakoma ya kwanta, kallonta yake a karo nafarko da yaji ta d'an burgesa dan arayuwarsa yanason mace mai rik'on addininta, tunani yashiga yi yanaso yatuno tun da ya auri sumayya idan ya ta6a ganinta da alk'ur'ani tana karantawa..... muryar zarah ce takatse masa tunani tace ranka yadad'e ina kwana?
yarima batare da ya kalletaba yace lafiya.
zarah kwanciya tayi gefensa nan suka koma bacci.
wajen 8am zarah tafarka daga baccin da take, kallon yarima tayi da yake baccinsa hankali kwance yanayin yadda yake baccin ma saida tajinjina kai cikin ranta tace baccinma cikin izza akeyinsa, doguwar fuskarsa take kallo cikin ranta tace wannan da ummi yake kama dan kyauntane yad'auko, gaskiya ya... gabantane taji ya shiga fad'uwa dasauri tajanye idonta daga kallonsa, ahankali tasafko daga saman bed d'in tad'auki alkyabbarta tasaka sannan tafita daga d'akin.
ko da takoma part d'inta kuyanginta suka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa, ko da tashiga kitchen ruwan zafi tadafa wanda yasha kayan k'amshi sannan tasoya chips,
bayan ta gama bedroom d'inta tashiga taga angyarasa tass dan haka tawuce toilet tayi wanka, bayan ta fito gaban dressing mirror tazauna tad'and'ara kwalliyarta sannan tabud'e wardrobe d'inta tad'auko material blue mai ratsin lemon green tasaka sannan tad'aura alkyabbarta lemon daga sama, ta dad'e tana kallon kanta a mirror sannan tafito tatarar da kuyangarta kande ta shirya breakfast d'in a tray tana jiran fitowarta.
zarah tana gaba hinde tana bayanta sukaje part d'in yarima, hinde a saman dining ta jera sannan tafita.
zarah tura k'ofar bedroom d'in tayi ahankali, ido suka had'a da yarima da yafito wanka, murmushi tasakar masa tace barka da safiya, yarima janye idonsa yayi daga kallonta yana taje kansa yace barka.
zarah ahankali tataka zuwa wajen bed d'insa tagyara sannan tafita takoma parlour tagyara masa tare da kunna turaren wuta, nan da nan d'akin yagauraye da k'amshi.
zama tayi takunna TV tana kallo bud'e k'ofar da akayine yasa tamaida kallonta ga yarima da yafito ya yi gwanin kyau yana ta zuba k'amshi, ko inda take yarima bai kallaba yawuce yanufi dining, zarah mik'ewa tayi tabi bayansa, ita tajanyo masa kujera yazauna sannan tayi serving d'insa, itama tajawo kujera gefensa tazauna tana wasa da yatsun hannunta
yarima batare da ya kalletaba yace ke bakya breakfast d'in.
kallonsa zarah tayi fuskarta d'auke da murmushi tace nafison kai kafarayi ni zanyi daga baya.
yarima ta6e baki yayi baice komai ba yacigaba da breakfast d'insa, bayan ya gama mik'ewa yayi yanufi bedroom d'insa.
zarah binsa tayi da kallo har yashiga, bai wani dad'eba yafito zarah ganin zai fita yasa tace Allah yakiyaye adawo lafiya, yarima batare da ya kalletaba yace Ameen sannan yaficce.
zarah had'a breakfast d'inta tayi, bayan ta gama bedroom d'insa tashiga tagyara sannan takira kuyangarta tazo tad'auki sauran breakfast d'in tafita.
da rana ma haka tashirya masa lunch mai rai da lafiya takai masa part d'insa.
around 9pm coffee tahad'a ma yarima bayan ta gama shiryawa tayi cikin shirin bacci taje part d'in yarima, a bedroom tasamesa yana shirin kwanciya fuskarta d'auke da murmushi tace ranka yadad'e barka da dare.
yarima batare da ya kalletaba yace barka.
bakin gadonsa zarah tazauna ta aje cup d'in coffeen a saman bedside, bayan yarima ya gama zarah tace masa ga coffee nahad'o maka, yarima kallonta yayi yaga itama kallonsa take fuskarta d'auke da murmushi zuwa yayi yazauna gefenta tamik'o masa cup d'in, yarima k'ar6a yayi yana d'an sha a hankali saida yasha kusan rabin cup d'in sannan ya aje tare da mik'ewa yanufi toilet.
bayan ya fito saman bed d'in yahau yakwanta ganin haka yasa zarah takashe gloves masu haske tabar marassa haske sosai, sannan itama takwanta gefensa, bayan kamar minti biyar ahankali tamaida kanta a saman k'irjinsa, ba yarima ba hatta ita kanta zarah saida taji wani iri,
muryar yarima taji yace ya dai?
zarah cikin wata irin muryar da ita kanta batasan tana da itaba tace bakomai ji nayi kwanciyar batayi min dad'iba saisa,
yarima kallonta yayi sannan yamaida idanuwansa yalumshe.
zarah murmushi tayi tace wannan mutumin jin kansa yayi masa yawa, tunowa tayi da lecture d'in da Hajiya kubra tayi mata, ahankali tad'ago kanta tana k'are ma kyakkyawar fuskarsa kallo tana tunanin ta yadda zata 6ullo masa, yarima bud'e idonsa yayi yana kallonta yace wannan kallon fa?
zarah har ta bud'e baki zatayi magana bata ankara ba saidai jin bakinsa tayi cikin nata, zarah biye masa tayi tashiga nuna masa nata salon, ammah nan da nan yarima yarikitata tafita hankalinta batasan lokacin da yarabata da rigar jikintaba, ko da tadawo hankalinta kyarma tashiga yi tana neman turesa ammah ta kasa. nan tafara k'wallah muryarta tana rawa tace dan Allah kadaina bana so.
yarima yanayin yadda tayi maganar ta so tabasa dariya, murmushi yayi yace ai naga abinda kikeso kenan,
zarah fashewa tayi da kuka tace wlh bashi nakeso ba dan Allah kakyaleni bana so, yarima shareta yayi yana jinta tana ta magiyarta ammah bai saurara mataba,
ko da ahankali yabi da ita ammah saida zarah tayi kuka, bayan ya samu nutsuwa janye jikinsa yayi yatashi yabar zarah tana kuka yaje yayi wanka.
bayan ya fito komawa yayi yakwanta, zarah harara tashiga wurga masa karaf suka had'a ido dasauri tajawo towel tad'aura tamik'e taje tashiga toilet, saida tagasa jikinta sannan tayi wankan tsarki.
bayan ta fito rigarta tamaida sannan takwanta chan k'arshen gado tare da juya masa baya, yarima murmushi yayi yajuyo da ita batare da yace komai ba yajuya chan gefen, zarah da mamaki take kallonsa cikin ranta tace shi kuma wannan me yake nufi da hakan? d'an guntun tsaki zarah taja sannan tagyara kwanciyarta.
da asuba bayan sunyi sallah bacci suka koma zarah ba ita ta farkaba sai wajen 11 da mamaki tabi d'akin da kallo, jin ba alamun yarima a d'akin yasa tamik'e har parlour tazo taduba ammah babu alamunsa zama tayi saman kujera tare da dafe kai tace badai fita yayi baiyi breakfast ba?
mik'ewa tayi tagyara ko'ina sannan tafita tabar d'akin, ko da takoma part d'inta ji take ba dad'i tausayinsa yakamata ganin baici komai ba yafita, wayarta tajawo takirasa har saida takusan tsinkewa sannan yayi picking.
zarah jin yayi shuru yasa tace dafatan ka tashi lafiya? yarima shuru yayi nad'an lokaci sannan yace lafiya.
zarah marairaicewa tayi tace shine kafita bakayi breakfast ba?
ai naga bacci kike, cewar yarima.
zarah kamar zatayi kuka tace ai da ka tasheni na had'a maka,
yarima shuru yayi baice komai ba,
zarah tace ko inhad'a yanzu inbada akawo maka?
yarima yace no kar kidamu kibarsa kawai, yanzu ina aiki ne bye,
bayan ya kashe wayar zarah murmushi tayi tare da bin wayar da kallo, dialing din number d'in number d'in abbah tayi suka gaisa sannan yaba mama itama suka gaisa a wajensune takejin labarin yarima jiya yaje suka gaisa mama ce take shaida mata har kayan abinci ya aiko musu, zarah murmushi tayi har cikin ranta taji dad'in yadda yake mutunta iyayenta har da 'yar k'wallarta, bayan sun gama wayar tashi tayi tashiga kitchen had'add'ar fried rice tagirka wadda taji kayan lambu sannan tayi pep chicken, bayan ta gama kunun aya mai dad'i tahad'a.
sawa tayi aka d'auka aka kai masa part d'insa.
da dare tun da takwanta part d'inta juyi kawai takeyi tana jin duk badad'i musamman ma idan ta tuno yanzu haka yana chan tare da gimbiya sumayya sai taja tsaki, a k'arshe tajanyo wayarta tahau chart ba ita ta safkaba sai wajen 1am sannan tasamu tayi bacci.
A chan 6angaren gimbiya sumayya tun daga ranar da suka had'u da zarah da yarima bata k'ara sa zarah a idoba dan a yanzu batada aiki da tazauna sai chart tana gudunar da online business d'inta da zinat ta jonata, harkokinta kawai take kud'i suna shiga a account d'inta.
da dare shiryawa tayi taje part d'in yarima saida sukayi 'yar rigima sannan suka kwanta.
zarah tun da tayi sallar asuba bacci takoma ba ita tafarka ba sai wajen 11am nan tayi wanka tashirya, sannan tafito tanufi part d'in yarima dan a lokacin tasan ya fita, tana zuwa daidai lokacin kuku d'insa yake shirin fitowa daga part d'in yarima d'auke da kayan abinci ganinta yasa yaduk'a Cikin girmamawa yagaisheta.
zarah cikin ranta tace toh wannan dama shi yake girka ma yarima abinci? zarah cikin sakin fuska ta amsa har yatashi zai fita nan zarah tace am me kake da suna?
washe baki yayi yace ranki yadad'e nine kuku halladu babu irin girkin da ban iyaba nine nake girka ma yarima abinci.
zarah tace ayyah Allah sarki halladu toh kayi hak'uri zan d'an dakatar da kai daga yi ma yarima girki dan nafiso yaci na matansa.
kuku cike da tashin hankali yaduk'a yace ranki yadad'e kiyi hak'uri kibarni incigaba wlh ta nan nake samu ana biyana.
murmushi zarah tayi tace kar kadamu hakan bazai shafi albashinka ba za'a cigaba da biyanka, kuma naji ance tunda shugaban masu kula da girkin gidannan yarasu ba'a nad'a waniba toh kaje kazama madadinsa.
cike da jin dad'i yaduk'a yak'ara yi mata godia, murmushi zarah tayi tace bakomai kaje ai ka cancanci fiye da haka tunda ka san aikinka.
bayan ya fita zarah gyara d'akin tayi fess sannan takoma part d'inta tashiga kitchen, burabiscon shinkafa da miya tayi masa sannan tahad'a had'ad'en zo6o tasaka a freezer.
bayan ta gama wanka tashiga tayi tashirya cikin gown d'inta ash colour har k'asa tana sharar k'asa sannan tayi rolling da veil d'in rigar tayi kyau sosai.
parlour takoma tazauna tana jiran dawowar yarima, saida ta daidaici lokacin da yadawo sannan tasa aka d'aukar mata abincin suka nufi part d'insa suna shiga daidai lokacin yarima da gimbiya sumayya suka fito daga bedroom d'insa, cike da mamaki gimbiya sumayya take kallonta cikin ranta tace wannan yarinyar bazata daina shiga hurumina ba?
zarah ganinsu saida gabanta yafad'i murmushi tayi tare da d'an rissinawa tace ranku yadad'e barkanku da fitowa, yarima ne kawai yad'aga mata kai.
gimbiya sumayya kamar daman jira take cikin 6acin rai tace ke! banason shishigi wa yabaki izini kigirka ma mijina abinci? abin naki yana nema yayi yawa watau har ranar girkina sai kin zak'e ma mijina?
zarah murmushi tayi tace ranki yadad'e ba haka bane kawai gani nayi mu yafi dacewa mugirka masa ba kuku ba.
sumayya a fusace tace toh sarkin iyayi toh bari kiji ba za'a girkaba ke in girkawar kikeson yi toh kibari sai ranar girkinki ba nawaba, murmushi zarah tayi batace komai ba tamaida kallonta ga yarima tace ranka yadad'e lunch fa yana jiranka,
yarima wucewa yayi yanufi dining nan zarah tabisa suka bar sumayya tsaye takaici duk ya cikata, a gaban idonta zarah tayi serving d'in yarima sannan tawuce tafita tabar d'akin, sumayya ji take kamar tashak'eta dan bak"in ciki, tsanar zarah nan tak'aru a ranta, ta dad'e a tsaye sannan daga baya a fusace tawuce tafita takoma part d'inta, saman gadonta tafad'a tare da k'walah ma shugabar kuyanginta kira mairo, cikin sauri mairo tazo, sumayya cike da 6acin rai tace bani wayata, dasauri mairo taje tad"auko mata wayar tamik'a mata rikicewa tayi ganin uwargijiyar tasu tana k'wallah, cike da tashin hankali tace ranki yadad'e me yake faruwa? sumayya batace komai ba takar6i wayar takira ummanta, ummah tana d'auka cikin 6acin rai tace badai akan wannan gajar yarinyar bace kike kuka,
sumayya cikin shashek'ar kuka tace ummah kece kike hanani d'aukar mataki akan yarinyar chan toh wlh nagaji da abinda takemin,
a chan 6angaren sultana sadiya da take zaune mik'ewa tayi tafara zagaye dakin cikin 6acin rai tace wlh nabaki dama kid'auki duk matakin da kikaga ya dace, kikwaci mijinki tun kan wannan maýyar tak'wace miki shi, kema ai har da naki laifin, sumayya tsinke wayar tayi batare da sun gama magana ba, dan a rayuwarta ta tsani taji ummah tace tana da laifi.
kallonta tamaida ga jakadiyarta da take tsugunne tace zaki iya tafiya, jakadiyar d'ago kai tayi takalli gimbiya sumayya tace ranki yadad'e yanzu akan wannan yarinyar kike 6ata ranki? aini daman tunda naganta banga alamun mutunci a tare da itaba ranki yadad'e a duk lokacin da kike 6ukatar taimakona ashirye nake zan taimaka miki wajen ganin kin kwaci mijinki daga hannunta, tana kaiwa nan tak'ara dukar da kanta tace Allah yahuci ran gimbiya nabarki lafiya, mik'ewa tayi har zata fita daga d'akin sumayya ahankali tace dawo muyi magana.........

_~Masha Allah *Dr Zain* ina tayaka murnar kammala novel d'inka mai suna *YAN GUDUN HIJIRA* hakika ka fad'akar, ka ilmantar sannan ka nishad'antar gaskiya na jinjina ma namijin k'ok'arin da kayi a cikinsa Allah yabada ladar abinda kafad'a daidai, kura-kuren da suke ciki Allah yayafe maka sai munjiki a new novel 😍~_
_*My classic Feedoh marubiciyar SUHANA yau page d'in nakine kiyi yadda kikeso da shi my friendy ina ji da ke har cikin zuciyana Allah yabarmu tare*_
*PAGE* 2⃣8⃣
ko da jakadiya tadawo tatsugunna, gimbiya tattare nutsuwarta tayi tamaida gareta tace bakomai yasa nakirakiba sai dan naga alamun zaki iya taimaka min, inaso kirik'e min sirrina Indai kikayi haka toh zaki ji dad'ina ammah duk ranar da kika nemi kitona min asiri. murmushin mugunta gimbiya sumayya tayi sannan tace kinsan wacece ni
jakadiya duk'ar da kanta tayi tace ranki yadad'e kar kidamu a kodayaushe ina tare da ke zanyi duk abinda kikeso.
jinjina kai gimbiya sumayya tayi tace shikenan zaki iya tafiya
zarah ko da takoma part d'inta zama tayi saman cushin cikin ranta duk sai taji bataji dad'in abinda tayi ma sumayya ba dan tasan hakan da tayi bai daceba, ko da daman tayine dan tanuna mata talakka ma daidai yake da kowa, kuma duk saboda haka take daurewa tana nuna ma yarima kulawa dan har a lokacin batajin sonsa a cikin ranta, jikinta taji duk yayi sanyi cikin ranta tace insha Allahu bazan k'ara shiga hurumin da banawa ba dole inje inbata hak'uri dan bansan yanayin da zata shiga ba.
sawa tayi aka fara kira mata kuku nan tayi masa bayani tace yakoma bakin aikinsa ammah banda ranar girkinta, dan bata buk'atar mijinta yaci girkin wani ranar girkinta, nan yayi mata godia sannan yatashi yafita cike da jin dad'i.
zarah tashi tayi tanufi part d'in gimbiya sumayya daidai lokacin sumayya tafito daga bedroom d'inta, cikin 6acin rai sumayya tace me kikazo yi min nan munafuka? ko munafuncin da maitan akazo yimin nan?
toh bari kiji Indai kin shanye yarima toh ni kurwata fes take duk wani maita da asiri bazasuyi tasiri akainaba.
zarah k'wallah ce tacika mata ido ahankali tace dan Allah kiyi hak'uri da abinda yafaru wlh...... A fusace sumayya tace wlh me munafuka? toh bari kiji wlh dole kirabu da mijina duk wani zak'ewarki daman ku 'ya'yan talakkawa haka kuke baku iya samun wajeba ina gargad'inki da kifita harkar mijina inko ba hakaba zan fiddo miki halina a fili zakisan wacece gimbiya sumayya,
zarah k'wallar da take cikin idonta tanemi tazubo dasauri tagogeta tace dan Allah kiyi..... ke! ni fice kiban waje tun kan in karyaki a nan wajen, matsiyaciya kawai.
zarah da mamaki take kallonta ahankali tajuya tafita tabar d'akin kwata-kwata bataji dad'in yadda gimbiya sumayya takasa fahimtarta ba.
tun daga lokacin zarah tadaina shiga sabgar yarima indai ba ranar girkinta bace.
_*Bayan Sati 'Daya*_
zarah tana zaune saman cushin hannunta rik'e da wayarta tana operated d'inta, kiran da yashigo wayartane yasa tabi wayar da kallo cike da mamaki ganin mai kiranta, ahankali tayi picking tare da yin sallama, daga chan 6angaren ciki-ciki yarima ya amsa mata sannan yace kizo inason ganinki, yana fad'in haka yakashe wayarsa.
zarah cike da mamaki tabi wayar da kallo cikin ranta tace ko me zanyi masa, mik'ewa tayi taje tad'auko veil d'inta tayafa sannan tafito tanufi part d'insa.
sumayya da bata dad'e da shiga ba zaune take gefensa tace sweetheart kiran me kakemin a wannan lokacin ko akwai abinda kake buk'ata? banza yarima yayi yakyaleta, har ta bud'e baki zatayi magana shigowar zarah yasa tafasa a wulak'ance tad'aga kai takalleta cikin tsawa tace me kikazo yi mana nan kuma uwar shishigi? zarah d'an rissinawa tayi tace barkanku da hutawa, sumayya tace kifita kibamu waje tun kan ranki ya6aci.
zarah kallon yarima tayi da yake kallon TV ammah hankalinsa yana wajensu, ganin baida niyar yin magana yasa tajuya zata fita,
muryar yarima tajiyo yace umurninta zakibi ko nawa?
ahankali zarah tajuyo takallesa har a lokacin kallonsa yana ga tv, ahankali yajuyo yakalleta tare da nuna mata kujera tazauna,
key d'in mota yad'auko yamik'a ma sumayya yace ga wannan key d'in motarki ne da nasiya miki,
sumayya kar6a tayi tana juya key d'in tace dagaske tawa ce yarima? cike da Jin dad'i tarungumesa tace nagode sosai gaskiya naji dad'i, Allah yabarmu tare d'an bak'in ciki kuma saidai yamutu.
murmushi zarah tayi tace Allah yasa alkhairi Aunty gaskiya natayaki murna, sumayya harararta tayi tace inma bak'in ciki kike toh saidai kimutu.
yanayin yadda tayi maganar taso taba yarima dariya, d'ayan key d'in da yake hannunsa yamik'a ma zarah yace kekuma ga naki, zarah da mamaki take kallonsa ji take kamar a mafarki ahankali tace ni kuma?
yarima yace kikar6a mana, zarah tasowa tayi tad'an rissina takar6a tace nagode Allah yasaka da alkhairi Allah yak'ara girma da d'aukaka,
sumayya da tunda taji yace ga ta zarah yasa tacanza fuska, cikin 6acin rai tace ban fahimcekaba? ya naga kaba wannan d'iyar talakkawan kana nufin matsayinmu d'aya da ita ko me?
yarima shuru yayi yakyaleta, sumayya a fusace tace gaskiya yarima baka kyautamin akan me zaka dinga had'ani da wannan 'yar ma..... kallon da yayi matane yasa takasa k'arashe maganarta, maida kallonsa yayi ga zarah da kanta yake sadde k'asa sannan yace motocinku suna parking space zaku iya zuwa kugansu, ke za'a fara koya miki taki ko da ace ba fita zaku dinga yi ku kad'ai ba na mallaka mukune abisa ra'ayin kaina.
zarah ce kawai tace toh mungode Allah yasaka da alkhairi Allah yak'ara bud'i, mik'ewa tayi tace nabarku lafiya sannan tafita tabar d'akin takoma part d'inta.
sumayya kallon yarima tayi tace haba yarima gaskiya banajin dad'in abinda kakeyi min.
yarima da mamaki yake kallonta yace sumayya me nayi miki?
shuru sumayya tayi batace komai ba,
kifad'a min abinda nakeyi miki Wanda ba daidai ba, cewar yarima.
Jin batada niyar yin magana yasa yamik'e yashige bedroom d'insa yabarta nan parlour, cike da 6acin rai sumayya tatashi takoma part d'inta.
tun daga ranar yarima yasa aka fara koya ma zarah mota kasancewar sumayya da dama chan ta iya.
*Bayan kwana biyu*
gimbiya sumayya ce tafito daga part d'inta zataje turakar mahaifiyarta, tsaye tayi tana kallon zarah da tanufi part d'in yarima bayanta kuyangarta ce d'auke da tray.
gimbiya sumayya kallon kuyangarta mairo tayi tace ya kike ganin ya dace inyi inaso kar yarima yaci abincin,
murmushi mairo tayi tare da d'an rissinowa ahankali tayi ma sumayya rad'a nima kaina bansan abinda take cewa ba saidai gani nayi gimbiya sumayya tayi murmushi tare da jinjina kai tace hakan kuwa za'ayi yanzu nasan yarima bai dawoba, mukoma ciki nafasa fita.
Bayan sun koma gimbiya sumayya sawa tayi aka duba mata fitowar zarah daga part d'in yarima, Bayan anzo anfad'a mata mik'ewa tayi tanufi part d'in yarima fuskarta d'auke da murmushi.
yarima ba shi yadawoba sai around 3 o'clock, zarah saida ta daidaici daidai lokacin da tasan yadawo sannan tatashi tanufi part d'insa kasancewar itace take da girki ranar.
tana shiga part d'insa daidai lokacin yafito daga bedroom d'insa hannunsa rik'e da waya yanayi, kallon zarah yayi da take murmushi sannan yawuce yanufi dining ko da yazauna zarah serving d'insa tayi sannan tazauna kusa da kujerar da yake zaune tana jira yagama waya.
gimbiya sumayya tana ganin wucewarta murmushi tayi tace munafuka yau zanso inga yadda zaki kwashe da yarima bari ma inbi inga yadda za'ayi wannan dramar.
lokacin da gimbiya sumayya tashiga part d'insa daidai lokacin yarima yagama wayar da yake, ganinta yasa zarah tamik'e tsaye fuskarta d'auke da murmushi tace ranki yadad'e sannu da zuwa,
murmushi gimbiya sumayya tayi tace yauwa gimbiyar yarima,
da mamaki zarah takalleta dan wannan ne karo nafarko da taga murmushi a fuskarta gimbiya sumayya,
yarima d'aukar spoon d'in yayi yad'ebo abincin zai kai bakinsa, kallon sumayya yayi da tazuba masa ido yace inzakici kizo kizauna kici.
gimbiya sumayya jayo d'aya daga cikin kujerun tayi tazauna nan zarah tayi serving d'inta, yarima ahankali yakai lomar farko a bakinsa, yana fara taunawa dasauri yazubar da abincin yana yamitsa fuska, zarah da mamaki take kallonsa tace yarima lafiya?
mik'ewa yayi dasauri yashige bedroom yanufi toilet, zarah kallon sumayya tayi itama sumayya kallonta tayi tace me yake faruwa?
zarah tace nima ban saniba ammah bari inje ingani dasauri tatashi tabisa a toilet tajiyosa yana ta kakarin amai, dagudu tabisa tarik'osa a rikice tace me yake faruwa please kafad'a min?
kuskure bakinsa yayi yafito yabud'e freezer yatsiyayi hollandia yasha, kallon zarah yayi da take tsaye yawurga mata harara yace wannan wane irin iskancine?
daidai lokacin gimbiya sumayya tashigo tace wai sweetheart me yake faruwa?
zarah tace me nayi maka?
harararta yayi yace au kina nufin bakisan abinda kikayi ba?
zarah tace wlh ban saniba.
yarima fizgota yayi yanufi dining da ita, kallonta yayi yace d'ibi abincin kici,
zarah d'iba tayi takai baki wani irin gishiri da yaji taji dasauri tazubar, cikin tashin hankali tace nashiga ukku ya akayi hakan takasance?
harararta yarima yayi yace kitambayi kanki, kwashi kwanukanki kifitar min daga d'aki,
zarah kwallah ce tacika mata ido tace wlh bansan yadda akayi hakan yakasanceba nidai lafiya lau nayi girki na dan Allah kayi hak'uri bari toh inje indafa ma mai d'an sauk'i.
hanya yarima yanuna mata yace kwashi kayanki kifita,
gimbiya sumayya tana tsaye duk dad'i ya cikata, ahankali tatako inda yake tace sorry sweetheart bari inje insa akawo maka abinci, kallon zarah tayi da take kwashe kwanoni tace ammah dai baki kyautaba wlh ya dai kamata kigyara halinki.
murmushi zarah tayi tad'auki tray zata fita, yarima kallon gimbiya sumayya yayi yace kema bita.
gimbiya sumayya tace haba yarima ni kuma me nayi?
hararar da yawurga matane yasa tawuce dasauri tafita cikin ranta tace tunda dai naci nasara ai bazan damu da kowane wulak'anci zakayi min ba....
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_👑👑👑

_*Wannan Page d'in nakune my Facebook fan's ina ganin sak'onninku nagode sosai inaso kusani nima inaji da ku irin sosai d'innan*_
*PAGE* 3⃣7⃣
bayan ta gama shirin fitowa tayi kuyanginta biyu suka take mata baya zuwa turakar dada, da sallamarta tashiga parlourn lokacin sultana sadiya da wasu mata ukkune sai dada kawai a cikin parlourn.
daga dada sai matan kawai suka amsa mata ammah sultana sadiya inba hararaba babu abinda take wurga mata har zarah tazauna k'asa cike da girmamawa tagaishesu nan suka amsa mata,
d'aya daga cikin matanne tace sannu 'yanmata kema kinzo kiga abun arzik'in ko?
sultana sadiya ce tayi karaf tace ko kuma tazo gulma ba, dada ce takalli sultana sadiya tace haba 'yarnan ko baki ganetabane? matar yarima fa ce,
murmushi sultana sadiya tayi tace ammah dada bakiga cikinmu tazo tazaunaba ko nan akwai sa'anta?
dada rik'e baki tayi tace oh ni.
d'aya daga cikin matan ne tacema zarah matso kusa kiduba ashe surukace, murmushi zarah tayi sannan tamatso sama-sama taduba kayan tana jinjina kai dan k'arshen kud'i an kashesu a wajen anzuba kaya nagani nafad'a, kasa sakin jiki tayi ganin kallon da sultana sadiya takeyi mata dan haka tayi murmushi tace masha Allah, Allah yasa alkhairi,
gabad'ayansu suka amsa da Ameen sannan tayi musu sallama tamik'e tabar d'akin.
daga nan tawuce part d'in iyayen yarima, lokacin da tashiga parlourn ummi ce da rahma sai Aunty husna (yayar yarima) zaune suna tattaunawa, gaba d'ayansu suka amsa mata sallamar da tayi,
ummice cikin sakin fuska tace oyoyo daughter,
murmushi zarah tayi tare da zama k'asa cikin girmamawa tagaishe da ummi,nan ummi ta amsa mata, sannan tagaishe da matar da taga tana kallonta, Aunty husna amsa mata tayi fuska sake, rahma ce tamik'e tace ummi bari inshiga daga ciki induba d'unkunan da aka kawo min, zarah ahankali tace rahma ina wuni?
lafiya kawai tace sannan tawuce tashiga bedroom d'inta.
Aunty husna kallon ummi tayi tace ummi wannan fa ammah ban santaba ko?
murmushi ummi tayi tace zarah ce matar yarima itace wadda akayi bikkin baku k'asar,
sannan ummi tace zarah wannan itace yayar yarima itace husna.
d'ago kai zarah tayi tad'an kalleta sannan taduk'ar da kanta.
dariya Aunty husna tayi tace ji wani kicifi miye nawani satar kallona? toh ai kin ganni nadai fi mijinki kyau.
dariya ummi tayi tace kindai fi sa ammah yarimana yafiki.
zarah k'ara duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya.
Aunty husna tace haba ummi bama za'a ta6a had'amuba wannan d'an naki da jin kansa yayi yawa ko aurennan fa sai a wajenku nakeji kuma ko da nayi masa magana jiya da muka dawo yace min dai zai kawota,
ummi murmushi tayi tace ai my son abun nasa sai shi.
husna da take kallon zarah tace zarah halan ku ma yana yi muku miskilancin?
girgiza kai kawai zarah tayi alamun a'a
dariya husna tayi sannan tace kina dai karesane, yanzu dai nice babbar yaya dan haka kisashi yakawoki gidana kimin wuni.
ahankali zarah tace toh Aunty husna.
mik'ewa husna tayi tace ummi bari inshiga wajen dada,
ummi tace toh shikenan sai kin fito,
kallon zarah tayi tace zarah kigaishe da kishiyar taki tunda ita batazo muka gaisaba ko da kema d'in da sunan wajen ummi kikazo.
murmushi zarah tayi tace Allah Aunty husna bansan kinzoba da tun d'azun nazo, wucewa husna tayi zata fita tace bawani nan.
bayan ta fita ummi kallon zarah tayi tace zarah kinshiga wajen su dada?
zarah cike da jin kunya tace eh ummi naje naga lefe Allah yasa alkhairi,
Ameen, sannan tamik'e tace ina zuwa,
bayan kamar minti ukku sai ga ummi tadawo da wata leda saida tazauna sannan tamik'a ma zarah tace ga anko d'inki daman d'azun nake cema rahma zan aiketa takaimiki, zara kar6a tayi tace toh ummi nagode, nan zarah tabud'e hand bag d'inta tad'auko cheque d'in da yarima yabata tace ummi ga wannan ya bamu muyi hidimar bikki.
murmushin jin dad'i ummi tayi tace aikam dai kin gode ki aje wajenki.
ummi daman na ashoben ne,
ummi murmushi tayi tace no ki aje, ni nasaimiki ashoben yanzu sai kishirya kije kikai d'inki ko kuma inturo miki madam zainab tazo ta aunaki dan ta iya d'inki sosai, sannan idan kina buk'atar wani abu sai kisa akaiki kisiyo.
zarah tace toh ummi nagode sosai Allah yak'ara girma da d'aukaka, Allah yak'ara rufa asiri.
ummi ta ji dad'in addu'an sosai tace Ameen zarah,
nan zarah tayi mata sallama tatashi takoma turakarsu,
daidai da zata shiga sai ga yarima da shaheed zasu fita, kallonta yarima yayi da mamakinta taji yace har kin dawo?
itama kallonsa tayi tace eh tare da gaishe da shaheed, murmushi shaheed yayi yace lafiya lou amaryarmu, kinga najanyo miki ango zamuje rabon IV,
murmushi zarah tayi tare da kallon yarima da yatsareta da ido, sannan tamaida kallonta ga shaheed tace ai kai ne angon yanzu, Allah yasa alkhairi ,Allah yasa ayi damu.
cikin jin dad'i shaheed yace Ameen amarya, gaskiya naji dad'in addu'an nan saidai ince Allah yabarki da angon naki,
zarah kallon yarima tayi nan sukayi ma juna murmushi, sannan yarima yace toh sarkin surutu yanzu dai kazo mutafi ko infasa zuwa, dasauri shaheed yayi gaba tare da cewa amarya sai mundawo,
toh zarah tace sannan takalli yarima da yake tafiya tace sai kun dawo dear,
cak yarima yatsaya daga tafiyar da yake batare da yajuyoba saida yad'anyi murmushi sannan yace Allah yasa,
itama zarah murmushin tayi sannan tawuce tashige gida.
da ta isa part d'inta zama tayi saman cushin nan tabud'e ledar tana kallon anko d'in, less ne brown colour, sai material d'in dinner maroon sai head d'in da za'a had'a silver ne, bayan tagama dubawa mik'ewa tayi takai ta adana sannan takwanta saman 3 seater tana kallo.
bayan sallar magrib madam zainab tazo har gida ta auna zarah nan zarah tabada kaya kala biyar ad'inka mata nan madam zainab tayi mata alk'awalin nan da kwana ukku zata kawo mata d'inkinta.
A chan 6angaren su yarima bayan sun gama kai I.V d'in ahanyarsu takomawa gida shaheed ne yake driving d'insu juyowa yayi yakalli yarima da yake jingine da sit d'in da yake, murmushi shaheed yayi yace ranka yadad'e duk gajiyarce hakan?
kallonsa yarima yayi yai murmushi cikin tsokana yace kawai ina tunanin auren shaheed ne kamar a mafarki.
dariya shaheed yayi yace to ya aka iya tunda kaima ka aje har biyu.
uhm shaheed kenan kaima kasan indai ason rainane da yanzu ban aje mace ko d'ayaba dan aure baya cikin plan d'ina a wannan lokacin kaduba fa kagani duka shekaruna nawa?
dariya shaheed yayi yace ai memartaba ya kyauta da yasa kayi aure tunda a k'arshe ji kayi mace d'aya bata isarka saida kak'ara da wata, ai kai gaba takaika.
tsaki yarima yaja yace kai dai kasani,
eh d'in ni nasani kuma harda kai cikin sanin nawa.
uhm da rabon inhana wani auren k'anwata.
wani irin burki shaheed yaja jikake k'iiitt ya tsaya, dasauri yajuyo yakalli yarima da shima yake kallonsa rik'o hannun yarima yayi yace dan Allah yayanmu kar kaimin haka wlh inason rahma kamar raina.
yarima fisge hannunsa yayi daga rik'on da shaheed yayi masa sannan yace indai kaimin biyayya toh, inkuma kacigaba da rainani sai insa afasa.
Allah yahuci zuciyar yaya yarima duk yadda kakeso haka za'ayi.
oya ja motar mutafi.
cikin sauri shaheed yaja motar yace angama ranka shidad'e,
dariya sukasa gaba d'ayansu sannan yarima yakoma yajingine kansa kamar bashine yagama yin dariya ba.
*WANSHE KARE*
yarima sawa yayi aka tara dukkan ma'aikatan gidan yabada kud'i da atamfofi aka raba ma mata, maza kuma yabada yadi da kud'i suma aka raba musu, nan sukaita murna suna shi masa albarka tare da yi masa addu'a.
lokacin da yarima yafito daga part d'insa zai fita gaba d'ayansu suka taru suka duk'a suna masa godia, murmushi kawai yarima yayi tare da d'aga musu hannu sannan yawuce.
Zarah tun da tatashi wani irin nishad'i takeji wanda ita kanta tarasa murnar me take.
kuyanginta da ma'aikatanta sukazo cikin murna suka nuna mata kyautan da yarima yayi musu tare da ce mata tak'ara yi musu godia wajen yarima, murmushin jin dad'i tayi dan har cikin ranta taji dad'in abinda yarima yayi.
yarima sawa yayi aka kawo ma rahma pics d'in design d'in gado da kujeru nan taza6a yace aje ayi mata room nd bedroom shine gudunmawarsa, ba rahma ba hatta su ummi sunji dad'i nan sukaita shimasa albarka.
6angaren shaheed ma yarima d'aukarsa yayi a mota yakaisa shagon d'inkinsa aka aunasa nan akace ma yarima zuwa jibi za'a kawo masa kayan, shidai shaheed mamakin yarima kawai yake dan baisan lokacin da yabada ayi masa d'inkuna ba, ko da yatambayi yarima shuru yayi bai tankasaba ganin haka yasa shaheed shima yaja bakinsa yayi shuru.
da dare zarah bayan tayi wanka saida tashafe jikinta da mayuka masu k'amshi da humra sannan tad'auki 'yar night gown d'inta wadda iyakarta gwiwa tasaka mai hannun vest, sannan tafeshe jikinta da turaruka kallon agogo tayi taga goma saura dan haka tad'auki hijab d'inta har k'asa tasaka sannan tafito tanufi part d'in yarima,
tana shiga a parlour tacire hijab d'in talinke ta aje sannan tabaza gashinta yasafka a kafad'unta, bud'e bedroom d'in tayi tashiga,
yarima da yake zaune saman gadonsa yana dannar wayarsa jin anbud'e k'ofa yasa yamaida kallonsa ga k'ofar, tunda yakafeta da ido bai d'aukeba.
zarah cikin takunta mai jan aji tatako tanufo gadon fuskarta d'auke da murmushi tahau, har a lokacin idanuwan yarima suna a kanta,
hura masa ido zarah tayi nan yak'yafta cikin sauri yajanye fuskarsa daga kallonta.
tallabo fuskarsa zarah tayi suka kalli juna nan tasakar masa murmushi, yarima zuba mata ido yayi sai chan yace ba dai haka kika tafoba,
shagwa6e fuska zarah tayi tace ya za'ayi intafo haka bayan nasan da mutane a gidan, gaban mijina kawai nazo haka.
yarima bakinta yake kallo tunda tafara maganar yanayinin yadda takeyi ne yaburgesa, fari zarah tayi masa da ido tare da cewa kallon fa?
janye idonsa yayi daga kallonta tare da ta6e baki sannan yacigaba da dannar wayarsa, zarah fisge wayar tayi daga hannunsa,
kallonta yayi yace ya haka? kibani akwai abinda nakeson yi.
bayanta tamaida hannuwanta tare da mak'e kafad'a tace nak'i,
murmushi yayi tare da kwanciya yalumshe idonsa, zarah zuba masa ido tayi tana murmushi sai chan takwanta itama saman k'irjinsa nan gashin kanta yarufe masa fuska.
fuskarsa d'auke da murmushi batare da ya bud'e idonsaba yajanye gashin, zarah d'agowa tayi tana k'are ma fuskarsa kallo nan k'irjinta yafara bugawa ahankali takai bakinta cikin nasa.
yarima kamar daman jira yake nan yacafke batare da ya bud'e idonsaba sukacigaba da kissing d'in junansu, kowa nuna k'arshen k'warewarsa yake nan duk suka fita hayyacinsu daga nan kid'i yacanza, dan yarima baibar zarah ba saida yabata wahala sosai shi kansa yasan ya wahalar da ita jurewa kawai tayi.
bayan komai ya lafa zarah jawo blanket tayi tarufe jikinta cikin d'an hasken da yake d'akin takai dubanta ga yarima da yake kwance idanuwansa a lumshe ammah fuskarsa d'auke da murmushi, saman jikinsa takoma takwanta tare da gyara musu rufin blanket,
ahankali taji yarima ya rungumeta tare da jan ajiyar zuciya,
k'ara gyara kwanciyarta tayi tanajin wani irin sanyi a ranta ahaka bacci yayi awon gaba dasu kowa da abinda yake sak'awa cikin ransa.
kiran sallar farkone yatashi yarima daga baccin da yake ahankali yajanye zarah daga jikinsa yazuba mata ido yana ganin yadda take baccinta a nutse ya dad'e yana kallonta sai kuma chan yajanye idonsa tare da mik'ewa yanufi toilet.
bayan ya fito saida yashirya sannan yaje yashiga tashinta, dakyar zarah tabud'e idanuwanta sannan tamaida talumshe, ahankali yarima yace kitashi lokacin sallah yayi.
juyar da fuskarta tayi gefe d'aya cike da jin kunya sannan tace umhum natashi.
jin haka yasa yarima yawuce yafita yatafi masallaci.
saida zarah taji fitarsa sannan tamik'e dak'yar tanufi toilet saida tagasa jikinta sannan tayi wankan tsarki tare da d'aura alwallah, bayan tafito rigarta da hijab tasaka nan tagabatar da sallar asuba.
bayan tagama a nan saman darduma tanad'e nan bacci yayi awon gaba da ita.
yarima ma koda yadawo daga masallaci bai shiga bedroom d'inba a parlour saman 3 seater yayi kwanciyarsa.
sai wajen k'arfe takwas yafarka nan yatashi yanufi bedroom, koda yashiga a saman darduma yaga zarah kwance tana bacci nan yawuce yashige toilet.
bayan ya fito a gurguje yashirya sannan yad'auki wayarsa da key d'in mota yafita saboda akwai patient d'in da zai ma operation nan da 'yan mintuna.
zarah ko da tafarka kallon agogo tayi ganin har 10:30am yasa cikin sauri tamik'e ganin ba yarima saman gadon yasa tafito parlour nan ma wayam cikin ranta tace Allah yasa wanka yakw ba fita yayiba.
har tagyara bedroom d'in ammah bataji k'arar ruwaba dan haka taje taduba toilet bakowa nan tagane yarima baya nan bataji dad'iba dan tasan dak'yar idan yayi breakfast.
saida tagyara masa ko'ina fes sannan tafita tabar d'akin takoma part d'inta
yarima sai wajen 4pm yadawo gida
bayan yayi wanka kwanciya yayi saman gadonsa dan yahuta saboda a gajiye yake yau.
gimbiya sumayya ce tashigo fuskarta d'auke da murmushi tace ashe kadawo? yarima baice mata komaiba nan taje tahau gadon takwanta gefe tare da tsaresa da surutu shi dai yarima idanuwansa a lumshe suke bai tanka mataba domin surutun da take duk ya ishesa, ganin haka yasa gimbiya sumayya tad'anyi murmushi tace sweetheart na isheka da surutune? yarima batare da ya bud'e idonsaba yace wani abu kike buk'ata?
haushi yakama gimbiya sumayya ganin kusan tambayar da yarima yake mata kenan idan yaga tana shige masa ko da kusan hakane ammah bakowane lokaci bane sai tana buk'atar wani abuba.
ahankali tace haba yarima meyasa kake min haka yanzu banda ikon zuwa wajenka sai idan ina buk'atar wani abu?
yarima banza yayi mata baice komai ba, bud'e k'ofar da akayine yasa duk suka maida hankalinsu ga k'ofar,
zarah tsaye tayi tana kallonsu cike da mamaki kishine k'arara yabayyana a fuskarta ganin sumayya wajen yarima alhali kuma duty d'intane, yarima cikin rashin damuwa yamaida idanuwansa yalumshe,
inda sumayya itakuma take ta wurga ma zarah harara kamar idanuwan zasu fito. chan sai tace malama lafiya zakizo kiyi ma mutane tsaye kina kallonsu?
Zarah abun ya bata haushi ganin sumayya tana nema taraina mata wayau wannan shine adoki mutum sannan ahanasa kuka, d'aure fuska zarah tayi tace malama ba wajenki nazoba wajen mijina nazo dan haka babu ruwanki, zarah takawa tayi ta isa wajen gadon tahau d'ayan gefen yarima takwanta tare da d'aura fuskarta saman k'irjinsa tace dear ashe kadawo, bacci zakayi?
yarima shuru yayi bai tanka taba ganin haka yasa takai hannu tafara shafar fuskarsa cikin wani irin siga.
haushine yakama sumayya ganin yarinya k'arama tana neman taraina mata hankali dan haka itama komawa tayi takwanta tana shafar gashin da yake kwance saman k'irjinsa, nan ita da zarah suka dinga wurga ma junansu harara,
cike da jin haushi zarah takai bakinta ga na yarima tafara kissing d'insa, sumayya cikin 6acin rai tace kam ke ni zaki nuna ma tashanci?
ahankali zarah tazare bakinta daga cikin na yarima tayi murmushi tace Auntyna kin mance yau duty na ne?
yarima duk yana jinsu yayi shuru yakyalesu.
harara sumayya tawurga mata tare da cewa uban dutynki ke har kin isa daga kin samu antaimaka an aureki shine zaki zo kinuna min kema daidai kike da ni.
yarima bud'e idonsa yayi tare da tashi zaune fuskarsa a d'aure yace bakuda hankali zakuzo min d'aki ku duka biyun kukwanta min?
sumayya cike da nuna ita ta isa tace ai itace tashigo dan neman rigima
zarah tace ammah ai yau duty nane tayi min shishigi
yarima fuskarsa babu walwala yace kutashi kufitar min daga d'aki.
sumayya cike da isa tace ammah ai.....wani mugun kallo da yawurga mata yasa tayi shuru.
ganin haka yasa zarah tasafka daga saman gadon tana kumbure-kumbure nan itama sumayya tasafka.
yarima hanya yanuna musu da hannunsa fuskarsa ba alamun wasa ganin haka yasa gaba d'ayansu suka fita daga d'akin kowa yana hararar d'an uwansa.
gimbiya sumayya tace ke wlh idan kina min shishigi sai na miki dukan da bazaki iya tashiba saboda tare da yarima kikazo kika sameni.
inma banda abun talaka da yasamu waje sai yanuna yafi mai gida zak'ewa.
murmushi zarah tayi tace kar kidamu miji dai kike tak'ama da shi toh nima ina tak'ama da hakan sannan kuma arzik'i na Allah ne shi yakeba wanda yaso yahana wanda yaso dan haka yakamata kisan haka, nabarki lafiya gimbiya sumayya tana gama fad'in hakan taficce tabar sumayya tsaye domin ta kashe mata baki bata d'auka zarah zata iya magana hakaba.
sannan daga baya itama taficce tana sak'e-sak'e cikin ranta.
yarima suna fita yakoma yakwanta tare da dafe kansa yana mamakin irin halin wad'annan mata nasa da kwata-kwata basu jituwa indai za'a had'u sau goma toh sai anyi fad'a sau goma koda ya san laifin duk na sumayya ne.
Zarah tana komawa d'akinta batabi takan kuyangintaba tashige bedroom tafad'a saman gado nan tafara wani irin kuka haushin sumayyane yacikata da tsananin kishin *yarima suhail* tabbas ayanzu tasan tana ma yarima wani irin so da baya misultuwa, tabbas ta yarda da maganar malam bello da yace zata so mijinta saidai idan bai amsa sunan namijiba.
A ranar haka tasha kukanta batada walwala ko kad'an kuyangi da bayinta duk sunyi mamakin ganinta acikin wannan yanayi.
sumayya ma ko da tashiga d'akinta korar kowa tayi tafad'a saman gadonta tajanyo wayarta takira ummanta
ummah bugu biyu tad'auka tun kan tayi magana sumayya cikin fushi tace ummah nagaji nagaji wlh natsani inbud'e idona inga yarinyar chan cikin gidan nan.
ummah cike da damuwa tace me yake faruwane?
sumayya tace ummah wlh so take tashiga tsakanina da mijina sai wani shishige ma yarima takeyi yau ma muna tare tazo tatak'uleni rigima ak'arshe yarima yakoramu gaba d'ayanmu wlh ummah zan iya kashe yarinyar nan akan yarima.
ummah itama cikin 6acin rai tace wlh ba'ayi yarinyar da zatazo tahanaki sak'ewa a gidan mijinkiba dole ma ne ind'auki mataki ammah kidaina maganar kisa kibari abi komai a sannu.
sumayya tace ummah wlh yarinyar nan batada kunya
sultana sadiya tace koma dai menene kema harda laifinki sumayya kawai dai ina goyon bayankine.
sumayya d'if takashe wayarta cike da jin haushin ummah tunda itama tace tana da laifi.
wayar zinat takira har saida takusan tsinkewa sannan zinat tad'aga tun kan tayi magana sumayya tace ke wai sai kinga dama zaki d'aga waya
zinat daga chan 6angaren tace kiyi hak'uri dear yanzu dai meke faruwa naji muryarki kamar kina cikin fushi.
sumayya tace hmm zinat bansan ya zanyiba wlh yarinyar chan ce tatisoni gaba.
zinat tace ban fahimtaba meyake faruwa?
sumayya kwashe abunda yafaru tsakaninsu tayi tas Tafad'a ma zinat.
zinat dariya tashiga yi har sumayya tafara k'ulewa...