Shirin tafiya office yayi tsaf bayan kammala break fast kamar yanda suka saba ya kammala tare da zaro tissue dake gefensa ya goge hannayensa da bakinsa...ido ya kashe mata alamar yana bukatar rakiya...kaf a kan idon hajiya mama murmushi ta mayar masu tare da basu wajen dan har aranta yanayin soyayyar yaran tana burgeta.
Mikewa tayi cikin natsuwa ta karba jakan hannunsa tareda taka masa tana yar rausaya taku cikin aji ta sha riga da sket sun dan kama ta kadan tana murmushi inda tsantsar kyaunta ya bayyana kaf double dimples nata huh.. Wani kallo Areef ya ke mata tamkar yau ne farkon haduwarsa da Amal dan bai taba sanin akwai wani sirri boyayye dake tattare da ita ba sai yau..hancinta ya lakuta yace ur modan pretty sweetat i love yhu.
Sunkuyar da kanta tayi dan atyms tana jin kunyarsa sosai duk wata rashin kunya ta ajiyeta gefe banda raya soyayyarsu babu aikin da sukeyi yanzu...sallama sukayi tayi masa fatan alkhairi ta koma ciki.
Tuki yakeyi sautin wakar chrisbrown ma heart tana tashi a hankali da wani sanyanyan kamshi dake tashi acikin motar yana bin wakan a hankali yana tunu yanda Amal dinsa ke masa wani murmushi lallai Amal ta cika mace harda rabi Allah kacika mana burinmu ya fada tareda sauke ajiyar zuciya, har ya isa ma aikatar su tunanin ta yakeyi.
Zamansa keda wuya aka sanar dashi yana da bakuwa tun dazu take jiransa.
Oryt ta shigo.. Ya fada tareda janyo wani file dake gefensa
Sallama tayi cikin siririyar murya...tayi wata shiga ta english wears ne masu kame jiki riga da wando pink ta sha gogul space brown wanda ba lallai kaga kwayar idonta ba..ta karaso cikin taku dai dai wanda yasa kaf illahirin jikinta sai ya motsa duk taku daya ta ja kujerar dake gefensa ta zauna tana taunar chewing gum ta janye glass din tana kallonsa.
Areef tuni jikinsa ya mutu aransa babu abinda yakeyi banda A uzubillahi minash shaidanirrajim a ransa gabansa dukan uku uku kawai yakeyi yana ja baya...me ya kawoki anan kuma muhibbat?
Hmmm...ta gyara zama tace magana nake son yi dakai Areef, hadin kanka nake nema pls.
Ina kika sanni, ina kika kai matsayin magana dani, meyasa a gidanmu baki nemi magana dani ba sai a office dina?, meyasa kike neman shiga rayuwarmu ne?, ke wace irin mayyar mace ce, karkiyi tunanin akwai abinda zaki iyayi dan cin galaba akaina muhibbat...nabaki minti biyar ki fada ki kama gabanki dan wannan banzar shigar taki zata iya zubar mun da mutunci a ma aikata tata...ya fada ransa a bace.
Murmushi ta sake sakar masa sannan ta ce...Areef duk wani wulakanci da zaka yi mani bazai dameni ba madamar zaka saurareni, kuma ba wani abu yasq nake binka ba nake son magana da kai face so da kaunarka da nake Areef, tun ranar da nayi tozali dakai kayi mani satar da nakasa gane ma ajiyarta...kabani hadin kai muyi aure Areef, Amal tana tare da tsohon saurayina mubeen kuma aure zasuyi...
Dakata!...ya daka mata tsawa yace idan kina hauka to kar ki kuskura kizo kaina dan ni ba irin samarin da kike tunani bane dan haka kitashi kibani waje yanzu yanzu ko nasa a fitar dake yanzun nan!
Idan kayi shawara i will be back, thanks ta tashi ta fice guiwa a sanyaye.
Zufa ta fara keto masa duk da kuwa a cikin a.c yake, maganar muhibbat ta tsaya masa, zuciya bata da kashi, anan yafara yan sake sake wanda zuciyarsa ta fara raya masa lallai bazaiyi ba ace Amal yanda take haka da kyau ga diri amma bata da saurayi dama tuni yake wannan tunanun..haka yaji kansa yafara juya masa...keys na shi ya figa ya fice zuwa gida dan bazai lamunci cin amana ba.
Tafiya yake amma baisan inda yake nufa ba kasancewar ransa a bace yake kuma bai taba tunanin haka daga gun Amal ba .
*** *** *** *** ***
Katon katon na biscuit da su chewing gum, sweert, goro da duk abubuwan daal ada ta tanadar wajen bukata yayin saka ranar aure sune aketa shugowa da su a gidan maimuna wato matar Abdul'ahad kuma mahaifiyar Areef.
Sallama ya yi tareda shigowa cikin gidan bayan an gama juye kayan a daidai bakin kofar dakinta.
Wash Allah na...ya fada yayin da ya zauna ya cire hukar kansa.
Maimuna kuwa kallonsa tayi ta murtuke fuska..sannu danzuwa ta fada ba tareda ta kalli inda yake ba.
Yauwa.. Yauwa uwar ango..ya fada cikin zolaya.
Waye angon?
Danki mana, Areef gobe za a raba goro ga kayan nan mun siyo gobe zakuje kukai saiki sanar da makwafta.
Ji tayi tamkar ta dora hannu saman kai ta kwala ihu dan bakin ciki, amma dai Alh kunyi mana adalci?
Komai mu bamuda mutuncin da zakuyi shawara da mu?
Wai ina Areef yake ne bazaizo ina nemansa ba!
Banza yayi da ita ya fada bathroom dan watsa ruwa, yabarta tanata sababin da tafasa, dan ya dauketa mahaukaciya...lolx
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
17
Kai tsaye dakinta ya shiga ya sameta tana kwance tana yan juye juye, wanda babu abinda takeyi face tunanin sahibin nata Areefullah.
Amal!...ya kira sunanta in a serious tone wanda ya sa ta firgita...innalillahi wa innailahirrajiun ta fada a raza ne tareda dafe kirjinta...yayanah lafiya.
Idanunsa sunbi sun kada jawur tamkar wanda ya yini yana sharar kuka...wani kallo mai dauke da alamar tabaya yake mata fuskarsa babu wasa acikinta...Amal waye saurayinki?
Cikin mamaki ta sauko da kafafunta bakin gefen gado tareda maida kallonta na mamaki akansa yaya...wane irin saurayi kuma?
Am just asking yhu, so just give d d answer huz ur boy friend!
Uhmmm...yaya kenan ai kafi kowa sanin wace ce Amal kuma na tabbatar ko a ina zakayi shaidata.
Bazanyi ba!, kawai ki bani ansar tambayata in ba haka ba ranki zai mugun baci n zanje wajensu dady right now...ya fada cike da bacin rai.
Yaya waye ya fada maka waima inada saurayi?
Muhibbat kawarki..
Ohhh shine dama take ta bibiyarmu dan taga ta wargaza tarayyata dakai...to bata isa ba
Yaya pls sit down, zan yi maka bayanin komai and inaso kayarda dani wlh yaya iya gaskiya ta zan fada maka.
Tun a lokacin yake ganin lallai Amal ta raina masa hankali, wato muhibbat ta fada fasa gaskiya har ita tun tuni ta kasa fada masa whyl yasha yimata irin wadanna tambayoyin...zama yayi guiwa a sanyaye yana kallonta dan jikinsa yagama yin sanyi, zuciyarsa ce take ta bugawa.
Yaya banida saurayi kuma ban taba saurayi ba tunda nake sai kai kasan halina kasan yanayin takuna trust me bazan cuceka ba..ta kawashe kaf labarin abinda ya hadata da mubeen ta fada masa.
Ana ya soma yarda da labarin Amal akwai kamshin gaskiya wanda ya tabbatar masa da cewa lallai muhibbat shu'umar mace ce, sai dai kuma kashhhh son da yake wa Amal ya ragu ba kamar yanda yakejinta a zuciyarshi ba.
Baka ce komai ba yaya...
Na yarda Amal, zan koma office.
Bakamun dariya ba pls smyl for me.
Ya dan mayar mata da yake wanda baikai ciki ba.
Bataji dadin hakan ba, amma ta share ta rakasa ya fice.
Duk a wannan lokacin hajiya mama bata gidan taje fadawa danginta batun sa ranar su Amal da za a yi gobe idan Allah ya kaimu.
*** *** *** *** ***
Rana ta zagayo, gida ya cika makil ba masaka tsinke inda ake ta hada hadar rabon goron Amal da Areef, farin ciki fal a fuskar yar kyakkyawar dattijuwar wato hajiya mama wanda take ganin burinta ya gama cika insha Allahu.
Maryam mahaifiyar Amal da maimuna mahaifiyar Areef suna dayan bangaren gidan suma da tawagarsu, wanda hakan yasa maimuna damar fadan ta cikinta, bata da wanu fata da ya wuce asamu yar tangarda tsakanin yaran suce sun fasa...waya ta lalubo ta dannawa Areef kira...cikin yan mintuna kuwa ta shifa bugu daya ya dauka, salamu alaikum umma inayini ya taro ya fada cikin zakuwa.
Eh...haka fa, har kake tambayana ya taro, to ban sani ba, kazo ina son ganin ka yanzu
Umma ayi hakuri dady ya aikeni ina hanyar juyowa.
Batace komai ba ta kashe wayar tana kuta, dan ita aganinta sam an rabata da babban danta da ada bata da kamarshi.
Amal kuwa tana dakinta da kawarta salma, inda take bata labrin yanda sukayi da muhibbat har ta bata number Areef... Hmmm muhibbat mayaudariya ce, ni bazan yi mata magana ba kawai saidai taji andaura aure na da yaya Areef.
Kwarai ma kuwa ki samata ido, ni wlh ban taba ganin mace marar class irinta ba, salma ta fada cike da mamaki.
Haka suka cigaba da tattaunawa tareda neman mafita akan shaidancin muhibbat.
An tsaida ranar auren yaran zuwa wata biyu cif bayan rabon kayan sa rana da akayi...kowa ya watse aka bar gida daga hajiya mama sai husband n wife to be acikinsa...inda ta bukaci ganinsu tayi masu nasiha mai ratsa jiki.
Tayi masu nuni da karsu dauki zuga ko hango wani abu ga waninsu, tareda yi masu kyakkyawan fatan alkhairi.
Abin mamaki Areef fuskarsa babu yabo babu fallasa akan lamarin shi a ganinsa kuma Amal ta sure masa tunda har ta boye masa ta tabayin saurayi bayan shi.
Kallonsa takeyi cike da mamaki, ta tashi ta dawo daf da shi bayan shigewar hajiya mama bed room nata...yaya..?ta kira sunansa cike mamaki
Dagowa yayi idonsa yayi jawur kamar mai shirin fashewa da kuka...naam ya amsa yana shirin mikewa.
Saurin shan gabansa tayi tace...yaya Areef what do mean, ko kana nufin u're nt happy akan engagement da akayi mana?, rana ta farin ciki agaremu amma kai ka kasa bayyana naka farin cikin tamkar anyi maka dole, whatz wrong wit yhu?
Babu komai kaina yana ciwo, i wanna go n rest pls.
Ranta ya so ya baci ta kauce tabashi hanya ya fice zuwa dakinsa.
Dakin ta itama ta shige kasancewar ranta ya baci ganin yanda Areef ya fara canja mata.
Waya ta janyo ta tura masa text...
_Gobe ina da test around 8:00am,Idan zan samu zaka ajiyeni, idan bazan samu ba let me knw naje nabi keke napep, thanks_.
Ta tura masa nan da nan yai delivering bai bi takan wayan ba yayi wurgi da ita sama gado ya fada yafara rera kuka tamkar wanda aka aiko wa da mutuwar mahaifinsa....tirkashi!
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
18
Gari ya waye ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta tsanwar atamfa, dinkin ya karbeta sosai, ba wata kwalliya tayi ba dan ko powder fuskan ta bai gani ba, illa ta shafawa lebenta lip glue gudun bushewar baki, yafa mayafinta tayi ta dora dan kwalinta saman kai batareda ta daura shi ba ta fito falo inda ta same su hajiya mama da Areef suna karyawa.
Wanda ita bata saba ganin Areef yayi break fast ba tareda tana kusa da shi ba, koda kuwa bazata ci komai ba.
Mamaki ne ya rufeta, ta kauda kanta tamkar batasan Allah ya ajiye shi a gun ba, dan ya kusa kaita makura, haka shima ko kallo bata ishe shi ba.
Ahhh Amal kin fito ne?, hajiya mama ta fada cike da kulawa.
Eh hajiya mama gud morning, Amal ta fada tareda rusunawa.
To Allah bada sa'a, saidai banga kinci komai ba yau, dafatan lafiya
Wlh hajiya mama am satisfied test ne a gabana kuma na makara.
To banda abinki kin hada kayan break kuma kice bazaki ci komai ba, bayan kuma kinsan kinada test din amma saida kika tsaya kika hada mana komai.
Hajiya mama tamu...ta fada tana yaken bakin ciki ganin yanda Areef ya nuna halin ko in kula akanta...natafi hajiya mama..ta sakai zata fice.
Areef tashi ka mikata mana tunda kai gama.
Bai bata ansa ba ya mike kawai tareda jan keys na motansa yafice fuuuuuu...dan ba haka yaso ba.
*** *** *** *** ***
Muhibbat dadi ya rufeta ganin yanda taga fuskar Areef ta canja tun a lokacin da take bashi labarin Amal da Mubeen, wanda ita kanta tasan akwai sharri a ciki, ita dai batada wani buri da ya wuce taga ta mallakeshi ya zama nata.
Nan take tayi saving number din Areef as MY HANDSOME, danna masa kira tayi tana ta ringing amma ba a daga ba, hakan yasa ta yanke shawarar sace zuciyarshi ta hanyar tura masa zafafan messages.
Kayya...muhibbat batasan halin Areef ba, da tasani da bata yanke wannan gurguwar shawarar ba.
_IForget The Whole World, And Lost In Your Silky Soft Arms I Love This Feeling Of Being In Love With You I Wanna Be With You Every Day, Every Moments!_
_Muhibbat S. Saulawa_
Ta tura masa na take yayi delivering.
Karar kiran da akayi masa bai dauka ba da shiga message din yasa Amal yi masa wani irin kallo mai alamar tambaya.
Daidai bakin get ya ajiyeta, yace idan kingama ki kirani ko kimun text, fuska a daure yafada.
Kallonsa takeyi tamkar ta fashe da kuka, ganin yanda Areef dinta ya canja mata cikin dan kan kanin lokaci, dole ne na dauki mataki ta fada a ranta.
Ina magana ko bakyaji na, am late fa, kuma kinfi kowa sanin yanayin aikina...yana magana fuskanshi tana kallon gefen sa tamkar daga waje yake magana dawani.
Hmmmm lallai...ta fada tareda bude murfin motan....bata amsashi ba itama ta fice abinta.
Yaja motansa yayi gaba.
Tuki yakeyi saidai kaf tunaninsa anbi an dagula masa shi, yarasa gane kansa.
Aiki take tayi da kai komo a kitchen din kasan cewar ta kammala session nata na karatu wato 100L, ji tayi kamar haya niya a cikin gidan nasu tayi saurin fitowa ta sama mahaifiyarsu maimuna ta rike bakin rigar Dadynsu lallai sai ya sallameta.
Tunga taja tana salati, kasancewar Arfat yarinya ce mai hankali da natsuwa ga sanin ya kamata, karasa wa tayi wajen ta kama hannun mahaifiyarta ta niyyar ta saki rigar mahaifinsu.
Umma ina ganin wannan ba dacewa bace, shifa aure daraja ce dashi, bazaka hana ayi aure ba kuma bai kamata kasa akasheshi ba kasancewar shima fa yanada rai, kuyi hakuri dady tayi maku shishigi..ta fada tana kallonsa idonta ya ciko da kwalla, ganin yanda kullum iyayenta suke hatsaniya akan maganar auren Areef da Amal.
Babu damuwa Arfat jeki cigaba da aikinki Allah ya maki albarka.
Ameeen ta fada ta juya jiki babu kwari dan tana son sasanta iyayenta, saidai suna ganin kamar shekarunta basu kai wannan matakin ba.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
19
Kiransa ta sakeyi ganin bai biyo missed calls nata ba kuma baiyi replying text nata ba..
Zaro wayan yayi a gefe aljuhunsa ya duba yaga bitch sunan daya saka mata kenan...mtsw yaja dogon tsoki sannan ya yi picking.
Bai jira ta ce komai ba ya fara da daka mata sawa...muhibbat kike kowa?!, idan ke mayya ce to kisawa ranki kurwar Areef tafi karfin kamu a wajenki, wlh wlh wlh idan kika sake kiran wayana ko kikasake zuwa gidanmu ko office dina sai nasa an yi maki mugun duka...banza dakikiya.
Murmushi ta saki...tace Yaya Areef nawa...dama tuni na shirya makaman yakina akanka dan na san dole na fuskanci kalubale kala kala daga gareka kafin nasamu karbuwa, kuma zan jure duk wani wulakancinka madamar dazaka amince da tayin danazo maka dashi.
Bai sake ce mata komai ba ya kashe wayan tareda zare sim din anan take yayi gutsu gutsu dashi ya karya ya jefar....doguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da fadin Alhamdulillah..ya kara sautin karatun alqur'ani da yakeji har ya isa office din.
Yau kam ji yakeyi tamkar an biya masa hajji fuskarsa cike da annuri, yana aikinsa yanda ya kamata...kwatsam tunanin princess dinsa wato Amal ya fado masa aransa wanda ya dakatar dashi daga aikin da ya kusa kammalawa...wayansasa ya dauka don kiranta yaji yaya an gama test din...sai yayi rashin sa'a wayan nata akashe...huh...Allah yasa ba fushi kikayi ba my princess ya fada kasa kasa.
Sako ya tura mata kamar haka
_I Love You From The Bottom Of My Heart. And I Hope We Are One Heart Beating At One Time.So much missing ur Smiling Face My Princess._
_A.A AYUD1_
Idanunsa ya lumshe yana hango fuskar kyakkyawar yarinya wanda a yanzu ya riga ya gano bakin zaren abinda ya rage masa shine ya idasa kitse shi.
*** *** *** *** ***
Kuka takeyi riris tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa, ganin irin kiran da take tayiwa layin nasa amma yaki tafiya, wannan wane irin wulakanci ne Areef yayi mata?, wai dame Amal ta fita?, k bata da kyau ne ko bata iya tsara kalami bane, wai miye aibunta?, haka ta cigaba da jerowa kanta tambayoyin da tarasa gane amsoshinsu.
Tunaninta daya shine taje tasamu hajiya mama ta sanar da ita, inyaso koma wane irin kallo Amal zatayi mata saidai tayi mata, da haka ta kwanta takosa gari ya waye dan taje.
Alh Abdallah da uwargidansa babu abinda sukeyi face yan shirye shiryen bikin Amal, wanda bai wuce saura wata daya ba, komai sun tanada dan shagulgulan bikin.
Gidan tashigo fuska babu annuri dan ita abubuwan da Areef yake mata sun fara damunta, da gangan ta kashe wayanta danma tayi masa karyan batada charge koda ya yi mata magana, duk da tasan ba lallai ya damu da rashin kiransa da tayi ba, wanda ita yau ta yanke shawara su gurfana gaban hajiya mama dan sanin matsayinta a wajen Areef.
Kai tsaye bathroom ta fada dan watsa ruwa da dauro al awala..
Inda ta samu riga doguwa mara nauyi ta saka, ta gabatar da sallah azahar.
Hajiyatah ko barci kikeyi...ta fada yayin fitowar ta daga dakinta ta nufi dakin hajiya mama...fuskarta asake.
Hajiyarmu dai ko yau ni ba tawa bace?..tajiyo muryar kamar daga sama.
Turo baki tayi ta juyo tayi masa wani kallo ta watsar ta shige dakin hajiya mama.
Binta yayi ciki...hajiya kinga yarinyar nan ko?
To me ya hadaku yau kuma?, hajiya mama ta fada yayin rufe littafin zadul muslimat da take karantawa.
Bayan ta ta boye tace wlh hajiya mama yau kotunki zamu shiga dole sai anyi mana shari'ah...
Laaaa...bayan ni danace kiyi abu bakyayi sannan zaki ce haka babu komai...ya fada cikin shagwaba...to yanzu na dawo hajiya mama kice tabani abinci na yunwa nakeji.
To ai itama inajin shigowarta kenan ko?
Nima yunwae nakeji...ta turo baki cikin shagwaba.
Oya lets go to kitchen ki dafa mana indomie kinji yar kanwata...ya fada cike da rigima a idonshi.
Kallon mamaki Amal takeyi masa bayan taga irin rabuwar da sukayi daya kaita sch, hmmmm kawai ta fada ta mike ta fice ya bita da kallo...dan yanayin tafiyar ta yana daya daga cikin yake burge Areef.
Tashi yayu yabi bayanta...hajiya mama tayi murmushi tace kaya da yani kenan.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
20
Dakinta ta fada tare da turo kofan dakin...yana biye da ita yana magana amma tayi shiru ta kyale shi.
Haba princess of mine, bai kamata muna haka ba fa, aurenmu ya kusa fa, ya kamata muyi facing abubuwan da ke gabanmu...ya tura kofan dakin yana magana.
Yaya pls kabarni na huta agajiye nake.
Zama yayi bakin gefen gadon inda tayi saurin direwa kasa ta ja hijabi ta rufe fuskanta.
Hmmmm...yaja dogon numfashi, pls ma princess nagane kuskurena bazan sake ba pls, and muhibbat da take bamu matsala na yaga rigar mutuncinta na fada mata maganar da inada tabbacin bazata sake shiga rayuwarmu ba, na canja sim ma in short here is d sim park, ya zaro daga aljihunsa ya mika mata a marairaice.
Nan take tausayinsa ya kamata...ta mike zaune tace...Alhamdulillah da kayi saurin fahimta da kanka, Allah ya kara tsaremu.
Ameeen ya fada fuskarci cike da farinciki...to princess wlh am too tired ina son zuwa nayi wanka pls me zan samu na jefawa yan cikina.
Dariya yabata tace...sai kace wani rago maza fa suna da dauriyar yunwa...jeka huta zan maka abinci yanzu.
Oryt sweetat..ya mike ya fice.
*** *** *** *** ***
Haka rayuwar zuri'ar ta cigaba da tafiya cikin yan tangarda inda da ga karshe komai nasu ya daidai ta gwanin ban sha awa.
Maimuna ce ta gurfana a gaban Alh Abdul'ahad...kanta a sunkuye take magana, Alh kayi hakuri akan abubuwan da suka faru insha Allah baza a kuma ba sharrin shaidan ne.
Maimuna, aini bana maki wani kallo face dama rashin fahimta da gane muhimmancin lamarin, amma tunda kin gane Alhamdulillahi, Allah yakara kyauta gaba.
Nagode maigidana, Ameeen.
Ta fada tana mai yi masa wani irin kallo mai cike da kauna acikinsa.
Murmushi ya mayar mata yace...amma fa kin wahalar da zuciyata Uwar dakina.
Uhmmm...Haka dai kace..ainima ka wahalar da tawa zuciyar...
Kukan adnan ya dakatar da firar tsofaffin masoyan inda ya rugo a guje ya fada ma mahaifiyar tashi yanata borin kuka, wai Ayman ya dakeshi.
Ta shirya tsaf don zuwa gidan hajiya mama wanda shine waje na karshe da take tunanin idan taje bata samu karbuwa ba to fa kashinta ya bushe...shiga ce tayi ta lace blue inda komai nata hadin sky blue dinne tayi, shigar tayi mugun amsarta kasancewar ta yar duma duma, babu abinda ke tashi a jikinta face daddadan kamshi mai sanyaya zuciya..ta dauka hand bag dinta ta fice.
Ta fiya takeyi saman titi taku dai dai kasancewar bata samu mai a daidaita da wuri ba.
Bakin wata kwalbati taja tunga ta tsaya tanata taunar chewing gum...
Taci sa a bata dade ba saiga mai a daidaita ta tsaida shi tareda yi masa kwatancen gidan hajiya mama wato gidansu Areef da Amal.
Fira sukeyi irin ta masoya bayan kammala cin abincinsu...banda dariya da annushuwa babu abinda kake gane bayyane a fuskokin nasu...yaya yaushe zamuje gida wai?
Ido ya fiddo waje yace wato kin gaji da ganina kullum ko?
No i dont mean dat ma prince kawai ina so muje muyi mash kwana biyu kowane gida sai mu dawo.
Dariya tabashi dan lallai Amal batasan mutae ba.. Wato muje nan gidan mu kwana biyu muje cen ma haka duk muna tare ko?, ya tambayeta cike da mamaki..ke bakisan cewa za ayi bamu da kunya bama.
Habada dai...ta fiddo kyawawan nata idanun itama...suna cikin haka suka jiyo sallama.
Kallon kallo Areef da Amal sukayiwa junansu jin muryar Muhibbat da sukajiyo tamkar a cikin mafarki.
Areef yasa hannunsa yacewa Amal...shhhhh alamar karta ce komai...ya mike zuwa daf da bakin kofar falon.
Waye ne?!.
Uhm...uhm kana cikin kenan, nice Yaya Areef ta fada in a guilty tone..kanta a kasa.
To wajen wa kikazo yau kuma karya?!, wacce batasan darajar AMINTAKA ba?
Hmmmm...yaya Areef kenan, ba wajenka nazo ba..ba kuma wajen Amal nazo ba wajen hajiya ma....dakata!
Ya daka mata tsawa wacce ta hanata karasawa yacigaba da zuba mata mugayen kalaman da zasu sakata ta hankalta.
Amma dukansu babu wanda ya sosa zuciyarta madamar zata mallaki Areef.
Ikon Allah....abinda Amal ta fada kenan wanda yasa ta kataso daf da inda suke maganar, wanda yasa ta watsawa muhibbat wani irin kallo mai kama da zaki gane bakida wayo..
Duk a wannan lokacin hajiya mama bata san wainar da ake toyawa a gidan ba.
Muhibbat kuwa ta toge babu inda zata tafi sai tagana da hajiya mama.
Allah wadaran marar zuciya!