Shiru tai tana tunani, kayan da aka aikomai dashi wanda ke kan gado ya d'an kura ma ido alamar tunani kafin ya dawo da kallansa kan mahaifiyarsa yace " Umma zan shirya."
Kai ta d'aga sannan ta mike ta dafa kafadarsa d'aya tace " duk hukuncin da ka yanke ina tare da kai dan kuwa na tabbata d'ana bazai bani kunya ba."
Bata jira amsarsa ba tai waje.
Abu Turab ya shirya tsaf ya fito daga d'akinsa, inda yake zama ya wuce dan bayin sa su nad'amai rawani.
Tunda ya shigo suke kallansa dayake sunsan baya gani yasa suka kura mai ido kowa da abinda ke ransa nan fa suka dan fara gulma da ido wanda duk yana ganinsu.
Rawanin dayake so ya basu nan suka nad'amai, ya sa takalmi yace su tafi.
A kofar gida yaga wani bawa rike da doki yasha ado, bawan na ganin Abu Turab ya taho da gudu ya dan rusuna yace " Ranka ya dade ha doki nan inji magajiya."
Murmushi yai sannan yace " ayya? Ya za'ayi? Gashi na riga na aikama Barga akan ya aikomin doki sai dai ma maida wannan gun Bargan gudub kar a maka fada akan rashin isar da sakonka da wuri.
Bawan yai saurin sunkuyawa yace "Tuba nake D'an Sarki."
Abu Turab yai murmushi sannan yace " ba haushi naji ba ina dai gujema fada ne."
Kallan d'aya daga cikin bayinsa yai yace " sanar da Barga ya baka dokina."
Cikin mamaki yace " Ranka ya dade ai ba'a mai....."
Katseshi yai da cewa " hakan nakesansa."
To, abinda ya fada kenan yai saurin fara tafiya.
Bai dade ba sai gashi da rike da dokin Abu Turab ya hau.
Sai daya bari Sarki zai fita hawa sannan ya shiga cikinsu, bai bari sun ganshi a gida ba.
Tunda ya shiga cikinsu kuwa ake kallansa, kowa mamaki wannan wanene haka?
Dama tawagar Abdulmajid ya shiga, dan kara gudun dokin yai ya matsa bayan Abdulmajid kadan.
Nan fa kowa ya fara kallansa, mutand sai juyowa suke ana nunashi da hannu, ganin yanda ake nunuwashi yasa Abdulmajid ya tsargu ganin saitinsa ne.
Kallan na kusa dashi yai yace " menene?"
Juyawa yai shima, cikin mamaki ya kalli Abu Turab sannan ya matso inda Abdulmajid yake yace " Yarima ai kaninka ne yake bayanmu."
Murmushi yai dan dama yasan da zuwan nashi, sunyi shiri sosai dan kuwa d'inki Magajiya tasa aka mai irin wanda zai saka a wannan ranar, wanda hakan sab'awa ne ga al'adarsu ace anyi anko da Sarki balle kuma bai sani ba.
Ya sake murmushi tunawa dayai dokin ma kwalliyar irinta Sarki sukasa akamai.
Sai yanzu ya fahimci dalilin dayasa ake nuna Abu Turab.
Sai da sukaje inda Sarki zai d'an tsaya kafin ya juyo alokacin ne Abdulmajid yaga yanda ake ta nuna Abu Turab, dariya ya kunshe ya juyo dan ganin yanda ma kayan yamai.
Sai dai me????
Idanu ya zaro sosai cikin tsananin mamakin abinda idanunsa suka ganemai, me ke faruwa? Menene hakan?
Shi kansa Sarki ya fahimci yanda mutane suke nune nune, hakan yasa ya tambayi Galadima yace " meke faruwa?"
Nan Galadima yasa aka bincika.
Matsowa yai wajen kunnen Sarki ya rad'amai.
Ransa ya b'aci sosai nan ya bada alama akan su juya.
Haka sukabi har suka koma gida.
Abdulmajid kam sukuku ya karasa wannan hawan zuciyarsa tana ta san taga wani irin hukunci Mai Martaba zai yankema d'an lelen nasa.
Suna isa akazo aka sanar ma Abu Turab akan Mai Martaba na nemansa a fada.
Yasan za'ai haka shiyasa ya sauka zuciya d'aya ya bada dokinsa ya nufi fadar.
Dayaje zai shiga sai ya ajiye sandarsa sannan ya shiga ciki.
Zama yai irin zaman gurfana d'in nan, Mai Martaba ya kalli dumbun manyan mutane masu mukamin sarauta dake gun, sai dai wannan karan yazamarmai dole duk san da yakema d'an nasa ya mai tambaya a nan Saboda yau a matsayin Sarki yake ba uba ba.
Abu Turab ya kalla fuskarsa a had'e sosai yace " Me zaka fad'a game da wannan shigar ta cin zarafi dakai?"
Nan fa aka kara kallansa, Abdulmajid wanda ya shigo yanzu yai murmushin jin dadi tare da zama.
Abu Turab yai shiru baice komai ba, kallansa Mai Martaba yai yace " in har bakada amsa akan hakan to lalai ne ka fuskanci hukuncin masarauta."
Ya fad'a tare da kauda kai.
Abu Turab kansa na kasa yace " Tuba nake in har shigar danai laifice a tsarin masarautarmu."
Nan fa kowa ya kara kallansa, rigace ta shadda wacce ta tsufa kana ganinta kasan tsohuwace, sannan na babbar riga a jikinsa ya maka wani tsohon rawani, wannan shigar ko a cikin gida ba yinta yake ba balle a gun hawa cikin jama'a.
Hisham ya kalleshi yace " kanasan kace shigarka batada laifi kake nufi ko me?"
Abu Turab ya kalleshi fuakarsa a sake yace" kuskure nane sai dai ina fatan amin afuwa."
Cikin takaici Mai Martaba yace " Abu Turab! Nasan ba gani kakeyi ba dan haka laifin bayinka ne zasu amshi hukuncin barinka kayi wannan shigar dolene su fuskanci hukunci mai tsauri."
Abu Turab ya kara kasa dakai cikin kalar tausayi yace " ko wani hukunci ne amin domin kuwa sun bani kayan da ya kamata insaka sai dai daga laushin kayan da yanayin su yasa nasan ba nine na dace da kayan ba, sai dai hakan baisa na musa ba na saka kayan dan kuwa bansan ya suke ba da idona, ka gafarceni Mai Martaba ina fitowa aka sanar dani kayan irin naka ne sak, sannan dokinma irin kwalliyarka ne dashi, wannan yasa na hanzarta na janyo kayan dabansan ya suke ba na saka sannan na aika Barga ya bani dokina nasa amaida mai waccan."
Jin kalamansa lalai sun ba kowa mamaki, Abdulmajid kam cikin tsoron kar asirinsu ya tuno yai saurin cewa " menene shaidarka ta fadar haka? Kana tunanin ko me kace yarda zamuyi?"
Abu Turab wanda ana cemai Mai Martaba na kiransa ya tura Salau(mai kula dashi wanda suka fi shiri) akan ya d'aukomai kayan nan,sannan ya aika Barga yazo.
Nan yace " Salau!"
Daga waje Salau ya amsa da karfi.
Nan ya shigo rike da kaya.
Abu Turab yaba shi kuna ya ware kayan anan kowa ya gani, to fa!
Nan aka fara magana kasa kasa.
Abu Turab yace " ka gafarceni Ranka ya dade ba gani nake ba bare nasan da haka."
Barga! Nan ya amsa shima daga waje sannan ya shigo.
Abu Turab yace " wani irin kwalliya ne da dokin danasa a dawom dashi?"
Nan Barga ya musu bayani.
Mai Martaba cikin tsananin mamaki yace " wanene ya aikoma da kayan da kuma dokin?"
Abu Turab yad'an sadda kai tunowa yai da yanda suka karashe da mahaifiyarsa.
Harta fita ta dawo tace " Abu Turab! Me kake san yi dan hankalina bazaj kwanta ba sai naji."
Ya kalleta yace " bazansa kayan ba haka kuma bazan hau dokin ba, na tabbata akwai wani makirci akasan wannan kayan da dokin zanje inga wani irin makircine sannan insan abinyi."
Muryar Galadima ne ya katseshi da cewa " kayi shiru."
Cikin Abdulmajid da Waziri ne ya d'ebi ruwa, tsoro da fargaba ya kamasu, duk suka runtse ido saboda tsoron abinda zai ce.
Abu Turab ya d'ago yace " ina wannan wanda baya ganin zai sani? Tuba nake ranka ya dade sai dai nikaina bansani ba andai aiko ne ance ga kayan dazansa."
Mai Martaba ransa a b'ace yace "dolene abinciko wanda yai wannan laifi dan kuwa bazan laminci irin haka ba."
Abdulmajid ya kurama Abu Turab ido lalai ba shakka yaran nan da saninsa.
Suna fitowa ya bi Abu Turab zaimai magana, ya tsaya kusa dashi yace " kai!"
Abu Turab ya kalli gefensa sannan yad'an matso kadan yace " karka damu nikaina bansan waye ya kawo kayan ba."
Yana fadar haka ya juya suka tafi.
Mamaki ya kama Abdulmajid ya bishi da kallo, kallan na kusa dashi yai yace " na fadamai dalilin kiran danamai?"
A'a sunansa kawai ka kira.
Abdulmajid yai dan murmushi yace " wasa farin girki."
*#ABU TURAB🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
_Kuyi hakuri jina shiru da kukai jiya da shekaran kiya, hakan ya faru ne saboda wani dalili nawa, 👏🏼 nagode kwarai_
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*22*
Abdulmajid da sauri ya karasa bangaren Magajiya, ko salama baiyi ba ya fad'a, tana zaune tana duba wasu kaya da tasa aka kawo mata, kayan mata ne aka d'inko kala kala.
Jin shigowar mutum yasa ta d'ago dan ganin wanene.
Abdulmajid ne ya karaso inda take ya zauna ransa a b'ace.
Kallansa tai yace " Yarona lafiya ko sallama babu."
Ya kalleta yace " Umma da alama mun sakema yaran can dayawa."
Ta kalleshi tace "bangane ba? Ni na dauka zakazo cikin murna kamin bayanin abinda ya faru da yaran can, shiyasa naki yardama kowa ya sanar dani nafisan inji daga bakinka."
Abdulmajid yai dan ajiyar xuciya yace " Ai baisa kayan ba, da alama mun sakema yaran nan dan yana makaho shiyasa har yake ganin zai iya takara damu."
Magajiya tamai kallan bata gane ba, nan ya kwashe komai ya gaya mata, wani sansanyan murmushi ne yaga ta saki ta kalleshi cikin murmushin tace " shine kake wannan fushin?"
Kallanta yai cikin mamaki, ta sake wani murmusawa tace " yaro man kaza, karka badani mana Yarimana."
Kallanta yai baice komai ba, tace " yaushe ma aka auri uwarsa, yaushe shima aka haifeshi, yaushe aka daina mai tsarki da wanka? Yaushe ya san kansa?"
Ta sake wani murmusawa tace " ko kamanta haryanzu baisan kalar fuskarsa ba bare yasan na uwarsa bare kuma tamu?"
Abdulmajid ya fahimceta, dariya yai sannan yace "a maida anin kan uwarsa?"
Magajiya tace " in har Mai Martaba ya nemi jin ba'asi to ka tabbatar komai ya koma kan Uwarsa."
Dariya ya saki yace "Allah yabarmin ke Umma Magajiya."
Murmushi tai tace " yaune isowar Khadija fa."
Ya kalli kayan yace " au shiyasa naga kaya kala kala a gabanki? Ashe 'yar d'akinki ce zata dawo."
Cikin jin dadi tace " daurewa kawai nake na rashinta, amma kaga yanzu tunda Inna Lami take akwance sannan ga shi ina tunanin turawa takarda had'in aure zuwa masarautar Kano shiyasa nakesan ta dawo."
Kallanta yai yace " auren wa?"
Tace "auranka mana dolene in nemi masarauta mai karfi in had'a auranka saboda nan gaba ko menene ba wanda ya isa tunanin saukeka daga matsayinka ko kwace ma mulkin ka."
Kallanta yai yanasan magana amma ina bazai iya ba, dan bai taba mata musu ba, kayanta tacigaba da dubawa.
Jiki a sanyaye ya mike yai waje, shikam bai shirya wani aure yanzu ba amma bai isa cewa komai ba, a tsarinsa yafisan yai auren farinsa auren soyayya tunda dai yasan dama shi dolene yai mata dayawa, yana tunanin ina shi ina soyayya da wani bayan an riga an mai aure?
******
Washegari.
Yana fitowa daga d'an nesa ya hangota tana tafiya, tsaki yaja yace " sai na takama yarinyarnan birki."
Kallan na bayan sa yai yace " kiramin yarjnyarcan, ina bangarena."
Ya juya zuwa bangarensa.
Yana shiga yaga an kawo mai abinci ga bayin da suka kawo nan a tsatsaye suna jiran isowarsa.
Zama yai baice musu komai ba, umarni ne ya basu dolene in suka kawo mai abinci sai yaci yaji yamai kafin su tafi.
Da sallama ta shigo fuskarnan tata a d'aure tamau, shima fuskarsa ya had'e bai amsa mata ba ya d'ago ya kalleta.
Kanta na gefe, jitai yace " duk ku fita kubarni da yarinyarnan inasan magana da ita."
Nan sukai waje, itakam haryanzu kanta na gefe.
Kallanta yai yace " ke baki iya gaisuwa ba?"
Bata tanka mai ba.
Ya kalleta yace " zo ki zubamin abinci, tunda naga alama uwarki bata isa dake ba, kullum kina hanyar gantali."
Wani mugun kallo ta bugamai sannan tace " ko karuwanci nakeyi meye naka a ciki?"
Hannu taga ya had'a ya fara tafi sannan ya mike ya tako zuwa kusa da ita, idanunta ta kawar tace " malam lafiya?"
Ganin yanda ya matso daf da ita yasa ta fara matsawa, haka ya dinga matsowa har takai jikin bango.
Hannu yasa a jikin bangon ya tareta yace " abinda kukeyi kenan da makahon?"
Kallansa tai ta had'iyi yawu sannan ta daure tace " yaushe raban ma daka ganni a gidan? Wai ni mena tsolema ne?"
Dariya yai yace " na tsani duk wanda yake san makahon can, balle ke harda dadin rashin kunya."
Sauri tai ta sulale ta kasa ta juya da sauri zata fita, hannunta ya fizgo da karfi, ya dawo da ita gabansa yace " me? Bakyasan kwalliyar da kikai ta goge ne ba tare da kinje gunsa ba?"
D'agowa tai takalleshi cikin takaici.
Ya saki murmusawa yace " ahh ya zakiyi? Gashi kuma baya gani bare ya yaba."
Hannunta tashiga kwacewa, ganin yaki saketa yasa tace " wlh zansama ihu, kasani sarai kuma zan iya."
Kafad'a ya d'aga mata alamar ko a jikinsa yace " Go ahead."
Lab'anta tad'an ciza sannan ta kalleshi ta kara hade rai tace " malam sakeni ko?"
Kallanta yai ba alamar yana da niyyar hakan.
Ta kara cewa Malam sakeni ko?"
Yace "Mairo kenan, inhar kinasan in kyaleki dolene ki daina zuwa gun waccan yaran ki dinga zuwa guna duk da nidin bawai sanki nake ba ko burgeni kike ba sai dai inasan yanayin fuskarki da shape na jikinki."
Iska ya hura kad'an a bakinta tace " hakan kadai kakeso."
Gira ya d'aga mata alamar eh, yamai murmushi sannan tace " sakeni to, indai wannan ne kacal.
Nan ya saketa yana kallanta, tace " nagode sai anjima."
Zai sake magana yaga tayi waje.
Hakoransa yad'an had'e yace " na tsani yarinyar nan, bawanda ya rainani kamarta."
********
Mairo kam tana fita ta gyara mayafinta tafiya kawai take amma gabanta sai fad'uwa yakeyi, haka ta isa b'angaren Basira.
Bayan sun gaisa ne, Basira ta kalleta tace "Mairo yanzu sam kin daina zuwa, yauma sai dana aika kizo sannan kika zo."
Kanta na kasa batace komai ba, kai kadauka irin salahan nan ce.
Basira tace " dama so nake ku fita da Abu Turab gari, na tabbata yau yana bukatar iskar cikin gari bawai ta gidan nan ba."
D'agowa tai tanasan tambayarta abinda ya faru, sai dai bazata iyaba.
Tace " To."
Basira ta kalleta cikin kauna tace " bari a kirashi."
Ta kara cewa to.
Abu Turab yana d'aki a zaune yana karatun alqur'ani, nan aka sanar dashi sakon Basira.
Mikewa yai ya bud'e drawer din da kayansa ke ciki dan canzawa.
Kurama d'ankwalim dake ajiye a gaban kayan ido yai, baice komai ba sai dai ya dade a tsaye yana kallan d'ankwalin.
Kafin ya jawo wani kaya,har ya rufe kofar ya bud'e ya janyo d'ankwalin yardashi yai a kasa sannan ya sura kayansa, ya kara kallan kasa sannan yai waje.
Ya rasa dalilin dayasa yakejin zuciyarsa ba dadi bayan ya yarda dankwalin, sai dai menene dalilinsa na ajiye kayan yarinyar da tunda ta tafi ko sakon gaisuwa bai kara samu ba? Wata zuciyar tacemai wa zata aika? Bayan duk ba sanka suke ba? Shikam ya rasa me yasa yakejin zafinta bayan ya tabbatar ba laifinta bane.
Haryakai kofa ya koma d'aki ya d'au d'ankwallin ya maida cikin drawer din sannan yai waje.
Yana shiga yaga Mairo a zaune, karasa wa yai ya kara gaida mahaifiyarsa.
Mairo ta gaisheshi ya amsa.
Basira tace " tunani nake ko zaka fita gari yawo."
Kallan gefenta yai yace " gari kuma?"
Tace " eh, kullum kana gida a zaune shiyasa nai tunani ko zaka zaga gari dukda ba gani zakai ba amma ina ganin zakaji dadin hakan."
Kai ya jinjina alamar gamsuwa yace " bari na sanar ma....."
Da sauri tace " ku fita kai da Garzali da Mairo kawai."
Kallanta yai yasan me take nufi, dan dama ya dade da sanin so take wata alaka ta shiga tsakaninsu da Mairo.
To.
Abinda yace kenan ya mike.
Mairo itama ta mike ta musu sallama.
Garzali na bayansa ita kuma tana d'an kusa dashi kadan, shikuma yana tafe rike da sanda.
Sun shiga gari ta gefen ido yana ta kallan yanda mutane suke haba haba, ba shakka wannan shine burinsa ya zauna cikin mutane kamar yanda kowa yakr yi bawai gidan sarauta ba.
Jitai yace " Mairo yanzu anbar rigima dai da alama."
Kallansa tai tace " lalai Yaya sai kace wata yarinya?"
Yace " ah lalai ashefa kin girma."
Baki tad'an turo tace " shekarata fa 1."
Yace "16? Amma bakiyi aure ba?"
Fuska ta d'an had'e tace " ba mijin ne."
Ya d'an juyo kadan yace " wanda rannan ya biyoki fa?"
Tsaki tadan yi tace "rashin aikinyi ne yamai yawa."
Yace " da alama dai akwai wanda kikeso ne shiyasa."
Kallansa tai a ranta tace "sosai ma."
Ta d'auka a zuciyarta ta fada sai jitai yace " da gaske?"
Kallansa tai tace " wasa nake."
Murmushi yadanyi yace " kar ki tsaya ruwan ido ki samu saurayin da yake sanki ki aura, bawai wanda ke kike so ba."
Kallansa tai zuciyarta ba dadi tace " kamar yanda haryanzu baka manta da Khadija ba?"
Tsayawa yai cak, ba tare da ya juyo ba, matsowa tai inda yake tace " karka damu Ya Turab ba wanda yasan hakan, ko ince ba wanda zan fadawa."
Bai san sanda ya kalleta ba, yace " me kike nufi? Ko kin tabaji da bakina na fada miki haka?"
Murmushi tamai tace " wani sa'in sai inga kamar kana kallona."
Fuska ya had'e ya juya kai yace " amsarki nake jira."
Daurewa tai tace" a lokacin da Khadija ta tafi bafa yarinya bace ni yaya, ban manta abinda ya faru a lokacin ba, sannan duk sanda muka zauna dakai zancenka kenan khadija tace kaza, ko khadija tayi kaza, a lokacin bansan me hakan yake nufi ba, sai dai daga baya na fahimci meke faruwa."
Abu Turab ya juya yace " banasan wannan maganar, sannan ni khadija banaji ko ganinta ma in nai zan iya ganeta."
Yana kaiwa nan ya cigaba da tafiya."
**********
Tunda suka taho a hanya take kwance kamar mai bacci sai dai zuciyarta fal take da tunani kala kala, Ya Turab!
Abinda zuciyarta take fada kawai kenan, anya zata iya ganeshi? Dan ita kamanninsa ma harsun fara bace mata.
Ba shakka tasha wuya sosai bayan komawarta kano, sai datai sati biyu tana zazzabi zancen ta kenan a maida ta gun Ya Turab kai kace shine ya haifeta.
Yaran gidan har tsokanarta sukeyi suke cemata Aunty Turab.
Duk sanda zatai addu'a kafin ta fara rokon komai sai tamai addu'a, ita har mamaki ma take da haryau bata taba mantawa da addu'ar ba in har tai sallah.
Ko zai ganeta? Dan wani zuwa da Abdulmajid yai shekarar data wuce data tambayeshi Abu Turab cemata yai wai soyayya suke da Mairo, sannan gwara ma ta cire wani lamarinsa, dan shi kam ya ma manta da ita.
A da bata taba tunanin wai san shi take ba, itadai a matsayin yaya ta d'aukeshi sai dai ganin ta kasa cireshi a ranta yasa Aunty Nana wato babbar yarinyar gidan ta fada mata soyayyace bawai 'yan uwantaka ba."
Kanta ta kara kwantarwa jikin motar, ya zatayi in har yama kasa ganeta?
Dama gashi iyayenta nema suke su had'ata da wani yaron babban d'an siyasa a garin kano yake.
Ajiyar zuciya tai sannan ta kara lumshe idanta.
*ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*23*
A hanyarsu ta dawowa ne wani ya biyo Mairo da gudu, yana kwalla mata kira.
Abu Turab yanaji ganin taki tsayawa bare amsawa yasa shima bai tanka mata ba, sai dayazo daf dasu yanata haki na gudu yace "Mairo kina jina?"
Kallansa tai tace " nibanji ka ba, lafiya?"
Ta fad'a tana kallan Abu Turab daya cigaba da tafiyarsa.
Leda ya miko mata yace " gashi."
Cikin fada tace " nameye shi kuma?"
Kai ya sosa yana shirin yi mata magana, yana d'agowa yaga bata gun, kallanta yai yanda take dan sauri.
Da sauri itakam ta karasa gun Abu Turab tace " Yaya ba jira?"
Yace " har kin gama zancen?"
Tace "zance kuma?"
"ki koma dan muma gida zamu wuce, sai da safe."
Abinda ya fada kenan ya cigaba da tafiyarsa.
Turus tai agun idanunta suka d'an ciciko, meyasa Abu Turab baya ganin yanda ta damu dashi?
Shikam ko a jikinsa har suka isa gidan.
Yana shiga daga bakin gate yaji ankira sunansa.
Yasan muryar waye, fuskarsa yad'an saki kadan ya juyo saitin inda yaji kiran.
Sabi'u d'an gidan galadima ne ya karaso gunsa, cikin farin ciki yace "Ranka ya dade daga ina haka?"
Abu Turab ya d'an murmusa kadan yace " naje ganin gari."
Sabi'u ya kalli Garzali yace "dafatan ba abinda ya faru?"
Garzali zaiyi magana Abu Turab yai saurin cewa " ba abinda ya faru, sannan inhar ka damu da ni nan gaba inzan fita kazo ka d'aukeni."
Dariya Sabi'u yasa yace " Angama Ranka ya dade, nima daga gun Mai Martaba nake akan maganar binciken abinda ya faru yau."
Fuska Abu Turab ya had'e yace "kai akaba aikin binciken?"
Fuskarsa d'auke da mamakin ganin yanda Abu Turab yai yace " eh, da wani abun ne?"
Abu Turab ya girgiza kai alamar a'a sannan yace " ka koma gida ka kwanta kace bakada lafiya, inyaso zuwa gobe sai ka turo fada a sanar da rashin lafiyarka."
Sabi'u yace " saboda me? Ni ai ina ganin nine na dace da binciken saboda sanar ma Mai Martaba gaskiya abin."
Abu Turab yace " shine dalilin dayasa ai banasan ka amshi wannan aikin."
Kallan Mamaki Sabi'u yamai, Abu Turab ya sa hannu alamar yana nemansa, da sauri Sabi'u ya rike hannunsa yace "ganinan"
Hannunsa ya rike yace " Sabi'u ka manta wacece Magajiya ne? Ina tsoron karkaje daga bincike ta juyo da rashe kanka, dan na tabbata bazata taba bari a gane itace ba, saboda haka ka barni da ita ni zansan wanda ya kamata yai binciken."
Sabi'u ya fahimceshi kwarai hakan yasa bai musa ba yace " shikenan zanyi yadda kace."
Nagode.
Abinda Abu Turab ya fad'a kenan.
********
Tare suka shiga cikin gidan suna tafe suna 'yar hirarsu.
Yazo yin kwana inda zai shiga b'angarensa, wata budurwa ya hango a tsaye a jikin katangarsa, kanta na kasa da alama ba shiga zatai ba kuma da alama basan barin gun takeba.
Harya dauke idanunsa ya kuma maidasu kanta, baiga fuskarta ba sai dai kallo d'aya zaka mata kasan 'yar wani ce.
Sabi'u ne shima idanunsa suka kai kanta, daidainan ita ma ta d'ago, suka had'a ido.
Da sauri ta juya ta shige ta baya.
Sabi'u yai murmushi yace " yau kuma wa na samu?"
"kai da wa?"
Kansa yad'an shafa yace " wata ce da alama biyoni tai sai sai kunya ta hanata tsayuwa."
Kai ya girgiza yace " kana fama."
Tana tsaye ta lungun ta zuro kanta kad'an, idanunta ne suka ciciko da kwalla a hankali wani zazzafan hawaye ya taho mata, kallansa kawai takeyi tana mamakin yanda zuciyarta ta kasa mantawa dashi, har yanzu baya gani? Abinda zuciyarta ta fada kenan.
Hawaye ne suka cigaba da zubowa sosai sai dai sam ta kasa tsayar dasu.
Har suka shiga tanannan a gun ta dade sosai kafin ta juyo ta fara tafiya.
B'angaren Magajiya ta shiga.
Da sallama ta shiga.
Magajiya ta mike cikin tsananin farinciki ta rungume ta.
"lale lale da zuwan Khadija ga, Uwata barka da zuwa."
Mamaki sosai bayinta suka shiga yi, hatta Abdulmajid yayi mamakin ganin Uwarsa ta mike tsaye saboda taro wani ba sarki ba.
Khadija cikin farinciki tace " Nasameku lafiya Umma?"
Magajiya ta saketa ta jawota suka zauna, kallan bayinta tai tace " ku kawo mata abinci."
Tsugunawa tai tagaida Magajiya sannan ta kalli Abudulmajid ta gaisheshi.
Kallan ta yai shima cikin farinciki ya amsa sannan ya d'ora da cewa "inakika tsaya bayan tun dazu aka aiko akan kin shigo?"
Kanta ta sunkuyar batace komak ba, Abdulmajid ya hade rai cikin kuluwa yace "badai Gun......"
D'agowa tai fuska a had'e itama tace " bangane ba?"
Zaiyi magana Magajiya ta katseshi da cewa " Yarima banasan haka, akan me zaka takurawa Uwata daga zuwanta? Na tabbata nan ta fara zuwa."
Khadija ta d'auke idanta daga kanshi, shikam ido ya kura mata yana zargin anya kuwa ba gun waccan yaran taje ba?
Abinci kala kala aka shiga jerawa, Magajiya tasata a gaba tana ci suna hira, bayan ta gama ta sa aka d'auko mata jakar kayan datasa akadinka mata, Khadija cikin jin dadi tace " nagode sosai Umma."
Magajiya ta kalleta tace " yaushe zakije duba Inna Lamin?"
Khadija tace " zuwa gobe, amma ya jikin nata?"
Abdulmajid yai dan kasa da kai yace " jiki fa ba sauki tana nan dan ko fitsari a kwance take, 'ya'yanta duk sun kama gabansu ba mai kula da ita, hmmita kam wannan gwara ma ta mutu ta huta."
Magajiya ta d'an tabe baki, khadija ta kalleshi tace " ko ma menene Yaya bai kamata ka fadi haka ba, addu'a kawai zaka mata, amma nikam Umma bakya ganin Baba ne yakamata ya d'aukota ta zauna a gunsa, ta yaya za'abar ta ita kadai a gida?"
Magajiya ta kalleta tare da canza fuska tace " kin fadama Hisham din haka?"
Tace " yanzu abin ya fad'omin."
" Tun kafin ya hauki da fada karma kimai wannan zancen, ke dai kije ki dubata gobe."
Khadija zata sake magana Magajiya tace " Khadija bansanki da musu ba."
Shiru tai batace komai ba, sai dai tana ganin hakan bai dace ba, yaza'ayi ace 'yan uwanta da 'ya'yanta duk sun watsar da ita?"
*******
Bayan anyi sallar isha'i ne Jakadiya tazo ta sanarmai da sakon Mai Martaba akan yana san ganinsa.
Shida Garzali suka fito, bayan ya shiga ya zauna ne Mai Martaba ya kalleshi yace " Nayi dogon naxari akan abinda ya faru sannan na sanar ma Sabi'u akan yai bincike akan abinda ya faru, tunda naga shine na hannun damanka."
Abu Turab kansa na kasa yace " Abba!"
Kallansa Mai Martaba yai ba tare da ya amsa ba, dan raban dayaji ya kirashi da Abba tunda ya mallaki hankalin kansa.
Abu Turab ya cigaba " wani hukunci zaka d'auka akan wanda ya aikata hakan?"
Sarki yace " dole ne ya fuskanci hukunci mai karfi."
Murmushi ya saki sannan yace " ko da kuwa Magajiya ce?"
Kallansa yai yace " me kake nufi?"
Abu Turab yace " a matsayin d'a nazo gunka inaso d'a da mahaifinsa suyi magana bawai sarki da d'ansa ba."
Sarki ya kalleshi yace " shine nace mai kake nufi?"
Abu Turab ya d'anyi shiru kafin yace " zaka iya hukunta Matar da take da mukami fiye da kowa?matarda yayanta yake waziri?matar da d'anta yake magajinka?matar da duk yawancin masu mukamin nan suke a kasanta?"
Sarki ya kalleshi ranshi a b'ace yace " Turab!"
Abu Turab ya d'an sunkuyar da kai yace " tuba nake ranka ya dade bawai da wanj abin na fadi hakan ba sannan ba wai nace itad'in ce tai ba sai dai ina tunanin mu binne maganarnan inhar hukunta mai laifin zai iya zama wani abu."
Sosai ran Mai Martaba ya b'aci mai Abu Turab yake nufi?
" bance itace tai ba sannan ban san wanda ya aikata hakan ba, ina tsoron kar ka kasa yanke hukunci ne in laifi ya fada hannun manya."
Sarki ya kalleshi jiki a sanyaye yace " kaima kanasan kacemin baka yarda dani ba? Kaima kana ganin nid'in ragon sarki ne wanda bazai kya hukunta Matarsa ba?"
Kai Abu turab ya girgiza jikinsa shima yai sanyi yace " bawai hakan nake nufi ba sai dai banasan na zama sanadiyar saka cikin tsaka mai wuya."
Murmushin takaici yai yace " na sani ban kula da ku ba kaida mahaifiyarka lokacin kana yaro sannan na sani laifinane da bana shiga duk wani harka data shafeku sai dai na sani bazaka taba gane dalili na nayin hakan ba."
"so kake ka karemu, bakasan a gane damuwarka a kanmu bare a mana illa." jin wannan zance daga bakin Abu Turab yasa ya kuramai ido.
D'agowa Abu Turab yai ya kalleshi, jiyai zuciyarsa ba dadi, ko dai ya dau abin da zafi ne?"
Ga mamakinsa gani yai Sarki ya saki wani sansanyan murmushi sannan yace " Alhamdulila d'ana ya girma."
Baisan sanda ya kalleshi ba cikin mamaki.
Sarki yamai alama da hannu akan ya matso.
Da sauri yad'auke idanunsa, Mai Martaba ya kara mai alama da hannu sannan yace " na sank kana gani Turab."
Idanu Abu Turab ya zaro Sarki ya mike da kansa yazo inda yake, kansa ya d'ago saitin sa yace " na sani da dadewa, na janye idona ne daga nuna maka saboda banasan ruguza abinda mahaifiyarka ta shirya ya ruguje."
Idanunsa ne suka ciciko, kai ya girgiza mai yace " ka manta mai kace? A matsayin Uba kakeso muyi magana? Yau a matsayin uba nake, daga kabar nan zan koma sarki in kuma manta da abinda ya faru tsakanin mu."
Idanu ya runtse yama kasa magana sam, Sarki yad'an had'e fuska kadan yace " ina Abu Turab dina wanda baya shakka ta? Jarumin da nake farincikin samun d'a kamar sa?"
Baisan sanda yad'an murmusa ba.
Sarki ya kalleshi yace " me ka shirga game da abinda Magajiya ta maka?"
Abu Turab ya kalleshi yace " bazan iya fadama Sarki ba, sai dai ina neman alfarma akan kaba Abdulmajid umarnin yin binciken abinda ya faru."
Bai kara tambayarsa va yace " shikenan, sai me kuma?"
Yace "inaso ka taimaka ka cigaba da nuna rashin damuwa dani da kuma hukuntani sosai in nai ba daidai ba."
Yace "shikenan, sai kuma me?"
Kai ya girgiza yace " su kenan."
Murmushi sukama junansu.
Abu Turab ya mike zai tafi, jiyai mahaifinsa yace " yanzu mun zama d'aya kenan ko?"
Ba tare da ya juyo ba yace " dama can d'aya muke."
Yana kaiwa nan ya bud'e kofa.
Yana fita ya had'e fuska sannan ya tsaya a waje kamar irin an mai fadan nan sosai, ya dade a tsaye kafin jiki a sanyaye ya fara tafiya, tuntube yai saura kiris ya fadi da sauri Garzali ya taimaka mai sukai gaba.
Jakadiya ta tabe baki sannan tace " da alama ansha fada, ai naso a nan akai ba a kuryar d'aki ba."
Nace hmmmm
*ABU TURAB TEAM 🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*24*
Abu Turab yana shiga d'akinsa ya rufe tare da jingina a jikin kofar, tausayin Mahaifinsa ne yake ratsa jikinsa ace kana san abu amma saboda kana mulki baka isa ka nuna ba? Lalai shikam wannan mulkin sam baya kansa.
Haka ya kwanta bacci zuciyarsa fal da tunani kala kala.
********
Washegari a fada Mai Martaba ya umarci Abdulmajid akan ya d'aurashi akan aikin binciken abinda ya samu kaninsa.
Ba Abdulmajid ba kowa na fadar sai da yai mamakin wannan al'amari, ai ko ba'a fada ba kowa yasan ba wata soyayya ko mutunci a tsakaninsu, amma ace shine zaiyi binciken?
Andulmajid ya kalli Mai Martaba cikin tsananin mamaki, kafin ya daure yace " insha Allah zanyi binciken abin in sanar maka."
Yana fitowa Hisham ya biyoshi, Hisham ya kalleshi yace " me ke faruwa?"
Abdulmajid ya dan kurama kasa ido sannan yace " abinda ke faruwa?" Umm yad'anyi ajiyar zuciya yace " wannan shine tambayar da zan fara nemanma amsa."
Hisham yace " muje gun Magajiya nikaina inasan ganinta."
Bayan sun isa gunta ne sun gaisheta, Abdulmajid ya sanar da ita abinda ke faruwa, murmushi ne mai sanyi ya bayyana a fuskarta ta kalli d'an nata tace " hmm lalai Turab ya girma sai dai Tsohon doki yafi sabon takalmi."
Abdulmajid ya mata kallan rashin fahimta, "Tsi tsi tsi tsi" abinda tai da bakinta kenan tana jijiga kai tace " karka badani mana Abdulmajid, ba shakka Turab abinda ya nema mahaifinsa yamai kenan jiya.
Hisham yace " nima naji labarin zuwansa sai dai naji ance fada aka mai?"
Baki ta tabe tace " ko da wasa ni nasan ba fada aka mai ba in har fada ne mezaisa ya shiga kuryar d'aki? Sannan da yamma ya riga ya umarci Sabi'u akan yai bincike sannan yau da safe ya maidashi kan Turab ne hakan yake nufi?"
Hisham ya kalleta yace "amma hauka yake da zai umarci Abdulmajid? Bayan yasan ba sanshi yake ba."
Abdulmajid ya kalli Magajiya yace " Umma kina nufin yayi hakan ne saboda karmu d'aurama mahaifiyarsa laifi? Tunda yasan ai ni ban isa ince mahaifiyarsa bace hakan zaisa a zargeni."
Magajiya ta mai alamar jinjina da hannu tace " kwarai kuwa Yarima na ashe ka harbo jirgin."
Dariya Abdulmajid yai yace " lalai yaran nan, yana makaho har......"
Katseshi tai tace " munyi sakaci da muka ragamai muna tunanin makaho ai baya ganin komai, masarauta fa muke?sannan jinin mahaifinsa da kakansa suna yawo fa ajikinsa."
Hisham ya kalleta yace " yanzu meye abinyi?"
"Hmm farko dai tunda ya maida wasan kanmu dole ne mu buga wasan, ai hakorin dariya shi yakanyi cizo."
Kallan mamaki suka mata, tai kalli Abdulmajid tace " ka nutsu sosai kaga yanda zan buga wasan."
Shiru yad'an biyo baya kafin Hisham yace " ni kuma wani abu d'aya ne yake damuna, me yasa haryanzu sarki ya kasa neman ma Abu Turab magani?tunfarkon zuwan sa da yadanyi na shekaru kad'an yanzu sam baya turo masu magani, ko ya hakura ne da makantar yaron....."
Magajiya ta d'an kankance ido tace "ko kuma ya warke ba."
Idanu suka zaro suka kalleta, shiru tai tana tunani kafin ta mike da sauri tace " me yasa hakan baizo min ba?"
Da sauri ta kalli Hisham tace " Hisham aika a kiramin yaron nan."
Abdulmajid shima ya mike hankalinsa a tashe yace "Ya zamuyi in har yana gani? Kenan za'a iya bashi mulkina!"
Magajiya ta bugamai wani kallo tace " so kake ka zama rago akan wani makahon daya warke?"
Hisham ne yai waje da sauri ya tura baiwar Magajiya akan ta aika a kira Abu Turab.
Shiru tai tana tunani kafin tace " aika a dafomin ruwa mai zafi sannan a zubo a roba, a kuma zubo ruwa mai sanyi shima a roba."
Shiru tai tana tunani kafin ta fita da kanta, ba shakka hankalinta ya tashi, ya zatai in har yana gani? Kenan tunda raina musu hankali yakeyi kenan.
********
Zaune yake yanashan ruwan zafi wanda yasa aka dafa mai da kayan kamshi, zafin cittar yasa yake d'an lumshe idanunsa, shigowar Garzali ce tasa ya bud'e idanunsa.
Zubewa yai a kasa ya sanar dashi sakon nemansa da Magajiya takeyi yanzu.
Bai amsa ba ya cigaba da shan shayinsa.
Sai daya gama sannan ya mike ya shirya ya fito, Garzali ya taso da sauri yazo kusa dashi.
Tafe suke yana rike da sandarsa, idanunsa ne suka kai gun jiya inda yarinyarnan ta b'uya, ya rasa me yasa yakeji kamar ana kallansa.
Yana kallan gun kuwa suka had'a ido.
Da sauri ta b'oye tare da dafa kirjinta dayake bugawa da sauri, a tsorace tace " ya ganni?"
Kai ta girgiza tace " ta ina zai ganni?"
Shikansa jikinsa ne yai sanyi yana tunanin abinda ya gani, kawar da abin yai a ransa har suka karasa b'angaren Magajiya.
Tana zaune a kilisarta, Abdulmajid na gefenta, Hisham ma na d'aya gefen nata ya shigo.
Sai daya zauna sannan Garzali ya fita.
Gaisheta Abu Turab yai ta amsa tana karema idanunsa kallo kansa na kasa, kallan zargi takema a haka tace " Me ya faru ne sam ka daina zuwa gaisheni."
Murmushi ya d'anyi yace " Da alama Umma Babba san ganina ne yasa kika manta nazo kwanan nan."
Kallansa tai tace "haba? Amma ya akai nakeji kamar na dade banga d'ana ba?"
Yace " zan dinga zuwa akai akai in har kinasan ganina."
Tai dan murmushi sannan tace " bari a kawo ma abinci kaci, yau takanas nasa a ma d'ana abinci, dan na kula bana baka kulawa yanda ya dace."
Ya jita sai dai bai tanka mata ba, nan tasa aka jera mai a binci tace " bismillah."
Hannu ya saka yana shashafa kwanukan alamar baya gani, kwarai yaga ruwan zafin dake daf dashi, tunani ya fara yi me ya kawo ruwa wanda yake turiri kusa dashi? Kana kallan ruwan kasan yanzu aka juyeshi, ba shakka zargin ganinsa takeyi, bazai taba ba mahaifiyarsa kunya ba dan kawai ya faranta ransa ba, hannunsa yakai kan ruwan zafi da saninsa ya sa hannunsa zuciya d'aya.
Azabar dayaji ne yasa ya zare hannun da sauri ya rike hannun cikin jin zafin zugi da radadin da yakemai.
Kallan juna sukayi suka saki murmushi ba shakka baya gani.
Da gudu ta karaso ciki tashin hankali, hannunsa ta kama da sauri ta saka cikin ruwan sanyi.
Kuka kawai takeyi hankalinta yayi tsananin tashi.
Magajiya ta mike itama tace " lafiya Abu Turab?"
Ta fada tare da nunama Abdulmajid ya d'auke ruwan zafin.
Nan ya d'auke ruwan.
Kallansa tai tace " garin yaya? Ina lilahi wa ina ilaihi raji'un, me ya faru? Badai ruwan wanke hannu danace su kawomin bane suka kawo na zafi, inaji sun d'auka kafata zan gasa wacce ma bige jiya."
Ba wanda ya kulata tsakanin Abu Turab da Khadija.
Shikam yama kasa komai zafin hannunsa da kuma ganin Khadija sun sa sam yama kasa cewa komai.
Kuka take sosai ta mike da gudu ta fita, dawowa tai d'auke da zuma a kofi ta shafamai, Magajiya duk ta rikice.
Abu Turab ya daure ya kwace hannunsa sannan ya mike yace " bakomai Umma Babba ba laifinki bane na sani, ke mai zaisa kisa a kawoma d'anki makaho ruwan zafi haka? In har dama ba neman halakashi kike ba, wanda nasan ke kuma ba hakan bane a gunki."
Ta bud'e baki zatai magana yai waje.
Ba shakka ta tabbata magana cikin magana ya fada mata.
Khadija ta kallesu dukansu cikin kunar rai sannan tai waje da gudu.
Binsa tai inda yake ta rike hannun daya kone ta sama tace " yaya muje a baka magani."
Fuska ya d'aure tamau sannan ya kalli Garzali yace " wacece wannan d'in take tabani?"
Garzali ya kalleta, zaiyi magana tai saurin cewa " Yaya Khadija ce, nice kasani ba cutar dakai zanyi ba."
Hannunsa ya fizge yace " ta ina kenan na san ba cutar dani zakiyi ba? Ko na sanki ne da harzan iya miki shaida?"
Sakeshi tai idanunta suka ciciko a hankali tadanyi baya kadan tana mai kallan tsananin mamaki.
Garzali wuce muje.
Tana tsaye anan har suka kule sam tama rasa abinda zatai tunani.
Jiki a sanyaye ta koma b'angaren Magajiya.
Taje shiga taji suna dariya, Hisham yace " da alama dai idannan bam yake baya ganin komai."
Dariya Abdulmajid yai yace " tab amma fa ya daure dan ruwan zafi ba wasa bane."
Bud'e kofar tai da karfi cikin tsananin mamaki ta kallesu.
Tace " da saninku?"
Dif sukai kowa ya kura mata ido.
Hawaye ne suka shiga zubo mata ta girgiza kai tace " kuna 'yan uwa, ko ba 'yan uwantaka ai akwai na musulunci, tayaya zaku samu mutum wanda Allah ya d'auke ganinsa ku samai ruwa ya kone? Nazo da niyyar muku magana akan barin Inna Lami a halin da take bayan na dawo daga gunta, sai in tarar da wanda yafi nata?"
Kuka ne yaci karfinta tace " anya akwai tausayin imani a zuciyoy......"
Wani wawan mari Hisham ya mata wanda batai zatan jinsa ba.
Kuncinta ta rike ta kalleshi, kasa magana tai, waje tai da gudu taba kuka.
*#ABU TURAB TEAM🤝🏼*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
_ina baku hakuri jina da kukai shiru, wayatace tad'an samu matsala nagode kwarai da kulawarku, naga sakwaninku na kuma gode, plz wanda yamin magana baiga namai reply ba yai hakuri whatsapp dina baiyi restoring old messages dina ba, nagode._
*25*
Turab yana shiga ya bud'e kofar d'akinsa yasa kai zai shiga kenan yaji muryar Garzali yace "Ranka ya dade ana nemanka."
Juyowa yai yace " wa?"
Garzali yai kasa dakai, Abu Turab ya kalleshi yace "Umma ce?"
"Tuba nake ranka ya dade."
Idanu Turab ya rufe, Garzali ya tsugunna da sauri yace " Tuba nakeyi."
Abu Turab ya juya har yakai kofa sannan ya tsaya yace " ka fada mata komai?"
Garzali yace " a'a bansan waye ya sanar da ita xuwan mu can ba, ina shigowa ta turo inxo, tambayata tai me ya faru a inda mukaje....."
Katsetshi yai yace " tambayar da maka itace ka fada mata komai?"
Garzali yace " nadai sanar da ita kunan dakai amma bansanar da ita wani abu ba daga wannan."
Takawa yai ya cigaba da tafiyarsa fuskarsa a d'aure.
Xama yai irin zaman daya sabayi a gaban ta, wato lankwashe kafa, kansa na kasa kallansa tai cikin kulawa tace " muga hannun."
D'agowa yai ya mata murmushi yace " Umma karfa ki damu ba wani abu bane nine bansani ba na taba ruwan zafi sannan a lokacin aka samun zuma a gun."
Ido ta kuramai cikin kulawa da tausayi tace " Turab ba sai ka dage ba wajen b'oyemin gaskiya ba dan hankalina ya kwanta, banaji ko yaro ne yaji xancen nan naka zai yarda."
Kallanta yai yace " Umma."
Yanda ya kirata yasa bata amsa ba sai kallesa datai.
Ajiyar zuciya yai yace " Umma ina neman alfarma a gunki."
Idanunta na kansa bata dauke ba haka kuma batace komai ba ya cigaba " abu d'aya nakeso kimin, dan Allah Umma ki rage damuwa dani."
Cikin tsananin mamaki ta kalleshi sai dai yanayin yanda yai maganar yasa ta kasa magana.
Idanunsa yadan rufe kadan sannan yace " gidan sarauta muke, sarautar ma inda makiyanmu sukai yawa, na tabbata a gidan nan kaf daga ciki har waje in har mukace muna neman wanda yake kaunarmu dari bisa dari banaji zamu samu mutane goma cikaku, in muka dauke bayin dake karkashin mu, yanayin yanda muke rayuwarmu ni dake dole ne sai mun sadaukar da rayuwarmu dolene mu sha wahala in har munasan zama cikin kwanciyar hankali, sa damuwata a ranki da kuma shiga wani hali in har abu ya sameni ina ganin babbar matsala ce, saboda dole wani sa'in zan nemi b'oye miki wani abun saboda gudun shiga wani yanayi da kikeyi."
Kallansa tai jikinta yayi mugun sanyi, tanasan sanar dashi abinda ya samu yayanta sai dai a yanda tasan Turab tana ganin in har yasan abinda ya faru dasu to fa lalai tana ganin xai cire wani farinciki a ransa ne ya juya rayuwarsa zuwa d'aukan fansa wanda ita kuma tana san farincikin danta dukda kuwa tasha alwashin hukunta wanda yama yayanta hakan.
Kallanta yai ganin yanayin datake ciki yasa ya runste idanunsa da karfi sannan ya mike yai hanyar fita.
Jiyai tace " shikenan Abu Turab."
Tsayawa yai sannan a hankali ya juyo ya kalleta, ta mai murmushin yake sannan tace " hankalinka ya kwanta?"
Kallanta yai cikin wani yanayi, sannan a hankali ya taka inda take zaune ya tsugunna gabanta yace "Umma do u trust me?"
Kallansa tai tace " me kenan?"
Dariya yad'anyi kadan yace " nufina kin yarda dani?"
Kai ta d'aga mai, ya dan murmusa yace " shikadai nake bukata, yardarki gareni, in har kin yarda dani inaso ki yarda xan kula dake bazan bari wani abu kuma ya samen ba sai dai abinda Allah ya kaddara."
Kai ta jinjina mai tace " nagode Abu Turab, sannan insha Allah ba abinda zai sameka."
Mikewa yai ya mata sallama zai fita.
Mairo wacce ta kawoma Basira gwaza wacce mahaifiyarta ta dafata ta fere ta sa ma kula, taxo shiga taji yana cema Basira do u trust me? Wanda hakan yasa ta koma ta tsaya.
Jin alamun fitowarsa yasa ta juya da sauri zatai waje garin sauri kafafunta suka harde, baya tai luu kamar zata fadi.
Cikin hanzari ya karaso ya tareta.
Idanunta ne suka sauka akan nasa, kallansa tai cikin tsananin mamaki, da sauri ya saketa dan sam ya manta ashefa batasan yana gani ba.
Jikake tim ta fadi a kasa, sosai taji xafin faduwar saboda sam bata zaci zai saketa ba, kallansa tai kamar tai kuka dan bakin ciki.
Hannu yasa yace " sannu faduwa kikai?kina ina?"
Haushi ya kamata ta mike ta matso inda yake tace " yaya fadamin gaskiya, da saninka ka sakeni ko?"
Gefen inda take ya kalla yace " me kike nufi?"
Sake baki tai cikin salon shagwaba tace " inba haka ba tayaya ka taimaken kuma zaka sakeni?"
Murmushi yai dan tabbas yaga faduwar datai yasan taji zafi yace " au so kike in rike ki?"
Kallansa tai tace " yaushe nace haka?"
Iska yadan furzar yace" lalai Mairo da alama aure kikeso."
Ya juya da sandarsa ya fara tafiya.
Takaici ma ya hanata magana, aure takeso? Me yake nufi da hakan?
Kallansa tai ta baya a hankali tace " na tabbata mun fa hada ido dashi."
Tana neman amsar tambayarta taji muryar.
Lantana taji tana cewa " Mairo? Me kike anan a tsaye?"
Juyowa tai ta kalleta idanunta sun dan ciciko, kusa da ita taxo ta ajiye kula tace " kiba Umma."
Ta juya da sauri tai waje.
Abu Turab kam b'angarensa ya nufa yana bud'e gate, bayinsa suka taho da sauri suka karasa bud'e mai kofa.
Ciki ya shiga, yana zama Garzali ya mikomai abu a bakar leda.
Yace "Ranka ya dade gashi an aiko a kawoma."
Yace "Magajiya?"
Garzali yace " a'a wlh bansan waye ba kawai kawowa akai, dana tambaya inji waye sai wacce ta kawo ta juya da gudu."
Ya gane Khadija ce, bai sa hannu ya amsa ba yace " ajiye anan kwanciya nake sanyi."
Ajiye wa yai ya mike a hankali yai waje.
Yana fita ya kalli ledar, shiru yai yana tuno fuskarta, fuskar daya dade yana san gani duk yanda yaso ya yage ta a ransa ya kasa, dan karamin tsaki yaja sannan ya sa hannayensa kan goshinsa.
Khadija kam bayan ta aikamai da magani gida ta tafi ta shige dakinsu ta fada gado ta kwanta, kuka kawai takeyi tana jin xafin abinda akama Turab.
Duk yanda mahaifiyarta tai akan ta bude kofar taki, ko abinci kinci tai.
*********
Yau kwanan Basira ne, ta shirya tsaf ta nufi bangaren Mai Martaba.
Bayan sun kwanta ne ya kalleta yace " Basira."
Kallansa tai ba tare da ta amsa ba, yacigaba " me kike tunani game da auren Turab?"
Kallan mamaki tamai tace "aure? Takawa ka manta Abdulmajid baiyi aure ba?"
Kallanta yai yace " na sani sarai sai dai inatunanin auran sa zai sa matsayinsa da kimarsa ta karu a gun mutane sannan inasan nemarmasa matar da zata taimakeshi yanda ko ansan yana gani ba wani wanda ya isa ya nemi cutar dashi."
Kallansa tai tace "ban gane ba?"
Yace " me kike tunani game da hadin aure da 'yar sarkin kano?"
Kallansa tai tace " Bilkisu?"
Kai ya daga mata alamar eh.
Kallansa tai jiki a sanyaye tace " amma kana ganin za'a bashi? Na farko shi makaho ne a idan duniya sannan Bilkisu ita kadaice mace a gun Sarki Muktar wato sarkin kano, ni nafi mai sha'awar mairo 'yar gidan Barde."
Kallanta yai yace " Na fahimceki sai dai ina so ki sani Abu Turab ba mijin mace d'aya bane sannan yana bukatar mace kamar Bilkisu saboda taimakamai wajen hawa mulki."
Da sauri ta mike zaune cikin tsananin tashin hankali tace " me? Mulki?"
Kallanta yai ya daga mata kai.
Idanu ta zaro cikin tsananin mamaki, yace " Bilkisu ita Magajiya takesan aurama Abdulmajid in har ya aureta ba makawa sai ya hau mulki, bakya tunanin abinda zai faru da rayuwar ku ke da Abu Turab kn har Abdulmajid ya hau mulki?"
Kallansa tai duk tama rasa ta cewa dan ta tsorata da zancen.
Ya kalleta yace " Abu Turab shi kadai ne wanda ko bayan raina na tabbata bazai wulakanta ahalina ba, bazai wulakanta mutanena ba, bazai rushe rayuwar dana gina a kasa ta ba."
Kai kawai tashiga girgizawa tana tsoron abinda zai faru da wannan sabon lamarin.......
*ABU TURAB TEAM*🤝🏻
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*26*
Kallansa tai cikin tashin hankali tace " mai kake nufi da kalamanka? Nasani ka fini iko da Abu Turab sai dai ina rokonka kabar maganar nan a kan gadon nan, ni zan manta munyi wannan maganar dakai."
Jitai yace " kin taba jin inda akai magana bayan wanda aka fadama maganar yaji sannan yace zai manta maganar? Ai magana ana manta tane in batada mahimmanci."
Kallansa tai tace " dan Allah kabar maganar nan, nafisan Turab ya auri Mairo ya bar gidan nan dan samun farincikin rayuwarsa."
"In kuma kaddararsa ce mulkin fa?" Jin maganar tai batai zata ba, Kallansa tai batace komai ba.
Shima bai tanka mata ba ya kwanta tare da juya bayansa.
Ta dade a zaune tana kallansa kafin ta kwanta.
Idanunsa a bud'e suke tunani yakeyi " bazai iya sanar da ita su Magajiya sune sanadiyyar makantar Abu Turab ba saboda bayasan ya sanya mata damuwa da kuma shiga wani yanayi najin wannan zancen.
Ba shakka shikanshi jin wannan zance ya daga mai hankali matuka, kamar wasa d'azu da rana Khadija yar gidan Hisham ta samu barde da sakon Lami akan dan Allah tanasan Mai Martaba ya ziyarceta dan akwai magana mai mahimmanci da takesan sanar dashi.
Ganin yanayin aikin dake gabansa yasa ya aika Barde akan yaje yaji menene.
Zuwan Barde ya taradda ita cikin mugun hali, tana kwance ko mikewa bata iyayi, ba kowa a gunta d'akin banda wari ma ba abinda yakeyi wai a hakan ma zuwan Khadija ne ta gyara mata d'azu.
Barde ya kalleta tare da dubata, ya d'ora da cewa "amma ya akai ke kad'ai anan?"
Tana kwance sai numfarfashi takeyi tace " Barde."
Kallanta yai cikin tausayawa yace " Mai Martaba wani uzuri ya rikeshi shine yace inzo inji menene, bai san jikin naki haka yakoma ba."
Hawayene suka gangaro mata tace " Barde ni tawa ta kare dan banaji ko gobe zan kai a duniya, dan Allah ka nemarmin yafiya agun Abu Turab, Basira da Mai Martaba."
Kallan mamaki ya mata yace " ban gane ba."
Hawayene suka kara kwaranyu mata tace " nice sanadiyyar makantar Abu Turab dan kuwa nice na je gun malami aka makantar dashi, kwanakin nan ko bacci na fara ganin yaro nakeyi ba ido yana tsaye a gabana, na tabbata laifin danai ne yake bibiyata, na sani alhakinsa ne ma ya kwantar dani haka, 'ya'yana da 'yan uwana da nake komai dan faran ta musu rai duk sun gujeni....."
Kuka ne yaci karfinta wanda yasa ta kasa karasawa, jikin Barde ne ya mutu mamaki da tsoron wannan al'amari yasa ya taho daga gidanta ba tare da ya gamajin kalamanta ba.
Idanu mai martaba yadan runtse a ransa yace " bazan taba yafe musu ba."
Babban bakin cikinsa shine a matsayinsa na sarki bashida hujjar hukuntasu, na farko bashida kwakwarar shaida sannan inma yana tunanin Lami zata zamarmai shaida ya tabbata Magajiya juya abin zatai kanta ko za'ai me bazata taba cewa itace sila ba.
Ba shakka sanya Abu Turab a mukamin Sarki ita kadai ce hanyar da zai sa ya hukuntasu ta ruwan sanyi wanda yafi na zafi kuna.
Dolene Abu Turab ya auri Bilkisu dan kuwa wannan shine mataki na farko na cinma burinsa.
Basira ma bacci ya gagareta ta rasa abinda ke mata dadi, itakam ba wata 'yar sarki datake so Mairo takeso ta bashi ko dan farincikin sa na nan gaba.
***********
Washegari da safe Abu Turab ya tafi garden din mahaifinsa wanda a yanzu shike zama agun dan kebencewa daga hayaniya, yana zuwa gun ne a duk lokacin da yake bukatar yin dogon nazari game da wani abu.
A zaune yake akan kujera ta karfe dake gun, shukoki kala kala ne a gun, wanda ya kayata gun, kansa ya kwantar a kan saman kujerar ya lumshe idanuwansa tare da dora hannunsa daya kone akan goshinsa.
Kana ganinsa kaga mai bacci, shigowa tai a hankali gun, tafiyarta takeyi mai sanyi tana tafe tana duba inda yake, cak ta tsaya a yayin data han goshi akan kujera, tunda ya fito ta biyoshi, sannan matsayinta yasa fadawan dake gadin kofar shiga gun basu hanata shiga ba.
Murmushi ne ya bayyana a fuskarta ganin yanda ya ke, ta dauka bacci yakeyi hakan yasa ta tako a hankali tazo inda yake.
Ta bayan kujerar ta tsaya ya zamana tana tsaye saman inda ya kwantar da kansa.
Hannunsa ta kalla gun yayi jaa har yanzu amma bai duri ruwa ba.
Kallansa takeyi tanajin wani sanyi na ratsa dukkan sansan jikinta.
Jin kamar mutum na kusa dashi yasa ya bud'e idanunsa a hankali.
A hankali ya kara maida idanunsa ya lumshe dan ya tabbata mafarki yakeyi, ba wanda ya taba biyoshi gun sannan in ma ana biyoshi mai zai kawo Khadija nan?
Idanunta ne suka ciciko a hankali tace " yanzu fa bazai ganni ba ko?"
Idanunsa ya kara budewa ya daurasu a kanta, itama kallansa tai.
Da sauri ya mike zaune ya dan maze yace "akwai mutum anan ne?"
Khadija batace komai ba, jin yayi shiru yasa a ranta tace " da alama bai san dani ba."
Dawowa tai ta gabansa ta tsugunna tare da tagumi kallansa kawai takeyi, ba shakka su Magajiya da Mahaifinta sun bata mata rai sosai wannan wace irin muguntace?
Abu Turab yana ganinta amma sai yai kamar bai ganta ba.
Sunfi minti talatin a haka kafin daga bisani ya mike rike da sandarsa.
Yace " na dauka nayi magana akan wanene anan ko? Ko dan bana gani an dauka bana jin motsi da numfashin mutum?"
Idanu Khadija ta zaro itama ta mike tsaye, juyawa taga yayi zai tafi da sauri ta sa hannu ta rike rigarshi ta baya.
Tsayawa yai va tare da ya juyo ba, yace " wanene?"
Shiru tai batace komai ba, rigarsa ya fizge ya fara tafiya da sauri ta sa hannu batasani ba ta riko hannunsa.
Tsayawa yai sai dai wannan karan ya juyo.
Hannunta ta kalla da sauri ta sakeshi tace " Yaya nice."
Fuskarsa a d'aure yace "kece wa?"
A hankali tace " Khadija ce."
Gani tai ya sake juyawa zai tafi.
Gabansa tasha da sauri, shikuma yai kamar bai ganta ba ya taho ya dauka in ya taho zata matsa ita kuma bata taba tunanin zai zo daf haka ba.
Jikinsu ne ya hadu da juna wanda tsoro yasa ta rike rigarsa tai baya da sauri, shi kuma rike rigarsa datai yasa ya fada kanta suka fadi tare?
Idanunta ta rufe saboda tsananin kunya, shikam kallanta yai sosai dan bai taba kallanta daf da daf ba sai yau.
Idanunta a rufe tace " Ya ka d'agani!" Cikin shagwaba tai maganar kallanta yai yace " da wayace ki yarda ni?"
Tace " ni kuma? Yaushe?"
Mikewa yai tare da sa hannu ya d'agota hannu tasa ta rufe fuskarta.
Juyawa taga yayi zai tafi sai alokacin ma abin yazo mata to ma in taji kunyarsa inama ya gani?
Daurewa tai tace "Yaya kayi hakuri."
Yace "game da me kenan?"
Tana tsaye a bayansa tace "game da komai ma."
" niban fahimci hakurin da kike bani ba ai."
Hawaye ne suka fara zubo mata, cikin kuka tace " na konewar da kai wanda su Umma Babba suka ja ma."
Fuskarsa a had'e yace " wannan kuma menene naki a ciki? Meye naki na bada hakuri?"
Kallansa tai ta baya tace " taya zaka ce haka Yaya?"
Cikin bacin rai ya Juyo ya kalleta yace " kukan me kike kuma?"
Cikin kuka tace " ni kaina so nake hawayen su tsaya."
Dan karamin tsaki yaja yace " abinda ya kamata kuma nakesan naji kin ban hakuri akai da alama ma bakisan shi ba, bana bukatar kukan ki ba kuma na neman ban hakurin ki."
Juyawa yai kamar zai tafi.
Rigarsa ta sake rikesa amma hanzu hannun rigar ta rike, a hankali ta furta "Yaya kayi hakuri tafiyar danai ba tare da nama sallama ba."
Jikinsa ne yai sanyi, bai juyo ba, ta kara share hawayenta zatai magana ya juyo cikin bacin rai yace " kinsan kwana nawa nai ina jiranki? Awanni nawa nai ina nemanki? Lokuta nawa na bata ina tunanin dawowarki? Zaki tafi menene inkincemin zaki tafi? Hanaki zanyi? Ko dan Kinga na dogara da zuwanki a koda yaushe? Sai dai inaso ki sani na dade da mantawa da ke da jiranki."
Juyawa yai ya fara tafiya, tsugunnawa tai kawai tasa kuka.
"Ba laifina bane yaya, ba laifina bane nikaina banso tafiya ba, ba laifina bane."
Abinda kawai take fada kenan.
Yana jinta yai waje shikanshi kukanta har jikinsa yake ji.
Yana fita ya jingina da jikin kofa ya dade a haka kafin ya sa sandarsa ya fara tafiya.
********
Mairo ce zaune tana wanke wanke tanayi tana 'yar karamar mita dan itakam ta tsani abinda ake mata, mahaifiyarta su biyu ne, kishiyar babarta sam bata sa nata 'ya'yan aiki amma ita kullum ita ake sawa aiki kuma tanayi ba a gode mata sai tai magana mahaifiyarta tace batada hakuri.
Sa'arta ta gani ta gun kishiyar mahaifiyarta ta kalleta tace " nikam Karima wai nikam sai yaushe zaku biyani kudin wata?"
Karima ta kalleta tace " kudin wani watan kuma?"
Mairo ta harareta tace " na albashin aiki da kuka daukoni mana."
Karima tace " ban gane ba"
Mairo cikin masifa tace " nifa bazan laminci wannan rainin hankalin ba ehe, sai kace wata 'yar aikinku?"
Muryar maman Karima taji a bayanta tace " to bazasuyi ba kedin meye aikinki? Tunda kinki aure?"
Mairo tai dariya tace " dan ma dai bani kadai bace banyi auran ba."
Karima tace " da wa kike?"
Mairo tace " wanda ya tsargu, haka kawai tunda mai taya mu aiki tai tafiya kullum ni nake aiki ni ba 'yar aiki ba bakuma baiwa ba?"
Jitai an dada mata duka a bayanta ta juyo da nufin masifa, mahaifiyarta ta tagani, ta kalleta tace " Mairo bana hanaki ba?"
Turo baki tai batace komai.
*ABU TURAB TEAM 🤝🏻*
.🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*27*
Garzali ne ya biyoshi suka nufi fada dan yanzu aka aiko akan yaje saboda Abdulmajid zai sanar da binciken dayai.
Bayan sun zauna ne Abdulmajid ya dawo tsakiya sannan yace " Ranka ya dade na gama bincike."
Galadima ne yace " to munajinka."
Abdulmajid yai d'an gyaran murya sannan yace " bincike ya nuna mana cewa ba kowa bane ya jawo wannan abin ba sai mahaifiyarsa."
Jin wannan zance yasa mutane suka fara kananan magan magan, Abu Turab kam wani murmushi ya saki kansa na kasa a ransa yace " they take the bait."
Kallan Abdulmajid kowa yai, Mai Martaba ya kalleshi yace " meye hujjarka na fadar haka?"
Abdulmajid ya gyara zama yace " Mahaifiyarsa tanasan asan shi wanene, ma'ana asan shidin d'an sarki ne, sannan tayi hakan ne dan mutane su farga susan akwai wani magajin sarkin bayan ni."
Mai Martaba yace " wannan ita kadai ce hujjarka?"
Kai ya girgiza alamar a'a yace " tayi abu kala biyu, na farko in har yasa mutane zasu sanshi saboda kayansa da kuma yanayin dokinsa, na biyu kuma ba wanda zaiyi zarginta sai dai kowa yai zargin Magajiya, kunga ta jefi tsintsu biyu da dutse d'aya."
AbuTurab ya d'ago kai yace " Bravo! Ba shakka wannan ma abin dubawa ne."
Mamaki hakan yaba Abdulmajid ya dauka abin zai tadamai hankali.
Barde ne ya katse mai tunaninsa da cewa " shaidu fa?"
Abdulmajid ya juya yace " shigo."
Nan wani bawa ya shigo wanda kowa ya sani bawa ne wanda ke kula da al'amuran Magajiya na waje bana ciki ba.
Daga can bakin kofa ya zube ya gaidasu, Abdulmajid yace " wannan bawan bawa ne ga Magajiya shi Mahaifiyar Abu Turab tai amfani gun aika mai da kaya dan gudun kar a gane itace."
To fa? Nan kowa yad'an fara magana kasa kasa.
Abdulmajid ya kalleshi yace " sanar damu abinda ka sani."
Muryarsa na rawa alamar tsoro da dana sani yace " tuba nake ranka ya dade amma abinda Yarima mai jiran gado ya fada haka yake, ranar nazo wucewa Baiwarta wato Lantana ta mikon kaya tace " dan Allah sauri nake dan mikama Abu Turab, basai ka shiga ba kawai ka bada a kofar shiga ka wuce."
Salati mutane suka fara dayawa sun gamsu dan sunsan ba yanda za'ai bawa yazo gaban mai martaba ya gilla karya haka.
Abu Turab yai murmushi sannan yace " Ammm ina Mai bada shaidar nan?"
Bawan yace ganinan Yarima."
Abu Turab yace " ka tabbata duk abinda ka fada gaskiya ne?"
Yace " hakan yake Ranka ya dade, ina ni ina karya gaban Takawa."
Abu Turab yace " haka ne, sai dai nima ina rokon a bani dama namai tambaya."
Mai Martaba yace " inajinka."
Abu Turab yace " inaso ka bani amsar tambaya ta cikin sauri ba tare da kaja min lokaci ba, inaso daga na tambayeka ka sanar dani amsa."
Kai ya daga.
Abu Turab yace " A ina kuka had'u?"
"Gaban Turakar Magajiya."
"Hmm kenan can ta bika saboda tana san ta aikeka?"
Muryarsa ce tadan sarke yace " banida masaniya akan wannan."
Yace " me yasa daka kawo kayan baka ce inji Lantana ba bayan a iya sanina wanda ya kawo kayan ance ya sanar da wanda ya aikosho?"
Inin na ya fara cikin tsoro yace " hmm hmm nima sauri nake hmm shi yasa....."
Abu Turab ya karseshi da cewa " ok na gane, saurin da kakeyi ne ya hanaka sanarwa ko?"
Da sauri yace haka ne.
Abu Turab yace " kenan bayi nane sukai karya tunda sun sanar dani an fada musu wanda ya aiko da kayan?"
Bawan yai shiru, Abu Turab yace " na fahimceka, yanzu tambaya d'aya zan maka, dakai da Lantana wanene yafi wani matsayi a gidan nan?"
Cikin rashin fahimtar zancensa yace " na fita."
Abu Turab yace " Good! Ka fita matsayi meya saka ka yarda ta aikeka?"
Gaban Bawan ne ya fadi ya fara inda inda "hmm dama...."
Katseshi Abu Turab yai yace " dama me?"
Shiru yai dan ya rasa bakin magana, Abu Turab yace " bari na aika a kira Lantana da alama kunada wata ala'aka da ita wanda ba wanda ya sani, dan hakan ne kadai zai sa mu fahimci dalilinka na zuwa aikenta."
Hankalinsa ne ya tashi da sauri yace " wlh ba haka bane ni banma taba magana da ita ba, ina dai gani suna zuwa gun Magajiya amma wlh ko sau d'aya bamu taba magana da ita ba....."
Shiru yai jin ya kauce hanya a zancen sa.
Abu Turab yace " to fa yanzu wace maganar zamu yadda da ita?"
Galadima a harzuke yace " wannan shaidar bamu yarda da ita ba dan ta nuna itadin bakin ganga ce."
Idanu Abdulmajid ya runtse dan bakin ciki.
Wani mugun kallo ya bugama Abu Turab, nan mutane suka fara kananan maganganu, lalai dama ance makaho yanada tasa baiwar da alama Abu Turab akwai kwakwalwa, ganin ne dai da Allah ya d'auke mai.
Kallansa Mai Martaba yai cikin jin dadi, Abdulmajid yace " inada wata shaidar."
Mai Martaba yace " muna jinka."
Wanda ya kawoma Abu Turab doki ne ya shigo, bayan yayi gaisuwa Abdulmajid ya kalleshi yace " sanar damu abinda ya faru."
Nan yace shidai an aikeshi ne yakai doki bangaren Abu Turab.
Abu Turab ne ya katse Abdulmajid wanda ke shirin magana yace " tabbas muryarka ce naji a lokacin, sai dai tunda ba gani nake ba bazan san kaidin bawan wanene ba."
Kansa na kasa yace " bawan Magajiya ne."
Murmushi Abu Turab yai yace " kenan duk bayin Magajiya ta nemo?"
Abdulmajid ya bugamai kallo baice komai ba, Abu Turab yace " amma ni mai ka sanar dani a lokacin? Wa kacemin ya aiko ka?"
D'agowa yai yad'an kalli Abu Turab, gabansa ne ya fadi, duk da yasan baya gani amma baisan me yasa ba sai yaga kamar yana kallansa, kwarjini Turab yamai dama gashi duk cikinshi ya gama rud'ewa a waje dan kuwa yaji duk abinda ya faru da d'aya bawan.
Shiru yai baice komai ba, Barde yace " zancen banza kenan, tayaya ana tambayarsa ya kasa bada amsa."
Mai Martaba ne yai gyaran murya yace " Kana da wata shaidar? Dan wannan shaidar naga farar kura ce."
Abdulmajid kasa yai dakai a hankali yace " tuba nake ranka ya dade banida wata."
Mai Martaba ya kalli Abu Turab yace " kaifa? Kanada ta cewa?"
Abu Turab yace " ina neman alfarma akan mai martaba ya yafema wanda ya aikata wannan laifin gudun samun babbar matsala garin bincike, dan na tabbata duk wanda ya aikata hakan tabbas bazai yarda a gane shi bane."
Mai Martaba yace " zanyi tunani, amma wad'an nan bayin da sukai shaidar karya inaso a kullemin su."
Da wannan fada ta tashi, kowa yana yaba kwazon Abu Turab.
Hisham kam da Abdulmajid a cike suka isa gun Magajiya, bayan taji komai ta kalli Abdulmajid bai yi auni ba yaji ta wanka mai mari.
Tashin hankali, d'agowa yai cikin tashin hankali dan tunda aka haifeshi ba'a taba dukansa ba sai yau, Magajiya ta kalleshi tace " wannan shine shirmanka na cewa in barma zaka d'au mataki da kanka? Wannan shine abinda kwakwalwarka kawai zata iya karantama?"
Hisham wanda yaji dukan kamar a fuskarsa ya daure yace " kiyi hakuri Magajiya."
Kallan Abdulmajid tai tace " ku bani guri."
Nan suka mike jiki a sanyaye, Hisham na fita yai 'yar karamar kwafa a ransa yace " wlh wannan marin bashinshi kika co kikira d'ana ya hau mulki zakisan kin mareshi."
**********
Bayan sati d'aya.
Abu Turab zaune a gun mahaifiyarsa yanacin abinci sai dai zuciyarsa nata tunanin tun randa yaga khadija bai sake ganinta ba har yau, ko dai ta koma inda ta tafi da ne?
Yana neman amsar tambayarsa yaji sallamar Mairo.
Amsawa yai va tareda ya juyo ba.
Gefensa ta karasa ta gaisheshi sannan tace " Yaya ina Umma?"
Yace "Mairo tana ciki, kwana biyu?"
Murmushi tai tace " na da'uka ko daina zuwa nai bazaka nemanba bare ka tambayen dalili."
Juyowa yai yace " tanan kika b'ulo?"
Tace "Ba haka bane yaya gaskiya ce ai na fada."
Yace " hmm, ina saurayin naki? Ki fada mai fa in har yanasan in ba da ke sai yazo ya kwashi gaisuws."
Fuska ta had'e tace "ni bansanshi ba."
Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa wanda har hakwaransa suka fito, daidai nan Basira ta fito, kallansa tai cikin jin dadi tana ganin yanda yake tsokanar Mairo, kana ganinsu kasan suna cikin farin ciki, lalai dolene ta tilastamai auren Mairo.
Yana gama cin abinci yanashan ruwa Garzali ya sanar dashi nemansa da Sabi'u yake.
Mikewa yai ya sa hannu zai dauki sandarsa, da sauri Mairo ta d'auke sandar ta b'oye tana dariya.
Yace " Mairo nasan kece, mikomin in fita, in kuma baki ban ba zan fita a haka duk abinda ya samen kece."
Da sauri ta mikomai tace " yahkuri yaya."
Amsa yai ya fita baice komai ba.
Kallo ta bishi dashi tanajin wani abu na ratsa ta.
*********
A waje yaga Sabi'u yiyai kamar zai wuceshi, Sabi'u yace " ganinan mutumina."
Ya karasa maganar tare da dafashi.
Abu Turab yace " Badai aiko ka akai ba ko?"
Yace " Mai Martaba ne yace inzo dakai."
Fuskarsa a hade yace " dama nasan bazaka kazo dan radin kanka ba."
Sabi'u yace " Abu turab kaikasan dalilina, kana gani yanda nake sha fada agun Mahaifina na bayasan in ware ga wanda nakeso saboda gudun nan gaba."
Abu Turab yai murmushi yace " da gaskiyarsa, tunda yasan Abdulmajid ne next emperor kaga kuwa yana tsoron kar Abdulmajid ya hukuntaka na shakuwa dani."
Sabi'u yai tsaki yace " in kuma kaine fa?"
Tsaki Abu Turab yai yace " zaka fara ko?"
Sabi'u yace "Allah sau dubu kafi Abdulmajid matsalar ido ce kadai kuma......."
Abu Turab ya katseshi yace " muje dan Allah."
*********
Sun isa gun hutawar Mai Martaba inda yake zaune rike da wasu takardu yana dubawa, bayan sun gaisheshi ne Mai Martaba ya kalli sabi'u hakan yasa ya mike yai baya dasu.
Shiru ne ya biyo baya kafin Mai martaba ya kalli Turab yace " Abu Turab!"
Yanda ya kira sunansa ne yasa Abu turab kallan mahaifin nasa.
Cigaba yai da cewa "Inaso gobe Asabar dakai da Sabi'u ku ziyarci masarautar Kano."
Kallansa yai cikin mamaki, sai dai baice komai ba.
Mai Martaba yace " Zakuje Masarautar ne da nufin ziyara sai dai inaso ka samu keb'ewa da Bilkisu 'yar Sarkin garin."
Cikin mamaki yace " ban gane ba Abba."
Mai Martaba yace " Inaso duk yanda zakai kayi dumin sace zuciyarta."
Mamaki ne yasa Abu Turab ya kasa magana.
Mai Martaba yace " Umarnine na baka ba shawara ba, inaso ka kwana a garin kamar kwana biyu, a wannan lokacin ka tabbatar Bilkisu ta aminta dakai."
Kansa na kasa yace " bazan tambayi dalili ba dan nasan ba kirana kai a matsayi uba ba, ka kira ni ne a matsayin Sarki, zanyi abinda kace sai dai inada tambaya, a makaho xan je mata?"
Sarki yace " wannan na bar maka hukuncin domin ni Sarki ne wanda baisan d'ansa yana gani ba."
Nagode, kawai abinda yace kenan ya mike.
Suna fita daga gun ya tsaya cak, jiyake kamar zuciyarsa zata fashe.
Sabi'u ka dafashi yace "me yasa baka musa mai ba?"
Yace " ta ina zan musamai bayan Umarnin Sarki ne bana uba ba?"
Sabi'u ya kalleshi cikin tausayi yace " amma nifa hadin auren ya birgeni, Bilkisu itakadai ce gun Sarkin kano aurenka da ita zai karama matsayi da kuma daraja agun mutane."
Abu Turab murmusawa kawai yai baice komai ba, Sabi'u ya kalleshi yace "yanzu ya zakai?"
Juyowa yai saitinsa yace " Sabi'u nasan bazan samu abinda zuciya ta takeso ba dan haka banga wani damuwa ba akan auren wata, ban dauki auren nan wani abun ba banda biyayya da kuma raba gado da wata ba."
Dariya ce ta kama Sabi'u yace " raba gado?lalai Turab bakada kyau, taya zaka dauki auren 'yar sarki akan raba gado?"
Tsaki yad'an ja yace " to fadamim, soyayya ce?aminta ce?yan uwan taka ce? Ko kuwa shakuwa ce?"
Dariya Sabi'u ya sakeyi baice komai ba.
********
Acan gidan Waziri kuwa Hisham kuwa tunda Khadija ta dawo zazzabi ya rufe ta yau sati d'aya kenan tana fama da zazzabi da ciwon kai.
Wannan kenan
*ABU TURAB TEAM 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*28*
B'angaren Mahaifiyarsa ya nufa, tana zaune gefenta kuma Lantana ce, daga bayanta kuma a tsaye Mairo ce take mata kitso, jiki a sanyaye yai sallama.
Dukansu suka amsa nan ya karasa ya zauna a kasa tare da lankwashe kafafunsa.
Basira ta kalleshi sai dai batace komai ba, d'agowa yai yace " Umma gobe zani Kano."
Gabanta ne ya fadi dan kuwa tasan me zaije yi kanon.
Sam ta manta da Mairo dan kuwa hankalinta ya tashi, ta kalleshi tace " ka amince da ganin yarinyar ne ko kuwa har auren?"
Idanu Mairo ta zaro cikin tsananin tashin hankali, kallan Abu Turab kawai tayi, shima jin kalaman Basira yasa ya d'ago ya kalli Mairo.
Ganin yanda idanunta sukai yasa ya kalli Basira kansa na kasa yace "Mairo bamu guri."
Jin haka yasa Basira ta juyo da sauri ta kalleta, ganin yanda kwallq ta ciciko mata yasa tace " Lantana shiga da ita d'aki
"
Mikewa Lantana tai ta ja ta ciki, suna shiga ta zube a kasa tare da hade kanta da gwiwarta, ba kuka take ba sai dai yanda takeji a ranta tabbas taso ace ma kukan takeyi.
Tana iya jiyo muryar Basira sama sama tana cewa " Abu Turab nifa wannan hadin auren bai kwantamin ba, nafisan ka auri Mairo ko dan samun nutsuwarka da kuma kwanciyar hankalinka."
Dan murmusawa yai yace " Umma kinaso ne na karya umarnin Sarki ko me? Abba ya kiranine a matsayin Sarki bawai a matsayin Uba ba, sannan maganar Mairo nicewa tai tana sona ko kuwa nice nace ina santa?"
Shikam yasan tana sansa sai dai yayi hakan ne dan sa Umma ta saduda, ya cigaba da cewa " itama ta kanon xan dai jene kawai inbi Umarnin da aka bani amma tana 'yar sarki guda d'aya tilo mai zatai dani? Makaho?"
Basira cikin bacin rai tace " Da farko amsarka xan ba, na tabbata kai kanka kasan Mairo tana sanka, sannan kaima nasan haka, sannan na biyu shi mai martaba cewa yai kaje a Makaho?"
Gaban Mairo ne ya fadi, Lantana jin haka ta taso fa sauri daga inda take a d'akin tace " tashi ki shiga can ciki."
Mairo ta kalleta tama kasa magana mikewa tai a hankali ganin yanda ta tsaya kamar me shirin faduwa yasa Lantana ta riketa, ji sukai Abu Turab yace " yace inje a duk yanda naso, nima haryanzu ban tantance a me zanje mata ba."
Jitai kanta yayi wani irin sarawa, cikin rawar murya ta kalli Lantana tace " meke faruwa?"
Lantana ta kamata suka fara tafiya, sai data kaita canciki sannan ta kalleta tace " ba abinda ya faru nikaina bansan me suke nufi ba."
Mairo ta kalleta tace " amma dai ba kina nufin in yarda da kalamanki ba ko?"
A makaho xakaje mata? Ta maimaita maganar da Basira tai sannan tacigaba da cewa " me hakan yake nufi? Duk wanda qwaqwalwarsa take aiki na tabbata xai gane magana ce aka yita mai ma'ana biyu, a makaho zakaje mata?ko da ido?"
Lantana ta kalleta cikin tsoro, Mairo ta mike ta tsaya gaban Lantana tace " zan gyara tambayar dana miki d'azu, Yaya yana gani?"
Idanu Lantana ta runtse batace komai ba, Mairo tace " zan kara gyara tambaya ta, Lantana meyasa yake pretending din baya gani?"
Lantana ta girgiza kai tace " nima bansan komai ba, da sauri tabar d'akin tare da janyo kofa."
Mairo tai shiru tana tunani, me yasa yaya yana gani yake nuna baya gani? Wani irin abu ne yau takeji haka? Abubuwan da sukai ta faruwa dashi yana yari ta tuna, kai ta girgiza tace bazai yiwu ace pretending yakeyi tun da ba sai dai in warkewa yai."
A can bangarensu Basira kuwa, kallansa tai tace " Abu Turab harga Allah zaka cemin baka san Mairo tana sanka ba?"
Kallanta yai yace " Umma!"
Tace " ni mahaifiyarka ce nasan abinda zai taimakeka gun samun farincikinka, Mairo zata kula dakai, zata taimakeka ni aguna ita kadaice zata dawoma da farincikinka."
Idanu ya runste yace " nifa Mairo kanwa tace ban taba tunanin zaman aure da ita ba."
Jiyai tace " sai ka fara yanzu."
Mamaki ne ya kamashi yace " Umma nawa nake? Shekarata kwatakwata nawa? Taya zakumin zancen auren mata ba d'aya ba har biyu a rana d'aya wanda kuma duk cikinsu ba alakar soyayya dake tsakaninmu?"
Basira tace " Ba takura maka zanyi ba sai dai inaso ka duba ra'ayina ka kuma ba shawarata lokaci mai yawa."
Sunyi shiru kafin tace " tashi kaje."
Mikewa yai ya fita, d'akinsa ya shiga ya kwanta akan gado yana kallan sama.
Mairo ce ta fito kana ganinta kasan tana cikin wani yanayi, Basira ta kalleta tace " Mairo jeki gida zansa a karasa min kitson."
Kai ta girgiza alamar a'a tace " a'a Umma bari na karasa miki."
Basira tace " jike Mairo, ninace kije ai."
Jakarta kawai ta d'auka ta mata sallama tai waje.
Tafiya kawai takeyi amma zuciyarta fal take da tunani kala kala tama rasa ta inda zata samo amsoshin tambayoyin.
Jitai an fizgo hannunta, a tsorace ta juyo, janta kawai taga yayi soron kusa da gun ya sata a ciki.
Hannunta ta shiga fizgewa ta hada cewa " Malam meye hakan? Sakarmin hannu ko?"
Baisake ta ba ya d'ora da cewa " da dan rashin mutunci kina ganina kika wuce ni?"
Kallansa tai cikin takaici tace " Malam sakeni dan Allah, ni ba muharamarka ba zaka wani dinga rikeni? In magana zakamin kamin da baki."
Murmushi taga ya saki yace " Karki damu saura kiris ki zama matata dan na kula shi kadai ne yanya mafi sauki da zan daidaita miki sahu."
Kallansa tai cikin takaici tace " in zama matarka? To ko nidin baiwa ce banaji kamada damar yanke hukunci akaina bare kuma....."
Katseta yai tare da sakin hannunta yace " kin dai san nidin waye kin kuma san matsayina a garin nan, ko Mahaifinki bai isa in yanke hukunci ya canza min ba."
Dan karamin tsaki taja sannan ta kalleshi ido cikin ido tace " Abdulmajid kake ko wa?"
Idanu ya zaro ya kafeta dasu, tacigaba " Zan maka kashaidi xa gargadi na farko kuma na karshe, in har zamuyi magana dakai ka kiyayi min abubuwa guda biyu, na farko kada ka kuskura ka kara rikeni ko ka taba ni ko da kuwa hijab din jikina ne, na biyu kuma kada ka kuskura ka dinga sako iyayena in muna magana, ni yanzu banda lokacin ka abinda ke gabana yafi karfin na tsaya ina bata lokacina."
Matsawa tai da nufin wucewa, fizgota yai da karfi ya bugata jikin bango yace " ke harkin isa ina magana kina magana, har kina da matsayin da zaki kira sunana gatse gatse har kice zakimin gargadi?"
Ajiyar zuciya tai tace " in kaji haushi inji sammaci."
Tana gama fadar haka ta ture hannunsa tai waje.
Kallan bayanta yai cikin kuluwa yace " mu zuba mu gani, ina tausaya miki in kika shigo hannuna, auranki kuma ya zama dole a gareni."
Yanajin haushin yanda baya iya yanke mata hukunci duk wulakanci da zatamai.
Itakam ranta a bace tai gaba, tana kokarin fita taga wata kamar Khadija ta wuce, binta tai da kallo cikin mamaki da san tabbatar da abinda zuciyarta ke zargi.
Khadija kam bata kula da ita ba dan ba lafiya ce ta isheta ba yanzun ma daliline ya shigo da ita.
*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*29*
Khadija bangaren Magajiya ta isa, tana shiga ta taddata a zaune, karasawa tai ta gaisheta, Magajiya ta kalleta cikin kulawa tace " Khadija sannu, ina nan hankalina a tashe ina tunanin yanda jikinki yake, Khadija ya akai haka? Duk kin rame."
Khadija ta d'ago ta kalleta bata bata amsar tambayarta ba sai jitai tace " Umma an tura wani ya dubo Inna Lami?"
Magajiya tad'an tabe baki kadan sannan ta kalleta tace " na tura, sunce jikin da sauki."
Hawaye ne ya zuboma Khadija tace " Umma me yasa bakwasa tausayi a ranku?"
Hade rai Magajiya tai tace " KHADIJA!"
Khadija tana kuka tace " makociyar Inna Lami ba ta aiko a sanar daku jikinta yayi tsanani ba?"
Magajiya tace " a yaushe akai hakan?"
Khadija tace " amma tace ai ta sanar da Yaya, Umma Allah ya d'auki ran Inna Lami, ita kanta bata sani ba tunda ita tasan ta sanar da Yaya ta dauka anje an dauketa, ita kuma a ranar tai tafiya, sai jiya da ta dawo ta shiga gidan ta ganta duk ta kumbura da alama ma ta dade da rasuwa, nan tasa aka kira mutane aka mata sallah aka kaita, d'azu da naje take sanar dani......"
Kukanta ne ya tsananta sanda tazo karshe.
Tace "Umma Inna Lami fa kanwar Mahaifiyar ku ce, tayaya zaku..."
Ya isa haka!
Abinda Magajiya tace kenan, d'agowa Khadija tai ta kalleta, dan tayi maganar ne da kakkausar murya.
Magajiya tacigaba " Ya isa haka Khadija, Inna Lami ta rasu Allah ya jikanta, zansa aje gidan, ke kuma jan maganar ya isa, ba kuma na san ki kara tada maganar nan."
Kallanta Khadija ta shiga yi cikin tsananin mamaki, Magajiya ta kalleta tace " ki tashi ki koma gida zan aiko miki da magani da abubuwan bukata, banasan ki dinga kwanciya ciwo akan abinda bai kai ya kawo ba."
Sam ma ta rasa me zatace sai kallan mamaki kawai datake binta dashi.
Ganin batada niyyar kara magana yasa Khadija ta mike ta fito daga d'akin.
Ba shakka yau taga abin mamaki ace d'an uwanka na jini? Sannan harda wani wai batasan taga tana kwanciya akan abinda bai kai ya kawo ba? Kenan abinda sukama Turab da wannan rashin kula da Inna Lamin da sukai ba wani abin bane a gunsu?
Samun kanta tai kawai da bin hanyar da zata kaita gun Abu Turab.
Sai dataje kofar shiga ta tsaya tana tunani me zatace mai?
Tabbas ganinsa ne kadai zaisa taji saukin wannan abin.
Tura kofar tai a hankali, Mai kula da gun ne ya taso ya gaisheta, a hankali ta furta Ya Turab nanan?
Yace " eh yana ciki, a sanar mai da zuwanki?"
Tace " bari na shiga ai kasan ni ko?"
Kallanta yai yace " na sani amma taya....."
Gani yai kawai tayi gaba batama san yanayi ba.
Falo ta duba ganin bayanan yasa ta tsaya taba kallan falon, idanunta ne suka kara zubo da wasu kwallar sannan a hankali ta nufi kofar d'akinsa kwankwasa wa tai daga ciki yace " waye?"
Shiru tai sai kuma ta kara kwankwasawa.
Mikewa yai ya bud'e kofar.
Kallanta yai sannan yai saurin kauda kai ya kara cewa " waye?"
Kallansa ta shiga yi hawaye na zubo mata, a zuciyarta tace "Yaya ina cikin wani hali, su Umma Magajiya, Yaya, da Abbana sun fara bani tsoro, banaji suna da digon tausayi a zuciyoyinsu, Yaya ya zanyi in canza su? Ya zanyi in nuna musu hanyar gaskiya?"
Hawayenta ta shiga sharewa, jiyai zuciyarsa na kuna ya tsani yaganta tana kuka, gashi yaga ta rame sosai da alama rashin lafiya tai, daurewa yai ya juya da nufin komawa ciki, jiyai tace " nice Yaya."
Juyowa yai yace " Khadija? Me kike a nan?"
Ta daure tace " ganinka kawai nazoyi, ya hannun naka?"
Fuska ya had'e yace " me zaisa ki damu da ciwon da baikai ya kawo ba, bayan kece kike bukatar kulawa?"
Daurewa tai tace " yaya ya warke?"
Labansa yadan ciza yace " Khadija meke damunki? Me yasa bakya fahimtar abinda nake nufi? Kina tunanin in kika nuna damuwarki akan ciwona kika wulakanta naki lafiyar zanji dadi? Me yasa kike san ki dinga sani cikin damuwa?"
Kallansa tai fuskarta cike da mamakin kalamansa, tace " Yaya."
Idanu ya d'an runtse yace " please in har kinasan ki nuna kulawarki a kaina to ki kula da lafiyarki."
Juyawa yai ya koma ciki, ya rufo kofar.
Shiru tai sai hawaye da suke zubowa daga idanunta, jingina tai da jikin kofar, shikansa yana shiga ya jingina da jikin kofar.
Idanunta a lumshe tace " Yaya."
Bai amsa mata ba sai dai yana jinta, tacigaba " Kayi hakuri yaya, kayi hakuri da rashin sanar dakai tafiyata fa banyi ba, kasan ina zaune a gunka lokacin da aka aiko inje, ina zuwa aka sani a mota ko gida ban shiga ba, kayi hakuri da rashin nemanka dabanyi ba, tunda naje garin ba'a kara barina na zo ba sai wannan dawowar."
Iska tadan furzar sannan tace " Yya kayi hakuri na abinda su Umma Babba sukama, sannan kayi hakuri na rashin baka hakuri da sukai."
Ransane ya bace ya bud'e kofar da karfi, hakan yasa tai saurin gyarawa ganin ta kusa faduwa, a fusace yace " meyasa kike bada hakuri? Me kikai? Me yasa kike bada hakuri a koda yaushe? Bayan wadanda ya kamata su bada hakurin basusan ma sunyi laifi ba? Me yasa Khadija? Meyasa kike neman tadamin hankali?"
Kai ta shiga girgizawa har ya gama fadan sannan tace " Yaya na san....."
Katseta yai yace " Khadija meyasa bazaki fahimceni ba? Banasan kina yawan bani hakuri hakan na sa inji kamar nine nake miki laifi."
Daurewa tai tace " Nadaina yaya."
Yace " Khadija please....."
Murmushi ta kakaro tace " na daina Yaya, nazo ne dan ina cikin wani hali zuciyata bata kawo min kowa ba sai kai, shiyasa nazo."
Kallanta yai yace " me ya sameki?"
Murmushi tai tace " hmm inama Yaya kana gani? Da kaganni ina ma murmushi."
Shiru yai baice komai ba, tace " Haryanzu addu'ata kenan, Allah ya bud'ema idanunka."
Murmushi taga yayi, itama murmushin tai sannan tace " Ahh da alama zuciyata tayi sanyi,duk da hankalina haryanzu bai kwanta ba."
Yace " me ya faru kuma?"
Tace " Inna Lami ta rasu."
Yace " yaushe?"
Kallansa yai tace " ba'a san yaushe bane."
Kallan mamaki ya mata, ganin zata d'ago yasa ya kauda kai yace " ban gane ba."
Zama tai a kasa a jikin bango, ta kama rigarsa tace " Yaya zauna plz."
Zama yai dan ya kula tana bukatar mai lalashi."
Zayannemai komai tai.
Hankalinsa ya tashi, lalai mutanen nan basuda imani, wato abin ma harda jininsu?
Khadija ta d'ora da cewa " Yaya in kaine me zakayi?"
"Hmmm in nine ba abinda zanyi."
Tace " ba abinda zakai?"
Kai ya d'aga alamar eh yace " me zanyi to? Abin nan dai ya riga ya faru, sannan mutanen na basu nuna tausayawa ko dana sani ba, ni da nake d'a me kike tunanin zanyi? Sai dai...."
Shiru yai hakan yasa tace " sai dai me?"
Yai ajiyar zuciya yace "sai dai dole girma da darajarsu zai ragu a idona."
Tace " na fahimceka Yaya na kuma gode."
Mikewa tai tace " yau naji dadin dana dade banji ba duk da wata zuciyar tana tausayawa Inna Lami, sai dai wata zuciyar tana farin cikin zama tare da kai danai wanda na dade ban samu ba."
Baice komai ba, tace " nagode yaya."
Ta fada tare da tafiya.
Kallo ya bita dashi sannan ya mike a hankali ya koma ciki.
Ya zaiyi? Ya zaiyi? Ba shakka yanasan Khadija sai dai yana ganin auransa da ita ba mai yiwuwa bane, tsanar Magajiya da ahalinta ne suka kara shigarsa jin labarin da khadija ta bashi.
Kansa ya dan shafa yace " Ya zanyi?"
*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*
🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*30*
Wajen karfe sha biyu na rana ya fito daga bangarensa sanye da shadda mai kyau da tsada da yake kayan mu na da masu kyau ne da quality kai ka dauka sabuwa ce, yayi kyau sosai sannan ya zuba wasu kayan a cikin yar karamar jaka tunda Mai Martaba yace kwana biyu zasuyi a can din.
Sabi'u ne ya zo kusa dashi yana dan tafi yace " Yayai Ango ai da alama Bilkisu takace, ta ina zatai wasa wannan saurayin ya wuce ta?"
Fuska ya d'aure tamau yace " zaka fara ko?"
Sabi'u yazo gefensa yace " Nadaina Ango."
Abu Turab yace " matsalarka ce wannan, mikam mu tafi."
Su biyu suka fito dan ko Garzali bai dauka ba, dan Mai Martaba yace zuwan nasu kano ya zama sirri.
Bangaren Mahaifiyarsa yaje ya mata sallama, duk da ranta baiso sai dai tamai fatan alkairi, ta kudura a ranta in har Bilkisu ta aminta dashi to fa yana aurenta zatasa ya auri Mairo, in kuma bata amince ba to dama ita hakan take so.
Ya fito suka shiga motar da Mai Martaba ya umarcesu suje, suna fita daga kofar gidan ya ga Mairo jikin katangar gidan a tsaye, sun hada ido sai dai da sauri ya dauke na sa idan, ya tabbata fitowa tai dan taga tafiyarsa, shikam tausayinta yake, yana kuma mata fatan samun miji na gari.
Sunyi da nisa, jefi jefi suna dan taba hira, sun danyi shiru kafin Sabi'u yace " Abokina!"
Turab yace " ya akai kuma? Dan nasanka sarai wannan Kiran kira ne na tambaya."
Sabi'u yace " tun jiya nakeso nai ma tambayar sai dai na rasa ta inda zan fara, ba kuma nasan mu samu sabani saboda ita."
" ina jinka."
Sabi'u yai shiru kafin ya dan kalli titi sannan yace " me kake nufi da a makaho zanje mata?"
Abu Turab bai ko kalleshi ba bare yaga alamar mamaki a tambayarsa, Sabi'u yana tukinsa yace " ba wai naso naji maganarku bane da mai martaba sai dai jin maganar nai daga inda nake tsaye."
" Ina gani."
Abinda Abu Turab ya fada kenan, cikin tsananin mamaki Sabi'u ya gangara gefen titi yai parking, Abu Turab ya kalleshi yace "meye abin tsorata? Harda tsayawa?"
Sabi'u yace " ban gane kana gani ba?"
Murmushi Abu Turab yai yace " Kaya ruwan toka ne a jikinka ka sa hula baka, sannan kaidin fatsi ne, kanaso in cigaba?"
Sabi'u idanunsa a waje yace " Yaushe ka warke?"
Abu Turab yai murmushi yace " that's not important, ka wuce muje."
Jiki a sanyaye Sabi'u ya tada mota, da kyar ya iya furta amma me yasaka pretending?
Shiru Abu Turab yamai, jin haka yasa yasan bazai amsa mai ba, sun dade a haka kafin Abu Turab yace " sanar dani halayenta da akace ka binciko."
Sabi'u yace " Bilkisu ita kadai ce mace a gun Sarkin Kano, yarinyace mai kyan gaske, dan kowa yana fadan irin kyan datake dashi, mace ce mai tausayi ayanda aka fada tanada saukin kai, ko kadan batasan a tozarta wani."
Shiru yai hakan yasa Abu Turabya kalleshi yace " shi kenan?"
Kallansa Sabi'u yadanyi yace sai dai tanada matsala d'aya.
Abu Turab ya kalleshi yace " na me kenan?"
Sabi'u yace " batasan a komenene a hadata da wani, wannan dalilin ne yasa taki aminta da duk mazan da suke kawo mata hari, a yanda naji ita kishi ko na menene batasan tayi dan tanada zafin kishi."
Tsaki Abu Turab yai yace " zancen banza takeyi kuma kenan baya yarda da kanta ba, in har tanaji da kanta tana ganin komai nata yayi 💯 banaji ya kamata ta dinga wannan shirman, wannan alamace na akwai abinda take lacking."
Sabi'u ya girgiza kai yana dariya yace " lalai Turab bakada kyau, yanzu kishin ma sai ka fassarashi? To ita kishin in hallitarta ce fa?"
Baki yadan tabe yace " sai ta danne shi tunda ba ita tai kanta ba."
Sosai yaba Sabi'u dariya, haka sukai ta zancen Sabi'u na kara dariya, sun isa kano da la'asar gidan Sarki suka wuce direct, Mai Martaba sarkin Zariya ya riga ya sanar da Sarkin kano akan zuwan nasu, suna zuwa aka wuce dasu ma saukin su, aka kuma turo musu bayi guda uku masu kula dasu.
Sunyi wanka sunyi Sallah sannan aka kawo musu abinci.
Abu Turab ya kwanta akan gado tare da daure hannunsa kan goshinsa kamar yanda ya saba, Sabi'u ya kalleshi yace " Malam Makaho sauko muci abinci."
Murmushi yadan mai yace " fara ci."
Sabi'u ya matso kusa dashi yace " kodai ka kosa ka ganta ne? Dan na kula tunaninta kake yi."
Abu Turab ya juya mai baya yace " kasan ni din ai ba kai bane."
Saida Sabi'u ya kusan gana cin abincin sannan shima ya sauko dan kadan yaci ya mike ya fito wajen harabar gidan.
Wata yarinya ya gani wacce batafi shekara 12 ba tana leko shi.
Alama ya mata da hannu akan tazo, tsayawa tai tana wasa da yatsun hannunta, Abu Turab ya tako har inda take ya dan rusuno yace " yan mata me kike anan?"
Kallansa tai tace " Kaine Yarima Turab?"
Cikin mamaki ya kalleta yace " kin san ni ne?"
Kai ta girgiza tace " Aunty na ce ta aikon inganka."
UmmaBilkisu?kina nufin Gimbiya Bilkisu?"
Kai ta daga alamar eh, sannan tace " amma karka fada mata kaji."
Murmushi yai yace " naji kedin wacece to?"
Tace " babana shine Yarima Nazir magajin sarki."
Kai ya jinjina zaiyi magana yaga ta juya da gudu, mamaki ne ya kamashi ya juya bayansa, ganin Sabi'u yasa ya fahimci ganinsa ne yasa ta gudu, murmushi yai sannan ya juyo.
Sabi'u ya karaso yace " Kai da waye?"
Abu Turab ya juya yace " bakowa."
Sabi'u ya matso yace " an turo wai bayan Magrib zamuje."
Harararsa yai yace " Zamuje ina?"
Sabi'u ya matso wajen kunnensa yace " Zance mana."
Abu Turab yace " dakai zanje zancen?"
"Eh mana, da kai da wa?"
"Sry Malam ni kadai zanje."
Sabi'u yace "Mai Martaba cewa fa yai in bika."
Kafadarsa ya dafa yace "sry mutumina amma ni kadai zani."
*******
A can kuwa Bilkisu ce xaune a d'aki, Munnira tana shigowa ta kalleta tare da mata alama da hannu akan ta matso, sannan ta sallami masu kula da ita, kallan Munira tai tace " Munnira ya?"
Munnira tace " Nikam Yamin UmmaBilkisu dama kibarmin shi."
Harararta Bilkisu tai tace " abinda na aikeki kiyi kenan?"
Munnira ta turo baki tace " Nidai shi zan aura."
Bilkisu ta harareta tace " ni tashi kiban gu bansan kayan haushi."
Bayan Magrib bayinta suka kara shigowa aka gyarata sosai,wasu kaya ta saka sun mata kyau sosai, karan miski ne an mata doguwar riga, dashi an sanye wasu duwatsu faga tsakiyar rigar, tayi kyau sosai, alkyaba aka sa mata a saman kayan.
Abu Turab kam ya hade rai sosai ganin Sabi'u ya nace akan sai ya bishi, haka Sabi'u ya hakuri shi kuma ya fito bayin da zasu sadashi da inda zasu hadu suna gaba.
Sai da sukaga ya shiga ya zauna sannan suka fito.
Bilkisu kam Jakadiya ce ta kawota, ta kwashi gaisuwa agun Turab sannan ta fita.
Kan Bilkisu na kasa bayan ta zauna, Abu Turab ya d'an kalleta kadan, tabbas tanada kyau sai dai shi wannan bai dakeshi ba.
Bayi ne suka shigo da tire dauke da kayan marmari suka jere a gaban Turab.
Har suka fita ba wanda yace ufan a cikinsu, ta gefen ido take kokarin san ganinsa sai dai ta rasa me yasa takejin wata irin kunya.
Kallanta yai yace " bako iya gaisuwa bane?"
D'agowa taita kalleshi, maganar da zatai ne ta tsaya mata sakamakon hada idon da sukai.
Kasa tai da kanta batace komai ba.
Shima shiru yai, sun dan dade a haka kafin yace " da alama bacci ne ya kamaceni."
Kallansa tai tace " da wuri haka?"
Yace " to me zan miki? Kinyi shiru, nima nayi shiru to me zamu jira?"
Baki ta d'an turo kadan tace " Barka da isowa." A hankali tai maganar
Yace " ni banji me ma kikace ba."
Dan Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace " Da alama kanada mita."
" ni ba mace ba mai zai hadani da mita?"
Tad'an tabe baki tace " mata ne kadai ke mita?"
" ban sani ba, wannan kuma ke za'a tambaya ai."
Kallansa tad'anyi zatai magana ta d'aga girar sa duka biyun yace " baki gama kallan nawa bane?"
Idanta ta d'auke da sauri tace "wa yace ma kallanka nake?"
"Yarinyar da kika aiko na d'auka ta sanar dake kamannina da yanda nake."
Kanta ta juyar gefe, cikin kunya tace " wace yarinyar kenan?"
Kafada yadan daga yace " bansanta ba."
Shiru tai a ranta tace " Shi wannan haka ake zancen? Neman fada? Ita ta saba duk wanda yazo gunta tofa wasa ta zaiyi tayi itakuma tana dauke kai.
Jitai yace " kina tunanin wani irin zance nakeyi haka ko?"
Kallansa tai batace komai ba, yace " baki sanni ba, nima bansanki ba yauce ranar da muka fara ganin juna, bazan yabeki akan abinda ba haka ba, ba kuma zan kusheki ba akan abinda ban sani ba, banida tabbas zamu kara haduwa da juna kinga kuwa bazanso in bar tarihin karya ko dadin baki agunki ba."
Kallansa tai ta kasan ido, ba shakka kalamansa sun mata dadi.
Kanta na kasa tace " Amma ai ina gani ya kamata ka nunamin ko na maka alamar so ko aminta da hadin da akai."
Murmushi yadanyi kadan yace " Bana sanki!"
Cikin tsananin tashin hankalin jin wannan kalmar yasa ta d'ago ta kafeshi da ido, iska yadan furzar yace " kina sa ran daga ganinki sai in fara sanki?"
Idanunta tai kasa dasu batace komai ba, yace " Bilkisu!"
Kallansa ta karayi, yace " kina da kyau na tabbata kowa na fada miki haka, kinada mulki wanda ke kanki kinsan haka, sai dai inaso ki sani karkiyi tunanin hakan zai na soki, ba wai dan abinda kike dasu baimin ba sai dai dan ni ban yarda da wadannan sune abinda ya cancanta ba a so, sannan ban yarda da love at first sight ba."
Jiyai tace " sai me ka yarda dashi?"
Murmushi ya mata yace " sirri ne."
Shiru ne ya ratsa na 'yan dakiko.
Jiyai tace "Nagode."
Kallanta yai cikin mamaki yace " name fa?"
Tace " Na gaskiya daka fadamin."
Yace " Ina miki fatan alkairi a rayuwarki, ana tabbata ba lalai mu kara haduwa ba."
Mikewa yai zai tafi, jiyai tace " in kuma na bukaci hakan fa?"
Juyowa yai cikin mamaki ya kalleta bai amsa mata ba.
Wani sansanyar murmushi tamai tace " Ban taba had'uwa da mutumin daya fadamin gaskiya ba sai kai, da fari na fara jin haushi sai dai a hankali na fahimci gaskiya dama d'aci gareta."
Kallanta kawai yake baice mata komai ba.
D'agowa ta kara yi ta sakar mai murmushi tace " Da alama kai zaka gaji masarautar Zariya."
Cikin mamaki ya kalleta sannan yace " me kike nufi?"
Tace "sani ne bakai ba ko kuma bakasan ne na fahimceka? Na tabbata ka san cewa bazan auri wanda bashine zai gaji sarauta ba, sannan tunda mahaifinka ya turoka nan alamace ta kai yakeso ka mulki masarautar sa."
Gabansa ne ya fadi cikin mamaki yace " aurenki haka yake nufi?"
" Da farko ance mana baka gani sai dai daga baya aka kara aikowa akan ka samu sauki."
Idanunsa ne suka dan rage girma ya matso kusa da ita yace " waye ya sanar daku hakan?"
Murmushi tamai tace " na sani sirri ne dan nima ni kadai Mahaifina ya sanar ma hakan, da farko abin yaban haushi dan a gaskiya wannan dalilin ne yasa na tura Munnira ta ganka, sai dai yanzu na fahimci kanada dalilinka nacemin baka gani da alama da bakaso zuwa ba."
Wato da bayan sunyi bincike sunji labarin baya gani, amma mai martaba ya aiko da sakon yana gani.
Mikewa yai daga tsugunnan dayai a gabanta, baice komai ba yai waje ransa a b'ace.
Kenan saboda dalilin nan aka turoshi? Shikuma harda kokarin yi mata sauki dan bin umarni?
Ba shakka ransa ya bace na biyomai ta bayan gida da akai...